Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

K'ADDARA CE CHAPTER 7

K'ADDARA CE CHAPTER 7

- - Post a Comment

 K'ADDARA CE CHAPTER 7


Bayan sungama wayar Hajiya zagaye d'akin tashiga yi tana tunanin mafita hannu tasa cikin baki tace kai gaskiya ba zanyi wasa da dama ta ba inrasa wad'annan mak'udan kud'in dubu d'ari biyu ai ba wasaba nasamesu ai na fara warkewa.


Toh wai ma wannan yarinyar ko zata amince?  Murmushi tayi tace idan taji mak'udan kud'i ai dole ta amince domin kud'i sune abokan rayuwa babu mai gudun dukiya sai marar rabo dole insameta muyi magana domin tafiyartata ita zata fiye mana, ga arzik'i har gida wa zai k'i.

Account number d'inta tatura mashi kamar yadda yayi mata alkawali zai fara turo mata tafara ta6awa sai gashi ya turo mata 50,000 d'in.


Dadaddare bayan sungama komai Amina tana d'akinta ta samu ta lalla6a Ameerah da tasha rigima ta yi bacci, 

Hajiya tashigo d'akin da sallama bakinta a washe,

Amsa mata tayi tana mamakin zuwan hajiya d'akinta a wannan lokacin.

Hajiya batadamu da mamakin da taganiba a fuskar Amina tasamu gefen katifa tazauna tana fuskantar Amina tace kina mamakin zuwana ko?  Toh alkhairi ne yake tafe da ni magana nakeso muyi da ke.

Tashi Amina tayi zaune daga kwancen da take tace ina saurarenki hajiya.

Gyara zama hajiya tayi tace yauwa daman akan maganar Alh faruk ne ya ce yanaso ayi miki visa kije chan dubai kiza6o kayan da kikeso na aurenku domin hakan zai fi kinga kema za ki bud'e idonki idan kikaje kema, yanzu ya kike ganin za ayi?

Amina kallon hajiya da tunda ta fara maganar take cikin mamaki tace hajiya ban d'auka harda ke ba cikin wad'anda sukeso su cutar da rayuwata ba kin fa san Alh faruk ba mutumin kirki bane kawai yanason  yacutar da rayuwatane  yabiya buk'atarsa da ni,


Hajiya kar kud'i su rud'eki idanuwanki surufe ki aikata abinda bai daceba ya kamata kiyi tunani kisan hanyar nan da kika biyo ba mai 6ullewa bace agareki.

Komawa Amina tayi takwanta tare da juwa ma hajiya baya duk takaici ya cikata.

Jikin hajiya duk ya yi sanyi da maganganun da Amina tafad'a mata dakyar tatashi ba tare da tayi ma Amina magana ba taficce daga d'akin.

Amina tana jin fitarta tatashi taje tarufe d'akinta takoma takwanta tsoki taja tace wai miyasa kud'i suke rud'ar mutane?  Meyasa hajiya takeson saka hannunta wajen ganin an6ata min rayuwa?  Me natsare masu suke jifana da Sharri, ya ubangiji kakawo min d'auki wannan wace kalar K'ADDARA CE? Rayuwar yanzu kowa nashi yasani bai damu da halin da d'an wani zai shigaba.

Ta dad'e tana juyi sannan daga baya bacci yad'auketa.

Tun daga ranar magana ba ta had'ata da hajiya gaisuwa ce kawai take shiga tsakaninsu .

STORY CONTINUES BELOW

Hajiya bak'in ciki ya cikata ganin ga samu ga rashi duk ita kad'ai, duk sai taji tana jin haushin Amina saboda duk itace silar rashin samun kud'inta.

Saboda kar tatona mata asiri saisa takyaleta domin batason mutuncinta yazube a idon mutane.

Ko da takira Alh faruk tafad'a mashi yadda sukayi da ita bai ji dad'in rashin amincewarta ba ammah dole yahak'ura yace ma hajiya bakomai idan nadawo zamuyi magana,  kar kidamu saura dama d'aya tarage idan nadawo kika taimaka min zan baki kud'in ba wai na fasa bane,

Washe baki hajiya tayi tace toh Alhaji Allah yadawo mana da kai lafiya. Tun daga ranar basu k'ara wayaba.

Alh faruk ya ji haushi sosai na rashin amincewar Amina ammah ya ci alwashi idan yadawo da tsiya ma sai ta amince mashi domin shidai yana sha'awarta sosai.


Bayan wata d'aya Alh faruk ne zaune a d'akin hajiya maimuna saboda murna hajiya tarasa inda zata sa kanta abinci mai rai da lafiya aka kawo mashi.

Kallon hajiya yayi yace am hajiya daman taimako d'aya nakeso kiyi min akan Amina, ni dai tun ranar da nafara ganinta sha'awarta take d'awainiya da ni,  dan haka nakeso kitaimaka kishawo min kanta.

Zaro ido hajiya tayi tace Alhaji gaskiya kayi hak'uri wlh yarinyar ce ta cika taurin kai dayawa,  kuma fa sai inga daman aurenta kayi ai da zai fi.

No banida buk'atar hakan,

Hajiya idan kika shawo min kanta zan baki cheque na 500,000.

Dafe k'irji hajiya tayi tace dagaske kake Alhaji?

Eh mana ga wannan kifara ta6awa kafin komai yazama normal sai in ida cika miki.

Cheque d'in 100,000 yarubuta yamik'a mata,

Zaro ido tayi jiki yana kyarma tace nagode Alhaji na maka alkawali zan shawo maka kanta ko ta halin yayane, saboda rud'ewa hajiya har k'asa taduk'a tana ma Alhaji godiya.

Kallonta yayi yace tashi hajiya ya isa haka.

Toh toh Alhaji bari inje inkira maka ita kugaisa,

Jiki yana 6ari hajiya tatashi tanufi d'akin Amina.

Dasallama tashiga lokacin Amina tana zaune tana linke kayansu da ta wanke, 

ta yi mamakin ganin hajiya domin rabonta da tashigo d'akinta tsawon wata d'aya kenan tunda wannan abun yafaru a tsakaninsu,

Washe baki hajiya tayi tace linki kike d'iyar albarka?

Ba tare da Amina ta k'ara kallonta ba tace eh hajiya.

Ina d'iyar taki sarkin k'iriniya naga tunda tafara rarrafe ba ta zama yawonta kawai take.

Murmushi Amina tayi tace tana wajen baba salame tunda taga ta sanya hijab zata koma restaurant shine talik'e mata saida tatafi da ita.

Toh ikon Allah ai hakan shi yafi kema ai kindinga hutawa kokuma naga batada kyuwa tana yadda da kowa,

Yauwa Amina kije ga Alh faruk chan ya zo kugaisa ashe sai jiya yadawo daga dubai d'in naga ma har tsaraba yazo miki da ita ai bawan Allan nan yana hidima da mu.

Amina ko inda take bata kallaba tacigaba da linkinta kamar bataji abinda hajiya take cewa ba.

Saida hajiya tace Amina da ke fa nake magana,.

Hajiya gaskiya kiyi hak'uri ni fa ba sonsa nakeba  kuma fa ba mutumin kirki bane ba ni yakeso ba kawai jikina yakeso.

Harararta hajiya tayi  tace ke wlh wata irin kud'd'ace ana ce miki ga gabas kina ke yamma zakiyi, wa yace miki ba mutumin kirki bane? 

Ke yanzu ai sha'ani kawai akeyi ki auresa kihuta babu ruwanki da halayyarsa, kowa ai lalube yakeyi a cikin ibadarsa.

Ammah ai hajiya Alh faruk d'an iska ne.

Keh!  Ya isa haka dan kinga ina lalla6aki shine zaki kawo min k'abali da ba'adi?  Toh wlh baki isaba sai kinje.

Amina tana fushi tajawo hijab tasanya, hajiya tace ko 'yar powder babu bare jambaki.

Ko kallonta batayiba taficce daga d'akin tanufi d'akin hajiya ranta a 6ace.

Sallama tayi fuska a d'aure tace lafiya kake kirana?

Murmushi yayi yace kizauna mana sai muyi magana.

Ta6e baki tayi tace bana buk'atar hakan,  Alhaji kafita daga harka ta, ni fa ba sonka nake ba wai miyasa kakeson shiga rayuwata ne?

Kaima nasan ba sona kakeba kawai jikina kakeso  kuma insha Allahu ba zaka samu daga gare niba.

Tashi Alhaji yayi daga inda yake zaune  yanufi inda take sai da yazo daf da ita yazama suna jin numfashin juna

sannan yace Amina tunda nake ban ta6a neman wani abuba nasara a rayuwata  kisa a ranki kamar na sameki ne kikwantar da hankalinki muyi komai cikin ruwan sanyi idan har kika bani had'in kai zan baki one million naira.

Dariyar rainin wayau Amina tayi tace karik'e kud'inka bani buk'ata Allah yasa duka dukiyarka zaka tattaro ka bani toh banso domin jikina ya fi k'arfinka malam ya kamata kakama girmanka.

Amina dole fa ki amince da ni wai ke miyasa kike abu kamar ba 'yar hannu ba? Ko kinso ko kink'i dole kikoma karuwata kuma babu Wanda ya isa yashiga tsakanina da ke a garin nan.

Zaro ido Amina tayi gabanta yafad'i ammah tadake tanuna bata tsorata ba tace Allah saidai kayi abinda zakayi ammah baka isaba,

Wlh da inzama karuwarka na k'wammace inmutu a talauci.

Ke babu fa wanda ya isa yahanani aikata abunda nayi niyya

Hayaniyarsu ce hajiya da take tsakar gida tajuyo da sauri tanufo d'akin tashigo ganinsu a tsaye cirko-cirko kowa rai a 6ace yasa tace wai me yake faruwa ne? .......

Wai me ke faruwa ne? Amina kina da hankali kuwa?

Amina a wulak'ance tajuyo takalli hajiya tace tunda banda kwad'ayi dole inkasance marar hankali wlh hajiya kuji tsoron Allah meyasa kukeso kuga kun 6ata min rayuwa. 

Kar kimance talauci ba hauka bane,  kwad'ayin abun duniya ne kawai yake d'ibanku kukeso kumance da lahira.

Keh Amina dakata kar kice zaki mana wa'azi tun kafin ahaifeki aka karantar da mu mukasan mai kyau da marar kyau, dama da haggu kuma talauci ai abun k'i ne. Kuma Alh faruk ne dole ki amince mashi.

Alh faruk yace hajiya kibita ahankali ba na buk'atar yardatta, komai nasa a gaba dole in sameshi babu ja da baya dan haka kusaurareni duk lokacin da nadawo dole ta amince da buk'ata ta,

domin zan baki mamaki Amina zan nuna miki ni d'an baiwane mai sa'a wannan Alkawali ne nayi ma kaina.

Wucewa yayi ransa a 6ace yaficce daga d'akin ba tare da yaji ta bakinsu ba.

Hajiya takalleta tawurga mata harara tace wlh dole ki amince mashi na san bak'in cikin dubu d'ari biyar d'in da yace za yabani kikeyi,

Kawai sau d'aya fa zakiyi daga baya fa sai kinemi gafarar ubangiji.

Ran Amina a 6ace tace ke hajiya bari kiji baki fa isaba kisani insa6ama ubangijina ba,

_Allah zamuyi ma wayau ne? Shi fa ya haliccemu yana sane da abinda muke aikatawa,  akan me ina sane insa6a mashi, kuma zina fa kukeso kusani inyi abunda saboda girman zunubin aikata ta al'arshin Allah har girgiza yake Allah ma dakansa ya ce kar mu kusanci zina_


_kar kimance Manzon Allah S.A.W yace ya ku mazinata kuji tsoron zina domin tanada abubuwa guda shidda,  ukku a duniya ukku a lahira. A duniya 1-mazinaci zai kasance bashida k'warjini 2-zai dauwama cikin talauci 3-kwanakinsa suna raguwa.  Ukku a lahira kuma 1-zai had'u da fushin Allah 2-Allah zai tsaurara mai hisabi 3-Allah zai azabtar da shi_


Girgiza kai Amina tayi idanuwanta suka cika da k'wallah sannan tace Hajita meyasa kike tunanin saboda son abun duniya zan aikata ta alhali na san illarta sannan ince zanyi wayau innemi gafarar Allah, Allah fa yana sane da duk abunda muke aikatawa, toh bari kiji hajiya ni ba haka nakeba kuma baku isa kusani doleba,

Duk abunku Allah ya fi ku domin Allah yana tare da mai gaskiya.

Hajiya ta harzuk'a da maganganunta ranta yak'ara 6aci cikin d'aga murya tace Ke! Ya isa haka babu yadda za ayi kizo gidana cin arzik'i kuma kinemi fad'amin maganar banza wlh indai kinason zama da ni dole kibi umurni na.

Ba tare da tsoro ko fargaba ba Amina takalli hajiya tsanarta k'arara tabayyana a fuskarta tace hajiya baki fa isaba kisani insa6ama ubangijina ba, inaso kisani gidan da kike tak'ama da shi zan iya bar miki abunki inbama k'addara ba miye zai had'ani da ke.

STORY CONTINUES BELOW

Ran hajiya in yayi dubu toh ya 6aci tace ke ni kikema rashin kunya?

Harararta Amina tayi tace eh d'in anyi miki kiyi yadda zakiyi.

Hannu hajiya tad'aga zata mareta, cikin zafin nama Amina tarik'e hannun tace kar ki kuskura hannunki yata6a fuskata idan har kika bari yata6a toh zamu kwashi 'yan kallo ni da ke dan haka ki kiyaye.


Tsaki Amina taja sannan tafice daga d'akin tabar hajiya a tsaye tana mamaki tace ashe daman yarinyar nan tana da baki haka?  Na d'auka irin wad'annan marassa maganar basuda wayau haka tab lallai dole ind'au tsatstsauran mataki akan yarinyarnan.


Amina tana fita d'akinta tawuce kukan da take dannewa ne yaci k'arfinta saida tayi mai isar ta.


maganganun Alh faruk ne suka fara fad'o mata a rai tabbas a yadda yayi maganar babu wasa a ciki,  dasauri tanufi wajen kayanta tafara had'awa tare da cewa indai inason kaina da arzik'i dole inbar garin nan inyi nesa da mutanen nan intsira da mutunci na domin shine kawai mafita agareni,

Cikin dubara tad'auki kayan talalla6a tanufi waje ba tare da kowa ya gantaba dan kar wani yafad'a ma hajiya.


Waje tasamu ta aje kayan sannan tanufi restaurant d'in, wajensu baba salame tanufa domin kar6ar Ameerah.

Baba salame takalleta tace lafiya Amina naganki haka?

Murmushi Amina tayi tace lafiya lou baba salame kawai dai kaina ne yake min ciwo.


Ke Amina Ke dai ragguwa ce ciwon kan kikema kuka keda har haihu kinyi.

Murmushi Amina tayi takalli Ameera da take hannun baba salame sai wasa take tace sannu baba kina ta fama da wannan marar jin ku?

Yoh ai daman ynz nake shirin shigowa inkawo miki ita kibata tasha yarinyar tana da hak'uri sosai tun d'azu fa ammah ko kuka batayiba.

Murmushi Amina tayi k'walla tacika mata ido takar6i Ameerah tace sannu baba salame angode sosai Allah yabiyaki adai yafe.

Hararar wasa baba salame tayi mata tace sai kace dai wadda zata mutu ko zatayi wata tafiya zakice wani ayafe.

Dariya Amina tayi tagoya Ameerah sannan taficce daga restaurant d'in wajen kayanta takoma tad'auka dasauri tayi gaba tanufi bakin titi,


Mai napep tasamu tace yakaita tasha


Hajiya wace tashar ciki?

Tsayawa tayi tana tunanin wane gari zataje domin yau dole tabar garinnan saboda ta tsorata da Alh faruk barema yadda yaci alwashi a kanta.


Muryar mai napep d'in taji ya k'ara tambayarta tashar da zasuje.

Bakinta ne taji ya kubce ta yi su6ul da baka ta ce ta kaduna.


Tun da suka isa mota tasamu tashiga hankalinta a tashe domin har a lokacin a tsorace take dan kar subiyota, saida suka dad'e sannan motor tacika.


Tafiya suke ammah kwata-kwata babu walwala a tare da ita tunani kawai take idan taje garin wace kalar rayuwa zatayi kuma a ina zatayi rayuwar tunda garin batada kowa da ma dai abbanta yana da rai da duk hakan bata faru da itaba,  kwallar idonta tagoge tare da jawo Ameerah da taketa wasa tana shirin yi ma wasu 6arna.

Sai wajen gab da magrib suka iso garin kaduna lokacin ta galabaita sosai ga yunwa ga k'ishirwa domin rabonta da abinci tun breakfast d'in safe da tayi.

Tun da aka safkesu masu hawa abun hawa suna hawa masu tafiya k'asa suka kama hanyarsu,  itama dai k'asan take tafiya domin aganinta ko ta ce tahau abun hawa batasan inda zata nufaba tunda bata ta6a zuwa garin ba.

Tafiya kawai take itama kanta batasan inda take jefa k'afarta ba domin a galabaice take ga gari ya yi duhu hanyar mutane d'ai-d'ayane suke giftawa  duk tsoro da fargaba suka cikata gashi tunda tafara tafiyar batacikaro da ko mai ruwa ba bare tajik'a mak'oshinta.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da tayi tafiya mai nisa sannan tahango wani masallaci daga can tsallaken titi,


Murna ce takamata domin lokacin har ta fara ganin bibiyu ta k'agara tasha ruwan domin tajik'a mak'oshinta dasauri tak'ara matsawa sannan cikin tanufi titin zata tsallaka.


Motace tatafo dagudu kasancewar mai motar sauri yake bata lura da tafowar motar ba hankalinta yana wajen masallacin sai da takai tsakiyar titin, duk yadda mai motar yaso yataka burki ammah ina sai da yabugeta ji kake k'iiiit,  zubewa tayi a tsakiyar titin tafad'i a gefe d'aya kayanta sukayi gefensu suma.

Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un kawai nacikin motor suke cewa.

Mutumin da yake zaune a bayan motar dasauri yabud'e murfin motor yafito yanufi wajen da take a kwance,  ganin hakan yasa driver d'in shima yafito.

Jaririyar da take bayanta ce tafara kuka dasauri Alhaji yad'auko yarinyar yakalli Malam idi yace kamata musaka a mota mukaita asibiti.

Dasauri suka sakata suka d'auko jakkarta itama sannan suka nufi private hospital da take a kusa mai tsada.

Da sauri aka kar6eta aka nufi emergency da ita cikin gaugawa domin ceto rayuwarta.


Yarinyar doctor ya amsa daga wajen daddy yadubata sannan yace babu wata matsala a tare da ita sai ta yunwa asiyo madarar jarirai adama abata tasha.

Alhaji yadubi Malam idi yace kaje kasiyo madarar jarirai abata,  Malam idi yace toh sannan yaficce dasauri.


Ko da aka siyo aka dama mata tasha sai takoma tayita bacci a hannun daddy.

Tunda aka shiga da ita dubata akayi sosai kasancewar k'wararrun likitocine a asibitin saida sukayi kusan awa biyu akanta sannan suka fito.

Dasauri su Alhaji suka tashi sukanufi inda likitocin suke yakalli babbansu yace doctor ya dai dafatan dai ta farfad'o?

Eh Alhamdulillah Alhaji kabiyoni a office

Bayansa Alhaji yabi, ko da suka isa wuri doctor yagwada mashi yazauna sannan yakallesa yace Alhamdullih anyi sa'a k'afarta ce tasamu karaya sai kuma kanta da yad'an bugu munsamu munyi mata d'auri yanzu bacci take za ta iya kai safe kafin tafarka saboda allurar bacci da akayi mata ammah zaku iya shiga kuganta.


Sannan ga drugs d'in da za a siyo mata,  kar6a Alhaji yayi yana godia sannan yamik'a ma doctor hannu suka gaisa


'Dakin da take yadawo domin dubata.

Kwance take saman sick-bed bacci kawai takeyi an nad'e kanta da k'afarta da bandage ga drip ansanya mata.

tausayinta yakama Alhaji yace yanzu haka duk inda danginta suke suna chan hankali atashe tunda basusan inda takeba.

Wayar Alhaji ce tafara ringing dasauri yafita daga d'akin, d'agawa yayi tare da yin sallama


Daga d'ayan 6angaren aka amsa masa tare da cewa Alhaji lafiya har yanzu baku isoba bayan ka ce min kuna hanya tun d'azun.

Numfashi yaja yace wlh ina ta so inkiraki hankalina ba a kwance yakeba ne wata yarinyace da d'iyarta muka buge yanzu haka muna a hospital.


Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Alhaji ya jikin nata da dai sauk'i ko?

Eh Alhmdllh karaya ce kawai sai d'an buguwa da tayi a kanta ammah dasauki yanzu haka bacci take gashi bamusan danginta ba bare mufad'a masu susan halin da ake ciki,  kiyi ma baba mairo magana tashirya ynz zan turo idi driver yazo yad'auketa sai tazauna da yarinyar.


Hajiya cikin tausayi tace toh Alhaji Allah yakiyaye gaba.

Ameen yace tare da kashe wayar.

'Dakin yakoma yakalli malam idi yace kaje gida kad'auko baba mairo sai tazauna da ita mu kuma sai mutafi.

Toh ranka yadad'e.

A chan gidan hankalin hajiya a tashe tanufi d'akin baba mairo da sallama tashiga

baba mairo da take ta shirin bacci ta k'ar6a mata.

Hajiya tace baba mairo daman Alhaji ne suka buge wata yarinya shine yace idan ba damuwa dan Allah zai aiko idi driver yatafi dake asibitin kikwana da yarinyar tunda ba a san inda za a gano danginta ba.

Subhanallahi dafatan dai basu ji ciwoba,

Alhmdllh babu abunda yasamesu, yarinyar ce kawai ta d'an bugu.

Toh hajiya Allah yakiyaye gaba bari inshirya kafin ya iso.

Ko da suka isa asibitin baba mairo suka gaisa da Alhaji tare da yi mashi jaje sannan ta amshi yarinyar da take hannun Alhaji tana bacci tagoyata.

Cikin d'akin suka koma baba mairo ta tausaya ma yarinyar sosai nan sukayi bankwana da su Alhaji suka kama hanyar gida.


Haka tazauna tana kula da yarinyar da ta farka sai tahad'a mata madara tasha sannan talallasheta tayi bacci ammah uwar yarinyar ko motsawa batayi ba.

Tun dasafe aka aiko malam idi da kayan breakfast,

Lokacin baba mairo ta yi ma yarinyar wanka itama ta yi.

Likita yashigo d'akin yace har ynz bata farka ba?

Baba mairo tace eh

Ohk akula sosai za ta iya farkawa kowane lokaci idan ta farka sai akiramu

Toh likita.


Sai wajen k'arfe goma Alhaji da Hajiya suka iso asibitin.

Gaisawa sukayi da baba mairo tare da tambayar mai jiki, Alhaji yace har yanzu bata farka ba?


Baba mairo tace eh ammah likita ya ce zata iya farkawa kowane lokaci idan ta farka sai akirashi.


Waje suka samu suka zauna kowa yayi shuru yana jiran farkawarta tausayinta duk yakama hajiya.

Ahankali tafara bud'e idonta fankar da take juyawa tafara gani bibbiyu maida idon tayi takulle.

Dasauri ta ida babud'e idonta da ta tuna abunda yafaru da ita.  dak'arfi tace Ameerah,  so tayi ta tashi ammah takasa.


Su hajiya da suke zaune maganarta yasa suka ankara da ta farka da sauri sukayo wajenta yayin da Alhaji yafita domin kiran doctor.......

Sannu su mummy sukeyi mata itadai binsu kawai take da kallo hawaye suna zuba da idonta dakyar ta bud'e baki tace ina d'iyata?  Juya baya baba mairo tayi tanuna mata Ameerah da take goye a bayanta tana bacci tace gatanan.

Lumshe ido Amina tayi jin kanta kamar zai cire saboda ciwo.

Daidai lokacin Alhaji yashigo tare da likita,  dubata likitan yayi sannan yayi mata allura yakalli su Hajiya yace abata wani abu taci sannan tasha magani,  toh sukace.

Su Hajiya da baba mairo suka taimaka mata tatashi tajingina da pillow sannan aka d'auko mata roba tayi brush a ciki.

Tea mai kauri aka had'a mata aka zuba mata dankali,  dakyar suka lalla6ata tasha tea d'in rabin cup sannan tad'an ci dankalin kad'an, magani aka bata tasha sannan takoma takwanta.

Alhaji yace zanje indawo kafin lokacin ta d'an k'ara samun k'arfin jikinta sai kutambayeta gidansu idan nadawo sai inje inga danginta domin susan halin da ake ciki saboda nasan duk inda suke yanzu hankalinsu a tashe yake.

Hajiya tace hakane Alhaji Allah yakiyaye hanya sai ka dawo.


Ameen baba mairo tace,

hajiya tace baba mairo kema ya kamata kije gida kiyo mana girki tunda gidan ba kowa su Fatima sunje school.


Toh baba mairo tace ta safke Ameerah tamik'a ma hajiya ita sannan tatafi.


Shuru d'akin yayi ba ka jin komai sai 6uruntu da Ameerah takeyi hajiya tana kula da duk wani motsinta kasancewar Amina ta lumshe idonta kamar tana bacci.


Saida tagaji sannan tafara kuka dak'yar hajiya ta lalla6a Amina tatashi tashayar da ita sannan takoma takwanta ta kwantar da Ameerah gefenta.

Sai wajen k'arfe biyu baba mairo tadawo da kayan abinci,

Dakyar suka samu taci abincin tasha magani, su suka taimaka mata tayi alwallah a inda take zaune tarama sallolin da ake binta.


Bayan ta gama hajiya ta kalleta tace d'iyata wai miye sunan naki,

Kallon matar Amina tayi sannan tasafke kanta k'asa ahankali tace Amina sunana.


Murmushi matar tayi tace masha Allah suna mai dad'i.

Wace anguwa kike domin aje afad'a ma danginki halin da kike ciki domin duk inda suke hankalinsu munsan a tashe yake.


Hankalin Amina yatashi tarasa me zata ce ma matar maida idonta tayi ta lumshe ba tare da ta ce komai ba.


Ganin haka yasa hajiyar takyaleta domin gani take kamar zafin ciwone.

STORY CONTINUES BELOW

Sai wajen magrib sannan Alhaji yadawo da kaya nik'i-nik'i yak'ara dubata, saida sukayi sallar magrib sannan suka koma gida sukabar baba mairo wajenta.


Baba mairo tadinga janta da labari ahankali Amina tafara biyemata ko da ba cika magana tayiba saidai tayi murmushi a haka har tafara sakin jikinta da dattijuwar matar.


Washe gari hajiya bata zo ba saidai ta aiko idi driver yakawo masu breakfast, Alhaji ne yalek'o yaduba su yatabbatar da ba a buk'atar komai sannan yatafi. sai wajen azahar sannan su hajiya sukazo,

Da sallama suka shigo lokacin Amina tana shan kankanar da baba mairo tayanka mata,

Kallon matar da suka shigo tare d's hajiya tayi masha Allah tace a cikin ranta saboda kyaunta ammah tana kama da hajiya sosai, sai kuma yaranta biyu kyawawa suma.


Gaishesu tayi cikin girmamawa, suka amsa mata fuskarsu d'auke da fara'a sukayi mata ya jiki


Ahankali tace dasauk'i, hajiya tace Amina ga babbar d'iyata nan sunanta khairat wad'annan 'ya'yanta ne.

Murmushi Amina tayi tace sannunku da hanya Aunty khairat,

Itama khairat murmushin jindad'i tayi tace yauwa Amina ya k'arfin jikin? Jiki Alhmdllh ya yi sauki

Toh masha Allah, Allah yak'ara sauki,

Gaba d'aya d'akin suka amsa da Ameen


Hannu tamik'a ma jawahir da tunda suka shigo take mak'ale da kakarta,  tace baby zo mugaisa.


Safka jawahir tayi daga jikin hajiya tanufi wajen Amina tana wangale baki,


Kallon yarinyar Amina take gwanin burgewa tace baby ya sunanki.

Cikin hausarta da bata k'wareba tace chawahir Kekuma Anci ko?

Murmushi Amina tayi tace eh.

Jawahir tace Anci za ki bimu gidanmu ko dady zai siyo mana ice cream ni da affan, ammah shi bai iya sha ba saidai mami take shanyewa kema idan kinzo sai musha tare.


Murmushi Amina tayi tace toh Jawahir zan zo.


Yeehhh Anci 💃🏻, Marairaicewa Jawahir tayi kamar zatayi kuka tace toh kice ma mami tadaina dukana kamar yadda bata dukan affan,


Dariya sukayi gaba d'aya sannan Amina tace toh zan fad'a mata.


Murmushi Aunty khairat tayi tace Jawahir sarkin surutu kedai baki gajiya sai kace ankunna bbc, Murmushi Amina tayi tace Aunty ai yaro mai wayau ya fi.


Aunty khairat tace kai ammah ita surutunta ya yi yawafa har sai kingaji idan tafara zuba (lol wa yaga my daughter jawahir 😍)


Aunty khairat tace wannan babyn ta bayan baba mairo takice ko?


Murmushi kawai Amina tayi.


Kar6an d'iyan Aunty khairat tayi tace masha Allah babynki ta had'u gaskiya ya sunanta.


Murmushi tayi tace Ameerah sunanta.


Masha Allah kamar kibani ita.


Toh Aunty nikuma ina son jawahir sosai wlh yarinyar ta burgeni.


Dariya mummy tayi tace toh kuyi musanya mana.


Dasauri Amina tace eh wlh mummy haka za ayi.


Dariya suka sanya mata.


Sunsha fira sosai Amina tasaki jikinta dasu kamar daman ta sansu, sai gab da magrib sannan Aunty khairat tabar asibitin,

Jawahir saida tasha kuka sosai akan dole sai Amina ta bisu sunje gidansu.


Amina itama bataji dad'in tafiyarsu ba.


Bayan kwana biyu Amina ta samu sauk'i sai dai d'an abinda ba za a rasaba, zaune take tana shafa mai bayan ta fito wanka, hira sukeyi sosai da baba mairo suna dariya, bayan tagama shiryawa tea tahad'a tana sha.


Daidai lokacin Alhaji da hajiya sai Aunty khairat suka shigo.


Alhaji yakalli Amina yace a'ah patient jiki ya yi kyau tunda ana ta hira harda dariya.


Murmushi Amina tayi ta duk'ar da kanta cikin jin kunya tagaishe da su.


Amsa mata sukayi tare da tambayar jikin nata.

tace Alhmdllh ya yi sauki.


Alhaji yace dafatan dai babu inda yake maki ciwo ynz.


Eh k'afarce kawai bata ida warkewa ba take d'an min ciwo,1

Toh masha Allah, Allah yak'ara lafiya daman munyi magana da doctor ya ce zuwa jibi insha Allahu za a sallameki,

Su Hajiya sukace masha Allah, Allah yakaimu ashe su Amina sai gida.


yauwa har yanzu dai baki fad'i inda zamu samo danginki ba, kinga kyau ace sunsan halin da ake ciki zuwa wannan lokacin inji Alhaji.


Tashin hankaline yabayyana a fuskan Amina tun lokacin da Alhaji yace za ayi discharging d'inta jibi, a cikin zuciyanta tace ina ma abarni a asibitin inyi ta zama domin nan ne rufin asirina idan aka sallameni kuma ina zanje ni da banda kowa a garin...


Maganar hajiya ce takatse mata tunaninda take tace Amina bakice komai ba wai miyasa da anyi maganar danginki duk sai kibi kicanza fuska.


Murmushi Amina tayi duk yadda taso ta6oye damuwarta ammah ta kasa duk'ar da kanta k'asa tayi tace Hajiya kubarshi kawai babu wata matsala idan nakoma dangin nawa zanyi masu bayani ba dole sai kunjeba nagode da d'awainiyar da kukayi a kaina.

Kallon mamaki suka bita dashi Aunty khairat tace haba Amina ya za ayi kice ba sai anjeba, idan kina ganin babu matsala a wajenki su baizama dole hakan takasance ba.


Kallonta Amina tayi idanuwanta sun cika da k'wallah tace Aunty khairat wlh ba zasuce Komai ba.


Daddy yace ammah ai zuwan shi yafi dacewa idan kina ganin ko akwai matsala toh kar ki damu ni nasan yadda zanbi dasu sufahimta.


Shuru Amina tayi takasa cewa komai.


Baba mairo tace wai miye abun damuwa a ciki kinsan dai ba zamu cutar da keba.


Dafa kafad'arta mummy tayi tace Amina idan akwai wata matsala kifad'a mana insha Allahu zamu taimaka maki ai yanzu anzama d'aya.


Hawayen da take dannewane suka zubo daga idonta dasauri tagoge har lokacin ta kasa cewa komai domin ba zata iya tona ma kanta asiri ba saboda tana tsoron rayuwarta ta nan gaba.


Mummy tace kid'aukemu kamar family d'inkine mu kifad'a mana damuwarki insha Allahu zamu taimaka miki.


Ahankali tabud'e baki cikin muryan kuka tace Hajiya ni ba 'yar nan garin bace iyayena sun rasu da dad'ewa mijina kuma ya sakeni wai ya gaji da zama da ni, nayi-nayi yafad'a min laifin da nayi masa ammah ya k'i yace intattara inbar masa gidan ni da d'iyata nikuma ganin banda kowa garinmu shiyasa nabaro garin domin yin nesa dashi zaisa ind'an rage jin zafin abinda yayi mani a nawa tunanin,


sai naza6i inzo nan garin inyi rayuwata toh ranar da nazo ranar su Alhaji suka kad'eni, tana gama fad'in haka tafashe da kuka cikin ranta tace ba zan fad'a maku gaskiyar rayuwata ba domin kar ku ma kugujeni kamar yadda ummah ta gujeni takemin kallon karuwa.


Aunty khairat saboda tausayi har da kuka. Baba mairo kuma sai salallami take tana tsine ma mijina da nace ya rabu dani.

Muryar mummy najiyo cikin tausayi tace kiyi hak'uri haka rayuwar take wasu mutanen basuda kirki, gaskiya mijinki bai kyautaba da ya iya rabuwa da ke alhalin ya san bakida kowa sai shi, kar kidamu insha Allahu zamu duba yarda za'ayi.


Alhaji da tunda ake maganar baice komai ba saboda ya tausaya ma yarinyar yace insha Allahu zamu taimaka maki kikwantar da hankalinki

kigode ma Allah da baki fad'a hannun mugayen mutane ba, kallon hajiya yayi yace insha Allahu idan aka sallameta za ta koma gidanmu tacigaba da zama.


Amina ta ji dad'in maganar mutanen domin itama tana da burin kasancewa tare dasu saboda taga alamun mutunci da sanin darajar mutane a tattare dasu.


Cikin sheshek'ar kuka tace nagode nagode nagode Allah yasaka maku da alkhairi yadda kuka taimakeni kuma Allah yataimakeku nagode sosai


Murmushi mummy tayi tace haba Amina ai anzama d'aya kid'aukemu kamar iyayenki kar kidamu d'a ai nakowa ne.......
Post a Comment for "K'ADDARA CE CHAPTER 7"