ALJANAR FATIMA CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ALJANAR FATIMA CHAPTER A

ALJANAR FATIMA CHAPTER A

- - Post a Comment

 ALJANAR FATIMA CHAPTER A


A Cikin kado anguwar hausawa dake babban birnin tarayya Abuja.anguwa ce mai lunguna gata da tarin bishiyoyin  mangorori hankan ne yasa anguwar take da inuwoyi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe 6 tayi to sai an haska fitila tsabar duhu in dai ba farin wata ba. Anguwa ce  mai tarin jama'a, ko ta ina ka duba mutane ne kowa na uzurinsa. Akwai masu saide-saide da yan shaguna da irin tsofafin nan masu saida kayan makulace na yara.

Wata yarinya ce sanye da doguwar farar riga wacce ta koma baka dan tsabar datti, Yarinyar fara ce kallo daya zakayi mata ka gane hakan saidai dauda ta masheta baka.  Gashin kanta mai tsayo ne amma rashin gyara yasa duk ya fara cicirewa tsabar datti gashi duk ya barbaje mata a fuska sai ta dage shi tukun take iya ganin gabanta.

Duk mai tausayi yaga yarinya to dole tausayinsa ya lunku a kanta. Domin tayi kalar ban tausan.  A hanakali take tafiya har ta isa bakin kofar wani shagon saide-saide.  Bakin kofar shagon taje tayi tsaye ta dan yace gashin da ya lilube mata fuska tana kallan cikin shagon. Shi kuwa mai shagon a lokacin ya dan duka daukar wani abu.  'Da dagowar shi duka hada ido da ita sai ji yayi gabansa yayi mugun faduwa.

Nana take yanayinsa ya canza kalo daya zaka mishi ka gane ya fusata ainun!, "Ke uban me zan baki iyee?, haka jiya ma kika zo kika min tsaye a kofar shago kina wani nuna min ciki da baki, gaki yau kin kuma Dawowo uban me zan miki".

Dayan hannuta ta daga ta dage baki hade da nuna yatsar ta cikin bakin tukun ta sauke shi ta nuna cikin ta kamar dai yanda tayi mishi jiya. Wanda duk me hankali in ya gani zai gane tana nufin yunwa take ji tana bukatar abinci,  Shima kuma kanshi ya fahimci hakan.

"Kaji rainin wayo ah! Lalai wannan baki sanni bane baki san bani da mutun ci ba to wllh yau zan nuna miki, to ni ubanki ne da zaki ringa nuna min kina jin yunwa ko dan kinga jiya korar ki kawai nayi ban taba lafiyar jikin ki ba.  Bari ki gani".
Nan take ya juya ya dauko dorina mai baki biyu wacce take jike dai mai dan tayi zafi yasa ta a mankyada Dama saboda yara ya saye ta. Goge bulalar ya fara yi domin abun man har yanzu akwai maski duk abun nan da yake yi yake yana surutai. Wato baki san na dade banyi zalinci ba ko ni dama zalinci ai rigata ce in banyi shi ba ji nake kamar a zigidir nake".  Juyowa yayi a zatansa tuni taji tsoro ta gudu ganin ya dauko bulala, amma sai yaga sabanin haka ta sake bude baki ta nuna mishi kamar yanda tayi dazun.

Kara fusata yayi da sauri ya bude yar karamar kofar ta kata ko ya fito. Baiyi wata-wata ba ya fara tsula mata bulala harda riketa yana fadin, "Bari in zane ki tukun gobe ma ai sai ki dawo kaji jarababiyar yarinya ni da ba ubanki ba taya zan baki abinci" yana yi ne yana dukanta tun tana kuka a hankali har ta fara ihu! Abunda da ya jawo hankalin mutane makwabtan shagon sa kenan. Sukayo mishi can  aka kwaci yarinyar shi kuwa sai masifa yake.  Wai ta rainashi gobe ma ta dawo.

Wani dan saurayi ne naga ya kama Yarinyar yana lalashita bai ko ji kyamar ta ba kamar yanda sauran mutanan gurin sukayi.  "Yi shiru yi hakuri yarinya kinji. Haba muktar yanzu dama rashin mutuncin naka har ya kai ga haka  ban sani ba?, Ai da na dauka rashin mutuncin ka da masifar bai wuce iya manya ba ashe hada yara". A cewar wanda ya kama yarinyar yana lalashi.

"Eh kamalu da ba ka sani ba kuma da ji kake yi yanzu kuma gashi ka gani da idanunka iyhee! Nayi rashin mutuncin in da yanda za'ayi dani ai sai ayi mugani".
Da jin haka mutanan wajen suka watse suka barsu su biyu a gun domin kowa gudu yake ya wa Muktar magana ya mai rashin kunya, Dama a wajen kamala ne kadai baya raga mishi duk rashin mutuncin shi yana tsoran kamala.

"Kadai kaji kunya wallahi, yanzu wannan karamar yarinyar me tayi maka da ka dake ta?".
Muktar ya wani taso da masifa kamar zai haiye kamal din, " Kai kamala ka bar ganin fa ina daga maka kafa wllh ba tsoranka nake ji ba, ya za'a yi kazo kana min maganganun banza a kan wata yarinya wacce gata nan dai kamar ma yar mahaukaciya domin wannan tafi karfin ace mata ma almajira, kawai tazo kofar shagona tana daga min baki wai yunwa jiya na koreta yauma shine ta dawo shiyasa zan zane ta gobe ma in ta dawo haka sai na zane ta". Yana gama fadar haka bai ko tsaya sauraren kamal ba ya juya ya shiga shagon shi.
Kamal jin saboda ta nema abinci ne ya dake ta dan takaici bai sake cewa komai ba ya kama hannun yarinyar ya nufi gidansa da ita dake ba nisa daga nan. Yana rike da hannuntq tana binshi suka shiga gidan, matarsa Khadija tana shara a tsakar gida tana jin salamar shi ta mike tsaye tana kalanshi tana kuma kalan yarinyar.

"Baby sannu da zuwa wannan fa daga ina". ta fada lokacin da take kokarin kama hannun yarinyar. Kamar rai a bace ya kwashe duk yanda akayi ya gayawa matarsa, khadija nada mutunci sosai nan take taji tausayin yarinyar da sonta a cikin ranta.  Gogewa yarinyar hawaye tayi hade da cewa, "Yi hakuri kinji yan mata share hawayen ya sunanki daga ina kike".  Wannan tagwayen tambayoyin ta jera mata, amma shiru yarinyar batayi magana ba sai ido da take binsu da shi.

Kamal ya maimata tambayar kamar yanda matar tashi tayi amma shiru. Sun tambaye ta ya kai sau biyar amma ko umh! Bata ce ba sai idanu da take binsu da shi. "Baby inaga fa wannan yarinya kurma ce shi yasa ma bataw Muktar magana ba".
"Kwarai nima nayi tunanin haka,  yanzu abunda za'ayi ki taimaka ki mata wanka ki zuba mata abinci taci bari inje in sayo mata wata rigar ji kafarta ko takalmi babu bari in hado da shi".  A cewar kamal domin yasan matarsa ba mai bijirewa umarninsa bane ko  mi ya gindaya mata inda ba na sabawa allah bane tana iyakar kokarinta.

"To baby a dawo lafiya". ta fada lokacin da ta mike shima kuma ya fita Kafin wani dan lokaci tuni khadija tayi wa yarinyar wanka ta wanke mata kai. Tsabar dauda saida ta bata kusan bokiti uku da mai tsantsami ce bazata iya ba domin ko ita tanayi tana dode hanci dan tsabar wari.  Bayan ta gama wankan bata mayar mata da rigar ba wani zaninta ta dauko ta liliba mata tukun ta shigar da ita ta zuba mata abinci. Ita kuma kamar wanda ya shekara baici ba haka ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama cin abincin sai ga kamala ya shigo da sabuwar riga da takalmi mai kyau. Ya kawo ya mikawa khadija yace "ki saka mata ni zan koma shago karki bari ta fita waje".

To khadija ta ambata. Kamala ya kalli Yarinyar mamaki ne ya cika sa ganin irin kyawan da ke gare ta ashe dama tsabar datti ne. Baidai ce komai ba ya juya ya wuce.
Khadija ta shafawa yarinyar mai mai kanshi tukun tasa mata kaya. Ta kuma tatara gashin kanta wuri guda tasa ribbon dinta ta daure mata kan, ta jawo ledar ta bude taga ashe doguwar riga ce mai wando harda dan gyale. Ta saka mata tukun ta mikar da ita tsaye ta tsaya ta kare mata kallo sama da kasa. Wow× Masha allah beautiful baby kenan,   yarinya da shegen kyau kamar aljana.

(Nasmat tace, kaji min mata me ya kawo maganar aljana kuma a nan ko dai so kike ki tunawa king)

Khadija tace "bari in saka miki jan baki da hoda kina so".  Lokacin tama manta da yarinyar bata magana. Bisa mamaki sai taga Yarinyar na girgiza kai alamun eh. Dan dariya taye hade da cewa "dama kina jin  magna ne bakya yi". 

Nan ma girgiza kai tayi alamun eh, Nan fa murna da farin ciki ya cika ta. Ta kuwa fara jero mata tambayoyi kala-kala.

'Acikin tambayoyin ne ta tambayi ina ne gidan su ta nuna bata sani ba ta sake tambaya ina iyayanki nama ta nuna bata sani ba har da hawaye. Khadija ta shiga lalashi tace "daga yau na zama maman ki kin yarda". Girgiza kai tayi alamun eh

Nan take khadija ta rungume ta cikin farin ciki domin allah ya zuba mata san yara kuma har yanzu allah bai bata haihuwa ba sau biyu ko ta sama cikin bari take.

(😭 ayya allah sarki allah ka bawa duk mai irin wannan matsala haihuwa sister na allah ya kawo πŸ‘πŸ½)

Haka dai ranar Khadija ta wuni cikin farin ciki duk ina tayi yarinyar na biye da ita tuni suka yi sabo har da wasanni a tsakanin su.   Da magariba haka kamala ya dawo ya tarar da su khadija ta bashi labarin duk abunda ya faru ta gaya mishi ashe tana ji magana ce bata yi.

Nana shima yayi mata mgana ta gyada kai. Kamala yace "To yanzu bata magana taya zamu san sunanta?".

Khadijah tace "kaji wata matsalar kuma ni nama manta in tambaye ta tun dazun. (Ta juya wajen ta) kin iya rubutu".  Yarinyar ta girgiza kai alamun a'a. Kamala yace "to mu saka mata suna waleeda mana tunda dai can dama muna san sunan".

Khadija tayi murmushin jindadi ta kalle ta tace,"Kin yarda sunanki waleeda?". Da sauri ta girgiza kai alamun eh tana dariya nan fararen hakoranta suka bayyana.

Bayyan isha'i sunci abinci sun suka danyi kallo kadan wajen karfe goma suka tashi ita kam yarinyar tuni tayi barci ma. Khadija ta dauke ta suka nufi daki suka kwanta a tskiya suka sakata khadija saida ta kare wa yarinyar kallo da kyau tayi murmushi tayi mata kiss haka shima kamala san yarinyar ya shiga zuciyar su lokaci guda.

Khadija saida ta dora wa yarinyar hannu ta dan rungume ta tukun ta fara barci.

Uhmmmmm wannan kenan😊
Misali  karfe 11:00pm   anguwar nan shiru kake ji ba motsin mutane sai kukan tsuntsaye na saman mangwaro. Badan fitulun sola da suka haske anguwar ba da duk jarumtar ka bazaka iya bi ka wuce ta cikin wannan layin ba.

Shaguna duk a kulle sai shago daya wato na Muktar shi kadai ne a bude inda sabo an saba kowa ya watse a barshi shi kadai a gurin domin sai yayi lissafi tukun yake tashi.  Zaune yake yana kirga cinikin da yayi yana washe baki domin yau anyi ciniki sosai a shago. Ta wutsiyar ido ya hangi kamar wani bakin abu na tafiya a kan hanya zai gifta ta kofar shagon shi.  Da sauri ya dago kai dan ganin miye amma wayam.

Komawa yayi yaci gaba da lissafin sa ba'afi seconds 30  ba ya kuma ganin wani jan abun kamar mutu kuma ya nufo shagon sa.  Da sauri ya sake dago kai a karo na biyu  nan ma baiga komai ba. Mamaki ne ya cika shi a fili yace "Kai miye haka kuma?".  Ajiye kudin yayi ya fita waje a sauri ya wa-waiga ko ina har saman bishiyoyin wajan amma shiru baiga komai ba.  Hakan tasa yace a zuciya "Ba komai kawai tsorata kaina ne nayi ashe".   Juyowar da yayi da niyar ya koma shago yayi tozali da abunda yasa ya kwada ihu! Hade da faduwa dan razana.

Ba komai idanunsa suka gani ba sai wannan yarinyar  tsaye a kan kujerar da yake zaune.  Fararen kaya ne a jikinta amma gaba daya sun baci da jini wuyanta a yanke jini na zuba har tsartuwa yake yi. Idanunta kuwa sunyi jawur jini na bulbula daga ciki haka hakuranta sun kara zarowa sun fito waje jini cike da bakin.  Kuma a hakan murmushi take wani irin sauti na fita kadan-kadan.............

😰 Kodai aljana ya zane πŸ™†πŸ»??

Muje  zuwa

Karkuyi zatan labarin Aljanar fatima ya canza ne πŸ˜€faAutan writers  KING BOY ISAH ✍🏻

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Part  3-4

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

Happy birthday
   ​UⓂⓂEIY ZEE​
         I'm happy for you 1+14 year. Lolz

Hmm gaba dayan shi pagen naku ne yanda naga kuna nuna kauna a kan littafin tun kafin in fara har dauka nayi abun yayi yawa ashe abun yafi haka. Bansan ya zan misalta yanda kuke san littafin autan nan naku ba.  Amma dai ga kyautar pagen a gare ku. Duk da nasan ban isa in biya ku da shi ba.
​UⓂⓂEIY ZEE​
         PHATEEMA
         SHAZEE
            AUNTY ASY KHALIL
           HAWWER.

ALLAH YA BAR MUN KU YASA KUFI HAKA. ALLAH YA KARA MUKU BAIWA DA BASIRA.

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
Us whatsapp's number.
08096831009
----

Muktar da gaba daya ya tsorace ya gigice har ya fadi. A hankali y dago kai dan kara tabbatar da abunda ya gani shin ko gaskiya ne ko kuwa idanunsa ne kawai suka nuna mishi hakan.  Abun mamaki a dagowar da yayi wayam yaga gurin ba komai. Yana nan dai a tsaye yana tunane-tunane wannan al'amari domin yasha kai karfe sha biyu amma tun da yake yau kusan shekara daya da bude shagon amma ba'a taba tsorata shi ba sai yau "shin ko dai da gaske gamo nayi" ya tambaya kansa.

Karar da ta doki dodan kunnan sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake.  Daga bangaren hannunsa na dama karar Kofatu kamar duban dawaki  ne suka nufo shi yaji.  Nan da nan ya juya a firgice yana neman fadawa shago.  Wasu bakaken hallitu ne wanda masu jikin doki dukan su bakake ne amma ba kai a jikinsu sune suka nufo shi a sukwane.

Koda idanunsa sukayi tozali da wannan mugun abu, hankalinsa ne ya dugunzuma dan tsabar tsorata a million ya fada shago bai ko tsaya kulle shagon ba haka kuma baisan lokacin da ya tsallake dogon bincin da ke raba masu sayayya da cikin shagon ba. A bayan bencin ya sama wani dan lungu ya labe yana maida nunfashi day-day. Duk jikinsa karkarwa yake idanunsa nan-da-nan suka saki ruwa.  Kuka ya farayi shabe-shabe ya fara magana a hankali cikin muryar sa dake rawa yana fadin "Wannan wane irin bala'i ne ni kam yau na shiga uku..."  Surutai ya tayi shi kadai sai da ya dau kusan mintuna 20 a cikin shago yayi lumi ko motsin kirki baya yi kuma karar dawakin nan har yanzu a kwaita.

Can dai yaga wannan bata yi ga zafin dake adabarsa sai gumi yake, hakan tasa shi fitowa daga inda ya labe a hankali ya dan leka kofar shagonsa wayan baiga komai ba sai karar da yake ji. Ya dade nan a tsaye ko zaiji karar ya ragu amma ba alamar raguwar. Ga zafin ya fara cin karfinsa ya fara magana cikin murya irin ta mai kuka ko gunguni. "Haba wllh fita zanyi bazan tsaya zafi ya kashe ni a banza ba. Wallahi fati zanyi ko me zai faru ya faru. Juyawa yayi ya dauki makulan shagon bai ko tsaya debe kudinsa ba. Ya fara yunkurin tsallakowa  bayan ya tsallako ne ya bi a hankali kamar munahiki ya leko shagon ta bangaren da yake jin karar.

Leka warsa keda wuya sai yaji kamar an dauke wuta dif! Karar ta dauke. Hakan ya bashi dama da karfin gwiwa na fitowa da sauri ya garkame kofar shagon yanufi hanyar gida da gudu-gudu sauri-sauri takun da yayi bai wuce 15 ba sai gani yayi wutacen nan gaba daya sun dauke dif!. Al'amarin da tasa shi yayi tsaye cik kenan. Kamar walkiya haka yaga wani farin abu ya gifta ta gaban shi duk da duhun amma yaga abun kamar mutun lokacin tsoro ya kara rufe shi, Suman tsaye yayi a gurin tsabar tsorata da yayi.

Sanda aka shafe kusan mintuna 10 yana wajen a tsaye ya rufe idanu alamun haske ya gani hakan yasa ya bude idanunsa ai kuwa sai yaga wutar ta dawo. Nan fa ya ranci ta kare ya zura a guje kamar wanda zai tashi sama.   Yana wuce wani mangwaro yajiyo dariya a saman shi, a cikin gudun ya wai-wayo abunda ya gani ne yasa shi har saida yayi tuntube karfin gudun yasa har sai da ya wuntsila yayi kungun bala.  Yarinyar nan ya gani kamar dazun duj jini na fita a jikinta kuma itace ta dage kai sama tana gagaba dariya marar dadin ji.

Bai kula da ko yaji ciwo ko baiji ba. Ya tashi ya ruga a guje yana ihu.  Bai daina ganin yarinyar na fito mishi a sifofi na ban tsoro ba har ya kawo gida. Da shigar sa gida ko tsayawa sa kubobin kawai banka kofar yayi. Dake yasan kyauran mai jamlock ne.

Da gudu ya fada daki UⓂⓂEIY ZEEY
(matarsa) na kwance a kan gado tana barci. Yabi ta kanta ya tsallaka dayan gefan tuni ya ja (blanket) bargo ya rufa duk zafin da ake fama da shi. Nauyin sa ne ya tayar da  Ummiey daga barci waigawa tayi dan ganin waye sai ganin shi tayi ya kudun-dune cikin bargo yana sauke nunfashi day-day tayi mamaki mutumin da baya san zafi ko kadan kullum in yazo sai ya mayar da fanka ta bangaransa amma yau gashi ya shiga bargo lalai ba lafiya ba.

"Mai gida-Mai gida baban HAWWER-baban HAWWER lafiya kuwa?"  Haka ta dinga jero mishi tagwayen sunaye hade da dadabarsa tana tambayarsa. Karkarwa taga duk jikinsa ya hau yi.  Domin shi kam abunda yake ji yayin da yake ji bashi take fada ba kuma ba muryarta yake ji ba.  Domin wata murya yake ji mai abun tsoro tana fadin "Mu...ktar...m..u..ktra" a slow muryar ke tafiya.

Ummiey ganin karkarwar da yake tayi yawa ta dan daga murya "Baban Hawwer lafiya kuwa".  Yayin da shi kuma yaji an daga mishi tsawa da wata muryar mai razanarwa ance, "Kai muktar magana fa nake maka".   Firgigit ya tashi zaune. Maimakon yaga matarshi ummiey. Yariyar nan ya gani kamar yanda take dazun dan yanzu ma tafi ban tsoro domin dogon gashin kanta mai-makon ya zuba a bayanta sai mikewa yayi tsaye cir! Yayi wani irin fadi A sama. ('Kai duk wanda yayi arba da wannan yarinya ala dole hantar cikinsa ta kada dan tsoro, In ma bai sume ba')

Muktar kuka ya farayi yana ja da baya-baya yana bata hakuri a haka har ya surmuyo kasa daga kan gado bai ko jira kuma ba yaci gaba da ja bayan.  Ummiey na gannin mai gidan nata ya fado daga kan gado yana kuma kallonta yana kuka ta tabbatar da ba'a hayyacinsa yake ba. Hakan yasa ta matso daga kan gadon ta sakko a hankali take binshi tana tambaya. "Baban hawwer wai me ke damunka ne?, ka min magana mana".

Yayin da shi kuwa yarinyar yake gani tana tunkaro shi hakan yasa ya kara sauri wajen jan gindin da yake yana yin baya yana fadin.  "Na shiga uku yau naga ta kaina, dan allah kiyi hakuri karki kashe ni shin dan naki taimaka miki shikenan nayi laifin da za'a azftar dani har haka. *DAGA TAIMAKO*   dan allah karki kashe ni".

Ummiey da jin wannan kalamai na fita a bakin mijin nata sai tayi tsaye cik! Tana kallon shi cike da mamaki tana cewa "Lalai baban hawwer yau ba lafiya kake ba. Yanzu ni din kake cewa zan kashe ka ni?".
Yayin da shi kuma yake jin wani abun daban sabanin abunda take fada.  Domin shi yarinyar yaga ta tsaya tana gagaba dariya kafin ta fada da murya mai fitowa bibiyu. "Kai muktar ka sani ka debo ruwan dafa kanka, a cikin kifayen da kake kamowa yau ka kamo ajali ka. Nan take yaga wata wulshe-shiyar wuka ta bayyana a hannun yarinyar.

Ihu! Ya fara kurmawa yana fadin "Wallahi na tuba baran kara ba, dan allah ki yafe min duk abunda kike so zan baki. Duk lokacin da kikaji yunwa ki dinga zuwa ina baki abinci ko da kuwa zakiyi ci Goma ne a rana amma dan allah ki taimaka kiyi min rai karki kashe ni".  Ummiey taga abun da mijin nata yake ya fara yawa harda ihu nan ta fara tunanin ko ta leka ta kirawo makwabcin su ne. Kuma sai dai tace bari ta karasa gare shi.  Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi................

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 5-6

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

THIS PAGE DEDICATED TO YOU.

NASMAT

ASMART

MARYAM AMIN

SIS HAFSAT

MMN AFNANN

KHADIJA BABY

KHADIJA πŸ€”

KHAIRAT πŸ’ƒπŸ»

MMN SADIQ

KAMALA MINNAH

Love is my everything. It’s everywhere. It’s in the messages you send me, it’s in the words you say to me and it’s in your eyes when you look at me. Love is in my heart and in my thoughts. Love is you and me. πŸ‘†πŸ½ I love them ☺

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

         *Karshen pagen baya...*
Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi»   Ummiey gaba daya ta firgice kamar ta kurma ihu! Itama.  Ganin mai gidan nan nata a kass sumame. A rude tayi waje tana zubda hawaye. Da sauri taje ta bude randar kasar ta wacce ruwan ciki yayi sanyi sosai kamar ansa kankara tasa moda ta kwalfo tayi cikin daki da gudu.

Tana zuwa batayi Wata-Wata ba ta kwaraya mishi gaba dayan ruwan da ta debo. Firgi-git ya mike zaune yana nishi yana yan waige-waige kamar wanda yake neman wani abu  dayan hannun sa kuma goge fuskarsa yake domin ruwanda Ummiey ta kwaraya mishi. Ganin baiga abun da yake zatan gani ba yayi saurin mikewa ya nufi kofar daki a guje ya rufe ya sakala kubobi biyu yana fadin.

"Ummiey wllh kashe ni zatayi taimaka ki kama a jawo wardrobe  din nan a kara rufe dakin".  Ummiey kam tsaye tayi ta saki baki tana kallansa yanda duk yabi ya rikice yake abu kamar mahaukaci.  "Baban hawwer wai  lafiyar ka kalau kuwa? Ya kake wasu irin abubuwa ne haka wanda ban taba ganin kayi kwatan-kwacin kalar su ba?".

Tsawa ya daka mata kamar yanda ya saba dama baya jiya mata dadi, ba dan Ummiey mai hakuri ce ba da tuni ta bar masa gidansa to amma sai akaci sa'a irin matan nan ne masu hakuri tayo gadon gidansu dake babban ta shine limamin masalacin juma'ar anguwar kuma baban malammi ne masani.  Itama kuma haka tayi sauka har biyu.
Zabura tayi tsawar da ya daka mata.  "Nace miki kizo ki kama wannan wardrobe din mu kai mu rufe kofar aljana ce in ta sake shigowa kashe ni zatayi".

Ummiey sai yanzu ta gane mijin nata gamo yayi. "Baban hawwer wacce aljana kuma"?.  "Oh! My god ya fada. Tunda bazaki kama min ba baza ki taimakawa mijinki ba so kike ta halaka ni to bari in kai ni ai zan iya". Kiki-kiki ya jawo wardrobe har kofar dakin ya danne kofar. Danne wa keda wuya yaji an fara girgiza kofar dakin da gudu ya haye gado ya lulube. Ummiey ce tazo kanshi ta fara tofa mishi addu'o'i har allah ya taimaka barci yayi gaba da shi.

Tunda asuba da ya tashi yaci gaba da zabur-zaburansa. Ummie na tofa mishi addu'a amma taga abun yafi karfita hakan yasa ta dauki waya ta kira babanta tana kuka ta gaya mishi duk abunda ya faru. Yace gashi nan zuwa. Mukhtar ba abunda yake  sai surutai duk bayan yan mintuna kuma sai ya dinga tsorata yana boyewa yana fadar "gata nan gata nan".!   Ummiey ita kanta ta shiga rudani.

Ba'afi mintuna 20 ba malam hamza ya karaso gidan koda Mukhtar ya jiyo sallamarsa da gudu ya fito ya makal-kale malam yana surutai saida malam yayi da gaske tukun ya raba jiknsa da na Mukhtar lokacin ya fara tofa mishi adduo'i tukun ya samu haukan da yake ya dan lafa malam yasa shi ya zauna a tabarma da ummie ta shimfida. Bayan sun zauna ne malam ya fara karanta ayyatul kursiyyu tare da sauran ayoyi masu karfi.  Ba'a dade da fara karatun ba sai ganin wannan yarinyar ta bayyana cikin kayan da Khadija ta saka mata.  A gaban malam ta zauna hade da musu sallama. Muktar har zai ruga malam ya zaunar da shi. Hatta ummie ta tsorata domin ganin abun tayi kamar a mafarki.

Malam ya kalle ta yace "baiwar allah me wannan mutumin ya miki an bani labarin irin azabtar da shi da kika yi jiya". Muryar ta ba dadin ji tace, "ka tambaye shi malam shi ai yasan abunda yayi".  Malam baiyi gardama ba ya juya ga muktar ya tambaye shi me ya mata. "A tsorace yac malam wallahi ba abunda nayi mata shagona taje tana nuna alamun yunwa take ji a rana ta farko na kore ta a rana ta biyu kuma ganin ta takura min na dake ta".

"Karya kake muna fiki azzalumi macuci, Ko daya ba dan wannan ne na shiga rayuwarka ba. Wannan ma nayi ne dan in tabbatar da rashin mutuncin ka da mutane ke fada sai naji kai da bakin ka ma fada kake. Malam muktar Shin har ka manta abunda kayi shekara daya da rabi baya da suka wuce?.  Yarinyar ta fada cikin tsiwa tana hararen shi. Nan fa kwakwalwarshi ta shiga juya mai yana kokarin tuno wani abu.  Ganin ya shiga dogon tunani ta sake daga mishi wani tsawan wanda ita kanta ummie ta firgita kamar ta fada daki taji.  "Kaaaai!  Mugu wato har ka manta yaron da ka kashe ka rabasu da dukiyarsu ka raba yaya da kanwa. a fadama ko?".   Dummm!  Gaban muktar ya fadi jin ta tado zancen da a tunaninsa ba wanda ya san shi daga allah sai shi sai kuma wannan yarinyar.  (What!) "Yaron da ya kashe?".  Ummiey da malam ne suka fadi hakan a tare.

Bugun kirjinsa ne ya tsananta nan take jikinsa ya fara bari. Motsowa ya farayi gaban Yarinyar yana fadar "Dama ke aljana ce ban sani ba. Don allah ki rufa min asiri karki tona wannan sirrin duk abunda kike so  zanyi amma ki taimake ni karki tona wannan sirrin...."  Tsawar da ta daka mishi ce ta tsayar da shi nan take ta wani bata rai fuska ba wal-wala. "Bani bace domin dani ce da bazaka kwana ba a ranar. Ka basu labarin abunda ka aikata wa wannan yarinyar da kanka, in kuwa ba haka ba yanzu ka gayawa yan garin ku". Ta karashe maganar cikin daga murya. Nan take tsoran Mukhtar ya karu. "To-to bari in fada amma dan allah karki min komai".

Malam da diyarsa ba abunda suke sai kallo da sauraren ikon allah. Ummiey tunani take shin wannan wane BOYAYYEN AL'AMARI ne? Wanda bata sani ba game da mijinta. Ita dai bayan mugun halin sa da kowa yasan da shi bata kuma san da wani ba. Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari..............................

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 7-8

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU.

_*QUEEN HAUWANCY AUTAR MARUBUTA*_ πŸ€“

_I love you to the moon and back, and you know that. I will never let you down, even if you make me mad, you can always ask me advice, I will never leave you._

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» ```Duk illahirin yan writers na zamani suna ji dake yar auta kaman yanda nake ji dake nima ☺  kina sakamu nishadi Da  Littafin ki πŸ’žπŸ’¦πŸ’žILLAR BASHIπŸ’¦πŸ’žπŸ’¦ 🀣🀣🀣 Ni ban taba jin irin wannan gidan sunan ba hatta ruwan da za'a sha ma bashi mai ruwan ya zuba 🀣 Dan akuya za'a yanka shima bashi 🀣 Abincin gidan bashi🀣 Kayan miya bashi🀣 Ba beauty bama koni bazan tsaya ba 🀷🏻‍♂πŸ™‡πŸ»

Kina wuta ina binki da fetur yar kanwata 😜Allah dai ya kara basira```

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

         *KARSHEN PAGEN BAYA*
Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari
» Ya fara da cewa Kimanin Shekara daya da rabi baya da suka wuce, lokacin ba'a fi watani uku da yin aure na da Ummiey ba. Lokaci ne da na shiga mawuyacin hali talauci ya min dankar kazar uwar ba'u. Ba komai ne ya kara zafin talaucin ba sai matsalar da muka samu da ogan gare jin mu na bar aiki.

Nayi buga-buga na shiga na fita domin in sama abun yi amma abun yaci tura, duk inda na nema aiki bana samun aiki. Ranar wata laraba da naga abinci sakawa a baki ma yana shirin gagarar mu, Hakan tasa na shirya na dauki gatari na nufi jeji domin nayo itace na sayar. Hanya nabi ina tafe ina tunanin yanda rayuwa duniya tamin tutsun  jaki lokaci guda na surmiyo kasa.
Rashin sa'a na ya tsananta ni kam bansa yama zanyi ba domin ko faskaran ban iya ba.
Naje ratsa wata fadama naji kamar maganar mutane a cikin wani dan lungu  ina lekawa naga wasu yara ne guda biyu na dan tsorata da ganinsu kamar yanda suma suka frigita yarinyar ta kankame na mijin wanda ya kasance yayanta ne. Bayan yan tambayoyi da nayi musu suka bani amsa nan na dan saki jiki da su. Nace su fito muka sama waje muka zauna na tambaye su me sukeyi a nan. Namijin ne ya kalli kanwarsa hade da cewa "Rasheda in fada mishi".  maganar da Yarinya tayi ya tabbatar min da yarinya ce mai wayo da hankali.  "Eh yaya na ganshi da manyan kaya ina ganin kamar mutumin kirki ne ba irin su kawu mansur ba".  Yaron yace "To amma amana".  Na kallesa nace mishi "yaro ka yarda dani bazan cuce ku ba. Saidai ma in taimaka muku".
Kwarai a lokacin da tausayin su a raina.

Yaron ya shiga bani labari kamar haka:  Yace mahaifinsa mai kudi ne duk anguwar babu kamarsa a dukiya. Yana da kani daya yaya daya. kawu abba da kuma kawu Mansur kawo abba shine karame wato kanin babanmu saurayi ne kuma shi mutum ne mai tausayi sabanin kawu mansur wato yayan su shida baban mu.  Kawu abba yana san mu sosai mun shaku da shi sosai dake a gidan mu yake da zama shima yana da dakinsa daban. Hatta makaranta shi yake kai mu.
Ranar wata alhamishi ce mun dawo daga school muka tarar da abban mu da kuma kawu mansur suna rikici cacar baki abun kamar a buga. bamu san me ya hada su ba, koda ganin mu sai kawu mansur ya nufo hanyar fita wajen har ya kusan zuwa kofa ya juyo yayi bakaken maganganu hade da barazana wa baban mu, sannan ya fice  baban mu yaji haushi sosai  domin a lokacin daki ya shiga ya rufo.  Kawu abba kuwa yaje yana tambayar maman mu ta fada mishi abunda ya faru amma taki gaya sai dai itama zubda hawaye take.

Da da dare.
Har wajen karfe  sha daya baban mu baiyi barci ba domin kuwa yasan halin dan uwan nasa zai iya turo mishi barayi su kwashe kudin kamar yanda ya fada.  Kudin wasu filayan sa ne guda biyu ya sayar million biyu da rabi shine kawu mansur yazo ya tsare shi wai sai ya bashi million daya yaja jari. Shi kuwa baban mu yace yayi hakuri ba yanzu ba yanzu akwai abunda zaiyi da kudin. Shine abunda ya faru har kawu mansur yaji haushi ya hau fada harda barazana.

Karfe 12:30am da yaji shiru-shiru ya kwanta a tunaninsa dama barazana ce kawai.  Bai dade da kwanciya bq yaji hayaniya a kofar gida kuma kamar muryan mai gadi can kuma sai yaji ya kwala wani ihu! Wanda ya shaida mishi ba lafiya ba. Cikin sauri ya dauki jakar kudin ya nufi dakin kawu abba wanda muma a can muke a kwance. Bayan ya tayar da mu ya bawa kawu abba jakar kudin yace mu gudu ta kofar baya ga barayi nan sun zo wai shi zai tsaya in suka zo yace kudin basa a tare da shi.

Kawu abba yayi juyin duniyar nan a kan baban mu ya taso ummanmu mu gudu tare amma yaki. Jin ana bubuga kofar palo ana neman ballata a shigo yasa ya ja hannun kawu abba har bakin kofar baya ya bude muna muka shiga nan fa muka bude yar kofar muka hau gudu. Bamuyi nisa ba mukayi yo wani ihu wanda muka tabbata na baban mu ne. kawu abba ya mika min jakar yace mu shiga wani dan lungun mu buya bari yaje ya gano.  Haka kuwa akayi muka shiga wani dan guri mai duhu muka boye shi kuma ya koma,  ko da shigarsa palo sai ya tarar an kashe baban mu da maman mu 'yan daban suna ganinshi sukayi chaf da shi suna cewa ga wanda aka bawa ajiyar kudin.

Baban cikin su wani kato ne baki mumuna fuskarsa kadai abar tsoro ce.  Shine ya tambayi kawu abba cikin tsawo ya fada mishi ina kudi amma yaki.  Nan fa suka hau bugo naushin sa da mangarar sa. Hada masu  yankarsa da dai yaga zasu kashe shi sai ya tsaida su yace zai fada.  Nan take ya shaida musu kudin na wajen mu kuma ya nuna musu hanyar da muka bi.  Koda gama nuna musu sai ogan barayin nan yasa hannu biyu ya murde wa kawu abba kai nan ya fadi matacce, su kuwa suka biyo hanya neman mu.
Tun daga nesa na hange su sun nufo hanyar da torch a hannunsu suna ha haskawa da dai naga in suka iso gare mu ba shakka sai sun gan mu. Nan take na kama hannun kanwata na dauki jakar muka ruga a guje. Har mun danyi nisa tukun suka hango mu.  Suka kuwa rufa mana baya,  tsabar gudu ban sani ba ta tsakiyar wasu masifafun karnuka na anguwar mu nabi. Ai kuwa suka hayayako har sun nufo mu kuma suka juya sakamkon jin gudun barayin nan. Nan muka barsu suna fama da karnuka inda mu kuma muka tsero fada mar nan yau kwana biyar kenan da faruwar haka in mukaji yunwa sai in dauki kudi in shiga gari in sayo mana abinci.
Wata doguwar ajiyar zuciya nayi da jin labarin yaron nan. Nace "masa yanzu ina kudin?".   "Zan dauko maka ne kawai domin na yarda da kai ina ganin tausayi a idan ka kamar bazaka cuce mu ba".   A cewar yaron, kallonsa nayi nace "gaskiya ka fada yaro ni ba kamar kawun ku mansur bane ku dauke ni kamar kawun ku abba".    Nan take yaron ya tashi yaje ya daga wasu ciyayi ya fido katuwar jakar ya kawo gabana ya ajiye.  Kwata-kwata  yarinyar bazata haura shekara 8 ba shi kuwa babban namijin  zaikai shekara 13 ko sama da haka.

Koda ya kawo jakar gabana ya bude naga makudan kudin dake ciki kudin da ban taba ganin masu yawansu ba a duk tsawan rayuwata.  Nan take naji zuciyata ta canza daga tausayi ya zuwa rashinsa zuciyoyi suka fara aikin bani shawar wari wasu na cewa in kashe yaran nan in mallaki kudaden wata zuciyar kuwa na cewa in dauke su in kaisu gidana.  Daga karshe dai na aminta da shawara ta farko wato in kashe sun nan kuma na fara tunanin hanyar da zan bi dan kashe su. Sai kuma na tuna a kusa da ruwa fa muke, banyi wata-wata ba nasa kotar gatari na na bigi kan yaron domin nasan shine zaifi bani matsala nan take ya fadi kasa matacce, da ganin haka sai yarinyar ta fara ihu! Ni kuwa ganin zata tona min asiri na shake wuyanta har ta langabe gaba dayansu na kwashe su na zuba a wani ruwa dake wucewa ta tsakiyar  fadama. Ruwan yaja su ya tafi da su, ni kuwa na dauko kudin na dawo gida nayi karyar cewa gonar mu na sayar mutane kuwa ciki harda matata da babanta gashi suka aminta sukayi farin ciki.  Ba'a dade ba na bude shago na kama sana'a dan gudun kar kudin su kare. Ko da ganin na sama wannan kudi sai na shiga sabuwar rayuwa wato ta rashin mutunci bana ragawa kowa kuma bana san kowa ya raga min watta matata taga canji sosai a tare dani, ko ta bangaren addini na samu tawaya domin ko makaranta daina zuwa nayi wannan shine abunda ya faru inji Mukhtar.

"Innalilahi wa'inailaihir raji'un". Wannan kalmar ce take fita a bakin Ummiey da kuma mahaifinta. Nan da nan ummiy ta fara kuka tana fadin "Mukhtar haka kake dama ashe zaka iya kashe mutum ashe ba iyakar rashin mutun cin kawai kake da shi ba harda rashin imani?".  Haka ta jero mishi wadan nan tagwayen tambayoyin wanda shi kanshi baisan wace kalar amsa zai bata ba sai kawai hawaye dake fita a idanunsa da gani kasan yayi nadama. Ummiey zata daga baki tayi magana abbanta ya dakatar da ita. Lokacin aljanar tace ina zuwa.

Bat! Ta bace lokaci daya kuma sai gata ta dawo ita da wata yarinya wacce da gani a galabaice take tana cikin kunci da tsadar rayuwa kaysn jikinta kadai zasu fada maka hakan.  Koda yarinya da aka kawo mai suna maryam taga Muktar sai ta fashe da kuka ta tashi ta ruga a guje, har ta kusa kai bakin kofa aljanar nan ta mika hannunta wanda a nan take ya kara tsawo ya kamo maryam dake shirin guduwa.  Koda ji an sakalota sai ta fara kokarin kwacewa tana fadar "Shine ya kashe yaya sadiq dan allah karku bari ya kashe ni, macuci ne".

Aljanar tace kwantar da hankalinki kawata ba abunda zai miki tsaya baya na. Mukhtar yayi matukar girgiza da ganin maryam wanda shi a tunaninsa saida ya kasheta tukun ya Jefata ruwa. "Wannan itace yarinyar da Mukhtar ya kashe yayan ta kuma yayi yunkurin kashe ta itama amma allah baiyi ba. Ta kubuta da rayuwarta daga mutuwa wanda ta fada wata rayuwar kuma wacce gwarama mutuwar da ita.  Wannan yarinyar da kake gani fadamar nan ta koma mata gida duk sanyi duk zafi a nan take da safe take shigowa gari ta nemi abincin da zataci da dadare kuma ta koma fadama.  Kwana uku baya nazo wucewa na ganta ana mata tamkar yanda kamin wato taje neman taimako ya bata abinda zataci ya kore ta. Ta koma gefe zauna tana kuka saboda tsabar yunwar da take ji dan duk ranar bata sa komai a bakinta ba. Koda naga haka sai na rikida zuwa tsohuwa na kai mata abinci bayan taci ne nake tambayarta ina iyayenta nan ne ta bani labarin duk abunda ya faru. Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya....………………………

Aikin ki na kyau aljanar fatima.

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 9-10

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

_Wannan pagen duk girmansa na masoya king ne a duk inda kuke._

πŸ’ƒπŸ» *Kowa ni yake jira to gani na iso, Samari yan mata na nesa ku marmatso. Domin kar ayi babu ku haka sam! Sam! Bani so.  Wannan pagen ku ne karku bari ya wuce wanda aka baya nan bai more kallo ba* πŸ’ƒπŸ»πŸ˜œ

😍 wayyo my fans you will kille me with you love. Ina sanku ina alfahari daku  *ANA TARE* supports 😘🀝

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

         *KARSHEN PAGEN BAYA*
Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya.»   Mukhtar ko dai ka mayarwa da yarinyar nan dokiyar ta ta hanyar bata duk wani abu da ka mallaka ta sanadiyar dukiyar su, ko kuwa ka zame mata ahali kamar yanda ka rabata da yayanta a baya, Dole ka bata kulawa kamar wacce zaka bawa diyarka ko kuma ma tafi haka. Domin da bazarta kake rawa.

Malam ya kalli aljanar yace "lalai wannan hukunci yayi duk mai adalci haka zai yi, saboda haka ni na aminta Mukhtar sai ka zaba daya kodai ka tatara duk abunda ka mallaka hatta gidan nan dan da a gidan haya kake ka mayar mata ko kuwa ka rikr ta zabi ya rage ga mai shiga rijiya ko ya shiga ta kai ko ya shiga ta kafa. Mukhtar yace na aminta da zabi na biyun zan riketa amana isha'allah domin ni yanzu NAYI NADAMA sannan zan ci gaba da rokon allah ya yafe min laifukan da nayi, Kuma na gode wa wannan aljana da ta tsamo ni daga cikin halaka. Maryam zo mana daga yau kin zama 'yata".  Ya mika mata hannu da farko taki amincewa saida aljanar tasaka baki tukun.

Ummiey farin ciki tuni ya mamaye ta jin ta sama 'ya a bagas! Ta sama mai maye mata gurbin yarta hawwer da ta mutu.  Aljanar ce ta wani tashi saman iska gaba daya iskan wajen ya hau zagaya ta ita kuwa ta fara wata kalar shu'umar dariya marar dadin saurare, Magana ta fara yi muryar na fitowa uku-uku  bazaka iya banbance namiji ne ke maganar ba ko mace ko kuwa yarinya.  "Nice nan aljana SUFURATU marainiyar aljana, Sai na cika burina na ganin ba maraya da zai kasance a cikin kunci. Aikin ma yanzu na fara. Sannan Mukhtar ina gargadin ka a kan maryam kuma ka zama mai adalci domin zan dinga bibiyar rayuwar ku".

Sama tayi kamar wacce ake ja tana tafe tana gagaba dariya, su kuwa da gaba daya in aka fitar da malam ba wanda bai tsorata ba, domin ummiey har dan fitsari ne ya fara kubice mata.   Tun suna ganinta har ta bace cikin gajimare. Malam ya kara yiwa Mukhtar nasiha sannan ya bashi addu'o'i wanda zai tuba ga allah ya kara da cewa ya yawaita sadaka, tukun ya musu bankwana ya koma. Su Mukhtar sunga abun mamaki yau kam duk cikin su ba wanda tsoro ya sake shi, nan fa aka shiga tarairaya da tattalin maryam dan gani suke kamar itace ma aljanar.

Acan gidan kamala kuwa da asuba da suka farka sama ko kasa suka nema yarinya suka rasa sun shiga rudu da tashin hankali don har ga Allah yarinyar ta shiga ransu fiye  da zato, a cikin su ba wanda  baiyi mafarkinta ba. Khadija ta zauna tayi zugum ba abunda take sai faman kuka tana tuna yarinyar nan da irin shakuwar da ta shiga tsakanin su tun a jiya.  Yau komi bata iya ci ba har wajen karfe 9:00 ta zauna ne kawai ta zurawa kofa ido a zatanta zataga ta shigo. Kamal da yaga abun yayi yawa yayi lalashin amma kamar kara haukatata ne yake. "Khadija tunda kinki hakura tashi muje nemanta".  Firgigit ta tashi da gudu ta shiga ta dauko hijab. Sun taho sai sauri take tana leke-leke wani wajen ma har gidaje take tatan bayawa. Amma har wajen 11 babu labari. Duk sun gaji sunyi tikilis.  Sufuratu tazo wucewa ta hange su a karkashin wata inuwar mangwaro da sauri ta sauko kasa tazo daidai inda suke, ita har tama manta da su, "Allah sarki da gani nemana kuke na gode da halacin da kuka min bazan taba mantawa da ku ba. Badan aikin dake gaban Sufuratu nada yawa ba da ba makawa DAKE ZAN ZAUNA".duk abunda take fada baji ba suke kuma basa ganinnta.  Kwasar su tayi ciki  abun da baifi seconds 5 ba ta kaisu gida. Mamaki iya mamaki sunyi shi ya akayi hakan ta faru mu da muke tsaye a gindin bishiya kuma gamu a gida. Tambayar dake dauke a bakin ko wannan su kenan.

"Na tafi sai mun sake haduwa" gaba daya sunji an fadi wannan saidai basu san taka mai-mai ta inda muryan ta fito ba. Nan fa suka shiga dube-dube.  Aljana Sufuratu kenan yarinya ce a cikin aljanun ma domin da kadan zata haura shekara 150 musulmar aljanace labarin ta nada dan tsayi da abunda yasa ta fara taimakon marayu. Kasan cewar itama yarinya ce yasa tafi shiga rayuwar yara marayu, dan a ganinta sunfi ban tausayi. Indai taga yarinya cikin wahala saita bibiya rayuwarta ta kuma san labarinta. A yanzu haka ta bar garin abuja ta nufi bauchi.

Inda ta sauka a G.R.A anguwar masu kudi ce, kowa harkar gabansa yake yi tankama-tankaman gidaje ne tsabar rana da akeyi yasa kowa yana cikin gidansa. A farkon anguwar Safuratu tayi gamo da abunda ya bata mamaki wata yar digil gilar yarinya ce karama wace in tayi gudu takai 10 years ko 9 da rabi. Sanye take da kaya atamfa dinkin riga da sket sun mata kyau sosai da gani kasan ba yar talaka bace.  Kanta wani dan bokitin ruwa ne wanda da gani kasan yafi karfinta jan haline kawai yasa take dauke da shi sai jibi take da alamun gajiya a tare da ita daga nesa ta debo shi.  Ba wani abu yabawa Safuratu mamaki ba sai ganin gari da wuta kuma zaiyi wuya a sama gidan da ba tanki a anguwar.  Hakan yasa tace a ranta bari ta bita sai taga wace marar mutun cin uwace wannan, da take neman hallaka diyarta. 

kofar wani gida ta kalla nan take ta saki murmushi, da kyar ta samu ta sauke ruwan ta ruga da gudu kofar gidan nan wata yar baby ce (Diyar roba ta dauka)  nan fa ta sama waje ta zauna ta fara wasa da ita ta bar ruwan da ta dauko din kan titi, dake motoci basa wucewa. "Kutumelesi lalai fatima yau kuwa zaki daku wato har kin sama damar taba yar babyn nuratu ko".  Kafin ta juyo tuni yarinyar dake maganar ta warce yar babyn hade da kifa mata mari wanda saida ta gigice. Kuka ta farayi Wiiii!-Wiii  ta juye ta kalli wacce ta mare ta din tace "Wllh sai na gayawa mama asiya".  "Jeki ki fada din kiyi sauri kar kuda ya riga ki". Cewar mai marin,

Fatimar bata kara cewa komai faman kuka da take ga hawaye ga jibi abun yayi mata biyu. Zuwa tayi taje ta fara kikiniyar dora bokiti a kai,Da kadan ta fadi ita da ruwan badan Safuratu tayi sauri ta tallafa mata ba. Dungwai-Dungwai ta hau titi ta tafi tana kugin kuka. a bakin wani makeken gida ta tsaya tana kwalla kira "Me gadi bude-me gadi".  Aljana safuratu dake binta a baya ta tsaya ta kare wa gidan kallo tas! Taga a duk anguwar gida daya ne za'ace sunzo daya da wannan gidan ta girman shi da kyawan shi, da gani kasan an kashe nera, "To ke kuwa me zakiyi a nan gidan ko wata sabuwar tsokanar ce domin bana tunanin yar nan gidan ce ke".  Safuratu ke magana ita kadai.  Mai gadi ne ya taso da sauri yana masifa "Ke ki tsaya inzo in bude mana kin ishi mutane da kira". Bayan ya bude ya gallah mata harara wa kuma ya tabaki kika zo kina bude mana baki?".  "Zulaihat ce ta mare ni". Ta fada lokacin da ta wuce ciki, "Dan an dan mare ki shine zaki ishe mu da kuka kuma, yarinyar nan dai anyi ja'ira".

Tun a kofar falo ta fara kira "Aunty ameera-aunty ameera". Da sauri ta fito tana mata masifa to jarababa kin dawo wato har kinzo kin fara takurawa mutane".  Ameerar ke fada haka lokacin da ta sauke mata ruwan tana juyewa. Hanyar daki ta nufa da sauri ta kamota, ubanki nace Fatima dan iskanci ina zaki?. Ko kina nufin wannan ruwan ne zai ishe ni wanki?".  "Aunty zuwa zanyi in gayawa mama asiya Zulaihat ta mare ni".  Ta fada tana shashekar kuka "Muna fuka ai ba'a banxa zata mare ki ba da abunda kika mata, oya ni wuce ki karo min ruwa wllh sai kinyi sawo uku nan gaba". Rushewa tayi da kuka "wllh ni dai na gaji wajen yayi nisa aunty ki tausaya min ki deba a can". Wani tankin ruwa ne ta nuna da yatsarta ya cika sai zuba yake ma. A lokacin Safuratu ta gane cewa ba rashin ruwa yasa aka tura fatimar ba mugunta ne kawai.

"Kan uba! Iyee fatima ni zaki dinga fadawa kin gaji in aike ki kice kin gaji?".  Kwashe ta da mari tayi dan karfin marin  har saida ta kusan faduwa.  Wani sabon kukan ta dora dashi mai karfi. Da gudu naga wata budurwar ta fito daga falo tazo ta kama fatima tana kalan waccan, "Haba ameera wai miyasa ke muguwa ce bakya jin tausayin yarinyar nan ko kadan shin so kike ki kashe ta ne?. Kin turata debo ruwa dan iyayi bayan ga ruwa nan yanzu kuma kina dakar ta gaskiya karki kara dukanta".

"An daka din kiyi abunda zaki yi bari ma ki gani inci ubanta a gaban ki inga ubanda ya isa ya hanani". Fatimar ta nufa ta daga hannu zata kara marinta da sauri Wacce ake kira Iddau charaf! ta rike hannun, "Ameera wllh bazaki dake ta ba a kan me wato ita batada gata ko?". Ameera tace, "Sake min hannu, sakar min hannu".  "Anki a saki ki kwace in kina da karfi".  Haba wa ai kafi ta rufe baki tuni Ameera tayi kukan kura ta chakume ta, nan fa suka hau kunce harda naushe-naushe. Safuratu na tsaye tana kallan ikon allah abun ya fara rikitata.

Wasu yan mata ne a daki su biyu kusan kansu daya da kadan dayar ta dara daya Zan iya cewa daya shekarar ta 12 dayar kuma 14. Daga ganin su kaga mararsa jin magana ta kwaliyar da sukayi ma kadai ta isa ta sheda maka hakan ba kauya wa day ba wannan kwaliyar taci uwar ta kauyawa day a hauka. Kamar ance wa mai suna Asma'u ta kallo waje ta window.  Wani dan kara tayi na jin dadi nan da nan ta mike.Yawa bigi ciki aunty ameera, karki bari ta kada ki aunty iddau". (fiddausi suke kira da iddau) koda jin haka naga dayar ta bar abunda take da gudu tazo ta haye kan gadon itama ta fara leke. Tsalle tsalle suke suna dunkule hannu suna fadin bamu rabawa saidai mu kara zugawa bigi cikin dan bari bakin. Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take so............

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 11-12

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

😍😽 *IN DEDICATION TO YOU OUR NASMAT* _Ina ji dake wllh in kikayi fushi dani ina zan saka kaina πŸ˜ͺ Da bazarku nake rawa ZAMANI You're my blood body Au!_ πŸ™ŠπŸ€£

😍 I love you all my fans πŸ’ƒπŸ»

Even if you haven’t found your love yet, don’t worry, with time comes a lover! 😍😘

```FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----```

*Afuwan Readers nayi amfani da SUFURATU  Maimako SAFURATU a farkon pagen baya.*

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take so...»Wata mata ce mai jikin sosai  da gudu ta fito tana "kai kai ku bari mana" Da kyar ta samu ta raba su a cikin su kowacce taji jiki. Sai Huci suke suna hararen juna. "Me ya hadaku kuke fada ku da kullum bakwa rabo da rigima kamar Ba yan uwa ba". "Momy wai dan na daki waccan shegiyar yarinyar shine tazo wai zata rama mata". Ameera ta fada tare da nuna Fatima dake tsaye gefe tana hawaye.  Harara matar ta galla mata tare cewa "muna fuka ai kinga ta koma gefe tana hawayen munafurci, ke kuma Fiddausi wllh hawainiyarki ta kiyayi ramata, in badan iskanci ba saboda ta dake wannan Yarinyar zaku kama fada da yar uwarki".

Asama'u da Nasima (Suke kira da nasmat) Ba karamin haushi sukaji ba ganin mama asiya taje ta raba fadan.  Mtseewwww!  A tare suka ja tsaki, "Wannan mama Asiyar gaskiya mu dai bata gyara mana ba wallahi allah ya isa". Cewar Nasmat.  Asma'u taja tsaki mtswww!,  "Ni har ta bani mugun haushi wallahi Duk da tana momy na.  ta wani taho tubur-tubur da ita kamar kaza buloras irin lutayan nan kinsan fa basa iya tafiya sosai in suka girma bari kiga irin tafiyar maman mu".

Nan fa Asmart ta sakko ta fara nuna kalar tafiyar, harda irin Dafe kugu yanda yan lukutaye suke in sun gaji.  Da sauri nasmat ta sakko "dallah malama ba haka take ba bari kiga ni".  Itama kwakwayan tafiyar mama asiya ta shiga yi.  Bayan tayi tafiya mai dan tsayi Asmart na tsaye na kallo da gudu ta dawo tana fadar "kuma bari kiga yanda take in taci ta koshi ta kasa tashi daga kwance".  Kwantawa tayi Rairan a kan katifa tukun ta fara wani jujuyawa tana irin juyin nan da karfi abun in kagani dole kayi dariya.  Asmary ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Daga bisani kuma ta dan tabe fuska alamun tayi fushi.  Kulli ta kaiwa asmart a baya "Dan ubanki ki bari mamana ne fa".  Asmart ta mike tsaye dariya ta kusan kubuce mata,  matawa nayi kuma ai ke kika fara. Gaba daya suka saki dariya har suna rike ciki kamar mahaukata.

Fiddausi ta tace "Haba mama asiya ya za'ayi.....". Tun kafin ta idasa maganar mama asiya ta daka mata tsawa  "Ke rufe min baki wallahi ko in gwab gwabje ki yanzu a gurin nan, marar kunya"  Fiddausi tafiya tayi tana bubuga kafa tana gunguni. "Ke me kike cewa. Zagina kike ko?".  "Ni dai bance komai ba".  Kunnan fatima mama asiya ta kamo hade da jawota gabanta. "Munafuka ke kuma zo nan uwar iyayi, wato dan an dan bige ki ne kike wa motane kuka ko, to na kori mai rama mikin muga kuma uban da zai ramamiki yanzu".

Dankwashin ta tayi a kai hade da cewa "Ameera gata nan ki mata abunda kike so inga wanda ya isa ya hana ki ko uwarta tazo nan bata isa ba balle ma tuni ta bar duniyar". Tana gama fadar haka ta tura Fatima ta fada jikin Ameera ita kuwa ta koma falo. Koda jin mama asiya ta fadi haka Sai ran Safuratu yayi mugun bace tuni idanunta soka koma jajur kamar garwashi, "Wato.marainiya ce shiyasa kuke gana mata azaba ko to kunyi na karshe". A cewar Aljana Safuratu tana maganar ne a kusa da su amma su ko kadan basa ji.

Ameera ta dauki bokitin ruwa ta kara dorawa Fatima a kai maza wuce ki debo min Ruwa wllh sai kinyi sawu uku ko mutuwa zakiyk ba kuka ba".  Fatima tana kuka abun tausayi ta kama hanya ta koma debo ruwa, bayan taje ta debo a gajiye ta kawo amira ta juye ta kara bata bokitin wai ta koma. Fatima ta fashe da wani kukan domin ji take kafafunta kamar zasu tsinke dan gajiya, amma ba yanda ta iya dolenta ta karba ta tafi tana tagal-tagal mai gadi shi kanshi ya gaji da bude mata kofa, tuni ta bata mishi rai shi ba abun ya bigeta ba yayi ta aikinsa domin yasan yanda take a gun alhaji  Fatima na tafiya a gajiye jiri ya fara debarta  nan take ta fadi kasa a galabaice.  (Wayyo Rashin uwa)

Wani alhaji ne yake tafe a cikin wata dan kareriyar mota tun daga nesa da ya hange ta ya fara cewa "Wa nake gani haka kamar mama ta?. Bai tabbatar da itace ba saida ta tafi faduwa, ai kuwa yana ganin ta fadi ya danno motar kamar wanda zai tashi sama dan tsabar gudu. Aljana Safuratu tayi niyar taimakawa fati kenan taga motar nan ta dirfafo gare su hakan yasa ta koma gefe.

Wani mugun birki yaja ji kake kiiii! Kafin motar ta karasa tsayawa ya fara kokarin fitowa.  "Mamana! Mamana!" (Sunan da yake kiranta da shi kenan dan sunan kanwar mahaifiyarsa kenan wacce ta rike shi)
Tashi mamana me ya same ki, da sauri ya dauke ta yasa ta a mota sai ma da zai shiga mota tukun ya hangi dan bokitin can a gefe Ya kuma dubi jikin fatima ya ganshi a jike "tabbdijam Lalai Asiya baki so zaman lafiya ba".  Abunda ya fada kenan ya shiga motar ya fara tafiya.  Sanyin AC ne ya farfado da Fatima daga yar guntuwar sumar da tayi.

"Oyoyo dadyna Yanzu kazo?.  Abunda ta fada kenan lokacin da ta kara matsawa jikinsa ta dan jingina da shi.  "Mamana me ya sameki ne na ganki a nan a kwance kuma da bokiti kusa da ke ga jikinki a jike ina zaki?". Shiru tayi na dan lokaci tukun tace "Baba ruwa naje debowa zanyi wanka". Hararar da ya daka mata tasa tayi saurin cewa "Aa baba ba wanka ba wanki zanyi".  Kalansa tayi taga ba annuri a fuskarsa nan take ta sake canza magana "Baba dama shukoki ne zanba ruwa basa san ruwan gidan mu". Tsawar da ya daka mata ta firgitata abunda abbanta bai taba mata ba kenan nan take ta fashe da kuka. Rai a bace yace, "Mamana ban sanki da karya ba karya ba halin mutanan kirki bane shin waya koya miki karya, in kuwa kika ce karya zaki dinga min to wllh kinji na rantse bazaki sake ganin hakoran dariyana ba".

Cikin kuka tace,
"Dady kayi hakuri wallahi zan fada ma Aunty Ameera ce tace sai na debo mata ruwan wanki wannan sawuna na uku kenan  gashi na gaji amma taki ta hakura ta barni in huta". "What!  Yanzu duk kankartar ki ameera ta aike ki dauko ruwa?".  Kai ta daga mishi  "A ina kike dibo ruwan?, Su Asma'u basa gidan ne?".  "A can wajen makarantar mu ne. Dady suna gidan mana a daki suke ma".

"Innalilahi!". Ji yayi kamar ya fashe da kuka domin allah ya gani ko shi bazai iya sawu biyu ba daga gidansa zuwa can balle ma wai ace wannan yarinyar kuma harda ruwa a kai. Ranshi ne yayi mugun baci Fatima sai surutu take amma saidai ya kada mata kai dan ko maganar ji yake bazai iyaba.

Da gudu ya karasa kofar gidan ko daga odar da yake ya isa kasan ya dau zafi, dan in kana kusa da shi sai ka rufe kunnuwa,  da gudu mai gadi ya zo ya bude  yana shiga ya parking din motar ya futo a fusace ya nufi Garzali mai gadi baisan hawa ba baisan sauka ba yaji saukar mari a kumcinsa. "Garzali ashe kai aikin banza ne ban sani ba ashe a banza nake biyanka kudina in wata yayi".  Cikin murya mai rawa "Afuwan ranka ya dade bansan laifin me nayi ba". "Au bakama san miye laifinka ba ko uban wa yace ka budewa Fatima kofa yanzu in diyarka ce dan gidan ku zaka barta taje debo ruwa ne. To daga yau wllh in na sake kamaka da irin wannan laifin a bakin aikin ka".  Fuuu!! Ya wuce kamar jirgi  mai gadi ba abunda yake sai bada hakuri harda durkusawa a gun. Bayan alhaji ya danyi nisa ya tashi yace a kan wannan yar banzar yarinyar ana min barazana da aikina".  "Me kake cewa?". Inji alhji  "Aa Alhji cewa nayi ayi hakuri zan kiyaye".

Tun daga kofar falo ya fara kwala kira "Ameera! Ameera!". yana janye da hannun Fatima.  Nan danan saiga ta ta fito Jikinta na rawa dan tasan abunda ta aikata ko kadan batayi tunanin abban nasu zai zo war haka ba. "Dady gaaa..". Saukar tagwayen mari da taji ne ya hanata idasa maganar sai ihuu! da ta kwada mai karfi!  Kafin kace me falon ya kusan cika Da yara da manya bansan haka gidan nan keda iyalai da yawa ba sai yanzu.

Asiya ce tazo ta rungume Ameera dake faman kuka. Alhaji ya fara magana.
"Ke dan ubanki baki da hankali ne ya za'ayi ki aiki wannan yarinyar wai ta debo miki ruwa har can wata uwa duniya baga kanan ki nan ba wanda suka fita me ya hanaki aike su ko zaluncine kawai abun, to wai ma inace dazun nan da aka kawo wuta Nasa aka kunna soma?".   "Haba alhaji dubi fa yanda ka kunburawa yarinyar nan kumatu kamar dai ba yar uwarta ta aika ba, kawai fa uniform dinta ne zata wanke kasan farare ne shine fa ta aiki Fatima ta debo mata ruwa a can kasan yafi na nan haske". Asiya ce ke maganar lokacin da take lalashin yar tata.

"Asiya! asia! Sau nawa na kira sunanki,.?". 3 Ta bada amsa a Hatsale,  "To wllh asiya ki fita a idona zan miki rashin mutuncin da bakiyi zato ba wato duk ke kike daurewa yaran gidan nan gindi suke abunda suka ga dama ko?. To bari kiji in gaya miki wllh duk wanda yake so muyi zaman arziki da shi a gidan nan to karya ya taba mamana in kuwa mutun bai yarda ba ya gwada taba ta yaga abunda zai farubda shi".   Yana gama fadar haka ya kama hannun Fatima ya nufi dakinsa.  Ya fara tafiya kenan asiya ta fara gunguni kamar yarinya "Shikenan wato sai a raba kan yara a hana su shakuwa da juna". Maganarta ce tamai zafi sosai yaji bazai iya daurewa ba. Sakin hannun fatima yayi da gudu ya Nufe ta, Abunka da lukutar mata bata da gudu ta ruga amma baisha wuya ba wajen kamota. Koda yaje sai yasa kafa ya kwalfe ta nan  ta fadi ta fara wash! Wash! Wayyo ya karya ni.  Bai ko tsaya kallanta ba ya wuce ya dakinsa shida fati.

Asmart da Nasmat ne suka kalli mama asiya tukun suka bushe da dariya ganin ta a kasa kamar an zaunar da buhun masara.  Kowa na gurin abun ya bashi dariya har kishiyoyin nata guda biyu dake tsaye a gefe. Saidai kowa yasan jarabarta duk gidan dama ba wanda zai iya mata dariya sai wannan biyun marar ji.  Ai kuwa kafin kace me ta yunkura da kyar ta tashi tubur-tubur ta nufe su wai da niyar ta kamosu ta daka,  kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.................

Hmmmmm Gidan nan za'a sha kallo naga alama.

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boyπŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 13-14

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU

☘ *UMMU BASHIR* ☘

*ZAINAB YUSUF*

*HUSAINI ATK (80K)*

```FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----```

               *KARSHEN PAGEN BAYA*

kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.

»» gidan ALHAJI SALIM S.O kenan babban gida ne dake cike da iyalai. alhaji salim mata hudu  gare shi saidai daya ta mutum yanzu uku ke a raye.  Asiya uwar gida  yaranta biyar biyu mata sune AMEERA DA ASAMA'U. Maza uku SAFIYANU babban danta  sai mai mishi YUSIF. Da kuma yayan ameeera ABBA.

Mai biwa asiya ZUWAIRA 'Ya'yanta hudu FIDDAUSI.  NASIMA. ABDUL Sai ALIYU.   A  yanzu HAUWA'U Ce amarya yaranta biyu kadai kanana ILIYASU ABUBAKAR.

Shekarar hindatu (Mamar fatima) uku a gidan ta rasu sai dai ta mutu ta bar fatima tana yar shekara biyu.  Yarinyar fara kyakyawa a duk gidan tafi kowa kyau domin ita ta dara mahaifiyarta ma kyau. Alhj kamal kuwa ya dauki duk san duniyar nan ya dora a kan fatima domin yana jin tausayinta sosai kasan cewarta karama kuma marainiya hakan yasa ya dauki amanarta yabawa asiya.

Irin san da yake nuna mata shi ya jawo mata ta zama kamar jaba a gidan in aka cire Fiddausi, maza da mata yara da manya baki daya ba mai ragawa fatima a gidan bata samun sauki da farin ciki sai abbanta na gida.

Hakan yasa ma in baya nan sai ta shiga daki abunta wani lokacin tata barci wani tym din kuma tata kuka abunta. idan ta tuno mahaifiyarta. A labarin da nake baku yanzu fatima takai shekara 9 da rabi a duniya ta iya yiwa kanta komai. Dan ko da tana karama bayi mata ake ba, Asiya da dauda take barinta.  Fatima na shan wuya sosai Domin har ta saba da wahalar da yan uwan nata suke bata bama kamar  Asmart, da Nasmat. Wadan nan biyu ba irin wuyar da basa bawa fatima.

*Cigaban labarin*
Washe gari Fatima ce ta tashi daga barci ta kalli dan agogon dake ajiye a kan mirror dakin nasu firgigit ta zabura ganin karfe 6:10 bata yi sallah ba. Sauran yan uwan nata mata da suke tare a dakin ta kalla. Sai bacci suke abunsu. Fiddausi kawai ta tayar domin ita tace ta dinga tadata. fatima sauran ta kalla ita ba abun ta tashe su ba tasha fada in bataci sa'a bama har duka. Tashi tayi ta nufi ban daki a guje. Tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah. Naji muku haushi sosai da baku ji karatun yarinyar nan ba.

A hankali bayan tayi fatiha take jan suratul Ψ§Ω„ΨΊΨ§ شية  ghaashiya. Muryarta na fitowa a hankali. Kamar kar karatun ya kare. Tayi zaman tahiya kafin ta karasa ta sallame. Tun kafin matar ta karaso take kwalla uban kira. "Fatu! Fatutu!" Da karfi. Fatima najin haka ta kama sauri allah-Allah take ta idar da sallah kafin matar ta shigo.

domin tasan halin mama asiya kwarai bata bata dadi kuma tafi kowa musguna mata a gidan.  Asiya dingishi take sakamakon double faduwa da tayi jiya. Banko dakin tayi.

Kamar wacce zata karya shi. Ta tsaya a gurin ta kama baki. "Iyye! Gaga  'yar banza wato sai yanzu ma kike sallah baki tashi da asuba kinyi ba ko?. inji mama asiya. A zuciya kuwa tace "yarinya kina kokari domin kuwa ni banma yi ba tukun". Daidai lokacin fatima ta idar da sallah ta juyo ta dan risina tace, "mama asiya ina kwana". Dan ban kwana ba zaki ganni ne dan ubanki?.  Sunkuyar da kai kawai fatima tayi. "Munafuka Kaganta kamar wata salaha. To da ban kwana ba zaki ganni ne?, Tambayarki nake, Maza-maza ki iske ni a kitchen.
Yau dake zamu hada kayan kari. Saura kuma ki ki zuwa da wuri ta kama kunnan fatima ta murda. "Kinga kunnan nan to sai na cira shi. Ko in ba-ba-laki in yaso in bada kudin dori".

Faima sai da tayi dan kara domin zafin da taji na murda kunnan gashi har yanzu taki sakinta. Asiya tace. "Bazaki bar yiwa mutane ihu ba sai kin tada mana yara. Maza ki iske ni a kitchen kinji ko?". Gyda kai fatima tayi tace "naji gani nan zuwa mama". Mari ta wanka mata. "Wacece mamarki din?, Allah ya suttura in haifi yarinya kamarki".  Ta nuna wasu yan mata dake gefe a gado suna ta sharar barci tace "kinga yarana can ba kamarki ba". Mtseww Ta ja tsaki ta fice.

Nan ta bar fatima tana kuka. Ta zubda hawaye sosai tukun ta tashi taje da sauri ta shiga bedroom tayi brush tukun ta canza kaya ta fito. Dugi-dugi ta nufi kitchen. Fatima tasha wuya sosai a kitchen din dake gaba daya ake haduwa ayi girki a gidan. ba mai tausaya mata a cikin matan baban nata duk su ukun miko wancan kulkula wannan wanke can gyara can. Ba mai tausaya mata ko ganin kankantarta a cikin matan.  Bayan an kamala ita suka dinga dorawa kulolin abincin tana kaiwa dinner.  Saida aka kamala komai tukun suka korata daki kuma suka ce in ta shiga ta kwanta kmr mai barci kar ta yarda alhj ya gane cewa ta tashi balle ma ya gano tayi aiki. Haka ta tafi tayi yanda sukace ta hau gadanta tayi shiru. Tana ajiyar zuciya. Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.
...................................................

Mujee zuwa.

Autan writers nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 15-16

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

😘 Abunda yake raina zana fitar na huce takaici, suyaya ku a raina zana fada bazan boye ba.........

πŸ’ƒπŸ» ALAMAR TAMBAYA TANA GA MAI YAWAITA TUNANI, MUSAM DA NASHI CIKIN SOYAYYAR READERS NA. NA KWANA CIKIN TA NA RASA WANDA ZAI FIDDANI SAI KU MASOYA NA WANDA KUKE DA KYAU NA KAMANNI,   NA RIKE KAUNAR KU A RAINA TA ZAUNA.. NAYI SHIRINA ZAN BAKU DUKA PAGEN GA😜😜😜😜😝

♥ BANI DA BAKIN GODE MUKU MASOYAN ALJANAR FATIMA, TUN  YANZU KAFIN AJE KO'INA MASSAGES DINKU SUN FARA RUTATOWA CIKIN WAYA TA.  INA GANIN SAKONNIN KU INA JIN DADI SOSAI, ALLAH YA BARMU TARE. DA MASU KIRANA INA GODIYA, KUNA A HEART NA MUSAMMAN .♥

'YAN PHARIDAH KHAMSHI NOVELS

SAMEE KHAIRAH NOVELS

BIGBOY ISA NOVELS

BIGBOY ISAH FANS

ZAMANIWRITERSASSOCIATION
DA MA SAURAN SU....

BAN MANTA DA KUBA 'YAN WHATSAPP GROUPS INA GANIN SAKONNIN KU INA GODIYA.  ANA TARE, ANA TAREN TARE, ANA MUGUN TARE.LOLZ

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

               *KARSHEN PAGEN BAYA*

~Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.~

```»»Wajen cin abincin bangare-bangare ne wajen yara mata daban haka maza ma daban. Bangaren uwaye kuma sunsa abincin gaba an zubawa kowa nasa saidai ba damar ci. Sai alhj ya fito. Asiya tayi tsaki tace, "wai ace abincin ma sai an sawa mutane doka a kai, ji dallah yanda ya bar mutane najin yunwa yaje yayi zamansa...". Shiru tayi sakamakon jin yara sun
Fara hayaniya alamun shigowar alhj kenan. Idan ya shigo duk rashin jin yaro sai ya natsu domin bashi da wasa. Bayan yaje ya zauna. Uwayan wato matansa. Suka fara gaishe sa tukun suma yaran maza da mata masu dan wayo suka biyo layi daya bayan daya suna gaida shi. Yayi mamaki da baiga fatima ba a cikin yan zuwa gaishe shi din ba. Da zai tambaya kuma sai ya kyale.

Shi ya fara yin bismillah ya fara kai abincin baki tukun kowa ya fara ci. Dokar cin abincin kenan sai ya fara cin indai yana gida tukun kow zaice. Fatima kuwa tana daki ga gajiya ga yunwa kuma sun sata barcin dole. Saidai kwata-kwata barcin yaki zuwa domin yunwar dake kwakwalar ta. Tana jin kwaram niyarsu ana cin abinci kamar ta fito sai dai kuma tana tsoran tayi laifi. Domin tasan in ta saba musu to yau ta shiga uku ko abincin rana baza su bata ba. Haka suke mata idan tayi musu wani laifin. Su sakata aiki mai tsanani kuma su sata azumin dole horo da yunwa. Haka dai ta hakura ta kwanta tana kuka.

Bayan an gama cin  abinci kowa ya kama gabansa dake yau weekend ba makarantar sai islamiya. Alhj ya koma dakinsa amma sai ya kasa natsuwa da ya tino baiga fatima ba. Hakan yasa ya fito ya tambayi matan "wai ina fatima ni ban ganta ba". Asiya tayi farat! Tace "uhmm alhj kai da kasan halin yarinyar nan da shegiyar lalata. Tana can dakin yara tana barci nayi-nayi in tashe ta tayi sallama amma taki tashi".  Ta fadi hakan ne domin ta jawa fatima duka.

cikin fada yace "asiya wace irin banzar magana ne kika fada min kina nufin fatima bata tashi ba har yanzu. me yasa kika zama muguwa maciya amana iyee! asiya. yarinyar nan fa marainiya ce amanarta na baki. amma yanxu dan allah ace duk kin tashi yaranki sunyi wanka har sun karya amma ita dake ba yarki bace shine zaki barta har wannan lokacin bata karya ba. yanzu karfe 9:30 fa".   Ta wani marairaice "haba alhj in kuwa kace haka baka min adalci ba.  yanzu duk irin tatalin da nake wa wannan yarinyar kana so kace baka gani alhj. Ni ai a ganina rashin tashin ta din ma da nayi duk a cikin gata ne. Na barta ne ta hutawa rant....".

Tsawa ya daka mata. "Ke dallah rufe min baki bana san wannan zakin bakin naki. Maza wuce ki kira wo min ita". Murguda baki tayi ta tashi tana gunguni. Wai irin wannan ai sai yaja a rainata a gaban kishiyoyinta ake mata wannan abun "Dama jiya ka targada ni dan mugunta". Alhj yace "me kikace". Juyowa tayi. "Aa ni banyi magana ba". Ta wani gallo mishi harara. Ta nufi dakin yara. Fatima najin turo kofarta tayi maza ta rufe idanunta kamar mai barci.Asiya kuwa tazo ta kama tikarta "fati!-fati!, Tashe munafuka kinzo kin kwanta wato sai barci kike.maza jeki kiyi brush ki zo wannan masifafan mutumin na kiranki". Fati bata ce komai ba ta sauko taje tayi brush ta dawo. Tazo gaban asiya tace nayi. Rigarta ta gyara mata ta kuma dan go goge mata fuska kamar da gaske. Tace "idan kika yarda kika ce kinyi aiki kuma kika gayawa alhj ni nace ki dawo daki ki kwanta to ni dake ne a gidan nan kinsan dai halina sarai".

Fatima tace "bazance ba aunty". Dankwashinta tayi a kai. "Kinci uwaki. Nice aunty wato bama mama ba ko. Wuce muje". Fatima ta shiga gaba asiya na binta baya.  Alhj kallo daya yayi wa fatima ya gane tana jin yunwa. Bata karya ba. "Momyna". sunanda yake kiranta da shi kenan. Kinci abinci kuwa. Girgiza kai tayi tace aa ynz na tashi a barci. Barci kuma?, wato bakiyi sallah ba ko?. Bana ce ki dinga kula da sallah ba ki bar wasa da ita". "Dady nayi fa tun da wari nayi sallah sannan na koma barcin".  "That good haka nake san ji momyna".

Juyawa yayi ga matan nasa wanda duk sun Zuro musu ido ba abunda suke sai hararen fatima. A cikin zuciyqrsu kuma tsanarta na kara fadada. "Wace tayi abinci?, Ina abincinta?". Ya tambaya Zuwaira tace, "alhj wane abinci kuma ai gidan nan ba wani sauran abinci duk an cinye tana can tana barci". Alhj yace "Yanzu Dan tsabar mugun hali yarinyar bata ci abinci ba shine kukaki ajiye mata. Ko dan kunsan ba 'ya'yanku bane. Wato ita Marainiya batada uwa ko".  Bai tsaya jin abunda zasuce ba yaja hannun fatima yace "zo muje in saya miki abinci mamana". Yaja hannunta suka fita.

Nan ya bar mata sai surutai suke yi. Har asiya na cewa "wai anya kuwa uwar yarinyar can ba asiri tayiwa alhj ba kuma har yanzu bayan ta mutu yake tasiri a kan yarta ba.nifa abun ya fara bani tsoro".  Zuwaira tace "haba aunty barta mana ai gasuwa zatayi a gidan nan domin ko yar aiki sai tafita jin dadi wllh. Yarinya karama sai kini bibin tsiya". Hauwa tace, ai wallah ni kadai nasan muguntar da na shiryawa yarinyar nan, zaku gani da idanku".  Yar guda sukayil a tare suka hada hannu.

Mota suka hau alhj yaja saida suka je wata rumfar mai shayi tukun ya faka ya fito yajawo hannunta suka shiga suka zauna yasa a soyo mata indomei da kwai da kuma zallar wainar kwan da kofin shayi biyu. Kudi ya kashe musu dai sosai a gurin. Fatima saida taji cikinta ya cika nat! Domin kuwa rabanta da ta sama isashen abinci tun waccan juma'ar da taje gidan su wata kawarta ta wasa. Mota suka hau suka nufo gida tafiya ake fatima sai waige-waige take yi ta kalli can ta kalli can. Tana kallan shaguna. "Dady tsaya-dady-tsaya". Bai shirya ba ya take birki. Ya fara tambayarta "miye kika tsaida mu mamana?".   "Dady danyi baya, Yi baya dady". Baiyi gardama ba yayi baya da motar. Saida suka zo saitin wani shago tace ya tsaya. Da gudu ta sauko taje tana kokarin dauko wata yar baby. Wacce suke a jere duk na sayarwa ne.

Mai shagon ne ya fito yana neman dukanta alhj ya dakatarda shi. Yace "mamana miye haka kika zo zaki daukar musu abu na sayarwa ne fa ko baki sani ba?". "Na sani dady wannan nake so ka saya min ina santa sosai kaga munyi kama da ita kuma ma dady kaga wannan tafi ta nuratu kyau da girma".  Dan Murmushi yayi kadan yace "ke kuwa me zakiyi da wannan katuwar diyar robber ai tayi girma duba karama mn. Wannan tafa kusan kaiki tsayi".  "Aa baba ni wannan nake so".  Alhj ya kalli mai shagon ya tambayi kudin diyar robar. Mai shago yace "dubu bakwai".  Alhj yace ina zuwa. Mota ya koma ya dauko kudi  "kash! Ashe na baro kudin a gida".  Saura dubu uku ne a hannunsa. Ya dawo cikin yanayin damuwa gashi mutumin baisan shi ba. Balle yace in ya fito zai kawo mishi. Ita kuwa fatima rike take da yar tsanar ta fara wasa da ita.

Ya dawo yace "malam na manta kudina ne a gida kaga saura dubu uku canjina kayi hakuri ka rike wannan ka bamu yar robar in yaso idan na fito zan kawo maka". Mai shagon yace "ai ina ban sanka ba bazan taba yarda ba. Kaga kawai in bazaka saya bane to".

Alhj ya kalli yar tasa yace fatima "kinga yanzu bani da canji zo muje gida in dauko kudi sai mu dawo in saya miki".  Fatima ta saka kuka ta kankame yar tsanar gam a kirjinta, wai ai ita baza'a rabata da yar babyn ta ba. Alhj yayi-yayi da ita ta bari ya dawo amma taki. Ba yanda ya iya dole wayarsa ya bawa mai shagon ya rike ya basu yar babyn kafin ya dauko mishi kudin. Haka kuwa akayi. Mai shago ya karba yaje shago ya ajiye tukun ya dauko musu wata yar karamar akwati. Ta kayan yar babyn ce. Suka karba fatima sai murna take ta dauki yar babyn wacce ta kusa tsayinta tasa a mota suka tafi gida    tunda suka taho a hanya yar babyn ta fara kwai-kwayan fatima. In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama     ............................................... . .........```

            *KARSHEN PAGEN BAYA*
~In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama~
```»»Tun a mota yar babyn ta fara magana. a cikin wata irin karamar murya. "Sunana safuratu ina tayaki murna da sayana da kikayi". Fatima ta juya domin ganin mai magana bataga kowa ba. tace "abba kaine kayi magana Yanzu?". yace "aa magana kikaji nayi". tace magana  naji ko yar babyna ce?. alhj murmushi yayi yace "'yar baby kuma ai ba irin mai magana bace bakiga batada speaker ba...?. Kafin ya rufe baki wata siririyar murya ta kara magana, "Zan dinga saki dariya, zan dinga baki labarai masu dadi, amma ni fa ba'a barina da yunwa, kuma ni kullum sai anyi min wanka an canza min kaya anyi min make-up....."  alhj tsurewa yayi domin yaji tabbas yar babyn ce ke magana a tsorace ya fige yar robar yana dudubata wai ko zaiga speaker a jikinta amma bai gani ba. ita kuwa fatima murna kawai take da jindadi yar babynta na magana. alhj yace "fatima 'yar babynki ce fa mai maganar nan to amma ni banga speaker a jikinta ba"
.  fatima ta karbe abunta tace "Baba ai itama da baki take yi kamar mu baka gani bane?".

yace "eh ni ban gani ba, amma bari in na koma zan tambayi mai shagon inji ko tana magana. Domin ni ta bani tsoro fa mamana".  Haka dai yaci gaba da tuki cike da mamaki har suka karasa gida. fatima ta sauka da gudu tana murna ta nufi cikin gida rungume da yar babynta a parlo ta iske duk yan gidan yara nata rashin ji masu wasa nayi masu rigima ma hk. ai kuwa yan yaran na ganin yar babyn suka yo kan fatima wannan ya karba wannan ya figa wai ko wane yaro sai ya je gurin uwarsa ya kama kuka wai a kwace a bashi. can wasu yara marar ji guda biyu daya ya kama wajen kan yar babyn daya kuma ya kama kafafun sai jayaya suke wannan yana so ya karbe wannan ma yana so ya karbe fatima kuma sai kuka take zasu karya mata yar baby gashi  ba dama tayi mgn.

lokacin alhj ya shigo. "kai! kai! ku wane irin mararsa jin magana ne. zaku balla mata abu bata kayanta maza". mika mata sukayi. ta karba ta nufi dakinta asiya ta harare ta tace a zuciyarta "munahika ai alhajin zai tafi zaki ci ubanki". alhj yace "yanzu ku kuna gani a gabanku zasu batawq yarinya abu a gabanku amma ko kuyi magana. haba asiya kece babba fa ko sauran basuyi magana ba ai ya kamata ke kiyi mawa yaran magana". "uhm ai ni kullun a wajenka marar adalci ce to amma yanzu kai ga adalci nan a fili ka nuna mana, tunda ga yara nan da yawa a gida kuma duk yayanka ne amma ace ka ware fatima ita kadai ka saya mata abu. wannan shine adalci ko?". Ran alhj ya bace har zaiyi mgn kuma sai ya fasa ya wuce up stairs. yaje dakinsa ya dauko kudi yq fito yayi tafiyarsa.

su Zuwaira sukayi dariya sukace "aunty asiya kin min daidai ke kadai ce maganin alhj a gidan nan". asiya tace "hmm ku kyale sa ai yau saina toya yar babyn nan muga ta tsiya sai inga me zaiyi haba ya zai dinga fifita wacce kudabukar yarinyar a kan sauran yara bari inje gurinta". su Zuwaira binta kawai sukayi da kallo. ta tashi buzun-buzun ta ta nufi dakin yara. fatima zaune take a kan gadanta ta zaunar da yar babyn tana cin bisket itama tana tura mata a baki. tana ci ci diyata daga bakin. kawai sai taga bakin ya bude. bata wani firgita ba sai ma dadi da taji. ta tura mata bisket din tace "kin koshi.?

lokacin asiya ta karaso gurin ta kama yar babyn da hannu daya ta wullata jikin bango ta fado tim!  ta kuma wanke fatima da mari "shegiya yarinya me kike a nan tun dazu ina can ina jiranki zan aike ki kin wani shigo daki kin zauna. dama nasan wannan yar babyn da kika samu ita zata dinga hanaki aiki amma bari ynz in dauke tq in yayankata  in toya muga ta tsiya". fatima ta fashe da kuka tana bawa asiya hakuri karta yanka mata ya' abun mamaki fatima na fara kukan suka jiyo kuka a baya. asiya ta juya baya. yar babyn ta gani a zaune tana kuka harda ruwan hawaye

Abunda yayi mutukar tsorata Asiya kenan, da gudu taje ta shige karkashin gado, fatima na ganin haka ta sauko tuni tama bar kukan ta fara dariya, mama asiya ta bata dariya.  Zuwa tayi ta dauka yar babyn tana lalashinta. "Yishiru-Yishiru diyata. Mama asiya ce ta taba min ke ko?"  Kunnuwan asiya sunji lokacin da yar babyn tace "Eh itace". Cikin wani karamin voice, "To yi shiri bazata sake ba".  Asiya a dan tsorace ta fito daga nesa tace "Au! Fatima dama yar tsanar taki tana magana?". "Eh mama asiya ai tun a mota ta fara magana, babama ya dauka bata magana". Asiya tace "to dan kawo ta mu gani".  Amsa tayi ta duduba amma bataga speaker ba. "Fatima ina speaker da wajen sa battery?".  Mama ai da  baki take magana kuma ba'a saka mata battery, yanzu nayi mata wankq bata bushe ba".

Abuda ya fadowa asiya a rai shine. Hawayen da ta gani wato ruwan da fati tayi mata wanka ne. Ai kuwa ta maka diyar da kasa tasa katuwar kafarta ta taka tabi ta samanta ta wuce tana hararen Fatima hade da cewa. "Dauki yar iskar yar tsanar ki, ko dan wannan ai tama wuce yar tsana a girm saidai ace *ALJANAR FATIMA*.  Fatima bata tanka mataba da sauri taje ta  dauki yarta taci gaba da yin wasa da abunta.

A falo ta iske su Zuwaira suna nan inda suke basu tashi ba. Asiya tana dan dangeshi ta karasa ta zauna ta saki wani gwabran nishi. Wanda yasa su Zuwaira saurin tambayar "Lafiya dai aunty babba, fatan kin yayanka shegiyar yar tsanar nan..."  Tarar nunfashinta tayi ta hanyar cewa, "Ina fa 'yar tsana da ta tsoratani. Ashe wai tana magana, ban sani ba ina shiga dakin na karbe ta na maka a bango juyawar da zanyi sai naganta tana kuka harda hawaye. Ai kafin kice me tuni na shige karkashin gado na dauka ai aljana ce, washh! Wllh har yanzu gabana faduwa yake".  Su hauwa najin haka suka kwashe da dariya hararar da ta daka musu ita tasa su hadiye dariyar dan dole. "Wai ina su asmart ne ko har yanzu basu dawo daga wajen kitsan ba". Asiya ta tambaya. "Eh wllh kinga har yanzu basu dawo ba, Ni jirama nake su nasan su zasu lalata wannan 'yar tsanar". Zuwaira ta bata amsa. "Ai kinji shiru gidan dake basa nan".

Su Nasmat kuwa na can gidan kitso  gaba daya su hudun harda Fiddausi da ameera.  Dake mai kitsan tasan halinsu suna zuwa tace su zata fara yiwa su tafi abunsa.kafin  a gamawa asmart kitso saida nasmat ta Zubar da duk ruwan gidan, wai wanke kai take daga ta wanke sai ta shinshina tace wari yake. su Fiddausi dama basuyi magana ba dake sunsan halin ta idan ma sukayi mata magana baji zatayi ba. Da sauri mai kitsan ta burbura tayiwa asmart kitson Nasmat duk ta jike kan, Amma a haka mai kitsan tace tazo a mata dake ya dansha iska. Haka itama asmart tata barna kafin a gamawa nasmat saida tasa yara sunfi biyar kuka a ciki harda wanda ta fasawa kai. Jini na zuba yaran tafi ya gayawa uwarsa. Asmart tazo ta kama nasmat kitsan ma ba'a gama ba sauran layi biyu. Amma a haka suka gudu, basu zame ko'ina ba sai gidan aunty Sakina yayar mamar su ce. (Wato mama asiya.)

,
Matar yar lukuta wacce itama jikinta ya kai na mama asiya. Nan ta tashi tana musu sannu da suwa. Bayan sun gaidata. Tace, "Asma'u uwayen rashin ji ziyara aka kawo min yanzu da yamman nan?".  Bayan sun kalli junane asmart tace "Eh mama asiya ce tace mu zo kuma ma a nan zamu kwana".   Sakina tace to madallah ai naji dadin zuwanku dama ga aiki nan kaca-kaca ya min yawa a gida sai ku dan kama man muyi sauri mu gama kan magariba". Cikin daga murya nasmat tace, "Kutumelesi kiji wannan matar wai mu tayata aiki". "Yaseen ni dai bazanyi ba saidai ke ki tayata". Cewar Asmart "Kutt kinga malama yayar mamar ku ce ba yayar mamana ba. Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata".  "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.....,.............```

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 19-20

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

IN DEDICATION TO YOU
*KHADIJA CANDY*  *_ALLAH YA BAR ZUMUNCI, YASA KIFI HAKA NA GODE DA ADDUO'IN DA KIKE MIN. KEMA KUMA ALLAH YA KARQ MIKIN DUMBIN BASIRA DA HIKIMA DA FASAHA, ALLAH YA KARE MANA KE DAGA SHARRIN MAHASSADA DA YAN ADAWA DA MAKIYA. ALLAH YA TSARE MANA KE DAGA SHARRIN DARE. SHARRIN RANA, FATAN KOFOFIN ALKHAIRAI SU BUDE A RAYUWAR KI DUK NA SHARRIN SU GARKAME.  AMIN YA ALLAH.*_

_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

               *KARSHEN PAGEN BAYA*

~Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata".  "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.~

```»»Aunty Sakina da ta saki baki tana kallansu ita kallansu take abun yaso ma ya bata dariya kuma sai ta basar. Ta cire takalmin ta ta fara kwada musu da sauri suka saki juna. "Kaji yan iskan yara daga zuwa zaku mayar min da gida kamar gidan dambe?, To wallahi bazan iya ba ku tatara ku koma na gode allah ya baku ladan ziyara". Suna jin ta fadi haka sai suka shiga bata hakuri Da rokonta a kan tayi hakuri ta barsu.

Bacin rai tanuna musu sosai ta murtuke fuska tace, wallahi kafin in futo daga dakin nan ku bar gidan nan in kuwa ba haka ba wallahi sai jikin ku ya gaya muku". Tana gama fadar haka ta shige dakin. Su kuwa kofar dakin sukaje duk su biyun sukayi Neldown kamar wasu mutanan kirki.

Sanda tayi kamar mintuna biyar tukun ta fito daga dakin sun bata dariya a yanda ta sansu da rashin ji yau sune roko harda durkusawa. Nan dai tace musu ta hakura amma fa aiki ba'a janyewa'.  Da sauri sukace "Mun yarda".

A can kuma gidan mai kitso uwar yaran da aka fasawa kai ce, tazo da wani danta saurayi dauke da wata gora. Da ganin  matar kasan jarababa ce, ko yanayin tafiyarta zai iya shedama ba da alkhairi take tafe ba.  "Wace yar kutu... Ce ta fasawa yarona kai, ku nuna min ita yanzu itama insa a rotsa mata nata kan". Matar ce ta shigo gidan da wannan furucin lokacin da dan nata kuma ya daga gorar yana shirin makawa duk wacce aka nunu. Da gudu Fiddausi da Ameera suka Ruga dakin mai kitso. Tana shirin binsu Mai kitsan ta shiga gaba ta tare kofar dakin tana "ki saurara basu bane ki saurare ni, kannansu ne basu ba". Tsayawa tayi tana jijiga.  "To ai anzo a dai-dai kenan yanzu in nasa aka fasawa daya daga cikin yayyen nasu kai, kinga ai anyi 1-1 ko". Aa dan allah ba haka za'ayi ba kinga nidai kitso suka zo min nan kuma sun tafi gida tun lokacin da sukayi wannan ta'asar. So abunda yafi shine ki bisu can gidan Alhaji salim din".

"Kutumelesi dama yan gidan alhaji salim ne. Kai zo muje ba zama lafiya yau zasu san sun takali wutar dafa kansu".  Fuwww!! Ta wuce yaran na binta bayq da kulki a hannu. Tun daga get suka fara rikici da mai gadi, yaki barinta tq wuce, sanda ta shsmmace shi tukun ta ingiza shi ya fadi da sauri suka shiga.  "Asiya! Asiya! Asiya!". Da duk illahirin karfin sautinta take kwalla wannan uban kiran. Ta cire gelen dake makale a kafadarta ta daura a ku'gu.

Da sauri su asiya da sauran yan gidan suka fito suna tambaya "lafiya-lafiay". Cikin masifa da tsiwa tace, "Ina fa lafiya ai tunda kuka ganni a haka kunsa ba lafiya ce ta  kawo ni ba. Wannan bala'eun 'yaran naku ne suka fasawa dana kai dan haka nazo ko dai a fiddosu insa a fasa musu kai. Ko kuwa kuga tashin hankali".  Nan ta fara jijiga tana cewa dan saurayin nan ya matso kusa ya shirya.  Asiya tace "Innalilahi yanzu su asmart bazasu barmu mu huta ba, Rikicin nasu ba iya gida ya tsaya ba kenan.  Kinga mariya zo muyi wata magana".

Mariya tace itafa ba inda zata sai an fiddo da su asmart ta rama wa yaranta tukun ta tafi daga gidan nan domin har wani hauka-hauka take tana tsalle-tsalle lokacin da Asiyar kecewa suzo su sasanta. Da kyar asiya taja hannunta bayan dakunan su. Basu fi mintuna biyu ba suka fito suna washe hakora. Gaba dayan fishin da Mariya tayi ya zama tarihi ba abunda take sai godiya wa hajiya. Sauran matan sunyi mamaki abun ya daure musu kai. Mariya tayi musu sallama tacewa Dan saurayin "Kai zo mu tafi ai na yafe musu".  "Haba mama Najeef fa aka fasa wa kai shikenan munzo a rama kice wai kin yafe".  "Kai zanci ubanka fa wai bani nake maka magana ba?".  Yana dan gungunin sa ya bita suka fita.  Sunje fita mai gadi ya leko ta kofa hade da cewa "Jarababiya kawai allah ya isa turenin da kikayi". Da sauri ta juyo a fusce zatayo kansa "Me kake cewa". Habawa ai da gudu ya shige dakin ya rufo.

Bayan su Asiya sun koma cikin falo Zuwaira tace "wai aunty dukan matar nan kikayi ne ko kusa warning kikayi mata. Naga lokaci daya ta wani saukko".  Yar dariya asiyar tayi hade da cewa, "Hmm ba ko daya daga ciki kinsan fa in kikaga mutum na irin haka to in kika bincika harda talauci a ciki, Naira 500N na bata kawai nace taje ayi mishi magani, Shine fa kinji harda su godiya".   Dariya sukayi gabaki daya Hauwa'u tace "Gwara da kikayi haka wllh dan da alhaji ya zo ya tarar da ita. Bama su asmart ba mu kanmu bazamuji dadi ba".  "Ashe dai kina ganewa gashi yau a dakina yake kinsan yanda muke da shi dama. Ai shiyasa nayi saurin watsawa Wutar nan ruwa".

************

Kwance take a daki ita kadai  tana barci. Wata mahaukaciyar dariya mai gigitarwa ce ta daki dodan kunnan ta. Bata shirya ba ta tashi zumbur! A tsorace, tana waige-waige "Alhaji! Alhaji! Dubawa tayi gefan wajen wayam ba alhaji. Hahahahahaha! Dariyar mace ta jiyo kamar a downstairs a dan tsorace ta tashi ta bude kyaure a hankula ta laleka bataga komai ba, hakan yasa ta idasa fitowa. Da fitowarta Kofar dakin ta taji an banko da karfi kamar za'a balla, dan kara tayi ta zabura kuma. Lokaci ta nema bude kofar amma sai taji kamar an Garkameta da kwado. Abunda yayi mutukar girgizata kenan. A saman dakuna ne guda hudu dakinta ne a can karshe sai na Zuwaira sai na Hindu wanda yanzu alhaji ya mayar nasa. Na karshen kuwa na Hauwa'u ne.   Dan lungun dakunan a haske yake fes da fararen Gululuka. Lokaci daya tada wutar ta fara farfari. Kwayayen suna wata irin girgiza dariyar Yarinya ne ya biyo baya dariyar marar dadin ji.  Ahhh!  Ahhh! Da karfe ta fara ihun itama. Ta durkushe a gurin ta sa hannaye ta rurufe kunnuwanta. Hade da runtse idanu. Dif! Taji komai ya tsaya an bar dariyar haka kwayayin sun daina girgiza da farfarin da suka. Mikewa tayi cikin kuka kuka ta fara tura kofa da karfi  tana fadin "na shiga uku ni Asiya me ya fito dani.  Gashi sai tsorata ni ake yi".

Ta baya taji an tabata wata murya yara taji ance "Mama Aciya juyo cigan ni nayi kyau?".  A hankali ta fara juyowa dan ganin mai maganar a tsorace. Koda idanunta sukayi tozali da mai maganar Aljanine yazo mata asuffar Iliyasu babban Dan hauwa. Kanshi a rabe yake gida biyu  hayaki ne ke fita da wani turiri a ko wanne bare.  Aisiya na ganin haka jikinta ya fara bari ta hau kyarma.  Dariya taji ya farayi marar dadin saurare. Ya nufo gunta yana fadin "Nayi Ceau (kyau) kuwa mama aciya(Asiya)?".  ta kwada ihu! Ta zuba guje ta nufi Downstairs tsabar firgicewa Bata iya kirga iya matatakalan da take tsallakewa. Sabanin 'da, da in zata sauka da Daya-Daya take yi a hakan ma a hankali.

Tana saukowa tayi wata uwar tirjiya a falo nauyin jikinta da kadan ya rinjayeta ta fadi.  Ba wani abu yasa ta tsayawa ba. Sai ganin wata yarinya da ke zaune a Falon cikin wasu fararen kaya masu dauke ido. Yarinyar ta juya bayane bata iya gane ko wacce ce. Hakan yasa ta fara matsowa a hankula tana kiran sunayen yaran gidan wanda take tunanin ko daya daga ciki ne. "Dan ubanki fatima me kike yi ne a nan?. Cikin wannan dare?". Shiru bataji amsa ba hakan ya tabbatar mata da ba fatimar bace. A hankali take tafiya tana nufar wajen da yarinyar take. "Ba fatim bace?. Shimsiya ce? Sa'adatu ce?. Ko dai salma ce?".  Sunan jikokin ta take ta jerowa wanda take tunanin ko sune.  Lokacin ta karasa wajen mika hannu tayi tana karkarwa kamar ta taba kamar karta taba. Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin..............,......```

TOFA MUJE ZUWA READERS.  YANZU ZAMUGA GWANAYEN TSORO. AN FARA KENAN

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boyπŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 21-22

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

IN DEDICATED TO ALL ZAMANI WRITERS. *ALLAH SARKI YAN UWANA UBAN GIJI ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR MU. A KULLUM GURINA INGA ZAMANI BA'A BARMU A BAYA BA. ALHMDULILAH KULLUM CIGABA MUKE. ALLAH YA KARA BASIRA, YAN UWANA DOMIN NI KAMAR YAYYAI NA NA DAUKE KU. AUTAN KU NE KING NA AUTAR KU QUEEN. ALLAH YA BARMU TARE YA KARA HADIN KAI. AMIN* ♥

.

               *KARSHEN PAGEN BAYA*
_Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin._
»» Aljanar a sufar shamsiya take, jikar Mama asiya hannaye biyu tasa da karfi ta shake wuyan dogayen faracen hannunta masu shegen kaifi. Bakin shamsiya wani bakin abune mai kaure ya fara zuba. Kuma idan ya zubo din a kan mama asiya yake sauka.  Mama asiya in banda ihu  da neman ceto babu abunda take. Da dai taga ba ko alamun mutane a gida wanda zasu kawo akaji.

Nan ta fara ihu tana kokarin kankare hannun Aljanar da ta makure mata wuya. Aljanar ce ta bude idonu hade da dakawa Mama Asiya tsawa. Ai kuwa fitsari ya fara zubowa harda dan guntun kashi da ya zubo.  Fitsarin matseshi take amma zuba yake tsirrr! Duk jikin ta karkarwa yake. Magana na rawa "Haba shamsiya dan allah ki sake ni karki kashe ni me nayi miki ne?, nice fa mahaifiyar babanki".  Mama asiya ce ke fadar haka.   "Keeeee!  Anji ke kika haifi mahaifina to ke kika haife ni ne ni?, Shin a yanzu ni dake waye baba ma?". Muryar mai kamar amsa kuwa aljanar ke magana da shi domin in tana yi dakin har wani jijiga yake yi.  "Wallahi kece, kwarai kece baba. Kece uwata ma. Kece ubana, kece yayana, kece yaya ta kece.....".  "Keee yimin shiru".  Gum Mama asiya tayi ta tsaya da lissafin kafafunta sai rawar karkarwa take fitsari kuwa duk sanda aljanar tayi mata tsawa sai ya subuce ya kwararo.   "Hahahhahahjahahhaha!

Aljanar ce ta dake kai sama tana wannan muguwar dariyar. Mama asiya ta dan shammace ta ta ware iya karfin da hannuwa biyu ta tura ta. Can aljanar ta fadi gefe. Tubur-tubur abu ga mai jiki ba gudun kirki, ta nufi hanyar Hawa sama, gaba daya wutar dakin ce ta dauke duf!  Mama asiya bata daina gudu ba saida ta hadu da bango kanta ta buda ji kake gum!! Ta kuma zube kasa kamar an yarda buhun gero thom!  Kanta ta dafe tana wash! Wash!  Aljanar ta gani tazo dai-dai saitin kanta da wata wuka wulshe-shiya a hannunta.  "Hahaha- wato ni zaki tserewa ko?. Wukuncin ki kisa ne". Da fadar haka ta daga takobin sama ta caka ma mama asiya a ciki.

Wani Mugun kara ta Saki ta tashi zaune tana nishi daya-daya tana laluba cikin ta jin ko da gaske ne abunda ya faru.  Karar da tayi ya tashi alhaji zumbur! Ya fara tambaya "lafiya-lafiya"? Sai yanzu mama asiya ta fahimci cewa mafarki ne take ganin cikinta lafiya lau kuma haka kanta bata jin wani radadi. Alhaji ni kam wallahi bazan yarda ba ashe yarinyar nan mayya ce da wuka fa tazo zata kashe ni a mafarki, wallahi sai na dauki mataki a kanta, to ni kuwa me na tsare mata ne take nema ta cinye kurwata danya".  Duk surutun da take alhaji binta yake da tambaya. "Wacece?, wai wace yarinyar".  Budar bakin ta tace "Wace yarinya kuwa in ba wannan mayar...". Ta dan dakata tana tunani in fa tace shamsiya abun bazaiyi tsari ba.    "Wace"?.   "Wannan mayar 'yar taka ce Fatima, duk taimaka mata da nake a rayuwa wai ashe mayya ce ni tazo zata kashe".  Tsawa ya daka mata nan da nan ya murtuke fuska, "Asiya bana san iskanci fa, bana san tambadar nan taki, kinje can kin tabo aljanunki sun motso shine zaki likawa marainiya wato. To wallahi kar in sake ji".   Gungune kawai tayi, Alhaji kuwa ya kwanta ya juya baya abunsa.  Mama asiya na zaune kamar ance ta kalli wajen mirror. Ihu! Ta kwalla ta rukun-kume alhaji kamar wacce zata shige jikinsa.  Yarinyar ta gani a cikin mirror tana kiranta.  Alhaji yana jinta ya kyale ta, can kuma saj yaji lema a jikinsa wanda yasan wannan ya wuce na gumi.

Tashi yayi yana "Asiya wai miye a jikinki nake ji sharaf!". Har tashin da yayi a rike take gam da shi idanunta a rufe. Wata mahaukaciyar dariya alhaji ya kwashe da ita, Irin wacce ya jima baiyi ba harda kama ciki. Asiya ido a rufe taki budewa tunani take in ta bude zata sake ganin aljanar, Jin dariyar alhajin taki ci taki karewa, yasata bude ido a hankali bata ko kalli wajen mirror ba. "Alhaji ai dole kamin dariya wannan mayar 'yar taka so take sai ta kashe ni ta huta".   "Asiya kalli jikinki fitsari ne fa kika sharara duk kin bata gadon, Hahaha wai duk tsoran ne haka harda fitsarin wando?".

Sai lokacin Asiya ta lura da jikinta sharkaf take ta jika kayan barci  da fitsari.  A kunyace ta tashi da sauri ta nufi bandakin da ke cikin dakin domin tayi wanka.  Bayan ta shiga ta juya baya tana kokarin Cire riga sai ji tayi wata kalar muryar 'Yan yara tace "Yauwa Shannunki da Juwa".   Da gudu ta fito daga bayan dakin taje ta fada kan alhaji ta shishige mishi. Alhaji na niyar tashi yaje ya canza kaya domin ta jika shi amma sam ta hana  ta rufe idanu ko budewa batayi.  A haka suka kwanta har safe. Tun da safe taje dakin su fatima ta iske ta ta idar da sallah tana barci, nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun................

Ku danyi hakuri da wannan  yaseen yau bana jin type din.

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 23-24

NA.  πŸ‘‘ KING BOY ISAH πŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU*

QUEEN HAUCY 😘 = *ILLAR BASHI*

BEAUTY QUEEN 😘 = *BADDEEYERH*

UMMU AFNANN = *FATIMAH*

ZUWAIRA MADADA 🍼 = *MATA DA MIJI*

MARYAM 'YAR MAMA = *RAINAN KAUYE*

BEIBOH = *YASMEEN*

😍 _DA KYAU JARUMAI NA ALLAH YA KARA BASIRA_

           *KARSHEN PAGEN BAYA*
~nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun.~
Fatima tace tayi sallah amma mama asiya bata barta ba saida tasakata kuka, "Shegiya mayya wato shine jiya kika zo zaki cinye ni ko. Harda wani canza suffofi ko kin dauka bazan gano kece ba". Faddausi ce ta farka jin kukan Fatima, "Mama asiya wallahi tayi sallah ita ta tayar dani ma".  Mama asiya tace to uwar iyayi ni ai ba bugwan  sallah nake mata ba, wannan yarinyar da kike gani mayyace ban taba sani ba sai jiya nima. A mafarki tazo min tana faman cinye ni, badan Allah yasa kurwata jaruma bace".  Fiddausi dai jinta kawai take yi tana mata kallan muguwa azzaluma domin tasan duk maganganun Mama asiya ba gaskiya a ciki.  Mama asiya ce ta dankwashi kan Fatima hade da cewa "Yi mana shiru munahika mayya kawai, ai yau sai kinci ubanki a gidan nan bara alhaji ya fita. Kuma yanzu ma ki biyo ni kitchen kina jina?".  "Eh gani nan zuwa'. Buzu-buzu mama asiya ta  juya ta fita bata jima ba Fatima ta bita baya,  Fiddausi tabi bayan Fatima da kallo tace, "Kaico 'yar yarinyar da baki wuce a goya ba amma tun yanzu kin fara shiga kitchen, Allah dai ya kawo miki mafita".   "Ameen". Fiddausi taji ance maganar ta fito daga saitin dan karamin gadan fatima ne, ganin ba kowa a gun  tsoro ya kamata da sauri taja blanket ta rufe tayi luff!. Kamar kullum yau ma fatima tasha wuya a kitchen bayan irin Aikace-aikacen da tayi ga kuma Mama asiya daga anjima sai ta rankwashi kanta tace "Mayya kawai allah yasa dai karki cinye mana 'ya'ya dan wallahi yarona daya in ya kamu da koda ciwan kaine ke zan bincika".

Dake Mama asiya tabawa sauran kishiyoyin nata labari suma sai suka hau tsangwamar Fatima da dukanta hade da bata aiki mai wahala, Wai suma kashedi suke mata karta kama musu nasu yaran. Ita dai Fatima ba abunda take sai kuka sai in sunyi maganar karta kama musu yara tace "Toh" al halin ita bata ma san miye wata maita ba. Sanda fatima tasha wuya sosai ta kuma yi kuka ba adadi kafin  a gama hada breakfast din. Bayan sun sako ta taje ta rungume 'yar tsanarta tana kuka. "baby na kiyi hakuri na barki ke kadai. Wadan can mugayen ne suka ta zalunta na".  Yar baby ce ta kama kuka nan Fatima tasa ta a kafada tana jijiga ta tana bata hakuri.  "Momy bayi inje in yama miki". Wata siririyar murya ce ta fito daga 'yar tsanar. Fatima bata ji tsoran komai ba. "A'a baby na kinga su manya ne ki kyale su. Allah zai saka mana, naji malamin islamiyar mu yace, duk wanda aka zalunta allah zai saka masa".  Yar babyn ce tace "To na fasa zuwa".    Yauwa yarinyata muje in miki brush da wanka tukun  inzo in miki kwaliya mai kyau".  Tana gama fadin haka ta warci 'Yar babyn da hannu daya ta je ban daki. (Wai aka ce 'Kuruci dangin hauka)  bayan fatima ta ajiye ta tace. "Haaa, bakinki", nan take bakin 'yar robber ya bude. Hakora ne reras! A jere fatima dake yarinya ce ba ruwanta batayi tunanin wani abuba. Ta sa brush ta fara gurzar bakin.  Tana farawa bakin ya fara jini. Fatima na ganin jini ta daka da gurzar bakin ta zuba ruwa ta wanke mata tukun tace, "Gaskiya mai shagon da muka sayo ki baya da mutun  ci kuma kazami ne duba fa yanda ya bar miki hakori suka lalace baya miki brush".  Aljanar ce tace "Ko sau daya bai taba min ba".  Nan dai fatima taci gaba da mata wanka suna hira. 

Kyauran ban dakin aka turo da karfi, Ameera ce ta shigo. "wai ke Fatima dan ubanki bana hanaki magana a bandaki ba?. Ko baki  san ba kyau ba?".   "Yi hakuri aunty wanka nakewa Baby na".  "Kutumelesi kaji 'yar banzar yarinya wato barnar ruwa zaki tarkarwa mutane ko, To daga yau sai yau kar in kara ganin kinwa wannan 'yar tsanar wanka kuma ma kawo ta nan, yanzun nan zan kona shegiya kowa ma ya huta, Kawo ta nace magana fa nake miki".  Fatima kuka ta kamayi tana boye 'Yar babyn a bayanta tana fadin "Dan allah aunty ki bar min abuna ina santa wallahi". Tsawa ameera ta daka mata wacce tasa saida ta firgita  matsowa tayi kamar zata mika mata kuma sai ta sulale da gudu ta ruga waje ai kuwa amira ta bita suka hau tsere. Ameera ta kusan kamata kenan. Fatima tayi wata zilliya ta Bi ta karkashin ameerar ta wuce, sai ji kake ameera Tum! Ameera tasha kasa. (SHI YASA BA'A SO BABBA YABI YARO, BA KYAU DAN IN BA'A CI SA'A BA SAI KA FADI. AKWAI WANI UBA DA YABI DANSA DA GUDU. A LAYI CIKIN JAMA'A YARAN YA KADA SA. YARO DA KAZA DUK KUSAN DAYA NE. WAYO AKE MASA AYI CHARAF A KAMA. IN MA KABI DA GUDU TO KARKA YI GUDU MAI NISa.) Fatima Direct dakin abbanta taje tana kuka yana ganinta ya bar abunda yake ya kamo hannunta. "Mamana zo nan waya taba min ke tun da sanyin safiyar nan?
Cikin kuka Fatima tace "Dady wai aunty ameera ce zata toya min Babyna wai kuma tace kar in kara mata wanka, yanzu ma da gudu ta biyo ni". Ran alhaji ne ya bace. Ya kama hannun Fatima yace muje gunta. A falo suka isketa tana wash-wash.

Alhaji  bai bi ta kan wash! Din da take ba ya bal-bale ta da fada hade da mata kashe karta kara shiga sabgar Fatima. Su Asmart ba rabuwar arziki sukayi da Mama sakina ba. Bayan tusar da suka ta banka mata da dare a daki kamar bodarai. Da asuba asmart ta tashi wai tea zata hada. Madarar da suka zuba su biyu ta wuce ka'ida domin saida shayin yayi kauri kamar wani koko.  Sakina na ganin haka basu gama sha ba ma ta kora su gida.  Da wuri suka je gidan lokacin ba'a kai ga cin abinci ba.  Tare da su aka ci sunci Sa'a ba wanda ya gayawa alhaji basu kwana a gida ba.  Bayan anci abinci an watse alhaji yayi musu salama ya tafi office.  Nan fa mama asiya ta kira Fatima suka mata dan banzan duka ita da sauran matan wai kashe ne karta cinye musu yara Mama asiya kuma na cewa karta sake biyota mafarki. Waje suka korata can Fatima ta koma bayan dakuna ta zaunar da  'Yar tsanar ta facing dinta tana kuka.  Yar babyn itama kukan ta fara.  Abun ya bawa Fatima dariya itama kuma sai babyn tabar kuka ta fara dariya.  Nan dai sukata wasanni.

Su Nasmat da asmart makaranta suka taho basu ma ko tsaya jiran su Fiddausi ba da sauran yara kamar da gaske suka yo sakko, alhalin kowa yasan ba karatun ba suke. A hanya Nasmat ke cewa asmart
"Ni fa wallahi yau mugunta nake ji, Dan haka yau kan mai Tsautsayi".  Dariya Asmart tayi      tace 'yar iskar karya kawai".  Nasmat ta bata rai, "Ke ce dai 'yar iskar karya. Amma ni yau muguntar ce kawai a kai na".      "Yauwa yanzu zamu kure mai cika baki". Inji asmart "Ga wani makaho can yana faman tsallaka rami jeki tunkuda shi in da gaske muguntar kike ji".   Jakar kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami...............

Ni kuwa nace Allah yasa aljani ne πŸ˜„πŸ˜ƒπŸ˜ƒ

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 25-26

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

_*IN DEDICATED TO 'YAN BOKO HARAM WA SOYAYYA TA.*_

*SHUGABAR TADA BOMB* πŸ’£ FATIMA. (DAUGHTER)

*MAI BADA UMARNIN KAI HARIN* πŸ’£ Hadiza hadi (Niger) 😑

*'YAR KUNAR BAK'IN WAKE* πŸ‘§πŸΏπŸ’£
Zuwaira (madara) πŸ˜‘πŸ˜”

_Kunci nasara kai harin da kukayi  babban birni  zuciya ta, inda kuka  kashe mutum uku Biyu kuma na nan suna zubar da jini. Shi yasa ma gaba dayan yau banda sukuni. Kuma yaseen wuta Bal-Bal_ 😑

πŸ’¦ QUEEN HAUSYπŸ’¦

I love you too much.
You kill me with you love 😘

  *KARSHEN PAGEN BAYA*
_Jakar kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami._

»»Irin tsofafin almajiran nan ne, yana yunkurin tsallaka wani rami ya kasa. Nasmat na zuwa kamar wacce zata taimaka mishi dan har magana sai da tayi mishi. Sai da ta duba ko ina taga ba mai kallan ta kawai ta ingiza shi cikin ramin,  suka ruga a guje ita da asmart suna waigen sa suna mishi dariya. "Wannan wane irin yara ne da mugun hali haka, yanzu ina fama da kai na ki zo ki hankada ni rami salon in Karashe naka shewa ko, Jeki Allah ya isa. Allah zai hada ki da gaman ki kema".   Basu ce mishi komai ba gaba suka kara suna ta jan fada har suka isa makaranta. Malamin na ganin su ya murtuke ya bata fuska, "Kai ku zo nan dan ubanku, yau sai kun gaya min ubanwa ya daure muku gindi, yanzu karfe Goma zaku shigo aji".  Gaba dayan su gunguni sukayi, kamar ba su ya kira ba suka nufi bench suka zazauna. Kowa ta fiddo al'qura'ani kamar da gaske karatun zasuyi. "Kai wai ba da ku nake magana ba?".  Nan ma basu tanka mishi ba. Abunda ya fusata malam Dalhat kenan,  Ya nufo su da zureriyar dorina.  Shaf! Shaf!  Kake jin karar dorinar da karfi yake dukan su. Bayan yayi wa ko wacce daga cikin su dorina biyu, A ta ukun Nasmat ta Rike bulalar tare da mike wa tsaye.  "Malam ya ishe ka haka". Asmart ta fada ido cike da kwalla.

Cikin kuka-kuka Nasmat tace, "Ki kyale sa yaci gaba Wallahi ya sake dukana sai na mishi abunda bai yi zato ba". Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar malam ya saki baki yana kallan su, a zuciya yace, 'Ashe rashin kunyar nan ta su da ake fada har ya kai haka, Ni kuwa zanyi maganin ku".  Bulalar ya fizge da karfi ya fara zafga musu kan uwa da wa bi, da gudu suka fita har suna bankade muta ne. Ko laidar Al'quranin ba wanda ya dauko a cikin su.  Ko wacce hawaye ne shabe-Shabe a fuskarta Asmart na cewa, "Wallahi bazan yarda ba dole sai na dauki mata ki, chabb! Lalai wannan malamin bai sani ba ne".  Nasmat ta ciji labe. "Hmm kyale sa wasa yake damu".  Cikin gari suka shiga yawo gida jen kawayen su, sai da suka Dai-Dai ci lokacin tashi a Islamiyya yayi tukun suka koma gida.

Shigar su gidan suka tarar gaba ki daya mutanan gidan sun fito ana faman shiga motoci, da sauri suka karasa suka tamabaya ina za'a je, Mama asiya tace, "'yan gantali har kun gama iskancin kun dawo ko?, nasan dai ba makaranta kuka je ba, kunga Wallahi ku kiyayi rayuwa gwara ku tsaya ku mayar da hankali kuyi karatu, Ni kai na yanzu haushi nake ji da bansan komai ba a karatun Alqur'ani  kuma kuma nasan ko Fatiha cikin ku da kyar in da wacce zata iya kai wa dai-dai".   Kallan juna sukayi hade da sosai kai Asmart tace, "Mama asiya ina zuwa?".   "Au! Har kun manta yau bikin Haleematu?".  Wani irin tsalle Asmart tayi "Ashe yau ne".  Kokarin shiga mota ta farayi aka hanata, Akace sai taje ta canza kaya. Da gudu taje ta canzo Ko kwalliya batayi ba tazo ta shiga mota. Nasmat kuwa tana guri   A tsaye ta wani bata Rai. "Ke bazaki je bane? Kowa na gidan zashi ko har yanzu 'yar banzar gabar nan ta rashin hankali kuna yinta ke da Haleema?".  Zuwaira ce tayi wa Nasmat magana. "Allah ya sawa ke inje gurin  bikin haleema, Ai ko mafarki nayi naje wajen sai na farka kuma in na farka sai nayi sadaka".     Juwaira bata ce mata komai ba t shiga mota. Motoci biyu ne cike. Har sun fara tafiya. Asmart ta leko. "Yauwa nasmat ban gaya miki ba. Wannan tsinaniyar yarinyar tana can tana mana wasa da kayan Makeup wai tana wa 'yar tsanarta kwalliya. Kije kici ubanta dan Allah".   Tun asmart bata karasa maganar ba Nasmat ta zungura da gudu ciki  gidan.

Direct dakin su ta nufa, tana zuwa ta shako wuyan Fatima ta baya ta fara gallah mata mari. Fatima kuwa ta hau kuka da ihu!, "Wato ke dan ubanki 'yar baby kike wa kwalliya da kayan mu ko".   Fatimar hakuri take bata amma taki ji sanda ta mata lilis! Kamar yanda ta fada yau 'yan  muguntar ne a kanta.  Kunnan Fatima ta kama tana ja. Ba arziki Fatima ta ringa binta tana rike kunnen dan karta ji mata ciwo.  Sai da ta kai ta har kofar gida, mai gadi  duk da yana tsoran alhaji sai da ya bude kofa domin yasan Bala'in Nasmat Da Asmart. "Dan ubanki bazaki zauna a gidan ba, kuma Wallahi in kika tafi wani waje na fito waje naga bakya nanto kema kin dan sauran".  Nasmat ta juya zata shige gidan Fatima ta riko kafarta "Aunty dan Allah ki bani baby na to".  Hararen ta tayi ta kuma sa kafa ta haure ta can Fatima ta fadi tana kuka.  "Bara inje in yan-yanka babyn dan ubanta itama ke da ganinta sai a lahira in 'yar Tsana na zuwa".    Wani kukan Fatima ta ci gaba da bada wa amma Nasmat bata saurare ta ba ta shige cikin gida ta bar Fatima nan tana kuka.

Mai gadin ganin yau gidan ba kowa kuma yana da 'yan uzuririka shima. Fitowa yayi har zai wuce kuma sai ya tuna Fatima na kofa karta shiga, Katan kwado ya koma ya daukko ya zo ya garkame gidan. Yayi tafiyarsa.   Nasmat a fusace ta shiga ta daukko 'yar babyn ta nufi kitchen da ita. Wuka ta dauka mai shegen kaifi ta fara dada rawa a jikin Robar amma ko kayan dake jikin babyn sunki ko bancile.  Canza wukar taje tayi a cewar ta ba kaifi ne.  Fara da dara wukar ta ke da wuya aka fara knock din kofar kitchen din da karfi abun  kamar za'a balla.  Ta dan tsorata kuma sai ta jure. "Uban waye?".  Shiru ba'ayi magana ba. Jin anyi shiru yasa taci gaba da abunda take yi.  Ganin wuka taki ta kama babyn ta dauko galan din kalanzir ta ajiye babyn a kasa ta jike ta sharaf! Tukun ta dauko ashana. Zata kyasta kenan.  Wani mugub karan buga kofa ya kara dakar mata kunne. Ba  tsoran koma Nasmat ta daka ashar, hade da cewa"wane dan ku... Uba ne? Mai gadi nasan kai ne wallahi in na fito ni da kai ne".   Bata rufe baki ba aka kara bubugawa wannan karan harda murya ta mai gadi sak! Da yace "Ki buuuudeeee".  Abun ya fusata ta jin muryan mai gadi. Ashanar ta kyasta!  Ta wula wa yar babyn  nan  take wuta ta kama ta fara ci.  Tana ganin haka farin ciki ya kamata tayi mugunta.   Saura kai mai gadi ta fada lokacin da ta nufi kofa rai! A bace domin har yanzu bugawa ake. Tana bude wa taga wayam, bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa. Kofar dakin su tafi an rufo garam. Alamun wani ne ya shiga...............................

🀣🀣🀣 *Yau wata zata ci uban ta. Na tausaya mata.lolz*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 27-28

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

_*IN DEDICATED TO ALL ALJANAR FATIMA FAN'S. INA JINJINA MUKU NA YABA DA IRIN KAUNAR DA KUKE WA BOOK DIN. SANNAN INA BAKU HAKURI MASU KORAFIN PAGE YANA KADAN WALLAHI I'M BUSY. KUCI GABA DA HAKURI. IN DA JIRGIN SAMA YAJE HAWAINIYA MA TAJE IN DAI ZA'A LALA BATA. LOLZ*_

*KARSHEN PAGEN BAYA*
Tana bude wa taga wayam, bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa. Kofar dakin su tafi an rufo garam. Alamun wani ne ya shiga..

»»Kofar dakin ta nufa cikin fushi tafe take da sauri rai a bace, tana zuwa kofar dakin tasa hannu zata bude kenan wani makeken kadangare irin mai jan kan nan ya fado mata a kai. Wani mugun ihu ta saka, ta fara tsalle-tsalle tana zagaye katan falon tana zazage-zazage da Kara  duk ta dauka yana jikinta ashe ya fado tun tuni. Ta dade  tana yi sai da ta tabbatar baya jikin nata tukun ta dan saki jikinta  ta hau dube-dube.  Bata hakura ba kofar ta sake tun kara da niyar ta bude wannan karan ma kadangare ne karami ya fado mata wannan karan cikin riga ya shigar mata. Nan ta fara ihu ta fadi kasa tana ta mirgine-mirgine. Kadan garen ya fita. Tashi tayi zaund tana Raraba idanu.  A zuciya tace "to wai me ma ya kawo kadangaru falo?".Kuma Wallahi sai na shiga dakin".  A fusace ta tashi sanda ta dai-dai ci kofar dakin tukun ta zura a guje. Ta bankade kyauran ta fada karfin gudun nata ya rinjaye ta ta fadi sauran kadan da ta yi karo da katanga.

Suman tsaye tayi a gurin. Dan ganin wani make ken maciji da ya fasa kai yana layi da kai. Nasmat ta san tana matsawa a gurin sai ya sare ta.  Karkarwa ta fara yi sai hawaye sharr! Kuka wii! Wii cikin kukan da take tana ihu!  "Wayyo mama na na mutu na lalace, dan Allah maciji kayi min rai kayi min aikin gafara, Wallah bazan kara Fashin sallah ba, kuma Wallahi bazan kara fashin zuwa makaran ta ba".  Ihun take tana ta zuba Surutai! Da rantse-Rantse  macijin ne ya dan kara bude kai nan take yana zaro harshe yana mayarwa. Kara tsurewa tayi da taga macijin yana kara matsowa a hankali. Tsoranta ne ya karu ta fara ihu! Tana karkarwa.  Sululu macijin yaje ya fara hawa kafarta. Tana jin haka sai fitsari Sharr! Gaba daya ta jika wajen. Sannan tayi tsaye cik kamar gunki ta rufe ido. Har yanzu dai macijin hawa kanta yake. Jima kadan taji baya nan. Bude ido tayi can ta hange shi ya shige ban daki su.  Da gudu tayi waje ta zo dai dai falo kenan wuta gaba daya ta dauke, dama nefa ce. Duk da rana ce amma bata iya ganin gabanta. Juye-juye ta fara yi tama rasa ina zata nufa. Ji tayi an shafe ta ta baya an wuce. Wani razana nan kara ta saki "Wayyo!" Cik kuma ta tsaya waje daya duk da bata gani amma tana jin motsi kamar mutum ya nufo inda take. Abunda ya taho din tana jin karar tafiyan saura kadan ya kara so gurin ta sai aka dawo da wuta.  Wani gwabran nun fashi ta sauke nan ta du duba amma ba komai a gun. Kan armchair ta zauna tana nunfashin wuya. "Wash! ni Nasmat yau naga bala'i wannan katan maciji idan ya sare ni ai in ana Wuce lahira ma sai na wuce".

Sukur-sukurtu taji a baya da sauri ta juya Taga ba komai, hahhahahh!  Dariya tayi da kanta tukun tace, "Lalai yau na tsorata".  Yar baby ta tuno da sauri ta tashi ta nufi kitchen domin gano ko ta idasa kone wa?.  Tana bude kyauran Kitchen din tayi tsaye hade da Zurawa guri daya ido, mamaki ne karar ya bayyana a fuskarta. Ganin yar babyn gata nan  a kwance inda ta yarda ta amma ko alamar an jika ta da kalanzir babu balle ma Wuta.  "Kai!, ban gane ba nafa kona wannan abun kafin in fita. To ko bata jin wuta na?. To amma bari inga a gaba na zan kona ki yar iska".   Galan din gas ta dauko a wannan karon  ta bul-bulawa yar babyn ta kyasta asha na ta wulla mata. Nan take wuta ta kama bal-bal farin ciki ne  ya lulube ta domin yau mugunta ce fal! A ranta. "Kyal-kyal-kyal-kyal, hahahahahahaha, hihihihijijhehehehehrhr". Sautin wata iriyar mahaukaciyar dariya ce da ke fitowa daga falo ya daki dodan kunnan Nasmat da ke tsaye itama tana kallan yar babyn tana dariyar mugunta.  Kofar ta bude a hankali ta Leka, fatima ta hanga zaune kan kujera ita ce mai uwar dariyar nan.  Nasmat na ganin ita ce sai ta bata rai ta Idasa fitowa..

Ishar ta maka. "Fatima ku....banki".  Shiru Fatima tayi ba tare da ta wai-wayo ba, Cikin sauri Nasmat ta karasa gurin tana zuwa kuwa ta Falle Fatima da mari ta baya. Gugur-gugur kai ya fadi kasa ya fara taya jini na fita a jiki. Gangar jikin ma Kasa ta fadi jini ya fara malala. Hannuwa biyu Nasmat ta dora a kai ta maka wani uban kara, Ta nufi gurin gangar jikin fatima ta rugume ta a kirji "Wayyo Allah na na shiga uku na lala ce, Fatima Wallahi ba kashe ki nayi niyar yi ba. Dan Allah ki tashi yanzu in su momy suka zo me zan gaya musu, Yau na shiga uku".  Kuka take sosai ba kukan rashin Fatima sai kukan rashin abunda zata ce.  "Ai da raina ban mutu ba Sake ni".  Gangar jikin Fatima ce ke magana. Shiru Nasmat tayi ta tsurawa Wuyan da har yanzu jini ke zuba ido.  Domin taji kamar daga nan taji magana  sai dai bata tabbatar ba. "Ni ki sake ni nace". Wata murya ce a shagwabe ta fadi hakan. Kafin a karasa maganar tuni Nasmat tayi wulli da gangar jikin Fatima din tayi hanyar kitchen a guje kamar wacce zata tashi sama. Gangar jikin tsaye ya tashi ya je ya daukko kan ya riko a hannuwa biyu A hakan Fatima ta nufo Nasmat da ke can bakin kofar kitchn tana kokarin bude wa amma kofar ta ki bude wa. Fatimar tana fadin "Aunty nasmat mayar min da kai na- mayar min da kai na".  Kuka ne ya subuce wa Nasmat tana tura kufa tana waigen baya tana fadin "Wayyo Allah momy na".   Gangar jikin Fatima ya kusan karasowa kenan kofa ta bude. Har Nasmat ta zura kafa zata fada kuma sai taja birki.  Yar babyn ta gani ta nufo ta tana kuka ga wuta na cin jikinta kuma hawayen jini ne ke fita a idanun ta. "INNAHU MIN DAUDA WA, INNAHU MIN SULAIMANA, WA BAZAN KARABA NA TUBU KU YAFE NI".Da karfi Nasmat din ke fadar haka tana karkarwa. Da dai taga wannan ba mafita bac...........................

AYI MIN AFUWA BUSY YASEEN

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 29-30

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

PAGEN YAYI MIN DADI SHIYASA NA BAWA BEST FRIENDS NAWA.

Usaini atk 80k

Shamsuu Bin Yerhyer

Mustpha Rogo

Abdul King Article

Musa Umar Abdullahi

Shatu muhammed

Aisha adam

Ahmed tijjaniyu

*HAKIKA KU MASOYA NA NE NA GASKIYA, KUNA A SAHUN GABA CIKIN MASOYA NA. INA GODIYA DA BIBIYAR LITTAFAI NA DA KUKE ALLAH YA BARMI YARE.*

Nasmat a guje ta bar wajen nan suka hau zagaye falo. Gangar jikin fatima dauke da kanta a hannu jini na zuba tana bin nasmat di  tana fadin "Auntu dan Allah ki tsaya ki samin kaina". Fadi take tana maimatawa tana biye da nasmat din. Haka itama bangaren yar babyn bin Nasmat take tana fadi  "Aunty  kashe min wuta wayyo! Wuta na cina".  Gaba daya sun zagaye falon sun mishi kaca-kaca da jinin da ke zuba.  Nasmat abun ya zame mata biyu ga tsoro ga karfin maganar tasu har cikin kwalwarta, Ta dai fahimci wannan so suke su Haukata ta. Allah ne ya bata sa'a ta ta nufi kofar fita a falo tana kamawa kofar ta bude da sauri ta rufe kofar ta jingina da kofar tana shasheka.  Hamdala ta farayi a nufin ta ta rabu da su.  "Aunty ki kashe min wutar".  Wani uban kara ta daka "waaaaaayyooooo Allah na"  ta runtuma a guje tana kiran me gadi. 'Yar babyn ta bita baya Nasmat dakin mai gadi ta leka shiru ba kowa. Nan taje ta fara kokarin Bude kofa taji a garkame da kwado.  Juyowa tayi ta zube a kan  gwiwoyin ta tana bawa aljanar hakuri.

"Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, daga yau bazan sake takurawa Fatima Allah wallahi tallahi na rantsi da uwata da ubana ku....."   "Kheeeeeeeee! Yi min shiru,  muguwa kawai azzalumam".  Cikin wata iriyar murya mai karsashi da ban tsoro Aljanar ke magana.  "Daga yau sai yau idan har na sake ji ko gani kin wa Fatima ko harara, ki san da sani dan Wallahi sai na taba lafiyar jikin ki, kina jina?".    Da sauri "Eh naji *ALJANAR FATIMA* daga yau Wallahi na dai na".   Wata dariya 'yar tsanar tayi mai ban tsoro wanda kasa kanta girgiza take kamar jirgin dan kara zai tashi.  "Oya to dauke ni kije ki min wanka da kwalliya".   Zaro ido Nasmat tayi ta kara make wa a jikin gate din dan tsoro. "Keeee! Ba dake nake ba".  Jiki na karkarwa Nasmat ta taso kamar bata san tafiya hannun na karkarwa ta dauki 'yar tsanar ta wani mimike hannu kamar wacce ya dauki abun kyama. "Au! Kyamata ma kike oya Rungume ni".  Nasmat kamar ta fashe da kuka a mugun tsora ce take.  A haka taje tayi wa yar babyn wanka a tsorace Sai da 'yar babyn ta bata wuya sosai a wajen wankan. Domin sai nasmat na mata wanka ta zuro hannu ta kama hancin ta ja da karfi, ko kunne.   Nasmat sai dai yi kara kawai.   Bayan gama wankan aljanar tasa Nasmat ta zo tayi mata kwalliya ta dauko akwatin ta tasaka mata kaya masu kyau.

"Yanzu abunda nake so shine ki dauke ni ki kaiwa Fatima kice mata dama wanka ne zaki mini, karki yarda kice mata nayi miki wani abun kina jina".  Da sauri ta amsa "Eh zanyi hakan aunty aljana".  Nasmat ta fada murya na karkarwa.   'Yar tsanar tasa dan guntun hannunta ta wanke Nasmat da mari. Da sauri Nasmat ta dafe kunnu domin zafin marin. Kuka ta fara wii!-wii!  Harda hawaye.  Tsawa aljanar ta daka mata. " Rufe min baki, Ki kira ni da *SAFURATU*  KO  *ALJANAR FATIMA* In kuwa ba haka ba zaki san da sani".  Gum Nasmat ta kame baki duk da kukan yaci karfin ta sai dai ba yanda zata yi aljana ta saka ta gaba. Hawaye ne kawai ke zuba a idanunta. "Muguwa ashe mugunta ba dadi kuke cutar marainiyar Allah kaf! Gidan nan banda alhaji da fiddausi ba wanda zan saurara wa sai na dauki mumunar mata ki a kanku.  Sannan yanzu abunda nake so shine. Bayan kin kaiwa Fatima ni ku wuce gidan baki da ita kina jina"?.   "Eh", farin ciki ne  ya ziyarci zuciyar Nasmat domin kuwa abunda take so kenan Taji maganar mugunta. Aljanar tace sai taci uban kowa a gidan.  Daukar 'yar babyn Nasmat tayi ta fita da ita anyi sa'a kuwa lokacin mai gadi ya dawo, Wata muguwar harara ta galla mishi lokacin da ta zo giftawa. A zuciya tace "Mugun mai gadi ko hada kai ma aka hada baki, Wai dan kuu... Uba sai yanzu zai dawo bayan na shiga tarkon Aljanah".

Kwance suka Tarar da Fatima a kofar gida sai sharara barci take ta gaji da kuka.   Nasmat rike da 'yar tsana a hannnu wacce duk sanda ta kalle ta bata marmarin karawa don irin hararen da take aiko mata. A hankula ta tayar da Fatima ko ita Fatima tayi mamaki abunda bata taba gani a gun aunty nata ba kenan. Ko Nasmat taga mamaki a fuskar Fatima a zuciya yace "Yarinya wuya ce mai saka kafuri sallahr dole".   Kallan Fatima tayi Cikin fara'a "Fatima Ga 'Yar babyn ki dama fa wanka ne zanyi mata. Yanzu tashi zakiyi mu tafi gidan biki".  Fatima cike da Zumudi ta karba "Na gode aunty na tayi kyau sosai. Amma mama asiya tace baza'a je dani ba".   Murmushi Nasmat tayi, "Karki damu baza ta ce komai ba ai dani za'a je".  A zuciya kuwa tace "Yarinya ai ko Mama Asiya taga bala'in da na gani dole ta tsure ta amshi duk wani umarni ko da ta san bazai yuyu ba".  Fatima tace to "muje muyi wanka ko Ko aunty?".  Nasmat kallan Aljanar tayi irin kallan da babyn ta watso mata ya nuna mata alamun bata yarda da wannan ba.  "A'a 'yar kanwata ai sai mu makara tashi muje nima ko uniform bazan cire ba". A hakan kuwa Nasmat ta tsayar musu da napep suka hau. Har yanzu jikin Nasmat bai daina Rawa Ba.  Allah-Allah take su sauka ta bace musu a gidan  biki ta rabu da bala'i.  Ba'a jima ba suka isa kofar gidan.  Nasmat ta shiga gida kenan domin ta karbo wa mai Napepk kudin sa ta bar fatima nan rugume da babyn ta.
Wasu 'yan mata ne suka zo wuce wa, Idan daya ya kyalla kan yar babyn Fatima hakan yasa tace wa abokiyar tafiya. "Laaaa! Kawata dubi wata 'yar tsan mai kyau muje mu ganata". Suna karasa wa gurin hadiza ta warci yar babyn ta maka ta da kasa tasa kafa ta taka.  "Haba kawata wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke d..,.". Tasss! Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun...........................

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 31-32

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

😘 *WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA LITTAFINπŸ‘‡πŸ½

πŸ™†πŸ»‍♂ *'YAR AIKIN GIDA NA* πŸ™†πŸ»‍♂

*SHAZEE* Allah ya karo basira Aljanar Fatima taji dadin kyautunan pages da kike bata hakan ma yasa ta tasa ni gaba a kan sai na baki wannan.  πŸ™Š Yauwa kuma ina so muyi sirri a bani number hafsat zan aike ta wajen BOKA MAI KWARAN GWAL! 😜 .lolz

πŸ‘πŸΌ *BADA HAKURI* πŸ‘πŸΌ

Masoyan littafin nan ina baku hakuri bisa rashin jina da kuka yi jiya. Naga sakonin ku da masu kira na. Na gode 😍 I luv yhuu All my fans. 

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Haba kawata wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke d..,.". Tasss! Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun.~

»»Dafe kumatu tayi, "Kai! Kai! Kai! Kut...uba yau za'ayi bala'i  a wajen nan wato dan na yarda wannan tsinanar 'yar tsanar shine zaki mare ni ai kuwa bazan taba yarda ba". Kafin kawar tata tayi magana tuni hadizar ta wanka mata mari. Nan  fa sukayi hau kunce. Fada ya kace ba. Duk abunda yake faruwa a kan idan Nasmat Ita kuwa tasan abunda ya hada fadan hakan yasa ta kyalkyalewa da dariya harda rike ciki.  'Yar tsanar ce ta mata wata iriyar harara wacce tasa bata shirya ba ta dakata da dariyar.  A hankali taje   taba wa mai adai-daita kudinsa tace wa Fatima "kinga dauko 'yar babyn ki mu shiga ciki".  Da sauri Fatima ta share hawayen da suka fara zubo mata. Ta dauko 'yar Nasmat ta kama hannunta suka shiga ciki. Safuratu ganin sunki rabuwa da fadan ne. Ta zo ta fara kan uwa da wabi. Mari sai dai kaji kara tass! Tass an rasa  daga ina yake fitowa.  Ba arziki suka rabu da gudu suka bar wajen domin sun maru ba laifi. Da shigar su Nasmat falon. falon suka iske mata ne damkam a ciki su mama asiya suka fara wurgo mata harara,

Umma ce ta taso wacce itace mahaifiyar Haleema da ake wa auren kuma yayar Mama asiya ce. Yanayin jikin su da na asiya duk daya itama yar lukuta ce. "Nasmat ke wacce irin doluwa ce?, Da zaki taho mana da wannan marar jin yarinyar. Ko zaki zo ai bai kamata ki zo mana da wannan ba, Ke kinsan cewa jina na ko kadan bai hadu da wannan kazamar yarinyar ba".  Umma ce ke fadar haka.  "Umma ni gani nayi an barp ta a gida ita kadai shi yasa ma nace ta taho mu tafi. Mama asiya ce ta taso tubur! Tubur!  "Kanwar uwarki ce ita din  da zaki ji ba dadi dan an baro ta a gida.  Dallah fidda muna ita waje kuna ji daga shigowar ta har ta dumame falon da wari".  Umma tace "Zo nan kawo 'yar babyn nan dan ubanki daga yau ta zama ta khaleel". Warce diyar tayi ta mikawa wani marar jin yaron ta dan lukuti.  Fatima kuwa ta fashe da kuka ba komai yasa ta kuka ba sai kwace mata 'yar baby da akayi.  Wani mugun dadi ne ya ziyarci zuciyar Nasmat ganin abunda su Umma suka aika ta, domin yau cikin mugunta take. Waje Fatima ta koma ta sama wani waje ta zauna ta saka kanta tsaka nin kafafunta tana kuka a hankali. Nasmat kuwa tasan amare suna sama kuma tasan Asmart ma na can amma ta tsaya kawai so take ta ga abunda zai faru.   Khaleel ana bashi 'yar tsanar waje yayi da gudu. Wajen wasu marar jin abokan nashi yaje. Suna ganin ta kuwa wani daga cikin su ya rugo da gudu ya dau ki wuka wai yanka ta zasuyi. Sai da aka kwantar kamar dan akuya wukar kawai zasu dora nan take ta fara girma kafin su ankara tuni ta koma make kiya  abun tsoro.  Rugawa sukayi da gudu khaleel ne rike da wuka sai ya daga kai yake kallanta shi yaki rugawa.  "Yanka ni mana khaleel".  Abunda take fada tana mai-mai tawa  kenan  nan take tsoro ya ziyarci khaleel din karkarwa ya fara bai ankara ba yaji saukan bulala.

Gudu yake yana kuka hade da soshe-soshe yana kiran uwarsa. Daga ganin sa kaga  wanda ake bi ina zane wa sai dai in ka duba baya babu wani wanda yake biye da shi domin  aljanar a bace take. A million ya shigo gidan Nasmat na jin kukan sa a tsorace ta ruga a guje bayan mama  Asiya ta wani makal-kale ta. Khaleel ne ya shigo yana kuka Da sauri Umma ta tashi ta tarye shi "Auta na lafiya, auta lafiya". Bayan ta ya boye yana nuna hanyar waje matan da ke falon duk suka dubi gurin ba komai.  Da sauri ta juya tana jijiga da gani kasa  bala'i ya tashi. "Waya taba min kai auta fada min ko uban waye wallahi sai naje naci mutun cin sa, fada min waye". Cikin kuka yace "Yar babyn Fatima ce".  "Kai bana san shirme fada min waya dake ka". Amsar da ya kara basu kenan *"ALJANAR FATIMA* Ce".  "Ok kwace ma tayi kenan bari inzo". Buzu-buzu ta fita a waje ta sama Fatima rike da 'yar babyn mari ta wanka mata, "Ke dan ubanki in bawa yaro na abun yayi wasa shine zak kwace, kawo ta dan uban ki" warce wa tayi ta koma ciki Fatima kuwa kuka ta kama yi domin ita dai a iya saninta taga Khaleel ya wuce yana kuka bai dade ba kuma taga ya fito ya kawo mata yar babyn ta da kanshi.

Umma na shiga da 'yar tsanar Nasmat tayi wani mugun tsalle a firgice ta fada bayan kujera A tsorace tayi muky! Tana saurare su.  Khaleel na ganin Umma ta shigo da yar babyn ya kara fashewa da kuka ya ruga a guje ya makal-kale Mama asiya kamar zai shige jikinta. "Bana so! Bana so! Karku kawo ta". Abunda khaleel din ke fada kenan ganin  uwar tasa bata daina nufo shi da yar tsanar ba ya sa ya tashi ya zuba a guje sama.

Rike baki Umma tayi "Ah! Ashe tsoranta ma yake har na wani bashi. Komawa tayi daga bakin falo ta wurgawa Fatima 'yar tsanar  "Dauki tsiyar ki gata nan tsoranta ma yake yi".  Fatima cike da farin ciki ta bar kuka ta dauki abunta ta rungume. Masu dafa abinci ne suke ta zuzubawa sun karasa kowa sai dai ya zo ya dauki nasa da na 'ya'yansa  Fatima najin yunwa tsoro take taje ta dauka  ga abincin a Take away amma tana tsoro a mata fada. Yunwa ta kai mata karo koma taga har yara na zuwa dauka ba'a hana su hakan yasa itama ta tashi dugwi-dugiw ta nufi wajen da aka jera take away din.  Tasa hannun zata dauka kenan, taji an daka mata tsawa sai da ta zabura firgi-git "Keeee!  Dan ubanki waya baki izinin ki zo nan balle ma har ki dauki abinci?".  "Dama-dama yunwa nake ji mama asiya". "Kinci ubanki maza wuce idan anyin sauran abincin shi za'a baki". Magana tayi wa masu dafa abincin tace kar wacce ta yarda ta bawa fatima abincin in kuwa wata ta bata sai ta hadu da fishinta. Tana gama fadar haka ta dauki abincin guda uku ta nufi falo. Gaba daya hudun ta saka gaba da niyar ci. Lomar farko  ta na kai wa baki ta zubdo da sauri. Nan take kowa da ya kai abincin baki sai ya zubdo saboda masifafan gishiri da ke cikin abincin duk wanda ya kai baki sai yaji kamar dai gishirin ne yayi loma da shi.  Ran jama'a ya baci hakan yasa sukayi tururuwa suka wa masu aikin abincin caaa! Kamar zasu cinye su dan masifa. Mama asiya ce ta juyo ta kalli Fatima mugunta ce ta motso hakan yasa ta dauki abincin daya tana murmushi "Fatima to ga abincin ci ko".  Da sauri Fatima ta karba domin masifar yunwa take ji.  Loma ta fara kaiwa hannu baka hannu kwarya. Gaba dayan matan gidan kallanta suke suna dariyar mugunta, Ita dai fatima kallansu take ta rasa me yake basu dariya domin kuwa ita lafiya lau take jin abincin da dadinsa. Wata tsohuwa ce ta shigo gidan bara sanye take da bakar hijab doguwa har kasa, fuskarta duk a tatabe.

Bara tayi da farko suka ce hakuri kamar hadin baki. Ta kara nan ma suka bata hakuri. Kamar bata ji ba a karo na uku ta sake yi musu bara. "Masu gida a taimaka min da abinci ko kanzo ne ko saura in sama abunda zan zuba a ciki na rabo na da abinci tun jiya".  Sauran muta nan ne suka fara balbale ta da masifa Umma tana murmushin mugunta ta dauko abincin har guda biyu ta sa tsohuwar ta zauna. Ta bata abincin suka koma gefe dan suyi dariyar mugunta. Lomar farko tsohuwar ta zubdo tana  kakarin amai.Dariya suka hau kyakyatawa kamar me. "Haba bayin Allah ya zaku bani abincin da zai kashe ni wannan abinci ko gishiri".   Asiya ta taso cike da masifa kamar zata hade tsohuwar. "Kinga tsohuwa bama san ciki da rashin mutunci da rai nin wayo, Dan kutu....uba  ba sao da aka baki hakuri har sau  biyu ba kika ki hakura kuma yanzu an baki shine zaki wa mutane tsiya".  Cike da Tsokala da tsiya mama asiya ta juya "Jama'a ku karo mata Takeaways uku ta kara ta kai wa jikokinta".  Gaba dayan gidan dariya suka hau yi mama asiya harda dukawa tana Rike ciki.  Dagowar da zatayi taji saukar mari ya bada sauti. Tasssss! abunda ya dakatar da dariyar jama'a kenan.  Hannu Daya mama asiya tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin ba komai a gurin tsohuwar ta bace.Saukar  Bulala  taji a bayanta...................
....

Yau wasu sun dauko ruwan dafa kansu. 

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 33-34

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

😘 *WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA MOMCY DIN MU.  MUNA SANKI MUNA KAUNAR KI. MUNJI SAKON KI A BAKIN 'YAR UWAR MU,
QUEEN MEARYAM ('YAR MAMARMU)*

       We love you too♥
   BY ALL ZAMANI WRITERS.

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Hannu Daya mama asiya tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin ba komai a gurin tsohuwar ta bace.Saukar  Bulala  taji a bayanta...~

»»Da sauri ta fara so sa baya tana ra raba ido.wata bulalar aka zubga mata wacce tafi ta dazun ma zafi abunda yasa ta rugawa tubur-tubar cikin jama'a tana ihu! Kenan duk. Aljanar binta take tana zane wa tuku  ta koma kan uwa da wabi, domin kowa duka take ai kuwa gida ya hargitsa mutum.na tsaye ko yana gudu sai dai yaji saukar bulala. Haka suka fara rantar ta kare suna yin kofa, Nasmat na jin gida ya hargitse ta kwashe da dariyar mugunta domin tasan (A rina, wai an saci zanin mahaukaciya) Wata mata ce aka biyu da gudu ta shigo dakin, karan bugo na tashi amma ba ka ganin mai dukan. Nasmat na ganin haka tayi wani juyin da bata shirya ba. Da gudu ta nufi saman bene (upstairs)  ai kuwa matar ta biyo ta tana ihun neman ce to. Nasmat na ganin haka ta kara wuta. Tana karkarwa ta fada dakin da amaren suke ta turo kofa, Tayin saurin Saka kuba. Ta jingina baya tana haki. Gaba dayan 'yan matan ne suka hayaya ko mata kamar zasu cinye ta danya. "Ke wace iriyar ce da zaki shigo wa muta ne ko sallama babu kin tsorata muta ne". Wasu 'yan mata uku ne suka fadi hakan cikin daga murya.  "Kuyi shiru Aljanu ne aljanu". Haleema ce ta taso cike da masifa. "Kutumelesi Lalai yau zakiyi bayani wato ke dan rashin kunya har kika iya tako kafarki zuwa wajen biki na oya to wallahi kama hanya in ba so kike yanzu mu kwashi 'yan kallo da ke ba.

Bar ganin ina amarya wallahi sauke gwa-gwaran nan zanyi inci ubanki".  Duk da Nasmat taji haushin zancen Amma sai ta basar domin jin Matar nan ta zo bakin kofa sai bubugawa take tana fadin "dan Allah ku ce ce ni ki bude zata kashe ni". Karkar wa Nasmat ta fara yi tsoranta ya karu abun ya zame mata biyu ga masifar haleema ga kuma wacce aljana ta biyu.  "Sister Haleema dan Allah kiyi hakuri zan fita, Wallahi nima ba da gangan na shigo ba aljanu ne a gidan yanzu ma aljanace ta biyu mu ni da wata kinji ta nan tana bubugawa". Wani dogwan tsaki amaryar taja tare da kama hannun Nasmat tana kokarin bude kofa ta tura ta. "Aljanu ko to wallahi sai dai su kashe ki amma sai kin fita. Ke sunci kut.....ubansu ma aljanu". Kafin ta rufe baki taji saukar wani lafiyayen mari wani har sai da taga taurari.  Juyo wa tayi, "Kai kai kai kika mare ni Nasmat. to wallahi  yau banga mai raba ni dake ba a gidan nan". Nasamt kafin ta bude baki ta ce l ba ita ta mare ta ba.

tuni Haleema tayi kukan kura ta kai mata chakuma (kamar zakaru na fada) suka fara bige-bige da naushe-naushen juna su kuwa 'yan matan amaryar sun kai su shabiyar a dakin harda Asnart a ciki amma ba wace tayi yunkurin rabawa. Haka dai suka ci gaba. Saukar bulalin da suka fara ji kamar daga sama yasa suka dan saki juna ko wacce idan ta cike da kwalla. Jin an dakata da dukan nasu kamar hadin baki suka kara cakumar juna. Wani Razana nan kara ne ta cika dakin wanda suka rasa daga ina ya fito. "Kaaaaaa!". Nan fa suka saki juna suka durkushe ko wacce ta rufe kunnuwan ta domin karar yayi yawa. Haka 'yan matan amarya ma gaba dayan su kowa ya rufe kunne suna raraba ido. "Kuuuuu taaaashiiii tsayeee". Wata murya ce wacce in kaji ta kai kanka sai ka firgice gata da karfi ga tsoratar wa. Haleema da Nasmat tsatsaye suka mike ko wacce karkarwa take kamar su ruga su bar dakin. Haka yan matan amarya wasu suka shige cikin (wardrobe) wasu suka haye kan gado suka rufe da blanket kowa dai  da wajen da yake nufa neman mafaka. Asmart kuwa kofa ta nufa da gudu nufin ta ta bude ta gudu. Tsawa aka daka mata. "Keeee inaaaa zakijeee". A wajen ta fadi ta fara zubda hawaye "Ba ko ina".

Ta fada murya na karkarwa cike da tsoro. Tana waige-waige saman Silin ta kalla da taga kamar wani baki baki ta wutsiyar ido. Ihuu! Ta kurma hade da Runtse idanu tasa hannaye ta rufe kanta. Kan mace ne a yanke gashi buzu-buzu fuskarta babu kyan gani abun tsoro. Kan reto yake a sama shine ke maganar.  Su Nasmat koda suka daga kai suka kalle ta sai tsoran su ta karu ba wacce ta sake yunkurin Motsi da kanta balle ta kalli sama.   "Watooo kuuuu waiii gabaaaa kuuuuukeee yiiii tsakaaaa niiiin kuuu koo?".  Cikin sauri suka hada baki gurin cewa. "A'ah".  Cikin tsawq "Ku rufe min baki marar kirkin banza da akayi kuna 'yan uwan juna kuma ku musulmain ne amma kuke gaba da junan ku. Ku rungumi juna daga yau kar in sake ji. Ko bayan auren haleema  ne".   Cikin sauri suka Rungumi juna suna karkarwa.  Hahahhahhhah!  dariya ce mai firgitar wa ta kaura de dakin. "Sauran kuma in sake samun labarin kuna gaba. Sannan Kar wacce ta yarda ta fita daga dakin nan a cikin ku in dai ba lokacin kai amarya ne yayi ba kuna jina?".  Wannan karan har 'yan cikin Durowa (wardrobe) sai da suka amsa da karfi "To". Bat! aljanar ta bace.

Tsakar gida gaba daya ya hautsine tun daga farkon layin zaka iya juyo masu ihu nayi masu kuka nayi haka ma masu karatu addu'o'i nayi.  Kofar ta kulle har yanzu kuma zanar su ake ba'a dai na ba. Fatima kanta ta tsorata da gudu ta tashi rike da yar babyn ta nufi wani  keji ta shige ta boye dan gudun kar a banke ta. Kafin kace me Mata wajen biyar ne suka shiga keji dan ce tan kansu. fatima kam matse ta akayi gam. Macen da ke bakin kofar Kunama ta gallawa cizo ihu ta kwada ta fita a guje tana Soshe-soshe.  Gida gaba daya ya hargitse kowa ta kansa yake yi. Abincin ma tuni an zubda shi an tatake. Ga kofa ta kulle taki buduwa.  'Yar tsohuwar nan ce ta bayana a sama kamar tsutsuwa fuska a murtuke. Wata tsawa ta daka wanda tasa gaba ki dayan gidan ya kara hargitse wa. Ba abunda ya kara haddasa cin kosan gidan sai falo da shima yaki buduwa.

Mata kam wasu ban daki suka shige harda masu shiga cikin tukunya dan tsoran bulalar.  "Kowa ya tsaya kar ya matsa a inda yake".  Aljanar ce tayi magana cikin daga murya abunda ya tsayar da guje-guje da ake faman yi kenan.  "Wato ku marar imani ga abinci a gaban ku ba na uwarki ba bana ubanki ba almajira tayi bara harda masu daga sauti gurin bada hakuri. Ke kuma Waccen 'yar lukutar matar (Ta nuna Mama asiya da yatsa)  kece muguwa har da bani abinci mai gishi ri nayi magana kika ta so baki ga girma na ba a haka kamar zaki bige ni ko?".   Mama asiya jikinta ne ya hau bari murya na rawa "A'a dan Allah kiyi hakuri bansan ke aljana bace, wallahi dama taimaka miki ne zanyi dan na.....".   "Rufe min baki, (Aljanar ta daka mata tsawa) Makaryaciyar banza, Ku kuma abunda yasa nayi muku wannan hukuncin dan ku kiyaye gaba ne. Ni Aljana ce ba mutum ba. Da mutum ce da kun wulakanta banza kenan. Wai ace a cikin ku kuna ganin wannan matar zata ci min mutunci ba mai bada hakuri ko dakatar da ita sai ma dariya. Kunci sa'a ni musulmar aljanah ce ba muguwa ba amma da yau sai nayi muku tatas a gidan nan duk da sai na farfasa muku jiki".

Shiru sukayi babu mai ko motsawin kirki kowa a tsora ce yake. "To abunda nake so da ku yanzu shine Ga mai gidan nan da 'yan anguwa a kofar gida sunzo jin me ke faruwa, kar wacce ta yarda ta bude baki ta fadi abunda ya faru, Duk wanda aka tambaya yace ba komai.  Sannan baku ba fita daga gidan nan sai bayan an kai amarya. Duk wacce tayi yunkurin fita kuwa zata hadu da fishina".  Tana gama fadar haka ta bace bat!  Kofar gidan kuwa da su Alhaji ke  faman ballawa ta bude wayam. Shigowa sukayi suka ga gidan yayi kaca-kaca nan suka hau tambaya me ya faru kowa sai dai yayi shiru da bakin sa. Masu dan kokari da rashin tsoro ne ma suke cewa babu komai. Nan dai su Alhaji suka gaji da tambaya sukayi fushi suka bar gidan suka  koma harkokin su na shirye-shirye daurin aure.

Tsakar gidan tsitt! Kake ji babu mai wani kuzari duk sun jigata marar dauriya ma daga cikin su kuka suke wasu kuma na Soshe-soshen inda suka sha bulala. Wata Yar siririyar mata ce ta mike tana fada. "Wallahi ni sai na fita na tafi gida. Sai dai in kashe ni zata yi ta kashe kawai dan zalunci daga zuwa wajen biki a tsare mu kamar wani gidan maza".  Jakar ta ta dauka tasa takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa kofar gida, taji an kama kafarta ta baya an wani warto....................................

*TASHIN HANKALI*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 35-36

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

DEDICATED TO YOU:
☺ *SISTER NA HAFSAT IBRAHIM* ☺
NAGA DOGON COMMENT, NAJI DADIN ADDU'O'IN KI DA FATAN ALKHARIN DA KIKA MIN. NA GODE KUMA KEMA ALLAH YA BAKI DUK ABUNDA KIKA ROKAR MIN. (Ana tare)

😘 _All my fans thanks 4 You love and supported. Allah ya bar zumuncin. Ina ji da ku sosai da bazar ku nake rawa._😘

πŸ€£πŸ˜‚ _*WATO YAU INA TYPING INA DARIYA BAN TABA DARIYA GURIN TYPING KAMAR NA YAU BA. UHMMM BA SAI NACE KOMAI BA KU KARANTA TUKUN. NAJI DAGA GARE KU MY FRIENDS I LUV U OLL*_ πŸ€£πŸ˜‚

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Jakar ta ta dauka tasa takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa kofar gida, taji an kama kafarta ta baya an wani warto.~

```»» Kafarta ta fadi Janta akayi kiiii! Tana ihu hade da wuntsile-wuntsile, Zaka ga ana janta amma idanunka baza su gano maka mahalukin da ke jan kafar tata ba. Sai da aka kai ta can gaban mutane sannan aka barta, Zaune ta tashi tana kuka tana wage-wage, jama'ar wajen wanda basa da jumurin dariya har sun fara gagaba ta. Suka ji wata tsawa wacce tasa kowa yayi tsi!. Gidan shiru kake ji ko fitsari ba wanda ya yarda ya tashi yara da manya, haka suma can saman beni suna cikin daki sunyi tsi! Sunyi zugum suka ji ana Kwankasa kofar daki. Wasun su tuni sun kankame juna kowa na ihu yana kiran momynsa. Shiru ba wanda ya sama damar bude kofa hannun mace suka gani ya zuro ta jikin kaure ya murda key nan take ya bude. Nan fa tsoran su ya karu ba abunda ya kara tsorata su sai ganin wata kyakyawr zankadediyar budurwa fara ce tas!. Sanye da doguwar farar riga daga ka ganta kaga balarabiya. Wannan ya tabbatar musu da ba mutun bace aljana ce domin basa da alaka da Larabawa. Hannun budurwar rike take da Wani dan karamin akwati mai marika. Nufo su tayi tana murmushi. "Ina Amaryar ta so in miki makeup". Ta fada lokacin da ta durkusa tana kokarin bude dan akwatin. Haleema da Nasmat kamar ba abokan gaba ba domin haleema makal-kale Nasmat tayi Nasmat kuwa kokarin raba ta da jikinta take domin karta jawo mata.  Aljanar ta tsaya tana kallan su gaba dayan 'yan matan amaryar kokarin turo haleema suke gaban aljana ita kuwa tana kara make wa.  Sakin baki aljanar tayi tana kallan su ganin haleemq bata da alamar tahowa. Tsawa ta yi musu wanda ya rikita dukan su kanta ya fara futar da hayaki. Gaba daya sun firgice jikin halima na rawa ta taho tana wani kwabe fuska jiki na rawa. Daga tayi tako daya sai ta tsaya ta wai waya baya kamar ta ko ma. Aljanar ce ta wani harari kawayen amaryar da idanunta wanda sukq fara komawa ja. Da sauri mutum uku suka turo haleema da karfi. Ta fada jikin Aljanar ta dan rungume ta "Haba 'yar uwa ta ya kike tsoro na bafa cutar da ke zanyi ba". "To", din karfi da yaji Haleema ta fada jiki na bari.   Nan Aljanar ta zaunar da ita ta fara Gyara mata fuska. Wasu kayan shafe-shafen ma kai baka taba ganinsu ba. Sai da ta gyara mata fuska ta fito fes! Tayi kyau sosai, Aljanar ce ta juwa musu fuskan Haleema "Tayi kyau kuwa 'yan uwa". Da karfin su kamar hadin baki ba wacce aka bari wajen cewa. "Eh tayi kyau". Duk tsoro suke ji. Sai da Aljanar ta gama gyara ta sosai har gwagwaran sai da ta sake hada mata mai kyau.  "Kuta shi mu fita yau kowa sai yawa amaryar nan huduba. Cikin hanzari suka tashi saboda tsabar tsoro. Gaba Aljanar

Amaryar na binta baya sai 'yan matan amarya da suka rufo musu baya. A tsakiyar falo Aljanar ta zaunar da haleema ta ce su dakata ta kira wo muta nan. Ba garda ma duk suka ce "To". Fita tayi waje mutane anyi Tsuru-tsuru kowa sai tunani yake, wannan gidan biki baiyi dadi ba. "Sannun ku da hutawa uwayen amarya ko?, To ban ware kowa ba ku shigo ku mata hudu ba".  Kamar daga sama suka jiyo maganar da sauri suka waiga duk wanda ya kalle ta ya san Aljana ce hakan yasa duk a tsorace suka tashi dan bin umarnin ta har rige-rigen shiga daki ake. Kuri sukayi wa amaryar inda ita kuma Aljanar ta tashi sama tana kallan kowa.  Jin sunyi shiru sun saka amarya gaba kowa sai raraba idanu yake Ta daka musu tsawa. "Kuyi mata hudu ba nace ba ku sata gaba ku kalla ba". Kafin kace me dakin ya cika da hayaniya kamar makaranta haya-haya wani bai ma san abunda ke fitowa a bakin sa ba, kawai tsabar tsoro ne. Jin sun cika mata kunne ta kara musu wata tsawar wacce tafi ta farkon kara da ban tsoro. Da yawa sun zabura koya ya kama bakinsa yayi tsitt!.  "Au! Dama haka ake huduba a garin ku?. Oya daya bayan daya zakuyi"   mama asiya ta nuna da doguwar yatsa. "Ke fara".  Mama asiya na karkarwa. "To, Amarya kina jina ki bi mijin ki sau da kafa kiyi masa ladabi da biyaya banda Rai ni shi shugaba ne a gare ki. Banda daga mishi murya duk abunda ya saka ki kiyi".  Shiru ce ta biyo baya. "Au! Shikenan kin gama?". "Eh, A'ah" ta bada amsa.  "To duk ke kina wa mijin ki hakan?".  "Eh ina mishi mana". Ta fada tana murmushin dole. "Shikenan zan bibiyi rayuwar ki idan naga akasin haka to ke ma kin san sauran".  Cewar Aljanar bata tsaya sauraran amsar ba.cikin daga murya ta nuna Zuwaira Da yatsa ke da kike noke-Noke oya saura ke".  Zuwaira a firgice kamar ta saki fitsari ta fara karkarwa tsabar tsoro. "Too too niii dammmaa abuuu!!!...".   "Ke ki natsu kiyi mana magana sak!, In ba haka ba yanzu in mayar dake Mage".    Hannu zuwaira ta dora a kai. "Na shiga uku dan Allah kiyi hakuri karki mayar ni kyanwa.

Haleema ki tsaya kiyi tunani yanzu kin girma kin zama cikakar mace ki natsu ki zabi kawayen kirki masu nuna miki hanyar tsira karki dauki masu Janki juwa hanyar halaka. Wannan wani zama ni ne ya zo mana wanda shawarar kawaye ke bada babbar gudun muwa wajen kashe aure. Ki tsaya ki natsu ki gane aure shine darajar 'ya mace ki zauna da mijin ki lafiya......". Taf! Taf! Taf!  Aljanar ta fara tafawa zuwaira da jin haka sau duk suka dau tafi..Aljanar tace kinyi kokari.  A haka aka tayi  duk illahirin matan da suke dakin hatta kawayen amarya kowa sai da ya to fa bakin sa ko baka da abun fada sai ka lalibo.  In kaki kuwa sai dai kaga ta zuro hannuta tun daga can sama ta wanke ka da mari. Haleema tun tana dauka har ta kai ga sai dai ta ce "Eh", Kawai ko ta daga ma kai.

Wasa- wasa Dai abu har dare yayi anawa amarya nasiha. Dare nayi lokacin kuwa 'yan daukar amarya suka zo ko ta kan Alhji yayi nasiha ba'a bi ba. aka dauka Kowa na zumudin aka basu amaryar su.mata ko daya ba'a sama wacce ta tafi rakiyar amarya ba. Domin duk wacce ta fito daga cikin gidan. Sai tace "Alhmdulilah". Ta ari ta kare ko mai wai-wayen gidan babu. Haka 'yan matan amarya ma duk wacce ta fito sai ta ruga a guje ta nufi hanyar gidan su. Kamar dawa ki haka mata suka cika layin da guje-guje.  Ganin za'ayi abun kunya ba 'yan rakiyar amarya yasa  mama asiya da umma suka roki su Zuwaira da su taimaka a raka amarya.  Su Fiddausi da su nasmat sune a matsayin kawayen amarya su hudun su kuwa su zuwaira a matsayin manyan mata. A tsorace suka kai amrya gidan ta suna kai ta kuwa kowa sauri yake ya fito. Ganin suna shirin tafiya su kyale ta ita kadai gata itama a tsara ce take. Kuka ta saki ta biyo su tace wallahi sai dai a koma tare baza su barta ita ka dai ba. Ganin da gaske take da kyar Fiddausi ta ce tayi hakuri su zauna har angon ya zo. Nan ma da kyar ta yarda. Su mama asiya ansha bulala duk jiki sai radadi. Ana tafiya a mota sai cewa direba (Driver) yayi sauri take. Kowa a tsora ce yake sai da suka karasa gida tukun hankali ya dan kwanta. Su Juwaira a kujerun fali suka zube kowa najin jiki hade da tsinewa gidan bikin. Nasmat da asmart Dakin su suka nufa domin suyi fitsari dan ya matsi ko wacce a ciki. rige-rige suka fara da gudu wajen shiga dakin. Sai da aka .  kusan zuwa toilet din Nasmat ta tuno da macijin nan na dazu. Birki taja a gurin tayi baya.  Taki fada wa Asmart dan mugunta.  Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje. Nasmat na ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su mama asiya na ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka nufi hanyar fita a............................```

Taki fada wa Asmart dan mugunta.  Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje. Nasmat na ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su mama asiya na ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka nufi hanyar fita a.~

»» Su mama asiya Har karo suke yi ita da kishiyoyin ta wajen fita. Har anzo tsakar gida tukun Aamart tace "Nasmat wai miye ake wa gudu?".  Tambayar da sukaji Asamart tayi ne yasa duk suka ja birki suka tsaya. Nasmat cike da mamaki tace "Me kika gani  a bandaki kika yi ihu!?". Kyankyaso na gani mana, Shine na tsorata ke kuma sai naga kin rugo ai na dauka wani abun ne kika gani". Dogon tsaki sukaja kusan tare, kowa na haki tukun suka fara wa junan su dariyan. "Kaga 'yan iskan yara kun tsorata mu ai mun dauka Aljanar ce ai ta biyu mu har gida".  Inji hauwa.  Komawa sukayi cikin gidan gaba dayan su a tsorace suke ga barci ga gajiya amma ba wacce take da karfin halin shiga dakin ta ita kadai. fatima ita kam tuni har tabi lafiyar gado tun shogowar su ta farko.  Suna nan zaune a falo har alhaji ya dawo. Da ya dawo suka tayar mishi da rikici domin ko wacce sai da ya rakata daki sai ta rufa da bargo tukun yake fitowa.  Fiddausi kuwa sai wajen karfe sha daya angon haleema ya zo tukun tace gida zata. Da kyar suka lalaba ta ta yarda zata kwana a dayan dakin sai safe ta tafi.

Yau kusan kwana Biyar da faruwar hakan, kusan kullum sai Nasmat ta hadawa Asmart tarko domin ta taba Aljanar ko fatima amma har yanzu shiru kake ji.  Abun na matukar cin ran Nasmat domin tasha zuga Asmart ta ci uban fatima ko kuma ta yiwa 'yar babyn wani abu amma ba abunda yake faruwa. Suna zaune a tsakar gidan kan but din motar baban su Fatima ta zo wuce wa Rike da 'yar tsanar ta.  "Ke dan ubanki zo nan".  Cewar Asmart, Fatima ta zo. "Muga 'yar babyn nan kullum kina tare da ita kamar mayya". Fatima bata so ba dan  gudun kar a dake ta, ta mika wa asmart 'yar tsanar. Nasmat a tsorace take tun da Nasmat ta zo shiyasa ma ko uffan bata ce ba, Yanzu ma badan ta so take zaune a gun ba kawai dan mugunta ne, So take kawai asmart ta tsokalo wa kanta.  Asmart na karbar 'yar tsanar ta juya ta ciki da bai, tana kare mata kallo. "Fatima naji ance wai babyn ki na magana ko?".  Cikin fara'a Fatima tace "Eh mana tana cin abinci ma kuma idan aka bige ta ko na barta ita kadai har kuka take yi".  Asmart ko da jin haka sai ta buga 'yar tsanar da kasa da karfi Tum!.  Fatima sai binta kawai tayi da kallo. Asmart ta wani dauke Fatima da mari har sai da ta fadi nan take ta fara kuka. "Shegiya  ma karya ciya kince tana kuka idan an dake ta to yanzu me ya hana tayi kuka?".  Asmart ce ke fadar haka lokacin ta diro daga kan bayar motan.  Taje ta dauki 'baby Doll din ta kama kan ta murda da iya karfin ta, da mugunta so tayi ta cira kan amma yaki cire wa.  Fatima kuwa kuka take tana fadin "Aunty dan Allah karki kashe min babyna".  Nasmat har yanzu zaune take kan mota sai kallan drama take, Cikin ranta farin ciki cike fal! Dariya ce ta mugunta ta kamata lokaci guda ta fara kyal kyalata. Suna hada ido da 'yar tsanar tayi gum baki. Domin gani tayi kamar hararen ta take.

Asmart kuwa 'yar babyn tayi a kasa ta fara tataka ta tana tsalle tana dira a kanta. "Wato har rai ne da ita da kike cewa karna kashe miki ita kenan, To gashin nan ta mutu".  Wani tsalle da tayi gefan takalminta ya dan Daki gefan gashin kan 'yar robar wanda har wani dan guntun gashin  ya tsinke daga kan.  Fatima na ganin haka ta kara fashewa da kuka. Da sauri taje tana kokarin kwatar 'yar ta tana cewa. "Dan Allah aunty kiyi hakuri kinga har kin fara tsinka mata gashi".   Asmart ta sunkuya ta dauki diyar "Au! Ashe fa gashi gare ta aunty yolash! Kenan, amma fa idan aka dan rage wannan gashin zata fi kyau dan haka bari inje in mata aski".  Tana fadar haka ta nufi falo da gudu Fatima kuwa ta bita tana kuka tana cewa ta bata diyar ta.

Nasmat na ganin haka ta kyalkyale da dariya harda rike ciki tace "Asmart yau zaki ci ubanki, kin dauki ruwan da zai dafa ki".   Haka su asmart suka wuce su mama asiya a falo da gudun tsiya fatima na binta tana kuka. Asmart na shiga dakin tayi sauri ta rufe dakin tana dariya. Fatima nan ta tsaya tana kuka tana faman bu buga kofar.  "Ke fati uwarki nace, ko baki ji ba". Hauwa ce ke maganar. "Kaji 'yar iskar yarinya mutane na zaman su suna hutawa zaki zi ki ishe su da kuka".  "Mama hauwa aunty Asmart ce ta kwace min babyna".  Fatima ta fada tana kara rushewa da kuka.  Afusace hauwa tayi kanta tana mata fada har da duka ta kora ta waje. Asmart na shiga dakin ta wullar da 'yar babyn a kasa hade da taka ta ta nufi wajen kayan kwaliyar su tana neman reza ita da gaske iski zatayi wa 'yar tsanar.   Wani dan tsalle tayi na jin dadin ganin rezar nan fa ta zo ta zauna ta aske wa

'Yar tsanar kanta tas!.  Tana kallanta ta kyalkyale da dariya, "Amma fa kinyi kyau sosai yar yarinyar fatutu, bari in ma kan nan kiss".  Ta fada cike da zolaya ta manna wa kan 'yar babyn kiss. Uhhhmmahhh, Ai kuwa taji bakinta da kan kamar ansa gam an like. Jatayi da niyar raba bakin ta da kan 'yar babyn ai kuwa yaki rabuwa bakin nata ya manne  Tun tana daukar abun wasa har ta kai ta ga fara kuka tana jan kan ki!ki!-ki!ki!  Amma yaki fita. Hawaye shabe-shabe ta tashi ta nufi kofa tana kuka tayi-tayi ta bude kofa taki buduwa. Ihuu! Ta farayi tana neman dauki amma shiru gidan kamar ba kowa.Hannu tasa ta kama gangar jikin 'yar babyn taja da karfi sai ji tayi ta fizge ta. Ai kuwa ta wullar da ita can jikin bango a tsorace tana mai da nunfashi daya-daya. Fitsarin wuya taji da sauri ta shiga ban daki lokacin taji harda kashi ma.  Tana tsugune ta fara jin wata 'yar siririyar dariya na fitowa daga dakin. tun anayi a hankali har aka fara da karfi abun yayi matukar tsorata ta domin bata san mai kalar dariyar nan ba a gidan. Wani hayaki kuma taga ya fara shigowa ta kasar kofar toilet din. Bata gama ba ta wanke a hankali ta dan bude kofar a tsora ce. Hayaki ne cike da dakin baka iya ganin na gaban ka ga kuma dariyar har yanzu yi ake. Mamaki da tsoro suka kara ziyartar Asmart a lokaci guda. Wajen da take jin dariyar ta nufa tana tafe a hankali duk da ba wani ganin gabanta take sosai ba.  Tana tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani kuma daga ciki dariyar ke fitowa.  Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.......................

*Kuyi hakuri kadan neee*

Ni kuwa Idan nice Asmart sai na daga naga ko ma miye. Kai/ke fa???. Lolz

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 39-40

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU, ZAINAB ZEE*

*Hip hip hip hurray, Happy birthday to you*

🍰 *ZAINAB ZEE* 🍰

And

🍰 *BIEBOH*  🍰

*Ina taya ku murnar zagayowar haihuwar ku. Allah ya karo wasu shekarun masu amfani. Ya yafe zunuban da kukayi a shekarun da suka wuce. Ya kuma linka ladar* 😹 It's you day.

~Tana tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani kuma daga ciki dariyar ke fitowa.  Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.~

»»Hannu na karkarwa cike da tsoro ta kama dan bak'in mayafin ta fizge karfi. 'Yar babyn ta gani kwance rufda ciki itace mai dariyar.  "Aikin banza ashe wannan abarce ma har na tsorata".  Asmart kafa tasa ta dan buge ta abunda ta gani yasa ta fara ja da baya. Idanun 'yar tsanar ne wani irin bak'in jini ke fita a matsayin hawaye ga wasu manyan hakora da suka zazaro waje wani abu take taunawa tana dariyar kamar danyan nama hakan yasa bakin ta shima yayi ja idanunta kuwa sun koma baki da ja. Sabanin bakin da fari.  Heheheheheheheh, "Baki san nice ba ko?. To da kin dauka wace a ciki?". 'Yar babyn ce take magana cikin wata 'yar siririyar murya. Nan take jikin asmart ya fara rawa saboda tsoro magana na rawa-rawa, "Dan Allah kiyi hakuri ki rabu dani Wallahi bansan ke aljana bace. Wallahi na dauka diyar roba ce".  HahahahHahhha "Wata dariyar mai karfin gaske 'yar robar tayi wacce tasa sai da Asmart ta rufe kunnan ta. "Wato ke azzaluma ko kina zatan zan kyale azzalumai irin ku ne? Muddun da rai! Na da lafiya ta bazan dinga sasauta wa azzalumai irin ku ba. Musamman masu cutar marayu.  Yanzu in kina so in hakura ba abu mai wuya bane kawai zo ki dauke ni ki min wanka ki mayar min da gashi na".  "To, To".  Da sauri asmart ta fada, Lokacin taje da niyar Daukar 'yar babyn amma tayi iya kokarin ta ta raba ta da kasa ma abu ya gagara. Ita kuwa aljanar sai gagaba wata kalar dariya take marar dadin ji. "Oya daga ni mana ko so kike yanzu in fara taba lafiyan jikin ki?". Dan Allah kiyi hakuri *Aljanar fatima,* wallahi nayi-nayi na kasa ne".  Hihihihihihh. "To tunda dai kika ce min Aljnar fatima naji dadi kuma na rage miki aiki amma da ko shekara zamuyi baza ki iya rabani da kasa ba. Yanzu abunda nake so jeki ki tsinto gashina ki zo ki mayar min abuna".

Asmart na karkarwa tace, "To ai dakin duk hayaki ne bana ganin gaba na.  Tana rufe baki hayakin ya dauke gaba daya taga kamar ba'a taba yinsa bama.  Da sauri ta nufi wajen ta fara tsinto gashin da ta aske a kan Aljanar 'yar babyn.  Sai da ta tsinto gaba daya tazo ta mikawa aljanar a tsorace tace "To gashi". "Au! Miko min kawai zakiyi?  Zo ki mayar min kamar yanda kika aske min in kuwa ba haka ba yanzu kiga karshen mugu". Da sauri Asmart ta matsa kusa ta fara kokarin mayar da gashin da ta aske. Daga ta dora sai taga gashin ya fado, aljanar kuwa sai dariya take. Asmart tuni ta gaji, ta kuma gaya wa aljnar itabkuwa tace dole sai ta mayar mata da gashin ta kamar yanda yake a da.  A smart taci gaba. Tana yi ta fashe da kuka da karfi. "Keeeeeeee!!!". Wata muguwar tsawa aljanar tayi wa asmart tana yi kuwa dakin yayi duhu rundum. Asmar bata iya ganin ko tafin hannunta balle aljanar da ke gabanta. A zuciyar ta tace " wannan dama ce ta in tsere dan haka yanzu bari inyi nan nasan ta nan kofar fita take".  A hankali ta tashi kamar barauniya take sanda. Kafarta taji tana takawa kamar a cikin hakukuwa. Abun ya bata mamaki  ta fara zance a zuci, "To me ya kawo wannan hakukuwan cikin daki kuwa?, dakin da ake share wa kullum. Ahhh! Wayyo Allah kafa ta". Asmart tace yayin da taji ta taka wani abu kamar kaya ya kuma shige mata cikin kasa. Dake har yanzu mugun duhun na nan bata san ko me ta taka ba. Kuka ta fara tana Yarfa hannu tama manta da Aljanar. A wajen ta zauna sai lokacin ta tuno da ashe aljana na kusa. Hakan yasa ta rike baki ta gam. Rintse ido tayi hawaye na zubowa ga radadi zafin da take ji.  Bude ido tayi haske fayau sai dai kuma a inda ta tsinci kanta ne abun yayi matukar girgiza ta da bata mamaki. Wani mugun daji mai wasu irin itatuwa wanda bata taba ganin kalarsa ba ko a TV gasu dogaye ga kuma fadi. Duk sunyi inuwa wa waje. Yanayin wajen kadai abun tsoro ne ko kukan tsuntsu babu balle kayi tunanin zaka sama mutum.  Wa-waigawa tayi ko ina iya ganinta bata hangi karshen dajin ba. Kuka ta kara fashewa da shi, domin wannan ba karamin tashin hankali bane a gare ta. Sai yanzu idanta ya kai ga kafarta  da ke zubda jini ashe kaya ce ta taka. Kara rudewa tayi ganin jinin dake zuba hannu ta dora kai ta fashe da kuka tana surutai na neman taima ko daga uwar ta da dangin ta.Da dai taga kukan baya yi. Sai ta fara kokarin cire kayar, daga ta dan sai ta sai ta saki kara, "Wayyo",  Haka dai tatayi. "Kee! me kike a nan". Wata muryar ce katuwa ta fadi hakan, Kamar daga   sama Fatima taji maganar

A firgice ta juya firgigit!. Wasu irin mutane ta gani masu mugun abun tsoro. 'yan kanana ne kamar yaro dan shekara 6 haka. Amma kawunan su a mulmule suke kamar kabewa Gasu manyan  idanunsu kananu 'yan mitsi-mitsi. Ko wanne daga ciki gashi ne buzu-buzu a kan ba tsari.  Asmart ihu ta kurma ta sa hannu ta fizge kayar ta tashi ta ari ta kare.  Su ma kuwa sunkai su goma suka rufa mata baya. Sa'arta  daya basa da gudu domin kan yake rinjayar su. Suta faduwa. Gudu suke cikin wannan kunkurumin daji asmart  duk da tayi musu nisa bata tsayawa wai waye. Sai da tayi gudu sosai tukun ta sama gidin wata bishiya ta jingina tana haki.

Bata fi mintuna biyar ba taji wani irin gurnani a bayanta. A hankali take juyawa a tsorace.  Wata bakar damusa ce mai jajayen ido. Sai bude baki take yi tana lasar harshe. Mugun tsurewa asmart tayi, da baya-baya ta fara tafiya damusar na kara matsota.  Saurin da damusar ta fara ne yasa asmart ta juya ta runtuma a guje tana ihu! Da musar kuwa tace dake aka hada mu. Gudu take iya karfin ta tana waige. Wani makeken gida taga ya bayyana a gabanta. Batayi wani tunani ba ta Afka! Ciki  ta rufo kofar, gida ne makeke mai kayan kwaliya da filawoyi iri-iri sai dai bata ga kowa a cikisa ba. Sannan ba dakuna sai daki daya wani wangame me wanda yake a bude sai wani jan labule dake sanye a kofar dakin shi ya hana aga cikin dakin. Asmart tunani take taje ko kuwa ta tsaya nan. Daga karshe dai ta yanke hukuncin gwara ma taje in ma kashe ta aljanar nan zata yi gwara ta kashe ta ta huta. Gadan gadan ta nufi dakin ta yace labule cike da jarumta tana shigewa Kyauren dakin ya rufe gam. Can Asmart ta hango wata mata tsaye Sanye da riga baka doguwa. Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta. Cikin Masifa da daga murya Asmart tace "Ke.............

Yaseen na gaji. Kuyi hakuri da wannan.

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 41-42

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU* 😍 πŸ‘‡πŸ½

*Mzz Dady*

*Rabi'atu Shua'ibu*

*Layuza*

*Phateema*

*Teemah*

*Maimunat (Aunty maimuna)*

*Ummu Azza..*

😍 Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare πŸ™‹πŸ»‍♂

🎀🎼 *YAU TAMBURAN GIRMA NA BUGA DOMIN MASOYA NA,* ☺

🎀🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* πŸ‘―

🎀🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* πŸ‘―

🎀🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* πŸ‘―

🎀🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,*  πŸ‘πŸΌ *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺

🎀🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,*  πŸ‘πŸΌ *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺

🎀🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,*  πŸ‘πŸΌ *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺

πŸ‘ΈπŸ»πŸŽ€ Dan Allah masoya Kuyi hakuri

🀴🏻🎀 Dan Allah masoya kuyi hakuri.

M INUWA 2 🀑

       *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta. Cikin Masifa da daga murya Asmart tace "Ke....~
"Ke wai wace ce, me kika zo yi gidan mu?, Ke wacce irin muguwa ce?". Cikin karfin hali Asmart ke watsawa matar ta tsaye wacce ta tabbatar da itace Aljanar. Duk yanda ta ci cije ta kafe ta cire tsoro. Dariyar da aljanar nan ta bushe da ita sai da ya tsorata Asmart din dan sai da taji kamar ta ruga. "Keeee!". Aljanar ta fada lokacin da ta dago kai da karfi  gashin kanta ne ya wani mi mike tsai-tsaye idanuwanta jajawur Wasu ba kaken abubuwa kamar  tsutsotsin suna yawo a ciki. Fuskar tata a tabe take bakin ya wani jirge share gudu, Hancin ta a wani tabe yake. Idan kawa Aljanar nan kallo guda baza kayi marmarin karawa ba. Ko asmart kauce kai tayi da taga hakan. "Lalai samun waje wato kece yau har kike ce min Muguwa ko Asmart?".  Da wata iriyar murya Aljanar ke magana wacce tasa Asmart cikin tsoro da fargaba. Duk rawar kan da take da farko yanzu ta daina karkarwa ma ta somayi. "Sunana Safuratu Ko kice *ALJANAR FATIMA* ko kadan bani bari ayi zalunci balle ni inyi. Ko da yake inayin zalunci sosai ma amma fa a kan irin ku azzalumai, Yarinya ce 'Yar karama gaba daya kun fita do wai me ta tsare muku miye abun zaluntar ta in baku taimake ta ba marainiya ce fa".  Murya na rawa Asmart ta daga baki da niyar magana. "Baaa.....". Tsawa Aljanar ta daga mata "Me zaki ce min baki da abun cewa Kalmar *YI HAKURI* Kuwa ke ma baki dauke ta a komai ba yayin da kika tashi zaluncin ki, Dan haka nima yanzu dole in zalunce ki ba sani ba sabo".  Aljanar na rufe baki ta nuna Asmart da yatsa. Sai gata tayi sama tana ihu! Tana harbe-harben iska Da kafa. "Hahhhahhhhahhahhahah. Yanzu kuma kinsan me zanyi?, Kasa zan sake ki kanki ya daki Dutsen can ya rabe biyu kinga an rage mugun iri".  A smart ihu! Ta fara tana bada hakuri hade da rantsuwa baza ta kara zaluntar Fatima ba.

Kafin ta rufe baki tuni Aljanar ta sake ta kasa tayo tana ihu!.  Ganin ta kusan zuga kasa gashi saitin dutse ne, Ta rintse idanu ta sadaukar. Ji tayi ta fado a katifar ta. Abunda yayi matukar bata mamaki kenan. Tashi tayi da sauri tana waige-waige cikin dakin abun ya daure mata kai, Tunanin da take wannan mafarki ne ki gaske. Ganin ba kowa a dakin yasa tayi magana a bayyane. "Shegiyar Aljanar muguwa yar...".  Kafin ashar din da tayi niyar fada ya karasa fitowa taji wani abu ya diro a kanta ta baya. Ihu ta fara yi "Wayyo  Allah na na shiga uku na lalace Dan Allah dan annabi kiyi hakuri Wallahi bazan kara ba". Da karfi Asmart din ke magana. 'Yar babyn ce ta diro gabanta. Tana mata dariya.

Mai wani irin siririn sauti. "Dama zuwa nayi in gaya miki wannan abun da ya faru a tsakanin mu ni dake in kika 'yarda kika fadawa wani Ke ma kinsan sauran". Tana fadar haka ta bace bat!. Asmart na ganin haka ta Tashi ta fito da gudun tsiya daga dakin. Nasmat na zaune a Falo ita da Ameerah suna kallo sukaga Asmart ta wuce a guje tayi waje. Nasmat ta tashi ta bita a guje tana wai-wayen  kofar dakin. Haka ameera ma ta biyo su. A tsakar gida Asmart ta tsaya tana Maida nunfashi. "Ke uban miye kika wani rugo da gudu. Kin tsorata mutane".  "Kyankyaso ne". Asmart tace wa Ameera. "Asmart Wallahi in kika kara mana wannan iskancin san naci ubanki. Ya zaki ringa fitgita mutane?.

Ameera na fadar haka ta juya ta koma ciki. Asmart tsuke baki tayi tana kwaikwayan maganar Ameera din. Nasmat ce ta Dan dake ta. "Ke gaya min me akayi ni dai nasan yanzu ba kyankyaso bane. Tunda naga baki fito da 'yar babyn ba".  Wata muguwar harara asmart  ta dakawa Nasmat. "Yar banza ni ai ba ruwa na dake ke dama ashe kinsan abunda ake ciki shine kika min shiru inawa aljanar tambada. Waii!! Ai yau naga ta kai na. Al'quran har na fidda rai!".  Labarin  abunda ya faru da ita taba wa Nasmat tace harda targa de. Sai dai tana duba wa kuma taga babu. Abun ya bata mamaki matuka. Nasmat ce ta fara gagaba dariya mai makwan taji tausayi dariya harda rike ciki. Sai da taba wa Asmart haushi ta cika tayi fam! Kamar wacce zata fashe tsabar zuciya. Sai da Nasmat tayi dariya mai isarta tukun ta tsagaita ta bawa Asmart labarin abunda ya faru da ita ranar Biki ta kara da cewa "Zuwan da nayi Gidan bikin ba dan Allah bane Aljanar ce ta tilasta ni tasa nayi mata wanka harda kwaliya". Hahahhahhahahhaha Asmart ta fara gagaba dariya ta rike ciki. Nasmat ta bata rai "Bansan iskanci fa Asmart kinsan dai ni yayarki ce".  Hhahahhahh "Sorry ni kinsan abunda ya bani dariya ma wau da Kika mari fatima kan ya guntule kuma ta dauko ta biyo ki da shi zan so inga ya kika yi a lokacin.

"Nasmat ta danyi murmushi Sannan tace "Hmm ai ranar naga tashin hankali wallahi.  Kai a yanke fa ya biyo ni yana magana".   Asamrt tace "Ai kinyi kokari da nice da suma zanyi a gun". Yatsa Asmart ta dora a kan habarta alamun tana tunani. Can kuma sai tace "Nasmat ni kuwa inaga mun sama hanyar da zamu ringa yin mugunta a sauka ke". "Ban gane ba me kike nufi?".

"Yanzu zan fahimtar dake, Sa nin kanki ne gaba daya mutanan gidan nan mugaye ne ga Fatima, abu kada take musu su hauta da duka ko Zagi. To kinga kuma a yanzu daga an taba ta aljanar  ke rama mata".  Tsallan murna da jin dadi Nasmat tayi"Shegiya Asmart kanki yana ja sosai. Kinma san me na tuno da kika fadi wannan maganar. Wallahi sai na tuno malamin islamiyyar mu shi ya kamata mu danawa bomb".  Hahhahaha "Kyale mugu Ai mu shikenan mun sama hanyar mugunta kum....".  Fatima ce ta Rugo da  gudu hannunta rike da 'yar baby, ta nufo su tana cewa "Aunty 'Ya ta na kuka wai madaya take so". Su kuwa suna ganin ta suka yi waje da gudu..
_____________________

Kullum tunanin su Nasmat a kan yanda zasuyi su hada malamin su da Aljana ne. Yau ma zaune suke su biyu  a falo asmart ce tace. "Ni Wallahi bana so mu fara yin muguntar nan a kan kowa sai malam, Wai shi mugu zai ga mugunta ai. Yanzu dai hanyar da zamu bi dan mu hada su fada ya kamata mu nema".   Nasmat tayi tsaki, "Ni fa tsoro ma nake aje yafi karfin ta kinsan fa duk karfin aljani malami in dai mai tsoran Allah ne sai yaci ubansa".  Hahhaha Asmart tayi dariya "To ai kinji yanda kika ce in mai tsorab Allah ne, kin manta irin zaluncin Malam habib Jifa dan yana san wannan tsigai din duk wanda ya ko harare ta ne sai ya dake sa. Wani lokacin ma fa ba'ayi mata komai ba sai ta hada mutum da malam dan mugunta".  Nasmat tace "Zainab  ba, Ai ni haushin ta nake ji Allah yasa Aljanar ta hada har ita yanda take 'yar siririyar nan kuwa zatayi gudu". Dariya suka yi gaba daya. Suna cikin dariyar sai ga Ameera ta shigo hannunta rike da leda baka. A yangace ta zo ta zauna a gefe daya ko kallansu batayi ba. Su kuwa tun da ta shigo ledar suke kallo sun san saurayin ta ne ya kawo mata wani abun.

Tana bude ledar kamshin soyayar Kaza ya daki hancin su kamar wanda aka kira suka zo suka zauna a gefanta suna Lasar harshe kamar mayu.   Kaza ce dankwaleliya da Robar Madara katuwa mai sanyi. πŸ˜’ Muguwar harara   Ameera ta wulla musu hade da tsawa. "Nasmat Asmart ku kiyaye ni Wallahi zanci uban yarinya. Kaji yara kamar mayu daga ganin abu sai ku wani taso kamar an kira ku".  "Haba auntynmu ai gani mukayi kayan Allah na Annabi ne". Cewar nasamt  "Kaji uwar iyayi wato duk zaman mu dake ban isa a ce min aunty ba sai yau dan an ganni da dan abu na ko. To wallahi ba wanda zan bawa". Zumbur Asmart tace "al'quran sai munci".

"Sai kunci saiku.....".  Ameera jin wayar ta na kara ta tsaya da maganar da ta dauko, Ta kara wayar a kunne. "Hello Habibina, Ok in fita?. To gani nan. (Just 5mints). Tana fadar haka ta tatara kayanta ta tashi cike da zumudi ta nufi dakin su. Kallo kawai su Nasmat suka bita da shi.  Tana shiga dakin taga Fatima a kwance rungume da 'yar ta sai barci take. Da har tayi niyar tayar da ita kuma sai ta fasa a cewar ta idan ta tashe ta Fatima ma cewa zatayi sai ta bata namanta. Bayan ta tabbatar da ba kowa a dakin su nasmat basu biyo ta ba kuma. Karkashin gado ta  tura ledar ta lulube da bedsheet ta fita da sauri amsa kiran masoyin ta dake kofa yana jira.  Su Asmart kamar jira suke ta fita da gudu har rige-rige suke wajen shiga dakin. Bincike suka farayi da kyar suka gano ledar a karkashin gado. Kamar kazar ta uwarsu ce, Kowa ya ciri cinya daya-daya da sauri suka cinye abu ga marar gaskiya. Yegot din kuwa kowa korba Uku-uku suka yi suka hakura. Dariya Nasmat tayi na mugunta can kuma tace "To yanzu ya zamuyi". Dan jum kadan

Asmart tayi tukun ta kyalkyale da dariya. Nasmat tace "Miye?".  "Kinga kalle ni dai kawai samin ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman taje ta ajiye a kan gadan Fatima da take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta Sannan ta shafa mata abun madara a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta...................................

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 43-44

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU* 😍 πŸ‘‡πŸ½

*HASSAN ATK TANKO*

*HUSAINI ATK TANKO*

*UMMU BASHIR*

*BEAUTY QUEEN*

*SAMEE KHAIRAH NOVELS*
_Jinku nake a can karkashin Zuciya na_

*PHAREEDA KHAMSHI NOVELS*
_Kuna sani inji kamar ni King din gaske ne_ lolz

*BIGBOY ISAH FANS*
_Kukan na daban ne banda kalaman da zan yabe ko ko gode muku sai dai ince. Allah ya saka muku Allah ya barmu tare_

*KINGBOY ISAH NOVELS*
_Kun riga da kun zama 'yan uwa na jinku nake kusa da Raina. Auntys da sisters king dai na ji daku Allah ya bar zumunci_

😍 Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare πŸ™‹πŸ»‍♂

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Kinga kalle ni dai kawai samin ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman taje ta ajiye a kan gadan Fatima da take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta Sannan ta shafa mata abun madara a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta.~

»»Kara bushewa da dariya. Da sauri suka fita daga dakin suka koma falo suka zauna suka ci gaba da tadin su kamar basuje ko'ina ba.  Ameera na dawowa dakin ta shiga a bakin kofa tayi birki tana kallan kan gadan Fatima.  Murje idanu tayi domin ta tabbatar da abunda idan nata ke hangowa gaskiya ne ko kuwa.  "Kutu...". ta kawo ashar ta maka yayin da ta nufi wajen Fatima din a masifance. Dim! Dim!  Ta hau ta da kulli baji ba gani, bata ma da kuka ta farka bata sana hawa ba batasan sauka ba sai duka kawai da taji. "Wallahi, yau sai naci ubanki a gidan nan wato har ni zan ajiye abu ke munafuka ki dauko ki ci min".  'Yar babyn ta dauka tayi tulli da ita a bango sannan ta kama Fatima da hannu biyu  ta daga chamak!. A falo ta dire ta ta dauki wayar charger ta fara bulala ta.  Kuka sosai Fatima tak tana fadin "Aunty me nayi miki?, me nayi miki?".  Ita kuwa baji ba gani kawai dukanta take, Fiddausi na kitchen tana jin kukan Fatima ta fito a guje tana zuwa kuwa ta dauke Ameera da mari. Dafe inda aka mare ta din tayi "Kanbuh!  Ni kika mara".  "An mare ki azzaluma kawai so kike ki kashe wannan yarinyar ne ko dan kinga bata da mai rama mata ne".  Safuratu dake gefe wadda su basa ganin ta tace, "Ga mai rama mata nan kuwa".  kukan kura Ameera tayi ta cakumi wuyan Fiddausi nan itama kuwa ta kamata suka fara kunce da da naushin juna. Can Allah bawa Fiddausi sa'a ta wulla Ameeera da kadan ta fada kan Asmart  t goce tana dariya. Ameera a fusace ta taso ido cike da kwalla ta kara kama Fiddausi. Su Nasmat kam gefe suka koma suna ta kyalkyala dariya suna kuma kara zugawa. Karar dariyar su ce ta fito da mutanan gidan. Fitowar mama asiya tayi dai-dai da kwada Ameera da kasa a karo na biyu. Da gudu ta rugo tubur-tubur tana zuwa kuwa ta nufi Fiddausi ta dauke ta da mari.

Kaji 'yar iskan yarinya mutuniyar banza kawai, kashe ta zakiyi sanin kanki ne kin fita karfi amma ki ke mata irin wannan kadi?". "Ai in ban kashe taba ita zata  Fatima". Inji Fiddausi ta fadi tana kara murtuke fuska.  Mama asiya ta rike baki cike da mamaki "Innalilahi, Wai dama saboda wannan mayyar yarinyar ne kike nema ki kashe 'yar uwarki. To Wallahi bari kiji daga yau Sai yau kar in sake ganin kunyi fada da 'yar uwarki a kan Waccan tsinanar Fatimar ko kashe ta zata yi ba ruwanki to ta mutu mana miye amfanin ta dama".  Fiddausi hararen Ameera tayi da take gefe ido ya kawo kwalla. "Chabb! Wallahi bazai yuyu ba. Taya ina kallo za'ayi zalunci a gaba na Wallahi ko yanzu ta dake ta sai na rama mata. A'ah a kan me".  "Haka kika ce, Haka kika ce. Wai ni kam Fiddausi yaushe kika zama marar kunya fitsara ra haka ne. Wai yau har ni kike kallo idona kina mayar min da magana san ranki?".  Duk abunda ake Su Zuwaira gefe kallo kawai suke ba wanda yayi magana a cikin su. Mama asiya ta kama hannu Ameera ta tura ta. "Je ki daki Fatima muga a gaba na zata rama mata din ne?".  Ameera kuwa ba kunya ta nufi gurin Fatima da sauri da nufin Fatima ta wanke ta da mari da juyowar ta kuwa Fiddausi ta dauke ta itama da mari mama asiya ce ta nufo ta da sauri da nufin ta dake ta. Da sauri zuwaira ta shiga tsakanin su. "A'a Wallahi bazaki dakar min 'ya ba haka kawai. Ai idan ki zo bincike ya kamata ki fara yi ba zartar da hukunci ba".

Mama Asiya tace "Au! Ni zaki wa gorin 'ya zuwaira, To naji malama bari inyi bincike kamar yanda kike so. Amma fa in aka kama Fatima ce da laifi yau ba mai kwatar ta a gidan nan ni da kaina zan ci uwarta". Ta kalli Ameera  tace "Ke gaya mana me Fatima tayi miki, Duk da dai nasan kece mai gaskiya amma tunda Su malama Bincikatu ansa mu ai dole muyi bincike".  A shagwabe Ameera ta fara magana "Mama wai fa habib ne ya kawo min Kaza da yegot Nazo na zauna kafin in fara ci shine ya kira ni.To dan kar in barwa wadan can jarababun su cinye min shine na tashi naje na kai karkashin gado ashe Fatima na jina shine tayi kamar barci take sai da taga na fita ta dauki ta cinye min cinya biyu Yegot din ma ta kusa shanye wa bari kiga sauran da ta bari". Tana fadar haka ta Nufi daki da sauri domin ta dauko. "To kinji ko?, Kinji ai ke mai Fatima to kinji munafurcin da tayi ko har yanzu kina goyan bayanta?, Bari ta zo da kazar Ai Kinga sai ki biyata tunda har kinda Karfin halin rama mata in an dake ai bazaki Rasa zuciyar biya ba in tayi barna".  Mama asiya ce ke kallan Fiddausi tana fadar haka. Fiddausi kam bata ce komai ba amma a zuciyar ta tana shakkar maganganun Ameera. Asmart Rai a bace ta dan matsa wajen kunnan  Nasamat tace "Assha abu ya baci fada ya tsaya a kan mutane ni kuwa Wallahi Aljanar na so taci uban Ameera".   "Ke dai bari ai nima naji haushi Wallahi, Bomb din nan bai tashi a  dai-dai ba".

Ameera na bude kofa taga mage ta kama ledar Kazar da baki ta nufi ban daki da gudu. Ai kuwa ta bita tana "Keeey! Keeey!".  Tana wurwurga hannau alamun korarta take.  Tuni magen ta Shige Toilet din. "Wallahi sai na amso abuna ba bandaki ba ko cikin kashi zaki shiga. Shegiyar mage ko daga ina ma oho".  Ameera ke maganar yayin da ta nufi bandakin da sauri.  Tana bude kofar ta Zura kafa sai ji tayi kamar anja kafar ta fadi kasa sharaf!.  Magen ce tazo tabi ta kanta da gudu har yanzu da ledar a bakinta. "Wash! Wash!". Ameera ta fada ta kuma tashi cikin karfin hali ta bi magen dake taga karkashin gadan Su Nasmat ta shiga. Zuwa tayi ta durkusa ta tura kai Tana lekawa. Magen taji ta kama hancin ta. Wani mugun ihu!  Ameerar tayi. Dan ji tayi kamar zata cire mata hanci  da sauri ta fiddo kanta tana laluba hancin ko jini ya fito. Sai da taga babu tukun ta dan sama natsuwa. Kamar daga sama sai jin magen tayi ta duro a kanta ta fara yakushin ta tana karta mata farce a ko'ina Ihu! Ta fara tana faman kaka be ta. Can Allah ya bata sa'a ta yi wurgi da magen. Magen na zuwa kasa sai kuma ta mike da kafa biyu ta fara tafiya irin ta mutana. Murmushi magen ta nufo Ameera tana yi "Kawata ni zaki di ga yiwa iyen wannan?. Ce kace dai baki shan ko ni wacece ba ni ce fa". Magen ke magana wa Ameera maganar irin ta yara. Karkarwa Ameera ta fara. Mugun tsoro ne ya kamata nan take ta fara kuka domin tama rasa abunda zatayi.

Durkushe wa tayi kasa tana bada hakuri hade da cewa magen tayi mata rai!.  Wata 'yar siririyar dariya magen tayi lokacin da ta zo tana zagaya Ameera da kafafunta biyu biyun kuwa tana jujuya su kamar hannu.  "Haba kawata ni fa ba abunda zan miki ko baki gani ni ba ni ce fa".  Aljanar ta fadi haka lokaci da ta tsaya a gaban ameera ta tsura mata idanu da suka juye suka koma Ja Blue. Ameera kallo daya tayi mata ta kara tsoracewa. Domin ko a tarihi bata taba jin mage mai (blue eyes) ba, wannan  ya tabbatar mata da cewa aljana ce. "Dan Allah kiyi min rai!. Me nayi miki dan Allah me na tsare miki idan naman kike so ki dauka Wallahi na yafe miki, kuma Wallahi nayi alkawarin zan sayo miki rago dan Allah amma ki kyale ni".  Murya na rawa Ameera ke magana haka duk jikinta rawa yake. Magen hannu tasa a bayanta ta fiddo w wani dan  bakin glass (ko daga ina oho) makala shi tayi a fuska. "To shikenan tunda kin tsane ni na tafi bazan kara kawo miki ziyara bama".  Ameera cike da farin ciki tace  "To Mama na Allah ya tsare hanya". Magen ce ta juyo "Au! Na manta ban gaya miki ba na iya kitso ko za'ayi miki?".  Da sauri Ameera ta dago "A'a Wallahi na gode jiya aka min". Ta bude kai "kin gani ma". Ta bude kai kafin ta dago taga ba magen sama ko kasa. Tashi tayi cike da tsoro tana waige-waige a dakin.  Fitsarin tsoro ne yazo. Da sauri ta nufi ban daki dan ta juye shi.  Bude ban dakin tayi hade da ihu!.  Itama ta cikin ihu tayi.  Ameera ce  ba bambanci ko kadan har kayan jikin ta. Baza ka iya banbanta su ba.  Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da dan yatsa "Ke wace ce ke mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen tambayar "Wacece ke ko aljana ce?...............................................

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 45-46

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU QUEEN HAUSY* 😘

Wannan page kyauta na baki, Ina taya ki murnar kammala littafin ki

πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦
*ILLAR BASHI PART 1*
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’§πŸ’¦πŸ’¦πŸ’§

Littafin ya fadakar kuma ya tunatar hade da Tsoratar wa ga masu cin bashi Suki biya. Ina fatan wannan ya zama izina ga masu irin halin Cin bashi Su tuba su Daina In kuwa ba haka ba Suma  Zasu iya ciyo bashin Aljana kamar yanda Yake a littafin😘

Mun gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya baki hakuri kici gaba suburbudo mana Littafai. Muna jiran Next 😘


*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da dan yatsa "Ke wace ce ke mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen tambayar "Wacece ke ko aljana ce?.~

»»Bangane me kike nufi ba. Ai nice Ameera dama akwai wata Ameera ne mai kama dani komai-da-komai kamai ni?.  "Aljanar ce ta kwada ihu! "Wayyo aljana" Ta nufi kofa a guje da ganin haka itama Ameera ta da sauri.  Mama asiya a tsaye sai fada take kirtawa Fiddausi ba wanda ya kula ta ihu! Suka ringa ji har na mutum biyu ta cikin dakin.  Hakan yasa suka tsare kofa da kallo. Ameera Aljana ce ta fara fitowa a guje tana ihu ta rukunkume Mama asiya da kadan ta kayar da ita. "Miye-miye?". Haka mama Asiya ta fara jero wa Ameera aljana tambaya ita kuwa kofan daki take nuna wa tana fadin "Mama Aljana...".  Kafin ta rufe baki sai ga Ameera ta Asali ta fito daga daki sautin Muryar ta da kuma ganin ta da akayi shi ya firgita duk  'yan dakin gaba daya akayo waje da gudu. Ameera kuka ta fashe da shi ta bisu a guje tana fadin "Mama ni ce fa wannan ce aljanar".  Mai gadi na dakinsa da jin ihun jama'ar gida da sauri ya dauko Adda ya fito ya nufe su yana kiran  "Mine ne-Mine ne?.  Nasmat da Asmart sune gaba wajen gudu da su ya fara cin karo basu tsagaita da gudun ba suka bashi amsa "Aljana ce". Da fadar haka ya buga ta kobi a kasa tayi dan kara cike da kuri yace. "Kul!-Ubanta Aljanar".  Ya nufi falo a guje Ya kusan isa kofar falo kenan sai ga Ameera ta  fito da ganinta yaja wani uban burki ya fadi kasa a tsora ce domin yaga Ameera a cikin 'yan gudu

"Dan Allah Aljana kiyi hakuri ki rufa min asiri na tuba bazan kara ba. Duk abunda na fada Wallahi cika baki ne  ban dauka da gaske Aljanar bace". Da sauri Mai gadin ke fadar haka yana jan kugu yana da baya-da baya,  Hannu Ameera ta mika mishi "Mai gadi Wallahi nice Ameera. waccan ce Aljanar Wallahi taba ni ka gani".  Ai kafin hannuta ya karaso gare shi tuni yayi wani irin juyi Ya tashi ya zabga a guje. Duk uban gudun da su Nasmat suke yi sai da mai gadi y tarar da su har ya wuce su, Bai bi ta kan bude gate ba domin gani yake kamar bata lokaci ne Ta kan Gate din ya haura su Nasmat lokacin suka karaso ganin sunja gate din a kulle yasa suka fara kokarin hawa ta gate  suma.  Tuni Suka haye Su juwaira mama asiya da hauwa Duk sun tsure Ga Nin Ameera ta nufo su Tana fadar "mama nice Wallahi ta kusa da ku ce Aljanar". Itama kuma Aljanar abunda take fada kenan cikin tsiwa Kara rikita Su mama asiya take da fadin "Gata nana aljana Aljana". Gaba dayan su rudewa suka yi kowa jikinsa rawa yake. Ganin wannan ba mafita bace Juwaira da Hauwa suka fara kokarin Haurawa ta gate din suma.  Mama asiya dake tasan jikinta yayi nauyi ko gwada wa batayi ba. Sai bada hakuri wa Ameera take.  Juyawa tayi ta kalli su Juwaira da har sun kusa haye wa. Wani mugun bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta. Domin taga zasu gudu su barta. Kafafuwan su ta kama da nufin itama ta hau kan gate, Abunka da mai jiki tana kamawa kuwa ta rinjayo su. Da nauyinta suka rikito kasa gaba daya. Ameera Aljana ta faki idanunsu ta mayar da hannunta key ta bude gate din Da gudu ta fita tana "kufito karta cinye ku". Tashi sukayi Kamar ba sune suka fado daga sama ba a million suka fito daga gidan Ihu! Suke da karfi suna fadin jama'a Aljana Ita kuwa Ameera bata dai na binsu ba.  Su kuwa su asmart lokacin da suka diro daga gate tuni mai gadi har ya kusan fita daga layin ai kuwa suma suka bishi tuni sun bar layin.

Tafe suke shida amaryarsa A tsakar gida sun nufo wajen mota da alamu fita zaiyi.Dam matashi ne cikin shigar sa ta 'yan sanda ASP Abdul King Article kenan. Ba abunda yake zurarwa amaryar nan sai karya. "Ai in gaya miki Zainab ba karami dace kikayi ba da kika same ni a matsayin miji. Wallahi kin gama dace wa".  "Allah mai gida". Amaryar ta fada cikin mamaki. "Allah kuwa. Ke kinsan irin jarumta ta kuwa?. Duk garin nan magana ta ake duk inda kayi sai dai kaji ana maganar Asp Abdul King Article, Irin barayin da nake kamawa da 'yan iska Allah yayi yawa da su. Ke ni fa ko Aljani yayi sata in dai a yanki na ne ina tabbatar miki kafin Gobe sai na shako shi".  "Kai mai gida Aljani kuma?, Ni fa gaskiya tsoran Aljanu nake yi".  Hahahaha 'yar kuntuwar dariya ya yi "Kamar dai kin manta labarin da na baki ranar nace na kama barawo Aljani kin dauka wasa nake ko?. To ai shekaran jiya ma na kama aljani barawo". Ya fada yana  wulwula yar feston din dake hannun sa.  "Innalilahi, bani labari mai gida". "Wani dan iskan barawo muka kama a Kasuwa ya saci waya ashe   Alja...". Bai karasa maganar ba suka jiyo ihun su mama asiya Ana Aljana-Aljana. Mai gida kamar fa Aljanar nake ji

Ana fada kuma kamar neman taimako suke".    "Ai na gaya miki da na damki wuyan  barawan nan na fara jibga..." Asp ne yake wannan maganar dan a manta da Zancan. Zainab ta fahimce sa hakan yasa ta takura mishi Sai da ta tursasa shi a kan sai yaje ya gano. Bai so ba cike da tsoro ya nufi gate din tana biye da shi a baya. A hankali ya bude gate din ya dan leka lokacin kuwa yaga su Juwaira a guje sun wuce suna faman ihu ciki har da Ameera ya gani. Juyawa yayi baya dan ganin abunda ke binsu din. Yana ganin wannan ameerar sak! take da ta gaban. Tsoro ne ya kamasa dan yagane alamun wannan ce aljanar. Da karfi ya juya ya banke  Amaryar tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje. Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a mats........................

Alqur'an Na gaji πŸ™Š Dama yau bajin type din nake ba.

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 47-48

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

*DEDICATED TO YOU* 😘 ♥♥
Mineert Jibir
Jiddah A Adam
Musa Umar Abdullahi
Bilkisu Yusuf
Ummu Muhsin
Sadiya Bala
Hauwa Agabi
Maryam M Gidado
YearRya Yr Abba
Rabiu Shehu Ps
Jamila Mahmud
Naseer Saleh Babaiye
Sunusi Yusuf Jammo
Yariman Masoya
Maman Kawu
Yusuf Jibril Umar
Aslamiyyat Islam

*HAKIKA KU MASOYA NE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI NA KUMA GODE DA ADDU'O'IN KU. HAR KU WANDA BAN AMBATA BA. KUMA RAI NA. A KWANA A TASHI WATA RAN ZAKU GANKU.*

Nasha dariya ba laifi. Saura kuma yanzu zakuyi taku.

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Da karfi ya juya ya banke  Amaryar tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje. Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a matse yake...~
_»»Haka itama Zainab haka Duk da wajen ya matse su Sai da ta kutsa ta shiga. Shiru suka yi na 'yan mintuna. Zainab tace "Mai gida wai miy...".  Kafin ta rufe baki yasa hannu ya toshe mata baki. Yana cewa. "Kiyi shiru karta jimu". Ciki  rada.  Sun kai kusan mintuna 10 a cikin sunyi mukwai. Tukun can Asp ya dan leko dakin ganin ba komai yasa ya karashe fitowa. Kai gado ya fara yana wash! Wash!. "Mai gida gaya min wai me ya tsorata ka haka ne?. Nayi mamaki abunda ya tsorata ka yanda kake jarumin dan sanda mai fada da Aljanu..." Zainab ce ke maganar kafin ta karashe zancen da ta dako. Asp ya katse mata  "Keee!. Rufa min asiri wane ni fada da Aljani kinga karki jawo min".  "Haba mai gida kamar ba kai ne yanzu ka gama fada ba. Kace kana kama aljanu kana cin...". Nan ma bata karasa zancen ba ya dakatar da ita.   "Zainab nafa ce miki ki raba ni da zancen aljanun nan. Ke inda kinga Aljanun da suka biyu wadancan muta nan da daga nan sai dai a dauko ki kinyi dogon suma. Kai!, Ban karashe tabbatar da jarumta ta ba sai yau".  Asp ya fada yana kallan Zainab dake tsaye bakin ta dauke yake da uwayan tambayoyi. "Bani labari mai gida dama ba Aljana daya bace, ni ji nayi kamar suna fadar Aljana-Aljana".  Asp ya gyara zama tukun yace "Ai in gaya miki ba aljana daya bace. Aljanu ne sunkai dari tun daga farkon layin nan in gaya miki aljanu ne har kofae gida.abunda yasa kuma kika ji su suna fadar Aljana, Ai wata Narkekiyar Aljana ce a gaba. Kingata wata makekiya kamar bishiyar kuka. Idanunta in gaya miki sun kai girman tulu. Ga wasu uwayen hakora Kai fin su da gani sunfi Raiza. Hancin ta kuwa sai a tusa mu mu biyu. Gashi a wani tabe Bama wannan ba wuta ce ke fita ta cikin sa. Kanta kuea wani makeke duk girmansa ba gashi sai wasu kwara uku dogaye wanda suka zubo mata har kusan gwiwa. Gata baki kirin"._

_Karkarwa Zainab ta farayi domin tuni Tsoro ya kamata. "Innalillahi, Mai gida Wallahi har naji mugun tsoro ya kama ni. Da gaskiyar ka da ni ce na ga wannan mugun abu Wallahi da suma zanyi a gun. Na gode Allah ma da yasa ban gani ba".  Tana fadar haka ta nufi kofar daki ta garkame cike da tsoro ta dawo ta haye kan gado can ta dukun-kune wai ita da gaske tsoro ya kamata.  Dariya yayi, "Hahahhahah kai haba dai Xainab karfa ki bani kunyi. Ba'a san matar dan sanda jarumi irina da tsoro ba, Ai ke baki ma san wani abu ba. In gaya miki lekawar da nayi Wai Aljana nan tayi man nuni da hannu alamun in zo. Ni kuwa naga tama raina min wayo hakan yasa na dalla mata wata muguwar harara irin wacce nake wa kananun aljanu suna zabgawa a guje, nan take itama kannun aljanun da suke tare da ita wajen guda goma suka zube sume.To wai ashe ita har ta ji haushi Nan fa ta fusata   ta nufo ni gadan gadan.  Abunda fa yasa na rugo da gudu kenan._

_"Lalai mai gida kai sadauki ne kuma jarumi. Ai in da ni ce da sai dai a dauko ni a group".  Wani dan kara ne suka ji alamun an dan taba kyaure, Ai kuwa Zainab ta kwadda ihu! Kafin kace kwabo Asp king Abdul tuni har ya haura gado ya Shige blanket. Jin shiru ba abunda ya shigo dakin ne ya sa ya fito nan ya fara kokarin Cire kayan 'yan sanda dake jikinsa. "Yallabai ya naga kana faman cire kaya kai da zaka p
Office?". Zainab ta tambaya, "Amma sai yau na gane bakya kauna ta. In fita wato aljana ta wujijiga ni ko?. To in gaya miki ina nan ba inda zani yaseen yanzu bara in kira Dpo in sheda mishi bani da lafiya"_.  

_Asmart da Nasmat tare da mai gadi ashe da suka sha kwana wani waje suka samu suka boye. A cewar mai gadi "Aljana ta fimu gudu duk gudun mu sai ta kamo mu gwara mu labe kawai ta zo ta wuce".  Ameera aljana ita ce a gaba wajen gudu sai Zuwaira da Hauwa suna biye da ita. Can baya kuwa Mama asiya ce a tubur-tubur Gudun da take yau bata taba yin kalarsa ba. Ameerar gaskiya tana ce mata "mama ki tsaya ni ce".  Duk sanda Ameera ta fadi haka ita kuwa sai taji kamar cewa tayi. Tsaya in yanka ki hakan ke sawa tana kara kaimi  a gudun nata duk da ta gaji.  Ameera Aljana tsakanin kwana-da-kwana ta bace bat!.  Su Zuwaira na shayo kwana suka ga ba mutum. Tsayawa sukayi cik!  Suna haki. Su asmart ne suka fito daga inda suke a boye suka fara Wa su Juwaira tambayoyin "Ina Aljana". Juwaira tace "Bakugwa Ameera ta shayo kwana ba?".  "Ko daya mu bamu ga wata Ameera ba".  Cikin daga murya Hauwa tace "To alqur'an wannan itace Aljanar tunda kuka ga...".  Bata karashe magana ba sai ji tayi anyi ciki da ita. Dake bakin kwana take kuma lokacin su Mama asiya suka karaso a guje.  Sanda suka wuntsula domin da karfi mama Asiya  ta bangaje ta.  Ameera na shayo kwana gaba daya suka yi shirin rugawa. "Ku tsaya- Ku tsaya wallahi ni ce Ameera ta gaban ce Aljana wacce ta fara zuwa".  Tsayawa suka yi a tsorace suna kare mata kallo. Kallan zargin da suke mata yasa ta miko hannun "Ga hannuna wata ta taba ma taji Wallahi ni ce"._

_Kowa baya-baya ya farayi Hauwa ce ta kama Asmart tana kokarin Turo ta wai ta taba taji. Ita kuwa Asamrt ba abunda take sa kakafe wa tana cijewa, Ihu! Ta fara da taga hauwa ta fara turo ta da karfi ga Ameera na matsowa. "Wayyo Allah uwa ta, wayyo baba wayyo jama'a ku taimako zasu kashe ni".  Asamart ce mai fadar haka da karfi.  Abun ne ya bawa Juwaira haushi Zuwa tayi ta tunkuda Asmart da karfi. Ta fada jikin Ameera ta rungume ta. da ganin haka sai kowa yayi duk sai suka ji dadi sai yanzu suka 'yarda da Ameerar ta gaskiya ce. Nan fa aka fara tafka mahawara wasu na fadin a koma gida wasu na cewa Wallahi ba abunda zai mayar da su. Har yanzu mai gadi Bai fito  ba daga inda yake a Labe domin shi gaba daya kunya ma yake ji. Kamar daga sama suka jiyo maganar alhaji. "Innallilahi Wa'inna illaihir raja'un, Mai zan gani haka".  Alhaji ne ya fadi haka lokacin da yake kokarin fitowa daga mota.  "Me ya faru Asiya nake ganin ko a Waje Cikin ku ba ko mai gyale?". Mama asiya da take a tsugunne dan tsabar gajiya da tayi ta Dago. "Yo alhaji tunda m ma baka ganmu ba zannuwa ba Ai sai ka gode wa Allah. Aljana ce  fa Ta koro mu daga gida".   Alhaji ya bata rai yace "Bana san zancen banza Aljana ko dai tsoran ku. Oya kowa ya shiga mota". Yana fadar haka ya juya ya shiga gidan driver ba yanda suka iya domin sun san halin Alhaji dole suka hakura suka shishiga.   Sai da suka isa kof Alhaji yata oda a nufinsa mai gadi ya zo ya bude. Sai ma lokacin suka tuno da mai gadi. Fiddausi tace "Baba ai harda mai gadin muka gudu tare ma muka buya da shi". Tsaki alhaji yaja kawai ya fito ya bude Gate din da kansa suka shiga. A falo suka tarar da Fatima tana kallon Tv  tana wasa da Babyn ta ba abunda ya dame ta._

_Su mama Asiya jaraba suka bita da shi wai wata kil ma itace aljanar. Alhaji na shigowa duk sukayi tsi! "Gobe zanyi tafiya wajen wani aiki kuma zanyi kwana biyu can, Yanzu ma shirye-shirye na taho in fara domin Tashin asuba zamuyi. Idan da mai matsala zata iya biyo ni ta fada".  Yana fadar haka ya kama hannun Fatima yaja ta suka nufi sama.     Suna tafiya Mama Asiya tace "Wai baku lura da wani abu kuwa". Gaba daya suka tambaya "Kamar me kenan?".  "Wannan yarinyar ni fa ban yarda da ita ba. Dama ban fada muku mayya bace ai inaga itace ta zama Ameera dan ta tsorata mu domin gaba dayan mu mun tsora ta mun gudu amma ita kungo a kanta".  Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama asiya tace amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci uban......................._

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 49-50

NA.  ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘

πŸ‘‰πŸ½✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*  ✍πŸ»πŸ‘ˆπŸ½

DEDICATED TO YOU BLOOD ME 😍😘

*TRIPLE QUNEENS*πŸ˜‰

*QUEEN HAUWA HAUSY* πŸ˜˜πŸ‘ΈπŸ»

*BEAUTY QUEEN* πŸ’‹πŸ˜

*QUEEN MARYAM 'YAR MAMAR MU* 😍😘

☺ _→ABUNDA YAKE DAINA, ZANA FITAR NA HUCE TAKAI'CI, SOYAYYAR KU A RAI NA ZANA FADA BAZAN BOYE BA←JINKU NAKE A CAN KARKASHIN ZUCIYAN.   INA SANKU SOSAI IRIN TOTALLY DIN NAN_ 😁

'YAN UKUN ZAMANI KENAN πŸ˜‰

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama asiya tace amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci ubanta…~

_»»Washe gari tun da asuba Alhaji yayi musu bankwana bayan ya bar musu duk abunda zasu buka ta kafin dawowarsa. Mama Asiya kule take da Fatima hakan yasa tun da Asuba taje ta taso ta ta zo ta fara saka ta Aikace-Aikace. Wai sai tayi mopping din gaba daya falo. Har wajen karfe 7  Fatima  na fama amma bata gama  Ba, lokacin Duk matan gidan sun fito domin yin girki. Juwaira da hauwa ne suka taho a jere. Lokacin Fatima na faman goge TV din da ke makale jikin bango sai dadage take yi domin tsawanta bai karasa wa.  Zuwaira ce ta lalabo ta bayanta ta yi  mata wani mugun Dundu kamar wacce ta sama sa'arta. Fatima kuka ta kwalla da karfi. Da fara kukanta hauwa ta Wanka mata mari "Ke rufe mana baki dan uwarki ko in kara miki yanzun nan".  Fatima ba dan taso ta matse bakin ta da hannu kukan na dan fitowa a hankali. "Shegiya kinibabba uwar iyayi, Yau shine zaki tarki wani goge-goge Na karya wato kinga alhaji baya nan dan kinsan yau dakuwa zaki yi a gidan nan shiyasa kika fara aiki tun yanzu ko?". Inji hauwa, Zuwaira tace "Dubi ma duk kin bata wa mutane waje da jurwayi Baki iya komai ba 'yar iska kawai". Kama kunnan Fatima tayi ta murda. "Fada min Uwarwa ta saka ki mopping kika bata mana Falo...".  Maganar Mama Asiya suka ji wacce ta taso yanzu daga barci. "Ni na saka ta domin Yau bata da hutu a gidan nan". Gaba daya suka juya a tare "Au! Aunty babba ke kika saka ta ashe. Af! To ba laifi ai". Lokacin  Mama Asiya ta karaso gurun tana murmushi mugun ta tana kare wa Falon kallo. A zuciya tana cewa "Lalai yarinya kin aikatu". A fili kuwa wata muguwar harara ta daka wa Fatima. "Muna fuka kin wani tsare ni da idanu kamar mayya kina wani kukan karya, Maza wuce kitchen".  Ta Make ta a kai da hannu.  Fatima tana kuka Ta shiga gaba suka bita baya su ukun sai zagin ta suke.  Da aka shiga kitchen Fatima ta aikatu sosai. Domin wani abun ma yafi karfin ta kawai saka ta suke. Su ukun ma sun wa aikin yawa amma dan mugunta suka ki barin Fatima ta tafi ta huta.  Yau dan wake suke yi da Tea ba'a dauki lokaci ba  aka karasa. Zuwaira ce tace wa Fatima ta Tsiyayo man gyada a galan. Duk da tasan Fatima da kyar take iya karka ta galan din. Fatima ba gardama ta dauki mazubi taje ta fara Kokarin bulbulowa. Wani mai ne dan kadan ya Zuba a kasan mama Asiya na juyowa ta gani. Sai ta hau Fatima da duka da kuma masifa haka suma sauran._

_Fatima ta sha wuya gashi sun bige ta sun kuma wanata kuka. Hauwa ce tace, "Munafuka wato kin zubar wa da mutane mai salon yayi saurin kare wa ubanki yazo ya kama mana jaraba yace Ban nata sa muke yi ko. To Wallahi bari kiji Duk yau bake ba abinci a gidan nan". Mama Asiya tace "yauwa kinyi min dai-dai Abunda nake shirin yi kenan. Dan ubanki tunda watan azumi ya kusan kamawa ai dole ki fara koyan azumi. Dama azumi ba sahur yafi lada".  Da fadar haka suka bushe da dariyar mugun ta harda tafa hannuwa.  Fatima kuwa kuka ta saka domin tasan halin su in suka tashi mugun tarsu har fiye da haka yi mata suke. Aljana Safuratu dake tsaye Tana kallan su duk abunda suke. Itama dariya tayi Tace "Tunda kuka yanke wannan hukuncin. Nima na yanke irinsa a kanku. Ni da ku muga wanda zai cika, Ni nace kune bazaku ci abinci ba sai gobe".  Da fada Haka ta sake fashewa da dariya. Duk abunda take kuwa babu mai jinta kuma babu mai ganinta.  Mama asiya ce ta Juye dan waken a wata katuwar kulu wanda tasan Fatima baza ta iya dauka ba. Amma tace dole sai ta dauka Ta kai dinner room,  Fatima  ba gardama taje aka dora mata a kai tana kuka. Tun a nan ta fara Kokarin faduwa. Badan Mama asiya tayi sauri  rike wa ba da duk ya zube. Ai kuwa zagi suka bita da shi gaba dayan su. "Tsinanna so tayi ta zubar kowa ya rasa, To Allah baiyi ba". Zuwaira ce ke fadar haka. Oya karbi wannan saura kuma suma ki zubar, Wallahi da sai na daure ki a gidan nan na zane ki. Na kuma sa kowa na gidan nan ya miki bulala Goma-Goma". Mama asiya ta fadi haka lokacin da ta Dorawa Fatima wasu uwayen farantai da Cokula ta kai Dinning. Fatima da kyar ta kai su domin sun mata Nauyi Haka ta dawo ta kuma jidar wasu kayan abincin. Sai da aka shirya komai tsabb! Dan wake kusan cike da wani katuwan kula. Ga kuma tea da bread._

_Mama Asiya ce tace wa Fatima taje ta sako kayan islamiyar ta tazo ta tafi makaranta.  To kawai ta fada ta nufi dakin su tana shashekar kuka. Gaba dayan 'yan dakin barci suke sai Asmart da Nasmat Da suke zaune suna tsara wani abun suna dariya da gani kasan ba abun Arziki suke kitsawa ba.  Suna ganin Fatima ta shigo suka taso daga inda suke da sauri suka nufe ta ganin tana shirin kuka kuma fuskarta da gani ta sha uban kuka.Nasmat cike da iyayi ta kama Fatima ta dora ta kan gado ta fara share mata hawaye,  Tana fadin, "'yar kanwata waya taba muna ke ne kika taho kina kuka?".  Tana shashekar kuka tace "Ba su mama asiya bane suka ta saka ni aiki kuma suka ce baza su bani abincin kari ba, Wai sai dai in tafi makaranta a haka".  Asmart cike da tausayawa Tace "Ayya 'yar kanwata yi hakuri bar kuka taso muje in miki wanka Kuma in zaki tafi makarantar ma sai in baki Naira Hamsin ki karya". Cike da zumudi Fatima ta Amsa "Toh Aunty Na na gode".  Tashi tayi Asmart tayo mata wanka nan suka zi su biyun suke yi mata kwalliya.  Ko Fatima kanta da take yarinya abun ya bata mamaki, Sai dai hankalin ta bai ka ta gano akwai wani abu a kasa ba.  Asmart ce tace "Fatima daga yau mun daina dukan ki. Kuma mun daina Zagin ki kinji?". Cike da farin ciki Fatima ta Rungumi Asmart "Na gode aunty amma har 'yar baby nama kun dai na Dokanta ko?". Kamar hadin baki da sauri suka ce "Eh daga yau baza mu kara ko taba ta ba". Suna fadar haka suka kalli juna dariya ce ta kusan Kubuce musu jin Sunyi  magana a tare. Nasmat  ce ta datse dariyar ta kalli Fatima tace, "Wai in tambaye ki, 'yar babyn ki ta iya Karatu?".  'Yar dariya Fatima tayi tace "Sai dai magana ko in dauko ta kiji?". Da sauri Nasamt tace aa ba sai kin dauko ta ba, Abunda nake so dai shine yau mu tafi da ita Islamiyya dan ta koyi karatu, Ai kina so kiji tana yi ko?".  Eh fatima tace. "Yauwa yau da ita zamuje Islamiyya ta koyi karatu Daukko ta in goya miki". Cewar Asmart.  Da sauri Fatima ta dauko kayanta  na islamiyya ta saka. Tukun ta daukko 'yar babyn A tsorace suka goya mata ita._

_Suka saka mata hijab dake hijab din doguwa ce Ta rufe 'yar tsanar ba'a ko ganinta. "Karba kudin, Kije wajen mai.shayin can kice ya baki tea Da bread kinji?. In kinci sai ki tsaya a gun ki jira mu yanzu zamu shirya mu fito kinji?". Fatima tace to ta Nufi hanya ta fita. Da fitar ta su biyun suka fara gagaba dariya. Harda rike ciki Dariyar ce ma ta tashi sauran 'yan uwansu da suke barci. Asmaet ce ta dan tsakaita da dariyar ta kalli Nasmat tace "Kai sister amma kwanyar ki naja  ba lalai ba malam ya tsallake wannan target din gaskiya kin iya mugunta".  Nasmat tace "Kyale dan iska Nasan yanda ya tsani Diyar roba. Ko 'yar karama ce. Balle wannan katotuwar. Nasan sai yayi boll da ita in ma bai ce zai toyata ba. Kinga kuwa ita Aljanar ba kyale sa zata yi ba. Wata kil tun a gaban mu ta fara cin ubansa". Wafa dariyar suka dora da ita.  Hauwa ce ta shigo tayi musu magana tace su fito su ake jira ayi breakfast.  To suka ce tukun suka tayar da sauran. Suka je suka yo brush.  A falo aka  baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta fito. Ba'a jima ba sai gata ta fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da  niyar Zuzubawa kowa, Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko alamar lema ma babu balle..............._

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 51-52

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

*DEDICATED TO YOU MAH BLOOD NASMAT ('YAR MUTAN ARKILLAH, AUNTY AMA. KU KAM NA DABAN NE A GARE NI* 😍😘

😍 *SO AKAN CE HADI NA RABBAH, ZUCIYA KU TAKE YABAWA. NASMAT HAR DA AUNTY AMA,  IN BABU KU SAI DAI A DAKAH GUMBA* πŸ˜” *BAYYANAR SO GA WANDA KAKE SO, YA FI RIBA NI KU NA ZABA* 😘

☺ _KOMAI DADI AI BAYYI ZAMA DA MASOYA BAH. SO YAY MIN RANA DAMA DA BAZARKU NAKE TA RAWA KUMA INA._ ☺

_INAI MAKU FATAN ALKHAIRI. DUK ZAMANI WRITERS KU FITO_ πŸ™‹πŸ»‍♂

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~A falo aka  baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta fito. Ba'a jima ba sai gata ta fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da  niyar Zuzubawa kowa, Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko alamar lema ma babu balle.~

_»Kular kamas da ita ko alamar dan wake babu, Domin  a bushe ma take,  Sakin baki hauwa tayi tana kallan Su Mama asiya, Ganin kallon yayi yawa asiya tace "Ya dai hauwa lafiya kuwa, Ki zuba mana dan wake mana kowa fa ke yake jira". Karkato mata kullar tayi suka ga kular wayam, "Kutu.... Me zan gani haka?, To ina dan waken  da yake kusan cike da Kula". Asiya ta karbi kular har shinshinawa tayi taji ko alamun dan wake ma babu. "Kutt! To alquran Wannan ba kular da muka zuba dan wake ce ba. Haba kuji fa ko kamshin dan wake babu a ciki". "Tashin hankali gobarar gemu, To waye zaiyi mana wannan aika-aika ina Fatima?".  Zuwaira ke maganar tana kallan su Nasmat da suma sunyi tsuru-tsuru sai kallan iyayen nasu suke. "Fatima ai tun  dazun ta tafi makaranta tace mana kunce yau baza ku bata abinci ba".  Dajin haka gaba daya hankalin Fiddausi ya tashi Ta bata rai "Haba mama yanzu kun kyauta kenan?. Ya zaku kora yarinya da sanyin safiyar nan makaranta ba tare da ta karya ba. alhalin kuma kunsan ba'a taso wa sai Karfe sha biyu ake tasowa".  Gaba dayan su wani mugun kallo suke wa Fiddausin " buhun ubanki Fiddausi ah! Kaji 'yar zamani, Yanzu mu zaki wa wa'azi To abinci dai in gaya miki yau ko kwaya fatima bazata ci ba acikin gidan nan. Bama iya yanzu ba". Cewar Mama asiya, Zuwaira tace 'Kyale 'Yar banza kamar yanda ta tafi da yunwa ke ma haka zaki tafi da ita tunda kinga kular dan waken, Kuma ba mai sani in kuma shiga Kitchen"_

_Gaba daya su Mama asiya ma haka suka fada, "Dan haka kawai Hauwa raba burodin nan kowa ya zuba tea yasha ya hakura".   Tashi tayi ta jawo daya daga cikin maka-makan biredin wajen guda takwas. Wuka tasa ta yanka tsakiyar biredin mamaki ne ya bayyana a fuskarta ta tsaya tana kallan biredin Cikinsa yayi baki kirin wasu 'yan kananan kwaruka ne ma a ciki suke yawo.  "A'a jiya fa aka sayo wannan biredin bai kamata ace ya lalace yau ba". Asiya ce ta taso daga kan kujerar da take a zaune "Lalacewa kuma kamar ya?". Hauwa ta mika mata biredin tagan shi rube, "Ikon Allah, A inaga wannan shine marar kyau din bara muga".  Wani ta dauko ta yanka shima dai haka ba kyau. Gaba daya sai da suka fasa sauran bire din duk Sun lalace daga ciki amma bayan Ko alamar lalacewa babu. Asiya ta hau jaraba. Tana zazagen Gidan biredin.  "Wannan ai rainin hankali ne, da zalunci. Ya zasu bawa mutane Rubaben Bread to Wallahi sai na mayar musu anjima". Tsaki Ameera taja. "Mtseewww! Mun kusan makara ga malamin mu bashi da mutunci  bari mutum ko tea ne ma yasha". Tashi tayi ta dauki kofi ta karkata wani filas nufin ta ta tsiyayi shayi. "Kan uba!". Abunda ta furta kenan. Gaba daya aka juyo aka zuba mata na mujiya. "Wai ku yau kawai so kuke kuyi mana horo da yunwa kenan. Nan ai ruwa ne zallah ko zafi ma babu". Hauwa tace "mu gani" Ta dauki kofin "lah! Wallahi da gaske take ruwa ne zallah  bayan kuma Ni da kai na na zuba tea a cikin nan"._

_Shiru su mama Asiya suka yi ido kawai suke bin Jama'ar gun da shi. "Mtseew To Wallahi ni dai bazan kuma shiga kitchen a yanzu ba. Haba kamar wata jaka?". Cewar Mama Asiya.  Zuwaira tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba".  Fiddausi tace "To mu dai makaranta zamu tafi sai a bamu kudin Break".   Dari bi biyu mama asiya ta bisu da shi. Tace "Kowa yaje ya sayi abunda zai ci mu dai ba wanda zai kara koma wa kitchen".  Watsewa akayi kowa yaje yayi shirin makaranta.   Su mama asiya kuwa mai gadi suka bawa Naira Dubu suka aike shi yaje ya soyo musu Indomie da kwai.  Asmart da nasmat a wajen mai shayi suka tarar da Fatima ita har ta karya Tana zaune tana jiransu. Suma kudi suka bayar aka dafa musu indomie tukun suka nufi makaranta._
*______________________*

_Zaune yake yana cin Garau-Garau Yana ci yan girgiza kai daka ganshi kasan yana jin dadin abincin Sai da abincin ya rage baifi Cokali hudu ba ya kare, Mutumin ya Wani murtuke ya bata rai!. "Rafi'at!  Rafi'at!  Rafy!".  Kiran yake kwalla mata da karfi. Ba'a jima ba sai ga wata budurwa ta fito ba laifi tana da kyau dai-dai gwargwado. Gaban shi ta durkushe "Mai gida gani". Mari ya kwada mata wanda har sai da taga Taurari nan fa ta kwada ihu!. "To fa safiyar ai tayi, Ke dai Rafy baki yi dacen miji ba ko kadan Wallahi".  "Wai har yanzu Umar bai dai na dukan Rafy ba". Makwabtan su ne ke wannan Hirar. "Ina fa malam ai kullum sai ya dake ta".  "Ashsha! Kai amma dai Allah ya shiryi Umar, gashi daga kayi masa magana sai ya hau ka da masifa yace Ai ba matar ka bace".  "Ai lamarin sa sai Addu'a, Rafy tana da hakuri"._

_"Cikin bacin Rai da masifa umar yace "Yanzu ke Dan Uwarki kinsan wake bai dawo ba shine zaki kawo min abinci wato inci inshiga mutane Ina tusa ana kallona Ana dariya, Haka kike so ko?".  Ya fada yana kallanta. Cikin kuka tace "Mai gida dan Allah kayi hakuri Wallahi na dauka ya dahu ne".  Cokali ya dauka ya kara cika shi ya kai baki, Sai da ya kusan hade shi gaba daya ya Furzo!. "Kan uba!  Ai banji bama sai yanzu haka kika cika yaji a abincin ashe, Ashe so kike ki kashe ni". Da sauri ya tashi ya nufi daki. Kamar tasan abunda yake shirin yi ta fara fadin "Mai gida dan Allah kayi hakuri bazan kara ba Allah". Fadi take da karfi tana mai-maitawa. Da wani Bakin Belt ya fito yana zuw kuwa ya fara Zane ta. Yana Fadin "Bari ni in illataki kafin ki kashe ni".  Ihu! Take tana bashi hakuri amma shi ko kadan baya da alamar Sasautawa balle ma ya kyale ta. Da dai taga yana neman ya hallaka ta sai ta tashi ta ruga da gudu waje, Domin Tasan ba wani wanda zai kawo dauki. Haka yake in yana bugon ta mace ta zo Kwatar ta har ita yake hadawa ya daka. In kuwa namiji ne ya kore shi._

_Fitar ta tayi dai-dai da isowar su Fatima sai tin gidan. Haka ta fito tana kuka shi kuwa ya biyo ta yana fadi "Oya zo wuce ki koma ciki, Ko kuwa Wallahi yau in farfasa miki jiki". Hakuri kawai take bashi tana karawa. Dake tasan halinsa Ba dan ta so ba ta shige gidan a guje.  Su Asmart kuwa abun ne ya basu mamaki. Nasmat tace "Kuturun uba!. Lalai akwai masu hakuri yo ai ina kamar wannan Wallahi mutumin nan bai isa ya dake ni in kyale sa ba, Wai dan yana aure na, Haba kamar wani ubana".  Dariya Asmart tayi. "Wai ke sai yau kika taba ganin wannan azzalumin kenan. Ranar mu ai har ciki sai da muka shiga ni da Ameera ai kuwa ya biyo mu da kadan y zabga min bulala".  Gaba suka yi Aljana Safuratu kuwa tun da taji zancen su nasmat ta fita daga Jikin 'yar tsana,Tace "wannan matar tana bukatar Taimako na, Kuma zan taimaka mata.  Cikin gidan ta shiga ta iske su ya zaunar da ita yana fadar, "Yi min shiru muna fuka. Yanzu zan fita kuma ga naira Hamsin can a cikin aljihun rigar da na cire ki dauka ki auno shinkafa kiyi Cefani ki dafa min Farar shinkafa da miyar tumatur (Jar miya). Cikin kuka tace "Haba mai gida naira hamsin ai baza ta isa ko cefane ba".  Tsawa ya daka mata hade da daga hannun " Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min. Kuma Wallahi idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran".  Yana gama fadar..........................._

*TABB! LALAI ANYI MUGU A NAN*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
mu kayi like.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 53-54

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ˜’ *YAU SAI INGA WANDA ZAICE NAYI MINTSILI, (KARAMI) PAGE* πŸ€”

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

_*WANNAN PAGEN DIN NAKU NE*_

✍🏼  *ZAINUDEEN ZAIN* ✍🏼  😘

✍🏼   *SANAH S. MATAZU* ✍🏼😘

✍🏼 *SANAH SHAHADA* ✍🏼 😘

✍🏼  *RASH KARDAM* ✍🏼 😘

_Malamai kuma abokai a gare ni. Ubangiji Allah ya albarkaci Rayuwar ku, Yasa ku gama da duniya lafiya. Ku Ukun Allah ya baku mazaje na gari wanda zasu zame muku rahama, wanda zasu zare mayafin bakin cikin ku, su lulube ku da na farin ciki.  Haka kai ma dan uwa Zainudeen, Allah ya baka Salahar mace mai sanka dan Allah mai hakuri da juriya. wacce zata Zame maka haske ta kore duhu a cikin rayuwarku._ 😎 Ameen Allah ya amsa....

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min. Kuma Wallahi idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran".  Yana gama fadar.~

_≥»Yana gama fadar haka ya juya ya fice daga gidan. Safuratu tsaye tayi tana tunanin ta ina zata fara ji da wannan matsala, Can kuma sai ta bace bat!. Rafy na zauna sai kuka take abun duniya ya ishe ta ita kam yanzu bata ma san miye abun yi ba. Wata dattijuwa ce tayi salam  Rafy cikin Kuka-kuka ta amsa matar ce ta zo daf! Da ita ta sama waje ta zauna Rafy ba abunda take sai binta da idanu wanda sunyi jawor dan tsabar kuka. Matar ce ta danyi gyaran murya tukun ta kalli Rafy cike da tausayawa "Rafy Nasan kina cikin matsanan  matsanan ciyar damuwa, Naji labari kullum wannan mugun mijin naki sai ya dake to dan haka ne ma..."  Da sauri Rafy ta daga mata hannu  "Dakata baiwar Allah naji na gode da tausayawa amma ba ruwan ki wannan Kaddarar rayuwa ta ne, Dan haka dan Allah tashi ki tafi abunki". Matar ta dan muskuta kadan tace, "Haba Rafy ki saurare ni mana ni taimakon ki zan...". CikinTsiwa Rafy tace "Dakata malama nace bana bukata ki tashi ki tafi abunki, Wai ke din wace ce me ruwanki". Rafy ganin matar na neman dauko wani sabon zance ta tashi ta kama hannunta ta jata har waje tana cewa. "Naji na gode da shawara".  Tana tura matar waje ta garkame gidan da sakata sama da kasa. Juyowa tayi da wani kukan na Takai'ci A zuciya cewa take "Ba taimakon bane bana so. Amma Nasan bazaki iya taimaka min da komai ba".   Daga bayanta taji maganar matar tace "Rafy kiyi hakuri amma fa ni bazan bar gidan nan ba sai na taimaka miki"._

_Rafy na juwa taga Wannan matar ce sai ta kwada ihu! Ta ruga daki a guje nan ma ta rufo dakin._
*__________________*

_Su mama Asiya ne zaune a falo har wajen goma da rabi basu karya ba suna jiran Mai gadi har yanzu bai dawo ba. Mtseeww Mama Asiya tayi tsaki, "Wannan mai gadin sai naci ubansa in yazo Wallahi. Haba wannan ai iskanci ne. Ya zai barmu ko kari babu ya tafi uzurinsa". Tana rufe baki sai gashi ya shigo da sallamar sa.  Mama Asiya kular take kallo tana mata  fassarori Iri-iri kamar da abu ciki kamar babu.  Yana karasowa ya ajiye kular a kasa ta saki sauti Kwangal! Daga ji kasan ba komai a ciki, Gaba daya binsa suke da mugun kallo, Jira suke kawai yace bai samo ba su bal-bale shi da masifa. "Hajiya Wallahi matsala aka samu wajen Mai shaye Biyar naje Duk inda naje sai in samu indomie din ta kare". Zuwaira tace "Kuturun uba!, Amma wallahu kayi mugun rai na mana wayo Akwai mai shayin da za'a je gunsa A rasa Indomie ne?"._

_Haba kyale shi Zuwaira, Inaga dai Wa'adin zamansa a gidan nan ne ya cika. Amma in ba iskanci da rainin wayo ba ya za'ayi ace kamar mu mu aike ka ka dawo mana da kula wai babu".  Mai gadi ganin Aikin sa ya fara tangal-tangal yasa shi fara bada hakuri. Yana cewa "Dan Allah kuyi hakuri karku min sanadin aiki na Wallahi in kuna ma so yanzu sai inje in sayo in dafa muku".    "Kutumelesi Dallah tashi ka bace mana karka fusata ni yanzu in sallame ka a aiki, Dan ma ka raina mana wayo mune zaka yiwa girki?".  Tashi yayi ya fita da sauri ya barsu nan suna tsaki.  Hauwa ta kalle su "Ni fa Wallahi bazan iya wannan abun ba, wannan ai cutar kai ce kawai ku tashi muje mu dafa ko indomie ce".  Zuwaira tace "Sai dai in ke zaki yi taimako ki dafo min ki kawo min. Amma ni tunda nace bazan shiga kitchen ba to bazan shiga ba sai rana tayi".  Mama asiya tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba sai dai ki taimaka ki daho ki kawo mana".   Mikewa Hauwa tayi zumbur! "Kuturun kare, To alqur'an ba wacce zanje inyi aiki in dafa abu in kawo mata tana nan ta Mimike kafafu a falo tana shakar AC".  Mama Asiya ta tashi tana nuna Hauwa da yatsa "Ke karki kuskura, Wallahi karki kuskura ki zage ni".   "Ni kam ban zagi wata ba amma dai maganar abinci nace bazan daho in kawowa wani ba". Tana fadar haka ta wuce ta nufi kitchen._

_Inda suke ajiye kayan abinci ta shiga. Tsaye tayi tana kallan dan Sito (store ) Taga wayam ko Kangon buhu babu balle ma asama mai wani abu a ciki. Haka ma kwalilikan indomie babu ko daya. Tsawa tayi cik! A wajen tama rasa abunyi. "Aunty Asiya!, Aunty Asiya!".  Tun daga can take kwalla kira Asiya na jinta amma tayi kunnan uwar shegu, ta kyale ta. Sai da ta gaji da kwalla kiran tukun ta fito ta gayawa su mama Asiya abunda ke faruwa. Tubur-tubur ta tashi da sauri ita da zuwairar suka nufi kitchen din hauwa na biye da su.  Tsaye sukayi suna kallan Store din suna kallan juna._
*_______________*
_Rafy na daki duk tsoro ya kamata kallan kofar kawai take.  Mace ta gani ta ratso ta cikin kofar, Wani mugun kara tayi a tsorace ta haye kan gado ta wani kudun-dune cikin blanket. "Sunana Safuratu  ni aljana ce amma ba muguwa bace ni. Dan ni nama tsani mugu, Naga mijin ki kuwa mugu ne shiyasa ma nazo dan in taimake ki. Dan haka ki saki jikin ki karkiji tsoro na".  A hankali ta dago tana hada ido da Matar kuma sai ta kara shigar da kanta cikin bargon. Tana magana cikin tsoro, "Dan Allah kiyi hakuri ki tafi na gode amma mijina ba mugu bane dazun ma laifi nayi masa shiyasa ma ya dake n...."  Kafin ta rufe baki Aljanar ta daka mata Tsawa wanda sai da ya rikita ta gaba daya. "Bana san iskanci fa, Wato dan kinga ina lalabaki shine kike min wannan kafiyar Yanzun nan zan mayar dake kaza kuma in kashe mijin naki in baki bani hadin kai nayi abunda ya kawo ni Salun alun ba".  Dajin haka Rafy tayi sauri ta fito. "Dan Allah kiyi hakuri karki mai dani kaza Wallahi zanyi duk yanda kika ce Aljana".  Aljanar ta dan matsa kusa da ita ta zauna. Rafy duk a tsorace take. "To da dai yafi, Kuma ina so ki saki jikin ki ki kaddara a ranki Kamar da mace 'yar uwarki kike magana Ba Aljana ba.  Yanzu fara bani tarihin rayuwar Auren ku shin baya sanki ne Yake miki irin wannaj duka ko kuwa?".   Hawaye ne yq fara Go slow daya bayan daya a idanunta kafin tayi magana cikin kuka._

*A social net muka hadu da Umar har soyayyar mu ta zama ta zahiri Domin dan anguwar mu ne ban sani ba sai daga baya. muna san juna sosai. Nida umar matsalan da aka samu shine Iyayena masu kudi ne Shi kuwa umar Okada yake da shi yake ciyar da iyayesa ma. Bayan nayi candy sai baba na yace aure zaiyi min kuma auren gida. Wato da dan yayan shi zai hada ni. Ni kuwa na nuna rashin amincewa ta nace umar nake so. Yayan baban nawa dake shi ya kawo shawarar a hadani da dan nasa da yaji nace umar nake so sai ya hakura ya janye. Yace ba laifina bane tunda ba'a tambaye ni wanda nake so ba. Mahaifina kuwa gaba daya ya kasa fahimta. Daga karshe ma cewa yayi zaiyi min Aure da Umar din kuma zai min duk abunda uba kewa 'yarsa amma idan wata matsala ta biyo baya kar in ko nufi hanyar gidansa. Haka na amince domin ji nake bazan iya rayuwa da kowa wanne namiji in ba Umar ba. Haka aka daura auren mahaifina duk a fusace yake dani ko hudubar kirki baiyi min ba. Wannan gidan umar ya kama mana haya muna zaune lafiya lau ba wata matsala kullum sai farantawa juna rai. na tsawan wata biyu, A cikin wata na uku umar ya bullo da wani sabon tsari wanda gaba daya ban sanshi da shi ba. Yau wata na biyu kenan Kusan kullum sai umar ya dake ni. Ba fira mai dadi irin ta ma'aurata. Na kai kararsa gurin iyayensa Suka kira shi a gabana suka mishi tatas, Suka mai fada sosai a nan yace bazai kara ba. Ranar da muka dawo gida Kashe ni ne kawai umar baiyi ba.  Gida kuwa sau daya naje da suna yaji Babana ya koro ni yace ma karya kara ganin kafata a gidansa duk abunda ya faru dani ba ruwansa wai ni naja wa kai na. Ranar da Umar yake jin mugunta yasan bani da kudi kuma yasan babu mai bani haka zai dauki Kudi kalilan kamar yanda yayi yau. Yace in mishi wani abincin mai tsada wanda yasan kudin da ya bani bazasu yi ba. Idan ya dawo ya iske banyi ba haka zai same ni yata maka kamar jaka.  Nayi kuka na zubda hawaye a kullum kuma addu'a nake Allah ya kawo min mafita Ni kam ba kudi nake so ba. Farin ciki da soyayyar da Umar ke min a da su nake bukata su dawo.*

_Safuratu tayi ajiyar zuciya tukun ta dafa Rafy tace, "Allah sarki haka rayuwar take, wani sai kayi masa tuwan shinkafa idan ya tashi sai kaga ya biya ka da bak'in kanzo. Ina so in miki Albishir da cewa Allah ya amsa addu'ar ki. In sha Allah zan mayar miki da mijin ki kamar da zan sai ta shi. Amma fa sai kin bani hadin kai".   Rafy ta kalle ta cikin kuka, "Me zaki mishi, dan Allah karki taba lafiyarsa Wallahi ina sanshi duk abunda yake min ban taba fatan rabuwa da shi ba. Ni kam fata na a gare shi Allah ya shirya min shi".  Dan murmushi Safuratu tayi, "Karki damu ba abunda zai same shi nayi miki alkawari, Misali yanzu idan umar zaiyi tafiya na kwana biyu haka, Zai iya kai ki gidan ku yq musu bayani kuma su amince?".   Rafy girgiza kai tayi alamun aa. "Sai dai gidan Yayan babana". Aljanar tace "Ok dauko hijab dinki mu tafi can".  Tana fadar haka ta tashi ta fito waje. Ita kuwa Rafy ta yi sauri ta dauko hijab da fitowar ta maimakon ta tarar da Safuratu sai Umar ta iske tsaye cikin manyan kaya ya wani bata rai!.  Durkusawa tayi tana karkarwa dan tsabar tsoransa da take ji. "Me gida sannu da zuwa, yaushe ka dawo".  Cikin fada yace ban sani ba ina abincin da nace kiyi".  In-ina ta farayi "Um um, dama-dama.."  Harara ya wurga mata. "Dama me?, Shin yanzu da kika sako hijab ina zakije?".  Kuka ta fara tana fadin Wallahi ba "Inda zani".   Dariya Umar din ya fara yi ita kuwa ta saki baki tana kallansa cikr da mamaki domin rabun ta da ganin umar na dariya Tun baya da wata biyu.  "Matsoraciya ashe haka kike mugun tsoran Umar din. To ba Umar bane wannan *ALJANAR FATIMA* ce, Nice nayi sufarsa nayi kyau kuwa?"._

_"Eh kwarai mai gida kayi kyau".  Ta fada da sauri Aljanar ta fahimci har yanzu Rafy bata yarda ba shiyasa ma tayi mata Muryanta, Sai a lokacin Rafy ta yarda ta mike tsaye. "Yanzu zuwa zamuyi in kai ki gidan yayan babanki ince masa zan danyi tafiya ne na kwana biyu, Kuma ba dadi a barki a gida ke daya shiyasa ma na kaiki ce, Ni kuma sai in koma sufarki in dawo nan in saita Umar tukun. Kina ganin yayan babankun zai yarda kuwa?".   "Eh zai yarda". Inji Rafy "Ok to muje".  Fitowa sukayi suka nufi gidan yayan baban nata Safuratu tayi kamar yanda ta tsara suka ci sa'a kuwa ya amince ya karbi Rafi'at.  Safuratu kuwa ta fito ta koma gidan a matsayin Rafy din...._
*________________*

_Su Asmart suna ganin an kusa zuwa makaranta sai suka kunce wa Fatima 'yar babyn daga bayanta suka bata a hannu. Nasmat tace "Yauwa 'yar kanwata kinga daga yau 'yar ki zata iya karatu. Yanzu muna shiga cikin makaranta ki Je ki kaiwa malam ita kice karatu za'a koya mata kinji".  Murmushi Fatima tayi wanda ya fito da gibinta ya kara bayyana kyawanta. "To aunty Nasmat amma Dai A kusa dani zata ringa zama ko?".   Asmart tace "Eh mana ai a ma kan cinyar ki zata ringa yin karatun".  Su nasmat Tare suka shiga makarantar. Suna shiga suka jiyo sautin karatun malam din a Aji na 4. Ajin su kenan Asmart tace, "Yauwa Fatima kinji Malam can a jinmu dan tsaya anan ki bari muna shiga muka zauna sai ki kai mai kinji?.  "To". Fatima tace nan ta sama waje ta dan zauna. Tana wasa da yarta. Su Asmart gaba suka yi suna dariya harda rike ciki. Nasamt cikin dariya tace "Har naga ana yin sama da malam ana bugawa da kasa, domin nasan sai ya daki Fatima ko yayi wa 'yar babyn wani abu".   Asmart tace "wannan ai a zaune take ke dai muyi sauri muje yanzu zaki sha kallo. Bayan sun shiga sun zauna ba'a dade ba sai ga Fatima ta shigo ajin da sallama tana murmushi, hannunta rike da 'yar babyn. Malam ya jawo wata aya yaje rabi kenan ya tsaya cik!  Yana kallan Fatimar.  Haka gaba dayan 'yan aji zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab yau ta banu tunda ta shigo wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta nufi ind.……………………………………………………_

😰 *MUGAYE SUN HADA MATA BOMB. ALLAH YASA MA YA TASHI HAR DA SU.••••*

*DOMIN SAMUN FARKON LABARIN DAMA WASU LITTAFAN. SHIGA CIKI BLUE DIN NAN, KA/KI YI LIKE NA PAGE MU, TUKUN KA/KI DUBA KASA.*

*Fb.me//Zamaniwritesassociation*

Ko nan
*Fb.me//Bigboyisahfans*

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 55-56

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😎 *WANGA PAGE SADAUKARWA NE GARE KI AUNTY NA. 'YAR MUTAN KATSINAWA.* 😎

🌹 *FATIMA MAMAN ALI* 🌹

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Haka gaba dayan 'yan aji zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab yau ta banu tunda ta shigo wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta nufi ind.~

_»»Malamin Fatima ta nufa tana murmushi, sai da taje gabansa tukun ta tsayar da 'yar babyn da kafafun ta ta kalli malam da ya murtuke ya bata Rai yake kallanta. "Ina kwana malam, dama 'yar babyn na kawo a ringa koya mata karatu ta iya Surutu karatu ne kawai bata iya ba. Kuma so nake ta ringa yi".  Kafa yasa yayi Ball da 'yar tsanar da karfi ta bigi jikin bango ta fada kasa tum!. A fusace ya juya ya kalli 'yan aji  "Ina nasmat da Asmart?".   Gamu nan suka fada a tsure. "Oya ku fito nan".   Sumi-sumi suka tashi suka je gaban sa suka durkushe.  "Kune manya ku zan wa hukunci domin ita yarinya ce bata san komai ba. Me yasa kuka bar Fatima ta taho makaranta da wannan Tsinannan abun?".  Cikin hadin baki suka ce "Wallahi Malam ba tare muka zo ba".  Karya kuke tare da ita kuka zo mana". Rantse-Rantse suka hau yi wai su alambaran ba tare suka zo da Fatima ba. Da malam yaga suna so su Bata mishi lokaci sai ya juya ya kalli Fatima. "Ke Fatima fada min gaskiya in kuwa kika min karya sai na yanka ki. Tare kuka zo ko A'a?".   Su Nasmat ta kalla ko wacce a cikin su Uwar harara yake Tillo mata hade da gatsina duk dan karta fada.  "Eh Malam wallahi tare muka zo".  A fusace ya juya gare su.  "Da Ni zakuyi wa karya ko Dan uban ku?. To ku jira hukunci kar wacce ta motsa daga nan". Hakuri suka shiga bashi shi kuwa bai ko tsaya sauraren su ba. Ya fita waje bai jima ba ya dawo hannunsa da wuka.  'Yar babyn ya dauka a yaje saitin gaban allo, "Kai ina so duk ku saurare ni, daga yau duk wanda ya sake yin ganganci ya shigo cikin makarantar nan da 'yar tsana, Kai bama a makaranta ba Ko a hanya na hadu da mutum da ita wallahi sai jikinsa ya gaya masa._

_Ya kalli su Nasmat  tukun yaci gaba da cewa, "Sau nawa ina yi muku bayani ina fada muku Mala'iku na rahama basa zama a wajen da wannan gunkin yake, mu kuwa so muke mu kasance da su a ko da yaushe. Dan haka in kunje gida ku gaya wa babban ku na kwace 'yar babyn Fatima".  Yana gama fadar haka ya sa wuka ya yayanka 'yar tsanar har gida shida. Tukun ya kwashe ta ya fitavda ita ya watsa saman soro. Dadi da farin ciki ne suka ziyarci su Nasmat. "Shikenan malam ya jawo wa kansa yau zai gane kurensa". A cewar Asmart, Nasmat tace "Ke ni fa tsoro nake ya zo ya dake mu wallahi".  Ya daka din mana ai ba komai ni kam bazan ji zafi ba ko ya bige ni domin kuwa nasan shima yau zai bugu kum...".  Bata karashe maganar ba Sai ga malam ya shigo hakan yasa ta garkame bakinta tashi shiru. Yana zuwa kuwa ya dauki bulalar sa sai da yayi musu goma-goma da karfi tukun yace su koma mazaunin su Fatima ma yace ta koma Ajin su. A cikin su Nasmat ba wacce tayi kuka Dan farin ciki ma suke yi wai yau malam ya tabo Alkakai._
*_______________*

_Umar kuwa yana fitowa daga gidan ya nufi gidan iyayensa ya gaida su dauki mashin dinsa ya fito bai zame a ko'ina ba sai wajen abokinsa mujaheed bayan ya parka mashin Ya sauka fuskarsa dauke da murmushi yaje ya mika mashi hannu suka gaisa shima yana kallansa yana 'yar dariya. "Abokina ashe kana gari shiru kamar kayi tafiya baka ko lekowa mi gaisa kai da kake da mashin".   Umar sai da ya sama waje ya zauna tukun yace, "Haba mujaheed ya za'ayi in ki zuwa gurin ka da gangan, Wallahi kawai ayyukan ne sai a  slow".  "Gaskiya ne abokina to me ke Going?. Tun da naga fuskarka dauke da murmushi nasan a kwai labari".  Hhhhhhhhh Umar yayi Dariya, "Gaye shiyasa nake san zama dakai Wallahi, domin kai din akwai kwalwa. Gashi dai har ka gano ni".    "Eh mana bani nasha".  "Kasan dai zance gizo baya wuce na koki, Maganar shawarwarin da kake bani ne kai gaskiya abun nayi min dadi, Yanzu gidana sai abunda nace ayi shi za'ayi Rafy gaba daya tsorona take ji. Yanzu fa idan na ajiye kara baban ta ma ya ajiye mu kowa yace karta tsallaka to Wallahi a yanda take jin tsorona idan nace ta tsallaka na baban ta sai ta tsallaka wallahi"._

_Dariya sosai Umar yayi yace "Gaskiya ne abokina ai nake gaya maka mace kullum kana bude mata hakora kuna wasa da ita wallahi gaba daya raina ka zatayi ta ringa ma abubuwan da taga dama, amma idan ya kasance tana jin tsoran ka, Haba Malam a nan zaka ji dadin rayuwa. kai ni fa yanzu haka maganar nan da muke yi gidan nan haka na fito ban bata ko kwandala ba kuma nace Dambun nama nake so da gasasar kaza. Dan tsabar tsoran da take min har russuna wa take tana godiya tana cewa an gama mai gida. Yanzu nasan ko bata da kudi sai ta ara ko kuma ta sayar da wani abun nata taje ta sayo min kafin in dawo".  Duk maganar da yake Umar sakin baki yayi kawai yana kallansa. Dajin yazo karshen zancen umar yace "Kanbuhu! Ashe ni wannan yarinyar rainani tayi. Ni fa nake gaya maka Yanzu Naira Hamsin ne na bata nace ina san shinkafa da miya amma shine ta tsaya tana min surutai wai kudin ko cefane bazai isa ba balle Ma a auno shinkafa ashe kawai dukan da nake mata ne har yanzu bai sa tayi hankali ba".  Muhajeed ya kama baki "Kai! Kai! Lalai kuwa bata horu ba. A hakan ma nake gaya maka dan fa baka sakar mata hakoran dariya ne amma da farat! Daya ma cewa zatayi bazata yi ba".  Daga jin haka Umar ya mike jikinsa har rawa yake, Muhajeed yace "Abokina naga ka mike ina zaka?"._

_"Hmm, abokina kenan ai mikewar nan da kaga nayi ba inda zani gida kawai zan koma. Domin a yanda ka bani labarin matarka take ma in dai ba haka Rafy ta ringa min ba zuciyata baza tayi sanyi ba. Kuma wallahi in taki min biyayya yau sai na sumar da ita dan ubanta".  Yana fadar haka ya mikawa Muhajeed hannu sukayi masabaha ya hau mashin dinsa yayi dogon ja. Mujahedeen na ganin Umar din yayi nisa sai ya kalle shi ya kashe da dariya yace "Banza kawai gara ka hadu da mace mai hakuri sai azbatar da ita kake. Uban waye zai wa matarsa duk abubuwan da nake fada maka in ba irin ku dolaye ba. Shege ni dama KA SAKE TA NA AURA".  Umar har ya kusa gida ya sama passenger nan ya tsaya ya dauke sa. Shine ya juya akalarsa i zuwa cikin gari...._
*__________________*
_Mama Asiya, Zuwaira, Da Hauwa  babu abunda suke yi in ba uwar hamma ba ta yunwa."mun shiga uku wannan wanne irin bala'i ne to wai me ke faruwa a gidan nan ne.  Dazun a gurin kari Munzo mun iske babu Dan wake biredi a rube haka store ba komai. Gashi mun aika Mai gadi sayan indomie babu yanzu mun aike shi sayan abinci Ya dawo nan ma babu. Gashi har Azahar tayi gaskiya ni bazan iya jurewa zama da yunwa ba. Wallahi gidan mu zani ina dalili Azumin dole".   Kamar hadin baki suma sauran suka mike "Ai muma bamuga ta zama ba wallahi". Kowa dakinta ta nufa ta daukko hijab kusan tare suka fito. Zuwaira ce a gaba ta nufi kofar fita a falo da niyar bude wa. Tana bude wa ta zura kafa da niyar fita sai ji tayi an hankado ta baya, Haka tayi baya ta fadi Tabar!, Dariya mama Asiya ta kyalkyala, "Saurin me kika haka harda faduwa?". Dan mugunta Zuwaira taki fadawa Mama Asiya turo ta akayi. Ai kuwa Asiya na zura kafarta da niyar fita. Da karfi aka hankado ta baya kamar buhun Hatsi haka tazo kasa Tum!. Badan Zuwaira ta goce ba da a kanta zata fado.  Zuwaira da Hauwa me zasuyi in banda dariya, Dariya harda rike ciki Suna cikin Dariya suka ji kofar ta koma ta rufe da kanta da karfi. Hauwa taje tayi-tayi ta bude amma ina..._
*_______________*

_A cikin islamiyya karatu ake amma su Nasmat hankalin su kan malam duk motsin da zaiyi idansu na kanshi. Ko waje ya fita sai sun bishi wai su kawai sai sunga yanda zata kare shi da Aljana. Bayan sun dawo aji an shigo littafan Fiqhu  Malam ya kalle Nasmat "Ke Zanyi miki tambaya a cikin littafin.Ahdhari (Ahalari)  Minene farkon abunda yake waje ba ga Baligi?".  Tsuru Nasmat tayi tana zara idanu ta kalli Asmart cikin Rada "me zance?".   "Oho alquran nima ban sani ba". Malam ne ya daka mata tsawa "ke tambayar ki fa nake yi"  A zabure tace "Malam abunda ya kamata baligin ya sani shine Mahaifiyar sa da uwayen sa da kannansa da abokansa da makwabtansa".  Ta juya ta kalli Asmart "Dan Allah ko ba haka bane". "Haka ne mana" Nasmat ta bata amsa a takai'ce. Gaba dayan ajin suka bushe da dariya.  Malamin kansa yaso yayi dariya kuma sai ya bata rai tsabar takai'ci bai kuma ce mata komai ba yace. "Maryam minene farkon abunda ya wajaba baligi?". Mikewa tayi cikin zazakar muryar ta ta fara bayani._

*"Farkon abunda ya wajeba ga baligi  ya Inganta imanin sa sannan yasan abunda zai Kyauta farillan Ainihinsa kamar hukunce-hukuncen  sallah Dana tsarki da azumi. Yana wajaba a gare shi ya kiyaye hakokin ubangiji, Ya tsaga ga umarnin Allah da hanninsa, Ya tuba ga Allah (SWT), Tun kafin yayi masa azaba".*
  _"Attakah biirrr".  Malam ya fada gaba daya ajin aka kaurade da fadar "Allahu akbar!". Wajen Nasmat ya zo ya mata bulala biyu, Hade da yi mata fada._
*______________*

_Tunda umar ya shiga gari bai dawo ba sai Wajen magariba.  Yana fara'a amma da shigar sa gidan ya wani daure Fuska. "Rafy! Rafy!"  Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito Tsaye kerere tayi masa. "Gani".  "Ina abincin da na saki kiyi min?".   "Banyi ba" ta bashi amsa a hatsale  Hannu ya daga da karfi Da niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike hannu........................._

πŸ€£πŸ˜‚  *Tabb! Ramin mugunta su Nasmat a gina sa gajere*

πŸ™†πŸ»‍♂ *Umar kuwai baisan Aljana bace, Pls aci gaba inji ya zasu kare* 😁

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 57-58

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

*DEDICATED TO MY JIGO ZAMANI WRITERS ASSOCIATION * IN san duk masoyan wagga kungiya

✈❤ *JIRGIN ZAMANI* ❤✈
*Mun hau mun shillah Ahhha ha* 😁 *JIRGIN SO ZAYA TASHI KU KADAI MUKE JIRA 'YAN GATA DUNIYAR SO KUNE DA SARAUTA.*
☺ 🎢🎡🎢 _Ku na gano da ku nake san rayuwa._

🎢🎡🎢 _Naga kuna da tausayi kunyi a rayuwa._

🎢🎡🎢 _Zanen dutse hali kuce bashi goguwa._
___

🎢🎡🎢 _Tarbiya ko a harshe ashe akan gane mai itta littafan ku da kansu sun nuna._ 😘

🎢🎡🎢 _Nayi dare ku ban masauki gidan ku in kwana._  πŸ˜› _Kuzo ku shigo har abinci zamu muku kwadan rama_ πŸ™Š ZAMANI WRITERS ASSOCIATION 😘❤ *WE LOVE U ALL ZAMANI WRITERS FANS*

'YAN PHAREEDAH KHAMSHI NOVELS KUYI HAKURI WALLAHI PAGES DIN NE YAKE TSAYI IDAN NAYI COMMENTED SAI SU NUNA YAYI NAUYI. TO KAFIN RABASHI BIYUN SAI WANI UZURIN YA FIZGE NI. PLS

       *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito Tsaye kerere tayi masa. "Gani".  "Ina abincin da na saki kiyi min?".   "Banyi ba" ta bashi amsa a hatsale  Hannu ya daga da karfi Da niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike hannu.~

_»»Gam ta rike hannun, Umar yaja-yaja  ya kasa kwace hannunsa hakan yasa ya kara kai dayan hannun ds karfi da niyar ya dake ta shima rike shi tayi. Yayi juyin duniyar nan ya ware iya karfin sa domin ya kwaci hannun sa amma ya gaza hakan yasa ya bar kokarin kwatar hannun ya wani bata Rai!, "Sakar min hannun"  yana fadar haka ta sake shi, Tsayawa yayi a gurin yana kare mata kallo har haske ta yayi da Torch ya tabbatar kums matar shi ce. A zuciya yake fadar "Anya kuwa wannan Rafy ce?. Dama Rafy na da wannan karfin take bari ina jifgarta?". Juyawa yayi ya kara kallan ta. "Bakiyi ba kika ce saboda me  to kika ki yi?".  A fada ce yake maganar "Saboda baka bar min kudi isasu ba mana". "Au! Kuma dan na baki kudin da basu isa ba shine ke baza ki cika ba kiyi yanda matan Kirki suke yi ko?".  Da sauri ta bashi amsa "Sana'ar me nake yi?, ko kuma kana bani kudinka ne?. Kare mata kallo yake sama da kasa Mamaki ne yake karuwa a gare shi. Shi badan ma ya haskata kuma yaji muryar matar shi ce ba da sai yace ba ita bace, Domin yanda yasan Matarshi a kwana nan mugun tsoranshi take yi. Yanzu tsoran dokan ta yake tunda yaji Wani sabon karfi a gunta. Juyawa yayi ya nufi kofa da niyar fita. Ai kuwa ta baya ta kama rigar shi ta jawo shi kamar wani karamin yaro "Ina zaka je baka bani abinci ba?".  "Sakar min riga malama masallaci zani". Murmushi tayi tukun tace, "To mai gida a dawo lafiya. Amma maganar abincin dare fa?". Bata rai yayi "zan sayo na kawo". Yana kokarin tafiya tace "To naji amma fa wallahi in ka dade sai na saka hijab na bika na lalubo duk inda kake".  Bai ko saurare ta ba ya kada kai yayi gaba  Sai sake-sake yake a ranshi._
________________
_Fatima tunda taga an yanka mata 'Yar baby an jefa sama take kuka. Gaba daya yau batayi karatu ba kuka kawai take malamin ajin ya dake ta amma take yin shiru Haka lalabo ma ba wanda baiyi ba. Ita kuwa taki. Ba yanda ya iya dole ya korota waje. Waje ta samu ta sauna ba abunda take sai kuka tana kallan saman soron da aka jefa mata 'yar baby. A haka har aka tashi gaba daya makarantar,Fiddausi ce tazo da kyar taja ta suka tafi gida domin da kiyawa tayi wai ita bazata je ba sai an dauko mata babyn ta. Sai da Fiddausi ta dake ta tukun.   Su Nasmat kuwa gaba daya ajin aka watse aka barsu zaune ba abunda suke sai leke wai jira suke malam ya fito su bishi baya suyi ganin kwaf!._

_Nasmat tace "Asmart anya kuwa wannan ya fada tarkon da muka haka mishi?!".  Asmart tayi 'yar dariya tace "Haba ke kuwa me kike ci na baka na zuba, Ki jira mana ni nasan bazata taba kya...".  Bata karashe maganar ba taga malam ya fita daga makarantar da sauri ta dauki jikar ta ta nufi hanyar fita a ajin. "Yauwa taso, taso gashi can zai fita".Baya suka bishi ba tare da ya sani ba daga Sunga zai waigo sai su labe. haka in suka ga ya tsaya wata majalissa sai su sama waje su labe suna lekensa. Haka dai suka ci gaba da tafiya ba tare da ya gansu ba har ya isa gida. Yana zuwa ya shige gida su kuwa a bakin kofa suka tsaya suna kace-nace.  Malam na shiga gidan ya fara jin kauri na tashi. "Masa'auda! Masa'auda!". Ya shiga kwalla wa matarsa kira. Gyaran muryar tayi alamun tana ban daki. Da sauri ya nufi daki domin daga nan kaurin ke tashi. Heater ya iske jone a socket An sata cikin ruwa. tayi  daga gani ta dade a jone domin ta kusan tsotse ruwan tayi daga sama kuwa tayi jawur har  wayar ta fara narke wa.  Cikin hanzari malam ya kai hannun da niyar ya zare ta a jikin socket din, Ai kuwa yana kamawa  abun ya hade masa biyu ashe robar ta fara narke wa ga kuma shocking. Wani mugun ihu ya kwada yayo waje a guje yana yarfa hannu yana fadin "Innalillahi!".  Su Nasmat da suke kofa kamar jira sukeyi suna jin ihun! Suka afka cikin gidan a guje. A tsakar gidan suka ja burki ganin malam tsaye yana yarfa hannu yana kallansu. Lokacin Masa'uda matar malam ta fito daga ban daki da sauri tana tambaya lafiya.  Malam kuwa harara ya watsa wa su Nasmat "Kai uban me ya kawo ku nan?".  Kallan juna suka tukun suka juya suka kallesa kamar hadin baki suka ce. "Taimako muka zo yi, (Emergency)".  "Taimako to uban waya yace muku ana bukatar taimako a nan".  Asmart da sauri tace "Malam munzo wuce wa ne sai mukaji anyi ihu! Shine muka zo dan muga me ke faruwa"._

_"Oh!  To daga ina kuke yanzu ko kuna so kuce min da aka tashi daga makarantar ba gida kuka tafi ba yawan ganta kuka fito?". Malam ya fada rai a bace.  "Wallahi A'a malam ziyara muka je mu".  Malam ya zaro idanu "Ziyara gidan wa a nan layin?.   Ba nan layin bane can ne gaba kadan gidan wata kawar momyna ko a gida ka ansan zamu zo".   Malam yace "To Shikenan naji kuma Wallahi in gaya muku in na tambayi Fiddausi ko Ameera gobe suka ce min ba haka ba, to jikin ku sai ya gaya muku maza ku wuce gida".  Cike da haushi da takai'ci suka juya suka fita a gidan. Tsabar bacin Rai sun dade suna tafiya amma Ko kala ba wanda yace Sai Tsaki kala-kala da yake fitowa a bakunan su. Can asmart ta kalli Nasmat, rai a bace kamar tayi kuka tace "Ashe dai dama Aljanar nan  mu ta raina?, kinaga fa duk abunda malam yayi mata ko tsawa batayi mishi ba".    Nasmat tace "Ke dai bari abun ya kona min rai, Wai ace duk abunda mukayi munyi a banza malam sai ma kara mana duka da yayi. Amma fa kuma inaga Aljanar ta mutu ne?".   Da sauri Asmart ta kalli Nasmat "Haba dai, Dama aljanu suna mutuwa ne?".  "Eh mana baki ji malam adamu yace Idan suka rikida suka koma wani abu  idan ka kashe abun shikenan ka kashe su ba.  Misali idan aljani ya koma maciji in kika kashe macijin shikenan Aljanin zai mutu, To kinga kuma Wannan 'yar tsana ta koma kuma malam ya yayanka 'yar tsanar shikenan  ta mutu kenan"._

_Asmart najin haka tayi wani tsallan farin ciki da jin dadi. "Wayyo da kuwa naji dadi Wallahi, Domin da Fatima ta shiga uku kullum da sai na sakata kuka sau uku. Kuma duk dukan da aka mana a Islamiyya sai na rama a kanta".  Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya ta dora da cewa "Ke dai bari mu isa gidan Ai ni kadai nasan abunda zanyi wa Fatima yanda Aljanar ta gasa ni itama sai ta gasu".  Suna hirar har suka karasa gidan. Yanayin da suka tarar da gidan yasa basu nema Fatima bama kowa ta kansa yake. Domin Duk wanda ya shigo gidan ba damar fita sai gida ya garkame in kaje da niyar budewa Kuwa kasha mari. Haka suka kwana a ranar su mama asiya ba wanda yasa ko kwayar gero a baka._
_____________________

_Umar ne zaune gurin mai shayi ya saka a dafo mishi Indomie da kwai. Sai washe baki yake ana hira. Bayan wani dan lokaci daban aka miko Mai indomie mai zafi a flat wacce aka lulube da wainar kwai sai tururi Take kamshi na tashi. Karba yayi sai Hadiyar mugun yawu yake.  Cokali daya yayi ya kai na biyu ya lumshe ido domin dadin da yake ji na Wainar kwan. Kamar daga sama yaji anyi ciki da Filet din indomie din duk ya warwatse masa a jiki. Da bude idansa da fitowar "Kutumar uba!".Daga bakinsa Duk daya, ba kowa bane Rafy ce tayi kwallo da Farantin indomie din takuma yi tsaye kerere tana hararen sa. "Ke dan iskanci da rainin wayo ni kika biyo har nan kika zubarwa da Abinci?".   "Eh an zubar din mugu macuci kawai". Ta bashi amsa a hatsale   Hannu ya daga ya kai mata mari cikin hanzari ta Duke. tana dagowa kuwa ta wanka mishi mari Tass!!!....................._

Yaseen na gaji

*Turkash!!!*


Post a Comment for "ALJANAR FATIMA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...