ABOKIN MIJI NA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABOKIN MIJI NA COMPLETE

ABOKIN MIJI NA COMPLETE

- - Post a Comment

 ABOKIN MIJI NA COMPLETE


Wai kai sai wani d'oki kake kamar wanda yau aka kai maka matar."

"Abokina bazaka gane bane Wallahi tunda na auri  Husna ban ta6a kusan tantaba kai baka tunanin zan shiga hakk'inta?" Ya k'arasa maganar fuska d'auke da damuwa.

Wani dad'i ne ya lullu6e Yusuf sannan yace

"To ai sai kayi hak'uri tunda kasan tsoro take ji kuma idan kayi bata cire wannan tsoron ba Wallahi ciwo zaka ji mata kaca-kaca."

  Gaban Farooq ne yayi mummunar fad'uwa sannan yace
"To Abokina menene mafita?" Ya tambaye shi.
"To mafita dai d'aya ce kawai ka hak'ura har sai ranan da Husna ta bude baki tace ka kusanceta."

Waro ido yayi yace
"Kai Wallahi Husna bazata iya cewa na kusanceta ba koda kowa zamu shekara ne sai dai kawai na cire tausayinta nayi abinda yake raina dan kuwa Wallahi yana damuna kasan dai abinda Doctor yace mun."

   Wani kallon tsana Yusuf yayiwa Farooq sannan yace
"Kenan kayarda ka kashe 'yar mutane ko?
Dan kuwa nasan kai bazaka sausauta mata ba."

  "No Yusuf yanzu nazo wajen kane dan kabani shawara saboda kai ka dade da mata kuma kaine aminina dan haka nazo gunka please Abokina ka taimaka mun."

  Murmushi mugunta Yusuf yayi sannan yace
"To shawara ta d'aya ce kajira ta nan da sati d'aya idan kaga babu halamun buk'ata a tattare da  sai kawai kayi abinda kayi niya."

  "Hmm to Allah yakaimu nan da satin amman Wallahi nikam a matse nake."

  Haka dai suka tayi a tsakanin su sannan suka yanke akan sai nan da sati.

   Yusuf ne ya rak'oshi har gida a lokacin da suka shigo gidan wani wawan k'amshi ne ya daki hancin su Wanda sai da gaba d'ayan su suka shiga wani hali.

  Zaune take akan d'aya daga cikin kujerun da suka zagaye parlour.

  Swiss lace ne a jikin ta Wanda ya amsheta kamar dan ita akayi.

Farooq ne yayi sallama wanda Yusuf ya kasayin Sa.

   Amsa musu tayi cikin zazzak'ar muryan ta sannan ta tashi tana musu sannu da zuwa.

  Yusuf sake rikicewa yayi da ya kalli halitattar Husna Wanda bai ta6a tsammanin tana da shi ba.

  Farooq ne ya d'an bigeshi yace
"Kai kuwa sai kace Wanda baka Santa ba sai wani kallon ta kake" ya k'arasa maganar cikin zolaya.

  D'auke idon shi yayi a kanta sannan yace
"Wallahi abokina sai naga kamar Yau ta chanza mu....."

  "Sannun Ku da zuwa"
Yusuf yayi saurin amsawa da cewa
"Yauwa sannu amarya ya kike?"

Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau Ya Yusuf, ya Anty Hafsat?" Ta tambaye shi.

"Lafiya ta k'alau gobe insha Allahu zan kawota ku wuni saboda Ku fara sabawa tun yanzu."

  "Kai amman naji dad'i Wallahi ya Yusuf Allah yakaimu."

  Shikuwa Farooq yana zaune yana kallon amaryar Sa wacce duk kallon da zai mata sai yaji wani abu a jikin shi.

  Juyowa tayi tace
"Sannu da zuwa ya Farooq."
"Yauwa sannu uwar gidana uwar 'ya 'ya na ya kike?
Ya kuma kad'aici."
"Alhamdulillah
Ya office?"
"Alhamdulillah My Angle."

Wannan kalamai na Farooq ne ya fara 6atawa Yusuf rai hakan ne yasa shi katseshi da cewa

"Abokina nifa yunwa nake ji muci na gudu nima gida na."

Murmushi Farooq yayi yace
"To ai ga abinci a dining muje mana."

Haka kuwa suka tashi suka nufi dining dan cin abinci amman ina Husna Sam ta kasa sakewa dan wani kallo Yusuf yake mata hakan ne yasata tashi tabar abinci.

  Bayan sun kammala sun koma parlour in zauna Yusuf yace da Farooq
"To Abokina ni zan gudu amman dan Allah kar ka kusanci yarinyar nan Wallahi yanda na fahimceta har yanzu tsoro ne a ranta kagani dai ko abinci ta kasa ci."

  "Eh nima dai hakan nagani amman kasan bazai yu na zuba mata ido ina kallon ta ba, dole sai nayi abinda yake rai na."

   Mugun kallo ya masa sannan yace
"To naji ka k'irata kuzo Ku rakani zan wuce."

Haka kuwa ya tashi yaje ya kirata suka rakashi bakin motar shi sannan suka dawo cikin gida.

   Bai tsaya a ko inaba sai gidan shi,
ba laifi yau tayi wanka tayi kwalliya har da turare ta saka a gidan ta abinda rabonta da shi har ya manta.

Sallama yayi ya shiga kamar yanda yayi tsammanin a parlour ya sameta kwance akan three siter.

  Amsa mishi tayi ya shiga
"Sannu uwar 'yan jin dad'i ai daman nasan kina nan kwance."

  Turo mishi baki tayi tace
"Sai yanzu kadawo kasan inajin yunwa."

Kallon ta yayi yace
"Wai ni bawan kine da zan dinga dafa miki kina ci to Wallahi Yau bazan dafa ba sai dai ki kwana da yunwa."

   Mik'ewa tayi da k'yar ta zauna tace
"Haba ya Yusuf kaima kasan bazan iya fad'awa ba kuma ko na daga bazan iya ci ba ko naci ma amarwa nake."

  "To Allah yasa kar ki iya ki zauna nikam bazan dafa ba" ya k'arasa maganar yana hayewa sama d'akin shi.

  Ita kuwa cewa tayi
"Oho dai idan baka dafa ba zan iya badawa a siyomun."

  Haka kuwa tabawa Isyaku mai wanki da guga kud'i ya siyo mata tsire  kasan cewar tanada yogurt a friez.

   B'angaren Farooq kuwa hankalin shi gaba d'aya baya jikin shi yanda yau yaga Husna........

*​Taku har kullum Momyn musaddiq​*πŸ“š✍🏻

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ™†πŸ»πŸ˜­ *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

*DEDICATED TO SADNAF*

  ​​​```Wannan page d'in naki ne ke kad'ai My Sadnaf kiyi yanda kike so dashi nabaki shi kyauta​​​```

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 6~10​*

Yanda yaga Husna tana mishi wasu irin salo Wanda bai ta6a tsammanin ta iya irin su ba haka kuwa shima ya biye mata suka ci gaba da jin dad'in su.

  Ringing d'in wayan shine ya dawo da su daga duniyar da suka tafi.

   Ganin Number Yusuf ne yasashi d'auka da sauri ya kara a kunnen Sa.

  "Hello Abokina bakayi barci ba" Yusuf ne ya tambaye Farooq.

  "Eh Wallahi banyi ba amman dai lafiya ka k'irani cikin wannan daren?"

  "Lafiya k'alau kawai dai na kiraka muyi hira idan amarya tayi barci."

  "Hira kuma nida inada mata kaima kanada me zaisa muyi hira bayan ga matan mu."

  "To sarkin iyayi ai cewa nayi idan sunyi barci ko kai naka har yanzu batayi ba?"

"Eh batayi ba sai nan gaba."

  "Kai dai kawai bakason muyi amman me zaisa Husna zama har yanzu batayi barci ba."

  "To shikenan tunda baka yarda ba to gatanan kaji muryan ta" ya k'arasa maganar yana mik'a mata wayar.

   Wani dad'i ne ya lullu6e Yusuf daman abinda yake nema kenan gashi kuma ya samu.

  Kar6an wayar tayi ta saka a kunnen ta badan ta so ba.

   "Hello Yaya Yusuf baka yarda cewa banyi barci ba?" Ta tambaye shi.

   Murmushi jin dad'i yayi yace
"Ina kuwa zan yarda bakiyi barci ba dan nasan wannan lokacin ba abinda zakiyi."

   "To shikenan sai da safe." Ta kashe wayan.

   Ba dan yasoba saboda yanzu a rayuwar shi ba abinda yake so kamar yaji muryan Husna.

   Shi kuwa Farooq tsaki yaja yace
"Wallahi Yusuf ya cika matsala war yanzu zai kira mutum a waya kawai ya katsemun jin dad'i na" ya k'arasa maganar yana rungumo Husna.

   "Husna dan Allah inason na miki tambaya ina fatan zaki bani amsa."

   Gyara kanta tayi wanda yake k'irjin Farooq sannan tace
"Ina jinka ya Farooq."

  "Husna meyesa kike tsoro na? Kike tsoron bani hakk'ina?"

   Juyowa tayi ta kalli fuskan shi sannan tace
"Wanne irin tsoro Yaya?"

  "Husna nasan tunda aka kawoki gidan nan kike tsoron had'a shinfid'a da ni shiyasa nima na barki har sai wannan tsoron ya fita amman kuma naga har yanzu banga kina buk'ata naba."

   Rufe fuskan ta tayi Alamun jin kunya sannan tace

"Aa Yaya kar kasa mala'ikun Allah su tsine mun."

  "Amman har yanzu baki bani amsa na ba."

  "Yaya Wallahi ba wani tsoron ka da nakeji ba,  sai dai kasan duk wata mace dole sai tayi far gaban first night d'in ta."

  Murmushi yayi sannan yace
"To yanzu kin yarda da nayi abinda naga dama?"

  Wani irin kunya ne ya lullu6e ta wanda ya sata  tusa kanta tsakanin pilo.

   To yanzu tashi muje muyi alwala mu gabatar da sallah raka'a biyu.

  Bata amsa mishi ba sai ma kara danna kanta take ganin zata 6ata mishi lokaci ne ya d'auke ta zuwa bathroom.

   Alwala sukayi sukazo suka gabatar da sallah sannan ya musu addu'a sosai tukun suka nufi gado.

Sai  Yau Farooq yasan cewa yayi Aure sun faran tawa junan su sosai sai misalin k'arfe d'aya na dare Farooq ya barta.

Farooq ji yake kamar zai mayar da Husna ciki tsabar yanda yake jin k'aunarta yana k'ara shiga cikin zuciyar shi.

  Yau Husna ta shayar da shi madarar soyayyar ta.

   Ita kuwa Husna taji maza Wanda haka yasata narkewa sai faman kuke-kuke take na shagwa6a.

   Toilet ya shiga ya had'a mata ruwa mai d'umi sannan ya dawo yace mata
"Heartbeat tashi na d'aukeki muje na miki wanka."

  Turo bikin ta tayi gaba tace
"Aa Yaya nima zan iya kabar shi kawai nayi."

  "Aa Heartbeat nasan kin wahala bazaki iyayi ba kibari kawai na miki."

  Kuka tasa mishi tace
"Yaya nace zan iya Wallahi zan iya kayi hak'uri nayi"......

  " Aa Baby kar kiyi kuka dan Allah tashi ki shiga ina jiranki."

  Tashi tayi ta shiga
Tana shiga shi kuwa ya cire beshit d'in ya chanza wani sannan ya cire mata wasu sleeping dress masu d'an nauyi.

  Fitowa tayi d'aure da towel da sauri ya k'araso inda take yana mata sannu yace mata
"Sannu Babyna zo muje na saka miki sleeping dress."

   Sake narkewa tayi tace mishi
"Ya Farooq jikina yana mun ciwo."

   "Ayya sorry Heartbeat ko zan kaiki hospital ne?"

  "Aa basai munje hospital ba."

  "To ko nasake had'a miki ruwan zafin ne?
Shiyasa nace ni zan miki amman kika k'i."
 
  Bata mishi magana ba ta wuce.

   A hankalin ta k'arasa bakin gadon  ta zauna.

D'auko kayan yayi yasa mata ya kwantar da ita sai da ya tabbatar tayi barci sannan shima ya shiga toilet.

  B'angaren Yusuf kuwa dad'i yake ji sosai dan kuwa ya tsorata Farooq ko ba komai burin shi zai cika.

   Tashi yayi yaje d'akin Hafsat a zaune ya sameta tana chart hakan ne yabashi daman k'arasawa.

  "Bakiyi barci bane?"
" Eh amman yanzu zan kwanta."
"Daman in son na fad'a miki gobe insha Allah zamu tafi gidan Farooq zamuje mu wuni."

  "Gaskiya kuma fa ya kamata mu tafi gidan shi."

  "To sai ki shirya gobe 8:30 zamu tafi."
  "To Allah yakaimu goben."

  Washe gari Farroq shida kanshi ya shiga kitchen dan had'a musu breakfast.

   Dankali ya soya musu da eggs sai kuma tea.

Bayan ya gama da yadawo d'akin se ya same zaune tasha kwalliya sai k'amshi take sha ga kuma kayan da ta saka sun bayyana suranta.

  K'arasowa wajan ta yayi yana murmushi yace
"Heartbeat har kin warke kinsha irin wannan kwallayar gaskiya ya miki kyau."

  Wani irin fari da ido tayi wanda yake k'ara mata kyau sannan tace
"Na warke mana ya Farooq ko bakason na warke ne?" Ta tambaye shi.

  "Aa na isa ai ni nafiki damuwa,
Yanzu ba wannan BA tashi muje dining muyi breakfast."

   Tashi sukayi suka nufi dining amman suna zama sukaji...........

```​​​Masoya littafin BARRISTER JANNART ina mai baku hakuri da jina shiru nayi niyan yimuku shi Yau amman kuma zazzabi ya hanani plz ina mai neman addu'ar ku​​​```

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

​```DEDICATED TO MOMYN SULTAN```

```​​​Wannan page d'in nakine ke ked'ai Momyn sultan kiyi yanda kike so da shi na bakishi kyauta​​​`

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 11~15​*

Sallaman su Yusuf sukaji daga k'ofar parlour dan su ko bude k'ofa basuyi ba.

  Farooq ne yaje ya bud'e musu,  ganin abokin shi da matar shine yasashi yin murmushi sannan yace
"Aa Abokina kaine da sassafan nan?"

  "Eh nine ko bakason zuwan mu ne?"

"Aa bai kai ga haka Ku shigo sannun ku da zuwa." Ya k'arasa maganar yana nuna musu hanya.

   Hafsat ce ta kalli Farooq sannan tace
"Abokinka  kad'ai Ka sani ko?"
"Aa k'anwata kiyi hak'uri ai dole na gaida ki."

   Gaba d'ayan su a parlour suka zaune itadai Husna badan ranta yaso ba saboda kwana biyun nan ta kasa gane me Yusuf yake nufi.

   Farooq da Hafsat ne suka gaisa cikin mutun ci da girmama juna saboda it a Hafsat ta d'auki Farooq tamkar yayan ta.

  Shikuwa Yusuf sai faman zuba ido yake nason yaga Husna amman ina bai ganta ba hakan ne yasa yace da Farooq
"Wai kai ina Amaryan ne ko har yanzu bata tashi a barci ba?"

   "Aa ta tashi tana dining ko breakfast bamuyi ba."

  Ita kuwa Husna yanayin kayan jikin ta ne yahanata tashi hakan yasa ta koma gefe ta zauna.

  Yusuf ne yace
"Yauwa nima haka yunwa nake ji kutashi muje mu karya."

  Haka kuwa suka tashi suka nufi dining.

  Tsayawa yayi cak ko motsawa ya kasa sai faman lashe le6e yake kamar sabon maye ya zuba mata ido musamman yanda yaga na shanun ta sun kunburo a cikin k'aramin riganda ta saka.

  Farooq ne yace
"Ya katsaya ne bazaka zauna ba."

  Sai a lokacin ya d'an motsa sannan yace
"Zan zauna Amarya me ta girka mana?"

  "kai yau ba nata girkin bane nawa ne."
"Kana nufin kaine kayi girki?"
"Eh nine wani abune?"
"Aa ba komai kawai dai naga ga Amarya ne."
"Kai kabari kawai yau Heartbeat d'ina batajin dad'i."

  Wani wawan juyowa yayi ya kalli Farooq sannan tace
"Me yake damunta."
"Zan fad'a maka amman ba yanzu ba muci abincin mu kawai."

  Ita dai Husna batada bakin magana saboda duk wani iri take jinta.

   "Ya Farooq"  ta furta a hankali.

  Matsowa yayi kusa da ita yace
"Na'am my Angle."
"Dan Allah kabani hijabi na a d'aki."

Sai a lokacin shima ya gane abinda yasa taki sakin jiki bare tayi magana.

  Da sauri ya mik'e ya shiga d'aki ya d'auko mata k'aton hijabi har kasa ya bata ta saka.

Sai a.lokacin tace
"Sannun ku da zuwa Anty Hafsat."
"Yauwa sannu Amarya ya kike?
Ya Amarci?"

  Cikin jin kunya tace
"Lafiya k'alau
Alhamdulillah."
"To ni kuma baza'a gaidani ba?"Yusuf ne yayi magana.

Murmushi tayi tace
"Aa wallahi Ya Yusuf zan  gaida Ka
Ina kwana."
"Sai da na rok'a za'a gaidani banaso."

  Farooq ne yace "to yanzu dai muci abinci ba wai surutu ba."

  Haka kuwa sukaci abincin su duk da Husna ba dad'in cin abincin take ba saboda Yusuf ya zuba mata ido duk motsin da zatayi.

  Bayan sun kammala parlour suka koma suka zauna shi kuwa Farooq zan Husna yayi tace suje ya chanza mata kaya.

  Kusan 30 minutes sukayi wajen chanza kaya wanda duk ya dami Yusuf ji yake kamar ya bisu yaga me sukeyi.

  Sanye take da wata atamfa me d'an green a jiki Wanda ya mata kyau sosai duk da ba wani kwalliya tayi ba,
Rike suke da hannun junan su kana ganin su sai sun baka sha'awa.

  Farooq kenan da matar shi Husna.

Wani bak'in kishi ne ya bige Yusuf wanda yasa zuciyar shi bugawa da k'arfi amman sai ya danne yace
"Wai kai Farooq bakajin kunya ne dan Allah?
Kana gani a gaban mu zaka rik'e mata hannu kuna tafiya."

  Cikin mamaki Farooq yace
"Haba Abokina wannan fa Matata ce ko kamanta lokacin da Ka auri Hafsat a gabana kake d'aukanta dan ni na rik'e hannun ta shine rashin kunya."

   "To naji kayi hak'uri kazo Ka zauna muyi hira."

  "To tashi muje parlour na yau akwai labari."

Wani kallo ya mishi sannan yace
"Dan meye sa bakason mu zauna anan tare da matan mu?"
"Kai dalla cewa nayi zan baka labari kuma banson suji."

  "To shikenan muje."

Haka kuwa suka tashi suka wuce parlour Farooq.

"To inajin Ka menene labarin?"
"Abokina jiya na kusanci Husna nasan wacece ita kuma nima na samu lafiya Alhamdulillah."

  Tunda Farooq ya fara magana YusufYa shiga cikin wani hali wanda shi kanshi baisan dalili ba.

  Sai kuma yace
"Haba Farooq dan meyesa Ka kusanci yarinyar nan a yanzu?"

Cikin mamaki Farooq yace "kamar yah ban gane ba?"

  "Ina nufin ai dakabari sai zuwa wani lokaci."

```​​​please kuyi hak'uri da wannan ba yawa jikin ne har yanzu ba dad'i​​​```

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ​*πŸ“š✍🏻

*DEDICATED TO FATY AZLAND*
```Wannan page d'in naki ne me kad'ai my Azland kiyi yanda kike so da shi na baki shi kyauta```

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 16~20*

"Kamar ya Yusuf?
Dan meyesa kake mun haka ne?
Yau fa aure na wata d'aya amman sai jiya nasamu.".......

  Katseshi yayi da cewa
" to naji nataya Ka murna amman ina baka shawarar kar kabari tayi ciki yanzu dan wallahi nima na Hafsat ba so nake ba dan zai hanaku jin dad'i."

  "Hmm kai wallahi kacika matsala naji kuma nagode shikenan."

"To yanzu tashi muje nifa inason na zauna kusa da mata na ina kallon ta."

"Kai wallahi maye ne kaida kullum kuna tare shine yanzu zakace kanason kallon ta" ya k'arasa maganar yana kallon shi yana dariya.

  "Naji dai tashi mutafi wallahi inason kallon mata ta."

  "To tashi muje."

B'angaren su Husna kuwa hiran su suke sosai da Hafsat,  itama Hafsat ta sake jiki da Husna dan taji tanason ta.

  Husna ce tace
"Anty Hafsat me kike son kici zan shiga kitchen na d'aura abinci."

"Aa Husna komai kika dafa zanci dan bana sha'awan komai."

  Ta tashi zata shiga kitchen kenan sai gasunan sun shigo Farooq ya bud'e baki zaiyi magana amman Yusuf ya rigashi da cewa
"Aa Husna ina zaki naga kin tashi?"

  Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace
"Kitchen zan shiga d'aura girki."

Farooq ne yace
"Yauwa yayi dai-dai muje muyi girki kai kuma sai Ka zauna wajen matar ka kafin mu gama" yana k'arasa maganar ya ja hannun Husna sukayi kitchen.

  Shikuwa Yusuf wani bakin ciki ne ya lullu6eshi daman shi yazone dan Husna kuma gashi ta tashi wanne hanya zaibi dan ya dawo da su.

  Ai kuwa a take wani abu ya fad'o masa da sauri ya mik'e shima ya shiga kitchen d'in.

  "Haba dan Allah ya munzo gidan ku zaku shiga kitchen Ku barmu a parlour."

  Husna kam har ta tsorata dan batayi tsammanin mutum ba.

  Farooq ne yace
"To Idan bamu girka muku abinci ba ya zamuyi kenan?" Ya tambaye shi.

  "Abu mai sauki anjima kaje kasiyo mana."

  Da k'arfi Farooq yace
"Abincin siya!
Sanin kanka ne kasan bana cin abincin siyarwa Yusuf dan Allah kaje Ka zauna yanzu zamu gama mu dawo."

  Zuciyar shi cike da Kuna ya dawo ya zauna yana kullah abinda zai shirya.

   Gyaran murya yayi sai a lokacin Hafsat ta d'aga ido ta kalleshi.

  "Hafsat inason nayi mana gyaran gida kuma bansan ina zamu komaba inason kafin ki haihu an gyara mana gidan mu."

  Cikin mamaki Hafsat take kallon shi sannan tace
"Gyaran gida fa kace? naga gidan namu ba abinda ya sameshi duduma yaushe aka ginashi auren mune fa."

  "Eh nasani Sweetheart bakyason idan anzo suna aga sabon gida?"ya tambaye ta.

  Sai a lokacin Tayi murmushi tace
"Gaskiya ne kuma fa wallahi sai yanzu na fahimmace ka."

  "To shine bansan ina zamu zauna a mana gyaran gidan ba, kinga ai bazai yu mu zauna ana gyara ba ko?"

  "Ai kuwa haka ne to ai ko gidan haya zaka iya kamawa kafin a gama gyaran."

  Wani mugun kallo ya  watsa mata sannan yace
"Haba wanne irin gidan haya?
Ki bari kawai zan samu zuwa gobe ko anjima."

Ita dai kallon shi kawai take dan tasan akwai dalilin wannan maganar nashi.

   Su Farooq kuwa suna girki suna zuba soyayyar su haka sukayi har suka kammala.

  Rice and stew sai kuma salat da kunun aya wanda yasha kayan had'i
A dining suka jera komai da komai hatta plate da cups sai da Farooq ya d'auko ya ajiye sannan ya bar wajen.

  Kasan cewar suna gamawa aka kira sallan azahar Farooq yaja Yusuf suka wuce masallaci su kuma sukayi  sallahn su.

  Gaba d'ayan su suna zaune suna ci Yusuf kam baya magana sai kwasan na gara yake.

Bayan sun kammala cin abincin parlour suka koma suka zauna Yusuf ne yace
"Abokina daman akwai maganar da nake so na fad'a maka."

  "Owhk ina jinka."
"Inason zanyi gyaran gida amman kuma banida wajenta zama da mata ta zuwa lokacin da
za'a gama mana."

  "Gyaran Gida kuma Yusuf?
Me yasamu gidan naka da zaka gyara?"

"Kana gani dai Hafsat ta kunsan haihuwa to banason ayi suna ban gyara mana gidan ba."

"Owhk na fahimceka kana so ka fara gyara kenan."

  "Yauwa ashe ka gane, to amman banida inda zamu koma da zama kafin a gama gyaran."

  "Owhk wannan ba matsala bane zan bud'e muku wancan part d'in sai Ku zauna."

  Wani mugun murmushi yayi sannan yace.......

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Ido cike da k'wallar muna furci yace

"Nagode Abokina Allah yasaka maka da alkhairi bansan me zance maka ba banida bak'in yi maka go"........

  Katseshi yayi da cewa
" Haba Yusuf menene a ciki idan ni ban maka ba waye  zai maka a duniyar nan dan Allah ka daina gode mun,  ka godewa Allah kawai. "Ya k'arasa maganar ya rumgumarshi.

  Husna kuwa gabanta ne yashiga fad'uwa dan kuwa tasan akwai wani abinda Yusuf yake shiryawa.

   Hafsat ce tace
" mun gode Ya Farooq nima naji dad'i haka wallahi dan kuwa kullum muna tare da Husna."

  Yusuf kuwa a zuciyar shi cewa yake
"Wallahi Farooq sai kabarmum Husna nafika sonta saboda kai bakasan menene so ba dan haka sai na shiga tsakanin ku na rabaku."......

  Maganar Farooq ya katseshi da cewa
" ai kar kidamu Hafsat yanzu kam ga Husna sai Kuna wuni tare kunga ko wanne a cikin Ku zaiji dad'i. "

  Yusuf ne yace
"To yanzu Hafsat ki tashi mu tafi gida mu fara shirye-shirye kinga gobe zamu dawo nan da zama."

  Farooq ne yace
"Kai wallahi kacika gaggawa kabari mana Isyaku ya share muku gidan."

  "Eh haka ne amman yanzu ka sashi ya share dan Allah."

  "To shikenan ba matsala Allah yakaimu goben."

  Gaba d'aya suka amsa da
"Ameen Thumma Ameen."

  Suna gama maganar Yusuf ya d'auki matar shi cikin farin ciki sukayi gida.

Suna fitΓ  Farooq ma ya fita.

  Suna tafiya Husna ta shiga gyaran gida tayi shara tayi moping duk da ba wani kurane da gidan ba.

  Kitchen ta shiga ta d'aura abinci nan da nan ta gama kasan cewar tuwon semo da miyar ku6ewa d'anya sai kuma  banana juice.

  Burner ta kunna nan da nan gidan ya d'auke da k'amshi.

  Wanka tashiga bata wani dade ba ta fito d'aure da towel akwatin k'anan kayanta ta bud'e.

  Wani riga da wando ta fidda ta saka Wanda ba k'aramin kyau ya mata ba.

Rigar pink sai kuma wando white sai ribom d'inta shima pink zama tayi a gabΓ n mirror ta fara tsara kwalliya.

   Farooq kuwa da yafita gidan Hajiyar  shi ya nufa dan sanar da Ita dawowar Yusuf gidan sa.

  A parlour ya sameta zaune akan sallaya da halamun ta idar da sallah ne.

  Sallama yayi ta amsa masa ya shigo.

  Gaidata yayi cikin ladabi da biyayya Ita ta amsa cikin so da k'aunar d'an ta.

  "Umar lafiya kazo da yamman nan?"
"Eh mummy lafiya k'alau daman Yusuf ne yace zaiyi gyaran gida to shine yace bashida wajen zama."

  "To shi kuma wanne irin gyara zaiyi bayan gidan nashi sabo ne."

  "Eh Mummy saboda Hafsat takusan haihuwa shiyasa yake son ya d'an kinkintsa."

  "To ya zakuyi kenan?"
"Eh Mummy nace yazo ya zauna a d'aya part d'in shiyasa nazo na fad'a miki."

  "Hmm Umar ba wai na hanaka ba kasan rayuwar yanzu ba tabbas kar ka ajiye abokin ka a gidan daga baya wani abu yabiyo baya."

  "Aa Mummy insha Allah ba abinda zai biyo baya kimana addu'a kawai."

  "To shikenan Allah ya had'a kawun nan Ku."

"Ameen Thumma Ameen Mummy."

"Ya Husna tana lafiya ko?"
"Lafiyan ta k'alau Mummy tace na gaida ki."
"To ina amsawa."
"Mummy inasu Khadijat da maryam ne banjisu ba?"
"Eh basu dawo a islamiya ba."

Haka dai sukayi ta hiran su sai da magriba ya tafi.

B'angaren Yusuf kuwa suna zuwa gida ya fara had'a musu kaya nan da nan ya had'a kayan su gabaki d'aya ya saka a bayan motar sa sannan ya koma yace da Hafsat zai kai kayan su gidan yana zuwa.

  Haka kuwa akayi akan hanya magriba tayi mishi sai da ya tsaya a masallaci yayi sallah sannan ya wuce.

  Bayan Farooq yayi sallah ya dawo gida tun kafin ya shiga gidan yaji wani sanyayan k'amshi ya bige mishi hanci.

  A parlour ya sameta zauna tana kallon Arewa24 hakan yasa yak'i yin sallama ya lalla6a ta baya yaje ya rumgume ta.

  Wani irin tsorata Husna tayi dan batayi tsammanin mutum ba murya yana rawa tace
"Dan Allah waye kayi hak'uri ka barni."

  Dariya ne ya kama Farooq ganin yanda tayi hakan ne yasa shi juyata ta kalli fuskan shi.

  Ajiyar zuci tayi sannan tace
"Kai Ya Farooq dan Allah wallahi ka tsoratani."

"Kai My Angle kinga yanda kikayi kyau kuwa."

Murmushi tayi sannan tace
"Thank you"

  Bud'ewar kofa sukaji sai da yashigo sannan ya musu sallah.

  Farooq ne ya amsa mishi amman ina Yusuf ya tafi wata duniyar ganin Husna cikin wannan kayan.

  Farooq ne yace mishi
"Aa Yusuf lafiya ko kamanta wani abu ne?"

  Sai a wannan lokacin ya dan matsa yace
"Aa nazo ne karbi key d'in parlour."

"Owhk bari na shiga na d'auko maka."
"Owhk ina jiranka nakawo kayan mu ne."

Farooq bai kulashi ba ya shiga ya barsu a parlour.

"Amarya amman kinyi kyau irin wannan kwalliyar duk Farooq kikayiwa?"

  Wani kallo ta watsa mishi sannan tace
"Idan banyiwa mijina ba wa zanyiwa?"

  Murmushi yayi yace
"To mukuma meye amfanin mu?"

Kin kulashi tayi
Tayi kamar ba da Ita yake ba.

  Sake matsowa yayi yana leka ta sai faman kallon kirjinta yake Ita kuwa duk ta damo Farooq ya dawo dan idan ta tashi wando ya matse ta abin zaifi haka.

Shi kuwa mayen yana nan yana ta faman kalle-kallen shi sai ga Farooq..............

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​πŸ“š✍🏻

*DEDICATED TO MARYAM S BELLO*

​​​```Wannan page d'in naki ne ke kad'ai maryam kiyi yanda kike so na baki shi kyauta kiyi yanda kike so.​​​```

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 26~30​*

Farooq ya fito da sauri ya matsa gefe d'aya kamar mutu min kirki.

  "Yauwa gashi nan sai yanzu na samu."

  Kar6a yayi bai kulashi ba ya fita ya bar musu parlour.

"Ya Farooq meyesa Yusuf yake shiga mana cikin gida kamar nasa gidan?"

  "Husna kenan, ai Yusuf a matsayin d'an uwa na yake gidan shi da wannan duk d'aya ne dan yashigo ai ba wani abu bane." Ya k'arasa maganar yana rungumota.

  Itadai duk abin ya dameta amman tunda yace haka batada bak'in magana.

  *​TUSHEN LABARI​*

Marigayi Alhaji Ibrahim shine mahaifin Farooq wanda yarasu a wani hatsari da yayi.

Alhaji Ibrahim mai kud'i ne sosai wanda ya rasu yabarwa yaran sa.

  Farooq su uku ne a wajen iyayen sa.

  Shine Babba sai Khadija sai kuma maryam Hajiya Aisha itace mahaifiyar su.

  Hajiya Aisha macece mai hak'uri da mutunta juna kasancewarta ba mai rikici  hakan yasa mutane suke k'aunarta.

Farooq yayi karatu sosai shima yanzu haka yana aiki a bank ba da dukiyar da mahaifinsu ya bar musu ya dogara ba.

  ​*WANENE YUSUF?​*

Yusuf d'an k'awar Hajiya Aisha ne wanda mak'oftaka ya had'asu har suka zama 'yan uwan juna.

  Yusuf da Farooq jinin su ya had'u sosai hakan yasa farooq d'aukan Yusuf ya dawo dashi gidan su.

  Tare suke komai har Wanda basu Sani ba suna cewa uban su d'aya.

  Shi kuwa mahaifin Yusuf ba wani k'arfi yak'e da shiba, yanada wani k'aramin shago a bakin layin su yana sai da kayan tireda.

   Haka rayuwar su yakasan ce komai tare har Allah yakawowa Yusuf mata wato Hafsat ya aura.

   Hajiya Aisha ce tayima Yusuf aure hatta sadaki itace ta biya hakan ba k'aramin dad'i yayiwa mahaifiyar Yusuf wato Habiba ba d'an batayi tsammanin hakan daga garesu ba.

    Bayan Yusuf yayi aure ne Farooq ya samu budurwa wacce ya gani yake so.

  Husna 'ya ce ga Alhaji Aliyu da kasuwa ne cikakke Wanda kowa ya sanshi.

  A lokacin da Farooq ya bayyanawa Yusuf Husna ya nuna kar ya aureta amman yanda yaga Farooq ya nace sai ya barshi ya aure ta.

  Ranar auren Farooq Yusuf ya sake rikicewa yanda yaga Husna ba hijabi a jikin ta,  kasan cewar bata cire hijabi a jikinta.

  Ranar dinner ne Yusuf ya gama haukacewa yanda yaga shigar Husna a wannan lokacin yayi alwashin raba Farooq da matar shi.

  Ranar da suka raka Farooq har sunbaro gidan Yusuf ya kira shi a waya yace kar yasake ya kwanta da Husna saboda zai iya ji mata ciwo har ta kwanta a hospital hakan ne yasa Farooq tsorata ya yarda da maganar Yusuf.

  Ko wanne rana sai Yusuf ya kawowa Farooq wani karya har tsawon wata d'aya.

  ​​​```WANNE SHINE TA K'AITACCEN LABARI SU.​​​```

*​CIGABAN LABARIN​*

Washe gari da sassafe Yusuf ya d'auko Hafsat suka dawo gidan su Farooq ko a barci basu tashi ba.

  A cikin barci Farooq yaji ana kwankwasa musu kofa wanda hakan ba k'aramin tsorata shi yayi ba dan baiyi tsammanin mutum war yanzu ba.

Tashi yayi ya fito ganin Yusuf tsaye ne abin ya bashi mamaki tambayan shi yayi da cewa
"Yusuf lafiya ko jikin Hafsat ne?"

  Murmushi yayi mishi yace
"Aa ba jikin ta bane mun dawo ne so munaso muyi breakfast a gidan ka."

  "Kai wallahi ka cika matsala yanzu fa 6:30 ne shine zaka damu breakfast?
To wallahi ko a barci bamu tashi ba."

  "Kana nufin bazamu shiga gidan ka ba kenan?"

"Aa nifa ba haka nake nufi ba,  kawai dai nace bamu tashi a barci bane amman dan shiga gida ne bismillah,  ina Hafsat d'in take?"

  "Owhk bari na kirata tana mota jirani nazo."

  Shi kuwa Farooq mamakin abotarsu yake da Farooq yanda suka saba da wasu abubuwa.

    Gaba d'ayan su a parlour suka zauna Hafsat ce tace
"Nifa wallahi yunwa nake ji a taimaka mun da abinci."

  Wayyo hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Yusuf ba dan daman Allah Allah yake yaga Husna.

Farooq ne yace
"Gaskiya yanzu Husna barci take saboda jiya daddare bata samu tayi barci ba,  sai dai kishiga kitchen ki girka ko Indomic and egg" ya k'arasa maganar yana kallon ta.

  Yusuf ne Wanda maganar ba k'aramin 6ata mishi rai yayi ba yace
"Wai dan meyesa kake mana haka ne?
Dan Allah Farooq ka tasheta tayi mana gaba d'aya mu nima yunwan nake ji."

  "Haba dan Allah Yusuf na fad'a maka yanzu tasamu tayi barci please kayi hak'uri mana."

  "Owhk Hafsat tashi mu bar mishi gidan sa" yana fad'an haka ya mik'e zai fita Farooq yayi saurin shan gaban shi yana cewa

"Haba kai kuma daga fad'an haka shine har kayi fishi bari na tashe ta yanzu."

  Wani shu'umin murmushi yayi sannan ya dawo ya zauna.

   Ita kuwa tana k'ance sai faman shan barcin ta take hankalin ta kwance ba abinda yake damun ta.

  Zuwa yayi ya zauna a bak'in gadon ya zuba mata ido sai da yayi kusan 5mins sannan ya d'an shafa bayan ta yana wasa da gashinta jin hakan ne yasata tashi ba shiri.

  "Sorry My Angle na tashi ki ko?"

Murmushi tayi mishi sannan tace
"A'a."

"Owhk ki tashi ga su Yusuf sunzo kuma wai yunwa suke ji please tashi mu shiga kitchen kunsan yau zan tafi office."

  Gaban ta ne yayi mummunar fad'uwa dan Ita yanzu batason Yusuf yazo gidan nan amman ba yanda ta iya.

  "Ya naga kinyi shiru lafiya dai ko."

  Murmushi tayi tace
"Ba komai tashi muje."

  Haka ta mik'e ta saka k'atuwar hijabi har k'asa sannan suka fita.

  Suna fitowa sukayi arba da Yusuf daman idon shi yana gurin wani murmushi ya sakar mata Wanda yasa gabanta ya fad'i amman kuma sai ta basar ta watsa mishi nata hararar.

   Zama tayi a gefe d'aya tace
"Ina kwanan ku."
"Lafiya k'alau amarya ya kike?"
"Lafiya k'alau, Anty Hafsat ya jiki."
"Jiki Alhamdulillah wallahi yunwa nake ji."

  "Ayya bari nayi sauri na had'a miki."

Yusuf yayi wuf yace
"Ai nima haka yunwan nake ji a taimaka mana mu biyu yanzu."

  Kallon shi tayi sannan tace
"Hmm kajira na gama."

Allah sarki bawan Allah Farooq yana gefe yana kallon su sai da yaga Husna ta wuce kitchen sannan ya bita.

  Yusuf ma mik'ewa yayi ya bisu........

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

  πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA* πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ*​πŸ“š✍🏻

*DEDICATED TO MY FAN'S*

```Ina kuke masoya ABOKIN MIJINA to ga wannan page d'in na Baku shi kyauta duk da nadan bazai isheku ba ko WACCE ta d'auki kalma d'aya ```

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 31~35*

Yusuf mik'ewa yayi ya bisu kitchen d'in lokacin da yashiga samu yayi Farooq yana kissing d'in Husna wani abu yaji ya daki k'irjinsa amman kuma sai ya daure ya shiga yana cewa
"Yauwa bari nima na tayaku dan mu gama da wuri."

  Farooq ne yace
"Haba kai kuwa kabari mana yanzu ai zamu gama kagani fa doya ne" ya k'arasa maganar yana nuna doyar.

  Yusuf kuwa wuk'a ya d'auka yana cewa
"A'a wallahi kabari na tayaku muyi mu gama mu tafi aikin mu."

  Husna wacce tunda ya shigo ya fara maganar bak'in ciki ya lullu6e ta, ko kallon sa batayi dan kuwa yanzu ta fara gane shi.

   Kallon Farooq tayi Wanda sai faman washe hak'wara yake tace
"To ni zan koma parlour wajen Anty Hafsat kuyi girkin tare."

  Da sauri Yusuf yace
"Haba amarya ya zaki bar mana girki ai kinsan bazamu iya ba idan ba ke ."

  Farooq yace
"Haba sweetheart idan kika tafi ai kinsan bazamu iya ba please ki tsaya mu k'arasa."

  Bata kulasu ba ta fere doyanta ta d'aura sannan tazo tayi egg sos.

   Bata wani d'auki lokaci ba ta kammala amman kuma ko wanne motsi idan Husna tayi a idon Yusuf dan ko kad'an baya d'auke idon sa akan ta.

  Farooq ne ya jera komai a dining sannan shima yaje ya shiga wanka.

  Hankalin Yusuf gaba d'aya yana kan d'akin da Husna ta shiga dan kuwa yasan wanka taje yi.

   Bata wuce 30mins ba ta fito cikin wani atamfa mai ratsin pink a jiki Wanda ya amshi jikin ta  ba wani kwalliya a fuskan ta.

   Gaba d'aya sune suka zauna a dining Yusuf ne ya zauna a kujeran da yake kallon na Husna dan ko me tayi yana kallon ta, hakan ne yasa  Husna mik'ewa ta zauna akan cinyar Farooq tana cewa
"Honey ni a baki nakeso kabani bazan iya ci ba" tana maganar cikin shagwa6a.

  Kara tallafota Farooq yayi yace
"An gama my angle."

  Wani bak'in kishi ne ya ziyarci zuciyar Yusuf yanda ya sashi ya mik'ewa yana shirin barin parlour ne Farooq yace mishi
"Yusuf lafiya kuma zaka fita bakayi breakfast d'in ba?"

  Wani kallo Yusuf yayiwa Farooq sannan yace
"Bazan zauna kuyi wannan rashin kunyar a gaba na ba."

  Husna ce tayi wuf tace
"Wayyo Allah Honey yunwa nakeji kabani naci mana."

  Da sauri Yusuf ya fita dan idan ya tsaya kallo ta idan baiyiwa Farooq suka ba to zuciyar shi zata buga.

   Bayan ya fita sauka tayi a kanshi tace yaci dawuri ya tafi wajen aiki kar yayi lett.

   Shi kuwa Yusuf yana fita mota ya hau yabar gidan gaba d'aya dan shi bazai iya zama ba amman wallahi Yau sai ya dawo ya bayyana mata abinda yake ran shi.

   Ita kuwa suna gamawa Farooq ta raka mota ya tafi dawowa tayi wajen Hafsat wacce da halamun barci ne yake damun ta.

  Tambayan ta tayi da cewa
"Anty Hafsat barci kike ji ne?"
"Eh wallahi Husna barci nakeji sosai."
"To ki kwanta mana."

Ai kuwa tana ajiye kanta barci yayi gaba da ita.

  Husna tana ganin haka ta d'auki wayan ta ta kira Hajara mai lalle dan tazo yanzu tayi mata.

  Ai kuwa tayi sa'a Hajara bata aikin komai nan da nan tazo ta fesa mata lalle.

Bayan an gama mata tashin Hafsat tayi tace ta tashi itama a mata,
amman sai tace A'a ita zata shiga part d'in ta.

  Tana shiga Hajara tayiwa Husna shara da moping duk ta goge mata gidan ta fess.

  Sallaman ta tayi ta tafi sannan ita kuma ta d'aura girkin dare.

   Shima bata d'auki lokaci ba ta gama tuwon shinkafa da miyar ya kuwa Wanda yasha kayan k'amshi da nama.

  Ciki ta shiga dan yin wanka.
Tana Barin parlour Yusuf ya shigo dan yasan Farooq yanzu bai dawo ba.

  Ganin bata parlour ne ya tabbatar da cewa tana cikin d'aki.

  Hanyar d'akin ya kama dan kuwa yau komai zai faru sai dai ya faru.

  Ita kuwa tana toilet tana wanka dan bata son Farooq ya dawo bata shirya ba.

  Cikin d'akin ya shiga yana du6e-du6e amman ina 6e ganta ba har zai fita sai yaji motsi a toilet.

Wani shu'umin murmushi yayi sannan yayi hanyar......

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Wani shu'umin murmushi yayi sannan ya kama hanyar toilet d'in da take.

  Bud'ewa yayi a lokacin ita kuma ta d'aura towel a jikin ta kenan sai gashi nan ya shiga toilet.

  Ita bata kula da shiba dan ita sauri take, shi kuwa duk ya haukace a kallon ta.

  Juyowan da zatayi sai kawai taga Yusuf a toilet tsaye yana kallon ta.

  Wani irin ihu ta saka sannan ta fashe da kuka tana rok'on shi akan dan Allah ya fita.

  Kin fita yayi sai ma kara matsowa inda take yake ita kuwa duk tsoro ya mamaye ta gashi ba hanyar gudu.

  Sai da ya matso daf da ita yana lashe harshe sannan yace
"Daman nazo ne nafad'a miki abinda yake zuciya na Husna,
Husna ina sonki wallahi idan ban sameki ba mutuwa zanyi please ki taimaka mun ki taimakawa rayuwa na."

  Wani kallo ta mishi sannan tace
"ban gane na taimaka maka ba Yusuf me kake shirin yi?"

  Kara matsowa yayi sannan yace
"Yauwa dan Allah inason kibani had'in kai ina yin six da ke ko kuma ki raba auren ki na aure ki sai ki zabi d'aya a cikin biyun dan Allah Husna."

  Ita dai Husna ba abinda yake fita a jikin ta ni ba zufa ba,  zuciyar ta tana zugawa Amman kuma sai ta daure tace
"To sai mu fita a toilet mu k'arasa maganar dan naga mai muhimmanci ne."

  Haba wa tana fad'an haka yaji wani dad'i a rain shi dan gani yake tarkon shi ya kamata.

  D'aki suka koma,  shi kuwa har da zama a bak'in bed ban ji yake shine angon.

  Hijabin ta ta d'auka da sauri ta saka, Yusuf ne yace
"Haba Husna ta d'an meyesa zaki rufe mun jikin ki baki san inajin dad'in ganin shi hakan ba?"

  Wani kallon tsana ta watsa mishi sannan tace mishi cikin d'aga murya tace
"Tunda jikin na uban ka ne ba,
To wallahi Yusuf ka fita a ido wallahi zan d'au mataki a kanka banza alade kawai mai bin matar a abokin shi" ta k'arasa maganar tana wani irin huci.

   Wani kallo ya mata sannan yace
"Wallahi idan baki bani had'in kai ba wallahi sai na kashe Farooq idan yaso sai naga da wa zakiyi tunkaho."

   Husna da jin haka ta rikice idanun ta sukayi bak'i bata ganin komai hakan ne yasa ta d'aukan kwalba ta kwad'awa Yusuf a goshi.

  Ai kuwa nan da nan Yusuf jini ya wanke mishi fuska,
Da gudu ya fita yabar gidan dan yaga alamun idan ya zauna Husna zata kashe shi.

  Yana fita ya hau mota ya wuce hospital d'an kuwa ba k'aramin ciwo ya ji ba.

  Ita kuwa Husna yana fita ta fad'a kan gado tana kuka sosai dan batasan ya zatayi ba.

  Waya ta d'auka ta kira Mummyn ta amman ina har 3 missed call bata d'auka ba hakan ne yasa ta sake kwanciya wani sabon kuka.

   B'angaren Farooq kuwa hankalin shi duk ya tashi kasan cewar Yusuf yak'i d'aga masa waya dan yasan fishi yake da shi.

  Har magriba Husna tana nan tana aikin kuka tana tunanin ta ina zata lullowa al-amarin Yusuf dan yaga ba da wasa yazo mata ba.

  Tana cikin tunani wayan ta ya fara ringing da sauri ta d'auka ganin Mummy.

  "Hello mummy nashiga uku Yusuf zai kashe ni wayyo Allah mummyna ki taimaka mun dan Allah" ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka.

  Mummy wacce bata san me Husna take nufi ba tambayan ta tayi da cewa
"Husna lafiyan ki kuwa?
Me aka miki?
Me Yusuf ya miki?"
Duk wannan tambayan tayi mata a lokaci d'aya.

  Ai kuwa nan da nan Husna tabawa Mummyn ta labarin abinda Yusuf yake mata tun randa aka kawo ta.

  Shiru na d'an lokaci tayi sannan tace
"Mijin ki yasan da wannan abinda yake faruwa?"

  "A'a Mummy bai sani ba,
kuma wallahi ko na fad'a masa bazai yarda ba saboda ya yarda da Yusuf fiye da tunanin mu, Mummy kuma cewa yayi sai ya kashe shi fa."

   "Husna wannan al'amarin ba na waya bane, ki tashi kishirya ki saka kayan ki kar kibari mijin ki ya gane kina cikin damuwa,  kuma kar kiyi kurkuren fad'a masa dan ba yarda zaiyi ba, kiyi hak'uri zuwa gobe zamuyi abu d'aya."

  " To Mummy nagode. "
"Yauwa 'yar albarka kar kibari yagane kina cikin damuwa kinji."

  Haka dai sukayi sallama sannan ta tashi ta shirya tayi kwalliya.

  Bayan Yusuf ya tashi daga hospital gida ga dawo, part d'in shi ya shiga ko sallama babu.

  Hafsat ganin ya shigo ba sallama gashi goshi a fashe yasata mik'ewa tana tambaya lafiya?
Amman ina kin kualta yayi yashiga d'akin shi ya rufe.

  Farooq yana dawowa gida part d'in Yusuf ya shiga d'an yasan yadawo gida kuma ga motar shi a ajiye.

  Bayan ya shiga sun gaisa da Hafsat yake tambayan ta ina Yusuf, cemishi tayi yana cikin d'aki.

  Kwankwasa k'ofar yayi sai da ya dad'e sannan ya bud'e mishi yana shiga yagan shi goshi a fashe da sauri ya k'araso wajen shi yana tambayan shi me yasa me shi.

  Ko kallon shi baiyi Ba yace mishi
"Acceded nayi."
Cikin zaro ido Farooq yace
"Haba Yusuf yanzu har zaka mun fishin da zakiyi acceded baka fad'a mun ba."
"No Farooq ba wani ciwo naji ba shiyasa ban fad'a maka ba."
"To naji tashi muje hospital yanzu."
"Naje gashi nan an bani magani."
"Kaci abinci ne?"
"A'a ban ci ba."
"To tashi muje muci tare."
"A'a kaje kawai bazan iya ganin wasu abubuwan da ya haramta ba."
"Kaga dan Allah tashi muje kaifa bakada lafiya."
"Kayi mum alk'awarin bazakayi komai a gaba na ba."
"Eh naji dan Allah tashi muje."
  Haka suka tashi suka fita suka zo part d'in shi.

Suna sallama gaban Husna ya fad'i amman sai ta d'aure ta amsa musu cikin sakin fuska.

  Tashi tayi tanayiwa Farooq sannu da zuwa,  cikin sakin fuska ya amsa mata sannan yace mata
"My angle muje dining kinga Yusuf yayi acceded bai fad'a mana ba kuma yunwa yake ji yaci abin ci yasha magani."

  Kallon shi tayi tace
"Ayya Yusuf acceded kayi ?
To Allah ya sawak'e"
Tana maganar tana wani basarwa.

  Abin ci sukaci suka tashi sannan Farooq yabashi magani yasha.

  Suna zaune suna hira shi kuwa Yusuf yana kallon Husna yana tunanin ne ya kamata yayi mata wani shawara ya yanke Wanda da haka yakama ta ya fara.

  Suna cikin  hira kawai ya rik'e kai yana ihu wai yana mishi ciwo.

  Farooq wanda hankalin shi gaba d'aya ya tashi ya rik'e shi yana addu'a a haka barci ya d'auke shi a wajen.

  Farooq ne yace da Husna
"Alhamdulillah tunda munsamu yayi barci ki d'auko blacker na rufe shi kinga sai dai ya kwana ana."

  Badan ran ta yaso ba taje ta d'auko Farooq ne ya rufe shi suka kashe mishi wutan parlour suka shiga ciki.

  Suna shiga ya tashi ya zauna yana zuba wani uban murmushi........

  ```TURKASHI!```

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

  πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

​```DEDICATED TO MARYAM BINTU​```

```​​​DAN ALLAH JAMA'A KUNΓ€ MUN HAK'URI KUBARI KUGA INDA LABARIN YA DOSA YANZU NE FA KUKA FARA JIN LABARIN GABA D'AYA PAGE 9 NE FA MUKAYI AMMAN DUK KUN K'OSA DAN ALLAH KUYI MUN HAK'URI KUJI YANDA ABIN YAKE​​​```

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

 
*​Page 40~45​*

Suna shiga d'aki Husna bata wani bata lokaci ba ta d'auki hijabin ta tasaka  tana shirin fita,
Farooq yace mata
"Ina kuma zaki tafi Husna?"

  Kallon shi tayi sannan tace
"Gidan mu zan tafi mana."
"Kamar ya gidan Ku?
Me aka miki da zaki tafi gida a Daren nan?"
"Ya Farooq zan fad'a maka gaskiya,
Bazan iya kwana tare da namijin da ba muharramina ba a cikin gida d'aya ba,
Kai yanzu kana ganin abinda kayi ya dace ?
To wallahi idan har Yusuf anan zai kwana wallahi bazan kwana ba."

  "Haba Husna mutumin nan fa Bashi da lafiya kina gani kulawan mu yake buk'ata dan Allah kiyi hak'uri mu kwana,
Kuma ma naga kwana d'aya ne."

  "Hmmm Ya Farooq kenan!
Wallahi kaji na rantse bazan kwana a nan ba Wallahi gidan mu zan tafi tunda naga Aboki yafi matar ka muhimmanci a gareka."

  "Wai Husna bakida hankali ne kike fad'a mun haka?
Karfa ki manta Yusuf tamkar d'an uwana ne na jini dan meyesa bazamu taimaka masa ba?"

"Tai mako fa kace!
Wallahi sai dai kai ka taimaka masa bad'ai ni ba,
Kuma kana cewa shi tamkar d'an uwa yake a gurinka,
Eh naji amman kai kana tsammanin Yusuf zai kaika gidan shi yace ka kwana a parlour bayan ga matar shi a cikin gidan?"

Sai da ya d'an yi jimm sannan yace
"Kwarai kuwa Husna nafi k'arfin haka a wajen Yusuf."

"Kaga ya Farooq yanzu bamuda lokacin kace nace kawai kayi abu d'aya ko ni ko Abokin ka kaza6a."

  "Wayyo Allah na Husna ya kike son nayi?"
"Owhk hakan yana nufin kazabi abokin ka."
"No Husna dan Allah kar ki tafi kibarni dan Allah na rok'eki."
"To bari ma kagani mummy zan kira a waya ta turo mun driver dan wallahi bazan iya ba na kwana da k'ato a cikin gida" ta k'arasa maganar ta danna waya.
Da sauri ya warce wayan yace naji zan tashesa ya tafi.

  Wani farin ciki ne ya lullu6e ta dan daman hakan take nema amman kuma bata nuna yanda Farooq zai gane ba.

   B'angaren Yusuf kuwa yana la6e yana jinsu dan kuwa duk abinda sukeyi a kunnen sa sukayi shi.

  Yana jin Farooq ya nufo k'ofa hakan ne yasa shi gudu Wanda har yana buguwa da gini baya ganin gaban shi.

  A daddafe ya zo ya kwanta dan kuwa kan shi ya bugu amman ba damar magana.

  Farooq shi kad'ai ya fito dan yau Husna da gaske take ba da wasa ba.

  A kwance ya sameshi tamkar marar lafiyar gaske,
Shi kuwa Farooq duk tausayin Yusuf ya mamaye mishi zuciya.

   Zuwa yayi ya zauna a bakin kujeran da yake kwance a hankali yake tashin sa tamkar wani Baby,
Shi kuwa Yusuf yana jinshi amman yayi banza da shi.

  Sai da Farooq yayi da gaske sannan Yusuf ya tashi.

  Yana tashi yayi dai-dai da kwankwasa k'ofar parlour.

  Farooq yake tambaya waye?
"Ni ce Ku bud'e mun."
Jin muryan Hafsat ne yasa shi mik'ewa ya bud'e k'ofar.

  "Wai yau kai a gidan su zaka kwana ne?
Ya kabarni har yanzu ina zaune ina jiranka amman shiru?"

  Farooq ne yace
"Ayya kiyi hak'uri yanzu ma da zan rakashi."
"Owhk tashi mu tafi."
Wani haushin su ne ya kamashi sannan yace
"Wayyo Hafsat nifa banda lafiya kuma gaskiya ina tsoron gidan nan ni kad'ai kawai kizo mu kwana a parlour nan."

  Wani kallon tara bai cika goma ba tayi mishi sannan tace
"Gaskiya naga alamun rashin lafiyar gaske a tattare da kai,
Gaskiya kan ka ya bugu sosai Wanda har ya kawar maka da hankali."

  Wani kallo ya mata yace
"Ke Hafsat banason zancen banza ni sa'anki ne kike fad'a mun haka?"

"Eh ai naga hakan a tattare da kai ne,
Dallah malam tashi mu koma namu gidan kujimun mutum fa" ta k'arasa maganar tana dariya dan ita abin gaba d'aya dariya ya bata.

  Ganin zai 6ata mata lokaci Bashi da niyar tashi,
Hakan ne yasa ta rik'e mishi hannu ta fara Jan shi.

"Wai ke Hafsat baki da hankali ne?
Dallah sake mun hannu."

"To naji kazo mu tafi."
Haka ya tashi ya fita ba dan son ran shi ba.

  Washe gari da asuba Farooq yaje duba abokin shi.

  Yana tafe bayan sun gaisa yake tambayan shi ina Husna.

"Husna tana barci bata tashi ba dan jiya bamu kwanta da guri ba."

  Wani bak'in ciki ne ya mamaye shi amman kuma ya daure yace
"Gashi kuma yunqa nake ji."
  "To Hafsat bata tashi a barci bane?
Ai da ko tea ta d'aura maka kafin gari ya gama waye wa."
"Kayya Abokina kasan Hafsat ba wani abin kirki zatamun ba."
"To shikenan bari na d'aura maka ai yanzu zaiyi."
"No Abokina!
Munada mata kuma zaka shiga kitchen?
Wallahi ban yarda ba."

"To ya zanyi kenan?"
"Tashi muje ka tashi Husna ta d'aura mun."

Kallon shi Farooq kawai yake dan shima yanzu abubuwan da Yusuf yake ya fara isan shi.

  "A'a gaskiya yanzu bazan tashi matata a barci ba gaskiya,
haba Yusuf ga taka matar a gida amman sai tawa matar?"

  "Owhk kanason kamun gori ne ko me?
Na rigaka aure fa Farooq."
"Ai wannan ba maganar aure bane,
No kawai nace matata Ba zata tashi yanzu ta d'aura maka breakfast ba wallahi"............

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

​*DEDICATED TO REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​*

πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†πŸŽ‚πŸ†

​​​```​HAPPY ONE YEAR ANNIVERSARY REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS WISHING YOU ALLAH BLESSING NOW UNITS THEN​​​​```
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

  ````​​​​​​Alhamdulillah, Allah mum gode maka da kakawo wannan rana mai albarka​​​​​​```

```​ALLAH UBANGIJI KASA ALBARKA A CIKIN WANNAN KUNGIYAR TAMU, YA ALLAH KA KAREMU DAGA SHIRRIN MAK'IYA, YA ALLAH KA K'ARA MANA BASIRA DA HAZAKA, ALHAMDULILLAH ALLAH MUN GODE​```

  ​​​​​​```INA KIKE!  YABON GONI YA ZAMA DOLE FATY AZLAND DOLE MU YABA MIKI KECE SANADIYAR HAD'UWAR MU A WANNAN GIDA MAI TARUN ALBARKA,
ALLAH YASAKA MIKI DA MAFIFICIN ALKHAIRI​​​``` ​​​

​UP​πŸŽ‚
      ​UP​πŸ†
           ​UP​πŸŽ‚
                 ​UP​πŸ†
           ​UP​πŸŽ‚
    ​UP​πŸ†

​REAL​πŸŽ‚
    ​PURE​πŸ†
    ​MOMENT​πŸŽ‚
       ​OF​πŸ†
     ​LIFE​πŸŽ‚
     ​WRITERS​πŸ†

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

  ​​​```GABA DAI GABA DAI PURE MOMENT OF LIFE WRITER MUNYI NISA BAMA JIN K'IRA, MAK'IYAN MU FADAWAR MU MUNA GABA SUNA BINMU A BAYA​​​```

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 46~50​*

"Haba Farooq Yau ni kake fad'a ma haka?
Laile ka kyauta kuma nagode da abinda kamun."

"Wai kai Yusuf meye sa baka son Hafsat tayi maka abu sai mata ta?
Girki dai ko wacce a cikin su ta iya,
Kuma ma lokacin da banyi aure ba ai nata kake ci, kawai yanzu ka canza kace sai na Husna meyesa?"

  Wani kallon ya watsa masa sannan yace
"Eh Yusuf yanzu bana buk'atar na Hafsat sai na Husna idan kuma bazaku bani to shikenan."

  "Wallahi Allah kaji na rantse ko Husna bazata d'ora breakfast yanzu ba kawai ka tashi matar ka ta d'aura maka."

  "Kai Farooq kar kanemi fad'a mun magana mana."
"Ai ba fad'a maka magana ba ne gaskiya ne ya za'ayi ga matar ka a gida amman sai dai naje na tashi tawa wannan abin ya fara isata."

  "To Farooq bari na fad'a maka gaskiya,
Abincin matar ka nake buk'ata fiye da tawa matar."

Wani kallo Farooq ya mishi yanda bai fahimmaci me yake nufi ba sannan
"Ban gane me kake fad'a mun ba Yusuf?"

  "Eh Farooq wallahi nata nake so."
  "Wai Yusuf anya yau lafiyan ka kuwa?
Anya ba maganar Hafsat bane gaskiya da tace a kaika hospital?"

  "Kai Farooq kar kanemi fad'a mun magana wallahi zaka sani!
Komai nake fad'a a hankalina nake nasan me nake fad'a saboda kar kayi kuskuren sake fad'an haka" ya k'arasa maganar yana wani huci kamar tsohon zaki.

  Shi kuwa Farooq tsayawa yayi yana kallon shi sannan yace
"Ikon Allah!
Allah yabaka hak'uri."

Tashi yayi ya fita ya koma part d'in shi.

  Yana shiga parlour ya tarar da Husna har tayi shara da moping ta d'aura girki,
Abin ya Bashi mamaki sosai dan tana barci ya fita ya barta.

  A kitchen ya sameta durkusawa tayi ta gaida shi,
Cikin sakin fuska ya amsa sai kuma abinda sukayi da Yusuf ya fad'o masa.

  "Ya Farooq ya jikin Yusuf d'in?"
Ta tambaya.
"Da sauki jikin sosai."
"To Allah yakara lafiya."
Daga nan suka ci gaba da aikin su nan da nan suka kammala.

  Wanka sukaje sukayi a tare bayan sun fito sun shirya dining sukaje dan cin abinci.

  Hankalin kwance suke cin abin cin su,
Shi kuwa Farooq yama mance da wani Yusuf saboda Husna yau da wani irin salo ta tashi.

  Suna gamawa 8:30 ya fita har bakin mota tarashi sai da taga fitan shi sannan ta dawo cikin gida.

  Duk wannan abinda suke a gaban idon Yusuf dan kuwa yana tsaye yana kallon su.

  Yana ganin shigar ta cikin gida ya biyo bayan ta da sauri.

  Ko sallama bai mata ba ya shiga cikin parlourn ta tana zaune tana kallo kawai ganin mutum tayi a tsaye.

Da sauri ta mik'e tana cewa
"Lafiyar ka kuwa Yusuf zaka shigo mun gida ko sallama babu?"

  Wani murmushi ya aika mata sannan yace
"Haba Husna nifa masoyin ki ne,
Wallahi inason ki meyesa ke bazaki biyoni ba?
Haba dan Allah wallahi baki dace da Farooq ba dani kika dace,
Ki biyoni kiji dad'in rayuwa."

   "Kai d'an akuya kayi gaggawar barmun gida idan kuma ba haka ba to wallahi zan maka raunin da yafi wannan na goshin naka."

  Dariya yayi sannan yace
"Ai wannan abin ganin shi nake duk a cikin so ne dan kuwa duk lokacin da na ganshi wani dad'i take lullu6e ni dan kuwa aina tunawa da kene."

  Wani bak'in ciki ne ya sake lullu6e ta dan yanzu batasan yanda zata mishi ba,  katseta yayi da cewa
"Haba Husna kefa wayayyiyace kina abu sai kace bakiyi makaranta ba ,
Please kizo gareni zan faranta miki idan kud'i kike so zan baki ko nawa ne nidai buri na kawai ki raba auren ki ko kuma ina zuwa kullum muyi sex sau d'aya kawai a rana" ya k'arasa maganar yana kashe mata ido d'aya.

  "Kai Yusuf wallahi ka fita a idona bazan baka had'in kai ba sai me?
Bak'in alade kawai ni nafi karfin ka sai dai kaje kanemi uwarka dan naga itace dai-dai kai amman ba niba,
Kuma kayi gaggawar barmun parlour idan ba haka ba zanyi maganin Ka yanzu."ta k'arasa maganar tana nunashi da d'an yatsa.

  Shi kuwa duk wannan zagin da tayi mishi ko a jikin shi sai ma zama yayi a d'aya daga cikin kujerun parlourn yana cewa
"Nifa yunwa nake ji kikawo mun abin ci."

Kallon shi tayi sannan tace
"Abin ci kake buk'ata ko?
Yanzu kuwa zan kawo maka."

"Yauwa ko da kefa kinji 'yar gari."

Ai kuwa tana shiga kitchen wuk'a ta d'auko ta tun karo shi.

  "Me zakiyi da wuk'a Husna?"
"Kaciya zan maka dan kuwa Yau sai nacire abinda yake sakaka iskanci."

Dariya yayi yace
"To sai kumun gani nan a gaban ki."
  Ai kuwa tunkaro shi tayi fuskan ta ba halamun wasa tazo mishi,
Ganin ba da wasa take ba yasa shi cewa
"Wai Husna bakida hankali ne?"
  "Eh shine yanzu nakeson na nuna maka."

  Ai kuwa da gudu ya fita a parlour yana cewa
"Kuji mun mahaukaciyar mata nace miki anayin kaciya biyu ne."

  Ai kuwa yana fita taje da gudu ta sakawa k'ofar key sannan ta dawo ta fashe da kuka.

  B'angaren Farooq kuwa tunda yaje office ya kasa komai sai tunanin maganar Yusuf yake.
"Me Yusuf yake nufi da haka?
Wato dan na sake mishi shine har yasamu yake mun haka?
To ai kuwa idan har yace haka zai mun wallahi ba mai rabamu da shi sai Allah." Ya k'arasa maganar yana busar da iska mai zafi.

  Hafsat tana zaune a parlour Yusuf ya shigo da gudu kamar Wanda aka biyo shi ai kuwa itama tashi tayi ta bishi dan ita a tunanin ta wani abu ne ya bishi.

  "Ke dallah me kike wani bina?"
"Gani nayi Ka shigo da gudu meyesa zan zauna abin ya kamani."
"To ba wani abu bane fita kibar mun d'aki."

  "Kai dai kasani ace  mutum kullum sai masifa."

  "Ke ni sa'anki ne" ya k'arasa maganar yana binta da gudu.

  Tana fita ya rude d'aki yasa key ya k'oma ya zauna yana tunanin me zaiyiwa Husna.

  ​​​```Tur kashi! Me kuma Yusuf zai sake kullawa!!!​​​```

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Wani abu ne ya fad'o masa a lokacin ya mik'e ya d'auki key d'in motar shi ya fita yabar gidan.

  Husna kuwa tana nan tana tunanin wanne irin hukunci ya kamata ta d'auka akan Yusuf dan kuwa idan tayi wasa zai mata abinda batayi tsammani ba.

  Wayan ta ne ya fara ringing wanin number mummyn ta ne yasata d'auka da sauri
"Hello Mummy."
"Zo ki bud'e mun k'ofa."
Kawai ta kashe wayan.

Da sauri ta tashi taje ta bud'e runguman ta tayi tana yimata oyoyo.

  Cikin parlour suka shiga drinks ta kawo mata sannan suka gaisa.

"Husna nazo ne akan maganar ki ta jiya hankalin mahaifin ki ya tashi sosai shine ma yasani zuwa yanzu,
Husna me yake faruwa ne?" Ta tambaye ta cikin damuwa.

  Hawaye ne suka zu6o a idanun Husna sannan tace
"Mummy ina cikin matsala, ina cikin tashin hankali wallahi wannan Yusuf d'in ya takurawa rayuwa na yanzu haka kinga wannan wuk'ar da shi na koreshi Mummy wallahi kullum ina cikin far gaban abinda zai faru" ta k'arasa maganar cikin kuka.

  "Kinga Husna kiyi shiru kiyi hak'uri insha Allah zamuyi abinda ya kamata, yanzu abinda nake son sani shine mijin ki yasani?"

  "A'a Mummy bai sani ba."
"To kiyi k'ok'arin sanar da shi dan wannan ba k'aramin al'amari bane."
"Mummy bazai yarda ba, wallahi ya aminta da Yusuf dari bisa dari."
"Husna wannan ba k'aramin abu bane, ba abinda zamu zauna muna kallo bane dan haka kiyi k'ok'arin sanar da shi tun yanzu."

  "To Mummy insha Allah yau zan fad'a mishi duk abinda yake faruwa."
"To shikenan Allah ya taimaka."

  Bayan nan kuma suka danyi hiran su sannan mummy ta tafi.

  Tana tafiya ta sake saka key ta koma ciki dan gabatar da aikin abinci.

  Farooq kuwa tunda ya tafi office ya kasa komai sai faman tunani abinda yake ta tunani shine maganar da Yusuf ya fad'a mishi.

  K'arfe biyar yana cika ya tashi bayar wajen aikin dan bazai iya yin komai ba.

  Gidan su ya wuce dan gaida mahaifiyar sa.

  Yau kam yasamu kowa a gida sai faman hira suke a tsakanin su.

  Ganin Yayan nasu ne yasa su yin shiru dan kuwa tsoron shi suke.

Gaida shi sukayi sannan ko wacce ta bar parlour.

  Hajiya ce tace
"Farooq lafiya kuwa na ganka a wannan lokacin?
kuma  da alamum fuskan ka akwai damuwa."

  "Mama wallahi yau bana d'an jin dad'i ne shi yasa amman ba komai."

"To Allah ya sauwake,
Ya yanayin zaman Ku da Yusuf ina fatan ba abinda yake shiga tsakanin Ku dan nasan zaman tare dole wata rana za'a sa6a."

  "Lafiya k'alau Mama sai dai d'azo mun d'an samu matsala amman ba komai ya wuce."

"Farooq banason ka 6oyemun komai idan wani abin ne ka fad'a mun banason abinda zai dameka."

  "A'a Mama wallahi ba wani matsala bane."
"To nidai inajin a jikina kamar akwai abinda yake faruwa kuke 6oye mun."
"Wallahi Mama babu komai."
"To Allah yasa."
"Ameen Thumma Ameen"
Bayan nan kuma suka kama wani hiran.

  B'angaren Yusuf kuwa sabon Sim yaje ya siyo sannan ya dawo gida.

Part d'in Husna yazo amman sai ya tarar a rufe murmushi yayi sannan ya zagaya ta k'ofar baya.

  Ai kuwa yayi sa'a
bud'e yake hakan ne yasa shi shiga da sauri ya rufe.

  Ita kuwa Husna ta gama girki tana shirin shiga wanka,
Motsin mutum taji ta bayan ta juyawan da zatayi Yusuf tagani tsaye yana kallon ta.

  A tsorace take kallon shi.
Murmushi yayi sannan yace
"Kina mamakin gani nane masoyiya?
To kar kidamu ai ina tare da ke a ko wanne lokaci ."

  Wani kallo ta watsa mishi sannan tace
"Ai wannan kai ta dama, kuma daman ina Allah Allah kazo yau na nuna maka cewa har yanzu baka cika d'an iska ba, dan wallahi yanzu ba mai hanani yi.maka kaciyan da nayi niya in yaso sai naga da me zakayi iskan ci."

  "Yarinya ni kuma yau nake son na nuna miki cewa bakida wayo ko kad'an, kuma a yau sai nayi abinda yake rai na."

Wani mugun tsoro ne ya mamaye Husna dan kuwa tasan yanzu ma ba mai taimakon ta sai Allah, amman ta daure tace
"Yusuf kenan! ai ni bana soron wannan kuma ina tunanin zaka komawa Hafsat babu shi dan kuwa yankewa zanyi kowa ya huta."

  Kin kulata yayi sai ma matsowa yake kusada ita yana lashe harshe ai kuwa tana ganin haka ta fita da gudu bata tsaya a ko ina ba sai kitchen, biyota yayi yana dariya yana cewa
"Kina jin zaki tsere mun ne Husna?
Ko ina zaki shiga a gidan nan baki isa kice zaki gudu ban biki ba."

   Ai kuwa tana juyawa ta d'auki wuk'a ta tsare shi da shi sannan tace
"Ka tsaya a inda kake kar kasake ka motsa."

  Ai kuwa gani nayi Yusuf ya tsaya a waje d'aya kamar wani gunkiπŸ˜‚
(Ashe su Malam Yusuf ana tsoron πŸ”ͺ)

Matsowa ta farayi wajen shi yana ja da baya sai da yazo bakin k'ofa sannan yace
"Husna wallahi bazan cire wannan abin a rai na ba, kuma idan baki amince mun ba wallahi zan kashe Farooq kuma kema na lalata miki rayuwa sabon haka ki zabi d'aya ko mutuwar mijinki ko kuma nayi abinda nake so da ke"..........

  Ai kuwa bai k'arasa maganar da yake ba Husna tazo da gudu zata yake shi ya kauce shima  fita yayi da gudu ai kuwa a garin bud'e k'ofa sai da ta yanke shi a hannu sosai tana cewa
" shege maye wallahi kasake dawo wa sai na kashe ka." Ta k'arasa maganar tana kuka.

  Jinin da yake jikin wuk'ar da wanda ya dan d'iga kasa k'in gogewa tayi dan tanason Farooq yazo ya gani.

  Yusuf yana shiga part d'in shi kenan motar Farooq ya shigo.

  Kwankwasa k'ofar yake sosai amman Husna bata bud'e ba dan batayi tsammanin shi yanzu ba ta d'auka Yusuf d'in ne har yanzu.

  Wayan ta ya kira yace tazo ta bud'e mishi k'ofa.

  Da "To" ta amsa mishi sannan taje ta bud'e.

Tana bud'ewa ta rungume shi tana kuka tana fad'in
"Dan Allah ya Farooq ka d'auke ni a gidan nan Yusuf zai kashe dan Allah" ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka.

  Rike hannun ta yayi suka shiga parlour.

  Cikin rashin fahimta yace
"Husna meye yake faruwa please ki daure kimun bayani."

  Ai kuwa nan da nan Husna ta fad'awa Farooq duk abinda  yusuf yake mata har yanzu yau sukayi.

  Wani irin kukan kura Farooq yayi Wanda nan da nan ido nunsa suka koma ja jijiyoyin kanshi gaba d'aya suka bayyana.

Wani irin mik'ewa yayi Wanda bai tsaya a ko ina ba sai part d'in Yusuf.

    ​​​```WAYYO YAU MUN BANU ME FAROOQ ZAI AIKATAWA YUSUF?``` ​​​

  ​```AMSA YANA WAJEN KU MASU KARATU​```

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq*​  πŸ“š✍🏻

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

  πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

​DEDICATED TO MARYAM BINTU​

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι›n Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 56~60​*

Wani irin mik'ewa yayi Wanda bai tsaya a ko ina ba sai part d'in Yusuf.

Ko sallama baiyi ba ya shiga cikin gidan,  Hafsat tana zaune a parlour har ta tsorata dan batayi tsammanin mutum a yanzu haka ba.

  Mik'ewa tayi tana tambayan shi
"Ya Farooq lafiya?"
Kin kulata yayi ya wuce d'akin da yasan zai samu Yusuf.

  Ai kuwa yana shiga ya fad'a kanshi da duka yana cewa
"Yusuf ni zaka yaudara?
Duk amincewar da nayi da kai shine zakaci amana ta?" Yanda yaga Yusuf yayi shiru ne yasa shi tsayawa da dukan da yake mishi sai a lokacin Yusuf yace cikin k'aramar murya
"Farooq banta6a tsammanin akwai wacce zata shiga tsakanin mu ba, kuma banta6a tsammanin zaka saka hannu ka dake ni akan abin da ban aika shi ba" kuma sai ya fashe da kuka sannan yaci gaba da cewa
"Ko menene na maka kamata yayi ka tambaye ni kaji ko haka ko ba haka bane amman Farooq kana zuwa sai duka wanne irin abu nayi maka haka?
Husna bata son zaman mu a gidan nan dan haka bari yanzu zamu tashi mu bar maku gidan Ku."

  Jikin Farooq ne yayi sanyi dan shi gaba d'aya banyi wani tunanin tambayan Yusuf abinda ya faru ba ce mishi yayi
"Yusuf kayi hak'uri banyi tunanin tambayan ka ba dan gaba d'aya ido nuna sun rufe amman dan Allah kayi hak'uri,  kuma kana maganar barin gidan Husna gidan ta ne?
Ko ita ta sakaku?
Ban yarda ta bar gidan nan ba, amman ison ka fad'amun gaskiya magana."

  "Wallahi tun lokacin da kagabatar dani wajen Husna tun a lokacin nake cin karo a wasu abubuwan da ban gane mata ba, amman ni nasan mutun cin kai na kuma bazan iya cin amanar ka ba, kai aminina ne meyesa zan ci amanar ka?
Yau kuma dalilin da yasa na shiga gidan na dawo a hospital kenan sai ga Husna ta fito tace mun wai kad'angare ya shiga mata parlour naje na cire mata shine ina shiga ta rufe k'ofa wai sai nabiya mata buk'ata."

  Rintse idon shi Farooq yayi sannan ya bud'e idon yayi jajerr kamar jar gauta sannan yace
"Ni Husna zata ci amana!
Husna ta rasa Wanda zata nema sai ABOKINA?
Kuma bayan nan tayi mishi k'azafin zina!
Wallahi Husna sai kinsan kinyi wannan abin sai na foraki."
Ya k'arasa maganar cikin wani irin yanayi sannan ya tashi ya fita.

  Wani mugun murmushi Yusuf yayi sannan yace
"Banza wawa wallahi sai na rabaku sai na bata rayuwar Ku" ya k'arasa yana dariyar mugun ta.

   Husna kuwa tunda ya fita take tunanin abinda zai faru dan ita tsoro take ji kar Yusuf yajiwa Farooq ciwo shigowar shine ya katse mata tunanin ta.

  Shigowa yayi yana cewa
"Ke Husna ni zaki yaudara?
Husna aminina Yusuf kike nema?
Husna kin cuci kanki kuma wallahi sai kinsan kinyi wannan abin.".....

  Katse shi tayi da cewa
" Ya Farooq meye ya far"....…

Katseta yayi da wata lafiyyar mari Wanda yasa taga walk'iya sannan yace
"Rufe mun baki munafuka ashe duk wannan abinda kike mun munafurci ne to wallahi sai kinyi da nasani munafukar banza,
Kuma bazaki ta6a rabani a aminina ba."
Ya wuce ya shiga d'akin shi.

  Durk'usawa tayi a wajen ta fara kuka sosai dan kuwa yanzu ba mai cireta a cikin wannan masifar sai Allah.

  Har K'arfe goma na dare Farooq bai fito cin abinci ba hakan ne yasa Husna shiga d'akin dan ya fito ya ci abinci.

  Sallama tayi ta shiga amman ina bai amsa mata ba duk da haka bai dameta  ba ta durkusa tace
"Ya Farooq kayi hak'uri ka fito kaci abinci."

  Ko kallon ta baiyi ba bare samun wani amsa ta kusan minti biyar a haka wani wawan tsawa ya daka mata wanda sai da yasata zama gaba d'aya sannan yace
"Ki tashi kibar mun d'aki idan kuma ba haka ba wallahi zaki fuskanci fushi na."

  Kuka ta fara tana cewa
"Haba ya Farooq meyesa bazaka yarda da ni ba?
Meye sa zaka amince da maganar Yusuf?
Wallahi karya ya fad'a mak.".......

  Katseta yayi da cewa
" ke Husna ki rufe mun bakin ki wallahi idan ba haka ba zan sa6a miki yanzu anan,
Kinyiwa Yusuf k'azafin zina shine kike so na yarda?
Husna banyi tsammanin zakici amana ta ba saboda haka ki tashi kiban waje bana son ganin ki" ya k'arasa maganar cikin tsawa.

  Mik'ewa tayi ta fita da gudu tana kuka mai cin rai.

  Shi kanshi Farooq baya son kukan ta amman idan ya tuna maganar Yusuf sai yaji kuma ya tsaneta.

  Gaba d'ayan su kwana sukayi basuyi barci ba musamman Husna wacce duk abin duniya ya ashe ta.

  Washe gari da sassafe ta fito ta gama breakfast dan kuwa yau da wuri Farooq zai fita.

  Ta gama komai ta gyara gidan ta ko ina fess sannan taje tayi wanka ta shirya sannan ta wuce d'akin shi.

  Tana yin sallama ya dakatar da ita da cewa
"Ke kidakata kar ki kuskura ki shigo mun cikin d'aki kinji na fad'a miki."

  Batayi magana ba ta juya ta bar mishi d'akin hawaye yana bin fuskan ta.

  Parlour ta koma ta zauna tana tunanin wannan rayuwar da kuma ta fad'a.

  Fito yayi cikin wata T-shirt blue da black d'in wando Wanda ya amshi jikin sa sosai ko kallon inda take baiyi ba ya wuce,
Ya bud'e k'ofa zai fita tayi sauri tace
"Ya Farooq ga breakfast d'in ka fa."

Ko kallon ta baiyi ba ya wuce ya fita a gidan.

Wani irin kuka ta saka ta fad'i..........

```​​​Kuyi hak'uri da wannan ba yawa please``` ​​​

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq*​πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA* πŸ™†πŸ»πŸ˜­

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ*​πŸ“š✍🏻

​```DEDICATED TO MY FANS, no need for long essay you know​ ​iπŸ’”youπŸ’― one love πŸ’žana mugun tare irin totally d'in nan ``` πŸ˜πŸ’žπŸ’”❤

*Masoya na naga sak'onin Ku kuma naji dad'i k'warai da gaske musamman wad'an da suka kira ni dan jin lafiya da wad'an da suka min text nagode matuk'a kuma ban barku a baya ba masu bina pc da masu nemana a groups suna tambaya lafiya nagode nagode k'warai kuma naji dad'in hakan nima yinku 😍 ina sonki ❤irin sosai d'in nan*πŸ‘„πŸ‘„πŸ’‹πŸ’‹πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’˜πŸ’˜

Follow me on wattpad @momyn Musaddiq830

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 61~65*

Wani irin kuka ta saka ta fad'i tana fad'in
"Wallahi Ya Farooq karya Yusuf ya fad'a maka meyesa zaka yarda da karyan." Kukan ne ya hanata k'arasa maganar ta.

   Shi kuwa Farooq ya rasa me yake mishi dad'i dan gaba d'aya jin shi yake wani iri dan baya son kukan Husna.

  B'angaren Yusuf kuwa farin ciki ne fal a fuskan shi dan kuwa tarkon shi ya kusan kamawa.

  Wayan shi ya d'auko da wannan Sim d'in da ya siya ya canza sabon Sim d'in sannan ya fara kiran wayan Husna.

  Tana zaune a inda take tana tunanin yanda rayuwar ta ya koma taji wayan ta tana ringing da sauri ta d'auko amman sai taga bak'on number har ya katse bata d'auka ba sai da yayi 5 missed call sannan ta d'auka.

  Muryan Yusuf da taji ne yasata danna recording sannan ya fara cewa
"Haba Husna bantaba tsammanin zaki mun haka ba, yanzu akan wannan banzan Farooq d'in shine duk kika shiga wannan rayuwar?
To wallahi idan baki amince mun ba sai kinshiga Wanda yafi haka,
Kuma ina mai tabbatar miki sai na kashe Farooq wallahi wannan alk'awari ne na d'auka."

  Wani wawan tsaki ta ka mishi ta tashe wayan.

  A fusace Yusuf ya mik'e yana cewa
"Lalle yarinyar nan ki raina ni wallahi yau sai nayi maganin ki." Mik'ewa yayi ya nufi part d'in ta.

  Yana shiga kuwa yayi sa'a a bud'e take hakan ne ya bashi daman shiga ciki.

Ita kuwa Husna tana ajiye wayar barci yayi gaba da ita.

  Shi kuwa Farooq har yayi nisa ya tuna yabar wasu takaddu a gida hakan ne yasa shi guyawa ya dawo.

Yusuf kuwa yana shiga parlour ya saka key sannan ya tunkaro inda yaga Husna kwance.

  Tsayawa yayi a kanta yana kare mata kallo sannan yasa hannu ya fara shafar fuskan ta.

  Kamar a mafarki taji ana ta6ata ai kuwa tana bud'e ido taga Yusuf zaune a kusa da ita wani wawan ihu ta saka sannan ta mik'e da niyar gudu amman ina ba dama ya riga da ya kamata.

  Wani wawan cizo ta saka masa Wanda yasa shi ihu amman duk da haka yaki sakin ta.

  Marin ta yayi sannan yace mata cikin fad'a
"Ke Husna idan yau baki amince mun ba wallahi sai na kashe Farooq a yau kuma na kashe mahaifin ki da mahaifiyar Farooq gaba d'ayan su" yana fad'an haka yayi dai-dai da shigowar Farooq yana tsaye a k'ofa yana jinshi.

  Wani irin abu yaji ya ziyarci zuciyar shi dan bai ta6a tsammanin Yusuf zai ci amanar shi ashe gaskiya Husna take fad'a mashi.......
Maganar Yusuf d'in ne ya katse shi da cewa
"Ai yau gaki a hannu na sai yanda nayi da ke saboda haka gara ki nutsu dan kuwa ba mai ceton ki.....jin yayi ana k'ok'arin bud'e k'ofar parlourn hakan ne yasa shi jan Husna cikin d'akin ai ina Farooq da yaji ihun Husna yayi yawa ai tuni ya rikice ta k'ofar baya ya shiga dan gaba d'aya ya fita a hayyacin shi.

  Hmmmm nida nake gefe nace " ran maza ya 6aci."

  Da gudu ya shiga cikin gidan amman har Yusuf ya shiga da ita cikin d'aki yana k'ok'arin cire mata kayan jikin ta.

  Wani irin wawan shak'a Farooq yayiwa Yusuf Wanda sai da numfashin sa ya d'auke na d'an wasu seconds sannan suka dawo.

  Ai kuwa Farooq wani irin duka yake ma  Yusuf dan gaba d'aya idon shi ya rufe duka yake mishi  ta ko ina baya ji baya gani kawai dukan shi yake.

Ita kuwa Husna wacce tasha wuya a wajen Yusuf a gefe ta zauna tana maida numfashi dan kuwa ba k'aramin wahala tasha ba.

  Gaba d'aya Yusuf ya fita a hayyacin sa saboda dukan da Farooq yake mishi duk ya farfasa mishi jikin sa duk ya gala baita.

  Husna ce ta tashi tana bawa Farooq hak'uri akan ya barshi amman ina Farooq baya jin komai.

  Ganin yana ji mishi ciwo kamar Wanda zai kashe shi hakan ne yasa ta kira Hajiya Aisha a waya akan tazo Yau ba lafiya a gida.

  Hajiya Aisha ta rikice gaba ki d'aya dan abinda bata ta6a jiba kenan tsakanin Farooq da Yusuf amman sai gashi yau sune suke fad'a koma menene wannan babban abu ne shine kawai abinda ta fad'a.

  Koda taje gidan Farooq baya hayyacin shi dan kana ganin shi kamar Wanda kanshi ya ta6u.

  Hajiya da Adamu driver ne suka k'arasa inda suke da sauri dak'yar Adamu ya kwace Yusuf a hannun Farooq.

  Hajiya ce ta rik'e Farooq tana cewa
"Farooq meye yak'e damun ka?
Bakada hankali ne kake mishi irin wannan dukan?"

  Farooq ya fara magana cikin wani irin murya da bai ta6ayin irin ta ba, yace
"Yusuf ni zakaci amana?
Na amince da kai Dari bisa Dari amman k'arasa da me zaka saka mun sai da neman mata ta?
Kama bayan hakan nasani na zalunci baiwar Allah da batasan komai ba wallahi Yusuf kacuce ni."
  Wani irin kuka ne ya kufce mishi.

Hajiya dai batasan meye ya faru ba dan gaba d'aya kalaman Farooq sun rikita ta.

  Yusuf dai yana jikin Adamu driver dan kuwa yasha duka sosai ba daman magana.

  Hajiya ce tace
"Kai Farooq yanzu ba wannan ba Ka tashi mu kai Yusuf hospital dan kuwa yana jin jiki."

  Wani irin kallo yayiwa Hajiya sannan yace
"Mama ina ma ace yanzu naga mutuwa tazo tace idan ban kaishi hospital ba zata d'auke shi wallahi Mama sai dai ta d'auke shi daga baya sai nima a kashe ni amman wallahi kunji na rantse bazan kaishi ko ina ba!
Kuma wallahi Mama ko ke ban yarda ki kaishi ba,
Saboda ba son mu suke ba Mama".…......
Kuka ne ya kufce mishi yayi shiru bai k'arasa maganar ba.

  Hajiya dai ta rasa bakin magana dan bata ta6a jin wad'an nan kalaman a bakin Farooq ba.

```Kuyi hak'uri da wannan ba yawa```

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ˜­πŸ™†πŸ» *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​πŸ“š✍🏻

*​DEDICATED TO MY FANS​*

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 66~70​*

"Wai kai Farooq bakada hankali ne kake fad'a mun wad'an nan maganganun?
Ko kamanta wanene Yusuf kake fad'an haka akan shi."

  "Mama ni nasan Yusuf kuma nine sanadin komawar shi haka amman ya rasa da me zai saka mun Mama sai da Neman mata ta!"

  Wani irin zabura  Hajiya Aisha tayi tana kallon su dan maganar ba k'aramin razata yayi ba sannan tace
"Subhallahi!
Farooq me kake fad'a ne nifa har yanzu ban gane ba."

  "Mama ba yanzu ya kamata muyi wannan maganar ba sai kowa da kowa an had'u yanzu zanje gidan su Husna na d'auko iyayen ta dan kuwa abin har su ya shafa Mama."

  "Too Farooq amman ai koma menene sai ansamu Yusuf ya dawo hayyacin sa dan kuwa yanzu komai za'ayi baya hayyacin sa."

  "Wannan dai shi yasani sai dai mahaifiyar sa tazo takai shi hospital amman dai ba tawa uwar ba."

  "To wai ina ita Hafsat ne ko batasan me yake faruwa ba?"

  Sai a lokacin Husna tayi magana tace
"Mama Husna bata nan ta tafi awu."

  "To yanzu dai Farooq hak'uri zakayi mukai shi dan kowa yana Neman taimaka."

  "A'a Mama banaso!
Bana son duk wani abu da zai taimakawa Yusuf."

  Haka sukayi tayi da Hajiya Aisha dak'yar ta samu ya amince amman hakan ma da sharad'in ba shine zai kai suba kuma ba driver ba sai dai su hau napep dan bashi ya siya mishi motar ba.

  Haka kuwa suka d'au shatar napep har zuwa wani k'aramin hospital Wanda yake kusa da unguwar su.

  Magunguna aka bashi sai kuma aka mishi allura guda biyu sannan suka dawo gida.

  Koda suka dawo yaji saukin jikin sa dan yanzu baya jin ciwon da d'azu yake jin shi.

  Shi kuwa Farooq suna fita yasa Isyaku ya tattara komai da yake na Yusuf ne yakai mishi gidan shi baya son ganin su a gidan shi.

  Komawa part d'in shi yayi ya sami Husna zaune tana kuka wani sabon sonta ne ya lullu6e shi da tausayin ta dan har baya son ya tuna irin abinda ya mata tsakanin jiya da yau.

  K'arasowa yayi wajen ta jiki a sanyaye sannan ya zauna ya zuba mata ido cikin dashashiyar murya yace
"My Angle dan Allah kiyafe mun wall".........katse shi tayi da cewa
" A'a Ya Farooq dan Allah karka rok'eni akan abinda kamun, nasan cewa duk laifi nane da ban sanar da kai abubuwan da yake faruw.".......
Shima katseta yayi da cewa
"A'a Husna karki d'aurawa kanki laifin da ba naki ba,
Kinyi k'ok'arin fahimtar da ni amman na nuna miki  ba haka ba dan Allah kiyi hak'uri da abinda nayi miki abin takaici ma shine nasa hannu na mare ki Husna."
Sai kuma ya fashe da kuka yana jin wani irin abu yana ziyartar zuciyar shi da kuma tunanin abinda ya kamata ya kara yiwa Yusuf dan ba wannan kad'ai ya kamata yayi mishi ba.

  B'angaren Yusuf kuwa Hajiya Aisha gidan ta ta wuce da shi sai da yasamu yayi wanka sannan yace mata zaije ya dawo.

  Ce mishi tayi
"A'a Yusuf daman yanzu ma kawai dalilin da yasa na kawo ka gidana,
Ina son ka fad'a mun gaskiyar abinda ya had'a ka da Abokin ka?"

  Wani kallon raini ya watsa mata sannan yace
"Meyesa bazaki tambayi d'an naki ba sai ni?
To bazan fad'a ba idan kin damu.ki koma gidan nashi ya fad'a miki" yana k'arasa fad'ar haka ya ja mata tsaki ya fita.

  Hajiya Aisha baki bud'e ta bishi da kallo dan bata ta6a tsammanin irin wannan rashin kunyar a wajen Yusuf ba.

YΓ n fita gidan su ya shiga a kan taburma ya sami Inna zaune tana tsintar shinkafa ko sallama baiyi ba ya shiga.

  A tsorace ta mik'e tana cewa
"Subhallahi!
Yusufu me yaji maka ciwo haka a jikin ka?"ba rashin sallaman shi bane ya dame ta.

  "Inna wallahi zan fara kisa a cikin garin nan,
Inna kiga abinda wannan matsiyacin Farooq yamin!
To wallahi Inna duk abinda ya same shi shiyajawa kan shi."

  "A garin yaya yaji kama irin wannan raunin naga fa duk jikin ka ya kunbura?"

"Wai Inna akan nace inason matar shi ai naga matar ba dan shi kad'ai akayi ta ba."

  Ai kuwa Inna Habiba mik'ewa tayi tafara zuba masifa
"Ai wannan zance banza ne kuma wallahi bazan yarda akan wannan abin a jiwa d'ana ciwo ba,  dan yace yana sonta dan meyesa shi Farooqun bazai saka ka aura ba?
Zancen banza da na wufi" ta k'arasa maganar cikin masifa.

  "Inna ki bari kawai goyon bayan ki nake buk'ata idan kin amince mun da nayi komai shikenan ni burina ya cika."

  "Na amince Yusuf kuma Allah yayi maka albarka ai banga dalilin da zaisa ayi maka irin wannan dan banzan dukan ba."

  ​​​```(Nida nake gefe nace
"Ashe komai da Yusuf yake ba laifin shi bane")​​​```

   Anan duk ta fad'a mishi irin abubuwan da ya kamata yayi dan wannan ba abin wasa bane.

  Hajiya Aisha ce ta kira Farooq a waya tace sazo tare da Husna tana son magana da su.

  Nan da nan suka amsa kiran ta dan basa wasa da kiran Iyayen su.

  Suna fita sai ga Yusuf shima ya shiga Isyaku ne ya k'arasa inda yake yace mishi
" kayi hak'uri Ogana yace kar nabarka kashiga cikin gida,
Kuma duk wani kayan Ku an mayar muku dashi gidan ku. "

  Wani irin kallo ya watsawa Isyaku sannan yace
"Ka bud'e mun gate nace idan kuma ba yanzu zan fito nayi maganin ka."

  "Gaskiya sai dai kayi hak'uri saboda maganar Ogana zanbi."

  Ai kuwa Yusuf yana jin haka ya fito a cikin motar ya fara nausar Isyaku,
Nan da nan suka fara dukan junan su,
Ai daman Isyaku kamar nema yake suka yayiwa Yusuf sosai dan kuwa har fasa mishi hanci yayi.

  Haka Yusuf yaja motar shi da gudu yabar k'ofar gidan.

```​​​Kuyi hak'uri da wannan wallahi yanzu haka kaina ciwo yake dan kar kuce banyi muku ba shi yasa nayi muku.​​​```

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

A parlour suka samu Hajiya zaune tayi tagumi tamkar wacce aka aiko  mata da mutuwa,
Sallaman su ne ya dawo da ita daga tunanin da take.

  Amsa masu tayi cikin sanyin murya sannan suka k'araso.

  Farooq ne yace
"Mama lafiya kika mana k'iran gaggawa?"

  Kallon shi tayi sannan tace
"Farooq inason Ka fad'a mun gaskiyar abinda ya had'a ka da Yusuf?"

  Kallon ta yayi sannan yace
"Mama kamar yanda kika ji d'azu na fad'a Yusuf neman Husna yake da fasik'anci, kuma bayan haka Mama sai yace mun Husna ce take neman sa".........

Haka dai duk yabata labarin abinda ya sani.

  Ajiyar zuci Hajiya tayi sannan tace
" Husna meyesa duk wannan abinda ya faru baki sanar da mu ba?"

  "Mama nayi k'ok'arin sanar da ya Farooq amman sai ya nuna mun ba haka ba hakan ne yasa nayi shiru ban sake maganar ba amman na fad'ama Mummyna tasan komai duk abinda yake faruwa tasani."

  "To Alhamdulillah daman haka nake son ji dan kuwa wannan ba k'aramin al'amari bane ace Aminin mijinka yana Neman ka ai kuwa abun sai addu'a,
Kai kuma Farooq kayi wauta bai kamata ka sakewa Yusuf haka ba,
Kuma lokacin da Husna take k'ok'arin sanar da kai ai da Ka tsaya ka saurareta dan kuwa zaman aure ba abin wasa bane, bare kuma Neman aure ciki aure kaga wannan babban abu ne."

  "Haka ne Mama lokacin ido na ya rufe bana ganin laifin Yusuf ko kad'an,
Amman yanzu nayi nadamar hakan kuma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba."

  "To shikenan amman a yanda naga Yusuf yabar gidan nan kamar a fusace ya fita dan nima sai da ya fad'a mun magana."

  Cikin zafin nama Farooq ya d'aga kai yana kallon Hajiya sannan yace
"Mama me Yusuf ya fad'a miki?"

Murmushi tayi tace
"Hmmm Farooq kenan ka barshi kawai yarinta ce irin ta Yusuf shi yasa ya fad'a mun amman ba komai kar Ka d'auki abin da wani manufa."

  "Mama wallahi sai na nunawa Yusuf shi ba komai bane,
Mama har Yusuf zai bud'e baki ya fad'a miki magana?
Lallai akwai tashin hankali,
Ke Husna ki zauna a nan zanje na dawo na d'auke ki kar ki sake ki fita ke kad'ai, dan yanzu ke rayuwar ki yana cikin barazanar Yusuf."

  Hajiya ce tace
"A'a Farooq ban yarda kaje kana tashin hankali da Yusuf ba, duk da shi bai d'auke mu a bakin komai ba to mu mu d'auke shi."

  Kafin Farooq yayi magana Husna tace
"A'a ya Farooq wallahi Yusuf yayi alk'awarin kashe ka dan Allah kar kafita ka tunkare shi dan kuwa nasan a shirye yake" ta k'arasa maganar cikin kuka.

  Wani irin kallo Farooq yayi Wanda ban ta6a ganin yayi irin ta ba sannan yace
"Husna Yusuf ne yace miki zai kashe ni?"

  Alamu tai mishi da kai sannan tace
"A lokacin da Yusuf ya kirani a waya yake fad'a mun nayi recording duk abinda yake fad'a bari na kunnah muku kuji."

  Hajiya Aisha kam suman zaune tayi dan bata ta6a tsammanin Yusuf zai musu haka ba bare ma akan mace.

  Ai kuwa Husna ta Kuna musu wannan d'aukan duk abinda Yusuf ya fad'a mata duk sunji.

  Wani abu ne yazo ya bugi zuciyar Farooq Wanda yasa shi mik'ewa ba shiri,
yana shirin fita suka jiwo muryan Habiba daga waje tana ta faman zuba masifa.

  Hajiya ce tace da Farooq
"Farooq ban yarda kayiwa matar nan magana ba kawai ka fita kayi tafiyar ka."

  Ido nunsa gaba d'aya sunyi ja cikin wani irin murya yace
"Haba Mama so kike wad'an nan mutane su kashe mune kamar yanda suka fad'a?
Dan meyesa zakice nayi shiru akan kuma mu akan cuta?
Haba Mama abinda suke mana yayi yawa gaskiya,
Ko wannan shine saka mak'on halaccin da muka musu?" Sai kuma ya kasa k'arasa maganar dan har Habiba ta shiga cikin parlour.

  "To sannun Ku munafukai to ta Allah ba taku ba!
Kunso kashe mu d'a Allah bai nufa ba sai kuma kubi ta wata hanyar dan kuwa Yusufu yafi karfin ku wallah"........
  Dakata Malama ki mana shiru,
Ku har kunada abinda zaisa mu kashe ku?
To Baku isa ba idan kuma wannan shine saka makon halaccin da muka muku to kuje mun gode."

  "Kai Farooq ni kake fadawa haka?
To bari kaji ko uwar Aisha bata isa ta fad'a mun haka na k'yaleta ba bare kuma kai dan cikina."

  Hajiya kam rasa bakin magana tayi dan bata ta6a tsammanin Habiba zata fad'a mata irin wannan maganganun ko a bayan idon ta, amman sai gashi a gaban idon ta, a gaban Sirikar ta take fad'a mata.

  Bak'in ciki ne ya ishi Farooq hakan ne yasa shi fita yabar gidan gaba d'aya idan kuwa ya tsaya zaiyiwa Habiba ba dad'i.

  Bayan ya fita ne ta kalli Husna tace
"Ke kuma munafuka wacce batasan ciwon kanta ba, har Yusuf zai nuna yana sonki kik'i?
To ina mai tabbatar miki kina cikin wahala har karshen rayuwar ki." Tana fad'an haka tafita tabar gidan.

  B'angaren Yusuf kuwa gidan shi ya koma yaje tayi wanka ya canza kayan shi sannan ya d'auki key d'in motar shi ya fita dan kuwa yau bazai bar Farooq ba.

  Ai kuwa Yusuf sake komawa yayi gidan Farooq amman sai ya tsaya a bak'in gate dan ya tabbatar idan ba a gidan ba bazai same shi ba.

  Bai dad'e da zuwa ba sai ga motar Farooq ta tafo tamkar wanda yake tseren gudu bud'e mishi gate Isyaku yayi ai kuwa Yusuf da gudu shima ya shigo dan yabar motar a waje.

  Farooq yana fitowa kawai yaji an rik'e shi ta baya ana dukan shi.

Ai kuwa Yusuf dukan Farooq yake dan kuwa ya shak'e mishi wuya sosai yayi yayi ya k'wace ya kasa ai gani nayi Yusuf ya zaro wata sabuwar wuk'a yana k'ok'arin yank.........

  ​​​```Tur kashi! Yusuf me yake k'ok'arin yiwa Farooq ne``` ​​​πŸ€”

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ™†πŸ»πŸ˜­ *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ​*πŸ“š✍🏻

*DEDICATED TO MY FANS*

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 76~80*

Gani nayi Yusuf ya zaro wuk'a yana k'ok'arin yankewa Farooq mak'ok'oro.

Isyaku ne ya k'araso wajen su da gudu ganin abinda Yusuf yake shirin aikatawa mai gidan shi,
Wani k'aton itace Isyaku ya d'auko ya k'wad'awa Yusuf a baya wanda sai da yasa shi ihu sannan ya sake Farooq ya jefar wuk'an da yake hannun shi.

  Sai a lokacin Farooq ya samu hankali sannan shima ya shak'e shi yana fad'in
"Yusuf kashe ni zakayi?
Yusuf ni Farooq kake shirin yankawa?
Wannan shine abinda zaka saka mun?
To Wallahi baka isaba sai dai ni naga bayan ka tunda kai ba d'an halak bane."

  Isyaku ne yazo ya fara k'ok'arin rabasu amman ina ya kasa saboda Farooq ba k'aramin shaka yayiwa Yusuf d'in ba.

  Shi kuwa Yusuf yaji mutuwa sai faman zare ido yake sannan cikin dashasshiyar murya yace
"Dan Allah Farooq ka yafeni na tuba kabar mun wuya na Zan mutu."

  Shi Farooq abin ma dariya ya bashi sannan yace
"Kai Yusuf kar ka raina mun hankali ni ba yaro k'arami bane, kuma kar kayi tsammanin yanzu ina tausayin ka, na tsaneka Yusuf na tsani mai son ka, wallahi nida kai har abada bazamu sake had'a hanya d'aya ba."

  "Dan Allah Farooq ka sakeni na daina daga Yau."

  Murmushi Farooq yayi yace
"Kaci albarkacin kira mun Allah da kayi na" sannan ya sake shi.

  "To bari kaji wallahi yanda nadau alwashin sai na kashe wallahi ba abinda zai hanani" Yusuf ne ya fad'a hakan bayan Farooq ya sake shi.

  Isyaku da yake gefe tsaye yana kallon ikon Allah sannan yace
"Yusuf kanada hankali kuwa?
Ko kasan irin kalaman da suke fita a bakin ka?
To kayi gaggawan".........
Yusuf ya katse shi da cewa
" kai dallah Malam kamun shiru munafuki kai ma bazan barka ba tunda naga bakin ku d'aya, kuma ina mai tabbatar maka kai ma sai naga bayan ka."

  Yana fad'an haka ya fita yabar su baki bud'e dan shi Farooq gaba d'aya ya kasa yarda Yusuf ne yake mishi wannan abin.

  Isyaku ne ya matso inda Farooq yake tsaye yace
"Yallabai gaskiya wannan al'amari na Yusuf abin tsoro ne, nidai a ganina ka kaishi police station zaifi maka kwanciyar hankali duk da bansan me ya had'a Ku ba, amman kuwa tabbas yana k'ok'arin d'aukan ranka."

  Ajiyar zuci Farooq yayi sannan yace
"Isyaku gaskiya nima wannan al'amarin Yusuf ya fara bani tsoro amman insha Allah bazaiyi nasara akan mu ka kwanta da hankalin ka ba abinda zai faru."

  "To Allah yasa amman kuwa wannan ba d'an albarka ba ne."

  Haka dai suka d'an tattauna sannan Farooq ya fita yabar gidan.

  B'angaren Yusuf kuwa yana fita motar shi ya shiga waya ya d'auka ya kira Hafsat.
"Ke kina ina ne?" Ya tambaye ta.
"Ina gidan mu amman yanzu zan dawo, wani abu ne?"
"Yauwa to ki zauna kar ki dawo sai na nemeki dan yanzu bana buk'atar ganin ki."
"Ban gane me kake nufi ba Yusuf."
"Eh abinda kikaji na fad'a miki shine abinda nake nufi." Yana gama fad'an haka ya kashe wayar sa bai tsaya a ko ina ba sai gidan Inna.

  Tana zaune a bakin kitchen nata da alamun dai abinci take da fawa.

  Shigowa yayi yana ta faman  masifa,
Habiba ce tace
"D'an albarka waye kuma ya sake ta6a mun kai?"
"Inna ki bari kawai ai da yanzu zakiji labarin nayiwa Farooq yankan rago."
"Yusufu yankan rago fa kace!
Baka tsoron wani abu ya biyo baya?"
"Inna abinda zai biyo baya ya wuce azo a kamamu ni da ke da Baba muma a kashe mu."

  Zare ido Inna tayi tace
"Dan jakar uba daman abinda kake son kayi duk dan mu mutu ne?
To wallahi sai dai a kashe kai da Uban ka amman nikam wallahi basu isa ba."
"To Inna kinata masifa ai ban mishi yankan ba."
"To nidai shawaran da zan baka kar kasake kayi wani abin a gaban mutane kasan su da gulma."
"Eh Inna amman wannan banzan Isyaku yasani shima Inna bazan barshi ba."
"Yayi kyau duk kayi maganin su dan kuwa ba mutunci gare su ba."
  Mahaifin Yusuf ne ya shigo da sallaman shi amman me ba Wanda ya amsa mishi sai ma tsakin da Habiba tayi mishi.

Bai kula su ba ya shige d'akin sa danshi gaba d'aya baya shiga harkar su.

  A nan dai Habiba duk tabawa Yusuf muna nan shawarar warinta sai da aka kira sallah magriba sannan yayi mata sallama ya tafi.

  Farooq baizo gidan Hajiya ba sai da yayi sallah isha'i sannan yazo d'aukan Husna.

   Gaba d'aya su ya samu zaune a parlour  tare dasu maryam da Khadija,
Sallama yayi musu suka amsa sannan ya shigo ya zauna.

  Hajiya ce tace
"Farooq ina fatan wani abu bai faru ba?"

  "Mama ai da yanzu har ankaini makwanci na."

  "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!
Farooq meye ya faru haka?"

  Ai kuwa nan da nan ya basu labarin abinda ya faru har yanda akayi Isyaku ta taimaka shi.

  Ita kam Hajiya kuka ta fara dan bata ta6a ganin irin wannan masifar ba, ace mutum da matar sa amman wani yana Neman k'wace masa har yana neman d'aukan ran shi.

  Husna tace
"Ya Farooq gaskiya ni ina tsoron komawa gidan can kabar ni anan kawai kuma kai ma ka dawo nan da zama."

   Kallon ta yayi sannan yace
"Husna kenan kina son munana masa muna jin tsoron sa tu yanzu?
Kinga komai zaiyi wallahi sai na tanka masa kuma bazan ta6a barin sa yaci galaba akan mu ba, saboda haka d'auki hijabin ki mu tafi."

  Khadija ce tace
"Yaya lalle Yusuf ya d'auko ruwan dafa kanshi dan wallahi bazan barshi ba."

  "To naji kubari sai gobe na dawo mu tattauna dan yanzu dare yayi."

  Bayan sukayi sallama suka fita.

  Ashe suna fita Yusuf yana la6e yana jiran su.

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ™†πŸ»πŸ˜­ *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

​```DEDICATED TO DEE​``` πŸ’˜
```​​​Ina kike surukata DeeπŸ’˜wannan page d'in gaba d'aya shi naki ne nabaki shi kyauta​​​```

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 81~85​*

  Suna cikin tafiya sukaga motar Yusuf tana binsu a baya.

  Farooq bai damu ba sai ma wani murmushi da yayi dan daman yasan so sake had'uwa.

  Ai kuwa tafiya suke Yusuf yana binsu har sai da suka isa gida sannan ya tsaya.

  Suna shiga Farooq yace da Husna ta shiga cikin gida yana zuwa.

  Kallon shi tayi cikin jin tsoro sannan tace
"A'a ya Farooq dan Allah kabar shi Ka dawo ni wallahi tsoro nake ji."
"Kinga Husna kibar jin tsoron Yusuf shi ba komai bane  ni d'in nan zanyi maganin shi dan naga idan na tsaya wasa tsaf zai kashe mu." Yana gama fad'an haka ya jiya ya fita ya barta tsaye jiki yana rawa.

  Yana fita ya ganshi tsaye kamar wani sabon mahaukaci dan irin shigar da yayi abin dariya ce amman da yake shima Farooq d'an kansane sai yasha kunu ya k'arasa inda yake.

  "Meye ya kawo ka gida na?
Ko yanzu ma kabiyo ni ne dan ka kashe ni?
To bari kaji kai da mahaifiyar ka karya kuke Kice zakuga bayan mu dan munfi karfin Ku, kuma naga alamun itace ta goya maka baya kake abinda kaga da"........
Katse shi yayi da cewa
" kai ka dakata ka saurareni dan ni ba wannan ya kawo ni ba,
Nazo dan nabaka wasu kwana ki idan har baka sake ta ba to wallahi Farooq zakayi mutuwar da ko sutura bazaka samu ba".....…
Marin da Farooq ya kai mishi ne ya hanashi k'arasa maganar shi bai ankara ba yasake jin wani marin sannan Farooq yace
"Kai naga alamun d'an mahaukaciya ne Wanda tuntuni bamu sani ba sai yanzu,
To bari kaji na fad'a kama Husna ce ko? to wallahi nida ita har abada ba wanda ya isa ya rabamu, kuma wallahi kayi gaggawan barin k'ofar gidan nan tunda ba na tsohon kaba ne" ya k'arasa maganar yana nuna mishi hanya.

  Cikin jin zafin maganar da Farooq ya fad'a mishi yace
"To shikenan wallahi nan da sati d'aya idan baka saki Husna ba wallahi kai da ita dama Uwar taka wallahi bazan barku ba,
Kuma da kake cewa ni d'an mahaukaciya ne kwarai kuwa dan yanzu ka ganewa idon ka."
Yana gama fad'an haka ya shiga motar sa ya tafi.

  Isyaku da duk yaji abinda suke fad'a ne ya k'araso inda Farooq yake yace
"Yallabai nidai wannan al'amarin Yusuf ya fara bani tsoro kuma fa akan matar ka ce!
Gaskiya wannan sai kunje kotu dan ba k'aramin abu bane."

  "Isyaku ni kaina al'amarin Yusuf ya fara isata amman inason na nuna masa ni ba sa'an sa bane, kuma idan ni ban nuna masa nafishi haukaba zai mun abinda yafi haka, shiyasa nake so nima na nuna masa nawa halin."

   "Kuma fa haka ne Yallabai, kaga fa d'azu da yazo na hanashi shiga wallahi sai da mukayi fad'a da shi."
"Sai hak'uri Isyaku mutane ne kowa da halin shi."
Yana gama fad'an haka ya shiga cikin gida yabar Isyaku yana mamakin wannan abin.

  Washe gari haka suka wuni kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa,
Musamman Yusuf wanda yanzu haka shirye-shiryen kashe Farooq yake.

  Ita kuwa Husna kuka kawai take dan gaba d'aya ji take itace ta jawo wannan masifar ga kuma wani masifaffan zazzabi da ya zuba mata.

  Farooq yayi-yayi su tafi hospital amman firr Husna taki dan yanzu ita ji take ta tsani komai.

*​BAYAN SATI D'AYA​*

Husna dai jiki ba dad'i sosai dan ko iya tashi batayi ga kuma tasa tunani sosai a ranta ganin haka ne yasa Farooq yaje ya d'auko doctor dan ya gaji da ganin ta haka.

   Bayan Doctor yazo yayi gwaje-gwajen sa ne ya tabbatar wa Farooq tana d'auke da cikin wata d'aya.

   Wayyo kuzo kuga murna a wajen Farooq dan har kyauta yayiwa Doctor.

   Ai kuwa wani irin gata Farooq yakewa Husna dan yanzu ba k'aramin so yake mata ba.

  B'angaren Yusuf kuwa yana zaune yana jiran Farooq ya saki Husna dan ko ba komai yayi masa bara zana a tsammanin sa Farooq zai saki Husna.

  Yusuf yan zaune har sati baiji wani labari ba hakan ne yasa shi zuwa gidan Farooq.

  Yana zuwa yayi sa'a Isyaku baya nan Farooq ya aike shi.
Shiga cikin gidan kawai yayi ba ko sallama.

  A parlour ya tsaya amman baiga kowa ba hakan ne, motsi yaji a cikin d'aki ai kuwa da sauri ya k'arasa ciki.

  Husna tana toilet tana ta faman kwara amai Farooq yana kanta yana mata sannu sai ganin mutum sukayi a kansu a tsaye.

  Wani Uban ashar Yusuf yayi sannan yace
"Farooq kana nufin Husna ciki ne da ita?
To wallahi baka isa ba sai na zubar da sh"...........
Wani  shak'a Farooq yayi mishi ya had'a kan shi da bango duka kawai yake mishi ba gaggauwata sannan ya fara cewa
" Yusuf Uban wa yabaka daman shiga gidana har cikin d'aki na?
Wa yabaka izeni ina tambayan ka." Ya sake shararamai mari.

  Ina Yusuf yaji duka sosai ya kasa magana sai faman zare ido yake dan bai ta6a jin irin wannan dukan ba.

   Sai da Farooq ya fara sassauta dukan sannan Yusuf ya samu ya k'wace jikin shi sannan ya fara cewa
"Wallahi sai na zubar da cikin nan ai daman na fad'a maka kar kabari tayi ciki shine ka bari ko?
To wallahi sai na rabata da shi."

   Ganin Farooq yana tunkaro inda yake ne ya sashi fita da gudu yabar d'akin Farooq ma ya bishi.

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ™†πŸ»πŸ˜­ *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ​​*πŸ“š✍🏻

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 86~90​*

Da gudu ya fita yabar gidan ya hau motar shi ya tafi.

  Komawa cikin gida Farooq yayi samun Husna yayi zaune tayi tagumi dan ita gaba d'aya hankalin ta ba a kwance yake ba.

  "Haba Husna dan meyesa zaki damu kanki akan wannan al'amarin?
Dan Allah na rok'eki ki daina sa wannan abin a ranki ko kin manta kina d'auke da ciki ne?" Ya tambaye ta.

   D'aga idon tayi ta kalle shi sannan tace
"Ya Farooq ya za'ayi hankali na ya kwanta bayan rayuwar mu tana cikin bara zanar Yusuf!
Kana jifa yana akirarin sai ya kashe mu to ya zanyi hankali na ya kwanta" sai kuma ta fashe da wani kuka.

  Zuwa yayi ya zauna a kusa da ita ya d'an kwantar da ita a jikin shi sannan yace
"To naji dan Allah ki daina kuka ko kina son cikin da yake jikin ki shima ya shiga damuwa?"
Alama a'a tayi mishi da kai
"To ki daina tunani insha Allah ba abinda zai same mu sai abinda Allah ya rubuta mana saboda haka kiyi hak'uri ki cire komai a ranki" ya k'arasa maganar yana shafar fuskan ta.
"To insha Allah na daina." Sannan ta goge hawayen da suke bin fuskan ta.

  Yusuf kuwa gidan su ya nufa yaje yayiwa mahaifiyar sa bayanin duk abinda sukayi sannan ya sanar mata Husna tana d'auke da ciki.

  Habiba ce tace
"Ciki fa kace Yusuf!
Ai kuwa yanzu sai ka hakura tunda tana d'auke da juna biyu."

  Wani kallo ya watsawa mahaifiyar tashi sannan yace
"Haba Inna wallahi bazan hakura ba sai dai shi ya hakura da cikin da matar dan ni zubar shi zanyi."
"Wai kai Yusuf me kagani ne a jikin wannan yarinyar duk kabi ka nace mata ga mata da yawa a gari."
"Inna bazaki gane bane  naga abinda na gani saboda haka kibarni kawai."
"To shikenan
Yanzu wanne shiri kake ne?" Ta tambaye shi.
"Eh to ni.yanzu abinda zan musu ma gaba d'aya na rasa amman Inna ki kawo shawara mana."
"To mai zai hana ka tura musu yan fashi idan yaso kawai su kashe su kaga ba wanda zai zarge ka."

  Wani wawan dariya Yusuf yayi sannan yace
"Inna Kice kwakwalwarki yana aiki har yanzu gaskiya naji dad'in shawaran ki nan."
"A to gashi nan dai yanzu na baka shawara mai kyau."
"Kwarai kuwa Inna gaskiya naji dad'i kin kawo abu mai kyau."

  Duk wannan maganar da suke a kunnen Mahaifin shi dan shi gaba d'aya baisan abinda yake faruwa ba sai da yaji suna fad'a.

  Gaba d'aya jikin shi yayi sanyi dan bai ta6a tsammanin haka halin d'an shi yake ba,  duk da daman halin Habiba amman bai ta6a tsammanin zata sa mutum ya kashe su ba.

  Fasa shiga gidan yayi ya juya ya fita ya koma shago dan gaba d'aya jikin sa rawa yake.
  'Yar k'aramar Nokia sa ya d'auka ya fara Neman number Farooq.

  Ai kuwa yayi sa'a ya shiga.
Farooq kuwa yana office yaga kiran Baban Yusuf da kamar bazai d'auka ba kuma sai ya d'auka dan shi a tunanin sa gaba d'ayan su bakin su d'aya.

"Hello Baba ina wuni."
"Lafiya k'alau Farooq yaya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Farooq ko zan samu ganin ka yanzu dan akwai maganar da nake son muyi amman ba na waya bane."
"Baba da fatan dai lafiya?"
"Eh to lafiya ba lafiya ba gaskiya kai dai sai.kazo."
"To shikenan Baba gani nan zuwa."
Yana fad'an haka ya kashe wayan yana tunanin me Baba zai fad'a mishi haka da gaggawa.

   Manager shi yayiwa magana akan an kirashi amman yanzu zai dawo bazai dade ba.

Motar shi ya hau bai tsaya a ko ina ba sai a k'ofar shagon Baba.

  Baba yana ganin shi yace mishi
"Yauwa Farooq sannu da zuwa amman dan Allah mu samu waje da ba kowa zai jimu ba dan maganar babba ce."

  Cikin mamaki dai Farooq yace
"To Baba mu shiga cikin gida mana."
"Yauwa to yayi kyau muje."

  Haka suka shiga cikin gida a babban parlour suka zauna sannan Baba yace
"Yauwa to inason ka kira mun Hajiya dan itama inason taji abin a kunnen ta."
  Farooq baiyi musu ba ya tashi ya shiga cikin gida dan kiran Mama.

  Bai dade da shiga ba suka shigo tare da Hajiya.

  Bayan sun gaisa ne Baban Yusuf ya fara da
cewa
"Zakuyi mamakin kiran Ku da nayi to ba komai bane daman illa abinda kunne na ya jiye mun shi yasa nake son na fad'a muku dan ceton rayukan ku."

  Cikin mamaki dai Farooq yace
"Baba meye ya Faru."
"Farooq yanzu ina shiga gida naji Habiba da Yusuf suna tattaunawa akan zasu turo muku yan fashi su kashe ku."

  Ba abinda Hajiya Aisha take cewa Wanda ya wuce
"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!"

  Baba ne yaci gaba da cewa
"Nidai gaskiya bansan meye a tsakanin Ku ba amman koma menene babba ne."
Ai kuwa nan da nan ya basu labarin duk abinda ya faru.

  Allah sarki bawan Allah Farooq shikam kasa magana yayi dan zuciyar shi ji yake kamar zata buga.

  Cikin rawar murya Hajiya tace
"Malam wannan wanne irin masifa ne Allah ya zarabce mu da shi!
Ace mutum da matar shi ace idan bai saketa ba sai an kashe sa."

  Cikin rashin fahimmata Malam yace
"Hajiya ban gane me kike cewa ba?"

  Ai kuwa Hajiya ta Bashi gaba d'aya labarin da ta sani, shi kanshi sai da abin ya bashi tsoron dan bai ta6a tsammanin haka Yusuf yake ta'addanci ba.

   cikin sanyin murya yace
"Farooq wannan ba k'aramin al'amari bane nidai a nawa shawaran ka kai wannan abin ga hukuma dan bazaka zauna su kashe ka ba,
Duk da su iyalaina ne bazan basu goyon baya akan mugun ta ba bare kuma kisan kai."

  Sai a lokacin Farooq yace
"Baba nagode Allah yasaka maka da alkhairi,
Amman Baba yaushe Zasu turo yan fashin?" Ya tambaye shi.
"Eh to amman inajin yau ne dan yanda suke maganar kamar Yau."
"To shikenan insha Allah Yau a hannun sojoji zasu kwana."
"To yayi kyau duk da iyalaina ne bazan goyi bayan su ba, Allah ya taimake ka."
"Ameen Thumma Ameen Baba nagode."
"Ba komai Farooq kunyi mana abinda ya fi haka saboda haka wannan ba komai bane."

  Hajiya Aisha kam in ba kuka ba ba abinda take dan ita tunda take a rayuwanta bata ta6a ganin irin wannan masifar ba.

  Bayan sun yanke hukunci sukayi sallama da Malam ya fita duk jikin shi a sanyaye.

  B'angaren Yusuf kuwa yana fita wani unguwa ya tafi inda asalin yan daba suke zama yaje ya same su sai faman shaye-shaye suke a nan ne ya basu address d'in Farooq da number gidan har photo Farooq sai da ya basu akan aikin kud'i million d'aya.

   Duk da Yusuf ba wani kud'i a account nashi sai da ya basu.

   Haka kuwa ya dawo gida cikin farin ciki dan yau burin shi zai cika.

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻

Farooq kuwa yana fita police station ya tafi
musu bayanin komai da ya faru kuma ya fad'a musu akan zuwan su na yau daddare.

   Ai kuwa D.P.O ya bashi mutane mota biyu dan su  kama su akan laifin da suke son aika tawa.

  Godiya ya mishi sosai sannan ya dawo gida Isyaku ya fad'awa komai dan baya son Husna taji labarin abin.

  Isyaku kam gaba d'aya ya tsorata dan kar yaje a garin kafin azo a kamasu su kashe sa hakan ne yace
"Yallabai gaskiya nikam na tsorata da wannan al'amarin ni yanzu zan tafi gida idan Allah ya kaimu gobe sai na dawo."

  Shima Farooq abin ma dariya ya bashi dan yaga alamun Isyaku tsoro yake ji sannan yace
"Haba Isyaku ya zaka bani kunya dan Allah gaskiya banyi tsammanin tsoro a tattare da kai ba."

  "Kai yallabai wannan al'amarin rai ne kaga kuwa ba'a wasa da shi."
"Kaga fa suma yan anayin sallah'n isha'i zasu zo kowa ya samu wajen b'uya ai sai anyi shiri,  kai yanzu abinda nake so kawai kabar k'ofar gidan a bud'e har yan sandan suzo."

  Cikin sanyin murya Isyaku yace
"To shikenan yallabai Allah ya tsare mu."
"Yauwa Isyaku haka nake son ji, Ameen ya Allah."

  Bayan haka kuma cikin gida ya shiga dan duba jikin Husna.

  Tana zaune a parlour tayi wanka tayi kwalliya Yau kam ba laifi tad'an ji saukin jikin ta sosai.

Sallama yayi ta amsa mishi ya shigo yana cewa
"Kai Maman Baby yau Baby ta barki kinyi wa Abban ta kwalliya kenan."

Dariya Husna tayi sannan tace
"Sannu da zuwa."
Yauwa My Angle ya jikin naki?"
"Jiki Alhamdulillah."
"To Allah ya rabaki da Baby na lafiya."
Dariya tayi sannan tace
"Ameen ya Allah,
Amman ya Farooq ya akayi yau kadawo da wuri haka."
"Eh lafiya k'alau kawai inason ganin ki ne."
Murmushin jin dad'i tayi sannan tace
"To na kawo maka abinci?."
"Kai My Angle yau har abinci kikayi mana?
Daman nayi missing girkin ki sosai wallahi,
Amman kuma gaskiya yau ya kamata nabawa Baby kyauta."
Dariya Husna tayi tace
"Kai gaskiya Bata buk'atar wannan kyautar naka."
"Ai kuwa tafi kowa so kedai muje naci abinci sai kiji sauran bayani."

  Haka suka ci abinci cikin so da kaunar junan su,  Farooq ko kad'an bai nuna gani abu a tattare a fuskan shi ba bare kuma Husna tasan halinda ake ciki.

  Yusuf kam shiri yake sosai dan dashi yace za'a tafi gidan Farooq d'in dan yana so ya harbi Farooq da hannun sa.

  Haka kuwa duk ya shirya har ya saka kayan da suka bashi da fuskan da zai saka saboda kar a gane shi.

  Misalin karfe goma na dare 'yan sanda sukazo suka zagaye gidan Farooq dukan su ko ina sai da suka b'uya sannan suka boye motar su a gaba da gidan saboda kar 'yan fashin su gani.

  Ai kuwa misalin Karfe goma sha biyu yan fashi suka zo gidan Farooq har da Yusuf shine yake jagoran su cikin gidan.

  Suna zuwa sukayi sa'a k'ofar gidan a bud'e yake hakan ne ya basu daman shiga cikin gidan cikin hanzari.

  Isyaku yana d'akin shi zaune dan gaba d'aya ya kasa barci ji yake idan ya kwanta zasujo su kashe sa duk da ga 'yan sanda ta ko ina a gidan.

  Suna zuwa direct part d'in Farooq sukayi sauran biyu kuma suka tsaya a wajen Isyaku.

Suna shiga d'akin Isyaku wasu police su biyu sukaje suka kama su.

  Suna shiga parlour a zaune suka sami Farooq akan sallaya da alama sallah ya idar yake addu'a.

  Suna zuwa suka fara nuna mishi bindiga .
Yusuf ne yaje ya zauna akan kujera ya d'aura kafan shi d'aya akan d'aya sannan yace
"Kai Yau kwanan ka ya kare daman kamar yanda na fad'a maka sai na kashe ka sai na kashe ka ne wallahi bazan ta6a barin ka ka zauna da matar da nake so, tunda kayi taurin kai tu yau lahira zatayi bak"..........
Ganin 'yan sanda sun shigo ne ya hanashi k'arasa maganar da yake yi.

  Gaba d'ayan su rikicewa sukayi dan basu tsammanin haka zai faru da su ba.

  Ai kuwa gaba d'ayan su aka kama aka kaisu police station.

  Yusuf kam sai wani muzurai yake da ido dan kuwa baisan ya akayi haka ya faru ba.

  Tunani yake ya akayi Farooq yasan abinda yake shiryawa amman ina ba amsa aka kwashe su.aka kai su station.

  Husna da tana cikin d'aki tana barci hayaniyar da tajine yasata tashi.

  Gaba d'aya abinda Yusuf yake fad'a taji a kunnen ta ba k'aramin razanata abin yayi ba.

Kukan ta Farooq yaji da sauri ya shiga d'akin dan baisan idonta biyu ba.

  Lallamin ta yake sosai amman tak'i yin shiru gaba d'aya Farooq ya fita a hayyacin sa yanda yaga tana kukan har cikin ran shi yake jin kukan ta.

  Cikin muryan kuka tace
"Ya Farooq meyesa baka sanar dani wannan abin ba da yanzu wani abu ya sameka ya kake son nayi?" Sai kuma ta fashe da kuka.

  Matsowa yayi ya rungume ta sannan yace
"I'm sorry my Angle banason na fad'a miki abinda zai tayar miki da hankali ne,  amman nasan duk shirin sa da yake yi mahaifin sa ne ya fad'a mun."

  Cikin mamaki Husna tace
"Ya Farooq wanne mahaifin nasa ?"
"Eh mahaifin Yusuf ne ya fad'a mun abinda suke k'ullawa shida mahaifiyar sa."
Nan da nan ya fad'a mata duk abinda Baban Yusuf ya fad'a musu har yanda yayi ya samu aka kama su.

  Ba k'aramin dad'i Husna taji ba dan da yanzu an kashe mata miji.
Cewa tayi
"Allah sarki.bawan Allah ashe ba halin su d'aya da d'an nashi ba."
"Wallahi sosai ma Husna ko ni da yake fad'a mun nayi mamaki da bai rufawa d'an sa asiri ba."
"Eh kaga kowa yayi gaskiya Allah yasaka mishi da alkhairi."

  Anan dai suka d'anyi hiran su sannan suka kwanta.

  Washe gari kuwa aka shigar da su Yusuf kotu Wanda aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya tare da hukunci mai tsanani.

*​Taku har kullum Momyn Musaddiq​*πŸ“š✍🏻
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ™†πŸ»πŸ˜­ *ABOKIN MIJINA*πŸ˜­πŸ™†πŸ»

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*​WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ​*πŸ“š✍🏻

​​​​````DEDICATED TO MY FANS, no need for long essay you know​ ​iπŸ’”youπŸ’― one love πŸ’žana mugun tare irin totally d'in nan``` ​​​ πŸ˜πŸ’žπŸ’”❤

*BISBILLAHI RAHMANIR RAHIM WASALLAHU ALAN NABIYYUL KARIM*

*MATAYEN ANNABI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESHI.*

*YA AURI MATAYE GOMA SHA D'AYA (11)*

```TA FARKON SU (S) KHADIJA 'YAR KHUWAILID, BAYAN TA YA AURI MATA GUDA GOMA (10) SUNE:
(S)AISHA 'YAR (S) ABUBAKAR
(S) HAFSAT 'YAR (S) UMAR
(S)ZAINAB 'YAR JAHASH
(S) MAIMUNA 'YAR HARIS
(S)SAFIYYA 'YAR HUYAYYI.```

  *Biyu sun rasu a wajen sa*
*(S) KHADIJA*
*(S) ZAINAB 'YAR*
*shi kuma ya rasu yabar sauran guda taran (9)*

  *KUYANGUNSA*
*Amman kuyangunsa su gudu (4) ne.*
*(S) MARIYATUL-KIBDIYYAH*
*(S) RAIHANATUL-KIBDIYYAH*
*DA WATA KUMA GUDA D'AYA WANDA (S) ZAINAB 'YAR JAHASH TA BASHI KYAUTA.*
*TA HUDU (4) KUMA YA SAMETA NE DAGA WANI SASHIN NA RABATATTU.*

*'YA 'YAYEN ANNABI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESHI.*

*'YA 'YANSA MAZA GUDA UKU NE*
*(S) ALKASIM*
*(S) IBRAHIM*
*(S) ABDULLAHI*

*'YA 'YANSA MATA GUDA HUDU*
*(S) FADIMATU*
*(S)ZAINAB*
*(S) RUKAYYA*
*(S) UMMU KHULSUM*

*DUKKAN SU DAGA (S) KHADIJA SUKE SAI (S)* *IBRAHIM SHI DAGA (S)* *MARIYATUL KIBDIYYAH YAKE, WADDA MUKAUKASU YA BASHI ITA KYAUTA.*

πŸ”š  πŸ”šπŸ’ž
  πŸ”š. πŸ”šπŸ’ž
    πŸ”š.  πŸ”šπŸ’ž
      πŸ”š   πŸ”šπŸ’ž

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 96~100*

Washe gari kuwa aka shiga da su kotu aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya tare da horo mai tsanani.

  Mahaifiyar Yusuf tayi kuka sosai dan bataso hakan ya faru da tilon d'an ta ba.

  Mahaifin Yusuf kuwa cewa yayi
"Komai aka mishi shi yajawa kanshi ai hukuncin ma yayi kad'an da an kara saboda masu irin halin sa sa gyaru."

  Farooq jikin shi duk yayi sanyi dan shi yana son Abokin shi tsakani da Allah amman ina Yusuf ba haka ya d'auka ba.

  Yusuf kuwa kuka yake sosai yanayin nadamar abinda ya aikata ya cikin kukan shi ne Dauda Wanda shine babban 'yan daban yazo yace da shi
"Haba Maza wallahi ka bani kunya banyi tsammanin haka a tattare da kai ba, yanzu kana nufin dan ankawo ka nan na shekara d'aya shine duk kabi ka damu kanka har kake kuka?
To bari kaji ni da yau zuwana uku kenan kuma ina fita sai naje nayi abinda nayi niya saboda haka ina baka shawarar kar kabari kud'irin ka na kashe Farooq ya fita a rain ka."

  Kallon shi Yusuf yayi sannan yace
"Yanzu sau uku kana shiga wannan wajen?"
"Kwarai kuwa kuma ina fita nake cimma burina."
"To yanzu yaushe zamu bar nan har na cimma nawa burin" ya tambaye shi.
"Kai shekara d'aya ne fa ai kamar yau ne saboda haka Abokina kar ka wani cire wannan abin a ran ka."
Murmushi Yusuf yayi sannan yace
"To shikenan nikuwa yanzu na d'aura damarar kashe sa tar da familyn sa."

  Shi kuwa Dauda dad'i yaji dan so yake ya d'aura shi wani hanyar.


*​BAYAN WATA TAKWAS​*

Yau ya kasance asabar Husna ta tashi da labour tun tana d'aurewa har takasa ta sanar da Farooq halinda ake ciki.

  Farooq yana ji ya rikice gaba d'aya waya ya d'auka ya kira Mama ya fad'a mata ce mishi tayi ya jirata tana zuwa amman kar ya sanar da mahaifiyar Husna, da to ya amsa mata yaje yasa Husna a gaba yana ta faman yi mata sannu.

Basu wuce minti goma da waya ba sai gata nan tazo cewa tayi
"Farooq d'auko kayan haihuwa mu tafi hospital."

Ai kuwa daman sun had'a kayan su tun ba yau ba alkwatin ya d'auka suka fita sai Aminu Kano hospital daman anan take awu.

  Suna zuwa aka shiga da ita kasan cewar haihuwar tazo ta.

  Basu wuce 15 minutes ba nurse ta fito d'auke da jariri a hannun ta.

  Farooq ne yayi saurin k'arasawa wajen ta yana cewa
"Nurse ta haihu ne?"
Dariya nurse d'in tayi sannan tace
"Gashi kuwa ga Babyn ka mai kama da kai itama Maman Babyn Lafiya ta k'alau" ta k'arasa zance tana murmushi.

  Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Farooq sai da yayi sujjada ya godewa Allah sannan ya mik'a hannu dan kar6an Babyn.

  Hanashi Nurse d'in tayi tace
"Wannan Babyn mai tsada ce bazan baka ita a haka ba."

  "To me kike so ki fad'a mun idan baifi k'arfi na ba zan baki shi."

  Dariya tayi ta mik'a mishi tana cewa
"A'a ba komai kawai zolayan ka nake."

"To dan Allah zan iya shiga naganta?"
"A'a ba'a gama gyara ba tukun nan." Tana fad'an haka ta wuce ko koma wajen Husna. "

  Hajiya kam tana tsaye tana kallon Farooq abin ma dariya ya bata dan kamar film take kallo take ji.

  Sai da yagama yiwa Babyn addu'a sannan ya wuce wajen Maman sa.

  "Sai da kaga kallon ta sannan zaka kawo min ita."

  Sai a lokacin Farooq yaji kunya magana ba ya mik'a mata Babyn.

  A lokacin Farooq ya kira gidan su Husna ya sanar da su wayyo kuzo kuga murna ta ko ina kan nace me mutane sun cika hospital.

  Farooq kuwa sai kiran 'yan uwa da Abokan arziki yake yana fad'a musu haihuwar Husna.

  3:00 pm aka sallame su suka koma gida cikin farin ciki.

B'angaren Yusuf kuwa ba k'aramin azaba suke shaba duk ya rame yayi bak'i fuskan nan duk gashi dan idan ka ganshi ma bazaka gane shi ba duk ya canza kamanni ga abinci ma sau d'aya ake basu a rana shima ba isarsu yake ba.

  Tunda aka saka Yusuf a gidan yari mahaifin sa bai ta6a zuwa ga duba shi ba sai mahaifiyar sa itama lokacin taje duba Yusuf a garin dawowa gida sukayi accident k'afan ta ya karye duk d'aurin da aka mata bayayi har aka hakura aka bari gashi yanzu haka za'a yanke farar amman ba kud'in aiki.

  Yusuf yayi nadama sosai yayi da nasanin abin da ya aikata amman yana fara nadama sai Dauda yazo ya canza mishi tunani.

  Ai kuwa yana d'aukar maganar Dauda dan ba k'aramin yarda yayi da shi ba.

  Haka suke rayuwar su cikin azaba ga aiki duk su sukeyin shi.

  Husna kuwa ba k'aramin kulawa take samu ba ta ko wanne b'angare dangin mijinta suna matuk'ar kaunar ta bama da sukaji labarin abinda ya faru a cewar su da wata ce ai tuni Yusuf yaci galaba akan ta.

  Haka rayuwar su taci gaba da tafi cikin so da kaunar junan su.

  Ranar suna yarinya tace sunan Hajiya Aisha anyi taro sosai dan Wanda bai sani ba cewa zaiyi aure ake.

  Da yamma akayi walima wanda Malama Khadija tazo tayi musu wa'azi akan zaman takewar aure.

  Washe gari ne za'akai Husna wanka amman ina Farooq yace shi baisan zancen ba dan shi baiyar da Husna taje gida wanka ba.

  Akayi-akayi Farooq yabar Husna ta tafi amman yace shi bai yarda ba sai da Hajiya tasa baki sannan ya bari badan ransa ya so ba.

Haka aka d'auki Husna aka tafi da ita wanka amman kullum sai faru yaje sau biyu ko sau uku a rana.

*BAYAN WATA BIYU*

Yau yake su Yusuf zasu fito a gidan yari Yusuf sai Allah Allah yake yaje gida yaga me yahana mahaifiyar sa zuwa d'auka shi.

  Ko wannen su yayi shirin tafiya dan duk yawancin su sunada mata harda yara.

  Shi kuwa Yusuf bai damu da rayuwar Hafsat ba bare kuma abinda yake cikin ta.

  Misalin karfe d'aya na rana aka barsu kowa ga tafi.

  Haka kuwa suka rabu bayan Dauda ya zuga Yusuf ya canza mishi tunani.

  A zaune ya sameta akan tuburma tayi tagumi tana tunanin wannan rayuwar da take ciki.

  Sallama shi da taji ne yasata d'aga kanta da sauri tana kallon shi.

Da sauri ya k'araso inda take yana cewa
"Inna meye ya same ki."

  Kuka Inna ta fashe da shi sannan tace
"Yusuf kai ne Ka dawo?"
"Eh nine Inna ki fad'a mun meye ya sani k'afar ki."

  Ai kuwa nan da nan Inna ta bashi labarin abinda ya faru da ita da rashin kud'in aikin gashi k'afar ta ru6e.

  "Inna yanzu yanke miki k'afa za'ayi?"
Kuka ta sake fashewa da shi sannan tace
"Eh Yusuf idan kuma ba'a yanke ba mutuwa zanyi kuma wallahi bana so na mutu."
"Kiyi hak'uri zanyi abu tunda dai yanzu gani na dawo."

Goge hawayen ta tayi sannan tace
"Kai matar Farooq fa ta haihu yarinyar har tayi wayo."

  Gaban Yusuf ne yayi mummunar fad'uwa sannan yace
"Inna yanzu sai da Husna ta haihu?"
"To ya za'ayi da abinda Allah ya k'addara."

  Baiyi magana na d'an lokaci sannan yace
"Inna ya labarin Hafsat?"
"Ai Hafsat ta haihu ta haifi 'ya mace sannan yarinyar ta koma yanzu ma naji labarin aure zatayi."
"Aure fa kika ce Inna!
Bayan ban sake ta ba."
"To amman ai ka koreta har ta haihu kaga kuwa ba aure a tsakanin ku."

  Tsaki yayi sannan yace
"To ni Inna zan tafi gida sai anjima zan dawo."
"To sai Ka dawo."
Daga nan kuma ya tashi ya fita bai tsaya a ko ba sai gidan sa.

  Gidan duk yayi kura duk ya 6aci a haka ya shiga bedroom d'in yayi wanka ya fito ya shirya cikin kanana kaya sannan ya d'auki key motar shi ya fita.


  Su Farooq kuwa soyayya suke sha sosai da matar shi ga 'yar su wacce suke kira da Samha hankalin su kwance ba abinda yake damun su.

  Yusuf kuwa yana fita wajen wani yaje yace mishi yana so yaje ya cire birkin motar Farooq zai biyashi da kud'i mai yawa.

  Ai kuwa nan da nan yaron ya amince daman aikin sa kenan.

  Yusuf gidan su ya wuce dan bai sanar da mahaifiyar sa abinda yake kullawa ba.

  Farooq ma gidan su yazo dan gaida mahaifiyar sa Bala ya ganshi ya biyo bayan shi.

  Buya yayi har sai da Farooq yayi parking motar shi sannan ya fito ya tunkaro inda motar yake.

Lokacin da yazo wajen motar cikicewa dan Yusuf ma anan ya ajiye motar sa kuma duk iri d'aya ne hatta color iri d'aya.

  Sai da Bala ya gama karewa motocin kallo sannan yazo ya cire birkin d'ayar motar sannan ya tafi.

  Yusuf ya kira a waya yace ya kammala aiki yazo ya biyashi.

  Cikin jin dad'i Yusuf ya amsa da to ya tashi yabar Inna ya fita ya hau mota ya tafi.

  Sai da Yusuf yahau babbar kwalta ga wata k'atuwar mota tana tunkaro shi ina yayi -yayi yataka birki amman ina babu haka wannan motar tazo ta taka Yusuf.

Ba abinda ake fad'a sai Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!

  Motar Yusuf tayi rugu-rugu wanda bazakayi tsammanin da mutum a ciki ba.
  Haka aka cire Yusuf jikin shi duk jini aka ajiye shi a gefe.

  Farooq kuwa ya tashi a gidan su zai dawo gida yaga kamar motar Yusuf ce take ci da wuta, da sauri tayi parking ya k'arasa wajen da gudu abinda idon shi ya gane mishi ne ya razana shi.

Da sauri ya k'arasa inda aka kwantar da Yusuf mutane sai magana suke dan 'yan wajen basu sanshi ba.

  Ai kuwa Farooq ana tafiya ya d'auke shi yasa shi a motar sa bai tsaya a ko ina ba sai Hospital.

  Yana zuwa aka kar6eshi akayi da shi emergency.

  Wani Doctor ne ya fita yace da Farooq yana son ganin sa, haka suka shiga office d'in doctor.

Bayani ya mishi sosai.akan k'afar Yusuf ba zata kara aiki ba sai ba an yake dan tayi rugu-rugu.

  Farooq ba k'aramin razana yayi ba dan baiso haka ta faro da abokin sa ba amman ba yanda ya iya haka Allah ya k'addara masa.

  Kud'in aikin Farooq ya biya akayi mishi duk wani abinda ake buk'ata Farooq ya biya sannan ya koma ya sanar da Hajiya Aisha.

  Itama ta tausayawa Yusuf dan yanzu ya zama abin tausayi.

  Haka rayuwar Yusuf ta koma ba k'afafu ya koma zama a kan keke.

  Mahaifiyar sa kuwa tanajin labarin accident da d'anta yayi a lokacin hawan jini ya bigeta ta rasu.

  *BAYAN SHEKARA D'AYA*

Yusuf na gani akan keken sa zaune yayi tagumi sai faman hawaye yake yayi nadamar duk.abinda ya aika ta.

  Gidan Farooq yazo ya nemi gafarar su akan su yafe mishi kuma duk ya sanar da su abinda ya aika ta.

  Farooq kuwa ya yafe mishi duk abinda yayi sannan yayiwa Allah godiya da ya shirya Abokinsa.

  Haka rayuwar su yaci gaba da tafiya cikin so da kaunar junan su.

Farooq yana taimakawa Yusuf sosai dan yanzu bashida aikin yi sai zama kan keke.

*Alhamdulillah!*
*Alhamdulillah!!*
*Alhamdulillah!!!*
*Alhamdulillah!!!!*

*ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODE MAKA DA KABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN KUSKUREN KE CIKI ALLAH KAYAFE MUN ALKHAIRIN DA KE CIKI ALLAH KA BAMU LADAN SHI*


Post a Comment for "ABOKIN MIJI NA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...