Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MARWAN CHAPTER C KARSHE

MARWAN CHAPTER C KARSHE

- - Post a Comment

 MARWAN CHAPTER C KARSHE


Lokacin da Abba yaje sallah masallaci anan yaci karo da labarin rasuwar Abubakar, sosai mutuwar Abubakar ta shige shi bayan ya koma gida jiki asanyaye ya kuma sanar da Umma halin da ake ciki dukda dama taji kamar sanarwar mutuwa ce amma bataji wanda aka ambata ba, tashin hankali ne ƙarara afuskar Umma sosai taji mutuwar har jikinta, duk wannan budurin da akeyi Maryam bata da labari saboda ba tashi zatayi sallah ba tana period, sai da gari ya waye sosai sannan ta fito ta wanke fuska sannan suka gaisa da Umma, ganin yanayin Umma ne ya tabbatarwa da Maryam akwai abinda yake damunta, zama tayi daga gefen Umma tace, " Umma lafiya ko bakyajin daɗi ne? " da tausayi afuskarta ta kalli ƴartata tace, " a'a lafiya ƙalau ba abinda yake damuna " badan Maryam ta yarda ba ta tashi ta shiga ɗakin Abba dan ta gaishe shi, ganin baya ciki ta fito tana cewa Umma, " Umma yau da wuri Abba ya fita ne? " gaban Umma ne ya yanke ya faɗi tana san sanar da Maryam halin da ake ciki tana fargaba, kafin Umma tayi magana suka ji sallamar Abba ya shigo, da fara'a afusakar Maryam tace, " au ashema ba nisa kayi ba Abba na shiga gaida ka baka ciki, ganin yanayin da Maryam take ciko yasa Abba ya gane cewar Maryam batasan me yake faruwa ba, jiki ba ƙwari ya kalli Maryam yace, " zo Maryamu inasan ganinki " ba musu Maryam tabi bayansa, aƙasan kujera ta zauna tana sauraron abinda Mahaifin nata zai ce mata, kallan ƴartasa yayi yaji wani irin tausayinta ya kamashi amma sai ya daure yace, " Maryamu kedai musulma ce kuma duk musulmi na ƙwarai ya yarda da ƙaddara mai kyau da marar kyau, haka ne? " da sauri Maryam ta ɗago tana kallansa ahankali tace, " eh Abba" jinjina kai yayi ya cigaba da cewa, " Maryamu inasan ki ɗauki maganar da zan gaya miki amataayin ƙaddararki, Allah yayiwa Abubakar rasuwa yanxu haka daga jana'izarsa nake " gaban Maryam ne ya yanke ya faɗi jikinta har karkarwa yake saboda rikicewa cewa Abba tayi, " Abba wane Abubakar ne ya rasu " ganin halin da Maryam ta shiga yasa Abba ya ɗauke kansa gefe yace, " Abubakar da aka tsaida muku rana dashi jiya, dukkanmu bamu fi ƙarfin haka ba kuma kowa ita yake jira, Addu'a itace abinda zamu rakasu da ita muma intamu tazo Allah sa mu cika da imani " Maryam kafe Abba tayi idanu jin maganganunsa take kamar amafarki, tashi yayi ya fice ya bata guri, wani irin ɗaci taji azuciyarta tashi tayi ta fito tsakar gida inda tabar Umma, tambayar Umma take cikin tashin hankali, " Umma da gaske Abubakar mutuwa yayi ? " Umma tace mata, " Maryam lokacinsa ne yayi addu'armu yake buƙata " Maryam durƙushewa tayi agurin tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, Umma ce ta dinga yi mata nasiha tana bata baki amma duk da haka Maryam bata sarara da kukan ba, ɗaki ma ta koma ta faɗa kan katifarta tana wani irin kuka, kamar wacce aka tsunkula zumbur ta tashi ta ɗaga filo ta ɗauko wayarta da sauri ta danna kiran number Abubakar cikin sa'a kuwa taji tana shiga, bugu biyu taji muryar Abubakar ya ɗauka kamar yanda ya saba, " Baby na yau kece da farar safiya haka? " ciro wayar tayi daga kunnenta tana kallan screen ɗin wayarta da hanzari ta maida wayar kunnenta tace, " Abubakar dama baka mutu ba? " murmushi taji yayi sannan yace, " Mutuwa kuma baby na so kike na mutu na barki ne " da sauri Maryam tace, " a'a banaso, ina zuwa zan ƙara kiranka " jefar da wayar tayi da sauri ta fita tsakar gida tace wa Umma, " wallahi Umma Abubakar bai muti ba yanxu na kirashi awaya mukayi magana " sororo Umma tayi tana lallan Maryam tace, " Maryam kar fa mutuwar yaron nan tasa ki kasa ɗaukan ƙaddara, Yanxu nan Mahaifinki ya dawo daga jana'izarsa kice wai kin kira shi ya ɗauka " Abba ne ya fito daga ɗaki yacewa Maryam, " Maryamu kintaɓa ganin wanda ya mutu ya dawo ne? " girgiza kai Maryam tayi sannan tace, " amma  wallahi Abba da gaske nake maka na kirashi ya ɗauka kuma munyi magana " ganin Maryam ta haƙiƙance da yasa Abba yace, " ɗauko mun wayar mugani " ba musu ta ɗauko waya tana ƙara kiran number Abubakar amma wannan karan sai ji sukayi wayar akashe " kallanta Umma tayi tace, " ni nasan ruɗewa ce kawai kikayi Maryam amma wanda ya mutu ay ya mutu hat abada " Maryam shiru tayi dan bata da wata shaida da zata faɗa su Umma su yarda da ita.+


           Ɗaki ta koma ta rafka tagumi tana ganin abin kamar amafarki, bayan wasu awanni ita da Umma suka shirya suka tafi gidan makoki, Maryam har suka fita gani take idan suka je kamar zata ga Abubakar sai dao tana dosar ƙofar gidansu taci karo da mutane suna karɓar addua, suna shiga cikin gidam suka samu Mahaifiyarsa na zaune banda kuka babu abinda take yi, hakan ne ya sa Maryam ta kuma tabbatar wa da kanta lallai abinda su Abba suke gaya mata hakane, Maryam tayi kuka kamar ranta zai fita musamman idan ta tuna da zamantakewar ta da Abubakar saboda mutum ne mai sauƙin kai duk wani abu da take yi mata yake, ko kaɗan bayasan ɓacin ranta, haka aka dinga zuwa yiwa Maryam gaisuwa har gida, lokaci ɗaya Maryam ta fige ta rame ta lalace ko abincin kirki bata iya ci danma Umma na matsa mata kuma tana haɗa mata da nasihohi, ƙawayenta Nafisa da Khadija sun taya Maryam jimamin rashin Abubakar harma wasu daga cokom tsirarun ƴan department ɗinsu sai da suka je mata gaisuwa.


         Satin Abubakar uku da rasuwa su Maryam suka koma sch har zuwa wannan lokacin rasuwar Abubakar bata gama sakinta ba sai dai ba kamar farkon rasuwar ba, wannan karan Malam Safwan ne zai ɗauke su course ɗin litereture, tun kafin su fara lecture suka farajin raɗe-raɗin labarinsa da halayensa, abu na farko da suka fara ji bayasan latti indai ya riga ɗalibi shiga hall to bazaka shiga ba, sai Attendence yana Attendence sau uku a semester amma acikin ukun nan da ɗaya yake amfani indai sunanka bai fito aguri biyu ko uku ba to baka da attendence, sannan kuma Assignment idan ya bayar da Assignment individual yake taking baya bayar da group asaignment kuma kowa sai yayi presentation, sannan a lecture ta farko yake fadar dokokinsa muddin ka karya ɗaya kai kajawa kanka matsala, dokarsa ta ƙarshe da yake jadaddawa ɗalibai itace ta kashe waya ko sa waya a slient, idan yana lecture yaji ringtone aɓangaren maza to ko su fidda mai wayar ko kuma roll ɗin da wayar tayi ƙara gaba ɗaya su fice, haka nan ɓangaren mata ma, sai dai Mlm Safwan ya iya koyarwa sosai yawancin ɗalibai na gane karatunsa kuma duk wannan dokokin nashi bashi da ƙwaron mark, bai cika sakin fuska ba haka nan shi ba mai tsuke fuska bane sosai  ɗalibai na matuƙar tsoronsa, haka nan suna matuƙar sansa saboda zaiyi wuya ya ɗauki department ace 70% to 80% basuyi winning ba, shiyasa yake shan yabo yake kuma shan zagi musamman akan tsatstsauran ra'ayinsa  Ranar laraba ƙarfe takwas na safe suke da lecture Mlm Safwan, Maryam tunda taji labarin halin Mlm taci alwashin kiyaye dokokinsa saboda bata da san wulaƙanci ko dizgi musamman agaban jama'a, shiyasa ta shirya da wuri da nufin ta samu riga Mlm Safwan shiga aji, cikin ikon Allah kuwa ƙarfe takwas saura minti ashirin ta ƙarasa cikin hall ɗin, kusan sama da rabin ɗaliban sun hallara saboda kowa takatsantsan yake karyaje ya samu matsala, tana zama Nafisa na ƙarasowa kamar tare suke tafe, zama tayi tana sauke ajiyar zuciya Maryam ta kalleta tace, " au dama kina bayana ne amma baki mun magana ba " cikin mamaki Nafisa tace, " kema yanxu kika ƙaraso ne? ni banma ganki ba wlh kinsan hankali shike gani " dariya Maryam tayi tace, " wallahi na ji daɗin gashin malamin nan inama sauran haka suke da sa tsaro, duba fa Nafisa wai yau kece a Sch ƙarfe takwas saura, ashe dama kina sani kike makara abun naki harda iya shege " Nafisa na shirin Magana Khadija ta ƙaraso, matsa mata sukayi ta zauna kallan Nafisa tayi da mamaki tace, " Kutmelecy wai yau Nafisa kece kika rigani zuwa? lallai Mlm Safwan da zafinsa yake tafe " kallansu tayi tana watsa musu hararar wasa tace, " Shi ɗin wa da har zai sani buga sammako kawai dai ra'ayi na ne " su Bilkisu dake bayan bencinsu dasu Maryam lokaci guda suka kwashe da dariya, Badiyya ce tace, " kina birgeni hajiyata inasan irin wannan cika bakin naki, gaki kinfi uban kowa tsoro kamar farar kura " wannan karanma dariyar sukayi Nafisa tace, " wallahi kamar kinsani dan yau Mama har mamaki na ta dinga yi  ina shiri, ke har tamabayata tayi nace mata wallahi wani mugun Malami ne muka haɗu dashi a Level two ɗin nan, buɗar bakinta sai cewa tai Allah ya ƙara tafi san irinsu masu takura ɗalibai wai sai mun fi maida hankali " haka suka yi ta hira ajunansu har lokacin da shigowar Mlm Safwan ya shigo ajin.+


            Kamar yanda yake ɗabi'arsa ce sanya manya kaya yau ɗin ma sanye yake da wani dakakken yadi ruwan toka fuskarsa sanye take da farin glass shigar ba ƙaramin kyau tayi masa ba, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo sai dai fuskarsa ba walwala, gaba ɗaya ajin tsit yayi kamar ruwa ya cinye su ba abinda kake ji sai ƙarar fanka, sai da ya ƙare musu kallo sannan ya gabatar musu da kansa da waɗannan dokokin nasa da suka isan kunnuwan su Maryam tun kafin zuwansa, cikin girmamawa sukayi tsit suna sauraronsa har ya kammallah, ƙarin abinda suka ji daga cikin tsarinsa yace musu, amatsayinka na ɗalibi idan uzuri ya kama ka yana lecture zaka iya fita ko da baka tambayeshi ba, sai dai duk lokacin da ka fita ka tabbatar da ka kawo kafin ya karɓi attendence, tunda inya gama lecture yana karɓar attendence hand to hand, muddin ya fara kaɓa baka cikin masu attendence, sosai suka nutsu suka fahimce shi yana gamawa ya tambayi waye Moniter ba ɓata lokaci ya tashi, ce mishi yayi yana buƙatar list ɗinsu gaba ɗaya cikin girmamawa Moniter ya amsa masa, lecture yake musu cikin ƙwarewa kuma da alama suna fahimta dai-dai gwargwado, awarsa biyu yana lectures daga ƙarshe da zai tafi ya fara karbar attendence, yana gama karɓa ya wuce office ɗinsa.

        Tun bayan fitarsa ɗalibai ke kace nace suke akansa wasu daga cikin ƴan matan ba ƙaramin birgesu yayi ba, wasu kuma haushi ya basu Maryam na daga cikin masu jin haushinsa, suna hirarsa Maryam ta yamutsa fuska tace, " wallahi Malamin nan ya cika iyayi gashi yaro dashi sai ƙafafa kuji wasu dokokin san rai? Waɗannan dokokin nasa ko a karatun muhammadiyya ba'a sa su, wai ni banasan kaza bana san kaza idan kuka karya doka ta ku kuka sani zaku gani a kan takardunku " duk waɗannan maganganun da Maryam keyi tana yinsu ne ciki kwaikwaiyon muryarsa, tana gamawa gaba ɗaya suka kwashe da dariya Khadija tace, " wallahi kuma sak kamar shi yake magana yasin kin iya kwaikwayar muryarsa " Habiba dake gefe tace, " wallahi ni kuma ba ƙaramin birgeni yayi ba ga kyau ga gayu inasan mutum ɗan gaye kamar wannan ji nake kamar ya tafi da zuciya ta " Fatima ce tai sauri tace, " tabɗi ashe kuwa zaki bushe dan wallahi ance ɗan wulaƙanci ne, wai wata ƴar level 4 da taje office ɗinsa, ance tana mutuwar sansa wallahi ji nai ance korar kare yayi mata " taɓe baki Maryam tayi tace, " ni wallah banga kyawun da yake dashi ba har ina mace da zanje ince insansa, haba aji down wallahi da na bada mata " Nafisa hararar wasa ta watsa mata tace, " a'a Maryam ingaskiya tazo afaɗa gaskiya Mlm Safwan ba mummuna bane, na dai yarda da maganarki da kikace bazaki je kice kina sanshi ba nima ina bayanki " gaba ɗaya suka amsa da, " atoh gaya mata dai " daga nan capteria suka wuce kowacce ta sayi abinda zata ci kafin sha biyu su kuma shiga wata lecture.


          *BAYAN SATI HUƊU*

                Su Maryam sun fito daga lecture kimanin ƙarfe goma na safe, suna bakin wata bishiya suna hutawa sai ga wani matashin Saurayi ya ƙaraso gurinsu akan lifan ɗinsa, sallama yayi musu cikin mutumci suma suka amsa masa sannan ya fara musu magana, " dan Allah Maryam idan bazaki damu ba inasan magana da ke " gaban Maryam ne yanke ya faɗi atake ta tsuke fuska ta ce, " gaskiya inada abinyi amma kayi hakuri " murmushi yayi yace mata, " dan girman ALLAH ki tsaya ki saurare ni " tamke fuskarta ta ƙarayi tace, " karma ka haɗani da Allah nace maka uzuri nake yi " Khadija ce tace, " Maryam girman ALLAH yafi komai ki saurare shi kiji meke tafe dashi " tana gama faɗa tace kalli Nafisa tace, " mu koma bakin hall ɗince kafin ta gama, tashi sukayi suka barta Maryam ta cika tai fam, cikin nutsuwa ya fara mata magana, " Nasan zaki mamakin yanda akayi nasan sunanaki, nidai sunana Nazir Adam kuma ina zaune da iyayena a unguwar ɗan agundi, ina sana'ar gyaran mota sannan yanzu haka ina level 4, na yaba da hankalinki da nutsuwarki shiyasa na ce bari na tunkare ki, Maryam tsakani da Allah nake sanki kuma banzo da yaudara ba ni ba irin samarin makaranta bane masu shagaltar da ƴanmata, ina fatan zaki fahimci kyakykywar manufata " Maryam na gama saureren sa tace, " naji kuma na nagode da wannan ƙauna da ka nuna mun amma gaskiya ayanxu babu soyayya agaba na " murmushi ya ƙarayi yace, " bazan tilasta ki ba ko intakuraki amma kiyi tunani zan baki nan da wasu kwanaki " Maryam na gama saurarensa tace, "  to shikenan nagode " cikin jindaɗi yace, " nabarki lafiya " ya ƙarasa maganar yana tada mashin ɗinsa, itama ta ɗauki jakarta ta ƙarasa gurinsu KhadijaNafisa da take gimtse dariyarta tun kafin Maryam ta ƙarasa ta fara ƴar dariya ƙasa-ƙasa, hararar wasa Maryam ta watsa mata tace, " Munafuka dariyar me kike mun haka? " tun kan Nafisa ta fara magana Khadija ta karɓe, " Maryam wallahi wulaƙanci ba kyau kuma wallahi bakiga yanda kuka dace da gayen cen ba" taɓe baki Maryam tayi tace, " Allah ko? to Allah bada ladan sheda " ta ƙarasa maganar tana gasawa musu harara, duk yanda suka so hirar Nazir fir Maryam taƙi bada fuska dan dole haka suka bar hirar suka shiga wata, lokacin sallah nayi masallaci suka wuce sukayi sallah daga nan suka koma lecture ƙarfe ɗaya.


Satin Nazir guda da tafiya ya ƙara komawa gurin Maryam sai dai yau ɗinma daya koma bai wani samu fuska sosai ba, nasara ɗaya ya samu da ya karɓi number ta, flashing ɗin number sa yayi a cikin wayarta yace tayi saving number sa, Maryam ko ta kan number bata bi ba bare tai saving, Nazir sosai yake ƙaunar Maryam kuma tsakani da Allah shiyasa duk shariyar da take masa ko kaɗan baya damuwa bare yaji zai iya rabuwa da ita, sannu ahankali yake kiranta wani lokacin ta ɗauka wani lokacin kuma har ta katse bazata ɗauka ba, ahaka har Nazir ya shawo kanta ta fara saurensa awaya tafi-tafi har ya kawo mata maganar yana san ya fara zuwa gidansu hira sam Maryam bata so haka ba, sai dai wata ɗabi'a ta Nazir ko kaɗan baya tsaida Maryam a sch da sunan suyi zance ko ganinta yayi sai dai yayi musu sallama ya wuce, shiyasa ma ko kaɗan su Nafisa ba su zaci Maryam da Nazir suna tare ba, da ƙyar da suɗin goshi Maryam ta kwatantawa Nazir gidansu aykuwa murna gurun Nazir ba'a magana, wata ranar juma'a ya shirya da Magriba yaje hira gurin Maryam dama kuma tuni ta sanarwa da Umma ita kuma ta sanarwa da Abba, ba laifi Maryam ta saki jikinta da Nazir har kuma ta farajin ƙaunarsa azuciya hira suka sha daga ƙarshe yayi mata sallama ya tafi.

Washegari da Maryam take gayawa su Khadija zuwan Nazir haka suka dinga tsokanarta suna mata tsiya, ita dai jinsu kawai take saboda idan ta tanka musu sun samu nayi kenan.Kamar kullin yau ma da suke da lecture Mlm safwan tun bayan sallar asuba Maryam bata koma ba aƙoƙarinta na ta ga ta ƙauracewa makara musamman yau da ya sanar musu zai musu test tunda sunxo ƙarshen semester, Maryam ko kyakykyawan breakfast bata tsaya tayi ba ta fice daga gidan, lokacin da adaidaita sahun su yazo kano line anan ya samu matsala taya tayi faci, adan dole suka sauka suka fara neman wani abun hawan amma abin takaici kowanne yaxo acike sai da ƙyar suka samu wata bus taxo saura gurin mutum ɗaya, aƙuƙuce haka su Maryam suka shiga ita sai maleji ta zauna, lokacin da ta ƙarasa Mlm Safwan ya shiga kenan dan saboda ma amota yake da sai Maryam ta rigashi shiga tunda ta ga wucewarsa, Maryam ilahirin jikinta rawa yake jiki asanyaye ta biyo bayansa, Mlm Safwan da tun shigowarsa yaji alamun tahowar mutum amma sai ya basar ya tsaya agurun tsaiwar Malamai, har taje zata gifta shi ya buga mata tsawa cikin tsuke fuska yana tambayarta, " where are u going? " saboda tsabar razana atake jakar Maryam ta faɗo daga kafaɗa cikin firgici ta marairaice tana faɗin, " Sir am sorry pls " tun daga ƙasa Mlm Safwan ya fara ƙare mata kallo yana yatsina fuska sannan ya kuma tanke fuska da alama yau ransa aɓace yake yace mata, " sorry for what reason? " shiru Maryam tayi wani irin gumi ne ya rufeta gabanta na dukan uku-uku musamman da idanun kowa yake kanta, azafafe ya kuma buga mata tsawa, " If u don't have something to say park ur self outside " tsugunnawa Maryam tayi zata fara roƙonsa, " Sir pls......... " ɗauke kansa gefe yayi yace, " I said work out or else....." bai ƙarasa maganar ba ya fara tattara takaddunsa aykuwa ganin haka yasa ɗalibai suka fara ihu akan sai Maryam ta fita, hayaniyar da taji tayi yawa yasa Maryam ɗagowa da niyyar fita, azabure ta zaro idanunta cikin tashin hankali take faɗin, " a'a Marwan ka bari karka cutar dashi Mlm Safwan bashi da laifi ni ce na taka dokarsa " ba Mlm Safwan ba hatta sauran students ɗin ido suka zurawa gurin da Maryam ta kallah take surutai, Marwan dake huci kallan Maryam yayi yace, " babu wanda ya isa ya hanani abinda nayi niyya tunda yasa ki zubda hawaye ayau basai gobe ba zai bar duniyar nan " Marwan na gama faɗin haka ya kum tunkaro gurin da Mlm Safwan ke tsaye " runtse ido sosai Maryam tayi tana faɗin, " a'a Marwan a'a....... " Katse ta Mlm Safwan yayi cikin tsawa yace, " lallai naki salon daban yake, kafin ke na koyar da dubunki amma bantaɓa cin karo da wacce ta iya wasan kwaikwaiyo irin naki ba, wai ko kinyi zaman zoo road ne? kina tunanin waɗanan surutan banza da wofin naki zasu sa na sauya ra'ayina ne ni zaki yaudara? lallai yarinya da sauranki ki kwashe mun tsumokaran ƙafafunki ki fece mun daga aji " yana rufe baki aji aka fara kuskus masu yiwa Maryam dariya nayi wasu ganin iya shege yasa Maryam tayi haka nayi masu tausayinta nayi wasu ma har cewa tai ko aljanu ta tayar, aɓangare guda suna Mamakin yanda suka ji Mlm Safwan na ƙwararo hausa kamar bai taɓa sanin wata kalma daga kalmomin turanci ba, Maryam da har lokacin Hankalinta na kan Marwan atsoronta kar yaje yayiwa Mlm Safwan wani abun gani tayi ya tunkari Mlm Safwan da wani mulmulallan ƙarfe, ganin haka yasa Maryam ta ƙwallah uwar ƙara ta tafi gurin Mlm Safwan da niyyar komai zaiyi gwara ya aikata shi akanta, daga nan bata kuma sanin abunda ya faru ba sai farkawa tayi ta ganta akan katifarta Umma na mata sannu, waigawar da zatayi gefe sai Khadija da Nafisa ta gani suna mata sannu kowanne jikinsa a sanyaye, tunowa tayi da Abinda ya faru tsakaninta da Mlm Safwan azabure ta cewa su Khadija, " Ina Mlm Safwan Allah sa bai kashe shi ba, dan Allah yana ina? " Umma da tausayin ƴartata ya kamata goge ƙwallah tayi tana jin ba daɗi azuciyarta.Gaba ɗaya hankalin Maryam ya tashi fargabarta ɗaya kar Marwan ya kashe Mlm Safwan, ganin halin firgicin da Maryam ta shiga yasa Khadija ta kalleta tace, " dan Allah Maryam ki kwantar da hankalinki babu fa abinda ya samu Mlm Safwan " idanu Maryam ta zurawa Khadija kamar mai nazari sannan tace, " karki yaudareni Khadija nasan waye Marwan wallahi xaiyi wuya ya ƙyale Mlm Safwan tunda ya ƙuduri muguwar manufa akansa " Nafisa ce tace, " wallahi da gaske muke ba abinda ya faru da Mlm Safwan hasalima shi ne ya kawo mu amotarsa har nan gidan " zaro idanu Maryam ta ƙarayi cikin Mamaki tace, " Mlm Safwan ne ya kawo mu har cikin gidan nan? Wannan mutumin da bashida mutumci " gyaɗa mata kai sukayi suna ƙara jaddada mata, mamaki ne ya kuma kamata ƙwarai afili ta furta, " Alhamdulillah Allah ƙara nisantamu daga sharrin Marwan " Umma da jikinta ya gama sanyi ahankali ta furta, "Aameen " banda su Khadija da har lokacin kansu a kulle yake suna tunanin wanene wannan Marwan ɗin da yake san cutar da Mlm Safwan, ahanzarce Maryam ta ɗago da kai tana tambayarsu, " Yauwa ya ya test ɗin kuwa Mlm yayi muku? " khadija janyo jakarta tayi sannan tace, " lokacin da kika faɗi gaba ɗaya aji mun ɗauka gwada Mlm Safwan kike yi har shi ɗinma sai da muka ga kin jima ahaka sannan Mlm Safwan ya tambayi sunanki aka gaya masa to sai ya dinga kiranki amma shiru, da yaga haka sai ya tambayi ƙawayenta muka fito shi ne fa yace anemo masa ruwa, bayan ankawo sai ya yayyafa miki ruwa duk da haka baki motsa ba sai da yayi addu'o'i ya jima yana tofi ruwan sannan ya yayyafa miki yana yayyafa miki kika farko kina surutai kina cewa kar Marwan ya kashe shi, da yaga haka sai ya kuma wani tofin ya yayyafa miki kawai bayan wani lokaci sai kika kuma faɗuwa sai yace mu ɗaukeki mu saki a motarsa, kafin mu dawo sai yace ya fasa yin test zai bada Assignment individual kuma presentation za'ayi, muna shigowa na copy Assignment ɗin shi ne yace mu rakoshi gidanku, lokacin da mukaxo Abba ya fito kenan ya ganmu to sai ya tsaya suka tattauna da Mlm Safwan mukuma muka shigo gida." ajiyar zuciya Maryam ta sauke sannan tace, " Allah sarki amma naji daɗi kuma insha Allah gobe naje makaranta zanje har office ɗinsa na yi masa godiya, ashe dai ba laifi yana da mutumci " Nafisa murmushi tayi tace, " wallahi bari kinga har dubu biyu ya bamu wai muyi kuɗin mota, taɓe baki Maryam tayi tace, " harda wani kuɗi ya baku cemasa akayi gidanmu basu da kuɗin da zasu baku na mota ne? " Umma ce tayi karaf tace, " ke Maryam me nakeji kina faɗa ne mutumin da yayi miki wannan halaccin har shi zaki tsaya kina ganin bekensa " shiru Maryam tayi bata kuma cewa komai ba.+


           Tashi Umma tayi ta fice daga ɗakin ta shiga kitchen ahankali Maryam ta gyara zamanta tana karɓar papper da Khadija ta fito da ita wacce ta copy assignment ɗin ajiki, sai da ta gama karantawa tsaf sannan tace, " Mlm Safwan ya cika ɗorawa ɗalibai aiki yanxu muje muyi assingnment mu kai typing sannan muyi presentation, duk wannan iyayin nasa ayaushe zamuyi naga semester ta ƙare, kuma naji ance har anfito da timetable amma draft yana nufin akansa zami dinga zuwa Sch kullin? " su Nafisa ma taɓe baki sukayi atare suna jan guntun tsaki, Nafisa tace, " wallahi fa ganemun hanya kina gani yanxu daga shi sai Mlm Asiya ya rage muyi covering, ita ma kuma gobe inajin zamu gama da ita " Khadija ta karɓe zancen da cewar, " Ni dama yayi according to numbers idan ranar yinka yazo sai kaje amma ace kullin kana hanya akan course ɗaya ay a tausayawa iyayenmu. "  guntun tsaki Maryam tayi tace, " yooo shi yasan matsalar kuɗi ne mudai da mike ƴaƴan Mlm shehu mu mukasan matsalar kuɗi, Allah dai ya ƙarawa iyayenmu buɗi kawai " gaba ɗaya suka amsa da, " Aameen " kamar wacce aka tsunkula Nafisa ta kalli Maryam tace, " kuttt wai ma da muke ta wannan kumfar bakin muna yiwa Mlm Safwan mita ga wacce xamu yiwa nan " ta ƙarasa maganar tana hararar Maryam,  ita ɗinma hararar ta watsa mata tace, " mitar me zaku min nina baku ne? " Khadija tace, " Wallahi zancenki haƙƙun ita ta janyo yayi mana haka yasin  da tuni mum daɗe da wuce gurin " kallansu Maryam tayi tace, " a'a wallahi yayi dai niyya dama, kunsan dai waye Mlm Safwan ni ban isa na hanashi abinda yayi niyya ba" Khadija tace, " to ya muka iya Allah sa hakan ne yafi alheri " gaba ɗaya suka amsa da, " Aameen " daga nan hira suka shiga su Khadija basu suka bar gidansu Maryam ba sai bayan azahar da suka ci abinci sukayi sallah sannan suka tafi.


STORY CONTINUES BELOW

          Da daddare bayan Sallar Isha'i bayan Abba ya dawo suna zaune suna hira gaba ɗaya har yaran gwanin sha'awa, Abba kallan Maryam yayi yace, " Maryamu ɗazu Malamin makarantarku ta sanar dani komai game da abinda ya shiga tsakaninki da shi, daga yaushe kika fara ganin Marwan ido biyu? " cikin nutsuwa Maryam tace, " ɗaxu ne kawai kuma daga lokacin ban kuma ganinsa ba " jinjina kai Abba yayi yace, " Allah ya sawaƙe Ashe har yanxu da sauran rina akaba, abinda nake so dake Maryamu ki cigaba da azkar da addu'a haka nan kwanciya bacci idan zaki kwanta ki tabbar kin tofe jikinki gaba ɗaya, Allah yayi mana maganin wannan masifar dole mu kuma tashi tsaye " Umma jiki ba ƙwari tace, " Ameen amma lamarin da bantsoro ana murna baƙo ya tafi ashe yana bayan gari " Abba yace, " eh insha Allah, Allah zai kawo mana ƙarshen wannan annobar, kuma hakan na daga cikin jarrabawar mu Allah ya bamu ikon cinye ta " Umma ta amsa masa.


            *Washegari*

               Su Maryam basu shiga Sch da wuri ba saboda basu da lecture sai sha biyu, wajen ƙarfe goma na safe suka ƙarasa cikin Sch abakin department ɗinsu ta samu Khadija azaune, Bayan sun gaisa Maryam ta ce, " wai uwar makararru bata ƙaraso bane " Khajida ta ce, " haba kema kamar bakisan Nafisa ba wallahi keda ganinta kila sai sha biyu saura, sai ta kusa makara ta dinga zabga sauri kamar za ta tashi sama " dariya Maryam tayi ta ce, " wallahi fa, ke tashi ki rakani office ɗin Mlm Safwan " Khadija ta ce, " au na manta fa kince zaki je yimasa godiya, amma fa wallahi bazan shiga ba abakin ƙofa zan tsaya ki shiga ki fito dan wallahi tsoron shiga nake " taɓe baki Maryam tayi tace, " idanma bazaki rakani bakin office ɗin nasa ba kiyi zamanki nina rasa irin tsoron da kukewa mutumin nan, ni inkinga tsorona dashi akan karya dokarsa ne saboda nasan ni ce nai ba dai-dai ba, amma mutum  baida wuta da aljanna tsoronsa name zanji, banda ma hallacin da yamum da ba abinda zai kaini office ɗinsa. " dariya Khadija tayi tace, " ayke ƙawata baki da tsoro ji fa rannan da zamu office ɗin Malama Amina duk jarabarta muna zuwa naga kin danna kai " murmushi Maryam tayi ta ce, " to tsoronme zanji, ke zo muje kar ya fita kinsan shi baya zama kamar ƴar yawo " dariya Khadija tayi sosai sannan suka wuce.

          Lokacin da suka je bakin office ɗinsa maza biyu suka gani abakin office ɗin a tsaye dukkansu jimamin shiga suke yi, sallama Maryam tayi musu sannan tace, " Layi ake ne kafin shiga? " ɗaya daga cikinsu yace, " a'a nace ya fara shiga ne yace sai dai ni na fara shiga " kallan kofar tayi tace, " akwai wani aciki ne? " eh wasu sun shiga amma...." motsin ƙofa ne ya katse su da sauri Maryam ta kalli gurun mace da namjij ne taga sun fito, wanda ya bawa Maryam amsa ne yace, " kaga sun fito zo mu shiga "  ja da baya wanda akayiwa maganar yayi yace, " Allah saidai ka fara shiga " ganin zasu ɓata mata lokaci tace, " wai shiga office ɗinne kuke ta daddagewa sai kace gun mala'ika zaku shiga, mtttsswww mutum ne fa kamar ku kuke da taraddadin shiga gurinsa, Khadija bari na shiga na fito " duk abinda ke faruwa Mlm Safwan na jinsu har yana murmushi azuciyarsa yake faɗin, " lallai wanna kowacce yarinya ce tana da ƙarfin hali kuma bata da tsoro salonta ya birgeni " saboda yasan mafi yawan ɗalibai idan suka je bakin office ɗinsa sun dinga, ki shiga ko ka shiga kafin su shiga gurinsa " yana cikin wannan tunanin yaji sallamar ta ta shigo, shigowarta yayi dai-dai da shigowar kiran wayarsa.


           Kujera taja ta zaune tana ƙarewa office ɗin kallo, waya taji ya fara, " Hello My Rigima kin manta dani ko?  " amsa aka bashi daga cen ɓangaren sannan yace, " hmmmm ni ban yarda kina missing ɗina ba bayan ma baki damu dani ba " amsa ta kuma da, " a'a wallahi Ya Safwan na damu da kai har su mommy amma ay na kusa dawowa " murmushi yayi yace, " to Allah ya dawo dake lafiya " ta amsa da, " Ameen, Ya Safwan kana Sch ne me  kakeyi a office ɗin nasan ƙila student na nan kowa yazo da complain ɗinsa " murmushi ya ƙarayi yace, " wallahi kamar kin sani My rigima ina office yanxu haka wata yarinya ce ta sani gaba sai mungama waya zanji tata matsalar " afusace Maryam ta kalli gurinsa jin abinda yace, dama tun da ya fara wayar haushi ya kamata waya yake sai wani kashe murya yake, kamar ba kowa agabansa uwar harara ta watsa masa ta ɗauke kanta gefe tana jin wani zafi azuciyarta, shi kuwa ko ajikinsa cigaba yayi da wayarsa cikin kwanciyar hankali, sun kusa minti biyar suna waya sai ayau Maryam taɓa ganin dariyarsa yana waya, da zasuyi sallama sai ji tayi yace, " I so much miss u my rigimi bari inji da matsalar gaba na i will call u later " haushi ne ya kuma tirniƙe Maryam cikin suɓutar baki tace, " ni ce ma matsalar " yaji sarai abinda tace tsuke fuska yayi yace, " me ye damuwarki " shiru Maryam tayi kamar bataji mai yace ba, shima ganin  tayi haka yasa ya ɗauke kansa ya cigaba da cike wasu takaddu dake gabansa, Maryam atunaninta zai kuma tambayarta ganin ya share ta yasa tace, " dama zuwa nayi nai maka godiya " bai kalli inda take ba yace, " me nai miki da kike gode mun " haushi ne ya kuma kamata aƙufule tace, " da ka kaini gidanmu nida ƙawaye na " sai lokacin ya dago kai ya ƙare mata kallo yana yatsina fuska sannan yace, " oh kece kika so tada bori jiya ko? oh sorry ba bori ba aljanu  " idanun Maryam ne suka ciko da ƙwallah saboda maganar ta mata ciwo, muryarta na rawa tace, " eh ni ce amma ay Allah ne ya ɗora mun " ta ƙarasa faɗa hawaye na zubo mata, kafeta ya kuma yi da kallo sannan yaja guntun tsaki yace, " da nace wani ne ya ɗora miki? look idan iya abinda ya kawo ki wajen nan kenan get out, naga kinfara kuka kar ki tayar mun da bishiyar bulikiya a office, dan yau bani da enough time idan kika kuma faɗuwa security zansa ya fitar mun dake, cen keda ƙawayenki ku ƙarata " hawaye ne keta bin fuskar Maryam ta rasa abin faɗa sai binsa da idanu da tayi, shima kallanta yayi yace, " ko yanzu ma tsohon mijin naki kika gani, to bari kiji ba Marwan ba ko uban Marwan ne nafi ƙarfinsa, park ur Darty legs out " ya ƙarasa magana yana nuna mata ƙofa da hannu, tsawar da ya buga mata har sai da su Khadija dake waje suka jiyo, jiki ba ƙwari haka Maryam ta tashi ta fice tana hawayGanin yanayin da Maryam ta fito yasa Khadija saurin ƙarasawa gurinta, samarin nan dake tsaye bakin ƙofa suna ganin Maryam suka kwashe da dariya, ɗaya daga cikinsu ne ya ce, " Kaga abinda nake gudu ko? Itama duk cika bakin kaga a inda ta ƙare wallahi dama ance baya ragawa mata har gwara maza ma " dariya ɗayan yayi yace, " wallahi kuwa nan ta cika mu da kuri sai gashi ya watsota waje harda hawaye, kai mutumina mu wuce nidai gobe na dawo " yana gama faɗa suka raɓa ta gefen Maryam dake tsaye tana hawaye, har sunyi gaba ɗayan ya juyo yace, " ƴanmata dama kin rufawa kanki asiri kin bar zubda hawayenki dan shi baima san kinayi ba, yana gama maganar suka ƙarasa ficewa daga gurin, Khadija duk ji tayi ba daɗi cikin sanyin jiki tace, " Maryam me Mlm ɗin yayi miki ko wani lafin kika yi masa? " duk lokaci ɗaya take jero mata waɗannan tambayoyin, cikin ƙunan rai Maryam ta ce, " ba abinda nai masa Khadija tsabar wulaƙanci ne da cin zarafin ɗan adam, Khadija bani na ɗorawa kaina ba Allah ne ya jarabceni dashi duk duniya bayan iyayena babu wanda yakaini jin ciwon lalurar dake tattare ni, Khadija Mlm Safwan baisan ƙaddara ba yana mun izgili da ciwon da ni kaina wayar gani nayi na ganni dashi amma babu komai ciwo bai wuce kan kowa ba Allan daya ɗoramun shi ne zai yaye mun shi, da nasan wulaƙancin da zai mun kenan da ba abinda zai kaini office ɗinsa, daga yau daga yanxu bana buƙatar taimakon kowa sai na Allah dana iyaye, Idan mutuwa nayi a makarantar nan bana buƙatar wani ya ɗauki gawa ta ya kaita gidanmu, duk wanda ya taimakan banyafe ba duniya da lahira koda kuwa kune....." da sauri Khadija tasa hannu ta rufe mata bakin tana faɗin, " Lafiya Maryam maiyasa kike haka kiyi shiru karfa Mlm Safwan ya ji ki " a harzuƙe Maryam ta fisge hannunta tace, " yaji mana Ubana ne ko yana da wuta da aljannah ne, Khadija tunda nazo duniya babu wanda ya taɓa gayamun maganar da tamun ciwo irin wannan, na tsani wulaƙanci da me wulaƙanta mutane " Khadija dake mamakin yanayin da Maryam ke ciki tace, " to kiyi hakuri muje dan Allah " gaba ɗaya jikin Maryam rawa yake saboda ɓacin rai, haka ta wuce suka tafi zuciyarta na suya, duk maganganun da Maryam ta faɗa akan kunnen Mlm Safwan sai alokacin yaji sam abinda yayi mata bai kyauta ba, nan take ya ji tausayinta ya kamashi musamman yanda yaji tana maganar tana shashsheƙar kuka, sai kuma labarin da Mahaifin Maryam ya bashi, tausayinsu gaba ɗaya ne ya kamashi yana jin ba daɗi azuciyarsa.+


       Wunin ranar gaba ɗaya haka ta ƙarasa shi cikin ƙunci da ɓacin rai, ta kuma ƙudiri niyya bazata kuma dawowa sch ba sai taji labarin timetable ɗin exams ta fito, haka ta koma gida jiki a sanyaye babu wata walwala, bayan kwana uku da faruwar haka Khadija ce ta kirata awaya, bayan sun gaisa Khadija take ce mata, " Maryam Balaraba ta kirani tace jiya da bamuje ba moniter yace Mlm Safwan yace wani satin xa'a yi submitting Assignment kuma yace yanasan ya gama da rabin class aranar, washe gari ya gama da rabi shikenan mun gama " taɓe baki Maryam tayi tace, " Nagodd Khadija amma bazan je ba " Khadija sororo tayi sannan tace, " Maryam mai yasa kike da kafiya ne? Wallahi da kije da karkije shi duk ɗaya ne agurinsa ke zaki jawa kanki matsala " murmushin takaici Maryam tayi sannan tace, " nasan da matsalar Khadija bawai duk gudun carry over bane? Khadija dan na samu carry over sai me? ba kaina farau ba ba kuma kaina ƙarau ba " Khadija ta ce, " amma ay ba hk aka so ba ko? " to saime Khadija ke Umma na kirana ina zuwa " Maryam ta ƙarasa maganar tana katse wayar " tayi haka ne dan gudun kar suyi ta ja'inja tsakaninta da Khadija.

        Da daddare bayan Abba ya dawo yake sanarwa da Umma zasu je gurin wani islamic chemist dake unguwar gyaɗi-gyaɗi mai suna ATTANZEEL ISLAMIC CHEMIST, cikin jin daɗi da farin ciki Umma da Maryam suka amsa masa.

       Washegari bayan sunje attanzeel, duk abubuwan da akewa mai jinnu haka Mlm Sulaiman yayiwa Maryam amma sam babu wani alamu data nuna, office ɗinsa ya zauna dasu Abba ya fara musu bayani, "  Alhamdullah duk wani abu mun aywatar dashi saidai babu wani yanayi ko alamun jinnu atattare da ita, sai dai abinda muka fuskanta shi wannan makirin aljani baya jikinta saboda riƙo da ibadarta ya kasa koda tunkararta, sai dai babbar matsalar irin waɗannan jinnun sukan hana yariya mijin aure, wasu zasu hana yarinya samari kwata-kwata bare miji ya fito wata ma sai ansa rana abu ya matso daga ɓangaren miji yace ya fasa, wata kuma sai anyi auren ma sai masifu suyita tashi tsakaninta da mijin har ta kaiga saki, ko mijin yaji haka nan yanajin haushin matarsa ko kuma matar taji duk duniya ba wanda ta tsana sama dashi, mugaye masu mugunta ma har kisa sunayi su dinga kashewa yarinya samari ko mazaje, mafita anan ita cs idan tana da saurayi dole agaya masa matsalarta kuma shima dole ya kasance mai azkar ne safe da rana, sannan dole a nemi wannan aljanin dake tare da ita a ƙone shi ƙurmus inba haka ya dinga kawo mata matsala arayuwarta. " ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace, " munji duk bayanan ka Mlm insha Allah kuma zamu bi duk shawarwarinka " Mlm Sulaiman yace, " Allah yayi mana muwafaƙa Aameen " tashi sukayi suka fito da daga gurin shi kuma Abba ya tsaya suka ƙarasa tattaunawa akan lamarin sannan ya fito kai tsaye suka wuce gida dukkansu jiki ba ƙwari.


         *RANA BATA ƘARYA*

      Mlm Safwan  ne tsaye gaban ɗalibai hall ɗin tsit kakeji kowa ya shiga nutsuwarsa banda ƙarar fanka ba abinda yake tashi, da ɓangaren maza ya fara idan namiji ɗaya ya fito yayi presentation sai mace ɗaya ta fito itama tayi, sannu a hankali suka dinga fitowa suna bada assignments ɗinsu har yayi rabin students kamar yanda ya faɗa ƙarfe sha ɗaya suka fito kowa ya shiga sabgar gabansa, su Khadija ne suke dube-dube da alama Maryam suke nema ganin zasu ɓata lokaci yasa Nafisa ta ɗauki waya ta kira ta, lokacin Maryam na kwance aɗaki da alama bacci ma take kiran wayarta ne ya tashe ta, hannu ta miƙa ta ɗauka da muryar bacci ta ɗauka take faɗin, " Yah iyalan Mlm Safwan kun fito ne? " ɗaga wayar Nafisa tayi ta kalli number da ta kira da tambayar da aka mata, cikin gatse ta ce mata, " a'a bamu fito ba, dallah Malama ina kika shiga mun fito bamu ganki awaje ba? " gutun tsaki Maryam tayi tace, " dama nace muku zan shigo makaranta ne da kuke nema na awaje, haka nan ina bacci kin tashe zaki isheni da masifa " haushi ne ya fara kama Nafisa cikin ƙufula tace, " Maryam karki raina mana hankali serious kina ina so muke mu wuce fa " ita ɗinma ta fara jin haushi cikin gatse tace, " ina gidanmu mana akan katifa ta " Khadija ce ta karɓi wayar tace, " to sababbu yanxu ma yi zakuyi, Maryam dan Allah kina ina wallahi yau da wuri nake san wucewa gida " ganin da gaske suke yasa Maryam tace, " wallahi ina gida Khadi....." Muryar Umma ce ta katse Maryam tana faɗin, " Maryam tunda kin tashi daga baccin zo kije gidan Kawunki Idris ki karɓo mun Lalle gun Umma Lubabatu, Maryam amsa ta ba Umma sannan tace, " yanxu na tabbata kun yarda ko? " zaro idanu Khadija tayi cikin faɗuwar gaba tace, " wallahi ko minti biyar bamuyi da fitowa dake tare ba daga cikin Hall, Maryam mai yake faruwa ne? " jim kaɗan Maryam tayi tace," wallahi nima bansani ba abinda na sani dai yau tun safe ina gidanmu ko ƙofar gida ban fita ba...." tana cikin magana sauran kuɗin wayar ya ƙare.


       Kiran wayar Nazir ne ya shigo ɗauka tayi suka gaisa cikin zumuɗi yace mata, " albiahirinki my love " murmushi tayi sannan tace, " goro me muka samu " cikin hanzari Nazir yace, " Yaya Auwalu ne ya samu Baba yace masa gidansu budurwarsa sunce masa ya tura manyansa, to shi ne fa nima aka tambayeni nace nima na shirya yanxu Baba yace cikin satin nan zasu zo neman aurenmu " ɗan jim tayi atake Abubakar ne ya faɗo mata, jin shirun da tayi yasa Nazir yace, " yadai ko bakya farin ciki ne? " murmushi Maryam tayi tace, " a'a ba haka bane naga da haɗuwarmu ko wata shida ba muyi ba amma kace zaka turo? " ɗan tsuke fuska yayi yace, " ashe dama ba sona kike ba Maryam? " sai alokacin Maryam taga kamar bai dace ba abinda ta gaya masa, da sauri ta ce, " a'a nidai karka ɗaureni ba haka nake nufi ba " Nazir daɗi yaji sannan yace, " to shi kenan sai ki gayawa Abba muji ta bakinsa " to shikenan bari ya dawo anjima" Maryam ta bashi amsa, daga nan hira suka shiga sun jima suna hira sannan sukayi sallama, sai kuma maganganun su Khadija suka faɗo mata ita kaɗai take nazarinsu.Lokacin da Mlm Safwan ya koma office ɗinsa bakinsa guntse da dariya ya shiga, sai da ya zauna akan kujera shi kaɗai yake murmushi tuno yanayin presentation ɗin Maryam yayi da yanda take motsa bakinta cikin nutsuwa, gaba ɗaya yanayin yarinyar burgeshi yake musamman irin kurinta da cika bakinta, sai dai lurar da yayi kamar ayau ɗin nan bata da walwala sam babu fara'a afuskarta, tashi yayi ya faɗa toilet ɗinsa da niyyar yayi alwala ya wuce masallaci dan gabatar da sallar azhar saboda kiraye-kirayen sallah da aka fara, bayan fitowarsa Maryam ya gani zaune akan kujera ta ɗora ɗaya kan ɗaya tana ƙara ƙarewa office ɗin kallo, cikin zuciyarsa yace, " ƴar rigima yau kuma komai ya dawo da ita office ɗina, lecture ta ce bazata ƙara zuwa ba taxo haka kuma office ɗina ma tace bazata kuma zuwa ba gashi ta dawo " sai da ya ƙare mata kallo sannan ya kuma tamke fuska yace, " wa ya baki izinin shigowa office ɗina? " shiru tayi sai da ta kalleshi tun daga sama har ƙasa sannan ta fara magana, " Safwan kenan, alokuta da dama mutane na bani mamaki kayi tsammanin wani abu nazo nema gurinka ne? Zuwa nayi domin na gargaɗeka kuma naja kunnenka karkaga kana da wani matsayi ka nemi wulaƙanta ɗan uwanka, ba anan take ba wani bakasan irin baiwa da darajar da yake da ita ba, kayi tunani mai kyau saboda shi ɗan Adam da kake gani daraja gareshi duk nakasar sa." Maryam na ƙarasa maganar ta miƙe tsaye tabi ta jikin window ɗin office ɗinsa ta wuce, tunda Maryam ta ambaci sunan sa kai tsaye jikinsa yayi sanyi bai kuma tsinkewa da lamarin ba sai da yaga ta bi ta jikin ƙarfen window ta wuce, juye-juye ya hauyi cikin mamaki da firgici ya fara furta, " Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un " cire hularsa yayi ya fara fifita fuskarsa da ita, gumi ne ya fara karyo masa mamaki na ƙara kamashi, wani tunani ne ya faɗo masa da sauri ya ɗauki mukullin sa dake kan table agaggauce ya rufe ƙofar office ɗin, kai tsaye inda yayi parking ɗin motarsa ya wuce da sauri ya shiga ya figi motar da gudun gaske.+


              Maryam dake ɗaki azaune tana nazari abun ne ya dame ta ta samu Umma ta sanar mata da yanda sukayi dasu Khadija, ita kanta jikin Umma sanyi yayi jiki ba ƙwari Umma tace, " Allah ka kawo mana ɗauki amma wannan lamari akwai ruɗani, amma bari Mlm ya dawo sai in sanar dashi halin da ake ciki Allah ya jishshemu alheri " Maryam ta amsa da, " Ameen " Hijabinta ta janyo ta tafi aiken da Umma tayi mata bayan wasu mintuna ta dawo ɗauke da saƙon da ta amso, bayan wani lokaci markaɗe Umma ta haɗawa Maryam ta ƙwala mata kira tana miƙa mata, kanta tsaye Maryam ta fice daga gidan wata mota ta gani daga gaban gidansu da mutum jingine yana danna waya, sai da taje gabda shi sannan taga kamar Mlm Safwan, cikin zuciyarta tace, " kai wannan mutumin mai yazo yi unguwar mu ne? " tun sau ɗaya data kalli gurin bata ƙara kallo ba sai ma tayi kamar bata ganshi ba har taje ta kai markaɗenta ta dawo yana gurin, mamaki ne ya kama Mlm Safwan ganin ta wuce shi ko kallan ƙurarsa bata yi ba, wannan karan ma har taje zata kuma giftashi da sauri yace, " Maryam " sai kuma yayi shiru ita ɗinma har ta ɗan tsaya sai kawai ta sa kai ta wuce abinta kamar bada ita yake ba, kunya ce taso kama Safwan saboda bashi kaɗai ne tsaye agurin ba wasu samari na daga gefe kan benci suna hira, ɗaya daga cikinsu ne ta kalli Safwan yace, " wannan yarinyar ƴar girman kai ce zata kulaka wallahi zaka daɗe Alh gwara tun wuri ka kama gabanka, dan bata kula kowa sai wani figaggen yaro mai Lifan yana tafe da doro kamar bukka" gaban Safwana ne  yanke ya faɗi ya rasa dalilin haka cikin son jin labarin Maryam Safwan yace, " au dama tana da saurayi? " karaf ɗayan ya karɓe zancen, " eh mana kafin shi ma tayi wani Abubakar ranar da aka sa musu rana aka wayi gari anmurɗe wuyansa har lahira ya mutu " zaro ido Safwan yayi kamar agabansa akayi cikin jimami ya dinga bugar cikinsu kaf suka kwashe labarin Maryam wanda suka sani suka gaya masa daga ƙarshe ɗaya daga cikinsu yayi ƙasa-ƙasa da murya yana ɗan waige yace, " amma fa naji ana raɗeraɗin wai aljani ne ya aureta sai dai bani da tabbas ɗin maganar " ƴan Kuɗi Mlm Safwan ya ɗebo ya miƙa musu aykuwa suka dinga zayyano masa godiya, kofar gidansu Maryam ya koma ya samu yaro ya tura shi yace ayi masa sallama da Abba sai dai Umma ta ce agaya masa baya nan sai magriba zai sameshi, Safwan najin haka ya koma motarsa yayi mata key ya bar unguwar da niyyar zai dawo ya samu Abba amma har ya tafi maganganun samarin nan ne ke masa yawo azuciya.


STORY CONTINUES BELOW

          Bayan magriba Umma na zaune ita da Abbaa suna hira take sanar da shi maganar da Maryam ta sanar mata game da Nazir, Abba yayi farin ciki sosai zuwa ɗan wani lokaci kuma sai yayi jim ganin yanayin da ya shiga yasa Umma tace, " Mlm lafiya kuwa? " kallanta yayi yace, " kice mata ta turo mun yaron inasan na sanar dashi matsalarta ne amma ina tsoron kar yace ya fasa auren ta " itama Umma jim tayi saboda abinda taji Abba yace, cikin sanyin jiki ta ce, " zan gaya mata kuma babu wani abu da zai faru Mlm  insha Allah " Abba ya amsa da, " Ameen " wannan karan ma Umma sanar da Abba tayi abinda ƙawayen Maryam suka kirata suka gaya mata game da ganinta da sukayi kuma wai har ta gabatar da presentation, abin ya jima ya na juya masa arai gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, duk wanda ya fahimci damuwar mutanen nan sai ya tausaya musu, Abba ne yace, " to ko Maryam ce taje amadadinta? " Umma ta ce, " to Mlm wannan kuma sanin gaibu sai lillahi " suna cikin haka yaro yayi sallama yace, " wai ana sallama da Abba" Abba jiki ba ƙwari ya tashi ya fita Safwan na jingine jikin bangon gidansu Maryam, yana ganin Abba har ƙasa ya duƙa ya gaisheshi cikin sakin fuska Abba ya amsa yana ƙara yaba hankali da nutsuwar Safwan, Shagonsa da yake zama da baƙi ya buɗe suka shiga bayan sun zauna, Safwan ya shiga yiwa Abba bayanin abunda ya faru tsakaninsa da Maryam tunda farko har zuwa abin mamakin da tayi masa, sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama, Abba sai godiya yake masa Safwan kallan Abba yayi yace, " haba Abba dan Allah ka daina mun godiya haka duk abinda nayi wa Maryam kamar kanwata nayiwa banajin daɗi idan kana yawan gode mun " Abba murmushi yayi yace, " haka ne Malam Safwan amma yabon gwani ya zama dole, Allah ya bamu sa'a ubangiji ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar " Safwan ya amsa da, "Ameen "


           Bayan kwana biyu Nazir ne zaune agaban Abba yana masa sharhin duk abinda yake tattare da Maryam, cikin ƙarfin gwiwa Nazir yace wa Abba, " Abba naji duk bayanan ka na amince zan auri Maryam ahaka cuta da mutuwa duk na Allah ne, Allah kuma ya shiga tsakanin nagari da mugu " Abba ba kaɗan ba yaji daɗin Maganar Nazir sosai ya ƙarajin ƙaunar Nazir azuciyarsa, cikin girmamawa sukayi sallama tsakanin Abba da Nazir.


        Abba zuwa yayi ya sanarwa da ƴan uwansa suma ba ƙaramin farin ciki sukayi da jin wannan maganar ba, bayan kwana biyu da wannan maganar iyayen Nazir suka kawo kuɗi da sa rana take aka tsaida musu da lokaci wata goma, wato bayan bikin ƴaƴansu Baba Ibrahim da wata biyu kowa farin ciki yayi dajin wannan abun farin cikin murna gurin Maryam da Nazir ba'a magana.


       Su Khadija rana suka tsaida suka sanar wa da Maryam zuwansu, kamar yanda suka gaya mata ranar wata Asabar wajen ƙarfe ɗaya na rana suka yi sallama agidansu Maryam, ta karrama su yanda yakamata hira suka ɗan taɓa sanna Khadija ta watsowa Maryam tambaya, " Maryam lokuta da dama lamarinki na ɗaure mana kai dan Allah ki wayar mana kai ko yaya ne munasan musan labarinki, nifa banda ma ina ƙaunarki zuciya ɗaya wallahi Maryam da sai dai kibi hanyarki inbi tawa, wai me yake faruwa ne ko dama ku ƴan biyu ne bamu sani ba kuma waye ne MARWAN? " murmushi Maryam tayi ta ce, " amma dai anyi ƴan iska wai dama ba zuwan Allah da Annabi kuka min ba " Nafisa ta karɓe zancen da, " kiji ƴar latsi da sai kawai muzo ganinki haka nan, Mlm mgnr kady a hanya ta ke ki fiddamu duhu dan wallahi nina fara wasi wa si azuciyata "  hararar wasa Maryam ta watsa musu sannan ta ce, " ku dallah jiya dai iyayen Nazir sun zo har sun kawo kuɗo antsaida rana dama cewa nai suprise zanyi muku....." kafin ta rufe baki lokaci ɗaya suka ɗauki ihun murna haɗe da kwashewa da shewa, sun tayata murna sosai sannan suka daɗa dawo mata da maganarsu ta farko, ganin sun takura yasa Maryam ta basu labarin ta ataƙaice, sosai suka tausaya mata agefe ɗaya suna tsokanarta wai ta je duniyar aljanu, Nafisa ce ta ce, " Maryam to ita waccen Maryam aljanar kuna zama kuyi hira da ita wlh bakiga ba komai naku iri ɗaya " ɗan jim Maryam tayi sannan ta ce, " ke nifa sau ɗaya na taɓa ganinta tun ranar da ta ɗauko ni daga kogon dutse har yau ban kuma ganinta ba " jiki a sanyaye Khadija ta ce, " oh ikon Allah ashe cikin aljanu ma akwai na gari na ɗauka duk tsinannu ne " gaba ɗaya suka kwashe da dariya, Maryam kallanta tayi tace, " ki cigaba da zaginsu yasin intajiki ba ruwana " ɗan waige suka farayi sannan suka faɗa cikin wata hirar, sai yamma liƙis suka fito daga gidansu Maryam lokacin da ta fito zata musu rakiya suna fitowa suka ga Mlm Safwan a inda ya saba parking ɗin motarsa, Khadija ce ta fara ganinsa da sauri ta zunguro su Maryam ta ce, " lah kunga Mlm Safwan " da sauri Nafisa ta kalli gun aykuwa shi suka gani, sunje wucewa ta gurinsa cikin girmamawa suka gaidashi ita kuwa Maryam ta ɗauke kanta gefe, sai da sukayi nisa Nafisa ta ce, " ko me ya kawo Mlm Safwan unguwar nan? " Taɓe baki Maryam tayi ta ce, " to waya sani nima ganina dashi na biyu kenan " Khadija ta ce, " kodai gunki ya lallaɓo ne? " wani uban ashar Maryam  ta lailayo sannan ta ce," wallahi kinja muku na fasa rakaku titi ku gaida gida " kafin suje uffan Maryam ta tura musu kuɗin da Umma ta bayar ta ce abasu kuɗin mota jaka, Nafisa na niyyar magana suka hangi Maryam cikin sauri ta juya, murmushi sukayi sannan suka wuce.   Lokacin da Maryam ta koma har lokacin Marwan na gurin da suka barshi sai dai wannan karan ya kifa kansa ajikin mota da alama yana cikin damuwa, haka taxo ta wuce shi tana watsawa bayansa harara jin anfara kiran sallar magriba yasa Safwan ya fara neman yaron da zai tura gidansu Maryam a aromai buta, yana cikin wannan nazarin sai ga su Hafsa nan su dawo daga makaranta, ganin yanayin kammanin su da Maryam shi ya tabbatar masa da ƴan uwanta ne, har sun kusa shiga gida Safwan yayi musu magana, Mustafa ne ya dawo Hafsa na tsaye a inda take, cikin girmamawa Mustafa ya gaisheshi Safwan ma fuska asake ya amsa sannan yace, " Abokina da Allah karɓomun buta nayi alwala mana " ba musu Mustafa ya wuce shi da Hafsa, ruwa ya kawo masa yayi alwala shima yayi sannan suka wuce masallaci, tun ahanyarsu ta dawowa yake tayi wa Safwan hira sosai yaron ya birgeshi, bayan sun dawo ƙofar gida Musatafa yace, " Baƙo ni zan wuce gida " murmushi Safwan yayi yace, " sunana Safwan ba baƙo ba, amma tun yanxu zaka shiga gida muna hira? " Mustafa ƙara kallan Safwan yayi yace, " wallahi sunanka yamun daɗi amma ni yaya Safwan zance maka, eh yanxu zan shiga Abba ya hana fitar dare kuma wallahi Aunty Maryam zuga gareta ko Abba baiyi niyyar yin faɗa ba sai ta hura wuta " murmushi Safwan yayi ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu ɗaya yace masa, " to ga wannan ka sha sweet " zaro ido Mustafa yayi yace, " a'a wallahi Umma ta hanamu karɓar kuɗin duk wanda bamu sani ba, saboda akwai ƴan yankan kai " dariya sosai ya bawa Safwan suna cikin haka sai ga Abba ya dawo akan lifan ɗinsa, da murmushi afuskarsa ya fara yiwa Safwan magana, " ah Malam Safwan kaine agidan sannu da zuwa "Mustafa barka da zuwa yayiwa Abba sannan ya wuce gida, Safwan cikin girmamawa ya gaida Abba har ƙasa, shago ya buɗe masa bayan ya shiga da mashin ɗinsa soro gaisawa suka ƙarayi akaro na biyu sannan Abba yace, " ay ɗaxu ma na biya ta gurin Malam Haruna yace mun bai kammala magungunan nan ba sai zuwa gobe ko jibi " Safwan yace, " eh nima munyi waya dashi ina nan haka yake faɗa mun, ɗan jim Safwan yayi sannan yace, " ayda tare da Daddy ma zamu zo to sai ya tashi da zazzabi shi ne yace sai ya ɗanji daɗin jikinsa tukunna zamu zo tare " da sauri Abba yace, " subhanallah Ashsha ya jikin nasa? " Safwan ya amsa da, " da sauki wallahi " Abba yace, " to bari nayi magana da mutanen gidan sai inzo muje ka kaini na duba shi, lafiya ay ita ce komai " Abba ya ƙarasa maganar ya miƙewa, kai tsaye cikin gida ya shiga bayan ɗan wani lokaci ya fito atare suka fita daga shagon, Safwan ya tada mota Abba ya shiga sannan suka wuce cen gidansu Safwan.+


          Safwan shi da Abba basu suka ƙarasa ba sai wajen bayan sallar isha'a, abakin wani katafaren gida suka fara horn da sauri mai gadi ya xo ya wangale musu get ɗin yana yiwa su Safwan barka da zuwa, acen parking space yayi parking motarsa kusan tare suka fito shi da Abba, Abba cikin zuciyarsa yake mamakin wannan katafaren gidan nasu Safwan, tsinkayo muryar Safwan yana faɗin, " Abba mu ƙarasa ciki " Abba bayan Safwan yabi ta wata hanya suka bi wacce ita ce zata sada su da sitroom ɗin Daddy, da sallama suka isa cikin falon Dattijon na zaune da alama yasan da zuwan su Abba, yana ganin Abba ya tarbeshi cikin sakin fuska suka gaisa, zama Abba yayi suka ƙara gaisawa yana duba shi da jiki, kafin wani lokaci tuni ancika gaban Abban da kayan drinks, bayan sun gaisa Daddy yace, " wallahi yau naso zuwa gurinka kuma sai na tashi jiki na ba daɗi, saboda wata muhimmiyar magana ce Safwan yazo mun da ita " murmushi Abba yayi yace, " wallahi haka ya gaya mun shi ne nace ma bari nazo na duba ka da jiki, Alh muna godiya ƙwarai da taimakon da Safwan yake mana Allah ƙara budi ya ƙara girma " cikin jindaɗi Daddy yace, " kai haba meye na godiya ya me jikin kuma "Abba ya amsa, " da sauƙi sosai, yauwa wacce magana ce Alh ko anan ay sai mu tattauna ko? " Safwan dake gefensu najin haka ya miƙe sumi sumi ya wuce, Daddy murmushi yayi yace, " Safwan ya same ni da cewar yaga ƴar wajenka Maryam yana so, to yace bayasan fara tunkararka sai ya nemi izinin mahaifinta, to maganar da nayi niyyar zuwa wajenka da ita kenan " jim Abba yayi yanayinsa duk sai ya sauya tabbas da babu abinda ya gifta tsakanin Maryam da zai bashi ita muddin ta amince tana sanshi amma babu yanda zaiyi, jiki asanyaye yace, " Alh banji daɗin zuwan wannan buƙata taku ayanxu ba, wallahi yarinyar nan jiya-jiya yayyena suka karɓi kudin auren ta harda sa rana " Daddy shi ma ɗan jim yayi sannan yace, " babu komai kasan fa matar mutum kabarinsa, kuma Allah yayi Maryam ba matar Safwan bace, Allah ya kaimu lokacin yasa damu za'ayi " Abba ya amsa masa, " Aameen ya rabbi, Alh nagode da fahimtata da kayi " daga haka hira suka ɗan taɓa sannan Abba yace zai wuce gida, Daddy ne ya kira Safwan akunyace ya shigo falon gaba ɗaya sai yaji kunyar Abba ta kamashi, Daddy kuɗi ya ɗebo masu yawan gaske ya bawa Abba amma fir yaƙi karba, sam Daddy baiji daɗi ba ganin ya nuna rashin jin daɗinsa yasa Abba ya amsa, Safwan har gida ya maida Abba yana zumuɗin dawowa yaji maganar da suka tattauna tsakanin Abba da Daddy.


              Safwan gaba ɗaya ya gama jin yanda sukayi da Abba gaba ɗaya jikinsa sanyi yayi, daren ranar haka yayi shi ido biyu sai juyi da yake yi, babban abinda ke damunsa da ya tuno cewar Maryam ambata wani, kimanin ƙarfen biyun dare duk yake wannan nazarin ahankali ya fara tuno abubuwan daya shiga tsakaninsa da ita, tuno bakin tsiwarta yayi da maganun da ta dinga faɗa cikin ɓacin rai, ahankali ya fara faɗin, " me yasa ne me yasa zan mata haka bayan nasan ba laifinta bane, wai ma ya akayi ban bayyana kaina ba tuntuni, waye wannan da yake soyayya da Maryam? " shi kaɗai yake surutansa kamar wanda ya zautu sai kusan asuba sannan bacci yayi gaba dashi.


          Abba zayyanawa Umma yayi duk yanda sukayi da Daddy, tana gama saurarensa tayi murmushi sannan ta ce, " Malam kenan aydama biri yayi kama da mutum ni dama tunda ka bani labarin irin taimakwan da yake yi wajen neman maganin Maryam na sa masa waƙafi, aykuwa Maryam da zata auri Safwan da ta mo re miji ita ta huta wani nata ma yaje ya huta....." uwar hararar da Abba ya balla mata ne yasa ta gimtse bakinta, cikin jin haushi Abba yace, " wato hajja har yanxu kina nan da halinki ko? " shiru Umma tayi bata kuma magana ba, Abba ma bai kuma bi ta kanta ba ya shiga sabgar gabansa, duk zancen da sukeyi Maryam najinsu afili ta furta, " wato dama shiyasa yake zaryar unguwar mu kenan, to yaje cen ya nemi wata ni ko aƙafa aka ɗauran bazan iya dashi ba " ta ƙarasa maganar tanajan guntun tsaki.

 

      _anya kuwa maryam? amma ajuri zuwa rafi_🤣


          Bayan wasu kwanaki exams su Maryam suka fara sosai ɗalibai suka dage da karatu kowannen ɗalibi burunsa ya samu ya kammala jarrabawarsa cikin nasara, Safwan tun daga wannan lokacin bashi da aiki sai tunani da damuwa da farko yayi ƙoƙarin ganin ya cire Maryam daga zuciyarsa amma sai haka ya gagara, ga wani irin kishi da yake ji musamman idan ya tuna wani zata aura, exams ɗin su Maryam tayi nisa har sun kusa kammalawa saura biyu su gama, ranar da zasuyi Education Safwan na daga cikin waɗanɗa zasu kula da ɗalibai, cikin sa'a kuwa hall ɗin da su Maryam ke zaune cen aka tura shi, ko kaɗan Maryam bata kula dashi ba har sai bayan da aka gama rarraba musu exams paper da answer sheet, Nafisa ce ta tsegunta mata shi aykuwa ran Maryam yayi dubu ya ɓaci, Safwan duk yanda yaso ɗauke kansa daga kan Maryam abun ya gagara ƙirjinsa har wani irin bugu yakeyi, sosai exams ɗin tayiwa Maryam daɗi da sauran ɗaliban da suka yi karatu sosai, bayan minti talata students suka fara fita, cikin farin ciki Maryam ta tashi da niyyar submitting Safwan ne Malamin dake amsar takaddun students, taje miƙa masa kenan bisa tsautsayi ta kusan yin tuntuɓe sai dai bata kai ƙasa ba sai hannunta da ya ture sauran takaddun hannun Safwan, lokaci ɗaya hankalin students ya dawo kan Maryam kowa na jiran yaji irin ruwan faɗan da Mlm Safwan zai rufeta dashi, amma ga mamako sai ji sukayi yace, " baƙya gani ne? what are u thinking? " adaƙile ta ce, " nothing" tsugunnawa tayi ta fara tattare takaddun ganin tana jan lokaci yasa shima ya tsugunna ya fara haɗawa, afakaice yace mata, " ko kina tunanin saurayinki ne? " Maryam da gayya ta ce masa, " kasan zuciya na tare da abinda take so, yanxu haka garin saurin zuwa na ganshi na watsar da takaddun hannun ka " ta ƙarasa maganar tana sakar masa murmushin mugunta, wani irin zafi yaji azuciyarsa sai kawai ya basar ya ƙarasa tattare takardun ƙasa sannan ya karɓi takardun hannunta, duk wanda ya gansu zaiyi tunanin wata hira suke mai daɗin gaske, atake ɗalibai suka bugawa Mlm Safwam Question mark, tana miƙa masa ta fice waje zuciyarta fal farin ciki.

           Bayan sun fito gaba ɗaya aykuwa ɗalibai suka dinga yi mata tsiya wai me tayiwa Mlm Safwan da bai mata masifa ba, wasu kuma suka dinga cewa tsoro yaji karta kuma sumewa irin yanda ta taɓayi, wasu kuma suce santa yake kowa da abinda yake faɗa, wasu ma har cewa suke ay ya faɗa tarkon ƙaunar ta ne shiyasa ya gagara ce mata uffan, ba abinda tace musu gaba ɗaya harsu Khadija har sukayi suka gama, sannu ahankali suka har suka kammala exams ɗinsu sukayi hutu.  Tun bayan sa ranar su kullin Nazir cikin mugayen mafarkai yake, sautari zaiga miyagun hallitu sun tunkaro shi gadan-gadan zasu hallakashi amma saboda ibadarsa cikin mafarkin zaita tofe su da ayoyin Allah, tun baya damuwa har abun ya fara damunsa akwai ranar da ya kwanta baiyi addua ba, cikin bacci yayi mafarkin wani baƙin sa na binsa da gudu har ya samu ya cinmasa, gani yayi san ya fara rikiɗa zuwa wata mummunar hallita mai ɗauke da dogayen farata da sauri takai hannunta wajen wuyan Nazir zata shaƙeshi, har ya fara jin zafin shaƙar cikin ikon Allah ya fara karanto ayatulkursiyyu, atake hannuwan hallitar ya fara narkewa yana rozayewa, firgigit ya tashi yana maida numfashi sama-sama bakinsa ɗauke da addu'a, ga mamakinsa sai ganin wani abu yayi ya fice daga ɗakin mai yanayin siffar baƙin kare, tsoro ne ya fara kama Nazir ganin haka yasa yaja bargo ya rufa yana daɗa maimaita ayatulkursiyyu, jikin sai karkarwa yake yi mamaki na ƙara kamashi bisa ga abinda ya gani.

        Washegari da safe Nazir yaje gaida Mahaifiyarsa bayan sun gaisa ta kalleshi sannan tace, " Nazir a ƴan kwanakin nan ina mugayen mafarkai akanka dan Allah ka dage da addu'a kasan halin mutane yanxu wannan ƴar sana'ar da kakeyi sai kaga wani ta tsone masa idanu, Allah ya tsare mana ku aduk inda kuke " Nazir gabansa ne ya faɗi amma sai ya dake yace, " Insha Allah zan dage mama " kallan tsafe tayi masa sannan ta ce, " meye wannan nake gani kamar layi-layin taruwar jini awuyanka, sai nake ganin kamar kuma shatin hannu kai da waye haka Nazir " da sauri Nazir ya kai hannu yana shafa wuyansa sannan yace, " Mama shati kuma? " da sauri ta ce, " shati mana gashi nan kamar wanda aka shaƙe " shafa gun yayi sai yanxu shima yaji ɗan alamun haka, shiru yayi baice uffan ba ganin haka yasa Mama ta ce, " kai Nazir ka gayamun kaida waye kukayi faɗa jiya nifa banasan tashin hankali, duniyar ma nawa take " cikin sanyin jiki Nazir ya ce, " wallahi Mama mafarki nayi jiya...." tas ya bawa Mama labarin abinda yake faruwa dashi, salati ta hau yi da sallallami cikin firgici ta ke faɗin, " bari mahaifinka yaxo dole atashi tsaye mahassada har sun fara kawo maka mugun hari yanxu da sunyi nasarar shaƙeka sai dai mu wayi gari da gawarka akwance " jim Nazir yayi sannan yace, " Mama nifa gani nake sharrin shaiɗanu ne kawai ba wasu maƙiya " sheƙeƙe Mama ta ke kallansa har ya gama magana aykuwa cikin hassala ta ce, " shaiɗanun ubanka ina nuna maka Annabi kana runtse ido, shaiɗanun tuntuni basu shafeka yanxu ba saida ka zama saurayi, wannan mafarkin naka babu ko tantama mahassada ne suna ganin Allah yasa maka nasibi a lamuranka shi ne zasu tsugunnar dakai su cucemu, to ta Allah ba tasu ba " Nazir shiru yayi bai kuma cewa uffan ba har Mama tayi faɗanta ta gama.+


           Mommy da Daddy gaba ɗaya sun rasa gane kan Safwan ko hirar kirki baya zama suyi shi dasu,  hatta Safiyya ƴar gaban goshinshi ba kasafai ya cika zama suyi wata doguwar hira sosai ba, ganin haka yasa Daddy da mommy suka kirashi domin jin meke damunsa, amsa ɗaya ce ya basu na cewar, " ba komai " duk yanda sukayi da Safwan fir nuna musu yayi babu abinda ke damunsa, mommy ce ta fito ido biyu ta ce ta gano musababbun damuwarsa akan Maryam ne, shiru yayi mata ba amsa sosai ya bata tausayi musamman da taga irin ramar da yayi har wani ɗan duhu yayi, nasiha tayi masa sosai da lallasheshi cikin tausayawa irin na ɗa da mahaifi.


           Kwanci da tashi ba wuya agurin Allah kwanaki da satittika na shuɗewa watanni na zuwa suna haurewa, tafi-tafi har biki na ƙara ƙaratowa har ya rage biki saura wata biyu lokacin su Maryam sun fara shiga shagalin bikin ƴaƴan su Baba Ibrahim, yayin da su Maryam sun tafi level 3 kena, tun wancen lokacin babu abinda ya kuma shiga tsakanin Maryam da Safwan, saidai ta kan ganshi lokaci-lokaci yaje gurin Abba su gaisa kuma takan ji irin yabon ƙyawawan halayensa agurin Abba da Umma, Nazir abubuwan da yake gani kullin banda gaba ba abinda suke yi, da iyakar sa mafarki amma yanzu har ido biyu yaken ga wasu abubuwan na tsoratarwa sai dai har zuwa wannan lokacin babu abinda ya taɓa cutar dashi, wani abu dake ƙara ɗaga masa hankali kullin yaje gurin Maryam ya dawo kwana yake ba bacci ya dinga jin jikinsa ana mintsininsa wani lokacin har ji yake kamar ana yagar naman jikinsa, sannu ahankali ya fara ja baya da zuwa gurin Maryam, da asati yakan je sau ɗaya amma da haka ta fara faruwa sai yayi sati biyu har uku ma baije ba, wata ranar da ya dawo daga gurinta ranar sun sha hira saboda gajiyar party Maryam bata so daɗewar Nazir ba, ganin ta fara jin bacci yasa Nazir yace mata zai tafi, kallansa tayi tace, " sai yaushe kuma? " jim kaɗan yayi yace, " sai next week " cikin tsuke fuska ta ce, " au bazaka xo ɗaurin auren su Fa'iza ba " ganin ranta ya ɓaci yasa ya ce, " au na manta gobe ne fa ko? " shiru tayi masa, Nazir ya ce, " to shikenan Allah ya kaimu goben, muma fa saura wata biyu ko? " murmushi Maryam tayi tana gyaɗa masa kai, hira suka ɗan taɓa sannan sukayi sallama, bayan ga shiga gida yana shiga ɗakinsa, yaga wani irin dogon mutum tsaye atsakiyar katifarsa ko ƙarshenshi bai gani ba, ja da baya ya farayi cikin tsoro sai ji yayi yaci karo da wani abu yana juyawa yaga wani ɗan wadan tsoho mai ɗauke da ƙafafuwan zakara tafka-tafka, wani irin ihu ya kwarma nan take ya fice daga ɗakin, da kyar yayansa da mahaifinsa suka samu suka rirriƙeshi cikin haki da tashin hankali ya fara nuna musu ɗakinsa yana faɗin, " wallahi aljanune aciki bazan kuma kwana aciki ba " ahankali mahaifinsu ya leƙa ɗakin amma ga mamakinsa sai gani yayi wayam ba komai, Mama ce ta fara magana, " Malam kaga abinda nake faɗa kuka ce mun ba haka ba, gashi har sun fara haukatashi ay " shi kansa jikinsa yayi sanyi da lamarin Nazir saboda lokuta da dama zai ji shi yana surutai shi kaɗai, jiki asanyaye yace gaskiya naga alama Allah ya kaimu gobe sai mu kaishi gurin Mlm Audi mai magani " Mama tace, " yauwa koda naji".


            A daren ranar Nazir sai a ɗakin yayansa ya kwana bacci ɓarawo shi yayi awon gaba dashi, cikin baccin ne yayi mafarki da Maryam cikin mummunar shiga bakinta ɗauke da wasu manyan haƙora wani irin jini mai yauƙi na fita daga bakinta, cikin murya mai amo ta fara yiwa Nazir magana, " kai ɗan taurin kai ka nace ka cije kace sai ka auri Maryam ko, naji tsofaffinka zasu kaika gurin mai magani gobe, to zamuga zuwan nasu gobe, kuma muddin baka janye maganar aurenka da ita ba ɗaya bayan ɗaya sai ka rasa kowa naka, sai na raba ka da kowa kafin auren sannan kai kuma na maka kisan wulaƙanci " firgigit Nazir ya buɗe idanunsa alokacin ne yaji kiran assalatu, yana san yaje gurunsu Baba aɓangare ɗaya kuma yanajin tsoron fita, jin motsin yayansa yasa ya ce masa yana san ganin su Baba, cikin muryar bacci yace masa, " kai atsohon daren nan me zaka musu? " Nazir gaya masa mugun mafarkin da yayi ya yi azabure ya tashi suka fita abakin ƙofa suka tsaya suna ƙwalawa Baba kira, shiru sukaji sai Mama ce ta motsa ta amsa musu tana faɗin, " Nazir badai jikin bane? " Nazir ya amsa, " ba komai ina Baba " sai alokacin ta kalli gefenta ta fara bubbuga ƙafarsa tana faɗin, " Malam Malam Malam ka tashi " shiru  taji ba alamar motsi attare dashi, jin haka yasa Nazir ya faɗa ɗakin yana haska gun da Baba yake suka ga anmurɗe wuyansa jini ta hanci ta baki na zuba, har kunnensa da idanunsa jini ne ke fita, cikin tashin hankali suka rufu kan mahaifin nasu suna kuka mai tsuma zuciya, cikin kuka Nazir ya fara magana, " shikenan ta kasheshi wallahi babu ni babu ita " da mamaki suke tambayarsa wacece, zayyana musu komai yayi aykuwa gaba ɗaya suka ɗauki salati suna aibanta Maryam da zuriyarsu, kowa yaga yanayinsu sai ya tausaya musu musamman Mama.

 

          Kimanin ƙarfe tara na safe akayi jana'izar mahaifinsu Nazir wajen tara da rabi Nazir ya ɗauko hanyar gidansu Maryam, alokacin tuni sunyi kwalliyar ɗaurin  aure ita da amare  fitowarta daga gida kenan Nazir na ƙarasowa kofar gidansu, da murmushi ta tare shi tana faɗin, " barka da zuwa amma ka ƙaraso da wuri ba african time....... " wasu ƙyawawan mari guda huɗu ya wanke Maryam dasu sannan ya fara magana, " matsiyaci mayya mai muguwar aniya ashe dama haka kike bansani ba, kin kashe mun mahaifi kin cinye kurwarsa mayya mai gadon maita kije na fasa auren ki auri maye ɗan uwanki annamimiya, na soki tsakani da Allah kika saka mun da muguwar sakayya Allah ya isa tsakanina dake Allah yayi miki abinda kika mun " Maryam mutuwar tsaye tayi cikin sanyin jiki ta ce, " Nazir mai ne maka ne? "  kinfi kowa sanin abinda kika mun kin kashe mun mahaifi kin zuƙe masa jiki kije keda rabbissamawati, bazanyi shari'a dake ba saboda bani da hujja amma kije insha Allahu sai kinga ƙarshenki yanda zai kasance" yana gama faɗar haka ya haye mashin ɗinsa ya fice da gudun gaske, duk abinda yake faruwa akan idansu Abba akayi da Baba Jamilu suna niyyar wucewa gun ɗaurin aure, ransu ba ƙarmin ɓaci yayi ba, Maryam saboda ɓacin rai durƙushewa tayi agurin tana kuka mai tsuma xuciya, gaba ɗaya gurin sai da suka tausaya mata, Baba Idris ne ya ƙaraso ya dafa ta ya fara magana, " tashi Maryamu kinji indai maita ce sai dai ya gani akansu kuma sai na nuna masa cewar ba shi kaɗai ne namiji ba, Allah yasa haka shi yafi alheri " yana gama faɗar haka yasa Raliya ta wuce da Maryam cikin gida, kai tsaye masallaci suka wuce kowa zuciyarsa ba daɗi saboda abinda ya faru da Maryam, bayan sun gaggaisa da mutane aka fara ɗaure-ɗauren auren har sai da aka ɗaura auren ƴanmata biyar ana shirin salamewa Baba Idris ya raɗawa liman akayi shela sannan aka ɗaura auren MARYAM da NAJEEB.  Abba dake zaune agefen su Baba Ibrahim zama yayi kamar mutum mutumi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, bayan ɗaurin auren gaisawa suka shiga yi da ƴan uwa da abokan arziki cikin farin ciki, angwaye kowa ka kalli fuskarsa zaka lura da irin tsantsar farin cikin da yake ciki, bayan wani lokaci tuni kowa ya watse angwaye suka tarkata zuwa gaida iyayen amare, Umma na cen gidan su Baba Ibrahim labarin abinda ya faru da Maryam ya sameta, hankali atashe ta fita ta dawo gida yanayin da ta samu Maryam ba ƙaramin tayar mata da hankali ya ƙarayi ba, sannu ahankali ta dinga rarrashinta har ta samu Maryam ta tsagaita da kukan da ta ke yi, ganin ta tsagaita da kukan yasa Umma ta fara tambayarta, " Maryam me ya haɗaki da Nazir inacen akace mun yazo yaci miko mutumci harda mammarinki? " idanun Maryam ne suka ciko da ƙwallah sannan ta fara wa Umma magana, " wallahi nima bansani ba Umma, jiya da dare lafiya ƙalau muka rabu dashi har yace mun zaixo ɗaurin aure, kawai da safen nan yana zuwa ya rufeni da duka yana cewa na kashe masa mahaifinsa, Umma har mayya ya kira wai na cinye kurwar mahaifinsa " Maryam na kaiwa ƙarshe ta faɗa jikin Umma tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sosai Umma take jin kukan Maryam har cikin zuciyarta, tausayin Maryam na daɗa kamata cikin sanyin murya ta dinga lallashinta har tayi shiru, sai dai cikin zuciyarta wani irin zafi da ƙuna ta ke ji saboda ɓacin rai maƙogaronta har ɗaci yake mata, banda hawaye ba abinda yake sauka afuskar Maryam, suna cikin haka Abba yayi sallama shi kansa kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da yana cikin matsananciyar damuwa, cen gefen ya zauna ya rafka tagumi cikin zuciyarsa yana tausayin wannan jarraba da ƴarshi take ciki, kallan tsaf yayiwa Maryam sanna ya fara mata magana cikin tausasawa, " Maryamu na " dagowa tayi ta kalli mahaifin nata sai kawai ta fara hawaye, kauda kansa yayi gefe ya cigaba da cewa, " Maryamu komai kika ga ya faru da bawa to rubutaccene daga cikin ƙaddararsa kiyi ƙoƙari ki cinye taki ƙaddarar sai kiga Allah ya kawo miki abinda yafi zama shi ne alheri agareki, Allah ya rubuta Nazir ba mijinki bane haka nan kinsan wani baya aurar matar wani, dama tuncen Allah ya rubuta Najeeb shi ne mijinki mu ƴan Adam mu muke namu shirmen " cikin mamaki Umma ta ce, " Najeeb kuma Malam " gyaɗa mata kai yayi yace, " ƙwarai Najeeb ɗan Yaya Idris, ganin wulaƙancin da Nazir yayiwa Maryam a idon jama'a yasa ya yanke hukuncin haɗa Najeeb da Maryam, dama cen haka Allah ya tsara sai dai muyi fatan Allah sa hakan shi ne ya fi zama mana alheri " wani sabon kukan ne ya ƙara tahowa Maryam ganin abun take kamar amafarki, cikin zuciyarta take ayyana, " yanxu shikenan babu ni ba Nazir wai anɗaura mun aure yau da Najeeb " kallanta Abba yayi duk da yana jin tausayin halin da take ciki ya ce, " nasanki Maryam ke mai biyayya ce inasan kimun biyayya ga wannan auren  da aka muku, banasan naji wata matsala ta ɓullo daga gurinki tunda shi ma da yake namiji yayiwa mahaifinsa biyayya, karki bani kunya Maryam ki nunawa duniya irin tarbiyyar da muka baki, Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya ya kauda fitina atsakani " cikin muryar kuka Maryam ta ce, " na maka alƙawari Abba bazaka taɓajin wani ƙalubale daga gurina ba " murmushin da bai kai zuci ba Abba yayi yace, " nasan zakiyi fiye da haka ma Maryamu na Allah yayi miki albarka " yana ƙarasa maganar ya tashi ya fice daga ɗakin, Maryam jikin Umma ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka mai ciwo, wannan karan Umma barinta tayi sai da tayi mai isarta sannan ta lallasheta tayi shiru.

+

           Baba Ibrahim shi ya tara su Abba gaba ɗaya a babban falonsa bayan kowa ya hallara da sallama bude zaman nasu sannan ya fara magana, " barkanku da wannan lokacin nasan zakuyi mamakin abinda ya taramu agurin nan, wannan zama maƙasudinsa na waɗannan yara namu guda biyu ne, wannan aure nasu yazo mana bagatatan babu shiri bare tsammani, dan haka na yanke hukuncin bawa Najeeb gidana dake cen ƙasa ya zauna kafin ya samu ya samu nashi mahallin,  tunda idan aka sashi neman mahalli yanxu anshiga haƙƙinsa duba da yanda auren nasu yaxo, sannan na yanke hukuncin tariyarsu zuwa nan da kwana uku masu zuwa, ina fatan hakan dana yanke yayiwa kowanne daga cikin ku? " Baba Jamilu ne ya karɓe zancen da, " ni aɓangarena wannan hukunci yayi dai-dai kuma ni na lamunce zanyi wa Maryam funitures da kujeru " Abba ɗagowa yayi yana bin ƴan uwan nasa da ido wani irin farin ciki na lulluɓe shi " Baba Jamilu ya ce, " Yaya wannan hukunci naka yayi dai-dai Allah ya basu zaman lafiya, na ɗaukewa Najeeb haɗa lefe ni zan haɗa masa " cikin jindaɗi Abba ya kalli ƴan uwan nasa zai fara magana Baba Ibrahim ya ɗaga masa hannun yana faɗin, " indai godiya zakayi Umaru bama buƙata sai dai idan shawara gareka muna sauraronka " Abba cikin ƙaunar ƴan uwansa ya ce, " bani da wata shawara bayan hukuncin daka yanke Yaya " sun ɗan tattauna maganganu  sannan suka tashi daga taron kowa ya watse.


         Abba na komawa gida ya samu Daddy da Safwan sun ƙaraso cikin girmamawa Abba ya tarbesu, cikin falon baƙinsa ya sauke su sannan suka gaisa gaba ɗaya, Daddy ne yace, " mun ƙaraso har angama ɗaurin aure mun kusa ƙarasowa mota ta ɗan samu matsala, ya taro ya jama'a? To Allah sanya alheri " cikin jindaɗi Abba ya amsa, " ashsha lamarin ƙarfen nasara ba tabbas, taro Alhamdulillah Alh, Ameen ya rabbi " Abinci da su drinks Abba yasa aka kawo wa su Daddy, tuwon shinkafa ne miyar taushe tasha manshanu da dambun shinkafa yaji zogale da Manƙuli, sai kunun tsamiya da haɗaɗɗen kunun aya, gefe ɗaya ga su lemon roba nan dana kwali, guri Abba ya basu aykuwa sunci abincin sosai Daddy yaji daɗin abincin musamman tuwon shinkafar, Safwan cokali biyu yayiwa tuwon ya koma kan dambun dama yafi san dambu aykuwa yaci shi sosai, sannan suka sha kunun tsamiyar, Abba yaji daɗin yanda suka saki jiki dashi har suka abinci sosai, Mustafa ne ya kwashe kwanikan sannan ya dawo ya gaida su Daddy, Safwan kama hannunsa yayi yace, " muje ƙofar gida abokina ka tayani hira " waje suka koma kan wani benci Mustafa na bashi labarin yanda ɗaurin auren ya kasance da yanda angwayen sukayi kyau suka birgeshi, Bayan Safwan ya gama saurarensa sannan yace, " ina Aunty Maryam ko tana gidan bikin? " ɗan jim yayi sai yanayin fuskar sa ta sauya, Safwan tambayarsa ya ƙarayi, " lafiya naga kayi shiru " fuskarsa ba walwala Mustafa ya zayyanewa Safwan duk abinda ya faru da Maryam har zuwa auren da aka ɗaura mata da Najeeb " sannan ya ƙara da cewa, " Yaya Safwan wallahi Aunty Maryam na bani tausayi tun ɗazu banda kuka babu abinda takeyi, kuma wallahi nasan ba ita ta kashe Baban Ya Nazir ba, ni wallahi nafi tunanin Aljanin nan na jikinta ne ya shirya wannan abun " da sauri Safwan ya miƙe tsaye yana jin wani irin suya azuciyarsa, gaba ɗaya ya rasa ma ta ina zai fara da wanne zaiji da auren da akace anyiwa Maryam ko da marin haɗe da cin mutuncin Nazir, Babban abinda ke sa zucoyarsa na harbawa auren cikin ɓacin rai ya furta, " bazai yuwu ba " cen gurun su Abba ya koma kamar wanda aka jefa haka ya faɗa ɗakinsa rai aɓace idanunsa sun kaɗa jawur, cikin huci ya fara yiwa Abba magana, " Abba Mustafa ya gayamun wata magana da gaske haka ne, wai Nazir yazo har gida ya mari Maryam " Abba na shirin magana Daddy yace, " cooldown my son, duk abinda akaji hakan ne nima yanxu ya gama mun bayani " jiki asake Safwan ya jingina da bango sulalewa yayi ya zauna kamar mara laka ajiki, idanunsa ne suka ciko da ƙwalla ya fara magana, " Abba mai yasa ni ba'a bani Maryam ba za'a bawa wani bayan ninafi dacewa da ita, Abba dan Allah kayi wani abu mana " tausayi ya bawa Abba sosai Daddy yace, " Safwan me yake damunka ne bakaji bayanin da na maka ba" Abba ne ya kalli Daddy yace, " Alh abi ahankali da Allah " Safwan kamar wanda aka zabura firgigita ya miƙe tsaye yana tambayar Abba, " Abba waye Nazir ɗin nan inane gidansu " ganin yanayin da Safwan ke ciki ba ƙaramin tsorata su Abba yayi ba, magana ya fara masa cikin kwantar da murya, " Mlm Safwan dan Allah kayi hakuri karka yanke hukunci cikin fushi, ka barshi yaje komai na duniya ɗan hakuri ne " Safwan bayasan musu da Abba hakan yasa ya koma ya zauna, Abba ya jima yana lallaɓar Safwan sannan sukayi masa sallama suka wuce gida.Gaba ɗaya zuciyar Safwan adagule take saboda ɓacin rai da baƙin ciki har suka je gida babu abinda Safwan ya ƙara cewa, sai lokaci-lokaci da yake furzar da iska mai tafe da huci, bayan sunje gida yana yin parking kai tsaye part ɗinsa ya wuce, yana shiga da ƙarfin gaske ya banke ƙofar yana ƙara jin wani irin tuƙuƙin baƙin ciki azuciyarsa, Daddy ba ƙaramin tusayawa Safwan yayi ba musamman da yaga ahalin da Safwan ya wuce sashen sa, yana shiga falo mummy ce ta tarbeshi cikin farin ciki tana masa sannu da zuwa, ganin yanayinsa ya tabbatar mata da akwai damuwa, tambayarsa tayi atake ya zayyane mata duk abinda yake faruwa, ɗan jim kaɗan tayi sannan tace, " Alh ni da wata shawara gareni da Safwan zai amince da ban haɗashi da Hanan ba ƴar wajen Hjy Salamatu, wallahi yarinya ta jima tana mutuwar ƙaunar Safwan dandai tana shakkarsa ne bata tunkareshi da maganar ba, kasan Safwan da miskilanci amma yazo yana wahar da kansa abanza da wofi, ita fa batasan ma yanayi ba kuma koda tasan yanayi ay aikin gama ya gama, tunda yarinyar nan anɗaura mata aure da wani " kallan tsaf Daddy yayiwa Mummy sannan yace, " na tabbata ke kika haifi Safwan kinfi kowa sanin halinsa ko? Kina ganin zai amince da ita kika neman haɗashi da ita?? " ita ɗinma jim tayi kamar mai nazari sannan ta ce, " gaskiya da kamar wuya dan ina ganin yanayinsa ko gidan nan tazo ta gaishe shi baya wani sakar mata fuska, amma dai zan gwada ingani " ɗaga kafaɗa Daddy yayi sannan ya ce, " to Allah yasa adace " Mummy ta amsa da, " Ameen, bari na ƙarasa gurin nasa " ta ƙarasa maganar ta miƙewa domin tafiya part ɗin Safwan.+


         Lokacin da Mummy taje part ɗin Safwan yana kwance akan gadonsa ya zurfafa akundun tunani, har Mummy ta shiga baisan ma ta shiga ba, ta jima tana kallansa sannan ta fara kiransa, harsai da ta kirashi sau uku sannan yayi firgigit ya tashi zaune yana faɗin, " Mummy yaushe kika shigo? " murmushin takaici tayi sannan ta ce, " kana nan kana tunani ya za'ayi kasan na shigo? " ɗan sosa kai Safwan yayi sannan yace, " Mummy hutawa kawai nake banji shigowar ki bane ba fa " gefen gadonsa ta zauna tana ƙare mai kallo sai yanxu taga irin figewar da yayi duk ya rame ya jeme sai haske ta yayi, gefe ɗaya kuma tausayinsa ne ya kama ta cikin rashin jindaɗin yanayin da ta ganshi ta fara magana, " yanxu Safwan rayuwar da ka ɗaukarwa kanka kenan? wai yaushe ka zama haka ban sani ba? Safwan kai da ƴan mata ke zuwa har gida gaidani ina neman koda gaisawa ce ka amsa gaisuwarsu kaine yau kabi ka rame ka lalace akan mace, macen ma da batasan kanayi ba macen ma da ba baka da hurumi da ita, kayiwa kanka faɗa Safwan yarinyar nan fa yanxu matar wani ce gidan wani za'a kaita " runtse idanunsa yayi yana jin maganar Mummy nayi masa kuwwa akunne, cikin rashin jindaɗin kalaman Mummy ya ce, " Pls Mummy ki daina cewa Maryam matar wani ce " sororo Mummy tayi tana mamaki, cikin mamakin kalaman Safwan ta ce, " idan bance Matar wani bace so kake ince matarka ce Safwan? lallai ka ɗebo da yawa nidama wata shawara ce na kawo maka, mai zai hana ka nemi Hanan ƴar gida......." hannuwa biyu Safwan ya haɗa alamar roƙo ya katse mommy da, " Dan Allah mommy ki bar maganar kowacce yarinya, ni babu wacce take gaba na, wallahi ayanxu  bazan iya auren kowacce yarinya ba inba Maryam ba " Mommy haushi ne ya fara kamata cikin faɗa ta ce, " aykuwa ashe kana da aiki tunda wacce kake mafarkin aure da aurenta, sai ka zauna kana nan zaune nan da wata tara zakaji ance maka ta haihu " ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin, wani irin tuƙuƙi yaji azuciyarsa cikin zafin rai ya dunkule hannu yana kaiwa pillow duka, cikin ƙarajin ya furta, " Nooooo, bazai yuwu ba " tashi yayi ya fara kewaye ɗakinsa lokaci-lokaci yana guntun tsaki.


          Maryam yanda taga rana haka taga dare kwana tayi tana kukan baƙin ciki da ɗacin zuciya, agefe ɗaya ga wata irin soyayyar Nazir da ta addabi zuciyarta musamman idan ta tuno irin rayuwar da tayi dashi abaya, da nuna kulawar da ya dinga bata da irin rayuwar da suka dinga shiryawa shi da ita harda sunayen da zasu sawa yaransu, tayi kuka kamar ranta zai fita daga ƙarshe ta tashi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah tana sallah tana hawaye tana kaiwa Allah kukanta.

       Washegari tun farar safiya sukaji ana bugun gida Hafsat ce taje ta buɗe, cikin girmamawa ta gaida umma Hasiya amma ko ƙurarta bata kallah ba, cikin masifa ta shigo gidan tana faɗin, " Umaru kana ina wato tuggun naku akan ɗana ya ƙare ko? saboda ƴarku tayi baƙin jini taƙi auruwa za'a liƙawa ɗana, shi Idiris ɗin ayba shi kaɗai ya haifi Najeeb ɗinba, saboda tsabar zalinci za'a liƙawa ɗana ragowar Aljani kawai dan acuceni " Umma ce ta fito cikin tashin hankali take faɗin, " Yaya Hasiya lafiya wani abu ne ya faru...." azafafe ta katse da, " riƙe Yayarki banasan wani Yayar munafunci, wallahi-wallahi duk abinda ya samu ɗana hukuma ce zata rabamu daku, ba ruwana da wani zumunci kowa kansa ya sani " Umma na niyyar magana Abba ya fito ya dakatar da ita sannan ya cewa Umma Hasiya, " Hasiya yau mu kika zo kina gayawa haka? " nuna shi tayi da hannu sannan tace, " au kuna mamaki ne? to wannan kaɗan ma kuka gani iyaye na ne ku da bazan gaya muku haka ba, azzalumi kawai ka sa anliƙawa ɗana sauran aljani banda ƙaddara me Najeeb zaiyi da wata Maryam " maganganunta ba ƙaramin ciwo suka yiwa Abba ba, kallan Umma yayi da ta cika tayi fam yace mata, " muje ciki " rai aɓace Umma tace, " amma Mlm..." katseta yayi da, " banasan jin wata magana " ba yanda Umma ta iya haka ta sa kai ta shige ciki zuciyarta na ƙuna, haka nan Umma Hasiya bata daina bambamin faɗanta ba, ganin sun barta atsaye ita kaɗai yasa taja ƙafarta ta fice, Maryam da tun shigowar Umma Hasiya ba abinda take banda kukan baƙun ciki, ahankali Hafsat take bata hakuri kallan ƴar uwartata tayi cikin kuka ta ce, " Hafsa bakyajin me take faɗa? ni da me zanji ne arayuwata wallahi da wannan ƙuncin rayuwar dama banzo duni......" da sauri hafsa tasa hannu ta rufe mata baki tana faɗin, " a'a Aunty Maryam dan Allah karkice haka kowanne bawa kika gani da tashi ƙaddarar " Hafsa ta jima tana yiwa Maryam nasiha ahankali har ta daina kukan sai dai kallo ɗaya zakayi mata ka tabbatar da tashin hankalin da take ciki.

         Umma cikin takaici ta kalli Abba ta ce, " Anya Mlm baza'a warware auren nan ba tun ba'aje ko'ina ba har anfara mata gori? " murmushin takaici Abba yayi ya ce, " ni da kike gani bazan iya butulcewa ƴan uwana ba, saboda na tabba ko mutuwa nayi bazasu zaɓawa Maryam gurɓataccen miji ba, wannan shirmen da tayi shi ne har yasa kika karaya? na tabbata ɗan uwana baisan zata zo tayi wannan rashin hankalin ba, mata kuna da ƙaramar ƙwaƙwalwa ita gani take abinda ta aika dai-dai ne ko, to Allah ya kyauta " Umma badan zuciyarta taso ba ta amsa da, " Aameen "

           Duk wasu shirye-shirye da ya kamata ayi ankamalla komai gidan Maryam madaidaici mai ɗaki uku ne da kitchen da Banɗaki, angyare mata ko'ina anjera mata kayan ɗakinta gefe guda ga saitin akwatinanta nan guda shiga gwanin birgewa haka nan kitchen ɗinta ba laifi anzuba mata kaya na misali duk da ba'a shiryawa hakan ba, amma gidanta babu inda ya samu naƙasu, ƴan uwan Umma ana gobe za'a kai Maryam duk suka zo amma na cen nesan basu samu damar zuwa ba sai na cikin garin doguwa,  Bayan sallar Isha'i Abokan Najeeb ne suka zo da motoci guda biyar sai motar da Baba Ibrahim ya bayar yace aɗauko Maryam aciki, Maryam tun safe banda kuka babu abinda takeyi ita kanta ta rasa wane irin kuka takeyi gaba ɗaya ji take zuciyarta adagule babu walwala, sallama akayi akace afito da amarya aykuwa nan Maryam ta fashe da wani sabon kukan tana rungume Umma, duk yanada Umma takai da dauriya sai da ƙwallah ta dinga zubo mata da ƙyar ta yakice Maryam daga jikin kanwar Umman ta riƙeta suka fita aka sata amota, dama ita kaɗai ake jira tana shiga driver ya bawa motarsa wuta.


        Kowa yaje sai yayi sha'awar gidan Maryam banda ita da ko kaɗan bata ma san ya fasalin gidan yake ba bare taji sha'awarsa, gaba ɗaya kowa ya watse daga ita sai ƙawayenta uku, Khadija Nafisa sai ƙawarta ta cikin unguwa mai suna Fatima, suna nan zaune kowa jikinsu gaba ɗaya yayi sanyi musamman yanda sukaji irin kukan da Maryam take, suna nan zaune Angwaye suka shigo ɗan barkwancin da ake tsakanin abokan ango da ƙawayen amarya suka yi, suka kawo kuɗin sayen baki suka basu sannan suka musu sallam suka fice, Maryam banda shashsheƙar kuka babu abinda take yi, murmushi Najeeb yayi yana faɗin, " haba My Marcy har yanxu kukan ne dan Allah ki bar wahalar da kanki wajen zubda hawayenki abanza " shiru Maryam tayi ko ba komai taji daɗi  kalamansa duk da batayi zato ba, Najeeb hannu yasa ya ɗauke mayafin dake kan Maryam yana murmushi, afirgice ya zaro ido ganin abinda ya gani afuskarta yana ja da baya, Maryam mamaki ne ya kamata ganin halin da Najeeb ya shiga cikin sanyin murya ta ce, " lafiya Ya Najeeb " kuma gwalalo idanu yayi yana jan jikinsa har sai da yakai ga lugun gado.Maryam na ganin haka ta fara waige ita kanta tsoro ne ya fara kamata atunaninta Najeeb ko wani abun ya gani, atsorace ta tashi tana dube-dube cikin tashin hankali Najeeb ya fara ihu yana faɗin, " wayyo Allah na shiga uku zata halakani ku kawo mun agaji " ya ƙarasa magana yana jan murfin ƙofar drower, lokacin da Najeeb ya buɗe fuskarta karo yaci da wata mummunar hallita mai ɗauke da idanu takwas baki biyu sai wani irin ƙaton hanci, gani yayi wani irin harshe ya zazzago daga bakinta yana ɗigar da jini, lokacin da Maryam ke tambayar Najeeb gani yayi ta buɗe wagegen bakinta mai ɗauke da wasu irin manyan fiƙoƙi, ta tunkaro shi gadan-gadan tana niyyar halakashi, yana nan zaune sai gani yayi Maryam ta fara rarrabuwa gida-gida har saida ta kasu gida goma sha biyu, wani irin gurnani mai ɗauke da amo ke tashi acikin ɗakin, ilahir jikin Najeeb karkarwa yake saboda tsoro da tashin hankali, daga cikin wannan abun tsoron wani gabjejen baƙin mutum ya gani ya mai ɗauke da siffar gwagwgwan biri, munin fuskarsa ce yasa Najeeb tunda yamai kallo ɗaya ya kasa ƙara haɗa ido dashi, cikin wani hargitsetstsen yare ya dinga maganganu harsai da yayi yare sunfi kala goma, sannan ya fara hausa cikin muryarsa mara daɗin saurare, " Kai Najeeb kayi gangaci daka aure Maryam kuma ayau basai gobe ba kwananka zai ƙare, kasan matar wa ka aura har kake murna da zumuɗin kunsantowa gareta? tabbas wannan shi ne kuskurenka na farko kuma nan gaba baza ka ƙara yin irinsa ba, abinda yasa tun rana ban kashe ka ba saboda nasan ba da saninka aka ɗaura auren ba, sai dai nayi duk iya ƙoƙari na wajen ganin na kashe mahaifinka saboda shi ne duk ya ƙulla wannan makircin, amma na ka sa saboda ruƙon addininsa amma yaunxu zan ɗauki fansa akanka kuma inbar masa shaida ajikinka ba tabbata gaba baxai ƙara wannan kuskuren ba, Ni YANZULAK ba'a shiga hurumina aƙare dani lafiya Maryam tawa ce har abada, bazata taɓa rayuwar aure da wani ba inba ni ba. " wani irin tsoro ne ya kuma kama Najeeb musamman da ya gama sauraren duk maganganun da Marwan yake yi, yana cikin wannan nazarin yaga wannan  Marayam ɗin da ta rabu gida bibbiyu kowacce ta fisge kanta da hannunta, sai iya gangar jiki amma kan na hannunsu daga jikin kan bakinsu ne ke ta ɓaɓɓaka wata iriyar dariya mara kyawun gani da daɗin sauraro, azabure Najeeb ya fara surutai ba kai ba fasali, " wallahi bana santa bani na ce su aura mun ita ba kuma duk abinda kake so zanyi, ni xanma sake ta yanxun nan wallahi, amma dan Allah karka kashe ni ni bansan matar ka bace amma na haƙura da ita. " Maryam kanta ne ya ƙulle ganin Najeeb na kallon wani guri yana surutai gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe da gumi, duk wanda yaga halin da Najeeb ke ciki sai ya tausaya masa, cikin kuka yake ta roƙon Marwan yana masa magiya, Maryam cikin tausaya ta fara yiwa Najeeb magana, " wai meke faruwa ne Ya Najeev dan Allah kamun bayani ko wani abun ka gani ne da yake baka tsoro? " ɗaya daga cikin Maryam ɗince yaji ta faɗi haka yana shirin yin magana, Marwan yasa hannunsa masu farata ya fisgoshi yana fyaɗa shi da jikin bango,  Maryam na tsaye sai gani tayi anɗauki Najeeb anbuga da kallo cikin tashin hankali ta furta, " Marwan kazo kenan " tana shirin Magana sai gani tayi wata mai siffarta ta fito ta jikin mirrior ɗinta tana sanye da wasu kayan sarauta masu kyawyn gaske,  kai tsaye gun da Najeeb yake ta tunkara cikin tsawa ta fara masa magana, " wai mai yasa duk lokacin da kuka ga abun tashin hankali ya bijiro muku bakya iya ambaton Allah ne, yanxu kana zaune wannan azalumin zaiyi nasara akanka, ka maida kai ka fara karatu ka ga ba abinda zai iya aikata maka " sororo Najeeb ya yayi yana kallon ikon Allah ita kanta Maryam da idanu tabi jabun Maryam tana mamakin ganinta.+


STORY CONTINUES BELOW

        Afisace Marwan ya kalli jabun Maryam ya ce, " Farzuka tarshibgisaku minsakalfis bakifasu wargasmika harbastika garɓamj " Falzuka kina neman ki kawo mun matsala wallahi ki kiyayi gaɗuwad mu dake. " murmushi tayi masa sannan ta ce, " yanzulak miamana lafsirdaku bakutinfaau " Yanxulak har yanxu kana nan fa halinka ko? " tana kaiwa nan ta ce wa Najeeb, " Najeev wannan taimakon kawai zan iya maka, saboda duk inda na kaika zai bika ya Cutar da kai, dabara ta ragewa mai shiga rijiya gareka. " tana ƙarasa maganar tabi ta gefen Maryam har zata tafi ta ce, " Takwara ki ƙara hakuri kowa da tashi ƙaddarar, ta rufe baki tana bi ta cikin morror ta wuce abinta.


     Da ƙarfin gaske Marwan ya fusato kan Najeeb da niyyar talitseshi, ganin ya nufo kansa gadan-gadan yasa Najeeb ya runtse idanunsa yana karanto dukkan wasu addu'o'i da suka zo bakinsa, jin shiru ba abinda ya sameshi yasa ya buɗe idanunsa amma ga mamakinsa sai gani yayi gurin wayam ba komai sai Maryam dake tsaye tana kallan sa, har zuww lokacin atsorace Najeeb yake sai dube-dube yake kamar yana jiran wani abun da zai fito daga wani gurin, ganin ya fara dawowa nutsuwarsa yasa Maryam ta fara masa magana, " Ya Najeeb dan Allah kayi hakuri wallahi....." katse ta yayi da, " saurara Maryam ba abinda zaki cemun, dama ansan kina da wannan matsalar shi ne aka haɗani da ke domin ahalaka ni wallahi da sake ba dani za'a wannan ɗanyen aikin ba, ganin idona aljani ya bayyana gareni yana zai kasheni ni kuwa mai yayi mun zafi, wallahi na gwammaci insakeki inyaso duk maganganun da za'a faɗa naji ayi ta faɗa, ni kinga tafiya gidanmu jeki gidanmu kema na sakeki ɗai-ɗai har saki uku " Maryam rasa abinyi tayi shin kukan na farin ciki ne ko na baƙin ciko zatayi cikin hawaye ta ce, " ka sakeni fa Ya Najeeb? " ko ta kanta bai bi ba ya miƙe tsaye yana gyara rigarsa cikin wani irin gurnani yaji gaba ɗaya dakin yana wata irin girgiza, baiyi aune ba sai ji yayi anfyaɗa shi da ƙasa wani irin garnaƙeƙen maciji ya gani ya tsago daga ƙasa akaurin macijin ya fi kaurin mutum sai dai kuma taayinsa ne babu adadi, wani uban ihu Najeeb ya saki yana karanto ayatulkursiyyu haɗe da zubawa aguje ko waiwaye baya yi, saboda tsabar tsoro da kyar ya samu ya buɗe ƙofar gidan gudu yake falfalawa tun iya ƙarfinsa, bai tsaya ko ina ba sai cen gidan mahaifinsa, lokacin da ya ƙarasa tuni tuni har sun rufe gida, bugu yakeyi cikin tashin hankali ba ƙaƙƙautawa, gaba ɗaya tsoro ne ya kama ƴan gidan aka rasa wanda zai buɗe ƙofar, sai Baba Idris ne yayi ta maza ya buɗe ƙofar aykuwa yana buɗewa Najeeb ya faɗa da gudu har yana banke mahaifinsa nasa saura kaɗan yakai ƙasa.


          Ganin halin da Najeeb ya shigo yasa mahaifin nasa ya banke ƙofar da ƙarfin gaske shima cikin hanzari ya rufawa Najeeb baya, Najeeb bai tsaya ko'ina ba sai cen ƙarshen ɗakin mahaifin nasa, gaba ɗaya ƴan biki kowa jikinsa yayi sanyi mahaifin nasa ne ya shiga ya fara tambayarsa, aykuwa kamar jira yake Najeeb ya fara zayyano zance tiryen-tiryen, Baba Hasiya najin haka ta karɓe zance ta fara sababi, " wallahi dama nasan za'a rina amma munyi ta barka tunda ka dawo mana lafiya taje cen Allah haɗa kowa da rabonsa " Baba Idris ko kaɗan baiji daɗin abinda ya faru ba atake ya ɗauki wayarsa ya kira babban yayansu wato Baba Ibrahim ya gaya masa duk abinda yake faruwa, Baba Ibrahim da kansa yace zai je ya taho da Maryam daga gidanta, hakan kuwa akayi kamar haɗun baki shi da Baba Idris kusan tare suka ƙarasa gidan atsugunne suka sameta tana gursheƙen kuka, tasota sukayi amota suka rufe gidan kai tsaye Baba Ibrahim ya wuce da ita gidansa, Maryam kusan kwanan zaune tayi tana kukan baƙin ciki, haushinta ɗaya bai wuce da za'a dinga cewa aurenta ya mutu adarenta na farko agidan miji ba.

         Washe gari Baba Ibrahim ne ya kira Abba yace yana san ganinshi, ba abinda Abba ya kawo kai tsaye ya wuce cen gidan, bayan sun gaisa Baba Ibrahim yake sanar dashi duk abinda ke faruwa, sosai Abba yaji ba daɗi amma sai bai nunawa ɗan uwan nasa ba,ahaka sukayi sallama ya wuce gida sai zuwa azahar sannan Maryam ta nemi wucewa zuwa gida da farko Baba Ibrahim yaso hanata amma ganin irin damuwar da take ciki yasa ya ƙyaleta, shi da kansa ne ma ya raka ta har cen gidan ɗan uwan nasa.


         A lokacin da suka isa ƙofar gidasu Maryam Safwan na jingine hikin mota, har ƙasa ya tsugunna ya gaida Baba Ibrahim ita kuwa Maryam da damuwa tayi mata yawa ko bi ta kan Safwab batayi ba, da mamaki afuskar Safwan yake kallan Maryam har ta wuce cikin gida, Abba ne ya fito suka kuma gaisawa da Baba Ibrahim akaro na biyu, sannan Baba Ibrahim ya ɗora da cewa, " Umaru dan Allah ku bawa yarinyar nan kulawa ta musannan saboda tana cikin matsananciyar damuwa, bari naje na dawo naga kana sa baƙo  sai muje garin kura akwai wani mai magani insha Allag za'a dace " Abba gaba ɗaya yanayinsa na cikin damuwa, cikin ƙarfin hali yace, " to shikenan Yaya Allah ya kaimu, kuma wannan ba baƙo bane shi ne Malamin makarantarsu da nake baku labari Malam Safwan " murmushi Baba Ibrahim yayi sannan yace, " ah dama shi ne Mlm Safwan " ya ƙarasa faɗa yana ƙara miƙa masa hannu domin su ƙara gaisawa, akunyace  Safwan ya miƙa mai hannu amma ba ƙaramin daɗi yaji ba musamman yanda Baba Ibrahim ya sakar mai fuska, sallama Baba Idria yayi musu sannan ya wuce gida, Abba har yana shirin buɗe musu falonsa Safwan ya ce, " Abba dama wucewa fa naxo yi nace bari nazo mu gaisa ba zama zanyi ba " Abba ya juyo ya ce, " haba Mlm Safwan ayko ruwa ka sha ko? " ɗab sosa kai yayi ya ce, " anya kuwa Abba, Alhamdulillah nagode " dawowa Abba yayi ya ce, " to shikenan Safwan, ya Alh yana nan lafiya? " murmushi Safwan yayi yace, " lafiyarsa ƙalau, am Abba dan Allah kayi hakuri karka ce ba maka shishahigi, akwai abinda yake damun Maryam ne ko ciwon nata ne ya dawo? " jim Abba yayi gaba ɗaya yanayinsa ya sauya cikin damuwa, sannan ya gayawa Safwan duk abinda yake faruwa, wani sanyin farin ciki ne ya ɗarsu cikin zuciyar sa farin cikinsa har fili ya gaza ɓoyiwa, shiru yayi kamar mai nazari sannan ya cewa Abba, " Abba mai zau hana mu koma cen gurin Malam tunda abun yayi matsi haka? " Abba kallan Safwan yayi ya ce, " sai abinda ƴan uwana suka yanke amma zab shawarce su duk yanda mukayi zanyi maka bayani. " jinjina kai Safwan yayi sannan yace, " hakan ma yayi Abba, yauwa dan Allah Abba ka dubi girman Allah ka bani number Nazir " shiru Abba yayi yana nazari cen sai ya ce, " Safwan dan Allah kai hakuri ka maida komai ba komai ba, ka manta da abinda yaron nan yayi mata komai na duniya ɗab hakuri ne " murmushi Safwan ya ƙarayi sannan ya ce, " wallahi-wallagi babu wani abu da zanyi na tada hankali gasalima magana nake sanyi da yaron akwai tambayoyin da zanyi masa " waya Abba ya ciro ya nemo number Nazir sannan ya miƙawa Safwna atake shi kuma ya ɗauka awayarsa, ba jimawa yayiwa Abba sallama ya tada motarsa ya wuce.

            Baiyi tafiya mai nisa ba ya gangara cen gefen hanya yayi dialing calls ɗin Nazir, sai da ta kusa tsinkewa sannan aka ɗauka sallama Safwan yayi sannan ya fara magana, " Mlm Nazir kana ina ne? " yayan Nazir ne ya ɗauka jin tambayar da aka mai yasa yace, " Nazir baya jin daɗi amma yana gida idan so kake ka ganshi " daɗi Safwan yaji musamman da yaji ya samu karɓa lokaci ɗaya, cikin sauri ya ce, " subhanallah, Allah ya bashi lafiya sai dai bansan gidan nasu ba, ko zaka ban address " atake yayan Nazir ya Safwan address ɗin gidansu daga nan sukayi sallama, Safwan ya bawa motarsa wuta.

             Safwan yana tafe yana tambaya har ya ƙarasa gidansu Nazir baisha wuya va saboda gidansu fitaccen gida ne duk da dai ba wasu masu ƙarfi bane sai rufin asiri, har cikin gida aka shigar da Safwan cikin girmamawa ya gaida mahaifiyar Nazir, bayan sun gama gaisawa Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai fashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun aganye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifin ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zamura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ra surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.Girgiza kai Safwan yayi ya ce, " ba abokin aikinsa bane kuma bata tsammanin wannan aikin sihiri sai dai aikin shaiɗanu, ba tantama wannan aikin Marwan ne  saboda labari ya riskeni Nazir yaje yayiwa Maryam cin zarafi harda mari kuma na tabbata Marwan bazai ƙyaleshi haka ba " kasaƙe Mama tayi sannan ta ce, " to yaro shi wannan Marwan ɗin haka yake ɗaukan abu da zafi dan Allah muje ka rakani inroƙeshi gafara yayi haƙuri ya yafewa yaron nan " murmushin takaici Safwan yayi sannan ya ce, " Mama shi wannan Marwan ɗinfa ba Mutum bane aljani ne " zaro idanu gaba ɗaya sukayi lokaci ɗaya cikin tashin hanakali Yayan Nazir ya ce, " to meye alaƙarta da aljani da har yake shigar mata faɗa? " jin wannan maganar yasa Safwan ya gane cewar basusan komai game da Maryam ba, sannu ahanakali ya warware musu komai game da ita, bayan gama ya kalli Mama ya ce, " nayi alƙawarin zan kaishi gurin wani Islamic chemist da yardar Allah, Allah zai taimaka asamu ashawo kan matsalar abun " kuka Mama ta fashe dashi tana faɗin, " yaro maganin Islamic chemist yafi ƙarfin barmu muje gun sauran masu magunguna sadakar ɗari biyu ɗari uku ta wadatar, gaba ɗaya ƙarfin mu ya yi ƙasa kuma.... " katseta Safwan yayi da, " Mama bana buƙatar ƙwandalarku haɗin kanku nake buƙata kawai idan kun amince ayanzu ma zamu iya tafiya " farin ciki ne ya kama Mama cikin jindaɗi ta fara korowa Safwan godiya harda hawayenta, da kanshi suka kama Nazir da yake ta binsu da idanu aka shiga dashi mota, Ƙanwar Mama ce ta zauna dashi abaya Yayan Nazir ya shiga gaba suka wuce, labari na iske ƴan zaman makoki suka fara sawa Safwan albarka suna gode masa bisa ga wannan taimako da yayi musu.+


         Suna hanya Safwan ya kira Abba ya sanar dashi halin da yaje ya samu Nazir aciki, sosai Abba ya tausaya masa cikin jimami ya cewa Safwan, " Mlm Safwan kaganmu mun kusa ƙarasawa AL-FURQAN ISLAMIC CHEMIST amma insha Allah muka dawo zan ƙaraso nazo na duba shi na ga jikin nasa " Safwan ya cewa Abba, " ay muna tare dashi zan kawo shi nan gurin Malam " murmushi Abba yayi ya ce, " ikon Allah to shikenan  mu haɗu acen kawai " da haka sukayi sallama Safwan ya cigaba da driven ɗinsa.


              Lokacin da Safwan ya ƙarasa Su Abba basu jima da ƙarasawa ba, a reception suka zauna bayan wani lokaci kaɗan Malam ya shigo duk abinda ya faru tsakanin Maryam da Najeeb haka suka bawa Mlm labari, Abba ya ƙara da cewa, " wannan yaron da ka gani shi ne Najeeb tunda wannan abun ya faru bayan ya koma gida da ya basu labari shikenan ya wayi gari da safe idanu sun makance, ga dai idanunsa abuɗe amma kuma cikin ikon Allah ya ce baya iya ganin komai " Abba na cikin wannan bayanin sai ga su Safwan sun shigo, babu wanda bai tausayawa halin da Nazir yake ciki ba, Maryam na ganinsa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, Baba Ibrahim ne ya kalleta yayi mata magana aykuwa kamar mai jira ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya, Safwan dake tsaye ji yayi kukanta gar cikin zuciyarsa gaba ɗaya ji yayi ba daɗi cikin zuciyarsa yake faɗin, " ina ma inada damar hanata da nayi iya yi na " Maryam cikin kuka ta kalli Iyayen nata ta fara magana, " Baba Idris ka dubi yanda bayin Allah nan suka koma basu ji ba basu gani ba amma ji baƙin zalincin da Marwan yayi musu, Abba dole nayi kuka tunda komai ya faru dasu ta sanadina ne " Malam murmushi yayi sannan ya ce, " Maryamu kenan, Marwan bai isa ya cutar da ɗaya daga cikinsu ba fa ce abinda Allah ya rubuta na daga ƙaddarar su ne, Allah ya hukunta haka sai ya faru dasu koda Marwan bai shiga rayuwarsu ba, insha Allah zamu roƙi ubangiji kuma muyi namu maganin na dai-dai gwargwado ko Allah zai bamu nasara ya basu lafiya " jinjina kai Maryam tayi sannan ta tsagaita da kukan nata, yaransa dake gefe yasa suka shiga da Nazir da Najeeb wani madaidaicin ɗaki, kan carpet aka kwantar da Nazir shi kuma Najeeb aka riƙe hannunsa aka zaunar dashi, Safwan number Daddy ya kira ya sanar dashi halin da ake ciki, aykuwa nan take ya ce masa gashi nan zuwa.


          Alwala Mlm ya sauka yaje yayi sannan ya shiga ɗakin hannuwansa ɗauke da kayan maganunguna sai yaransa biyu da ke take masa baya, suma kowanne da kayan haɗim magunguna ahannunsa, wani kaskon turare ya karɓa ya buɗe wani turaren kwalba ajuye acikin garwashin, sai wani galan da ke cike da ruwan addu'a acikin wanj bokiti ya tsiyaya, sannan ya bude wani turare mara daɗin kamshi baiyi wata-wata ba ya watsa musu shi take ajikinsu, bismillah yayi sannan ya fara karanto ayoyin suratul baƙara, lokacin da aka zubawa Nazir wannan turaren wata irin ƙara yayi mai ɗauke da kururuwa bayan wannan ƙarar sai sukaji yayi shiru, Malam yafi ƙarfin minti ashirin yana karatu sannan Nazir ya hau wata irin karkarwa, Najeeb ne ya zabura da sauri ya miƙe tsaye idanunsa sun kaɗa sunyi jawur, cikin tsananin tashin hankali Marwan ya taƙarƙare ya kwallah uwar ƙara sannan ya fara magana, " Mlm ka dakata ka saurara dan Allah ka daina ƙona ni kome kake so zanyi amma dan Allah ka ƙyaleni haka " Mlm tsagaitawa yayi sannan ya ce, " so nake ka dawo da bayin Allah nan yanda suke kuma ka fice daga jikinsu " shiru Marwan yayi yanajin Mlm na shirin cigaba da karatu ya ce, " eh naji zan fita amma bazan maida su yanda suke  ba. " Malam azafafe ya cigaba da karatu jin azaba na ƙara ratsashi yasa ya ƙara kwallah ƙara yana faɗin, " dakata ka saurara, naji na yarda zasu dawo yanda suke amma kuma Mlm ka sani duk wanda Maryam zata aura duk wannan ciwukan zasu koma kansa ne...... " Malam bai gama saurarensa ba ya cigaba da Addu'a yana bada umarnin acigaba da yayyafa wa Najeeb wannan ruwan addu'ar, duk abinda yake faruwa su Abba naji Maryam jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba banda hawaye babu abinda take yi,  Jabum Maryam ce ta keto ta jikin bango ta ƙarasa gurin Abba da murmushi afuskarta ta rissina tana gaida shi, Banda Maryam da Abba babu wanda ya ganta, Abba da murmushi afuskarsa yace, ƴata ina kika shiga shiru ko gaisuwa bakya kawo mun " gaba ɗaya kallan Abba suka yi da suka ga ya kalli gefe ɗaya yana magana shi ƙadai, murmushi tayi ta ce, " Abba yanxu ba lokacin hira banr bari na shiga na fito " tana ƙarasa faɗa ta juya ta kalli Maryam ta da zuba mata idanu ta ce mata, " takwara ina fitowa Wancen nataccen naki ya tasoni ina cen ina hutawa ta " bata jira mai Maryam zata ce ta tabi ta jikin ƙauren kofa ta shiga cikin ɗakin, murmushi Maryam tayi ta ce, " Namesake ki fito lafiya " Banda idanu babu abinda su Baba idris suka bi su Maryam dashi, Baba Ibrahim ne yace, " Umaru wato aljanu sun samu mafaka agurinka har buɗe muku idanu aukeyi ko " murmushi Abba yayi yace, " Maryam ce fa wacce ta ɗauko mana Maryam daga kogon dutse. " cikin rashin damuwa Baba Ibrahim ya ce, " auho na ɗauka wasu sababbi kukayi ay " Safwan sai ayanzu ya gane wacce ake magana akanta, cikin ta'ajibi yake jinjina kai kallan abun yake kamar acikin shirin film.2


STORY CONTINUES BELOW

            Jabun Maryam da sallama ta shiga cikin ɗakin, Mlm amsa mata yayi yana sauraren abinda zaiji daga gareta, ya gane cewar ba mutum bace tunda ba wannan ne karo na farko da fara arba dasu ido biyu ba, Marwan na ganin Jabun Maryam ya juya baki ya fara mata magana, " jaakidansmilaau kaydi markidu Falzuka? lasbahu misaku ogsikmisa yajakilman ratbaakin tafa kilman basu warhat minsa hijba fihga rasba tihsabkila munsabjiba warkinzasu" ( wannan karan ma kinzo xaki kawo mun cikas ko Falzuka? babu ruwanki da sabga ta wallahi wannan shi ne na ƙarshe da zan ɗauki mummunan mataki akanki " murmushin takaici tayi sannan ta ce, " YANZULAK, bazan juya baki na ba zan baka amsa ne ta yaren da suke fahimta, ni Maryam har abada bazan daina bibiyarka ba muddin kana kan turbar zalinci, Malam wannan da kake gani babi tausayi azuciyarsa shawara ɗaya zan baka ku ƙoneshi kowa ya huta amma duk izyar da zaku yi masa bazata sa shi ya saduda ba, anyi abaya naga haka jin yanda ya maida bayin Allah nan, wallahi indai ba ƙoneshi kayi ba to babh tantama ankashe maciji ne ba'a sare kai ba, kuma muna nan bazau bar yarinyar nan tayi aure cikin kwanciyar hankali ba, kai rayuwarma bazai barta tayi ta cikin jindaɗi ba " ta ƙarasa maganar tana kallan Mlm, cikin gamsuwa da maganar Maryam ya amsa mata, " tabbas nima abinda nake shirin yi kenan kika riskemu, kuma naji daɗi da Allah ya banbanta halayenku Allah yayi miki albarka ya saka miki da alheri " cikin jindaɗi Maryam ta ce, " Aameen Mlm, kuma nayi alƙawarin insha Allah akwai magungunan da zan nemo acen gaɓar wani taiku cikin ikon Allah idan ana musu amfani dashi zasu samu waraka " Masha Allah, Allah saka da alheri ya baki abinda kike nema na alheri " Mlm ya faɗa, Maryam ta amsa masa da, " Ameen " sannan tayi masa sallama akan zata dawo ta fice daga ɗakin, Sai da tayi wa Abba bayanin yanda sukayi sannan ta wuce cen gaɓar taikun HARBAJA.2


          Sosai  Mlm ya buɗe wuta akan Marwan yake karatu ba ƙaƙƙautawa, tun Marwan na iya magana har ta kai ga ƙarfinsa ya ƙare, Mlm bada ƙaimi yayi sosai yana babbake Marwam Najeeb dake birgima sai wani irin gurnani yake mai ban tsoron sauraro, bayan dogon wani lokaci sai gani sukayi Najeeb ya yanke jiki ya faɗi, banda gumi babu abinda yakeyi jikinsa zafi zau kamar wuta sai sauke numfashi yake sama-sama, ana gama ƙone Marwan Nazir ya kwallah wata irin ƙara jikinsa na wani irin karkarwa, sai bayan wani lokaci jikin nasa ya tsagaita da karkarwa, idanu ya zurawa Mlm cikin kamar mai nazari ahankali ya furta, " Bawan Allah dan Allah nan ina ne? " hamdala Mlm yayi sannan ya ce, " karka damu abokina babu abinda zai faru da kai " jinjina kai Nazir yayi yana ƙara ƙarewa gurin kallo sannan ya koma ya kwanta.


          Mlm da yaransa ficewa sukayi daga ɗakin a inda suka barsu Abba nan suka samesu, gaba ɗaya jikin Mlm da yaran sa jiƙe yake da gumi, sannu su Baba Idris suka dinga jero musu, amsa musu sukayi sannan Mlm yace musu su dakace shi zuwa wasu ƴan mintuna.

       Bayan awa guda Mlm ne zaune dasu Abba yana musu bayanin artabun da suka sha da Marwan, lokacin tuni Daddy ya riga da ya ƙaraso gurin, sosai kowa ya nuna farin cikinsa musamman da sukaji yanda akayi nasara akan hatsabibin shaiɗani MARWAN, magunguna kala-kala ya kawo cikin leda mai zane-zane guda biyu ya basu kowacce leda ɗaya ta Nazir ce da Najeeb, Maryam dake gefe wani irin farin ciki ne ya lulluɓeta jinta take kamar wata sabuwar halitta, Safwan na kallan duk abinda take yi suna haɗa ido ta ɓalle masa harara murmushi yayi ya ɗauke kansa gefe cikin farin ciki, bayan Mlm ya gama basu magungunan Daddy ne ya tambayeshi nawa za'a sallamashi, ɗan jim Mlm yayi sannan ya ce, " Alh abada abun ya sauwaƙa kawai " murmushi Daddy yayi yasa hannu a aljihu ya miƙa masa bandir ɗin ƴan dubu na dubu ɗari biyar, Mlm har ƙasa ya durƙusa yana godiya suma su Abba godiya suka jerowa Daddy, Yayan Nazir harda hawayen farin ciki, Daddy kallan Maryam yayi ya ce, " ƴata Allah ƙara lafiya ya kiyaye gaba " akunyace Maryam ta amsa da, " Ameen Daddy angode Allah ƙara girma da jinkiri mai amfani " Safwan da tunda Maryam ta fara magana kafeta yayi da ido, Daddy sosai yaji daɗin addu'ar Maryam, hira suka fara taɓawa suna cikin haka sai gani sukayi Najeeb ya fito yana ƙarewa gurin kallo, gaba ɗaya murna ce ta kamasu da ganin idanun Najeeb sun dawo garau, Jabun Maryam ce ta shigo gurin bakinta ɗauke da sallama, Maryam Abba sai Mlm sune kawai suka ganta haka nan cikin haɗin baki suka amsa mata, wani ganye ta miƙawa Mlm haɗe da wani farin magani sannan ta fara masa bayani, " atake wannan ganyen ahaɗa da garin maganin su dinga turare shi kuma wanda baya takawa adinga shafa masa sau biyu arana, ana buƙatar suyi haka na tsawon kwana bakwai sannu a hankali insha Allahu jikinsu zai warware yayi kyau " godiya sosai su Abba sukayi mata, kallan Abba tayi ta ce masa, " Abba ni zan wuce ina tunanin bazaku ƙara ganina ba, tarayya ta daku alheri ce sai dai har abada bazan manta daku ba, dan Allah Abba ka dinga sani cikin addu'arka kamar yanda zaka sa Maryam " Abba idanunsa ne suka ciko da ƙwallah ya ce, " ba tun yanxu ba na miki wannan alƙawarin, jinki nake kamar ƴarda na haifa muna godiya da karamcinki agaremu, Allah ya tabbatar da alherinsa agareki. "Jabun Maryam itama ji tayi duk ba daɗi, Maryam kallanta tayi ta ce, " nagode takwara bani da bakin godiya agareki sai dai ince Allah ya saka miki da gidan Aljannah " Malam ya amsa da  " Ameen" Jabun Maryam har ta miƙe sai Baba Ibrahim yace, " ƴata Maryam muna godiya amma zamu so muma mu ganki kamar yanda su suke ganinki " yana rufe baki sai gani  mai kama da Maryam yayi daga cen gefe atsugunne, kowa binta yayi da kallo suna mamaki, tashi tayi tayi musu sallama ta fara tafiya tun daga yanayin tafiyarta zaka tabbatar da ba jinsin bil adam bace, akan idanunsu tabi ta jikin bango ta ɓace abinta.

          Kowa jiki a sanyaye ya miƙe suka yiwa Mlm sallama, Nazir aka ɗauko kowannensu ya tafi nashi maganin zuciyarsu fal ta'ajibin Jabun Maryam.


STORY CONTINUES BELOW

          *BAYAN WATA UKU*


           Nazir ya warke garau dashi kuma duk abinda ya faru sai da yayansa ya bashi labarin komai, sosai ya ji kunyar Maryam bisa ga abinda ya aikata mata, haka shima Najeeb ya warware garau dashi kamar wani abu bai taɓa samun shi ba, Nazir har gida yaje ya nemi yafiyar Maryam bisa ƙazafin da wulaƙancin da yayi mata, sannan har number Safwan ya karɓa ya nemi address ɗinsa yake har gida shi da Mama sukayi musu godiya, sai ma da yaje yaga Safwan sannan yake mamaki ashe Mlm Safwan ɗin daya sani ne, cikin mutumci suka rabu Nazir na mamaki ashe dama Mlm Safwan nada mutumci har haka.

           Safwan ya maida unguwar su Maryam kamar nan ce makarantar kullin ya tashi daga aiki sai ya he cen da tana gida da bata gida shi dai zaije, ganin har anshafe wata uku yasa Safwan yayiwa Daddy magana akan yaje ya samu Abba, aykuwa hakan akayi Daddy na gama yiwa Abba bayani Abba yace, " Alh wannan ay tsakaninsu ne indai yarinya ta amince ay ni bani da ta cewa Allah ya tabbatar mana da alheri " Daddy ya amsa da, " Aameen " bayan haka da kwana biyu Safwan yaje unguwarsu Maryam ya sa Musatafa ya yi masa sallama da ita, da farko Maryam har ta ce bata je ba sai kuma ta tuno Abba yana gida, badan taso ba ta ja hijabinta ta fita yana jikin mota, da sallam ta ƙarasa gurinsa sai dai fuskarta atamke take babu walwala, Safwan rasa abinda zai cewa Maryam yayi ganin tsaiwar na yawa yasa Maryam tace, " Mlm ka kirani kuma nazo kamun shiru inbaka da abin cewa zan wuce ciki " murmushi yayi sosai tsiwarta ke birgeshi kallanta yayi ya ce, " dan Allah Maryam ki taimaka ki aure ni " rass taji gabanta ya faɗi sai ta basar ta ce, " kawai in aureka kasan inasanka ko banasanka ne? " ji yayi ba daɗi cikin sanyin murya ya ce, " Maryam wallahi idan ban aureki ba rayuwata na cikin wani hali dan Allah...... " katse shi tayi da, " dan Allah Mlm Safwan karmuyi haka da kai ni gaskiya bama ra'ayin aure yanxu atattare dani kayi haƙuri kawai " tana ƙarasa faɗa ta juya ta shige gida ko saurarensa batayi ba, wani irin tashin hankali Safwan ya shiga jiki ba ƙwari ya buɗe motarsa ya shiga ya figeta da gudun gaske, Bayan Maryam ta shiga gida Abba ne ya kira Maryam ya fara mata magana, " Maryamu na manta ban sanar dake zuwan Safwan gurinki ba, jiya mahaifinsa yazo mun da maganar Safwan game dake na ce masa yazo ya sameki ku tattauna idan kin amince shikenan tunda ke ce zaki zauna da shi, ya kika gani kin amince ya miki? " Maryam gabanta ne ya faɗi cikin zuciyarta tace, " na shiga uku dama Daddy ne ya fara yiwa Abba maganar idan kuma Safwan yaje yace bana sanaa fa? " jin shirunta yayi yawa yasa Abba yace, " Maryamu dake nake fa " da sauri Maryam ta ce, " eh Abba mun gama magana dashi " Abba yace ba kum gama magana ba so nake naji kin amince ko a'a " shiru Maryam tayi sai zuwa cen akunyace ta ce, " eh na'amince " murmushi Abba yayi yace, " tashi kije Allah yayi miki albarka" Maryam ta tashi jiki ba ƙwari tana amsawa mahaifin nata.


         Safwan tunda ya tafi yake sharara gudu kmr xai tashi sama, ikon Allah shi ne ya kai Safwan gida yana shiga kuwa babu wanda ya tankawa kai tsaye ya wuce Part ɗinsa, ganin yanayin da ya shigo yasa mommy da Daddy suka sha jinin jikinsu, jikin Daddy asanyaye ya cewa mommy, " ni anya yarinyar nan kuwa ta amince da Safwan bakiga yanayinsa ba " guntun tsaki Mommy taja ta ce, " to gashi nan dai ɗan yau ne idan ya nace da abu sai dai ka zura mai ido " Daddy zaro wayarsa yayi ya ce, " Bari na kira mahaifin ta mutum ne mai sauƙin kai zai gayamun duk halin da ake ciki " Daddy waya ya bugawa Abba cikin hikima ya tambayi Abba, Abba da murmushi afuskarsa ya sanar masa yanda sukayi da Maryam, gaba ɗaya daɗi ne ya kamasu cikin mutumta juna sukayi sallama, Daddy na gama wayar ya wuce part ɗin Safwan, sai da nayi knocking wajen sau uku sannan ya buɗe yanayinsa sam ba walwal, Daddy kallansa yayi ya ce, " Safwan ka manta inajiran jin yanda kukayi da Maryam amma mai makon kazo kace mun kun daidaita " da sauri Safwan ya ɗago yana kallan Daddy bakinsa har rawa yake ya tambayi Daddy ta sigar da bazai gano shi ba, " Daddy agurin wa kaji " murmushi Daddy yayi ya ce, " yanxu muka gama waya da mahaifinta shi yake sanar mun " daɗi ya kama Safwan aɗan kunyace ya shafa kansa ya ce, " ay Daddy kunya nake ji na gaya maka " dariya sosai Daddy yayi sannan ya fice daga ɗakin, Safwan uban tsalle ya buga hau gado saboda murna.

       Tunda haka ta faru duk wata damuwar Safwan ta yaye duk sati yake zuwa gurin Maryam, kullin yaje da irin soki burutsin da Maryam zata bullo masa, wata guda da faruwar haka Safwan ya turo manyansa aka kawo kuɗin da sa rana, wata uku aka tsaida farin ciki gurin Safwan abun baya musaltuwa, lokacin da su Khadija suka samu labari haka suka dinga yiwa Maryam tsiya suna zolaya, Maryam tun bata jin san Safwan sannu ahankali har ta fara jin ƙaunarsa, tun tana tsuke masa fuska har ta fara saki sai dai ƙaramar miskila take komawa agaban sa ba, magana ma sai ta ga dama take furtata zuwan Safiyya uku gurin Maryam tunda suka haɗu tasu tazo ɗaya, Safiyya na san duk abinda ɗan uwanta yake so.


STORY CONTINUES BELOW

      *RANA BA TA ƘARYA*


           Kamar yanda aka tsaida lokacin biki sannu ahankali kwanaki na tafiya har lokacin ya zo, saura sati biyu biki aka kawo kayan lefen Maryam guda takwas kaya na gani na faɗa duk wanda ya gani sai sun birgeshi, sun zuba mata kayan masu tsadar gaske haka aka dinga zancen acikin unguwa, ranar Umma kwana tayi ba bacci saboda farin ciki abin nema ya samu.

          Tun ranar laraba aka fara shagalin biki a event kala daban-daban, ƴan department ɗin su Maryam da yawansu tsegumi ne ya kaisu dan su bawa idonsu abinci, ansha shagali ango da amarya ba ƙaramin kyau sukayi ba, sun birge kowa da ya halarci gurin, ranar asabar ranar akayi dinner abun sai wanda ya gani, Ango vanda murmushi ba abinda yakeyi kallen Maryam yayi yanda tasha gyaran jiki ba ƙaramin kyau tayi ba, matsawa yayi kuka da ita ya raɗa mata akunne, " Pretty wai mai yasa ba kije ayi MARWAN DAY ba. " wata hararar wasa ta yiwa Safwan lokaci ɗaya suka sa dariya, sai da suka birge kowa agurin basuyi aune ba sukaji Jabun Maryam ta ce, " a'a baka faɗa dai-dai ba kace ayi YANZULAK DAY dai " dariya sukayi gaba ɗaya sannan ta musu Allah sanya alheri tabar gurin, haka akayi taro cikin jindaɗi aka watse.

             Washegari lahadi aka ɗaura auren Maryam da Safwan akan sadaki naira dubu ɗari, ɗaurin auren da ya samu manyan mutane daga garuruwa daban-daban, Abba da ƴan uwansa duk suna cikin farin ciki Umma kai ya ɗau zafi saboda taron jama'a, wajen ƙarfe shida ƴan ɗaukan amarya suka zo da motoco kala kala, kai tsaye gidan Safwan aka wuce da Maryam dake unguwar Badama layout, su Abba sunyi ƙoƙari sosai musamman da ya kasance su ba masu ƙarfi bane sosai, sai dai sun zuba mata kaya na gani na faɗa, Bayan sallah Isha'i Safwan ne da abokansa  guda biyu suka masa rakiya, itama daga ɓangaren Maryam Khadija da Nafisa ne, basu wani jima sukayi addu'o'i suka sallami ƙawayen amarya sannan suka yiwa Safwan da Maryam sallama suka ɗebo su Khadija a mota.


   _Asha amarci lfy_🤸🏾‍♀️


        *BAYAN WATA BAKWAI*

   

      Maryam ce zaune afalo tayi ɗai ɗai tana cin wainar fulawa Safwan na gefenta suna hira, wayar Maryam ce tayi ƙara number Khadija ta gani, ɗauka tayi bayan sun gaisa ta ce mata, " to mmn biyu kiyi magana abuɗe mata get muna ƙofar gida " Ihun murna tayi ko kashe wayar batayi ba take sanarwa da Safwan tana ƙoƙarin yunƙurawa da ƙyar, dakatar da ita yayi yana faɗin, " bazaki wahalar da kanki abanza ba bari nayiwa Ɗanlami magana, " yana gama magana ya danna number megadin ya sanar dashi zuwan su Khadija, bayan wani lokaci sai ga su sun shigo, hararar wasa ta bisu dashi tana faɗin, " marasa mutumci wai tun ranar da aka kawo ni sai yau kuka zo " Nafisa ta karɓe zancen da, " ke sa'a ma kika ci da cewa nai abari sai kin sauka  " Safwan ne ya shigo ɗakin cikin girmamawa suka gaisheshi suna zolayarsa, sunsha hira sosai sai yamma  suka yi mata sallama rakosu su Maryam sukayi, Safwan ya ɗebo kuɗin mota basu masu yawan gaske.

        

         Bayan wata biyu da Sati biyu Maryam ce ta haifo kyakykyawan jaririnta namiji, murna gurin waɗannan ɓangarori biyun ba'a magana, ranar suna jariri yaci sunan mahaifin Safwan suke kiran sa da Ansar, ranar suna ansha shagali kamar biki haka akayi taro aka watse cikin farin ciki da annushuwa.


    _TAMMAT BIHAMDULILLAH_2


   *INA GODIYA GA ALLAH DA YA NUNA MUN YAU DANA KAMMALA WANNAN LITTAFI MAI SUNA MARWAN, DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU IKON ƊAUKA KURAKUREN CIKI ALLAH YA YAFE.*

Post a Comment for "MARWAN CHAPTER C KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...