-->
 • Jelajahi

  ;ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (1) A DALILIN MATAR UBA COMPLETE (1) A DUNIYARMU COMPLETE (2) A GIDANA COMPLETE DOC (1) A TUNANINA COMPLETE DOC (1) ABBAS COMPLETE (20) ABDULKADIR COMPLETE (4) ABDULLKADIR COMPLETE (6) ABOKIN MIJINA COMPLETE (1) ADIYYA COMPLETE (2) ADIYYAH COMPLETE (1) ADUN WASU COMPLETE (1) AGOLA COMPLETE (1) AHUMAGGAH COMPLETE (17) AJALIN SO COMPLETE (19) AKAN SO COMPLETE (1) AL (2) AL-AMARIN ZUCI COMPLETE (4) AL'KALAMINE SILA COMPLETE (2) ALMAJIRA COMPLETE DOC (2) ALMAJIRATA COMPLETE (1) AMAL COMPLETE (8) AMAREN BANA COMPLETE (8) AMARIN ZUCI COMPLETE (1) AMININ MAHAIFINA COMPLETE (17) AMJAD COMPLETE (2) ARZIQI RABO COMPLETE (3) ASHE KECE COMPLETE (1) AUREN SIRRI COMPLETE (1) AUREN SOJA COMPLETE (1) BA SONTA NAKE BA COMPLETE (16) BABBAN GIDA CHAPTER 3 MP3 (1) BABBAN GIDA COMPLETE MP3 (23) BABBAN KUSKURE COMPLETE (1) BAGIDAJIYA COMPLETE MP3 (4) BAKAR MACE COMPLETE MP3 (27) BAKIN DARE COMPLETE (5) BAƘIN DARE COMPLETE (15) BANSAN LAIFINA BA COMPLETE (2) BARIKI IYAWA COMPLETE (1) BARIKI NA FITO COMPLETE (48) BARRISTER ASAAD COMPLETE (1) BATACCEN YANAYI COMPLETE (3) BATUUL COMPLETE (24) BAYAN RAI COMPLETE DOC (1) BINTU COMPLETE DOC (1) ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (11) CAPTAIN BILAL COMPLETE DOC (1) CIWON IDANUNA COMPLETE (1) COMPLETE (1) COMPLETE DOCUMENTS (10) CONEL AHMARD COMPLETE (6) DA'IMAN COMPLETE (1) DAMATA COMPLETE MP3 (24) DAN ADAM COMPLETE (37) DAN FASHI 🔫 COMPLETE (1) DAN MINISTER COMPLETE (1) DAWUUD CHAPTER 1 (1) DAWUUD COMPLETE (10) DIYAM COMPLETE (20) DR SALEEM COMPLETE (7) DR SAMEER AMEER COMPLETE (2) EL-MUSTAPHA COMPLETE (13) FARA YAR SHEHU COMPLETE (4) FARHA COMPLETE (21) FETTA COMPLETE (31) FIRGITA SAMARI COMPLETE (1) GAMAYYAH COMPLETE (14) GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE (1) GIDAN SARAUTA COMPLETE (14) GIDAN UNCLE COMPLETE (1) GIMBIYA SA (3) GIMBIYA SA'ADIYA COMPLETE (44) GWARMAYA complete (1) H novels birnin gayu (29) HAFSAT COMPLETE (3) HARSASHEN SO COMPLETE (37) HASKE COMPLETE (27) Hausa novels (35) HIKIMA COMPLETE (10) HUTU COMPLETE (13) IGIYAR RAYUWA COMPLETE (1) IN SO YAKI NE COMPLETE (21) IT IS PART OF THE GIFT COMPLETE (6) Ita (1) ITACE QADDARATA COMPLETE (14) JALILA COMPLETE (13) JAWAHEER COMPLETE (7) JINI DAYA COMPLETE (1) JINNUL AASHIQUE COMPLETE (1) JUYIN RAYUWA COMPLETE (3) K'ADDARACE COMPLETE (14) K'ANWAR MIJINA COMPLETE (1) KADDARA KO SAKACI COMPLETE (3) KAINUWA COMPLETE (9) kANDALA COMPLETE (10) KANO TA JIDDAH COMPLETE (1) KARUWA CE COMPLETE (1) KAWU NANE COMPLETE (1) KAWUNA COMPLETE (8) KE NAKESO COMPLETE (6) KIBIYAR KADDARA COMPLETE (2) KINA RAINA COMPLETE (10) KISHIYOYINA COMPLETE (2) KIYAYYAR ZUCI COMPLETE (3) KOMA KAN MASHEKIYA COMPLETE (3) KOMAI NISAN JIFA COMPLETE (3) KUDIRI COMPLETE (9) kula da kaya (1) LOVE HER SOFTLY COMPLETE (14) MABRUKA COMPLETE DOC (1) MAEESHA COMPLETE (3) MAIRO COMPLETE (5) makaranta duniya (31) MAKIRCI KO ASIRI COMPLETE (4) MAKOTAN JUNA COMPLETE (10) MARWAN COMPLETE (3) MATACCIYAR RAYUWA COMPLETE (36) MATAR SHEIKH COMPLETE (1) MAZA {ALLURAR GUBA}💉 COMPLETE (1) MEYE ILLAR YAYA MATA COMPLETE (24) MIJIN BUZUWA COMPLETE (2) MIJIN HANEEFAH COMPLETE DOC (1) MIJIN YARINYA COMPLETE (2) MRS AMIDUD COMPLETE (12) MRS GURAJE (4) MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE (43) NANNY COMPLETE (3) NAUFAL COMPLETE (2) NAYI GUDUN GARA COMPLETE (39) NI DA PRINCE COMPLETE (19) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE (32) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE MP3 (66) RABO AJALI COMPLETE (8) RAI BIYU COMPLETE (21) RAMUWAR GAYYAH COMPLETE (6) RANA DAYA COMPLETE (3) RANAR NADAMA COMPLETE (2) RAYUWAR ASMAU COMPLETE (14) RIBAR BIYAYYAH COMPLETE (1) RIKICIN WANI GIDA COMPLETE (11) RUDI NE KO BURI COMPLETE MP3 (2) RUDINE KO BURI COMPLETE MP3 (12) RUKAYYAH YAR ALBARKA COMPLETE DOC (1) SAKAMAKO COMPLETE (10) SAMU COMPLETE (7) SAMU YAFI IYAWA COMPLETE (6) SAWUN BARAWO COMPLETE (11) SHIMFIDAR MIJINA COMPLETE (1) SILAR AJALI COMPLETE (3) SILAR GIDAN AIKI COMPLETE (30) SOORAJ COMPLETE (5) soyayyah (1) SOYAYYAH CHAPTER COMPLETE (1) SOYAYYAH COMPLETE (12) SOYAYYAR MU COMPLETE (5) TAGWAYE COMPLETE (36) TAMBARIN TALAKA COMPLETE (1) TANTIRIN NAMIJI COMPLETE (7) TARKO COMPLETE DOC (1) TARKO COMPLETE MP3 (3) TATTALINTA COMPLETE (12) TAZARAR DAKE TSAKANINMU COMPLETE (13) THE BLIND'S MONEY COMPLETE (11) THE CITY COMPLETE (6) TSANANI COMPLETE (20) TSANGAYAR MATI COMPLETE (8) TUN KAFIN AURE COMPLETE (1) TUNTUBEN HARSHE COMPLETE (4) UMARNIN SAURAYI COMPLETE (2) UMMI COMPLETE (15) UNTIL I RELLY DO COMPLETE (14) UZTAZIYA KO YAR DUNIYA COMPLETE (1) WANENE SHI COMPLETE (14) WANI AURE COMPLETE (34) Wata (1) WATA BAKWAI COMPLETE M (17) WATA FUSKA COMPLETE (15) WATA SHARI'A COMPLETE (21) YANAYIN RAYUWA COMPLETE (14) YANKAR KAUNA COMPLETE (2) YAR ALMAJIRA COMPLETE (4) YAR FULANI COMPLETE (2) YAR GWA (1) YAR MAKIYAYA CHAPTER 1 (2) YAR MAKIYAYA COMPLETE (19) YAR SADAKA COMPLETE (2) YAR SHUGABA COMPLETE (42) YAR TALLAH COMPLE (1) YARE BIYU COMPLETE DOC (1) YARIMA ASHMAN (1) YARIMA KHALEED COMPLETE (7) YARIMA SUHAIL COMPLETE DOC (1) YAZEED COMPLETE (3) ZABIN SAMHA COMPLETE (6) ZAMAN HOSTEL COMPLETE (1) ZEENAT YAR JARIDAH COMPLETE (16) ZEHRA COMPLETE (15) ZUCIYA COMPLETE (27)
  Copyright © HAUSA NOVELS
  Best Viral Premium Blogger Templates

  Iklan

  KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER A

  A/I/S
  Tuesday, 25 May 2021, 5/25/2021 04:20:00 am WIB Last Updated 2021-05-25T11:20:48Z
  masukkan script iklan disini
  masukkan script iklan disini

   KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER A  *****-----*****

  Sanye take da katon ruwan kasan hijab din ta wanda ya rufe mata duk kan jikin ta.


  Fara ce, tana da idanu, me dogon hanci, tana da tsayi matsa kai ci.


  Tafiya take cikin nustuwa, har ta iso kofar wani katon gida.


  Da sallama ta shiga, ta gaida me gadin.

  "Baba ina yini?"


  Cikin sakin fuska ya amsa, mata da

  "Lafiya lou. Amina. Ya gidan da su Babar taki."


  "Suna nan kalou."

  ta bashi amsa.


  "Kwana biyu kin buya."

  Mai gadin ya tambaye ta.


  "Wallahi Baba makaranta ne shi yasa."

  "Toh Allah bada sa'a."

  "Ameen ya Allah!"

  Ta fada tana yin cikin gidan.


  A harabar gidan ta hango shi zaune akan kujera, hannun sa rike da jarida yana karantawa.


  Dattijun mutun ne, fari da shi, wanda daga kallon sa kasan mutumin kirki ne, ga addini. Dan gefen sa alkur'ani ne.


  Karasawa tayi wajen da sallama. 'Dagowa yayi ya amsa mata cikin sakin fuska.


  Durkusawa tayi, a kasa, murmushin kan fuskar sane ya dado, yace,

  "Sannu da zuwa."


  "Yauwah Abbah. Ina yini?"

  ta gaida shi.

  "Lafiya lou kuna lafiya?"

  Ya tambaye ta.


  "Lafiya Lou Alhamdulilah."

  Ta fada tana mika masa.


  "Daman goro ne, na ce, bari na kawo maka."

  Ta mika masa,

  "Amina kenan bakya gajiya dai kullum cikin hidima."

  Abba ai ba yawa, daman Farouk ne, ya ce, kana son goro shine nace bari na kawo maka."


  Murmushi yayi, ya ce

  "Allah sarki. Allah yayi albarka."


  Kanta a kasa ta ce,

  "Ameen Ameen!"


  "Na zata lafiya Ahmad karatu zaki dauke kafa. Sai dai gashi baki manta da mu ba."


  Murmushi tayi, ta girgiza kai.

  "Haba Abba ai da Ahmad yana nan da baya nan duk daya ne a guri na. yadda kuke mahaifa a gun sa nima haka kuke a guna."


  Kai ya girgiza, ya ce,

  "Allah sarki. To Allah dai yayi Albarka. Kuma gashi kinzo gidan ba kowa sai ma'aikata kawai."


  "To bafa na tafi in sunzo a gaishe dasu."

  Ta fada yana mikewa.

  STORY CONTINUES BELOW

  "A'ah!" Ya dagatar da ita. Yana cewa,

  "Tsaya na shiga na kawo miki alherin abin nan da kika kawo min."

  Kai ta fara girgizawa, tana fadin,

  "A'ah wallahi Abba nagode, bana bukatar komai."

  "A'ah Aminatu."

  Ya fada yana mikewa.

  "A'ah Abba wallahi nagode."

  "Ai ba kece kika ce nai miki ba. Ni naga dama zan miki. Kuma ma ai ba a maida hannun kyauta baya. Sai shaidan. Dan jira bari na shiga  daga ciki."

  Ya fada yana yin cikin gidan. Tsayawa tayi tana kalle kallen ta.

  Wata mota ce ta shigo harabar gidan. Kallon motar tayi. Wata babbar mata ce ta fito daga cikin motar.

  Sai Wata budurwar yarinya da baza ta wuce Aminatu ba ta fito daga dayan bangaren.

  Wajen da take suka karaso,

  "wacece wacan?"

  Uwar ta tambaya, hannu yarinyar ta saka a saman kanta tana hango wacece.

  "Ke!"

  Ta daka mata tsawa.

  Juyowa tayi wajen su da fara'ar ta. Ta durkusa, ta ce,

  "Ina yini Hajiya."

  Wata Uwar tsawa Ta daka mata.

  "Keee! Tashi! Ban yini lafiya ba zaki gannin haka. An gaya miki muna da bukatar gaishe gaishe ne anan wajen. Bama bukata zo ki fita."

  Ta nuna mata hanyar fita fuskar ta a hade kamar garwashi.

  "Fita!"

  Ta kuma daka mata wata uwar tsawar wacce tasa, Amina Firgita.

  Kallon mahaifiyar tasu tayi, ta ce,

  "Hajiya daman ba wani abu bane nazo gaishe kune."

  Wannan yarinyar dake gefen mahaifiyar ta, ta ce,

  "Da me?  Da me? Hajiya na magana kina magana kamar sa'ar ki. Dallah rufe mana baki. Wanda kike zuwa neman nasa baya nan ko dole ne soyayyar nan ne dole sai anyi ta.

  ke zo ki fita daga gidan nan."

  Hajiya ce ta kamo ta, ta kalle ta, ta ce,

  "kada ki saki ki kara shigo mana cikin gida in kuwa kika zo sai na ci miki mutunci. Wato kunji labari zai dawo shine aka fara lallabowa ko?

  To baku isa ba, ba kuma ba zai taba auren ki ba kin gane. Munafukai. In na kuma ganin ki a cikin gidan nan sai na karya ki."

  Suka finciko ta suka hankada ta turata waje. Tashi tayi ta fita tana kuka.

  Zagin ta suka tsaya yi, suna kiran ta mayya da karuwa.

  Suna tsaye a wajen suna maida magana Abbah ya fito daga cikin gida.

  Kallon su yayi, ya ce,

  "Ina yarinyar da na bari a nan."

  "Wacce yarinya?"

  Ummah ta tambaya.

  "Aminatu yarinyar da zata auri Ahmad!"

  Ya bata amsa.

  Kallon sa tayi, ta ce,

  "Yarinyar da zata auri Ahmad."


  "Ni dana bashi da wata Amina da yake so. Kuma, duk kulle kullen da kuke Alhaji, billahilazi kuma daina. Bazai taba yiyuwa ba.

  Talakawan kake nufi ....."

  "Kee! Kee!"

  Ya Dakatar da ita, Wani kallo yake aika mata wanda daga gani ransa yayi mummina baci.

  Magana ya cigaba cikin baccin rai yana nuna ta da hannun da ya riko kudi zai bawa Aminatu.

  "Kull wallahi Allah ki kiyayeni. Da talaka da mai arziki duka Allah ne yayi su, wanda yafi wani a cikin su shine wanda yafi wani tsoron Allah....."

  "Ai mun fiso."

  Ta katse shi yana cikin yin magana. Itama fuskar ta a hade.

  "Kiji tsoron Allah!"

  Ya fada yana kara nunata da hannun ta.

  "Muna tsoron sa daman."

  Ta fada tana tsare shi da idanu.

  Ta cigaba da magana.

  "Amman wannan dai, aure bazai yiyu ba."

  Kai ya girgiza, ya ce,

  "To yanzu, kun koreta ne? Ko yaya?"

  Kallon sa tayi, ta ce,

  "Bazan koreta ba. Gida nane tab."

  Barin su yayi, ya fice waje dan bin bayan ta.

  Bin sa sukai da Kallo, ta ce,

  "Kana basu dama da yawa fa."

  Ko juyowa beba bare tayi zaton samun amsa a wajen sa.

  'Yar ta, ta ce,

  "Mama rabu da shi. Hausawa na cewa *kwarya tabi kwarya fa.* "

  Mama ta karasa da,

  " *In ta hau akushi dugurgujewa zatayi* "

  "Shine Mama."

  "Zo muje ciki yarinyar kirki."

  Ta ja hannun ta sukai ciki
  Filin saukar jirgi na Aminu kano. Abba ne da Ibrahim kanin Ahmad sukaje tarar sa.

  Wani kyakyawan saurayi.


  Wajen mahaifin nasa ya karaso, ya rumgume shi, sannan ya karasa wajen dan uwan nasa shima ya rumgume shi. Kowa na farin cikin dawowar sa.

  Gida suka taho, wanda Na'ima dake, barander gidan su, take jiran karasowar Yayan nata. Ta fito a guje, tana fadin

  "Oyoyo! Oyoyo!'

  Mama ce ta fito da gudun ta itama, tana fadin.

  "Babban 'da yazo, babban 'da yazo."

  Murmushi yayi ya cire Na'ima daga jikin sa yayi wajen Mama yana rumgume ta.

  Rawa Mama take, yi suna mata dariya. Ta ce,

  "Ai dole na rausaya Babban 'da ya dawo."

  Na'ima ta kamo hannu, mahaifiyar tata, ta ce,

  Mama kinga yadda Yaya yayi kyau, yayi fresh kamar na shi ba."

  Mama ta ce,

  "England fa aka ce miki ke. Haba ko iskar su ma ai wani abu ce ga ruwan sha me kyau."

  "Sannu da zuwa Babban 'da."

  ta fada tana karayin rawa.

  Ibrahim ya ce,

  "Wallahi England ta amshe ka ka ganka kuwa."

  Murmushi Ahmad yayi, ya ce,

  "To ya zanyi na samu nutsuwa ne."

  Mama ta kamo hannun sa, ta ce,

  "Ya hanya?"

  Murmushi yayi, ya ce,

  "Alhamdulilah."

  Abba yace,

  "Kinga Hajiya mu shiga ciki. Dan wannan surutun naki."

  Ta ce,

  "Kyale ni Alhaji. Murna nake Babba 'da ya dawo."

  Ta kara cigaba da rawar da take yi. Gaba Ahmad yayi, Abba da Sani suka bi Bayan sa.

  Mama kuwa sai rawa take sai da Na'ima ta kamo hannun ta sannan suka shige ciki.


  Zaune suke a babban Falo, wanda yake da manya manyan kujeru maroon kala. Sai ruwan madarar labulaye da kafet dake dakin.

  Abba da Kannen sa biyu, sai Ahmad dake gefen su zaune a kasa.


  Kanin shi, Basiru, ya ce

  "Alhaji daman munzo mu taya ka murna da farin ciki game da irin namijin kokari da kayi akan danka Ahmad ya gama karatu ya dawo kasar mu."

  Kai Abba ya jinjina, Basiru ya cigaba da magana.

  "Ka cika jarumi,"


  Abba ya ce,

  "To nagode Allah saka da alheri."


  iIliya, ya ce,

  "Dole a jinjina masa, saboda irin tarbiyyar da ya bawa Ahmad  sai dai muyi fatan Allah sanya Alheri."


  Abba, ya amsa da

  "Ameen Ameen!"


  Dai dai lokacin Mama ta zo kawo musu ruwa. Gaisawa tayi sannan ta mike ta bar wajen.


  Labewa tayi, dan taji musuke cewa

  Baba Basiru, ya kalli Ahmad ya ce,

  "Ahmad muna maka murna da kammala karatun ka. Da dawowar ka kasar nan. Sannan kuma babban abin farin ciki da nayi da baka auro baturiya ka taho mana da ita a matsayin matar ka ba."


  Dariya sukayi gaba dayan su.

  Abba ya ce,

  "Ahmad ai daban yake, domin irin tatbiyyaar da nai masa bazai taba auro baturiya wacce ba al'adar mu daya da ita ba, addinin mu da kuma dabi'un mu."


  Baba Basir ya ce,

  "Gaskiya ne, saboda mu a zuri'ar mu, har yanzu ba mu samu wanda ya fandare daga al'ada da dabi'u mu da iyayen mu suka dasa akai ba."


  Baba Iliyasu, ya ce,

  "Wallahi kuwa mun gode Allah."


  Baba Basiru, ya kalle Abba ya ce,

  "To Alhaji mu zamu koma, mungode da irin tarbar da akai mana."


  Ahmad ne ya mike, ya ce,

  "Ah kafin nan bari na kawo muku tarabar ku ta turai."


  Ya fada yana murmushi, yayi cikin gidan

  Baba Basiru, ya ce,

  "Toh mungode fa. Allah yayi Albarka.."


  Mama na jin ya tashi ta shige ciki da sauri dan kar Ahmad ya ganta.


  Dakin sa ya shiga wanda dakin ma kan saabin kallo ne. Ba abinda babu a ciki.


  Envelope ya dauko, sannan ya dauko jakar da ya dawo da ita yana lissafo kudin can.


  Har zai xuba, Mama ta shigo dakin.

  Kallon sa ta tsaya yi,  ta ce,

  "Ahmad baka da hankali."


  Dagowa yayi da sauri dan yaga abinda yayi,

  "Menene?"


  "Wannan kudin duk su zaka bawa."

  Kai ya gyada mata. Ya ce,

  "Wai dala dari biyar biyar ne nake son na basu."


  Dukawa tayi ta kwashe envelope din tana fadin,

  "To bani nan wajen sunyi yawa. Dala dari biyar din wa.  Dalah!"


  Ta kwashe su dukka ta mika masa, tana fadin.

  "sunyi yawa, ka dibi na Nigeria ka ba sa musu a ciki "


  Ta mika masa envelope din. Kallon ta yayi,  ya ce,

  "Kudin Nigeria kuma. Ni ban dasu."

  "To bari kaga."

  Ta fada tana kunto gefen zanin ta.

  Wasu tsofaffin naira dari dari ne, guda biyu ta fito dasu daga zanin nata.


  STORY CONTINUES BELOW

  Kallo ya bita dashi. Ta mika masa, ta ce,

  "Gashi sa musu naira  dari dari. Ya ishe su."


  Ido ya zaro, ya ce,

  "Umma!


  "Menene?"

  Ta hade rai.


  "Kannen Mahaifin nawa? Na dauki naira dari dari na basu. Naira dari fa, Dari biyu fa kenan."


  "Baka da hankali na lura, to sai kaje ka tattaro kantin kwari da  singa ka hada ka basu. Su sukayi dawainiya da kai ne. Kasan me sukai wa mahaifin ka su da mahaifiyar su. Tinda baza ka iya ba ni bari ka gani."


  Ta fada tana daukar envelope din tana zuba kudin a ciki.


  Shi dai Ahmad baki ya saki yana kallon ikon Allah.


  Waje tayi.  Tana fada mishi kada ya sake ya fito ya zauna.


  Da fara'ar ta,  ta isa falon ta mimika musu  envelope din.


  ta ce,

  "To gashi dan kune ya ce abaku. Kowa da nashi"

  Karba sukai suna masu farin ciki.

  Baba Basiru ya ce,

  "Ai da kin kira shi mun masa godiya."


  "A'ah danku ne fa. har sai ya fito kun masa godiya. ina kai ina masa wata godiya."


  Kallon ta kawai Abba yake amman ya tabbata akwai abinda ta shirya daga gannin ta.


  Baki suke washe wa na ganin an basu abu a envelope, Dady kam kallon ta kawai yake.


  "Haka ne Hajiya ayi masa godiya sai anjima."

  "Toh sai anjima."


  Tayi ciki. kallo Abba ya bita dashi. Mikewa suka yi, suna cewa,

  "To Alhaji Allah kara arxiki sai anjima."


  "Toh ku gaida iyalain naku."

  .


  Suna fitowa daga gidan suka fara lissafin abinda zasuyi da kudin da aka basu.


  Dan har suna maganar daga gani kudin masu tsoka ne.

  *in banda  gwamnati wa ke kyauta a cikin envelope.* "


  Baba Iliyasu ya fada.

  "Wallahi kuwa."


  Baba Basiru ya ce, ai shi sai yaje wajen me dakin sa zai bude yaga nawa ne.


  Baba Ililyasu, kuwa ya kafe a lokacin zai bude dan ko sisi matar sa baza ta gani a kudi wajen nasa.  Baba Basiru ya ce,

  "Matar taka, amma kayi haka baka kyauta ba. A lokacin da baka dashi ta zauna da kai amman yanzu ka samu zakayi butul ci ko?"


  Hannu Baba  Iliyasu ya zira a aljihu, ya zaro envelope din, ya bude a hankali. Zaro ta ya tsaya yi, yana kallon naira darin dake cikin envelope  din.


  Tabo Baba Basirun yayi, ya ce,

  "Malam Basiru, kaga abinda ke ciki saboda Allah."


  Baki Baba Basiru ya saka, yana kallon ta.

  "Naira Dari fa."

  Baba iliyasu ya kara maimatawa.


  Dariya Baba Basiru Yayi ya ce,

  "To bari kaji na fada maka yarln nan bai da mantuwa ya tuna lokacin da ka zane shi dan ya doki yahuzan ka. Shi yasa ya tashi ramawa ta haka."


  Ya kuma kyakyacewa da dariya. Baba iliyasu, ya ce,

  "Lallai yaron nan yasan kan tsiya."


  Aljihun nasa, shima ya fara budewa. Juyowa yayi ya ce,

  "Amman yaron nan zan masa rashin Mutunci kamar ni zai yi wa haka. Ina kannin uban sa."


  "Me ya faru ne?"

  "Kala kalah!"


  Ya fada yana daga masa Naira darin sa. Dariya shima ya kwashe da ita.


  "Yaro yayi Dai dai kai Naira Dari ni Naira Dari."

  "To dan uban sa bara naje yi ne."


  "Muna dai kusan da baran ko?"

  "Zo mu koma gida."

  "Aah a'ah muyi hakuri kawai."

  Yaja hannun sa suka shige.


  Mami kuwa har masu DJ ta kida har gida aka saka mata ta dinga musu liki da yan dola dola


  Ranar son samu kudi dan daga dala sai dubu daya su ta lika musu daga ita sai yar ta Ni'ima ne suka sha rawa a cikin gidan.


  Daga nan sai masu kirari da suka dinga zugata tana musu barin kudi.


  Wasu yan mata ne su uku suka shigo gidan su Ahmad. Sai da suka gaisa da me gadi sannan sukayi cikin gidan.


  Da Ibrahim suka hadu suka gaisa, sannan suka tambaye shi ina Ahmad yake.


  Mami dake "tsaya tin shigowar su a  barander, ta wulla musu harara.

  ta ce,

  "Daga ina zuwa ina."


  "Lah Mami ina yini?"

  Bata amsa ba, sai tambayar ta da ta kuma nananatawa.


  "Mama daman munzo muyiwa Ahmad sannu da zuwa ne."


  Murmushi tayi, ta ce,

  "Eh Allah ya dawo dashi lafiya daga nan kuma sai me?" Sai kuyi waje ko?"


  "Da dadama ai Hajiya da kinsanar masa, yar tsarabar nan ta England an bamu."


  "Iyye, har wata tsaraba ma zai baku. Zaku fita ko kuwa. Tsarabar lafiya an gaya muku, ya kwaso England ne ya kawo dan ya  raba muku. Ba shakka masu gwadayin tsiya sai kusa kai ai ku fice ko?"


  "Hajiya naga mu dashi kamar mun zama yan uwa ko?"

  "Eh haka ne, ku fiita ko nasa a fitar da ku."


  "Me gadi. Me gadi."

  Ta fara kwada masa kira.


  Da sauri ya karaso,

  "Ka fitar dasu."


  Kallon ta sukai suka sheke da dariya suka juya suka fice.


  "Daga yau ka kuma barin yaran nan suka shigo a bakin aikin ka. Wuce kabani waje."


  "Ayi hakuri Hajiya  daman wajen Alhaji karami suka zo ne."


  Tsawa ta daka masa nidai ga abinda nace nan."


  "To ranki ya dade

  Kanin Ahmad da ke tsaya ya dubi mahaifiyar ta shi, ya ce,

  "Haba Hajiya. Sune sunzo Masa murna dawowar sa, saboda kinsan sa da farin jini.  Kowa na..,"

  Ya gyada kai dan takaici kawai. Mahaifiyar ta su da ta zuba masa ido ta ce,
  "Haba."

  Ta dan dok'a ta ce,
  "Sannu Baba. Yi hakuri kirawo su ku taru kuyi min dukan tsiya ka gane."

  Ta ciro takalmin kafar ta ta na fadin.
  "Ungo ungo takalmi na. Ungo."

  Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai yayi can lambun gidan,

  Mita ta cigaba dayi kamar zata doke shi. Tana fafin.
  "Wata kila acikin su akwai wacce ta kulo. Wani abu tazo ta mallake min shi na shiga uku, a rabani da dana ta cuce ni."

  Washe gari. Ahmad ne tsaye ya juya baya yana daukar abu a gefen TVn dakin su.
  Sanye yake da bakin wando sai brown din riga. Daga baya ma kadai yayi kyau bare kuma ya juyo. Sai tashin kamshi yake.

  Na'ima kanwar sa ce tafito daga cikin gidan da gudu tana fadin.
  "Yayah "

  Da sauri ya juyo dai dai karasowar Mamin su falon tare da kanin sa Ibrahim.

  Kasa Na'ima tayi da kai. Ta ce,
  "Yaya munga abun alheri angode."

  Ta karasa fada tana dariya, Mami ta kalle shi ta ce.
  "Allah ya shi albarka, Allah saka da alheri."

  Ahmad da tin da suka shigo dakin yakke kallon su, ya ce,

  "Na meye haka?"
  Mami ta ce.,
  "Honda da ka siya musu."

  Ido ya dage ya ce,
  "Af ai hakuri zakuyi ma tukkuna saboda akwai kudaden da nake jira da zarar sun samu insha Allahu za kuyi farin ciki sosai."

  Ya karasa maganar cikin nutsuwa da murmushi dauke a fuskar sa.

  Na'ima tsalle tayi ta rumgume Mamin su. Dady ne ya fito daga cikin yana kallon su.

  Kafin ya ce,
  "Yana nake ganin annushuwa haka lafiyaa?"

  Mami ta ce,
  "Kai kuwa, dan Albarka."

  Ta nuna Ahmad. Kallon sa Dady yayi, ya ce,
  "Me?"

  "Motoci ya siyawa kannen nasa."
  Dady yayi murmushi ya ce,
  "Ai jeep yaso siya nace A'ah ya siyi kasa kasa *dai dai ruwa dai dai tsaki.* "

  Ibrahim ya ce,
  "Ai Dady da ka bari ya siya mana Jeep din nan ai babbar harka tafi "

  Mami ta ce,
  "Kaji gaskiya."

  Dady yai murmushi ya ce,
  "A'ah. Wannan don ma tayi."

  Mami ta ce,
  "Ai Alhaji ai da an siyi jeep din nan da naa karaa nunawa yan unguwar nan babbancin mu tsakanin mu dasu."

  STORY CONTINUES BELOW
  Sallamar Amina ita ta tsayar da Mami daga maganar da take yi.

  Sanye take da pink din less riga da zani saai Hijab har kawa Ash kala.

  Amsa mata su Dady sukai ta karaso cikin falon.
  Durkusawa tayi, ta gaishe da Mami da Dady.
  Wani kallo Ahmad ya bi ta dashi tinda ta shigo har ta durkusa ya kasa dauke idon sa daga gare ta.

  Murmushi kan fuskar sa ya dadu. Haka nan farin cikin da yake ciki ya ninku wanda hakan ya nuna a kan fuskar sa.

  Ya ce,
  "Mami, Dady kun gane ta ai?"

  Mami ta kirkiri mirmushi yake wanda da ka kalle ta kasan be kai zuci ba.

  Ta ce,
  "Eh!"

  Dady kuwa dakuwa yai masa, ya ce,
  "Kwal uban ka. Mun san ta mana. Yarinyar bata yin sati sai tazo gaishe mu a gidan nan. Shiyasa ma ni nake son ayi kokari ayi auren nan da wuri. Saboda halayan ta masu kyau ne."

  Dakin duk murmushin suke na yabon da Dady yayi wa Amina. Amman banda Mami da Naima da suka hade rai suna ta buntsure buntsure.

  Dariya Ahmad yayi, yai cikin gidan da sauri.

  Dady ya sami gu ya zauna. Mami kuma ta matso gun Amina ta ce,
  "Naji ance mazajen kauyen ku sun kamu da hauka ko?"

  Kai Amina ta dago da sauri tana kallon Mami. Kai ta girgiza,
  tai magana cikin sanyi. Ta ce,
  "Ni ban taba jin wannan labarin ba."

  Mami ta ce,
  "Kinga kuwa ya faru.

  Dady ne ya ce,
  "Hajiya."

  Dagowa tayi ta ce,
  "Na'am."

  Da yatsa ya nuna ta ya ce,
  " *Ki fadi alheri ko kiyi shiru* "

  Mami ta ce,
  "Alhaji maganar nan ba karya gaskiya ne."

  Dady cikin fada ya ce,
  "Ni dai na ce, *Ki fadi alheri ko kiyi shiru* wacce irin mata ce ke ne. A'ah!"

  Mami ita ma ta hayayako ta ce,
  "To zance na gaskiya bari kaji bazan taba bari dana yaje ya aure matar da ta fito daga garin mahauka ta ba."

  Ta fada tana dage hanci. Ibrahim da Dady kallon ta suke.

  Ahmad dake kiran ta shi yasa ta amsa tayi ciki.


  Mami da sauri ta karasa gun Ahmad ta ce,
  "Ya ya?"

  "Kaya ne na ajiye kuma ban gani ba. Har da kudaden da nazo dasu."

  Mami ta ce
  "To ai kaine da ajiyar wasarai rai. Na kwashe su na adana maka."

  Sarka da ta gani a hannun sa shi ya maida hankalin ta ga hannun nasa.

  "Lah Mami daman kayan zan hada mata da wannan sarkar."
  Ahmad ya fada.

  Mami ta ce,
  "Wannan yarinyar. Wannan gold din sai ka bawa wannan yarinyar yar matsiya ta ai bata san darajar ta ba. Gwanda ka siya mata yar dari da hamsin ko ta dari biyu ma tayi tsada da yawa."

  Ta sa hannu ta amshi sarkar. Ahmad ya ce,
  "Haba Mami irin dadewar da mukai da ita ai ta cancanci haka. Kuma yau gashi na dawo Dady yana fadan irin kular da take daku kinga dan na bata wannan ai ba wani abu bane."

  Mami ta ce,
  "Duk mutumin da besan darajar abu ba in aka bashi wasarai rai zai yi."

  Ahmad ya ce,
  "Haba Mami dan Allah ki bari ko sarkar na baya."

  Mami ta kalle shi ta ce
  "To ba dai wannan ba. Kajini ai ba dai wannan ba."

  Tayi ciki ta barshi tsaye kamar zai yi kuka.

  Falon ya nufa, ya zauna daga gefen ta. A hankali ya rada mata akan tazo su fita.

  Mikewa tayi, ta ce,
  "Dady ni zan tafi sai anjima."

  Dady ne ya maida kan sa gare ta ya ce,
  "Tin yanzu kuma. To nagode ki gaida Maman taki."

  Ya zura hannu a aljihu ya zaro kudi. Ahmad ya kalla ya ce,
  "Ingo ka bata ta hau mota."

  Amsa yayi yana godiya. Itama godiyar tayi ta fita. Bayan ta yabi Dady ya bisu da kallo. Ganin ba tsarabar ta a hannun Ahmad yasa Dady ya Kira shi.

  Dawowa yayi ya ce,
  "Ahmad me ka kawo mata ne?"

  "Dady na manta kayan ta ne?"
  Dady ya kalle shi ya ce,
  "Kamar ya ka manta kayan ta ne. Bayan ka nuna minsu "

  "Uhmm uhmm daman Mami. Ta hada dasu bata sani ba kuma ta bayar."

  Kai Dady ya girgiza ya ce,
  "To yanzu ya kenan?"

  "Eh zan biya na siya mata wasu ne."
  Kai Dady ya gyada ya ce,
  "Shikenan Allah yayi albarka. ga wannan ka siya musu kayan abinci."

  Kai Ahmad ya girgiza ya ce,
  "A'ah Dady na siya musu. Nima yanzu a barni na samu ladan."

  Murmushin jin dadi Dady yayi, ya ce,
  "To Allah yasa albarka."

  Ya fice yana jin nishadi. A bakin kofa ya hange ta. Motar sa ya dauko yayi inda take da ita.

  Yana zuwa ya fito ya bude mata ta shiga sannan ya rufe ya koma mazaunin sa.

  Sai da suka fita daga cikin gidan sannan ya faka motar ya tsaya kallon ta.

  Dagowa tayi ta kalle shi ta ce,
  "Lafiya?"

  Murmushi yayi ya ce,
  "Kin canja. Ki kara zama beauty fiye da da. Ga wani haske da kayi ga kiba duk ke ka dai."

  Fuska ta rufe da tafin hannun ta ta ce,
  "Yanzu banda tsokana ai kai ne kayi haka. Bani ba."

  Ajiyar zuciya ya sauke, ya ce,
  "Gaskiya nayi kewar ki. Dan haka nan kusa zamuyi aure dan na huce kewar da nayi da hujja koo?"

  Fuska ta rufe tana murmushin jin kunya. Dariya yayi ya tada mota suka tafi.

  Mami ce zaune a falo cikin shiga ta *kasaita.* ta sanya wani farin less wanda a kalla kudin sa zai yi dubu saba'in.+

  Ta sha kwalliya an zuba gold hannu da wuya da kunne. Gaban ta lemo ne.
  Dady ne zaune a gefen ta. Yana sanye da farar shadda ya saka yar ciki da babbar riga.

  Dakin sai tashin kamshi yake, Mami ce ta kalle shi ta ce,
  "Alhaji kasan abinda kake son ya faru bazai faru ba. Dan *ba dani ba sa lallen kaza.* Ahmad dai ni na haife shi, kuma bazai taba yiyuwa abar shi yayi abinda yake son yayi ba."

  Tsaki Dady yayi ya ce,
  "Ahmad dan mune gaba daya,  ya kamata ki san lokaci ya canja. Ahmad ba karamin yaro bane da za a tilasta masa auren wacce baya son ya aura. Ya mallaki hankalin kaan sa. Kuma ni da sanin da nai miki yarinyar nan in tazo kina haba haba da ita, kina kaunar ta kwasam yanzu sai naga kin canja. Meyasa?"

  Mami ta ce,
  "To ai dole ne in canja tinda na riga na jiyo labarin zuri'ar su *Mayu ne,* Matsiya ta yan kauye, bazai taba yiyuwa ba bana kaunar yarinyar nan kwata kwata na *tsane ta.*  bana kaunar *zuri'ar su* kuma bazai taba yiyuwa mu hada zuri'a da su ba *mayu* bazai yiyu ba."

  Dady ya ce,
  Kinga wannan zargin da kike bashi da asali bare tushe."

  "Ai kuwa shi keda asali. Dan dana ya fita turai yai karatu shine wasu *kauyawan* banza zasu so to ce auna so,  *talakawa* dan su tatse shi. A'ah su mallake mun 'da bazai yiyuba wallahi.."
  Mami ta fada cikin fada tana dadaga kai.

  Wani kallo Dady yake mata dan ba karamin bata masa rai ba.
  Dady mutumin kirki ne wanda ya dauki *talaka da me kudi* duk daya.

  Ran sa a bace, ya ce,
  "wato dai in na fuskan ce ki kina kin auren nan saboda dai *talakawa* ne ko babu *wayewa* tattare dasu kuma basu da *kudi.* Haka ne?"

  "Kwarai kuwa haka ne."
  Mami ta abashi amsa.

  Dady ya ce,
  "To in be aure ta ba fada min wa kike son ya aura."

  "Haba Alhaji ga yan mata nan barkatai. Idan har baza ka iya zabar masa ba ka bar shi ya huta ya zabi wacce yake so ko kuma ni na zabar masa."

  Dady ya ce,
  "Kinga kiji *tsoron Allah* a cikin al amuran ki. Saboda tunanin ki ya fara sawa kina wuce *gona da iri*  "

  "Hmm!"
  Mami taja nimfashi kafin ta ce,
  "Kai dai tunanin ka be kai inda nawa yake ba. Dan ni nawa tunanin ya wuce inda kake tunani,"
  Kallon ta yayi, ya ce,
  "mene amfanin auren yayan masu kudin. Auren yar gidan  mutumci da tarbiyya shi ake kwadayi ba auren abun duniya ba. A abinda zakiyi alfahari da jikokin ki shi zakina hanga."

  Mikewa Mami tayi ta kalle shi sama da kasa ta bar wajen.

  Kallo ya bita dashi yana girgiza kai.
  "Allah ya shirye ki."

  Ya fada yana kurbar lemon gaban sa.

  Washe gari. Na'ima da Ibrahim na compound din gidan a zaune suna hira wata mota ce ta shigo gida
  STORY CONTINUES BELOW
  Kallo suka bi motar dashi. Wata yarinya ce, ta fito daga gidan baya.

  Alamar driver ne ya kawo ta dan sai da yazo ya bude mata sannan ta fito.

  Tana sanye da riga da wando, sai mayafi da ta sakala a wuya, kanta ba dan kwali sai gashin da aka kara mata ya zubo har gadon bayan ta.

  Ta fente fuskar ta da kwalliya kamar aljanna sai taunar cingom take daga kallon ta kaga kalar karuwai ko da batayi dasu za a hadasu.

  Wajen Na'ima ta karaso, ido Na'ima ta saka da hanci tana kallon ta.

  Sai da ta karaso gun ta ta gane ta. Da sauri ta mike tana rumgume ta.

  Kuka ta sakarwa Na'ima tana cewa,
  "Ina Mami take ina mami take?"

  "Ai Mami ta fita menene?"
  Kuka ta kara fashewa dashi ta ce,
  "Ba Ahmad bane."

  "Ya Ahmad kuma me yayi miki Zuwaira."
  Ibrahim da ke zaune ya turo baki ya saki tsaki.

  Mikewa tayi ta kama hannun ta suka shiga ciki.

  Suna zama a falo, ta kamo hannun ta, ta ce,
  "Haba Zuwaira indai maganar Ya Ahmad ne ki kwantar da hankalin ki. Ki daina sa damuwa aranki ai Ya Anmad kamar kin aure shi ne kin gama. Indai Mami na gidan kika ga baki aure shi ba sai dai Mami bata numfashi."

  Janta tayi jikin ta tana lallashin ta ta ce,
  "Kiyi hakiri."

  "Bayan dashi nake kwana dashi nake tashi wallahi na gama matowa akan son sa. Shine kadai wanda nake burin aure dan Allah ku taimaka min."

  "Yi hkuri yi hkuri."
  "Kuma Dadyn ku baya sona naga."

  Na'ima ta ce,
  "To mene na damuwa bayan ga wacce ragamar gidan ke hannun ta nan. Ita ke sawa take hanawa fa. Akwai wanda ya isa ya hanaki auren Ya Ahmad ne. Inda Mami na gidan nan ba wanda ya isa ya hana ki auren sa."

  Ta jata jikin ta tana bubuga bayan ta. Ibrahim da ke tsaye akan su tana jin duk abinda take fadi ya ce,
  "Ke zuwaira kike ko me? In kukan jini zakiyi sai dai kiyi amman Ya Ahmad yafi karfin ki yarinyar kirki me hankali da ilimi zai aura ba irin ki ba. Ba wai irin ki ba."

  Na'ima ta ce,
  "Haba Ibrahim! Haba Ibrahim! Wannan irin magan kake mara ddin ji. Yarinya na kuka kai da zaka lallashe ta sai kara tunzura ta kake."

  Ciki ya shige, ya ce,
  "Oho dai inda aure na Ya Ahmad bazai aure ta ba."
  *******-
  Mami na gani ta dau mota ta fita. Tafiyar sa'a daya da rabi tayi naga ta gangara wani dan karamin jeji.

  Motar ta ajiye ta fito ta daba a kafa dan ba hanyar mota daga ciyayi sai bishiyu a hanya.

  Nan ma tayi tafiyar akalla minti goma sannan ta karasa wajen.

  Wani mutun na gani zaune kansa ya tara gashi kamar wanda aka saka masa.

  Idanun sa a waje jikin sa sanye da wasu jajayen kaya, sai layoyi da duk suka rufe masa jiki.

  In banda wari ba abinda yake yi. Haka nan dattin jikin sa bazaka taba tunanin yana wanka ba.

  "Cuncun barun bun. Cuncun barun bun!"
  Shine abinda naji yana fada.

  Mami ce ta karaso wajen. Ihu tayi dan tasan kaidar sa ce ba aimasa sallama.

  Kuma ba a zuwa wanjen sa da tsarki sai ya zamo kana da janaba baka wanke ta ba ko ka gama haila bakai tsarki ba zaka je gun sa.

  Zama tayi, ta koro masa duk abinda take bukata. Dube duben su na yayi ya ce,
  "Wannan aikin nada wahalar gaske. Dan yarinyar ba a zaune take ba. Akwai tsari a jikin ta kuma bata wasa da sallah da addu'a."

  "Haka ne Burun kun. Amman addu'ar da takeyi ba wata ta arziki ba ce addu'a suke ita da maman ta dan su mallaki dana. Su mallaki kuma dukiyar sa. Shiyasa nake son ayi kokari a raba su kawai gaba daya auren ma ya lalalce. Yanzu ana maganar kai kudi shine nake son maganar ka tayi."
  "Cuncin burun bun. Cuncin burun bun."
  Sannan ya maida kallon sa gare ta ya kwalkele da datiya. Irin dariyar da Ma'aiki (SAW) ya haramta yin ta.  ya ce,
  "Aljanu na suna iyai min komai. Amman nakasa me yawan addu'a da me tsarki ba abu ne me sauki ba."

  Mami ta ce,
  "To yanzu ya zamuyi ni so nake kawai maganar auren ta lalace."

  "Cuncin barun bun. Cuncin barun bun."
  Ya sake fada tare da kallon Mami ya mika mata wani kullin magani ya ce,
  "ki barnada a motar da za'a je kai kudin aure."

  "Toh!"
  Ta fada
  Tsawa ya daka mata, ya ce,
  "Tashi ki tafi."
  Da saurin ta mike ta bar wajen. Motar ta ta dauka ta tafi gida da gudun gaske.

  Washe gari ta fito da kullin maganin duk tabi motocin gidan ta barbade su.

  Motoci ne guda bakwai a ajiye amman duk sai da ta barbada musu magungunan.

  Tana gamawa tayi cikin gida tana kulli maganin ta suke. A zanin ta.
  Bayan minti biyar Dady ya fito, tare da kannen sa Baba Basiru da Baba illiyasu.

  Drivern shi ya gani durkushe a wajen engine mota yana tabawa.

  Kallon sa yayi ya ce,
  "Ya akayi naga kana gyara mota. Muda zamu fita."

  Dagowa drivern yayi ya ce,
  "Eh wallahi jiya duk na gama komai amman yanzu nazo tada ta takiyi."

  "Takiyi?"
  Dady ya tambaya.

  "Eh takiyi.
  "To rufe muje waccan."

  "Ai Alhaji dukka motocin nan ba ta hawa. duk sun ki tashi."

  "Battery ne ko menene wai?"
  Ya tamabya.

  "Wallahi Alhaji ban sani ba."
  "To ka rufe motar ka kira bakanike ya duba su."

  Mami dake ta saman bene tana jin duk abinda ake murna take kamar ta fasa ihu dan dadi.

  Dady ne ya kalli kannen sa, ya ce,
  "Basiru Tinda munyi niyyar yin wannan abun muje mu hau Napep."+

  Ido Mami ta zaro tana satali a hankali.

  Waje suka yi inda Mami tai saurin dauko mayafi ta fito
  Da gudu ma ta karasa gun bokan ta.

  Tana fada masa abinda ke faruwa. Kuka ta saka masa.

  "Dan Allah kar ka bar tafiyar nan ta yiyu. Dan wallahi sun dau hanya."

  Tsafe tsafen sa yayi sannan ya dubeta.

  Yace,
  "Kar ki damu!"

  Sanin halin aiaikin bokan ta yasa hankalin ta ya kwanta.

  Gida ta tafintana jiran me zai je ya dawo.
  Su Dady na tafe cikin Napep kamar daga sama sai wani abu yazo ya tsaya a hanya abinda ya sa mai tukun kaucewa dan kar a hakala.

  Wannan yasa sukai wani karamin hatsari a gun.

  Asibiti aka tafi da drivern da yake shi kadai ne ya samu rauni.

  Dady ya kalli yan uwan sa ya ce,
  "Kuje ku kai su. ni zan karasa gidan su Amina."

  Ganin halin da yake ciki yasa Dady fasa zuwan gidan su Amina suka tafi aisibiti tare.

  Haka da su Dady suka dawo aka fada mata.

  Sosai tayi murna. Ahmad kuwa duk hankalin sa atashe dan shi ya fiso nan dan wani lokaci suyi aure su huta.

  Bayan kwana biyu, Mami taje kasuwar sabon gari.

  Wata dattijuwar mata ce ta ganta ta ce,
  "Ah hajiya! Ina kwana?"

  "Lafiya lou."
  Mami ta amsa da shi.

  "Ina gajiya?"
  Matar ta tambaye ta.

  "Lafiya."
  Matar ta Ce,
  "Wallahi tin da abin ya faru na kasa nutsuwa nazo nai.muku jaje."

  "Nutsuwa. Nutsuwa fa kika ce a ina zakiga an nutsu ai *Mayu* basu ba samun nutsuwa. Kuma ki fadawa yar ki ta fita daga hanyar dana dan anga yana da kudi,"
  Mami ta fada cikin fada.

  Matar ce ta ce,
  "Nayi mamakin jin wannan furucin daga bakin ki, kin bani mamaki baki kama da masu wannan abun ba."

  Mami ta ce,
  "Eh bakin nacin yar ki da takewa dana shi ya kawo wannan abinda na fadawa yar ki yafi karfin yar ki. tinda wuri ki fada mata taje can tanemi mijin aure."
  tayi gaba ta bar matar a tsaye.
  Wani gidan kasa ne wanda yake dauke da dakuna uku, sai bandaki da kitchen da dan madai daicin sakar gida.

  Gidan fes dashi an share shi ya sharu ko ina fes dashi. Amina ce zaune akan tabar ma.

  wannan matar da suka rabu da Mami ita ta shigo Da sauri Amina ta mike ta taro ta tana amsar kayan hannun ta, ta ce,
  "Sannu Mama."

  Da yauwah ta aamsa, tana kallon yar tata.

  Kallo daya yar taiwa uwar tasan ba lafiya ba.

  Kallon mahaifiyar tata tayi ta ce,
  "Mama lafiya kuwa?"

  STORY CONTINUES BELOW

  "Ina lafiya. Amina"

  "Mami me ya faru?"
  "Maman Ahmad na gamu da ita a kasuwa, bakiga gori ba da gorin talausci da tai mana ba."

  "Amman dai Mama bata zage ki ba ko?"

  Mama ta ce,
  "Ba gwara zagi da cin mutuncin da tai mana ba. Cewa tai fa mu *mayu ne* "
  "Mayu"
  Amina ta maimaita.

  "Sannan ta ce dan ta da kike so ba dan Allah kike son sa ba dan haka ki fitar mata daga harka da ki rabu dashi kinji."

  " *Innalillahi wainna illahir rajiun* ni nasan za arina."

  "Allah ka dube mu. Ni dai na fada miki wannan al amarin a barwa Allah. Mu dage da addu'a Allah zaba mafi alheri. In Ahmad mijin ki ne Allah ya baki shi in ba mijin. Ki bane Allah ya zaba mafi alheri."

  Kai Amina take gyadawa ta ce,
  "Mama zan yi aiki da duk abinda kika ce, amman wallahi ni ina son Ya Ahmad. Bazan iya rayuwa ba shi ba."

  Mama ta ce,
  "To shikenan sai kici gaba da addu'a Allah zaba mana mafi alheri."

  "Ameen!"
  Amina ta hade kai da gwiwa.

  Baba Basiru da Baba illiyasu ne zaune a bayan gari.
  Baba Basiru ya ce,
  "Malam illiyasu, hajiya ta shanya mu a rana."

  Baba illiyasu ya ce,
  "Ga wannan ranar sai kodar mu take yi."

  "To gani na zo."
  Mami ta fada tana shawo kwana. Kallon su take daya bayan daga daga sama zuwa kasa. kallon raini. Kafin ta fara magana. Ta ce.

  "Abinda yasa nace ku zo nan ku jira ni. Wani aiki nake aon kuyi min."

  "Aiki kuma wane irin aiki Hajiya?"
  Baba Basiru ya tambaya.

  Murmushi tayi ta zaro kudi daga cikin jakar ta. Bandir din yan dubu dubu guda biyu.

  Mika musu tayi kowa daya.  Kallon ta suka tsaya yai.

  Ta ce,
  "Amshi mana!"

  Hannu na karkarwa ya amsa. Shima dayan haka.

  Mami tace,
  "Wannan kudin da na baku dubu dari dari akwai wani aiki da zakuyi min akan shi. Sanin kan kune na *tsane* ta bana son auren nan. Shine nake son ku samu dan uwan ku wato mahaifin shi ku masa bayani na illar da yake son ya kulla na wannan auren. Ina son kuce duk abinda yake faru akan auren yarinyar nan da wannan yaron ya nace akan sai ayi ne. ku nuna masa babu alheri a ciki. Kungane me nake nufi."

  "Hajiya indai wannan ne babu matsala."
  Baba Basiru ya fada

  "In kuwa har hakan ya faru akwai dadi akan wannan."
  Mami ta fada tana yin gaba.

  Baba illiyasu ne ya kira ta da Hajiya!"

  Juyowa tayi, ta ce,
  "Hajiya dan Allah Hajiya *hakar ki zata cimma ruwa insha Allahu* kar kiji komai insha Allahu. Kamar ma ba ayi ba kamar anyi ruwa an dauke."

  Tafiya tayi tana me jin dadi.

  Da yamma Baba Basiru da Baba Illiyasu suka je wajen Dady.

  Suna zaune a falo Dasu da su da Ahmad sai Mami.

  Baba Basiru shi ya fara magana ya ce,
  "Wato shi aure ibada ne, kuma ba wanda ya isa ya hana hakan."

  Baba illiyasu ya ce,
  "Babu shi."

  Baba Basiru ya ce,
  "Amman sai dai abin dubawa ne, akwai hatsari."

  Baba illiyasu ya ce,
  "Babba ma kuwa."

  Dady dake kallon su cikin duhu ya ce,
  "Menene kuma abin hatsari a cikin wannan abun."

  Baba illiyasu ya ce,
  "Akan abun Ahmad man. Tin yaushe ake ta wannan al amarin amman yaki yiyuwa. Ai a fasa shi kawai kowa ya huta wallahi."

  Dady ya ce,
  "To naji yanzu ya kuke so ayi."

  Baba Basiru ya ce,
  "Kawai afasa kowa ya huta."

  Dady ya hada rai ya ce,
  "Hakan ba meyiyuwa bane gaba daya."

  Kallon juna su Baba basiru da Baba illiyasu suka yi.

  "Ba me yiyuwa bane."
  Dady ya maimaita.

  Mami ta ce.
  "Ai kuwa wannan abi ya ishemu ishara.duk abubuwan da suka faruwa bacin muna gani ai ya kamata ace an hakura."

  Ta fada tana dauke kai. Kai Dady ya girgiza.
  "Wannan abu sai ya faru dai. Amman bashi da wani sila da zancen aure na."
  Ahmad ya fada.

  Baba Basiru ne ya ce,
  "Kai yaro kake baka san komai ba. A lokacin da zamuje wannan waje motocin gidan nan kaf kin aiki sukai, duk da bamu hakura ba sai fashi munje mun hau napep amman sai hatsari da mukayo. Na uku aka sake rana sai aka aiko mana yarinyar bata da lafiya. Wanda ya kai har yanzu tana nan kwance a gadon asibiti bata tashi ba. Ina abu irin wannan. Daga in za a wani ba lafiya dai wani abu ya faru."

  Tinda yake magana Baba illiyasu da Mami ke gyada kai alamar sun yadda da batun nasa.

  Yana gama magana, Baba illiyasu ya ce,
  "Abu ai abin tsoro ne duk ranar da muka sa zamu gidan sai wani abu mara dadi ya faru. To in bai da alaka da wannan abun me yasa hakan ke faruwa."

  Daddy ransa yai mugun bacci ya kalle su ya ce,
  "Ku saurare ni. Abinda 'dana yake so. Nima shi nake so, ku babu wanda ya isa ya canja ra'ayi na akan wannan abun babu."

  Baba Basiru ya ce,
  "To bari mu gaya maka wallahi tallahi wannnan auren mun cire hannun mu, ba ruwan mu."

  Baba illiyasu ya ce,
  "Alhaji sai kuma muga yadda za ai auren nan ba da hannun mu aciki ba."

  Ahmad ya kalle su ya ce,
  "Kawu al'amarin naku ne suke ban mammaki. Jiya jiyan nan fa kuka bar gidan nan kuna goyan bayan wannan al amarin. Amman I am wonder yau kun dawo kuna wasu maganganu. Abin yana ban mamaki."
  Yai maganar cikin sanyi da nutsuwa dan abin ya daure masa kai.

  Baba Basiru ne ya zaro ido ya fara masa fada ya ce,
  "Kai kai kul kai mana rashin kunya mu iyayen ka ne. Muna magana kana sa mana baki sai na faffasa maka baki marar kunyar banza marar kunyar wofi,"

  Mikewa Ahmad yayi ya abar dakin

  Magana suka cigaba dayi inda Dady yai shiru be tofa musu komai ba.

  Bayan Sati biyu*


  Zaune take a tsakar gidan su wanda yake da yalwar iska. Gashi a share dashi ko ina tab.


  Tana sanye da bakar atampa wacce akai mata adon ja ajiki.


  An mata dinkin riga da siket dinkin yai mata kyau ya zauna a jikin ta kamar dan ita akayi.


  Fuskar ta ba kwalliya daga kwalli sai hoda da man lebe.

  "Assalamu Alaikum!"

  Taji ana sallama daga bakin kofa.


  Mikewa tayi ta amsa salmar da

  "Wa'alaikum salam."


  Tare da daukar hijab din ta ta zira saboda jin namiji ke sallamar.


  Lekawa soron tayi, Ibrahim ta gani. Murmushi tayi ta ce,

  "A'ah! Ibrahim kai ne."


  "Wallahi nine!"

  Ibrahim ya fada.


  "Bismillah ta nuna masa tabarmar da take kai.

  Karasawa yayi ya zauna.


  "Ina yini?"

  Ya gaishe ta.


  Amsawa tayi da

  "Lafiya. Ina gajiya?"


  "Lafiya."

  "Yasu Hajiya da Dady?"


  "Suna nan kalou. Daman nace bari na kawo miki wanan yan kayayakin ne."

  "Allah sarki. Ba kwa gajiya Allah ubangiji ya saka muku da alheri."


  "Ameen Ameen Ai ba komai an zama daya."

  Mama ce ta fito daga bandaki tayo wajen su.


  Tana fadin

  "Ibrahim ne a gidan namu."


  "Eh wallahi nine mama."

  "Sannu da zuwa."


  "Yauwah Mama ina yini?"

  "Lafiya lou."


  Suka amsa cikin girmamawa. Har tana tambayar yasu hajiya da Alhaji duk yace suna lpy.

  Amina ce ta tura mata ledo jin da Ibrahim ya kawo. Ta ce,

  "Mama kinga kayan da ya kawo min."


  Mama ta ce,

  "A'ah ah ah. Toh. Ibrahim bakwa gajiya dai. Angode Allah kara arziki."


  Ta fada tana yin cikin daki. Amsawa yayi da Ameen,

  "To ka gaida su Hajiya da Alhajin."

  Mama ta fada.


  "Zasu ji insha Allahu."

  Ibrahim ya bata amsa.


  Hira suka dinga yi da Amina yana bata labarin irin abubuwan da Ahmad ya tana dar mata.


  Ita dai in banda murmushi ba abinda take.


  Ya jima a gidan dan anan ma yaci abincin rana. Sai bayan La'asar yai musu sallama ya tafi,


  Mama na ta saka masa albarka da yi musu addu'a.


  Mami ce zaune a falo sanye da atampa super. Tayi kwalliya kamar yadda ya zame mata jiki.


  Ahmad ne zaune a kujerar dake facing tata.


  Sanye yake da bakin wando sai riga green kala, mai dogon hannu.


  Fuskar sa tayi kyau gashin kansa a kwance haka na sahen sa ma.


  Sai kamshi yake. Hannun sa sanye da agogon azurfa kamar yadda yatsan sa ma yake sanye dashi.


  STORY CONTINUES BELOW

  Mami ce ta kalle shi ta ce,

  "Nace ka rabu da yarinyar nan ka shafawa kan ka lafiya. Saboda na fuskanci cikin auren nan naku akwai hatsari mai girman gaske, indai har ka nace cewar sai ka aure ta."


  Ahmad ne ya fara magana cikin nutsuwa duk dan ya fahimtar da Mamin sa.

  "Mami menene dalilin da yasa bakya son in aure yarinyar nan,"


  Mami ta ce,

  "Yarinyar nan ko kadan ba sa'ar auren ka bace, ni nafi son ace ka auri yarinyar da duk garin nan za'a san cewa ka auri mace amman ba wannan zuri'ar mayun ba. Kuma na fison wacce zaka aura ka auro wacce zatai min biyayya."


  Ahmad ya ce,

  "Mami nifa Aminan nan tafiye min duk wata mace da kike gani. Babu macen da nake so ko inga na aura fiye da ita."


  "Saboda wannan 'yar mayun 'yar kauye, 'yar talakan kake wani cewa babu wacce ta kai ta agurin ka. Tafi kowa amman ga alama fa asirin su na mayu yayi tasiri akan ka."


  Kai Ahmad yake girgizawa dan sam maganar da Mami ke fadi ba ya son ta. Ya ce,

  "Mami wane irin asiri yadda nake son ta tsakani da Allah itama haka take so na. Mami yarinyar nan zaki fi kowa jin dadin zama da ita. Haka nan yarinyar akwai hankali nutsuwa da tarbiyya. ga ilimi arabi da bokon."


  "Rufe min baki shashashan banza. Kai ware ca. Duk ya'yan da nake samo maka yawanci ba a kasar nan sukai karatu ba. Ita kuwan fa. A makarantar gwamnati ce sai kuma F.C.E shine zaka hada ta dasu. Ko kana son kace min tafi su duk da hakan."


  "Mami baza ki gane bane. Ba anan abin yake ba Mami sai kiga dan makarantar gwamnatin da ba'a kula dashi ba yafi dan makarantar kudin kokari abin a kwakwalwa yake. Kuma nasan kika zauna da Amina sai kin sota fiye da yadda kike zato. Kuma Mami ni wadan da kike cewa naje gun su duk banga abinda suke da shi na wayewar addini da ilimin zamanin ba sai shashanci gaba dayan su. "

  "Ah lallai kamanta ni wace agurin ka, amman hakan ya tabbatar min da cewar, bazan iya lamunta ko in yadda da abinda kake kokarin yi ba."

  Mami ta karasa maganar tana mikewa ta bar masa dakin.

  kallo ya bita dashi yana girgiza kai. Zamewa yayi yana tunanin farkon haduwar sa da Amina.

  A lokacin da yake SS 3 ne, wata rana yana zaune a gida yaji yana son ya zagaya gari.


  Cikin gida ya koma ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin farin wando sai jar riga mai dogon hannu.

  In ka kalle shi kai kayi zaton babban mutum ne. Mota ya dau hanya.

  A titi ya yanke shawara inda zai je. Nan. Sabuwar gando yayi gidan wani abokin sa da yake yawan zuwa gun sa.


  A bakin gate yai parking ya dauki waya ya kira sa.


  Kafin fitowar sa ne, yake kalle kalen unguwar kamar ance daga kai ya hango ta sanye da katon hijab din ta har kasa.


  Kallon ta ya tsaya yi, "masha Allah"


  Ya furta afili be sam ma ya furta ba. Duk da tana da karamcin shekaru a lokacin dan daga kallo yasan bata wuce shekara goma sha uku ba zuwa sha uku zuwa sha hudu ba.


  Amma shi duk da haka yarinyar ta burge shi dan gaskiya a area su babu yan mata ko yara da yake gani cikin irin wannan shigar,


  Wanda shi kuma a duniya ba shigar da yafi so kamar ta. Dan ko agida in ya matsawa Ni'ima tayi shigar Mami hanata take.


  To yanzu ma abinda yaja hankalin sa gare ta kenan duk da in kyau ne akwai shi dan daga kallo daya ya gane bafula tana ce.


  Dan yadda tsarin jikin ta da farin ta yanayin ta hadi da kyan ta sun nunar masa da hakan.


  Ganin zata bace masa yasa ya dira daga kan motar da yake zaune.


  Bin bayan ta yayi har ya kamo ta.

  "Assalamu Alaikum!"


  Yai mata sallama wanda hakan yasa sauran kadan ta zura a guje dan ita ba a tabai mata irin haka ba.


  "Ina kuma zaki nai miki sallama baki amsa min ba."

  juyowa tayi ta bayyana dan ta firgita.


  Wani kyakyawan saurayi agaban ta yasa ta tsaya kallon sa.


  Murmushi Ahmad yayi ya ce,

  "Baki amsa min sallamar ba fa."


  Kasa tayi da kanta alamar jin kunya. Magana yayi ya ce,

  "Kuma nasan kinsan darajar amsa sallama ko?"


  Kai ta gyada masa sannan ta amsa,

  "Wa'alaikum salam."


  Muryar ta da yaji har sai da ya lumshe ido dan dadi.


  Kallon sa ta tsaya yi

  "Duk da ya rufe idon sa amman me kyau ne"


  Ta fada a fili tana tunanin azuciya ta fada. Idon sa ya bude ya ce,

  "Ai kinfini kyau."


  Baki ta rufe da hannu tayi gaba abin ta. Binta yayi da sauri ya ce,

  "Haba yar kwanta ina kuma zaki?"


  Juyowa tayi jin ya kirata da kanwar sa.  Kai ta dauke, ta ce,

  "Mama ce ta aiken ga yamma tayi sauri nake."


  Tayi gaba. Binta ya karayi ya ce,

  "To ai kya tsaya na raka ki ko?"


  Juyowa tayi a razane ta ce,

  "Ni tab a'ah dan a ganni da kai ace min yar iska ina kula maza. Bayan Mama ta ce min duk wanda ke kula maza a hanya kallon dan iska ake masa."


  Murmushi yayi ya girgiza kai ya ce,

  "To shikenan sai kin dawo."


  Da sauri ta bar wajen. A wajen ya tsaya har ta dawo amman bata ganshi ba. A baya abaya ya dinga binta har ta shige gidan su.


  Ya jima tsaye akofar gidan dan ya tabbatar da gidan su din ne.


  Ganin bata fito ba yasa ya koma wajen motar sa. Agun ya samu Kamilu abokin nasa.


  Kallon sa Kamilu yayi ya ce,

  "Ya ina kaje ne?"


  Murmushi yayi ya ce,

  "Wallahi wata yarinya na gani ta burge ni nabi bayan ta."


  "A ina take?"

  Kamilu ya tambaya


  Gidan ya gwada masa. Murmushi kamilu yayi ya ce,

  "Haba friend ni na zata wata babba ce."


  Murmushi shima yayi ya ce

  "Sai akace maka kuma son ta nake. Nace ta burgeni."


  "Haka ne yarinyar ba wanda bata burgewa a unguwar nan. Komai da ake son ga uwa ta gari ta samu. Sai dai rashin wadata dan talakawa ne. Mahaifin ta ya rasu Maman ta sai ita aikatau take samun na makarantar ta da na abinda zasu ci. Gidan nan shi kadai ne gatan su, tarbiyar yarinyar tasa kowa Yaya  take kiran sa da tasan sa da bata san shi ba. Haka nan gaisuwa sai dai bata ga mutun ba."


  Kai Ahmad yake jin jinawa jin bayan ko wacce Amina.


  Yarinyar ta bashi tausayi jin tarihin rayuwar ta.

  Tinda Ahmad ya tafi gida ya kasa sukuni shi dai so yake yasan wa wane hali zai taimakawa Amina.

  Yadda yaga rana haka ya ga dare dan da asuba har ya riga Dady fitowa.

  Abin da ya bawa Dady mamaki kenan yasan kuma ba lafiya ba tinda yaga haka.
  Washe gari da safe bayan sun gama kari suka shirya suka fita shi da Dady kasancewar ranar asabar ce ba skul.

  Sai da suka isa office sannan Dady ya kira sunan sa.
  "Ahmad!"

  "Na'am!"
  Ahmad ya amsa, idon sa duk sun fada.

  "Ahmad me yake damun ka. Yanzu kana da damuwar da zaka boye min."

  Kai Ahmad ya girgiza, Dady ya ce,
  "To indai haka ne fada min abinda yake damun ka."

  Kasa Ahmad yayi da kai, kafin ya ce,
  "Dady wata mata ce na samu labarin halin rashin da suke ciki shine abin yake damuna."

  Murmushi Dady yayi ya ce,
  "Yanzu mene abin damuwa anan. Ai fada zakayi kawai ayi duka abinda kake bukata. Ba ka zauna ka boye abu aranka ba. Wannan ba shine gatan da zakai musu ba."

  "Haka ne Dady."
  Ahmad ya fada.

  "To me kake bukatar ai musu?"
  Dady ya tamabaya.

  "Dady ni gani nake a basu kayan abinci me yawa da jarin kudi wanda zata na juyawa."

  "Haka za'ayi 'dana Allah maka albarka. Allah ya hore maka nasan jama'a zasuji dadin ka."
  ATM din sa ya muka masa yace
  "ka dau mota ta kaje ka siya musu kayan abinci da duk abinda ya kamata."

  Amsa Ahmad yayi yana masa godiya kai ka rantse shi ya bawa kudin nan kyauta.

  Motar ya dauka ya wuce sahad store.  Ba abinda be daukar musu na kayan masarufi ba. Dan komai biyar biyar ya dinga diba.

  Shinkafa buhu biyar tafiya ma haka macaroni cuscus, semovita, kalan din man gyada da man ja. Gishiri magi onga. Dukka.

  Ciki ya shiga yana zabar atamfofin sai da ya dibi kala ashirin da biyar sai lesses da shadodi. Kamar wanda aka de ya juya ya hangi wajen kayan kwalliya.

  Da sauri ya karasa wajen ya dinga jidar mata kayan kwalliya masu kyau da tsada.

  Sai da ya jidi iya yin sa ya debar mata turare da sure da under wears sannan ya je ya biya kudi bayan ya siya musu lemuka da ice cream.

  A wata mota aka loda kayan dan yawan su. Daga nan gidan su Amina kawai ya nufa.

  Sallama yayi aka amsa masa. Mama ce ta fito dan ita kadai ce agidan Amina ta tafi Tahfiz.

  Ganin Ahmad ta ce,
  "Shigo bawan Allah."

  Shiga cikin soron yayi ya gaishe ta cikin girmamawa ya ce,
  "Mama daman kaya ne aka kawo."

  "Kaya kuma?"
  "Eh!"
  Ya bata amsa.

  "Mama in sun zuba mayi maganar "
  "To ta nuna masa wani daki da ba komai aciki ya zuba kayan.

  Sai da suka gama tsaf ya biyasu sannan ya leka dakin wanda ya cika da yake dakin ba wani babba bane.

  Tabarma Mama ta shimfida masa ya zauna. Kara gaisawa sukai.
  Sannan Ahmad ya ce.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Mama nasan baki sanni ba, sai dai kiyi hakuri. Jiya ne nazo layin ku, shine naga Aminatu,"

  Nan dai ya kwashe komai ya gaya mata. Ya daura da fadin
  "Mama halin da aka fadan kuna ciki ya tsaya min a raina. Inda har na kasa bacci sai da takai mahaifina ya gane shine ya tambayen na fada masa. Wannan kayan da kika gani shi ya ban kudi in kawo muku."

  Yana gama bayani ya mike ya zaro kudi a aljihun sa, ya mika mata.

  "Wannan kuma ya ce ki ja jari."
  Ya mika mata ya ce,
  "To sai anjima."

  "Zo nan 'dan nan."
  Dawowa yayi ya durkusa a gaban ta.

  Kuka ta fashe dashi da sauri ya dago ya ce,
  "Haba Mama dan Allah kiyi hakuri, in na bata muki rai kiyi hakuri bazan kuma ba amman wannan kiyi hakuri ki amsa."

  "Ba haka bane 'dan nan ganin ban san ka ba Allah ya aiko ka dan ka tallafi rayuwar mu. Yanzu duk wannan namu ne, amman mungode Allah ubangiji ya muku tukwici da gidan aljanna. Banda bakin godiya gareku sai dai zan kasance kullum cikin yi muku addu'a har karshen rayuwa ta."

  Ta kuma fashewa da kuka, Ahmad da duk jikin sa ya kara sanyi yai kasa da murya ya ce,
  "Mama kukan ku na daga min hankali dan Allah ki daina. Kiyi murna ta wani fannin amman ba ta wannan ba. Kinji dan Allah ki daina kuka."

  Shiru tayi ta goge hawayen idon ta ce.
  "Na daina 'dan nan na daina. Ya sunan ka?"

  Mrmushi Ahmad yayi, ya ce,
  "Sunana Ahmad!"

  "Masha Allah Ahmad suna me dadi Allah yayi albarka ka nagode."

  Mikewa yayi ya ce,
  "Ni zan tafi sai wani.lokacin a gaida min da Amina."

  "To nagode nagode."
  Zata fito kenan ya ce
  "Aah Mama ki koma.nagode haka."

  "To shikenan."
  Ta koma ta zauna tana tunanin da man akwai irin wadan nan mutanen a duniya.

  Lallai ta tabbata duk wanda ya riki addu'a bazai tabe ba dan addu'a basa gajiya da yin ta ita da 'yar ta Amina.

  Ahamd na fita ya tafi office din Dady, Dady ya kalle shi ya ce,
  "Son har ka dawo."

  "Eh Dady. Kaga alert ko?"
  Kai Dady ya daga masa ya ce,

  "Na gani komai dai yayi ko, ko akwai bukatar da'di."

  "A'ah Dady in akwai zan sanar maka."

  "To zo ka tayani hada wannan takardun nan."
  Mikewa Ahmad yayi ya yi wajen yana hada masa su.
  Ahmad be jima da fita ba Amina ta dawo. Tana sanye da sky blue din riga da wando da hijab har gwiwa.

  Kayan a wanke a goge fes fes dasu. Ta shigo gidan da sallama. tin da ta shigo taga canji a wajen Mama.

  Kallon Mama tayi ta ce
  "Mama lafiya?"

  Murmushin kan fuskar Mama ne ya dadu, ta ce,
  "Amina zo kiga."

  Ta janyo hannun Amina. Dakin da suka jibge kayan ta nuna mata. Ido Amina ta bude fuska dauke da mamaki.

  "Mama wannan fa?"
  ta tambaya tana nuna kayan.

  Mama ta ce,
  "Wasu bayin Allah muka samu wadan da
  Suka kawo mana. Tukunna ma jiya da wane yaro kuka hadu baki gaya min ba"

  Tsoro ya kama Amina dan tasan halin Mahaifiyar tata bata son mu'amalar ta da maza. Wannan yasa tai tsuru tsuru tana tuna abinda ya faru jiya.

  Shirun da Amina tayi yasa ta gane a halin da take. Dan haka ta dakatar da Ita daga tunanin da take. Ta ce,

  "Yaron ne ya ji labarin mu abin ya dameshi shine mahaifin sa ya bashi kudi ya kawo kayan nan kinga kayan da har da jarin dubu dari."

  Kuka Amina ta fashe dashi ta ce,
  "Mama wallahi ni ban kula shi dan Allah Mama kiyi hakuri wallahi ki tambaya bana kula kowa a waje."

  "Kar ki damu Amina duk ya fada min abinda ya faru jiya da yadda kukai. Ki cigaba da kare kan ki da mutuncin ki. Allah miki albarka ya baki miji na gari."
  Hawayen Amina ta goge ta ce,

  "Mama nagode."
  Mama ta ce,
  "Yaron yana da hankali da nutsuwa ga tarbiyya suma Allah ya saka musu alheri ubangiji Allah yadda suka mana Allah musu fiye da haka. Ameen!"

  "Ameen!"
  Amina ma ta amsa da shi.

  Dubu daya Mama ta dauko, ta mikawa Amina ta ce,
  "Karbi kije ki siyo kayan miya ki sauri ki dawo kinji."

  Kayan jikin ta ta cire ta dauko kayan gida ta saka.

  Sannan ta fito ta amsa ta tafi cefane.

  Wannan dalilin shi yasa a ko da yaushe Ahmad kan zuwa gida duba Mama sai dai kullum in zai zo Amina bata nan.

  Amman kayan kwalliyar ta da kayan zaki na yara da yasan zata bukata duk zai kawo mata.

  A bangaren Ahmad ba karamin son ganin ta yake ba sai dai duk lokacin da zai zo da safe ko da yamma duk bata dawo ba.

  Dan in da safe ne, ranar makaranta ta tafi makaranta. in kuwa week end ne tin bakwai da rabi shima take tafiya. In ta dawo da yamma ta tafi makaranta. Haka alhamis da juma'a suma karfe biyu take tafiya makaranta.

  Wannan yasa basa haduwa sai dai sai dai kullum ya ce a gaishe da ita duk da tsanin son ganin ta da yake yi.

  Ta fanin Amina ma tana son ganin wannan bawan Allah da yake mata hidima shi da Maman ta.

  Kullum ta tashi sai tai masa addu'a haka nan kullum sai tayi tunanin wannan da ya tsayar da ita.

  Rayuwar da suke ciki ta tsanani ta kau ta dalilin Ahmad.

  Wanda shakuwa tai zurfi tsakanin Mama da Ahmad dan in yazo gidan shi ke taya ta aiki.

  Haka nan cefane duk tare suke har girki ma tare suke yi.

  In kaga Ahmad da Mama sai kayi tunanin ita ce mahaifiyar sa duk da Mamin sa ma na son sa. Dan duk cikin ya'yan ta tafi son sa.

  *Bismillahir Rahamanir Rahim*

  *Yanzu fa sai kunyi hakuri. Ba lokaci saboda makaranta.*
  *Nagode*
  Yau tinda  Amina ta dawo daga isilamiyya da yamma ta dawo da zazzabi wanda har washe gari da shi ta farka.

  Wanda hakan ya hana ta zuwa makaranta.
  Tana kwance a daki rufe cikin bargo bayan Mama tabata panedol ta sha.

  Mama na waje tana gyaran gidan bayan ta share gidan.

  Kayan Wanke wanke ta hada, ta dauko ruwa zata wanke.

  Dai dai shigowar Ahmad sanye yake da bakin wando da hakar riga sai tabarau dake idon sa.

  Kafar sa sanye da sau ciki da safa hannun sa daure da agogon azurfa. Tsintsiyar hannun sa gashi kwance kasancewar rigar me gajeren hannu ce. Farar fatar sa ta fito tai kyau da sheki.

  Mama na ganin sa ta mike tana masa murmushi, ta ce,
  "A'ah Ahmadu kai ne!"

  Murmushi yayi ya durkusa, ya ce,
  "Ina kwana Mama?"

  "Lafiya lou!"
  Ta amsa masa.

  Tana tambayar sa ya gida dasu Maman sa da Alhaji.

  Duk suna lafiya ya bata amsa da. Wajen kayan wanke wanken ya karasa yana cewa,
  "Mama wanke wanken za ayi ne?"

  "Eh Ahmad dan Allah ka bari kar ka bata jikin ka."

  "Haba dai Mama mene dan na bata jiki na."
  Ya zauna yana wanke mata kayan wanke wanken yana yi suna hira abinsu.

  Sai da ya gama tsab sannan ya koma kan tabarma ya zauna kusa da Mama.

  Kallon Mama yayi ya ce
  "Mama yau ba dumame ne?"

  Murmushi Mama tayi, ta ce,
  "Bari na dauko maka a daki na ajiye maka. Na manta kuma."

  Ta mike ta kawo masa. Ya zauna yana ci sai da ya gama ya kora da ruwan sanyi.

  Hira suke tabawa yana bata labarin karatun da zai tafi. Mama tai shiru dan ba karamin kewar sa ta tabbata zatayi ba.

  Suna zaune Amina ta fito da sauri daga daki bakin rariyar gidan ta matsa tana kwara mai.

  Da sauri Ahmad ya mike yayi gun ta yana mata sannu tana gamawa ya mika mata ruwa a buta ta wanke wajen.

  A hanakali ta mike tayo kan tambarma ba tare da ta lura da wanda ya bata ruwan ba.

  Jikin Mama taje ta kwanta, jikin ta zafi radau. Wajen ya wanke sannan ya koma kan tabarmar.

  A gefen su ya zauna ya kalli Mama ya ce,
  "Mama bata da lafiya ne?"

  Kai Mama ta daga masa ta ce,
  "Wallahi tin jiya da ya dawo daga makaranta."

  "Kuma ba kuje asibiti ba?"
  Ya tambaya.

  Mama ta ce
  "Ai tasha penedol.zazzabi ke damun ta."

  Jikin ta ya taba yaji zafi radau kamar wuta. Ido ya zaro ya janye hannun sa da sauri.

  STORY CONTINUES BELOW

  Ya ce,
  "Ku tashi muje asibiti."
  Mama ta ce,
  "Da ka bari anjima zan mika ta wancan sha ka tafin."

  "Haba Mama dan Allah ku taso."
  Amina da ke jikin Mama ta bude ido a hankali ta kalle shi.

  Shima ita yake kalla, da sauri ta rufe idon dan gani take kamar a mafarkin da ta saba ganin sa ne.

  Maganar sa ita ta janyo da hankalin ta,
  "Mama ku tashi
  ."

  Ya fada yana mika mata hijabn su da ya dauko a daki.

  Amsa Mama tayi, ta ce,
  "Ahmad ka dai ka nace ko."

  "To Mama tayaya zata abar ta da ciwo a jiki."

  Amsa tayi ta saka ta sawa Amina. Sannan ta daga ta a hankali suka fita.

  Bayan ya saka su a mota ya koma ya rufe gidan suka tafi.

  *MANS* Clinic suka wuce kai tsaya inda suke amsar magani suma in basu da lafiya.

  Suna zuwa ma'aikatan asibitin suka amshe ta.

  Test din tyhoid da maleria suka inda nan da nan aka dau jinin ta aka duba.

  A resullt din ta ya nuna tana fama da zazzabin cizon sauro dan haka nan wanda yasa ruwan jikin ta kunewa.

  Karin ruwa akai mata leda uku, wanda tin da aka saka mata take bacci.

  Sai bayan azahar ta farka dai dai lokacin ruwan ya kare.

  Sai da ta dan huta sannan Ahmad ya shigo da kula a hannu.

  Abinci ya kawo musu shinkafa da miyar kaji sai lemo da ruwa.

  Kallon sa take tinda ya shigo dakin.
  Gefen ta ya matsa ya ce,
  "Kanwata kin tashi ya jikin?"

  Kasa tayi da kai tana wasa da yatsu ta ce,
  "Da sauki."

  Mama ta kalla ta ce,
  "Mama zanyi Sallah."

  Daga ta Mama tayi ta taimaka mata ta kai ta bandakin dake cikin dakin.

  Alwala tayi ta fito tai sallah. Ahmad ne ya matsa kusa da ita ya zuba mata abinci.

  Mika mata yayi gaban ta. Kin dauka tayi sai da ya ce,
  "Kici mana!"

  Sannan ta ja. kadan taci tace ta koshi. Maganin ta ya dauko ya bata tasha.

  Ranar dai a asibiti suka kwana dan da dare ma shi ya kawo musu abinci.

  Be bar asibiti ba sai wajen sha dayan dare sannan ya koma gida da tausayin Amina dan ji yake kamar shine be da lafiya.

  Ko bacci kasa yi yayi, Ya rasa me yasa yake damuwa da al amuran Amina. Dan a duk sanda yaga tana cikin wani hali hankalin sa baya kwanciyya in har ba ya fitar da ita  ba.

  Wannan yasa yake tuhumar kansa da mene hakan. Yakan halakanta hakan da tausayin ta da yake ji.

  Dan shi a rayuwa be san wani kunci ko babu ba kuma hakan besa ya kasa gane halin da mara sa shi ke ciki ba wannan yake taimakawa duk wanda ya gani a cikin wani hali.
  Bai taba tausayawa wani kamar yadda yake tausaya wa Amina ba. Yana jin damuwar Amina kamar tasa ce.

  Da ya ga ya kasa bacci sai ya tashi ya shiga bandaki ya dauro alwala, ya tada sallah.

  Washe gari da safafe ya shiga kitchen yasa a hada masa break.

  Wanka ya koma yayi ya shirya cikin Farar riga ke dogon Hannu sai Bakin wando. Sandal ya saka ya fita yayi kitchen.
  Break din da ya saka a hada masa ya amsa ya shiga cikin wata 4matic  da Ya nufi asibiti.

  Lokacin da yake Amina na bacci sai Mami dake gefen ta a zaune.

  Shiga dakin yayi da sallama ya durkusa ya gaishe ta ya tambayi ta me jiki.

  Abincin ya turawa Mama. Yace,
  "Ga wannan!"

  Mama ta ce,
  "Ahmad baka dai gajiya ko Allah ubangiji yai maka albarka. Allah ya raba ka da iyayen ka lafiya Allah daura ka akan abinda kake nema."

  "Ameen!"
  Ya amsa ta dashi ya ta shi ya kalli Amina ya ce,
  "Bata tashi bane?"

  "Eh tinda tai sallah."
  "Ok bari naje gun.likita naji ya jikin nata."

  Ya fita. Yayi office, bayan sun gaisa me yake Tambayar likita jikin Amina,

  Likita ya ce masa jikin da sauki sai dai rashin gwari har yanzu zuwa anjima dai zasu duba suga ya jikin ko zasu basu sallama.

  Da haka suka rabu dashi. Yana komawa daki yaga ta tashi.

  Da kansa ya hado mata break ya zauna yana bata har ta koshi.

  Ragowar ta yaci sannan ya zauna suna hira jifa jifa.

  Sai yamma aka sallame su inda daga nan Ya zarce dasu store yai musu siyayya. Daga nan yai gida dasu yai musu sallamar sai gobe.

  Ranar yaji dadin ta dan ya yini da Amina duk da ba magana suke ba amman shi dai yan jin dadin kasancewar da sukayi a tare.

  Washe gari sai da suka tafi office tare da Dady sannan yake fadawa Dady rashin lafiyar Amina.+


  Dady ya tausaya mata dan yasan halin dan nashi akwai tausayi shima.


  Daga office ya fadawa Dady zai je duba Aminan Kudi Dady ya bashi ya ce, ya sai mata kayan dubiya.


  Yadda Dady ya ce yayi haka yai lokacin da yaje tana tsakar gida a zaune, gaban ta robar nono amman taki sha ita sai me sanyi.


  Ahmad ne ya shiga ya same ta tana fushi.


  Mama ya gaisar yai mata ya me jiki.


  Mama ta ce,

  "Me jiki yayi kyau gashi nan tana daru ma,"


  "Darun me kuma?"

  Ahmad ya tambaya.


  "Wai sai mai sanyi zata sha bayan tasan halin jikin ta be san sanyi yanzu zata fara mura."


  "To Aminatu kinji abinda Mama ta ce, kiyi hakuri ni nai miki alkawarin in kin warke zan kawo miki mai sanyi kinga lokacin sai ki jinya daya ba biyu ba ko?"


  Hararar sa tayi, a ranta ta ce, au yafi so ma nayi jinyar kenan,"


  Ganin bata ji dadin abinda ya fada ba dan yasan da zatai murmushi yasa, ya ce,


  "Mama ga wannan inji Dady sai dai har da kayan sanyi a ciki gashi an hana ta sha."


  Mama ta ce,

  "Ai kuwa bazata sha ba,"


  Jin ance kayan sanyi yasa Amina matsowa kusa da Ahmad ta rada masa akunne, ta ce,

  "Dan Allah kasa ta bani kayi hakuri kaji."


  Dagowa yayi ya kalle ta. wani abu yake ji wannan yasa yai saurin kawar da kansa.


  Kallon Mama yayi ya ce,

  "Mama ayi hakuri a bata ice cream din ta sha. Dan narke wa zai yi. Insha Allahu bazai mura ba."


  Ya fada. Girgiza kai Mama tayi ta mika mata ledar amsa tayi ta bude ta dauki roba daya ta fara sha.


  Gaskiya ba abinda zata ce ga Ahmad sai godiya dan  ba karamin gata yake mata ba.


  Ba abinda dan me kudi zai nuna mata a cima.


  Ranar tare suka yini dan har dare tare suka ci abincin dare dana rana.


  Duk zaman da sukai Amina bata kula shi sai satar kallon juna da suke.


  Sai bayan tafiyar sa mama ta kalli Amina ta ce,

  "Amina me yasa bakya kula Yayan ki duk da yana son miki magana naga ke kike share shi."


  Fuska Amina ta marai raice ta ce,

  "Mama ba kice kika ce ba kyau kula maza ba."


  Kai Mama ta gyada mata ta ce,

  "Amman wannan ai a gida ne, kuma ai bazai cutar dake ba. Kina gaishe shi in ya tambaye ki abu kina bashi amsa kinji ko?"


  Kai ta gyada mata. Mama ta ce,

  "To tashi kije ki alwala ki kwanta."

  mikewa Tayi ta fita.


  Washe gari da ta kama ranar asabar dan haka tahfiz zata amman saboda tayi fashi yasa bata da shirin tafiya.


  Tana zaune bayan ta gama taya Mama gyara gidan ta dauko alkur'anin ta tana ta bitar inda za'a karba dan bata samu damar yi ba.


  Ahmad ya shigo gidan da sallama. Mama ce ta amsa masa ya karaso.


  STORY CONTINUES BELOW

  Yana sanye da Milk din shadda. Kansa ba hula sai gashin kan sa dake ta sheki a kwance gwanin sha'awa.


  Mama ya gaisar sannan ya zauna, a hankali Amina ta ce,

  "Ina kwana?"


  Amsawa yayi da

  "Lafiya!"


  Yana kallon ta tai kasa da kai kamar ba ita ta gaishe shi ba.


  Mama ta dube ta ta ce

  "Mama wannan ayar zaki biya min."


  Ahmad dake zaune ya amshi Alkur'anin ya ce

  "Haddar ake yi."


  Ta ce,

  "Eh!"


  Ya ce,

  "To bari kiji yadda zaki nayin ta. Ki dauko carbi duk aya daya ki karanta adadin carbin kafin kigama zakiga kin iya."


  Kai ta gyada ta mike ta dauko carbi. Haka ya dinga kara mata tana yin yadda ya ce, nan da nan cikin kankanin lokaci ta kammala karantawar.


  Zuwa azahar har ta kammala iyawa. Jin dadin bitar da yai mata yasa bayan sunyi sallahar azahar sun ci abinci ta dauko jakar ta makaranta.


  Wani maths ne da chemistry take son ya koya mata dan dama tana neman wanda zai koya mata.


  Tana daukowa nan Da nan ya koya mata cikin sauki ta gane.

  To fa tin daga ranar shakuwa ta shiga tsakanin Amina da Ahmad.


  Dan har dare yake kaiwa agidan dan ya koya mata abinda bata gane ba.


  Kullum suna tare komai zatayi shi take tambaya shawara ta maida shi dai yayan ta.


  Haka nan shima da ita yake shawara komai tare suke. Dan dayawa ba wanda be san Amina da Ahmad ba.


  Duk da lokacin Amina na da shekara goma sha hudu shi kuma Ahmad na da shekara Ashirin da data.


  Yana biyewa duk wani shirmen ta haka duk abinda ta nuna tana so ko ya gane tana so zai siyo mata.


  Amina bata da matsalar komai. komai Ahmad ya dauki nauyin sa.


  Haka in tana gida zai zo suyi wanke wanke tare tai daura girki yai mata shara ko ta na wanke toilet yana yin wani abin.


  In wankin ne tare suke yana saba mata. Tana yin na biyu sannan ya dauraye ta shanya.


  Duk da shi baya yin nasa saidai ai masa. wanda suma yaso haka Mama ta ce a'ah hakan ma Allah saka da alheri


  Ahmad da Amina sun shakuwar da sam basa son rabuwa da juna basa taba yin awa goma sha biyu basu ga juna su ba.


  Dady yasan kullun Ahmad na gidan su Amina shi Dady yana zaton soyayya suke.


  Inda Mami bata san inda yake zuwa ba fadan tana tunanin suna tare da mahaifinsa.


  A kalla sunyi shekara da sanin juna inda shakuwar su ta kara karfin.


  A kuma dai dai lokacin lafiyar Ahmad waje karatu ya fito.


  Da farko ya fadawa Dady ya fasa fita waje saboda Amina.


  Dady ya yadda sai dai Mami da ta dire tace lallai sai ya tafi.


  Mami irin matan nan ne mafada ta wadan da suka kyamaci talaka.


  Dan da farko data ga Amina cikin shiga me kyau ta so ta. Sai da taji labarin su sannan ta juya musu baya.


  Inda Dady tinda ya ganta ya yaba da halin ta. Ya kuma aminta da dansa ya cigaba da basu kulawa iya bakin yadda zasu iya.


  Na'ima kanwar Ahmad ce me bi masa halayar Mama kaf ta dauko ga rowa da kyamar talaka ga isa da izza.


  Wanda Ahmad da kanin sa autan su suka dauko halayar Dady.


  Dady mutun ne mai addini da ilimi arabi da boko akwai son taimakawa marasa shi akwai tausayi abin hannun sa be rufe masa ido ba.


  Duk inda yaga mabukaci sai ya taimaka masa. Haka nan mutum ne mai saukin kai da hakuri.


  Wannan halaiyar tasa ba wacce Ahmad ya baro.


  Da farko sunan Dady Muhammad. Mahaifiyar Dady. Shi kadai ta haifa dan su Baba Basiru da Baba ililiyasu yayan kishiyar mana sa ne.


  Maman sa ta rasu tin yana karami ba karamar wahala yasha gun kishiyoyin Maman sa ba.


  Wanda a lokacin suke kada shi makaranta duk dan kada ya zauna a gida wanda kuma basu san gata suke masa ba.


  Su a tunanin su mugunta suke masa. Sai da ya kammmala Secondary aka dauki nauyin karatu sa a kasar waje sannan hankali Su ya tashi.

  shiyasa ake cewa, *In zaka gina ramin mugunta ka gina shi dai dai kai*


  Dady be tashi dawowa ba sai da yayi har master din shi dan yana gama degree ya fara aiki sannan ya cigaba da karatu.


  Inda bai tashi dawowa ba sai da yasan ya tanadi abun da yake bukata.


  Yana dawowa ya samu aiki a wani kamfani inda mai kamfanin mutumin kirki ne ya dauki Dady Kamar 'dan cikin sa.


  Wannan yasa ya bashi yar sa Bilkisu wato Mami ya aure ta.


  Ahmad shine dansu na fari sai Na'ima sai Ibrahim shikenan.


  Duk abinda Mami ta ce bata so to sai ta san yadda tayi ta batar dashi.

  To yanzu ma da taji bayanin Ahmad nason fasa tafiya tai tsalle ta Dire kan dole sai ya tafi.

  Ahmad da yake yaro me hankali da bin maganar iyaye, wannan yasa ya dauki kaddarar Allah ya fara shirin tafiya.

  Lokacin da Amina taji labarin tafiyar ba karamin tashin hankali ta shiga ba.

  Ta damu matuka kamar yadda Ahmad ma ya damu duk suna halakan ta haka da sabo da junan da sukai.

  Lokacin da tafiyar sa ta tashi kuwa kuka ta dinga yi.

  Ahmad da Mama ne ke lallashin ta. Dan shima karfin hali kawai yake yi.

  Amina kuwa, kuka sosai duk ta tada hankalin ta.

  A haka Ahmad ya tafi ya bar Mama da Amina cikin wani hali.

  Duk da ya damka amanar Su a wajen Dady.

  Ahmad ya je lafiya inda ya bar wa su Mama wayar da zasu na gaisawa.

  Wannan shi ya dan ragewa Amina kadaicin da take ciki.
  Dady be bar komai daga kulawar da Ahmad yake musu ba.
  Har dadi yake musu duk da bashi yake kai musu ba sai dai ya aika.

  Shakuwar su Amina da Ahmad kuwa ta kara yawa.

  Inda kullum sai sun sha waya kamar ba gobe. Da safe da rana da yamma duk suna makale da juna.

  Ko tana makaranta Allah, Allah take ta dawo su hadu.

  Haka nan duk lokacin da Amina ta samu lokaci sai taje gaida Dady.

  Dady na matukar jin dadi banda Mami da take jin haushin ta dan tin da taga tana shige musu take tunanin akwai wani abu tsakanin su da Ahmad.

  Duk da daga Ahmad har Dady ba wanda  ya fada mata wani abu. Amman ita tasan tabbas akwai wani abu aboye.

  Duk lokacin da Amina taje gidan in Dady baya nan sai Mami ta bata mata rai. Hakan be taba sa tasa abin a ranta ba.

  Duk saboda abinda Dady da Ya Ahmad sukai mata yafi karfin ta wulakanta ta. Wannan yasa take ganin girman Mami ita ma.

  Na'ima kanwar Ahmad ma duk abinda taga Mami nayi shi take dauka tayi. Duk da shekarun su kusan daya ne.

  Yau tin asuba ta tashi da wani irin ciwon ciki wanda bata taba yin kamar sa ba.

  Mama ta firgita da ciwon cikin da take. Dan ita Amina ta ce cikin tane ke ciwo.

  Suna zaune bayan mama ta bata kanwa Amina na kwance tana ta juyi Ahmad ya kira a waya.

  Bayan Mama ta gaisa da Ahmad ne, yake tambayar ta Amina.

  Kallon Amina ta yi kafin ta ce,
  "Gata nan ba lafiya."

  STORY CONTINUES BELOW
  "Ba lafiya Mama me yake damun ta. Ince kunje asibiti dai."
  Yai maganar cikin tashin hankali.

  Kai Mama ta kada alamar 'A'ah' kafin ya ce,
  "Ba muje ba na bata kanwa dai."

  Tini hankalin Ahmad ya tashi wayar ya kashe ya kira abokin sa Auwal kan yaje ya dauki su Amina yakai asibiti.

  Sannan ya kira Dr Usman ya ce yanzu za'a kawo masa patient ya duba ta dan Allah zai kira yaji kome ne akwai.

  Sannan ya kara kiran Mama ya ce,
  "Mama ga Auwal nan zai zo kaiku asibiti yanzu ku shirya"

  Ya kashe wayar kafin Mama ta ce
  "A'ah."

  Dan yasan halin ta. Ko minti goma ba ai ba sai ga Auwal nan yazo.

  Aikawa yayi suka fito sai *MANS Clinic* wanda aka bude musu folder.

  Suna zuwa aka kai ta office din Dr Usman.

  Nan da nan ya mike ya fara bincike kan ta.

  Ya gano matsalar ta ciwon mara ne,  kuma da yake wannan lokacin ta fara.

  Daki yasa a basu dan ga ba karamin gala baita tayi ba.

  Maganin ya rubuta da allura ya bawa Auwal ya amso musu.

  Fitar Auwal kenan Ahmad ya kira Dr a rikice yana tambayar sa me yake damun Amina.

  Murmushi Dr yayi ya ce,
  "Kai rago ne akan Amina. Komai na ka yana tsayawa in akace Amina bata da lafiya ko tana damuwa. Anya kuwa zaka iya tabuka wani abu in kukai aure in tayi laifi."

  Shiru Ahmad yayi kafin ya ce,
  "Dr Amina kanwata ce ba budurwa ta ba."

  Murmushi yayi, ya ce,
  "Shikenan in ta fito fili maji."

  Ahmad yayi dan murmushi ya ce,
  "Please fadan abinda ke damun ta mana."

  Murmushi Dr Usman yayi, ya ce,
  "Ai nasan in har ban fada maka ba baza ka bar ni ba. Da nace bazan fada maka ba amman nasan halin ka da damuwa akan Amina kaga kuwa dole na fada maka. Amina dai ta girma ne dan ta fara menstruation ne. Shine take fama da ciwon mara."

  Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya ce,
  "To yanzu ya za'ayi ta daina yi."

  "Eh to kaga farkon yin ta ne, watakila shiyasa ta sha wahala. Duk da kuma wasu duk yi sai hakan ta faru. Maganin kuma wasu yana musu aiki wasu kuma sai dai in har sunyi aure hakan zai daina faruwa. Dan haka sai dai yanzu zan bata magani da allura insha Allahu zata samu relief."

  Kai Ahmad ya gyada cikin damuwa ya ce,
  "To me dame zata na ci."

  "Eh ta rage shan suga sannan in tanayi ta daina shan ruwan sanyi tana shan ruwan dumi, sannan tana cin abinda zai kara mata jini da lafiya a jikin ta. In marar na ciwo kuma zata na dan gasa ta sanna.."

  Sai kuma yai shiru ya ce,
  "Kai da nakewa bayani ma bayan ai baka kasar ka bari nai mata da kaina kawai."

  "A'ah!"
  yai saurin katse shi tare da cewa,
  "Dan Allah fada min zan sanar da ita da kai na."

  Murmushi Dr Usman yayi ya cigaba  da fada masa tare da bashi shawar wari. Da haka sukai sallama yana masa godiya.

  Mama ya kira ya tambaye jikin nata. Bacci ma take mama ta fada masa.

  Ko da Dr Usman yazo tai mata duk abinda zai mata anan yake sanar da Mama silar rashin lafiyar tata.

  Mama ta jinjina kai. Tana zaune sai ga Auwal nan rike da ledoji a hannu.

  Take away yayi musu sai fruit da kayan abunda zasu bukata
  Dayar ledar kuma pad ce da sabbin fantis a ciki.
  Amsa Mama tayi tana godiya kafin ta leka cikin ledar ta ajiye.

  Amina ta jima tana bacci sannan ta tashi

  Lema taji ta kasan ta wannan yasa ta taba da hannu.

  Jini ta gani tuni ta zare iso sai da tai tunani sannan ta ce,
  "Kenan na fara period."

  Mama da tashigo dakin rike da wata karamar jaka ta karaso gun ta.

  Kallon ta yi, ta ce,
  "Sannu Aminatu. Ya jikin?"

  Da sauki ta fada tana shirin saukowa daga gadon.
  "Tsaya!"
  Mama ta fada tana shiga cikin bandakin. Ruwan dumi ta hada mata, sannan ta taimaka masa ta shiga dan yin wanka.

  Zanin gadon Mama ta cire ta fita ta wanke.

  Tana shigo Amina na fitowa. Leda Mama ta mika mata tace
  "kije ki saka ai kin iya ko?"

  Leka ledar tayi, tai saurin barin dakin, ta shige bandaki.

  Pad din ta saka sannan ta fito ta saka kaya ta koma kan gado ta kwanta.

  Mama ta ce,
  "Tashi kici ci abincu kisha magani."

  Mikewa tayi dai dai shigowar Auwal hannun sa rike da fulas din shayi

  Karasowa yayi ya kuma gaida Mama ya mika mata fulas din ya ce,
  "Ahmad ya ce a kawo shi zata sha kar ta saka suga."

  Amsa Mama tayi tana masa godiya shima.

  Fita yayi bayan yai ma Amina sannu.

  Ruwan zafin tasha, wanda taji dadin shan sa. Sai abinci da taci kadan ta sha magani ta koma ta kwanta.

  Bata jima da kwanciyya ba Dr Usman ya shigo sannu yai mata yana tamabyar jikin nata.
  Ganin da sauki yace zasu iya tafiya. Auwal da ya shigo dakin ya ce,
  "Daman yanzu Ahmad ya ce wai nazo na maida ku gida."

  Kayan su ya fita da su Mama ta kamo Amina suka tafi suna wa Dr Usman godiya.
  Auwal sai da ya biya ta Yahuza suya ya siyo musu Nama da fruit sannan ya maida su gida Mama sai godiya take.
  Da dare Amina na kwance rike da mara Ahmad ya kira bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta jikin Amina ya ce a bata wayar.

  Mika mata wayar Mama tayi ta fita. Amsar wayar tayi ta amsa a hankali.

  Jin muryar ta a haka yasa ya zabura ya ce,
  "Meenah cikin ne?"

  Kai ta gyada masa, ta ce,
  "Eh!"

  A hankali.
  "Sannu Baby Meenal Allah baki lafiya. Me kika ci da daren nan."

  "Tea na sha."
  Ido ya zaro ya ce,
  "Tea?"

  Kai ta gyada kafin ta ce,
  "Eh!"

  "Innalilahi wainna illahir rajiun!"
  Ya fada yana rike kai.

  Yana da na sanin hana Dr Usman fada mata da yayi.

  Saita kansa yayi ya ce,
  "Kinga Amina ai Dr Usman ya fada miki silar ciwon naki ko? To ya fadan shara dan da zaki gujewa dan haka ki rage shan sugar nasan halin ki da shan suka ki rage kinji."

  Kai ta gyada tana jin nauyin sa yanzu Dr Usmam ya fada masa ta fara jinin haila kenan.

  Kai abin kunya wallahi yanzu ai da abin zai na kallon ta kenan.

  Anan ya dinga fada mata abubuwan da zata kiyaye yi da wanda zata nayi.

  Ke har da wanka ya koya mata. Sannan ya fada mata yadda zata na gyara jikin ta.

  Tin daga lokacin Amina take fama da ciwon mara in lokacin ta yayi.

  Ahmad kuwa da duk lokacin da yaga ta kusa farawa zai na mata tini kan ta daina shan abubuwan zaki.

  Ita har kunya take ji. Dan da lokacin yayi zai mata transper kudi yace wannan na pad ne.

  Wani lokacin ma shi kemata tini. Haka nan har gida yake sa Dr Usman yazo yai mata allura.

  Dan ba karamin wahala take sha ba. Kamar ta mutu takeji.

  Duk lokacin da Dr ya zolaye shi akan Amina yana mamaki tinda ya san wani abin haka ne, bama akan damuwa da lafiyar ta.

  Zai iya rantsewa da in Amina na ciwo shima sai ya kwanta.

  Besan me yasa ba amman yana dangarta hakan da shakuwar da sukai.

  Duk da yasan duk abinda Dr Usman yake fada masa haka ne akan damuwar da yake akan Amina.

  Wani lokacin ma jikin sa ne kawai zai bashi bata da lafiya koma da ya kira zai tabbatar da haka.

  STORY CONTINUES BELOW
  **-----**
  Tana shekara sha shida ta gama makaranta a lokacin kuma sukai sauka. Suna da haddr izufi talatin da wani abu

  A lokacin Ahmad ya aiko mata da wata babbar Waya inda akai mata installing whatsapp.

  Sosai suka chat da Amina. A lokacin ya sa ta tura masa pics dinta dan yaga yadda ta zama.

  A lokacin da ta tura masa wani da take sanye da hijab tayi murmushi dimple din ta ya lotsa.

  Fararen hakoranta suka bayyana. Idanun ta sun yi kyau.

  Lokacin da ya ga hoton kasa motsawa yayi.

  Wani yanayi na daban yaji yana shigar sa. Wanda besan ko name ne ba.

  A zuciyar sa yana jin so da tausayin Amina wanda yake jin ba abinda bazai iya kashe mata koyi mata ba dan samun farin cikin ta.

  Ya jima yana kallon hoton kasa dauke idon sa daga kallon ta. Dan shekara biyu ba wasa bace.

  Ta kara kyau da girma ta yi haske, sosai ta canja kyan ta ya kara bayyana.

  Waya ya kira ta, bayan ta dauka ya ce,
  "Aminatu kin kara kyau da girma fa."

  Ido ta rufe da tafukan hannun ta kamar yana ganin ta ta ce,
  "Kai Yaya ka fiya tsokana duk kyau na ban kai ya kai ba. Haka nan girma kuma kaima ka kara yin sa ai."

  Murmushi yayi, ya ce,
  "Meenal Result din ku ya fito ne?"

  "A'ah Yaya wani satin muke saka rai."
  "To Allah bada sa'a gashi baki jamb ba. Dan haka zan yiwa Abokina Auwal magana za ayi miki komai. zan sanar da Dady kudin registration din da transport."

  "Kai Yaya dukka kuma Dady sai yai tayi. Nagode Yaya Allah kara girma arziki da budi. Allah baka nasara akan duk abinda kasa gaba. Allah ya jagorance ka ya muku sakkaya da mafificin Alheri....."

  Katse ta yayi da sauri ya ce,
  "Haba Meenal ai an zama daya duk wannan addu'ar haka. Mun gode kema Allah miki duk abinda kika rokar mana."

  Da "Ameen!"
  Ta amsa tana murmushi daga nan suka fara hira.

  Sun jima suna hira kafin suyi sallama.
  Sabon Shakuwa ce ta kullu tsanin Ahmad da Amina.

  Sun shakun da dayan su baya boyewa dan uwan sa wata damuwar sa.
  Bayan sati biyu Result din su ya fito inda akai siya mata form n FCE zata karanci Computer science.

  Sosai take murna. Inda lokaci kadan aka kafe sunayin su, nan da nan taje akai mata screening duk tare da Ibrahim da Auwal.

  Daga screrning taje akai mata medical check up. Duk inda sukaje da layi amman da yake Dady ya hada su da wani abokin sa da sunje ake gama mata komai.

  Bayan sati biyu sai ga admission letter ta har gida Ibrahim ya kawo mata.

  Registration ma shi da auwal sukaje aukai mata.

  Ahmad da komai kamar a gaban sa ake duk yasan anayi.
  Kudi ya turowa Amina da wasu dogayen riguna yan dubai ya ce na zuwa makaranta ne.

  Driver aka ajiye mata wanda zai kaita ya dauko ta. Duka abin nan da ake Mami bata sani ba.

  Haka nan duk wata Ahmad zai turo mata da kudi haka ma Dady zai aiko mata dashi.

  Kamar yadda duk wata sai ya aiko musu da kayan abinci.

  Amina bata da damuwar komai sai ta karatun ta da ta saka gaba.

  Tana baro point me kyau dan four point wani abu take samu.

  Bata samu carry over ko wani abu. A makaranta kowa sha'awar ta yake duk da bata da kawa sai mate ayi karatu a watse.

  Yasmeen ce ta makale mata har suka kulla kawance da juna.

  Ya kai tasan Ahmad shima yasan ta. Suna yawan gaisawa. Haka nan Mama ta santa ta yaba da hankalin ta.

  Samari da dama na son Amina amman ita bata taba basu fuska dan da an mata magana zata ce tana da miji.

  In tana bawa Ahmad labarin masu damuwan ta ba karamin damuwa yake ba sai dai kullum ya ce ta daina kula kowa ta maida hankalin ta kan karatun ta.

  Duk abinda Ahmad ya fada mata shi take dauka wannan yasa bata taba kula su. In kuwa mutum ya nace zata ce an mata miji ko tana dashi.

  In kuwa tana bawa Ahmad dramar da suke da samari Ahmad kanji ransa ya baci.

  Dan daga karshe cewa yayi tana saka nikaf ita kuwa aranta bata kawo komai tsakanin ta da shi ta dauke shi a matsayin dan uwan ta ne kawai

  Ta fannin Ahmad ma haka duk da yake shima ba kula yan matan yake ba duk yadda yan mata ke damun sa.

  Suna Zaune Amina da Yasmeen. Yasmeen ta kalli Amina ta ce,
  "Meenal wallahi kun dace da yayan ki zaku haifi ya'ya kyawawa."

  Shiru Amina tai mata kafin ta ce,
  Sai kuma akace miki soyayya muke "

  Dariya Yasmeen tayi ta ce,
  "Ai shikenan tinda ke ba a jin cikin ki daga ke sai Yayan ki."

  Shiru Amina tayi duk da tasan akwai mutane da yawa da suke mata kallon soyayya tsakanin ta da Ya Ahmad.

  Tana mamaki takan ce,
  "Ai Ya Ahmad ba tsara tabbane yafi karfi na. Sai dai a 'kanwar ina ni ina Ya Ahmad."  Komentar

  Tampilkan

  No comments:

  Post a Comment

  Terkini

  +
  ?orderby=published&alt=json-in-script&callback=labelthumbs\"><\/script>");