-->
 • Jelajahi

  ;ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (1) A DALILIN MATAR UBA COMPLETE (1) A DUNIYARMU COMPLETE (2) A GIDANA COMPLETE DOC (1) A TUNANINA COMPLETE DOC (1) ABBAS COMPLETE (20) ABDULKADIR COMPLETE (4) ABDULLKADIR COMPLETE (6) ABOKIN MIJINA COMPLETE (1) ADIYYA COMPLETE (2) ADIYYAH COMPLETE (1) ADUN WASU COMPLETE (1) AGOLA COMPLETE (1) AHUMAGGAH COMPLETE (17) AJALIN SO COMPLETE (19) AKAN SO COMPLETE (1) AL (2) AL-AMARIN ZUCI COMPLETE (4) AL'KALAMINE SILA COMPLETE (2) ALMAJIRA COMPLETE DOC (2) ALMAJIRATA COMPLETE (1) AMAL COMPLETE (8) AMAREN BANA COMPLETE (8) AMARIN ZUCI COMPLETE (1) AMININ MAHAIFINA COMPLETE (17) AMJAD COMPLETE (2) ARZIQI RABO COMPLETE (3) ASHE KECE COMPLETE (1) AUREN SIRRI COMPLETE (1) AUREN SOJA COMPLETE (1) BA SONTA NAKE BA COMPLETE (16) BABBAN GIDA CHAPTER 3 MP3 (1) BABBAN GIDA COMPLETE MP3 (23) BABBAN KUSKURE COMPLETE (1) BAGIDAJIYA COMPLETE MP3 (4) BAKAR MACE COMPLETE MP3 (27) BAKIN DARE COMPLETE (5) BAƘIN DARE COMPLETE (15) BANSAN LAIFINA BA COMPLETE (2) BARIKI IYAWA COMPLETE (1) BARIKI NA FITO COMPLETE (48) BARRISTER ASAAD COMPLETE (1) BATACCEN YANAYI COMPLETE (3) BATUUL COMPLETE (24) BAYAN RAI COMPLETE DOC (1) BINTU COMPLETE DOC (1) ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (11) CAPTAIN BILAL COMPLETE DOC (1) CIWON IDANUNA COMPLETE (1) COMPLETE (1) COMPLETE DOCUMENTS (10) CONEL AHMARD COMPLETE (6) DA'IMAN COMPLETE (1) DAMATA COMPLETE MP3 (24) DAN ADAM COMPLETE (37) DAN FASHI 🔫 COMPLETE (1) DAN MINISTER COMPLETE (1) DAWUUD CHAPTER 1 (1) DAWUUD COMPLETE (10) DIYAM COMPLETE (20) DR SALEEM COMPLETE (7) DR SAMEER AMEER COMPLETE (2) EL-MUSTAPHA COMPLETE (13) FARA YAR SHEHU COMPLETE (4) FARHA COMPLETE (21) FETTA COMPLETE (31) FIRGITA SAMARI COMPLETE (1) GAMAYYAH COMPLETE (14) GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE (1) GIDAN SARAUTA COMPLETE (14) GIDAN UNCLE COMPLETE (1) GIMBIYA SA (3) GIMBIYA SA'ADIYA COMPLETE (44) GWARMAYA complete (1) H novels birnin gayu (29) HAFSAT COMPLETE (3) HARSASHEN SO COMPLETE (37) HASKE COMPLETE (27) Hausa novels (35) HIKIMA COMPLETE (10) HUTU COMPLETE (13) IGIYAR RAYUWA COMPLETE (1) IN SO YAKI NE COMPLETE (21) IT IS PART OF THE GIFT COMPLETE (6) Ita (1) ITACE QADDARATA COMPLETE (14) JALILA COMPLETE (13) JAWAHEER COMPLETE (7) JINI DAYA COMPLETE (1) JINNUL AASHIQUE COMPLETE (1) JUYIN RAYUWA COMPLETE (3) K'ADDARACE COMPLETE (14) K'ANWAR MIJINA COMPLETE (1) KADDARA KO SAKACI COMPLETE (3) KAINUWA COMPLETE (9) kANDALA COMPLETE (10) KANO TA JIDDAH COMPLETE (1) KARUWA CE COMPLETE (1) KAWU NANE COMPLETE (1) KAWUNA COMPLETE (8) KE NAKESO COMPLETE (6) KIBIYAR KADDARA COMPLETE (2) KINA RAINA COMPLETE (10) KISHIYOYINA COMPLETE (2) KIYAYYAR ZUCI COMPLETE (3) KOMA KAN MASHEKIYA COMPLETE (3) KOMAI NISAN JIFA COMPLETE (3) KUDIRI COMPLETE (9) kula da kaya (1) LOVE HER SOFTLY COMPLETE (14) MABRUKA COMPLETE DOC (1) MAEESHA COMPLETE (3) MAIRO COMPLETE (5) makaranta duniya (31) MAKIRCI KO ASIRI COMPLETE (4) MAKOTAN JUNA COMPLETE (10) MARWAN COMPLETE (3) MATACCIYAR RAYUWA COMPLETE (36) MATAR SHEIKH COMPLETE (1) MAZA {ALLURAR GUBA}💉 COMPLETE (1) MEYE ILLAR YAYA MATA COMPLETE (24) MIJIN BUZUWA COMPLETE (2) MIJIN HANEEFAH COMPLETE DOC (1) MIJIN YARINYA COMPLETE (2) MRS AMIDUD COMPLETE (12) MRS GURAJE (4) MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE (43) NANNY COMPLETE (3) NAUFAL COMPLETE (2) NAYI GUDUN GARA COMPLETE (39) NI DA PRINCE COMPLETE (19) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE (32) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE MP3 (66) RABO AJALI COMPLETE (8) RAI BIYU COMPLETE (21) RAMUWAR GAYYAH COMPLETE (6) RANA DAYA COMPLETE (3) RANAR NADAMA COMPLETE (2) RAYUWAR ASMAU COMPLETE (14) RIBAR BIYAYYAH COMPLETE (1) RIKICIN WANI GIDA COMPLETE (11) RUDI NE KO BURI COMPLETE MP3 (2) RUDINE KO BURI COMPLETE MP3 (12) RUKAYYAH YAR ALBARKA COMPLETE DOC (1) SAKAMAKO COMPLETE (10) SAMU COMPLETE (7) SAMU YAFI IYAWA COMPLETE (6) SAWUN BARAWO COMPLETE (11) SHIMFIDAR MIJINA COMPLETE (1) SILAR AJALI COMPLETE (3) SILAR GIDAN AIKI COMPLETE (30) SOORAJ COMPLETE (5) soyayyah (1) SOYAYYAH CHAPTER COMPLETE (1) SOYAYYAH COMPLETE (12) SOYAYYAR MU COMPLETE (5) TAGWAYE COMPLETE (36) TAMBARIN TALAKA COMPLETE (1) TANTIRIN NAMIJI COMPLETE (7) TARKO COMPLETE DOC (1) TARKO COMPLETE MP3 (3) TATTALINTA COMPLETE (12) TAZARAR DAKE TSAKANINMU COMPLETE (13) THE BLIND'S MONEY COMPLETE (11) THE CITY COMPLETE (6) TSANANI COMPLETE (20) TSANGAYAR MATI COMPLETE (8) TUN KAFIN AURE COMPLETE (1) TUNTUBEN HARSHE COMPLETE (4) UMARNIN SAURAYI COMPLETE (2) UMMI COMPLETE (15) UNTIL I RELLY DO COMPLETE (14) UZTAZIYA KO YAR DUNIYA COMPLETE (1) WANENE SHI COMPLETE (14) WANI AURE COMPLETE (34) Wata (1) WATA BAKWAI COMPLETE M (17) WATA FUSKA COMPLETE (15) WATA SHARI'A COMPLETE (21) YANAYIN RAYUWA COMPLETE (14) YANKAR KAUNA COMPLETE (2) YAR ALMAJIRA COMPLETE (4) YAR FULANI COMPLETE (2) YAR GWA (1) YAR MAKIYAYA CHAPTER 1 (2) YAR MAKIYAYA COMPLETE (19) YAR SADAKA COMPLETE (2) YAR SHUGABA COMPLETE (42) YAR TALLAH COMPLE (1) YARE BIYU COMPLETE DOC (1) YARIMA ASHMAN (1) YARIMA KHALEED COMPLETE (7) YARIMA SUHAIL COMPLETE DOC (1) YAZEED COMPLETE (3) ZABIN SAMHA COMPLETE (6) ZAMAN HOSTEL COMPLETE (1) ZEENAT YAR JARIDAH COMPLETE (16) ZEHRA COMPLETE (15) ZUCIYA COMPLETE (27)
  Copyright © HAUSA NOVELS
  Best Viral Premium Blogger Templates

  Iklan

  KIYAYYAR ZUCI CHAPTER A

  A/I/S
  Wednesday, 26 May 2021, 5/26/2021 01:00:00 am WIB Last Updated 2021-05-26T08:00:39Z
  masukkan script iklan disini
  masukkan script iklan disini

   KIYAYYAR ZUCI CHAPTER A


  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 📑*
                1⃣
  *__________*📖
  BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM

  cike da tashin hankali suka shigo gidan,kallon sister ta tayi ba tare da tace komai ba ta shige d'aki.Fatima ce ta zauna gefen Maama tana kallon ta ido cikin ido,ta d'au lokaci tana nazarinta daga baya ta dafa kafad'ar ta tana mai kallon fuskar ta.+

  "Maama lafiya kuwa?in dai fa akan wad'an can azzalumai ne kwara kin sa ranki a inuwa don wlhy ba zai bari ba".

  Dagon numfashi kawai taja ba tare da tace komai ba ta d'auki butar da ke kusa da ita ta fara alwala.
  girgiza ta fatima tayi tana mai fad'in
  "Maama dan Allah ki daina wannan shirun yana damu na sosai".
  tana idar da alwala taja hijabin ta akan kofa ta fara sallar la'asar.
  "Allah ka mana mai kyau Fateema tace sannan ita ma tayi d'akin.a kan gado ta tadda Hafsat tana d'an duba takardun ta,don ita yanzu matsalar gidan su da mak'obcin su bata san ya zata kwatanta shi ba,mutum ne sam bai son cigaban mahaifin su,wai kuma a haka da abokai ne,bayi da burin da ya wuce yaga sun wulakan ta.Fateema ce ta dafa ta tana fadin

  "Tunanin me kike yi"?

  Kai kawai ta girgiza don dama sam ita ba mai son hayaniya ko magana bane.

  "Ni me matsalar Alhaji Munir ne?ya fad'a mana kawai kowa ya rabu da shi".

  Rufe takardun gabanta tayi bata ce komai ba ta zame ta kwanta.

  "Hafsat"!
  Juyowa tayi tana fuskantar Fateema amma bata ce da ita komai ba.ganin kamar fateemar bata da niyar magana ya sata bata baya.

  "Kada fa kiyi bacci da la'asar nan".

  Can kasa-kasa tace

  "Ba bacci zan yi ba".

  Shiru tayi tana tunani iri iri,yanzu haka rayuwa take?sam ita sanda aka haife ta ma bata san me jin dad'in rayuwa ba,lokacin da tayi wayo ma cikin talaucin ta sami iyayen ta da 'yan uwanta,kullum cikin bakin ciki maamar su take,Allah ma dai ya takaita suna samun na rufin asiri da kyar,saboda ita makarantar ta ma uncle nata ke biya,inda fateema ta kammala degree dinta amma shiru kake ji ba mijin aure.sai younger sistern ta dake ss1.yayun ta duk sun gama karatu ba aikin yi.ita kuma yanzu ne ma take part 1inda take karanta law.

  Sake juyawa d'aya bangaren tayi tana fuskantar fateema amma idon ta na kan ceiling ta rungune hannayen ta.sam dama can ba mai son hayaniya bace da kuma shiga jama'a,in kaga ta zage akan abu to fa an kaita bango ne.

  Ganin la'asar nata wucewa ya sata mikewa tare da fita daga d'akin.bakin kofa ta tsaya inda tace
  "Maama kin sha maganin ki kuwa?

  Da kai ta amsa mata.daga nan bata kuma cewa komai ba ta dauki buta ta dauro alwala.gefen maama tayi salla daga nan kuma ta kwanta kan cinyar Maama.shafa kanta Maama take ba tare da tace uffan ba.Hannun ta ta d'aura kan na Maama tana fad'i

  "Insha Allah komai zai tafi dai-dai".

  "Da yardar Allah Hafsat mun kusa yima talauci kuka".

  Kara rike hannun Maama tayi a zuciyar ta tana rokon Allah ya kawo karshen damuwar su.

  STORY CONTINUES BELOW

  Suna cikin haka Fateema ta fito.

  "Maama me za'a daura"?

  "Kije duk abunda kika samu a kitchen d'in ku d'aura,kuma kuyi suri dan Abban ku ya kusa dawa".

  Koda ta shiga kitchen d'in abubuwan da babu su suka fi yawa,sanar ma Maama tayi amma sai tace suyi wanda ya sauwaka.hakan ce kuma ta kasance ba jimawa suka gama.

  Har bayan magrib mahaifin su bai dawo ba,hankalin su in yayi dubu to ya tashi.a haka har akayi i'sha.nan ne fa ido ya raina fata.a sannu Abdullahi first born nasu ya shigo,daga baya kuma sai Naseer.duk hankalin su a tashe yake gashi an kira layin sa bata shiga.

  Suna nan a haka har karfe takwas na dare,nan fa mazan suka fita neman sa da kuma 'yan anguwa da suka lura cewa gidan tana cikin tashin hankali.da farko police station suka je amma ba wanda ya saurare su,saboda yanzu duniya sai in kana da shi ake kula ka.haka suka cigaba da neman sa cikin garin gombe.Hafsat kasa hakuri tayi Maama da Sister Faty suna kiran ta haka ta zame jiki tayi waje da wuri.

  Da farko Fateema taso binta,sai dai kuma baza ta iya barin Maama ita kad'ai a cikin wannan hali ba.sannan kuma fitar Hafsat da dare hatsari ne kasancewar ta 'ya mace.duk abun duniya sun had'u ma Maama.da wanne d'aya zata ji?da rashin miji ko kuwa 'ya?

  Sadiya ce tace zata bita amma Maama ta hanata.don bata isa da barin yaranta mata har biyu a waje da daddaren nan ba.

  Hafsat ko da ta fita tambayar mutani take ko son ga Abban ta,amma amsar d'aya ce kowa cewa yake bai ganshi ba.gaba d'aya ta gama hada gumi sai share hawaye take a lokaci d'aya kuma tana rokon Allah da ya bayyanar mata da mahaifin ta a duk inda yake sannan cikin koshin lafiya.

  Zuwa yanzu ta gama galabaita da azabtuwa zuciyar ta zafi yake mata sannan kuma kanta ji take kamar zai bar jikin ta.

  Jiri ke nemar zubda ta da wuri ta dafe jikin gini tana ambaton sunan Allah'n da duk yazo bakin ta.amma ina duhu-duhu ta koma gani daga karshe sai gata ta fadi kasa sumemmiya.
  A bangaren su yaya ma hakan ce ta kasance sunyi nemar duniya basu same Abba ba har zuwa d'aya na dare.dawa gida suka yi tare da shaida ma Maama nan Sister Faty ke sanar musu da rashin Hafsat.

  Hankalin su ba karamin tashi yayi ba nan suka kuma fita nemar ta,ga Maama kwance hawan jinin ta na neman tashi.Saudat kanwar Hafsat banda kuka ba abunda take inda sis Faty ma hawayen take.

  Comment shi zai sa nacigaba.in ba comment no update🤷‍♀

                                    Hafciey Musa✍
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 3📑*
  *__________*📖

  Ko da suka isa asibiti kin kar'bar ta aka yi a cewar su sai an nemo d'an sanda, sosai take kara rasa jini a jikin ta amma sam ba wanda ya damu, waya Hakeela ta d'auka tare da kiran Ummanta ta sanar da ita saboda tasan in ta sanarma Maama ba karamin rud'ani zata jefa ta ciki ba, saboda jiya taji suna chigiyar Abban su sai da asuba suka same sa sannan yanzu kuma ace ta kara musu wani.

  Ba tare da 'bata lokaci ba Umma ta iso asibitin, sosai ta tausayawa Hafsat ganin halin da take ciki da kyar ta lallaɓa Likitocin suka kar'be ta ta hanyar basu cin hanci.
  STORY CONTINUES BELOW

  Emergency aka wuce da ita tare da bata kulawar gaggawa sosai ta rasa jini a jikin ta, sai dai kuma bai kai ga wanda za'a kara mata wani ba bayan an gama treating nata sai aka sa mata ruwa tare da allurar bacci sannan Likita yace ba mai iya ganin ta yanzu har sai ta farka.

  Dole Umma da Hakeela da Driver suka nemi wajen zama.

  "Umma wallahi lamarin su Hafsat sai Allah, gaba d'aya fa sun zama abun tausayi".

  Dogon numfashi umma taja sannan tace, "Allah na sane da su Hakeela, wata ran duk wannan wahalar zasu neme ta su rasa, sannan wanda yake jefa su cikin ta kuma Allah zai toni asirin sa".

  "Allah umma sun cancanci a tausaya musu, musamman Hafsat wacce bata d'auki rayuwa a bakin komai ba, sam yarinyar bata da matsala da kowa".

  "Yanzu duk ba wannan ba, kamata yayi mu kira gidan su mu sanar da su".

  "A'ah umma,ina tsoron kada hawan jinin Maama ya tashi".

  "To ya zamu yi? ko so kike muyi ta rike ta basu sani ba har hankalin su ya tashi?".

  Kai kawai ta girgiza ba tare da tace komai ba, don tasan gaskiya umma ta fad'a ba yanda zasu yi su 'boye ma iyayen ta.

  "Yanzu kuje gida ke da driver ku samo mana abinci, ni kuma zan zauna da ita sannan yanzu zan kira Maamar ta na sanar mata".

  "To" tace jikin ta a sanyaye ta wuce,
  waya Umma ta d'auka tare da fara dialing number Maama.

  ********

  Maama dake zaune a tsakiyar gida ta rabka uban tagumi ganin yau da gaske abincin ranar gagarar su yayi, gashi su ya Abdoul da suka fita nema har yanzu ba wanda ya dawo cikin su.

  Abba dake zaune a kan sallaya ya kalle ta sannan yace, "Amina".

  "Na'am ta amsa".

  "Jiki na na bani wani iftila'i zai faru damu".

  "Haba Alhaji kada kace haka komai yayi tsanani fa maganin sa Allah ne, ni da zaka bi ta shawara ta ma in yaso ko karkara sai mu koma tunda nan d'in yafi karfin mu".

  "Kul! kada ki sake irin wannan maganar, so kike karatunsu Fatima ya salwanta, sannan su Abdoul kuma karatun su ya tashi a banza?".

  "Dama ni so nake ko noma in yaso sai suyi".

  "Ko bayan rai na kika sake irin maganar nan ban yafe ba".

  "Kayi haƙu.........."

  Bata karasa ba karar wayarta ya katse ta.
  Ganin Umman Hakeela ke kira sai tayi murmushi sannan ta d'aga wayar da sallama, bayan sun gaisa sai ta saukar da muryar ta ƙasa sannan tace,

  "Maamar Abdullahi muna asibiti fa".

  "Innalillah waye ba lafiya haka? ai da kin fad'a mini da tare zamu asibitin".

  Cikin tausayawa tace,

  "Hafsat ce tayi accident yanzu haka muna asibiti".

  Hafsat! ta maimaita sanda wayar ta zame a hannun ta,
  Abba ne ya kalleta cike da kulawa sannan yace

  "Me ya faru da Maama na?"

  "Acci....den....t tayi".

  Ta karasa maganar tana hawaye, miƙewa yayi da wuri yana fad'in,

  "Dauko mayafin ki muje".

  Da wuri ta zari mayafi silifas ma daban-daban tasa.

  Allah sarki uwa!!

  Adai-daita suka tare sannan suka nufi asibiti dukkan su cikin kid'imewa.

  Suna isa asibiti Abba har mantawa yayi bai bama mai adai-dai ta kud'i ba sanda ya tambaya hakuri ya bashi sannan ya basa kud'in, Maama kam dama ko jiran sa bata yi ba tayi ciki.

  STORY CONTINUES BELOW

  Umma suka tarar zaune tasha tagumi, tana ganin su ta miƙe da wuri tare da nufar su, ko gaisuwa basu yi ba Maama tace,

  "ina Hafsat d'in?".

  "Wai ba za'a iya ganin ta yanzu ba, amma ku kwantar da hankalin ku taji sauƙi".

  "To alhamdulillah" Abba yace.

  Maama kam shiru tayi don bata yarda da batun Umma ba, suma zama suka yi suna jiran ranar farkawar ta.

  Sis Faty da yanzu dawowar ta daga makaranta taga gida wayam, waya ta dauka tare da kiran Maama don jin inda ta shiga saboda tasan bata zuwa gidan makwabta.

  Sanar da ita Maama tayi kan cewa suna asibiti Hafsat tayi accident, Cikin jimami tace tana zuwa.

  Ya Abdoul ta sanar ma sannan ya Naseer daga nan ta shige kitchen don dafa musu abinci ta tafi da shi.

  "Innalillah"
  tace sanda taga basu da komai a kitchen d'in.

  "Wannan wace irin rayuwa ce, Allah kai kad'ai ka san abunda kake nufi da mu, ya Allah ka cire mu daga cikin wannan baƙin talaucin"

  "Ameen".

  Shiryawa tayi sannan ta zauna zaman jiran Saudat in ta dawo daga skull su tafi tare.

  Ba jimawa kuwa ta dawo kaya kawai ta canza suka wuce da ƙafa don ko sisi basu da shi.

  "Sis Faty mu kam haka zamu dawwama cikin talauci ne?".

  "Kaniyar ki saudat".

  "Ai kullum haka suke fad'a ke da Hafsy, yanzu duk nisan asibitin nan da ƙafa zamu?".

  "Koma gida ki zauna in baza ki iya ba, ba fa dole bane, na tausaya miki ne kada ki zauna ke d'aya".

  Shiru tayi bata kuma cewa komai ba,
  tafiya sosai suka yi kan Allah ya sa suka iso asibitin gaba d'aya sun gama gajiya, Saudat kam da kyar take numfashi, ruwa suka sha a masallacin dake cikin asibitin, nan suka ji dai-dai daga nan suka karasa ciki.

  Suna shiga ba dad'ewa su Hakeela ma suka shigo da kololin abinci, jera su suka yi sannan suka gaisa dasu Maama.

  Har lokacin Hafsat bata farka ba, tun suna jiran farkawar ta da ƙauna har sun fara tsorata.

  Haka suka yita zama har azahar shiru, tambayar Doctor suka yi ko lafiya, ya shaida musu ba komai.

  Sai kusan la'asar ta farka lokacin har su Yaya Abdoul duk sun zo, dan kud'in da suka samu suka sayi lemu suka kawo mata.

  Hannunta ne ya fara motsi kan ta fara juya kanta tana kiran,

  "Maama! Abba!".

  Nursece ta ƙarasa wajen ta tare da dan duduba ta, daga nan kuma ta fita waje tana tambayar ina 'yan uwanta? zasu iya ganinta saboda ta farka.
  Nan suka wuce ciki, kwance suka same ta ta bud'e ido.

  Sannu suka fara jera mata tana lumshe ido.

  A hankali ta fara kallon su d'aya bayan d'aya,kokarin mik'ewa take amma ta gagara,Umma ce ta taimaka mata ta jungunu da jikin gadon tare da sa mata filo a baya.

  Jin jikinta take tamkar ba nata ba,tausayin kanta da kanta ya kamata bata san sanda ta zubda kolla ba.abinci aka bata ma ta kasa ci.da kyar ta iya cin kad'an tana jin shi kamar magani.

  Bill Umma taje ta biya da kuma kud'in gado ba tare da sanin su ba.

  Ya Abdoul ne ya tambayi garin yaya haka ta faru?nan Hakeela ta sanar da shi komai.
  "Wannan ba hatsari bane,dama an shirya hakan ne a kanta"!
  Ayya kuyi hakuri da wannan.yau a skull na wuni.

  STORY CONTINUES BELOW

  Comments ne zai sani typing Akai-akai.
  *©Hafciey.*
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 2📑*
  *__________*📖

  Juyawa suka yi duk suna kallon sa.Maama ce ta mishi wani irin kallo dole yasa shi yin kasa da kanshi tare da yin shiru.Umma da ta fahimci haka kuma sai bata kuma cewa komai ba illa abincin da tayi serving kuwa.Maama da farko taki ci,da kyar su Hakeela suka lalla'ba ta,taci kad'an.saudat kam sai santi take a zuciyar ta,yaushe rabon da taci jan miya haka.su ya Abdoul kam sunki ci duk nacin Hakeela haka ta barsu.

  Abba ne ya kira su nan suka fita farfajiyan asibitin tare.

  "Abdullahi ya zamu yi da kud'in jinyar Hafsat gashi naga jikin nata ba wanda za'a ce za'a sallame mu yau bane".

  "Wlhy nima Abba abunda nake ta tunani kenan,da ace karamar asibiti dai-dai karfin mu aka kaita".

  "Ai ma sunyi kokari da suka kaita asibiti basu bari ta mutu ba".

  "Yau fa kwata-kwata ni abunda na samu d'ari biyar ne,Naseer kuma ba abunda ya samu".

  "Innalillah!innalillah!

  Abba ke ta maimaitawa.wannan wace irin bakar talauci ne.

  "Kuma cikin d'ari biyar d'in muka sai mata lemon d'ari biyu,d'ari uku kuma na bari na machine da zai maida mu gida,yanzu haka tunanin inda zamu samu abincin gobe da safe nake tunda Allah yasa anci na dare a nan".

  "Ni abinci baya gaba na,sai dai yunwa ta kashe mu.ina zamu samu kud'in biyan asibitin Hafsat"??

  "Abba insha Allah zuwa goben zamu ga yadda Allah zai yi da mu".

  Suna gama magana suka wuce masallaci don gabatar da sallar magriba.Nan suka ringa kai kukan su wajen Allah. Basu suka koma cikin masallacin ba sanda suka yi i'sha inda nan Naseer ya tarar da su.

  A jere suka koma cikin asibitin.

  "Excuse me"!

  Wata nurse tace.yaa Abdoul ne ya jura gare ta su Abba kuma suka tsaya daga inda suke.

  Receipt ta mika masa.Karba yayi sannan ya kalle ta cikin zuciyar ssa yana cewa

  "Amma yarinyar nan ta rainani,wato har aika na ma zata yi".

  A zahiri kuma kallon ta yayi irin na rainin hankalin nan sannan yace

  "Wannan fa"?

  yana juya receipt din a hannum shi.

  "Na patient naku ne".

  Tana gama fad'ar haka ta juya.ranshi ne ya 'baci sosai,daman kun san mai zuciya lokaci guda yake fushi.jefar da receipt d'in yayi a kasa yana hushi kamar wani zaki.Naseer ne ya dafa kafad'ar sa tare da tsunguyawa ya d'auki receipt din yana kallo.tabbas na Hafsat ce.

  "Yaa Abdool gaskiyar ta fa na Hafsat ce".

  Abba ne ya kar'ba tare da gani.tho kenan wa ya biya?yaa Abdoul ma juyowa yayi domin tabbatar da abunda suka fad'a.ko da ya kar'ba sai ya gani.
  STORY CONTINUES BELOW

  "Nasan ba mai biya sai Mamar Hakeela,shiyasa sam bana son mutum ya san ina cikin damuwa,ai wannan d'awainiya muka daura mata.wlhy banji d'ad'i ba".

  Shi kuma haka Allah yayi shi,duk da kasancewar sa talaka hakan bai sa shi nuna ma duniya ba don su tausaya masa,komao na rayuwar sa so yake ya dai-dai ta shi da kanshi.

  "Ni sam na rasa Abba wani irin mutum ne,an sauke masa nauyi amma yana mita".

  Cewar Naseer cikin zuciyar sa.
  Dakin suka karasa inda suka tarar da Hafsat kam ta sake komawa bacci.su Maama kuma sunq hira jifa-jifa.kallon Umma yayi sannan yace

  Hajiya ya kamata ku koma gida fa dare yayi".
  Murmushi tayi sannan tace

  "Hakeela ce zata koma,ni a nan zan kwana"

  "A'ah baza'a yi haka ba,ku koma tare dai".

  Da kyar aka lalla'ba Umma ta yarda zata koma.sosai Abba da Maama suka mata godiyar alkhairi da ta musu,tsam ita bata so su sani bama wlhy.
  ******
  Kwana sun 5 a asibiti aka sallame su inda kullum sai Umma tazo duba su,Hakeela kuma kafun ta tafi makaranta ko bayan ta dawo.taji saukivsosai don inda taji ciwo har sun bushe ta waje amma ta ciki kam bai bushe ba.

  Kafun su tafi Doctor yace yana son ganin 1 daga cikin iyaten ta.yaa Abdoul Abba ya tura saboda yau zai fita nema musu abinci tunda kullum Umma ke tura musu wadatacciyar abinci.

  Sanda yaa Abdoul yaje wajen doctor,doctor bai so haka ba,yaso ace Babba ne zai ji wannan maganar ba dai yaa Abdoul ba.

  "Sorry kaje kawai sai randa Dad naku is free yazo in fad'a masa,Mom naku ma baza ta iya d'aukar maganar ba".

  Fita yayi jiki a sanyaye yana tunanin wani irin matsala Hafsat ke da shi wanda za'a ce shi yayi karami yaji,wani jarabawa ce Allah ke son jarabtar su da shi kuma?yana tafiya yana tunani sai buge mutani yake yi tare da basu hakuri.ko da ya iso har su Maama sun gama shirya komai shi kad'ai ake jira.Kallon Hafsat d'in yayi cike da tausayawa da wuri ya kawar da kansa don jin hawaye na kokarin zuba daga idon sa.ita ma Hafsat d'in kallon sa tayi tana murmushi amma kuma zuciyar ta ji take kamar dutse aka sa a wajen.yana mata ciwo sosai sai dai tasan iyayen ta basu da kud'in da zasu ji jinyan ta shiyasa ta gwammaci in mutuwa ne ma tayi kawai tunda dama wajibi ce.

  Hannun ta ya Abdoul ya rike sannan suka fita daga asibitin.Adai-daita da sis Faty ta tare suka shigar da kayan su da ba wani yawa bane da shi sannan suka shige ciki suka yi gida.ko da suka isa gida sun tarar yau ma Umma ta tura musu abinci.mita Maama ta fara kan cewa d'awainiyar ya musu yawa ai.d'aki ya Abdooul ya wuce da ita,a bakin gado ya zaunar da ita.so yake ya tambaye ta ko doctor yace mata wani abu amma yana tsoron tayar mata da hankali tunda yanzu ta dawo daga asibiti.

  "Hafsy kwanta ki huta ko".

  Murmushi ta masa tana kokarin kwancjya,ya rasa meyasa tun bai ji aihnahin abunda yake damunta ba yake tsanananin jin tausayin ta.shafa kanta yayi sannan ya fice daga d'akin.da kallo ta bisa bayan ya fita ta lumshe ido.

  Me yasa yanzu kuma Zuciya ta ke ciwo,ina zamu samu kud'in magani ko jinya tunda naga yanzu abinci ma da kyar muke samu.
  a zuciyar ta take wannan tunanin.

  Wayar ta ce ta fara ringing. Waya ce irin raka ni kashin nan.hannu ta mika daga inda take ta dauko.kallon number tayi,tayi saving number amma kuma ba suna.sawa tayi a kunne ba tare da tace komai ba.

  "Salamu alaikum"
  aka ce daga d'aya 'bangaren muryar da baza ta ta'ba mantawa ba.wannan matar da mijin ta ya kaita gidan su randa ta suma.murmushi  tayi kamar tana ganin ta tare da cewa

  "Wa'alaikumsallama.kaka ya kike"?

  "Ina lafita Hafsatu,haka kawai nace tunda kin ki kira na ni bara na kira ki".

  STORY CONTINUES BELOW

  "Yi hakuri kaka ban ji dad'I bane tunda na dawo".

  "Allah sarki,to Allah baki lafiya nima gobe insha Allah zanzo na duba ki".

  "To Allah kaimu sai kinzo".

  Sallama suka yi akan goben zata zo.tana ajiye wayar ta dafe kirjinta da hannu biyu jin kamar zuciyar ta zata fashe.bara san lokacin da ta fara kuka kasa-kasa ba,in taji motsin mutum a d'akin sai ta la'be kamar mai bacci bayan kuka take yi.
  "Yaa Allah in mutuwa zan yi ka d'auki rai na da wuri kada iyaye na su sha wahala wajen neman kud'in ji mini jinya."

  Sosai take jin abun,addu'o'i kala-kala take,da kyar ta fara jin ya fara sauka.gaba d'aya ta gama galabaita a kan 'yar gadon.wani wahalallen bacci ne yayi awon gaba da ita.

  A waje kuma su Maama da sis Faty ne suke zaune ko akwai wad'anda zasu zo gaisuwa,amma ga namakin su ba alamar kowa.dama 'yan anguwan ba son su suke ba saboda bakin talaucin su da kuma dalili d'aya mai karfi wanda duk wanda yaji shi doke ya tsane su.basu damu da rashin zuwan kowa ba tunda 'yar su Allah ya bata lafiya.

  Abunda zai baka mamaki shine ko kad'an ba wanda ya tayar da maganan hatsarin Hafsat,irin suce ko zasu bincika wa yayi.

  A bangaren yaa Abdoul kuma ya kira Abba ya sanar da shi yadda suka yi da doctor.jikin Abba har 'bari yake yi saboda yasan al'amari ne mai girma.

  "Inshaa Allah yanzu ma zanje don lafiyar 'yata yafi mini komai".

  Wucewa asibiti Abba yayi zuciyar sa sai tsinkewa yake.sanda ya isa asibitin ma docctor'n yana duba patients don haka ya zauna zaman jiran sa.ya kai minti talatin a zaune kafun doctor ya fito.

  Office na doctor suka wuce.bayan sun gaisa doctor ya kura masa ido

  "Bangane ka ba"

  "Mahaifin Hafsat wacce aka sallama d'azun kace kana son gani na".

  "Ohhhh na gane,dama ba komai yasa na kira ka ba sai don sanar da kai ciwon da 'yarka ke tare da shi,duk da banda tabbacin baka sani ba".

  Cire glass na idon sa doctor yayi sannan yace

  "Na farko bisa accident da 'yar ka tayi zata koma sa glasses don ya d'an ta'ba idonta,ba sosai zata ringa gani ba,wani lokacin ma baza ta gani gaba d'aya,don haka ka gaggauta siya mata medicated glass".

  Ajiyar Zuciya Abba ya jaa jin ba wani abun tada hankali sosai bane.

  "Na biyu kuma......

  Sai yayi shiru!

  "Ina jin ka"!

  I am sorry to say 'yarka na da hall a cikin zuciyar ta"!

  "Hall"?

  "Ehhh rami,wanda in ba'a mata operation ba zata iya mutuwa a koda yaushe,sannan kuma a kasar waje zaku je a mata.ka lura da yanayin ta mana sam bata da hayani ya".

  Zufa ne ya fara gangara ma Abba wanda ji yake da mutuwa ma kawai yayi,don yasan yanzu kam lokaci yayi a talauci zai sa shi rasa rayuwar 'yarsa.

  "I am sorry doctor yace sannan ya mike.

  "Ku tabbata komai take so kuna mata sannan kuma kada a ringa d'aga mata hankali.saboda tashin hankali tamkar baraza na ce a rayuwarta.a kula don Allah ".

  Yana gama fad'an haka ya fice.

  Yaa Abdool da tunda Abba yace zai je asibiti shima ya bishi ba tare da sanin sa ba.jin abunta doctor yace ya sa shi fara salati a wurin ya fad'i sumemme.jin karar fad'iwar abu yasa Abba mikewa cikin sanyi jiki don ganin mene ne?

  STORY CONTINUES BELOW

  Abdool ya gani kwance!

  Comments naku ke kara mini karfin gwiwa,in naga ba yadda nake so ake yi ba zan bari....
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 4📑*
  *__________*📖

  Juyawa suka yi duk suna kallon sa.Maama ce ta mishi wani irin kallo dole yasa shi yin kasa da kanshi tare da yin shiru.Umma da ta fahimci haka kuma sai bata kuma cewa komai ba illa abincin da tayi serving kuwa.Maama da farko taki ci,da kyar su Hakeela suka lalla'ba ta,taci kad'an.saudat kam sai santi take a zuciyar ta,yaushe rabon da taci jan miya haka.su ya Abdoul kam sunki ci duk nacin Hakeela haka ta barsu.

  Abba ne ya kira su nan suka fita farfajiyan asibitin tare.

  "Abdullahi ya zamu yi da kud'in jinyar Hafsat gashi naga jikin nata ba wanda za'a ce za'a sallame mu yau bane".

  "Wlhy nima Abba abunda nake ta tunani kenan,da ace karamar asibiti dai-dai karfin mu aka kaita".

  "Ai ma sunyi kokari da suka kaita asibiti basu bari ta mutu ba".

  "Yau fa kwata-kwata ni abunda na samu d'ari biyar ne,Naseer kuma ba abunda ya samu".

  "Innalillah!innalillah!

  Abba ke ta maimaitawa.wannan wace irin bakar talauci ne.

  "Kuma cikin d'ari biyar d'in muka sai mata lemon d'ari biyu,d'ari uku kuma na bari na machine da zai maida mu gida,yanzu haka tunanin inda zamu samu abincin gobe da safe nake tunda Allah yasa anci na dare a nan".

  "Ni abinci baya gaba na,sai dai yunwa ta kashe mu.ina zamu samu kud'in biyan asibitin Hafsat"??

  "Abba insha Allah zuwa goben zamu ga yadda Allah zai yi da mu".

  Suna gama magana suka wuce masallaci don gabatar da sallar magriba.Nan suka ringa kai kukan su wajen Allah. Basu suka koma cikin masallacin ba sanda suka yi i'sha inda nan Naseer ya tarar da su.

  A jere suka koma cikin asibitin.

  "Excuse me"!

  Wata nurse tace.yaa Abdoul ne ya jura gare ta su Abba kuma suka tsaya daga inda suke.

  Receipt ta mika masa.Karba yayi sannan ya kalle ta cikin zuciyar ssa yana cewa

  "Amma yarinyar nan ta rainani,wato har aika na ma zata yi".

  A zahiri kuma kallon ta yayi irin na rainin hankalin nan sannan yace

  "Wannan fa"?

  yana juya receipt din a hannum shi.

  "Na patient naku ne".

  Tana gama fad'ar haka ta juya.ranshi ne ya 'baci sosai,daman kun san mai zuciya lokaci guda yake fushi.jefar da receipt d'in yayi a kasa yana hushi kamar wani zaki.Naseer ne ya dafa kafad'ar sa tare da tsunguyawa ya d'auki receipt din yana kallo.tabbas na Hafsat ce.

  "Yaa Abdool gaskiyar ta fa na Hafsat ce".

  Abba ne ya kar'ba tare da gani.tho kenan wa ya biya?yaa Abdoul ma juyowa yayi domin tabbatar da abunda suka fad'a.ko da ya kar'ba sai ya gani.
  STORY CONTINUES BELOW

  "Nasan ba mai biya sai Mamar Hakeela,shiyasa sam bana son mutum ya san ina cikin damuwa,ai wannan d'awainiya muka daura mata.wlhy banji d'ad'i ba".

  Shi kuma haka Allah yayi shi,duk da kasancewar sa talaka hakan bai sa shi nuna ma duniya ba don su tausaya masa,komao na rayuwar sa so yake ya dai-dai ta shi da kanshi.

  "Ni sam na rasa Abba wani irin mutum ne,an sauke masa nauyi amma yana mita".

  Cewar Naseer cikin zuciyar sa.
  Dakin suka karasa inda suka tarar da Hafsat kam ta sake komawa bacci.su Maama kuma sunq hira jifa-jifa.kallon Umma yayi sannan yace

  Hajiya ya kamata ku koma gida fa dare yayi".
  Murmushi tayi sannan tace

  "Hakeela ce zata koma,ni a nan zan kwana"

  "A'ah baza'a yi haka ba,ku koma tare dai".

  Da kyar aka lalla'ba Umma ta yarda zata koma.sosai Abba da Maama suka mata godiyar alkhairi da ta musu,tsam ita bata so su sani bama wlhy.
  ******
  Kwana sun 5 a asibiti aka sallame su inda kullum sai Umma tazo duba su,Hakeela kuma kafun ta tafi makaranta ko bayan ta dawo.taji saukivsosai don inda taji ciwo har sun bushe ta waje amma ta ciki kam bai bushe ba.

  Kafun su tafi Doctor yace yana son ganin 1 daga cikin iyaten ta.yaa Abdoul Abba ya tura saboda yau zai fita nema musu abinci tunda kullum Umma ke tura musu wadatacciyar abinci.

  Sanda yaa Abdoul yaje wajen doctor,doctor bai so haka ba,yaso ace Babba ne zai ji wannan maganar ba dai yaa Abdoul ba.

  "Sorry kaje kawai sai randa Dad naku is free yazo in fad'a masa,Mom naku ma baza ta iya d'aukar maganar ba".

  Fita yayi jiki a sanyaye yana tunanin wani irin matsala Hafsat ke da shi wanda za'a ce shi yayi karami yaji,wani jarabawa ce Allah ke son jarabtar su da shi kuma?yana tafiya yana tunani sai buge mutani yake yi tare da basu hakuri.ko da ya iso har su Maama sun gama shirya komai shi kad'ai ake jira.Kallon Hafsat d'in yayi cike da tausayawa da wuri ya kawar da kansa don jin hawaye na kokarin zuba daga idon sa.ita ma Hafsat d'in kallon sa tayi tana murmushi amma kuma zuciyar ta ji take kamar dutse aka sa a wajen.yana mata ciwo sosai sai dai tasan iyayen ta basu da kud'in da zasu ji jinyan ta shiyasa ta gwammaci in mutuwa ne ma tayi kawai tunda dama wajibi ce.

  Hannun ta ya Abdoul ya rike sannan suka fita daga asibitin.Adai-daita da sis Faty ta tare suka shigar da kayan su da ba wani yawa bane da shi sannan suka shige ciki suka yi gida.ko da suka isa gida sun tarar yau ma Umma ta tura musu abinci.mita Maama ta fara kan cewa d'awainiyar ya musu yawa ai.d'aki ya Abdooul ya wuce da ita,a bakin gado ya zaunar da ita.so yake ya tambaye ta ko doctor yace mata wani abu amma yana tsoron tayar mata da hankali tunda yanzu ta dawo daga asibiti.

  "Hafsy kwanta ki huta ko".

  Murmushi ta masa tana kokarin kwancjya,ya rasa meyasa tun bai ji aihnahin abunda yake damunta ba yake tsanananin jin tausayin ta.shafa kanta yayi sannan ya fice daga d'akin.da kallo ta bisa bayan ya fita ta lumshe ido.

  Me yasa yanzu kuma Zuciya ta ke ciwo,ina zamu samu kud'in magani ko jinya tunda naga yanzu abinci ma da kyar muke samu.
  a zuciyar ta take wannan tunanin.

  Wayar ta ce ta fara ringing. Waya ce irin raka ni kashin nan.hannu ta mika daga inda take ta dauko.kallon number tayi,tayi saving number amma kuma ba suna.sawa tayi a kunne ba tare da tace komai ba.

  "Salamu alaikum"
  aka ce daga d'aya 'bangaren muryar da baza ta ta'ba mantawa ba.wannan matar da mijin ta ya kaita gidan su randa ta suma.murmushi  tayi kamar tana ganin ta tare da cewa

  "Wa'alaikumsallama.kaka ya kike"?

  "Ina lafita Hafsatu,haka kawai nace tunda kin ki kira na ni bara na kira ki".

  STORY CONTINUES BELOW

  "Yi hakuri kaka ban ji dad'I bane tunda na dawo".

  "Allah sarki,to Allah baki lafiya nima gobe insha Allah zanzo na duba ki".

  "To Allah kaimu sai kinzo".

  Sallama suka yi akan goben zata zo.tana ajiye wayar ta dafe kirjinta da hannu biyu jin kamar zuciyar ta zata fashe.bara san lokacin da ta fara kuka kasa-kasa ba,in taji motsin mutum a d'akin sai ta la'be kamar mai bacci bayan kuka take yi.
  "Yaa Allah in mutuwa zan yi ka d'auki rai na da wuri kada iyaye na su sha wahala wajen neman kud'in ji mini jinya."

  Sosai take jin abun,addu'o'i kala-kala take,da kyar ta fara jin ya fara sauka.gaba d'aya ta gama galabaita a kan 'yar gadon.wani wahalallen bacci ne yayi awon gaba da ita.

  A waje kuma su Maama da sis Faty ne suke zaune ko akwai wad'anda zasu zo gaisuwa,amma ga namakin su ba alamar kowa.dama 'yan anguwan ba son su suke ba saboda bakin talaucin su da kuma dalili d'aya mai karfi wanda duk wanda yaji shi doke ya tsane su.basu damu da rashin zuwan kowa ba tunda 'yar su Allah ya bata lafiya.

  Abunda zai baka mamaki shine ko kad'an ba wanda ya tayar da maganan hatsarin Hafsat,irin suce ko zasu bincika wa yayi.

  A bangaren yaa Abdoul kuma ya kira Abba ya sanar da shi yadda suka yi da doctor.jikin Abba har 'bari yake yi saboda yasan al'amari ne mai girma.

  "Inshaa Allah yanzu ma zanje don lafiyar 'yata yafi mini komai".

  Wucewa asibiti Abba yayi zuciyar sa sai tsinkewa yake.sanda ya isa asibitin ma docctor'n yana duba patients don haka ya zauna zaman jiran sa.ya kai minti talatin a zaune kafun doctor ya fito.

  Office na doctor suka wuce.bayan sun gaisa doctor ya kura masa ido

  "Bangane ka ba"

  "Mahaifin Hafsat wacce aka sallama d'azun kace kana son gani na".

  "Ohhhh na gane,dama ba komai yasa na kira ka ba sai don sanar da kai ciwon da 'yarka ke tare da shi,duk da banda tabbacin baka sani ba".

  Cire glass na idon sa doctor yayi sannan yace

  "Na farko bisa accident da 'yar ka tayi zata koma sa glasses don ya d'an ta'ba idonta,ba sosai zata ringa gani ba,wani lokacin ma baza ta gani gaba d'aya,don haka ka gaggauta siya mata medicated glass".

  Ajiyar Zuciya Abba ya jaa jin ba wani abun tada hankali sosai bane.

  "Na biyu kuma......

  Sai yayi shiru!

  "Ina jin ka"!

  I am sorry to say 'yarka na da hall a cikin zuciyar ta"!

  "Hall"?

  "Ehhh rami,wanda in ba'a mata operation ba zata iya mutuwa a koda yaushe,sannan kuma a kasar waje zaku je a mata.ka lura da yanayin ta mana sam bata da hayani ya".

  Zufa ne ya fara gangara ma Abba wanda ji yake da mutuwa ma kawai yayi,don yasan yanzu kam lokaci yayi a talauci zai sa shi rasa rayuwar 'yarsa.

  "I am sorry doctor yace sannan ya mike.

  "Ku tabbata komai take so kuna mata sannan kuma kada a ringa d'aga mata hankali.saboda tashin hankali tamkar baraza na ce a rayuwarta.a kula don Allah ".

  Yana gama fad'an haka ya fice.

  Yaa Abdool da tunda Abba yace zai je asibiti shima ya bishi ba tare da sanin sa ba.jin abunta doctor yace ya sa shi fara salati a wurin ya fad'i sumemme.jin karar fad'iwar abu yasa Abba mikewa cikin sanyi jiki don ganin mene ne?

  Abdool ya gani kwance!

  Comments naku ke kara mini karfin gwiwa,in naga ba yadda nake so ake yi ba zan bari....
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 5📑*
  *__________*📖

  Ido Abba ya zare ganin yaa Abdoul ne kwance a wajen.da wuri ya fita domin nemo ruwa.kowa harkar gabar sa yake basu damu da Abdoul da ke kwance a wajen ba.da wuri Abba ya shigo da ruwa tare da watsa masa.nan take ya farfad'o yana ambata sunan Allah.

  "Sannu Abdoul".

  Duk da dauriyan sa kasawa yayi,da wuri ya rungume Abba yana kuka mara sauti.hakuri Abba ke bashi duk da cewa shi kanshi Abba da zai samu dama shima kukan zai yi,sai dai kuma kukar ba ita bace mafita.

  "Tashi mu tafi".

  Mikewa yayi suka fita daga asibitin.kallon Abba yake wanda ko gaban sa baya kallo,gaba d'aya yayi nisa cikin tunani.kasar wata bishiya yaa Abdoul yace su zauna saboda ya lura sam Abba baya hayyacin sa.bayan sun zauna Abba ya zame hular kansa yana fifita da shi saboda gumin da ke keto masa.

  "Innalillah!Abdoul yanzu haka zan zuba ido ina ji ina gani Hafsat ta mutu,Allah ne kad'ai yasan tun yaushe take fama da wannan ciwon,amma don hakuri irin nata ta gaza fad'ama kowa".

  "In shaa Allah Hafsat baza ta mutu ba".

  "Har yaushe zamu ringa fad'ar haka bayan mun san gaskiya ce,banda kud'in da zan biya ma Hafsat surgery sannan kuma banda wata kadarar da zan sayar".

  "Ni dai nasan Hafsat baza ta ta'ba mutuwa ba,yanzu dai kar mu fad'a ma kowa a gida mu fara shirye-shiryen neman kud'i.

  Wurin aiki suka koma dukkan su domin neman na abinci.
  A can gida kuwa sai yanzu Hafsat ta farka,ta dai ji saukin abunda take ji kam.kafar ta'daya ta fara saukewa sannan ta sauke d'ayan.mikewa tayi da kyar ta fito waje.cikin kafa ta samu suna tsincewa mai tsina sosai.zama tayi a bakin kofar tana fad'in

  "Maama sannun ku da aiki".

  Kallon ta tayi cike da tausayawa tace
  "Yauwa Hafsat sannu,har kin fito"?

  "Ehh Allah yayi".

  "Hafsy ya jikin"?

  "Da sauki sis Faty".

  "Ba abunda yake miki ciwo ko".

  Dariyar da iya baki ya tsaya tayi sannan tace

  "Ba komai sai wanda ba za'a rasa ba".

  Zama tayi ta kura musu ido dukkan su tana fatan kada Allah ya d'auki ranta har sai ta sanya su farin ciki a rayuwa,wannan bakar talaucin so take ace ita ce zata raba su da shi.yadda tayi tagumin zaka xe wata marainiya ce.suna a zaunen aka yi sallama.wacce Hafsat ke kira da kaka ce tazo.duk larfin ta ta had'a wajen mikewa gar da d'an gudun ta,jikin kaka ta fad'a tana mata oyoyo.rabon da suka farin ciki irin na yau a fuskar Hafsat ya dad'e,lallai wannan matar duk yadda aka yi tana da alaka da zuciyar Hafsat.yarinyar da ba kowa take sakewa da su ba sai gashi lokaci guda taso Kaka.

  Maama ce ta mike tana mata sannu da zuwa.wajen zama suka bata ta zauna Hafsat na manne da ita.kallon Hafsat tayi sannan tace

  "Yau kam ba kuka ne"?

  Murmushi kawai ta mata tana fad'in

  "Ya akayi kika gane gidan mu"?

  "Yayan ki ne ya mini kwatance".

  Gaisawa suka yi da Maama haka ma sis Faty ta gaishe ta.godiya sosai Maama ta mata kan taimakon Hafsat da suka yi ran can.duk da Kaka bata dad'e a gidan ba amma ta lura lallai su d'in talakawa ne kuma ta tausaya musu matuka,saboda su abun a tausaya ma ne.ba wani jimawa tayi ba ta sallame su sannan tayi gaba.

  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 6📑*
  *__________*📖
  Bayan tafiyar ta bada jimawa ba Abba ya dawo gida.ido ya kura ma Hafsat kamar bai ta'ba ganin ta ba,jikin ta ne ya bata ana kallon ta don haka ta d'aga ido.carab suka had'a ido.+

  "Sannu da dawa Abba".

  Kasa magana yayi illa karasa shiga gidan davyayi.zama yayi kusa da ita yana mai matukar jin tausayin ta.

  "Maama na ya jikin naki?ince dai ba abunda ke miki ciwo?

  "Ba komai Abba".

  Ta fad'a cikin sanyin murya.ganin kallon da Abba yake mata ya sata fara tsarguwa,anya irin kallon da yake matan nan bai gane me damunta ba kuwa?

  Mikewa tayi da wuri don ta shige d'aki amma ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunan ta.tsayawa tayi tana karanto innalillah a zuciyar ta.

  "Zo ki zauna mana Maama na,ko kin gaji da zaman ne"?

  "A'ah Abba".

  "Tho zauna ki jira yayan ki Abdoul".

  Aiko bai gama rufe bakin sa ba Abdoul ya shigo hannun sa rike da karamar laida.gaishe da Maama da kuma Abba yayi sannan ya samu wuri ya zauna yana jima Hafsat sannu da jiki.Ledar ya mika ma Abba.kar'ba Abba yayi sannan ya kalli Maama da ita ma shi take kallo.

  "Wannan glasses ne na sayo ma Maama na saboda likita yace idon ta ya samu damuwa baza ta na gani da kyau ba sai da glasses ".

  Shiru Maama tayi,ji take kamar tayi ma Hafsat d'in kuka,damuwa yayi yawa a cikin rayuwarta kuma dyk saboda mutum d'aya ne ko nace ahali d'aya,hankalin su ba zai ta'ba kwanciya ba har sai sun kace mata 'ya,duk sun fi karkata hankalin su kan Hafsat d'in fiye da kowa a gidan su.ba komai Allah na tare da masu hakuri kuma insha Allah burin su ya ruguza rayuwar Hafsa ba zai ta'ba cika ba.
  "Abba na a ina ka samu kuzd'in da ka saya mini glasses "?

  "Gashi amshi kisa Maama na,kin san dai Abban ki bazai sayo miki da kud'in haram ba ko"?

  "Amma.....

  "Saka kawai".

  Bud'ewa tayi daga cikin gidan sa sannan ta kare ma glasses d'in kallo daga nan kuma tasa a idonta.sosai ya mata kyau.

  "Hafsy irin wannan kyau haka"?

  Murmushi tayi sannan tace

  "Na gode ya Abdoul.

  Maama kuwa sai kallon ta take cike da sha'awa,ji take ina ma ace Abba zai yarda da ta tura wajen dangin ta saboda can zai fiye musu kwanciyar hankali.

  "Abba dan Allah ka fad'a mini inda ka samu kud'in nan in ba haka ba hankali na bazai ta'ba kwanciya ba".

  "Maama na mun sayar da wayar mu nida yayan ki ne".

  Ido ta zaro waje kamar na mara gaskiya sannan tace

  "Abba kuka sayar da wayar ku don ni?me yasa?har yaushe zaku cigaba da sadaukar da abubuwan da kuka mallaka a kaina?bani kad'ai bace fa yarinya a gidan nan,ga saudat da sis Faty duk suna da bukata.ni jiki na yana bani ba wani dad'ewa zan yi a duniyar bama".

  STORY CONTINUES BELOW

  Dibb zuciyar Abba da yaa Abdoul ya buga,lallai dole su tashi tsaye domin neman kid'in mata jinya tunda ita kanta tasan zata iya mutuwa a koda yaushe.ganin kamar zata tada hankalin ta yasa yaa Abdoul bata ruwa ta sha daga nan kuma suka fara aikin lallashin ta.da kyar ta sauko sannan tayi ma Abba godiya.

  *******

  Abba dan asalin jigawa ne wanda kasuwanci ya kawo sa garin gombe.su biyu iyayen sa suka haifa Allah ya d'auki ransu.shi da kanwar sa Zainab.bayan rasuwar iyayen su yayi ma Zainab aure da kud'in gadon ta shi kuma Nasa kud'in ya d'auka domin fara kasuwanci.yana da 'yan uwa dayawa kuma masu hali.Zainab na zaune gidan mijin ta cikin kwanciyar hankali saboda mijin ta nada hali sosai.yaran ta 3.
  sanda karayar arziki yazo ma Abba rasa komai nasa yayi.da can shi hamshakin mai kud'i ne,da su ake damawa wajen kasuwanci.sam bai ta'ba tunanin akwai ranar da zai talauce haka ba.gashi abun mamaki duk wanda yayi yunkurin taimakon sa shima watar talaucewan sa ya kama.l,hakan yasa ba mai son taimakon sa.mijin Zainab kam har ga Allah yaso taimaka masa amma Abba yak'i saboda baya son ya zama sanadiyar shigar da wani bakin talauci irin wanda yake ciki.da kyar ya yarda suka d'auki d'awainiyar makarantar Hafsat.garin su kuma in ya samu kud'i yakan je ya duba baffanin sa.

  Wannan kenan!

  Bayan accident nata da sati d'aya ta shirya domin komawa skull saboda yanzu kam sauki ya samu alhamdulillah.a bangaren Abba ma suna kokarin neman kud'i domin kaita jinya.da yake yanzu zuciyarta ya daina ciwo tunda dama sai an 'bata mata rai yake tashi shiyasa bata damu da ciwon ba.

  Shiryawa tayi cikin shigar ta ta hausawa da kuma talakawa tare da sa babbar hijab da ba wanda ya isa yace ga kalar kod'ewar kayan ta.sallamar Maama tayi sannan ta fice.sam Maama bata son zuwan ta makarantar saboda duk sanda ta fita sai wani mummunan abu ya faru da ita.addu'a Maama take Allah ya kare mata 'yarta daga Mahassada.

  Yauwa kamar kullum a titi ta tsata jiran abun hawa,ita kanta tsoro take ji don gani take kamar abunda ya faru wancan karon zai kuma faruwa.Hasbunallahu take ringa karantawa a zuciyar ta saboda ji take kamar zuciyar ta zai fito wahe ga gaban ta sai fad'iwa yake.tunda take bata ta'ba jin irin na yau ba hakan ya tabbatar mata lallai yau nummunan abun da ya saba faruwa da ita yau da wanin ta zai faru,dole rayuwar d'aya daga cikin 'yan uwanta ko iyayen ta na cikin hatsari.wani zuciya ne kuma yace mata khairan insha Allah. Da haka ta tare adai-dai ta ba don ranta yaso ba.
  Tana isa makaranta Hakeela na isa.cike da mamaki take kallon Hafsat da idonta ke sanye cikin glasses saboda kullum tana zuwa gidan su amma bata ta'ba samun ta da glasses din ba.

  "Yaushe kika fara sa glasses "?.

  "Medicated ne" kawai tace da ita suka cigaba da tafiya.kowa kallon Hafsat d'in yake.tana jin wata na cewa

  "Su Hafsat an girma harda sa glasses,yaushe ma suka samu na sutura har yarinya ta fara rigima".

  'Dayar kuma cewa tayi

  "Wata kila tayi saurayi 'dan iska,in sunyi iskanci sai ya bata kud'i kinga da shi zata ringa siyan abunda ranta yake so har ma ta taimaka ma tsohonta da kullum cikin kaya d'aya yake".

  Dariya sauran suka kwashe da shi.ji take kamar zuciyar ta zata fashe don irin zarafin ta da aka ci.Hakeela ce ta juya cikin fad'a zata nufe su saboda tasan ko shekara zasu yi suna zagin Hafsat ba tamka musu zata yi ba.kama hannun ta Hafsat tayi tare da girgiza mata kai.

  "Banda tsoro barta tazo mana.talakar banza".
  "Gani nayi uban ku ba raba arziki yake ba ko"?

  Cewar Hakeela da aka hanata zuwa tunda ba'a rufe bakin maganar ba.da wuri Hafsat taja hannunta suka nufi lecture hall.

  "Ke wai har yaushe zaki jure bak'ak'en maganganun wad'an nan?kullum da irin zagin da zasu miki ke kuma kamar wata shashasha baza ki ta'ba cewa komai ba".

  STORY CONTINUES BELOW

  Hmm kawai tace tare da girgiza kai.

  Sam ita bata damu ba,saboda tasan in bata tamka musu dole wata ran zasu gaji subari.Hakeela kam sai tsaki take don harga Allah Hafsat na bata haushi ko yaushe zata koyi fad'a ne sai Allah.

  Suna gama lectures suka kama hanyar gida saboda yawanci in dawa ne tana bin Hakeela a motar gidan su ko kuma ta koma da kafa duk da makarantar sun akwai nisa.

  Bayan ta koma gida ta samu 'yan gidan su kowa yaci uban tagumi.

  "Dama nasan dole wani abu zai faru".

  Ta fad'a a zuciyarta sannan ta shiga gidan da sallama.ciki-ciki aka amsa hakan ya tabbatar mata lamarin babba ne.wurin zama ta nema sannan ta gaishe su.amsawa suka yi kamar an musu dole.
  "yaa Abdoul lfy kuwa kuka dawo gidan yanzu har da Abva"?

  dama shi kam ta gama cika saura ya fashe ne,kuma jiran wanda zai masa magana yake.
  "Dallah rufewa mutani baki".

  yanda yayi maganar da tsawa sanda ta tsorata.bai saurare ta ba yaci gaba
  "Wlhy Alhaji Muneer ya raina ma mutani wayo.sanda yaga ana tsaka da talauci zai ce a biya sa kud'in sa,har da kai mu kotu,to wlhy ta Allah ba tasa ba kuma ba za'a biya na".

  Tana jin haka ta gane inda maganar ta dotsa.wannan mutumin KIYAYYAR ZUCIYA gare sa,kiyayyar su daga zuciyar sa yake fitowa,ba abunda ya rasa a rayuwa amma su ya hana su sukuni.
  "Banda iskanci komai na duniyar nan ya mallake ta,kowa yasan da zaman sa a jihar nan har ma wajen ta ba mai nuna masa kud'i,me zai hana sa kiyayyar ga abokan hamayyar sa sai mu?don kawai Allah ya jarabce mu da cin bashin sa".

  "Duk ba wannan bane yaa Abdoul,sai kace Hafsat d'in ce Alhaji Munir,yanzu dai dole gobe mu halarta a kotu kamar yadda tsammacin yace,yanzu dai abun yi mu nemi lawyer kafun gobe".

  Abba dai shiru yayi yana nazari.me yasa shekaru goma sha shida da suka wuce Alhaji Munir bai nemi bashin sa a wajen sa ba sai yanzu,duk yadda aka yi akwai lauje cikin nad'i.

  Yaa Abdoul da yaa Naseer fita suka yi domin nemo lawyer saboda sun san karya ne su ja da alhaji Munir aka case nan tunda dama sube marasa gaskiya.abokin yaa Abdoul suka kira inda yace musu yana gida don haka gidan sa suka je.lawyer ne mai zaman kansa duk da shekarun sa ba wani yawa bane da su.sun tattauna sosai akan case d'in inda ya tabbatar musu insha Allah nasara na tare da su.

  Komawa gida suka yi tare da sanar ma Abba yadda suka yi.shi dai yasan koma yaya ne baza su iya jaa da Alhaji Munir ba,bare ma sun san tabbas sun ci bashin sa.
  Hafsat dai ba abunda take ita da Maama da kuma sis Faty sai jimani
  Yaa Abdoul bakin ciki tab ya cika zuciyar sa.sun da suke neman kud'in jinyar Hafsat yanzu kuma ga wannan azzalumin ya taso da maganar kud'in sa da karya ne suce ga adadin sa kuma dolen su ko yafi haka su biya tunda kud'i ne wanda ba a irga su ba.dama Abba ya fad'a ko ba dad'e ko ba jima dole zasu nemi kud'in su.
  "Yanzu bayan duk abunda suka mana bai ishe su ba,kullum in Abba ya samu kud'i sai sunsa an kwace,mu kuma ya hana mu samun aiki,Faty da aka yi baikon ta ma ba muda kud'in da zamu mata aure,Hafsat kuma duk abubuwan da yake faruwa cikin rayuwar ta shike mata.Na rasa wani irin azzalumi ne shi".
  Haka a daren ranar suka kwana basu rintsa ba.
  Washe gari!!!!

  Ba wanda yayi yunkurin zuwa skull ko wajen nema,dukkan su shiri suka yi sannan suka wuce court.kusan lokacin da suka je ma sun makara.ga mamakin su ba mutum ko d'aya daga gidan Alhaji Munir...

  STORY CONTINUES BELOW

  Ku biyo ni domin jin wani hukunci alkali zai yanke ma Abba?ko kuma zai samu kud'in da zai biya?

  Comments ne jagoran rubutu na....in yayi kasa nima nayi shiru...
  Love yhu all.I mean only my fans❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 7📑*
  *__________*📖
  Tsit wuri yayi sai alkalin dake bud'e takardun gaban sa,karar su kad'ai ke tashi a wurin.agyaran murya yayi tare da basu umarnin zasu iya fara karan.lawyer mai kara wato lawyer'n Alhaji Munir ne ya mike bayan ya gaishe da Alkali ya fad'i dalilin da yasa suka shigar da kara.

  "Ya mai girma mai shari'a,nine lawyer'n mai kara.wannan mutum mara mutunci mai suna Alhaji Musa yaci bashin abokin sa wato Alhaji Munir kud'i da baza su fad'u ba kimanin shekara sha takwas kenan".

  Juyawa yayi yana kallon Abba sannan yace zai iya zuwa.wajen da aka tanadar ma masu bada amsa ya shiga.kallon sa lawyer'n yayi cike da tsana yace

  "Alhaji Musa me zai hana ka fad'a ma wannan kotu mai albarka cewa kaci kud'in Alhaji Munir kuma kaki biya".

  Numfashi Abba yaja sannan yace

  "Ehhh kud'i ya bani bashi kuma ban ci....

  "Ai ka gama zance tunda kace ka ci ba kuma abunda zaka sake fad'awa kotu.

  "Lawyer'n Abba ne ya mike yana kallon Alkali yace

  "Objection my lord,abokin aiki na kokari yake ya tirsasa Alhaji Musa wanda duniya suke gani kamar yaki biyan kud'in nan ne ya amsa laifin da bai yi ba".
  "Ka kula".

  Alkali yace ma lawyer'n Alhaji Munir.

  "Zaka iya zama"

  lawyer'n Alhaji Munir  yace.

  "Lawyer mai kare wanda ake kara ko kana da abun fad'i??
  "Ehhh".
  yace sannan ya mike

  "ya mai girma mai shari'a,wannan bawan Allah'n nan kallo d'aya zaka masa kasan cewa shi talaka ne da kyar yake neman naci da sha,sannan kuma a halin yanzu kud'in da suke so ya biya yafi karfin sa,ba abunda ya mallaka a duniya sai karamin gidan sa wanda koda za'a sayar bazai kai kud'in da za'a biya su ba.sannan magabar da nake maka yanzu haka 'yarsa ba lafiya bane da ita,ina rokon wannan kotu mai albarka da ta d'aga wannan zaman zuwa wani wata".na gode "
  yace sannan ya zauna.

  Dube-dube alkali yayi sannan yace

  "An daga wannan zamar zuwa wani wata".

  Mikewa duk mutanin kotun suka yi,yana fita suka bi bayan sa kowa na kananan maganganu.

  Gefe suka koma Abba na masa godiya.gida suka wuce har da shi don basu ga ta zama ba a cikin wata d'ayan nan.bayan sun isa gida sun sha ruwa kenan aka shimfid'a musu sallaya inda Su Maama da Hafsat suka yi ciki aka bar mazan a waje.gyaran murya jibril yayi wato lawyer'n Abba sannam yace

  "Abba dukkan mu mun san gaskiya d'aya ce,kuma tunda har Alhaji ya shigar da mara to yana son kud'in sa ne,ba wai kuma yana yana son kud'in bane don amfanin da shi sai dai yana da manufar tozarta ka a idon duniya ta yadda in ka lasa biyar sa kud'in sa sai aka sa a prison don haka nake gani cikin wata d'ayan nan ya kamata ku motsa jiki kafun yaci nasara a kanku".

  STORY CONTINUES BELOW

  "Jibril so kake mu koma kwana a titi ne?abunda ko mun sayar da gidan mu kud'in ba isa zasu yi ba, to ya kake so muyi ne?
  Cewar yaa. Abdoul.

  "Nifa duk wannan baya gaba na,duk abunda kula ga Alhaji Munir ya mini to dama kaddarerre ne a gare ni.ni yanzu kud'in jinya 'yata nake nema kafun na rasa ta.a shirye nake na fuskanci duk hukuncin da kotu ta yanke akai na tunda nasan na karbi kud'in sa".

  Yana gama fad'ar haka ya mike.dole yaa Abdoul ne sai yaa Nasir suka cigaba da tattaunawa da barrister jibril.

  A can d'aki kuma duk jimami suke sai ma Hafsat da taji zuciyar ta na son fara ciwo.da farko a kotu da Barrister jibril yace bata da lafiya ta zata wata rashin lafiyar ce ta kamata ake boye mata,sai daga baya tayi tunanin ko ciwon idon ta ne.Maama ma duk haka suka d'auka.

  "Aunty Hafsy yaushe uncle Sulaiman zai dawo"?

  "Ke mutani na cikin damuwa kina wani kira mana Sulaiman ".

  "Haba ai tambayar ki nayi".

  Shiru tayi ma saydat d'in don ta fahimci bata san inda yake mata ciwo ba.ita yanzu tasan ko mutuwa zasu yi cikin wata d'ayan nan karyan su ne suce sun samo makudan kud'i haka gashi Abba ba mai son taimako bane gudun kar wannam azzalumin ya tarwasa rayuwar mai taimakon sa,tho su yanzu ina zasu samu kud'in nan?in basu smu ba kuma haka za'a kulle Abban su har sai randa suka samu.gashi ko an kulle shi basu da ranar samu,kenan haka zai karashe rayuwar sa a kurkuku?yaa Allah ka kawo mana agaji.

  ******
  A bangaren Abba kam ya kasa tsaye ya kasa zaune,ido a rufe yake neman kud'in jinyar 'yarshi kan wata d'ayan nan ya cika saboda baya son shiga kurkuku ya barta da wannan cutar da bata san tana da shi ba a jikin ta,so yake ya raba ta da cutar.

  Ita ma ta kasa zaune ta kasa tsaye ba dare ba rana Addu'a take Allah ya kawo sanadin da za'a yafe ma Abban ta kud'in nan don tasan In ba yafe masa akayi ba bazai samu kud'in ba har Addu'a take Allah ya d'auki ran azzalumin kawai.amma kuma ai ba d'aukan ran shin bane mafita tunda yana da yara.kwata-kwata ita yanzu abun ya kulle mata kai.

  Wayar tace ta fara ringing irin ringing tune na nokia na da d'in nan,hannu ta mika tare da duba sunan.d'an murmushi tayi sannan tayi receiving call din da

  "Amincin Allah ya tabbata a gare ka my......

  "Ya baki karasa sentence naki ba dear".

  Shiru tayi yana kuma jiran ta gama jaa masa aji tayi maganar.aiko hakan ce ta kasance

  "Nayi fushi da kai ai,tun yaushe rabon ka da ka kira ni,ko text ma baka tura mini"

  Ta fad'i hakan tana tura baki.

  "Yi hakuri baby mijin naki ne aikin sa sai.....

  "Thom shikenan tunda kafi son aikin ka".

  tana gama fad'ar haka bata jira ta bakin sa ba ta yanke wayar.kallon ta Sis Faty tayi tana girgiza kai.Maama kam tunda taga yadda Hafsat d'in ke murmushi wajen d'aukar wayar ta gane da wa zata yi magana don haka sai ta fice a d'akin ita in an barta wai kunya.

  Sallamar mutum suka ji daga waje da gudu saudat ta fita don ta gane mai muryar.Sallaya aka shimfid'a masa ya zauna.

  Matashi ne mai kimanin 28yrs kyakyawan gaske sai dai shi ba fari bane kuma ba baki ba,sanye yake cikin kayan mutumci jumper fari tas.

  Sulaiman kenan!

  Cike da girmamawa ya gaishe da Maama inda saudat ke wasa da yatsun hannun shi,Maama kam idon ta a kasa har Allah Allah take su gama gaisawar.suna gamawa kuma ta mike tare da shiga d'akin Abba.gyara zaman sa mai kyau yayi sannan yaja kumatun Saudat

  "Ke ina gaisawa da surkuwata kina ja na da wasa ko?in aka fasa bani auren Addar ki fa"?
  ya fad'a yana ta'be baki.

  "Allah da ka huta sai a baka ni".
  Duk dariya suka kwashe da shi.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Banda abunka me abun so wajen Aunty Hafsy?mutum ba surutu ba,na tabbata ko kalaman soyayya bata iya ba".

  "Ta iya mana,ko bata magana ni a haka nake son abu na,me zanyi da ke"?

  "Haka kace ko wlhy duk randa kuka 'bata kada kace na shirya ku,kuma ko kunyi auren ni ba mai zuwa gidan ku bane".

  "Yi hakuri babbar kawar ango,yanzu je ki kira mini Addar ki na gama kotsawa na ganta.yi sauri tun kafun Abba ya dawo na takura".

  Aiko da wuri ta shige d'aki.

  "Aunty Hafsy Uncle Sulaiman na kiran ki".

  Kai kawai ta girgiza sabodavduk surutan da suke yi tana jin su.hijab ta saka don har ga Allah ita ma tayi missing nashi.

  Nesa da shi ta zauna tare da cewa

  "Sannu da zuwa"
  tana kallon sa.ganin sun had'a ido tayi saurin cire nata cikin nasa.cigaba da kallon ta yayi yana kallon yadda gaba d'aya ta lalace lokaci guda.

  "Baki da lafiya ne"?

  Ya jefo mata tambaya.

  Tana wasa da yatsun hannun ta tace

  "A'ah lafiya ta qalau me ka gani"?

  "Nifa ba irin su saudat bace da in kince ba komai sai na yarda.nace meke damun ki".

  Yayi maganar cikin had'e rai zuciyar ta ne ya fara bugawa.ya dawo da tambayoyin san nan ko.

  "Wlhy ki daina ganin nan gidan surkunaye nane,in baki fad'a mini ba cire hijabin nan naki zanyi naga meke damunki"

  Da wuri ta girgiza masa kai har hawaye ya fara zubo mata tace

  "Accident nayi".

  "What?kiyi accident har ki warke baza ki fad'a mini ba don ban isa da ke ba ko?

  Kai kawai ta girgiza masa.ganin tana hawaye yasa shi jan numfashi sannan yace

  "Yi hakuri ki daina wannan hawayen,ya jikin naki"?

  "Da sauki ta fad'a tana share hawayen ta".

  "Yanzu ke Hafsat kin mini adalci?ai kin san dai auren ki zan yi ba wai yaudara ba,auren da yanzu bai wuce wata biyu zuwa uku ba ya rage shine zaki yi accident baza ki fad'a mini ba?na yarda kina da zurfin ciki amma ai ni bokin rayuwar ki ne".

  "Kayi hakuri insha Allah bazan kara ba".

  "Tho na hakura bayan shi kuma me ke danunki"?

  "Ba komai".

  "Allah yasa ni yanzu zan wuce don kinga gidan surkunaye ne bai kamata na dad'e ba gobe da dare zanzo kada kiyi bacci.

  "Tho Allah kiyaye Hanya".

  Saudat ya kwala ma kira ta fito,hannunta tasa cikin nasa.kallon Hafsat yayi sannan yace

  "Baby na tafi".
  d'an murmushi ta masa.ji yake kamar ya d'auke ta ya tafi da ita don tausayin ta da yake ji.

  A waje kuma tsaraba ya ringa saukewa yana ce ma Saudat ta kai gida.abubuwa dayawa ya musu tsaraba sai dai bai danganci kayan abinci ba saboda akwai lokacin da yayi haka har Abba yaso fasa aurar masa da Hafsat don gani yake kamar ya raina karfin sa.
  Sulaiman saurayin Hafsat ce sun jima suna tare,sonta yake cike da tausayawa.Abba ya yarje mishi ya aure ta saboda yana da hali mai kyau.a halin yanzu ya riga da ya kai goron ta kuma dama wani course yaje yi.shi journalist ne.course na shekara d'aya yaje yi wanda sai jiya ya dawo.

  Wnn kenan!
  Hakeela najin labarin Sulaiman ya dawo ta d'au hanyar gidan su Hafsat.tana shiga da gudu ta fad'a kan Gafsat.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Congrats swthrt Sulaiman ya dawo".

  "Thanks"
  tace da ita.

  "Kinga yanzu zamu sha bikin ku".

  "Hmm".

  Tace saboda ita a yanzu bata aure take ba,ta case d'in Abban ta take gashi ko da wasa bata son Sulaiman yaji labarin.

  "Tunanin me kike"?
  Kai ta girgiza mata alamar babu.hira Hakeela ke janta da shi wani wuri ta amsa wani wurin kuma tace hmm.inda sabo duk sun saba da halin ta,gata da tsoro kamar farar kura abu kad'an kuma sai hawaye zaka ce shogo'be'bbiya ce.sai can gabannin Magarib Hakeela ta koma gida.

  Duk duniya Hafsat bata da kawar da ta fita,ita ce kad'ai ke fahimtar ta In tana cikin damuwa.Hakeela na sonta tsakani da Allah wanda ji take kamar zata iya bama Hafsat rayuwar ta shiyasa ma Hafsat d'in ke sonta.tun da su Hafsat suka dawo anguwan suka shaku da juna don dama sun san juna a makaranta.kullum Hakeela Kan bawa Hafsat labarin saurayin da take matukar son shi amma shi bai san tana yi ba.fuskar wayar ta hoton sa ne,na system nata ma haka.duk hoton sa da ta tsinta a social media zata je a wanke mata shi tayi enlargement nashi tasa a d'akin ta zaka ce d'akin shi ne.hauka kam ba irin wanda bata yi a kansa fatar ta dai randa zata gan shi ya so ta yadda take son shi.Hafsat ma abun na matukar bata mamaki,ita dai tasan ta amince zata auri Sulaiman amma ai bata masa mahaukacin son da Hakeela ke yi ma saurayin ta.kullum addu'ar ta d'aya Allah had'a Hakeela da saurayin ta wata rana.
  Rankatakab anguwan su ba mai shiga gidan su sai 'yan gidan su Hakeela.kowa kyamar su yake ji.su dai basu damu ba tunda ba zamar su suke yi ba...

  *****

  Washe gari kuma kamar yadda Sulaiman ya fad'a sai gashi yazo.kirar ta yayi a waya akan cewa ta fito yau ba zai shiga ba.Hijab nata ta d'auka sannan ta sallami Maama ta fice daga gidan.cikin motar sa ta same sa.knocking na glass d'in tayi sannan ta koma ta jungunu da motar.ba yau ta fara masa haka ba tsam bata da yarda,yayi mita har ya gaji ya barta.fitowa yayi daga cikin motar.gaisawa suka yi sannan ta saci kallon sa ta cire ido.Gyaran murya yayi sannan yace

  "Wai ke yaushe zaki daina abun kamar 'yar kauye ne?ce miki akayi zan cutar da ke?sannan na rasa inda zan cutar da ke sai a kofan gidan ku?

  Kanta a kasa tana wasa da bakin himar nata.kai kaaai ya girgiza don yasan yanzu in yace zai yi fushi ma kuka zata saka masa kamar yarinya karama.sam kuka baya bata wahala.

  "Tunda baza ki mini magana ba kira mini Hakeela mu gaisa".

  Shiru ta masa tana fiki-fiki da ido tare da satar kallon sa.
  Mika mata wayar sa yayi sai ta kar'ba saboda ya gabe nufin ta bata da carty.wayar na fara ringing ta d'an yi gefe.shi dai murmushi kawai yayi ya kura mata ido.so yake Allah ya nuna masa randa zai wayi gari ace ya mallaki Hafsat.komai na duniya insha Allah zai mata,kuncin nan ma duk sai ya yaye mata fatan sa dai Allah sa bayan aure ta canza ta saki jiki da shi.
  Tana gama ta juyo gare sa tare da d'an gurkusawa ta mika masa wayar.shi fa soyayyar tasu har dariya take basa,sai kace a kauye suke.kar'ba yayi da gan-gan ya had'a da hannun ta kad'an.ido ta zaro jikin ta har rawa yake yi da kyar ta iya samo muryar ta tace

  "Ya Sulaiman ka bari dan Allah "
  Dama haka kiran shi.

  "Me yasa zan bari"?

  Hawaye ta fara masa dai-dai lokacin Hakeela ta iso.kallon su tayi cike da sha'awa tana ma Hafsat dariyar mugunta.

  "Ya Sulaiman ai ba hannun ta kad'ai zaka rike ba".
  uwar harara Hafsat ta banka mata
  "Ayya ka bari kar Abba ya ganmu".

  Sakin hannun ta yayi sannan yace

  "Wannan tsoron naki wlhy ki rage sa,ance miki ni zaki ne da zaki ringa tsoro na haka?

  STORY CONTINUES BELOW

  "A mana afuwa,amaryar ta ka ne sai a hankali amma in shaa Allah zan mata fad'a.

  Gaisawa suka yi cikin mutunta juna Hafsat kam nata ido.dama kullum Haka su yi,in sun gaisa dai shikenan sai su kira Hakeela don ita ke tayasu hirar.duk wata magana mai mahimmanci kuma ta waya suke yin shi.

  Sun d'an jima kad'an kafun yace zai tafi.basu wuri Hakeela tayi don suyi sallama.ba tare da sanin ta ba ya matso kusa da kunnen ta.ji kawai tayi yace

  "I love yhu"!

  Cikin rad'a.da wuri ta juyo gare sa amma har ya shiga mota.dan durkusawa tayi dai-dai glass na driver tace

  "Na gode ka sauka lafiya".

  "Wannan kam ai ba wanda yafi ki iyawa ai".

  Murmushi kayi ta masa tana d'aga masa hannu ya wuce.Sulaiman ya riga da ya zama wani 'bangare na jikin ta wanda ji take in babu shi to da kyar ta rayusl sai dai Allah ma yasan sonda take mishi bai kai wanda yake mata ba.mahaifin shi na da kud'i sannan shima yana da aikin yi.

  Tana shiga gida taji karar shigar text wayar ta.dubawa tayi sai gani tayi ya tura mata carty.ajiye wayar tayi sannan ta nufi band'aki don tunda ya kama hannun ta take jin  fitsari Allah ma ya so shi bata masa a wajenba.ita kanta tana mamakin tsoro irin nata.Hakeela da suka gaisa da Maama tana shiri tafiya ta d'au wayar Hafsat tana wasa da shi kan Hafsat d'in ta fito suyi sallama.a kan text na Sulaiman ta bar wayar.

  "Nasan wannan shashashar kawar tawa ko godiya bata masa ba".

  A zuciyar ta ta fad'i hakan.

  Sakon godiya mai d'an had'e da na soyayya ta tura masa.

  Dai-dai lokacin da yayi parking a gida yana kokarin fitowa daga motar text d'in ya shigo.ganin "other Half"nashi ne ta tura text d'in sai ya bud'e yana murmushi.ba karamin dad'I yaji ba da yaga text d'in.
  Hafsat na fitow Hakeela ta mike tana fad'in
  "sai da safe kuma na tura ma Yaa Sulaiman naki text d'in godiya".

  "Kin kyauta,dama in na fito zan tura mishi.jeki dai ki fama da dream Man naki da bai san ki ba".

  Cike da mamaki Hakeela ke kallon ta.wato yanzu Hafsat ma ta fara fallewa.kofan gida ta raka ta sannan ta mata sallama.....
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 8📑*
  *__________*📖

  Tana shiga d'aki ta tura musu kofar don su uku suke kwana a d'akin,ita da Sis Faty sai Saudat,Abba kuma da Maama sai su yaa Abdoul su kuma su biyu don sune kad'ai maza,wurin kwanciya ta shimfid'a a kasa don yau kwanar sis Faty ne a gado,canji-canji suke don katifar bazai d'auke su su uku ba.

  Wasai take jinta cikin farin cikin da rabon da tayi irin sa har ta mance,sosai take nishad'i ko ba komai mai sata farin ciki ya dawo,juye-juye ta ringa yi akan shimdid'ar ta har ji take kamar baza ta iya bacci bama don farin ciki.

  A 'bangaren Sulaiman ma hakan ce ta kasance,ya kasa tsaye bare zaune,sai zaga d'akin yake,ji yake kamar ya jawo kwanaki don yaga ya aure ta,ganin bacci bai yi niyar d'aukar sa bane kuma ko ya kira ta yanzu ba d'aukawa zata yi ba yasa shi yin alwala ya fara nafilfilu.

  STORY CONTINUES BELOW

  Sai can tsakiyar dare bacci 'barawo ya sace sy dukkan su biyu.

  A 'bangaren Hakeela kuma rungume da hoton saurayin nat tayi har bacci ya sace ta.
  Kwana a tashi ba wuya wajen Allah,yanzu da zamar su Hafsat a court sati 2 kenan,baji ba gani kowa na gidan neman kud'i yake duk da sun san karyar su su tara abunda ake bukata,Hafsat kuma tana cigaba da zuwa skull ita da susisFaty inda wata ran Sulaiman ke zuwa d'aukar ta a skull,karatu kam a department nasu ma ita ke ja sosai,wasu muguwa suke kiranta don rashin sonmaganar ta,maganar dai sai in an manna result zaka gani a pepper'n ta.

  Yau ma kamar kullum tunda ta tashi makaranta suke zaune ita da Hakeela zaman jiran Sulaiman amma bai zo ba sai ma kirar su da yayi kan cewa syyi hakuri bazai samu zuwa ba,ko kad'an bata ji haushi ba tunda kullum yana zuwa,Hakeela cewa tayi bari ta kira driver'n ta amma Hafsat ta hanata

  "yau kam kizo mu gwada tafiyar kafar nan da ke".

  "Shikenan muje,amma duk inda muka gaji zamu shiga keke".

  Sam Hakeela ba son tafitar kafar take ba,amma don ta faranta ma Hafsat d'in ne ya sata yarda,suna tafiya suna hira.

  "Hafsy wlhy ko jiya sanda nayi mafarkin mutumi na".

  "Hmm".

  "Ai dama nasan hmm kawai zaki ce,wlhy ko ba don ke bace da sai nace miki ke ma bazan yarda da ke ba indai a kansa ne".

  "Shawara kyauta,ki nemi number wayar sa"

  "Kuma fa kin kawo shawara,wannan ne karo na farko a rayuwar ki da kika bani shawara mai kyau".

  Ta fad'i hakan tana dariya,kai kawai Hafsat ta girgiza don tasan in tace zata biye ma Hakeela sai Allah,tun basu je ko ina ba Hakeela ta fara marairaicewa amma Hafsat tayi kamar bata san tana yi ba,sanda suka yi tafiya mai nisa sannan suka tare adai-dai ta Hakeela sai ajiyar numfashi take saukewa.

  Suna sauka Hakeela ta biya shi sannan suka yi sallama kan cewa sai sun had'u gobe.

  Shigar ta gida ke da wuya ta same su sunyi jugum,kallon su d'aya bayan d'aya ta fara yi don inda sabo ai gidan su ya saba da shiga tashin hankali,tho na yau kuma ko wace irin tadhin hankali ne sai Allah.

  Bakin ta d'auke da sallama ta karasa,kallon su ta sake yi jiki a sanyaye ganin yau uban masu zuciyan baya wurin tace

  "Abba sannun ku,sis Faty lafiya kuwa"?

  Numfashi sis Faty taja sannan tace

  "Court ne suka turo wasika kan cewa nan da sati biyu in bamu kawo kud'in nan ba duk hukuncin da Alhaji Munir yace a yanke mana shi za'a yanke mana".

  "Innalillahi wai shi wani irin mugu ne?sam bazai bar mu mu numfasa ba"?

  "Kada kice haka Maama na".

  "Gaba Abba har tsawon yaushe zaka cigaba da hakuri?kana ganin tundahar Hafsat ma tayi magana ai abun yayi yawa ne".
  cewar Hamma Naseer.

  Shiru duk suka yi,Abb yasan inda zalunci ne tho lallai Alhaji Munir ya cika azzalumi,amma baya son yaran suna fad'an haka ko ba komai ai ya girme su.

  "Abba yanzu ina zamu samo kud'in nan,ka dai san in suka saka a kurkuku bamu da ranar samun wannan kud'in bare mu biya".

  "Kada ku damu,insha Allah hakan bazai faru ba".

  "Abba.......

  Bai jira ta karashe maganar ta ba ya mike don sam baya son ranta yana 'baci gashi har yau ya kasa fad'awa Maama cutar da Hafsat d'in ke d'auke da shi.

  Yana fita a gida asibiti ya wuce,wajen doctor'n da ya sanar da shi cutar da Hafsat d'in ke d'auke da shi yaje,ya koyi sa'a ba abunda doctor'n ke yi,vayan sun gaisa sai ya fara magana

  STORY CONTINUES BELOW

  "Doctor dama batun 'yata Hafsat ne na dawo,yanzu ba wata hanyar da zamu bi don yaye mata wannan cutar kafun Allah ya bamu kud'in mata jinya"?

  Kallon sa doctor yake tun da ya fara magana,lallai wannan mutumin abun tausayi ne,Allah mai iko,ga can masu kud'i suna rayuwar su yadda suke so ba abunda ke damun su,amma wannan mai nema da kyar shi ne Allah ya jarabci 'yar sa da wannan ciwon,kenan wannan ita ce tashi kaddarar,numfasawa doctor yayi sannan yace

  "Akwai hanya mana malam,akwai maganin da zaka saya mata sai ta ringa sha kullum insha Allah zata d'an ji sauki kan Allah ya baku kud'i sai a mata operation d'in".

  "Doctor kud'in zi kai kamar nawa?

  "Na sati d'aya dai dubu biyar ne".

  Cikin jimami ya fitar da kud'in daga aljihun sa,a dunkule kud'in suke,warwarewa ya fara yi sannan ya mika ma doctor,no ba'a nan zaka biya ba,zan rubuta maka maganin sai kaje ka saya,tho yace bayan doctor ya tubuta masa magani ya masa sallama sannan ya fice.

  Tausayin sa sosai doctor yaji amma yasan ba yadda za'a yi ya taimake sa,layin biyan kud'i ya shiga,ya shima a layin kan aka kso kansa kud'i ya mika bayan an basa receipt sannan ya tafi ya kar'bo maganin.

  "Yanzu wannan maganin ne dubu biyar?nida ban san sati nawa nayi ins tara wannan kud'in ba,don ma Allah ya soni in nayi dako ina samu ne,amma insha Allah zan na kolarin saya mata duk sati kan azo case nawa".

  Komawa gida yayi inda ya tarar har yanzu jimami suke,zama yayi yana kallon Hafsat d'in.

  "Maama na zo ga maganin ki".

  "Magani kuma Abba?me yasa ka saya ai na warke".

  "Ke dai zo ki kar'ba kawai batun warkewar ki ma bata taso ba,ina fata kinci Abinci?

  "A'ah yanzu hamma Naseer ya samo kud'i yayi shefene yanzu za'a d'aura".

  "Tgo ki tabbata in an gama bayan kin ci kisha magani".

  "Insha Allah Abba,amma magabin na me ne?

  Zuciyar sa ce ta buga,daurewa yayi ya d'auro murmushi a fuskar sa sannan yace

  "Doctor ne yace a ringa baki".

  "Tho na gode Abba Allah saka da alkhairi".

  "Ameen!ni bari na fita muga ya Allah zai yi da mu".

  "Allah bada sa'a a dawo lafiya".
  cewar Maama.

  Yana fita suka mike domin d'ura abinci suka bar Maama na tsince shinkafan,garau-garau ne don dama shine abinci talakawa a cewar wasu,basu jima sosai ba suka kammala don dama dukkan su basu sanyi da aiki.

  Zama suka yi tare da Maama suka ci inda zuciyar Maama ke rad'a mata Hafsat ta kusa daina cin abinci da ita,ita duk lokacin da abun nan yazo zuciyar ta tunani take ko mutuwa 'yarta zata yi,don ta kura akwai matsala don rabon Abba da ya kawo shefene gidan gaskiya ya kwana biyu,gashi kuma baice kwace masa akeyi ba,yanzu kuma ya sayo magani ya kawo wai ta ringa shaa.

  "Maama lafiya kuwa"?

  "Wlhy Hafsat naso tura ki can garin mu kije ki karasa karatun ki ko wajen goggon ku Zainab amma Abban ku yak'i,ban san me yasa ba zaman ki a nan sam bana so,da muna da hali wallahi da na aura ma Sulaiman ke,don zaman ki ba auren nan ma bana so".

  "Maama ki kwantar da hankalin ki,batun aure kuma ai ga Sis Faty ma hata yi ba me yasa ni kad'ai zaki jiyema tsoro,ki cire duk wani ugin shed'an a zuciyar ki dan Allah ".

  "Shikenan".

  Ita kanta sis Faty tafi son Hafsat tayi aure don ita a ganin ta karshe yaran Alhaji Munir zasu iya mata fyad'e sabod sun ganta kalar tausayi.

  STORY CONTINUES BELOW

  Ita dai Hafsat ta rasa dalilin da 'yan gidan duk suka fi karkata hankalin su a kanta fiye da kowa,ko dai ita ma hasashen ta na ta kusa mutuwa gaskiya ne?a haka har suka gama cin abinci sannan suka yi d'an aikace-aikacen gidan da baza'a rasa ba sannan ta sha magani,tana gama sha ta kwanta da niyar huta gajiyan skull Sulaiman ya tura a kirata,kamar bara taje ba don d'azun ya gama cewa yana da aiki amma yanzu har ya gama.ko da yake ya jima ai,hijan d'inta ta d'auka sannan tace ma Maama bari taje ta fice .

  Kamar kullum cikin motar sa ta tarar da shi,knocking ta mishi tana mamakin zuwan sa da la'asar nan,fitowa yayi yana kallon ta har cikin ido,hakan kuma ba karamin sata tsarguwa yayi ba.

  "Sannu da zuwa yaa Sulaiman ".

  "Yauwa kin dawo lafiya"?

  "Ehhh amma ai da baka zo ba tunda kace kana da aiki".

  "Nazo ne naga ko ran baby na ya 'baci".

  "Laa wlhy ba komai banyi fushi ba".

  Gyara tsayuwar sa yayi sannan yace

  "Hafsat nazo batun auren mu ne fa,so nake cikin wani sati na tura kud'in auren ki".

  shiru tayi tana nazari,tunda har Maama ta nuna tana son tayi auren ya kamata tayi amma kuma ai wani sati zasu koma court.

  "Tunanin me kike yi ne"?

  "Da so sanu ne ka bari sai sati na sama don ina son yin shawara da Maama kasan ba yadda za'a yi na yankewa kaina hukunci" .

  "Haka ne,dan Allah kiyi abu da jiki cux na gaji da zama ba mata".

  Ido ta zaro masa tana mamakin yau kuma da irin salon da yazo kenan?a ina kuma ya koyi irin maganar nan?

  "Hello"!!
  sanda ta tsorata.

  "Insha Allah amma pls ina son neman alfarma a wajen ka".

  Kan ya amsa wayar sa ta fara ringing.

  "Excuse me".
  Yace sannan ya amsa wayar,bayan ya gama ya kalleta tare da fad'in

  "Baby an kirani cikin next week d'in ma zanyi tafiya".

  Ajiyar zuciya ta sauke wanda sanda yaji.

  "Ina sauraron ki wace alfarma kike nema"?

  "shikenan ya wuce".

  "ina fatan dai ba abu kike 'boye mini ba"?

  "No ba komai wlhy".

  "Tho ni zan wuce kuma na gode don yau kam kin min surutu sosai,ina fatar a hankali-hankali zaki canza".

  Murmushi ta mishi tare sa masa sallama ta shige gida.

  Shi kullum mamakin irin soyayyar tasu yake,sai kace auren had'i,sam ba kalaman soyayya sai dai kunya.

  "Alhmdll da Yaa Sulaiman zai yi tafiya,satin da za'a yi case na Abba baya nan,dama tunanin yadsa zan fara cecmasa next week kar yazo wuri na nake sai gashi Allah ya taimake ni,Allah na gode maka.

  ******  ********  ******
  Rana bata karya sai dai......inji 'yan karin magana,yau Monday kuma yaune ya kama ranar da su Abba zasu koma court,ba abunda suka tanadar sai lawyer'n su da yake fatan suyi nasara don shi kansa yau bai san nayi ba,gaba d'ayan su shiryawa suka yi suka nufi court d'in.
  Suna shiga harabar court d'in suka manyan motoci a jere kusan guda 5 da alama yau kuma Alhaji Munir da rundunan sa sun zo court d'in lallai abu ya 'baci....
  Share
  Comments

  ©Hafciey
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  STORY CONTINUES BELOW

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 9 📑*
  *__________*📖shiga court d'in suka yi duk zuciyar su na dukan uku-uku,Barrister jibril ne a gaba da Yaa Abdool sai su Abba da. Hamma Naseer suna biye da su,su Maama kuma sune a karshe wanda Hafsat ce karshen shiga court d'in.

  Ahalin gidan Alhaji Munir suna zaune da iyayen su,Alhaji Munir kyakyawan dottijo ne mai kimanin shekara saba'in da biyar sai matar sa wacce ke gefen sa ita ma kyakyawa da ita,kallo d'aya zaka musu kahi sun shiga ranka sai dai kashe basu da hali mai kyau,yaran sa na daga bayan sa,lawyer'n sa kuma yana can hakimce zaman jiran lawyer'n Abba.

  Ko da suka shigo neman wurin zama suka yi inda gaba d'aya zuciyar su ke bugawa don su san ryau kam da kyar nasara ta zama tasu.

  Mikawa alkali takardar su akayi inda ya bud'e sannan aka fara kara,tun farkon abun ma yau sun san ba dad'i ko kad'an yayinda ahalin Alhaji Munir ke jifan su da kallon tsana.

  lawyer'n Alhaji Minor  ya gama gabatar da jawaban sa inda Alkali yayi gyaran murya

  "yanzu dai ba hujja da malam Musa zai kawo kotu ta yarda da shi tunda ya tabbatarwa kotu lallai yaci bashin Alhaji Munir,don haka muna jiran sa da kud'in don watannin da aka basa ya cika".

  "ya mai girma mai shari'a ko wannan kotu mai adalci zata bani damar gabatar da hujja ta ta karshe"?
  Cewar Barrister jibril.

  "Muna sauraron ka"!

  "Ba wai ina da ja da abunda wannan kotun bane kan hukuncin da zata zartar,amma kuma ya kamata ayi la'akari da halinda yake ciki,a halin yanzu burin sa bai wuce ya warkarwa 'yar sa cutar da take yawo da shi bane".

  "Objection my lord,ai mu ba zama mukayi a nan don a fad'a mana wanda ke da lafiya da kuma wanda bayi da shi ba cikun ahalin sa,kud'i aka ce ya kawo,kuma ai zai iya amfani da 'yar sa wajen ganin ya kwato kansa".
  cewar Barrister Alhaji Munir.
  "Lawyer mai kare wanda ake kara ko kana da hujjar tabbatarwa kotu kan cewa 'yar sa ba lafiya".

  "Ehh ina da shi saboda tare muke da doctor ".

  Gayyatar Doctor aka yi zuwa inda zai bada statement nasa.

  "Ya mai girma mai shari'a 'yar malam Musa na d'auke da cutar da ya kamata a tausaya mata".

  Kallon-kallo Hafsat ke yi da Maama inda 'yan gidan Alhaji Munir kuma ta'be baki suka yi don sun san yau dole za'a yita ta kare.

  "'Yarsa na d'auke da wata rami a zuciyarta wanda yake barazana ga rayuwarta sannan kuma zata iya rasa rayuwarta a ko wani lokaci kn har ba'a mata surgery ba wanda a kasar waje zasu yi shi ba a nan ba".

  Zaka iya komawa wajen zaman ka doctor mun gode.cewar Barrister jibril.

  "Ya mai girma mai shari'a kana ganin in har malam Musa na da kud'in da zai biya bashin nan da bai kai 'yar sa jinya ba?rayuwar 'yar sa na gaba da zaman gidan kurkuku da zai yi,shi abun tausayi ne kuma kamata yayi a tausaya masa".

  Kowa jingina kai yake don gaskiya sun cancanci a tausaya musu,Hafsat kuma wasu hawaye ne masu d'umi suke keto mata Abba ko sai jinjina kai yake inda Maama ta rungume Hafsat d'in a jikin ta,iyalan gidan Alhaji Munir kuwa ko girgiza ba wanda ya zirgiza bare su tausaya musu.
  STORY CONTINUES BELOW

  "A matsayi na na alkali mai adalci dole nayi hukunci bisa adalci,malam Musa na tausayawa 'yar ka da kuma halin da take ciki sai dai kuma ya zama dole yau a saka a kurkuku".

  Nannauyan ajiyan zuciya Abba yaja.
  Mikewa Barrister Alhaji Munir yayi sannan yace

  "Kuma bayan ansa shi a kurkuku iyalan sa zasu koma aikin bauta a gidan alhaji Munir har sai randa suka samo kud'in".

  Hafsat dafe kahon zuciyarta tayi ganin yadda rayuwa ta sake sauya musu,mikewa take kokarin yi amma ta gagara sanda ya Abdoul ya taimaka mata,rintse idonta tayi hawaye na fita tace

  "Dan Allah alkali kada a bar Maama na da 'yan uwa na suyi aiki a gidan su,ni zanje na musu duk wata bautar d suke bukata".

  Ta karashe maganar tana damke kahon zuciyar ta.

  Police ne yazo yasa ma Abba ankwa a hannu a wurin Hafsat ta durkushe tana kuka mai cin rai,tafiya da Abba aka fara yi inda suka fara jiyo sautin takun kafar mutum,tasayawa suka yi tare da zurawa kofar shigowar ido.

  Tafiya yake cike da izz da kuma ji da kanshi,tularen sa ne ya fara ankarar da mutani cewa wannan na miji ne ba mace ba,karasa shigowa yayi,matashi ne mai kimanin 32yrs fari sal da shi idanunsa manya-manya sai wani 'bata rai yake yi sanye yake cikin kananan jumper fari hannun sa sanye cikin aljihun sa.

  "Yaa HYDAR!!!
  Cewar d'aya daga cikin yaran Alhaji Munir.

  "Ya mai girma mai shari'a sunana Aliyu d'a ga Alhaji Munir ina mai bada hakuri bisa makara da nayi".

  "Ba komai"
  cewar alkali.

  Matar dake zaune kusa da Alhaji Munir ne tace

  "Alhaji ta dakatar da wannan gagarerren d'anka don wlhy ruguza komai zai yi".

  "Alkali gaskiya hukuncin da aka yanke tsam bai mini ba".

  Kowa kallon-kallo ake ma juna da magana kasa-kasa inda Hafsat ke durkushe a kasa tana kuka ciki-ciki.

  "Malam Musa yace bai da kud'in biya kuma kunga halin da 'yar sa take ciki,ni a shirye nake da na yafe masa bashin da mahaifi na yake bin sa yanzu amma a bisa sharad'i d'aya".

  "Alhaji nace maka ka dakatar da shi ba hankali bane fa gare sa".

  "Kar ki damu Hydar duk abunda zai yi yana da hujjar sa nayin hakan".

  Ai da wuri Hafsat ta mike idanunta zagir ko gani bata yi saboda babu glasses a idanun ta,fuskantar inda ta juyo muryar wannan Aliyun tayi sannan tace

  "A shirye nake da d'aukan ko wace rin sharad'i".

  "Fine tunda haka kika ce,alkali ka zama shaida ni Aliyu Hydar zan Auri 'yar Alhaji Musa Hafsat a bisa auren bashi,sannan kuma na yafe ma Babanta bashin da ake binsa duniya da lahira.
  "Ban yarda da wannan tayin naka ba".
  Cewar Abba.

  "Ni kumaHafsat 'yar malam Musa na yarda da auren d'an Alhaji Munir in har zai yafe ma baba na bashin sa".

  "Nima Alhaji Munir ban yarda d'a na ya auri 'yar talakawan nan ba".

  Tashin hankali!iyaye basu so yara kuma naso.
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•


  STORY CONTINUES BELOW

  *SHAFI NA 10📑*
  *__________*📖order!!!Alkali ya buga gudumar sa,nan take wajen yayi shiru.

  "Ku sani nan fa kotu ne ba kasuwa bane da zaku tsaya cece kuce,na baku minti biyar kuje ku shawo kan iyayen ku in ba haka ba kuma na zartar da tawa hukuncin".

  Fita Hydar yayi ba tare da yace komai ga mahaifin sa ba.

  "Alhaji tashi muje tun kan yaron nan ya samu jin kunya a idon jama'a".

  Mikewa suka yi a tare inda suka tarar da shi a wajen court d'in yana waya cikin nitsuwa,dafa kafad'ar sa mahaifin nasa yayi,juyowa yayi ya kalle sa
  "Hold on,zan kira ja anjima"

  Kashe wayar yayi sannan ya kalli mahaifin nasa

  "Dad lafiya kuwa"?

  "Ji iskanci,yanzu ya gama jagula mana lissafi a ciki sannan yanzu kuma yana tambaya afiya kkuwa"

  "Umma tunanin me kike yi"?
  da sauri tace babu.

  "Dad nasan kunzo jin dalilin da yasa nace zan auri Hafsat ce".

  "Ehh haka ne don gaskiya nikam hazan barka ka aure ta ba".

  Murmushi yayi tare da fad'in
  "Hmm,nasan dai a duniya baka kaini tsanar Malam Musa da ahalin sa ba,amma tunda nacw ina son auran 'yarsa ka yarda kawai bazan baka kunya ba I promise ".
  "Ban yarda ba kuma bazan yarda ba".

  "Dad trust me nace maka ina da reason na nayin haka,kuma dalili na ba komai bane sai ganin rashin amfanuwa da sa malam Musa a kurkuku da zaka yi,shine sanadin da har yau farin ciki na ya gaza dawa,ya ruguza rayuwa ta da na 'yan uwa na,ya cutar da mu,ya azabtar da mu sannan kuma kullum cikin cusa mana bakin ciki yake".

  shiru yayi na d'an wani lokaci sannan ya cigaba

  "Zan auri 'yarsa Hafsat kasancewar tana da ciwon zuciya wadda barazana ne ga rayuwar ta,zan ringa kashe ta kullum amma kuma tana raye,zan tabbatar da malam Musa ya tsani kansa,na tabbata duk randa yaga halin da 'yar sa ke ciki sai zuciyar sa ta buga ya mutu,bazan tsaya iya nan ba har sai na ruguza farin cikin ahalin sa kamar yadda yayi ma nawa".

  "Weldone Hydar!weldone"
  Cewar Daddy.

  "Gaskiya ni ban yarda da wannan shawarar ba,kana ganin wannan idanun Hydar kamar maye har shi zai ga mace ya bari".

  "Na yarda da d'a na,kar ki damu".

  Shi dai wucewa yayi bai ce da ita komai ba tunda ya samu yardar wanda yake so.

  A bangaren su Hafsat kuma suna fita waje ya Abdoul ya d'ebe ta da mari

  "in baki cikin hayyaacin ki ma yanzu sai ki dawo,kin san me kike shirin aikatawa kanki kuwa,aannan Hydar ba imani ko kad'an cikin zuciyar sa,so suke su kashe ko lokaci guda".

  "Ba ruwanka tunda rai nawa ne ba naka ba,kuma na tabbata da kaine ka tsinci kanka a halin da nake ciki kaima haka zaka yi".

  "Ohhh Allah na!Hafsat har yau fa baki san zafin ciwon kan ki ba,na yarda bamu da kud'in da zamu miki jinya,ina mai tabbatar miki zaki gwammaci ki mutu a gida da ki mutu a hannun wannan azzalumai".

  "Maama na kar kice zaki d'auka wannan hanyar saboda zaki kai kanki ga halaka,a shirye nake da naje ko wani mataki amma bazan bar ki ki auri Hydar ba saboda nafi ki sanin su waye su".

  "Abba in har kayi imani da kaddara to ka barni na auri Hydar,sannan komai kaga ya faru dani kaddara tace,wahala ko zalunci ba zai kashe ni ba in har kwana na bai kare ba,dan Allah Abba ban ta'ba neman alfarma a wajen ka ba amma gani yau ina nema,ka barni nayi auren nan tunda bai tsa'bawa Allah ba".
  STORY CONTINUES BELOW

  Zai yi magana tayi saurin had'a hannunta waje d'aya

  "Dan Allah nace Abba,kawai kayi addu'ar Allah sa hakan shine mafi alkhairi".

  Cikin jimami yace

  "Allah miki albarka Hafsat".

  "Ameen".

  Tace tare da rungumar sa tana kuka,ita kanta tsoron gidan take ji amma karfin hali kawai take yi.

  Maama kam har ta gama ganin an kawo mata gawar  'yarta inda sis Faty ke tausayin rayuwar 'yar uwar ta,don kawai ta kubutar da Abba ta jefa nata rayuwar cikin hatsari,Allah kai kad'ai kasan dalilin d'aura mana wannan bakin talaucin kuma kai kad'ai zaka iya fidda mu".

  "Abba muje,lokacin da alkali ya bayar har ya wuce".
  Cewar Hafsat d'in.

  Ya Abdool kam ji yake ina ma a barsa yayi ta dukar ta har sai ta dawo hayyacin ta.

  Komawa ciki suka yi inda su kad'ai ake jira,kallon Abba alkali yayi sannan yace
  "Malam Musa shin ka amince da wannan auren"?

  Shiru yayi har saida alkali ya maimaita tambayar a karo na biyu.

  Rintse idanun sa yayi sannan yace

  "Na amince amma....

  "Zance ya kare tunda ka amince,dama kai kad'ai ake jira don Alhaji Munir ya amince shima.

  "Innalilah,ni Musa nayi sanadiyar rugujewar rayuwar 'yata wacce ke fama da cuta,me yasa na biyewa zuciya ta?yarinya ta a shirye take don cece na,sannan ni kuma na bada rayuwar ta zuwa ga halaka,na tabbata Allah ba zai barni ba".

  Duk cikin zuciyar sa yake wannan zancen.

  "Alkali kuma karashe sari'a yayi inda yace zai halarci auren im Allah ya yarda.

  kallon su Hafsat yaran Alhaji Munir suke gani suke kamar kura aka bawa ajiyar nama.

  Watsewa aka fara yi inda kowa da kananan maganganun da yake.

  Ahalin Alhaji Munir kuma mota suka shige suna farin ciki don ko ba komai yanzu zasu ci uwar Hafsat yadda suke so ba tare da kowa yace komai ba.

  suma Hafsat hanyar gida suka kama cikin jimami,suna isa gida wayar ta ta fara kara.glasses nata tasa inda taga sunan
  Yaa Sulaiman

  A screen na wayar.

  "Innalillah tace don ta manta da baikon sa dake kanta.

  Muje zuwa💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃wasa farin girki.yanzu muka fara.

  Ina mai baku hakurin typing kad'an-kad'an da nake,wlhy test nake kuma ina baran addu'ar ku.
  Nida typing sai monday
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•


  *SHAFI NA 11📑*

  Innalillahi!!lallai duk abunda ya samu bawa Allah ne ya kaddara masa,wannan ita ce taka kaddarar isa,Allah baka lafiya dan uwa na.broda na yy accident ku tayamu da addu'a

  STORY CONTINUES BELOW

  *__________*📖hannunta har rawa yake amma ta kasa receiving wayar,yau me zance masa da zai yarda?wannan wace irin hali ne na tsinci kaina?jarabawar yau daban ta gobe daban,ya Allah ka yaye mana.

  Suna isa suka shiga gida jikin su duk a sanyaye,hanyar d'aki ta nufa Abba ya kira ta.

  "Hafsat ".

  "Na'am".

  "Yanzu kina ganin hukuncin da kika d'auka shine dai-dai?da wani idon kike son na kalli Sulaiman da iyayensa?so kike su d'auke ni mutunin banza?na tabbata komai ya faru da bawa kaddarar sa ce,zuwa gidan yari kaddara tace da baki dakatar ba".

  "Abba nima auren Hydar kaddara tace,rashin auren Sulaiman kuma kaddarar sa ce,dukkan mu uku ba wanda ya isa ya tsallaka kaddarar sa".

  "Banki ta naki ba,amma ke me kike tunanin zai ce,nayi biyan bashi da 'yata?

  "Abba in har zaka ringa tunanin yadda al'umma zasu fassara wannan abun tho fa baza ka iya da su ba,wani har abunda baka ta'ba kawa ranka ba zai kawo,don Allah maganar nan ta mutu a nan".

  Tana gama fad'ar haka ta mike zuwa d'aki zuciyar ta sai bugawa yake yi,Allah ma yasan duk abunda take yi dauriya ne don ita kanta tsoron gidan take ji,to ma waye wannan Hydar mai bakin zuciya da har ya iya hasasho wannan muguntar?mtsww ta Allah ba tashi ba.

  ***** ****** *****

  Tun daga ranar da akayi maganar auren Hydar da Hafsat 'yan gidan su suke cikin tashin hankali,tsam sun san kashe ta zasu yi a gidan,ita ko daurewa take yi ta hanyar nuna ko in kula,kuma yanzu auren saura wata d'aya kamar yadda suka ce suke son auren.

  Sosai Hakeela tayi bakin ciki jin an tsaida auren Hafsat nan da wata d'aya sannan kuma bada Sulaiman ba,rokon ta Allah annabi Hafsat ta ringa yi kan kar ta fad'a masa komai,as usual suna waya kamar ba komai.
  Alhaji Munir!!!

  'Dan asalin gombe ne wanda yake da jini da sarauta kasancewar sa d'an sarki,sai dai tsam shi ba son sarautar yake ba,sai ayi a sud'e a gidan sarauta babu shi.

  Harkar kasuwanci ya fara inda da yarda Allah ya samu kar'buwa don yanzu da shi ake ji a fannin kud'i.

  "Allah ya azurta sa da 'ya'ya da yawa,inda Maryam ce first born nashi sai kuma Zainab,daga ita sai Allah ya azurta sa da d'a na miji wato Hydar,bayan Hydar kuma sai Khaleel daga shi Amsa'u,khadija,Aisha,a takaice dai rayansa 8,inda shida mata biyu maza.
  Anty Maryam da Zainab sunyi aure da jimawa inda suma suna da yara uku-uku don tare akayi auren su,khaleel dai ganin ubansa nada komai yasa ko sana'a baya yi sai Hydar,inda sauran yaran kuma yanzu suke degree nasu,gidan dai kullum cikin rigima ake don sa'i da lokaci kakar su Hajiya Nenne takan zo gidan ta dad'e,kwanciyar hankali sam basu san shi ba kullum nuna 'yan ubanci ake,ba mai shiga shashin da bana uwar sa ba don mata biyu Alhaji Munir yake da.

  Munafurci ba wanda bai iya ba a gidan sai dai na wani yafi wani,kowa ba son d'an uwansa yake ba,amma kuma in anzo kan Malam Musa don tsanar da suke masa sai su had'a kai wajen ganin sun ruguza rayuwar sa.

  Khaleel irin yaran masu kud'in nane masu shaye-shaye,ya kan shigo gida baya hayyacin sa amma Mahaifiyar sa baza ta taba bud'an baki don masa holo ba.
  ****

  Gida ce babba yaji komai na more rayuwa,ko ina shiru kake ji,daga cikin gidan ta shan gefe akwai 'bangare biyu,wanda d'aya ya kasance na Hydar d'aya kuma khaleel.

  'Bangaren Alhaji kuma yana cikin gidan inda ya kasance gidan sama kuma a wurin matar sa da yaran sa mata suke,sai d'akin Hajiya Nenne in tazo.

  Falon shiru ba abunda ke aiki sai A.c da t.v,komai a falon neat yake kamar ba mutum.

  STORY CONTINUES BELOW

  Umma ce ta sauko daga upstairs inda Khaleel ke biye da ita a baya kamar wanda zai sha nono,a falo suka yad'a zango.

  "Wlhy umma ni tsam ban yarda da auren da Hydar zai yi ba,ya fake da zaici zarafin yarinya bayan shi kad'ai yasan me ya hango".
  "Aini tun farko nace ma Alhaji kar ya barsa,saboda nasan auren nan don amfanuwar kansa zai yi,mutum yana nan kullum fuska a tamke sai bakin hali".

  "Tho Umma kiyi wani abu mana,kinga auren ya kusa".

  "Ba abunda zanyi,bari dai muga iya gudun ruwan sa,don wallahi bazan barsu a d'aki d'aya ba".
  Tana gama rufe bakinta Hydar yasa kai cikin falon,sanye yake da half jumper black,sai hular da ya kafa a kansa,karya ne in ka gansa kace ba magidanci bane,duk da kasancewar sa d'an zamani kuma saurayi tsam bai fiya sa kananan kaya ba,in ka gansa da su tho a cikin gida yake,office kuma suit yake sawa,fuskar nan a tamke kamar koda yaushe.

  Wucewa yayi ba tare da yace da su komai ba

  "Dan Allah dubi rashin tarbiya".
  Cewar Umma,tana gama fad'ar haka ya tsaya cak tare da juyowa ya kalle ta,kasa tayi da kanta shi kuma girgiza kai yayi ba tare da yace komai ba yaci gaba da tafiya.

  Yana gama hawa upstairs yayi hanyar dama inda ya murd'a kofar wata d'aki a hankali,ba kowa a falon sai t.vn da ke aiki,direct bedroom ya wuce inda ya shiga da sallama.

  Wata mata ce kwance a kan gadon wacce ko baka tambaya ba kasan mahaifiyar sa ce,kallon ta yayi na d'an wasu mintuna sannan yaja dogon numfashi.

  "Ammi an wuni lafiya".

  Ido kawai ta lumshe,hannunta ya kamo tare da sa nasa cikin nata hannun

  "Allah baki lafiya Ammi,ki gafarce ni na rashin shawar ta ki,ni Hydar zan yi aure cikin wani wata".

  yadda yaga fuskar ta ya sauya hakan ne ya tabbatar masa cewa taji dad'in zancen auren nasa,hannunta ya d'aura bisa kansa da sunan ta sanya masa albarka.

  Ammin Hydar dai she is paralysis,ba inda ke motsi a jikin ta banda ido,komai na duniyar Allah sa an mata wanda yanzu da faruwar sa kimanin shekara uku kenan,kuma kowa yasan mahaifin Hafsat ne sila,wannan dalilin yasa Hydar shan alwashin sai yaga bayan farin cikin su a duniya.

  "Ammi naso ace kina da lafiya zanyi wannan auren"?

  Lumshe ido ta kuma yi.

  "Ammi 'yar malam...

  Bai gama karasa zancen sa na fad'a mata wacce zai aura ba wayar sa ya fara ringing,receiving yayi inda aka tabbatar masa ana jiran sa a office.gyara mata kwanciya yayi sannan ya kunna mata t.v tare da mata sallama ya fice.
  Kullum haka take rayuwa sai an d'aga sai an kwantar,abinci sai an bata,wanka sai an mata,ko farce d'aya bata ta'ba d'agawa ba,ba inda basu kaita jinya ba abun yaki,karshe dole suka dawo gida aka had'a da addu'o'i amma har yau ba nasara.

  Binsa da kallo kawai tayi a zuciyar ta take son masa magana amma ba hali.

  Yana rufe kofar yaja ajiyar zuciya don shi kad'ai yasan me yake ji duk lokacin da yaga mahaifiyarsa,sannan kuma tsanar Mal musa da kuma duk wani mai sonsa ke karuwa cikin zuciyar sa.

  Dai-dai ta kansa yayi sannan ya sauka downstairs cikin sauri,inda ya barsu nan ya tarar da su,ko ci kanku baice musu ba ya fice abunsa.

  "Banza"!

  "Fad'a kanka tsaye,wai shi in an barsa yana neman kud'i".
  *****

  'Bangaren Hakeela kuwa kullum zurfi take yi cikin son wanda bai san tana yi ba,zuwa yanzu kam bata da wata burin da ya wuce ta gansa,ta samu number'n sa amma ko ta kira baya d'agawa,hakan ba karamin d'aga mata hankali yake ba,don so take suyi aure tare da Hafsat.

  STORY CONTINUES BELOW

  As usual sun fito daga skull suna zaune kasar wata bishiyar don sai nan da minti talatin zasu koma lectures,kallon ta Hakeela tayi tana fad'in

  "Hafsat me zai hana ki fito fili ki gaya ma Sulaiman halin da kike ciki,ko so kike yaji a wani wur"?

  "Gaskiya bazan iya ba,wlhy tsoro nake ji".

  "Har yaushe zaki cigaba da tsoron nan naki ne?ke tsam abu ko bana tsoro ba sai kice kina tsoro".

  "Baza ki gane bane,kamar fa ke da dream Man naki ne ace wani zaki aura bashi ba".

  "Cab wlhy ni banga wacce ta isa ta kwace mini dream Man na ba,he is only made for me"

  "Kin ban dariya wallahi,mayb ma yana da mata".
  "A'uzubillah!Hafsat in har bakin ki bazai fad'i alkhairi ba gwara kiyi shiru,wannan wani irin mugun baki ne"?

  "Yi hakuri bazan kara ba,gaskiya kina son dream Man naki".

  "Son da ko Maamar sa ina ga bata masa".

  "Tho Allah bar kauna"

  "Ameen kawa ta,maganar auren ki fa"?

  "Ban gane ba".

  "Ina nufin batun shirye-shiryen da zamu yi".

  "Hmm Hakeela kenan,kin manta cewa ina d'auke da ciwon zuciya ne?rayuwa kalilan ya rage mini kuma na tabbata a gidan Alhaji Munir zan kare wannan rayuwar".

  Jikin Hakeela sanyi yayi.

  "Kawa ta ki daina fad'in haka don wallahi jiki na mutuwa yake".

  "Tho ya zamu yi ai shine gaskiyar don dole ne mutuwar nan zamu yita,don haka ni bazan ta'ba yin wani shirin shiga gidan Alhaji Munir ba,babbar matsala ta su barni naci gaba da zuwa skull ne".

  "Insha Allah zasu barki tunfa su ba jahilai bane".
  "Allah yasa,don yanzun ban son nuna musu ina so bare suji dad'in hanani".

  "Kinyi dabara mai kyau".

  Kwanci tashi ba wuya wajen Allah yau auren Hafsat saura sati biyu,amma har yau shiru kake ji ba wanda yazo daga gidan angwaye ko kuma ya aika wani abu duk da cewa dama su basu sa ran zuwan komai ba.

  A 'bangaren angwayen kuma sai shirye-shirye suke baji ba gani domin fita kunyar duniya,ko da auren na cin zarafi ne baza su zuba ido martabar su ya zube a idon jama'a ba.

  Sosai suke shiri ga yadda aka aake gina apartment na Hydar inda ya zamar da shi 2 bedroom sai 1 falo,a cikin falon akwai dining sai d'an karamin kitchen gwanin sha'awa,apartment nasan ba wani girma yakeda shi ba amma gaskiya ba karamin kyau yayi ba,sai dan katangar da aka masa tare da sa gate,daga gefe kuma aprtment na Hydar ne.

  Sosai ya kashe kud'i ya labta furnitures a falon da bedroom d'in don shi yafi son komai yayi ma kansa

  Komai neat zuwan Amarya kawai suke.

  cikin gidan ma ba'a barsu a baya ba domin sun canza komai na gidan,kullum Aunty Zaynab da Maryam a gidan suke wuni domin sjirye-shiryen biki don ko ba komai yaci suyi ma Hafsat tarbar da tafi wannan tunda uwar ta zata ci a gidan.

  A yau Saturday ne kuma Sulaiman ya dawo gari.

  Manage this pls,wlgy dadin comment naku yasa nayi typing yau.

  Ina mugun yin ku😍😍😍ku ci gaba da comment ni kumazanci gaba da suburbud'o muku littfi.muje zuwa💃💃💃💃.

  SHAFI NA12 📑*
  +
  *__________*📖Direct ya na isa gidan su Hafsat ya wuce don yana mugun kewar mutuniyar sa,a kofan gidan ya tsaya inda ya kira ta a waya,da kyar Allah ya sa ta d'auka don ma bacci take.

  "Salam".

  "Fito gani a kofar gida".

  A hargitse ta mike daga kwancen da take.

  "Baby kina ji na ne"?

  "Ehhh bacci nake amma bani minti biyar yanzu zan fito".
  "Tho dan Allah kiyi sauri don wallahi a gajiye nake ko gida banje ba".

  "Insha Allah ".

  Mikewa tayi tare da wanke idonta daga nan kuma ta nemi hijab,a kofar d'aki ta samu Maama.
  "Maama bari naje Sulaiman na waje".

  "Hafsat wai har yaushe zaki barsa a duhu ne,ki fad'a masa gaskiya mana,tunda har kika ki auren sa banga dalilin da zai hana ki fad'a masa ba".

  "Maama dan Allah kiyi a hankali kar yaji".

  girgiza kai kawai Maama tayi ita kuma ta fice waje.

  "Salamu alaykum".

  "Wslm Hafcy nah".

  kallon ta yake ko kebtawa baya yi,hakan ya sata fara sarguwa.

  "Hafcy gobe iyaye na zasu zo maganar auren mu".

  Gaban ta ne yayi mugun fad'iwa,kallon ta yayi don yaga yanayin tsoro ya bayyana a fuskar ta jikin ta har wani rawa ya fara yi.

  "Baby baki da lafiya ne"?

  kai kawai ta girgiza masa amma ta gaza magana.

  "Hafsat"!

  Kai ta d'ago tana kallon sa nan take hawaye ya cika idon ta,zuwa yanzu shima yasan haka kawai daga maganar aure baza ta fara kuka ba.

  Ana cikin haka sai ga Saudat ta dawo daga skull,da gudu ta d'ale jikin sa,rungumar ta yayi amma hankalin sa da idon sa na kan Hafsat,yana kallon ta yace

  "Saudat me ya samu Aunty Hafsat"?

  Kallon Hafsat d'in tayi sannan tace

  "Uncle Sulaiman ai tunda aka ce auren ta saura sati biyu in ta zauna sai ta rringa kuka".

  "Aure?da wa?

  Ai nan take ta fashe da kuka mai sauti,ganin kamar zata tara masa jama'a sai ya bud'e mota sannan ta shiga,shima shiga yayi ya zauna a mazaunin driver,saudat na baya.

  "Ina jinki".

  Kuka ta ringa yi,da farko ya zata yaranta ne irin na Saudat tace Hafsat zata yi aure nan da sati biyu amma yanzu ya fara yarda don haka kawai baza ta sa shi a gaba da kuka ba.

  "Saudat jeki gida in zan tafi zan kira ki".

  "Thom" .

  Gar ta fita yace

  "Saudat na bud'e miki boot ki d'auki tsarabar ki".

  "Na gode Uncle Sulaiman".

  Duk cikin yaran gidan saudat ce ta fita daban don ita kam baka ce kuma duk sun fita kyau sai dai akwai ta da son jama'a da kuma barkwanci haka yasa mutani ke son ta ba don haka ba kam....

  STORY CONTINUES BELOW

  "Hafsat kin san dai bana wasa da ke ko,wallahi ko ki bud'e baki ki mini magana ko ranki ya 'baci banda raini sai ki sani a gaba da kuka".

  "Yaa Sulaiman....

  "Yaa Sulaiman me?abunda Saudat ta fad'a gaskiya ne?

  "Ehhh".

  sake wayar sa yayi a kasa.

  "Waye mijin"?

  "Nima ban san shi ba".

  "Waya za'ba miki shi da zaki ce baki san shi ba".

  Shiru tayi,tsawa ya daka mata
  "Ba magana nake miki ba"?

  "Wlhy ban ta'ba ganin sa ba,muryar sa naji".
  Innalillahi ya ringa maimaitawa,nan take ya had'a gumi,kallon sa take tayi,wannan ne karo na farko da ta kura masa ido ji take kamar ta rungume sa yayi shiri,Allah ma yasan tana son Sulaiman sosai.

  "Fita mini a mota".

  Kallon sa tayi,bai kalle ta ba ya kuma fad'in
  "Nace ki fita".

  Jiki a sanyaye ta fita shi kuma yaja motar sa a high speed ya wuce.

  Gida ta shiga idonta zajir,kallon ta Maama tayi sannan ta girgiza kai,d'aki ta shige da gudu ta fad'a kan gado,kuka ta ringa rerawa ba kakkautawa,lallai Sulaiman wani 'bangare ne na jikin ta.
  ****

  Alhaji Munir ne zaune a falon shi da iyalan sa ana family meeting kan auren,tsara yadda abun zai kasance suka yi,bayan sun gama aka fara yin list d'in abinci da kuma sauran abun ciye-ciye a wajen biki,suna gamawa yace

  "Zaynab anjima in Hydar yazo ganin Ammin sa kice masa ina son ganin sa don ya kamata akai musu lefe".

  "Lefe kuma Daddy,ai bashin muce ita me abun lefe"?

  "Ba shawarar ku nake nema ba,ina sanar da ku ne,sannan kuma ba wanda zai je kaiwa cikin 'yan gidan nan don baza kuje gidan matsiya ta ba".

  "Shikenan Abba"

  Mikewa yayi ya fice inda Aunty Zaynab da Maryam suka wuce d'akin Ammi don Maamar su d'aya da Hydar,zama suka yi a bakin gado inda Maryam ke danne ma Ammi kafa Zaynab kuma tana bata abinci,a hankali take ci kamar mai koyo.

  Tsam basu so tsarin Daddy ba,akan me Hydar zai kashe kud'in sa wajen kaiwa Hafsat lefe,sai dai basu isa suyi magana ba.

  A haka har suka gama sannan suka mata wanka,kaya suka sa mata sannan suka kwantar da ita bisa gado yadda ya dace.

  Gyara d'akin suk yi don 'yan aiki basu shiga shashin ta,dama kullum Asma'u ko Fareeda ke gyarawa in kuma sunzo suke gyara wa.
  Yaran Ammi Biyar ne hudu mata d'aya na miji,umma kuma uky khadija khaleel da kuma Aisha.
  Sulaiman yana fita gida ya wuce,tsam ya kasa gaskata abunda ta fad'a,shin da gaske take ne ko kuma so take ta tsorata sa,amma kuma ai ba maganar wasa a tattare da ita,sunayen Allah yake ringa ambato har Allah yasa ya fara jin saukin abunalda yake ji.bayan Magrib ya d'auki mota bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan su,sallama yasa aka masa da Abba.

  Koda Abba ya fito ya gansa sanda zuciyar sa ta tsinke don shi kanshi bai san ta yadda zai fara fahimtar da Sulaiman ba,Allah ma ya takaita yaron akwai shi da tawakkali shiyasa yabi komai a sannu.

  Zama suka yi inda ya mika ma Abba hannu cikin girmamawa suka gaisa sannan yayi gyaran murya

  "Abba dama nazo batun aure na da Hafsat ce,gani nayi tunda na gama course na sai kawai muyi aure ita kuma nata karatun zata karasa shi a gida na".

  STORY CONTINUES BELOW

  Tausayin sa Abba yaji don yasan tabbas Sulaiman ya san komai amma kuma yazo masa ta wannan tsiga.

  "Sulaiman a rayuwa duk abunda Allah ya tsagawa mutum  ko ya kaddara masa dole zai faru da shi,in har Hafsat matar kace to ko ni nan ban isa na dakatar ba,in kuma yasa ba matar ka bane dabarar ka ko korewar ka bazai sa ka aure ta ba".

  Ajiyar Zuciya Sulaiman yayi don yasan tabbas anzo wurin,duk inda kaga ana ma mutum wa'azi ko basa hakuri to lallai ba shakka an cuce sa ne.

  "Haka ne Abba".

  "Sulaiman ina so ka bani hankalin ka da nitsuwar ka ka fahimci abunda zance,Hafsat an tsaida auren ta yanzu haka saura sati d'aya da kwanaki,sannan kuma kar kaga laifin Hafsat,ni zaka ga laifi na".

  Zuciyar Sulaiman ji yakrekamar ba nasa ba,yanzu yarinyar da ya gama kula da ita za'a d'auka a bama wani,kuma ai ba ko wani namiji bane zai iya zama da Hafsat,wani zaluntar ta kawai zai yita yi amma baza tace komai ba.

  "Sulaiman nasan kana jin zafin cikin ranka,kuma ni banyi niyad fayyace maka abunda ya faru ba,amma ganin natsuwar ka da mutunci ka yasa zan fad'a maka,Hafsat auren biyan bashi nayi da ita".

  Zare idanunsa yayi har hawaye un fara fita

  "Yanzu Abba matar tawa kayi biyan bashi da ita,na yarda ko nawa ne bashin zan biya maka amma wallahi bazan jure wani ya auri Hafsat ba".

  "Sulaiman mutani dayawa kafun kai sunyi niyar biya mini amma naki,abunda baka sani bama shine Hafsat na d'auke da ciwon zuciya,akwai rami cikin zuciyar ta wanda barazana ce ga rayuwar ta".

  "Hafsat d'in"?

  "Ehh muma bamu jima da sani ba,ban son d'aura maka d'awainiyar ta ko kad'an".

  "Abba a shirye nake nayi komai domin ta,kallo d'aya zaka yi ma Hafsat ta baka tausati,matasan mu na yanzu basu auren tsakani da Allah sai dai don biyar bukatar su na yau da kullum,Hafsat zata wahala hannun wanda zata aura tunda yasan cewa auren bashi aka yi mata".

  jingina kai kawai Abba yayi don yasan maganganun Sulaiman duk gaskiya ce.

  "Abba dan Allah na roke ka ka ruguza batun auren nan".

  "Sulaiman ka hakura da Hafsat don bazan iya ruguza auren ba saboda a court ne aka yanke hukuncin".

  "Innalilah".

  Yake maimaitawa lokacin da ya mike ko sallama bai yima Abba ba ya shige mota yana mai goge hawaye.

  "Tabbs ni Musa nasan Hafsat baza ta ta'ba samun mijin da zai sota yadda Sulaiman ke sonta ba,sonta tsakani da Allah yake,ya Allah ka basa damar tsallaka wannan kaddarar".
  Hawaye sosai Sulaiman ke yi wanda rabon sa da yayi kuka ya manta tun yaushe,yana isa gida gate Man ya bud'e mas kofa shiga yayi ko parking bai gama ba ya shige d'akin sa,Allah sarki abun taussayi ya zama,shi kansa bai san yana yima Hafsat irin wannan son ba,ya kuma yima kansa alkawarin ya d'au gaba da mijin ta..
  Yau aure saura sati d'aya,kuma 'yan uwan Abba da Mama daga nesa sun fara zuwa,Amarya kam gaba d'aya ta gama lalacewa don kuka,Sulaiman ya daina kiran ta kuma ko ta kira baya d'agawa,in kuma taa dame sa sai ya kashe wayar gaba d'aya,hakan ne ya dagula mata lissafi gaba d'aya.

  Yau ma kamar kullum ta shiga bandaki ta ringa kuka don tsam bata son wani ya fahimci halin da take ciki.

  Sis Faty ce ta bita har cikin band'akin don ta fahimci tun randa Sulaiman ya yanke kafar sa a gidan Hafsat ke shiga band'aki ta shafe awanni.

  "Har yaushe zaki yi ta kuka a 'boye Hafsat? Akan me zaki sadaykar da farin cikin ki don farant ma wasu"?

  da wuri ta d'ago kanta tana kallon Sis Faty a lokaci guda kuma ta share hawayen ta.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Nasan kina da dauriya amma kuma kada ki manta da ciwon da kike d'auke da shi,Hafsat gidan can ba sonki suke ba kuma baza su ta'ba sonki ba".

  Mikewa tayi da wuri ta fad'a jikin sis Faty

  "Ya zanyi ne sis Faty,wallahi bazan iya rayuwa babu Sulaiman ba".

  "Shhhhj insha Allah ke matar Sulaiman ce".

  Ta fad'a tana shafa bayan ta,Kuka sosai take don ganin yau kam ta samu mai rarrashin ta.

  Da kyar sis Faty ta rarrashe ta tayi shiru sannan ta wanke mata fuska suka fito,nan suke jin labarin cewa gobe Aunty Bilki na tafe(sister'n Maama)kuma ita ce fevorite Aunt nasu sosai take son su.

  Hakeela kuma ita da Umman ta sai shirya ma Amarya kayan gyara Amarya suke duk da Hafsat d'in ma bata sani ba,saboda basu so taje inda za'a mata kallon kaskanci.

  Maama kam nata ido inda Family ne suka d'auki nauyin bikin ganin Abba ba karfi sannan kuma basu san cewa auren biyan bashi bane.

  bari Mu leka gidan Angwaye!!

  Wow,gida an gama gyara komai Masha Allah kamar yau Amarya zata iso,kowa burin sa yaga matar da Hydar ya zage ya za'bo tunda shi aikin sa ne kad'ai a gaban sa,sannan kuma wace ce Alhaji Munir ya zage wajen gyara gida haka domin ta.
  Cikin gidan shiru duk da akwai bak'I sai dai dan hayaniyar da ba za'a rasa ba.

  Umma ce a falon ta tare da kawayen ta inda suke dad'a zuga ta jan cewa ai da Ammi da babu duk d'ayane don haka tayi yadda take so da dukiya,kuma sosai take jin dad'in shawarar su

  "Ai ni ran auren nan nasan Kowa na busy daga ita har 'ya'yan tan,don haka kulleta zanyi a d'ki kada ma makiya na su ganta bare suce ina da kishiya nakashesshiya".

  Dariyar shakiyan ci suka fashe da shi a haka suka cigaba da hirat su.

  Daddy kuma yanzu ya shigo gidan ta kofar baya,direct d'akin Ammi ya nufa,a falo ya tarar da su Zaynab da Maryam sai Asma'u da khadija wad'anda baza su wuci sa'annin Hafsat ba.

  "Sannu da shigowa Daddy".

  "Yauwa sannun ku"

  Wucewa bedroom yayi inda ya tarar da Ammi kwance kamar kullum,zama yayi bakin gadon sannan yasa hannun sa cikin nata yana mai shafa fuskar ta

  "Ki gafarce ni na rashin zuwa wajen ki kwana biyun nan,ribibin auren d'an ki ne".

  Lumshe masa ido tayi hakan ya sa shi fahimtar bata fushi da shi

  "Kullum rokon Allwnake ya nuna mini ranar da zaki koma kamar da,na gaji da kallon ki ciki. Mawuyacin halin nan".

  "Kin san me so nakemu koma irin rayuwar mu ta da gwanin sha'awa".

  Ita dai kallon sa kawai take,don haka yake yakan nemi lokaci yazo yayi ta mata hira har Allah yasa tayi bacci duk da umma ba son hakan take ba amma ba yadda ta iya,yau ma hakan ce ta kasance yana ta hira har tayi bacci,blanket yaja mata tare da shafa kanta ya fita,tsayawa yayi a falon yana kallon Aunty Maryam da Zaynab

  "Wai baku isar ma Hydar sako na bane"?

  "Dazun na kira sa yace zai shigo bada dad'ewa ba".

  "Allah yasa"

  yace sannan ya fice.
  Fitar sa tayi dai-dai da shigiwar motar sarauta gidan,Hajiya Nenne ce ta samu isowa cikin daren nan,nan take annurin fuskar kowa ta sauya don sun san mai gyara musu zama tazo.

  Aisha 'yar umma kam dad'i take ji don ko ba komai zata samu damar duba jikin Ammi kan a gama biki ba tare da kowa ya hanata ba,dama uwar su bata ta'ba barin su suje shashin Ammi duk da cewa yaran ma ba so suke ba,khaleel kam da shi da Aliya tunda Ammo ta kwanta basu ta'ba taka d'akin ta ba haka ma uwar su.

  STORY CONTINUES BELOW

  Khadija,Asma'u da kuma Aisha d'akin su d'aya sai dai basu fiya kula Aisha ba duk da ita tsakani ta da Allah take son su amma basu yarda ba,sunfi mayar da hankalin su kan jinyar Ammi.
  Hajiya Nenne na isa ta bud'e kofar falon tare da sa kai ciki,kallon t.v'n da gake aiki ba kowa tayi sannan tace

  "Zulai!Zulai!"
  Da sauri ummma ta fito
  "Sannu da zuwa Hajiya"

  "Wato don t.v'n bada kud'in ki aka saya ba shine zaki barsa yana aiki shi d'aya ko"?

  "Yi hakuti Hajiya"

  Tana gama fad'ar haka ta kashe tv'n,tsaki taja sannan tayi upstairs direct d'akin Ammi ta nufa.

  "Aikin banza,tsohuwa ce kamar mayya".

  Koda ta shiga d'akin Ammi ba kowa a falon sai Asma'u,gaishe ta Asma'u tayi sannan ta mata iso zuwa ciki.

  Duk jikin su rawa yake don ita bata san me sabo ba,kallon Ammi tayi sannan tace da su

  "Ya jikin nata"?

  "da sauki hajiya Nenne".

  Sannu tayi ma Ammi sannan ta juya zata fita sai ga Hydar ya shigo,d'an sunkuyar da kai yayi alamun girmamawa yayi sannan yace

  "Barkan ki da zuw Hajiya".

  Shafa kansa tayi sannan tace

  "Allah albarkaci rayuar ka Hydar".
  "Ameen yace kasa-kasa daga nan ta fita shi kuma ya shige.

  Yadda ya saba ma Ammi haka yayi saboda yau bacci take,sannan ya kalli Aunty Maryam yana fad'in

  "sis kika ce Daddy na son gani n"?

  "Ehh ko d'azun ma sanda ya tambaya".

  "Thom bari naje".

  Yana fita direct apartment na Daddy ya nufa inda ya shiga da sallama,a falo ya tarar da Daddy yana shan black tea,gishe sa yayi sannan yace

  "Ance kana nema na".
  "Ehhh Aliyu,so nake gobe kashirya zaka kaima Hafsat carty da kuma kud'ad'en da zata bukata".

  "An gama Daddy na barka lafiya".

  "Allah maka albarka"

  "Ameen".

  Yace sannan ya fice,shi fa komai zai yi mata yanzu don tabbatar da ta shigo hannu ya azabtar da ita yadda yake so...
  Washe gari!!!
  Tun da azahar su Aunty bilki suka iso ita da 'yar ta Murjanatu wacce take kawar Hafsat,farin ciki sosai Hafsat ke yi har ta fara manta damuwar ta,sosai suke nishd'i amma banda Maama wacce hanklin ta duk nakan duk wata motsin Hafsat d'in,tana matukar tausayin ta.
  "Hafcy zaki yi aure shine ko ki fad'a mini a waya,ai nayi fushi ba don Mommy bama da baran zo ba".

  "Yi hakuri Sweethearts".

  Hira ne sosai ya 'barke a gidan don ko baka tambaya ba kasan yau ana aure a gidan.
  Yaa Abdool kam ya d'au fushin duniyar Allah ya d'aura ma Hafsat inda Abba ko sai kokarin kare kimar s da mutuncin sa yake don yasan Alhaji Munir na kokarin kunyatar da shi,ya Naseer kuma ya tafi  katsina neman aikin yi.
  Karfe biyar na yamma Hafsat na kwance bisa cinyar Aunty balkee yaro ya shigo wai an sallama da Hafsat.

  "Je kace tana zuwa".
  cewr Aubty balkee.
  "Murjanatu d'auko mat hijab ki raka ta,na tabbata angon 'yata ce yazo".

  gardama ta fara yi sanda Aunty balkes ta nuna mata jama'a sannan tasa hijab d'in ta fice.

  STORY CONTINUES BELOW

  Mota ce kirar Venza maroon colour mai tinted glass,ita Hafsat d'auke kanta tayi don ko ba'a fad'a mata ba tasan cewa d'an Alhaji Munir ne.

  Gidan gefen na driver aka bud'e inda Sulaiman ya fito.

  "Hafsat "!!

  jin muryar sa da sauri ta d'aga ido,sai yanzu ma ya lura da a kofar gidan su yake
  "Yaa Sulaiman ".

  Kan ya sake magana Hydar ya bud'e kofar ya fito,kallon Sulaiman yayi cike da mamaki yace

  "Man ka santa ne"?

  "Ehhh"!

  Ido Hafsat ta kurama Sulaiman domim ita sam bata san Hydar ba don a court ma idonta ba glassses.

  "Hydar ka santa ne"?

  "Ita ce 'yar matsiyatan da zan aura".
  😨😨😨😨Hydar zai auri mata ko ince budurwar abokin sa..
  .

  Yaseen in naga ruwan comment irin na kwanannan zan cigaba da suburbud'o muku.

  Na gode kwarai ga masu yima kani na ya jiki,Allah saka da alkhairi.
  [2/6, 21:16] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA 13📑*
  *__________*📖kallon Hydar d'in Sulaiman yayi don yanzu ya tabbatar da lallai Hafsat ce yarinyar da Hydar ya tsana.
  "Daga ganin maza har tsumi ya tashi,jibi yadda take wage hakara,kai Allah wadaren naka ya lallace ballaga kawai".

  "Hydar pls"

  cewar Sulaiman,ita duk masifar da yake ko a jikin ta,idanun ta duk nakan Sulaiman sanda taji yace Hydar hakan ne ya sata d'aga ido domin kallon Hydar d'in.

  Mota ya bud'e inda ya ciro carty'n gayyata da kudad'e masu yawa ya watsa mata a fuska.

  "Nasan baku arzikin yin shagalin bikin ga wannan".

  Sulaiman ne ya kalle ta sanna yace

  "Kayi gaskiya Hyfdar,'yan mata yanzu duk yadda suka kaiga son ka da sunga wanda yafi ka kud'i zasu rabu da kai don kwad'ayin abun duniya kuma harda goyon bayan iyayen su"
  Shidai Hydar bai san inda zancen ta dosa ba shiyasa ma yace

  "Hmm"
  Kawai,itakuma Hafsat ta san sarai da ita yake,shiga motar Hydar yayi yana fad'in

  "Man muje ko ana jira na a office ".

  Matsowa kusa da ita Sulaiman yayi kamar mai mata rad'a yace

  "Wallahi ki shirya bazan taba barin ki kiji dad'in rayuwa ba dai-dai da minti d'aya tunda kince ke mayaudariya ce".

  Hannu yasa a aljihu sannan ya fiddo da kud'i ya bud'e tafin hannun ta yasa mata

  "Ga tawa dugumawar,ai dai hannun mu zaki shigo".

  Yana gama fad'ar haka ya shiga mota suka tafi a wurin ta durkushe tana kuka,Murjanatu ce ke kokarin d'agata amma ta gaza sai ga Hakeela.

  "Lafiya kuwa take kuka haka kamar wacce aka cire ma rai"?

  STORY CONTINUES BELOW

  "Sulaiman ne yaci mutuncin ta".

  "Wani Sulaiman kuma"?

  "Wanne ya wauce Sulaiman nata".

  "Gaskiya da kamar wuya don Tsam bayi da halin nan,ga kud'i nan an watsar a kasa duk kina nufin Sulaiman ne"?

  "No wannan angon ne yayi haka don ni a fahimta ta su abokanaye ne da Sulaiman d'in".

  "Innalillah,wannan wace irin musiba ce yanzu kuzo muje gidan mu Umma na na nemanta dama".

  Kwashe i.v da kid'in Hakeela da Murjanatu suka yi sannan suka nufi hanyar gidan su Hakeelan,a falo suka tarar da Umma.

  "Amarya ba kya laifi koda kin kashe d'an masu gida".

  ita dai Hafsat kanta a kasa don sai yanzu take bakin cikin amincewa da auren Hydar,yanzu kenan haka zata ringa kallon Sulaiman amma bashi ne mijin ta ba,gashi ya musu mugun fahimata da kuma d'aurama kansa bakin halin da bai dace da shi ba.

  Murjanatu ce ta gaishe da Umma inda tace su tafi d'akin Hakeela zata yi magana da Hafsat d'in,ba musu kuwa suka tafi.

  "Hafsat ki cire duk wata damuwa a ranki,Sulaiman dai Allah ya kaddara ba mijin auren ki bane,wanda zai aure ki kuma in har ya fahimci son wani kike to kin shiga uku".

  Shiru kawai tayi tana sauraron Umma don matar akwai kirki.

  "Hafsat na had'a miki kayan gyara dan Allah ba don ni ba ki daure ki sha".

  "Umma nifa ba gyaran da zanyi".

  "Kenan ni ban isa da ke ba"?

  Da wuri ta girgiza mata kai.

  "thom ki ringa zuwa kina amfani da shi don kinga gidan ku jama'a sunyi yawa".

  "Tho kawai"
  tace amma ba don zata yi ba,wasu masu amfani Umma ta ringa bata sai dan dilkan da aka shafa nata na minti talatin.

  A 'bangaren su Hakeela kuma poster Murjanatu tayi ganin yadda Hakeela ta cika d'akin ta da hoton wani gari,har ma da enlargements nasa.

  "Hakeela wannan kam brother'n ki ne"?

  "No dream Man nane".

  "Tho Allah kyauta"
  tace don tasan ita ko hauka tayi ba mai barin ta tayi wannan haukar a gidan su,carty'n kawaye suka cire inda Hakeela taja ta suka raba ma 'yan anguwa frnds kuma sai sunje makaranta gobe.

  Bayan minti talatin ta wanke nan take jikin ta ya d'an yi laushi ita kanta taji canji a jikin ta.

  Tana wankewa suka kama hanyar gida inda suka tarar dama jiran su ake yi.

  "Wannan kam angon ya gama tafiya da imanin ki ne Hafsat kuka dad'e".

  Kanta a kasa ta girgiza kai.

  "Mommy zo muyi close door meeting ".

  Murmushi Mommy tayi tana kallon 'yan wurin sannan a hankali ta mike don tasan akwai matsala,can 'bangaren Abba suka nufa.

  "Mommy wallahi wannan mijin nata bashi da mutunci,watsa mata kud'in fa yayi".

  "Tho ya zamu yi Murjanatu,kin san dai auren na biyan bashi ne dole tayi hakuri da halayyar sa".

  "For how long Mummy,wannan ma fa a waje kenan in kuma ta shiga gidan fa"?

  "Ki bar wannan maganar,in shaa Allah ba abunda zai faru don da addu'a zamu bita yanzu dai kuje da Hakeela da kuma saudat ku raba carty'n tunda walima kad'ai zata yi.

  "Tho tace gami da juyawa".

  ****

  Al'amura na tafiya yadda ake so ta dukkan 'bangare biyun inda Sulaiman ya d'au alkawarin tarwase farin cikin Hafsat kamar yadda ta masa inda Hydar kam aikin sa kawai yasa a gaba.
  Aliyu Hydar Munir shine cikekken sunan sa,matashi ne mai kimanin 32yrs,business yake yi inda ya mallaki Company na designing kaya latest onces,sosai yake samun cigaba a harkar inda rabon da yayi amfami da kud'in mahaifin sa har ya manta,cikin sana'ar sa yake biya ma kansa dukkan bukatun da bai gagare sa ba sai kuma na kannen sa da ba kullum yake yi ba don Daddy ne ke musu.

  Knocking kofar akayi

  "Yes come in".
  Seketariyar sa ce ta shigo tare da ajiye masa files a kan glass table nasa sannan ta d'an dukar da kai

  "let's call it a day".

  Kai kawai ya d'aga mata sannan ta fice,cigaba da duba files nasa yayi inda yasa bairon a bakin sa yana cigaba da bin files d'in.

  Shi tsam a office d'in bai shiga harkar kowa duk da kasancewar sa boss,sai dai kuma gaba d'aya masu aiki a karkashin sa tsoron sa suke ji don had'a rai da yake da kuma rashin sakewa da mutani,yakan tsawatar wa mutum in yayi ba dai-dai ba a office amma in an fita waje kayi duk abunda zaka yi wannan ba damuwar sa bace.

  Yana cikin dubawa wayar sa tayi ringing,idon sa akan file d'in ya mika hannu ya d'auki wayar tare da sawa a kunnen sa.

  "Ohk gani nan zuwa yace sannan ya kashe wayar tare da d'aukan key'n mota ya fice.

  Direct gida ya wuce ind ya tarar da Hajiya Nenne ta tar su duk a falo kamar masu kar'ban gaisuwar mutuwa.

  "Sannu da hutawa Hajiya".

  "Yauw barka da dawa".

  Tana fad'in haka ya haura upstairs don dama shi ba don su ya shigo ba,direct d'akin Ammi ya nufa inda ya tarar komai yayi dai-dai,sallamar su yayi sannan ya dad'a karema d'akin kallo.

  Furnitures ya canza ma Ammin shi saboda yace ma Daddy kada ya canza mata shi zai canza,leka bedroom d'in yayi yaga tana bacci don haka ya fito tare da rufe mata kofa yayi downstairs.

  "Wallahi mutum ya kuskura na kama sa da laifi a kwanakin bikin nan sai ya bar gidan nan,kuma nasan wasu kullum fatar mutuwa suke mini amma bazan mutu ba,in mutum yace karya nake tho ya gwada ni,kuma duk ku tashi ku bani waje".

  duk mikewa sukayi kowa da abunda yake fad'i a zuciyar sa,don wallahi in har Hajiya Nenne ta tsane ka to fa taka ta kare,bata da zama har sai taga karshen ka.

  Ganin duk sun watse sai ya wuce apartment nasa don shima he is off for d day,tun a falo ya cire takalmin sa sannan ya wuce bedroom inda ya rage kayan jikin sa tare da d'aukar towel ya yafa a kafad'ar sa yasa slippers ya shige tiolet,ya d'au lokaci sosai kan ya fito d'aure da towel,zama yayi a bakin gado ya kurama waje d'aya ido alamar tunani yake

  "Saura kiris".

  yace sannan ya ta'be baki tare da mikewa ya nufi wardrobe ya fara neman kaya.
  Khaleel da yaga sanda Hydar ya wuce shashin sa murmushi kawai yayi tare da fad'in

  "Kai da aurowa nida morewa don wallahi ni zaka aura ma".
  Yau ranar alhamis kuma a yau ne gidan amarya zasu yi walima gobe bayan sallar juma'a a d'aura aure.

  [2/13, 20:05] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA 14📑*
  *__________*📖shirye-shirye gidan Amarya suke na walima don yanzu kam kowa ya gama zuwa,ita dai Amarya bata damu ba sai dai kuma komai zaka yi ya kamata ka nemi albarka wajen Allah.+

  Da kyar Aunty Balkee ta sa aka mata lalle don taki yarda wai bata da wannan lokacin,anty balkee'n ma tana yi ne kawai don idon jama'a amma ba don komai ba saboda ita kanta baza ta bawa auren goyon baya ba.

  Sosai lallen ya mata kyau duk da cewa ba wani mai nauyi bane saboda ta hana a mata mai nauyi,kanta kam ba batun kitso ko zuwa saloon yadda take haka ta barshi sai Mai da tasa.

  Bayam Azahar aka kawo mata kayan da zata sa inda ya sha bam-bam dana sauran amare,ba za'a ce mai kyau ba haka kuma ba za'a ce mara kyau ba dai dai karfin su.

  Tayi kyau sosai barin ma da aka mata light make-up,Saudat sai tsalle ake Aunty Hafsat zata yi aure.

  Su Murjanatu da Hakeela ne kawaye sai wasu wad'anda Hafsat d'in ke mutunci da su,a kawance kam sun san abokanaye zasu zo ayi maganar aure da kawaye amma shiru kake ji.

  Jama'a ba laifi wajen bikin inda Aunty balkee ce ta kasance kirjin bikin inda sun sha wa'azi kam sosai,Hafsat kam bakin ciki take ji don tasan da yanzu Sulaiman zata aura fa.

  Taro ya watse lafiya ba komai kowa da kananan maganganun da yake.

  Bayan watsewar walimar ne ta sake wanka tare da nufar d'akin su yaaAbdoul domin hutawa ita da Hakeela Murjanatu na can tana taya Anty balked hidima.

  A kan katifar ta kwanta inda Hakeela ko ta zauna bakin katifar.

  "Hafsat yau ce kwanan ki ta karshe cikin gidan nan,daga gobe gidan surkunayen ki zaki na kwana,by d way a wani anguwa ne"?

  Banza tayi da ita don sai yanzu ta tuna cewa tabbas yau ce ranar karshe da zata sake kwana a gidan su,

  "Hakeela ki mini alkawarin in nayi aure zaki na zuwa gani na".

  "Na miki Hafsat bazan iya barin ki ke kad'ai a gidan ba,insha Allah zan na zuwa in ya fita aiki".

  Hakeela na shiru suka ji shewan mata daga cikin gidan.

  "Bari na ga meke faruwa".

  Kai kawai Hafsrta gyad'a mata.

  Masu mata ne suka kawo lefen Hafsat,akwati set biyu sai kayan iyaye da na pendonaye,sosai kaya yayi kyau sai albarka ake sawa inda harda goron d'aurin auren gobe aka kawo.

  "Lallai Hafsat tayi goshi,irin wannan kayan".

  Kowa abunda yake fad'i kenan sanda Hakeela ta iso,turus tayi tana kallon kayan don ko ba'a fad'a mata ba ta san Hafsat ba talaka zata aura ba,tayi murna matuka saboda ance kaso wa d'an uwanka abunda kaso ma kanka.

  Da gudu ta koma wajen Hafsat tare da rungumar ta

  "Hafsy kayan lefen ki fa aka kawo".

  Gaban ta ne ya fad'i tace

  STORY CONTINUES BELOW

  "Lefe kuma"?

  "Ehhh mana bai ce miki yau za'a kawo bane"?

  "A'ah".

  Me wannan Hydar yake nufi da nine,harda wani lefe,tho wallahi ya tsaya iya matsayin sa don zan juri ko wani wulakanci amma bazan yi zaman aure da shi ba.

  A zuciyar ta take wannan tunanin.

  "Hafsat tunanin me kike yi"?

  "Babu komai".

  Tana gama fad'ar haka ta mike tare da gabatar da sallar ish'a tana mai rokon Allah ya tsare ta daga sharrin Alhaji Munir da kuma 'ya'yan sa,Allah Allah take kada gari ya waye don tasan gobe tata ta kare.

  A can cikin gida kam sai taya Maama murna ake inda ita kuma sai dai ta ta'be baki don bata ga wani abun farin ciki ba.

  Karfe 10 na dare amma zaka ce na sfe don hayaniyar dake tashi a gidan,wasu bacci suka fara yi inda wasu kuma ke ta hirar yaushe gamo.

  Tsam Hafsat ta kasa bacci duk da ance bacci 'barawo ne,sis Faty ce ta kalle ta daga kwancen da take tace

  "Hafsat daga gobe fa shikenan,kin gama zaman gidan nan sai dai gidan azzaluman nan,dan Allah duk sanda kuka kuntata miki kada kice zaki ji kunyar fad'a".

  Kuka Hafsat ta fashe da shi tare da kwanciya jikin Sis Faty inda Murjanatu da Hakeela ke rarrashin ta.

  abu kamar wasa sai ga jikin ta har d'umi yayi,kiran Anty balkee suka yi don tazo taga 'yarta har da shid'ewa.

  Rarrashin Hafsat ta ringa yi amma taki daga baya sai ta hau ta da holo ko zata bari

  "Ba a kanki aka fara aure ba kuma ba'a kanki za'a gama ba,kowa na tausaya miki don tausayi kam,amma Allah yafi mu sanin dabarar da yasa ya za'ba miki can matsyin gidan aure,shin Ko baki yi imani da kaddara bane"?

  Kai ta girgiza.

  "Tho kukan nan ya ishe ni haka,gashi can an kawo lefen ki ma".
  shiru tayi tana kukan zuci a haka Aunty balkee ta tafi ta barsu.

  Aunty Balkee na fita ta fashe da sabon kuka,haka ta yita kuka har asuban fari.

  Tunda garin Allah ya waye ranar alhamis suke ta shirye-shirye,su Aunty Maryam da yaran su duk sun dawo gida,Ammi kan ji hayaniya amma ba halin shiga cikin jama'a.

  Kasancewar baki sun halarta a gidan hakan ya hana Hydar shigowa yau,don bai son shiga taron mata.

  Tun safe Ammi taki cin abinci wai sai an kira mata Hydar,yin duniyar Allah anyi amma taki ci,sanda aka kira sa a waya sannan ya bar duk wani abunda yake yi ya nufi gida.

  Yana parking ya fito direct d'akin Ammi ya wuce,rungumar ta yayi daga kwancen da take don yasan duk duniya bata da wanda take so irin sa,don ma yafi tausayin ta.

  Abinci ya d'auka tare da ajiyewa akan cinyar sa ya fara bata,kar'ba tayi taci sanda ta koshi.

  "Ammi kiyi hakuri wallahi jama'a ne suka hanani shigowa".

  Shiru dai ba amsa,shafa kanta ya ringa yi har tayi bacci.

  "Sis ku kula da ita pls,cuxx gobe bazan samu shigowa ba sai dare".

  "Dan Allah ka kokarta ka shigo if not baza ta yarda taci abinci ba".

  "Insha Allah"
  yace sannan ya musu sai da safe.

  Koda ya koma 'bangaren sa Sulaiman ya kira a waya inda sulaiman ke fad'in

  "Na Hafsat komi dozen,bada kanka a sare taje gida kace ya fad'I,gobe war haka ka angwance".

  STORY CONTINUES BELOW

  "Hmm kai dai Allah shirye ka".

  "Meke tafiya ne"?
  "Naga missed call naka ne d'azun kuma ina meeting ".

  "Ayya zan tambaye ka jikin Ammi ne".

  "Jiki da sauki na gode sai da safe".

  "Nasan zaka ce ka gaji da surut,Allah tashe mu lafiya angon Hafsat".
  Kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba,mikewa yayi tare da leka bedroom na Hafsat d'in yaga komai dai-dai sannnan ya koma d'aki.

  Washe gari!!!

  tun a safe ake ta hayaniya a gidan Hafsat ko da bata yi bacci ba jiya yanzu take yi,kowa mamaki yake amarya da bacci yanzu.

  Har Azahar ba wanda ya tashe ta don sun san da kuka zata tashi musu,inda ake ta shirye-shiryen tafiya d'aurin aure,don a masallacin kusa da gidan za'a yi.
  Bayam sallar juma'a aka d'aura auren Hydar da Hafsat kan sadaki dubu d'ari.
  A wurin Hydar yayi sujjada.
  "Hafsat tashi an d'aura auren ki".
  Cewar Hakeela.

  "Innalillahi na zama matar aure"

  Sai kawai ta fashe da kuka.

  Bari muka comments.
  Enjoy d weekend.
  [2/13, 20:05] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA15 📑*
  *__________*📖Hawaye shar ke fita daga idanunta ba kakkautawa,rungumar ta Hakeela tayi tana rarrashin ta.

  "Me abun kuka Hafsat?ke fa kika ce kinji kuma kin gani,wallahi naso da nawa auren yau aka d'aura da dream Man na".

  Ita dai bata sauraronta,Aunty balkee ce ta shigo ta tarar da su a haka.

  "Mrs Hydar"!

  Ko kallon inda Aunty Balkee take ba tayi ba.

  "Hakeela jeki Akwai d'an hayanta da zaku kimsa mata ke da Murjanatu"

  "Tho Aunty Balkee".

  Fita tayi ta basu wuri,matsowa kusa da ita Aunty Balkee tayi sannan ta kama hannun ta

  "Hafsat auren nan dukkan mu ba so muke ba,amma akan me zaki ringa nuna ma duniya ke auren bashi kika yi,so kike kowa ya ringa zagin Abban ki"?

  Kai ta girgiza

  "Ni nafi ki tsanar wannan auren saboda ke baki san me aure ba,auren soyayya ma ya aka kare bare wanda ba soyayya,ki saurare ni da kyau,ahare wannan hawayen kin".

  Sharewa tayi ta juyo tana kallon Aunty Balkee.

  "Daga an kai ki d'akin ki ko Hakeela bai dace ki ringa fad'a mata abunda ke tafiya cikin rayuwar auren ki ba,ki rike shi sirrin ki ne duk da tarin bakin ciki da zalunci ne zai kasance cikin sa".

  "Tho Aunty"

  "Kuma kada ki yarda ki sakarwa Hydar jikin ki,iya bautan da suke so ki musu shi kuma tsakanin ki da shi ido,kuma ba wai nace ki raina sa bane fa,saboda Allah bai damu akan kiyayya ko soyayya kuka yi auren ba,aure dai aure ne kuma Allah nason mace ta ringa kyautatawa mijin ta"

  STORY CONTINUES BELOW

  "Aunty dama d'aki d'aya zamu zauna"?

  "Oho nikam ban san musu ba,in d'aki d'aya ne ma sai ki kama kanki,sannan bagun Sulaiman kuma ko yazo gidan gaisuwa ne tsakanin ku,kada ki yarda ki nuna ma Hydar d'in son shi kike".

  Shiru kawai tayi don yanzu ita ji take gwara ta mutu ma yafi mata.

  "Abu na karshe kuma ki kyautata ma mahaifiyar sa saboda itama uwa ce a gare ki".

  "Thom"tace amma a karkashin zuciyar ta tasan ko sama da kasa zai had'u ba zata yi musu biyayya ba tunda sune silar halinda mahaifin ta ke ciki,sosai Aunty Balkee ta ringa mata wa'azi sannan ta karashe zancen ta da fad'in

  "Kuma wannan tsoron naki da koke-koke ki ajiye shi a gidan nan".

  "Thom".
  A 'bangaren angwaye kuma bayan an d'aura aure sai taya Alhaji Munir murna ake yi ba wanda yazo inda Abba ke tsaye shi da Yaa Abdool da kuma Baban Murjanatu sai 'yan uwan su da suka zo halartar d'aurin aure,shi ba anunda ya basa mamaki kamar Sulaiman da ya gansa amma ya nuna bai san sa ba sai shagalin sa yake.

  Indon Hydar da ke tsaye da abokan sa ne ya kai kansu
  "Excuse me"!

  Yace da su sannan ya nufi inda su Abba ke tsaye,yaa Abdool na ganin sa ya juya zai tafi carab Hydar ya rike hannun sa,juyowa yayi sai kawai Hydar d'in ya rungume sa tare da rad'a masa

  "Haba surki na,kai da ya kamata ka tayani murna sai ka guje ni?yau dai buri na ya cika na auri kanwar ka sai yadda naso zanyi da ita,sannan kuma ku jira zuwar gawar ta gidan ku".

  Yana gama fad'ar haka yayi breaking hug d'in yana murmushi,shike da takaici yaa Abdool ke kallon sa.

  Durkusawa zai yi gaban Abba ya gaishe sa Abba yace

  "Bar shi kawai banda bukatar sa".

  Mikewa yayi yana kallon yaa Abdool tare shu'umin dariya,har ya fara tafiya yaa Abdoul yace

  "Hydar!

  Carab ya tsaya ba tare da ya juyo ba,matsowa kusa da shi yaa Abdool yayi sannan yace muje gefe,da farko kamar ba zai je ba ko me ya tuna sai ya bi shi,idon Daddy duk a kansu ya rasa me Abdoul zai ce ma Hydar saboda yasan abun kad'an zai sa Hydar cewa zai sake ta yanzu.

  "Hydar wannan ne karo na farko a rayuwa ta da zan roki mutum abu,kuma ba don kowa ba sai don Hafsat".

  Ta'be baki yayi

  "Hydar nasan baka son ta kuma itama haka,don haka ka rike girmar ka kada komai ya shiga tsakanin ku".

  "Excuse me mallam,mata dai mata ta ce ba ta wani ba kuma sai yadda nayi da ita ba wanda ya isa ya fad'a mini yadda zan bi da ita tunda ni na biya sakadi".

  "ina kara gargad'in ka Hydar kada ka mata komai".

  "In kuma nayi fa".

  "Hmm kasan dai Allah d'aya ne dai ko,randa ka kuskura ka ta'ba ta ba da yardar ta ba,ni Abdool sai nasa an lalata yaruwar Asma'u kanwar ka kamar yadda kayima nawa".

  "Kai har ka isa kasa a lallata rayuwar kanwata"?

  "Ohh ashe haka kanwa take da dad'i,nidai na gargad'e ka in kuma kana tantama ka gwada,in kanwa ta ta hanyar aure ka fanshi budurcin ta ko taka kanwar ba ure za'a fansha,a sha angwanci lafiya".

  Yana gama fad'ar haka yayi tafiyar sa.

  Lallai Abdool yayi gaskiya,in har bana son kanwar sa to meyasa na aure ta,don son zuciya irin tawa?

  "A'ah don Ammin ka,ka manta yadda ubanta ya tarwatsa farin cikin mahaifiyar ka,ya maida ta komai sai an mata har magana bata iya yi,shin ka mance yau kusan shekara uku baka ji muryar mahaifiyar ka ba,ko so kake ka ce mini zaka iya barin ahalin da suka jefa ka cikin wannan halin suyi walwala,wulakanta 'yar su da zaka yi shi zai nuna musu mahimmancin Ammin ka a rayuwar ka,na roke ka Hydar kada ka karaya".
  Cewar Daddy.
  STORY CONTINUES BELOW

  "Lallai basu cancanci a tausaya musu ba,dole na ruguza farin cikin su".

  Yana gama fad'ar haka ya wuce mota.

  Haka rayuwar sa take,mutum ne mara son sa kai cikin al'umma sannan kuma tsam bai da son surutu da kuma jama'a,harkan gaban sa yake yi,wani lokacin in ya zurfafa tunani sai ya gano cewa abunda ya faru da Ammi kaddarar ta ne,Allah ne ya kaddara mata ba kowa ba,amma haka daddy zai ringa zuga sa har sai ya sauya masa tunani kam ya barsa.

  "Wannan Hydar dole nasa ido a kansa,tun yarinyar bata shiga hannun sa ba har ya fara wannan tunanin,lallai zulai tayi gaskiya na cewa kada a had'a su d'aki d'aya,ai nasan tana fara fad'a masa Allah yace Annabi yace shikenan Hydar kam zai bijire mini,dole nasan nayi da su dukka".

  Juyawa yayi tare da komawa cikin jama'a inda yake ta murmushi amma hankalin sa na kan yadda zai 'bullowa Hydar.

  Bayan d'aurin aure reception ya biyo baya inda aka ci aka sha.
  A gidan angwaye kuma daga kannen sa har yayun sa duk sunyi lalle sannan sun d'inka kaya masu kyau na gani na fad'a,tsam gidan basu samun walwala saboda takuran Hajiya Nenne gashi ko a jikin ta har aiki take sa su yi cikin jama'a inda Umma zata yi ta 'bata fuska amma a banza don ko inda take Hajiya Nenne bata kallo.

  Kid'a ke tashi a tsakiyar gidan amma karyar wanda yace zai yi rawa,kace gidan bana biki nane amma duk da haka bai hana qasu surutu ba.

  Yanzu ma sa Umma tayi a gaba kan cewa ita zata yi abincin da za'a tarbi amare.
  "Banda munafurci irin naki,har ni zaki munafurta,Hydar zai yi aure amma ba'a damu da na san 'yar gidan uban wa zai aura ba,koma wacece ai dai zata zo gidan nan kuma zan ganta"

  "Hajiya...."

  "rufe mini baki,cikin kunci Umma ta cigaba da aikin tana kuma jiran shigiwor Hafsat gidan don sai ta sauya mata kamanni tunda a kanta Hajiya Nenne ta sata girki,yaushe rabon da tayi girki.
  'Bangaren Khaleel kuwa sai shashewa yake a apartment nasa tare da abokan sa,giya da taba ne cike a gaban su.

  "Yau dai Hydar ya gama mini komai,mata har gida fa ya kawo mini".

  "Aboki na kace ajiyar nama aka bawa kura".

  "Sosai ma,ga yarinyar 'yar dai-dai,gaskiya yau da ina da abunda zan bama Hydar matsayin tukwici da na basa,gashi baya shan giya bare na basa".

  "Lallai kace yau kana cikin farin ciki".

  "Mara misltuwa ma".
  'Bangaren su Aunty Maryam kam har sun fara shirya muguntar da zasu tare ta da shi,inda ji suke da'ba mata wuka ne kawai baza su iyayi ba.
  "Hafsat tashi kiyi wanka don anjima kad'an zasu zo d'aukar ki".

  "Nifa ba inda zanje Aunty Balkee".

  "Wannan kuma ai baki isa ba,zaki tashi ne ko sai na 'bata miki rai".
  Mikewa tayi tana jin ciwon zuciyar ta na neman tarwatsewa amma ta daure don bata son d'aura ma iyayen ta d'awainiya tunda tafiya zata yi.

  Koda ta shiga bandakin ta dad'e tana saka wannan ta kunce sanda Aunty Balkee ta sake biyota kan tayi wanka ta fito.
  Sosai ake had'a mata kayanta inda Abba yace yana son ganin ta,Aunty Balkee ce ta rakata har kofar d'akin sa kan ta juya,da sallama ta shiga ciki.

  "Wa'alaikumssalam shigo Maama na"

  Shiga tayi tare da zama kusa da kafar sa.

  "An wuni lafiya Abba"?

  "Lafiya kalau Maama na,kinga dai yau zaki bar gidan nan,a matsayi na na mahaifin ki dole na miki nasiha kan ki tafi".

  STORY CONTINUES BELOW

  kasa tayi da kanta.

  "Kinga dai can gidan bance akwai mai son ki ba,kuma baza su ta'ba sonki ba saboda wani laifi mai girma da na aikata a gare su".

  Da wuri ta d'aga ido tana kallon Abba.

  "Ehhh Hafsat laifi ne mai girma wanda ko kece a matsayin su baza ki ta'ba yafe mini ba".

  "A'ah Abba nasan ba zaka ta'ba cutar da wasu ba,shin wani irin laifi ka aikata a gare su da har suke shirin ganin bayan iyalan ka".

  "Laifi ne wanda baki ba zai iya furtawa ba,sannan batun ba zan iya cutar da wani ba ao dan Adam ba abun yarda bane".

  "Ma roke ka Abba ka fad'a mini abunda ka aikata a gare su".

  "Mu bar wannan zancen,in kinje gidan can kiyi taka san-san da kowa da kuma komai dake gidan,ke har abincin su ko abin sha ki bi shi a hankali don zasu iya sa miki guba,sannan batun kud'in bukatar ki na yau da kullum zan na kokartawa ina tura miki,kuma kada kiyi wasa da makarantar ki".

  "Tho Abba amma....

  "Nace ki manta da wancan zancen,kuma ban yarda ki kuntata ma wanda bai miki ba.

  "Thom"
  tace nan yayi ta mata wa'azi har goshin magrib sannan ya fice,umman Hakeela kuma tazo ta d'ura mata magungunan da ita bata ga suna da wani amfani ba.

  Bayan sallar ish'a motocin daukan amarya suka fara zuwa.

  Zo kaga yadda 'yan anguwa ke zumud'in  shiga mota a tafi gidan amarya,aiko kowa ya samu shiga wasu motocin har sunyi gaba saura na amarya da kawayen ta.
  Hafsat kuka ta ringa yi wa Maama kan cewa ita ba inda zata je,da kyar aka raba ta da jikin Maama inda aka sa ta a mota,motar ma ta Hydar ce,kuka take yi har cikin ranta inda Aunty Balkee da goggon ta d'aya ke cikin motar tare da ita sai Murjanatu a gaba.

  "ku barta kukan dad'i take yi".

  Cewar driver'n motar wanda ya kasance Sulaiman ne,kuma ko ba'a fad'a mata ba tasan shine.

  tashar da motar yayi inda guda uku ne kad'ai a bayan su saboda sauran duk sun tafi.

  Gudu yake sosai da su akan titin kamar zasu tashi sama.

  "Malam dan Allah kayi a hankali saboda amaryar wani ce,yana can yana jira".

  Cewar Murjanatu kuma da biyu ta fad'a.

  Ko kallon ta bai yi ba sai dai ranshi ya 'baci don kishi,a hankali ya koma tuki har Allah yasa suka isa.

  Sosai ake busa algaita har yana toshe kunne,ga 'yan gidan sarauta sun zo sai kirari ake ma Hafsat,kowa fitowa yayi don tarbar Amarya har da Hajiya Nenne inda kowa ke son ganin ta Ammi kuma na can kwance a d'aki.

  Aunty Balkee ce ta fara fitowa sai goggonta,hannu Aunty Balkee ta mika mata inda Sulaiman keji kamar ya gudu da ita tunda sun fita,hannu ta mika ma Aunty Balkee sannan ta fito.

  Kirri aka ringa mata yayinda aka musu iso zuwa apartment na Hydar.
  sosai suka yaba da kyau gidan da kuma tsaruwan d'akin Hafsat d'in,kan gado aka zaunar da ita 'yan gidan da dangin su sai shiga da fita suke yi.

  Hakeela kam basu iso ba har yanzu saboda abokin angon da ya d'auke su yawo ya tafi da su.

  Su Hafsat da yanzu sun kai awa d'aya da zuwa ba suka ko kalar abincin gidan ba bare ruwa.

  Murjanatu fita tayi inda taci karo da Sulaiman.

  "Ya dai kawar Amarya"?

  "Wallahi kunji kunya,ai in mu baku kawo mana abin sha ba zaku kawa wadanda suka rakota,ko ce muku akayi in baku bamu abin sha ba zamu mutu,kunja makiya sai zagin 'yar mutan suke".
  STORY CONTINUES BELOW

  "Maida wukar shiga mota muje".

  da kyar ta yarda suka je,Restaurant suka je inda ya musu takeaway mai yawa,sannan suka kama hanyar gida.

  Suna parking ta d'auki ledojin inda Sulaiman ya tayata da wasu,carab akan idon Hydar,karasawa wajen su yayi yana fad'in

  "Man daga ina haka"?

  "Wlhy amaryar ka aka bari da yunwa naje nemo mata abinci".

  Hararar Murjanatu yayi kan ya wuce apartment nashi ba ko kunyar mutanin dake d'akin ya cusa kai ciki,kowa da ido yake binshi inda a tsakiyar falon ya tsaya tare da fara zabga mata kira.

  Hafsat!Hafsat!

  ai cikin ta ne ya kad'a ga tsoron shi da ya shige ta,sanda ya kira a karo na uku sannan ta d'au hanyar falo...
  Comments
  Share.
  ©Hafciey.
  [2/13, 20:05] Hafciey Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA 16📑*
  *__________*📖kafar ta har rawa yake yi yayinda take fitowa daga d'akin.

  "Kul d'in ki Hafsat,kada ki kuskura ki nuna masa tsoron sa kike ji".

  "Tho Aunty Balkee"

  Saita nitsuwar ta tayi a corridor sannan ta fito falon,kallo d'aya ta masa ta cire kai.

  "Ya dai malam,ka tsaya mini kiran mahauta".

  Cike da mamaki kowa ke kallon ta har shi d'in,ashe dai yarinyar ba yadda yake tunani bace,a ganin sa ita abar tausayi ce ashe ma jar wuya ce ita.

  "Sa idon ki a kasa,kada ki kuskura ki sake ki kalle ni cikin ido in ina magana saboda ban san ke kanwata ta nawa bace".

  "Fad'i damuwar ka sauri nake".

  Wani haushi ta bashi ba,Allah ma yasa shi bai mai dukan mata bane ba don haka ba da ya 'balla mata mari.

  "Da ke da muyunwatan 'yan uwan ki ku tsaya masayin ku,in kina zaton kun tashi daga talauci kun shigo arziki tho ba haka bane,kada ku kuskura ku sake rokon abinci don mu bamu son mabarata,kuma ban yarda Mata ta tayi bara ba".

  "Excuse me malam,matar ka a ina,kuma in abinci ne baza mu ci ba,amma kuma wannan ya zama karo na karshe da zaka zaga mini dangi,in kotu ta yarje maka da aure na bata yarje maka da zagin dangi na ba".

  tana gama fad'ar haka ta amshi lodojin da yake hannun Murjanatu ta bud'e hannun sa ta sa masa.

  "Mu kwana lafiya".

  Ta fad'a sannan ta koma d'aki,duk da ido suka bita inda kafar ta nauyi da sanyi ya mata,tana shiga ta maida kofar ta rufe.

  "Weldone Hafsat gwara da kika masa haka,I am proud of yhu,in har yazo da cin zarafin ki ki rama,in kuma baya shiga harkar ki tho ki masa biyayya iya iyawar ki".

  "Allah Aunty baki ji yadda na tsorata bane,kawai dai nayi ne".

  "Ina tausayin ki cikin wannan gidan Hafsat,anya kuwa ko abinci zasu baki"?

  STORY CONTINUES BELOW

  "Abincin su bai dame ni ba".

  A can falo kam tana fita ya fice,kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake

  "Wannan mijin Hafsat bashi da kunya bare mutunci".

  Yawancin mutani watsewa suka ringa yi cikin daren don a cewar su baza su kwana cikin gidan marasa mutunci ba.

  Hydar kuma yana fita ya gamu da Sulaiman a bakin kofar apartment d'in

  "Welldone Hydar gwara da ka mata haka zata san matsayin ta,kuma ni nasan hanyar da in kabi zaka kuntata mata,kawai ka hanata zuwa skull".

  Kallon Sulaiman yayi sannan yace

  "Ya akayi kasan hakan zai kunta ta mata"?

  "Bincike nayi a kai,daga ita har iyayen ta zasu ji haushi don kusan da ita suke dogaro,in yaso in kaga kamar zasu shigar da kara a kanka sai kawai ka maida ta aiki a karkashin ka".

  "Kai gaskiya bazan iya bata gurbi a company na ba".

  "No ba wani matsayi nake nufi ba,ko da guge-guge ko kuma mai serving mutani coffee ne".

  "No Man ita fa mace ce fa,duk abunda ya same ta I will be responsible ".

  "Manta Dallah ba abunda zai same ta".
  ***************
  Hakeela da sai yanzu suka gama gantalin su suka karaso,tsayawa kallon gidan tayi.

  "Lallai Hafsat ta warke,irin wannan gidan"?

  "Madam ga can apartment na amaryar ku".

  Abokin angon ya nuna musu,nufar wurin suka yi bayan sun masa godiya,suna gab da isa apartment na Hafsat Khaleel ya fito daga nasa,karo suka yi da Hakeela.

  "Oucch baka ganin inda kake zuwa ne"?

  "Dallah malama rufe mini baki".

  Jin muryar sa kamar yana cikin maye ya sata d'ago ido ta kalle sa,dib zuciyar ta ya buga saboda akwai kama na jini tsakanin sa da wani wanda in ba ta tabbatar ba baza tace ga mai shi ba.

  "Mtsww zaki masa mini ne ko sai na bankad'e ki"?

  Wata kawa ce ta janyo Hakeela gefe inda shi kuma ya wuce,nufar apartment d'in suka yi tana tsaki,direct bedroom ta shige bata tsaya ko kallon falon ba.

  "Murjanatu tsam abunda kika yi bai dace ba,ki duba yadda kika zubarwa 'yar uwar ki mutunci wajen mijin ta fa".

  "Me kuma Murjanatu tayi Aunty"?

  "Ku kuma sai yanzu kuka iso?abunda kuka yi bai dace ba,yanzu in iyayen ku sunji da abokin ango kuka tafi me zamu ce musu"?

  "Aunty kiyi hakuri".

  "Ai dole na,ga can Murjanatu ma ta jazo ma Hafsat".

  "Kamar ya"?

  Nan Aunty ta fad'a mata komai.

  "Tho kice rashin tarbiya a jinin su yake mana,yanzu wani d'an gidan ya buge ni a waje kuma wallahi yana cikin maye".

  Zaro ido Hafsat tayi tare da tashi zaune tace

  "Na shiga uku maye".

  "Ehh wallahi tambayi su Firdausi ma kiji".

  "Hmm Allah shirya"
  Aunty Balkee tace inda Hafsat ko ke tunanin wannan anya gidan masu tarbiya ce kuwa,yayan su ba hankali saura shi kuma da shaye-shaye,nidai ban san wani laifi na aikata a rayuwa ta ba da Allah ya zaba mini wannan gidan,bugu da kari abokin tsohon saurayi na nake aure.
  Dare na tsallawa duk aka watse inda aka bar kawaye sai Goggonin ta guda biyu da kuma Aunty Balkee,sis Faty da dama can taki zuwa gidan don gudun ganin takaici da 'bacin rai,bacci kowa ya fara yi banda Hafsat inda take ta tunanin yadda zata rayu cikin wannan babbar gidan,kada fa ita ma su lalata mata tarbiyar,sai can irin karfe 2 bacci 'barawo ya d'auke ta".

  STORY CONTINUES BELOW

  A can cikin gidan surkunayen ta kuma tunda aka shigar da ita 'bangaren ta kowa ya fara tofa albarkacin bakin sa ganin yarinyar kam 'yar gidan talakawa ce ba mai kud'i ba,don daga yanayin wad'anda suka kawo ta zaka gane,a falo aka baje inda kowa da harkar da yake yi,bayan isar su da kamar minti goma Hajiya Nenne tace ma Umma akai musu abinci.

  kasancewarHajiya Nenne a gidan sarauta take tasan yadda ake mutunta bak'o.

  Tho kawi Umma tace mata inda ta wuce kitchen.

  "Ai wlhy sai dai su mutu da yunwa amma abinci kam ba za'a basu ba,mika ma 'yan aiki kulolin abincin tayi tare da cewa su tabbatar Hajiya Nenne ta gansu sanda zasu fita da abincin,daga nan kuma su kai apartment nasu su ci.

  Godiya sosai suka mata amma karkashin zuciyar su sun tausayawa Hafsat wacce Allah Bai sa tayi dacen Surkuwa ba,yadda ta fad'a haka su kayi wannan yasa Hajiya Nenne bata san cewa ba a kaima su Hafsat abinci ba,Sulaiman kumaa yaga sanda suka nufi apartment nasu da kulolin da ya dace a kai ma amarya,hakan yasa shi tambayar su nan suka sanar masa saboda sun san bazai mayar ma Umma ba.

  "Da k'yau Umma,gaskiya kin san abunda ya dace,tunda kin gama playing role naki ni kuma bari na d'aura daga inda kika tsaya".

  Hakan yasa shi tsara fita da Murjanatu sayan abinci,suna gab da isa gida yayi ma Hydar text kan cewa'yan uwan tasun roke sa abinci kuma bayi da enough kud'i Hydar ya tura masa.

  Yadda yaga 'bacin rai a fuskar Hydar lokacin da ya shige apartment nasa murmushi yayi yana shfa gemun sa tare da fad'in

  "God job Sulaiman,Hafsat ke kuma yanzu na fara sai na zama munafuki tsakanin ki da Hydar,wannan soman ta'bi ne".
  'Bangaren Ammi ma sun mata kwalliya ta hanyar sa mata kaya mai kyau da tsada wanda Hydar ya saya mata,sam yau bata damu ta gansa ba don tasan yau ango yake.
  A haka suka kwana a gidan.
  Washe gari!!!

  Tun karfe bak'wai aka tura musu abinci daga gidan su Hafsat saboda wad'anda suka koma jiya sun fad'i wulakancin da aka musu,sosai sunji d'ad'in turo musu abincin da akayi,kowa ya riga Hafsat tashiwa daga bacci saboda sun riga ta bacci,sallah tayi tare da yin brush sannan aka gaggaisa.

  Ana kawo abinci kuma ta zauna taci saboda na gidan su ne.

  Sai karfe 10 aka shigo musu da karyawa,inda Hakeela ce ma tayi karambanin bud'ewa,abun mamaki d'umame ne cikin kular,ba wanda ya damu saboda sun san zasu yi wanda yafi haka.

  Yauma 'yan uwan sa sunyi ta shiga 'bangaren Amarya amma ba wanda ya ganta,saboda ta kwance lullu'be da hijab mai kauri.
  'Dakin Ammi bayan sunyi breakfast sai Asma'u da Fareeda suka ce

  "Aunty Mryam bari muje 'bangaren Amarya".

  "Thom ku tafi da su Iman".
  yaran su kenan.

  "Yehhh zamu je wajen matar uncle Hydar".

  "Ku dawo lafiya".

  Yaran sai tsalle suke da dariya inda Ammi ke bin su da kallon sha'awa,su Aunty Maryam basu so barin su Fareeda ba kawai dai ganin idon Ammi ne.

  Suna isa 'bangaren cike da kasaita suka nufi bedroom,a bakin gado suka zauna ko gaisuwa babu,su Iman ne suka ce

  "Ina matar uncle Hydar d'in"?

  Ba wanda ya ko kalli inda suke,ganin yara ne kuma laifin wani ai baya shafan wani yasa Unty Balkee fad'in

  "Gata can"
  ta nuna musu Hafsat d'in da hannu.

  da gudu suka hau kan gadon har jikin Hafsat.

  "Na shiga uku yaran nan zasu karya ni,hakan gidan nan yake da Yara"
  a zuciyar ta take fad'in hakan.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Aunty ki tashi muyi hira".

  Suna fad'a suna jijjiga kafar ta.

  Ganin zasu sa jikin ta yin tsami yasa Unty Balkee fad'in

  "Aunty'n tayi bacci,ku bari in ta tashi sai kuyi hira".

  "Thom" suka ce tare da natsuwa.

  Su Asma'u kuma sai kallon kaskanci suke musu inda Hakeela da Murjanatu ke musu irin kallon,gajiya  da zaman ya sa su tashi tare da kama hannun yaran suka tafi.

  "Kai gaskiyyaran gidan daga matan har mazan ba tarbiya,wad'an nan ko ba'a fd'a ba kannen Hydar ne saboda suna kama a fuska da kuma hali,wai kud'I hauka ne kam".
  Fad'in Murjanatu kenan.

  "Rufa mana baki".

  "Haba Aunty Balkee ai gaskiya ta fad'i".

  "Ba nace kuyi shiru ba Hakeela".

  "Munyi,gwara ma Murjanatu ta san angon,ni rowan sa ma Hafsat ke mini".

  "Kada ki damu Hakeela insha Allah anjima zaki gansa".

  "Tho Allah yasa.
  Aiko su Asma'u ma suna komawa suka ringa zagin su Hakeela wai ai kawayen amaryan basu da kunya,idanun su a soye,sanin Ammi bata son taji anci naman wani yasa Aunty Maryam cewa suyi shiru.

  Hajiya Nenne kam umma ta jefa mata maganin bacci cikin tea,wannan dalilin yasa tunda tayi breakfast take bacci,'yn gidan ko sun samu nitsuwa.
  Bayan sallar la'asar kowa ya fara shirin zuwa wajen bud'an kai,kaya mai tsada Umma da yaranta suka sa,haka ma kawayen ta.

  Su Aunty Maryam sun zuba k'yau har kamar zai zuba,ga Ammi ake kwance ma haka,suna shirin fita bayan sun gama shirya yaran su Hydar ya hau kiran Aunty Zaynab,receiving tayi

  "Sis kuna ina ne"?

  "Gamu yanzu zamu tafi wajen bud'an kai".

  "Ammi fa"?

  "Tana bacci".

  "Tho kada ku bar ta ita d'ata,cikin ke da Sis Maryam d'aya ta zauna da ita".

  "ohk".

  Suna gama waya tace ma Aunty Maryam suje kawai ita zata zauna da Ammi,hakan ko akayi.

  Gida kam a cike makil da mutani inda mutani da dama daga dangin su Hafsat d'in ma sunzo bud'an kai.

  'Bangaren Amarya kuwa heavy make up aka mata saboda Hydar d'in ne ma ya tura mai make-up d'in su kuma sun zata daga cikin gidan ne,shi bai son abunda zai sa yaji kunya ko kad'an a idon jama'a.

  Kayar ta mai tsada ta saka inda da ka ganta zaka ji kamar ka sace ta.
  Camera Hydar ya bama Iman tare da fad'in

  "Dear in an bud'e kan Aunty'n ki ki d'auko mini ko,kuma ko Mommy'n ki kada kice mata ni na aike ki".

  "tho me zaka yi da shi"?

  "Zan nuna ma Ammi".

  Yana gama fad'ar haka ya shafa kanta tare da bata kud'i yace ingo wannan,daga nan ya shige mota.

  Aiko ana fitar daHafsat Iman ta ringa mata pics har ka kaita wajen zaman ta,sai kamshi take,kud'in Ammi aka fara bada wa inda ta bata dubu d'ari sai sarka mai tsada da sallaya,Qur'an sai sharbi.

  Umma kam ban tayi niyar bayarwa ba amma gudun jin kunya ya sata bada dubu hamsin,inda su Aunty Maryam ma su biyu sun bata dubu d'ari.

  Haka 'yan uwa suka cigaba da bayarwa kuma alhamdulillah ta samu kud'I sosai.

  Asma'u ce ta bud'e kai inda kowa ke ta sa albarka don Amarta kam ta gama had'uwa,Iman kuma sai d'aukar ta pics take ta hana camera Man d'in ma sakewa.

  A haka aka kare bud'an kai kowa sai pics yake da Amarya,su Umma da Aunty Maryam dai don ganin idon jama'a suke yi,yayinda Aisha 'yar Umma kallo d'aya tayi ma Hafsat taji ta shiga ranta.

  Bayan watse taro kowa yayi cikin gida a gajiye inda sai yanzu Hajiya Nenne ta farka,tana ganin magrib ya kawo kai kuma har an gama bud'an ki ta fara bala'I.

  "Wannan wace irin bacci ne sai kace ta mutuwa,amma wallhi matar Hydar da bakn kafa ta shigo gidan nan tunda har ban ganta ba,tsam bata da goshi".

  "shikenan ita ma ta shiga layin blacklist na Hajiya".
  fad'in Aisha kenan.

  A daren Aunty Balkee da dangi suka koma gida inda amarya kad'ai aka bari sai kawaye,kuka sosai Hafsat ta ringa yi a daren.

  Haka suka kwana rarrashin ta.

  Washe gari 'yan gidan maza ma suka fara watsewa inda su Hakeela kuma suka sake music a falon sai sha'anin su suke.

  Can gidan mazan ma kowa na harkar gaban sa.

  Sai bayan Asr suka gyara mata shashin ta tare da fesa turaren wuta mai kamshi,ko ba'a fad'a maka ba kasan shashin Amarya ce,wanka suka sata yi inda suka mata light make-up sai kayan ta mai kyau suka bata ta sa.

  Zaman jiran abokanayen ango suke inda sai bayan magrib suka zo,Hafsat na can d'aki suka barta yayinda suke ta'ba hira da abokanayen ciki kuma harda Sulaiman wanda ya baje kan kujera.

  "Ina angon naku ne"?
  cewar Hakeela.

  "Yana waje 'yar sa ta saida shi".

  jin haka sun san 'yar sis tar shine.

  "Kuma me na tambaya tunda kuma rowar amaryar kuke mana".

  "Amarya kam ai zamu bar muku ita har sai kun gaji da ita.

  Sallamar su abokanaye suka yi tare da fad'in dare yayi suzo su maida su gida saboda lokacin har anyi ish'a.

  Shiga suka yi suka sallami Hafsat inda suka barta tana kuka.

  "A sha amarci lafiya swthrt".

  Hakeela ta fad'a sannan taja mata kofa.

  Fita suka yi inda a harabar gidan suka ga Hydar.

  "Ina mai tambayar ango gashi can".

  duk juyawa suka yi don ganin sa inda shima lokacin ya juyo yana fuskantar su.

  Hakeela na sauke idon ta kan sa tace
  "Shine angon".

  "Ehh Aliyu Hydar".
  Mota ta bud'e ta shiga inda dumi keta karyo mata cikin zuciyar ta take fad'in
  "Na shiga uku,innalillahi dream Man na Hafsat ta aura".
  Shiko yana ganin fitar su daga gidan ya nufi apartment nasu,khaleel ne ya gan shi
  "Wannan d'an iskan ba dai nace wajen amarya ta za shi ba,sanda nace ma Umma tayi wani abu tak'i.

  Hydar na shiga apartment nasa yasa sakata,daga nan ya nufi parlour,shiru ba kowa a falon sai kamshi,direct bedroom na Hafsat ya shige,daga kwancen da take tana jin motsin mutum a falo amma taki motsi har ya shigo,jin yayi ma kofar key ya sata fara karanta innalillah,har bakin gadon ya iso.

  "Hafsat!
  shiru
  Hafsat!

  ya kuma kira a karo na biyu yana cire jaren sa,tsarai yasan tana jin shi don haka ya girgiza kai.
  Yana gama shirewa ya aijye shi kan mirrow tare da rankafowa ya d'ago ta daga kwancen ta...

  [4/24, 13:52] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA17 📑*
  *__________*📖Rintse idanun ta tayi da karfi tana ambaton sunayen Allah da duk yazo bakin ta.+

  Bai sake ta ba sanda ya zaunar da ita.

  "Malam lafiya kuwa?"

  Kallon ta yayi amma ko inda yake bata kallo.

  "Lafiyar ce ta kawo haka,tashi ki had'a kayan ki ba a d'akin nan zaki na kwana ba".

  Shiru ta masa bata ce da shi komai ba illa sauka daga kan gadon da tayi,yana ganin haka shi kuma ya rataya garen sa a kafad'a yayi waje.

  shirya kayan ta tas tayi tana jiran ya nuna mata masaukin ta,don ita dad'i ma taji tunda ba d'aki d'aya zasu na kwana ba.

  Yana fita d'akin sa direct ya wuce inda ya rage kayan jikin sa sannan ya shige tiolet,ya d'au kusan 20mins yana wanka,ko da ya fito sai yaja stool ya zauna tare da shafa lotion,daga nan kuma sai ya gyara zaman ganshin kanshi sannan ya sa white sleeping robe,kamshi yake sosai don tularen da ya fesa,yadda yake shirin zaka ce ko wani wajen za shi.

  Wayar sa ya d'auka sannan ya nufi d'akin,yana bud'e kofa ta mik'e tsaye.

  "Kin gama?"

  Ta tambaya fuskar sa a had'e,kai kawai ta iya d'aga masa.

  "Abinci fa,kin ci".

  tsaki taja can ciki-ciki,ita bata gane masa ma,mugu ne ko akasin haka,jin ta manna masa hauka sai ya fice tana bin sa a baya har suka isa apartment na 'yan aikin,knocking yayi inda Baaba Ladi tazo ta bud'e masa.

  "Barka da dare  Hydar".

  can ciki-ciki yace barka dai.

  "Wani taimako zan iya muku?"

  "Ga Hafsat a nan zata ringa kwana".

  Kallon Hafsat d'in tayi tana fad'in
  "Shigo mana".

  Tana shiga ya juya yayi tafiyar sa abun sa.

  A kasa ta zauna tare da kare ma d'akin kallo akwatin ta na daga gefe,Baaba Ladi ce ta shigo d'akin ta ganta tana takure.

  'Yata hau gadon ki kwanta in yaso ni na kwana a kasa".

  "A'ah ba za'a yi haka ba,kinga ni kwanciyar kasa ba yau na fara ba,kwanta kawai abun ki".

  "tho Allah miki albarka".

  "Ameen".

  "Kinga bari na baki ko borgo ne in yaso sai ki shimfid'a kan ki kwanta".

  "Tho na gode".

  Tasan dai karyar ta tace zata kwanta kan tiles babu bargo,mika mataBaaba Ladi tayi I da ta karba ta shimfid'a sannan aka bata filo,kwanciyar ta tayi ko a jikin ta son ta san wannan ma kad'an ta gani.

  Iya tausayi Baaba Ladi taji tausayin ta,amarya ce da kwana a d'akin 'yan aiki,Hydar dai ba mugu bane sai dai in koya masa ake yi.

  Da haka suka kwana,asubar fari Baaba Ladi ta tashe ta tayi sallah sannan ta koma ta kwanta.

  STORY CONTINUES BELOW

  'Bangaren Hydar ma haka ya kwana saboda dama ya saba shi kad'ai yake kwana,ba wata damuwa cikin ransa.

  Maama da Abba kam sun kwana cikin tunanin halin da 'yar su ke ciki inda ya Abdoul kuma yasan dole Hydar yaji tsoron abunda ya fad'a masa ya bar kanwar sa.

  Tana cikin bacci taji ana zuba mata ruwa mai tsanyi a jiki,a firgice ta mike tana goge idanun ta,umma ta gani.

  tsunkuyawa Umma tayi tare da d'ebe ta da mari.

  "Dan uban ki ce miki akayi hutu kika zo yi ne,irin mana kin samu A.c gidan uban ki babu".

  Shiru tayi bata ce da ita komai ba,kara d'eban ta da wani marin tayi,nan take da dafe kuncin ta tana hawaye.

  "Maza tashi mu wuce ciki".

  Ta fad'a tana jan ta har Allah yasa suka isa cikin apartment nasu,jefa ta cikin kitchen tayi sannan tace da Baaba Ladi

  "Daga yau kuma ku huta,Allah ya kawo mai dafa muku".

  Duk da ido suka kalle ta inda Baaba Ladi ta tausaya mata saboda tasan karya ne ta iya girka abinci kusan kala uku ko wani rana,na safe uku na rana uku na dare ne dai ake guda d'aya sai kayan kara vitamin a jiki.

  Goge hawayen ta tayi sannan ta kalli Baaba Ladi tana fad'in

  "Me zan dafa".

  "Bari na nuna miki 'yata".

  Umma fita tayi ta basu wuri tare da ce ma Baaba Ladi in ta taya ta a bakin aikin ta,ita ko tayi niyar ko mezai faru sai ta taya ta.

  Nuna mata ta fara yi tana yi tana jan ta da hira duk don ta manta abunda aka mata,ita dai ko a jikin ta don ta d'au alkawarin ko ma mene ne zata iya jurewa tunda an janye bashin da ke kan Abban ta kuma ai tasan lokaci kalilan ya rage mata zata mutu daga nan labarin yazo karshe.

  Suna gamawa Baaba Ladi ta barta domin jerawa a dining,tas ta jera su.

  "Yanzu duk kije ki kira su,amma ki fara da Hajiya Nenne,d'akin ta ne a hannun hagu,ku ma ki tabbatar kin gaishe ta da girmamawa".

  "Insha Allah ".

  Hawa upstairs d'in tayi,yadda Baaba Ladi ta fad'a mata haka tayi,tsayawa a kofar d'akin Hajiya Nenne tayi sannan ta tsaita nutsuwar ta.

  "Salamu Alyaikum".

  "Wace marasa albarka ne ina cikin hutawa ta za tao ta ishe rayuwa ta,shikenam don gidan ku ba kwanciyar hankali nima sai ku bi ki tashe nawa hankalin,nace wace ce?"

  Muryar ta har rawa yake yi tace

  "Hafsat ce".

  "Mtsww shigo".

  Allah mai iko,wannan matar kuma wace ce ita.
  ,tura kofar d'akin tayi tare da shiga kanta a kasa.

  "Ina kwana Hajiya".

  "Da ban kwana ba zaki gqn ni,kuma waya bami izinin zuwa har d'aki na,gaki mara kunya ko har zaki iya kallon mwayar idanu na,gaskiya Aliyu bai yi dacen mata ba".

  cize bakin cikin ta da 'bacin rai tayi sannan tace

  "Dama na kammala abinci ne shine nace bari na kira ki".

  "Sanda kika gama kiran kowa sannan zaki zo kaina,ko jeki bani cin abincin".

  "Allah huci zuciyar ki Hajiya,ke ce wacce na fara kira".
  d'an kasa tayi da muryar ta ba kamar na d'azun ba tace
  "Tho je ki ina zuwa".

  Ita dama haka take,akwaita da son girma,mikewa Hafsat tayi ta fice tana mamakin'yan gidan,kowa da klar tasa bakin hali.

  STORY CONTINUES BELOW

  'Dakin Umma ta nufa inda mamshi ne ke tashi,knocking tayi umma tace

  Shigo"
  Don a zaton ta Khaleel ne,shiga tayi ba ko gaisuwa tace

  "Na gama".

  "Tho tashi ki bani wuri,tsaya ma tukun uwar ki bata miki tarbiyar gaisuwa bace?".

  Ita tsam ta manta,don ko me mutum zai mata a duniyar nan baza ta ki gaishe shi ba.

  "ki gafarce ni".

  "Dallah tashi ki bani wuri,talakar banza,wato a tunanin ki da kin auri Hydar shikenan dad'in rayuwa ya zauna miki ko?"

  Mikewa tayi ba tare da tace komai ba ta fice.

  "'Dakin Ammi take ta kallo da alama ba mutani awurin,yanke shawar koma waye ne a d'akin in taje zata gani tayi,tana gab da isa kofar Asma'u ta fito.

  "Kada ki kuskura ko da wasa ne kice zaki shiga d'akin nan,duk randa kuma kika shiga sai na tsare wannan kan ki".

  Ita dama ba ma'abociyar magana bace don haka ta juya tayi tafiyar ta ba tare da tace da ita komai ba.

  "Baaba na gama bari naje na watsa ruwa".

  "A'ah baki gama ba,jira zaki yi har sai sun fito dukka kinyi serving nasu sai ki basu wuri domin cin abinci".

  Shiru tayi bata ce komai ba kuma bata tafi ba,morrow babba dake bayan ta ta kalla,zar hannun Umma a kumatun ta,nan take ta sake jin wani hawayen don dama ita kam raguwa ce ba'a raba ta da kuka.
  Khaleel ne ya shigo falon inda ya tsaya kare mata kallo ko kunyar idon Baaba Ladi bai ji ba,wucewa yayi yana lashe baki.

  "Hafsat kiyi hankali da wannan,kanin Hydar ne kuma yana shaye-shaye".

  "Thom na gode".

  Don ta gane shine Hakeela ke fad'I.

  Da haka dai Asma'u da Fareeda suka fito,sai su Aunty Maryam dan ba su koma ba sai yau,Khadija da Aisha ma suka fito,sai Umma,Hajiya Nenne ce karshen fitowa don Daddy yana da breakfast meeting.

  Hydar ne ya shigo falon inda ya haura upstairs bai ce da kowa komai ba,tura d'akin Ammi yayi ya gan tana bacci,rufe mata yayi sannan ya sauko kasa.

  "Hafsat in kinje serving nasu ki gaida Hydar".

  "Ehem".

  Don taga gidan ba wanda yake son ta sai Baaba Ladi kuma dole tayi abunda ta sa ta.

  "Oya jeki,ina jiran ki,in kin gama sai mu tafi.

  Zuwa tayi inda ta fara serving Hajiya Nenne,sannan tayi serving umma,zata yi serving Khaleel Hydar yace

  "Ke sauri fa nake ".

  Dole ta juya gare sa dukkan su sai kallon ta suke har hannun ta ya fara rawa,serving nashi ta fara yi sannn tace

  "Ina kwana".

  D'aga ido yayi ya kalle ta sannan ya mayar da idon sa kan wayar sa ba tare da ya amsa ba.

  "Ke ki kula fa,naga kamar dottin himar naki na shiga mini abinci".

  'Daga ido tayi ta kalli Baaba Ladi inda Baaba Ladi ta girgiza mata kai.

  Serving nasu Aunty Maryam tayi tare da gaishe su,su Asmau kam ko ba'a fad'a mata ba tasan age mate nata ne don haka bata gaishe su ba,Khaleel ne karshe can ciki-ciki ta gaishe shi,daga shi kuma sai yaran su Aunty Maryam,shafa kansu duk tayi sannan tayi serving nasu tana fad'in

  "Ku ci da wuri kada ku makara".

  Carab Aunty Zaynab ta kar'ba

  "Dan can da baki nan ai basu makara,iskanci kawai wa zaki nuna ma kina son yara".

  STORY CONTINUES BELOW

  Shiru tayi sannan ta mayar da sauran kwanun kan kitchen ta sa hannun ta cikin na Baaba Ladi zasy fita.

  "Ina kuma zaki je?"
  Ummi ta tambaye ta,ba tare da ta juyo ba tace

  "Zanje na sha magani".
  jin tayi shiru bata ce komai ba sai kawai suka fita.

  A 'bangaren Hakeela kuma tun a cikin mota take jin kamar ranta zai fi ta don bak'in ciki,suna isa gida da gudu ta shege d'akin ta tare da rufe kofar da wuri,rufe kofar ne ya jawo hankalin iyayen ta,da wuri suka rufa mata baya don ita ce kad'ai 'yar su.

  "Hakeela lafiya kuwa".

  "Hajiya ina ga da mun barta kawai,ina jin zafin rabuwa da Hafsat ne ke damun ta".

  "Ehh kayi gaskiya mu bar ta kawai".

  Da wannan shawar suka barta inda suka tafi d'akin su.

  Hakeela kam cire takalmin ta tayi tare da yin wurgi da shi,daga nan kuma ta hay fasheshen kayan d'aki ba ji ba gani kamar mahaukaciya,cire d'an kwalin kanta tayi tare da wargaza kan da ba kitso,sak mahaukaciya ta fito,sanda ta gaji da haukar sannan ta zare babbar enlargement d'in Hydar wanda yafi sauran kyau,zama tayi a kasa tare da kurama hoton ido.

  "Y Hydar,kasan tun yaushe nake dakon son ka,na so ka tun ban san kai na ba,Hydar na so ka tun lokacin da businesse naka bai bud'u ba,ashe dama kaine Hydar da Hafsat zata aura,ni ana wa wautar na manta Aliyu da Hydar duk d'aya ne,in an barni na Hafsat ne Hydar nawa kuma Aliyu".

  Shiru tayi tana kallon hoton sa hawaye na zuba kan fuskar sa a hoton.

  "Shin yanzu kana nufin na barwa Hafsat kai,me yasa baka ta'ba barin mu ga juna ba,na tsane ki Hafsat!na tsane ki".

  Ta fad'a sanda ta buga hoton a kasa da karfi ya fashe,a kasan ta kwanta ta ringa rere kuka mai cin rai,ga koshi ga kwanar yunwa,ga ta ga Hydar amma yana matsayin mijin kawar ta,kuka ta ringa yi bata san sanda bacci yayi nasarar d'aukar ta ba.

  da safe ma da mugun zazza'bi ta tashi,dafe goshin ta tayi da kyar ta mike,tiolet ta fad'a inda tayi alwala sannan ta fito dayi sallah,rokon Allah tayi kan ya bata juriyar barwa Hafsat mijin ta tunda sun riga da sunyi aure,cikin ikon Allah kuma tana idar da sallar tayi bacci ko da ta tashi ma sai taji saukin abun a ranta ta kuma bar ma Hafsat mijin ta.

  Hydar ko yana gama breakfast ya ja tissue ya goge bakin sa sannan ya d'au key'n motar sa yayi gaba.

  Yana isa office yayi parking motar inda security ya kar'bi key d'in don goge masa motar kan ya citizen ko da ya shiga kowa mik'ewa yayi ana gaishe sa,kusan duk 'yan wurin mata ne,d'ai-d'ai ku ne maza,direct mik'ewa yayi zuwa office nasa,ga mamakin sa ya tarar da Sulaiman zaune yana wasa da biro.

  "Ango dama yau zaka fito ne,na zata amarya zata rike ka ne ai".

  "Hmm".

  Kawai yace sannan ya zauna.

  "A kawo maka coffe ne?".

  Kai ya girgiza masa,lallai yau ya tabbatar Hydar yayi aure,mutum da kullum a office yake karyawa,tho ma wani irin zama za su yi ne,shi ba magana ba ita ma haka.

  "Hlo tunanin me kake?"

  "Babu me ka gani?"

  kai ya girgiza masa tare da bud'e system ya fara aiki,shi dai Sulaiman da ido yake bin sa yana nazarin sa,to ko dai ya angwance da Hafsat ce,kai gaskiya Hafsat ba zata bari ba.
  Hafsat ko suna isa shashin su ta wue toilet sanda ta sha kukan ta na zagin da suka mata sannan tayi wanka ta fito,abinci Baaba Ladi ta bata amma taki ci,cim-cim na auren ta taci ta sha ruwa sannan ta had'iye magani.
  STORY CONTINUES BELOW

  Kwanciya tayi domin Allah ma ya san aikin da ta yin nan ta gaji,wayar Baaba Ladi ne ya hau ringing,receiving tayi sai kawai tace

  "Tho Hafsat ga waya mijin ki zai miki magana......
  Comment
  share

  ©Hafciey
  [4/24, 13:53] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA 18📑*

  Wannan shafin sadaukarwa ne ga Napeesa,sai yadda kika yi da shi.

  *__________*📖Kallon wayar ta saya yi.

  "Ke Hafsat yana magana fa".

  sawa a kunnen ta tayi ba tare da tayi magana ba,dib zuciyar ta ya buga sanda taji Muryar Sulaiman ne,kenan tsufan Baaba Ladi har ya kai munzulin da baza ta iya tantance muryar Hydar da na Sulaiman ba.

  Shiru ta masa ba tace komai ba,ganin yadda Baaba Ladi ta kafe ta da ido ya sata cewa
  "Tho naji".

  Sannan ta kashe wayar,tana bak'in cikin kar'bar wayar tun farko,banda iskanci ya kira kuma yayi shiru bayan sallamar da yayi,kenan ita yake son ta fara magana ko.

  "In kin gama ki tashi mu lek'a cikin gidan ko akwai aikin da zamu yi".

  "Toh".

  Tace sannan ta nemi hijab tasa a jikin ta,mik'ewa tayi sannan suka nufi cikin gidan,sauran 'yan aikin kam dad'i suke ji tunda sun daina aiki kuma zasu karbi salary,ita kuma tayi babu salary,ko da suka isa falon sun tarar da su Aunty Maryam sun fito zasu tafi,ko sannu ba su ce da ita ba,'bangaren ta ma haka ne,sai yaran ne suke mata bye-bye sai kawai ta cire kai don bata shirya kar'bar wani zagin ba,bayan sun fita ita kuma ta shige kitchen nan suka fara had'a abincin rana.

  "Jeki tambayo Hajiya me za'a dafa".

  "Baaba wallahi tsoron ta nake ji".

  "Ki daure ki je,ni in naje zan sha zagi".

  Fara hawa upstairs d'in tayi kafarta har rawa yake yi don tana tsoron kada Umma ta sake d'eban ta da mari irin na d'azun,knocking kofar tayi amma shiru,ta kai kusan minti biyar sannan tace

  "Shigo".

  Tura kofar a hankali tayi sannan ta shiga kanta a kasa.

  "shegiya munafuka to me na sa kai a kasa,ba dai leken asiri kike son mini ba,to ko uban ki bai isa ya leka asiri na ba bare ke".

  Jin an ambaci sunan uban ta hakan ma sai ya tuna mata da gida,ko wani hali iyayen ta suke ciki sai Allah,yaushe tazo gidan ma har ta fara manta nasu gidan don damuwar gidan nan.

  "Me za"'a dafa?"

  Ta tambaya tana hawaye kasa-kasa.

  "kije ki ce ma Baaba Ladi ta fad'a miki abunda ya dace a dafa yau,ai tana da time table na girki".

  Ta mike zata fice kenan Khadija dake kwance a bayan Umma tace

  "Ke ki had'o mini tea yanzu ki kawo mini don na fara jin yunwa,kuma ki tabbatar kin wanke hannayen ki da kyau".

  STORY CONTINUES BELOW

  Ba tace komai ba ta fice tana jin Umma na cewa shegiya d'iyar talakawa,ko da ta sauka kasa fita shashen tayi tana kuka,Baaba Ladi na kiran ta amma tayi banza da ita,da gudu ta shege shashin su inda ta wargaza kayan ta domin nemar wayar ta,aiko ta gani sai dai kuma bata yi sa'a ba saboda babu carty gashi bata san wa zata aika ba".
  Kuka ta ringa yi tana tuna gida inda a can zasu iya yin komai domin farin cikin ta,amma anan gashi daga a mare ta sai a sheganta ta a zagi uban ta,ya Allah ka d'auki rai na da wuri ko zan huta da wannan rayuwar kuncin".

  Dafa ta da aka yi ne ya sata d'ago yjajayen idanun ta tana kallon Baaba Ladi

  "Hafsat wannan kukan ba inda zai kai ki,in zagin ki aka yi ma gwara ki saba saboda 'yan gidan nan ba imani bane gare su,duk abunda suka miki ki nuna baki damu ba,hakan ne zai kunta ta musu".

  Share hhawayen ta tayi sannan suka koma kitchen d'in suka fara had'a abinci,ita gaba d'aya ma ta manta da aikan Khadija,suna cikin aiki taji an shake wuyar ta,

  "Innalillahi Hajiya kashe ta zaki yi ne?"

  "Bar ni na kashe 'yar shegiya tun kan ta kashe mini 'ya".

  Baaba ce ta fara kokarin kwace Hafsat d'in ganin yadda idanun ta suka kad'a kuma tasan Umma zata iya kashe ta kuma ta zauna lafiya tunda d'iyar talakawa ne.

  Jefa ta a kasa Umma tayi sanda taji ciwo a goshi,d'auke ta da giceccen mari tayi tana fad'in

  "Dan uban ki kin manta ke baiwa ce a gidan nan,har kin isa Khadija ta aikeki,ki,ki zuwa,wato so kike ki kashe ta ko,to kan ki kashe ta ni sai na kashe ki,jibgar ta ta fara yi ba ji ba gani Baaba Ladi na ta kokarin kwace ta ta gagara,ana cikin haka sai ga Khaleel,ai yana ganin haka ya nufi kan Umma cin maye,ture ta gefe yayi sannan ya d'ebe ta da mari.

  "Khaleel ni uwar ka ka mara?"

  Cikin muryar maye yace
  "Umma kiyi hakuri ban san lokacin da na mare ki bane".

  "Ba komai,ai nasan baza ka ta'ba mari na ba,muje ciki".

  kama hannun sa tayi suka shige ciki,Baaba Ladi kuma da wuri ta nufi wajen Hafsat d'in,taimaka mata tayi ta mik'e sannan suka fice zuwa 'bangaren su,kan gado ta d'aura ta.

  "Baaba bani maganin ciwon zuciya ba,kirjina zafi kamar zai fashe".

  Da wuri ta 'balla ta bata sannan ta nemoo pracitamol ta had'a mata.

  "Kin kwanta ni zanje na gama aikin".

  Kai kawai ta d'aga mata don jikin ta duk yayi nauyi,rabon da a duke ta sai tace tun tana jss class amma da girman ta Surkuwa ta rad'a mata duka,gaskiya Maamar. Hydar bata da imani su kashe ni kawai su huta.

  Kuka yanzu ma ta ringa yi,cikin kukan taji wayar ta na ringing da wuri ta share hawayen ta sannan ta d'auki wayar tayi receiving.

  "Salamu alaikum".

  "Amarya ba kya laifi ko da kin kashe d'an masu gida,y kike ya amarci?".

  Lafiya Hakeela ya Umman ki?"

  "Tana lafiya ya naji muryar ji a dashe,kar kice mini Ango bai d'aga miki kafa ba?"

  Shiru tayi hakan yasa zuciyar Hakeela bugawa,shikenan Hafsat ta gama zama mallakin Hydar

  "Ayya Hakeela anjima ki kai ma Maama waya ko kuma kice su kira ni ina lewar su".

  "Insha Allah sai anjima don yanzu haka ina skull,yaushe zaki yi resuming?"

  "Next week in shaa Allah,ki na sa min attendance pls".

  "kar ki ji komai,insha Allah zan sa miki sai anjima".
  STORY CONTINUES BELOW

  "Yauwa na gode".

  Ba jimawa bacci ya d'auke ta inda Baaba Ladi kuma tayi saurin gama komai gudun kar Umma ta ganta.

  Hajiya Nenne ma yau take shirin barin gidan domin ta saba da zaman gidan sarauta,shirya mata kaya ta saka aka yi inda ta fito falo domin ganin me ke tafiya cikin gidan,ba kowa illa 'yar aikin da take d'an goge-goge,zama tayi kan 1 seater ammat taji abu ya tsoke ta,da wuri ta tashi tare da sa hannu don ganin mene ne,magani ta ciro,kallon maganin ta tsaya yi don tabbas wannan maganin bacci ne,gashi an cire guda biyu sauran kuma na nan,to waye wanda baya samun bacci cikin gidan da har sai ya sha maganin bacci?

  "Zulai!Zulai!

  Duk 'yan gidan fitowa zuwa downstairs suka yi jin Hajiya Nenne ce ke kora,Umma ma jiki na 'bari ta fito

  "Zulai nasan ba mai sayan maganin nan a gidan nan sai ke".

  "Hajiya bani bace...

  "Ai ba yau kika fara mini karya ba bare na yarda,fad'a mini me kika yi da shi".

  Aisha ce tace

  "Hajiya Nenne ai Umma bata shan maganin bacci,saboda tun da aka fara bikin nan ban ga tayi dogon baccin da za'a xe maganin ne ya bugar da ita ba".

  "Kina nufin in maganin ya bugar zaka yi ta bacci ne?"
  "Ehhh zaki de'bi awanni kina bacci ba tare kin farka ba ma".

  "Kar nace shi kika bani ranar bud'an kai".

  Da wuri Umma ta ringa girgiza kai
  "Munafuka shine mana wato don asirin ki yaki kanani shine sai ki had'a mini da magani ko,to bari Muniru ya dawo yau sai kin bar gidan nan,kuma tafiyar baza nayi bs sai naga kin tafi".

  Durkusawa tayi a gaban Hajiya Nenne

  "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri,na yarda nayi kuskure ki hukun ta ni iya son ran ki amma dan Allah kada ki sa Alhaji ya sake ni,bazan iya rayuwa babu shi ba".

  "Aiko dole ki koyi rayuwa babu shi,d'azun naji kina kir'ba yarinyar nan matar Hydar kamar jaka aka ajiye miki wai zata kashe miki 'ya,nima bari nawa d'an yazo na fad'a mishi cewa zaki kashe ni".
  "Hajiya dan Allah ki bar maganar can,ki yafe mini".

  "Bazan yafe miki ba har sai naga an sake ki,ai nasan kullum kan bin gidan bokaye kike yi don ki mallake d'a na da gidan nan,to nikam baki isa da ni ba,yaranki daga mai shaye-shaye sai mai taurin Kai".

  Shiru tayi don tasan ko mutuwa zata yi Hajiya Nenne baza ta canza shawarar ta ba,Aisha ko jin ance d'azun tayi ma Hafsat duka ya sata zare jikin ta ta nufi 'bangaren Hydar d'in,ga mamakin ta taga a rufe,tana hanyar komawar ta shashin su ne taci karo da Baaba Ladi.

  "Baaba Ladi ina wuni"

  "Lafiya Aisha daga ina kike?"

  "wallahi naje 'bangaren ya Hydar ne sai kuma naga basu tashi ba ma daga shi har matar ta sa".

  "Sun tashi mana,ai matar sa na 'bangaren mu zo muje".

  Tsarai tasan sun tashi tunda har Umma ta iya dukan ta,kawai dai bata son Baaba Ladi taji ne.

  Lokacin da suka shiga d'akin ma tana baccirtausayin ta ne ys kama Aisha bata san likacin da zubar da hawaye ba

  "Allah mai iko,Umma kuma daga samun yar mutani sai ta kashe,Yaa Hydar d'in ne ma ya barta,da ace zai d'au hukunci dole Umma ta natsu".

  "Ai abun ya mata yawa,kowa fa a gidan nan tsanar ta yake yi har Hydar d'in,shi da ya kamata ya kula da ita ko don ciwon dake jikin ta amma sai ya barta ko oho,su kuma ganin 'yar talakawa ne bari su kashe,wannan KIYAYYAR ZUCIYAR har ina?"

  STORY CONTINUES BELOW

  "Ni dai wllahi ban tsane ta ba kuma bazan tsane ta ba saboda laifin wani baya shafan wani,in uban ta ya musu abu me nata a ciki".

  "Wannan kuma a tunanin ki ne ba nasu ba".

  "Baaba bari naje sai in ta tashi insha Allah zan zo,kuma in ta tashi ki bata ruwan zadi tayi wanka da sgmhi don jikin ta yayi karfi,ita ce ma abun tausayi,da mai baki suka samo sun isa su mata haka ne?"

  "Shikenan Insha Allah zan mata yadda kika fad'a".

  Tafiya tayi inda Baaba Ladi kuma ta hau ninke kaya.
  ***** ***** *********

  Sulaiman ko bayan Hydar ya gama arranging presentation nasa sai ya ce da shi
  "Man bari naje ina da meeting ".

  "Ohk a dawo lafiya".

  Yana fita Sulaiman ya jawo wayar sa dama bata shiga pattern ba,dialing number Baaba Ladi yayi domin yace a kaiwa Hafsat waya sai kuma yayi sa'ar suna tare,koda aka mika mata wayar taki magana da taji muryar sa ta kashe sai kawai yayi murmushi domin ya d'au kudurin sai yasa Hydar ya fara zargin ta da bin maza a waje,wasa da wayar ya ringa yi har Allah yasa Hydar ya dawo a gajiye.

  "Sannu da aiki fa,ko zan kai ka gida ne amarya ta maka massage".

  "Noo bar ta kawai ita ma ta huta"

  Yadda Hydar yake nufi daban da yadda Sulaiman ya fassara

  "Hydar wallahi ka daina biyewa Hafsat,wuya ya kamata ka bata kk don d'aukar fansa,ka manta Ammin ka ne ki haka zaka zubwa Hafsat ido,wulakanta ta zaka yi ta yadda ko almajiri aka bawa bazai kar'ba".

  Sosai maganar Sulaiman ke masa tasiri a zuciyar sa,bayan sun gama ne yace bari yaje ya lek'a Ammin shi.

  Yana isa gida ya tarar ba kowa a falo,upstairs ya nufa kuma shigar sa tayi dai-dai da tashin ta,rungumar ta yayi yana fadin
  "Sannu Ammi,tun jiya na kawo miki hotob surkuwar ki kina bacci,zare camera yayi a aljihun sa sannan ya duba hotunan har Allah yasa ya iso kan na Hafsat, nuna mata yayi nan ta nuna 'bacin ranta a fili domin tasan tabbas Hafsat 'yar Malam Musa ne saboda akwai kama.
  Shima sosai ranshi ya 'baci ganin Ammin shi ma bata son ta,yanzu ne ya kamata ya d'au fansa akan Hafsat,lokaci yayi da zai nuna mata ruwa ba sa'ar kwando bane.

  Enjoy d weekend,sai mun had'u ran Monday.
  Comment
  share
  ©Hafciey
  [4/24, 13:53] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  Mommy Zee ke da Namecy Nah ga kyautar page

  *SHAFI NA19 📑*
  *__________*📖Kallon ta yayi tare da girgiza kai sannan ya mik'e ya fice,su Asma'u ya tarar a falo suna ganin ya fita suka koma bedroom d'in.

  "Ammi ko akwai abunda kike so ne?"

  Shiru tayi bata ce komai ba,ita fa ba tsanar Hafsat tayi ba yadda Hydar yake tunani,to amma kuma ba bakin da zata fahimtar da shi hakan,ita ta yarda da cewa laifin wani baya shafan wani.

  STORY CONTINUES BELOW

  *********

  Sai yanzu Hafsat ta tashi daga bacci,ko da ta tashi ma lokacin sallah ya kure mata gashi har magrib ya kusa,toilet ta shige inda ta wasa ruwa sannan tayi alwala,bayan ta idar da sallar ne Baaba Ladi ke tambayar ta ya jikin dai,da sauki ta amsa mata.

  "Yanzu ki huta bari na duba miki abinci".

  "Tho"

  Kawai tace don tasan tana jin yunwa,Tuwo ta kawo mata wanda suka dafa a shashin su,kad'an taci tace ta koshi saboda gaba d'aya jikin ta ba karfi,wata katuwa ta zauna ta jibje ta ba gaira ba dalili.
  ********

  Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya cikin gidan alhaji Munir,kullum da salon muguntar da Umma ke yiwa Hafsat,ita dai sai dai tayi ta kuka har ta fawwalawa Allah lamarin ta,yanzu da auren ta sati uku kenan kuma ba nata da yazo gidan sannan kuma har yau ba labarin makarantar ta,ganin zata cutu in har ta cigaba da yin shiru ya sata yanke shawar yau koma me zai faru sai ta tambayi Hydar don shi ma rabon da ta ganshi ya kwana biyu.

  Bayammn sun gama serving abincin dare Umma ta zage ta iya son ranta sai suka koma shashin su,kallon Baaba tayi sannan tace
  "Baaba bari naje wajen shi".

  "Shi wa kenan?"

  "Hydar"

  ta fad'a cikin sanyin murya.

  "Yanzu ki rasa inda zaki je sai wajen Hydar,mutumin da kullum 'yan gidan su cikin tozarta ki suke amma shi bai ta'ba nuna alamun rashin jin dad'in sa ba,to ma uban me zaki je ki masa?"

  Nan take idon ta ya kawo hawaye don zagin Umma na d'azun ma ta daure ne kawai.

  "Nifa bance ki mini kuka ba,ai dole su ringa wulakanta ki yadda suke so,da an miki magana sai ki fara zubda hawaye kamar don ke kad'ai aka yi hawaye".

  "Dama zanje na tambaye sa batun makaran ta nane don na gaji da zaman bautan nan,kuma ana ta wuce ni".

  "Ohhh yanzu naji zance,da na zata kanki zaki kai masa ai".

  Da sauri ta girgiza kan ta.

  "To je ki wanke fuskar ki sai ki tafi".

  Mikewa tayi kamar wacce klyi ya fashe ma a ciki ta shige band'aki ta wanko fuskar ta sannan ta zura hijab tayi hanyar fita.

  "Kada ki dad'e.

  "In shaa Allah.

  Apartment nashi ta nufa sai jero Addu'a take yi Allah dai ya bata jarumtar da zata mi shi magana,cikin sa'a kuma ta samu gate d'in a bud'e,zata shiga kenan Khaleel ya damke hannun ta tare da janta

  "Waye ne,nikam ka sake mini hannu na".

  Ita duk azan ta ma Hydar d'in ne sanda taji yace

  "me ruwan ki da koma waye ne".

  Ido ta zaro cikin tsoro don kowa ya ja mata kunne akan Khaleel mashayi ne.

  "Ka sake ni bana so".

  "Ai ko dole ki so,don rashin wayo ya jefar da ke a d'akin 'yan aiki da dare yayi kuma sai ki ringa binsa turakar sa".
  "Ehh ba ruwan ka ai miji nane".

  "Eyee!yarinya da ke har kin san miji?"

  janta ya ringa yi tana tirjewa har ya kusa shiga part nasa da ita,yana dab da shiga taji an riko d'ayan hannun ta ta waje,da wuri ta juya don ganin wane nene.

  "Kar ka kuskura ka shigar da ita".

  Da wuri ya sake ta jin muryar Hydar d'in ne,shi kuma Hydar d'in hannun ta ya kama.

  STORY CONTINUES BELOW

  "Wallahi ko da wasa ka sake ka ta'ba jikin ta sai na maka abunda baka ta'ba tunani ba".

  shi dai shiru yayi ma Hydar d'in bai ce komai ba,hannun ta yaja suka nufi nashi 'bangaren.
  "Shege wallahi gobe sai na fad'awa Umma,ita zata san yadda zata yi ta yanda ko mai sunan ta baza ka so ji ba".

  suna shiga apartment nashi yasa sakata,direct falon suka nufa,sanda suka shiga falon sannan ya kura mata idanu rai a 'bace yace

  "Me ya fitar da ke war haka?"

  Shiru tayi idanunta a kasa.

  "Hafsat nace me ya fitar da ke?"

  "Dama wajen ka zan zo".

  "Waje na kuma?"

  "Ehhh".

  Numfashi yaja sannan yace
  "Zauna".

  Zama tayi tana mamakin anya kuwa ma Hydar d'in ne.

  "Dama batun makaranta na ne".

  "Malama tashi ki bani wuri,na zata bukatar kud'i ne ma yakawo ki".

  Da wuri ta d'aga ido ta kalle sa sannan tace

  "Dan Allah ka barni mana".

  "Ba nace ki tashi ba,kuma wallahi duk randa kika sake fita wane ya rike ki ba ruwa na,na fad'a miki".

  Mikewa tayi tana fad'in

  "To wallahi ko ka so ko ka ki makaranta dai sai naje".

  Tana gama fad'ar haka ta fice,da ido kawai ya bita yana girgiza kai.

  Tana fita sauri ta fara yi har kamar zata fad'i don tsoron kada Khaleel ya fito ya rike ta,tana shiga d'akin su taja dogon numfashi sanda Baaba Ladi taji.

  "Ke ko lafiyar ki kuwa,ko dai biyo ko aka yi ne?"

  "A'ah ba komai".
  "To zo ki kwanta".

  Kwanciya tayi ta bawa Baaba Ladi baya,tunani take shin ta fad'a mata abunda Khaleel ya mata ne ko kar ta fad'a mata.

  Ita ma Baaba Ladi nazarin ta take,sgin me zai sa tayi hamdala da ta shigo,da haka duk suka yi bacci.
  Bayan sun gama aikace-aikacen gidan kuma kowa yayi breakfast sai suka koma shashin su,yau dai Allah yasa iyayen ta basu sha zagi ba saboda Umma tun safe ta fita don haka na'a yi breakfast da ita ba.

  Wayar Baaba Ladi ta kar'ba aro sannan ta sa number'n Abba,bugu d'aya ya d'auka,tana jin muryar sa ta toshe bakin ta don kukan da yazo mata,da kyar ta iya amsawa da

  "Wa'alaikussalam"

  "Maama na ke ce?"

  Dyad'a kai tayi kamar yana kallon ta sannan ta danne kukar ta tace

  "Ehhh nice Abba ya kuke".

  "Muna lafiya kullum cikin tunanin ki muke har mun yanke shawarar gobe Fatima zata je ta dubo lafiyar ki".

  "ai lafiya ke 'buya Abba,rashin lafiya kuma baya 'buya".

  "to masha Allah ya mijin naki?"

  Shiru tayi sai da ta d'au lokaci har Abba ya zata ta katse kirar ne sannan tace

  "Duk suna lafiya".

  Hakan ne ya tabbatar masa da ba lafiya kenan,yasan ko kashe Hafsat suke yi ba zata ta'ba fad'a a gida na,don haka ya mata nasiha sosai sannan suka yi sallama tana hawaye,suna gama wayar Baaba Ladi tace
  STORY CONTINUES BELOW

  "Yanzu na dawo daga cikin gida kuma Hajiya ta dawo tana neman ki".

  "To bari naje naji ko lafiya ne".
  ko da taje Umma cewa tayi ta kawo mata tea,jikin ta har rawa yake yi don tsoro ta had'a mata tea ta kawo,cike da tsana Umma ta kalle ta sannan ta kar'bi kofin ta kai baki,ihu ta sake saboda zafin da ya ratsa ta,cikin jin haushi ta janyo hannun Hafsat din ta tsoma yasarta cikin tea mai zafi,ita ma Hafsat d'in ihu ta sake wanda sanda Hajiya Nenne ma ta sauko saboda har yau bata koma ba,zaman jiran dawar Daddy take daga tafiyar da yayi ya saki Umma.

  "Ke Zulai kashe musu 'ya zaki yi?"

  Da wuri ta sake hannun Hafsat d'in tare da cup d'in don ita ta zata Hajiya Nenne ta koma.

  Kuka Hafsat take yi amma ba mai sauti ba,nan take hannun ta ya d'aye ji take kamar hannun ba'a jikin ta yake ba,Hajiya Neene ce da kanta ta d'auko zuwan zafi daga kitchen sannan ta tsoma hannun Umma a ciki,nan ta sake ihun da har sai da 'yan aiki duk suka shigo.
  "Ke ma kiji in da dad'i,ke kuma Jafsat tafi wajen Hydar ya miki jinya tunda uwar sa ce ta kona ki".

  Fita tayi tana hawaye a tsakiyar gidan suka had'u da Hydar,kallon ta yayi ganin tana kuka sai yace

  "Ke da wa,kina tafiya kina kuka sai kace yarinya karama".

  Bata kula sa ba ma don ita yanzu ta tabbatar da 'yan gidan zasu iya kashe ta har lahira.

  Jan hannunta da aka kona yayi nan take ta saki ihu.

  "Ke me haka".

  Matse hannun ya sake yi nan ta kuma sakin ihu,hakan ya tabbatar masa inda ke mata ciwo,zaro hannun yayi daga cikin hijab d'in ta ya kalla

  "Subhanallahi,garin yaya kika kone?"

  Ya fad'a cike da tausayi,ganin ya tausaya mata ita kuma sai ta fashe da kuka.

  "Wani ne ya kona ki?"

  Da wuri ta gyad'a masa kai.

  "Waye?"

  "Umma".

  Shiru yayi kamar mai tuna wani abu sai kuma yace

  "Jeki Baaba Ladi ta sa hannun cikin kankara".

  Tafiya ta fara yi nan shima ya juya ya nufi wahen parking motoci ya d'auki motar s ya bar gidan.

  ita ko tana nuna ma Baaba Ladi hannun tace

  "Hafsat zama zaki yi sai ta kashe ki ki huta,ki daina nuna mata tsoro".

  "To".

  Tace sannan aka sa hannun cikin ruwan sanyi sannan aka shafa mata magani.
  Umma kuma Hajiya Nenne na tafiya d'akin ta ita ma ta haura upstairs,Khaleel da yanzu shigan sa ya tarar da Khadija na mata fifita tare da mata sannu,Aisha kuwa tana tsaye sai bin su da ido take yi.

  "Ke kuma munfauka,wato kinji dad'in abunda ta mini da baza ki ce mini sannu ba ko?"

  "Allah huci zuciyar ki Umma,tun d'azun fa nake jero miki sannu".

  "Umma bar ta kawai,me kika nema da munfauka kika rasa,nasan ita har aaddu'a take yi Daddy ya dawo don ya sake ki".

  Ganin sai zagin ta suke yi ya sata jan jiki ta tayi waje,fitar ta kuma yayi dai-dai da shigowar Khaleel,korin Khadija waje yayi a cewar sa zasu yi magana da Umma,tana kunkuni ta fita,ko sannu bai ce ma Umna ba yace

  "Tun yaushe nake ce ki shiga tsakanin Hydar da yarinyar nan kika ki,a cewar ki ba d'aki d'aya suke kwana ba,to in dare yayi bin shi take yi d'aki ba wanda ya sani".

  STORY CONTINUES BELOW

  "Ai banga ta zama ba tunda naga kamar Hajiya ma hankalin ta ya karkata zuwa ga yarinyar,Hydar kam ai dama tun can munafuki ne saboda tunda tazo gidan nan bam ta'ba jin ya musgunama ta ba".

  "Umma ni fa tsoro na d'aya,kada yarinyar nan ta d'au ciki muna zaune,saboda kinga Hydar ma yana da magaji kuma dole nasan Daddy zai ajiye tsanar Hafsat a gefe ya bawa d'an ta katson shi na dukiyar sa".

  "Kuma gaskiyar ka ne Khaleel,me yasa ban yi wannan tunani ba,yanzu abunda zamu yi shine ka nemi mata kai ma kayi aure,kaga in matar ka ta riga tasa haihuwa mune da gidan nan".

  "Gaskiya Umma nikam banda niyar aure yanzu".

  "Ai dole kayi ko don mu amfanu".

  "Umma kawai ki san yadda zaki yi ki raba su,kuma ko tayi cikin ki zubar".

  "Wad'annan duk zanyi su,amma dole kayi aure".

  "To shikenan tunda haka kika ce,amma a ina zan samu mata ke kanki kin san ba hankali bane gare ni".

  "Ai sanun mata shine abu mafi sauki ko kaine shaid'an zaka samu nata tunda muna da kud'i".

  "To batun Hajiya Nenne fa?"

  "Yanzu ma daga wajen malami na nake,insha Allah ba abun da zai faru".

  "Ai shiyasa nake son ki".

  A zuciyar sa ko takaici da bakin ciki ne,taya zata ce yayi aure shi da Hafsat yake hari.

  ******
  Aisha ce ta lalla"ba taje wajen Hafsat,sallama tayi Baaba Ladi ta amsa,gaisawa suka yi sannan tace

  "Ina Aunty'n nawa?"

  "yanzu ta shiga band'aki,ti jira ta".

  Zama tayi a bakin gado tana jiran fitowar Hafsat d'in,bayan ta fito ne take ta kallon Aisha tana mamakin me ya kawo ta wajen su.

  "Aunty har kin fito?"

  Wani kunya ce ya kamata don tasan Aisha sa'ar tace amma take kiran ta da Aunty.

  "Hafsat magana take miki fa".

  "Ehh na fito ina wuni".

  "Laa ai ni zan gaishe ki bake zaki fara gaishe ni ba,ya hannun ki".

  "Da sauki".

  Kallon Aisha tayi iya nazarinta cikin gidan ita da Hydar ne basu da mugun ta,saboda sukan nuna damuwar su in abu ya sami mutum,akwatin kayan ta taja inda ta ciro doguwar riga sannan taje toilet tasa,tana dawa kuwa ta zauna domin gyaran gashin ta.

  "zo na gyara miki shi".

  Murmushi tayi sannan tace

  "Da kin bar shi kawai".

  "A'ah dan Allah zo na gyara miki".

  Zuwa tayi Aisha ta gyara mata kai sannan suka yi breakfast tare,nan Aisha ke janta da surutu amma ita sai dai tace hmm ko tayi murmushi,hakan yasa Aisha fahimtar halin su iei d'aya da Hydar a rashin sin magana,ta jima sosai don har Hafsat ta bata cim-cim nan ta zauna raci don na auren ma da aka bawa dangin miji zubarwa suka yi acewar su baza su ci abincin gidan matsiya ta ba".

  Sallama ta musu gudun kada Umma ta dara neman ta, zata tashi kenan qayar Hafsat ya hau ringung,tyawa tayi Hafsat d'in tayi receiving call d'in

  "Hello Hakeela ya kike".

  "Lafita qalau Hafsat,dama na kira ki ne don na shaida miki gobe zan zo mu wuni".

  "Allah kaimu don ina gida".

  "To shikenan sai nazo".

  Shiru Hafsat d'in tayi alamar tana tunani

  "Nasan damuwar ki baza ta wuce inda zaki ajiye ta ba,ba zaki so ta ganki a d'akin ma'aikata ba".

  STORY CONTINUES BELOW

  Cike da mamaki take kallon Aisha taya akayi tasan abunda kw zuciyar ta,baza ta so Hakeela ta ganta a d'akin ba kar taje ta fad'a a gidan su.

  "Kar ki damu nasan me zanyi".

  Kai kawai ta girgiza sannan Aisha ta tafi.

  "Hafsat me ne?"

  "Baaba ina tsoro kar in ta ganni a cikin ku taje ta fad'a a godan mu,ba qai nafi karfin zama a cikin ku bane A'ah Maama ta nada hawan jini kada ya tashi".

  "Lallai Hafsat ke yarinya ce amma mai hangen nesa,kada ki damu Aisha zata san nayi,tsam ita kad'ai ce cikin yaran matan gidan nan bata kyaman 'yan aiki".

  "Allah sarki".

  "Ita bata d'auki halin 'yan uwan ta ba tsam".
  Aisha ko tana fita apartment nasu ta nufa inda direct d'akin su ta shige ta sa key,number Hydar ta ringa dialing amma baya picking,sanda ta gaji don kanta ta bari...
  Zaman jiran Hyar d'in ta fara yi...

  Comment
  share

  ©Hafciey
  [4/24, 13:53] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
                *1441H/2020M.*
                
     

  ®☄
  *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

      '''🎐 G•W•A🎐'''
  _*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_


  *NA MARUBUCIYA:-*
  *HAFCIEY MUSA✍🏼*•

  ~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

  *SHAFI NA 20 📑*
  *__________*📖Haidar ko yana can tare da Sulaiman a office wanda ya zama masa super glue duk fitar sa da shigar sa a kan idon Sulaiman,shi ya rasa dalilin Sulaiman na rashin zuwa wajen aikin sa sai dai ya zauna tare da shi.

  Daga lokacin da Aisha ta fara kirar sa Sulaiman ne ya fara ankara,sai yaki ya fad'awa Haidar d'in saboda wayar a silent take kuma shi a zaton sa Hafsat ce ke kira don ya 'batarwa Haidar din hankali kada ya lura da wayar sai yace

  "Haidar ya batun skull na Hafsat ne?"

  "Skull dai ina kokarin ganin komai ya tafi dai-dai".

  Ido Sulaiman ya zaro ganin haukar da Haidar ke shirin yi,yanzu yana nufin zai bar ta ta koma skull,lallai in ya zubawa Haidar ido abun ba zai masa kyau ba.

  "Yanzu kana nufin zata koma makaranta?"

  "Nifa baka ji daga baki na ba".
  "To me kake nufi?"

  Shiru yayi bai ce da shi komai ba hakan ne kuma ya b'ata wa Sulaima rai wato har shi Haidar zai yiwa banza kuma duk akan Hafsat

  "tunanin me kake yi Man?"

  "Babu fa bari na tafi akwai aikin da zanyi".

  Hmm kawai Haidar yace don ya fahimci akwai abunda ke damun Man d'in.

  *****

  Aisha tayi zaman jira har ta gaji sai gab da magrib Haidar ya dawo tana jin k'arar motar sa da gudu ta fito daga d'aki ta nufi apartment nashi,a k'ofar ya same ta.

  "An wuni lafiya ya Haidar".

  "Lafiya".

  yace sannan yaci gaba da tafiyar sa,bin sa ta fara yi da sauri-sauri har suka isa

  STORY CONTINUES BELOW

  "Ya Haidar dama nazo na tambayi wata alfarma ce a wajen ka".

  "Alfarma? kamar ta me kenan?"

  "Dama Aunty Hafsat ce zata yi bak'uwa kuma bai dace ta ganta a shashin ma'aikata ba saboda k'ima da mutuncin mu zai zube".

  "Ban damu ba in taga dama ta hanata zuwa,ita bata da bakin magana sai ke".

  Yana fad'an haka ya shigewa d'aki tare da tura k'ofar ya rufe,juyawa tayi tana tafiya a lokaci guda tana wasa da yatsun hannun ta

  "Yanzu me zance da ita,bai kamata nace mata ya hana ba".

  Tsaki taja sannan ta koma 'bangaren su sai zafa da marwa take yi ina ma ace gobe Umma bata nan da sun zauna a falo.

  Haka tayi ta safa da marwa kuma bata samo mafita ba har gari ya waye.
  Washe gari tun da akayi breakfast take zaman jiran fitowar Haidar daga apartment nasa a wajen motar sa don yau bai yi breakfast da su ba.

  can ta hango shi yana tafe cikin bakar jumper tasha aikin wuta ya kafa hula a kansa,agogon hannun sa yake duba time don gani yake kamar ya mak'ara

  "Ya Haidar ba dai kyau ba kam Allah tsare ka daga duk wata abar cutarwa".

  Kallon ta yayi sannan ya cire kai tamk'ar bai ganta ba da wuri ta sha gaban sa tana fad'in

  "Ya Haidar dan Allah ka bata wallahi rashin tabbacin zaka bata ne ya hanata zuwa".

  Tsaki yayi game da danna key'n motar sa ya bud'e,kafar sa d'aya yasa a waje d'aya kuma na daga ciki ya tada motar,fuskar tausayi ta masa inda ko inda take bai kalla ba yasa d"aya kafar sa cikin motar ya rufe k'ofar yayi gaba.

  Da kallo ta bi sa ji take tamkar tayi ihu ko zai taimaka mata,ba ita ta bar wajen ba sanda taga gate man ya bud'e masa kofa ya fita cikin sanyin gwiwa ta nufi apartment nasu Hafsat.

  Bakin ta d'auke da sallama ta shiga kuma lokacin ta tarar suna breakfast,jarumta ta arowa kanta knda suka gaisa sannan Hafsat ta mata bismillah

  "A'ah ki kawai yanzu na gama nawa a cikin gida".

  Cigaba da breakfast suka yi inda ta d'aura kafar ta d'aya kan d'aya tana girgizawa.

  "Aisha lafiya kuwa naga kamar da masifa kika zo".

  "Bar ni da mijin ki Allah ya 'bata mini rai".

  "ya hanaki 'bangaren sa ko?"

  Kan tayi magana ma gate man yayi sallama amsawa suka yi inda aka basa izinin shigowa,gaisawa da Baaba Ladi suka yi sannan ya kalli Hafsat yace

  "Ga wannan inji Alhaji karami wai a ba ki".

  Hannu ta mik'a ta tar'bi keys da yake mik'a mata,wani farin ciki ne ya lullu'be Aisha bata san sanda ta rungume Hafsat ba,sallama ya musu sannan ya fice.

  "Wow dama nasan Yaa Haidar ba zai ta'ba hanawa ba,yanzu gama da wuri sai muje mu karka'be d'akin sannan muyi mata girki".

  "To amma kina ganin Umma baza ta miki holo ba?"

  "Kada ki damu sai tasan ina can ne zata yi holo bare yau Hajiya Nenne ta rufe bakin masifar".

  Ta fad'a tana murmushi.

  Suna gamawa suka sallami Baaba Ladi sannan suka nufi 'bangaren,d'akin Hafsat d'in suka fara gyarawa sannan d'akin Haidar d'in wanda da kyar Hafsat ta yarjema Aisha shiga ita kuma ta tsaya gyara falo.

  Nan take suka gyara ko ina yayi sab sannan suka fishe turarukan wuta daga nan kuma suka shige kitchen.

  Ba abunda babu cikin fridge d'in na girki sai abunda ba za'a rasa ba.

  STORY CONTINUES BELOW

  Fita Aisha tayi ta aiki me bawa flower ruwa sannan ta dawo suka cigaba da aiki cikin d'an lokaci suka gama,jerawa suka yi a dining sannan Aisha tasa Hafsat d'in shiga toilet tayi wanka.

  'Daya daga cikin kayan dake cikin akwatin ta na aure Aisha ta fitar mata amma tace ita baza ta sa ba.

  "Dan Allah ki manta da komai ki sa".

  "A'ah zan sa wanda aka mini na hana gori".

  "To ki tsaya a nan bari naje na d'auko miki".

  "dan Allah kiyi sauri".
  Fita tayi ba jimawa sai gata ta dawo kunna t.v tayi sannan ta nufi d'akin Hafsat d'in ta kai mata kaya.

  "Yauwa na gode".

  Bata wuri tayi tasa kayan inda ta dawo ta d'aura mata d'an kwali.

  Gamawar su yayi dai-dai da shigiwar su Hakeela shashin ta,da gudu Saudat ta d'ale jikin Hafsat d'in

  "Aunty Hafsy tunda kika tafi ko kira babu".

  "Yi hak'uri Saudat aiki ne ya mini yawa".

  "Lallai Hafsat don kina d'okin gani Saudat  shine ni ko sannu ba za'a mini ba".

  "Yi hak'uri dan Allah ".

  Cewar Aisha
  "Ayya swthrt yi hak'kuri da Allah".

  "ke ko me yayan ki yake bawa Aunty'n kin nan da tayi jiki haka?"

  "Ai baki bazai iya fad'ar sa ba".

  Ita dai Hafsat murmushi kawai tayi inda tace in sun gama tsokanar ta sai suzo suci abinci.
  Murmushin ya'ke Hakeela tayi tana ta bin Hafsat da kallo mai kama da harara a fakaice sai mamakin irin canjin da Hafsat ta samu takeyi.
  Mikewa Hafsat tayi ta sake gayyatarsu zuwa dining inda A'isha ce tayi serving nasu sannan tayi excusing nasu kaman zataje wani wuri nan kuwa wuri ta basu tasan matsayinsu na kawaye baza a rasa wani magana da suke son tattauna shi a asirce ba.
  Bayan sun gama cin abinci sun dawo parlor suna kallon TVn da already A'isha ta kunna ne Hakeela ta dubi Saudat taga hankalinta kap ya koma kan TV.Nan da can ta dudduba ta tabbatar babu kowa snn ta juyo ta dubi Hafsat tare da matsowa dab da ita.
  Murmushi Hafsat tayi tana Mai baiwa Hakeela attention d'inta domin kuwa ta fahimci kamar akwai magana a bakinta.
  "Kawata ya kwana biyu?ina can sai kewarki nake anya ko kina kewata?"
  Murmushi Mai sanyi Hafsat tayi tace

  "Ka jiki da wani zance,ai idan nace ina kewarki ma to kamar bana kewarki kenan!"

  Ta'be baki Hakeela tayi a cikin ranta kuwa tace.

  "munafuka..."

  Gyaran murya tayi snn cikin k'asa k'asa da murya tace
  "Ya ya angon naki yake?"

  Hafsat jin an d'auko chapter'n Hydar sanda taji gabanta ya Fad'i Amma saita basar tace..
  "Uhm ya na nan"

  Danne qullutun bakin cikin datake ji Hakeela tayi tace...
  "Kajiki da wani magana kawata,nasan Yana nan Mana,ina nufin ya yanayin zamankun?"

  Murmushi kawai Hafsat tayi batace komai ba tana Dan wasa da bangle da ke hannunta.

  Harararta Hakeela tayi k'asa k'asa sannan cikin kara kankanta murya tace,

  "I hope babu wani damuwa dai Koh?"

  "Uhm bbu...."

  Hafsat tafada tana faman mayarda hankalinta kan TV dukda dae ba kallon take ba amma ita sam- Sam batason maganar Hydar din dasukeyi,itakuwa Hakeela ta dage saboda tana so ta samu wani idea dai da zata dogara kanshi wurin fara yakar Hafsat....
  STORY CONTINUES BELOW

  "k'awata idan fa akwai matsala ki daure kifada min I'll help u look for a solution,ba komi yasa kika ga na matsa ba saboda na rigada nasan halinshi ne,kinga Kuma duk abin da zai cutarda ke bazanso shi ba k'awata".
  Ckn K'osawa Hafsar tace..

  "Hakane..."

  Hakeela ji tayi makokonta ya cika ganin Hafsat taki ta bud'e mata wata hanyar da zasu fara discussing fully kan zamansu da Hydar....

  Mikewa Hafsat tayi cikin sauri Hakeela tace...

  "ina Kuma zakije?"

  Murmushi ta mata tace.

  "Zan kawo muku lemo ne kinga bai kamata kuna zaune haka babu wani Dan abin refreshment basaboda yanayin weather."

  "Eh hakane,"

  Hakeela tafada tana gyara Zama,

  "But kiyi sauri ki dawo fa k'awata saboda  har yanzu ina kan bakata saimun tattauna don wallahi bai isaba ya cutar min da kawa!"

  "Uhm"

  kawai Hafsat tace ta nufi fridge tad'auko drink da two glass cups kowani motsinta akan idon Hakeela sai kissima abubuwa takeyi cikin ranta murmushi kwance kan fuskarta.

  "So gayamin...."

  Hakeela tafada still re-emphasising bayan Hafsat ta tsiyaya musu drink din.
  "Ya yake treating d'inki like yanadai girmamaki Koh? Kar yaga yanayin yadda kukayi aure yace zai rainaki?"

  Murmushi Hafsat tayi ta d'auki remote tafara scrolling channel,Sam ita batason discussion kan Hydar Amma Hakeela ta daddage,dakyar dai while changing station Wanda hakan yasa saudat tadan juyo tana duba wake canza channel sannan ta sake maida hankalinta kan kallon.Sanda tayi choosing channel sannan tace.

  "A'ah bbu abin da yake mini Kuma dai Yana bani girma na daidan gwargwado".

  Daam! Hakeela taji gabanta yafad'i karfa gayen nan yafad'a tarkon Hafsat!
  Mazewa tayi tace...

  "Aikuwa gwara,to 'bangaren yan gidan fa? Dan naga suma Yan duniya ne"

  "A'ah bawani damuwa saidai yan wainda ba a rasawa"

  "Hakane...wallahi kawata duk Wanda yace zai takaki karki ragarmai karma wannan khaleel din,Amma dai Hydar d'in Yana biya Miki dukkan bukatunki Koh kawata?"
  Dukda tambayar tayiwa Hafsat nauyi Amma saita basar tayi kaman bata fahimci kan me Hakeela'n take magana ba,haka kawai ta tsinci kanta da cewa...

  "Eh,domin har saloon ma yakan barni naje wataran yasa driver yakaini"
  "Innalillahi...."
  Hakeela tafad'a a razane hakan yasa Hafsat zabura tace...

  "lafiya?"

  Dasauri Hakeela ta dai-dai ta kanta domin kuwa shock ne ya kamata jin yakan iya sa driver ya kaita kenan aje- aje zaifara kaita da kanshi...
  "Haba Hafsee,kenan shi bashida lokacin kaiki saidai driver ya kaiki kina matsayin matarshi?gaskiya Hydar dinnan Dan rainin hankaline"
  Tafada cikin masifa-masifa tanason kauda damuwa da kishin da k shimfid'e kan fuskarta,
  Dariya kad'an Hafsat tayi sannan tace

  "InBanda ke kinsan ai aiyuka ne suka Sha Mai Kai,ni ba ma wannan ba,bani labarin bayan rabuwa".

  Kwa'be baki Hakeela tayi tace..

  "wani labari ne babu wani labari fa,gashi kece ma kike min rowan labarin mijinki?"
  STORY CONTINUES BELOW

  "No ba haka bane".
  "Toh yaya ne?"

  Sharewa Hafsat tayi ta ce,

  "Kinfa Kara kyau kika yi wani fresh".
  "Ki jiki da zaulaya kyau aisai ke....."

  Bata Karasa Fad'in abin da takeson fad'aba idonta yafad'a kan hoton Hydar Wanda ke makale dai-dai saitin TV dukda ba sosai yayi murmushi ba Amma hoton ya bala'in yin kyau.

  Lumshe ido Hakeela tayi cikin ranta tace...

  "inshallahu dai...."

  Katseta Hafsat tayi ta dafa kafadanta tace.

  "Ya dai?"

  "Babu....maganar me mukeyi ma....?"

  Tafad'a cikin son kauda kallon tuhumarda Hafsat ke mata.

  Hakadai Hakeela ta cigaba da yimata tambaye- tambye domin Tasha ruwan cikin Hafsa Amma fafur taki bata had'in Kai har lokacin tafiyar su yayi.

  Hakeela sai Santin gidan takeyi tana ta kitsa maganganu cikin ranta,a Kuma dai-dai lokacin Aisha tashigo rikeda wani babban pack Wanda akayi wrapping nashi..

  ganinsu cirko-cirko yasa ta ja birki da alamu ma Shirin fitowa suke.

  Da murmushi kan fuskarta tace..

  "me zan gani haka ba dai tafiya zakuyi ba?"

  "Aikam ynxu muke Shirin fita kinga lokaci ya ja kar muyita Zama har oga ya dawo kinga baxan ma samu attention na kawatan ba".

  A ranta kuwa Allah Allah take Aisha tace suzauna Mana suga dawowarshi inyaso ma saisu gaisa Amma taga Aisha bata baiwa maganar muhimmanci ba illa mikawa Saudat pack d'in datayi tana cewa...

  "mun gode mun gode sosai da ziyara saimun sake ganinku"

  Ckn murna saudat ta mata godiya yayinda Hakeela dai yake tayi tana ji kaman tayi strangling nasu duka daga Aisahr har Hafsat.

  Haka suka rakosu har gate Aisha taki basu chance balle tasamu maybe befor going tasamu wani information to haka ta like musu har suka rabu sannan suka juyo Aisha nata zaulayar Hafsat kan karfa tayi kuka Dan k'awarta ta tafi becos nasan Zaki iya"
  Itadai Hafsat batace komi ba tayi murmushi har saida suka iso kofan apartment d'in Aisha ta dubi Hafsat tace...

  " Inaga ke kad'ai Zaki kimtsa wurin nan domin wallahi inada urgent work da zanyi sorry"

  Zaro ido Hafsat tayi ta ce

  "Laaaa no problem wallahi na gode sosai jeki kiyi aikinki nima yanzu zan kimtsa wurin sharp-sharp na kulle na koma wurin Baaba"

  Smiling Aisha tayi tace,

  "ok ba matsala zamu had'u a can d'in kingama  sai na kar'bi key d'in na maida masa zuwa dare inya dawo"

  Gyad'a Kai Hafsa tayi tare da rungumar ta sannan suka rabu da Aisha ita tayi sashensu itakuwa Hafsat ta shige sauri-sauri tafara kimtsa wurin tana so tayi tagama dai before lokacin dawowarshi yayi.

  "Alhadulillah!"
  Tafurta ganin harta turare wurin da turaren wuta ta fesa room freshener bai dawo ba.

  Cikin gaggawa tafito tana jawo k'ofar a bayanta juyawarda zatayi taji "gau" ta gwara goshinta da na mutum.

  Saurin dafe goshinsu sukayi dukkansu biyu suka furta "awch" a tare  yayinda tafadi nata cikin yanayi na jin zafin gwaruwar shikuwa daga kaji yanayin yadda ya furta awch din zaka fahimci akwai shagwaba ciki......🤪

  'Dago kai tayi ta kalle sa da kuma wanda ke bayan sa.

  "Sannu da dawa".

  Kamar ba zai amsa ba sai kawai yace

  "Uhmm".

  Wucewa take k'ok'arin yi yace

  "Ina kuma zaki je,baki ga bako bane?"

  ji tayi kamar ta d'ebe sa da Mari

  "A'ah Haidar barta kawai in bata son na shiga kila ta gama shiryawa dawar ka kai d'aya".

  Haidar dai bai ce komai ba ita kuwa Hafsat ta san makirci ne ya kawo sa da goshin magrib nan.

  "Bismillah"

  Tace sanda ta shige falon,bin ta suka yi a baya inda Haidar yayi hanyar bedroom nashi yana fad'in

  "Hafsat!"
  tsaki taja a ranta sannan tabi bayan sa Sulaiman naji kamar ya mutu don bakin ciki.

  Ganin yana k'ok'arin shiga bedroom nasa ya sata saurin cewa

  "Gani".

  ba tare da ya juyo ba yace

  "Ki basa abinci".

  Yana gama fad'ar haka ya shige bedroom d'in,ita ko kwaikwayon maganar sa tayi sannan ta murkud'a baki ta juya.

  Yana shiga d'akin yaga canji ajiyar zuciya ya ja sannan ya rage kayar jikin sa tare da shigewa toilet.

  A can falo kuma Sulaiman ganin ita d'aya ta fito sai binta da kallo yake bai damu da cewa ita matar wani bace.

  "Dama da ba muyi girkin ba ina zai samu wanda zai bashi".

  Cikin zuciyar ta ta fad'i hakan a Zahiri kuma dining ta nufa ta duba abincin da ya rage sannan tazo ta ajiye mishi kan center table ba tare da tace da shi ko sannu ba,ruwa da drinks ta kuma kawo masa sannan ta nufi hanyar waje.
  "Ko mini magana ko kada ki yi ba damu na zai yi ba kuma Hydar dai nazai ta'ba son ki ba saboda yana da budurwa".

  da farko kamar ba zata juyo ba sai da ya ambaci sunan Hydar da kuma Ba zai so ta ba sannan ta juyo gare sa

  "Da ina maka ganin zaka sauya shiyasa nake girmama ka bana tamka maka ashe ba haka bane,Ko Hydar ya so ni ko ya tsane ni wannan ba matsalar ka bane,sannan batun yana da budurwa kuma ban damu ba saboda shi mijin mata hud'u ne,amma a yanzu ni duniya ta sani matsayin matar sa".

  Ido ya zuba mata yana mamakin inda ta koyi jarumta,ya bude baki zai yi magana kenan Hydar ya fito sanye da brown jallabiya

  "Man muje lokacin sallah yayi in mun dawo sai ka k'arisa abincin".

  "No muje daga can zan wuce,amarya na gode da k'aramcin ki a gare ni".

  Ko kallon inda yake bata yi ba.

  Sulaiman na gaba Hydar na biye da shi a baya,waigawar da Sulaiman zai yi da niyar masa magana ya gansa ya nufi wajen Hafsat, ido ya zaro yana ganin ikon Allah.

  Hydar ko yana nufar ta k'irjin ta ya hau duka.

  Hannun sa yasa ya rik'o hannun hagun ta da Umma ta kona ta da safe,tallafo hannun yayi zuwa fuskar sa don ya kalla da kyau inda Sulaiman ko a zaton sa kissing na hannun yayi.

  Idonta a k'asa bata ce da shi komai ba,sakin hannun ta yayi sannan yace

  "Ki kulle k'ofar ba yanzu zan dawo ba".

  Yana gama fad'ar haka ko amsar ta bai jira ba ya tafi,a k'ofar falom ya tarar da Sulaiman suka fice.

  ******

  'Bangaren Umma kuwa ido a rufe take nemawa Khaleel mata don ta rantse sai Khaleel yayi aure cikin watan nan.
  Aisha kuwa bayan ta kammala abunda zata yi sai ta faki idon Umma ta wuce 'bangaren su Hafsat.

  A yau d'in ne kuma Hajiya Nenne ta bugawa Daddy waya nan yace mata kada ta damu yana hanya.....

  Love yhu wujiga-wujiga fans na k'iyayyar zuciya.


  Komentar

  Tampilkan

  No comments:

  Post a Comment

  Terkini

  +
  ?orderby=published&alt=json-in-script&callback=labelthumbs\"><\/script>");