Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMARNIN SAURAYI CHAPTER B KARSHE

UMARNIN SAURAYI CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 UMARNIN SAURAYI CHAPTER B KARSHE


Bayan ta ƙaraso ta gaishe da Abba da Mama amma bakowa ne bai samu damar karɓa mata ba sai ma tambayar da suka jefa mata.+

Abba yace, "Safiyya ashe kin san halin da ƴar uwarki take ciki amma kika kasa faɗa mana?".


Tace, "wani hali Abba....!


Ai bata kai ga k'arasawa ba ya daka mata tsawa haɗi da faɗin.


"Ki bani amsar tambayar dana miki?".Jikin ta na karkarwa tace, "Abba kayi haƙuri amma ni ban san wane hali take ciki ba".


Mama ce tace mata, "baki san tana ɗauke da ciki ba ne".


Aikuwa Mama na rufe bakin ta, Safiyya ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kana tace.


"Wallah Mama ban sani ba".

tana faɗa tana kuka.


Abba ne yace.

"Ba komai Safiyya kuma ina fatan baki biyema halin taba?kuma daga yau narabaki da ita kada ta koya miki mugun halin ta, kuma kisani wallahi bazaki zauna min a gida da wannan ciki ba, dan haka ki tattara kayanki ki koma wurin wanda yayi miki ciki na bar masa ke har abada, dan wallahi daga yau na cireki daga cikin zuri'a ta, kuma bari kiji minti biyar na baki ki tashi ki barmin gidana ko na illataki" .

yana faɗin haka ya shigewar sa ɗakin sa.Kuka mai tsanani Hafsat keyi kamar ranta zai fita,rasa bakin magana tayi dan gabaki ɗaya kalaman sa sunyi mata tsauri.


Ko Mama abunda Abba yace yayi mata zafi kuma tasan tunda ya furta to ba abinda zai canja,dan haka taja bakin ta ta kulle amma zuciyar ta na mata zafi.


Safiyya najin abinda Abban Hafsat yace dan haka da gudu taje gida su ta zo da Baban ta.


Tace masa ga Abban Hafsat can ya kore Hafsat.


Safiyya na fita sai ga Abban Hafsat ya fito a ɗakin sa,kallon Hafsat yayi haɗi  da antaya mata harara kana yace, "bazaki tashi ki barmin gidana ba?".


Kafin tayi magana Marwan da Ammar suka fara bashi haƙuri,magana yafara musu cikin faɗa yace, "bari ma kuji wallahi duk a cikin ku duk wanda ya taimaka mata ko da bayan idona ne to banyafe ba". sai Mama tace, "a'a ka dai ce ta bar maka gidanka amma ba ruwanka tsakanin ta da ƴan wuna ta, kuma tabar maka gida taje ina Abbansu?, komai zakayi yana da kyau ka dubi gaba dan komu muna da namu laifi....kafin ta rufe bakin ta  ya daka mata tsawar da tasa tayi shuru bata shirya ba.


Duban sa ya kai ga Hafsat yace,"ki tashi kibarmin gidana kafin nasa afitar dake".


Ahankali ta tashi ta fara tafiya har ta kai ɗakin ta,kayan ta ta haɗa gabaki ɗaya ta fito tana kuka mai cin zuciya,kallon ta Mama tayi tace, "kinga abinda kika jama kanki kika kuma jamin dan haka......Abba ne yafito yace Mama tayi masa shuru kana ya dube Hafsat yace, "fita ki barmin gidana" yana faɗa yana nuna mata ƙofar fita.


STORY CONTINUES BELOW

Kuka take kamar ranta zai fita,   ta kama hanyar fita Mama ta dube Abba tace, "yanzu barin ta zamyi ta tafi? to ina zata je?".


Sai Abba yace, "tafiki sanin inda zata je" yana kawai nan ya koma cikin ɗakin sa.


Gabaki ɗaya kannen ta kuka suke lokacin da zata fita,har ta kawo bakin ƙofa sai ga Safiyya da Baba ta sun ƙaraso da sauri Safiyya ta ƙarasa wajanta tana faɗin, "ina zakije haka da kaya?".Tace, "Abba ya koreni yace na bar masa gidan sa,...Baban Safiyya ne ya katse musu magana yace Safiyya taje ta kiramasa Baban Hafsat.


Shiga tayi tafaɗa masa ba jimawa ya fito fuskarsa haɗe ba alamar fara'a.

Bayan sun gaisa da Abban Safiyya sai Baban safiyya ya faɗa masa abunda Safiyya tafaɗa masa tace ya kore  Hafsat shin ko gaskiya ne?.

Bayanin da  Safiyya tayi masa to shi Abban Hafsat yayi masa kana yace, "wallah bazata zauna gidana da cikiba,Alhaji Abbakar minene banyi ma Hafsat da har zata saka min da cikin, wallah bari gaji yanzu ko ganin ta bana sonyi, gabaki ɗaya Abban Hafsat ya rikice duk yadda Baban Safiyya yaso yayi haƙuri Abban Hafsat yaƙi,kunsan abu ga mai haƙuri idan ya tashi bai iya ba.


Da Baban Safiyya yaga Abban Hafsat yaƙi haƙuri sai yace, "tunda kace bazata zauna gidan kaba to ni zan ɗau Hafsat ta zauna gidana har nayi mata aure.....tun bai kai da rufe bakin shiba sai Abban Hafsat yace, "kada kasoma kace zaka haɗeta da ɗiyan ka dan zata lalata musu tarbiya".


Sai Baban Safiyya yace, "naji kuma na ɗauka Allah ya shirya min su gabaki ɗaya" rigima sukayi sosai da Baban Safiyya kafin su rabu.


Baban Safiyya nafitowa falon Abba dube su Hafsat yayi yace,"ko zo muje gida" yana faɗin haka ya kama hanyar gida sa ranshi a ɓace.Suna isa gidan su Safiyya sai Baban Safiya ya kira Ummar Safiyya ya faɗa mata abunda ake ciki kuma ya shaida mata cewa Hafsat nan gidan zata ci gaba da zama har Allah ya sauke ta lafiya kuma  ya kawo mata mijin aure.


Aikuwa Ummar Safiyya najin ace Hafsat zata dawo gidan da zama ta fara kumfar baki tana faɗi, "itakam gaskiya baza'a kawo mata Hafsat a gida ba salon tazo ta lalata mata tarbiyar yara,wallah bazata yarda ba" sai da ta kai ƙarshin zanci sai Baban Safiyya yace,"wallahi ba wanda ya isa ya hana Hafsat zama ana gidan, nan ya dinga ci mata mutunci har yace idan tasake cewa Hafsat bazata zauna gidan ba bakin auren ta,ba shiri ta kama bakin ta,Safiyya yace da ita suje ɗakin ta su cigaba  da zama ita da Hafsat,ba musu suka je ɗakin.
Bayan kwana biyu da faruwar haka gabaki ɗaya Hafsat bata da natsuwa, gashi ko fita batayi kuma ko takira shi a waya baya ɗauka.


Kuma yanzu ko barci take mafarkinsa take, ko me taki tunanin sa take, gabaki ɗaya ta koma wata iri gashi Ummar Safiyya da ƙannen ta har ma da yayun ta duk sun tsane ta abu ka ɗan sai Ummar Safiyya ta dinga yimata faɗa, sosai abun ke ɓata mata rai amma sai ta dake ma zuciyar ta saboda irin yadda Safiyya da Baban ta ke nuna mata amma daba dan suba da tuni ta bar gidan .

Yau ma kamar haka  suna kwance da dare dan har bacci ya ɗauke su tana cikin bacci taji kamar antsaƙure ta,da sauri ta zabura ta tashi,komai bata gani ba, lokaci ɗaya  taji tana son taji koda muryar sa ce dan haka ta ɗau waya ta kira koda Allah zai sa ta samu.


Missed call biyar tamasa amma bai ɗauka ba,har taso ta aje wayar ta kwanta sai tace bari ta koma kira,aikuwa tana kira ringing  da bai wuce uku ba ya ɗaga tare da faɗi, "wake magana?".


Toilet ɗin dake ɗakin ta shige kana tace, "Hayat nice fa,baka ganeni ba?".


Yace, "oh nagane shin kece?lafiya dai ko?".


STORY CONTINUES BELOW

Tace, "eh kodama nakirane naji ko lafiya kake?".


Yace, "eh ƙalau nake"...har zai katse kiran tace Hayat kayi haƙuri nasan ko dan mi kake fushi dani amma in har nasamu fita zan zo dan nayi missing ɗinka sosai, kuma kayi haƙuri ka yafemin idan na ɓatama"......tana faɗi tana fitar da ƙwalla.


Gajiya yayi da surutun ta dan haka ya datse kiran batari da yaji sauran zancin ba,daga baya ta lura da ya kashe wayar dan haka taci gaba da kuka dan gani take kamar ta aikata babban laifi fushin da ya keyi da ita.

Washi gari baya sungama aikin su na gida ita da Safiyya sai Mamar Safiyya ta shirya tafita unguwa ta barta daga ita sai Safiyya tace sai ta dawo.


Fitar ta ba da jimawa ba Safiyya ta kwanta barcin rana,aikuwa Hafsat naganin haka taje tayi wanka ta shirya cikin hanzari ta bar gidan, tana fita ta tsayar da mai napep ,basu tsaya ko ina ba sai  gidan sa, kuɗi da suka rage mata taba mai napep kana ta shiga gidan.


Parlour  tasame shi yana waya, da sauri ta ƙarasa jikin sa tana faɗi, "Missing you Hayatee nah".

Yana jinta jikinsa ya ɗago ya kalle ta haɗe da katsi wayar da yakeyi, dan jinta kawai yayi dan har taso ta bashi tsoro,har ya buɗe baki yayi magana ta haɗe bakin ta danashi tana kissing ďinshi kamar tasamu lolipop,lokaci ɗaya ya fara karɓar saƙon da take aika masa, martani yafara mai dama ta sannan yafara  ƙoƙarin rage mata kayan jikin ta,

bayan ya cire mata ya fara romance ɗinta son ranshi,daukar ta yayi ya kai bedroom ďinsa daga can yafara sarrafata  yadda yake so,dan kowane  buƙace yake da wani.Sosai hankalin Safiyya ya tashi, lokacin da ta farka bataga Hafsat ba dan ta ɗauka ko guduwa ne tayi sabida abinda mamar take mata,sai da taga kayan ta hankalin ta ya ɗan kwanta.

Tunani tafarayi to ina Hafsat ta tafi ne tasan ba gidan su tajeba .Shiko ya samu jaka sai yadda yaso yakeyi da ita,tagaji iya gajiya amma takasa buɗe baki tace ta gaji,sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.


Sai da suka ɗan huta ta ƙara shigewa jikin sa,a hankali ta buɗa baki ta fara faɗa mishi abinda ya faru da ita,sannan ta ƙara da cewa, "Hayat ko na ɗauko kayana na dawo nan da zama zan fi samun natsuwa bisa ga inda nake".

Sai da ya kalle ta kana yace, "a'a kada ki dawo dan nima ko wata bazanyi garin nan ba zan koma garin mu dan nagama aikin dana zo yi".

Kuka ta fara masa wai zata bishi garin su,bai kulata ba yaci gaba da abinda yake so da ita.


Roƙon sa tayi ya barta taje gida amma yayi kamar bai jita ba,sai can yace taje ɗin kuma gobe ta dawo.

Wanka kawa tayi ta sanya kayan ta tafito,roƙon sa tayi ya bata ƙuɗi ta hau napep,sai da yagama jamata aji kana ya ɗauko dubu ɗaya ya bata yace taje.Taci sa'a koda ta dawo mamar Safiyya bata dawo ba Safiyya kadai ta isake a tsakar gida tana safa da marwa.Kallon ta Safiyya tayi tace, "daga ina kika fito?".

Bata karɓa mata ba ta shige ɗaki ta barta tsaye,ɗikin Safiyya tabi ta tace, "dake nake magana kinyi min shuru"


sai Hafsat tace, "mi zance miki to, fita nayi ko so kike na faɗamiki inda naje,to ba aikina kikayi ba bare na faɗa miki"  tana magana tana antaya mata harara.

Komai Safiyya bata sake cewa da itaba dan tasan ba ida taje sai gidan shegen saurayin ta kuma ta ɗau alwashin sai ta ci mutunci sa duk ranar da ta ganshi.Ko da dare yaya ba wanda yayi ma ɗan wunsa magana har  suka zo kwanciya ,Hafsat a tunanin ta Safiyya bacci take dan haka ta ɗau waya ta kirashi,bayan ya ɗauka ta gasheshi to fa nan suka cigaba da fira amma mafi yawan firarsu ta batsa ce,hirar ce ta dame Safiyya wai a ce ƴar uwar ta ke wannan firar dan haka ta farar kuka har da shisheka, kukan Safiyya da Hafsat taji ne yasa tayi sauri ta katse wayar kana tace, "Safiyya lafiya kike kuka?".


Kyaleta Safiyya tayi dan abin nan na Hafsat yanzu tsoro yake bata, a ce har mutum yayi sanadiyar barin ka gidan iyayenka amma ka kasa barishi wannan wani irin so ne,tana kuka tana tunani cikin zuciyar.


Jin da tayi Stuna in bata amsa mata ba yasa ta ƙaraso wajan ta hawayen da suka Zuni matane ta goge tace, "My Safiyya kiyi haƙuri nasan dan kinji wayar danakeyi ne kike kuka,wallahi Safiyya koni zuciya ta na ƙuna abinda nakeyi dashi amma ya zanyi dan wallahi bani da natsuwa duk banji shiba ko bantare dashi ba, nidai abinda nake so dake kiyi min addu'a kada na mutum ina cikin wannan hali kinji ƴar wuta".

Jikin ta Hafsat ta faɗa gabaki ɗayan su kuka suke mai ciki da kunar rai.

Haka Hafsat taci gaba da zama gidan  su Safiyya   har aka kuma hutun makarantar su amma duk ranar da tasamu damar fita sai taje wajansa,itako yanzu Safiyya da dare yayi take tashi kuma ta tashe da Hafsat suyi alwala sufara nafil-fili suna kai kukan su ga Allah.

Kuma cikin ikon Allah yanzu Hafsat tarege jin soshi a zuciyar ta sosai.


Bayan sun koma makaran ta da kwana biyu ranar Safiyya na zaune class ɗinsu sai ga wata ƙawar ta tazo wajan ta kuma ƙawa ga Hajara dan abinda yasa Safiyya ta barta saboda taga ko ina Hajara take itama tana can danshi ta bar ta...

Bayan sun gaisa sai ƙawar ta Ummi tace,"ina Hafsat kwana biyu na daina ganin ta?".


+

Sai Safiyya tace, "tana nan lafiya".

Sai Ummi tace, "kice dai da dama,wace lafiya ne da ita tana ɗauke da ciki".


Sai Safiyya ta haɗe fuska kana tace, "wani ciki?" tana faɗa tana hararar ta.

Sai Ummi tace, "Safiyya bari kiji wallahi ba abinda zaki ɓoye min gami da Hafsat wanda ban sani ba, tun farkon haɗuwar ta da Anwar har cikin da yayi mata ba wanda bansani ba,ni dai shawara zan baki dan naga irin cin zarafin da yakema Hafsat yayi yawa, shiyasa na yanke shawar nazo na faɗa miki abinda ake ciki dan ki nema mata mafita,amma idan zaki sau rareni, dan nasan haliki na rashin kulani shiyasa tun wancan lokacin ban faɗa miki ba amma mikika ce zaki saurareni ko yaya?".

Murmushi Safiyya tayi mai ciyo kana tace, "ina jinki ki faɗa min".


Sai Ummi tace, "komai na faɗa miki kiyi haƙuri dan nasan zakiji zafi sosai".


"Kifaɗa ina jinki"....tafaɗa haka ataƙaice.Sai da Ummi ta numfasa kana tace, "zaki iya tuna lokacin da Hafsat tasamu saɓani da Anwar? har ta ji ko ganin sa bata sonyi,to ba komai bane ya kawo haka sai rabata da mutuncinta na ƴa mace   da yayi, ta hanyar samata maganin da zai gusar da hankalin ta,ita ko tundaga lokacin ta daina kulashi,ince ma har wajanki ya zo amma kika kasa shawo masa kan Hafsat,to da yaga yaki samun nasara gareku sai yaje gun Hajara ya faɗa mata abinda yake so tayi masa,ita ko Hajara da son kuɗi tace zatayi masa,to fa tundaga lokacin Hajara tafara bibiyar Hafsat har tasamu ta fara kulata har tayi nasarar rabaki da ita, to fa lokaci ne Hajara ta fara yimata magiya kan ta yarda su shirya da Anwar amma Hafsat taƙi,to da Hajara taga Hafsat ta faye kafiya sai kawai ta kaita wajan wani malami ta faɗa masa abinda take so yayi mata,bayan yayi mata aikin da zai sa ta yarda da Anwar, kuma duk abunda yasa ta bazatayi masa musu ba,anyi kuma aiki yaci dan komai sai Anwar yace Hafsat keyi takeyi , koda kowa uwar  ta ce tace tayi in har Anwar bai yadda ba bazatayi ba,ya maida ta kamar matar sa, sai yadda yaso yakeyi da ita kuma ba wai dan baya son ta bane a'a yana son ta sosai sai dai yanzu yace bazai iya auren taba saboda taki yarda azubar da ciki,dan haka nake son kije ki nemar mata makarin abinda sukayi mata ko zata samu sauƙin abunda ke damunta".


Hawaye masu zafi ke fita daga idon Safiyya,kallon Ummi tayi tace, "yanzu Ummi kin san komai amma kika kasa sanar dani,ashe bason Allah kikemin ba, dan da son Allah kikemin da kin faɗamin abinda kika sani gami da ƴar uwata".


Ummi tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi koni bansani ba sai daga baya,saboda yanzu ita Hajara ta kamu da son Anwar kamar ta mutu shiko yace ko zaman bariki ba zai iyayi da ita ba, bare har ta kai ga aure,to lokacin ne Hajara ke bani labarin yadda tayi sanadiyar soyayyar su da Hafsat".


Kuma wallah nasan yanzu ko kashe Hafsat  Hajara na iyayi akan Anwar,dan haka ku ɗau mataki" ...tana faɗa tana tashi tace,


'Kinga tafiya ta dama nazo ne na faɗamiki saboda har gobe kina matsayin masoyiya ta, dan haka sai anjima".....tana faɗa tana tafiya.


Magana Safiya take so tayi mata amma  saboda biƙin ciki kasa buɗe baki tayi sai kukan da takeyi kamar ranta zai fita.


Ko lecture basu gama ba Safiyya taje wajan Hafsat tace tazo suje gida.


Hafsat tambayar Safiyya lafiya zasu je gida kuma gashi ko locture basu gama ba,Safiyya nuna mata tayi suje gida dan ita ko natsuwa bata da,ita ko Hafsat ta kafe bazata jeba,kuka Safiyya ta sanya ma Hafsat tana faɗi sai sunje,kukan da Safiyya keyi ne yasa Hafsat jikin ta yayi sanyi ta yarda zata bita suje gida amma ba dan ranta yaso ba, dan taso Safiyya ta tafi ta barta dan tanaso idan tagama lecture taje gidan Anwar.


Bayan sun fita school ďin suka tsayar da mai napep  Safiyya tagaya masa sunan unguwar da zai kaisu,kallon ta Hafsat tayi kana tace, "ina zamuje ne?".

Safiyya batayi mata magana ba har suka kai inda zasuje.


Bayan sun sallame mai napep kana suka shiga wani gida da sallamar su,bayan an karɓa musu,suka gaida wata tshowa, bayan ta karɓa sai Safiyya tace, "lnna ina Malam?Allah dai kasa baiyi nisaba?".

Sai wadda ake kira da lnna tace, "a'a yana ɗakinsa,mikika kawo masa dakike neman sa".


Bata bata amsaba ta wuce ɗakin malam.


Bayan sun gaisa da Malam tayi masa bayani abinda ya kawo ta gami da Hafsat,tana masa bayani tana kuka,sai Malam yace, "ki daina kuka Safiyya,insha Allah komai yazo ƙarshe".


Magani ya haɗa mata dana hayaƙi dana sha harda na wanka ya bata zaitun da habba yace ta rinka shafawa duk lokacin da tayi wanka.


Godiya tayi masa sosai sannan ya tambayeta Mamar ta tace lafiya ƙalau suke.


Har zasu fito daga gidan Malam ya ɗauko husunul musulim ya basu ita da Hafsat yace ko wace safiya surinƙa karatunsa,kana yayi musu faɗan da suriƙa addu'o i nema kariya ako wace rana.

Sallama sukayi masa kana suka wuce gida.Tundaga lokacin suka cika gaba da yimata magani ba dare ba rana, kuma duk abin nan da ake Mamar Safiyya bata san mike faruwa ba,duk da iyayenta ne keba Hafsat magani amma bai sa tasani ba.Kuma cikin ikon Allah yanzu  abin yayi ma Hafsat sauƙi sosai, dan yanzu har kiran ta yake amma ba ko da yaushe take ɗauka ba kuma yanzu so yake tazo suyi bankwana dan satin nan zai koma gida.....

__________📖* Ko yau suna zaune a ɗakin su ita da Safiyya suna fira sai wayar ta tafara ringing,duba saman secreen ɗin wayar tayi,Hayateenah taga ya bayyana,da sauri ta datse kiran kana ta kashe wayar gabaki ɗaya.


Kallon ta Safiyya tayi tace,"hala waya kira kika  datse kiran?".


Sai da taya tsane fuska kana tace, "Anwar ne yake dumuna da kira,amma nasan maganin sa gobe ko yakira ba zai samu ba".


Har Safiyya ta buɗe baki tayi magana sai suka ji Mamar Safiyya na ƙwala musu kira.

Da sauri Hafsat tace "ga Mama can na kiran mu kitashi muje".......tana faɗa tana tashi tsaye.

Suna ƙarasowa sai da Mama tayi ma Hafsat wani kallo kana tace, "ga wankin yara can ki ɗauka kiyi har da na Yayan su dan shima yace ki wanke masa kayan sa,kuma saura kada ki wanke ya fita".


Tace' "tau Mama zanyi da kyau".

Duban ta ta maida ga Safiyya kana tace,"ke ko je ki shirya zan aikeki gidan su lnna"....mahaifiyar Mamar Safiyya kenan.

Tace, "tau Mama bari mu ɗan  rage wankin nan sai natafi".

Ai tun Safiyya bata kai da rufe bakin taba Mama ta daka mata tsawa wadda bashiri ta rufe bakin ta.


Hafsat tafiya tayi wajan tulin wankin da ke zobe a ƙasa ta ɗauko ta kai bakin fanfo ta ɗauko kujera dan ta zauna dan yanzu bata iya wani dogon duƙe,aikuwa tun ba takai da zama ba Mama ta daka mata tsawa tari da faɗin, "kada ki zauna kiyi shi a haka,salon ki zauna kiyi min wankin da bai fita ba?".


Sai da Hafsat ta goge hawayen da suka zuba a idon ta kana tace, "wallahi Mama bana iya duƙi sai naji marata ta kulle, dan Allah ki bari na zauna zan fi jin daɗi....ai tun bata rufe bakin ta ba sai ga Abbas Yayan Safiyya ya fito daga ɗakin sa yana faɗin,


"Oh Mama ce zata faɗa kina faɗa?dan baki da kirki baki da tarbiya,ashe rashin tarbiyarki ba wajan bin maza ta tsaya ba harda ciwa manya mutun ci?".


Safiyya na ɗakin su taji duk abinda ke faruwa har lokaci da yayan ta kema Hafsat faɗa,abinda taji  ya faɗane yayi mugun ƙona mata rai dan haka bata san lokacin da ta fito ba.


Cikin hanzari tafito d'akin su tana faɗin, "wallahi Yaya kaima baka wuce k'addar da tasame Hafsat ba, da har zaka buɗa baki kayi mata faɗe....... ba ta kai da rufe bakin ta ba taji saukar mari har guda biyu wannda ya gi-gita ta lokaci ɗaya..

Ba ta kai da dawowa hayyacin taba tafara jin saukar duka ta kowane fanni na jikin ta.

Dukan ta yake yana faɗin, "ni zan faɗa kina faɗa ehh?".

Ilata ta taga zayi dan haka da gudu ta yi hanyar d'akin su.


Tana shiga ta kulle ɗaki kana taci gaba da kuka tana mai tausayawa Hafsat.


STORY CONTINUES BELOW

Koda yaje d'akin yaga ta kulle dan haka ya dawo wajan Hafsat,ita ko tunda taga abinda yayiwa Safiyya  ta duk'a haka nan  ta fara wanki tana jin ba daɗi ajikin ta.

kallon ta yayi yace, "wallahi minti kad'an nabaki ki kammala Kuma duk basu fita ba hmmmmm Allah kad'ai zai karb'arki a gidan nan"......yana fad'a yana ficewa a gidan gabaki d'aya.


Haka nan Hafsat taci gaba da wanki tanayi tana share hawaye,sosai ta wahala kafin ta kammala,kuma tana kammalawa Mama ta hadata da wanki-wanke da shara da aikin abin ci,aikuwa tana kammalawa sai zazzab'i ya rufeta,sai da Safiyya ta lallab'a taje wani pharmacy ta karb'o mata magani.

Haka dai ta kwana a wannan ranar wahalce.


  ******


Yau Monday rana school ce kuma babbar rana ce ga y'an makaranta kowa ne ɗan makaranta burinshi yaga ya isa cikin school d'insu cikin lokaci.

Safiyya ce tafito daga d'akin su ta same Hafsat kichen tace, "Hafsat wai mekikeyi a kichen kuma kinsan muna da lecture k'arfe ta kwas kuma yanzu 8:30 gashi ko shiri bakiyi ba,to har yaushe zamu kai school d'in?".


Tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi Mama ce tasani d'aurama yaran can ruwan wanka kuma gashi wutar ma tak'i ru-ruwa".


Sai Safiyya tace, "kitashi kije ki shirya sai na k'arasa kafin ki fito sunyi zafi".


Tace, "tau Safiyya"..... tana faɗa tana tashi.


Har zata shiga ban d'aki ta watsa ruwa sai ga Mama ta fito daga d'akin ta.


Magana ta fara mata cikin faɗa-fad'a "me zakiyi a ban d'aki? ba aiki nasaki ba ne?".


Har zatayi magana sai ga Baban Safiyya ya shigo gidan.


Kallon Mama yayi da Hafsat dake tsaye yace, "lafiya na ganko haka cirko-cirko?".


Sai Mama tace, "aki nasakata shine taki tayi min".


Sai Baba yace, "amma kin san yanzu lokacin makaranta ne kuma zaki sata aki salon su makara,to bawani aikin da zatayi sai tadawo makaranta"......yana fad'in haka yace Hafsata tayi sauri ta shirya su wuce makaranta.


A gurguje ta shirya dan ko beark bata yiba suka Kama hanyar school d'insu.


Takwas saura minti biyar suka isa makaranta,kai tsaye kowa class ɗin su ya wuce, aikuwa bata jima da shiga ba sai ga malamin su yashigo dumin su fara karatu.Basu jima da fara karatu ba sai ga sak'o yazo daga office d'in sugaban makaranta, bayan d'an sak'on yayiwa Malamin bayanin abinda aka aikoshi na kiran  d'aliban da aka umarce shi,malamin ya bada izinin a kira su,nan kowa ya fara kiran su,kuma daga cikin su Harda Hafsat a ka kira.


Bayan ankira sunan su aka umarce su da suje office d'in sugaban makaranta acan ake neman su.


Aikuwa ana faɗin haka gaban Hafsat yayi mummunar fad'uwa, lokaci d'aya wasu hawaye suka fara zoba a idon ta,tunani tafarayi ko korar ta za'ayi sabida batayi jarabawa ba ko sunji labarin tayi cikin shege ne?aikuwa tana kawowa nan a tunanin  ta fashe da kuka mai k'unar zuciya, kuma gashi ba mace a cikin wad'an da aka kira dukan su maza ne bare ta samu sauk'in abinda take ji.


Haka taci gaba da biyar su har suka kai office d'in sugaban makaranta.Gaban tane ya ba da dummmm lokacin da za su shiga offece ɗin,amma ta dake ma ranta had'i da addu'a kana ta shiga.


Office d'in cike yake da malamai har ma da waɗan da ba malaman makarantar ba,sukuwa d'alibai wanɗa da aka kira suna gyefe d'aya suna jiran a fad'a musu abinda yasa ake kiran su,ma fi yawan su maza ne,dan mata ba su wuce uku ba,wajan da mata suke ita ma nan tazo ta tsaya.


Bayan zowan su da mintuna ƙalilan sai shugaban makaranta ya fara jawa bi.


Bayan ya kammala abinda zai ce kana ya mai da duban sa ga d'aliban da suke tsaye yace, "ba komai yasa muka taraku anan ba,sai dan wani abin farin ciki da ya samemu Kuma ya same ku,amma ga wanda yaji yana so ko iyayen shi za subar shi,Wannan abin farin cikin shine gwamnati ce ta ba  da  scholarship ga ɗalibbai mafi hazaƙa kuma waɗan suka ci jarabawa,  suje k'asa she daban-daban suyo karatun master,amma bamu ce dole sai kaje ba, a'a in kana da ra'ayi kuma iyayen ka za su barka to muna maka barka da zowa,Inma baka da ra'ayi ba komai sai kafad'a asa musu son zowa".


"Dan ko wane department zamu d'au mutum biyar mafi ƙwazo a cikin su, kuma waɗan da suka ci wannan jarabawar da ta gudana, amma idan kin san,ko kasan, baza kaje ba ko ba'aza a barka ba to ku faɗamuna,dan haka mun baku kwana uku kuje  koyi shawara da iyayen ku sai kozo ku gaya muna dan bama son lokaci ya kule,dan gabaki daya wannan ta fiyar ba zata wuce sati uku ba insha Allah".


Hafsat najin wannan maganar ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,saboda jin daɗi har da 'yar kwalla ta fitar.


Har suka fara fita bata sani ba saboda ta tafi duniyar tunani.


Wadda ke kusa da ita ta dan ta ɓata sannan ta san me ake ciki.


Da fitowar su cikin office  ɗin,cikin zomud'i taje class ɗin su Safiyya dan ta faɗa mata abinda a ke ciki.


Da zowan ta bata tsaya komai ba ta fad'a jikin Safiyya dan ita har ta manta abinda take d'auke dashi sai da Safiyya tayi mata magana a tsorace tace, "Hafsat! baki gudun kijima kanki ciyo ne?".


Ba sarwa tayi kana tace, "My Sufy tashi kiji wani abin farin ciki da ya sameni,yanzu aka aiko kiran mu a office d'in sugaban makaranta, wallahi na d'auka korana za'ayi dan kin san banyi exmas ba,kinga yadda gabana ke famar dukan uku-uku wallahi har k'walla sai da ta zobo min kafin muje,ashe ba kurana za'ayi ba...... nan ta faɗa mata abinda ya wakana,sosai Safiyya tayi murna dajin har da masoyiyar ta cikin wand'an da zasuje waje suyi karatun master,murna da farin ciki wajan Safiyya ba'ace wa komai dan kamar ma tafi Hafsat jin dad'in abin.


Suna gama lecture basu tsaya b'ata lokaci ba suka wuce gida dan su faɗi abin farin ciki da yasa mesu.


Koda sukaje Mamar Safiya tafita unguwa dan haka suka cigaba da aikin su inyaso da tadawo su faɗa mata.


Sai bayan isha'i tadawo kuma ko da tashigo suna sallah,dan haka kai tsaye ta wuce ɗakin ta.Bajimawa da shigar ta sai suka ji sallamar  Baban Safiyya,dan haka da sauri Safiyya taje ta shin fiɗa masa ta barma haɗi da kawo masa abinci da ruwa.


Dan koda ya shigo Hafsat bata ida sallah ba.


Bayan yaci abinci ya koshi kana Hafsat tazo ta gaisheshi haɗi da ɗauke kwanokan da yaci abinci.


Mama ce ta fito daga ɗakin ta tazo ta zauna saman tabarmar da yake zaune.


Gasheshi tayi kana suka fara taɓa fira.


Safiyya ce tace, "Hafsat tashi muje mugaya ma Baba da Mama abin farin cikin da ya samemu".


Sai Hafsat tace, "a'a kije kigaya musu dan gabana sai dukan uku-uku yake dan ji nake kamar baza'abar ni naje ba........

Safiyya tace, "a'a ki tashi muje insha Allah za su barki". Ba musu ko ta tashi sukaje wajan da Baba da Mama ke zaune,zama sukayi haɗi da gaishe da Mama.

+

Basu jima da zama ba sai ga Yayan Safiyya ya shigo shima inda ya gansu nan yazo ya zauna.


Sai da sukayi ƴan second  Safiyya ta buɗe baki tayiwa Baban ta bayanin abinda ke faruwa.Aikuwa tun bata kai ƙarshin zancin ba sai Mama tace, "tunda muna mahaukwata sai mu barta taje har wata ƙasa karatu ko?ko wannan karatun da takeyi anan gida me tasa ka ma iyayen ta dashi bare yanzu taje wata ƙasa, gaban idon mu ma tayi bare bayan idon mu,dan haka ni ban baka shawara ka barta taje wata ƙasa karatu ba,amma in ka yarda da shawara ta".....tana faɗa tana kallon Baban Safiyya.Tana rufe bakin ta sai Yayan Safiyya yace, "wallahi ba ina da zata je kawai da ta haihu ka haɗata da liman ɗin unguwar nan dan kaga har yanzu bai sake aure ba tunda matar sa ta rasu kaga sai yayi maneji da ita dan inba shi ba ba mai iya auren ta".


Sai da suka gama faɗar abin da zasu faɗa kana Baban Safiyya ya ɗago da kansa ya dube su ɗay bayan d'aya kana yace,"wannan surutun naku bashi zai sa nace baza ta jeba a'a idan nayi ra'ayi na barta taje ba wanda ya isa yahana  taje dan haka kuriƙe shawarar ku har nace zan nemi kubani shawara".


Kallon sa ya maida ga Hafsat kana yace, "naji abinda kuka faɗa amma zanyi shawara zowa safe duk abin da na yanke zan gaya miki" yana faɗar haka ya tashi ya bar wajan batari da ya sake magana ba.


Suma suna ganin ya tashi suka tashi dan sukoma ɗakin su.

Bakin ciki da ta kaici duk ya cika Mama dan shi ko magana ta kasa.


Suna shiga ɗaki ba wanda yayi magana a cikin su har sukayi shirin kwanciya haɗi da addu'a suka kwanta.


Ba jimawa da kwanciyar su wayar ta ta fara ringing amma tanaji ta share sai da akayi mata miss call uku kana ta ɗauko wayar  ta duba taga wake damun ta da kira yanzu da dare,ba ƙuwar number  tagani har taso taƙi ɗauka sai kuma ta ɗauka haɗi da kara wayar a kunnin ta.


Ba'ayi magana ba dan haka itama batayi magana ba, sai can taji ance "Hafsat".....gabanta ne ya faɗi sabida ko a cikin mafarki taji wannan muryar zata shaida ta.

Ƙo ƙarin katsa wayar ta fara sabida gudan kada ya haifar mata da wata matsala.

Kamar yasan abinda take da niyar aikatawa dan haka ya fara magana kamar zayi kuka yace, "Hafsat nasan ni mai lafine amma dan Allah kada ki barni wallahi nasan kin fikowa sanin irin son da nake miki Hafsat,ki taimakeni kada ki barni,kuma wallahi yanzu ashiryi nake da na aureki Hafsat please kada ki barni dan yanzu haka tunda kika barni akwance nake nakasa cin komai I love you My Sweet baby inasonki over"....haka dai yayi ta cika ta daɗan baki har ta fara jin wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta.

Hankali ta ɓuɗa  baki tace, "kana wata magana kamar da gaske, amma kabari gobe mayi magana"..tana faɗin haka ta katse kiran dan ko  magana ƙasa-ƙasa takeyi masa sabida bata so Safiyya ta gane dawa take waya.STORY CONTINUES BELOW

Irin yadda yaji tayi magana ya gane cewa zayi nasara dan haka tana katse kiran yayi wani tsalle haɗi da yin wata shewa mai ciki da jin daɗin samun nasara.


Abukin sa dake kusa dashi yace, "hala anyi nasara da zaka buga wannan uwar shewa?".


Sai da Anwar ya murmusa kana yace, "sosai,dan gobe nasa zata zo nayi yadda nake so da ita inyaso da yamma na bar garin kaga ko baza ta saki gani na ba kuma nima bazan saki tunata ba daga ƙarshe ma na manta da ita".


Sai wannan abukin sa Lawal yace, "shegin kaya kaki fa Anwar,kana yadda kaso da Hafsat wallahi,amma tunda kai ka gama da ita ni mi zai hana ka haɗani da ita ko naji wannan daɗin da kake kwasa  a wurin ta".


Kallon baka isaba ya wurga masa kana yace, "dan kaji nace zan manta da ita, to bari kaji koda ace na koma gada wallahi duk lokacin dana so na kusan ce ta sai ta yarda kai bari kaji in har ban aure ta ba to bawani ɗa namijin da zai aure ta dan banji zanyi iya yarda wani ya kusan ce taba in bani ba".


Sai da ya kai ƙarshin maganar sa Lawal yace, "ai gani nayi kana da Hajara.....aikuwa tun bai kai ƙashin zanci ba ya katse shi da faɗi idan kana so muci gaba da mutun ci kada kasa kiyimin zancin wata Hajara"....yana faɗin haka ya tashi ya shige bedroom ɗin sa dan ba ƙaramin bacin rai yake ba idan aka taso masa zancin Hajara.    ******


Koda gari ya waye bayan sun karya Baban Safiyya ya aiko kiran Hafsat a ɗakin sa.

Da Sallama ta shiga ɗakin sa haɗi da gaisheshi, bayan ya amsa ya dube ta kana yace, "Hafsat jiya nace kibari nayi shawara,to gaskiya nayi tunani akai kuma nayi shawara, dan haka kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki gaskiya bazan iya bari kije ba a matsayena na mahaifin ki kuma mariƙin ki,ba dan komai yasa nace haka ba sai dubin abinda ya faru ne tsakaninki da iyayenki ,kuma babban abinda ya hana na barki shine cikin da kike ɗauke da shi,dan haka kiyi haƙuri idan Allah yace kije nan gaba sai kije idan kuma bai kaddara ba sai kiyi haƙuri,dan ni yanzu burina ki sauka lafiya kuma kusamu miji nayi muku aure ke da Safiyya,dan gaskiya naso na ƙi barinku ku ƙarasa wannan karatun sai kuma naga koda na ƙi barinku to ba aure zakuyi ba dan haka nace da zaran kin haihu zan muku aure keda Safiyya insha Allah".Tunda taji Baban Safiyya yace ba zata jeba gabanta ya bada dummmmm to tunda ga wannan maganar bata saki jin miyake faɗa ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jinkin,sosai maganar sa tasa ta damuwa,amma bata nuna masa ba,sai ma cewa datayi "bakomai Baba Allah ya tabbar muna da alhairi".....tana faɗin haka ta koma ɗakin su.


Inda tabar Safiyya nan tazo ta same ta,Safiyya naganin tashigo ɗaki jikin ta a sanyaye sai tayi saurin cewa, "Hafsat me Baba yace ne naganki a haka?".wayin cewa tayi kana tayi mata bayanin yadda yace mata,tana mata bayani amma sai ta nuna bata damu ba,amma a zuciyar ta ita kadai tasan mi take kiyastawa aciki.Sosai Safiyya taji zafin haka dan da badan tasan halin mahaifin ta da magana ɗaya ba da tasake tunkarar sa.Haƙuri tacigaba daba Hafsat har ta nuna mata ita ko ajikin ta,kuma Allah ne bai nufi tajeba,amma a zuciyar ta ita kaɗai tasan me take shiryawa.


Haka suka cigaba da fira har sukayi aiki suka kammala.

Biyu dai-dai ta shirya zowa school dan biyu darabi Hafsat ke da luctura,ita ko Safiyya yau bata da luctura kuma batajin daɗin jikin ta bare ta raka Hafsat makaran ta,dan tunda taji baza a bar Hafsat taje ba taji jikin ta duk ba daɗi, dan har  ƴar ƙwalla sai da tayi.  Tana sauri tashiga makaranta, ita kuma Hajara zata fito,gabaki ɗayan bata lura da ita ba sai da taji sunyi karu dawani mutum,dan haka da sauri Hafsat ta ɗaga kanta,aikuwa tana ɗaga kanta dan taga dawa tayi karu,waza tagani inba Hajara ba.Gaban tane yayi masifar faɗuwa lokacin da tayi ido biyu da Hajara,Addu'ar neman tsari ta farayi a zuciyar ta,har dai tasamu ta buɗe baki tace , "kiyi haƙuri dan Allah wallahi ban lura dake ba".....tana faɗin haka ta ƙarasa daga cikin makaran ta batari da taji me Hajara zata ce da ita ba.


Ita ko Hajara ranta inayayi dubu ya ɓaci dan haka tayi kwafa haɗi da antaya ma bayan Hafsat wani kallo kana ta wuce.Saura kaɗan tayi late dan tana shiga malamin ya shiga.


Ƙarfe 6:00,dai-dai suka gama lecture,da sauri tafito dan tasamu bus tashiga takoma gida cikin lokaci dan tasan halin Mama ko takoma kan lokaci sai tayi mata faɗa bare ma bata koma ba,amma ina dan tana ƙarasuwa bus ɗin natashi da mutane cike.Aikuwa tana ganin sun ɗaga tabuga wata ubar ƙara haɗi da faɗin "ya Allah!.Gashi mafiyawan mutane sun watsa,amma ya ta iya dole tajira zowan wata bus.Tana cikin tsayin jira bus sai ga wata ƴar budurwa tazo wajan ta wadda bazata wuce sa'arta ba tace, "Hafsat mikikeyi anan har yanzu baki je gida ba".


Sai da Hafsat ta kalle ta haɗi da tunanin ina tasan ta kana tace, "ina jiran bus ne".


Sai wannan budurwar tace, in badamuwa kizo musaukeki dan bus kam ba yanzu ba".


Irin kallon da Hafsat tayi mata ne yasa tace, "nasan haliki baki da yadda,amma tunda bazaki jeba ni zan tafiya ta tunda ke ko ƴan class ɗinku bazaki gane ba".


Sai Hafsat tace, "a'a wallahi,ina tunani idan nasanki ne,amma kiyi haƙuri muje ai nagode ko bakin hanya ne ki sauke ni sai na ƙasa".Sai wannan buduwar tace "har gida sai munkai ki".


murmushi Hafsat tayi haɗi da godiya kana suka tafi bakin wata baƙar motar da akayi picking  wadda ko glass ɗinta baki ne.


Suna karasowa wajan motar  ta ɓuɗe mata murfin motar  tace, "Hafsat shiga".

Gaban tane ya faɗi amma sai tayi bismillah ta shiga.


Tana shiga sai aka rufe marfin da sauri suka tada mota suka wuce batari da wannan budurwar ta shiga ba.


Suna tafiya sai wannan buduwar tayi murmushi kana tace, "Hafsat kenan inkinsan wata baki san wata ba"....tana faɗan haka itama tashiga wata motar ta bar wajan.....

* Mamar Safiyya ce ke kwalama Safiyya kira,da sauri safiyya dake ɗaki tafito haɗi da faɗin, "gani Mama".

+

Kallon ta tayi haɗi faɗin, "har yanzu Hafsata bata dawo ba?tana can ta tsaya wajan shiri-ritar da ta saba kenan".

Sai Safiyya tace, "a'a mama kila bus ce bata samu kan lokaci ba,amma bari nakirita naji ko sun taso"....tana faɗa tana shiga ɗakin ta dan ta ɗauko wayar ta.Koda takira wayar akace mata wayar kashe take,amma duk da haka bata haƙura ba sai famar kira take tana faɗin, "tasan duk wayar ta ba kashe take ba network ne  ,dan haka tace bari ta aja zowa ajima idan bata dawo ba tasake kira duk da tasan tana kan hanya"...tayi maganar ne ita Kaɗai.


Sunanan suna jira har akayi magarb har a kazo da isha'i,kuma gashi duk aka kira wayar ta sai ace kashe take,sosai hankalin Safiyya ya fara tashi dajin Hafsat shuru bata dawo ba.Ita ko Mama sai zoba masifa take wai Hafsat ta tsaya wajan shiriritar da tasaba,sosai faɗan kema Safiyya ciyo dan abin yazo ya haɗe mata waje ɗaya, ga rashin jin Hafsat ko a waya ga masifar Mama.

Mama nacikin wannan masifar sai ga Baba ya dawo gida,nan Mama tashiga yimasa bayani wai Hafsat tun safe da taje makaranta har yanzu bata dawo ba,sosai hankalin Baba ya tashi,aiko yace bai ga zama ba,bari yaje makarantar yagani ko wani abu ya tsaida ta?.


Har zai fita sai Yayan safiyya Saminu yace, "Baba kada kaje ka wahal da kanka, dan nasan ba inda taje sai gidan saurayin ta".....ai tun bai kai da rufe bakin sa ba, Baba yayi cikin sa yana masa faɗa,sai da Baba yayi masa faɗa sosai kana ya bar gidan da sunan yaje ya nemu Hafsat.


Har zai fita ya kwalama Safiyya kira yace tazo sutafi tare dan ita tasan kan makarantar,ba musu ta ɗauko mayafin ta tafito suka tafi.
******


Hafsat na shiga cikin motar, wani mutum wanda bata san ko waye shi ba ya rufe mata baki haɗe da ɗaure mata fuska,dan duk ihu da take ba mai jinta har suka tada mota suka bar  makaranta,Basu tsaya da ita ko ina ba sai wani gidan.


Tunda sukayi packing ɗin motar gaban ta ke famar dukan uku-uku,ina ba ambatun Allah ba ba abinda takeyi a ranta,tanaji suka ɓuɗe marfin motar suka fitar da ita,sai da suka isa da ita parlour gida kana suka kwance mata fuska haɗe da buɗe mata baki.


Aikuwa tana ɗago idonta wazata gani inba  Anwar ba,wani uban zabura da tayi kamar bata ɗauke da komai ajikin ta.


Nunisa da ɗan yatsa ta farayi har tasamu ta ɓuɗa baki tace, "Anwar dama kaine kasa a ɗaukoni?minayi ma Anwar? mikake nema dani?dan Allah kabarni hakanan na huta,wallahi ina cikin gararin rayuwa,wadda sabida kai na faɗa acikin ta,duk abinda kayimin baiyi isheka ba sai ka kasheni ne!to gani kashini,macuci azalumin,kayimin ciki kuma karabarni,sanidiyar ka nabar  iyayena"....ai tun bata kai da rufe baki ba ya wanke ta da mari har guda biyu,wanda lokaci ɗaya ta rasa inda kanta yake.


STORY CONTINUES BELOW

Nunin ta ya farayi da ɗan yatsa kana yace, "waye sa'arki da zaki riƙa buɗe baki kina faɗi masa magana sun ranki ehh?Narabaki da iyayenki kuma yanzu zan rabaki da wadda kika fiso dan haka wallahi sai kinyi dana sanin faɗamin maganar daki kayi" ..yana faɗa yana nuninta da ɗan yatsa.


Waɗanda suka kamuta ya duba kana yace,"koje ko nemunin Safiyya duk inda take,kuma nabaku zowa nan da gobe"....ai tun bai kai da rufe baki ba,cikin hanzari da kaɗuwa da maganar sa tafaɗa jikin sa tana faɗin,"Anwar dan Allah kada kayi min haka wallahi na yarda duk abin da kakeso zamakashi amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,dan Allah na ruƙeka"....tana faɗa tana wani kuka mai kunar zuciya.


Har yaran nasa zasu tafi dan cika umarinin da ya basu sai kuma ya tsaida su yace suji rashi falo zasuyi magana da Hafsat.


Bayan sunfita ne ya dubeta kana yace, "idan har baki son nataɓa lafiyar Safiyya to sai kin yarda da abinda zance,amma idan baki yarda ba wallahi ba makawa sai nasa anɗauko min ita gobe,amma idan kinyar da to ba damuwa".


Kallon sa tayi kana tace, "inaji kafaɗa idan zaniya ɗan".


Yace, "dole ma ki iya,kuma daga yau zaki zauna gidan nan har tsawun sati ɗaya,kuma duk abinda kikasan kina min wancan lokaci zakiyi min shi a yanzu, dan haka idan har kin yarda to amma idan baki yarda ba sai nasa su ɗaukomin ita gobe".Idontane ya cigaba da fitar da hawaye kana tace, "dan Allah  kayi haƙuri Anwar kabarni na koma gida, na yarda sai na riƙa zowa har sati ya cika"....tun bata rufe bakin taba ya kwalama yaransa kira yace gobe su ɗauko mishi Safiyya.Cikin hanzari ta faɗa jikin  haɗi da faɗin, "na yarda Anwar duk abinda kakeso zan maka amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,amma kasani yanzu bani da wata isassar lafiyar da zan riƙa abinda nake maka a da,dan kasan cikin dake jikina baya bani lafiya"....tana faɗa tana share hayen ta.

Wani kallo yake jifa ta dashi kana yace, "yanzu kina nufi har yanzu biki zobar da wannan cikin ba? to bari kiji daki zobar da karki zobar duk ɗaya suke a wajena dan sai kinyi abinda nace kiyi"...yana faɗin haka ya kama hanyar bedroom ɗinsa batare da yasake magana.


Itako faɗuwa tayi saman kujerar parlour ta fara rera kuka kamar ranta zai fita,tana kuka tana ruƙun Allah ya kawo mata mafita.Koda suka kawo bakin gate ɗin makaranta tsit yake sai ɗai-ɗaikun mutane dake wucewa amma ba alamar wata bus.

Cikin makaranta sukayi packing  ɗin motar su,cikin hanzari Safiyya ta fito ta nufe class ɗinsu,koda ta ƙarasa ba kowa aciki dan haka da sauri ta wuce hostel wajan abukan karatunta,abukiyar karatun ta Maryam ta fara cin karu da ita, Safiyya tace, "yauwa Maryam, nace Hafsat tashigo makaran ta yau kowa?".


Sai Maryam tace, "eh ta shigo dan kusa dini ma ta zauna har aka gama luctura".


Safiyya tace, "wallahi ita nake nema dan har yanzu bata koma gida ba".


"Aikuwa ana gama lecture  tace bari tayi saura tashiga bus dan bata son  magirb tayi mata kan hanya"...cewar Maryam.


Har Safiyya zata wuce sai ga Saratu ko ita abukiyar karatun suce, har zata wuce taji suna zanci Hafsat dan haka ta ƙarasu garesu tace,


"Safiyya Hafsat kam tajima da tafiya dan gaban idona ma tashiga wata mota baƙa ita da wata yarinya,amma ban san yariyar ba, ina dai yawan gani yarinyar tare da Hajara".


Gaban Safiyya ne ya bada dummmmm,lokaci guda jikin Safiyya yayi sanyi,dan da ƙyar tasamu ta ɓuɗa baki tace musu, "nagode bari na koma gida wata ƙila ta isa"....tana faɗar haka ta kama hanyar da zata kaita wajan da tabar Baban ta.


Tana isa wajan sa ta ɓuɗe mota tashiga tana mai faɗin, "Baba muje ƙila ta isa gida,dan antabbartarmin da tashiga mota".


Tana faɗin haka bai tsaya wani jiraba ya tada mota suka bar makarantar.

Koda suka isa gida akace bata dawo ba,sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi,irin tashin hankalin da Safiyya taga yashiga ne dan haka taje wajan da yake tsaye  tace,


Baba ka daina tada hankalinka akan ɓatan Hafsat,Hafsat bata ɓace ba, ta dai je gidan saurayin ta wanda yayi mata ciki,abinda yasa nace haka sabida ko jiya da dare bayan mun kwanta, dan ita atunanin ta bacci nake, inajin abinda tace dashi,naso nayi mata magana tunjiya amma na fasa nace sai naga tasake wayar dashi....sai da ta numfasa tace, zan yarda wancan lokacin asiri yayi mata amma yanzu nasan bawani asiri atare da ita.....nan dai tagaya musu asirin da Anwar yayi mata a wancan lokaci.

Baban Safiyya ya kalle Safiyya jikin sa asanyaye yace, "zaki iya gane gidan nasa kikai ni gobe?".


Shuru tayi bata bashi amsaba,kafin ta buɗa baki tayi magan Yace, "dole gobe ki kaini gidan, dan bazan iya barin ta awajansa ba,amana na ɗauko ta fa,dan haka ko ina Hafsat take sai na nemuta,dan ban sani ba ko yanzu asiri ne yayi mata"....yana faɗin haka ya fice daga gidan gabaki ɗaya.Kukan datayi ne har ya saukar mata da zazzaɓi mai tsanani dan koda yafito daga bedroom ɗinsa kwance yasame ta saman kujera jikin ta sai famar karkarwa yake saboda zazzaɓi.


Hankali ya ƙarasu gareta,hannunsa ya kai jikinta lokaci ɗaya ya ɗauke yana mai faɗin, meke damun ki hala naji jikin ki da zafi?".


Komai bata ce dashi ba sabida ko bakinta ta ga-gare ɓuɗewa bare tayi magana.

Dayaga alamun bazatayi magana ba yace, "wallahi ba ruwana da wani zazzaɓi, duk baki tashi kika fara aikin ki ba wallahi gobe sai anzomin da Safiyya"....aikuwa tana jin furicin sa,da sauri ta zabura ta miƙi zaune haɗi da faɗin, "nashirya mi zanyi maka yanzu"....abinda tayi ne ya bashi dariya dan haka ba san lokacin da yayi dariya ba....

[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY NA'IGE✍🏼*•

*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*TUKWAICI GA:-*
*Masoyiya kuma aminiya Maman Kulsum,wannan shafin nakine kiyi yadda kike so🥰🥰*

*SHAFI NA 16📑*

*__________*📖 Nuni yayi mata da ta zauna saman cinyar sa,ba musu ko ta tashi ta zauna,tana zama ya sanya wata sassanyar ajiyar zuciya,sabida jin fatar shi da ta ta sun haɗu waje ɗaya,shi kansa ya san yana son Hafsat so ba nawasa ba amma a zahirin gaskiya ba za'aya auren ta ba duk son daya kemata,kuma ba dan komai ba  sabida yariga da yasanta ƴa mace,kuma da ta yarda zata zubar da cikin wata ƙila ya yarda ya aure ta.

Jikinsa ya ƙara sanya ta, kana ya fara shaƙar ƙamshin dake fita jikinta, hannun sa ya kai saman sassan jikin ta ya fara shafar ta, lokaci ɗaya yaji wani sanye ya mamaye zuciyar sa,sosai yake son taraiya da Hafsat  ba dan komai ba sai dan yadda yake samun natsuwa da ita sose.

Ita kowa tunda taji ta saman jikin sa wasu hawaye masu zafi suka fara fita a idon ta,uwa uba lokacin da ya ɗora hannusa saman jikin ta,jikin ta ne ya fara karkarwa sabida  baƙin cikin ɗaura hannusa da yayi kuma ga ciyo da ke ɗawai niya da ita.
Bukinsa ya fara ƙoƙarin ɗaurawa saman nata, lokaci ɗaya ta fara ka-karin amai haɗi da sauka saman jikinsa, Wani baƙin ciki ne ya rufe shi bai san lokacin da ya kifeta da mari ba kana yace,
"Wallahi Hafsat muddin kina buƙatar kanki da lafiya kibi abinda nake so, dan wallahi ko aman jini ki kai sai nayi yarda nake so dake ko nayi miki abinda har ki mutu bazaki mantani ba,dan haka maza kije ki gyara jikin ki ki sameni bedroom yanzu nan".
Yana faɗa yana kama hanyar da zata sada shi bedroom.

Sanin halinsa da tayi dan haka ta tashi taje ta gyara jikin ta kana ta sameshi a bedroom ɗin sa.

Koda ta shiga ɗakin yana waya yana faɗin, "My love kin san na kusa dawowa kuwa?,dan haka ki fara shirin, dan kin san dana dawo ba jimawa za'ayi aure na dake".

Daya ke hands-free yasa dan haka tana jin dun abinda suke fada.
tace, "hmm My dear har kasa naji ƙunya".
Murmushi yayi kana yace, "kada ki damu ba jimawa zan cire wannan kunyar take dan ni tana cutar dani".
Mumushi tayi mai ɗan sauti kana tace, "yaushe zaka dawo inason na kasance cikin shiri?".

Yace,"a'a bazan faɗa ba akoda yaushe dai ki kasance cikin shiri kinji tawa".
Tace "to tace dashi".
Haka dai suka cigaba da waya cikin so da ƙaunar junan su.

Bayan sun kammala wayar ne ya kai duban sa ga Hafsat dake tsaye kamar wadda aka dasa kana yace, "kinyi min tsaye akai, ki ƙaraso mana".
Jikin ta a sanyaye ta ƙaraso gareshi,
Tana ƙarasowa ya jawuta jikinsa haɗi da sanya bakin sa cikin nata,to fah daga nan labari ya sauya.

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari tunda safe Baban Safiyya yace suje ta gwada masa gidan Anwar,hijab ɗinta tasaka batare da tayi ko beark ba suka kama hanyar gidan Anwar.

Sunsha wuya kafin tagano gidan dan har za su juyo su dawo gida sai tagane gida,amma kuma ganin gidan da sukayi baiyi affani ba dan gidan kulle yake kuma koda suka tambaya akace mai gidan ya jima da barin garin.

Sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi na rashin ganin Hafsat,dan koda suka dawo gida ba inda ba suneme ta ba amma basu ganta ba,dan haka Baban Safiyya ya yanke shawarar yaje ya sanar da Baban Hafsat abinda ake ciki duk da yasan bai rasa jin ɓatan Hafsat a unguwa amma gwanda yaje ya ƙara sanar dashi koda ya sani.

Da yamma bayan ya dawo daga kasuwa ya shirya yaje wajan Baban Hafsat.

Koda yaje wajan Baban Hafsat,bayan sun gaisa kana Baban Safiyya ya faɗa masa abinda ke faruwa gami da ɓatan Hafsat.

Sai da Baban Hafsat ya numfasa kana yace, "Alhaji Aliyu to miyasa zaka tare ni da wannan magana bayan tun wancan lokaci na shaida maka na fitar da Hafsat daga cikin ƴaƴana,amma kuma yanzu kazomin da wannan zanci,dan haka bana son wannan zanci dan Allah daga yau kada ka ƙara haɗani da ita".

Har Baban Safiyya zaiyi magana sai Baban Hafsat yace, "a'a kada kasoma, kai kaji zaka iya riƙunta kuma yanzu tace bata so duniya take so tabi dan haka ka kyale ta ga duniyar nan ta ishe ta riga da wando".
Yana faɗar haka ya shigewar sa  gida ransa a ɓace.

Haka baban Safiyya ya dawo gida jikinsa a sanyaye kamar ba lakka ajikinsa.
Haka dai suka canye kwana biyu suna neman ta amma basu ganta ba,daga baya sukayi haƙuri suka cigaba da addu'a Allah ya bayya nata.

Tunda sallah asuba da ta farka tayi wanka haɗi da ɗuru alwala tayi raka atanin fajar kana tayi sallah asuba,tajima zaune tana istigifari da hailala da addu'a nema tsari daga sharin mutum da aljan.
Bakwai saura ya farka haɗi da wata irin miki,gyafin da take ya kalla kana ya buɗa baki yace, "waya baki umarnin ki tashi daga nan ehh?".

Ko kanta bata ɗago daga ƙasa ba tace, "lokaci sallah ne ya bani umarnin tashi".

Aikuwa cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya ƙaraso gaban ta yana nunin ta da ɗan yatsa kana yace,"saki faɗin abinda kika ce?".

Irin yadda yake mata maganar ko ita ta tsora ta sosai dan haka bata ce komai ba taci gaba da lazumin ta amma gaban ta sai dukan uku-uku yake.

Magana yayi mata cikin tsawa yace taje ta haɗa masa beark,aikuwa ba musu ta tashi taje kitchen ta fara haɗa masa abinda yake so.

Tana tashi yabita da kallo haɗi dayi mata kwafa kana yace,"zanyi maganin ki,nan ba da jimawa ba".
Yana faɗin haka ya kama hanyar da zata sadashi da toilet.

Ita ko badan komai ta tashi tashiga kitchen ba sai dan kar ya hanata zowa makaranta.

Agurguje yayi wanka ya fito dan so yake yaje gun Hajara ta rakashi wajan malamin da yayi masa aiki akan Hafsat a wancan lokaci dan ko yanzu so yake ayi masa aki a kanta,dan yaga yanzu sai wata gardama take mishi idan yace tayi masa abu saɓanin da.
Koda ya zo parlour tana kitchen bata ƙarasa aiki ba dan haka ya sameta kitchen ɗin yace, "ya fita yadawo yanzu".
Bai jira cewar taba yafita yana ta sauri kamar wanda akayi ma kyata zata tsere masa.

Key yayi ma motar sa, kana ya kama hanyar da zata sada shi da layin buge,dai-dai kan kwanar gidan yayi packing ɗin motar sa.

Yana fitowa a mota ba abinda ya fara cin karo dashi ina ba condoms ba, tsaki yayi kana yace, "shiya bana sun zuwa wannan unguwar sabida haka".
STORY CONTINUES BELOW

Kwanar ya shiga,aikuwa yana shiga sai ga ƴan mata da samari sai fitowa suke cikin ɗakunan da suka kwana,wasu da alamu ma matan aure ne dan  ga sunan har da goyon su,abin dai sai wanda yagani,yana ƙara tafiya sai yaga wata yarinya ita da wani saurayi za su shiga wani ɗaki, kuma daka ganta ita ƴar makaran tace dan ga kayan makaranta  nan ajikin ta na secondary school,   ɗaki suka buɗe suka shiga kana suka rufe ƙofa.

Gab da zai shiga ɗakin Hajara yaga wasu samari su biyu sai tunkuɗar wata yarinya suke suna faɗin, "wallahi yau sai kin bari muna ɗaki tunda ba ubanki ne ya bamu kuɗin da zamu biya ba".

Ita ko sai turjiya take wai ba inda zata je.

Da suka ga zata ɓata musu lokaci suka tisa ƙyayar ta gaba suna faɗin,"shigiya jarababba wallahi mungaji dake dan haka yau sai kin bar muna ɗakin mu".

Yarinya ta sosai dan idan ka ganta bazaka ce tasan wani abu ɗa namiji ba,tsaki yayi haɗi da ƙarasawa ɗakin Hajara.
Yana zuwa ba Knocking ba komai yatura ƙofar ɗakin ya shiga.
Cikin sa'a koda ya shiga ba kowa aciki dan ko ita tana toilet tana wanka,koshi dan yaji motsin ruwa ne ya tabbatar da haka.
Zama yayi sama katifar dake ya she a ɗakin yana jiran ta.

Bai jima da zaman ba sai gata tafito daga ita sai wani ƙaramin towel da bai rufe cinyar taba.
Bata ma lura dashi ba sai da yayi gyaran murya kana ta san da zaman sa.
Aikuwa suna haɗa ido dashi wani sanyi daɗi ne ya ziyarci zuciyar ta lokaci ɗaya,dan haka bata san lokacin da ta faɗa jikin sa ba.

Ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya fara amma sai ya tuna  da akin da zatayi masa dan haka ya kyale ta,jikin sa ta fara shafa duk da baya so amma abinda ya keson tayi masa ya hana ya dakatar da ita.

Ita ko da taga bai da katar  da itaba yasa ta kai bakin ta zuwa nasa ta fara kissing ɗinsa,ba yadda ya iya haka yabiye mata har suka samu biyan buƙata kana ya jawo ta jikin sa haɗi da kai mata kiss a baki kana yace,
"My dear na,ina so ki kaini wajan malamin da ya taɓa yimin akin akan Hafsat".....ai tun bai rufe baki ba ta ɗago kanta da sauri ta dube isa kana tace,

" nifa bana sun kana min maganar ta dan a rayuwa ba ƴar da na tsana kamar ta".
Da ƙyar dai yasha kanta ta yarda zata kai shi amma sai laraba da ƙarfe uku na dare yazo su tafi dan lokaci ne ake zowa wajan malamin.
Yace, "to sai yazo".
Yana faɗa yatashi ya shiga toilet yayi wanka,jikin sa ta goge masa haɗi da tayashi sanya kayan sa.

Har mota tarakashi gab da zai shiga mota ya juyo ya kalle ta kana yace, "Hajara yanzu shikenan kin bar hostel kin dawo nan dazama ko".

murmushi tayi haɗi da faɗin,"sai mun haɗu ko".

tana faɗar haka ta wuce ta barsa batare da taji mi zai ce ba.
Key yayiwa motar sa kana ya dawo gida, koda ya shigo zaune ya same ta tashirya tana zaman jiran dawowar sa.
Kallon ta yayi yace, "ina beark  yunwa nakeji".   "yana dining".   Tafaɗa haka ataƙaice.
Sai da tabari yagama beark tazo tace mishi makarnta take sun zuwa sabida lecture ne da ita ƙarfe goma.
Wani kallo yabita dashi kana yace,  "bawani makaranta so dai kike ki tsere,amma kisani bana gudun ki gudu dan na san da kanki zaki dawo gareni, kana yace zaki iya tafiya".
STORY CONTINUES BELOW

Yana faɗin haka takama hanyar fati,har zata ɓuɗe ƙofa ya dakatar da ita yace ta bari yazo ya kaita da kansa kuma zai jiri da tagama abinda take ta dawo in kuma ba haka tasan sauran.

Ba musu ta tsaya har ya kammala abinda yake yazo ya kaita makaranta.

Da shigar ta school bata tsaya ko ina ba sai office ɗin shugaban makaran ta.

shugaban makartar ya  bata wata takarda wadda akayi ma signing yace taje ta kaima iyayen ta su sa hannu,idan sun sa sai ta kawo dan wani sati za suwu ce abuja daga can kuma kowace a bata  ƙasar da zata je karatu.

Bayan ta fito ɗakin shugaban makaran ta tashi ga class ɗinsu,bayan sun gama lecture tana sauri ta fito ne sai ta haɗu da ƙawar ta Maryam.
Hafsat bata ma ganta ba sai Maryam tace, "Hafsat ran jumu'a yaushe kika koma gida dan naga Safiyya sai nemanki take?".

Murmushi Hafsat ta ƙaƙalo kana tace,"tana fita niko na koma".
Sai Maryam tace, "gaskiya Hafsat Safiyya na son ki da yawa kinga yarda tabi tarikice kuwa".

Mumushi Hafsat tayi haɗi da cewa, "bari na wuce sai gobe idan na shigo".

Tana faɗar haka tafice batare da ta tsaya jin me zata ce ba.

Da sauri take tafi har tafita daga makarantar, bakin gate ta ganshi yana jiran ta dan haka bata tsaya komai ba tashiga motar sa  suka wuce.
Tana wucewa Safiyya na  fitowa daga class ɗinsu,Maryam tagani zata wuce hostel dan haka da sauri taje gare ta tayi mata magana.
Juyuwa Maryam tayi haɗi da yimata murmushi kana tace, "Safiyya Hafsat kike nema ne hala".

Sai tace,"eh wallahi har yanzu bamu ganta ba".
Tace, "yanzu fah naga Hafsat kuma tare muke har aka gama lecture".
Safiyya tace, "yanzu!".
Ta faɗa haɗi da zari ido.
Suna cikin wannan maganar sai ga ƙawar su Saratu tazo tace, "nima naga Hafsat yanzu bakin gate tashiga wata mota".

Wani baƙin ciki ne ya turnuƙata,tace kena Hafsat su ta rainama hankali tana gidan saurayin ta.  Tayi wannan maganar a zuciyar ta.
Kallon su tayi tace, "oky nagode sai anjima".
Tana faɗar haka takama hanyar fita makaranta,sosai ran ta ya ɓace wato Hafsat suta mayar  ƴan isaka  wanɗanda basu da aikin yi, to daga yau ba mai koma shiga harkar ta inta iya ta tabbata tare dashi.

Gida ta koma dan ko lecture da zatayi bata tsayayi ba sabida ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba.

Cikin sa'a koda ta isa gida Baban ta  bai fita ba,bayan ta zauna sai Mamar ta ce, "har kin dawo ne?".
Sai tace, "eh Mama".  Sai ta kalle Baban ta da idon ta da sukayi ja-jir tace, "Baba Hafsat fa bata ɓata ba"......nan dai ta faɗa musu abinda tasani.

Ko Baban Safiyya ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma bai ce komai ba sai Allah kashirya.
Mama ko inda take fita ba nan take sauka ba kuma tace wallahi ko Hafsat tadawo baza ta zauna gidan ba.
Ko Yayan Safiyya shima yayi faɗa kamar ya shaƙo Safiyya tunda itace mafarin zuwan ta gidan.

Tunda Hafsat tashiga makaranta duk abinda take akan idon sa har maganar da sukayi da Maryam,abin da kwai bai sani ba shine shigar ta office ɗin shugaban makaranta.

haka ya dawo da ita gidan sa ba abinda take masa sai aikin bauta amma yana kai ta makaran ta tayi abin da zatayi ya mai data har akazo darin da za su je wajan malamin su shi da Hajara.

STORY CONTINUES BELOW

Tun shabiyun dare ya fara jin cikin sa na murɗawa har akazo lokacin da sukayi yazo sutafi,kuma lokacin ne ma cikin nasa ya fara yimasa wata murɗa wada yasa yafita haiya cinsa lokaci ɗaya.

Ita ko bata masan abinda ake ciki ba sai gab da asuba tana tashi ta ganshi cikin wannan halin sosai hankalin ta ya tashi dan haka cikin hanzari ta ɗauko wayar sa,kuma sai tara waza ta kira tunda bata san kowa nasa ba.
Har aka gama sallah asuba tarasa ya zatayi sai can ta tuna da akwai mai gadi gida,dan haka da gudu taje ta sanar da mai gadi abin da ke faru,aikuwa mai gadi na shiga cikin gidan ita ko ta lallaɓa ta ɗau kayan ta na makaran ta ta gudu.

Cikin sa'a tana fita tasamu dan acaɓa ta faɗa masa suna unguwar su suka kama hanya.....

*#Vote*
*Comment*
*Share*


*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼.*

*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*


*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 17📑*

*__________*📃 Bakin ƙofar gidan tace ya sauke ta,kuɗi tabashi haɗi dayi masa godiya,dan ƙuɗin da ta bashi sunfi hakanan amma ya amsa baice da ita komai ba,gidan ta kaman hanyar shiga har takaɗa ƙafar ta ɗaya sai Yayan Safiyya Abbas yazo da sauri ya tare ƙofa haɗi da antayamata wani kallo kana yace,"wallahi ba inda zaki shiga dan ba gidan ubanki bane, sai da kika gama lalacinki zaki ɗauko wasu shegun ƙafafunki kice kizo gidan ubanki ko?, To barikiji tun wuri ki kama gabanki tun ban illatakiba".

Haƙuri ta fara bashi tace, "wallahi Yaya ba inda naje sune suka saceni"....tun bata rufe baki ba ya wanke ta da wani mari wanda yasa ƙiris kaɗan ta kai ƙasa.

Suna cikin haka sai ga Mama ta fito taga wake musu hayaniya bakin ƙofar gida.
Hafsat tagani tana ƙoƙarin tashigo shiko Abbas ya hanata shigowa,aikuwa da sauri Mama ta ƙarasa wurin tana kunfar baki tace, "wallahi baki isa kishigo gidannan ba,tunda ba ubanki ne ya gina munashi ba".

Roƙun Mama  Hafsat tafariyi amma Mama taƙi koda saurarin ta,daga ƙarshe ma Mama komawa tayi gida ta ɗauko mata kayan ta ta jefomata su waja.
Mazan dake zaune bakin ƙofar gidane suka taso suna ba Mama haƙuri amma ko kallo basu ishetaba,kuma gashi Baban Safiyya bayanan yayi tafiya tun jiya,kuma Safiyya ma batanan jiya gidan gwaggon ta ta kwana.
Mutanin dake wajan da suka ga Mama taki haƙura ita da yaranta sai ɗaya daga cikinsu ya dube Hafsat kana yace,"kinga tunda sunce baziki shigar musu gidaba to kije ki koma gidan iyayenki zaifimiki".....tun bai rufe bakiba sai ga Ammar ƙanin ta yazo wajan,da sauri ya ƙarasa gareta yana faɗin,"Aunty daina kuka zo muje gida kinji,ai kema kinada gidan uba dan ba shegiya ceke ba".

STORY CONTINUES BELOW

Kai ta fara girgiza masa kana tace, "a'a Ammar kaji ne bazanje ba"....jikar kayanta ya ɗauka haɗi da jan hannunta yace dole sai sun tafi,ba yadda ta iya haka suka tafi gidansu.

Suna isa gidan har zasu shiga sai ga Baban ta ya fito domin ya tafi wajan aiki sai yayi arba da su,wani kallo yayiwa Ammar shida yake riƙi da hannuta da jikar ta kana yace, "wazan gani a gidana?, wallahi muddin kana son kankai da lafiya kabata kayan ta ta ɓacemin da gani".....tun bai rufe bakinsa ba ta durƙusa gabansa tana kuka tace,

"Baba dan Allah kayimin haƙuri wallahi ba lafina bane dan Allah Abba ka koma bani wata dama".....wata uwar tsawa ya daka mata wadda yasa ta haɗe sauran maganar da zata faɗa bata shirya ba.

Tswar da yayi ne yasa Ummar Hafsat fitowa bata shirya ba.

Hafsat tagani durƙushe da ƙasa ita da Ammar suna ba Baba haƙuri,da sauri ta ƙaraso garesu kana tace, "Hafsat lafiya waya taɓamin ke"....tsawa Abban Hafsat yayi mata haɗi da yimata nuni da ta koma cikin gida.

Gabansa tafaɗi tana kuka tana faɗi, "dan Allah Abban Hafsat ki barmin ƴata "......kallon da yayi mata ne haɗi da wata tswa wadda tasa ta komawa cikin gida bata shirya ba.

Yana ganin Ummar Hafsat ta koma gida yayi ma Ammar nuni da yashiga gida,ba musu ko yashiga ita ko Hafsat ya nuna mata hanya kana yace, "tunda duniya kike so to gaki gata".. ...yana faɗar haka ya maida ƙofar gida ya rufe yabar Hafsat durkushe da ƙasa tana kuka.

Tana ganin ya maida ƙofa ya rufe ta tashi ta haɗa kayan ta zata fara tafiya kenan sai taji zuciyar ta tafara ciyo,lokaci ɗaya mararta ta fara murɗawa amma duk da haka sauri take ta bar unguwar tasu.
tayi nisa kaɗan da unguwar ciyon mara yataso mata wannada bata taɓa jin irinsa ba kuma lokaci ɗaya ta gagara tafiya,wani waje ta samu domin ta zauna amma kafin ta ƙarasa ta faɗi,lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafafun ta kuma gashi hanyar mutane basu cika bintaba sai ɗai-ɗai ku.
Tanacikin wannan uwar wuyar sai ga wani mai napep ya fito cikin unguwar,tun bai ƙaraso wajan ba yaga mutum yashe aƙasa sai birgima yakeyi,har yasu yayi tafiyar sa sai kuma ya tsaya,jinin da yaga yana fita jikinta ne yasa ya ɗauke ta da sauri yasa cikin napep yashiga ya wuce hospital da ita.

Emergency room aka kaita,taimakon gaugawa suka bata kuma cikin ikon Allah sai gashi ta dawo cikin hayyacinta,kana sukayi mata allurar bacci.

Doctor ne yafito riƙi da ta kardar magani yaba wannan mai napep yace yaje ya sayo yanzu nan,ba musu ko yaje yasayo magani da ƴan kuɗin da yasamu yanzu da safe har ma da ragoyar najiya,aikuwa yana kai ma Doctor magani bai tsaya komai ba ya kama ga bansa.

Bayan doctor yasa mata ruwa da magani yafito dumin suyi magana da wannan mai napep amma bai ganshi ba,haka yayi tajira har yamma kuma bai dawo ba,kuma gashi anasun akaru wasu maganukkan da babu.

Har akayi magarb bai dawo ba,kuma lokacin   ta farka da ƙarfin jiki sose,Nurses ɗin dake kula da sune taje tasanar da doctor farkawar ta,dan haka da sauri sai gashi yazo,kallon ta yayi kana yace,

Mike miki ciyo yanzu?".

Tace, "ba komai".

Yace, kin tabba ta".  "Tace eh".
Wanda ya kawoki bai dawo ba har yanzu dan naso nayi masa bayani amma tunda bai dawo ba bari nayi miki bayani dan naga jikin naki da alamun sauki".

Mamaki ta farayi to waya kawo ta, gani kamar zata ɓata masa lokaci ne tace, "to inaji".

Yace, "da farko dai kiyi haƙuri dan cikin dake jikinki ya zobe.....ai tun bai rufe baki ba wasu hawaye suka fara bin kuncinta haɗi da  jero ma Allah godiya cikin ranta.

STORY CONTINUES BELOW

Haƙuri ya ƙara bata ganin hawayen dake zuba a idonta sannan yace,"kuma kina yawan sa damuwa aranki,dan haka ki daina dan kina gab  da kamuwa da ciyon zuciya".

A hankali ta ɓuɗe bakin ta kana tace, "insha Allahu zan daina".

Tambayar ta yayi tana jin unwa tace eh,Nurses yayiwa magana yace taje ta kawo mata tea da magani.

Bayan Doctor yafita ta kai dubanta ga kayanta dake kusa da ita,tashi tayi taje gun kayan   ta duba kana  taga komai akwai dan haka hamdala tayi kana taje toilet tayi wanka,tana fitowa sai ga Nurses tazo da tea da magani aikuwa tanasha ta ƙara jin ƙarfin jikinta sosai ba jimawa sai bacci yayi awun gaba da ita.
Ba ta farkaba sai da gari yawaye kuma koda Doctor ya dubata ba wata matsa dan haka ya rubata mata magani haɗi da bata kardar sallama.

Yana sallamar ta tashi tayi ta haɗa kayan ta tafice,mai napep ta tare ya kaita makaranta,bayan ta sallameshi ta ɗau kaya tawuce hostel,ɗakin ƙawar ta Naja'atu tashiga kuma koda taje bata sameta ba dan suna cikin makaranta,kayanta ta aje kana taje ta kwanta,bata jimaba da kwanciya ba bacci yayi aun gaba da ita.

Koda su Naja'atu suka dawo daga lecture bata farka ba sai kwasar bacci ta take.
Dubanta Naja'atu tayi sosai taga Hafsat ce kwance a gado,dan haka da sauri tashiga tashe ta,a hankali ta fara ɓuɗe idon ta ta sauke su kan Naja'atu da sauri Naja'atu tace,
"Hafsat dama kinshigo makaranta amma bakije office ɗin shugaban makaranta ba har anyi summiting ɗin takardun da akace iyaye suyi signing dan gobe ne za suje abuja,dan haka kitashi kiyi sauri ki kai kafin yafice daga makarantar".

A hankali Hafsat tace, "Naja'atu wallahi bazan iya zowa ba dan ban da lafiya,amma kiɓuɗa jikata ki ɗauka ki kaimasa".

Naja tace,"a'a bazaiyi nakai ba dan kinsan sai kinyi signing dan haka tashi narakaki muje".

Ba yadda ta iya haka ta tashi suka tafi office ɗin shugaban makaranta,cikin ikon Allah suka sameshi akayi duk abinda ake kana suka dawo hostel.

Bayan kwana biyu da faruwar haka jikinta ya warware sosai dan yanzu ba abinda bazata iyayi da kanta ba,kuma ba abinda ake sai shirye-shiryen tafiyar su.

Yadda Baba maigida ya same Anwar sosai hankalinsa yatashi dan haka yafito da gudunsa yaje wani gida maƙotansu ya kira wani maigadi ya kamamasa suka kaishi hospital....*#Vote*
*Comment*
*Share*


*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼.*


*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 18📑*

*__________*📃 Yasha wuya kafin a samu ciyon cikin ya lafa,sai da a kace musu  ya samu  bacci sannan Baba mai gida hankalinsa ya ɗan kwanta lokacin kuma ya tuna da yarinyar  da tazo ta sanar dashi amma yanzu ba gantaba to ina   take?.

STORY CONTINUES BELOW

Tunda Baba Safiyya ya shigo garin, kan hanyar sa ta zuwa gida wani maƙofcin sa ya taresa ya faɗa masa abinda matar sa da ɗiyansa suka wa Hafsat,sose ya nuna bacin ransa a kan haka dan haka bai tsaya wata-wata ba ya ƙarasa gida da sauri ransa a matuƙar ɓace.
Tun a suron gida yafara  ƙwalama Mamar Safiyya kira yana faɗin, "Suwaiba! Suwaiba! Suwaiba!.
Gabanta ne yayi mutuƙar faɗuwa dan abu mai wuyane kesa Baban Safiyya yakira sunan ta,amsawa tayi jikinta a sanyaye.

Kallon da yayi matane yasa ta ƙarashiga tashin hankali kana ya buɗe baki yace, "an cemin Hafsat ta dawo amma kin koreta keda ɗiyanki, to bari kiji wallahi duk inda Hafsat take sai kin nemumin ita,muddin kina son kici gaba da zama gidan nan".....yana faɗin haka ya ficewar sa gidan  ko takan maganar da take masa bai tsaya bi ba.

Sosai Hankalin Maman Safiyya ya tashi kuma lokaci ɗaya ta fara dana sanin abinda tayiwa Hafsat.

Ɗakin Safiyya tashiga ta faɗamata abinda a ke ciki kana tace, "Safiyya wai ina kika san Hafsat na zuwa?".

A hankali Safiyya ta buɗe baki tace, "wallahi Mama ban saniba , aikune kuka koreta da kunbari Baba yazo duk hukunci da yayanke ba shikenan ba amma kuce sai kun koreta,kuma ni ko makaranta na daina ganinta bare nasa ran zan ganta".

Sai da Mamar Safiyya ta shafe hawayen da suka zobu mata kana tace, "idan Allah ya kaimu gobe kiƙara dubumin makarantar ku, ko Allah nasa tana can".
Safiyya tace, "tau Mama Allah yasa a dace".
Tace "Ameen Safiyya".
Haka suka kwana Baban Safiyya na zuba musu masifa.

Ita ko Ummar Hafsat tunda Abban Hafsat ya umarceta da ta koma gida aikuwa tana shiga gida ta fara kuka mai cin rai,lokaci ɗaya ta fara tunanin ƴan uwanta da iyayenta, dan da tana tare da iyayen ta da bazaiyi mata haka ba, gashi yanzu ya rabata da iyayenta kuma yanzu ya rabata da ƴarta kwaya ɗaya tak, lokaci ɗaya ciyon zuciyar ta yatashi, cikin ƙanƙanin lokaci tafara fita hayyacin ta,aikuwa Abban Hafsat naganin haka ya hankalinsa yayi ƙololowar tashi,da sauri ya ɗauke ta yakai mota suka wuce hospital dan a lokacin sheɗarta tayi sama kamar zata fita.

Bayan kwana biyu da dawowar shugabanin makarantar su abuja aka aika kiran ɗaliban da za suyi wannan tafiyar,bayan kowa yazo aka bashi duk wani abinda zaya buƙata acan kana aka faɗama kowa ƙasar da zaije karatu,haɗi dayi musu nasiha mai ratsa zuciya, Hafsat ita da wasu maza huɗu su za suje India karatu haka  dai akaraba kowane department namiji huɗu mace ɗaya, kowane da ƙasar da aka turashi.
Bayan angama rabamusu kayansu da wani abin affanin su kana akace kowa yaje yayi bankwana da iyayensa da ƴan uwansa da kwana uku ne suka ragemusu da su tafi, kuma ga rana ta uku za suwuce abuja dan daga canne za suyi tafiyar.

Bayan angama yi musu bayani kowa ya kama gabansa, wasu ma suna fitowa suka wuce gidan iyayensu, murna fil a zuciyar su.

Saɓanin Hafsat , dan inkowa na murna ita kuka take haɗi da fargaba, dan itakam ba wanda tasan zata je tayiwa ban kwana dan ba mai sonta dan ko iyayenta sun koreta bare ma wasu, haka ta koma hostel ciki da baƙin ciki da danasanin bin *UMARNIN SAURAYI* da kuma biyema Hajara.

Tana isa hostel ta faɗi kan gado tafara kuka kamar ranta zai fita, Naja'atu ba irin magiyar da batayi ba ta faɗa mata damuwar ta amma taƙi, daga baya data ga bata son faɗamata ta dawo rarrashin ta tana faɗin, "haba Hafsat keda yaka mata ki kasance cikin farin ciki amma gashi sai kuka kikeyi, ai Allah ya kamata kiyima godiya bakiyi ta kuka ba, ai duk gamu muna so amma Allah ke ya zaɓa dakije dan haka dan Allah kitashi ki daina kuka please".....haka dai tayi ta bata magana har tasamu ta daina kuka kuma daga baya sai ga zazzaɓi yarufe.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun isa hospital likitoci suka dubata kana suka bata gado, sai da ta kwana sannan Ummar Hafsat ta farfaɗu, bayan likitoci sun ƙara dubata suka tabbatar da ciyon ya lafa kana suka ba Abban Hafsat izinin shiga ya ganta.

Koda ya shiga tana kwance kanta na kallon cilin alamu kamar tunani take, a hankali ya ƙaraso gab da gadon da take wance, ƙujerar dake wajan ya jawu ya zauna kana ya ɗura hannansa saman nata, sai a lokacin tasan da yashigo, dubansa tayi haɗi da fitar da kwalla kana tace, "Abban Hafsat, inason nayi maka wata magana wadda ban taɓa yimaka irin taba, dan haka bari kaji, da farko dai inason naje ga iyayena, na biyu kuma ina har kanaso nacigaba da zama da kai amatsayi mata to ba shakka sai ka nemumin ƴata wallahi ban zan iya jure rashin taba a halin da nake ciki, muddin kana so nacigaba da rayuwa sai kanemun ƴata......kukane ya kufuce mata lokaci ɗaya ta furta ashe haka iyaye keji idan ƴa-ƴansu sukayi nesa da su?".....tarine yaci ƙarfinta kuma gashi  tana tari sai jini ya biyu baya, sosai hankalinsa ya tashi dan haka da gudun sa yaje ya ƙira doctor, koda Doctor yazo halin da yasame Ummar Hafsat baƙarimin  tayar masa da hankali yayi ba, sauran ƴan uwansa likitoci ya kira suka zo dumin a ceto rayuwar ta.

Wannan karun Abba  da yaransa  gabaki ɗaya hankalinsu ya tashi aka rasa ma me rarrashi wani, su yaran sai kuka suke aka rasa wazai ba wani haƙuri a cikin su, lokaci ɗaya shima ya fara tuni ƴan uwansa.

Baban Safiyya ne ya hana kowa zama yace wallahi sai sun nemumi shi Hafsat kan su samu kwanciyar hankali, aikuwa haka suka je neman ta amma duk inda suke tunanin zata je bata jeba, sosai hankalin mamar Safiyya ya tashi da ita da yayan Safiyya dan Baban Safiyya yafi ganin laifinsu akan nakuwa.

Mamar Safiyya tace ma Safiyya taje makarantar su taga ko tana can, sai Safiyya tace bata can da yanzu weekend ne amma wata ƙila Monday tashiga.

Haka dai suka cigaba da nemanta cikin kwana biyu hankalin su tashe.

Anwar yanzu yasamu sauƙi dan har abinci ya kanci saɓanin lokacin da aka kawoshi, bayan ya dawo hankalinsa yake tambayar mai gida Hafsat, sai mai gida yace shi bai saki ganin taba tun lokacin da tafaɗimin baka da lafiya.
Hankalinsa ne ya tashi sose amma yayi alwashin da ya fita daga hospital duk inda take sai ya nemuta.

Tunda dare duk wani abin buƙata Hafsat ta haɗashi  cikin ikon Allah da taimakon ƙawar ta Naja'atu dan yanzu Naja tasan waye Hafsat itama tasan waye Naja.

Tun ƙarfe huɗun dare ta tashi tayi wanka haɗi da shiryawa dan ita bata son ajirata kuma gashi antabbatar musu ƙarfe shidda na safe za su tashi zowa abuje dan ƙarfe goma jirginsu zai ɗaga.

Bayan tashirya suna zaune suna fira  Naja'atu ta ɗako wasu kuɗi ta bata tace, "Hafsat, ga wannan canjin kiriƙi a hannuki kafin su baku kuɗi yana da kyau kirƙi koda kinga wani abu ko ace kasaya da kanka".

Kai Hafsat tafara girgiza mata kana tace, "dan Allah Naja kibarsu wallahi ko yanzu nagode da karmcin da ki kayimin dan Allah kibar kuɗinki dan nasan duk wani ɗan makaranta yana buƙatar kuɗi".....tun bata rufe bakin taba sai Naja tace,
"Nasan da haka amma duk baki karɓa ba bazan ji daɗi ba".

Ba yadda ta iya haka ta karɓi kuɗin haɗi dayimata godiya sose.

Suna zaune a ka kira sallah asuba dan haka suka tashi sukayi alwala suka gabatar da sallah.

Hospital koda Umma ta farka ba abinda take kira sai sunan Hafsat, Abba na cikin bacci yaji ta farka kuma da sunan Hafsat a bakin ta, doctor yaje ya faɗa masa farkawar ta.

Bayan doctor yazo ya ƙara dubata kana ya koma yimata allurar bacci kana ya dube Abba yace, "gaskiya yana da kyau kaje kanemu mai wannan sunan dan wallahi da gani tana buƙatar taga mai wannan sunan, kuma kodan matsalar ta ya  kamata kanemuta dan mu kan
mu zamuji daɗin haka ".

STORY CONTINUES BELOW

Yana faɗan haka yafice daga ɗakin ya bar Abba da tunani.

Tunanin yaga bashine mafita ba dan haka yakira  ɗansa Marwan yace yayi sauri yazo dan fita yake sunyi.

Ba ɓata lokaci sai ga Marwan yazo yana zuwa yayi masa sallama ya fice daga hospital hankali ta she.

Sai da ya fito ya fara tunanin ina zaije neman Hafsat, a nanne hankalinsa ya tashi saura kiris ya faɗi ƙasa a wannan lokacin.
Gidansu Safiyya ne ya faɗomi shi a rai, dan haka da sauri yayiwa mota kye ya tafin gidan nasu.

Yana isa gidan dai-dai Safiyya tafito domin taje makaranta neman Hsfsat,da jiya ba wanda ya runtsa a cikin su dan Baban ta yaki bari kowa ya runtsa sai masifa yake musu.

Tana ganin Abban Safiyya da sauri tazo gareshi ta fara gaidashi, bai ma karɓa ba ya jefumata tambaya yace,

"Safiyya ina Hafsat?".
Kasa karɓa masa tayi sai da yasake mai-mai tamata kana ta ɓuɗa baki idonta na fitar da kwalla kana tace, "muma itace muke nema yanzu ma haka school ɗinmu ce zanje na ƙara dubawa ko zan sameta".....tun bata rufe bakinta ba Abban Hafsat yace,
"Shigo mota mutafe ko Allah nasa mudace".

Tace, tom". Haɗi da buɗe mota tashiga.
Har zasu tafi sai ga yayan Safiyya yafito, ganisu dayayi ne yasa da gudunsa ya zo garesu, bai ma tsaya tambayar ina za su je ba ya buɗe mota yashiga kana suka kama hanya..

Tun shidda saura  motocin da za su kaisu abuja suka ƙaraso, kuma ba ɓata lokaci duk waɗanda za su yi tafiyar suka zo kowa yashiga motarsu, kuma kowace mota namiji huɗu macce ɗaya.

Kowa ƴan uwansa suka rakoshi saɓanin Hafsat da ƙawarta ta rakota, lokacin da zata shiga motar jikin Naja ta laƙe sai rusar kuka take ba ƙau-ƙautawa, da ƙyar Naja ta rabata da jikinta tana bata haƙuri kana ta buɗe mata mota tashiga dan tafiya za suyi.

Har motoci za su fara tashi sai Hafsat ta buɗe jikarta ta dauko wata takarda taba Naja tace dan Allah kibawa Safiyya".

tana bata motoci suka fara tafiya.....

*Dan Allah kuyi haƙuri da wannan*

*#Vote*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼*•

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 19📑*

*__________*📖 Hawayen da suka zoba a idonta ne ta shafe haɗi da ɗaga musu hannu har suka fita daga makarantar, sose ta  tausaya ma Hafsat  wannan halin da takeci,  ita dai fatar ta Allah yasa Hafsat suyi nasara a karatun da suka je.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan kamar minti goma da tafiyar su, sai ga motar  Abban Hafsat  ta shigo hara bar makarantar cikin hanzari, suna shigowa Safiyya ta hango Naja zaune tayi tagumi kamar mai tunanin wani abu, tun Abban Hafsat baiyi packing  ɗin mota ba tace,
"Abba  bari naje ga ƙawarta can nasan wata ƙila tasan gun da take"....tun bata rufe baki ba yace, "je kisame ta Safiyya".
Da sauri ta ɓuɗe marfin mota tafito ta ƙarasa wajan da Naja'atu ke zaune tana tunanin Hafsat.
Sallama tayi mata haɗi da gaishe ta, Naja  ta amsa mata haɗi da  murmushi a fuskar ta kana tace, "Safiyya ke kuwa nake nema kuma gashi har sun wuce baku haɗu ba, amma tabani saƙo nabaki".....cikin hanzari Safiyya tace, "wace?"
Tana faɗa tana zare ido.

Jikin Naja a sanyaye tace, "Hafsat".
Jikin Safiyya na karkarwa  tace, "ina taje Naja".
Ahankali ta ɓuɗi baki tace, "kin san ai tasamu scholarship na zuwa india karatu, to shine  suka je yanzu ".

Ido ta zare kana tace, "Hafsat ta tafi kenan? ina zanganta Naja, dan Allah ki gayamin ina zan sameta, wallahi muna matuƙar buƙatar  ta".....kuka ne ya kufuce mata sose wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar da zatayi.
Wajan da Abba yake shida Yaya Abbas suna hangota, dan haka da sauri suka ƙaraso gare ta suji mitake ma kuka.
Ko da suka ƙaraso tafaɗa jikin Naja sai rusar kuka take kamar ranta zai fita tana faɗin, "Naja dan Allah ki gayamin inda zangan ta".....Abban Safiyya ne da ya ƙaraso yace,

"Safiyya lafiya kike kuka? kodai ta ɓata ne?".
Baki ta buɗe tana son magana amma ta kasa sabida kukan da yaci ƙarfinta.

Naja ce tamasa bayanin abinda ake cike.
Ai tun  bata kai da rufe bakinta ba, Abban Safiyya yayi magana cikin rawar murya  yace, "wani airport za su shiga jirgi?".
"Na abuja".  Tafaɗi haka ataƙaice.
Hankalinshi ne yayi ƙolo-lowar tashi, aikuwa ba shiri yakai zaune haɗi da dafe kansa, dana sani da baƙinci suka haɗe masa waje ɗaya, tunani ya fara to ina zai ganta? da sauri ya miƙe tsaye kamar wani zararre , duban sa ya kai ga Safiyya yace, "ta tashi mutafi" ba musu ta tashi sai famar rusa kuka takeyi.
Irin yadda Naja taga halin da Abban Hafsat ya shiga a wannan halin ne yasa hawayen da suka maƙale a idonta tun tashi su Hafsat suka zobo bata shirya ba.
Yana ƙarasawa wajan mota ya buɗi mota ya shiga, suma suka shiga dan shi Yayan Safiyya kasa magana yayi sabida bai san mi zai ceba.

Gida ya sauke su kana  ya koma hospital, koda ya shiga ɗakin da Mama take lokacin ta farka, kuma sai sunan Hafsat take faɗa, gashi jininta ya hau kuma duk wani taimako da likitoci za su bata sun bata amma jinin yaƙi sauka dan ko bacci takasa samu sai sunan Hafsat da take kira.

Abinda ya gani ne lokacin da ya shiga ɗakin yayi matuƙar bashi tsoro, dan ƙirs kaɗan ya kai ƙasa, ɗayan likitan da yaga shigowar sa ne yayi masa magana yace,
Kazo da Hafsat ɗin ko?".

Abban Hafsat rasa bakin magana yayi,sai can da yaga likita ya tsare shi da ido kana ya buɗa baki yace, "gatanan zuwa, amma bari² na kirata"..... Yana faɗin haka ya fice bai ma tsaya jin mi likita zai ce ba.

Yana fita daga ɗakin yaga Ammar zaune yayi ta gumi yana tunani, sunan sa ya kira kana yace, "Ammar ba tunani ya dace kayi ba, addu'a ita tafi dacewa da ita, dan haka ga kuɗi ka riƙe ko za su buƙaci wani abu kasayu, dan ni yanzu wanuri zanje na dawo, amma kar kaga najima ban dawo ba dan zanje wani wuri mai ɗan nisa".
STORY CONTINUES BELOW

Yace, "tau Abba Allah ya dawo da kai lafiya".

Yace, Ameen".....kana ya fice daga hospital ɗin cikin sauri.
Mai napep ya tsayar ya faɗa masa wurin da zai kaish, ba ɓata lokaci ya isa ta shar mota, kuma koda yaje motar abuja saura mutum biyu ta ciki, dan haka yace sutafi shi zai biya kuɗin ɗayan, ba ɓata lokaci suka ɗau hanyar abuji ciki yake da fargabar Allah kasa ya ganta.

  *****
Hajara ce tafito cikin shiryan ta cikin wasu ƙananun kaya musu bayyanar da surar jikin  mutum sose, iya kyau tayi, sai da kashiii, idan ka  ganta bazaka ɗauka ƴar musulmi bace, tafiya takeyi kan titi sai can ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wurin da zai kaita kana tashiga, basu tsaya da ita ko ina ba sai hospital ɗin da aka kwantar da Anwar.

Bayan ta sallame shi taƙarasa cikin ɗakin da aka kwantar da shi, tana wata tafiya kamar bata son taka ƙasa.
Ahankali ta tura ƙufar ɗakin da yake kwance tashiga, kwanci ta tarar dashi yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, dan idan ka ganshi zaka zata lifiyar sa ƙalau.

Kamar anshigo ɗakin yaji,  dan haka da sauri ya buɗi idonsa, Hajara yagani, itako tana ganin ya farka da sauri ta ƙaraso gareshi tana faɗin,

"Gaskiya kaji sauƙi sose "....tana faɗa tana sakar masa da murmushi haɗi da kai hannuta saman nasa.
Sai da yagama yimata wani kallo kana yace, "eh naji sauƙi, dan yau ma nake son su sallameni naje gida dan so nake muje kikaini wajan Malamin da kikace".

Tace, "to kama daina wahalal da kanka da wadda kake danta ta bar ƙasar gabaki ɗaya".
Tun bata rufe baki ba ya ɗago kansa da sauri yace,"wace kenan!.

Yafaɗi haka cikin razana.

"Hafsat". tace dashi ataƙai ce.

Ido ya zare haɗi da cakomuta kana yace, "ina kika kamin ita?".

Dariya ta sanya masa kana tace, "scholarship tasamu, yanzun nan ba jimawa motocin makaranta suka ɗauke su zuwa airport ɗin abuja dan acan ne za su tashi.

Ai tun bata rufe bakin ta ba ya ɗauko waya yakira wata number, ana ɗauka yace, "Salim zai samu jirgin da zai kaini abuja yanzu?".
Bansan mi akace dashi aɗayan ɓangarin ba yace,   "oky ganin zuwa yanzu".

Ko kallon ta baiyi ba ya ɗau kayansa ya bar hospital ɗin, batari da an sallame shiba.

Har zai fita tayi sauri taci gabansa tace, "ina zakaje ne?".

Ko kallon ta baiyi ba ya ture ta gyafe ɗaya ya fice warsa.
Bayan shi ta biyu tana kiran sunanshi, yana jinta amma yayi kamar bai jiba.
Haka har yazo kan ti-ti ya tsayar da mai napep ya shiga tana kallo amma batayi gi-gin magana ba dan taga yau ba sauƙi,  filn jirgi ya kashi, kuma yana sauka ba ɓata lokaci jiringin nasu ya ɗaga.

Tunda suka shiga motar ta haɗe kanta da ƙafafunta sai famar rusar kuka takeyi kamar wadda za'a raba da ranta.

Ko waɗan da suke tare a motar ba wanda bai mata magana ba, har dai suka gaji suka kyaleta, tana kuka haka dai har bacci ya ɗauke ta.
Cikin ikon Allah tara da rabi suka isa airport ďin Abuja, kuma koda suka ƙaraso ba ɓata lokaci suka shiga jirigi suka wuce India.

Minti talatin da ta fiyarsu sai ga Anwar ya dira garin abuja kuma aka tabbatar masa da basu jima da tashi ba.

STORY CONTINUES BELOW

Wata ƙara yasaka sabida wani bakin cikin da ya rufeshi, rasama abinyi yayi, sai can ya ciji yatsa kana yace,
"wallahi ko ƙarshin duniya kika kai Hafsat sai na nemuki, bari makarantar india".

Awa ɗaya da tafiyar su Hafsat sai ga Abbanta ya shigo garin abuja, ba ɓata lokaci yasa aka kawoshi airport ɗin garin,  tambaya yayi ko jirigin india ya ɗaga aikuwa aka tabbatar masa da ya ɗaga nan da awa ɗaya da suka wuce.

Aikuwa ba shiri sai ga hawayen baƙin ciki sun fara zoba a idonsa, lokaci ɗaya ya fara rawar sanyi, kuma lokaci ɗaya ya hango halin da matar sa take ciki, ba shiri ya samu waje ya zauna haɗi da dafe kansa.....


*#VOte*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY NA'IGE✍🏼*•

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 20📑*

*__________*📖  Ya kai kusan minti talatin a wajan yarasa mi zaiyi, zaman da ya keyi yaga bashine mafita ba dan haka ya tashi jikinsa a sanyaye ya tafi.
Tashar mota ya koma, kuma cikin ikon Allah koda yaje mutan ɗaya ake jira motar ta tashi, haka yashiga bawani ƙarfin gwuwa atari dashi.

Safiyya da Yayanta suna shiga gida Baban ta yafara tambayar su ina Hafsat?.

Gaba ɗayansu kasa magana sukayi,dan kowane bakinshi yayi masa nauyi sose, tambyar su ya ƙarayi cikin faɗa², Safiyya  har ta buɗi baki tayi magana sai kuma ta rushe da kuka tana faɗin,

"Baba dan Allah kayi haƙuri".... tsawa ya daka mata kana yace "baza ku faɗamin wurin da kuka kaimin ƴar ba?".
Abbas ne yayi ƙarfin halin buɗa baki yayi masa bayani, ai Mamar Safiyya najin haka ta faɗi ƙasa tana ba Baban Safiyya haƙuri, shi Baban Safiyya sabida baƙin ciki kasa magana yayi, bai ce komai ba ya saka takalman sa ya fice gidan, sabida yasan da ya buɗa baki ba zai faɗi abu mai kyau ba.

Sai bayan isha'i Abba ya sauka, masallaci  yaje yayi sallah, yajima zaune yana addu'a samun mafita  kana ya tashi yaje hospital jikinsa a sanyaye dan duk yinin yau ba abinda yasama cikin sa sabida tsananin tashin hankali.

A hankali ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita, Ammar ya fara cin karu dashi yana zaune saman kujera yana kallon Mamar sa, buɗa ƙofar da akayi ne yasa ya kai dubansa ga ƙofa, Abban sa yagani, aikuwa da sauri yazo yatare shi haɗi da faɗin, "Abba barka da zuwa".
Sai da ya zauna kan kujera kana yace, "Ammar ya jikin Ummar taka?".
"Da sauki yace".

Dubansa yayi da kyau kana yace, "tun yaushe take bacci hala".
Yace "bayan fitar ka ba jimawa".
Tea ya haɗa yasha kana yace bari yaje gida yayi wanka idan ya dawo sai Ammar yaje.

Tunda taga Anwar yashiga ke-ke napep yabar ta  tsaye takasa koda ɗaga ƙafa ta tafi bare ta mutsa, sose abin da  Anwar yayi mata ya bata tsoro, to me Hafsat take dashi wanda ita bata da?, tunanin ne taga bashine mafita ba tayi kyafa kana ta tsayar da mai napep, sunan wata ungwa  tafaɗa mishi tashiga ya kaita.

Abba na fita Umma ta farka haɗi da ƙiran sunan Allah, da sauri Ammar da ke kusa da ita ya ƙaraso gareta yana faɗin, "Umma ya jikin, mike miki ciyo?".

Buɗar baki tayi ahankali tace, "Ammar ba abinda kemin ciyo yanzu" sai da ta ɗan huta tace, "ina Abbanka yake ko har yanzu bai zomin da Hafsat ba?".
Ammar kasa magana yayi sai can yace, "kiyi haƙuri Umma nasan zai zo da ita".

Komai bata saki faɗa ba, amma tayi alwashin in har dai ta fita daga wannan hospital to ba shakka sai taje gida ganin iyayenta, dan tasan ko hakkinsu na kanta, amma ya ta iya tunda ba laifinta bane.

Bayan kwana biyu da faruwar haka jikin Umma yayi sauƙi sose dan har abinci tana iya ci da kanta, sai dai wasar ɓoyar da ake tsakanin Abba da Umma, dan yanzu baya son shigowa sai tayi bacci, dan baya son ta tambaye shi Hafsat.

Itako da ta lura da haka  data ji alamun zai shigo sai tayi kamar bacci take har sai yafita kan ta buɗe idonta.
Yau Monday, Doctor nashigowa ya tambaye ta yatakeji gami da lafiyar ta, sai tace batajin komai, magani yarubuta mata haɗi da takardar sallama kana ya ƙara jamata kunne akan ta daina sa damuwa aranta.

Bayan Doctor yafita Ammar ya ƙira Abban sa ya sheida masa ansallamesu, ba jimawa kuwa sai ga Abba yazo sutafi, kayansu suka saka a mota kana suka shiga suka tafi gida, amma duk wannan abin Abba yakasa haɗa ido da Umma har suka ƙaraso gida.

Yana sauke su ya wuce wajan aikin sa, da yamma bayan ya dawo daga aiki har zai shiga gida sai suka haɗu da Baban Safiyya, bayan sun gaisa sai Baban Safiyya yace,
"Kunɓatar min da ɗiya hankalinku ya kwanta ko?".
Murmushi Abban Hafsat yayi kana yace, "ayi haƙuri Alhaji,fushin zuciya ne da sharin sheiɗan, amma dan Allah ayimana haƙuri wallahi yanzu haka ni kaɗai nasan halin da nake ciki, amma dan Allah kar ayi fushi damu a cigaba da sanyamu a addu'a".

Sai da Abban Safiyya yayi murmushi kana yace, "ba komai, kuma inaji ajikina ƴata tana hannun nagari, kuma insha Allahu lafiya zata dawo".....daga nan suka cigaba da firar su, daga baya sukayi ma juna sallama suka wuce.

Ƙarfi tara da rabi na dare, jirgin su Hafsat ya sauka a airplane ďin India, aikuwa tunda jirigin ya sauka taji gabanta ya fara dukan uku-uku, lokaci ɗaya wasu hawaye masu zafi suka fara antayu mata, abukin tafiyar sune Sulaiman yace, "Hafsat ki shafe hawayinki ki taso mu fita".....yana faɗa yana tashi domin su fita.
Bayan sa tabi har suka zo matakalal jirgi, yana gaba tana biye dashi suma sauran na biye da su, aikuwa tana taka matakalar farko, sai wani iska mai haɗi da sanyin daɗi ya ziyarce ta, bashiri ta buɗa baki haɗi da ɗago harshin ta tafara yiwa Allah kirari.....

[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


+
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY NA'IGE✍🏼*•

*TUKWAICI*
*Sa'adatu Kaseem Yahaya, wannan pagen nakine ki kaɗai kiyi yadda kike so🥰*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 21📑*

*__________*📖 A hankali taci gaba da ta kawa saman mattakalar  jirgin har ta sauko, suna sauka gaba ki ɗaya, ba jimawa sai gashi anturu motar da zata kaisu makarantar.
Bayan angama duba jukkunan su kana suka shiga mota suka kama hanyar da zata sa dasu  da makaranta, basu tsaya ko inaba sai bakin gate ɗin  makarantar, kafin su shiga daga ciki sai Hafsat ta dago da kanta, dan tun lokacin da suka shiga motar kanta na kasa taƙi ta ɗago bare taga jajayin fata .
Aikuwa tana ɗago kanta sai da tayi suman zaune, dan ganin wannan katafariyar makaranta da tayi sai da tayi tasbihi ga Allah, makarantar tabi da kallo, wadda aka rubuta sunanta da manya haruffa, wato (GALGOTIAS UNIVERSITY).
Bata ƙarasa kallon ba direban motar ya shiga cikin makarantar, bai tsaya dasu ko ina ba sai gyefin saukar baƙi da ke cikin makarantar, bayan sun shiga sun zauna aka kawo musu abin motsa baki, bayan sun kammala kowanin su yayi wanka ya ɗan huta kafin safe sai su fara shiga makarantar.
Sulaiman ne ya kalle abukain tafiyar sa kana yace, "wai ina Hafsat?, ayya taci wani abu kuwa?, dan nasan ƙila bataci komai ba tana can tana sana'ar ta ta kuka".

Sai ɗayan wanda akekira da Safuwan yace, "wata ƙila bata ciba, amma bari nayi mata knocking idan ta fito zamu gani ko taci".

Yana faɗa yana tashi dan ya ƙarasa ɗakin da akayi mata ma sauki.

Knocking da bai wuce uku ba ta  ɓuɗe, wannda tagani bakin ƙofar ɗakin yasa ta ƙaƙalo murmushi haɗi da yin   ƙasa da kanta, kafin ta ɓuɗa baki tayi magana  yace,
"Idan kin kammala muna son magana dake".

Tace "tom gani zuwa".
Yana barin wajan itama ta koma ɗakin ta shirya jikinta tasaka hijba kana ta fito  wajan su.

Sallama tayi musu, suka amsa haɗi da bata izini sannan ta shigo.

Bayan ta shigo ta gaishe su haɗi da musu ban gajiya kana ta zauna.
Dukan su suka amsa kana suka tambaye ta ko taci wani abu ba kuka taje tanayi ba?.
Sai da tayi murmushi kana tace, "wallahi naci kuma na koshi".

Suka ce to hakan yafi sannan suka ɗan taɓa fira gami da yadda karatun su zai kasance a wannan ƙasar, bayan sun ɗanyi shuru sai Sulaiman  ya dube su kana yace,
"  Gami da zaman Hafsat  hostel ne, duk da hostel ɗin ƙasar yana da kyau amma ina ga kamar zaifi in kin yarda ko kun amice sai na kaita gidan Yaya ta dan itama karatu takeyi anan kuma tanada miji da yaro ɗaya, amma shi mai gidan nata sai wani lokaci ya kan shigo kuma ba zai wuce kwana biyu ba ya koma, dan wancan lokacin da nazo acan na zauna kuma naga zaki fi jin daɗin zama acan gaskiya, amma inkunga hakan yayi muku kuma yayi miki".
STORY CONTINUES BELOW

Gaba ki ɗayan su sukayi na'am da maganar sa  kana ya dube Hafsat da tayi shuru ba tace komai ba yace, "Hafsat mikika ce akan maganata".
Ahankali ta ɓuɗa baki tace, "ba abinda zance tunda ni ban san kan ƙasar ba, amma tunda kai kasan kan ƙasar duk yadda kayi ba komai, sai dai kar mutakura ta".
Yace, "a'a kar ki damu dan Aunty Shemah ta wuce haka".
Sai da suka gama tattaunawa kana tafito ta koma ɗakin ta kafin safiya ta waye aba kowane class sai kuma ta wuce gidan da zata zauna.

  *******

Wata unguwace mai napep ya sauke ta, bayan ta sallameshi tashiga wani longo tana shiga tafiya kaɗan sai tazo ƙofar wani ɗaki, da yake ɗakunane jere a unguwar kuma da gani ɗakunan hayane, na tsaka daga cikin su ta tura ƙofa tashiga.
Ƴan mata biyu ne aciki ɗayan na  kwance ɗayan na shirin kayan sawar su, aikuwa suna ganin ta gabaki ɗaya suka buga shewa haɗi da faɗin,
" Matar Anwar ce tazo wurin mu?".
Sun faɗi haka ciki da tsokana.
Tsaki ta musu  kana tace, "kubarni da ɗan iska, wai yau ni zaima walaƙanci akan wata banzar yarinya, wallahi naga har yanzu kansa bai daina rawa ba, amma dani yake zanci".

Tafaɗa haka ranta amatuƙar ɓace.
Ɗayan wadda ke kwance mai suna Zahara ita tace, "me ya haɗaki da Anwar ɗin naki hala?".
Kafin tayi magana sai ɗayan  mai shirin kaya wato Hafiza tace, "ta tsoniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ni dai wallahi Hajara da zaki bi tawa da kinbar Anwar da Hafsat, dan wallahi ko da zaki je wurin bokayin duniyar nan ba zai iya rabuwa da Hafsat ba, dan ni nasan son da yake ma Hafsat cikin jininsa yake, amma dan baki da imani kikabi kowace hanya kika lalata musu zama to gashi gaki ya aure ki .....aitun bata kai da rufe baki ba Hajara ta miƙi tsaye zata cikumo ta sai Zahara tayi saurin tashi tariƙi Hajara tana faɗin, "dan Allah Hajara ki kyaleta idan har ta isa tasa Anwar ya aure Hafsat, kuma bari kiji, wallahi Anwar koda mi yake taƙama sai ya aureki barin ni dashi, ai inyasan wata bai san wata ba".
Hafiza tace, "kanku akeji"  tana faɗin haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice batare da tasaki magana ba.

Tana fita sai Zahara ta dube Hajara da tacika tayi fam, abu kaɗan take jira ta fashe, Zahara irin yanayi  da taga Hajara tashiga yasa ta  ƙarasowa jikin ta sose, haƙuri ta fara bata kan ta ɗura hannunta saman dukiyar fulaninta, haɗi da kai bakinta kan na Hajara,kissing ɗinta cikin sigar rarrashi.
Sai da suka gama fanɗarewar su kana Zahara ta ƙara matse Hajara jikita tana faɗi, "ke daina sama ranki damuwa, indai Anwar ne kina zaune zaki gansa dan haka ki bar  komai a hannu na nasan yadda zanyi da shi".
Dubanta Hajara tayi, taga da gaske take dan haka tace, "nagode masoyiya ta, haka dai suka cigaba da firar su daga baya kuma Hajara tayi mata sallama ta koma unguwar su.

Tunda Umma ta dawo daga hospital ta daina sakin jikinta da Abba dan yanzu ma haduwa wuya take musu, yau ma da dare bayan ya dawo daga masallaci ta kai masa abinci yaci har yayi shirin kwanciya sai gata ta turu ƙofar ɗakinsa haɗi da sallama.

Bayan ya amsa mata ya ɗago da kansa ya kalleta ciki da son matar tasa yaci, "ƙaraso daga ciki Fatima".
Ba muso ta ƙaraso ta samu waje ta zauna nesa kaɗan dashi.
Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi saurin cewa, "Abban Hafsat, dama maganar da zan faɗa itace, ina son zanje gidan iyayena dan ina son naje na  gansu, ko banza najima banje ba,kuma idan naje bazan dawo ba har sai ka nemumin ƴata".
Tana faɗar haka ta miƙi dan ta fita.

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗin, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah karki barni wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, kuma zanci zuwa gida ki bari idan nasamu huta muje tare, dan koni ina son naje naga gashesu"......ai tun bai kai ƙarshin zanciba ta fice daga ɗakinsa yana kiranta amma tayi kamar batajiba ta shige ɗakinta haɗi da rufe ƙofa.

Tanda ta rufe ƙofa ta fara kuka mai cin zuciya da baƙin cikin rashin inda  ƴar ta take, amma a gaskiya baza iya cigaba da zama ba Hafsat ba, inhar yana son taci gaba da zama dashi sai ya nemu mata ƴar ta, dan gobe tunda safe zata ta kama hayar garinsu ko da kuwa ba zata gane gidan ba, dan ita gani take bazata gane gida ba, dan rabunta da gida kusan shekara ashirin, aikuwa tana tuna haka ta fara kuka maicin zuciya.
Ko da yazo ga ƙofar yaga har ta rufe, ai basan sanda ya dafe kansa ba haɗi  da faɗin "ya salam".....kansa ne yaji ya fara sarawa, dan haka ya koma ɗakinsa ya zauna haɗi da ɗauko magani yasha kana ya kwanta.

Koda gari ya waye bayan sun gamala komai sun shirya sunyi beark aka turu azo dasu cikin school ɗin.

Bayan sunje aka ba kowa nasa abinda za'a bashi kana akayi musu jagora zuwa class ɗinsu.

Bayan sun gama lecture ne sai Saulaiman shida abakan tafiyar su suka kai Hafsat gidan Aunty Shemah, kuma gidan ba nisa da school ɗin, shiyasa batayi wuyar ganewa ba.
Bayan sun shiga gida Aunty Shemah ta karɓe su hannu biyu² haɗi da kawu musu kayam mutsa baki, bayan su ɗan ci abinda ta kawo musu nan Sulauman ya ƙara yimata bayani akan Hafsat itama Hafsat ya ƙara yimata bayani akan Aunty Shemah.

Aunty Shemah sose tayi murna da samun abukir zama, dan zaman kaɗaice bayayi mata daɗi, dan mijinta bayar da taje ko inaba daga makaranta sai makaranta,wani ɗaki ta nunama Hafsat tace tazo ga ɗakin da zata zauna ,tashi tayi tabi bayan ta tanuna mata ɗakin, sose ɗakin yayi mata kyau, dan ɗakine mai haɗe toilet da ƙaramin  gado da wadiruf, bayan komai ya kammala sai Sulaiman yayi musu sallama yayi tafiyar sa.

*Wanene Anwar*

*#Veto*
*Comment*
*Share*


*©SUMY NA'iGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼*•

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 23📑*

*__________*📖  da hanzari matar dake ƙofar gidan tayi saurin ƙarasowa gareta tana faɗin, "Fati kitashi kinji"....tana faɗa ta ɗauku ruwa ta shafa mata a fuska.

Ba ɓata lokaci sai numfashin ta ya fara dawowa dai-dai, cikin hanzari Ummar Hafsat ta tashi tana riƙi Mama tana kuka mai cin zuciya tana faɗin, "Mama dan Allah kuyafemin".
Kafin tayi maga Baban ta dake kwance yana jin ance Fati ya tashi daga kwanciyar da yake, bakin sa na karkarwa yace, "wa na keji kamar muryar Fatina, koda gizo ne takemin ko mafarkin da na saba ne?".

Mama ta ɓuɗa baki cikin sanyi jiki tace, "eh Malam Fati itace"..tun bata rufe baki ba ya fara wa Allah hamdala kana yace, "Fati ƙaraso gareni kinji".
STORY CONTINUES BELOW

Ba musu ta ƙaraso gareshi tana faɗin, "dan Allah Baba kuyafemin nasan niyi kuskura amma dan Allah ina neman afuwarku".
Yace, "ba komai Fati, na yafemiki har a wajan Allah, kuma naji daɗin ganinki ina yaraye bam mutuba, sai dai dan Allah abinda nakeso dake shine Fati kuriƙa zumunci ko bayan raina kada kiyar da ki katse zumuncinki da ƴan uwanki,amma yanzu idan an kwana biyu ki shirya kije duk inda ɗan uwanki yake ki sada zumunci"....nasiha yayi mata sose akan tariƙa zumunci, daga baya suka tashi suka ƙarasa cikin gida.
Bayan kwana biyu da zuwan Ummar Hafsat gidan iyayenta ta kwashe duk abinda ke damun ta na ɓatan Hafsat har cikin da Hafsat tayi ta gaya musu, sose hankalin su ya tashi da suka ji wannan labarin, Malam da Mama  faɗa sukayi mata sose kana suka nuna mata ba abinda yaje mata haka face katse zumuncin da tayi, bayan komai ya lafa suka bata magana mai sanyi kuma sukayi mata alƙawarin za su taya ta addu'a Allah ya bayyana ta duk inda take.
Mamar ta  tace, 'ke Fati ke da mijinki bansa wanda yafi wani laifi ba, ace ka kwashe shekaru kana cikin garin sokoto amma kakasa leƙa ƴan uwanka, dan mi Allah bazai jarabe ku ba, ke kin kama waje kin zauna baki damu da kowa ba shima haka, wallahi kuntafka kuskure babba, amma muna ƙara godiya ga Allah da har ya nuna muku dai-dai".
Kuka Ummar Hafsat keyi kamar ranta zaifita.
Kwanta uku cin garin sai ga Abban Hafsat ya zo, aikuwa shima kansa yasha faɗa a wajan iyayenshi daga baya suka haƙura suka karɓeshi, bayan komai ya lafa shima ya faɗama ƴan uwansa abinda ke faruwa, sose mahaifinshi yayi masa faɗa kana yace ba komai ya ja masa haka ba sai katse zumunci da sukayi.
Da yake garin su ɗaya da Umma, bayan komai ya ɗan dai-dai ta tsakanin shi da iyayenshi kana yaje can wajan iyayen Ummar Hafsat suma suka ɗura daga wajan da iyayenshi suka tsaya.
Bayan kwana biyu da zuwan sa sun ɗan huta shida  Ummar Hafsat duk ida wani ɗan uwa yake sai da sukaje, haka da yayi ne Ummar Hafsat ta ɗan ji sanyi har ta fara saki jikin ta dashi, satin su uku garin dange sannan suka dawo cikin garin sokoto.

Gari na waye wa Anwar ya shirya ya isa part ɗin iyayensa, koda yaje suna parlour zaune suna fira, sallamar Anwar da sukaji ne ta katse musu fira, da sauri iyayen nasa suka ɗago kai suka kallesa haɗi da mamaki a fuskukin su.
Kafin suyi magana ya ƙaraso garesu yana faɗin, "Daddy , Mumy barka da safiya".....yana faɗa yana kwanciya saman cinyar mahaifiyar sa.
Daddy ne ya buɗe baki yace, "Son saukar yaushe? haka akazo ko ka faɗa mana sai kayimana bazata?".
Sosa ƙyar kansa ya fara kana yace, "afuwan Daddy , garin ne naji ya isheni yasa nazo tun cikin dare".
Da sauri Mumy tace, "au kace tun cikin dare ka  dawo".
Yace, "eh Mumy, amma kuyi haƙuri gajiya nayi da garin shiyasa na dawo"....kafin ya rufe bakinsa sai Daddy yace,
"Ai na ɗauka danaga ka jima acan ka samo muna sirika".

Murmushi Anwar yayi amma bai ce dasu komai ba, sai can yace, "Mumy yaunwa nakeji haďamin breakfast".
Tace, "tau autana taso muje dining kayi beark ɗin".
Daddy yace, "tashi muje har ni muyi beark ɗin....haka sukaje dining Mumy ce tayi serving ɗin su  suka fara ci.
Kowa naci abinda ke gabansa amma ban da Anwar da ke jujjuya spoon ɗin dake hannusa.
Mumy ce ta kula da haka dan haka tace, "auta na, mike dumunka naga komai baka ciba sai juya spoon ke yi".
murmushi ya ƙaƙalo kana ya buɗa baki yace, "ba komai Mumy"....kafin ya rufe baki Daddy yace, "Son bana son karya kafaɗa muna abinda ke damunka dan tunda ka shigo na fahince akwai abinda ke damunka".

STORY CONTINUES BELOW

Ƙyyar kansa ya fara sosa kana ya sadda kansa ƙasa yace, "Daddy ba komai, kwai wani abuki nane da bashi da lafiya kuma nake son naje dubinsa amma ina gudun kuce yawon yayi yawa bazan jeba".
Kallon sa Daddy yayi yace, "hmm kai dai auta faɗi gaskiya, ai bazan ce haka ba, zaka iya zuwa dubinsa aduk lokacin da ka gadama".
Murmushi yayi haɗi da  godiya ga mahaifin nasa kana yace, "Daddy ba fa nan yake ba india yake".

Sai Daddy yace, "a'a ba komai "dubiyace Allah dai ya baka ladar zuwa, amma dai ba jimawa zakayi ba autan Hajiya".

Da ameen ya amsa kana yace, "au Daddy ba da kai ba kenan"....ya faɗa haka ashagwaɓan ce, kana ya ƙara da cewa "next week insha Allah zanje".....fatar ahairi sukayi masa haɗi da sama ɗan nasu albarka.
Suna fitowa lecture ita da ƙawar ta Zeenatu, bayan sunyi ma juna sallama ita takama hanyar da za su haɗu da Aunty Shemah ita ko Zeenatu ta kama hanyar hostel.
Wajan da sukayi parking ɗin mota ta nufa dan ita gabaki ɗaya ta manta da maganar da sukayi da Sulaiman da  yace idan ta fito lecture yana nemanta.

Tunda ta fito yake kallon ta tana tafiya cikin natsowa, a hankali take taka ƙafar ta har takowa gab dashi, bata ma lura da mutum ba har tazo zata wuceshi, da yaga alamun bata ganshi ba dan haka ya ɗauku waya ya danna kiran ta, tana tafiya taji wayar ta tafara ƙara, wayar dake hannuta ta duba taga wake kiranta, dan ita atunanin ta ko Aunty Shema ce? dubawar da zatayi sai taga sunan Sulaiman na yawo saman screen ɗin wayar ta, tunawa tayi da abinda yace mata, ɗagowar da zatayi sai sukayi ido huɗu dashi, zaune yake sai aikamata da wani ƙayataccin murmushi yake, wanda ke ƙarama fuskar sa kyau da annuri.
Akalar tafiyar ta ta juya zuwa wajan da yake, shiko sai famar kallon ta yake kamar yau ya saba ganin ta, kallon da yake mata ne bata so, shiyasa sai famar tura baki takeyi waje, shiko hakan da take ba ƙaramin kyau yake ganin tayi ba, haka dai taci gaba da tafiya har ta ƙarasa wajan da yake.
Kujera dake kusa dashi ya nuna mata yace ta zauna, kamar ba zata zauna ba sai kuma ta zauna, littafin dake hannta ya ƙarɓa ya fara dubawa har ya kammala kana ya ɗago kansa ya kalleta yace, "ba ko gaisuwa".
Murmushi tayi haɗi da buɗa baki tace, "ina wuni Yaya Sulaiman".....bata kai da rufe baki ba yace, "waye yayanki hala? mama kiriƙe gaisuwar ki bana so tunda sai da na ruƙa".

Murmushi tayi haɗi da faɗi, "kai mana".
Yace, "a'a nikam kije kinemu Yayanki ba dai niba".
Alamun kuka tayi tace, "tau shikenan bari natafi tunda kai ɗin ba yayana kaki ba".

Ido ya zuba mata yana kallonta, dan yadda take magana yana masifar burgeshi, lokaci ɗaya yaji wata gogowar sonta ta ƙara laulayi zuciyar sa.
Mayafinta ya riƙe yana faɗin, "sorry My kanwa, kallonta yayi yace haka yayi miki ko?".
Bakinta ta cinnu gaba alamun yayi mata.
har ya buɗa baki zaiyi magana sai ga Aunty Shemah ta ƙarso tana faɗin, "au nan kake tsayar min da ita kana hana ta shiga  lecture ko?".
Kafin yayi magana tace, "Hafsat tashi muje, idan kana son ganinta kazo gida amma adaina tsayar min da ƙanwa makaranta".
Murmushi yayi haɗi da haɗi hannayi sa waje ɗaya yace, "tuba nake Aunty, insha Allah bazan koma ba, amma akowane lokaci zanzo gidan naku".

Tace, "naji tana" faɗar haka suka fara tafiya.
Har suka shiga mota suka tafi gida Aunty Shemah ba tace da Hafsat komai ba, bayan tayi wanka ta shirya ta fito parlour dan tayi ma Aunty magana idan akwai abinda tayi mata ya ɓata mata rai ta yafe mata, dan taga kamar fushi take da ita.
STORY CONTINUES BELOW

Tun bata ƙarasa parlour ba sai ga Affan ɗan Aunty Shemah ya zo da gudun sa  yana faɗin, "oyoyo Aunty".
Hannayita ta ware shiko ya shige yana murnar ganinta.
Ɗaukar sa tayi suka ƙarasa falo, zaune suka sameta tana duba wasu books ɗinta, a hankali ta zo ta zauna kusa da ita, bayan ta zauna ta gaisheta, bayan ta amsa suka ɗan jama kaɗan amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai, Hafsat ce ta katse shuru da faɗin, "Aunty ".
Kanta ta ɗago ta kalle Hafsat tayi mata kallon ya dai.
Sai da ta sadda kanta ƙasa kana tace, "Aunty dan Allah in akwai abinda nayi miki  kiya femin, naga kamar fushi kikeyi dani".
Sai da Aunty Shemah ta haɗi fuska kana tace, "abinda naga kinayi ɗazo shine bamin daɗi ba, ace tun yanzu har kin fara rashin shiga class, to bari kiji muddin kina son tamu tazo ɗaya sai kin aje komai ki kama karatu, bana son kiriƙa tsaye da wani makaranta da sunan wani zance, ban yadda da wanna ba koda ace Sulaiman ne ƙanena, kuma aganina karatu kika zo ba wata shiririta ba, dan haka nake haɗaki da Allah ki dana tsayi kina zance makaranta, in ma mutum yace yana sonki zaki iya bashi dama yazo nan ya sameki amma ni a makarnta bana so gaskiya, dan ko iyayenki ne baza su barki ba, kuma ni har ga Allah tunda na ganke jin kin shiga raina".

Sai da ta kai ƙarshe zanci Hafsat ta ɗago da kanta tace, "kiyi haƙuri Aunty, kuma insha Allah bazan koma ba, duk da sai dana fito class ne, amma bazan sake ba koda ma can ba ra'ayi na ba ne".
Nan dai suka cigaba da firar su shiko Affan sai gwalamniya yake musu kamar yana jin miso ke faɗa.

Bayan kwana uku da dawowar Anwar ya fara shiri-shirin zuwa india.
Tunani ya fara to idan yaje india wace makaranta Hafsat take, da yaga abin zai bashi walaha ya fara tunanin kiran Hajara dan yasan ita ce zata samu masa address ɗin duk inda take.

Kwance take tana tunani Anwar da koma yadda zai shigo hannuta lokaci ɗaya, sai ji tayi wayar ta na ƙara, wayar ta ɗauka ta duba screen ɗin wayar , sunan da tagani ne yasa tayi picking bata shirya ba.

A kunne ta kara wayar  amma bata yi magana ba sai da  ta tsaya fitar da numfashi a hankali, dan ita kanta tasan tana son Anwar so bana wasa ba.
Da yaji batayi magana ba yasa ya buɗe baki yace, Hajara kin min shuru kamar baki san waya kira ba".
Tambaya ta jefamasa tace, "yanzu kana ina ne".
"Kaduna".  haka yace da ita ata ƙaice..... kana yace da ita wani aiki nake son nasaki shine nace bari naji ko zaki iya?".
Tace, "inaji faɗa idan zan iya zan faɗa idan ma bazan iya ba zan faɗa".
Yace,  "zaki iya,  yace, address ɗin makarantar da Hafsat take nake so asamun na andia".
Wata dabara ce ta faɗu mata tace, zanyi maka amma da sharaɗin".....yace, "faɗi sharaɗin naji".
Tace, "a'a sa idan kazo zakaji sharaɗin".
Yace, "ba damuwa idan kinsamu sai ki faɗa nazo inyaso sai ki faɗamin sharaɗin kafin ki bani address ɗin".
"Naji zanje na samu, amma idan har ba ka yarda da sharaɗin ba to koda nasamu bazakaji komai daga waje na ba".
Yace, "kar  kidamu".  haka dai suka cigaba da waya daga baya kuma sukayi sallama.
Tunda lokacin Hajara ta bazama neman address ɗin Hafsat na andia....

*#Vote*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
         *1441H/2020M.*
              
   

STORY CONTINUES BELOW

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼*•

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 22📑*

*__________*📖  Anwar hafafin ɗan garin kaduna ne, sunan mahaifin sa  Alhaji Umar, fittacin ɗan kasuwa ne kuma babban ma'akacin gwamnati, yayi suna a cikin gari kaduna sose, dan kowa yasan  Alhaji Umar dallah-dallah ,mahafiyar sa  Hajiya Ruƙayya, suna da yara huɗu, Zainab, Hafsat, Sajida, sai autansu Anwar, iyayen su suna nuna musu so da ƙauna sosai, musamman Anwar da ya kasance auta, dukan su sunyi karatu mai zurfi sannan sukayi  aure, yanzu Anwar ne ya yarage baiyi ba, kuma koshi iyayen sa na son yayi amma sai wani ƙaƙale² yake musu shi sai yayi karatu mai zurfi, bayan ya kammala karatun sa ne ya ƙaƙalo zuwa sokoto dan ya dubama mahaifin sa wani ƙamfanin shi, to acan ne ya haɗu da Hafsat har ya fara soyayya da ita, sosai yake son Hafsat kuma har cikin ransa aurin ta zaiyi sai daga baya sheiɗan ya shiga tsakanin.
*Cigaban labari*

Anwar dake airport sai kai da komowa ya keyi yarasa abinyi, ji yake kamar yayi tson-tso ya ganshi Indian, rasa abinyi yayi dan haka ya tsayar da ɗan aceɓa yace ya kaishi wata unguwa.

Dai-dai wani katafarin gida ya ajeshi, kud'i ya bashi bai ma tsaya karb'ar canjiba ya wuce cikin gidan, mai gadi na masa magana amma ga baki d'aya hankalin sa bai tare da shi shiya sa bai karb'a masa ba ya wuce cikin gidan.
Bai tsaya ko ina ba sai wani ƙayataccin falo wanda aka ƙawatashi da kayan ado na more rayuwa,iya haɗuwa wannan falon ya haɗu, ɗayan kujerun ya zauna haɗe da dafe kansa lokaci ɗaya yaji kansa ya fara sarawa, carpet ɗin dake shinfiɗe atsakar parlour ya kwata, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awun gaba dashi.

Aunty Zainab ko da ta fito kwance ta ganshi a tsakiyar parlor, ba tama ganeshi ba sai data kara masa kallon kana tagane Anwar ne, da sauri ta ƙaraso gareshi tafara ta dashi tana faɗin, "Anwar lafiya katashi mike damunka?"....tafaɗi haka ciki da firgici.

A hankali ya fara ɓuɗa idonsa da sukayi masa jawur yace, "Aunty"..... girgizashi ta farayi ciki da tashin hankali tana   faɗin, "mike damunka haka duk ka rame kayi baƙi, kafaɗamin dan Allah?".

Irin yadda yaga ta rikice duk tawani tada hankalinta yasa ya buɗa baki yace, "ba komai Aunty, lafiya ce ba nida kwana biyu amma yanzu nasamu sauƙi".
Bata yarda da abinda yace ba amma sai ta kyaleshi tace, "tau Allah ya ƙara lafiya, amma katashi kaci wani abu".

"A'a Aunty  yanzu zan koma sokoto dan gobe nake son na koma gida dan har yanzu ban koma ba"......kafin ya rufe baki tace, "mi kazoyi abuja yanzu?".

Yace, "wani aiki ya kawuni nida abokina kuma koda nazo har ya wuce Indian "..... tace, "to duk da haka sai kaci wani abu kafin katafi.

Ba musu ya tashi ya ɗanci kaɗan kana yayi mata sallama ya wuce warsa.

filin jirgi ya isa, ciki  ikon Allah ya samu  jirgi ya shiga ya dawo da shi sokoto, gidansa ya isa koda yaje ga baki ɗaya  garin yaji yayi masa zafi dan haka lokaci ɗaya ya fara haɗa kayansa kamar wani ma haukwaci, dan gaskiya bazai iya bacci a cikin garin ba, gara yabar garin ko yaji sauki abinda yake ji aransa.

STORY CONTINUES BELOW

Tunda aka nemi Hafsat ba a ganta ba Baban Safiyya ya daina kula kowa a gidansa, ba yadda Mamar Safiyya batayi ya haƙura ba amma yaƙi, sose suka shiga damuwa na rashin kulasu da Baban Safiyya ya daina.

Shiko Abbas Yayan Safiyya wani tashin hankali ya shiga wanda lokaci ɗaya har kwanci yayi kuma duk ba komai ya jawu haka ba sai rashi ganin Hafsat, dan yanzu shi kaɗai yasan ya yakeji na rashin Hafsat, dan ko ba afaɗa masa ba yasan ya kamu da son ta, kuma so bana wasa ba, dan ji yake a ransa duk inda take sai ya nemuta,dan a halin yanzu ji yake bazai iya rayuwa ba inba ita.

Safiyya ma duk tabi ta ƙare dan yanzu ko abinci da ƙyar take samun ci, ga school duk bata jin daɗin zuwa kuma gashi sun kusa fara jarabawa amma komai ta daina ganewa saboda rashi ƴar uwata.l

Tunda safe Umma ta fara shirin tafiya garinsu, ta haɗa duk wani abin buƙatar ta, tana cikin shirin tafiya sai ga Abban Hafsat ya shigo ɗakin ciki da tashin hankali, da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗi, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah ki tausayamin wallahi ina cikin tashin hankali, kuma dan Allah ina son ki tsaya ki saurareni kona minti ɗaya ne Fatima".....yana faɗa amma  kamar ya durƙusa mata sabida kaɗuwa.
Ba abinda tace dashi, kuma bata fasa haɗa kayanta ba dan ta tafi.
Daya ga ba alamun wasa acikin lamarin ta dan haka ya ƙarɓe jikar da take koƙarin fita da ita yana faɗin, "Fatima bari kiji duk son da kikewa Hafsat nafiki sonta nesa ba kusa, kuma bazan hanaki zuwa gida ba, amma kibari gobe insha Allah zan kai ki da kaina, kuma kisani fa Hafsat ba ko ina tajeba  sai wajan karatu"....nan dai ya faɗa mata duk abinda ya sani game da Hafsat.
Sose Mama tayi kukan rashin ƴarta, amma duk da haka tace sai taje ganin iyayenta, ba yadda ya iya haka ya kaita tashir mota tashiga mota ta tafi garin su tabar Abba cike da kewarsu.
Awa ɗaya ta kaita tashar garin dange, napep ta hawa ya kaita  cikin garin, tunda tashiga garin gabanta sai famar dukan uku-uku yake, bakin wata ƙofar gida mai napep ya ajeta, tunda ya ajita gabanta ya ƙara tsananta faɗuwa, sallamar mai napep tayi kana ta ɗau kayan ta dan ta ƙarasa cikin gidan, gab da zata shiga gida taga wani ɗan tsoho kwance da alamu ma bashi da lafiya, har zata wuce shi sai kuma ta ƙara kallonsa, gabanta ne ya bada dummmm ai basan lokacin da tasake kayanta ba ta ƙarasa gareshi tana faɗin Baba! Baba! lafiya kuwa na ganka haka?".....tafaɗi haka tana mai sanya kuka.
Kafin ya buɗa baki yayi magana sai ga wata mata ta kurnu kai dan taga wake kuka.

Ita kuma Umma mutsin da taje ne yasa ta ɗago kanta, ɗagowar da zatayi aikuwa sai ganin wata mata tayi tsaye tana kallon ta, suna haɗa ido ta zabura da ƙarfi ta tashi tana sun tayi magana amma takasa, bawani ɓata lokaci sai gashi ta faɗi ƙasa sume.

******

Sose Hafsat ke jin daɗin zama da Aunty Shemah, kuma tana jin daɗin karatu ba kamar da tana najeria ba, dan yanzu idan kaga Hafsat kamar ba ita ba, sose kyauta ya ƙara fita kamar wata balara ba.
Yau ma kamar kullum tana ɗaki kwance tana duba wusu books ɗinta sai jin wayar ta tayi tana ƙara, kamar baza ɗauka ba kuma sai ta ɗauka, suna Sulaiman taga ya bayyana, ba ɓata lokaci ta danna picking ,kafin ta ɓuɗa baki tayi magana yace, "ki samemu muna parlour muna jiranki".
Kafin tayi magana har ya datse kiran.

Cikin tsanaki ta tashi ta gyara jikinta kana ta sanya hijab ɗinta tafito falon gidan.
Ahankali take tafiya cikin natsuwa har ta kawo cikin parlour haɗi da sallama abakinta, izini sukayi mata da tashigo, tana  buɗe labulen ɗaki sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi  yayi mata, itama ta mayar masa da martani  haɗi gashe da su, amsawa sukayi da nuna faricikin ganinta afuskar su.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun gaisa Sulaiman yace, "Aunty wai me kike ba  ƙanwar taki ta koma kalar indian"......ya faɗa haka yana kallon Hafsat yana murmushi.

Sai Aunty Shemah tace, "kodai ka ƙyasa".

kafin yayi magana abukin tafiyar su Lukuman yace, "Hafsat shikenan kin bar mu tunda kin samu Aunty gashi ko a school baki neman mu".
Murmushi tayi tace, "a'a wallahi ba haka ba, lokaci ne babu amma naso na kai muku ziyara wannan satin".
Sai Sulaiman yace, "bawani nan ke dai kin samu Aunty kin manta damu"....haka dai suka sha firarsu, daga bisani kuma sukayi musu sallama suka tafiyar su, amma ako da yaushe Sulaiman na kirata yana tambayar ta koda tana buƙatar wani abu, watarana ko bata buƙata yakan yumata aiki, sose take jin daɗi yadda yake kula da ita, amma awani gyafe tsoro takeji.

Yau Monday tunda sassafe tashirya dumin taje makaranta, parlour ta fita ta same Aunty zaune tana jiran fitowar ta, Aunty Shemah na ganin ta fito murmushi ya bayyana afuskar ta kana tace, "Hafsat ki ƙaraso muyi breakfast muwuce school dan ƙarfe 8:00 zan shiga lecture kuma saura ƙan ɗan lokaci ya cika".
A gurguje sukayi beark suka fito suka wuce makaranta, koda suka isa saura kaɗan Aunty Shemah ta makara, dan haka suna shiga tayi parking ta fito batare ma da ta kashe mota ba ta bar ma Hafsat kye ta wuce warta.
Mota ta kashe  haɗi da zare kye ɗin motar ta fito ta rufe, juyuwar da zatayi sai tayi arba da ƙawar ta Zeenatu, wadda suka haɗu da ita a nan kuma class ɗinsu ɗaya, kuma itama ƴar najeria ce, murmushi suka sakar ma junasu  suka gaisa kana suka kama hanyar  class ɗinsu, suna cikin tafiya sai jikin Hafsat ya bata kamar ana kallonta, juyuwar da zata yi sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi tayi masa kana ta gaisheshi,  magana yayi mata yace idan tagama lecture yana neman ta, tace tom sai ta fito.

Gaba ki ɗaya Anwar ya kasa zama ya kasa tsaye ba shiri ya kama hanyar kaduna cikin dare dan shi kam bazai iya zama garin sokoto ba Hafsat ba.

ƙarfe biyun dare ya isa garin kaduna, koda ya isa gida ko part ɗin iyayensa ba shigaba ya wuce part ɗinsa, ciki da damuwa  .....


*Bani da bakin magana gareku, ku ƙara haƙuri pls, abubuwane sukayi min yawa, dan Allah ina baran addu'a gareku pls*🙏


*#Vote*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITE'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 24📑*

*__________📖*  Bayan kwana biyu suna zaune da Aunty Shemah parlour  suna fira sai suka jiyo sallama bakin ƙofar parlour, tun kan su ƙarɓa sai affan ya zo da gudu yana faɗin, uncle, uncle".
Sulaman hannayensa ya ware Affan ya shiga jikin sa yana faɗin, "my son lafiya kake?".
STORY CONTINUES BELOW

Sai da suka ƙaraso cikin parlour kana Affan yace, "eh uncle". surutu ya fara mishi amma Sulaiman bai kulashi ba ya kai dubansa ga Aunty yace, "My Aunty ya kuke ya gida?".
Kafin ta amsa masa ya kai dubansa ga wajan da Hafsat ke zaune duk ta ta kura, dan ba wani kayan kirki ne ajikinta ba kuma gashi yayi musu bazata, tana so ta gaisheshi amma ta kasa sabida yadda ya kifeta da ido, shiko  yaƙi ya janye idon sa, sai jira yake ta gaisheshi, ita ko ta kasa buɗa baki ta gaisheshi, muryar Aunty Shemah ce  da yaji ta amsa masa haɗi da tambayar sa yaushe zai je gida, sannan ya mai da duban sa ga Aunty Shemah yace, "wata ƙila gobe na wuce".

Tace, "bawani wata ƙila dole gobe kaje, sabida zuwanka dole ne dan inba kaje ba sai aɗauka dan baka sonta ne zaka ƙin zuwa".
Suna cikin firar sai Hafsat ta sulale tayi ɗakin ta.
Duban Aunty yayi da kyau kana yace, "kada ki damu Aunty insha Allahu gobe zanje".
haka suka cigaba da fira har wani lokaci.

Duban  wajan da Hafsat take zaune yayi, amma sai yaga bata wajan, dubar parlour ya fara amma bai ganta ba, lura da haka da Aunty Shemah da tayi sai tace, "wai Sulaiman me ke son afkuwa ne  gareka gami da Hafsat?".  murmushi yayi haɗi da sose ƙyyar kansa, bata jira cewar saba tace,
"bari na turumaka ita".  tana faɗar haka ta tashi taje ɗakin Hafsat.
Bata jima da tafiya ba sai ga Hafsat tazo parlour  sanye da wata atamfa wadda akayi ma ɗikin riga da sikit, sose kayan suka karɓe ta duk da ba wata kwaliya tayi ba.
Zama tayi kan kujera da ke nasa dashi kaɗan kana tace, "ina wuni Yaya Sulaiman".  Bai amsa ba  sai ido da ya zuba mata yana kallonta kamar yau ya fara ganin ta.
Har zata sake maga yace, "ƴan matan Aunty ya karatu". Murmushi tayi haɗi da sadda kanta ƙasa kana tace, "alhamdullah".

Shuru ya biyu baya sai can tace, "ashe Yaya munsamu ƙaruwa, Allah ya raya akan sunnanh". da yake matar shi ta haihu shine Aunty Shemah ta gaya mata kuma dan haka ma zai koma najeria  yayi weekend ya dawo dan iyayen sa sun da meshi akan sai yaje, kuma in bai jeba za suga kamar dan bai son matar ne yaƙi zuwa, ba dan ranshi yaso ba ya amnci zai je.
Kallon ta yayi yace, "ko zaki je gobe muje tare in zan dawo sai mudawa tare?".... kafin ya kai k'arshin maganar tace, "a'a ni ba inda zanje sai na kammala karatuna gaba ki ɗaya". kallon baki isaba yayi mata kana yace, "idan ƙarshin shekara tayi naga mai barikin anan".
Murmushi  tayi tace, "Yaya Sulaman ai nasan ko kai bazaka bari na koma najeria ba sai na kammala".

Yace, "hmmm nasan ko yanzu aikwai abinda ya hana ki zuwa, da ko dan kiga sahibinki zaki zo muje".
yafaɗi haka zuciyar sa na ƙuna dan ba abinda yafi tsana kamar ya tuna Anwar.
Duban sa tayi ido cikin ido tace, "wake nan?".

Sai da ya aikai mata kallo mai kama da harara yace, "kin fi kowa sani".

Tsaf ta gano wajan da ya nufa amma sai ta sauya magana tace, "gobe da ƙarfe nawa zaka je".
Ƙyaleta yayi  kamar bai jiba har ta koma mai-mai ta masa amma bai ce mata komai ba, kuma tasan sarai yaji ta amma ya ƙyaleta.
Tashi yayi ya kama hanyar fita batari da yace mata komai ba, tana ganin haka da sauri tazo gareshi tana faɗi, "haba Yaya Sulaiman me na maka yanzu nan". tana faɗa kamar zatayi kuka.
Hankan da tayi magana ne yasa ya dubeta, lokaci ɗaya yaji son ta na ƙara fizgarshi, ji yake kamar ya jawota jikin sa, a hankali ya fara taka ƙafar sa har yazo gab da ita, kallon ta yayi ido cikin ido da  yace, "ba abinda kikayi min sai dai ina son ki kulamin da kanki kafin na dawo, duk da nasa Aunty na iya ƙoƙarin ta amma dan Allah ki ƙara kula".
STORY CONTINUES BELOW

Kwarjini yayi mata dan haka ta kwada idon ta kyafe ɗaya tana faɗin,"kar kadamu Yayana insha Allah zan kiyaye". irin yadda suke magana da junan su gwanin ban sha'awa.
Har zai tafi tace, "bakayi sallama da Aunty ba?".

Yace, "zan dawo gobe kafin na wuce". bai bari yaji mi zata ce ba ya fice warsa.
*******
Duk wata hanya da zata samu masa address ɗin ta bi kuma cikin ikon Allah ta samu masa sunan makarantar da take, amma abu ɗaya ne bata samar masa ba, wanda ita kanta bata sani ba gidan data ke zaune.
Bayan ta kammala komai ta kirashi ta faɗa masa, yace ta turu masa, sam ta manta da alƙawarin da suka yi tsakanin su, bawani ɓata lokaci ta tura masa da address ɗin, sai da ta tura masa kana ta tuna, sose hankalinta ta ya tashi, dan haka ta ɗau mayafinta ta fice taje wajan ƙawar ta zahara .
Shiko Anwar tana tura masa bai tsaya ɓata lokaci ba ya fara bincikin makaranta, bayan kwana biyu da fara bincike ya gano duk wani abinda yake buƙata, dan haka ya fara shirin tafiya.

Ana gobe zai tafi yaje ya same iyayen shi ya faɗa musu cewa gobe idan Allah ya kai mu zai tafi india, addu'a suka mishi haɗi da fatar tafiya lafiya da dawo lafiya.
Safiya na waye wa ƙarfe bakwai jirginsa ya ɗaga zuwa india.

Shiko Sulaiman tunda sassafe yazo yayi musu bankwana ya wace filin jirgi yashiga jirigi ya wace najeria.
Mama ko tunda suka dawo daga garinsu ta ɗan ji sanyi har ta ɗan dawo dai-dai amma ba kamar daba, dan burinta a kullum ta ga ƴar ta ta tadawo hannunta.

Haka shima Abba, dan ako da yaushe ba abinda yake sai addu'a da sadaka,  Safiyya  ko  ako da yaushe tana wajan su tana ɗan rage musu kyawar Hafsat, Yayan Safiyya shima ba'a barshi abaya ba, dan yanzu ko kasuwa yaje duk abinda ya sayo ma iyayenshi shi yakan sayo ma iyayen Hafsat, dan yanzu sose yake kula da iyayen Hafsat da ƙannin ta.

Ƙarfe goman dare jirgin su Anwar ya sauka ƙasar india, Sulaman ma haka ya sauka najeria.
Anwar na fitowa cikin jirgin sai yaga har abukinsa ya zo ɗaukar sa, sose sukayi murna da ganin junan su, ba ɓata lokaci ya ɗauke shi zuwa masaukin sa dake cikin makarantar, da yake koshi abukin nasa karatu yake amma shi wannan sheƙar zai kammala.

Ɗaki ɗaya ne mai ɗauke  da gado da wadirif, iya haɗuwa ɗakin ya haɗu da idan ka ganshi sai kace ba school ba, ba wani ɓata lokaci ya shiga toilet yayi wanka ya ci abinci kana ya kwanta bacci.

Shima abunkin nasa yana ganin ya samu bacci shima ya kwanta.

Koda gari ya waye bayan sunyi breakfast Anwar ya sanar da abukin sa abinda ke tafi dashi.
Sai da ya kai ƙarshe sai Abukinsa Nura ya dubesa da kyau yace, "ko dama nasan wannan zuwa ba danni kazo ba, amma ba komai  zan tayaka neman abinda kazo nema har sai kasameta, da yake tunda ƴan najeria suka zo ban wani haɗu da suba, amma kabar Monday duk wani ɗan makarntar zai fito kuma insha Allah za'a dace".
Murmushi Anwar yayi kana yace, "shiyasa nake sonka, dan tunda nayi bincike na gano makartar kuce nace abu yazo gidan sauki".

Yana faɗar haka suka tafa haɗi da dariyar samun nasara.

Tunda Sulaiman ya tafi jikin sa duk ba daɗi sai ji yake kamar wani abu zai same sa, amma haka yaci gaba da addu'a har a kazo ɗaukar sa.

Tana cikin bacci ƙarfe ukun dare sai ta farka cikin razana sabida wanin mummunar mafarkin da tayi, wanda ya bata tsoro matuƙa, ba wani ɓata lokaci ta tashi taje toilet ta ɗauru alwala tazo ta tada sallah.....

STORY CONTINUES BELOW

*#Vote*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITE'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 25📑*

*__________📖* gidan iyayen sa ya sauka ya gaishesu kana ya wuce gidansa,  part ɗinsa ya wuce kai tsaye bai ma bi taka matar tashi da Baby da aka haifar masa ba ,tana parlour  zaune  ita da ƙanwar ta da wasu ƙawayen ta, alamun shigowarsa taji dan haka ta dube ƙawayen ta  tace dasu dan Allah kujira ni ina zuwa, tana faɗar haka ta ɗau Baby ta kama hanyar part ɗinsa, duk da bata da cikakin sanin da zata ce shine amma jikinta har wani karkarwa yeke burinta ita dai ta ganshi gata gashi.

Yana isa part ɗinsa, ko kayan jikinsa ba tsaya yarage ba ya ɗau waya yakira Aunty Shemah, bayan ta ɗauka sun gaisa yake tambayar ta Hafsat, sai da ta wani haɗe rai kana tace, "ai kana da number ta".
Yace, "na ɗauka kuna tare ne amma kiyi hakuri naji kamar ranki ya ɓaci".
Tace, "a'a ba haka bane kawai naga ko iyayena baka bari na ji lafiyar su sai ka ɗauku min wani zance".
"kiyi haƙuri Aunty na". Tace, "ba komai, ka kirata kaji dan naga yau kamar bata jin daɗi"..... ai tun bata kai ƙarshin zancin ba ya datse kiran nata.
Number ta ya kamu ya saka kira, kwanci take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, tunanin mafarkin datayi jiyane takeyi, wayar tace da ta shiga rura ta mai data daga duniyar tunani, wayar ta ɗauku haɗi da danna picking ta kara a kunni ta.
Sallama tayi masa ya amsa, bayan ta gasheshi haɗi da masa ban gajiya kana yace, "naji muryarki kamar mara lafiya?".

Murmushi tayi kana tace, "lafiya ta ƙalau ya Baby tah".

karki tambayeni dan sai da nace kizo ki ganta kikace a'a, kin ga ko ba dole na faɗamiki ya Baby take ba".

Tace, "kayi haƙuri Babban Yayana". har zayi magana sai aka turu ƙofar ɗaki, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yaci gaba da firarsa.
Jikita a sanyaye ta fara takawa har ta kawo wajan da yake kwance, Baby ta aje kusa dashi kana ta zauna zaman jiran ya gama waya, baya ya gama kana ta ƙaraso kusa da shi tana faɗan, "Baban Baby barka da zuwa".
Sai da ya ɗau Baby kana ya amsa mata haɗi da tambayar ta  lafiyar ta.
Baby ya zubama ido  wadda tunda ya ɗauke ta yaji sonta na shiga zuciyar sa, huɗuba yayi mata yana gamawa sai Maryam ta dubeshi tace, "wani suna zaka saka mata?".
Batari da wani tunani ba yace, Hafsat".

Dubansa tayi da kyau tace, "kenan ka canja suna dan na zata  sunan Mumy zaka sa".
STORY CONTINUES BELOW

Yace, "a'a sai wani lokaci nasa insha Allah".
Haka dai ya daure yana fira da ita kana ya tashi yaje yayi wanka ta kawu masa abinci yaci, amma duk abinda yake ɗiyar na hannusa, wanka ne kawa da zaiyi ya ijeta.
Yana cikin haka sai akaturu ƙofa, abukin sa Jabir yagani tsaye yana masa wani kallo, a hankali ya buɗe baki yace minayi zaka yimin wannan kallon haka".

Kafin ya bashi amsa Maryam ta gashe da Jabir kana ta ɗau Baby ta fice.

Bai ce dashi komai ba sai da ya shigo  cikin parlour yace, "wai yaushe zaka gama  course ɗin da kajeyi ne?".

Sai Sulaiman yace, "sai ta gama ".

Jabir yace, "wallahi ni nasan bawani course da kaje, kajene dan kayi tsaron ta, to bari kaji wallahi baka isa ka tsareta ba, dan yanzu kazo nan amma bakasan meke faruwa acan ba, ni dai shawara ta gareka ka dawo kacigaba da aikin ka kuma kariƙe matar ka duk yafiye maka bin sauran wani".....tun bai kai ƙarshe ba ya ɗaga masa hannu yace, "Jabir daka ta!".
Idonsa ya ɗago ya kalleshi waɗan da saka sauya lokaci ɗaya yace, "bari kaji Jabir wallahi ko ɗa ɗay-ɗaya har ashirin Hafsat ta haifa tare da Anwar ba ta hanyar aure ba wallahi sai na aure ta muddin tace ta amice da haka".
Jabir yace, "har yanzu baka san waye Anwar ba, kuma waye Hafsat ba, kuma nasa ko yanzu Anwar yaje ga Hafsat zata yarda dashi dan tana masa son bana wasa ba".

Irin yadda yada yaga bacin rai afusakar Sulaiman dan haka ya tashi ya kama hanyar fita, sai da ya kawo gab da ƙofa kana yace, "nasan baka san me nasani ba gami da Anwar ba, to bari kaji yanzu haka Anwar yahe  india". yana faɗar haka ya rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi kana ya bar gidan ciki da ƙunar zuciya.
Aikuwa Sulaiman najin haka basan lokacin da ya tashi zaune ba, "yana faɗin wallahi ƙarya ne".

Ba tsaya wata-wata ba ya ɗau kye ɗin motar ya bar gidan, School ɗin su Hafsat yaje  neman Safiyya da ƙawar ta Naja'atu.
Shiko Jabir ba abunda ya tsana kamar yaji abukin sa yace zai aure Hafsat, dan shi aganinshi bata dace da Sulaiman ba, dan shi abinda yafi tsana hulɗa da talaka.
Koda ya isa school ɗin ba kowa ya samu ba, sai ɗai-ɗaiku, sabida ana weekend dan haka ya samu wata cikin ƴan makarantar taje hostel take ki rumasa Naja, amma koda taje Naja batanan taje gida weekend.
Koda ta zo ta gaya masa hauka ne kawai baiyi ba, kuma gashi bai san gida ko ɗaya daga cikin su ba, dan haka ya shigo mota ya dawo gida, Allah ne ya kaishi gida lafiya dan yadda yake gudu kamar ya gaji da ransa.

Yana zuwa gida ya kasa zama ya kasa tsaye, dan haka ya shiga mota ya kama hanyar gidan iyayen sa.
Parlour  ya tarar da Mumy sa da Abbansa, tunda ya shigo suka zuba masa ido suna kallon sa, Abban sane ya fara magana yace, "Yaro na mike damun ka na ganka haka kamar kana cikin tashin hankali?".

Sai da ya sauke ajiyar zuciya yace, "eh to Abba dan akwai wani abinda ya taso gami da karatun da naje can india  shine nake son gobe na koma"......tun bai rufe baki ba Mumy sa tace, "kar kasoma dan idan ka ga ka bar ƙasar nan to anyi suna, na gaji da wannan ƙaƙale-ƙaƙale naka fa, tunda akayi auren nan baka zauna ba bare ku fahinci juna kai da Maryam, dan haka ba inda zaka je".
Sai da ta gama Abban sa ya dube shi kana yace, "my Son kaje kashirya idan Allah ya kaimu gobe sai kaje  ɗin".

Har Mumy zatayi magana Abba ya ɗaga mata hannu haɗi da faɗin "fatar alhairi kawai nakeson kiyi masa".
Ba dan ranta yaso ba tayi masa fatan alhairi haɗi jadda da masa yaje ya tambaye Maryam duk abinda bata da tagaya masa.
Yace tom haɗi da tashi dan yaje ya fara shirin komawa, har zai fita Abbansa yace, "son wani suna kake so asawa yarinyar nan".
STORY CONTINUES BELOW

Sai da ya sosa ƙyya kana yace, "Hafsat". Yana faɗa  ya fice bai jira cewar su ba.
Wani sanye daɗi ne ya mamaye Mumy ita da Abba, sai Abba yace "mun gode da wannan kyautar".

Ita Mumy kasa magana tayi sabida daɗi, dan sunan mahaifiyar ta ne, kuma tunda ɗiya ta taso asa mata amma ƴan uwan Abba suka hana sai yanzu da Allah ya yarda asa ga jikar ta.

Kafin ya koma gida sai da ya tabbatar da ya samu bisa da duk wani abun da yake buƙata.
Lokacin da ya faɗawa Maryam tafiyar sa, har kuka sai da tayi amma dayake mai sanye ce daga baya tayi masa addu'ar tafi lafiya da dawo lafiya.
Tun shida na safe jirginsu ya ɗaga zuwa india, sune basu sauka ba sai cikin dare.

Koda ya isa masaukin sa sose yagaji dan haka ya watsa ruwa ya kwanta.

  *****
Tunda tayi sallah asuba bata sake kwanciya ba, gyaran gida tayi kana ta hada musu beark, bayan ta kammala taje tayi wanka tashiriya, cikin sauri tayi beark sannan tazo ɗakin Aunty Shemah tace zata tafi sabida lectura ne da ita da safen nan, key ɗin mota Aunty Shemah ta bata haɗi da iyimata adawo lafiya sabida ita yau bazata je ba.
Karɓa tayi da sauri ta ƙarasa wajan aje mota, tana shiga tayi mata key ta fice da sauri sabida gab take da ta makara.
Anwar tunda yayi sallah asuba ya tashi ya shirya dan tun yau yake son ya fara ne manta, sabida bashi da lokaci, dudu  sati ɗaya ne zaiyi ƙasar, abukin sa na shiryawa suka fita zuwa cikin makarantar.

Sulaiman sabida ya gaji bai farka da wuri ba, dan ko sallah yau  sai da ya makara baiyi ba, kuma yana gama sallah sai da ya kwanta, aikuwa koda ya farka rana ta fara fitowa, cikin hanzari ya shirya ko beark bai tsaya yayi ba ya kama hanyar gidan Aunty Shemah.

Koda yaje parlor ya tarar da ita tana beark, sallama yayi kana ya shigo, ido da baki ta zuba masa sai kallon sa take kamar yau ta fara ganin sa.
Ƙarasowa yayi ya zauna kana ya gaisheta, ba ta karɓa ba sai jefa masa tambayar da tayi "miya dawo da kai yanzu?".
Sai da ya ɗau kofin tea  kana yace, "akwa abinda ya mai dani, Aunty ina Hafsat?".
"Hafsat ta mai daka ko".
A'a Aunty, su Mumy na gaisheki kuma sunci kin daina kiransu".
Shareshi tayi dan sose ya bata haushe ace ya dawo jiya.
Sai da ya ta kurata da tambaya tace, "taje makaranta".

Ƙofin dake hannunsa ya aje yace bari nazo.
Mamaki ya cika ta, dan haka takasa baki sai kallon sa takeyi, dan ta lura yadda yadamu da Hafsat ita bata damu da shi ba, sai ma gani take kamar batasan yana son ta ba.
Tanayin parking ta fito haɗi da kulle motar, tana cikin haka sai ga ƙawar ta Zeenatu ta ƙaraso  tace,  "kizo muyi sauri mutafi dan munkusa mu makara, "tace to muje" .

Tafiya suke suna fira har suka kusa kai class.

Anwar da abukinsa sai sauri suke su isa wajan da suke tunanin zasu ganta, tafiya suke ita da Zeenatu, shiko Anwar yana bayan su shida abukinsa, dan har yasu ya ijesu ya wuce sabida basa sauri sai wata tafiya suke kamar basa son taka ƙasa, kuma ga hanyar da zata sada su class ɗinsu akwai cinko so da yawa, abukinsa ne ya riƙeshi yace mubi komai cikin natsowa insha Allahu zaka ganta".
Badan yaso ba suka biyewa tafiyar su har suka kawo hanyar da zata sada su class kana suka raba hanya.

    ********
Kamar wadda aka koro sai gata tashigo ɗakin tana faɗin, "Zahara! Zahara!.

Da sauri ta fito daga toilet  tana faɗin, "Hajara lafiya kuwa kikazo min haka?".
Tace, "ina lafiya tunda Anwar ya asirceni duk abinda yace namasa shi zan masa, amma ni duk abinda na nuna masa ina so wallahi bayayimin, gashi yanzu nabashi address ɗin shegiyar yarinyar nan, dan haka nake son ƙarfe ukun dare ki rakani  muje wajam Malam kinga sai na kwanan anan iyaso lokaci nayi muje".

Sai Zahara tace, "to mi kike son iya gami dashi Anwar  da Hafast ".
Hajara tace, "ni so nake iya masa abinda baya ganin kowa sani, sannan ita ko akorota daga karatun da take a india, dan na tsane jin tana can , kinga idan ta dawo tana gani tana ji muyi Aure da Anwar inya so tazo tanamuna wanki da wanke-wanke".
Tafawa sukayi haɗi da sanya dariya mai ciki da ma'anuni da yawa.

Tun biyu da rabi na dare suka tashi suka shirya kana suka ɗau hanyar gidan Malamin su....

[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITE'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 26📑*

*__________📖* Basu jima da fitaba saka samu ɗan acaɓa wanda zai kaisu wannan ƙauye, koshi da ƙyar yayar da zai kaisu, tafiya suke amma tafiyar taƙi ƙarawa dan ɗan acaɓa yaga haka yasamu waje yayi parking kana yace, "ku sauka". Sauka sukayi sun ɗauka ko wani abu zai gyara.
Dabansu yayi yace, "wai nawa ne zaku bani da har zaku kawuni cikin wannan jeji?".

Hajara tace, "nawa kake so mu baka?".
Yace, dubu biyu zaku bani".

Kuɗi Hajara ta zaro ajikarta ta miƙa masa, karɓa yayi haɗi da tada babur ɗinsa, Zahara na ƙoƙari ta hau shiko yaje babur da guda ya bar ti-tin, kururuwar kirasa suka fara amma ko alamar ya tsaya babu.

Hannu Hajara ta ɗaura akai tana faɗin, "yau munshiga uku".... kafin ta rufe baki sai ganin motar ƴan sanda tayi a gabansu, tashin hankali  wanda ba'asa masa rana, kafin su ankara ƴan sanda biyu sun fito cikin motar suna faɗan, "ƴan isaka, duk kune ke ƙara lalatamuna ƙasa". Suna faɗa suna saka su cikin mota, kuka Hajara da Zahara suka fara suna faɗin "wallahi mu ba isakanci ne yafitar da muba".... kafin ta kai ƙarshin zancin ɗaya daga cikin ƴan sanda ya buga mata kulki abaki, bashiri sai ga jini ya fara tsiyaya abakin Hajara, Zahara naganin haka taja baki ta rufe kukan ma da take  haɗiye shi tayi batare da ta shirya ba.

Ƴan sanda suna sasu suka ja mota sai police station ɗin dake cikin ƙauyi garin.
   *********
Koda Sulaiman ya isa school bai ma bi takan lectura ɗinshi ba, ya fara neman Hafsat, sai da yaje class ɗinsu ya ganta  zaune suna karɓar karatu  sannan hankalinshi ya ɗan kwanta, tunani yayi yace gwara yaje yaga ko suna da lectura yashiga, yana gama wannan tunani ya kama hanyar da zata sadashi class ɗinsu.

Gab da zai bar block ɗin su Hafsat, aikuwa sai ya hango Anwar zaune gab da class ɗin su Hafsat.

Gabansa ne yayi mummunar faɗuwa, lokaci ɗaya yanemi natsowar sa ya rasa, maganar abukinsa Jabir ne ya tuna, kuma lokaci ɗaya ya fara girgiza kai yana faɗin, "kenan da gaske ne,waye yaba Anwar address ɗin Hafsat, sai wata zuciya tace itace ta bashi da bata bashi ba taya yasan makarantar da take har yasan class ɗin da take.
Jiri ya fara ɗaukar sa lokaci ɗaya, dole yasamu waje ya zauna haɗi da laluba wayar sa  aljihu, Aunty Shemah ya kira, tana ɗauka ko Sallamar datayi bai tsaya karɓa ba yace, "Aunty, bayan tafiya ta wani yazo wajan Hafsat?".
Yayi magana ciki da ɓacin rai.

Sai da ta sauke numfashi kana tace, "Sulaiman, wai mikake son zamane akan Hafsa?, yariyar da bata damu da kaiba wadda bata masan kana son taba, haba Sulaiman ka sassautawa rayuwarka gami da Hafsat ko kasamu natsuwa".

Ba abunda yace da ita sai ƙara mai-mai tamata tambayarsa.

Abun taga bana wasa bane tace, "a'a ba wanda yazo kuma ba inda taje sai yau da tafita makaranta".

STORY CONTINUES BELOW

Tana faɗar haka lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya kana ya datse kiran.

Warin da yake zaune nan yaci gaba da zama har ta fito daga lectura,  yana ganin sun fara fitowa da sauri ya tashi ya ƙarasa bakin class ɗin nasu.

Fitowar ta keda wuya ita da Zeenatu yaja hannunta haɗi da karɓar hand out ɗin dake hannunta, ita abin tsoro ma ya bata,  tabayan class ɗinsu yabi da ita har sukaje wajan datayi parking ɗin motar ta, magana taso tayi mishi, amma irin yadda taga fuskarsa haɗe yasa taje bakinta tayi shuru, magana yayi mata fuskarshi haɗe, yace ta bashi key ɗin mota, ba musu ta ɗauko ta bashi, buɗewa yayi tashiga kana yashiga yaje motar bai tsaya ko ina ba sai gidan Aunty Shemah.
Yana  yin parking tabuɗe marfin mota tafito, shima ya buɗe ya fito, koda ya fito har tafara takawa zuwa cikin gidan, cikiin zafin nama ya zawuta ta faɗu jikinsa, kallon-kallon suka farayi tsakanin su,  rabata da jikin sa  yayi kana ya fara magana cike da ƙunar zuciya yace, "waye Anwa?!.

Gabantane ya bada dumm, lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi haɗi zubda hawaye masu zafi saboda tunawa da wannan sunan da tayi, tana cikin haka taji yasake tambayar ta.
Rasa miza tace masa tayi, dan bata san ya akayi ya san Anwar ba, kuka ta fara mai cin zuciya tace karda ace wani abu zai samuna, tafaɗi haka duk acikin zuciyar ta.
Magana ya fara cikin faɗa-faɗa yace, "ashe har yanzu kina tare da Anwar Hafsat, gayamin me Anwar keda wanda bani da, nasan ke kika bashi address ɗinki dan ya kawo miki ziyara, to bariki ji wallahi duk son dana kemiki zan iya ajeshi muddi kikace zaki cigaba da hulɗa da Anwar"....har ya buɗe baki yayi magana  amma takasa fita sai ƙoƙarin riƙe zuciyar sa yake wadda ke masa zafi kamar tafasa ƙirjinsa ta fito.
Tunda ya fara magana Hafsat ke kallonsa dan ita gabaki ɗaya tarasa wajan da yasan Anwar, faɗuwar dataga yana ƙoƙarinyi kuma gashi riƙi da ƙirjinsa alamun zuciyarsa na ciyo, ai bata san lokacin da tazo garisa tana kuka tana ƙoƙarin tareƙo shi kar yafaɗi amma ina, dan koda ta isa gareshi ya kai ƙasa, rasa mizatayi tayi kuma takasa ƙarasawa cikin gida kuma takasa ƙarasawa garishi komawa tayi kamar wata zararriya kuka ma yaƙi zo mata bakin tane tasamu ya buɗe lokacin tasamu ta fara anbatun Allah, aikuwa tana fara anbatun Allah sai gashi tayi hanyar part ɗin Aunty Shemah ciki da tashin hankali.
Parlour tasamu Aunty Shema tana duba wani book dake hannuta, cike da tashin hankali tace, "Aunty kizo karya mutu!".

Da sauri Aunty Shemah ta ɗago kanta arazane tace, "waye zai mutu?".

Kasa magana tayi, hannun Aunty Shemah taje suka tafi batari datayi magana ba.
Tun kan su isa Aunty Shemah tagan shi kwanci rai ga hannun Allah, ai da hanzari taje gareshi, kasa magana tayi lokaci ɗaya taje wajan maigida takirasa yazo suka sashi mota taje suka wuce hospital.

Taimakon gaugawa likitoci suka bashi, cikin ikon Allah sai gashi ya farfaɗo, alurar bacci sukayi mishi kana suka fito.
Suna fitowa Aunty Shemah ta taresu da yajikin nasa, tabbar mata da sukayi jiki yayi sauƙi dan nan da awa ɗaya zai farka da ikon Allah.
Sai a lokacin ita da Hafsat suka saukar da  ajiyar zuciya mai sanyi.
Cikin ikon Allah yana cika awa ɗaya ya farfaɗo, kuma alhmadullah dan yasamu sauƙi sose, likitocin naganin haka suka basu Aunty Shema damar ganin sa.
Aunty Shemah ta fara shiga ɗakin, aikuwa tunkan ta ƙaraso gareshi yace, "Aunty ina Hafsat?".

Mamaki abin ya bata amma ta basar tace, "Sulaman miyasameka haka har ya tadamaka da ciyon zuciya?".

Kafin yayi magana sai ga Hafsat tashigo ɗakin, ƙarasowa tayi wajansa kana tamasa yaji, bai karɓa ba sai jefumata tambayar da yayi.

Yace, "da gaske wajanki yazo, kuma har yanzu kuna tare?".
STORY CONTINUES BELOW

Sai da tashefe hawayen da suka zuba a idonta kana tace, "Yaya Sulaiman kabar wannan zanci har sai munfita daga nan, bakaga bakada lafiya"..... Tun bata rufe baki ba yace,

"Idan har kina son nasamu sauki to ki gayamin gaskiya".
Ita dai Aunty Shemah sai kallon su take saboda mamaki da tsoron Allah duk yacika ta.

Ahankali ta buɗa baki tace, "wallahi duk abinda kake magana akai bansan dashi ba, to waya ga yamaka nayi alaƙa da Anwar, kuma waya gaya maka har yanzu munatare, wallahi ni tunda na bar Anwar bansaki ganin saba har ila yanzu, kuma dan Allah kadaina yimin zancishi in har kana son ganin farin ciki na".
Tafaɗi haka tana mai haɗa hannayen ta waje ɗaya.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kana yace, "duk zan baki amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma daga yau na ba zaki sake fita school ba har sai ya bar ƙasar nan".
"badawa".
Haka tace dashi ataƙaice.

Ita dai Aunty Shemah ba abinda take sai kallon ikon Allah, dan sose abun nasu ya bata mamaki, kena duk ciyon sone yatada mishi da ciyon zuciya .

Bata ida mamaki ba sai da taga Sulaiman ya tashi tsaye kamar bashine suka kawo rai ahannun Allah ba.

Duban su tayi bata ce dasu kumai ba, tace, "to tunda kungama muje gida".
Tana faɗin haka ta kama hanyar fita batare da tajira mi zasu ce ba.
Bayan ta suka bi har suka kawo wajan mota, buɗewa sukayi suka shiga kana taje motar, basu tsaya ko ina ba sai gida....

Tundaga lokaci Hafsat bata sake fita makaranta ba, shiko Anwar, ba inda bai je nemataba a school ɗin amma bai ganta ba, har hostel yasa adubu masa amma bata can, kuma gashi lokaci ya tafi amma baiyi komai ba, sose hankalinsa ya tashi na rashin ganinta, har yake tunanin kodai Hajara bata bashi address ɗin dai-dai ba, yace ko idan ya bincika bata bashi dai-dai ba, to sai ya wahalar da ita, dan sose ranshi ya ɓaci na rashin ganin Hafsat da baiyi ba.
Da yaga alamun bata cikin makarantar ya fara shirin dawowa gida n9....

*#Vote*
*Comment*
*Share*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITE'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 27📑*

*__________📖*  Anwar yana gama shirin tafiya lokaci kawai yake jira, amma ransa bai yi daɗi ba sose, dan yaji zafi rashin ganinta, yana cikin haka sai ga iyayensa sun kirashi bayan ya ɗauka haɗi da gashesu, Abban sa yace, "Anwar nace kaje gidan Yayan ka Aminu  kuwa? duk dana san baya ƙasar amma kafin ka dawo kaje ka kaima iyalinsa ziyara".

Shi sam ya manta dawani Yayanshi sai yanzu da Abbansa ya kirasa.

Anwar yace, "to Abba zanje zuwa anjima dan yau ma nasun na taso amma tunda zanje gidan Yaya Aminu to sai gobe dan nasan idan naje Aunty Shema nacewa sai na kwana kafin nadawo, har ma idan taji nayi sati garin nan".

STORY CONTINUES BELOW

Abba yace, "ba damuwa amma daga kwana ɗaya ban aminci ka kuma kwana ba, kadawo gida sabida akwai aiki da yawa a office".

Yace, "tau Abba insha Allahu zan dawo, ka gaishemin da Mumy tah".
Abba yace, "naƙi kai kakirata".
Murmushi Anwar yayi kana yace, "yanzu kuwa Abba". Yana faɗar haka ya datse kiran.

Mumy sa yakira suka sha fira kuma ya tabbar  mata zaije gidan Yayanshi Aminu daya ƙara kwana ɗaya sai ya dawo gida.
Tunda ya hanata zuwa makaranta bata sake zuwa ba, kuma shima tunda suka dawo hospital bai ƙara dawo gidan ba.

Tunani maganar sa ta farayi inda yace wai in har tana tare da Anwar zai barta, tana kawowa nan tayi ƙwafa kana tace, "yau da a ce duk abinda ke duniyar nan na Anwar ne, kuma zai malkamata shi to bazata ƙarɓaba bare ta dawo masa sabida ƙinsa da take.

Tana cikin wannan tunani taji marata tafara ciyo kaɗa-kaɗan magani ta ta tashi ta ɗaku tasha amma kamar ma anci ta ƙara dan wata ƙirsa ce tamata aikuwa bashiri tafara birgima a cikin ɗakin, sose take wahala indan zatayi period kuma idan ciyo yazo har ƙafafu take riƙe mata shiyasa yanzu da take kwance ta kasa tashi ta ɗauku magani bare ta ƙara sha taji ko zata samu sauki.
Anwar kiran Yayanshi Aminu yayi ya bashi address ɗin gida, aikuwa da bashi bai tsaya wani ɓata lokaci ba yabi address ɗin gida sai gashi har ƙofar gida.

Knocking yayi musu ba jimawa akazo aka buɗe masa yashiga, parlour  yashiga da sallamar sa, Aunty Shemah ce dake zaune ta ƙarɓa masa  haɗi da ɗago kanta ta dubeshi sose.

Aikuwa tana gininsa ta faɗaɗa murmushi haɗi da faɗin, "wazan gani a gidannan".

Murmushi yayi haɗi ƙarasowa ya zauna kusa da kujerar da take zaune.

Gasheta ya fara kana yace, "ina Affan?".

Tun kan tabashi amsa sai gashi yafito da gudu yana faɗin, "Aunty zansha  Ice cream".
Yafaɗa haka kamar zayi kuka.

Tace, "baka ga Uncle ɗinka bane naji baka gasheshi ba".

Sai alokacin ya lura da mutum zaune, aikiwa da saurin shi yashiga jikinsa yana murna yana faɗi" "Uncle ɗina yaushe kazo, kazo kabani lce cream".

Aunty Shema tace, "shi bai san komai ba sai abashi lce cream".  rigama taga zaiyi musu kuma bazai bari su gaisa ba dan haka ta tashi taje ta ɗauko masa ta bashi, yana murna ya karɓa yana faɗin, "naje wajan Aunty Hafsat".

Aikuwa yana faɗin Hafsat sai da gaban Anwar ya bada dumm.

Kallon Aunty Shema yayi yace, "baƙine daku a gidan ?".

Tace, "eh ƙanwata ce tazo".

Yace, "oky".
Tace, "saukar yaushe Anwar kuma ya kabar su Mumy da Daddy?".

Wallahi nayi sati ɗaya ƙasar nan, gabaki ɗaya na manta da kuna ƙasar nan ai da nan zan sauka, amma kuyi haƙuri dan ƙila yau ma zan kuma dan naso nayi muku  kwana ɗaya amma gaskiya bazan iyaba sabida ƙasar duk naji bata yi min daɗi".
Yakai ƙarshin zancin damu baiyane afuskarsa.

Aunty Shemah tace, "bawani kai dai dan Yayanka bashi ƙasar ne shiyasa baza zauna ba, kuma na gode".
Yace, "a'a Aunty zan dowo nan bada jimawa ba insha Allah".
Gabaki ɗaya jikinsa duk yayi sanyi kuma kamar kar yaji Affan ya faɗi sunan Hafsat.

Aunty Shema tace, "amma sai zuwa anjima zaka tafi ko?". Yace, eh".

Suna cikin haka sai ga Affan ya fito ɗakin Hafsat da gudunsa yana faɗin, "Mumy zo Aunty batada lafiya".

STORY CONTINUES BELOW

Gaban Anwar ne ya ƙara faɗuwa yarasa dalilin haka.

Aunty Shema tace,  "mike damunta?".
Komai baice da itaba sai ma hannuta da yaje, ba musu  ta tashi ta bishi zuwa ɗakinta.

Kwance ta sameta sai birgima take atsakiyar ɗaki, da sauri Aunty Shemah tazo gareta tana faɗi, "subuhanallah, Hafsat meke damunki, irin yadda taga tana riƙi ciki ya tabbatar mata cewa marata ce ke ciyo, dan haka ta ɗauko magani ta bata tashi.

Bata jima da bata maganin ba ciyo ya fara lafawa, bawani ɓata lokaci bacci yayi awon gaba da ita.
Aunty Shemah na shiga ɗakin Hafsat, sai ga Sulaima ya shigo parlour ɗauke da sallama abakinsa, Anwar dake zaune yana kallon labaru ya amsamasa tare da miƙa masa hannu suyi musabaha, hannun ya bashi sukayi musabaha

Kafin ya bashi hannu sai da ya kalleshi sose ya tabbatar da Anwar ne, ranshi ne ya ƙara ɓaci, kenan shi tamaida marar hankali ita da Aunty Shema, to yaji ba ita ta bashi address ďinta ba to yanzu waya bashi na gidannan, yana cikin wannan tunanin sai Aunty Shemah tafito daga ɗakin Hafsat.

Tana fitowa taga Sulaiman ya sadda kansa ƙasa, ƙarasowa tayi tana faɗin, "waye nake shirin gani yau a gidannan".

Ɗago kansa yayi haɗi da sanya wani murmushin sannan ya  gaishe ta.

Sai da ta zauna ta amsa kana tace, "yanzu nake shirin nakiraka nace maka Hafsat ba lafiya, amma yanzu tasamu sauki dan tana shan magani bacci yayi awun gaba da ita, sai idan ta farka sai ka ɗan dubata tunda ita naga alamun ba duba kanta take sonyi ba".
Dubanta yayi yace, "tana inane?".

"Tana ɗaki". Haka tace dashi.

Tashi yayi yashiga ɗakinta, kwance ya ganta kuma da ganin baccin datake bana daɗine ba, dan lokaci-lokaci sai ta yatsane fuska.

Karasowa yayi wajanta hannusa ya ɗura kan nata yaji ko da zafi, ba zafi sose amma da alamu tana jin jikin.
Anwar zaune yake amma duk lokacin da suka anbace Hafsat, sai yaji gabansa ya faɗi, sose yaso yaga wannan Hafsat sabida shidai yana jin wani baƙun al'amari atare dashi gami da ita, amma sai ya basar dan yasan wannan ba ita bace.

Bayan ya gama dubata ya fito kafin ta tashe yayi mata wasu tambayoyi.

Falo yasame su Aunty da Anwar zaune suna fira, har yaso yafita kuma sai yadawo ya zauna, bai jima da zamaba Anwar ya miƙi yana faɗi, "Aunty ni zan tafi dan so nake na sauka cikin lokaci dan Daddy yace min aiki yayi yawa office".

Alamun rashin jin daɗin ne ya bayyana fuskar ta tace, "bawani ba kadai yi niya ba, kuma na gode ka gada su Mumy".

Haƙuri ya bata tare da tabbatar mata bajimawa zai dawo kuma wajanta zai sauka.
Addu'ar sauka lafiya ta masa sannan yayi ma Sulaiman sallama ya fice.

Yana fita Sulaiman ya dube Aunty Shemah da idonsa da sukayi ja yace, "Aunty waye wannan?".

"Anwar ƙanin Baban Affan ne, da Babanshi da Babanshi uwa ɗaya Uba ɗaya".
Yace, "tun yaushe yazo nan?".

"Iya karsa awa ɗaya" tace dashi.

Har ya buɗe baki yayi magana sai ga Hafsat ta fito riƙi da ciki tana faɗin, "Aunty ki kaini hospital zan mutu".
Tana faɗa tana tangaɗi alamun zata faɗi, saura ƙiris ta faɗi Saulaiman dake zaune yayi sauri ya tare ta tafaɗa jikinsa.
Bawani ɓata lokaci suka wuce da ita hospital.

Wata hospital ce ta mata  wadda yataɓa aiki a  can suka wuce da ita, suna isa da ita likitoci suka karɓeta suka wuce da ita ciki ɗakin bincike, sai da suka kammala komai sannan suka fito sukace yasamesu office.
STORY CONTINUES BELOW

Suna isa office ɗin nasu bayan sun gaisa da yake sun sanshi sose, sabida wancan lokacin yayi aiki a hospital ɗin kuma sose suka ji daɗin zama dashi dan ba yadda basuyi ya zauna yaci gaba da aiki dasu ba yace a'a shima zaije ya taimakawa ƙasarshi.

Duban doctor yayi yace, "ya mai jikin ina fatar tasamu sauki".

Sai da doctor ya gyara zaman sa yace, "eh ta  samu sauƙi sose kuma idan takiyaye dukukin da zamu bata kuma ta kiyaye shan magani to zata sauma sauƙi dan haka sai ankula sose".
Aunty ta dube doctor tace, "mike damunt?".

Sulaiman yace, "a'a Aunty ai ba sai munji ba kawai mu barsu suyi aikinsu".

Aunty tace, "a'a gwara muji inyaso akiyaye gaba".

Tace, "Doctor inajinka".

Doctor yace, "dama bawani abu babba bane lokacin dai datayi miscarriage ba awani bata kula sose ba, kuma gashi tana buƙatar haka dan yanzu idan ba  kulaba aka aji wannan abun da ya tushe mata mahaifa yakan iya zama sanadiyar haka bazata sake ɗaukar ciki ba".

Wata ajiyar zuciya Aunty ta sauke mai ƙarfi kana tace,  "ayi mata duk abinda yakama doctor".
Tana faɗar haka bata tsaya komai ba ta fito daga office ɗin ranta aɓace.
Irin yadda Sulaiman yaga ta fito jikinsa duk sai yayi sanyi dan shi bai so doctor yayi bayani akan matsalar Hafsat ba,  da yasan zatace ayi mata bayani wallahi da bai bari ta shigo office ɗin ba, tunanin yaga bazai ƙareba, dan haka ya tashi yabita yaji mi zata ce.
Tunda Anwar ya bar gidan gabansa ke famar faɗuwa har inda yazo masaukin sa ya haɗa duk wani abun buƙatar shi yayi sallama da abukinsa sannan yarakashi filin jirigi.

Shidda na yamma Anwar yabar ƙasar india zuwa ƙasar sa ta haihuwa wato nigeria.
Koda yaje har tashiga mota shi kadai take jira, dan da ace makulin motar na hannuta da tuni tajima da bari hospital ɗin.

Yana ƙarasowa yashiga  motar yaja suka tafi gida, har suka isa ba wanda yayiwa ɗan uwansa magana.

Yana yin parking ta buɗe mota tafito zuciyar ta na ƙuna sabida wani baƙinciki da ya rufe ta.
Bayan ya kashe motar ya bi bayan ta, parlour yasame ta sai safa da marwa take cikin parlour.
Ɗayan kujera ya zauna kana ya dube ta yace, "Aunty"......kafin ya kai ƙarshe tace, "dakata Sulamain! bana son jin komai daga bakin ka, wato ni kamai da wawuya marar hankali shiyasa har za ka ɗauku budurwar dakake tare da ita ka kawomin gida matsayin ƴar makaranta wai ita mai kamun kai ko!  kuma har kana iƙirarin auren ta, to kasani daga yau ba kai ba ita dan haka kar ka kuskura kadowo da ita gidannan kuma yanzu zan kira su Abba na gaya musu abinda ake ciki, ni kodama nayi mamakin abin da ya maidaka ƙasar nan da sunan karatu ashe kai kadai kasan karatun da zakayi".

Haka taci faɗanta har ta gama bai ce da ita komai ba, sai da aka ɗau lokaci yana zaune kana ya buɗe baki yace,

"Haba Aunty wallahi bansanki da haka ba, ni nasan Aunty na mai tausayi ce da kuma  haƙuri kuma nasan Aunty na bata zartar da hukunci har sai tayi bincike akai, dan haka nake ruƙunki dan Allah ki tsaya ki saurareni plees".

Dubanta yayi yaji miza tace amma sai yaji bata ce komai ba, irin yadda yaga tabada natsuwar ta yasan zata saurareshi.

"kamar yadda kika sani ina son  Hafsat so bana wasa ba dan tun lokacin da na fara haɗuwa da ita makaranta nakamu da sonta, amma itako alokacin ba soyayya ce gabanta ba kartu shine gabanta shiyasa ko saurarena bata tsayayi ba, ban jima da haɗuwa da itaba ne nazo ƙasaranan dan na yi phd,    sai dai duk wani mutsi nata idan tayi sai nasani koda kuwa bani tare da ita, kuma dakika ce Hafsat yarinya tace wallahi ko ɗaya, ni banta sanin Hafsat ƴa mace ba, ke ba itaba duk wata mace babu ta inba Maryam matata ba, Aunty,  Hafsat daki ka gani wata ƙaddara ce ta afka akanta, wadda duk wani musulmi mai imani ya tausaya mata, data na nigeria Allah ya haɗata da wani sheɗanin saurayi wanda ya illata mata rayuwa kuma duk da haka bai bar ta ta huta  ba yaƙi ya rabu da ita, nikuma lokacin dana samu labarin haka shine nayi shige da fice  har tasamu  scholarship na tafiya waje karatu ko zai rabu da ita, to nayi nasar rabasu amma yanzu haka yananan yana neman ta ruwa ajallo, danshi na hanata fita makaranta kwana biyu wannda ke da  ita  baku san  dalilil haka ba".
STORY CONTINUES BELOW

Dubanta yayi yace, "Aunty labarin Hsfsat nada tsayi amma kiyi haƙuri sabida duk lokacin dana tuna sai nayi ƙwalla, amma wani lokaci zan baki insha Allah".

Kallonsa tayi da kyau kana ta buɗa baki tace, "yanzu har kasan yadda take amma kake ƙoƙarin kajefa kanka aciki, to bari kaji koda zan yarda taci gaba da zama gidannan to bazan yarda ka aureta ba, dan da alamu ba ajinka bace, dan haka nake baka shawara tun wuri kaciri wannan so dakake mata dan gaskiya bazamu barka ka aure yarinyar da bata da kamunka ba".

Yace, "Aunty kuyi haƙuri dan inaji ajikina rasa Hafsat dai-dai yake da rasa raina, Aunty bansaki da haka ba, kuma ki gayamin gaskiya, zaman da Hafsat tayi agidannan akwai  abinda tayi wannda zai nuna rashin kamun kanta?".

Kai ta girgiza masa alamar a'a.
"Kingani dan haka Aunty kirufamin asiri karki bari kowa yaji wannan maganar kuma kitaya ni da addu'a".

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kana tace, "na fahince ka, kuma insha Allah ba maijin wannan zance".

Yace, "yauwa Aunty na, na gode sose".

Murmushi tayi kana tace,  "yaushe zaka zo muje muga yadda jikin nata yake?".

"Sai gobe, sabida ina tunanin idan muka tafi tare da ita zamu dawo inyaso taciga da shan maganinta".
Tace, "to haka yayi".

Sallama yayi mata yatafi da sunan gobe zai dawo.

    *******
Safiyya ce kwanci ɗakinta ita kadai, ba abinda take sai aikin tunanin ƴar uwata Hafsat, tayi kuka har tagaji na rashinta, gashi har yanzu ko waya basu taɓayi ba, kuma ga Babanta har yau fushi yake dasu, duk abu yazo ya haɗe mata waje ɗaya, dan yanzu maganar da ake Baban ta yace wata biyu ya bata ta kawo masa miji dan aure zaiyi mata, kuma ita duk cikin masu sonta bataji wanda ya kwanta mata araiba, tana ciki haka taji Yayan ta Abbas na kiranta, da sauri ta tashi ta fita.
Zaune ta samesu shida Mama zaune, ƙarasowa tayi ta zauna kusa da Mama tana faɗin, "gani Yaya".

Wata leda dake gabansa yace, "gashi kije ki kawa Umma, kice ina gaisheta anjima zanzo".
Karɓa tayi tace tau bari nasa hijab ɗina".
Tana sawa ta ɗauka tafice Mama tace tana gaisheta....


*#VOTE  COMMENT SHARE*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 28📑*

*__________📖*  Koda taje gidan su Hafsat, sose Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo".

Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu nida Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nanne, nasan da kinzo".

STORY CONTINUES BELOW

Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar".
Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka.
Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙincikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sose ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bincika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka".
Magana take amma hawaye na zuba a idonta.
Safiyya ma da taga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bincike koda Allah zai sa musamu number ta".

Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka.

Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta.

     *******
Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station  sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?.

Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu,  shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala.

Gaban DpO  aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?".

A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane".

DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane".

Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa.

Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?".

Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu".

Takai karshin maganar tana kuka sose.
Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita.

Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?".

Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat".

Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi".

Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije".

Tace, "a'a  tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika.
Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu.
Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu.
Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu.

STORY CONTINUES BELOW

Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila.
Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi  kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah.
Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin,

_Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._
_Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._

Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta.

Gyafin Umma ma haka ta kasance.

Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata.

Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan.
Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso".

Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na".

Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan".

Tana faɗa tana jan kuma tunsa.

Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke".

Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu.
Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?.

Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida".

Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida.
Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani".

Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye".

Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah.
   *****

Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa,  dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu.

Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji....

*#VOTE COMMENT SHERA*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITES ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

STORY CONTINUES BELOW

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 29📑*

*__________📖*  Tana kwance ɗakin su Zahara, dan tunda suka dawo bata koma ɗakinta ba, bari tayi har ta ɗan dawo dai-dai, dan tasan da taje can ɗakinsu zasu cikita da tambaya miya faru da ita, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta na ƙara, tsaki taja sannan ta ɗauka daniyar tayi piking, aikuwa sunan da taga ya baiyana kan screen ɗin wayar ai basan lokaci da ta tashi zaune ba haɗi da faɗi, "Zahara zo kigani".
Tafaɗi haka ciki da farin ciki.
Zahara dake toilet da sauri ta fito, kafin tayi magana Hajara ta nuna mata wayar ta da ke rura, sunan da taganine yasa tayi guɗa haɗi da taka rawa, sannan tace, "kada ki ɗauka barshi har sai ya kawo kanshi".
   Hajara tace, "kodama bani daniyar ɗauka, aikuwa haka tayi ta ƙarar har yagaji da kira ya aje wayar zuwa ajima ya koma kira  ko zai ta ɗauka.
Anashi ɓangare ba ƙaramin haushi yaji na rashin ɗaukar wayar da batayi ba, lokaci ɗaya yaji gwara yaje da iran yadda yakeji shi baya iya zama bai gantaba, part ɗin iyayensa ya nufa cikin sa'a koda yaje lokacin suka fito dan yin beark, ƙarasowa yayi wajansu kujrar dinning yajewo ya zauna sannan ya gaishesu, bayan sun amsa sai Mumy ta dube Anwar da kyau, kana tace , "Autana, wai mike dumunka naganka yau duk kawani ya mutse kamar ba kaiba".

Sai Daddy sa yace, wallahi tunda yaje sokoto ya dawo nake ganinsa haka, kafaɗamuna idan akwai abinda ke damunka muji idan zamu iya baka taimako sai mu baka, amma katsaya kana tawani ɓoye muna abu, gaskiya bamasan haka".
Yakai ƙarshin maganar yana dubin Anwar ranshi kamar a ɗan ɓace.
Jikinsa a sannyaye yace, "a'a Daddy ba abunda ke damuna gaskiya, kuma da kukace duk na yamutse, ai kwanan ina fama da zazzɓi ne shiya kawo min haka amma yanzu alhmadulillah".

Ba dan sun yarda ba suka ce to Allah ya ƙara lafiya.
Daddy yasake magana haɗi da duban Anwar yace, "kuma kashin sati nasama za'aje neman aurenka da Saudat, ƴar gidan Alhaji Sambo".
Da dauri Anwar  ya ɗago kansa yace, "mikace Abba!.

"Abinda kunnenka yaji shi nace".

Yace, "gaskiya Daddy ni ba ita nake so ba".

Ai Daddy da Mumy  lokaci ɗaya suka ɗau salati  kana suka ce atare, "baka sonta!!.

"Eh" yace dasu, ai tun bai rufe baki ba Daddy yace, "wallahi Anwar karya kasha kuma baka isaba dan bazaka maidani ƙaramin mutum ba, farko kace kana so yanzu kuma kace baka so, to bari kaji wallahi ba gudu baja da baya in har kaga ba iyiba to ɗayan mune bashi da rai".
Yana faɗar  haka suka tashi domin su bar wajan ransu amatuƙar ɓace, wato su Anwar zai rainawa da hankali ya maidasu ƙananan mutane.

Shima ɗin ranshi amatuƙar ɓace ya tashi ya je ɗakinsa, key ɗin motar sa ya ɗauka, ai fusace yazo ya fige motar ya kama hanyar garin sokoto.
Gudu yake kamar ya fira sama  cikin awa huɗu sai gashi yazo garin sokoto, hanyar da zata sadashi da unguwar da Hajara take zaune ya ɗauka, gudu yake ko kallon gabansa bayayi, kwatsam gaji abu yaba da gab gab, har yaso yaƙi tsayawa, amma irin yadda yaga mutane sun taso masa yasa ya tsaya amma ba dan ransa yaso ba.
Kuda yafito cikin motar yazo wajan dan yaga waya bige, wani mutum shi ba tsofo ba kuma shi ba yaro ba, yagani kwance da alamu ko numfashi bayayi, aikuwa Anwar na ganin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin hanzari yasa wasu daga cikin mutanin aka ɗaukeshi a kasa mota kana suka wuce hospital.

STORY CONTINUES BELOW

      *******
Kwance take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jikinta, wayar tace ta fara rura, ɗauka tayi batare da ta buɗe ido ba bare ta duba wake kiranta, muryarsa ce dataji yasa ta shaidashi .
Sallama yayi mata kana ta karɓa sannan ta gaisheshi, shuru ne ya biyu baya sai can yayi magana cikin kasalaliyar murya yace, "Hafsat".

Da taji haka sai da taji wani abu ajikinta kana ta buɗe baki can ƙasan maƙoshi tace, "na'am Yaya".
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "yajiƙin naki, ina fatar kinsamu sauƙi".

Tace, "sosai kuwa dan yanzu wasai nake jina kamar banyi ciyo ba".

murmushi yayi kana yace, "kodama  nace bari na gayamin ko zakije gida kiyi hutun ƙarshin shekara a can? inyaso idan hutu ya ƙare sai nabiya miki kuɗin jirgi ki dawo".
Tun bai kai ƙarshin zancen ba tace, "Aunty Shema zata je ne".
Yace, "a'a ita sai ta kammala zata koma dan kwanannan mai gidanta zai zo".

To nima gaskiya bazanje ba, dan koni bazan sake komawa gida ba sai na gama karatu gabaki ɗaya, amma inaso idan kaje kayi min abu ɗaya, ka karɓumin number Safiyya da Naja'atu please".

Rasa mi zaice da ita yayi, dan haka yace, "tom naji, ƙoƙari datse kiran ya fara, sai tayi saurin faɗin, "in ba damuwa inaso na koma hostel da zama tunda mijin Aunty zai zo ka ga kar na takurasu".

Kasa magana yayi sai can yace duk yadda kikayi dai-dai ne".
Yafaɗi haka ransa a ɓace yana faɗa ya datse kiran batare da ya ji mizata sake faɗa ba.
Tanajin yadda yayi maganar tasan baiji daɗin abinda tace ba, amma ita gaskiya ji take idan yazo yatar da ita gidan kamar ta takurashi dan haka ma yasa tayi wannan tunanin.

Ummar Hafsat ce zaune tayi tagumi abin duniya duk yabi ya dameta ga Baban Hafsat tun safe yafita har yanzu bai dawo  gida ba, kuma takira wayarsa amma ance kashe take, kuma gashi su Marwan har yanzu basu dawo ba bare tace su nemumatashi wata ƙila yaje wurin aikin sane, dan yanzu gabaki ɗaya duniya tayi musu zafi dan tun wancan watan aka sallame Abban Hafsat daga aiki, sabida wata sata da a kayiwa , company kuma a kace sai sun biya, haka Abban Hafsat ya tattara duk wata ƙadara tashi ya sayar yabiya su kuma suka sallameshi daga aiki, a cewarsu har dashi cikin masu yimusu sata, abubuwa duk sun tsaya dan ko karatun su Marwa ya tsaya sabida ba abinda za ayi afani dashi wajan cigaban karatunsu, abun dai sai wanda ya gani danshi yanzu sai sun fita kasuwa sunyi dako sannan zasu samun abinda suka ci, ko Baban Safiya yayi musu aike ko Abbas Yayan Safiya.

Yau ma kamar kullum akatashi ba komai a gidan, dan ko abin da zasu karya babu kuma gashi Abban Hafsat ko kwabo baya da, dan haka yace a bari yazo, fita yayi yaje wajan wani abokinsa ko da zai samu rance, to yana kan hanyar tafiyane ya kawo dan ya tsallake ti-ti bai san da wani abin hawa ba, dan haka yazo dan ya tsallaka, aikuwa yana dab da tsallakewa yaji wani abu yabashi gab-gab......

*#VOTE COMMENT SHERA*

*©SUMY NA'IGE*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
        *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

   '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITES ASSCIATION*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

STORY CONTINUES BELOW

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 30📑*

*__________📖* Tun lokacin bai saike sanin inda kansa yake ba sai a gadon hospital, lokacin da ya farko, da ƙyar ya  buɗe bakin sa  ba abinda yake ambatowa sai sunayin Allah, yana cikin haka sai ga Anwar ya shigo, da sauri ya karasa gareshi yana faɗin, "Abba sannu ka farka? ya kakeji yanzu?".

Bai ce dashi komai ba, sai da ya kuma wata magana yace, "Abba ko kana da waya a kira iyalinka a shaida musu halin da ake ciki?".

Sai da Abban Hafsat yaji an ambace iyalinsa sannan ya ɗago da kansa ya buɗe baki da ƙayar yace, " ina tunanin banzo da waya ba, amma idan kana da ita sai nasaka number yarona ko mai ɗakina  ka kira".
Yayi wannan maganar kamar sheɗar sa tafita daga jikinsa.
Sosai Anwar ya tausayawa halin da yake ciki dan har ga Allah bai da niyar ya tsaya, amma da yaga halin da wannan bawan Allah yake ciki yaji zai tsaya har yasamu ɗan sauki.
Wayar sa ya ɗauku ya miƙa masa yace, "Abba gashi kasanya number".

Ba musu ko ya karɓa, da ƙyara yake danna wayar har yasanya ya bashi yace yakira ya faɗa musu halin da a ke ciki.
Ringing da bai wuce uku ba aka dauka, Maryar namiji yaji dan haka yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake faɗa masa Abbanka yace, "a sanar da ku yasa mu haɗari dan yanzu haka an kwantar dashi asibiti, amma da sauƙi dan har ya farfaɗo kuma shi ya bada number ka a kiraka"....tun bai kai ƙarshin zancin ba sai Marwan yafara magana cike da tashin hankali yace, "dan Allah wanne asibiti?".
Wata hospital ɗin kuɗe ce  ya faɗa masa, yace gasu nan zuwa yanzu.

Aikuwa Marwan na gama waya da Anwar ya ƙarasa gida ciki da tashin hankali ya faɗawa Ummar su halin da ake ciki, hannun ta ɗura saman kai tafara kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar Marwan ya rarrashe ta tayi shuru kana suka shiriya sukaje hospital ɗin.

Dayake hospital ɗin da ya kaishi sannan na ce aciki garin sokoto, dan haka basusha wahala wajan gane wajan da yake ba.

Suna shiga ɗakin da Abba yake suka tarar da Anwar zaune kusa dashi shiko Abba yana bacci, da sauri Umma ta ƙaraso garesa tana kuka tana faɗan, "dan Allah kar katafi ka barmu Abban Hafsat".

Yana cikin bacci yaji kukanta, dan haka ya buɗe idonsa, hannu ya ɗura saman kanta, ɗagowa tayi da kanta, alamun yayi mata da tayi shuru , ba musu ko ta ɗan rage kukan da takeyi.
Anwar dake zaune yanajin sun ambace Hafsat sai da gabanshi ya faɗi, shi bai san mike faruwa dashi ba, duk lokacin da yaji sunan Hafsat sai yaji faɗuwar gaba.
Tashi yayi yayi musu sallama yace zuwa ajima zai dawo.
Da fitarsa bai tsaya ko inaba sai wajan da a kace masa zai ga Hajara, yana isa kuma a kace yanzu suka bar wajan, yinin ranar duk inda yake tunanin zai ganta yaje amma bai ganta ba, sosai yaji zafin wannan lamar yayi danasanin zuwan sa garinnan yanzu, dan da yasan haka zata faru dashi da bai zo ba, kiran sallah da yaji anayi ne yasa yayi parking ɗin motar sa yashiga masallace,  bayan an idar da sallah sai limamin wajan yayi karatu tare da  karanta wasu ayoyi na alƙur'ani kuma ya fassarasu har inda ya kawo cewa duk wani bala'i ko musiba idan sun afku gareka to ka yawaita sadaka, kuma duk wani abu dakake san samu to yawaita sadaka, nan dai limamin yaci gaba da wa'azi da nuna mahin mancin sadaka, sosai Anwar ya natsu yana saurarin abinda ake magana akai, dan rabanshi da yaje wurin wa'azi ko ya saurareshi har ya manta, bayan limamin ya kammala kana a kayi sallah isha'i sannan Anwar yafito daga cikin masallacin, aikuwa bai bar unguwar da yake ba sai da yafitar da kuɗi masu yawan gaske ya fara sadaka, da yake unguwar da ya tsaya marasa ƙarfi sunfi yawa, aikuwa sai ganin mutane kake suna fitowa maza da mata yara da manya wajan karɓar sadaka.

STORY CONTINUES BELOW

Duk kuɗin dake hannunsa sai da yara bar da su, kuma suna ƙarewa sai ga wata tshowa tazo wajansa tana faɗin, "dan Allah Alhaji ka taimaka min wallahi ƴata ce bata da lafiya kuma likitoci sunce sai ammata aiki kuma wallahi bamu dasu dan yariyar marainiya ce".
Tafaɗi haka hawaye na zuba a idonta.
Rasa mai zaiyi yayi dan kuɗin dake hannunsa sun ƙare dan haka yaje mota ya ɗauko cheque, rabin million ya rubuta mata yace gasu ayi haƙuri, sosai ƴar tsohor nan taji daɗi lokaci ɗaya ta fara suburbuɗu masa da addu'oi tana faɗin, yadda kayaye min wannan baƙinciki kaima Allah yaya ye makashi haka ta cigaba da kwararo masa addu'a har yabar wajan.
Masalacin da yayi sallah ya koma, limamin masallacin ya je sukayi magana dashi a kan zai gyara masallacin, dan masallacin yana son gyara sosai, dan haka ba ɓata lokaci ya rubuta cheque  ɗin million ɗaya ya bayar yace a gyara masallaci, sosai sukayi masa addu'a daga baya ya shigo mota ya dawo hospital dan yaga ya mai jiki.

Tuƙi yake amma sai jinsa yake kamar anɗauke masa wani abu aka.

Koda yaje asibiti jikin Abba Alhmdulillah dan sosai yasamu sauki dan shi abin har mamaki ya bashi, gaishesu yayi kana ya aje musu abinda ya sayo musu sannan yayi musu sallama kan sai da safe idan ya dawo, sosai suka yi masa godiya irin yadda yatsa ya jajirce akan ciyon Abba, dan yanzu sau tari mutum ya bige mutum amma ba zai tsaya ba bare ya bashi kulawa, wani ko ya tsaya da zaran ya kai shi asibiti zai gudu, amma shi ya tsaya har yana faɗin gobe zai dawo, tunanin da Ummar Hafsat keyi kenan.

Yana fita daga ɗakin sai ga Safiyya tazo ita da iyayenta da Yayan ta, Allah ne kawai bai haɗasu ba, dan saura kaɗan suyi karo da Yayan Safiyya akan hanya.

Yana fitowa a hospital bai tsaya ko ina ba sai ma saukin sa, yana shiga bayan yayi parking ɗin motar yafito bai tsaya ko ina ba sai falon gidan,  zama yayi saman kujera three seated ya ɗan huta, dan yanzu ji yake kamar an ɗauke masa wani abu kai, wanka yaje yayi sannan ya kwanta, wayar sa ya ɗauku ya kira iyayensa ya shaida musu wani uzuri ya kamashi na gaugawa yanzu haka yana sokoto, basuce dashi komai ba sai fatan alhairi.
   ___________________
Suna gama waya da Anwar wata ƙawarta takirata tace, "wai hala Hajara baza kizo birthday ɗina ba, kuma kinsa za'ayi casu".
Aikuwa Hajara najin haka tace, "kar ki samu damuwa yanzu zaki ganni".
Tana gama faɗar haka ta tashi tashiga toilet tayi wanka, sosai ta ɗan ɗasa kwaliya kamar wani abu bai same taba.

Kallon Zahara tayi dake zaune tace, "Zahara zaki rakani shukura hotel wajan birthday ɗin ƙawata?".

"A'a bazanje ba dan kinsan ba wajan zuwa nane ba".
Cewar Zahara.

Tace, "ba damuwa ni zanje sabida nasan akwai harka".
Tana faɗar haka ta kama hanyar fita daga ɗakin.
Zahara tace, "ki tsaya mufita tare inyaso kowa yaje wurin da zashi.

Haka kuwa sukayi dan suna kawowa bakin ti-ti ko wace ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wajan da zai kai ta.
Dai-dai shukura hotel aka aje Hajara, kuɗinsa ta bashi kana ta ƙarasa daga ciki, tun bata ƙarasa ba ta fara jin kiɗa natashi kamar zai tsaga ƙasa, koda ta ƙarasu wajan da aka kiɗan  yacika sosai, maza da mata kuwa sai rawa yake kuma cikinsu ba mai shigar kirki, kace su duk ɗiyan arnane.
Tana cikin tafiya taji an rungumuta ta baya, juyuwar da zatayi dan taga kowaye, bashiri taji bakinta cikin nasa, a hankali yake tafiya da ita har ya ƙarasa gaban musu kiɗa, a hankali ya cire ta daga jikinsa, da sauri ta ɗago ido ta kalloshi dan taga kowaye, murmushi ya sakar mata itama ta mai dar masa da martani, dan ta gane kowaye, lokaci ɗaya a ka cigaba da kiɗa suna rawa ciki da shauƙi.
Bayan angama kiɗa da raye-raye kuwa yazo ya zauna a ka kawo abin mutsa baki, suna cikin haka ita dashi sai ga wasu ƙawayen su sun zo suka ci tazo minti biyu, ba musu ko ta tashe taje, wani ɗaki suka shiga da ita, zama sukayi saman kujerun dake jere a cikin  ɗakin, basu jima da zama ba sai ga wata ƙawar su tafito tana tafe tana rangwaɗa kamar wata arniya, gaban Hajara tazo wani ƙofi ta miƙo mata tace, "karfi ki shanye dan ke kaɗai zan ba, kinsan kayan harka ba kuwa a ke baiwa ba".

Tafaɗa haka murmushi ɗauke a fuskarta.

Ba ɓata lokaci Hajara ta ƙarɓa ta kafa kai tanasha.

tunda ta fara sha suka fara wani murmushi mai ɗauke da ma'anuni da dama.

Bata ɗauke kai ba sai da ta shanye.

Ƙofin ta miƙo mata tana murmushin jin daɗi.

Fira suka tsayayi daga baya suka fito dan kowa yaje wajan da zashi.
Koda suka fito mafi yawan cin mutane duk sun watse dan suna can suna fira mutane har sun fara tafiya.

Koda Hajara ta zo wajan da suke zaune har wannan mutum yayi tafiyar sa.

Wajan ƙawayen ta taje suka cigaba da fira daga baya kowa ya kama gabansa.
Sabida dare yayi Hajara bata tsaya komai ba tadawo ɗakinsu sabida bata jin daɗin jikinta.

Tana zuwa ko ta kan Zahara bata biba tayi kwanciyar ta.

Tana cikin bacci taji kamar wani abu yana murɗarta, lokaci ɗaya ta sanya wata ƙara wadda yasa duk wanda ke layin sai da ya farka, Zahara dake ɗaki ɗaya da ita ciki matsanancin tsoro ta faraka haɗi da ƙarasawa wajan ta, ido tazara tare da ɗaura hannu a kai tana faɗin, "nashiga uku Hajara mi yasa meki haka?".

        *******
Sulaman tun daga lokacin bai sake kiran Hafsat ba, amma sai famar nemar mata aiki yake sabida baya son ya bar ƙasa batare da ta fara aiki ba, dan idan tana aiki albashinta zai isheta har tariƙe kanta batare da ta nemi taimakon kowa ba, kuma cikin ikon Allah ya samar mata aiki a wata asibiti, sosai taji daɗin haka dan haka tace zata cigaba da zama gidan Aunty shemah batare da ta koma hostel ba.

Sai da yaga komai ya dai-data wajan aikin ta sannan ya tattaru nashi da nashi ya dawo ƙasar shi ta haihuwa ciki da kyawar ta.

Ita ma haka ta kasance gareta da har kuka sa da tayi lokacin tafiyarsa.

Haka dai tacigaba da karatu kuma tana zuwa wajan aikin ta, batada wata matsala ko damuwa, matsalar ta itace yanzu Ummar ta take yauwan mafarki a ko da yaushe, dan tunda tazo bata taɓa kewar gida ba sai wannan lokaci, kuma bataji zata iya tafiya ba har sai ta ida phd, dan yanzu shekara ɗaya ce ta rage mata  .....

Soyayya mai ƙarfin gaske tashi tsakanin Hafsat da Sulamai, wanda a yanzu ji suke in ba ɗaya guda bazai iya rayuwa ba, kuma duk wani ɗan uwa Sulaiman yasa Hafsat, dan har waya sukeyi da iyayenshi, sosai suke sonta itama haka, kuma yanzu kowani burinsa yaga ya mallaki ɗan uwansa, ita kanta Aunty Shemah har mamaki take a kan wannan soyayya tasu, jira suke Hafsat ta ida karatunta sannan aje ayi maganar aure gidan su.

+

     ******

Bayan kwana biyu Abba yaji sauƙi sosai dan har an salame shi yadawo gida, kuma duk da haka Anwar yana kula da su sosai, dan tunda yazo gidan yaga halin da suke ciki suka  bashi tausayi dan haka duk bayan kwana biyu ya kanzo yaga yaya suke, kuma sosai yake taimaka musu, dan yanzu har makaranta ya maida su Marwa, Abba ko ya samar masa aiki a company siminti, kuma yanzu alhmdullih komai na Abba ya fara dawo ahankali, kuma ko Yayan Safiyya ba'abarshi a baya ba dan shima sosai yake kula da su Umma.


*A gurguje*


Zahar ciki da fargaba ta ƙaraso wajan da Hajara ke kwanace wadda ta naɗe waje ɗaya kamar ranta zaifi, lokaci ɗaya kamanunta suka canja, ba abinda ke fita bakin ta sai wasu yawu masu yauƙi, knocking ɗin ƙofar Zahara da akeyi ne ya fargar da ita, cikin tsoro da fargaba ta ƙaraso wajan ƙofar ɗakin tana faɗi, "waye?".


Muryar ƴan layinsu taji dan haka da sauri ta ƙarasa jikin ƙofara taɓuɗe musu.


Ko magana basuyi mata ba suka shigo ɗaki dan suga mike faruwa? Hajara da suka gani kwance sai birgima take kamar ranta zai fita.


Ɗayan wanda suka shigo ɗakin ya dube Zahara yace, "Zahara mike faruwa da ƙawarki?".


Jiki na ƙarƙarawa tace, "wallahi bansani ba koni haka na ganta".


Sai ɗayar mace tace, "to wallahi tun bata mutuba ki samu mai napep ya kaita can layi buge  ya aje dan wallahi ta mutu ɗakin nan sai ƴan sanda sun tambaye ki".


Sosai Zahara tashiga ruɗuwa, jiki na karkawa tace, "to yanzu ina zan samu mai napep cikin wannan dare?".


Sai ɗayar mace tace, "kizo muje ɗakin Yawale idan zai yadda sai ya ɗauko motarsa ya kaiki inyaso da kun aje ta kujuyu".

Haka ko ta kasance, dan da ƙyara Yawale ya yarda suka je, koda suka je mutane basu fara fitowa ba, dan haka suka ajeta dai-dai bakin ƙofar wani ɗaki suka tahowar su.

Koda mutane suka fito sukaganta yasha da ƙasa, waɗan da suka santa su sukaje school ɗinsu aka nemu ƴan garinsu aka haɗata dasu, su sukayi duk yadda za suyi aka kata gidansu, sosai iyayenta suka shiga tashin hankali lokacin da aka kawo musu ita, ita ba matattaba, ita ba mai rai ba, dan sose take jin jiki.

Koda labari yariske saurayinta, sosai hankalinsa ya tashi kuma duk wani bincike yayi amma bai ganu kamai gami da lamarin ba, dan ko ƙawayen ta antambaya amma bawani abu da akasamu wanda zai nuna ambata.


STORY CONTINUES BELOW

     ********

Suna tashi daga wajan aiki yashigo mota, bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar gidansu Hafsat, yana fitowa ƙanninta suka fara yimasa oyoyo sabida yanzu jinshi suke kamar wani ɗan uwansu, bai ma tsaya wani neman izini ba ya shiga cikin gida bakinsa ɗauke da sallama.


Ummu dake tsakar gida tana girki ta karɓa masa murmushi ɗauke a fuskar ta, kujera da ya gani ce ya zauna kana ya gashe da Umma.


Bayan ta amsa ya tambaye ta Abba, tun kam ta buɗe baki tayi magana suka jiyo sallamar Abba.


Amsa suka yi haɗi da gaisheshi.


Anwar da ya ganine ya faɗaɗa murmushin sa, hannu ya miƙo masa sukayi musabaha kana suka cigaba da firarsu.

Suna cikin haka har Umma ta kammala abinci ta kawo musu shida Abba suka ci, bayan sunci sun ƙoshi suka koma ɗura wata fira, suna cikin haka sai ga Safiyya ta shigo gidan ɗauke da sallama a bakin ta, gaishe da Umma tayi kana ta ƙasara wajan Abba dan ta gaisheshi, har ta buɗe baki tace, "Abba ina wuni"....bata kai da ƙarasawa ba sabida ganin Anwar da tayi zaune gaban Abba, cikin tashin hankali ta buɗe baki tace, mugu mika zoyi muna agida? ina ka kaimin ƴar uwata!".

Tana faɗar haka tazo gareshi haɗi da cungumo  masa rifa tana faɗi, "wallahi sai ka nemun ƴar uwa".

Irin yadda yayi mata shuru bai ce komai ba, yasa ta raramu wani icci dan ta buga masa,  da sauri Abba dake zaune wanda mamaki yaci kasa ya tashi ya karɓe iccin dake hannuta, amma duk da haka sai da ya shafe wani sashe na jikinsa.


Komawa tayi kamar wata zararriya, koma ɗauko wani tayi  dan ta buga masa da ƙyar Umma da Abba suka shawu kanta ta ɗan natsu, lokaci ɗaya ta fara kuka tana faɗin, "mi kazoyi gidan nan? Ko ka ɗauka ta nan ka karasamin ita?".


Gabaki ɗaya kan Anwar ya ɗauri, ga mamaki wanda ya a ddabe shi a zuciya, ahankali ya ɗago idonsa waɗan da sukayi jajar yace, "Safiyya dan Allah kiyi haƙuri ki nunamin wajan da take wallahi da gaske ina sonta, kuma ashirye nake dan na aure ta".

Wata harara ta antayo masa sannan ta fara kici niya ta ƙwace daga riƙon da Abba da Umma sukayi mata, suna cikin haka sai ga Yayan ta Abbas yashigo gidan, aikuwa kamar kar yashigo ta ƙwace daga riƙon da su Umma suka yimata ta faɗa jikinsa sannan tace, "Yaya Abbas ga wanda ya lalatamin Hafsat, shi ne sanadin rushi duk wani jin daɗinta, kuma shine yayi mata ciki kuma daga baya ya guje ta.... aitun bata kai ƙarshin zanci ba sai ga Abbas gaban Anwar zai kai masa naushe, da sauri Abba yace, "Abbas kada kasuma wallahi zan ɓata maka rai!!".

Faɗa Abba ya fara yi masu sosai sannan suka natsu, bayan komai ya lafa nan Safiyya ta faɗa musu komai wanda tasani tsakanin Anwar da Hafsat, sosai su Abba da Umma ransu ya baci, dan ita Umma sabida baƙin ciƙi kasa magana tayi ba abinda take sai kuka baƙin ciki.

Abbane ya dube Anwar da kansa ke ƙasa ba abinda yake sai dana sani da zubar da hawaye yace, "ashe dama haka rayuwar ka take? to ina maka  nasiha da kaji tsoron Allah, kasani duk abinda kake Allah na kallon ka, kuma ba abinda zance da kai sai dai nace kaje na barka da Allah".

Tun Abba bai kai da rufe baki ba Anwar ya durƙusa gaban Abba yana kuka kamar ransa zai fita yana faɗin, "wallahi Abba na tuba kodama sharin shaiɗan ne amma wallahi son gaskiya nake mata"....tun bai ka da rufe baki ba Abba da Umma suka shige ɗakinsu suka kulle ransu amatuƙar ɓace.


Abbas nagani haka ya tasa ƙeyar Anwar gaba yace ya bar musu gidansu kuma yaja masa kunne akan kar ya kuskura ya kuma dawo gidan.

Ciki da rashi abinyi Anwar yaja motar sa ya bar unguwar.

Allah ne ya kawoshi ma saukin sa, dan yadda yake jan motar ko gani bai yi, yana yin parking ɗin motar yayi haka ya buɗe marfi motar ya fito wani abu yaji ya dakar masa zuciya, lokaci ɗaya ya dafe ƙijinsa, cikin ƙarfin hali ya fito daga cikin motar dan ya ƙarsa falon gidan, ta ko ɗaya zuwa biyu ya faɗi a farfajiyar wajan lokaci ɗaya numfashinsa ya ɗauke.


STORY CONTINUES BELOW

Mai gida da ya gama rufe gate yazo ya shiga ɗakinsa yaga Anwar yashe a ƙasa kamar bashi da rai, da gudunsa yazo gareshi, rasa mi zaiyi yayi dan haka da gudun sa yaje wajan wani maƙocinsa ya faɗa masa halin da ake ciki, daya ke koshi abukin Anwar ne dan haka da sauri yazo suka ɗauke shi suka kaishi hospital.

Abbas yana ganin Anwar ya tafi shima ya kama hanyar gida, Safiyya ko ta zauna taci gaba da kuka, Umma ko sai da ciyon ta yatashi sosai tasha wahala kafin ya lafa.

Iyayen Anwar da suka ji Anwar shuru  dan haka suka kira wayar sa amma bata shiga dan haka hankalin iyayensa ya tashi sosai, dan haka ba ɓata lokaci suka kama hanyar sokoto dan suje suga ko lafiya ɗan su yake.

Koda suka isa garin sokoto suka samu labarin abinda ya same ɗan su, dan haka basu tsaya ɓata lokaci ba su tafi hospital ɗin da yake, da ƙyar suka samu aka bari suka ganshi sabida har yau bai farfaɗo ba, sosai hankalinsu ya tashi ganin halin da ɗansu ke ciki kuma autan su.


Koda suka tambaye doctor da ke kala dashi dan suji mike damun ɗan nasu, sai doctor ya shaida musu cewa ya kamu da ciyon zuciya saka makon wani abun da yake so ya samu amma bai samu ba, kuma likitan ya shaida musu suyi ƙoƙari su bashi abinda yake so inhar suna son yaci gaba da shaƙar numfashi a durun ƙasa.

Hankalinsu ya tashi sosai,  haka dan mahaifiyarshi taji  har kuka sai da tayi.

Kwanan su uku sannan Anwar ya farfaɗo daga dogon suman da yayi, bayan ya farfaɗo suka sake yi masa allurar bacci, sai da ya kwana huɗu sannan iyayenshi suka samu ganawa dashi.


Aikuwa yana ganinsu ya fashe da kuka yana faɗin, "Daddy zan mutu, ku taimaka min kuce su bani ita wallahi inasota sharin shaiɗan ne yashiga tsakanin mu amma wallahi har cikin zuciyata ina sonta....tari ya farayi mai haɗi da jini aciki, ruɗewa iyayensa sukayi dan haka da sauri suka kira likita suka shaida masa halin da ake ciki, da sauri suka zo suka fara bashi taimakon gaugawa.

Mahaifayar Anwar kuka take ba ƙau-ƙautawa, sabida halin da taga ɗanta keci, ƴa-ƴanta mata tayi ma waya tace su zo suga Anwar dan yayi nisa.


Sosai hankalinsu ya tashi dan haka su huɗu suka shigo jirgi zuwa sokoto.


koda suka zo suka ga halin da Anwar yake ciki hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, dan haka su yanke shawara zasu fita dashi waje a duba musu lafiyar sa, musamman halin da suka ga iyayayesu sun shiga, dan haka ba ɓata  lokaci akayi masa base zuwa ƙasar india.

Yayan su Aminu ɗan Yayan Daddy suka kira suka faɗi masa halin da ake ciki dan haka yace to su haɗu acan india dan yanzu haka baya nigeria.

Cikin kwana ɗaya   akayi musu base suka wuce ƙasar india, kuma cikin ikon Allah sai gashi ankawoshi hospital ɗin da take aiki.


Dayaki yanzu suna shiri-shirin kammala karatunsu, dan abu mai wuya ne kesa tayi wata ɗaya ƙasa, dan ita inbanda Sulaiman da gaskiya sai ta ƙara wasu watanni, amma tasan bazai bar ta taƙara koda kwana ɗaya ba bare wata ɗaya dan shi burishi a yanzu duk bai wuce ace ya mallake ta ba amatsayin matar sa.


Zaune take laptop na  gabanta tana wani bincike gami da karatun, wayar tace tayi ƙara, kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauku, sunan da taga yana yawo kan screen ɗin wayar ne yasa ta sanya wani murmushi wanda ya ƙarama fuskarta kyau da annuri, ɗauka tayi haɗi da karawa akunnin ta, sallama tayi masa amsawa yayi tare da faɗin amarya ta, i miss you".


Yafaɗi haka tare da rufe idonsa.


Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "miss you too angona".


Shuru ne yabiyu baya, sai can yace, satin nan ne za'ayi bikinku ko?".


"A'a sai wani sati".

Haka tace dashi ata ƙaice.


Gaskiya bazan iya jirin har wani sati ban ganki ba, dan haka ki shiya tarbona daga gobe zuwa jibi".


"Da gaske?".


"Ki zuba ido zaki sha mamaki, wani sanyin daɗine ya mamaye mata zuciya sannan ta buɗe baki cikin marai-rai cewa tace, "My ango nah".


Amsawa yayi yana mai jin wani sanyi azuciyar sa.


Tace, "idan ban saka aiki ba ina so dan Allah".... kuma sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa .


Yace, "ƙarasa mana ina ji".

Yafaɗa haka da sigar rarrashi.


Tace, "koda-kodama ina so in ba damuwa zan turu maka address ɗin gidansu Safiyya ka dubumin ita da iyayen ta dan Allah ba danni ba".

Ta karasa maganar kamar zatayi kuka.

"Dan wannan ne kike so kimin asarar hawayenki to karki suma, yanzu ki turumin anjima zanje insha Allah".


Wani murmushi jin daɗi ta sanye har shi kansa sai da yaji sautin murmushi, kana tace, yanzu zan turum ma".

Tana faɗa ta da tseki.

Kominti uku ba'ayi ba ta tura masa.

Aikuwa zuwa yamma ya shirya yabi address ɗin da ta bashi har ya kawo gidan su Safiyya.

Yaro aika yace yakira masa Safiyya, Ko da yaro yaje Safiyya na zaune sai aikin tunani take musamman yanzu da Babban ta ya matsa mata sai ta fitar da miji dan aure yake son yayi mata.


Tana cikin haka taji ance ana sallama da Safiyya, gabanta ne ya bada dummm, dan ita batayi dakowa yazo wajan taba.


Mamar tace  ace gata zuwa, kallon Safiyya dake zaune Mama tayi tace. "to maza ki tashi kije kin bar mutum waje yana jiranki".


Dan kar ma tayi mata magana yasa tana faɗar haka ta haɗi fuska.

Safiyya da taga alamu haka ba musu ta sanya hijab ɗinta ta kama hanyar waja.

Tsaye ta ganshi nesa da gidan su kaɗan, dan haka ta ƙarasa gareshi bakin ta ɗauke da sallama.


Amsawa yayi sannan tace, "bangane ka ba".


Sai da yayi murmushi  yace ko gaisuwa babu?  ina fatar kece Safiyya".


Yafaɗi haka ajere.

Kai ta girgiza masa alamar eh".


Sai da ya numfasa sannan yashiga yimata bayani dallah-dallah har sai da ya kammala.


Kuka ta sanya masa sannan ta durƙusa gabansa tace, "dan Allah ka taimaka min ka kaini wajan ta dan girman Allah".


Magana take hawaye sai famar zuba yake akan kuncin ta.

Magana yayi mata yace in har iyayen ki zasu yarda to zai kai ki har wajan Hafsat, sosai taji daɗin abinda yace da ita dan haka tace yazo suje ta kaishi wajan iyayen Hafsat yayi musu bayani ko za su samu natsuwa atare dasu.


Ba musu ko yayarda yaje yayi musu bayanin inda Hafsat take kuma da wajan da take zaune, godiya sukayiwa Allah kana sukayi masa godiya sannan suka ce in akwai yadda za'ayi  suna son suje  suga ƴar su, yace kar su damu su shirya zuwa jibe sai suwace.


Haba murna tsakanin Umma da Abba ba'a magana dan kamar anyi musu albishir da shiga aljannanh.

Koda Baban  Safiyya ya dawo Abban Hafsat ya gaya masa, sosai yayi farin ciki yace shima yana son yaje yaga ƴarsa.

Cikin kwana uku aka yimusu base suka wuce india.....  to asauka lafiya.

Tunda safe ta shirya ta fito tana faɗin, "Aunty ni dai zan wuce a taya mu da addu'a".

Daya ke yau za suyi jarabawar ƙarshe, addu'a Aunty Shemah ta riƙa kwararo mata har ta fice daga gidan.

Koda ta isa school ƙawar ta Zeenatu na jiran ta dan saura minti uku a fara exam, tana cikin wannan tunanin Hafsat ta ƙaraso wajan da take tsaye tace, "muje".

Batace da ita komai ba suka fara tafiya, suna kawo wa baki class ɗin suka tsaya sabida sai an yi bincike kafin kashi ga, sabida wata naura ce aka umarce kowanin su da yariƙa idan ta yarda da kashiga sai abar ka kashiga, haka dai har aka kawo wajan su Hafsat, ba ɓata lokaci suka shiga cikin class ɗin amma kowane mutum kujerar sa da na ɗan uwansa akwa ƴar tazara kaɗan, haka a ka gama musu bincike sannan suka zo dumin rubuta wannan exam mai zafin gaske.
Haka aka basu question paper, ba ɓata lokaci suka fara jarabawa.
10:00 AM, jirginsu ya sauka ƙasar india, bayan wasu ƴan lokutta akazo ɗaukar su zuwa gidan da Hafsat ke zaune wato gidan Aunty Shemah.
Dayake Aunty Shemah tasan da zuwan su dan haka duk abin da zasu ɓuƙata antana dar musu, amma duk wannan shirye-shirye da ake Hafsat batasan mi ake ciki.

Aunty shema dake zaune falo Affan sai famar surutu yake mata, shigowar motar da tajine ya bata tabbacin cewa sun ƙaraso dan haka ta tashi domin tarbunsu.
Tana ƙoƙarin fita sai gasu sun shigo cinki falon bakin su ɗauke da sallama.

Amsawa tayi fuskar ta ɗauke da murmushi haɗi da nuna mu su wajan zama haɗi gashesu dayi musu ya hanya.

Zama sukayi sannan aka kawu musu abin mutsa baki, bayan sunci sunsha aka nuna musu wajan da zasu ɗan huta, Safiyya ce ta kalle Aunty Shemah tace, "Aunty banga My Hafsat ba".

Sai da Aunty Shemah tayi murmushi sannan tace, "au na sha'afa wallahi ban sanar daku taje zana exam ɗin ƙarshe, daya ke wani satin ne zasu kammala kuma alokaci ne za'ayi biki".

Safiyya tace, "to Aunty sai yaushe zata dawo?".
Tafaɗi haka kamar zatayi kuka.
Dariya ta sanya Aunty Shemah sannan tace, "da sun gama zaki ganta karki damu ƙanwata".

Tafiɗi haka da sigar rarrashi.

Kowane masaukin sa aka kaishi, wanka sukayi su ka ɗan huta.

Bayan komai ya ɗan kammala suka dawo parlour suka zauna ana firar Hafsat da kewar ta da sukayi.

Itako suna fitowa waja exam bata tsaya komai ba ta shigo mota ta dawo gida.
Tanayi parking ɗin mota, Aunty Shemah ta dube Safiyya da ta rakufe waje ɗaya tace, "Safiyya ga Hafsat ɗinnan ta dawo...bata ƙarasa faɗa ba aka ruru ƙofar falon bakin ta ɗauke da sallama tana faɗin, "Aunty"....bata ƙarasa faɗa ba sabida abinda adonta ya gane mata shin ko gaske ne?.

STORY CONTINUES BELOW

Safiyya ta gani zaune sai famar yimata murmushi take, idonta ta murza dan ta tabbatar da abunda tagani, dubanta ta maida ga Aunty Shemah wadda ta kafa musu ido sai kallo take taga abinda zai afukwa, bakin ta buɗe da kyar tace, "Aunty wa² nake gani? kin ga binda nagani kuwa?".

"Sosai kuwa nagani, ko ba Safiyya ba?".

kafin tayi magana sai Safiyya ta taso daga ma zaunin datake, ta ƙaraso wajan da take tsaya, cikin hanzari ta jawota jikin ta ta rungume ta tana mai sanya kukan farin ciki, cikin kuka take faɗin, "Hafsat nece ƴar uwarki Safiyya"... aitun ba takai da rufe baki ba Hafsat ta ƙanƙame Safiya jikita tana kuka, rasa kukan mi takeyi tayi, na farin ciki ko na baƙinci, Aunty Shemah ce ta zo garesu tace, "haba ai kuka bai dace gareku ba Allah zakuyiwa godiya da ya nuna muku wannan ranar".

Haka dai Aunty Shemah tayi-tayi rarrashin su har suka natsu suka daina kuka, wajan da Safiyya take zaune suka je dan su zauna sai kuma me....idonta ne ya kai ga wajan da Ummar ta ke zaune.

Jikinta ne ya fara karkarwa baki ta buɗa tana so tayi magana amma ta kasa, dan haka da sauri ta bar jikin Safiyya ta faɗa jikin Ummar ta tana kuka farin ciki da na danasanin bin *UMURNIN SAURAYI* ƙara shigewa jikin Umma tayi kana ta buɗa baki tace, "Umma dan Allah kuya femin wallahi sharin shaiɗan ne"... tun bata kai ƙarshe zanci ba Umma ta rufe mata baki haɗi da ƙara sanya ta jikin ta tana buga bayan ta alamun tayi shuru.

Bayan ta ɗan rage kukan da takeyi ne sai Umma tace, "to ga Abbanki da Babanki ki gaishesu".

Da sauri ta ɗago kanta daga jikin Umma dan ta ga waɗan da ta ambata mata.
Abbanta tagani da Baban Safiyya, da sauri ta tashi daga jikin Umma taje gabansu ta faɗi durgushe tana kuka tana faɗin, "Abba dan Allah kuya femin".

Tana faɗa tana haɗa hanayen ta waje ɗaya.

Sai da Abbanta ya tashe ta yace, "a'a Hafsat ni zan ce ki yafemin dani nakasa daukar ƙaddara lokacin da abin ya afku gareki".

Tace, "Abba laifinane dan dole ce tasa kayi haka, kuma dan Allah Abba kaya femin".

Yace, "wallahi tun da jimwa na yafemiki sai dai muce Allah ya yafemuna gabaki ɗaya".

Wajan Baban Safiyya taje shima ta nemi yaye femata, shima yace batayi masa kumai ba kuma koda tayi masa ya yafe mata.

Daganan ta dawo wajan Umma ta zauna taci gaba da kuka, sai daga baya tayi shuru take tambayar su yadda akayi suka zo wajanta.
Nan suka bata labarin komai na zuwan su har kawo yanzu.
Sai alokaci ta kai dubanta zuwa ga Sulaiman dake zaune yana kallon ikon Allah, dan koshi har da ƴar kwalla sai da yayi dan yaga sahibar sa na kuka.

Suna haɗa ido taji wani sonshi da ƙaunar sa sun ƙara shiga zuciyar ta.
Suna cikin haka sai suka ji Sallamar mijin Aunty Shemah.

Ƙarasowa yayi cikin falon yana faɗin, "baki ne damu?".

Aunty Shemah ce tayi sauri ƙarɓa masa haɗi da gasheshi tace, "eh iyayen Hafsat ne suka zo wajan ta".

Tun kan ta ida rufe bakin ta yaje garesu ya basu hannu suka gaisa sannan ya zauna.

Dubansa Aunty Shemah tayi tace,"lafiya na ganka ƙasar nan yanzu?".

Yace, "ba lafiya ba kam, dan tun jiya su Zainab ɗin Daddy su Anwar ta kirani tace Anwar ba lafiya yanzu ma haka ankawoshi ƙasar nan dan su duba lafiyar sa, kuma koda aka zo dashi bai san inda kansa yake ba".
Da Saulaiman da Hafsat, suna jin an faɗin sunan Anwar gabansu yayi mummunar faɗuwa.

"Subuhanallah, to yanzu zakaje sai naje na gansa?".
Cewar Aunty Shema.

STORY CONTINUES BELOW

Yace, "naje wajan su amma yanzu wanka zanyi sai naje naga yadda abin zai kasance dan sunce in har bai farka ba sai anyi mishi akin zuciya".

Alamun tausayi ya bayyana afuskukin su sannan suka yi masa addu'ar samu lafiya mai affani, tare da faɗin suma zasu je suga jikin nasa.

Sosai yaji daɗin haka da sukace, dan haka ba ɓata lokaci ya tashi yashiga part ɗinsa dan yayi wanka kuma ci wani abu sannan suje.
Bayan kamar awa uku suka fito gaba ɗayan su dan suje suga mara lafiyar Abban Affan.
Mota uku sukayi sannan suka tafi.

Ɗaya Abba da Baban Safiyya da Ummar Hafsa.

Ɗaya ko Alhaji Aminu da Aunty Shemah da Affan.

Ɗaya ko Sulaiman da Hafsat da Safiyya.
Tunda suka kama hanya tafiya gaba ki ɗaya jikinsu yayi sanyi, Sulaiman ne ya katse shuru da faɗin, "yau dai gaki ga Safiyya".

Murmushi tayi sannan tace, "ni bama wannan ba, gabaki ɗaya sai naji bana son zuwa wannan dubiyar, dan kar Abban Affan ya ɗauke wani abu wallahi da bazanje ba".

Dubanta Sulaiman yayi yace, "sabida mi bazaki je ba". tace, "haka kawai bana son tafiyar".

"Ke dai faɗi gaskiya wazai ce baya son zuwa dubin masoyin sa".
Har zatayi magana yayi parking ɗin motarsa sabida sun kawo wajan da zasu aje motarsu kan su ƙarasa wajan mara lafiyar .

Abban Affan shine ke musu jagora har suka kawo wajan wata ƙofar glass wadda ananne mutum zai tsaya ya ga marasa lafiya batare da yashiga ba.

Dayake Hafsat nan take aiki dan haka ta nemi izinin da abarsu da su shiga daga ciki, mintuna ƙalila aka yardar musu dan haka ba ɓata lokaci suka shiga dan suganshi.
Su Abba sune kan gaba, tunda ya shiga ɗakin ya kefe wanda ke kwance kan gado da ido yana tunani kamar Anwar?.

Abban Affan ne ya farga dashi da yaji yana faɗin, "Hajiyar Anwar ya jikin Anwar?".
Kafin ta bashi amsa sai Abban, "Hafsat yace kar da kace min Anwar ɗin dana sani ne anan kwance?".
Gabaki ɗaya suka kalleshi kana suka ce, "eh shine, dama kasan shi kenan?".

Cewar Alhaji Amuni mijin Aunty Shemah.

Eh, "nasan shi, amma wanda nasani lafiyar sa ƙalau, kuma wannan naga bashi da lafiya".

Alhaji Aminu wayar sa ya ɗauko yanuna masa hotonsa yace, "ko ba wannan ba?".

Abba yace, ikon Allah, wallahi shine to yaushe ya kamu da wannan ciyo!".

Yafaɗi haka ciki da mamaki da kuma tausayawa, sannan yayi musu bayanin haɗuwar shi da Anwar har kawo yanzu, yakara da faɗin
tundaga lokacin bansake ganinshi ba kuma nayi nemansa dan har wayar sa naki ra amma sai a ce rufe take".

Safiyya ce ta ƙaraso wajan da su Abba suke dan taga shan wani Anwar ne ake magana akai, aikuwa tun bata kai ƙarshin wannan tuanin ba taga Anwar dake kwance kamar gawa, da suri ta ta dafe ƙirji tana faɗin, "Allah da gaske Anwar ne".
Hafsat dake tsaye ita da Sulaiman a hankali ta ƙaraso wajan Safiyya dan taga wanene suke magana a kai.

Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa lokacin da idon ta suka sauka akan Anwar wanda ke kwance dashi da babu duk ɗaya.
A Razane tace, "Anwar!!!!

Gabaki ɗaya kollo yadawo kanta, musmman Sulaman da yasan yadda take da Anwar.

STORY CONTINUES BELOW

A hankali² hannusa ya fara mutsi lokaci ɗaya ya fara tari abinda bai taɓa yi ba tun lokacin da aka kawo shi.
Suna cikin haka sai ga likitoci sun shigo sabida wata na'ura dake sanar dasu farkawar sa.
Likitocin na shigowa sukuyi musu alama da sufi fati.

Ahankali ya buɗe bakinsa yana faɗi, "Hafst"....har ya buɗe baki zai sake faɗa sai kuma shaiɗar sa tafara yin sama² cikin gaugawa likitoci suka fara bashi tai makon gaugawa.
Suna fitowa daga ɗakin sai Daddy Anwar ya dube su yace, "wai dan Allah wacece Hafsst".

Gabaki ɗaya kowa yayi shuru ya kasa magana sai da ya koma mai-mai tawa sannan Aunty Shemah tace, "gata nan Daddy".

Kallon wajan da aka nuna masa yayi amma wayam, dan tun kan likitoci su shigo suka suɗaɗa suka bar wajan ita da Safiyya, daga baya Sulaiman yabiyo bayan su suka shiga mota suka koma gida.
Kallon Aunty Shemah yayi yace, "bangan taba".

Duba wajan ta karayi sai taga basunan dan haka tace sun wuce .

Duban ta yasakeyi yace, "miye tsakanin ta da Anwar naga sai kiran sunanta yake tun muna nigeria?".

"Daddy wallahi bansani ba". Aunty Shemah tayi maganar

Yace, "to ki bincikar muna ita dan naga kamar akwa wani abu tsakaninsu".

Tace, "tau Daddy".

Sai Mamar Anwar tace, "to kinsan inda take ne?".

Tace, "wajena take da zama sabida karatu ya kawota ƙasar nan".

Sai Mama tace, "oky idan nasumu lokaci nima zan zo na tambaye ta".

Duk wannan abin da ake Abba da Umma da Baban Safiyya ba wanda yace komai har akayi aka gama sannan suka dawo gida.

*Agurguje*

Yaune bikin makarantar su Hafsat, dan haka tunda sassafe duk suka fara shirin zuwa wajan bikin da za'a gudanar, wanda a keyi adan ɗalibbai sun kammala karatunsu, dan haka zaka ga kowa ce ƙasa shaban ƙasar ta yazo ko waƙilinsa.
Harabar makarantar an gyarta kowa da wajan da aka tana darmasa, haka ma baƙi da kuma ɗalibai duk suna zaune wajan da yadace da su zauna, nan dai shukaban makaranta CALGOTIAS UNIVERSITY ya fara zawa bi cikin har shin turanci, sosai yaya bama waɗan nan ɗalibbai irin rawar da suka taka na wannan karatu, nan dai aka shiga faɗin ƙasar da ta ɗau na ɗaya da nabiyu dana uku, ƙaras india ita ce ta ɗauko ta ɗaya sai kuma Germany ita ta ɗau ta biyu sai nigeria ita ta ɗau ta uku a fanin na gaenacology.
Sosai shugaban ƙasar nigeria yaji daɗi a ransa ganin har da ƙasar sa na daga cikin waɗanda suka yi kwazo wajan karatu, haka dai akayi wannan biki aka gama ciki da jin daɗi da nuna farin ciki, bayan angama shugaban ƙasar nigeria yayi mu alƙawari da dama idan sun koma ƙasar su sabida ko can ya shirya musu bikin na musamma da kuma kyauta mai tsoka.
Bayan an watse Hafsat da abukanta ƴan ƙasar suyi ta ɗaukar hotona har da ƙawayen ta su Zeenatu haka sukayi ta ɗaukar hoto kowane sanye da kayansa na asibiti, kai abin sai wanda yagani.

Bayan ankammala suka dawo gida ciki da farin ciki musamman iyayen Hafsat da Safiyya.
Bayan kwana biyu da gama bikin suna cikin shiri dawowa gida nigeria , suna zaune falon gidan gabaki ɗayansu suna fira sai sukaji sallam.
Amsawa sukayi haɗi da gaishe su, Daddy Anwar ne da Mamar sa da yayunsa gudu biyu suka shigo.
Zama sukayi kana suka ƙara gaisawa da mutanin da ke zaune, Aunty Shemah ce taje ta kawo musu ruwa da abin mutsa baki sannan ta zauna ta kai duban ta ga Aunty Anwar tace, "Zainab ya mai jiki?".

STORY CONTINUES BELOW

Kafin ta amsa sai Daddy shi yace, " to yanzu da sauki dan har magana ya fara".

Gabaki ɗaya mutanin dake cikin falon har su Abba hamdala sukayiwa Allah kan sukara yima sa addu'ar cigaba da samun sauki.

Shuru ne ya biyu baya sai can Daddy Anwar yace, "Shema u, ina yarinyar nan Hafsat?".
Sai Aunty Shema tace, bari na kirata Daddy".

Tana faɗar haka ta tashi taje part ɗin da Sulaiman yake dan tasan tana can ita da Safiyya, haka ko ta kasance dan suna can suna shirya yadda bikin su zai kasance tace, "to Hafsat ki taso ina kiranki".
Tace, "Aunty wake kirana?".

"Idan kinzo zaki gansu".

Haka Aunty Shemah tace da ita itaƙaice.
Sai da Aunty Shemah tayi minti uku da bari wajan sannan ta kalle Sulaiman tace, "sweet dan Allah bari nazo sai mu ƙarasa".
Yace, "tom karki jima".

Safiyya tashi tayi tace, "kai da ganinta sai gobe".
Tafaɗi haka tana masa gwalo.
Murmushi yayi yace, "zaki sani".
Hafsat tace, "shareta yanzu zan dawo".
+
Koda suka isa falon zaune suka tarar dasu suna fira dan haka suka ƙaraso suka gaishesu sannan suka nemi waja suka zauna.
Mamar Anwar ce ta taso daga wajan datake zaune tazo wajan Hafsat, tace, "ƴata gani gabanki, dan girma Allah kiyafe ma Anwar abinda yashiga tsakaninku, wallahi jiya daya samu baki duk ya faɗa muna abinda ya afku tsakanin ku, wallahi banji daɗi ba, kuma ina ruƙunki da Allah yarda sai aɗaura muku aure tsakaninku...tun bata kai da rufe baki ba Hafsat tayi sauri ta ɗago kanta haɗi da yimata wani kallo.

Hawayene suka fara zuba akunci Mama Anwar.

Daddy Anwar da yaga Hafsat taƙi magana dan haka shima ya taso daga wajan dayake zaune ya zo gaban Hafsat ya ƙurfana yace, .... Da sauri Abba da Baban Safiyya sukayi sauri tareshi suna faɗin, "dan Allah Alhaji katashi wallahi taya femasa".

Kai ya fara girgiza musu hawaye na zuba a idonsa yace, "a'a ita nake sun ji daga bakin ta".
Gyara muryar da Ummar Hafsat tayi yasa Hafsat ɗago kanta ta dubeta, alamu tayi magana tayi mata, dan haka ba musu ta buɗa baki tace, "Daddy katashi wallahi na yafe masa har gaban ubangiji".
Takai ƙarshi zanci tana wani kuka mai cin zuciya.
Yayar sa Zainab dake zaune saman kujera ta taso tazo wajan Hafsat ta jawota jikin ta kana tace, " ƙanwata amma zaki aureshi ko"..

Sulaiman da yaga sun jima dan haka yabiyo sahunsu, dai-dai yana shigowa yaji Yayar Anwar nacewa zaki aureshi.
Kukan da takeyi ne ya tsananta lokacin da taji wannan magana daga bakin Aunty shi.
Shurun da taji tayi ne yasa tace, "dan Allah ki taimaka muna wallahi yana gab da muuwa, kuma shi kaɗai ne garemu namiji dan Allah ki tausaya muna, rashin sa babbar illace garemu".
Tana faɗar haka sai da Hafsat ta ɗago kai ta dube ta tace.....*#VOTE COMMENT SHARE*

*©SUMY NA'IGE*
[4/23, 06:58] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

'''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_


*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE.✍🏼*

*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITES ASSCIATION*

*WANNAN TUKWAICI : GA*

*S NA'IGE FAMILY*😘😘*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 33📑*

*__________📖* Tace, kuma sai ta kasa magana ba abin take sai kuka, dan gaskiya ita bazata iya barin Sulaiman ba ta aure Anwar.

Tashi tayi daga wajan da take ta shiga ɗakin ta tana kuka mai ƙunar zuciya dan ita kam gaskiya ba zata bar Sulaiman ba ta aure Anwar.
Safiyya ce tabi bayan ta sabida ko ita abin ya ɗaure mata kai.
Hafsat na barin wajan Maman Anwar hawayen ta suka tsanata zuba tana faɗin, "nasan bazata yarda ba, shikenan narasa shi".

Sulaiman dake tsaye yaji komai zuciyar sa sai famar bugawa take, har ga Allah shi yasan yana son Hafsat, amma ya tsane yaga babba mutum na kuka musamma mace, dan haka a hankali ya fara taka ƙafarsa har ya ƙaraso wajan su, dai-dai wajan da Maman Anwar take yazo ya durkusa kana yace, "Mama dan Allah ki daina kuka wallahi Anwar bai rasa Hafsat ba, dan ni shaida ne Hafsat nason Anwar sosai, sai dan ya gojeta ne yasa ta ji bata sonshi amma nasan ko yanzu saboda ni taƙi amincewa, amma ku bani nan da kwana biyu duk abin da na yanke za kuji".

Bayan kwana biyu

Suna cikin shiriye² sai ga wayar ta ta fara ƙara, sunan da tagani jikin wayar yasa ta sanya wani ƙayataccin murmushi mai karawa fuskar ta annuri haɗi da karawa a kunnin ta tare da yimasa sallam, bayan ya ƙarɓa yace, "in ba dawu kizo ke da Safiyya kurakani wani wajan".
Tace, "oky gamu nan zuwa".

Bayan sun kammala wayar ne ta kalle safiyya ta gaya mata saƙon Sulaima, ba ɓata lokaci suka fito dumin suje wajan shi.
Aunty Shemah da Umma ne a parlour dan haka suka faɗa musu sannan suka fita.
Dai-dai wajan motar suku sameshi, buɗe musu marfin motar yayi suka shiga, bayan sun shiga shima ya shiga yaje motar suka tafi.
Suna tafiya amma sai jan Safiyya yake da fira har mamaki abin ya ba Hafsat.

Hospital ɗin da aka kwantar da Anwar suka shiga, Hafsat har taso tayi magana amma tayi shuru bata ce dashi komai ba har suka zo gab da ɗakin da Anwar yake, kallon sa tayi tace,
Mi muka zoyi a nan?".

Kafin yayi magana ƙofar ta buɗe ya shiga ba tare da yace da ita komai ba.

Suna ganin ya shiga suma suka shiga.
Daddy Anwar da Mamarsa ce suka gani zaune suna gaisawa da Sulaiman da yashigo yanzu, aikuwa suna ganin Hafsat fara'arsu ta faɗaɗa haɗi da nuna musu wajan zama.

Gaishesu sukayi haɗi da tambayar ya mai ji sannan suka zauna wajan da aka nuna musu.

Mama ta amsa haɗi da nuna mata godon da yake kwance.
Suna cikin haka sai ga Aunty Zainab ta shigo ɗaki, ganin su Hafsat da tayi fara'ata ta faɗaɗa, ƙaraso tayi wajansu tana faɗin, "ƙanwata yaushe kuka zo?".

STORY CONTINUES BELOW

Sai da Hafsat ta sadda kanta ƙasa sannan tace, "yanzu muka zo".
Batace mata kuma ba taja hannuta tace, "zo muje gashi can kila yanzu yasamu bacci".
Sai da ta kalle gyafin da Sulaiman yake taga bai ma kallonsu sannan ta tashi haɗi da riƙo Hannun Safiyya suka ƙarasa wajansa.
Kwance yake amma jingi ne da filo idonsa lumshe kamar mai bacci, suna ƙarasowa Aunty Zainab tace, "Anwar yajikin naka?".

Bai ƙarɓa ba sai da akayi wasu ƴan seconds sannan yace, "da sauƙi Aunty".

Ya ammasa amma har yanzu idonsa rufe.

Safiyya ce, "tace yajikin?".

Wani abu yaji, dan ji yake kamar yasan wannan muryar, dan haka ahankali ya fara buɗe idonsa, waɗan da yagani tsaya ne yasa ya tashi daga jikingi nin da yake bai shirya ba, wanda ra bon sa da ya tashi zaune tun lokacin da wannan ciyon ya sameshi.

A hankali ya zuro ƙafarsa daniyar yatashi tsaye, aiko yana tashi bisa tsau-tsayi ya faɗi, lokaci ɗaya ta sanya wata ƙara tare da ƙarasowa gareshi cikin giɗimewa da nuna damu sosai a hakan haka.

ƙarar da su Daddy da Mama da Sulaiman ne sukaji dan haka da sauri suka zo dan suga mike faruwa.

Ƙoƙari tasheshi sukeyi itada Aunty, Daddy da Sulaman suna ganin haka suka zo cikin hanzari suka mai dashi wajan da yake.

Sam ta manta abinda ya afku sai sannu take jera masa kamar tayi kuka.

Aunty Zainab irin yadda taga tashiga wani haline yasa ta jawo ta jikin ta tace, "sorry ƙanwata ai ba abinda yasa meshi".

Suna cikin haka suka ji ya buɗa baki yace, "dan Allah Hafsat ki yafe min wallah na tuba, na bi Allah kuma nabiki"...kafin ya kai ƙarshe zancin Sulaiman yace, "ai magana taƙare Anwar ka kwantar da hankalinka, yanzu dai ga ka ga Hafsat sai dai fatan alhairi".

Yana faɗin haka sai da gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗago kai ta kalleshi, wanda shima yana kule da ita ta gyefin idon amma yayi kamar bai san tanayi ba.
Haka dai suka gama dubi sa ƙarshe sukayi musu sallama daniyar su tafi.

Har zasu fita Aunty Zainab ta kira Hafsat tace, "tazo, wajan Anwar suka ƙarasa da ita, kallon ta yayi yace, "Hafsat kiyafemin dan Allah"....tun bai kai ƙarshe ba tace, "har ga Allah na yafe maka Anwar, ka daina kuka zaka warke".

Godiya yayi mata, har zata juyo ta tafi yace, "to yanzu yashe zaki dawo?".

"Kafin mutafi zan dawo". Haka tace dashi ataiƙaice.

tana faɗin haka ta bar wajan ta ƙarawa su Mama da Aunty Zainab sallama sannan ta tafice dan su Safiyya har sun tafi.
Wurin da sukayi parking ɗin mota nan ta same su har sun shiga mota ita kaɗai suke jira.

Buɗe mator tayi tashi ga amma sai taji duk ta tsargu sabida haka da tayi duk taji bata kyauta ba.
Haka yaja mota ya kaisu wajan shopping sannan suka wuce gida.
Bayan kwana biyu da faruwar haka suka shigo jirgi suka dawo gida nigeria, abuja suka sauka sai da akayi bikin ɗaliban da sukayi ƙwazo waɗan da aka tura ƙasa she² sannan aka rabamusu kyauta mai tsoka, sannan kowa ya koma garomsu.
Su Hafsat na dawowa ƴan uwa da abukan arziki suka zo sunayi ma iyayen ta barka kuma da farinciki, haka dai mutane suke ta zuwa har ma dangin su Umma da Abba ba wanda baizo ba, bayan kwana biyu Hafsat ta shirya ta kai musu ziyara.
Kwananta biyu da zuwan ta suka fara bata maganin wankin ciki, bayan tayi kwana biyu tana shanvsa sai a ka fara bata wani haɗaɗin tsimi, bayan tayi kwana biyu tana shan sa aka bata wata zumu safe da yamma haka take shanta sannan basa bari tasha ko wani kalar ruwa bace natsimi , duk da ba taso amma haka Kakar ta ke tsare ta sai tashi, da kuka da komai sai tayi duk lokacin da zata sha amma Kakar bata damu ba, haka dangin Abban ta, kullum sai ankawo mata nono mai haɗe dawani abu a ce tashi haka har akayi sati biyu ko ƙofar gida basa barin ta fita, aikin gyaranta kaɗai sukeyi, ita kuma abin sai mamaki yake bata dan tasan sai mutum za shiyi aure akayi masa irin wannan gyaran amma ita gata ba aure ba amma sai wani gyara suke mata, bata ida shiga mamaki ba sai da taga ankawo Safiyya an haɗe da ita ina gyara.

STORY CONTINUES BELOW

Da dare suna ɗaki ita da Safiyya sai ta dube Safiyya tace, " wai hala aure za'ayi muna naga sai gyaranmu ake, wallahi ni abin nan ya shege min duhu ki fitar dani?".
Sai Safiyya tace, "wallah aure za'ayi muna har da Yaya Abbas, amma gwara kuwa dani Hafsat dan in kowa yasan wanda zai aure ni ban sani ba".
Ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye.

Kallon ta Hafsat tayi tace, wa kin zo da waye?".

"A'a kafin nazo suka karɓe".
Cewar Safiyya.

"Aunty Shemah nake son nakira sabida nace zan koma dubin Anwar amma ban samu dama ba, shine nake son ji ko yaji sauki".

Sai da Safiyya tayi mata wani kallo sannan tace, "kidaina maganar wani Anwar, dan yanzu kina gab da zama matar wani".
Sai Hafsat tace, "wallahi ba wani abu fah, kawai dai naga yadda yake jin jikine ya bani tausai".
"To addu'a zaki masa bawai kiriƙa mana maganar shi ba".

Haƙuri Hafsat ta bata daga baya suka cigaba da fira.
Yau jumu'a tunda safe da suka tashi bayan sunyi sallah Kakar Hafsat ta tisasu gaba ta basu wani abu kamar nama kuma kamar ba nama ba, tace sai sun canye, haka suka fara ci da kuka da komai amma sai da suka canye, bayan sun canye tace su tashi suje su shirya dan yanzu ita Safiyya za'azo a ɗauke ta ke ko yanzu zakije dangin Abban ki".
Ba ɓata lokaci suka shirya sannan kowa aka kaishi wajan da ta ambata.

Hafsat na zuwa wajan dangin Abba ta, suma suka fara tsumata haɗi da yimata wasu turarukka, ita abin yanzu har tsoro yake bata dan duk wanda zai zo to sai yabada abinda za'a bata, da yamma sai ga wasu mata guda biyu sunbzo da lalle jiƙe cikin wani mazo bi suka umarce ta dataje tacire kayan jikin ta za'ayi mata wanka lalle.
Sai da tayi musu kallon ƙasa da sama sannan tace, "wallahi bawan da zaiyi min wanka, wanka sai kace wata ƴar yarinya?".

Tafaɗi haka tana mai ɗauko hijab ɗinta tasanya.

Mahaifiyar Abba ce da taji hayaniyar su tazo dan tasan abu mai wuyane wannan ƴar book ta bari ayi mata wankan lalle.

Tana shigowa ɗakin sai tace ma waɗan nan matan "tunda bata bari ku gaya mata addu'ar da zatayi inayaso sai tayi da kanta".

Haka kuwa akayi dan Hafsat ca tayi ba wanda zai mata wannan wanka, ai ambar yayi haka dan yanzu kai ya waye, haka dai tayi taji ni-ni har tayi wanka ta gama dan atunanina ba addu'ar da tayi an ba jinini ba.
Tana fitowa aka ɗauku mata atamfa mai kyau gaske aka bata tasa sannan aka fesheta da turare mai ƙamshi sannan aka fito da ita aka kawuta wani ɗaki mai kyau aka zaunar da ita sannan aka fara kiɗin ƙwarya da waƙe-waƙe, lokaci ɗaya gida yacika sai sambar ka akeyiwa Kakar ta, wato mahaifitar Abba.
Ita dai Hafsat ba abinda take kwallo sai ikon Allah.
Haka dai sukayi ta kiɗi har goman dare, sannan suka fara watsewa, tana ganin sun fara watsewa ta tashi taje ta cire kayan da ke jinki ta dan duk ata kuri take, tana cirewa ta kuma watsa ruwa sannan ta kwanta.

Rana bata ƙarya, yau a ka ɗaura auren Hafsat, Safiyya, Yaya Abbas, wanda ya samu halatar manya mutane kai har ma da sarkin garin da manya-manyan ƴan siyasa, sosai wannan ɗauri auren ya ƙyatar, kuwa ka gani sai farinciki yake da sama wannan auren albarka, uwa Abba ida ka kale Abba da Baban Safiyya hmmm ba'acewa kuma, sabida dukan su fuskokin su ɗauke da farinciki suke.
Can na hago gyfin angaye waɗan suke sanye da farar shadda anyi mata zubi mai kyau gaske, bakinsu baya rufuwa sai famar ɗaukar hotona akeyi da su, hmmm can na hango Sulaiman da Yaya Abbas, ɗayan ne ban gane ba sabida nayi ta ƙoƙarin na gano amma ban gane saba, ina cikin son na gano shi sai Abidat tace dan Allah Sumy kallon ya isa haka muje zuwa anjima.

Ba musu ko nabi bayan ta muka je.
Tunda ta tashi daga bacci gabanta ke famar duka uku-uku, har tayi sallah mai kunshi da mai kitso suka zo amma duk bata jin daɗin ranta.
Haka dai aka gama kitso da kunshi har suka tafi ba abimda ya haɗa su na magana, da yadda takeji kamar tayi kuka.

Bayan an kammala ne sai ƙanwar Abbanta ta umarce ta dataje tayi wanka, bayan tayi wanka ta bata wani ɗanyi lace ta sanya, ba ƙaramin kyau tayi ba bare abu ga jinin fulani.
Bayan ta gama shirin sai aka kaita wani ɗaki wanda yake ciki da ƴan uwan Abbanta maza da mata, nan a ka sakata tsakiya, kowa sai faɗin albarkar bakinsa yake kuma suka ƙara shaida mata tayi biyaye ga duk wanda ya kasance miji a gare ta, sosai suka yi mata nasiha daga baya tayi musu sallama sabida an zo ɗaukar ta, , har za su fita sai Kakar tace su bari tazo, ba ɓata lokaci sai gashi tazo dawani abu cikin ƙwarya, tana ƙarasowa gabanta ta ɗago kanta tace, "kiyi basmala, aikuwa tanayi ta kafa mata wannan ƙwarya a baki har sai da ta shanya abinda ke ciki kaf, sannan ta ɗauke, sannan aka tafi da ita.

motoci da aka kawo suka shiga ita da ƴan uwan Abba ta sannan suka tafi cikin garin sokoto.
Suna isa da gudu ta fita daga cikin mota ta shiga cikin gida, aikuwa tana ganin Ummata ta faɗa jikinta sai kuma ta fara kuka, rarrashinta Umma tashigayi sannan taja hannuta suka shiga ɗakin Abba.
Bayan sun shiga sun zauna sai Umma tace, "Hafsat angirma, Allah ya nuna muna wannan rana, dan haka dan Allah Hafsat ki baiwa maraɗa kunya, kiyi zamanki aduk inda kika samu kanki, kinji ƴar ta, dan Allah karki bani kunya Hafsat".

ta kai ƙarshin maganar tana mai share hawayen ta.
Umma na gamawa Abba ya ɗura daga wajan da ta tsaya, shima har da ƴar ƙwalle ta.
Sannan yace, "yanzu za'a tafi dake Hafsat in ya so bayan wata biyu sai ki fara fita aiki kinji, kuma kiyimin alƙawari duk inda kika samu kanki zaki zauna?".

Bata kawo kumai aranta ba tace, "eh Abba".
Suna cikin haka akace ga sunan sun zo ɗaukar amaryar yar su, dan haka aka ɗauke ta zuwa wajan Baban Safiyya shima yayi mata huɗuba tare da yimasa alƙawarin zata zauna a duk inda tasamu kanta.
Lokacin da a kazo tafiya da ita da ƙyar a ka rabata da Safiyya da kowanin su baya so rabuwa da ɗan uwansa.

Haka a kasaka Hafsat mota suka kama hanyar garin kaduna.
Itama Safiyya haka akayi mata huɗuba sosai kuma akace ta zauna lafiya da kishiyar ta ta bata girman ta da dai sauran su, dare nayi aka ɗauke amarya Safiyya aka miƙata gidan mijin ta da batasan ko waye shiba.
Yaya Abbas haka abukansa suka rakashi dan ƙarerin gidanshi dake mabera.
Tunda ta sadda kanta ƙasa bata ɗago ba har suka kawo garin gaduna.
Dai-dai wajan wani dan ƙarerin gida sukayi horn, da sauri mai gida ya buɗe gate ɗin gidan, motar dake gabansu ce ta fara shiga sannan mai bimata aikuwa lokacin ne aka san amarya ta zo, dan haka lokaci ɗaya aka sauya kiɗi da bushi-bushi zuwa na tarbon amarya.
Sai da motacin da suka zo gabaki ɗaya suka gama shigowa sannan aka buɗe ma Amarya ƙofa ta fito, ahakali ƙanwar mahaifiyar ta tace kiyi basmala kafin ki fito, haka ko ta kasanci tayi basmala sannan ta fito, wani dan ƙarerin parlour ne aka shiga da ita ta zauna ita da ƴan uwanta, haka ɗuk wani dan uwansa zuwa yana gani amarya har akayi kiran sallah.
Bayan sunyi sallah aka kawo musu abinci da abinsha, bayan sun kammala sannan ƴan uwanshi da iyayenshi suka zo dan suga amarya bayan ankai ta wani ɗaki na dabam.

Da sallama suka shiga, ƙanwar Ummar tace kusa da ita ita karɓa tana faɗi ku ƙarso gata".....* Ƙanwar Ummar ta dake zaune ita ta karaɓa musu sannan suka ƙaraso cikin falo, ɗaya daga cikisu tace, "yau zanga matar Yayan Anwar wada akanta ya tashi rasa ransa".


Gabam Hafsat ne ya faɗi tace to miya haɗata da Anwa?.

Ta faɗi haka duk cikin zuciyar ta.


Tana cikin wannan tunanin taji anyaye mata mayafi da ta rufe fuskar ta, kanta ta kara saddawa ƙasa Yayar sa Zainab ce tace, "Hafsat buɗe idonki  ga iyayensa".

Gabanta ne ya sake faɗuwa karu na biyu, ana cikin haka sai ga Yayar shi ta riƙo hannusa tashigo dashi ɗakin, zaunar dashi tayi wajan da Hafsat ke zaune sannan suka riƙa ɗaukar su hoto, hanunsa Mamar sa ta riƙo ta haɗa dana Hafsat, lokaci ɗaya suka ji wani yarrrr, addu'ar samun zaman lafiya tayi musu sannan ta fice suma sauran ƴan uwasa haka sukayi sannan suka fita suka bar Aunty Zainab tare dasu.

Sai da tabari duk sun fita sannan Aunty Zainab  tace, " Hafsa, to zan gaya miki abinda baki sani ba, tunda sunce sai kinzo na faɗa miki, zan fara baki haƙuri sabida anyi wannan auren bata re da saninki ko amin cewariki ba, dan haka nake mai baki haƙuri bisa ga wannan abin da muka aikata kuma Allah yariga da ya tsara abinsa duk yadda muke so to idan Allah ya kaddara sai muyi haƙuri, ba abinda zance sai dai nace miki yau ke da Anwar kunzan miji da mata....tun bata kai da rufe baki ba Hafsat tace, what!!!.

Tafaɗi haka tari da miƙiwa tsaya tace, "wallahi bazai taɓa yuwa ba, ina Sulaiman?".

Ƙanwar Abbanta ce da tashigo ɗakin dai-dai lokaci da take magana tace, "gashi ko ya yuwu, Sulaiman kuma baruwanki dashi dan yanzu ba muharra miki bane".


Tafaɗi haka ciki da masifa dan ita gwaggo Saratu koda ma masifafface.


Hannu ta ɗura aka tace, "yau nashiga uku dan Allah ina kuka kaimin Sulaiman".

Ƙanwar Mamar tace tace, "kiyi haƙuri ƴa ta, Sulaiman shima yana can da amaryar sa".


Idon Hafsat ta zaro sannan tace, "wani Sulaiman?".


Wannda kika sani mana".

Haka gwaggo Saratu tace da ita.


Jikin ƙanwar Mamar ta Masa'uda ta faɗa tace, "Mumy ya haka ta kasance?".


A hankali ta ƙara janyota jikinta tace, "sai kin daina kuka zan gaya miki".


Ahankali ko ta share hayen ta tadaina kuka.


Waya suka ɗauka suka kira Abban ta sukace ya faɗa mata da bakin sa.

Kiransa sukayi haɗi dasa hands-free   ya fara faɗin, "Hafsat bari na tuna miki kafin na gaya miki yadda haka ta kasance, kinsan kimin alƙawari duk inada aka kaiki zaki zauna, kuma kituna hukunci musu  alƙawari idan sun saɓa, sannan ya ƙara da cewa, lokacin da iyayen Anwar suka zo suka nemeki  da ki aure ɗansu Anwar, to dakiƙa ƙi basu amsa ashe duk abin da ake Sulaiman yana tsaye yana jin komai, irin yadda yaga iyayen sun shiga wani hali danshi yace dasu sabida shi ne zakiƙi auren Anwar amma yasan har ga Allah kina son shi, bayan kwana biyu sai Sulaiman ya kaiku dan ku dube shi aiku nan kuwa ya ƙara tabbatar da tabbas kina sonshi, to bayan kun dawo ne ya yanke shawar zai barwa Anwar ya aureki ko dan a ceto rayuwar sa daga halin da yake ciki, kuma nan yanemi da mu amince masa ya aure Safiyya, haka kuwa a kayi dan  ke da Safiyya bawan da muka gayawa sai ankai ku gidajin ku, kuma dan Allah ina roƙonki da kici alƙawarin da kika ɗauka ki tsaya kiwa mijinki biyya da iyayensh".


STORY CONTINUES BELOW

Yana faɗin haka ya datse kiran.

Tana jin ya katsa wayar ta shige jikin Mumy ta Masa'uda sai kuka take kamar ranta ya fita.

Anwar ko tunda Auntyn shi ta fara magana ya suɗaɗa ya bar ɗakin.

Sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi shuru sanadin ciyon kan da ya tasoma mata.

Magani suka bata tasha, ba bata lokaci bacci ɗauke ta.


  Itace bata barka ba sai da asuba.

Tashi tayi tayi sallah, bayan ta idar da sallah tajima kan sallaye tana azkar da addu'a Allah yayi mata sauki abinda take kiji kuma Allah ya yaye mata son Sulaiman a cikin zuciyar ta kuma ya bata ikon biyya ga iyayin ta da mijin ta, tana haka  bacci ɗauke ta.

Sai kusan ƙarfe goma ta farka, wanka taje tayi  sannan ta shirya, beark aka kawo musu amma ita ƙin ci tayi da ƙyar aka samu tasha ruwan tea, bayan sun kammala akace su zo sukai amarya part ɗinta, daya ke gida ɗaya suke da iyayenshi dan sunce basa son yayi musu nisa dan haka suka zauna gida ɗaya.

Part ɗinta suka kaita wannda iya haɗuwa ya haɗu, dan tsayawa faɗar haduwar sa ɓata lokaci ne.

Bayan sun gama shiga ko ina na part ɗin sannan suka zo suka fara shiri tafiya, haba aikuwa Hafsat naganin haka tafara shirin kuka, da ƙyar suka rarrashita ta haƙura.

Amma lokacin da zasu shiga mota saida tayi kuka sosai, haka suka tafi ciki da jin daɗin karamcin da iyayen Anwar dashi kansa yayi musu.

Bayan sun tafi da awa ɗaya sai  su Aunty Zainab suka shigo, kuka suka tar da tanayi dan haka suka rarrasheta sannan sukayi mata sallama sannan suka tafi suka barta ciki da kewa.

Anwar ko tun jiya da ya suɗaɗa ya gudu bata sake gininshi ba har yanzu.

Gab da sallar magariba ta tashi taje tayi wanka ta shirya, tana idar da sallah sai gashi ɗakin, a hankali yake taka ƙafar sa kamar wani ɓarawo.

Zama yayi kan kujerar dake kusa da ita, haka yajira har ta gama azkar, saukuwa yayi daga kan kujer da yake zaune ya dawo saman sallayar da take zaune.

Kanta ta ƙara yin ƙasa dashi, lokaci ɗaya wani baƙin ciki ya fara rufe ta amma sai ta dake, sunayen Allah take ta kira a zuciyar ta har tasamu sauƙi abinda take ji.

Shiko rasa abinda zaice mata yayi sabida yana tsoron tace bazata zauna dashi ba.

Sun jima a haka kafin ya buɗe baki yace, "kizo muci abinci dan Allah ba danni ba".

Ya faɗi haka kamar yayi kuka.

Yada take bata ko ɗago ba bare yasa ran zatayi masa magana.

Ruƙonta ya farayi amma sai tayi banza dashi, da taga zai dameta sai ta tashi tabar wajan.


  Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su har tsawo sati biyu ba abinda ke haɗasu,

Yau ma kamar kullum yana parlour zaune yana kallo labaru sai wayar ta shiga rura, number da yagani ne yasa ya faɗaɗa murmushin sa, ɗaukar wayar  yayi tare da karawa kunninsa yana faɗin, "ango kasha ƙamshi".

Sai da yayi dariya mai sauti sannan yace, "sosai kuwa, ina fatar kaima kasha?".

Anwar bai bashi amsa ba sai yace, "ina amaryar taka?".

Sulaiman yace, "gata kusa dani".

Wayar ya bata yace, "gata ku   gaisa". amsa tayi suka gaisa da Anwar sannan tace, "ina Hafsat?".

Rasa mizai cemata yayi sai da Sulaiman yace, "ina amaryar taka su gaisa tace".

Kamar da ɗan tsoro yace, "bari na kai mata".

STORY CONTINUES BELOW

Sulaiman yace, "wato baku ma tare kenan, ko har yanzu baka sha mansha nu ba?".


Yana faɗin haka shiko dai-dai lokaci da ya shigo ɗakin da take dan haka baiyi magana ba, ƙarasowa yayi wajan da take zaune  a hankali yace, "ga Safiyya zakuyi magana".


Tunda aka buɗe ƙofar tasan shine yashigo amma ko mutsi batayi ba bare yayi tunanin cewa  zatayi masa magana.


Jin da tayi ya ambace Safiyya yasa ta ɗago kai  amma batare da ta kalleshi ba, wayar da ke hannunsa ta karɓa haɗi da karawa a kunninta, sallama tayi Safiyya ta karɓa, bayan sun gaisa, sai Hafsat tace, "Safiyya haka su Abba sukayi muna ko?".


Safiyya tace, "kenan sunyi miki bayani?".


Bata bata amsa ba sai Hafsat tace, "kenan kin san  za'ayi haka?".


Safiyya tace, "wallah bansani ba sai da aka kawuni suke min bayani".


Ta kai ƙarshin zanci kamar zatayi kuka.


Hafsat tace, "ni karkimin kuka, wa Yaya Abbas ya aure?".


Naja'atu ƙawarki".


"Wace Najaatu? Kardai kice min Naja'atu Nasir?".


''Ita fah".

Cewar Safiyya.


Ina suka haɗu?".


Sulaiman dake zaune tare da Safiyya yana jinsu sai yace, "kin fah cika mu da tambaya² kibari idan kinzo zakiji".


Marairaicewa tayi tace, "Yaya Sulaiman dan Allah kayi haƙuri".


Bai ce da ita komai ba sai Safiyya tace, "lokacin da mukaje india ne tazo nemana to koda tazo bama nan tunda ga nan yaji yana sonta amma bai gaya mata yace sai mun dawo idan kin amince zaki aure shi to shikenan idan ko baki amince ba sai ya gayama ta, to koda muka dawo yaji haka shine ya gaya mata ba ɓata lokaci akayi komai a kagama".

Sai da Hafsat taje dugon numfashi sannan tace, "kunji daɗin ku".


Safiyya tace, "ba wani jin daɗi biyyace kawai zamuyi ma iyaye, dan haka kema dan Allah duk abinda kike ji ki ajeshi ki tsaya ki kula da mijinki".


Nan dai tayi-tayi mata nasiha, daga ƙarshi kuma suka dawo kuka kafin suyi sallama.

Yana ganin ta fara kuka ya karɓe wayar  dake hannun ta, a hankali ya jawo ta jikinsa ya fara rarrashin ta, amma kamar ance ta ƙara, sai datayi mai isar ta   sannan tayi shuru.

Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su bawata jituwa har akayi wata biyu, dan idan ga tayi masa magana to suna gaban Daddy da Mama.


  Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya.


Yau Monday kuma yau ce ranar da zata fara fita aiki, bayan ta shieya taje ta gaishe da su Daddy da Mama sannan suka tafi ita da Anwar, bayan sun isa asibitin da zatayi aiki, kai tsaye a kayi mata jagora zuwa offce ɗinta, bayan ta zauna tayi ƴan rubuce² sannan ta tashi dan taza gaya wajan marasa lafiya, suna cikin jagayawa ita da wasu likitoce da waɗanda ke nuna mata yadda wajan yake, suna cikin haka sai sukaji kamar ana kiran Anwar, gaba ɗayansu shida ita suka juya dan suga wake kiransa.

Wata mata suka gani kwance saman gadon hospital, sai ɗaga musu hannu takeyi.


Ƙarasowa wajanta sukayi dan suga wacece ita?.


Koda suka zo wajanta amma basu gane taba, da taga alamu basu gane taba tace, "baku ganeni ba ko?".


Atare suka ce "eh".


Kallon Anwar tayi tace, "Anwar kar dai a ce labarin danaji ance ka aure Hafsat da gaske ne?".


Sai da suka kalle juna sannan yace, "eh da gaske ne".


"Allahu akbar, Allah ya nunamin ikonsa, duk yadda nashiga na fita dan kar kuyi aure yau gashi kunyi aure".


Ta kai ƙarshi zanci da kuka mai ƙunar rai.

Tace, "tun lokaci da kace kana son Hafsat abin baiyi min daɗi ba, sabida sai naga baka dace da ita ba dani kadace, dan haka tundaga lokaci na fara shiga da fita dan kar Hafsat ta amince maka amma ina ƙaddara tariga fata, dan sai da ta amince kuka fara soyayya, hakan ba ƙaramin baƙinciki naji ba, duk da haka banyi ƙasa a guwa ba, sai da naji wajan wani boka yayi maka akin da zai sa kalalata mata rayuwa haka kuwa a kayi to bayan komai ya afku kuma sai Hafsat ta guje ka, to ana cikin haka sai kazo wajena dan nan shirya ku da Hafsat, to a lokacin ne nasamu galabarku har nashiga tsakanin ku na rabaku, to duk da haka ban kyaleku ba, nan dai tagaya musu har ƙarshin zuwan datayi wajan malami da kuma yadda tace yayi mata akan Anwar, to anacikin haka wannan ciyon yasameni ta, a ka mai dani gida naci gaba da jinya, to ina cikin haka aka kawomin hotonan auren ku, to tunda ga nan bansake sanin inda kaina yake ba sai a wannan asibitin.


Tana kai ƙarshin zanci tayi haka tasake magana amma ina, sabida sheɗar ta sai sama da ƙasa takeyi.


Cikin hanzari likitoci suka fara bata taimakon gaugawa.

Tunda Hafsat tagano ko wacece take kuka har inada Hajara ta kawo ƙarshin zance.


Anwar kuwa yana ganin yadda take kuka yaja hannunta yace suje gida sai wani sati zata fara aiki.


Haka suka dawo gida ciki da Mamaki Hajara.


Har dare yayi Hafsat bata dawo dai-dai ba.


Bayan yayi wanka yayi shirin bacci  yaje wanta ya rarrashi ta har yasamu taci abinci daga haka dai yayi ta bata magana har yasamu abinda yake so a wannnan dare, sosai ya bata wahala danji yake sai yanzu yasan ta ƴa mace dan da safe har da zazzaɓi sai da tatashi da shi.

Haka dai suka cigaba da rayuwa, sosai yanzu Hafsat ta sake jiki dashi, shiko sai nuna so yake gareta.

Bayan sati ɗaya Hafsat taje asibiti ta bincike Hajara a kace ai tun ranar Allah yayi mata cikawa, sosai Hafsat taji zafi da faruwar haka.


Koda ta dawo gida ta sanar da Anwar amma bai wani nuna da muwa ba, sai dai Addu'ar da yayi mata.

Haka rayuwa tacigaba da kasancewa, dan yanzu soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakanin Safiyya da Sulaiman hakama Hafsat da Anwar dan Abin har namaki ya bani.

Koda taje ganin gida tasha mamaki, dan gababki ɗaya Anwar yasa anrushe wannan gidan anyi musu sabo, gaba ki ɗaya koma na gidan ya dawo sabo haka tazo tayi kwana biyu gida koshi da kyar ya barta, koda suka haɗu da Safiyya har cikin Safiyya ya fito haka ma Naja'atu, Hafsat ce ka ɗai keda shigar ciki, dan sai wani kwaɗayi take suko suna tsargowar ta.


Haka dai rayuwar ma'aratan ta kasanci cikin so da ƙauna, bayan shekara ɗaya Safiyya ta haifi ɗanta namiji mai kama da maihaifinsa itama Na'atu ta haifi ƴar ta mace, ita ko Hafsat ta haife ɗanta sak Anwar, murna wajan dangin Anwar da iyayensa ba'a magana kowa faɗi yake Anwar yasamu magaji, bayan angama shagalin biki tace zata kuma gida wankan jego amma Anwar yace shi sam bai san haka ba, da ƙyar iyayenshi suka rarrashe shi ya yarda tatafi.......

*ALLHAMDULILLAH*


To nima Hafsat na tafiya nikuma na aje alƙalamina🤩


fatan alhari gareku masoyan wannan littafi, inama kowa fatan alhairi.

Post a Comment for "UMARNIN SAURAYI CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...