Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

K'ADDARA CE CHAPTER 8

K'ADDARA CE CHAPTER 8

- - Post a Comment

 K'ADDARA CE CHAPTER 8


Baba mairo tace kikwantar da hankalinki Amina insha Allahu kika zauna wajensu hajiya ba zaki ta6a yin da kin saniba saboda mutuncin su da sanin darajar mutane da tausayin na k'asa da su.+


Murmushi hajiya tayi tace baba Mairo duk mu kad'ai? Yabon kan ai yayi yawa


Baba mairo tace kun ma wuce haka hajiya wlh tsakani na daku saidai addu'a domin banda abunda zan biyaku halarcin da kuke min.


Aunty khairat tayi murmushi tatashi tadawo kusa da Amina da har lokacin kuka take,

Jawota jikinta tayi tana lallashi tace kikwantar da hankalinki insha Allahu zakiji dad'in zama damu ba na tunanin zaki samu matsala daga 6angarenmu kema dafatan zaki zauna damu lafiya ko da naga alamar kama a 6angarenki ba za a samu matsala ba.


Share hawayenta Amina tayi tace nagode maku sosai da har kuka jawoni jikinku batare da kun sanniba kuma kuka yarda da ni Allah yasaka maku da alkhairi insha Allahu nima ba zaku samu matsala daga gareniba zan zauna daku tsakani ga Allah.


Alhaji yace masha Allah, Allah yabamu ikon rik'eki amana kamar sauran yaranmu, kema Allah yabaki ikon Zama damu tsakani ga Allah.


Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen ya rabb.


Hira suka d'anyi cikin nishad'i da farin ciki sannan su hajiya sukayi sallama suka tafi yarage daga baba mairo sai Amina da d'iyarta.


Baba mairo tazauna tayi ta ba Amina labarin mutunci da karamcin su Alhaji.

Washe gari kasancewar ran Thursday ne bayan idi driver ya kawo masu breakfast sunyi, fitowa sukayi suka d'an zagaya asibitin ko da k'afar Amina bata ida warkewa ba ammah ta ji dad'in hakan sosai.


Yauma kamar kullum mummy sai wajen azahar tazo takawo masu lunch bayan sun gaggaisa cikin girmamawa daga nan suka hau hira, mummy tana ta lalla6a Amina duk wani motsi da zatayi sai ta tambayi meke damunta, ko da kusan kullum haka take mata abun har mamaki yakeba ma Amina irin yadda mutanen suke kula da ita kamar daman chan sun santa.


Bayan sallar la'asar suna zaune suna kallo a T.V d'in da take a jikin bangon d'akin wasu 'yan matane biyu kyawawa sunci gayu sukayi sallama suka shigo.


STORY CONTINUES BELOW

Kar6a masu sukayi Amina tabisu da kallo d'aya daga cikinsu tana kama da hajiya.


Baba mairo tace oyoyoo 'yanmatan hajiya sannunku da zuwa


Murmushi sukayi sukace yauwa baba mairo dafatan mun sameku lfy?


Baba mairo tace lafiya lou.


Mummy tace har kundawo daga school d'in kenan,


Eh wlh mummy tun d'azun ma muka dawo, baki dad'e da baro gidanba muka koma.


Mummy tace ohk, kun dai ci abinci ko? Eh mummy


Kallon Amina sukayi sukace mummy wannan itace patient d'in tamu?

Eh mummy tace sannan takalli Amina tace Amina ga 'ya'yana nan sunxo dubaki school suke zuwa saisa baki ta6a ganin sunzo ba.


Murmurshi Amina tayi tace tace Allah sarki Sannunku,  ina wuninku? Amsa mata sukayi sannan sukayi mata ya jiki tace dasauk'i

Sukace Allah yak'ara sauk'i


'Dayar takalli Ameerah da take hannun Amina tace masha Allah babynki mai kyau kawo ta mugaisa.

Murmushi Amina tayi tamik'a mata ita,  Itama Murmushi tayi tak'ara cewa masha Allah fyn gurl Ameerah ko sunanta?

Eh Amina tace.


Baba mairo tace Amina wad'annan 'yanmatan hajiya ne wannan tanuna wadda ta amshi Ameerah tace itace fatima, wannan kuma tanuna d'ayar da tunda suka gaisa bata k'ara cewa komai ba sai shan k'amshi take tana danna waya tace itace Salma.


Amina tace Allah sarki sannunku.

Fatima tayi murmushi tace jiki ya yi kyau kenan Amina tunda har kina taka k'afar


Eh gaskiya Alhmdllh gobe ma za a sallamemu inji Baba mairo

Toh Allah yakaimu Allah yakiyaye gaba

Sukace Ameen.


Daga nan suka hau yin hira ita da fatima kamar daman sun san juna sai bayan isha'i sannan suka koma gida tare da su mummy


Amina bataso tafiyarsu ba, fatima ta burgeta sosai saboda sauk'in kanta irin na yaya khairat ko da mummynsu suka biyo cikin ranta tace ba kamar waccan salmar ba da taketa sha ma mutane k'amshi tana d'auke kai (lol su Amina gani d'aya fa kikayi ma salma ammah shine harda mata mummunar fassara ammah dai muje zuwa)


Ranar juma'a tun dasafe sukayi wanka suka shirya Amina tana ta d'okin barin asibitin kamar ba ita bace tace asibitin shine rufin asirintaba...lol

Sai wajen k'arfe goma Alhaji yazo da kansa yakawo masu breakfast, bayan sungama gaisawa yace anyi discharge d'in nata? Baba mairo tace a'a ko da likitan yazo allura yayi mata kawai ammah baice mana komai ba.


Alhaji yace toh shikenan bari inje office d'in doctor d'in, suka amsa da toh.


Amina Allah Allah take Alhaji yadawo sutafi domin ita a yanzu asibitin har ta gundureta kwana shidda da tayi ammah ji take kamar ta shekara d'aya daman rashin wajen zamane yasa taza6i zaman asibitin tunda batasan inda zataje ba lokacin.

Tare da baba mairo suka had'a kayansu suna jiran dawowar Alhaji

Ba afi minti sha biyar ba sai ga Alhaji ya dawo tare da doctor, dubata likitan yak'ari yatabbatar da babu matsala sannan yarubuta masu takardar sallama tare da wasu magungunan.


Idi driver ne yazo yakwasar masu kayansu yakai cikin mota, tunda suka kama hanya Amina murnar da takeyi takoma ciki duk sai jikinta yayi sanyi cikin ranta tace Allah gani gareka ko wace kalar rayuwa kuma zanyi a yanzu, hawaye duk suka cika mata ido cikin dubara tagoge ba tare da su baba mairo sun ganeba.


Tafiya sukayi ta kusan minti goma sannan suka iso wani dank'areren gida, horn driver yayi dasauri maigadi yazo yahangame masu gate ,


Amina sakin baki tayi tana kallon gidan cikin ranta tace wannan ko dae hotel ne aka kawoni uhm ni da ban ta6a zuwa hotel ba ya za ayi insan kalansa koma dai ina ne zan gani,


STORY CONTINUES BELOW

A wajen da aka tanada domin ajiye motoci suka nufa dasauri maigadi yazo yabud'e ma Alhaji k'ofar mota yana ta kwasar gaisuwa.


Fitowa su Amina sukayi tana biye da baba mairo suka nufi cikin gidan Amina bin ko'ina take da kallo baki a sake kamar wata sabuwar bak'auya, cikin ranta tace gaskiya masu kud'i suna hutawa a duniya mukuma muhuta a lahira _(lol ammah idan anyi kyakkyawan aikin sannan za a huta a lahirar domin babbar asarace mutum yazo duniya yakoma ma ubangijinsa ba tare da yayi kyakkyawan aiki ba, da talakka da mai kud'i duk d'ayane a wajen Allah babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi jin tsoron Allah, Allah yasa mudace)_


Baba mairo dariya kawai take ma Amina ganin yadda duk takoma, bata ida rud'ewa ba saida suka nufi main parlour gaskiya ya tsaru maka-makan kujerune a cikinsa Ash nd black colour labulen 'akin suma ash and black ne sai k'atuwar plasma da aka sa a bango, gefe d'aya kuma dining area ne, up step d'akuna biyu ne sai daga cikin parlour d'in ma akwai d'akuna biyu, Amina cikin ranta tace na shiga ukku kar dai ace 'yan yankar kaine nayi gamo dasu hawaye suka cika mata ido tace shikenan ni kuma tawa k'addarar kenan da nasan haka zan samu mutanen nan da ba zan amince masuba....

Maganar baba mairo ce takatseta daga tunaninta tace Amina ga wuri kizauna kafin hajiyar tafito bari inje ciki,


Saman lallausan karfe d'in da yake shimfid'e tsakiyan parlour tazauna a tsorace tare da k'ara rungume d'iyarta, daidai lokacin hajiya tafara safkowa daga saman step murmushi d'auke a fuskarta tace oyoyoo ga patient sannunku da hanya,


Waje tasamu tazauna sannan tace Amina kihau saman kujera kizauna mana ai kema yanzu kin zama 'yar gida kisaki jikinki mana.


Amina duk'ar da kanta tayi k'asa tace nan ma ya yi hajiya cikin girmamawa ta gaishe da hajiyar, cikin fara'a ta amsa mata tare da tambayarta k'arfin jiki.


Amina tace Alhmdllh.


Dai-dai lokacin Alhaji yashigo yace a'ah ashe kuna nan zaune murmushi mummy tayi tace eh muna jiran shigowarka ne, yace toh gani ai shima waje yasamu yaxauna.


Gyaran murya Alhaji yayi yace toh Alhmdllh Amina  muna tayaki murnan shigowa cikin family d'inmu dafatan zaki iya zama da mu, insha Allahu zamu zauna dake tsakani ga Allah kema muna fatan hakan daga gareki, dan Allah kar kibari aji wata matsala ta fito daga wajenki kizauna da kowa lafiya insha Allahu zakiji dad'in zama damu kisaki jikinki kimaida nan yazama kamar yadda zakiyi rayuwa a gidanku haka zakiyi a nan, kimance duk wata damuwa da tasameki kar kimance Allah yana jarabtar bawansa ta kowace hanya ya kamata muyarda da k'addara mai kyau da marar kyau, duk abunda kike buk'ata ga hajiya nan kar kiji komai kid'aukemu a matsayin iyayenki.


Amina hawaye takeyi tunda Alhaji yafara magana cikin ranta tace daman haka rayuwar take idan wani ya k'ika sai wani yasoka a rayuwa komai bak'in jinin mutum ba zai ta6a rasa masoyi ba

Share hawayen fuskanta tayi ahankali Amina tace toh insha Allahu daddy zan kiyaye nagode sosai da karamcinku a gareni insha Allahu zan zauna da kowa lafiya ba zakuji wani abu daga gareniba.


Su hajiya sukace masha Allah, Allah yabamu hak'urin zama da juna.


Amina tace Ameen

Alhaji ne yatashi yace idan da wata matsalar kunyi magana da hajiya sannan yafita.

Murmushi hajiya tayi tace taso muje ingwada miki d'akin da zaki zauna domin kihuta kafin agama abinci kici.


Amina tace toh sannan tatashi tabi bayan hajiya

Fita sukayi daga parlourn tafiya suka d'anyi kad'an sannan ta bud'e wani d'aki daga cikin d'akunan  da ke wajen mamakine yak'ara kama Amina  ganin wani had'ed'd'en d'aki da suka shiga babbane sosai komai na d'akin red nd black colour ne tun daga kan kujeru, gado, dressing mirror, wardrobe kai har labulen d'akin su ma kalar ne sai makekiyar plasma da akasa a bango komai na d'akin fes agyare yake sai toilet daga gefe d'aya, masha Allah Amina tace ahankali, juyowa hajiya tayi takalleta tace nan shine d'akinki ga toilet chan, Amina tace hajiya da dai anchanza min wani wannan ai ya min girma,


Hajiya tace a'a Amina bai miki girmaba kar kiji komai, ga d'akin baba mairo nan kusa da naki kikwantar da hankalinki duk abinda kike buk'ata kimin magana kid'aukeni kamar uwa agareki,


Toh mummy nagode sosai Allah yabiya ku, Allah yasaka maku da gidan Aljannah

 

Hajiya tace Ameen, kije kikwantar da Ameerah tunda bacci take kema kihuta kafin agama Abinci


Toh mummy

Murmushi Hajiya tayi sannan taficce daga d'akin


Saman makeken gadon takwantar da Ameerah sannan tazo tana k'ara k'arema d'akin kallo komai na cikinsa ya burgeta,  sannan taje tashiga wanka toilet d'in ya burgeta sosai da karambani tasamu tayi using da komai na cikinsa,


Gaban dressing mirror taje cike yake da kayan shafa mai da powder kawai tashafa sannan lipstick sai tafeshe jikinta da perfume,

 

Wajen jakkar kayansu da aka shigo masu da ita tanufa, cikin wardrobe tajuye kayan sai alokacin talura da k'ok'ewar da kayansu sukayi domin tunda tabaro gidansu kala shiddanan su take sanyawa sai wata atamfa da hajiya maimuna tabata, kunya ce taji ta kamata, dakyar talalubo wad'anda suka d'anfi dama tasaka,

Saman gadon takoma tazauna tajawo alqur'ani tana karantawa kafin afito masallacin juma'a tayi sallah.


Bayan tagama sallah zaune take saman darduma Fatima ce tashigo d'akin dasallama, Amina tana murmushi ta amsa mata, Fatima tace oyoyoo sister sannu da zuwa ina murnar shigowarki cikin family d'inmu, mun ji labarinki wajen mummy kikwantar da hankalinki insha Allahu zaki ji dad'in zama damu, Ameerah bacci take?,

Murmushi Amina tayi tace eh, nagode sosai,

Bakomai kitaso muje muyi lunch su mummy suna jiranki, shuru Amina tayi domin ita ba zata iya zuwa chan ba tayi, Fatima ta lura da hakan tace dole fa kisaki jikinki nidai kitaso kar su mummy sujimu shuru, ba dan tasoba tatashi daman bata cire hijab d'intaba da tagama sallah sai tabi bayan fatima,


Da sallama suka shiga parlourn, dining area suka nufa cikin girmamawa Amina tak'ara gaishe da su daddy, suka amsa mata fuska a sake, mummy tace ina kika baro Ameerah, ahankali tace bacci takeyi,

kujera Fatima tajawo mata tace take a sit please, batayi musuba tazauna Fatima ma zama tayi tayi serving d'insu kowa cin abincinsa yake hankali kwance ammah banda Amina da duk tabi ta takura juya cokalin kawai take..........

Ammah banda Amina da duk ta bi ta takura juya cokalin kawai takeyi, mummy ce ta d'ago kai takalleta tace Amina kici abincin mana, kisaki jikinki ai munzama d'aya, inkuma ba zaki iya ci gabanmu ba toh kid'auka kitafi d'akinki maybe zaki fi sakin jikinki, inkuma abincin ne bai mikiba sai acanza miki wani.+

Murmushi Amina tayi tace mummy ci nakeyi, hararar wasa fatima tayi mata tace me kikeci? Nima fa ina lura da ke tun d'azun ba abinda kikeci, inma zakici kici mu nan ba a wasa da ciki dole aci abinci inba haka ba ayi ma mutum d'ure.

Dariya so mummy sukayi daddy yace kubarmin d'iyata taci abinci na ga alama so kuke ku tisota a gaba

Dariya suka k'arayi ammah banda salma da tunda suka zauna bata kula kowaba, fatima tace sorry dady andaina, kace taci abincin.

Daddy yace Amina kici abincinki, cikin jin kunya tace toh daddy.

Bayan sun gama cin abinci Amina d'akinta takoma babah mairo tashigo suka d'an ta6a hira.

Bayan tayi sallar la'asar zaman taji ya isheta d'auko Ameerah tayi tanufi d'akin babah mairo ganin ba ta ciki yasa tafito zata koma d'akinta kenan sai ga fatima ta fito daga parlour, ganinta yasa fatima tanufo wajenta dasauri tana oyoyooo my daughter ta tashi kenan daga baccin, kar6an Ameerah tayi da taketa wangale mata baki sama tad'agata tana yi mata wasa itakuma tana ta dariya.

Kallon Amina tayi tace gaskiya inason d'iyarnan taki daman kibani ita.
Murmushi tayi tace toh gaki ga ta indai Ameerah ce dakanki zaki maidota saboda rashin jinta da 6arna.
Eh bakomai ahaka nakeso
Toh shikenan
Kizo muje parlour muyi kallo dan Allah kisaki jikinki nan ai gidanku ne.

Murmushi Amina kawai tayi tabi bayanta domin itama ta gaji da zaman d'akin

Zama sukayi ganin ba kowa yasa tasaki jikinta suka fara kallo suna d'an ta6a hira, Salma ce tafito daga d'akinta tana kiran sis wai kina ina kizo kiga wani ab...

Ganinsu a zaune yasa tad'an 6ata fuska, fatima tace sis gani nan fa
Ta6e baki tayi tace na ganki remote tajawo takoma saman kujera tazauna tare da canza channel zuwa _mbc2_,
Fatima tace kefa salma kin iya wulak'anci kina ganin muna Kallo ammah shine harda canza mana, ko inda suke bata kallaba taci gaba da kallonta domin ita kwata-kwata batasan meyasaba ta tsani yarinyar nan tun a asibiti da taganta.

Ganin haka yasa Fatima tad'au Ameerah tare da rik'o hannun Amina tace zo muje d'akina.
Murmushi Amina tayi tace muzauna nan
A'a mutafi chan muyi hira ni fa ban faye son horo film ba.
Wucewa sukayi suka shiga bedroom d'in da yake parlourn Amina saida tarud'e saboda tsaruwarsa kallon ko'ina take, murmushi fatima tayi tare da rik'o hannunta suka nufi saman kujerar da take d'akin suka zauna,
Fatima tana ta wasa da Ameerah suna dariya itadai Amina kallonsu kawai take tana murnushi, d'ago kai fatima tayi takalleta tace wannan d'iyan taki ammah ba dake take kamaba murnushi tayi tace me kika gani? Hmm Allah ta fiki kyau ko da kema kina da kyau ammah ba irin na my daughter ba,
ke dai kawai son kai zakiyi ammah wannan mummunar d'iyar zakice ta fi ni kyau,
Dariya fatima tayi tace haba jealous dai Kikeyi ammah ko k'afarta baki kamoba, kibari tak'ara girma zakiga yadda kyanta zai k'ara fitowa ni ai sai president zan ba ita,
Amina tace ko ba president ba
Dariya sukasa gaba d'ayansu
Hira sukayi sosai sai gab da magrib suka tashi,

STORY CONTINUES BELOW
d'akinta takoma d'akinta tayi sallah saida tagama addu'o'inta sannan tafito tanufi d'akin babah mairo da sallama tashiga ba laifi d'akin babah mairo yana da kyau ammah baikai nataba.

Baba mairo tace oyoyoo marabanku ke da kishiyata kike tafe, murmushi Amina tayi tace aikam dae babah mairo, waje tasamu tazauna tace d'azun saida nashigo naga bakinan, ayyah lokacin na shiga kitchen kuma da nagama na zo d'akinki lokacin baki ciki,
Babah ina wajen fatima ne, Allah sarki d'iyar albarka ai fatima akwai kirki.
Hakane babah ammah shine baki kirani nazo natayaki aiki ba?
Haba Amina keda kika dawo daga asibiti kike buk'atar kihuta shine zakiyi aiki, a'a gaskiya kibarshi kawai, babah na fa warke, toh kibari kik'ara warkewa.
Amina dan Allah kizauna da kowa lafiya ko da nasan ba zakiyi rigima ba domin tun a asibiti na karanci halinki bakida hayaniya komai sukace kibisu sau da k'afa
Toh babah insha Allahu nagode sosai.

Kiran sallar isha'ine yasa suka tashi.

Zaune take d'akinta ta gama ba Ameerah custard ta sha tana lalla6ata tayi bacci, Salma ce tashigo sallama tayi ciki-ciki ta6e baki tayi tace kizo su mummy suna kiranki a parlour, Toh Amina tace

Bayan ta kwantar da Ameerah tatashi tanufi parlourn da sallama tashiga ta taddasu Zaune suna hira tsugunnawa tayi ta gaishesu cikin fara'a suka amsa, mummy tace let us go d dinner ix ready.
Dining area suka nufa kowa yazauna Amina ta saki jikinta ta ci abinci ba kamar d'azunba barema da taga kowa hidimarsa yake ba mai kallonta.

Bayan sun gama ita da su Fatima suka tattare kwanonin suka kai kitchen da suka dawo mummy tace kuzo kuzauna muyi hira sannan kowa yaje yakwanta,
Hira sukeyi ammah banda Amina daga eh sai a'ah kawai take cewa.
Sai wajen past 9 sannan mummy tace kutashi kutafi kukwanta,
Tashi sukayi sukaimata sai dasafe sannan kowa yanufi d'akinsa.
Ko da takoma wanka tayi sannan tayi shirin bacci takwanta bisa lallausan gadonta.

Agurguje bayan kwana biyu Amina ta saki jikinta sosai tana zama tayi hira dasu ammah idan miskilancinta yataso sai tayi shuru, sun saba da fatima sosai ko da fatima za ta d'an girme mata ammah salma indai ba sa ta akayi takira Amina ba toh gaisuwa kawai take had'asu shima sai idan Amina ta gaisheta.

Yau kasancewar su Fatima sun tafi makaranta duk sai taji gidan ba dad'i gashi akwai masu gyaran gida komai yi masu ake babu abinda sukeyi.

Goya Ameerah tayi tanufi kitchen babah mairo tana blending din kayan miya tace  Amina kina buk'atar wani abune?
A'a babah wlh na gaji da zaman ne duk ba dad'i shine nace bari inzo intayaki aiki,
A'a Amina kibarshi kawai,
Babah dan Allah kibarni inyi,
kallon kajin da babah tafiddo daga freezer tayi tace babah wad'annan fa
Babah mairo tace pepper zanyi dasu
Toh bari inyi
A'a kibarshi
Baba kodai kina ganin kar inyi ba dad'i ne?
Hmm Amina nidai banceba, saida Amina tamatsa sannan tasamu baba mairo tabata tayi pepper d'in kuma tasa hannu sukayi girkin tare jalop rice ce sai coslow sukeyi k'amshin girki duk yacika gidan.

Suna cikin juyewa mummy tashigo tace babah yau me aka dafa mana duk k'amshi ya gauraye gida, a'ah Amina har dake ake girkin?
Murmushi tayi tace eh mummy zaman ne naji ya isheni shine nace bari inshigo intaya babah mairo aiki,

Mummy tayi murmushi tace mutanenki sun tafi school sun barki ko? Kema ai ya kamata asa ki bari Alhaji yadawo sai muyi maganar,

Amina ta ji dad'i sosai nan tayi ta ma mummy godia, mummy tace bakomai Amina ai duk d'ayane ke da su fatima,
Yauwa idan sun dawo zan aikeku gidan khairta, Amina cikin jin dad'i tace toh mummy.

Yauwa daman d'akinki zanje kiranki tafo muje parlour bak'uwa nayi,

Bin bayan mummy tayi sukaje parlour tagaishe da bak'uwar, mummy tace yauwa hajiya lami wannan ce.

Murmushi hajiya lami tayi tace toh hajiya kallon Amina tayi tace zo kiduba wanda yayi miki, Amina dai bata gane me ake nufiba tanufi wajen wadda aka kira da hajiya lami, ghanamosgo d'in da yake baganta tabud'e duk kayane tace kiza6a,

Amina kallon mummy tayi, Murmushi mummy tayi tace kiza6i kayan da kikeso.

Kayan ciki matar tafara fiddowa, Amina kasa za6a tayi, matar tatayata taza6i kala ashirin har da dogayen riguna, Aunata matar tayi sannan tatafi da wad'anda za a d'inko tabarmata dogayen riguna kala biyar,

Amina godia tayi tama Mummy harda kukanta saboda murna, mummy ce ta lallasheta.
Wajen k'arfe biyu su Fatima suka dawo daga makaranta, lokacin su Amina sun gama jera kulolin abinci a dining, bayan sun shirya suka fito suka nufi dining domin aci abinci,
Amina dakanta tayi serving kowa, tun da tabud'e kular k'amshi duk yacika masu hanci,

ci kawai suke salma tace mummy gaskiya abincin nan ya min dad'i sosai musamman ma pepper d'in nan Fatima tace uhm nima dai wlh na ji dad'insa sosai.

Murmushi mummy tayi tace nima dai ya min dad'i kunga wacce tayi shi nan, Fatima tace wow ashe daman kin iya girki haka? gaskiya sis abincinki zamu dawo ci ko munyi k'iba, dariya sukayi gaba d'ayansu ammah banda salma da tunda taji wanda yayi girkin tayi shuru ci kawai take domin ba damar tace ta k'oshi saboda ya mata dad'i.

Mummy tace baku isa kumaida min d'iya mai girkinku ba ku ma kuyi zuciya kudinga mai dad'i kamar nata,  ni kuyi sauri kugama in aikeku gidan khairat sukace toh mummy.

Bayan sungama kowa yanufi d'akinsa domin yashirya,
Wanka Amina tak'ara yi tayima Ameerah,
Simple makeup tayi daman ita ba gwanar kwalliya bace, Cikin dogayen rigunan da mummy tasiya mata tad'auko wata red mai ratsin bak'i tasanya tayi rolling da bak'in gyale tayi rolling  _(ko ni da naganta saida nace masha Allah saboda wani irin kyau da tayi kamar my sis zainab A😜 dandai Amina zata d'arata haske da tsawo..lol)_ feshe jikinta tayi da turaruka, sannan tashirya Ameerah tayi sannan tafito tanufi parlour,

Daidai lokacin fatima tafito daga d'akinta ta ci kwalliya cikin material blue colour tayafa gyale fari d'an k'arami ta yi gwanin kyau, tana kalllon Amina tace wow masha Allah sis kinganki kuwa u luk so cute wlh sai kikafito a 'yanmata shar kamar baki ta6a aureba kai gaskiya kinyi kyau,
Murmushi Amina tayi tace nagode, kar6ar Ameerah tayi tace my daughter ta fiki kyau ammah sannan tace yauwa ina zuwa, d'akinta takoma batafi minti ukku ba tafito hannunta rik'e da takalma bak'ak'e hills, wajen Amina tanufo tace kisaka wad'annan muga idan za suyi miki tunda naga kema bakida k'afa sosai, kar6a tayi tagwada aikam sukayi mata cif-cif fatima tace yauwa sai kisaka su,
Salma ce tafito daga d'akinta ta ci kwalliya sosai material ne maroon colour tasanya itama tad'auko d'an k'aramin gyale fari tayafa tafiya take kamar bata son taka k'asa har ta iso wajensu ita kanta da takalli Amina saida tayi mamakin kyaun da tayi cikin ranta tace ashe haka yarinyar nan takeda kyau, fatima tace sis kinyi kyau murmushi salma tayi tace ku ma haka sis.

Mummy ce take safkowa daga saman step fuskarta d'auke da murmushi tace kai 'yanmatana sunsha kyau kamar bakuba, murmurshi sukayi, tace masha Allah Amina kinganki kuwa kamar wata balarabiya, Dariya Amina tayi tace mummy bankai nan ba ai ankashe larabawa idan aka had'asu dani da dai su fatima kikace.

Mummy tace a'a kema ai da kyanki, harararta fatima tayi tace wlh kinfi ni kyau haske kawai nafiki,

Xaro ido tayi tace a hakan? Wlh kin cuci kanki.

Dariya mummy tayi tace ya isa haka kuzo kutafi ko kundawo dawuri wata bak'ar leda tamik'o masu tace gatanan kukai mata zata baku sak'o kukawo min. Sukace toh mom.......
Idi driver sukayi ma magana domin yakaisu, tunda suka kama hanya fatima da salma ne suketa hira itadai Amina kallon taka kawai take tana kalle-kalle saidai idan fatima ta sakota cikin maganar ne take d'an tankawa har suka iso horn idi driver yayi ganin number d'in motar yasa dasauri gate man yazo yabud'e gate d'in gidan wajen parking space suka nufa,

Cikin gidan suka shiga da sallama Aunty khairt da take kitchen ta amsa musu lek'owa tayi ta taga tare da cewa oyoyoo 'ya'yan mummy sannunku da zuwa, sukace yauwa Aunty khairat, kushiga ciki ganinan zuwa, suna shiga Jawahir ce zaune tana wasa da teddy d'inta ganinsu yasa tatashi dagudu tanufi wajen Amina tana oyoyoo Aunty d'aukarta Amina tayi tace oyoyoo my daughter ashe baki mance da ni ba, dariya fatima tayi tace mu kin mance damu kuma ban baki chocolates tunda bakimana oyoyoo ba,

6ata fuska jawahir tayi kamar zatayi kuka tace Aunty ina shan chocolate d'in zan miki oyoyoo, hannu ta mik'a ma fatima ta d'auketa tace yauwa ashe kinason shan chocolate, kumatunta salma taja tace muga bakin shan chocolate d'in, dasauri jawahir ta hangame baki tace gashi Aunty,

Dariya suka yi gaba d'ayansu sannan salma tace yauwa ashe zakisha chocolate.

Daidai lokacin Aunty khairat tashigo d'akin hannunta rik'e da tire lemune da swan water ta aje a gabansu sannan tasamu waje tazauna,

Gaba d'ayansu suka gaisheta ta amsa musu cikin fara'a, tace Amina ya k'arfin jikin? Aunty Jiki Alhmdllh ya warware, murmushi Aunty khairat tayi tace saisa naga kinyi wani kyau ba kamar a asibiti ba ciwo yamaidaki wata kala, dariya sukayi gaba d'ayansu,

kar6ar Ameerah tayi daga hannun Amina tace masha Allah my daughter ta girma, dasauri jawahir takoma kusa da mummynta tace mummy sabon baby kika siyo mana? Aunty khairat tace eh kina so ko? Mummy ina sonta babyn tana da kyau subarmana ita indinga wasa da ita, dariya Amina tayi tace toh munbar muku, murna jawahir takamayi harda tsallenta sunyi sabuwar baby, Aunty khairat tace toh je kid'auko hijab d'inki tana saman bedside na aje kibi ahankali kar kitashe min da d'ana kizo kije bala yakaiki islamiyya idan kindawo sai kigoya ta, tana murna tace toh mummy dagudu tanufi d'akin tad'auko hijab d'inta taficce.

Dariya sukayi gaba d'ayansu Amina tace jawahir kenan, Aunty khairta tace inba haka nayi mataba toh ganinku zaisa tace ba zataje islamiyya ba,

Aunty khairat tace gaskiya masha Allah Ameerah ta k'ara girma wai ynz watanta nawa? Amina cikin jin kunya tace na cikin goma take, dariya fatima tayi tace lallai Amina kinzama uwar fulani kedai komai sai kinji mashi kunya wlh kunyarki ta yi yawa ya kamata kirage ta, dariya sukasa gaba d'ayansu ammah banda Amina.
Salma ce tamik'a ma Aunty khairt ledar da take hannunta tace gashi mummy tace mukawo miki, kar6a Aunty khairat tayi taduba tace yauwa ashe matar ta kawo sak'on, aikam na ji dad'i wlh nagode, Fatima tace yauwa ta ce zaki bayar da sak'o akaimata,
Eh inkuntashi tafiya zan baku yananan daman na aje.

Hira sukasha sosai dan yau Amina ta yi mamakin yadda salma tasake suna hira da dariya har suna tsokanar Amina.

Tare da Aunty khairat suka shiga kitchen sukayi girkin dare,

Yau Amina ta ji dad'i sosai domin ko bakomai ta fita ta ga gari, ko da sukayi sallar magrib abinci suka zubo suka baje a k'asa sukaci a tare cikin jin dad'i,

Bayan sungama kowa yajawo mayafinsa sukace zasu tafi, 6ata rai Aunty khairat tayi tace maimakon ku kwana a nan gobe sai amaidaku?

Salma tace wlh Aunty khairat gobe akwai school, fatima tayi karaf tace kuma mummy kinsan fad'a zatayi mana saidai wani lokacin in munzo sai mukwana,

Aunty khairat tace Allah yasa dagaske, tashi tayi tace ina zuwa tanufi bedroom d'inta bata dad'eba tafito d'auke da ledoji tamik'a ma fatima da salma kowa d'aya tace ga kayan kwalliya, sai tamik'a ma fatima wata leda tace ga sak'on mummy kukai mata,

Wata jakkar kaya 'yar madaidaiciya tamik'a ma Amina tace ga wannan kema Amina, kar6a Amina tayi tana godia

Su duka Godiya sukayi mata sosai sannan suka fito tasa driver d'inta yamaidasu gida.

Ko da suka isa gida mummy tana parlour tana kallo dasallama suka shiga, cikin fara'a ta amsa masu,

Dukansu suka zube saman kujera, sukace mummy sannu da gida.
Murmushi tayi tace yauwa 'yan albarka sannunku da dawowa shine kukayi zamanku kuka barni da kad'aici kun kyauta,

Gaba d'ayansu sukace sowie mum wlh Aunty khairat ce ta tsaida mu ammah insha Allahu ba zamu k'araba

Cikin wasa mummy tace daman ai kun saba,
Sak'onta suka bata, kowa yagwada mata abunda Aunty khairat tabasu su Fatima kayan kwalliyane,
Amina kayane kala ukku sai na yara kala goma tazubo ma Ameerah sai turaruka kala ukku cikin jakkar,

Mummy ta ji dad'in kyautan da Aunty khairat tayi ma su Amina, tace kungode kowa yad'auki kayansa kutafi d'aki gashichan ana tada sallar isha'i...
Ko da Amina taje d'akinta Kwantar da Ameerah tayi da tun a mota tayi bacci, k'ara duba kayan tayi atamfa biyu sai less d'aya d'inkakkune sunyi kyau sosai, sannan taduba kayan da akaba Ameera Murmushin jin dad'i tayi, chan kuma tayi wani tunanin sai ga hawaye suna kwaranya daga idonta,
Gogewa tayi,
Tafito tanufi d'akin baba mairo da take kwance dasallama tashiga dakyar baba mairo ta amsa mata saboda jin yadda kanta yake ciwo, kallonta Amina tayi tace babah bakida lafiya ne? Murmushi tayi tace wlh kaina yake ciwo,
Subhanallah sannu babah, kinsha magani?
Eh nasha
Toh Allah yasauk'e
Ameen nagode Amina
Bakomai babah sai dasafe Allah yabaki lfy
Ameen

'Dakinta takoma, shirin shiga wanka tayi domin wankan dare ya zame mata jiki, bayan ta fito ta shirya, saman gadon tafad'a takwanta tare dayi masu addu'a itada d'iyarta duniyar tunani tafad'a murmushi take tayi da ta tuno irin rayuwar da sukayi da abbanta abun sonta, da ta tuno da ummah kuma sai taja tsoki domin gani take duk itace silar neman tona mata asiri,

Guy d'intane yafad'o mata a rai lumshe idonta tayi tana murmushi tace inama kadawo zuwa gareni wlh ina sonka kaine rayuwata da kai kad'ai zan iya rayuwa NI DA ZUCIYATA mun amince da kai ammah na san ka min nisa ba zaka ta6a sona ba yanzu haka ka mance da ni a rayuwarka ina ma zaka shiryu kadawo gareni muyi zaman aure ko da ace bakada komai nidai ina sonka miyasa kullum tunaninka yake hanani aiwatar da komai? Meyasa kashiga rayuwata lokaci guda? fashewa tayi da kuka jin yadda zuciyarta take bugawa  ita kanta tana tausaya ma kanta da tayarda tafad'a tarkon son Wanda baima san tana yi ba, ko da ta san K'ADDARA CE tahad'a ta dashi cikin kuka tace kuma ta dalilin K'ADDARA sonka yashiga raina yake d'awainiya dani, a kullum addu'ata shiryuwarka nake buk'ata.

Saida tayi kuka mai isarta sannan tatashi taje tawanke fuskanta tadawo takwanta tacigaba da tasbihi domin samun sauk'in zuciyarta ahankali bacci yayi awon gaba da ita.

Tun da tagama sallar asuba bata koma bacci ba saida taga gari ya fara wayewa sannan tatashi tashiga kitchen doya tafera dafata tayi da tadafu yam ball tayi masu sannan tahad'a masu kunun gyad'a mai dad'i
Parlour taje ta jera su saman dining table, sannan takoma kitchen tad'auko na babah mairo taje takaimata ganin tana bacci yasa ta aje mata sannan tafito tanufi d'akinta saman gado takoma takwanta..........


Post a Comment for "K'ADDARA CE CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...