Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR ALMAJIRA CHAPTER A

YAR ALMAJIRA CHAPTER A

- - Post a Comment

 YAR ALMAJIRA CHAPTER A


     Umma! umma!! umma!!! "kitashi karki mutu kibarmu a cikin wannan rayuwa me cike da tarin bakinciki da kuncin zuciya dan Allah umma kiyi hakuri ki bude idanunki" kuka sosai takeyi me cin zuciya, tana jijjiga ummanta dake kwanta akan wani tsamurarren katifa, ganin dai har yanzu umman taki motsawa yasa ta fita waje dan neman agaji, abun mamaki tana fitowa naga wani hadadden gida agefe me cike da abubuwan ban mamaki da al-ajabi, sake kallon ta nayi sannan na kalli d'akin data fito aciki, tunani nafarayi kodai 6angaren yan aiki ne ko kuma d'akin matar me gadi ne toh koma dai miye bari zan binciko mana daga baya.+


Wani me adaidaita ta tsayar sannan ta rokeshi akan ya taimaka mata su d'auko mahaifiyarta daga ciki, dafarko yak'i yarda saboda tsoron irin hali na d'an adam awannan zamanin daga baya kuma ya amince suka shiga suka fito da ita, basu tsaya ko inaba se government hospital dake cikin garin bama, kasancewar weekend ne asibitin shuru ba hayaniya ba kuma mutane dayawa, bayan anshigar da ita ta biya kudin me adaidaita sannan ta shiga dan biyan kudin ganin likita, wani kudi naga tafito dashi kamar tsumma duk ya kod'e ya sha lik'i kallon kudin ta tsayayi tana hawaye kamar bazata mik'a ba, ganin haka yasa account  din taji tausayinta tace tabari zata biya ai dari biyar ne ba komai insha Allahu baze gagara ba, godiya tayi mata bayan ta karb'i reciept sannan takoma gefen emergency inda aka kwantar da umma, tana zuwa likitan yafito yana share zufa kallonta yayi kafin yace "kibiyoni office dina".


Bayan sun shiga ya nuna mata gurin zama sannan ya bukaci reciept kafin ya fara magana kamar haka "agaskiya mahaifiyarki tana shan wahala, shawara daya ce kufitar da Ita waje ko kuma ku rasata domin tana bukatar wannan aikin da gaggawa".


Kallonshi tayi tana hawaye kafin tace "likita banida yanda zanyi domin banda wanda ze taimakamin ni nake bara nake aikin dako nake ciyarda mu dani da kannena biyar da kuma mahaifiyarmu, da ace inada hanyar da zan iya taimakon mahaifiyata afitar da ita danayi, ko kuma da ace inada kudin biyan aikin dana bada nawa ansanya mata domin bamuda kowa se ita" takare maganan tana kara sautin kukanta.


♣🌹♣☘♣🌻♣


                 Agida kuwa Amina,Habiba da Nusaiba sunata sharban kuka domin sun tausaya wa umma sosai ayanayin datake ciki, tabbas suna ganin rayuwa da jarabobi kala kala, umma itace gatansu yanzu kuma tana cikin halin rayuwa ko mutuwa domin kuwa indai bawani ikon Allah ba sunsan ayanda aka fitar da umma daker tadawo musu, suna cikin haka hauwa'u da Khadija suka dawo daga kasuwa gurin da Fateemah take wanke wanke awata me saida abinci kasancewar ciwon umma ya tashi da dare shiyasa sukaje domin ta basu ranchen kudi sukai umma asibiti, suna dawowa sukaji abunda ke faruwa nan suna suka bud'e shafin kuka kamar ance musu ta mutun.


Umma wato (Maheeda) d'iya ce ga marigayi alhaji aliyu bomoi, mahaifinta shahararren malamine kuma hamshak'in mai kudi, mahaifiyarta ta rasu tun aranar da aka haifeta, umma yar gata ce gaba da baya kuma yar sarauta domin mahaifiyarta d'iyar sarki ce mahaifinta kuwa na rike da mukamin hakimin gari, umma su biyar ne a gun mahaifinsu, hud'un yaran yadikkon ta ne wato matar babanta, mahaifiyarta itace ta biyu agun mahaifinta, kasancewar ta me sunan mahaifiyar babanta yasa take samun soyayya fiye da sauran yaran sannan kuma gata marainiya tausayin ta ya karu azuciyar mahaifinta, hakan yasa yadikkonta salame ta tsaneta kuma take kishi da ita domin tasan yanda mai gidan ke son marigayiya, gashi kuma son ya shafi d'iyarta har ake nuna banbanci tsakanin ta da yaranta injita da fada, haka rayuwa ya cigaba da tafiya musu har tayi aure tabar musu gidan inda matar babanta tayi sanadiyar mutuwar mahaifita dan taci gado sannan kuma ta raba ta da danginta aka manta da ita kuma tayi sanadin rushewar rayuwar aurenta....


     Ni sunana fateemah ana kirana da Noor kasancewar naci sunan kakarmu ta wajen uwa, mun tashi cikin gata irin wanda ko wani 'dan adam ke son kasancewa aciki, mahaifin mu babban attajirine wato Dr muhammad Nura, mu shida ne agun iyayenmu, nice babba shekarata goma sha-shida se Nusaibah me shekara goma sha-hudu sannan Hawwau me goma sha biyu, Habeeba nada shekara goma, Aminatu yar shekara takwas da autarmu khadijah mimi me shekara bakwai wacce taci sunan mahaifiyar babanmu, kuma tsakanin su da Aminatu ba nisa mun kasance yan gata kowa nason mu kota wani 6angare kwasam se wani abu yafaru wanda yasan yamu cikin wani haki na kuncin rayuwa mun rasa mahaifin mu alhali yana raye mun rasa dangin mu na kowani 6angare alhali suna raye sannan gashi wacce muke gani muji dadi tana cikin wani hali .


♣🌹♣☘♣🌻♣


Se guraren karfe biyu umma ta farfado daga doguwar sumar da tayi, farinciki ne ya cika zuciyar Noor, zuwa tayi ta rungumi umma tanayi mata sannu sannan taje ta d'auko ruwa da roba ta wanke mata baki bayan ta gama ta bata abinci seda taga ta koshi kafin ta bata ruwan da likita ya sayo musu sannan ta gyara gurin tafita waje dan wanke kular.


Bata dade da fita ba ta dawo tana sauri sauri dan kar umma ta bukaci wani abu, office din likita ta fara shiga ta ajiye mishi kular ta sake yi mishi godiya sannan ta koma dak'i gurin umma, se da suka kara awa daya sannan likita ya sallame su tare da basu magunguna kyauta da kuma kudin adaidaita, albarka kam likita yasha agurin umma dan se godiya suke mishi mara adadi suna fitowa harabar asibitin suka samu napep, kwatancen unguwar suka mishi sannan suka shiga, suna isa suka bashi kudinshi kafin suka shiga ciki.


"oyoyo umma oyoyo umma, wayyo Allah mun gode daka dawo mana da umman mu lafiya cikin koshin lafiya" shine abunda yaran ke fad'a da sukaga umman tashigo da kafafunta batare da taimakon wani ba, haka suka zauna suka zagaye ta suna hira suna mata adduar samun lafiya me d'orewa da kuma kudin da za'ayi mata aiki.


Horn din da sukaji ne yasa duk duka tashi suka nufi gurin taga, kod'add'en labulen tagar suka d'aga suka kallon me shigowa, atare naga duk suna share hawaye ashe kuka suke ni banma sani ba, kallon umma nayi naga tayi saurin goge nata hawayen tana cewa "hayya alal salah, duk muje muyi alwala gashi ankira sallah" tafada tana janyo Mimi daga jikin tagar, itama Noor ta rike hannun sauran kannenta suka kama hanyar waje dan yin alwala.


Komawa nayi waje dan ganin abunda ya sanya su kuka gaba dayansu harda umma amma kash na makara dan kuwa banga kowa ba se motocin dake ajiye a haraban gidan da kuma karnuka dake ta kaiwa da komowa.

Wata yarinya nagani wacce baza ta wuce 16 years ba tafito daga Credence High School wanda ke cikin al-quox a hanyar da ake kira sheikh Zayed road tana tafiya tana wakar ta da turanci Yasmin!!! shine abunda naji ankira ta dashi, juyawa tayi taga wanda ke mata irin wannan kiran, tsaki taja ganin dreban ta acikin motar domin yau batada niyar zuwa gida da mota tafi sha'awar tafiya da kafa amma tunda har moses ya riga yazo toh dole ta bishi dan akwai shi da naci, shi kuwa moses dariya ta bashi ganin yanda tawani 6ata rai kamar za tayi kuka seya tuna farkon haduwar su a supermarket lokacin taje sayan kayan zak'i mistakely ya buge ta kafin ya bata hakuri harta kwashe shi da mari takara gaba ,k'aran buga kofar motar yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya shiga sannan yaja mota suka nufi gida.


Kwantar da kanta tayi ajikin kujeran tana hawaye saboda ya 6ata mata budget in banda haka ba da yanzu har tayi nisa atafiyar ta amma ba komai tasan maganinshi murmushi tayi da ta tuna da irin muguntar da zata mishi, moses kuwa duk abunda takeyi yana kallonta ta mirrow shima murmushi yayi irin wanda tayi saboda yasan in har tayi haka toh akwai abunda take shiryawa shina kuma yasan tarkon daze d'ana mata.


Sake baki nayi ina kallon kofar gate din da suka tsaya lailai aljannar duniya kenan inbaka mutuba zaka sha kallo, gidan ya hadu iya haduwa domin tsarin ya zarce tunaninku, shiba tsarin ginin villa ba shiba whitehouse ba shiba gidan sarauta ba narasa awani 6angare zan ajiyeshi, garin kallo ashe har sun shige sun barni sedai wani lokaci dan Aufana tace kar in dira ta katanga.

2
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*

Dafe kirji tayi tana cewa "Wayyo Allah na umma aman jini? Zaro ido tayi tana kallon umman nata dake nishi sama-sama, dagudu sauran yaran suka fito jin irin ihun da yayar tasu ta buga, suna zuwa su kayi turus suna kallon abunda ke faruwa kowacce tafara hawaye tana ambator Allah aranta dakyer Noor ta iya daga kafarta ta isa gurin umma tana kuka tana mata sannu ganin dai hakan ba shine maslaha ba yasa tayi sauri ta fita waje dan neman abun hawa, batare da 6ata lokaci ba tasa mu wani dan tsoho wanda ya taimaka musu suka shigar da umma sannan suka d'auki hanyar asibiti.


Suna isa aka fito da gadon sanya marasa lafiya aka d'auki umma wanda har zuwa wannan lokacin aman jini bai tsaya ba, yaran na kuka sukabi bayan ta ita kuma noor ta tsaya ta sallami me adaidaita kafin ta bi bayan su.

Likitoci dayawa suka taru akan umma dan ceto rayuwarta amma Allah beyi zatayi surviving ba, sedai muce Allah ya jikanta yabawa yaran hakurin rashinta, ahaka suka fito ajere kowannen su na tausayawa yaran musanman likitansu wato dr affan wanda ya dade yana jimamin abun yama yarasa ta inda sefara tunkaran su da batun gashi babu wanda yasani nasu balle ya sanar dashi ko zesan yanda zeyi, hawaye yaji yana zuba a idanunshi, seda ya daidaita kanshi sannan ya fita ya kira noor, kallonta yayi sannan yace ta zauna.

Jiki asanyaye ta zauna tana jiran taji yau kuma menene jawabin likita Fateemah!!! "inaso ki bani hankalinki muyi magana ta fahimtar juna, kece babba kuma duk kin fisu sanin rayuwa saboda haka ki natsu ki saurareni".

Jin yanda yau yakira sunanta yasa ta bada hankalinta domin tasan bawasa acikin maganar tasa kuma duk abunda ze fada me mahinmanci ne, gyara zamanta tayi ta Tsura mishi ido kamar me kallon film, d'auke idonshi yayi daga cikin nata dan karta karya mishi zuciya sannan yace "Fateema zaman duniya 'yar hakuri ce domin kuwa abune me karewa, idan yau mune gobe ba lallai yazama muba sedai wasu kuma daban, idan yau ana damawa dakai gobe ze zama da waninka, mutuwa kuwa rigar kowace kuma dukkanin mai rai mamacine, Allah yana d'auke abunda kafiso badan ya musguna maka ba se dai dan ya jaraba imaninka, haka zalika yana baka abunda kakeso bawai dan ya faranta maka ba sedai dan ya jaraba imaninka inaso ki kasance me yarda da kaddara aduk yanda yazo miki kuma inafatan zakiyi kokarin cinye wannan jarabawa dake gabanki, ina mik'a ta'aziyya ta gareki Fateema ina bawa zuciyarki hakuri ina tayaki kukan wannan rashi da ku kayi Fateemah Allah yayi wa umma rasuwa wanda ya fimu sonta ya d'auki abunsa Fateema bsbu yanda zamuyi sedai muyi mata adduar samun dacewa" yakareshe maganar yana kuka mecin zuciya baze iya rikewa ba tabbas ya tsasaya wa wadannan bayin Allah.
Wani irin zabura tayi ta fita a office din da gudu ta nufi d'akin da aka kwantar da umma, ganin haka yasa kannen nata suka bi bayanta, atare suka isa jikin gadon da aka kwantar da umma, hannu na rawa Noor ta bud'e abunda aka rufe umman tasu dashi, wani irin kuka ne yazo mata da sauri ta fita waje seda ta isa haraban asibitin ta samu kasan wani bishiya ta zauna tana kuka me cin zuciya, duk wanda yazo wucewa ta gurin seya tausaya mata, a 6angaren kannenta kuwa kwanciya sukayi ajikin umma suna jijjigata suna kuka anrasa me rarrashin wani, tausayin kansu ne ya kama su lailai duniya ba komai bane dazu fa suka gama wasa da dariya suna murnar cewa tasamu lafiya ashe duk na bankwana ne.

Likita kuwa tana fita yabi bayanta, seda yaga tayi kuka me isarta ta fara ajiyar zuciya sannan ya nufi inda take, dutsen dake kusa da ita yaja ya zauna sannan yafara mata nasiha me ratsa zuciya, seda yaga jikinta yayi sanyi sannan ya jata suka nufi d'akin da aka kwantar da umman, zuwa tayi ta rungumi umman tana hawaye tana mata addua sannan taja k'annenta suka fita waje dan akai ta gida ayi mata sutura, batare da 6ata lokaci ba likita da abokansa suka sanya gawar a mota suka nufi gidansu Dr da ita amma seda suka biya ta unguwar su Noor aka sanar da mutanen unguwar kafin suka wuce, likita yayi mamakin ganin gidan su Noor wanda ba boyayye bani a garin bama amma dai se komai ya lafa ze tambaye su dangantakar su da wannan hamshakin mai kudin ko kuma dai saboda rud'ewa ne yasa basu lura da gidan da suka nuna mishi ba koma dai menene zeji daga baya, bayan anyi mata wanka aka kirasu suzo suyi mata adduar bankwana kafin a tafi da ita, kuka sukeyi suna manne ajikinta, dakyer suka iya yi mata addua sannan hajiyar affan tajasu zuwa falo dan afitar da umma, kowa agurin ya tausaya musu, bayan an mata salla aka kaita makwancinta sannan akafara zaman makoki, likita ke kar6an gaisuwa a waje ita kuma hajiya a
cikin gida tare da yaran.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*


Wani wawan ajiyar zuciya nayi danaga gate din gidan abud'e yanzu kam zaku sha labari dan daganin wannan  Yasmin din akwai daru, sad'af-sad'af na shiga cikin gidan kamar 6arauniya, ji nayi an rufe kafar gate din da karfi sannan an sanya key ta ciki ashe baba me gadi ne ya dan zaga waje shine yabar kofar a bud'e, da gudu nayi hanyar shiga gidan inayi ina duban bayana, ina zuwa narasa ta hanyar da ake shiga dan kuwa kofar me lock ne se an rubuta numbers, tsaki nayi sannan na juya zan koma inda na fito se naji Hubbeey tace ta gwada zagaye gidan kila insamu kofar shiga, ai kuwa hakan nayi inata bin gidan lungu da sako, chan na hango wasu mata biyu suna fitowa ta wani kofa da alamu dai masu aikin gidanne dan harda wani uniform pink da fari,6oyewa nayi seda suka wuce sannan na fito na shiga cikin gidan ta wannan kofar, ashe kitchen ne komai na ciki pink da fari gurin ya matukar burgeni, kutsawa nayi ta wani kofa dana gani amma miye se naga lock na alphabet, haushine ya kamani amma da na tuna da wani abu senayi murmushi nafara danne danne ai kuwa se gashi inasa enter ya bude ai da sauri nayi shigewata ina kwasan shokiii.

Wasu yan biyu nagani maza wanda baza su wuce ishirin da uku ba suna buga game din kwallon kafa, kowanne sanye da rigar jesse me red colour gasu farare tas kamar larabawa iya had'uwa sun had'u harse da Lipton lipty ta kyasa su.

Bayan nagama dasu na haura sama zuwa dayan falon shima irin wancan lock din nasa ya bud'e wani kya'yataccen falo nagani purple & pink sa6anin nak'asan me golden da ratsin bak'i lallai an narka kudi a cikin gidannan, wasu matan nagani yan biyu da baza su haura sha uku ba suna karatun al Qurani gwanin ban sha'awa seka rasa muryan wanda yafi dadin sauraro, ga k'yau kamar su sukayi kansu nikam gashin ne ma yafi d'aukan hankalina.

Bayan nagama kallonsu na haura dayan stairs din anan naci karo da falon daya chasa wancan dan kuwa wannan mutuwar tsaye nayi kalarsa ja da ratsin ruwan toka yaji royal chairs, wata mata nagani zaune akan sofa tana danne-danne a laptop da glasses a idanunta tanayi tana kur6an shayin larabawa ni inagama balarabiya ce ai fa shiyasa yaran suka gadota, bayan nagama na sake hango wani stairs din wannan karan abokiyar tawa nagani tana dansewa Yasmeen kenan yar gayu akwai ji dakai sedai akwaita da tausayi sosai, earpiece ne akunnenta tasha wando swagger bak'i da top purple kyakyawace domin ta d'ara kowa agidan ita ta fito sak mahaifiyarta da hasken da karamin ruwan.

Komawa nayi kasa inda na baro masu game anan naga wani handsome din wanda dagani yayansu ne domin yafisu girman jiki, yana zaune yana danna waya ya daura kafa daya akan daya yana murmushi da bansan Ko na miye ba, bari dai in leko almajirata inga me suke ciki Allah sarki bayin Allah abun tausayi.
Allah sarki Noor duk ta fige ta zama wani iri dama ba auki gareta ba gashi kuma ta sake lalacewa, rashin uwa babban cuta ne da bashida magani sedai fatan Allah ya jikan iyayen mu ya saka musu da gidan Aljanna.

Yau anyi sadakar uku kowa ya watse daga su se hajiyar affan, affan da kuma kanwarshi suhaila, kullun a cikin rarrashin su hajiya take kamar kullun yauma suna falo suna zaune ko wacce ta buga tagumi tana tunanin rayuwar duniya dadin dake cikinta da wahal- halun dake cikinta sukam sunga rayuwa domin sun d'and'ana kowani fanni na rayuwa, sunyi rayuwar jindadi na alfarma sun kuma shiga rayuwar ha'ulai sedai godiyar Allah kawai.Hawayen dake mak'ale a idonta ta share sannan tace "hajiya mun gode da irin d'awainiyar da kukayi damu kuma mun gode da karamcinku agaremu bamuda kalmar da zamuyi amfani dashi domin godiya agareku sedai muce Allah ya saka muku da gidan Aljanna, sannan munaso mu koma gidanmu yau dan Allah" tayi maganar cikin girmamawa.Kallonta hajiya tayi tana me yaba halayyar yarinyar gata da natsuwa ga hankali da sanin ya kamata "kar ki damu noor ai hakan yiwa kaine kuma ni ina ganinku ne kamar yaranda na haifa, maganar komawarku gida kuma zansa affan ya kaiku zuwa anjima, amma zamanku ku kadai ai baze yiyu ba inaga gwara ku zauna agidannan idan baza ku takuru ba tunda bakuda kowa agarinnan.


Murmushi dole ta yarfa wa fuskar ta sannan azuciyarta tace "mu kuwa muke da yan uwa agarin bama kuma mu mukeda abunda zamuyi tunkaho mu nuna isa ga koma waye amma ayanzu bamuda maraba da shara, umma kin tafi kin barmu acikin rayuwa me cike da kunci".


Azahiri kuwa cewa tayi "hajiya zamufi kowa farincikin kasancewa cikin zuri'arki amma sedai muna masu baki hakuri bisa hakan dan baza mu iya zama anan ba zamufi jin dadi idan muna rayuwa a inda zamu ringa gani kamar umma tana kewaye damu, sedai zamu rika zuwa miki akai-akai".


♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*

"Mammy! Mammy!! ana jau'anun very very hungry (mammy! mammy!! Inajin yunwa sosai sosai) kwanciya tayi ajikin mammy tana zuba shagwaba,Yasmeen kenan sarkin daru.


Kallonta mammy tayi tana nazarinta Kafin ta maida hankalin ta akan aikin da takeyi a computer tana cewa "if the food is in my stomach then take it out and eat (idan abincin acikina yake seki cire kici) i dont know why you are always lazy (bansan meyesa kike da ganda ba) you better leave here before i decend on you (gwara ki tashi kibar nan kafin inji miki ciwo.

Tashi tayi tana bubbuga kafa ta sauka zuwa kasa, tana zuwa ta samu yan biyu as usual suna karatun al qurani hararansu tayi sannan tace "ai ko kune yaran sarkin makka se hakan, haba kullun aikin kenan sekace ance muku ku kad'aine musulmai"  tsaki taja ta sauka zuwa dayan falon.

Anan kuma taga yayan su a falo yana barci tsaki ta sake ja tana cewa "mutun bashida aiki se barcin tsiya da chating Allah dai yasa amishi aure ya bar musu gidansu su huta da zalinci".

Har zata shiga kitchen kuma ta hango yan biyu suna buga game kallon su tayi daya bayan daya kafin tace  "aikin kenan dai daga sarakan musulunci se sarkin barci se sarakan buga game kowa da nashi salon  se kace gidan haya.

              Dr affan ne ya shirya domin mai dasu gidansu, hajiya ma ta shirya domin rakasu gida, batare da 6ata lokaci ba suka dunguma se babban housing estate dake cikin garin bama ayanda yaran sukayi kwatance hakanne dai yasake kasancewa Ita kanta hajiya tayi mamakin ganin unguwar da suka shiga amma daga baya seta alakanta da cewa kila ko aiki su keyi agidan ko kuma mahaifinsu megadi ne agidan.


Suna isa kofar gidan Dr yayi parking duk suka fito atare, karamin kofar suka bude suka shiga zuwa part din da aka ajiyesu, kasancewar masu gadin gidan sunsan da zaman su shiyasa babu wanda ya kula da shigowarsu ko wanne harkar gabansa yakeyi, bayan sun shiga sun zauna akan tabarman da aka shinfid'a musu hajiya tace "ashe gidan alhaji muhammad Nura kuke da zama?" ta fada tana karewa d'akin kallo cike da tausayin su.
                 

Noor ce tayi saurin cewa "eh agidan muke da zama muna taya matar sa aiki amma yanzu basa nan sunyi tafiya basu masan da rasuwar umma ba sedai idan sun dawo" tafadi hakanne dan kar wata acikin kannenta tafara zuba kuma kar hajiya tasake yi musu wani tambayar.


Tausayin su ne ya sake cika zuciyar hajiya musanman ganin irin gurin da suke zama acikin irin wannan gida na alfarma wanda tasancewa ai masu aiki sunfi karfin irin wannan gurin amma dai batasani ba ko awaje ne yakeda kyawawan halayya acikin gidan sa kuma mace ke juyi da kujeransa "shikenan Noor mu zamu tafi ki kula da kannenki kuma ki kasance me yawan ibada da neman tsari insha Allahu babu abunda ze sameku zan ringa zuwa idan na samu time shima affan ze ringa zuwa duba min ku, gawannan kuyi anfani dashi kafin insake muku aike" kud'i ta m'ika musu sannan ta tashi ta gyara mayafinta tayi musu sallama.


Godiya sukayi mata sannan suka mata rakiya har waje kafin suka dawo ciki suka zauna suka dasa wani dandalin kukan saboda kewar ummansu daya addabi rayuwarsu, Noor ce tace bari tashiga kasuwa gurin madam dinta tasanar mata da rasuwar kasancewar karta jita shuru dayawa kuma babu wani labari, dukkan su kowcce tace zata bita, haka suka dunguma zuwa cikin kasuwa inda madam tayi musu rashin mutunci ta kuma koreta wai saboda ta raina mata hankali shine zataki zuwa har wajen kwana biyar kuma bazata sanar da ita dalili ba ko tayi aiken kannenta kota wayar ummansu tabarta da asara saboda babu me wanke mata plate din da zata bada abinci, yanzu kuma jiya tasamu wata saboda haka ta kore ta taje gaba ko zata samu wani guri, haka su kayita kuka suna rokonta amma tayi kunnin uwar shegu dasu, ahaka suka dawo gida suna jimamin abunda ya faru.


♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*


Tana shiga kitchen ta hadu da Iya zata kwashi abincin masu aiki takai musu, tsayar da ita Yasmeen tayi sannan tace taje sama takawo mata wayarta yanzu yanzunnan.Haushine ya kama Iya amma yazatayi ai dolenta tayi tunda 'yar gaban goshin alhaji tayi aike inba haka ba zata iya rasa aikinta intayi wasa, ajiye ksysn abincin tayi sannan ta nufi cikin gida.


Tana tafiya Yasmeen ta d'auki abincin Moses ta zuba mishi dakekken maganin barcin data daka da yaji ta juya dakyau yanda babu wanda ze gane musanman kasancewar abincin jollof rice sannan ta dauki lemonshi na zobo ta zuba tablet ta jijjigashi harse da ya narke sannan ta ajiye su amazaunin su ta goge gurin ta wanke hannunta tana dariyar mugunta.


Tana gamawa Iya ta sauko ta rutsina ta m'ika mata wayarta kafin tace da ita akwai wani abun ko zata iya tafiya, batare da Yasmeen ta kalleta ba ta amsa da cewar ba komai taje kawai sannan ta koma ciki ta nufi dinning dan cika cikinta tunda kowa da abunda yake aikatawa ita kam bazata iya jiraba Allah ya gani tanajin yunwa sosai sedai su had'e a break fast din gobe ko kuma idan ta dawo k'ari zuwa anjima.
Akwana atashi asarar me rai, yau da gobe se Allah, ko wata rana darasine ga rayuwar dan adam, ayau akayi sadakar arbain inda maman dr Affan tayi bajinta wurin sarrafa abubuwa na musanman ciki harda kayan abinci wadatacce ga marayun Allah, da kuma sutura na alfarma, Noor dai babu bakin magana se kuka saboda ba suyi tsammani ba tabbas hajiya mace ce ta gari  wanda abun hannun ta be rufe mata ido ba, godiya su kayi ta mata suna kuka seda ta nuna 6acin ranta sannan suka tsagaita suna masu farin-ciki suna yiwa Allah godiya daya kawo musu d'auki acikin halin da suke ciki.

Bayan mutane sun watse suka gyara gidan su hade da shimfid'a sabuwar leda da kuma katifar da suka samu, farinciki ne ya kama mimi ganin cewa yau zata kwana a katifa me kyau me laushi, murmushi hade da hawaye suka bayyana a fuskar Noor ganin kannen ta acikin farin-ciki da annashuwa,tabbas Dr Affan wani haske ne acikin rayuwarsu. Washe gari da safe soyayyiyar dankali da kwai sukayi hade da shayi wanda yaji kananfari, kowacce fuskarta dauke da murmushi wanda ze nuna tsantsan farincikin da suke ciki sedai a6angare daya kewar umma ke dawainiya da zuqatan su, inama ace tare da umma ne ai da farincikin nasu se yafi hakan.


Bayan sallar azahar Dr Affan yazo dubasu harda tsaraban fruits cikin wani babban leda, mimi harda tsallenta da taga apple, d'auka tayi zata fara ci ba tare da ta wanke ba da sauri Noor ta kar6e tana yi mata fada akan hakan, shagwa6e Fuska tayi kamar za tayi kuka sannan ta bata hakuri, murmushi Noor tayi kafin ta bata tace taje ta wanke kuma tayi bismillah kafin ta fara ci, shi dai Dr Affan kallon ta kawai yake yanajin wani irin sonta na ratsa shi, yarinyar tana burgeshi ne kawai saboda bata da matsala ko kadan, gyaran murya tayi tana cewa "Dr yadai naji kayi shuru kuma ka tsareni da idanu, Allah dai yasa ba wani laifin nayi ba"? Murmushi Dr Affan yayi sannan yace "ai laifinki da yawa domin ba zasu lissafu ba se dai ad'anyi miki summary inda hali ki fara wanke kanki" har za tayi magana se taji karan horn din motoci alamun me gidan ya dawo da sauri ta kirkiro wasu excuses su kayi sallama da Dr sannan tayi shigewar ta ciki, shima motarsa ya shiga yana mamakin sauyin da ya gani agurin ta daga jin karan mota, se kuma ya kawar da zancen daya tuna cewa aiki suke agidan kila akwai abunda bata gama ba shiyasa take sauri..♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*


Murmushi Moses yayi lokacin da yagana kallon abunda Yasmeen ta aikata, rufe laptop din yayi sannan ya kira wani yaron shi dake aiki agidan me suna daniel, umarni ya bashi akan idan ankawo abincin shi kawai ya kar6a ya zubar inyaso yaje bigg's ya sayo mishi araibian zirbian da fresh milk, kar6an kudin yayi sannan ya fita dan cika umarnin ogan nasa..


Sallaya naga ya dauka ya shimfida bayan ya rufe kofan, mamakine ya kamani ganin ya tada kabbara, tambaya na farayi shin dama Moses musulmine? kuma menene dalilinsa nasa cctv camera acikin kitchen sannan meye alakarsa da danial, zazzakar muryansa ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana fada, (impossible inji bature) yanda naji yana fitar da karatun yanda ya kamata tare da kiyaye ka'idoji shi ya sani zaman dirsham domin nima kaina ya kunce narasa madafa..

A6angaren yasmeen wani irin farinciki takeji saboda ta kawar da me takura mata ko ba komai gobe zata shana ahanyar dawowa daga school tunda maganin na 48hours ta bashi, murmushi ta rinkayi ita kadai saboda tayi tunanin tarkonta ya kama, batasan cewa shima da nasa shirin ba.Ahaka rayuwa ya cigaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi, basu da matsala ta fannin abinci ko sutura se dai matsalar rashin umma da kuma rashin uban da yana raye amma tamkar basu da gata, yau sun wayi gari abincinsu yayi kasa domin befi yi biyu ba gashi Dr yayi tafiya kuma basu san lokacin dawowarsa ba hajiya kuma ta tafi umara dole su fita neman abunda zasu ci kafin dawowar hajiya, tashi Noor tayi ta shiga dan akurkin kitchin dinsu dan sarrafa musu abunda zasu ci, taliyar hausa kadai ya rage musu gashi babu kayan miya, sedai akwai maggi da yaji da kuma dan guntun man gyada, tafasa taliyar tayi gaba dayan sa sannan ta raba gida biyu ta zuba rabi a kula ta sa musu sauran a kwano me dan girma, soya man gyadar tayi sannan ta barbada maggi da yaji, Nusaiba ta kira tace takai musu d'aki sannan ta d'iba ruwan sha tabi bayanta...


Da dare ma taliyar suka ci suka sha ruwa sannan suka kwanta, Noor ce kadai idonta biyu tana tunanin abunda za suci washe gari duk da cewa akwai naira dari biyu a hannunta amma tasan baze kaisu zuwa dare ba dole dai sai ta fita tayi bara ko dako dan ta samawa kannenta abunda zasu ci koda ita zata kwana da yunwa, ahaka tayi ta saka da warwara har aka kira as-salatu idonta biyu, alwala tayi sannan tayi nafila kafinnan ta tashi nusaiba, itama bayan ta fito seda tayi nafila kafin ta tashi sauran, seda gari ya fara haske sannan suka koma barci, karfe takwas daidai Noor ta farka da sauri ta dauki hijabin ta tasa ta lalla6a ta fita saboda karsu tashi, wani shago taje nan kusa dasu ta sayi garin kwaki na dari se kuma garin filawa na dari sannan ta dawo gida, ajiye garin tayi ta daura ruwa awuta sannan ta kwa6a garin filawa tayi musu dan wake kasancewar suna da yaji da man gyada, seda ta gama sannan ta tashe su abarci, wanka su kayi gaba dayansu kafin sukaci abincin, da rana kuwa kwadon gari tayi musu me albasa da yaji kasancewar basu da garin kuli...
♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻уσвє*
*♣gαι∂αм*

Sanye yake cikin Wando da Riga yar kanti,ga wani bakin Glass ya kafa kamar wani Boss,dube-dube yafara yi ajikinsa don ko za'a iya samun mishkila,ganin cewa babu komi yasa ya fito waje yana kiran Dr Affan akan yayi sauri,shi kuwa Dr Affan ganin Sule shuru yasa yayi tafiyarsa bakin kwalta wajen majalisar su.
           

Ganin shuru bai ganshi ba shiyasa ya dau hanyar kofar sarki don yasan ba zai wuce yana gun majalisa ba, yana shan k'wana kuwa ya ganshi sai zuba yake ana hira,"Affan,nagama kazo mu tafi" ya fada kai tsaye yana faman goge takalmi. Affan na dago kai ya fashe da dariya ba sanya sai da yayi me isarsa alokacin har sule ya gama kuluwa yayi tafiyar sa sannan ya tashi ya nufa inda sulen yabi yana kiran sunansa "Sule!Sule!! dan Allah ka tsaya yi hakuri dan Allah ni bada gayya nayi ba".
hararansa Sule yayi sannan yace "in banda rainin hankali shine zaka tsaya kanamin dariya fisabilillahi meye ne bai yiba a wanka na eh?" ya tambaya yana duba jikinsa ta ko ina,shi kuma Affan gimtse dariyar sa yayi yana cewa "yi hakuri nidai kawai ganin yanda kasha Bak'ak'en kaya da Jan takalmi da hankie kamar wani dan mafiya shi ya sanya ni dariya, amma dai yi hakuri dole ma maryama taso wankan nan dan gaye dan kwalisa in kafaso dole ne abada hanya haba abokina dan murmusa mana eeh eeh" haka yayi ta mai kirari yana hura masa kai har sai da suka isa kofar gidansu maryama.
          

Dai-dai isarsu dai-dai fitowar Hajja Hadiza wacce kanwace ga maryama budurwar Sule, sake baki tayi tana kallon Sule kafin ta bushe da dariya sai da tayi dariyar ta mai isarta sannan ta lura ashe fa su biyu ne ai kuwa tana kai duban ta kan Dr Affan taji yagama tafiya da ita kallonsa take ba ko kiftawa,fitowar maryama ne yasa ta dakata da maryama ta ambaci sunan ta,sai da ta dan razana kafin ta juya tana guna guni ta dau hanyar gidan su Kubra kawarta inda aka aiketa sayan manja..
"kai masoyi wannan wankan duk nawa, gaskiya naji dadi kayi kyau sosai,kuma naji kishi akan duk wacce takalleka don kuwa tabbas sai ta sake kallonka" maryama  tafada tana mishi fari da ido,shi kuwa gogan kamar ya zuba ruwa akasa yasha don dadi har ya manta da rashin mutuncin da Hajja Hadiza tayi masa. Dr Affan ne yayi gyaran murya sannan yace "masoya ni zan wuce dama rokosa nayi,yanzu wajen kallon kwallo na nufa daga nan indare bai yi ba kila inbiyo mutafi tare in kuma 10 yayi sai dai mu hadu a gida".   

         
"Haba guy ya zakamin haka ai nazata tare zamu tafi ai,banma zaci zakaje wajen kallo ba" Sule yafada kamar gaske yana 6ata rai amma a zuciyarsa yaji dadin hakan "nidai kayi hakuri kawai muhadu a gida banson takura muku ne if not dana zauna har ku gama, amma kaga inna zauna kaima za kayi saurin gamawa saboda you dont want to keep me waiting,so kar kaji komai sai mun hadu kawai". ya fada yana bashi hannu, shima Sule ya mika masa suka tafa "shikenan tunda haka kace sai mun hadun nagode da rakiya". murmushi yayi sannan yace "haba dai abokina anything for you,toh gimbiyar Sulaiman sai kin sake ganina" "nagode Dr agaida gida".tafada tare da yiwa Sule signal akan su shiga cikin gida.. shi kuma Dr ya dau hanyar tafiya anguwar rasha don kallon kwallo.

6angaren Hajja hadiza kuwa Allah-Allah takeyi tayi tagama kar6an sakon takoma gida don ganin wannan kyakyawan saurayin itakam dai gaskiya tafad'a tarkon sonsa domin ya kasance irin namijin da take matukar so woow gashi da saje me kyau ga shi dark handsome ga ga ga kash "nikam Kubsi uma bata gama bane sauri fa nakeyi gaskiya".

Nazarinta kubsi tafara yi kafin tace "nikam Hajja Hadiza anya ba abunda kike 6oyemin kuwa, naga tunda kika zo ba'a nitse kike ba kuma da alama kina cikin farin ciki sai dai na fahimci ba'aso musan komi,amma intai tsami zamuji". tafada tana hararta da wasa, tsaki taja ta tashi tana cewa "kinga nikam barni tukun inji da abunda ke damuna kin tsaya kina dagulamin lissafi idan uma tagama dan Allah kibawa Laurat ta kawo min gida" bata jira amsar Kubra ba tayi tafiyarta abunta,ita kuwa Kubra ta saki baki tana kallonta "kwajimin karfin hali toh in Laurat din bata gida ba,kaii Hajja halinki sai keh".Sauri ta dinga yi kamar zata tashi sama, kai karshe dai sai da ta hada da gudu saboda gaskiya ta matsu ta isa gida tayi tozali da abun kaunarta handsome sunan da ta laqa mishi kenan a zuciyarta,koda ta isa gida kai tsaye karamin falon dake zaure ta nufa ko sallama babu tayi shigewarta ciki tana ta dube-dube amma bashi babu alamarsa, maryama ne tace "keh! lafiya zaki shigo bako sallama sai wani zare ido kikeyi kamar kina neman 6arawo" tafada tana hararar ta "yi hakuri" shine kawai abunda Hajja tafada sannan tayi ficewarta zuwa daki tana guna guni "shikenan mutun baya laifine haka kawai zaki min masifa agaban saurayinki wallahi ba zata sa6uba ina kyaleki ne don kawai kin girme ni amma wataran zan baki mamaki" tafada tana tamke fuska kamar agabansu, chan kuma kome ta tuna dasauri ta fita ta nufi dakin innarsu,da sallama ta shiga  "inna nasamu Uma tana aiki amma zata aiko Laure dashi anjima kadan " ba tare da uma ta daga kai ta kalle ta ba tace "shikenan jeki ai dama baban na kuma sai bayan isha yake dawowa ba damuwa" har zata sake magana sai kuma tafasa ta fita saboda yanayin da taga innar tasu kamar ranta a 6ace yake,sake komawa falon zauren tayi ta leka amma duk da haka bayanan, tsaki taja ta koma daki tayi sallah sannan tayi kwanciyarta don gaskiya ko abinci ba zata iya ci ba ayanayin da take ciki..

      


6angaren Dr Affan kuwa yama manta da ya ta6a ganin wata halitta me kama da ita, sabgar gabansa kawai yakeyi, sai wajen tara da rabi ya dawo gida har lokacin Sule bai dawo ba, wayar sa ya kunna yafara kallo,karfe goma ya kashe komi yabi lafiyar gado.

         


Sule kuwa sai sha daya saura ya dawo don sai da ya biya gidan yayarsa yaci abinci tukunna don kunyar cin abinci a gidansu maryama yakeyi..
      
        

STORY CONTINUES BELOW
Washe gari da safe tun karfe biyar saura ta tashi a barci duk da cewa bata samu barcin kirki ba saboda tunanin hand some duk sanda ta rufe ido shi take gani sai wajen daya da rabi barci 6arawo ya dauke ta..Tana tashi tagama aikinta da wuri kowa ma mamaki yake a gidan don kuma babu wanda ya kaita son jiki amma yau harta gama aiki ba tare da inna tayi dogon baki ba lailai akwai magana. bata kula kowa ba har ta kammala tayi wanka ta faki idon maryama ta dau wayarta ta nemi numbern Sule ta kwashe sannan ta ajiye mata wayan ta wuce gidan su Hajja Ghaji kawarta na kut da kut,takoyi saa ta taras da ita tana shirin fita itama "yadai mutumiyar da sassafe haka lafiya dai koh" Hajja Ghaji ta tambaya cike da mamakin ganin kawarta da sanyin safiya.. "ke dai bari zauna muyi maganar" tafada tana janyo kujeran karfe, bayan sun zauna Hajja Hadiza ta zayyana mata komai daga farko har karshe mamaki ne yaka ma Ghaji wacce tunda suke bata ta6ajin Hajja Hadiza ta yi mata magana akan wani saurayin da ta damu dashi take sonsa da gaske ba sai dai tayi ta zagin samarin tana cewa su Banki1 Banki2 Gara3 Gara4 Direba5 Direba 6 amma badai tace tana sonsu ba harma ta damu da lafiyar su da rashin sa, ajiyar zuciya tayi sannan tace "toh kawata ta ina zamu fara kenan yanzu don ni kaina ya kulle da wannan abun alajabin?" fuzgar da iska  tayi kafin tace "eh toh na dauko numbern saurayin adda maryama kinga sai mu kira muyi masa bayani koya kika ce?" "eh toh banki ta taki ba gwada kira toh muji inya shiga sai kiban nayi masa magana inbai yiba kuma sai mudau plan B" murmushin jindadi tayi sannan tayi saurin dialing numbern ai kuwa akayi rashin saa wayar akashe take "kash kinji wai switchoff" "sake kira dai may be network ne kinsan network yanzu bai fiya kyau ba inya shiga toh inbai shiga ba inaga da gasken ne akashe take" sake kira Hajja Hadiza tayi amma still akashe, wurgi tayi da wayar taja tsaki,Hajja Ghaji ce ta dauko wayar ta hadu ta mika mata sannan tace "inaga ki dan bari zuwa jibi tunda yau dai ba zuwa zaiyi ba saidai jibi in kinga basu zo tare ba in yaso sai mu dau plan B din,ki daure jibi kamar yau ne komai zai yi nomal muje kira kani gidan anty iyatu chan gangare" ba musu ta mike kamar wanda kwai yafashe a ciki tabi bayanta suka tari mai adaidaita suka kama hanyar gidan yayar Ghaji...


Ahaka tayi kwana biyun nan adaddafe kamar wata wacce tayi shekara ba lafiya har ta zube ta zama so silent kamar ba ita ba kullun sai tunani shi ne ya zame mata aikin yi.

         

Yau ya kama jumma kuma aranar su kayi zasu hadu da kawarta su yiwa saurayin yayarta su magana akan ya taimaka da lambar wayar abokinsa, tun safe take ta fara'a kamar anyi mata albishir da gidan aljanna,tana gama aiki saiga Hajja Ghaji ta iso cikin afterdress tayi roiling gyalen ta sai zuba kamshi takeyi,ita kuma Hajja Hadiza ba abunda takeyi sai kallonta sai kace zasu biki amma dai tayi kyau sosai abunta "kai kawata irin wanna kwalliya ai sai ki kwacen saurayi" tafada cikin  tsigar zolaya,hannunta ta kama suka shige daki "kinga yanzu ko nagama ayyuka na, yanzu dai bari inje inyi wanka domin ankusa fara sallar jumma kuma ana idarwa yake zuwa". tana magana tana daura towel "shikenan ban littafi in karanta kafin ki fito" mik'a mata littafin tayi sannan tayi ficewarta zuwa bandaki.
            
            
"Nikam wallahi zan wuce in barka, haba kullun in zakaje gun budurwa sai ka 6ata lokaci gunyin gayu, yau dai gaskiya bazan raka kaba iya kata masallaci zan dawo in tafi ziyara gidan yan uwa da abokan arziki tunda hajiya zata dawo wani sati daga nan zamu koma bama". inji Dr Affan wanda ke cika yana batsewa shi a lailai Sule ya 6ata masa rai sosai sosai...


Fitowa yayi yana gyara hullarsa ya zuba turare sai kanshi ke tashi kamar shagon humra kilama wanka yayi da ruwan turare waya sani ne "yi hakuri aboki afwan bazan sake ba muje koh". ya fada yana rufe kofa sannan ya dau sallayar su suka wuce masallaci "ai kai kullun haka kake cewa yanzu duk inda mukabi sai an kallo mu saboda irin wannan uban wankan turaren da kayi ai dai ko mace sai haka, ni kamar ma hadda hoda kashafa koh?" shidai Sule bai tanka masa ba har suka isa masallaci yana ta banbami karshe dai yayi shuru don kansa..


Hajja hadiza kuwa anyi wanka anyi kwalliya kamar wata amarya duk don zuwan abokin saurayin yayarta da bai san da zamanta ba,nata turaren kam haryafi na Sule kamar ta kwana cikin ruwan turare "kawata naji kamar har an idar da sallah koh". ta tambayi Ghaji wacce ke faman katanta littafi me suna DARASIN RAYUWA "eh tooh inaga dan niba sauraron sallar nikeba amma mai yiyuwa sun idar ai tunda kinji shuru kam" tafada tama cigaba da karanta littafinta.

           
Adda maryama ce ta shiga ita dai abun nasu na bata mamaki "kodai biki zasu kokuma bako zasuyi oho Allah masani" tafada acikin ranta kafin ta dau sallaya tayi sallah ta kimtsa kanta domin tarban masoyinta..

        
A 6angaren Sule kuwa yayi duk yanda zaiyi Dr Affan ya rakashi yace sam shifa zumunci zai yi yau,akwai guraran da ya kwana biyu bai ziyarce su ba, ba yanda zaiyi haka sukayi sallama kowa ya dau hanyarsa.

bai tsaya ko inaba sai kofar gidansu maryama, yana sauka a napep ya buga wayarta domin sanar mata isowarsa,su kuwa yan nema duk sun zuba kunne domin sauraron zuwan bakon nasu, koda su kaga tadau waya tana cewa "sannu da zuwa ganinan fitowa" duk sai suka cika da farinciki harma suka rigata fita, koda isarsu suka tarar da Sule shikadai gaisheshi su kayi atare kafin Hajja Hadiza tace "Mijin addarmu yau ba kazo da dan rakiya bane?"
murmushi yayi ganin cewa yau bata yimar shekiyancin data sababa kafin yace "eh toh da dai tare zamuzo amma kasancewar yanada wani uzuri shiyasa bamu taho tare ba amma bayanda banyi dashi ba yaki zuwa" kallon juna su kayi kafin hajja Ghaji tace "toh yayanmu zamu iya samun numbansa mu sai mu kirashi kila asamu yazo..Duk da cewa Sule bai kawo komai aransa ba amma kuma yayi mamakin damuwarsu kan Dr Affan sai dai kuma kawai ya basu numbern ya kuma yi watsi da zancen nasu..
Maryama dake bakin kofa takejin duk abunda su kayi taja dan karamin tsaki"dama wai akan wanda bai sanda zaman su bane sukayi wanka haka lailai sun ja wakan su aiki domin Dr Affan ba irin mazannan bane" ta fada aranta, "nikam inkun gama sai ku min izini in shigo da masoyina koh?" ta fada tana musu wani irin kallo wanda yasa ba shiri suka koma cikin gida "yi hakuri habibi, wadannan yaran ba hankaline dasu ba any way mu shiga ciki koh".
tafada tana yimishi murmushinta me kya'yatarwa..
Yau sun tashi basu da ko sisi ahannun su sannan babu wani abun sarrafawa acikin gidan, suna cikin jimami sukaga Noor ta tashi da sauri ta shiga cikin d'aki, bata wani d'au lokaci ba ta fito hannunta dauke da wasu kaya masu kyau, hijabi ta saka sannan ta fita ba tare da tace musu uffan ba, gidan kande dillaliya ta shiga chan kasan gidansu, kande ma'aikaciya ce akarkashin gidan wani alhaji da take aiki, kasancewar agidan take da zama shiyasa akasanta sosai acikin anguwar, dillalancinta ya shahara sosai domin bata da kirki indai akan kudi ne sannan akwai zafin nema bata da wasa ko kadan.Tana isa kofar gidan ta gaisar da baba mai gadi sannan ta nemi ganin kande, seda ta kai minti goma atsaye sannan mai gadi ya dawo yace ta shiga, godiya ta mishi sannan ta shiga da sallama, 6angaren yan aiki ta nufa, a tsakar gidan ta taras da kande tana sallamar wasu mata da alama abokan aikinta ne na cinikayya, gaisar dasu Noor tayi sannan ta samu guri ta zauna, bayan kande ta sallame su ta dawo kusa da inda Noor take ta zauna tana mata kallon raini, seda tayi me isarta sannan tace yadai meke tafe dake, wani gaisuwar Noor ta sake mata sannan ta mata bayanin abunda ke tafe da ita, zannuwan ta kar6a atamfofi ne masu kyau guda uku wadanda da gani zasu haura dubu bakwai bakwai tana dubawa seda ta dauki kusan minti sha biyar tana dube-dube sannan tayi musu kudi tayin walakaci wai dubu biyar, kallonta Noor tayi tana mamakin irin wannan rashin tausayi da zalunci, hawayen da ya zubo a idanunta ta goge sannan tace, Allah yayiwa kudin albarka ki kawo nagode, ta fadi hakanne saboda tarasa me ma za tayi da babu gwara ba dadi kannenta ne damuwarta indai zasu samu suci na dan kwana biyu kafin ta nemi wani abunyi ai babu damuwa, kande kuwa tausayin yarinyar ne ya kamata tabbas itama tasan babu wanda ze yarda ya saida zannuwannan ahaka, tashi tayi ta dauko dubu goma ta bata, kirgawa Noor tayi taga sun haura hakan seta dago ta kalleta tana neman karin bayani, murmushi tayi mata tace bakomai taje dasu domin hakanma wasu bazasu yarda ba tunda sabon sanine har yanzu yana cikin yayi, godiya Noor tayi mata sannan ta nufi hanyar gida tana me cike da farin ciki, raba kudin tayi gida uku tasa daya a rigarta daya kullun azaninta daya kuma ta rike ahannu, ba zato ba tsammani taga wasu kartai sun zagaye ta kowanne acikinsu babu annuri atare dashi, kallonta suke kamar sabbin mayu, budawa su kayi taga wani atsaye amma fuskarsa na kallon yanma, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta, babu abunda ta keyi se adduar neman tsari daga sharrinsu.Agida kuwa duk atakure suke akan rashin sanin inda Noor take, gashi takai kusan awa daya bata dawo ba sannan bata sanar dasu inda zataje ba kuma sunga ta fita cikin damuwa ga kaya ahannu, a iya saninsu dai bata irin haka duk inda zataje seta danar dasu saboda kar suyi ta nemanta, ganin shurun yayi yawa yasa mimi ta fara kuka tana cewa su nemo mata Yaya Noor, gaba dayan su hankalin su atashe yake bama kamar Nusaiba ta rasa ya za tayi da kannen nata...


♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻уσвє*
*♣gαι∂αм*Bangaren Dr Affan kuwa koda ya koma gida ya fita bai dawo ba sai wajen yamma, wayarsa kuma a gida ya barta saboda ya samu chaji.


Koda suka koma cikin gidan haka sukayi ta kiransa har suka gaji kowa ta wanke fuska duk sun cika da haushi.

"Toh kawata in kuma shima wajen budurwara yaje fa yakenan?" ta fada tare da tsurawa Hadiza ido.


"Haba Ghaji dan Allah karki 6atan rai mana,mai makon ki kwantar min da hankali kuma ke kike kokarin dagamin gaskiya ba naso kuma banji dadin hakan ba".
ta fada tana 6ata rai


"Yi hakuri kinji bazan sake ba amma in akwai taya zamu magance lamarin kikega? amma dan Allah ki kwantar da hankalinki ta abokin yaya Sule" tayi maganar cikin tsigar wasa don sanyaya ran kawar ta ta.


"Hmmm Ghaji kenan ai kibari zan iya yin komai indai har akan handsome ne domin kuwa sonshi yayi nisa a zuciyata ta yanda bana majin kira, gangar jikina shi suke muradi, ruhina kuma saida shi zai samu nutsuwa, kedai ki tayani addua amma ina me tabbatar miki da cewa bazan bar kowata mace ta sameshi ba inhar nima bazan same shiba, yamma nayi tashi in rakaki gida" tafada tare da mikewa tsaye.

Ghaji kuwa kallon ta takeyi tana nazarinta "wato fa da iya gaskiyar ta take magana zata iyayin komai lailaikam dole ta tayata da addua wannan wani irin sone?" ta fadi a ranta tare da mikewa tsaye ta dau gyalenta suka fita waje tayi wa inna saida safe kafin suka dau hanyar fita daga gidan kowa da abunda take tsakawa aranta game da wannan lamarin,bama kamar Ghaji da take hango irin matsalolin da ze auku domin akwai chakwakiya a wannan abu..Sule kuwa sai wajen la'asar ya tafi koda ya koma bai wuce gida ba ya tsaya a majalisa don adama dashi, sai wajen magariba ya shiga cikin gida alokacin shima Dr bai dade da dawowa ba, tare suka jera suka fita sallah a masallacin kofar gidansu..Koda suka dawo gida Dr bai bi takan wayarsa ba sai bayan da su kayi sallar ishai su kaci abinci sannan ya dau wayar don hawa facebook,yana budewa yaga 30miscal 25 nawata sabuwar number biyu na Sule daya na Aisha sabuwar kawarsa ta social media sauran biyun kuma na wata kanwarsa,bai bi takan sauran ba ya fara kiran sabuwar numbern don miscal din sunyi yawa Allah dai yasa lafiya,koda yakira sau biyu ba'a dauka ba se bai sake kira ba, ya kira kanwarsa suka sha hira sannan ya kira kawarsa Aisha itama suka dan labarta kafin ya sake dialing sabuwar numbern nan, kira daya aka dauka sai baiyi magana ba jin muryar mace "hello! hello!!" shine abunda take ta fadi,shi dai a iya sauraronta da yayi ya kasa gane muryar nata kawai sai ya kashe, yana kashewa ta kira har kamar bazai dauka ba sai kuma ya dauko "hello kana jina kuwa? "eh ina jinki, wake magana dan Allah kuma daga ina" sautin murmushin ta ya fara ji kafin tace "Hajja Hadiza ce kanwar budurwar abokinka yaya Sule ta unguwar ...." "okay nagane ya kike yasu maryama? "lafiya kalau ya aiki ai nayi ta kira dazu da naji shuru nace kila kanagun antin mu!" "eh chan naje" ya fada a takaice don har ya fara gajiya da surutun ta "okay shikenan dama na kira mu gaisa ne kayi saving numbern dan Allah" tafada kamar za tayi kuka jin cewa yana da budurwa "toh zanyi ki gaida maryama saida safe" bai jira amsarta ba ya kashe wayarsa gaba daya,yayi wulli da wayar sannan ya kwanta..

          
Itama a nata 6angaren wulli tayi da wayarta duk da cewa bata kashe ba tayi kwanciyarta tana mai bakin cikin cewa yanada budurwa kila koh ta fita kyau ko kuma ita tafi budurwar kyau, kai bazama ta fita ba ai itama kyakyawace komade meye bari zuwa gobe zata je gun Ghaji susan abunyi don kuwa babu mahalukin da ya isa ya mallaki Sale ita kuma bata mallaka ba kai karya ne bazai sa6u ba wai chacha a idi..

*Akwai sauran kallo*🤣🤣

Post a Comment for "YAR ALMAJIRA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...