Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 6

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 6

- - Post a Comment

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 6


Sabir kuwa a jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.+


Idon sa ya kada yai ja, lumshe ido yayi ya bude, ya ce,

"In in jiya da wa na ganki?"


Yayi tambayar ba tare da yasan lokacin da ta fito ba.


Kallon sa tayi ta ga ya canja amman bata kawo komai ba. Dan haka ta ce,

"Ni da Yayanah ne!"


Kai ya gyada kawai ya dauki waya yana dane dane.


Kallon sa tayi ta kuma narke murya ta ce,

"Naje?"


Kallon ta ya tsaya yi, kafin ya ce,

"Kunyi waya da Maryam!"


Kai itama kawai ta gyada masa. A zahirin gaskiya baya son ta tafi ta bar shi amman dole ta tafi.


Dan haka ya dinga mata tambayoyi. Sannan ya bata izinin tafiya.


Tana tashi ya bita da kallo har ta fita ta rufo kofar idon sa na kan ta.


Ido ya lumshe, yana me dafe zuciyar sa.

Tana komawa ta bawa Zainab labarin abinda ya faru da yadda suka hadu jiya.


Zainab dariya tayi ta ce,

"Wai ke baki gane wani abu ba."


Asma'u ta ce,

"Me zan gane me ya faru?"


Dariya kawai Zainab tayi ta ce,

"Allah bazan fada miki ba. In kin gano ka zo kiban labari."


Share maganar Asma'u tayi dan ta san Zainab akwai jan rai an kana son abu.


Daga haka suka zauna aka shiga wani lecture din.


Karfe hudu dai dai Yaa Aslam yazo, kiran Asma'u yayi bata dauka ba. Yasan tana massalaci. Dan haka ya fito ya zauna daga kasan bishiya.


Yana zaune ya hango Sir Sabir ya taho a cikin motar sa.


Kallon ssa yayi ya dan saki tsaki sannan ya dauke idon sa. Ya rasa dalili shi dai kawai gayen bai masa ba.


Shima kuma ta bangaren Sir din ya ganshi sai dai shi a duk sanda suka hadu sai yaji wata faduwar gaba


Yana zaune a haka Munasha ta gano shi. Gunsa ta nufa tana canja salon takun ta.


A hankali ta karasa gun tai masa sallama. Dagowa yayi ya na kallon ta daga sama zuwa kasa.


Ita kuma sai gyara tsayuwa take. Baki ya yamutse, kamar yaga kashi ya dauke kai.


Wani iri taji amman duk da haka ta dake ta ce,

"Sannu fa!"


"Yauwah!"

Ya fada kamar bai san wanda yai maganar ba dan kansa yana can kallon gefe.


Zatai magana kenan ya daga mata hannu. Sannan ya mike ya tsaya a gaban ta.


"Me kike nema ne?"

Ya tambaye ta yana juya mata baya,


Kallon sa ta tsaya yi tana hadiyar yawu.

"Wallahi sai na dan dani zumar gayen nn."


Ta fada a ranta. Tana kallon sa hadi da hadiyar yawu sai kace ta ga nama.


STORY CONTINUES BELOW

"Uhmm uhmm daman!"

Sai kuma tayi shiru.


Murmushi yayi mai sauti sannan ya juyo gare ta.

"Haba yan mata. Ki rike ajin ki na 'ya mace man. Nasan irin ku nasan kalar ku muna dasu daa yawa wadan da ke bibiyar mu. Ba wai son mu kuke haka kawai ba akwai wani abu a ranku. In da 'yar mutumci ce taga mutum tana son sa, ta san ta yadda zata tusa kanta gare shi har yasan da ita. Ba kamar ke da kikazo kika samen gaba da gaba ba. Kuma dan Allah kalli shigar ki. Wannan ba shigar ya'yan kirki bace, ko da zan so mace. Ba zan so macen da bata da kamun kai ba wacce ta gama tallata surar ta ga mazan waje ba."


Shiru yayi sannan ya ce,

"Kalle ki dan Allah kin kalli kan ki a mudubi kuwa kafin ki fito."

Kanta take kalla sai a lokacin taga shirga dake jikin ta ba mai kyau ba.


Kanta ya sha gashin doki har gadon baya, sannan ta saka riga da wando sun dame ta.


Sai wani dan karamin mayafi da ta yafa ta saka takalmi mai tsini.


Bilkis ce ta kara so gun ta ce,

"Kai Munasha kina wuta fa."


Shiru Maimuna tai mata, kallon su yayi ya ce,

"Yanzu wannan dawa kikai koyi, kinsan wadan da kikai koyi dasu ko, to turawa ne, Bayan Allah madaukakin sarki ya ce,

"Kada ku rike da al'adun yahudu da nasara kuma ya ce kada ku koyi abubuwan su wajen shiga sauya suna. Duk wanda ya jibanta al amaransa zuwa ga yahudu da nasara Allah (SWT) ya ce, ka zamto daga cikin su. Wato ya zamo su.' (Ma'ida 51)

"Kinga ko anan kinyi abu nawa irin nasu. Ji shigar ki. ji wani suna da aka kira ki dashi.

Manzon Allah (SAW) Yace,

'Duk wanda ya kwaikwayi wasu to shima ya zama shi.'

Haka nan Manzon Allah (SAW) ya ce,

'Mutun na tashi ranar alkiyama da wanda yake so.'

In kana son Allah da mazon sa kana yin abinda suka ce dasu zaka tashi. Haka nan in kana son wasun su, to da su zaka tashi.

Haka nan aya ta 57 a cikin suratul ma'ida. Allah madaukakin sarki yaba cewa,

"Yaku wadan da kukai imani karku riki wadan da suka rike adddinin mu da wasa da rudu' (yahudu da nasara) su ne suka rike addinin mu da wasa. Kar mu rike kafiri a cikin masoya (mudai dai yi mu'amala) muji tsoron Allah in mun kasance mumunai.

kiji tsoron Allah ki koma ga Allah dan daga shigar ki ya nuna min ke wace, kada ki manta daman sai da shaidan ya ce,

'Wallahi sai ya samu rabon sa.'

Wallahi ba kowa ke saka mana wadan nan ra'ayuyu kan ba in ba shi ba duk dan ya dulmiyar damu. Kiji tsoron Allah ki daina duk abinda kike. Duniya ba matabbaciyya bace, haka rayuwar mu a koda yaushe mai iya karewa ce."


Ya juya kenan yaga Asma'u da Zainab suna tsaya suna sauraran su. Kuka Maimuna ta fashe da shi ta zube a kasa. Da sauri Asma'u ta karasa gun ta ta dago ta.


Kallon Asma'u tayi idon tana fitar da kwalla. Kuka take sosai sai da kyar Asma'u ta lallashe ta tayi shiru.


"Asma'u daman mutum kan hadu da mutum in Allah yaso. haduwa ta ga Aslam shine shiriya ta da izinin Allah. Nagode Yaa Aslam nagode insha Allahu bazan kara aikata abubuwan sabo ba."


Sosai Yaa Aslam yaji dadi.

"Ba komai. Kiji tsoron Allah dai a duk inda kike."


Ya kalli Asma'u ya sakar mata murmushi. Zainab ya kalla ya ce,

"A'ah In-low ashe kina nan."


Murmushi tayi ta dan durkusa ta gaishe shi.


Gaba sukai shi da ita suna hira. Har take basa labarin yadda Maimuna ta dinga damun Asma'u akan sa.


Dariya yayi ya ce,

"Allah sarki. Ita kuma me tayi."


Zainab ta ce,

"Ai kasan Asma'u in yan mutuncin suna nan akwai saukin kai."


Sukai dariya gaba daya. Ya ce,

"Lallai kam. Amman dadi na da Asma'u akwai hakuri sai dai in aka kai ta karshe basan ya zata yi ba kuma,"


"Wallahi kuwa ba ruwan kowa nata ne, kowa tana iya zama da shi. Allah Asma'u bata da temper kowa sai taka ta yadda zata saka farin ciki da karatun ya. Bata da abokin fada bata da riko."


Murmushi yayi jin halayar Asma'u wanda shima ya san da su


Asma'u tana can lallashin Maimuna har sai da ta ga ta daina kukan ta nutsu sannan sukai sallama.


Bilkis kuwa duk da abinda Aslam ya fada ya ratsa ta amman bata jin zata daina abubuwan da take yi


Gun Maimuna tayi ta ce,

"Maunas......"


Bata karasa fada ba ta dakatar da ita ta ce,

"Bana son sunan nan ki kira ni da Maimuna in zaki iya"


Ta mike tayi gun motar ta tashiga ta fita daga makarantar a guje.


Baki Bilkis ta tabe ta shiga motar da Maimuna ta tabi bayan ta.


Asma'u kam suna tsaye ita da Aslam da Zainab.


Zainab na tsokanar ta da tini an kwace mata Yaa Aslam dinta.


Duka ta kai mata ta ce,

"Ai ba mai iya kwace shi sai Allah yaso."


Yaa Aslam ya ,

"Allah ma bazai so na ni na kine ke kadai."


Gira ta daga ta kalli Zainab ta ce,

"Kinji ko?"


Murmushi tayi tace,

"Allah tabbatar da alheri."


"Ameen!"

Duk suka amsa sannan sukai sallama ta shiga motar gidan su itama suka shiga ita da Yaa Aslam suka tafi.


A mota ma labarin yadda sukai da Maimuna ne yadda ya je gun ta a makaranta da lokacin da ta tambaye ta aikin sa da suna sa.


Dariya take shi kuwa ya hade rai. Kallon sa tayi ta ce,

"Me kuma nayi?"


Motar ya faka a gefen hanya ya kalle ta ya ce,

"Wai ke bakya kishi nane, daga nan baza ki gane me take nufi ba. Amman kin wani sake da ita."


Murmushi tayi ta ce,

"To Yaa Aslam ai sai mutum bai san matsayin sa a gun masoyin sa ba zai tsaya kishi. Ni da nasan ko da duk matan duniyar nan zaka aura sona daban ne a zuciyar ka haka nan kaunar da kake min baza ta taba tafiya ba kuma bame iya samun rabin ta daga wajen ka. Kada fa ka manta mukullin zuciyar ka nice. Tayya zan bude har wata ta shiga."


Dariya yayi ya lakace hancin ta fe,

"Ni dai ana kishi na dan baki san wasu mantan bane."


Murmushi tayi ta ce,

"Ina kishin ka man nafi kowa kishin ka da kishin masoyin sa saboda ni kadai nasan wane irin masoyi ne dani. Ina son ka. Ina kaunar ka bazan so wata ta rabe ka ba ni kadai nasan kishin da nake maka a cikin zuciya ta."

Haka rayuwar Asma'u ta cigaba da tafiya cikin kwanciyyar hankali da samun soyayya daga wajen iyayen ta da masoyin ta kuma yayan ta.+

Cikin satin biyun da yazo yi ba karamin shakuwa ssuka kara ba. Kullum shi zai kai ta makaranta ya kuma dauko ta.

Makarata sam ta daina yi dan haka kullum tana gaba da Sir Sabir ya shiga da ita yake yin tozali.

Yanzu Maimuna ta shiryu dan gidan ta ma da motar da take hawa duk ta siyar ta fara business sosai take karatu tana kuma taimakawa iyayen ta.

Dan duk karshen wata zataje gida. Haka duk zigar kawayen ta yan harka taki ta dauka.

Dan har sam ta canja ta koma ga Allah kullum hijabai take sawa har kasa.

Kasuwancin ta kuwa Allah yasa mata albarka dan a hostel duk abinda kake nema kaje gunta zaka samu banda kaya da take rabawa bashi da anyi albashi aba ta kudin ta.

Sosai suke mutunci da Asma'u da Zainab. Suna kara koya mata abinda bata iya ba tinda ita lab science take karanta.

Yau satin Yaa Aslam uku kenan a kano ya kasa komawa dan bai son ya tafi ya bar Asma'un sa.

Suna zaune a garden kamar yadda suka saba in sun dawo gida da wuri.

Aiki ya gama koya mata sannan ya kalle ta yai murmushi.

"Lafiya?"
ta tambaye shi.

Murmushi ya kara. Fuska ta shagwabe ta ce,
"Yaa Aslam Mene wai?"

Dariya yayi. Sai ta bata fuska kuma.
"Ayyah sorry yan mata na. Kinsan me?"

Da sauri ta girgiza kai. Ya ce,
"Wallahi kina yar karama na tuna lokacin da kullum kina saman cinya ta a zaune, ko bacci sai a guna zakiyi. Yanzu kuma kalle ki yadda kika girma kika zama mace."

Sai yayi dariya. Fuska ta bata ta ce,
"Allah Yaa Aslam din nan ko? Wai shekara nawa ma ka bani."

Ido yayo waje dasu ya ce,
"Tab! Allah yarinyar nan ko dan kinga ina kula ki ko?"

"Kaji ka Yaya. Wai ina zaune a cinyar ka ko nai bacci a gun ka. Yanzu fa ka daina la'akari da da ma wallahi dan nasan ka gamai min wayoo ne kawai kaga yarinta ta."
ta fada tana turo ba

Dariya yayi ya ce,
"Wallahi *Husnah* ke a autar ma ko ta karshe ce, rashin wayon ki rigimar ki ko?"

Ya fada yana girgiza kai. Ya ce,
"Dan ma Allah yasa na saba da wani zaki aura da na tausaya miki dan kafin ya saba da rigimar ki ko?"

Murmushi tayi ta ce,
"Shiyasa a ko da yaushe nake godewa Allah ya hadani da Yaya na. Yayan na ma wanda yafi so na. Wanda yafi kula dani wanda yasan komai nawa."

Murmushi yayi ya ce,
"Yarinya kin min wayoo nima zanje na samo wacce tasan ni."

Fuska ta bata ta ce,
"Akwai wace tasan ka ne sama dani. Kaga ni kanwar ka ce, zaka iya hukunta ni duk abinda nai maka Mami da Dady baza su ce komai ba. Amman kaje ka samo wacce mahaifin ta zai zo ya zane ka in ka taba masa 'yar sa."

STORY CONTINUES BELOW
Dariya yayi ya ce,
" *Husnah* kenan ina kaunar ki kaunar ki baza ta taba bari na ba. Da ita zan mutu."
Asma'u ta ce,
"Ya Aslam na maka alkawarin bazan taba barin ka ba zan kasance da kai a duk halin da kake ciki. Zan baka duk kan kulawa wacce ta rataya a kaina."

Yaa Aslam ya ce,
"Nima nayi miki alkawari...."

Da sauri ta katse shi da
"A'ah ni ba sai kayi ba."

Ya ce,
"Saboda me?"

Ta ce,
"Na yadda da kai zaka kula dani. Nasan ko ba aure a tsakanin mu zaka kula dani. haka kuma nasan zaka kasance dani. Wannan ma nasan zaka iya. Wanda zaka fada bana son yazo be faru ba shine kace baza kai min kishiya ba."

Kallon ta yayi ya ce,
" *Husnah* kenan baki yadda dani bane."

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah na yadda da kai. Ai ba mu san yadda Allah ya kaddara mana ba. Su wadan can nasan ko ba aure zamu kasance tare "

Murmushi yayi ya ce,
" *Husnah* Nai miki alkawari bazan guje miki. In dai soyayya tace kin gama samu, kuma insha Allahu babu kishiya."

Murmushi tayi jikin ta a sanyaye ta ce,
"Toh Ya Aslam. Amman ina tsoro wallahi."

Ya ce,
"Ki bar tsoro, ki sanya a ran ki za ayi auren mu. In Allah ya yadda zamuyi rayuwa, matsayin ma aurata za muyi shakuwa. Ba gudu ba ja da baya sonki zan tayi zan zauna dake har karshen rayuwa."

Kanta ta sunkuyar ta ce,
"Allah yasa."

"Ameen!"
Ya fada yana dago kanta.

Murmushin yake tai masa. Fuska ya bata ya ce,
" ki fadan damuwar ki?"

Murmushi tayi ta ce,
"Ina yawan jin faduwar gaba Yaa Aslam kuma nafi alakanta haka da soyayyar mu. Ya Aslam ina tsoro. Tsoro ma ba kadan ba."

Murmushi yayi dan shima ta sanyayar masa da gwiwa. Ya ce,
"Kinsa dai ki kadai ce a Cikin rai na ko? Wallahi *Husnah* ke kadai ce buri na da muradi na ban da burin samun wata mace in bake ba. filin zuciyata ko ta ina kece bake, ba sauran wajen da wata zata shigo shi to kwantar da hankalin ki."

Fuska a dan marairai ce ta ce,
"Kallon ka kadai nayi da ido nishadi yake sanya ni. Kai ne muradi na. farin ciki na abin alfahari na. Dole ina tsoron rasa ka da kai kadai na yadda na aminta da kai na fara soyayya dakai nake son kare ta in har na rasa ka ya kake zaton zan kasance."

Ya ce,
"Allah ma zai sa ke *tawa ce* "

Ta ce,
"Allah yasa."

Ya ce,
"Ameen!"

Shiru sukai ya ce,
"Kinsan me?"

Kai ta girgiza masa. Ya ce,
"Ina bude ido na farka a bacci ba wanda nake son na gani a dama na sai ke. Shi yasa da na tashi hoton ki shi nake fara kalla. Bana gajiya da kallon kyakyawar fuskar ki."

Murmushi tayi ta ce,
"Yaa Aslam ina rasa a cikin mu wa yafi son wani."

Ya ce,
"Kinsan me?"

Ta ce,
"A'ah!"

Ya ce,
"Ki bari sai munyi auren anan za a ga wanda yafi son wani. Ni dai nai alkwarain bazan taba saki kuka ba. zan ta faran ta miki zan kula dake insha Allahu."

Dariya tayi ta ce,
"Nima nai maka alkwaraiin kula da kai da sauke maka duk hakkin da ya hau kai na. Zan kasance mace ta gari me son farin cikin ka mai gusar maka da bakin cikin ka."

Hannun ta ya kamo, ya ce,
"Oya Alkawari."

Dagowa tayi ta kalli cikin idon sa ta ce,
"Nai maka alkawarin bazan taba daina son ka ba. Kuma zan kasamce mace ta gari a tare da kai kuma bazan taba guje maka ba."

Murmushi yayi ya ce,
"Nima na miki alkawarin bazan taba guje miki ba haka nan zan ta son ki har karshen rayuwa ta zan kasance mai saki farin cikin ki."

"Allah yasa."
ta ce,

Ya amsa da
"Ameen!"

Ta ce,
"Yaa Aslam duk abinda nake aka ce kai ko sai na saurare shi."

Murmushi yayi ya ce,
"Bajin dadin labari in ba naki ba, ba shauki ke ko acikin taurari kin yi daban. Kaunar ki nake yi kullum a cikin zuciya ta."

"Hmm Ya Aslam! Kenan"

" *Husnah* komai nawa naki ne ban da burin da ya wuce naki. Kume naki burgeni yake yi. Surar ki tamkar ke kika tsara ta ina matukar kaunar ki."

Ido ta rufe da hannayen ta. Hannun nata ya kamo ya ce,
"Dan Allah kalli yatsun ki abin sha'awa."

Janye hannun ta tayi da sauri. Fuskar ta ya kalla ya ce,
"Kalli fuskar ki me kyau."

Ido ta bude ta kalle shi. Ya ce,
"Kalli idanun ki masu kyau da girma da birkita tunani. Ina kunar su."

Baki ta dan turo, ya ce,
"Ya salam ai sai kisa nayi abinda ban shirya ba. Ina son bakin nan naki."

Kafa ta buga a kasa ta ce,
"Kai Yaa Aslam!"

Dariya yayi ya ce,
"Wallahi komai naki burge ni yake. Komai. komai nake nufi."

Mikewa tayi ta ce,
"Ni mu shiga ciki magariba ta taho."

Mikewa yayi ya bi bayan ta rike da littatafn ta.

Suna shiga ta haye sama dakin ta. Kan gado ta fada ta lumshe ido.

Dakin ya shiga ya ajiye mata littafan sannan ya kuma gefen ta yana kallon ta.

Jin ido na bin ta, ya sa tai ssaurin bude ganin shi tayi a gaban ta ya tsura mata ido.

Mikewa tayi zaune ta ce,
"Ya dai?"

Murmushi yayi ya mike ya ce,
"Ji kiran sallah amman kika zo kika kwanta ko? Ko bakya yi ne?"

Kai ta gyada masa, mikewa yayi ya ce,
"Bari nai alwala."

Ya shiga bandakin ta. Alwala yayi ya fito ya ce,
"To na tafi sallah. Ya kamata kiyi lazumi ko ki karanta alkur'ani tinda ba sallah zakiyi ba."

Kai ta gyada masa. Dan ya saba sanin in ba yin sallah take ba.

Ita wani lokacin tana daukar sa tamkar Yaa Buharin ta ne.

Watan Yaa Aslam daya ya fara shirin tafiya.

Asma'u ji tayi kamar me, dan kuka ta sha shi tinda ya ce mata zzai tafi.

Ranar Asabar ya saka tafiyar tashi. Ranar juma'a ya dauke ta ya kai ta shopping yai mata siyayya mai yawan gaske.

Amman duk jikin ta a sanyaye yake da ka kalle ta zaka san bata da walwala.

Haka suka dawo gida duk yadda yaso ta sake kasawa tayi sai dai ta dan yi masa murmushin yake.

Da dare bayan sun ci abinci ta shiga dakin sa dan taya shi hada kaya.

Shima yana kwance ya fito da kayan ya ajiye akan gado.

Tunanin shima rabuwa da ita yake. Kallon sa tayi ta wuce wajen kayan ta fara zuba masa a cikin akwatin sa.

Motsin ta da yaji shi ya sa shi bude idon sa. Kallon ta ya tsaya yi hada masa kayan take cikin sanyin jiki.

Jin idon sa akan ta yasa ta kalle shi, Murmushi ta sakar masa, ta cigaba da abinda taken.

Mikewa yayi zaune ya zura mata ido. Ko kiftawa baya yi.

Har ta gama bai dauke idon sa daga kallon ta ba.

Takalman sa ta fara hadawa ta gama ta koma gefen sa ta zauna.

Kallon sa ya dawo da shi kan ta, murmushi ta kara sakar masa.

"Yaya nah lafiya?"
Ta tambaye shi.

"Baby nah bana son ganin ki a damuwa,"
Ya fada yana kamo hannun ta.

Hannun ta. ta zare ta ce,
"Yaya nah naji sai kuma me?"

"Bansan menene ba. Amman bana son barin ki Asma'u bana son nima na tafi. Ki yadda nayi magana ai mana auren kinji."

STORY CONTINUES BELOW

Kasa tayi da kanta sannan ta ce,
"To Yaya nah yanzu in mukai auren karatu na fa. Kaga nazo gangara ka bari nan da wata shekara sai muyi aure ko?"

Kai ya gyada ya ce,
"Haka ne, amman bana son na rasa ki bana son nayi nesa da ke."
"Haba Yaya nah kar ka manta fa dazu kai ka gama lallashi na akan nayi hakuri muna tare ko?"

Hannun ta ya kamo ya matse shi a cikin nasa. Ido ya lumshe, sannan ya bude.

Kallon ta ya tsaya yi tin tana kallon cikin idon sa, har ta gaza kalla dan wani abu take ganin yana shiga cikin nata.

Lumshe idon tayi matsowa yayi kusa da ita. Ya ce,
"Asma'u ki riken Alkawari na kar ki taba bari na in dai ina cikin duniyar nan ina son ki yi min alkawarin ke tawa ce."

Idon ta, ta bude wanda suka canja kala zuwa ja, ta ce,
"Wallahi Yaa Aslam na maka wannan alkawarin bazan taba barin ka ba. Sai dai in kai ka bukata."

Ido ya lumshe samnan ya ce,
"Ni kuwa tayaya za'ai na bukaci rabuwa da rayuwa ta."

Murmushi tayi ta ce,
"Bare kuma ni."

Yayi murmushi.
"Bari naje na kwanta!"

Kallon ta yayi ya ce,
"Kamar mu kwana tare."

Murmushi tayi ta ce,
"Allah kawo ranar da zamu kwana taren."

"Ameen!"
Ya fada yana mikewa. A kofar dakin ta suka kara tsayawa sun dauki kusan minti ashirin suna tsaye sannan sukai sallama ta shiga.

Tana shiga daki ta fashe da kuka. Rasa kukan me take tayi amman ta san cewa ba zai rasa nasava da tafiyar Yaa Aslam ba.

Sai da taji kiran sa a waya sannan tai saurin shiga bayi tai wanka ta fito ta shirya sanann ta kira sa.

"Baby na kin kwanta ne?"
Ya tambaya daga can site din.

"Eh yanzu na kwanta."
ta bashi amsa.

Ya ce,
"To kiyi addu"a sai da safe."

Ta ce,
"Allah tashe mu lafiya."
Ta fada tana kashe wayar.

Washe gari tin asuba ta tashi ta yi duk abinda zata yi.

Wanka tayi ta koma gado tai kwanciyyar ta.

Sai karfe sha biyu sannan ta mike ta kara watsa ruwa ta shirya cikin wani tissue pink material wanda akai mata dinkin fitetgown, batai kwalliya ba.
Hoda da man lebe kawai ta shafa sai kwalli da ta saka a idon ta.

Falo ta fito ba kowa a sama a kasa ta dinga jin maganar su.

Sauka tayi a hankali ba ta kalle su ba sai da ta shiga kkitchen.

Ruwan zafi kawai ta hada ta fito falo. Sai da ta gaishe da Yaa Aslam da Yaa Buhari sannan ta nufi daining.

Zama tayi ta kasa shan tea din ma. Yaa Aslam ne ya mike ya shiga kitchen ya dafa mata indomie sai ya soya mata kwai.

Daining ya nufa ya zauna a kujerar dake facing tata.

Kallon sa tayi ta sakar masa murmushi.

Plate din hannun sa ya tura mata gaban ta. Ya daga mata gira alamar 'ta ci.'

Ja tayi ta saka spoon tana ta wasa da shi.

Amsar spoon din yayi ya fara bata a baki. A hankali a hankali har ta ci mai yawa sannan ta ce ta koshi.

Falo suka koma suna hira da Yaa buhari ita kuwa tai shiru sai dai ta kalli.wannan ta kalli wannan.

Kiran sallah aka yi wannan yasa kowa ya tafi dakin sa.

Alwala su Yaa Aslam sukai suka wuce massalaci.

Ita kuma a daki tai sallar tinda ta idar ta kasa tashi daga inda take har karfe biyu tana zaune.

Yaa Aslam ne ya shigo dakin cikin shirin tafiyar sa.

Yana sanye da Milk din wando sai maroon kalar riga mai dogon hannu.

Takalmin kafar sa ma maroon ne. sai tashin kamshi yake.

Tana ganin sa ta mike ta saki fara'a shima murmushin yayi ya kamo hannun ta suka fito.

Mami na falo suka tadda ta. Sallama yai mata suka fice tare.

Yaa Buhari ta gani a cikin mota yana jiran su.

Bayan mota suka shiga daga ita har shi har lokacin hannun ta na cikin nasa.

Wata zoben azurfa ya fito dashi daga cikin jakar sa. Ya zura mata a yatsan ta take hannun ya kara gaske yai mata kyau.

Sumbatar hannun yayi yana kallon cikin idon ta.

Lumshe idon tayi tana mai yin murmushi.

Suna zuwa airport din Yaa Buhari ya fita a motar.

Kallon ta yayi ya ce,
"Baby na zan tafi ki kular min da alkawari na."

Asma'u Ta ce,
"To Yaya nah Allah kiyaye hanya, kar ka manta da alkawari na nima kaji."

Ya ce,
"Insha Alalhu bazan manta ba!"
Yai mata kiss a goshi sannan ya fita.

Ta taga ya leko ya ce,
"Ki zauna ba sai kin ffito ba. Kai ta daga masa sai kuka kuma.

Kuka sosai take ba shiri ya koma cikin motar ya jata jikin sa yana lallashin ta. Amman kamar kara zuga ta yake.

Ya jima yana lallashin ta da kalamai masu sanyaya rai yaji ta daina kuka.

Bai daina shafa mata bayan ta ba da kwantar da hankalin ta. Sai da ya dauki minti goma a haka sannan ya dago dan ya ga me take.

Bacci yaga tana yi sai ajiyar zuciya take saukewa.

Murmushi yayi ya kwantar da ita sannan ya kara kissing nata a goshi.

Waya ya dauko ya dauki pics din ta sannan ya fita a hankali.

Yaa Buhari ya gani suka karasa ciki. Basu jina ba ya tashi. Dawowa mota Yaa Buhari yayi ya ganta tana ta baccin ta.

Motar ya tayar suka tafi gida a hankali yake tukin duk dan kar ya tashe ta.

Yana tausaya musu yana musu addu'a akan Allah ya mallaka musu juna su. Dan son da sukewa juna su shi gani yake kamar yayi yawa.

Kuma yana tausaya musu dan kar wani a bu ya faru bai san wane hali zasu shiga ba.

Har ya isa gida bata tashi ba. Daukar ta yayi ya kaita dakinta samman ya sanar da Mami sun dawo.

Sai magariba ta tashi. Tana bude ido taji idon ta a kumbure.

Taba su tayi sai kuma ta tuna da abinda ya faru dazu.

Wani kukan ta kuma saki ita kadai tayi iya yin ta sannan ta mike ta shiga ban daki.

Wanka tayi tayo alwala ta fito ta saka kayan bacci ta tada sallah tana idar wa ta kwanta anan inda take
Wani bacci ya kuma sace ta. Sai tara saura ta farka.

Bandaki ta shiga tai alwala ta fito tai sallah zata hau gado kenan sai ga Mami da Dady nan sun shigo.

Mami rike da katon tire a hannu. Gefen ta Dady ya zauna ya ce,
"Wannan shakuwar taku Asma'u tayi yawa. Yanzu inda Yayan naki yai aure ai sai Antyn ki tana jin haushi kiyi hakuri da kin gama karatu zaki je ki musu hutu kinji."

Kai ta daga tana masa murmushi sannan tai masa sannu da zuwa.

Abinci Mami ta zuba mata sai da ta ga taci ta koshi sannan suka fita daga daki
Kan gado ta koma ta kwanta kiran sa ne ya shigo.

Dagawa tayi cikin sanyin murya. Ta ce,
"Yaya nah ka isa lafiya yasu Momy da Dady?"

"Duk suna lafiya ya na baro ku?"
"Lafiya Alhamdulilah."

"Wallahi ina kewar Baby na."
Murmushi tayi ta ce.
"Nima haka."

Daga haka suka fara hirar su kamar yadda suka saba.

Sun jima suna hira sannan sukai sallama kowa ya kwanta.

*Uhmmm*


Post a Comment for "RAYUWAR ASMAU CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...