Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5

- - Post a Comment

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5


Pretty ce zaune a gaban wani boka. Kai sufar bokan ma kanta abar kyama ce da tsoro bare kuma warin da yake yi.+

Abinda take bukata ta gama fada masa.
buga kasa yayi yai dube duben sa sannan ya ce,
"Kin kawo aiki me wahala dan mutanen nan ba a zaune suke ba wajen ibada sai dai zan san yadda zamu yi muga ta wacce hanya zamu bi."

"Yauwah ni na fi so ma ita yarinyar a haukata ta yadda dole zai hakura da ita ko ta mutu ma."

"Kull!"
Yai mata wata tsawa ya ce,

"Wannan yarinyar har tafi Aslam tsari da riko da addini baza mu iya da ita ba. Tafi karfin mu."

Da haka ta zube masa kudi masu waya sannan sukai akan nan da wata daya ta dawo.

Daga nan ma Pretty ba gida tayi ba wajen wani bokan ta karayi suka karai mata alkawarin komai zai wakana yadda take so.

Da haka ta koma gida da murna abinda take so zai zo gare ta.

Dan har ta fara shirye shiryen auren ta da Aslam.

Aslam kuwa bai son wainar dake soyawa ba.
Shi dai bai da buri da muradin da ya wuce ya ganshi tare da Asma'u.

Kowa da yasan Aslam yasan Asma'u dan kowa yasan irin son da yake mata.

Abokan sa har tsiya suke masa su ce, ya makalewa karamar yarinya me ya gani agun ta.

Shi dai sai dai yai dariya dan son Asma'u daga Allah ne. Allah shi ya sa masa son ta a zuciyar sa yake jin bazai taba iya rayuwa ba ita ba.

Yasha fadawa Asma'u bazai taba barin ta ba ko ya ce,
"Ba zai taba daina son ta ko mata kishiya ba."

Duk kishin Asma'u sai dai ta ce,
"A'ah Yaa Aslam ka daina min irin wannan al kawarin Baka san me Allah ya tsara mana ba."

Shi in ta fadi haka wani lokacin har haushi yake ji.

Ita kuma tana tsoron ta sawa zuciyar ta haka Allah ya riga da ya tsara wani abun daban.

Tana son Aslam tana kishin sa kamar yadda shima yake son ta da kishin ta.

Dan yawancin wasu dogayen hijaban ta shi ya siyo mata dan zuwa makaranta. Daga doguwar riga sai hijabai su take sawa.

*********
Munasha ce zaune da kawar ta. Kallon ta kawar tayi ta ce,
"Wallahi ko mayya sai haka."

Munasha Ta ce,
"Da me fa?"

"Wannan yaron mana Aslam dan Allah ki kyale shi ki kama samarin harkar yanzu ba kudi basa shigo mana sosai saboda kin rage kula su wallahi."

Ido Munasha ta lumshe ta ce,
"A duniya mutum daya na taba so kuma shi insha Allahu sai na aure shi shine Nazir. Ko da na rasa shi Kuwa na rasa shi to bazan rasa Aslam ba wallahi Aslam ya min surar sa abar so ce ga kowacce mace da tasan 'da namiji. Kingan shi kuwa,"

STORY CONTINUES BELOW

Ta girgiza kai ta kwanta wallahi ba wanda yanzu nake sha'awa in ba shi ba. Shi kadai nake son nai tarayya da shi sai kuma my oga at top."

"Ni dai naji ki dauri kije gun Alhaji Usman kinsan babar harka ne, ko nawa kika nema zai baki kinga ko dasu masan yadda za ayi a jawo hankalin Aslam gareki."

Munasha ta ce,
"Kuma fa kin kawo magana wallahi dan Aslam zan je."

Ta mike ta fada wanka cikin minti biyar ta shirya cikin wani dan mini siket wanda ana gano kasan ta.

Sai yar half ves da ta saka ta bazo da gashin dakin ta gadon baya.

Tayi kwalliyar karuwai ta jefa cingum baki tana tauna sai kara take dashi.

Turare ta bade jikin ta dashi ta fita ta shiga mota sai guesthouse din Alhaji Usman.

Yasan da zuwan ta dan yafi sati yana jiran zuwan ta.

Yana falo a kwance yana trying number ta sai gata kamar daga sama.

Kan cinyar sa ta dane, tana masa wani kallo tana shafa shi.

Nan da nan ta burkita masa tunani tun a falo suka fara masha'ar su har suka koma daki.

A ranar a gidan ta kwana dan washe gari ma kin barin ta yayi ta tafi.

A kalla sai da tai sati biyu a gidan sannan ta tafi da milliyoyin kudi banda mota da ya mallaka mata.

Haka ta koma gidan ta da ta siya ta tadda Bulkis.

Mukkullin motarta ta da ta jefawa mata ta ce,
"Na bar miki."

Tsalle Bilki ta duka tana cewa da
"Da gaske!"

"Eh man! Kinsan ni yanzu na zama babar hajiya. Zan miki transper kudi. Amman ina son naje gida yau naga ya Baba take ciki."

Bilki ta ce,
"Sai yaushe kuma?"

"Sati daya zan yi."
Munasha ta bata amsa ta mike tana debo kayan da gida suka san ta dasu ta zuba a jaka ta shiga tai wanka ta saka wata kodadiyar atamfa dikin riga da zani.

Tana fitowa Bilki ta saka dariya ta ce,
"Amman fa da ace a haka kike da kin bada mata."

Dariya itama tayi ta ce,
"Ke dai bari baki ji yadda zanin nan ya dame ni ba."

"Wai dan Allah satin.kuwa zakiyi dan Allah kiyi kwana biyu ki dawo."
Bilkis tafada

Munasha ta ce,
"Aah bilki duk rashin iyaye na ina son su. Naje gun wani kato na yi sati biyu bare gun iyaye dan nayi sati. Aah wallahi."

Baki Bilkis ta tabe ta ce,
"Shikenan. Ki gaida su Baban."

"Zasu ji "
Ta dauki jakar ta tafi.

Napep ta tsayar ya kai ta har gida. Kannen ta sai murna suke sun san zasu samu dan abin tabawa.

Gun Babar ta taje ta gaishe ta. Baba sai addu'a take mata na samun nasarar karatu sannan ta gaida mahaifin ta.

Kayan abinci ta siyo musu bubun shikafa da katon din tafiya da macaroni.

Ta bawa Baba dubu goma Mama dubu biyar.
Daman ta fada musu tana dan siyar da abubuwa a makaranta wannan yasa suke zaton tana take samun kudi.

Duk abinda take akwai ta da ibada da biyayya ga iyayen ta.

Dan ita tazo gida ita ke yin komai haka zasu ta sa mata albarka.

Taje gidan su Nasir saurayin ta wajen kawar ta Rashida.

Anan Rashida take labarta mata Yaya ya kammala karatu sun rike shi zaiyi aiki shekara daya ya dawo.

Ba karamin murna Maimuna ta taya shi ba.
Anan suke hira da Rashida akan makaranta.

Rashida ta ce,
"Maimuna ki godewa Allah duk cikin mu ke ce kika samu jami'a mu duk sai kwaleji. Dan Allah ki dage ki fito da sakamako mai kyau. Kinga karatun nan shine gatan mu da na iyayen mu da ya'ya mu. In muka samu aiki zamu tai makawa iyayen mu. Ya'yan mu kuma mu koya musu. Dan Allah ki dage kinga sauran shekara daya da rabi kigama kinji."

Sosai Maimuna taji fadan Rashida kuma tasa a ranta zata tsaya tayi karatun ta gama lafiya.

Satin ta daya ta fara shirin komawa ita kan ta ji take kamar kar ta tafi amman kuma tana so taje ta tana din rayuwar ta tanan gaba.

Sannan tasa a ranta wannan karan zata tsaya ta fuskanci rayuwa tai karatu dan tasan tabbas karatun nan shine gatan ta.

Karuwan ci na dan lokaci ne in kuwa kana da ilimi ka samu aiki kana samun kobo da naira.

Da kuka ta tafi kannen ta suma sai kuka suke.

Tinda Munasha ta koma makaranta take karatu sosai.

Duk wanda tasan yana da kokari tai ta bibiyar sa kenan su kuma suna wulakanta ta suna zaton ba da gaske take ba.

Sai da suka ga da gaske take sannan suke koya mata.

Harka da maza kuwa tanayi jifa jifa amman yanzu kudi take tarawa bata fiya shaye shaye da siyi banza siyi wofi ba.

Kawayen ta da dama sun ja baya da ita dan ta rage kashe kudi da siyan kayan maye.

Bilkisu ce kawai suke tare itama kullum sai ta ziga ta amman bata dauka.

Wani lokacin sai taji kamar ta dauka sai kuma ta fasa.

Yau ta kama Asabar tinda Asma'u taje makaranta ta dawo ta shige daki take bacci

Yaa Aslam ya kira fin sau goma amman bata ji ba dan a silent wayar take.

Ba ita ta tashi ba sai hudu saura tin sha biyu da rabi take abu daya.

Wanka ta shiga tayi tayo alwala duk da bata sallah tana yin alwala dan alwala tana da tasiri a jikin dan adam.

Mai ta shafa ta hau kwalliya sai kace wacce zata biki.

Sosai ta fente fuskar ta da yake Asma'u akwai son kwalliya wannan yasa taje ta koya to makaranta ke hanata zama tayi.

Wani Golding codeless ta dauko ta saka.

Dinkin doguwar riga daga sama ta kamata daga kasa ta bude.

Mayafi ta dauko maroon kala, karami ta yafa jikin ta ta hade turaruka sannan ta dauki wani maroon kalar sandal ta saka.

Turare ta kuma yin wanka dashi sannan tafi daga dakin ta.

Tafiya take a hankali har ta karasa dakin Yaa Buhari.

Firij ta bude ta dauki robar ice cream din ta, ta sauka kasa.

Tafiya take a hankali tana sauka idon ta na kan wayar ta da taga missed din Yaa Aslma.

Har ta karasa ta zauna sannan ta dago kanta.

Wa zata gani!!!???

Dagowa tayi wa zata gani. Ido ta kara budewa tana kare masa kallo.

Sanye yake cikin Shadda Cream kala, kansa ba hula gashin nan ya kwanta luf luf.

Idon sa sun kara girma da haske sai hancin sa da ya kara fito wa. Dan karamin bakin sa ya kara zama pink sai sajen dake gefen fuskar sa da ya kara fito da kyan sa.

Murmushi yake mata hakoran sa farare suka bayyana hadi da lobawar kumatun sa.

Mikewa tayi tana kallonsa sannan ta karasa gun sa. Hannun sa ta kama. Sai kuma ta saki murmushi ta ce,

"Wai mafarki nake ne?"
Hannun ta ya kamo yayi saitin bakin sa ya zura sannan ya dan ciza.

Da sauri ta kwace hannun tana yarfewa ta ce,
"Yaa Aslam da zafi fa."

Murmushi yayi ya kamo hannun yana hura mata iskar bakin sa.

Ido ta lumshe ya ce,
"To ai naga baki yadda ni din bane."

Murmushi tayi ta bude ido. Ya ce,
"Missed nawa kika gani tinda zan taho nake neman number ki amman ba a dauka ba."

"Wallahi sai yanzu na gani. Bacci nayi."
Ta bashi amsa tana zuba masa ido.

Shima idon ya zuba mata, sun dau mintina. a Haka kowa ya kasa daina kallon dan uwan sa.

Kamar yadda Asma'u tayi kyau a idon sa ita ma haka taga kyan sa.

Hannu ya dago yayi wajen idon ta dashi yace,
"Wannan da wannan da wannan suna burge ni."

Ya nuna idon ta da hancin ta da dan karamin bakin ta.

Dariya tayi ta ce,
"Su kadai ko shikenan tinda su kake so ka cire na bar maka."

Murmushi yayi ya ce,
"To ai kinga wanda na fiso gaba dayan ta nan."

Ya nuna ta. Dariya tayi ta yi kasa da kanta.

" *Husnah* kinyi kyau. Wallahi kin fi kyau a fili akan hoto. Hoto yana ragen kyan ki. Kinga yadda kika kara girma kuwa. Allah ko yanzu ai mana aure nasan zamu samu babies ko?"

Ya karasa fada yana mata rada a kunne. Mikewa tayi zata bar gun ya kamo hannun ta.

Komawa tayi ta zauna ta yi kasa da kanta. Murmushi yayi ya ce
"Ko ba zata iya samu bane."

Duka ta dan kai masa, ta ce,
"Kai Yaa Aslam ko gaisawa ba miyi ba."

Ta fada dan ta kautar da maganar. Dariya yayi ya ce,
"Wayo ko? To ina yini Baby nah, ya kika tashi daga bacci kin yi mafarki na. Na miki kiss ko? Na miki....."

"Haka ake gaisuwar" tai saurin katse shi. Kai ya dan sosa, ya ce,
"Ya ake yi. Kinsan in ina tare dake komai yakan bace min."

Murmushi tayi tace,
"Wannan Yayan nawa."

Shima ya ce,
"Wannan Kanwar tawa."

Sukai dariya gaba dayan su. Sannan ta ce,
"Yaya ya hanya?"

STORY CONTINUES BELOW

"Lafiya Alhamduliah! Sai kika ganni ko?"
Kai ta gyada ya ce,
"An rage mana sati daya ne, shine na taho."

"Amman naji Dadi, ina Momy da Dady "
ta tambaya.

Ya ce,
"Suna nan lafiya suna gaishe ki Dady ya bada sako a baki."

Murmushi tayi ta ce,
"To nagode!"

Dakin ta kalla ta ce,
"Yaushe kazo ne?"

Ya ce,
"Tin karfe biyu."

"Kaci abinci.?"
Ta tambaye shi.

"Kema kinsan Mami baza ta bar 'dan ta da yunwa ba."
"Uhmm ina Mamin take ne?"

"Tana dakin ta. Dauko mana ice cream din musha kar ya narke."

Mikewa tayi ta kawo suka fara sha yana bata a baki har suka shanye.

Hira suke abinsu kamar me, in ka kalle su sai sun baka sha'awa dan sun dace da juna.

Sosai take bashi labarin ckul din ta shima yana bata labarin yanayin wajen aikin su. Har akai magariba ya tafi yayi sallah ita ma tayi sama. sannan suka dawo falo.

Mikewa yayi zai fita ta ce,
"Ina zaka?"

"Ina zamu dai?"
Ya fada yana nuna mata waje.

Mikewa tayi tabi bayan sa. Garden din gidan suka nufa suka zauna a kujera suna facing junan su.

Indai Yaa Aslam yazo kano nan ne wajen zaman su,

" *Husnah* ina son ki ina kaunar ki kece farin ciki na kece rayuwa ta."

Murmushi tayi. tayi kasa da kan ta
Kallon ta yayi ya ce,
"Duk adadin zancen da zan miki *Husunah* bazan yi san rai na ba. sako na zuciyata bakina ya furta ido ba bazai boye ba. kinyi kyau ke mai kyau ce, abu da zan sa ai mana. Zan sa ai mana sahamaki, abadan bazamu rabu ba."

"Sha makin me?"
Asma'u ta tambaya.

"Aure man! Asma'u aure shine shamakin da bazai taba raba mu ba."

Murmushi tayi ta ce,
"Ka iya Sassauta harshe ka wajen fada min abinda zai min dadi. Ya Aslam Wani lokacin ina tsoran kar ka guje min dan duniyar ga da fadi. Dare da rana ban da burin da ya wuce muyi tadi."

Murmushi yayi ya ce,
"Asma'u kenan Kimin hukunci yadda ya dace a sanda nai.miki laifi. Amman sai ki min adalci a sanda bani da laifi. In kuma naki na baki kulawa ki hada rami me xurfi. a sanda na canja wani hali kimin nasiha baki guje ni ba. Ki fahimce ni aduk abinda zan miki ki auna kiga a wane hali zan miki abin. Ni dai nasan a cikin hayacina bazan taba miki abinda bakya so ba."

Asma'u ta ce,
"Yaya Aslam kamar yadda Kayi dakon soyayya ta a ko ina ka bayyana ta a fili ina gudun masu yin kwace su san ina da dalilin son da nake maka kar su kwacen ka. Tarrayar mu dakai bata da karshe dan zuciya ta da son ka ta girma ta rayu kuma da son ka zata mutu."

Murmushi yayi ya ce,
"Asma'u kenan ba wacce zata kwace miki ni. Ni naki ne ke tawa ce."

Shiru tayi sannan ta dago idon ta har ya sauya kala. A kidime ya sauko daga kujerar da yake, yana tambayar ta
"Menene? Me nayi miki?"

Kuka ta fashe dashi. Jikin sa ya janyo ta yana lalashin ta har ta samu tayi shiru sai ajiyar zuciya da take sauke da karfi
Bayan ta yake shafawa a hankali har ta koma sauke ta a hhankali. Dago ta yayi ya ce,
"Me nayi miki?"

Kai ta girgiza. Ya kalle ta ya ce,
"Dan Allah ki fadan me yake damun ki zan fiki shiga damuwa in baki fada min ba."

Kuka ta kuma fashe da shi ta ce,
"Wallahi Yaa Aslam ina jin tsoro! Ina jin tsoron kar na rasa ka."

Sai ga wani kukan nan. Rumgume ta yayi tsam yana jin wani son ta na kara ratsa shi.

A hankali ya fara magana. Ya ce,
"Asma'u kinsan wani abu kuwa. Nasha yin istihara akan al amarin mu amman a ko da yaushe kara jin son ki da kaunar ki nake. Wannan ya nuna min cewa *ke alheri ce* dan in da ke ba alheri bace da Allah zai na yayen son ki na. Asma'u tin kina yarinya nake son ki tin baki da abinda za'a so ki dan haka ki daina sawa wani abu zai sa na rabu dake, ki daina tsoron komai ki dauka ni naki ne, ke kadai. Kamar yadda kema zaki zama tawa ni kadai. Haba ni dai nasan *Husnah* *tawa ce* "

Ya dago da kanta yana goge mata hawaye. Mikewa suka yi. Ya ce,
"Smile!"

ai kuwa sai ga shi nan ta saki murmushi, ya kai hannu zai taba dimple din ta tai saurin kaucewa.

Zama yayi yana dariya, ya daga hannu ya kira ta. Alamar tazo.

Kai ta make, murmushi yayi ya ce,
"Zo mu zauna dake masoyiya na amince dake a zuciya, aure na dake na shirya amana zan rike ba gajiya. Tinda kin min so na gaskiya, dan haka ban barin ki kisha wuya. Zan kula dake zinariya."

Matsawa tayi gunsa, ta ce,
"Naji dadi wazai min murna, nayi godiya a gareka, tinda kakira ni matar ka, zana baka dukan hakkin ka, ni bazan yadda a kushe ka ba. Tinda na yaba da halin ka saboda iya takun ka natsuwar ka, da tsarin ka ni na so ka.
Na zo mu zauna dakai a rayuwa na amince dake muyi auren sunnah."

Kallon ta yake yana mamakin kalaman ta, dan yasan ba sosai Asma'u ta fiya magana a gaban sa ba saboda kunyar ta. ya ce,
"Ni dake zan daura aure na zamo ango ke amarya, dakina a gidana zaki tare ki rangada kwalliya ki min ado me kyau. Farin cikin zaya daure, hawayen ki ni zani share, dake zan zauna na more. Miyi rayuwa mai inganci bazan taba saki kuka ba."

Ta ce,
"Kai ne zabi Allah yayi mini. Naji dadi kuma kayi mini. Ga hannu na kama ka hayar mini. Gidan aure ka kaini ka ajiye ni. A mata zai zama babu kamar ni. Matsayi mai girma zana baka. In kula dakai muyi soyayya mai tsafta da rikon amana."

Mikewa yayi ya matso gun ta. Kasa tayi da kanta.

"Oh my God! Ji yarinya sai kace bake kika gama magana ba yanzu kuma sai kunya. Wannan kunyar taki."
Ya fada yana nuna ta sai kuma yayi kwafa ya ce,
"Zan cire tane, wata rana sai kin manta da kin taba jin kunya ta kamar haka."

Mikewa yayi ya kalli agogon hannun sa. Ya ce,
"Tashi mu shiga ciki tara saura."

Da sauri ta dago ta ce,
"Dan Allah da gaske?"

"Zo ki gani."
Tayi wajen sa.

Rumgume ta yayi ya nuna mata.
"Uhmm to sake ni, Dady ya dawo tin dazu."

"Muna nan soyayya bamuji shigowar sa ba."
"Kai kayi soyayya ni banyi ba."

Ta fada tana yin gaba. Kamo ta yayi ya ce,
"Au ke bakiyi ba?"

Kai ta girgiza masa ta ce,
"Ni kuwa nayi soyayya."

Sakin ta yayi ta dan matsa ta juyo ta ce,
"Ina ni ina soyayya da yaya nah. Wallahi kunya nake ji."

Ta ruga a kuje. Murmushi yayi yabi bayan ta.

Falo ta shiga tana haki kallon ta Dady yayi ya ce,
"To fah Aslam yazo an manta da Dady ko *Husnah* "

Gun sa tayi ta ce,
"Aah wallahi ban san dare yayi ba muna garden!"

Aslam ne ya shigo shima gefen Dady yayi shida Asma'u suka sa shi a tsakiya suna masa sannu da zuwa.

Yaya Buhari ya ce,
"Wallahi Mami a gidan nan ba a so na."

Sai a lokacin Aslam ya kula da shi. Dariya yayi ya ce,
"Aah 'kanina ashe ka dawo,"

Kai ya dauke wai yayi zuciya. Dariya sukayi.

Asma'u tayi gefen sa ta ce,
"Sannu bro ya aiki?"

Banza yai mata. Kukan karya ta fashe dashi in kaji yadda ta fashe dashi kayi zaton na gaske ne. Nan da nan Yaya Buhari ya jata yana bata hakuri.

Dariya ta saki ta ce,
"Daman nace sai ka.kula ni."

"Kai amman yarinyar nan kinga lago na."
Ya fada yana daga ta daga jikin sa.

Daga haka suka hau hira. Har karfe goma suna falo sannan Aslam da Asma'u suka tafi gun cin abinci.

A can ma sun jima suna hira sannan suka ci abincin cikin so da kauna.
Aslam ya ce,
" *Husnah* ji nake ina ma anyi abin nan gidan mune mu sha soyayyar mu."

"Lokaci dai. Allah nuna mana."
"Ameen! Allah har na hango yadda zamuyi soyayya nake."

"Kai Yaa Aslam! Kana son soyayya."
"Dole naso ta *Husnah* dan wanda bai soyayya bai son dadin duniya nan ba soyayya tayi. Allah kuma ya bar mu da masoyan mu."

"Ameen!"
sannan suka mike suka koma daki. Sallama sukai wa su Dady kowa yayi dakin baccin sa.

Duk abinda ta saba tayi sai da ta gama su sannan ta kwanta.

A haka ma sai da suka kara yin waya kafin su kwanta.

Sun jima suna waya sannan sukai sallama bayan sunyi alwala.

Washe gari lahadi yini sukai tare. Ko gajiya da zama tare ko hira basa yi.

Sai dai ka jiyo murmushin su ko kaji dariyar su.

Mami dai bar musu falon tayi, haka suka yini a gidan.

Tare suka ci abinci suka yini sallah ce ke daga su.

Bayan sunyi sallahar la'asar, ne ya ce, Asma'u ta shirya ssu fita.

Wanka ta shiga tayi, ta fito ta saka Wata doguwar riga fara an mata ado da jan stones sai Jan mayafi da jan cover shoe. Wata jar jaka ta dauka.

Turare ta fesa ta fito tai dakin Mami.
Mami na zaune tana kallo Asma'u ta shiga
Kallon ta Mami tayi ta ce,
"Sai ina kuma?"

Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Zan raka Yaa Aslam ne."

"Toh! A dawo lafiya."
"Allah yasa."
Ta mike tayi waje.

A kasa ta samu Ya Aslam ya na sanye da farin wando da jar riga. Takalmin kafa sa ma ja ne.

Sai tashin kamshi yake yayi kyau. Yana ganin Asma'u yasaki murmushi ya ce,
"Wow My baby tayi kyau munyi anko."

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ta yi ta ce,
"Ka fini yi."

Wayar sa ya zaro ya ce,
"Zo mu dau selfie."

Gefen sa ta karasa ta tsaya matsowa yayi jikin ta, ya dauke su.

Ya musu fin kala biyar sannan ya dinga daukar ta.

"Yaa Aslam ya isa haka."
Ta fada saboda taga ba alamar tsayawa.

"To muje."
Ya fada yana kamo hannun ta. Fita sukai ya karasa gun Baba ya amso key mota suka shiga.

Shoprite suka shiga suka wuce cinema. kallo suka danyi sannan suka fito suka shiga ciki.

Sun shiga suka nufi gun kayan sakawa. Sosai yake jidar mata dogayen riguna masu kyau da tsada.

Haka ya nufi gun takalma da jakun kuna. Sosai ya kashe mata kudi sannan suka nufi gun alawa ya siya mata ice cream.

Bayan anyi total ne aka dibi kayan akayi wajen mota dashi.

Suna tafe suna hira taji ta bugi abu tayi baya zata fadi.

Da sauri ya rikota ta fada jikinsa. Kafin ta dago taji Yaa Aslam ya dago ta yana cewa,
"Ba dai matsala ko?"

Kai ta daga masa, kamshin turaren da taa shaka shi yasa tai saurin dagowa.

Ai kuwan shine, yana sanye da bakin wando da jar riga, yayi kyau sosai dashi.
Ba kowa bane face Sir sabir.
"Sorry!"
ta furta a kasan leben ta.

Yaa Aslam ne ya kama hannun ta suka bar wajen.

Sabir kowa kallo yabi su dashi. Yana me lumshe idon sa.

Suna fita ya ce,
"Sannu Baby na ko na dauke ki ne."
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah nagode zan iya tafiya ai."

A hankali suka karasa gefen Mota suka shiga suka bar wajen

Suna zuwa gida ana kiran sallah isha'i

Daki suka shige sukai sallah sannan suka sauko kasa.

A kasa suka samu har Dady ya dawo. Saannu da zuwa sukai masa sannu da zuwa
Abinci suka ci sannan suka koma falo ana hira.

Sai karfe tara suka tafi makwancin su.
Washe gari Monday. Tana gama abinda zatai ta shirya cikin wata pink kalar doguwar riga. Milk mayafi da takalmi ta saka. Sai pink kalar jaka.
Batai kwalliya ba fuskar ta daga hoda sai man lebe. Wajen Dady taje. Tare suka karya. Sannan ta fito.

Yaa Aslam ta gani a falon sama. Karasa wa tayi gun sa. Yana sanye da Bakin wando sai blue kalar riga mai dogon hannu.

Yayi kyau sai tashin kamshi yake.
"Yaya nah ina kwana?"

Ta gaishe da shi tana zama a hannun kujerar da yake.
"Lafiya lou. Ya Baby na ta tashi."

Murmushi tayi ta ce,
"Lafiya Alhamdulilah."
Sannan ta mike ta sauka kasa.

Basket din abincin sa ta dauko wanda ta zuba masa komai a fulas din sa.

"Mu tafi?"
Ya fada yana tambaya.

Kai ta gyada masa, dakin Mami suka yi sukai mata sallama sannan suka wuce zasu sauka.

Mantawa tai bata je gun Yaya Buhari ba. Wannan yasa tai ce
"Ina zuwa!"

Dakin yaa Buhari ta dosa, yana kwance ko alamar tashi bai yi ba.

Kara tai masa a kunne da sauri ya mike a firgice. baya ta dan ja ta ce,
"Ina kwana?"

Ta fada tana ja da baya a hankali. Ganin ya mike yasa tai saurin fita a dakin tana dariya.

Yaa Aslam dake tsaye yana jiran ta ya ga ta fito har ta sauka shima yabi bayan ta yana murmushi dan yasan tayi tsokanar da ta saba.

A bakin mota ya ganta a tsaya budewa yayi ta shiga ya rufe sannan ya shiga bangaren sa.

Tafiya suke a hankali suna hira abinsu. Har kofar department din su ya kai ta sannan ya kara mata kudi akan wanda Dady ya bata.

Sallama yai mata ya ce,
"Sai ya dawo daukar ta."

Sai da ta ga tafiyar sa sannan ta nufi ajin daukar darasin su.

Tana shiga taga Zainab zaune, karasawa tayi gun ta suka gaisa.

Batai minti biyar da zuwa ba sai ga Sir Sabir nan ya shigo.

Sanye yake da Milk din shadda ana mata aiki da milk din zare. Yayi kyau dashi.

Kasa tayi da kanta tuna haduwar su jiya. Lectures yake musu da yayi tambaya zai yi pointing din ta.

Tin tana jin kunya har ta sake tana bashi amsa. A haka suka gama lectures din.

Da zai fita ya duka zai dauki wayar sa, yai mata magana a hankali cewar ta same shi a office.

Wata faduwar gaba taji ta doke ta. A hankali ta daga kai ta kalle shi. Ita yake kalla saurin kawar da kan ta tayi tana wasa da yatsun ta.

Waje ya fita. Wata ajiyar zuciya ta sauke, ita bata san hadin ta da malamin nan ba amman dai tana ji yana burge ta ko dan saukin kansa.

Da kamar baza taje ba sai kuma ta ce da Zainab zataje ta dawo.

Fita tayi ta nufi office din nashi jiki a sanyaye.

Knocking tayi ya bata izinin shiga. Da sallama, ta shiga office din ta tsaya daga bakin kofa. Kallon sa tayi sau daya ta dauke idon ta.

Yana zaune a kan kujera gaban sa, farfesun kifi ne da Doya da kwai.

Kamshi ya cika office Din ci yake kamar baya son ci fuskar sa kuwa sai bata ta yake kamar mai cin magani.

Kallonsa ya maida kan ta ya kasa dauke ido daga kallon ta. Yana son yarinyar nan amman bai san ta inda zai fara ba.

Kawar da tunanin da yake yayi ya ce,
"Zo nan!"

Da kamar baza taje ba sai kuma ta dan matsa.

Kallon ta ya kara yi ya rasa mene dalilin kiran nata.

Kai ya dan shafa, ya ce,
"Zo kici!"

Kai ta girgiza ta ce,
"Na koshi."

Fuska ya bata, ya ce,
"Zamu bata inda zan na baki abu kina kinci. Maza zo kici."

Matsawa tayi ta zauna a kasa ba dan zata cin ba. Fulas din ya matsar mata dashi ya ce,
"Bismillah!"

Agogon hannun ta kalla sannan. Ta ce,
"Zan je nayi Assignment fa."

Ta yi maganar murya a shagwabe dan har ga Allah ta riga da ta saba da shagwaba in tana abu. bama in tana bukatar abu.
Sabir kuwa jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.


Post a Comment for "RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5"