Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAFSAT CHAPTER B

HAFSAT CHAPTER B

- - Post a Comment

 HAFSAT CHAPTER BWashe gari bata bude kofa ba se karfe tara na safe,a parlor ta sameshi ta hade sosai cikin wata dress thee green color ,har kasa ba karamin kyau tamata ba,ta watsa pink lipstic dinta se tashin k'amshi takeyi,tana kallonshi ya D'auke kanshi daga dubanta da sauri,itama basarwa tayi tamkar bata ganshi ba ta wuce warta kitchen,bayanta yabi da kallo sannan yayi k'wafa yace "Dolene na d'auki girmana,yarin yarnan Zata rainani,ita kuwa ganin datayi ya shareta yasanya ta kudiri niyyar ramawa, ha d'add'iyar indomie ta dafa se tashin k'amshin curry takeyi tasha kayan lambu,ta soya k'wai da kifin gwangwani a had'e,tafito plate d'aya daman tayi tana wakar jirgin soyayya,cikin parlor d'in tashigo ta daura kan dining ta bud'e fridge ta d'auko lemon gwangwani da ruwa d'aya tazo kusa dashi ta zauna,ta kalleshi da d'an Murmushi tace " Ina kwana yaa Yarima? " yana wani tamke fuska yace "lapia lau" ataikace...murmushin ta kuma yi a ranta tace Kayi da gwana wlhy, tana kai lomar farko ta lumshe ido ta sanya hannu ta Sosa kunne tace "Garin dad'i na nesa wlhy" tana ci tana waqar jirgin soyayya abinta,ahaka wayanta yasoma ringing,saam ce ta d'aga tana ihu abinci a bakinta,saam tace "Banza me kike ci?" Dariya tayi daidai lokacin data had'iye lomar dake bakinta tace "Banza wlhy Wannan had'a diyar indomie damukeci a gida yau ma Nayi,ina loma ina tunawa da Rolex tsinanne Nike kawowa skul amma seya wawushe ya barmu,yanzu kuwa ni kad'ai inci karena ba babbaka" Murmushi saam tayi "beb I'm really missin those days wlhy ina, mijinki?" D'an kallonshi tayi da k'asan ido taga shidinma satar kallonta yake tace "mijina kuma? Ohhh kicemun yaa Abdul,yana nan qalau" tsaki saam tayi "wannan wane irin magana ne Elly watch ur tongue" tsakin itama tayi tace

"Kinga nifa har yanzu Banyi wanka ba so,wlhy jina nake kamar a gidanmu,mantawa nake inada aure ma bare wani abu wai miji" bata rai saam tayi "Dan Allah ki dena karya jiki kinji,ba kyau abinda kike Wannan sirrin Kune be dace kina gayawa koda niba,nidai zancen yayin biki nane an fitar dubu goma sha biyu k'waya uku" ihu tasaka sanda ya kalleta tace "kaji manyan mata maganin k'ananun mata,d'an kara sending mun acc/number dinki plss zan miki sending yanzu,Choo biki on point* dariya sukai sunata hira kan daga bisani suyi sallama,ta zauna ta cinye indomie tatas tasha juice sannan tazo shan ruwa tana d'aga robar ruwan a bakinta ya taso a fusace ya dauke ta shuri atake ruwan ya tarwatse a parlor din, kallon mamaki tabishi dashi,kan tasamu bakin magana yafara masifa

" k'azama kawai,shiya sanya nakejin k'yank'yamin ki wlhy,banda kina yar k'auye kuma jaka menene na saka robar ruwa agaba ki saka ta a baki,bazaki nemo cup ki shaba? Wannan qauyancin nan gaba idan Nayi bak'i a d'aki zan riqa b'oyeki karki yarfani da Wannan halin na yayan kauyawa dakike nunawa" Tunda Elham take bazatace taji abinda ya b'ata ranta irin Wannan ba,ko zagin farko daya mata bekai Wannan baqanta ranta ba,ace mijinka ya kalle kan yace ma y'ar k'auyawa? " Wato iyauenta ne ma k'auyawan plus jaka ita matarsa itace jaka,lokaci d'aya idonta ya ciko da k'wallah take ta fara kuka,murya na rawa tace "Yaa Abdul nice jaka? Nice iyayena suke qauyawa agareka?" Kurun seya wanketa da lapiyayyen mari,yace "ni ban ambaci iyayen kiba karki kuskura ki sauya mun magana kinji na gaya miki wlhy" dafe wurin tayi ta wara ido tana kallonshi zuwa yanzu ta gama tabbatar wa kanta Abdul baze tab'a santa ba,kuma tama fara tsoron sa,sabida tasan wata rana dukna tsiya zatasha,da gudu tawuce d'akinta ta banko k'ofa ko wayarta bata tsaya d'auka ba" acan tafi awa biyu tana kuka dama gwana ce a Wannan b'angaren,indai kukane.Taso ta kira saam setaga tamkar wannan tonon asiri ne agareta,amma fa Elham ta fusata daganan ta dauki k'udirin baze k'ara ganin haqwaran taba har abada, bazata fasa girka masa yaci ba amma fa ko inda yake bazata k'ara zama ba har abada,tsanar sa me tsanani ya addabi zuciyarta,har wani tafarfasa zuciyar tata ke mata, a haka taje ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa jeans 3 quarter da bingilalliyar riga pink colour,Yaukam ba makeup ta kalminma flat aka Saka, murtuke da fuska tafito dama duk fuskar ya kumbura idanuwanta ta sunyi jajir fuskar nan tayi jajir abinka da farar mace,a parlor ta sameshi ko kallonshi batayi ba ta wuce abinta kitchen,rice and stew tayi da salat ta soya kaza ta had'a musu mango juice tun a kitchen ta zuba komai nata a plate takai d'akinta ta dawo ta kai masa Nasa dining,ta zo inda tabar wayar ta,ta d'auka tace "Yaa Abdul abincinka yana dining" ko kallonta beyiba seda ta juya yace "yauwa" murya can k'asa dama yunwa yakeji sosai daurewa kurin yake,ga gogan da masifar k'yank'yami becin girki sena gida....
Haka kwana ki suka shud'e har sati biyu kowa tasa ta fissheshi yakeyi,tunda tazo gidan bata tab'a Shiga side d'inshi ba koda tashiga dariyar data kwana biyu ba tayiba ta dinga tsulawa tamkar wata zautacciya har tana rik'e ciki,ba wani abu bane ya bata dariya irin yanda taga komai Nasa a har gitse ga boxers da singlet nashi tsilli tsilli masu datti,laundry basket nashi gwanin ban tausayi,kan gadonnan kuwa tamkar inda akayi yaqi,sosai ya bata mamaki ace duk iyayi da tsafta irin nashi d'akinshin a haukace, a ranta kuma tace "Laifi nane ai its my duty wlhy,Harma naji kunyar kaina sosai" komawa sashenta tayi ta saka wandon maza irin k'ananun nan masu yanka ata gefen cinyoyi,wanda da kad'an suka wuce duwawunta,ta sako vest baqa tafito sosai ta gyare d'akin ta turareshi da turarukan masu daukar hankali,tashige ban dakin sanda ta wanke boxers din da singlet duk sannan ta wanke ban d'akin a ranta tace "Ko matar malam jabir ai da haka ta ciwo kansa"# wani haske Ummie Aisha. Tana idarwa tafito daga part d'in a parlor d'inshi suka had'u da sauri ya dauke kanshi itama haka ko kallon shi batayi ba tace " Sannu da zuwa yaa Abdul" a wulakance yace "Me kikemun a d'aki kokuma wata k'ulallaiyar ce yanzu" yafad'a a maimakon ya am sa gaisuwarta ,Ras taji gabanta ya fad'i sosai da sauri ta d'ago ta kalleshi sarakan kukan se hawaye,ita yanzu sosai yake bata tsoro wlhy,murya na rawa tace "Bafa abinda na maka part d'in na gyara kurun" juyowa yayi jin muryarta na rawa yace "Ubanwa ye yace dake ina bukatar hakan,Wato dariyar dakika ga ina miki shine har ya baki damar ki saka k'azamin hannun ki kina damkar mun kaya ko?" Mamakinta ne ya karu waiita yake kira k'azama,batasan yaa akayi ta tsinci muryarta da furta "Kayi hakuri plss yaa Yarima" tsaki yaja yayi gaba,ita kuwa d'akinta ta wuce se nana tawa kanta takeyi "Bazakiyi kuka ba Elham kin gaji wlhy,koda bazaki ramaba ki nuna masa cewar be damekiba,kuma karki fasa neman ladarki" a haka da k'arfin hali ta share k'wallar ta,Shikuwa a haukarshi wai basanta yakeyi ba wani asiri ta masa yake jin sha'awarta,wannan kuma ba wanda ke zugashi se abokinshi dakesan yayi kuskuren sakin Elham shiya aure Wato khamis,kuma yayi k'udirin baze dakata ba harsai ya cimma burinsa......Acan ma ta manta wayarta batare da wata farga baba bayan tayi wanka tasha gayu ta nufi part din,da sallamarta ta Shiga ta sameshi yayi d'ai d'ai a kan gadon yana danne dannen wayarsa,be ansataba itama kuma bata damuba ta dauki wayarta ta juya harta kai k'ofa yace "Ke zonan" gabanta ne ya fad'i jin yakirata da ke,lokaci daya kuma taji ranta yabbaci,Wato har takai baze iya kiran sunan taba?" Jiki a mace ta juyo ta tsaya wurin gadon batare datayi magana ba,cikeda isabba tare daya kalletabba yace "Visa naki ya zama ready,nanda kwana ki uku zamu wuce London ki shirya kayanki,kuma yau da dare zamuje gidan me martaba ki musu sallama gobe zamuje gidan Su momy ki musu sallama jibi da sa sassafe zamubi jirgi mu sauka a Lagos, Friday zamu d'aga zuwa London" shagwabe wa tayi,wanda itafa harga Allah bata masan tanayi ba tace "yaa Abdul dan Allah kamun rai,bikin saam next week fa,kabari idan aka gama mana" wani mugun kallo ya wurga mata,yace a fusace yana mike wa tsaye"wai nikam a zatonki zaki yaudareni da Wannan shagwabar munafurcin,kinga bokanku be Ciba shine zaku zomun ta wannan hanyar,wlhy wannan tafiyar ba fashi,kar kuma ki yarda wai sabida inaso zanje dake,takura ni akayi wlhy,banza kwad'ayayyiya danla can matsa ki bani wuri" tayi alkawarin bazata kuma yin kuka agabanshi ba wannan ne ya sanya ta masa murmushin yake wanda akace yafi kuka ciwo tajuya batare datayi magana......

A d'akinta takasa yin kuka, tunanin irin rayuwar datakeyi da Abdul take tana mejin tsoron kalar zaman dazasuyi idan har tabar k'asar ita dashi kurun, sukuku ta wuni ranar ba karamin tashin hankali take cikiba,da magrib suka shirya zuwa gidan a b'angaren momy suka sauka,kayakyawar tarba tamusu,sunsha hira ko wannensu ya ware ya nunawa momy ba matsala a tsakaninsu,daganan suka wuce part d'in Fulani Habiba then suka wuce part d'in me martaba, ya musu Nasiha sosai akan zaman lapia da mutun ta juna kuma sun d'auka har zuci agabanshi,koda zasu tafi sarqar gwal ya baiwa Elham dalleliya me dauke da zobuna da awarwa raye,ta zuba godiya ba adadi sannan suka fito kai tsaye wurin mota ya nufa da ita sanda taga da gaske yake sannan tamkar zatayi kuka tace "Yaa Abdul bamuje mun gaisa dasu Innah da Baba ba" wulakance ya kalleta

"Au Baba me gadi wai,ina kinga da kanshi ya gaidani sanda muke shigowa kuma ai shine ya bud'e mana gate sabida duty d'insa ne,Kedai daki kaga ya dace ki gaidashi kije bazan hanaki ba,amma ni shi yake gaidani kuma Kema kin shaida hakan" wani bak'in cikine ya tarnak'owa Elham har wani d'aci takeji acikin yawunta haduye yawu tayi masu zafi sannan tace "Na sani ai Yaa Abdul bata yanda za'ayi me mulkin duniya ya gayar da me gadi,dama bance ka gayarda me gadi ko matar saba, amma y'ar me gadi ita ai tasan darajarsa kamar yanda tasan iyayen kowa,ta sani Babba babbane,sabida koba dan sun haifeta ba dole ta girmama Su" tana kaiwa nan ta juya,shi kuwa ya k'ura mata ido yana nazarin kalamanta....gaskiya Abdul akwai mugun hali,suk kalar zugae da khamis ke masa ai shima yanada hankalinsa be dace yanawa Elham haka ba....


Bayan kwana d'aya suka cira zuwa Lagos,har suka shirgi ba mewa kowa magana, ita ykamma tunda yaqi zuwa gaida iyayenta bata k'ara koda gaidashiba shikuwa ya nuna mata ko'a jikinshi,Suna hawa hanya gogan ya soma bacci ya daura kanshi a saman kafadarta,acikin baccin ya daura dayan hannushi saman cin yarta,ita dai batayi kokarin hanashi ba a haka har suka yi landing, hannunta ta saka tad'an bubbuga cibyarshi firgigit ya farka ganin shi ajikinta ya sanya duk yaji nauyi,shine ya rigata Mik'ewa yace muce, a hotel suka sauka d'aki d'aya ya kama musu badan yasoba,sedan yayiwa momy alk'awarin bazewa mamanta nisa ba har abada, Suna Shiga ta wuce Bathroom sabida ta gaji towel nata ta dauka a jaka yana kallonta tashige labulen d'akin ta daura towel d'in ta dabe wuce duwawu kadan ba,ta fito ta shige wankan,tana fitowa tazo Shafa mai,koda take zuwa ya dawo dagashi se gajeren wando,girjinshi faffad'a ga wani yalwa taccen lallausan gargasa kwance luf a ilahirin jikinshi se sheqi sukeyi,farar fatarsa ta kara nuna wa acikin bakin gashin tayi luf luf a jikinshi,gabanta ne yayi mummunan wannan karo na farko data fara ganinshi a haka,dan sauri ta dauke kanta tazo tana Shafa mai,haka kurun yaja mata tsaki yace


"Ke menene haka? Meye na zama daga ke se wannan towel bakida kunya ne ko bakisan bakida mara ba da tsirarara ba" kallonshi tayi batace k'alaba taci gaba da murza man shafawarta tamkar bada ita yake magana ba,k'wafa yayi ita kuwa tayi Murmushi,can kuma ta taso tazo kusa dashi ta sunkuya ta juya masa baya,sassauta towel d'inta tayi tace

"Yaa Abdul plss ka shafamun a baya yana mun k'aik'ayi" kamar yace baze yiba se kuma ya lak'uci man ya murza a hannunshi,taushin lallausan hannunshi sanda ya sauka a wuyanta tad'an b'ank'are bazatace ga abinda taji ba awannan yanayin,yanayine na musamman da bata taba tsintar kanta acikiba me wuyar fassara,hakan take awurin Abdul tunda yake beji skin me santsi da laushi irin na Elham ba,Shafa man yake yana lumshe ido yakuma kasa dena wa sanda taga ze rikitar da ita tace cikin wata murya "Yaa Abdul har yanzu?" Lum sassun ida nuwansa ya sauke akanta yace "sorry network news nake kalla hankalina yana can" Murmushi tamasa tace "Tom na gode" wata hatsa bibiyar rigar bacci ta saka me had'e da wandonta iya cinya zip ne ta gaban rigar se faman janshi takeyi ya sak'ale tamkar Zata fasa kuka tazo kusa dashi


"Yaa Abdul dan Allah ka rufe mun zip d'innan mana kaga fa se janshi nakeyi amma mak'ale" d'agowa yayi ya sauke idonshi daidai cikinta,flat tommy d'inta ya k'urawa ido yace aranshi "wannan Yarinyar anyi yar duniya" Tasowa yayi tsaye ya janyota ya manna jikinsu tamkar ze maidata ciki sannan ya d'an matsa kad'an ya kamo zip d'inta a maimakon ya ja zip d'in seya cura hannunshi cikin rigar ya shafi tommy d'in ta murya k'asa k'asa yace "Hafsat wai nikam yaushe rabonki da saka abinci a cikinnan,jifa yanda ya lafe" hannunta takai saman Nasa dake kan cikinta take ta k'ara masa wani shock ya D'auke numfashi tace "Yaa Abdul meye haka? Dan Allah ka dena banaso" idonshi da suka sauya launi sabida azaba ya sauke mata yace "Menayi kuma?" Shagwabe wa tayi "Dan annabi nidai ka rufe mun zip d'in yunwa nakeji" dakyar ya iya rufe zip d'in,a wahalce ya koma ya zauna,juyawa tayi tana dariyar mugunta a ranta tace "Indai ina duniya kuma muna tare seka duk'awa me gadi da ahalinsa wlhy" Har takai kofar fita zuwa parlor dake d'akin ta dawo


"Yaa Abdul I'm hungry fa" k'ura mata ido yayi yace "Nasani yoghurt zakice kina wanka na saka an kawo miki" D'an lumshe ido tayi tace "But yau har da gasasshiyar kaza irin me d'awafi d'innan zanci plss,wasu lokutan idan akayi wa Baba megadi albashi yakan siyo mana" k'irjinshi seda ya doka jin abinda tace sarai ya sani dashi takeyi yace "Shirya mu taka anan bayan hotel nasan ana saidawa" da sauri ta wani daka tsalla tace "Yauwa bara na saka hijab kin na" Murmushi yayi yafara tariyo tsallen datayi yanda mazaunan ta ke girgiza san ransu,Shifa harga Allah ya kusa ajiye zancen Khamis gefe, idanma asiri suka masa aiba laipi bane danya kusanci matarshi kumama koda zasu rabu ai Gara yasan ya Mora,beside kyautuwa ma yayi a karya taba sakin matarshi,tunda ai zab:in momy ce,da wannan tunane tunanen har tace "Yar megadi na jiran Sarki me jiran gado,nafa kimtsa" beji dad'in maganar taba amma seya basar ya Mik'e kawai ya zura jallabiya rsa ya ce "muje" haka suka jeera suna tafiya ba mewa wani magana acikinsu,suna karya kwanar layin ya rik'e hannunta,kallon shi tayi batace komai ba,acan suka siyo suka k'aro juice suka juyo,har suka iso ba wanda ke magana,anan suka bace tare suka cin ye kazar tatas,mikewa tayi ta wanke baki ta dawo ta haye gadon ta kwanta abinta cikin nutsuwa bacci barawo shine ya sungumeta suka ware..... Ba ita ta farkaba se Wuraren karfe biyu na dare dama tana tsammanin zuwan period nata,aikam ciwon mara me tsanani ne ya tasheta,a razane ta tashi sai kuka,se Innah take kira tana yarfe hannaye,a k'asa ya kwanta dama saman carpet acikin bacci yaji kukanta ya farka da sauri yazo ya dagata ya daurata akan cinyarsa

"Hafsat lapia menene ya sameki haka" tana kuka tace "Yaa Abdul na Shiga uku mtrl pain ke damuna mutuwa zanyi" tsoro yaji sosai ya rasa me ze mata,acikin rudu yace "Me ake baki Idan yana miki ciwo ne?" Kasa ansashi tayi tayita kuka se tambayoyi yake mata amma sa. Ta kasa amsashi sabida azaba,kan kace me wannan tafara amai me tsanani da gudu take zuwa toilet yin aman,a haka har kusan asuba dawowa tayi ta kwanta akan cinyarsa duk ya damu tanata kukan,hannu ya sanya yana d'an patting bayanta a hankali,da kad'an yaji shiru koda ya duba tayi bacci sosai ta bashi tausayi yalwataccen gashinta duk ya baje ya rufe mata fuska se gumi take had'awa hannu ya saka ya janye mata gashin a hankali ya sunkuya ya sumbaci goshinta yace "sorry my wife, u will soon be well" kasa d'agata yayi ya barta anan tana bacci nta har bakwai ta gota sannan ya lallab'a ya ajiyeta ya je sallah,kuma dawowa yayi kasan cewar flight nasu se dare ze tashi ya sanya ya shige cikin jikinta ya rungumeta sosai suka ci gaba da baccin Su,har cikin ransa yakejin wani dad'i jinshi ajikinta wanda ya kasa gane ko dad'in menene.


Basu suka farka ba se after 11,shine ya fara farkawa mamakin yanda suka k'ank'ame juna yakeyi,itama sarai ta farka amma seta kasa b'anb'are kanta daga cikinshi,haka kurun taji kwanciyar ajikinshi na saukar mata wata nishad'i dajin dad'i,duk sanda yayi yunk'urin tashi se yaga tana k'ara rik'eshi,gyara mata kwanciyar ta yayi ajikinshi ya rungumeta da kyau,k'urawa fuskar ta ido yayi yana murmushin dabesan dalilin shiba,hannunshi ya saka ya yaye mata gashinta daya rufe kyakyawar fuskar,idonta yake kallo yanda gashin idonta ya kwanta luf luf gasu zara zara,sumba ya manna mata a cute lips d'inshi.seda ta gaji da baccin k'arya sannan ta bud'e lumsassun idonta a hankali ta saukesu akanshi,Murmushi ya sakar mata ita d'inma ta mayar masa martanin Murmushi,yace "Sannu Elly how are u feeling now?" Wani narkewa tayi dak'yar tace "I'm feeling much better now but am seriously hungry" d'an gyara mata kwanciyar ya kuma yi yace "To ai ked'ince kin iya san jiki da yawa,baki bari ma na motsa ba balanta na na nemo miki abinda zakici nanfa ba gida bane" magana yakeyi d'auke da Murmushi a fuskarsa wanda shima besan tame ye yakeyi ba,lumshe ido tayi ta yamutsa fuska tace "Nidai abinda zanci plss" hannunshi ya d'aura akan gashinta yana shafawa a hankali yace "Elham to dake zan tashi kid'an tashi mana" a hankali ta raba jikinshi da nata tayi cikin toilet wanka tayi ta dawo d'akin ta tarar baya nan,ta zauna duk jikinta a mace yake ko man ta kasa shafawa, a haka yashigo ya sameta ta kwanta ta k'urawa saman d'akin ido,zama yayi kusa da ita yace "Chinese rice and meat balls, kokuma fried rice da paper chicken?" Turo baki tayi tace "Yaa Abdul shin kafa da safennan ni indomie zan ci" k'ura mata ido yayi yace " Elham a ina zan samo indomie yanzu? Dan Allah Kici wannan kiyi hakuri " batace komai ba ta sauko ta d'auki Chinese rice d'inta da meat balls ta fara ci sanda ta cinye tatas sannan ta sha lemo ta kalleshi "Yaa Moris kai bazaka ci abinci bane?" Murmushi ya sub'uce masa jin sunan data kirashi dashi yace "I'm OK nasha coffee yanzunnan" tashi tayi ta Shafa manta sannan tayi brush ta zo ta kalleshi tace "Yaa moris kaje parlor zan saka kaya" kwanta yayi ya bata baya yace "keda kika damu kya iya zuwa can ki shirya abinki ni ba inda zani" ya mutsa fuska tayi ta tab'e baki ta kwashi kayan taje parlor ta saka sannan ta dawo, wayarta ta d'auka ta juya zuwa parlor d'in taje ta kira Aunty husna,suna gaisawa tace "Aunty da kunya wlhy da kunya abinda kike cewa Senayi,jiyafa cewa yayi banida kunya" dariya Husna tai tace "kinga bawai rashin kunya nake Saka kiba gaskia ce kurun nake d'auraki akanta,kisani mijinki baze kawo kanshi gareki ba a wannan yanayin se kin janyo shi sosai ajiki,inasone ki saka abubuwan dakike a mizanin k'uruciya u stop being too serious kin gane ai?" Murmushi tayi tace "Yauwa Aunty Husnah na gode zanyi yanda kikace" daga haka sukayi sallama tana shigowa d'akin yace da ita " Elham zonan" batayi masa musu ba taje kusa dashi ta zauna yace "sanar dani menene ake baki idan kina kalar wannan ciwon dakikayi jiya? Na tsorata gashi bansan maganin dakike sha ba" d'an wara ido tayi irinna k'uruciya ta d'age kafad'unta tace "Lipton ake had'amun me d'acin gaske ba sugar kokuma nasha cock amma fa sam sedai yarage baya sauka kuma haka Innah tace se idan Nayi aure ze denamun ni banma yadda ba yanzu ita da momy duk haka suke cewa amma har yanzu be dena ba,gashi kuma Nayi auren kaga ni bara ma na kira momy na sanar mata Nayi auren amma mestral pain be dena munba" ta saka hannu ta janyo wayarta da sauri ya k'wace yace "ke bakida hankaline wai?" K'ura masa ido tayi irin cikin mamakin nan tace "Menayi kuma yanzu,ina Sune suka ce haka gashi yanzu nayi auren amma yamafi damuna" gano yayi kuruciyarta yayi yawa yace "How old are you Elham?" Kallonshi tayi tace "Kamanta kwana ki goma sha biyu na bawa Feenah August zan yi 17 nanda watanni shida masu zuwa yanzu ina 16/2 sha shida da Rabi" dariya ta sub'uce masa yace "Ban gaba jin inda mutum yace yana shekara kaza da Rabi ba just admit it ur just 16,kinga baki gane zancen Su momy bane suna nufin se i dan Kinyi aure kinada shekaru ashirin ne bazakiyi ba amma yanzu ur just 16 ai" dafe kirji tayi ta wara ido "yanzu kana nufin duk month Senayi haka se nan da shekaru uku da rabi?" Se kuma tasa kuka wiwi shi abinma dariya ya bashi janyota yayi yace "Kinga Elham bafa abin kuka bane,idan kin haihu ma kan nan da shekaru ukun ze dena" k'wace kanta tayi daga jikinshi tace tana kuka "Bayan Aunty Husnah data haihu tace da wahala daukan ciki sanda tazo aihuwa ma sumanta biyu Allah ni bazan haihuba" hannunta ya riqe "Yanzu dai ki dena kukan haka,idan mukaje London zance abaki maganin daze hana kiyi ciwon kuma tunda bakyaso ma bazaki haihuba so be it kinji?" Gyad'a masa kai tayi hadda share majina ya ce yana kwantar da ita "oya zoki kwanta da yamma zamuje yawo flight namu karfe 11pm ze tashi" wani patting bayanta yakeyi ita kuwa dama haka takeso sun shirya bashi wahala idan har ya kuskura ya kawo kanshi...... Ya Zata bacci takeyi jin yakira sunan ta kusan so biyu bata amsa ba,janyo wayar shi yayi yakira Khamis yana d'agawa yace
"Khamis Yarinyar nan Zata rikitar dani wlhy,kaga k'uruciya zallah wai Ashe dama rashin zama wuri d'aya ne ya sanya ban gane tanayi ba nifa inaga bazan iya rabuwa da itaba sam wlhy" d'biar sace idan ba headphone tofa hansfree yake saka waya seji tayi khamis yace " Baba wlhy duk cikin tsafine wayannan mutane naji ana fad'in ko gadin dasu keyi agida nku shekara da shekaru asirce iyayenku sukayi dama so suke Su k'wace muku sarauta kaga idan ta haihu in one way or the other d'anta ze gaje sarautar daga nan kuma kaga Su sun zama jinin sarauta,wlhy ai kawai karka yarda da wani kirsa nata kuna zuwa kamata k'azafin bin maza ka Turo da takardar saki uku awuce wurin tunda ba gyara,ni dazaka bi magana na ma ka saketan yanzu ka Adana takardar dakunje da wata d'aya ka sako Shegiya ka turota gida" nisawa Abdul yayi yace "Khamis zanbi sha'awararka amma dai se idan zan korotan zan rubuta" sallama sukayi khamis se murna yakeyi, da yamma sukace yawo cikin dare suka cira zuwa birnin London...... Had'adden gidan dabata tab'a ganin irinshi ba ya kaisu taga hadimai turawa se kira masa sir sukeyi ana gaidashi,ahaka ya nuna mata d'akinta ya barta nan,yana wuce dama rata ne bata samu ba ta ciro wayarta takira Aunty Husna,suna fara magana yana danno kanshi domin shigowa d'akin,da kukanta take magana
"AUNTY Husna nashiga ukuna,wani abokin Abdul me suna khamis naso ya mayar dani k'aramar bazawara,wai cewa ya masa asiri mahaifina ke musu danta gaji sarauta wlhy Aunty Husna mahaifina ko mahaifiyata sabida gudun irin wannan ba wanda yakesan aurennan kurun biyayya suka yiwa me martaba sabida k'imarsa ya wuce haka sannan kuma ya mutuntasu shi baya kyamar talaka wa ko kad'an,ni wlhy banasan yaa Abdul kodan wulakancin daya kemun Amma banaso na zama bazawar karfi da yaji,wlhy Aunty bamu masa asiri ba, mezamuyi da mulkin da zamu mutu mu Barshi a duniya? Me iyayena suka nema suka rasa dazasu ce dole se jininsu yayi sarauta,nifa a ganina Kobata hanyar ba idan Allah ya kaddara ze faru" nisawa Husna tayi

"Nasan da tashin hankali amma kiyi hakuri,da yardar Allah baze sakekiba,sanar dani in details me kikaji da kunnen ki?" Kwashe komai na wayar dataji sunayi ta fad'awa Husnah ta k'ara dacewar
"Sanar wa Abdul ne kurun banyiba,tunda suka zo gidana yake yawan kirana wai in kwantar da hankalina shi idan Abdul bayaso ze aureki,nace ina ka samo number na,wai Abdul ne ya ajiye wayarsa be saniba ya kwasa,idan shi Abdul besan darajataba shi ya sani,wai nayita yiwa Abdul rashin kunya idan ma ya sakeni shi ze aureni" mamakine yacika husan tace "har yanzu yana kiranki?"
"Nasaka number d'inshi a black list ai,haka kawai se inga kamar Abdul ne ya turoshi dama ni bansan meyake tunani ba akaina" jinjina kai Husnah tayi tace "Ki nutsu ki saurereni so yake ya kashe miki aure sabida shi ya aureki,ai Abdul bazeyi wannan gangancinba sabida haka ki san abinyi koda bakya sansa ki koyar dashi yanda ze soki,bazamu bari yaci galaba akanmu ba kinji,anjima da kaina zan kiraki in sanar miki hanyoyi masu sauqin bi" godiya tayiwa Husnah ta kashe ta zauna tana hawaye da kuka me d'an sauti tana magana "Allah ya isa khamis wlhy,inajin muryanka na gane Kaine tunkan ya ambaci sunanka,kazafin daka mun se anwa yarka wlhy" juyawa Abdul yayi yana mejin zafin abinda khamis ya masa aranshi yace Senayi uwar khamis kuwa wlhy,dama burinshi ya had'ani da momy tome na masa,Kodai zargi nane ya tabbata so yake na saki Elham yaa aura? Dama mana ranar se kallonta yakeyi kuma seyata matsayin akan zasuzo gidana,k'wafa yayi yashiga d'akin da sauri ta goge fuskarta tace tana murmushin yaqe

"Yaa Abdul yanzu nake shirin kiranka,yunwa fa na nakeji" kamo hannunta yayi yace "Elham kukan me kikeyi daga zuwanmu" k'ura masa ido tayi tace "Inna da momy nake missing da gida gaba d'aya" tausayinta yaji ga k'uruciya ga damuwa yace " keda kike da yaa Abdul d'inki a kusa mezai dameki kuma?" Murmushi tamasa kurin ya sanya hannu yaja hancinta yace "Idan na kuma jin kukannan bulala zan miki" maqe kafad'a tayi "ehmm ni banasan bulala fa ko askul idan za'a dakeni kula nake tayi inankiran momy" Jan hannunta yayi "muje our food is ready"....

Da dare zasu kwanta se tsoro takeji ita kad'ai a d'akin gashi wani irin qatoton d'aki ne,b'ingilalliyar riga ta saka iya cinya tazo parlor d'in ta zauna,kallonta yayi yana danna laptop yace " Elly dear baki kwanta ba?" Murmushi tamasa sannan tace "I'm scared"
"Of what Elham?" Murgud'a baki tayi ta tsuke fuska "I mean the bed room is very big can't sleep in there me alone" Murmushi yayi yace "Muje na tayaki kwana a d'akin kinji?" Binshi tayi abaya ya kashe laptop din ya kashe side lamp, edge d'in gadon taje ta kwanta tanata takure wa shi dariya ma tabashi,sanda ya bari tayi bacci sannan ya janyota jikinshi..

Wuraren k'arfe uku na dare ta farka,mamakin take sanda tazo jikinshi har haka,fitsari takeso tayi amma ta kasa koda motsi sabida yanda d'imin jikinshi ke saukar mata da kasala,a hankali ta ce "Yaa Abdul ka d'aga ni ina so zanje bathroom ne" be motsa ba sanda ta maimaita so kusan uku sannan ya bud'e idonshi a hankali ya sakar mata lallausan Murmushi dukda acikin duhu suke,hannu yakai ya kunna side lamp dake d'akin sannan ya sake riqon daya mata yace "Sorry na hanaki tashi bacci ne yamun nauyi" Mik'ewa tayi kurun ta gyara gashinta daya yamutse taje toilet d'in tayi fitsarin ta dawo,zaune ta taddashi tace+
"Lapia dai yaa Abdul?" Murmushi ya sakar mata " Ai komai Nisan dare idan aka tashe ni bana iya komawa baccin " b'ata fuska tayi tace "Ohhsh Allah dana sani ban tashe kaba wlhy,yanzu haka zaka yita zama kenan??" Kishin gid'a yayi yace parlor zanje inyi kallo kawai" zaunawa tayi kusa dashi tace "To nima zan bika muyi kallon tare"
"Noo plss karki damu,ki kwanta kiyi baccin ki kinji" mak'e kafad'a tayi "ehmm ni bazan kwanta d'inba zanje mu zauna tare kawai" Mik'ewa yayi yace "if u insist" Murmushi kurun tayi tabi bayanshi,Jennifer's diary yake kallo dai itad'ima zama tayi se dariya sukeyi sabida anata yin abin dariyar,bacci ne yafara fizgarta,ganin tana d'ingishi ya sanyashi dariya ya janyota jikinshi kanta ya datura akan cinyarshi yashiga Shafa lallausar sumanta "Kiyi bacci Hafsat,bacci kikeji naga alama" batayi musuba tashiga lumshe ido,har cikin ribs nata take receiving saqonnin dayake aika mata,a haka bacci barawo ya kwasheta,gogan shima a zaune yayi baccin basu suka farka ba se 7 wannan ma ita d'ince ta fara farkawa k'urawa fuskarsa ido tayi tana mamakin kyakyawar fuskarsa har acikin bacci,tana so ta tasheshi yayi sallah,taga alama ma kwanciyar na bashi wahala sosai sabida a saman kujera kanshi ya tafi sosai kasancewar a k'asa suke,tuna wa tayi da yanda Husnah ta koyar da ita yanda zatana tashin mijinta a bacci,Murmushi tayi aranta tace zan iya kuwa?? A hankali ta tashi daga jikinshi ta sanya hannunta tana Shafa kanshi a hankali,bud'e idonshi yayi ya sau kesu a kanta,da Murmushi ta tare shi tace "Kayi Latin sallah yaa Abdul ka tashi" Mik'ewa yayi a hankali batare da yayi magana yabar gurin, itama ta miqe tawuce d'akin ta,wanka tayi ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga mara nauyi me santsi da kyawun gaske kalar sararin samaniya ta tufke gashin kanta a tsakiya tayi masa style na donut, ta feshe jikinta da turaruka dama gashi tayi wanka da ruwan miski se tashin k'amshi takeyi tako ina. Parlor tafito har wannan lokacin be dawo ba,se can ya shigo cikin Shiga ta kananun kaya riga da wando,wandon jeans blue sa shirt kalar sararin samaniya shima yayi kyau matuka se tashin k'amshi yakeyi,zama yayi kusa da ita yace yana mai janyo hannunta

"Ur looking beautiful Elham" Murmushi tamasa tace "u too" hancinta ya d'an ja "ohh Really?" Langwab'e kanta tayi tace "yea Kayi kyau sosai,ko wurin budurwar ka ta nan k'asar zakaje?" Murmushi yamata yace "Ai itane zatazo karki damu da wannan" cikeda isa ya nuna wannan,gabanta ne ya yanke ya fad'i ta yi Murmushi tace "zanji dadi idan na ganta kuwa" kallonta kurun yayi ya mik'e ya bar wurin......

Rayuwa tayiwa Elham k'unci kasancewar tunda sukazo bata sake saka Abdul a idon taba tun kwanan farko, tsoro me tsanani ya shigeta,gashi se yan matan turawa masu masa aiki take gani suna kai kawo a part d'in shi,takuma tambayi d'aya daga cikinsu inda yake tace mata fitar asuba yakeyi ya dawo late,yau kusan kwananta shida kenan bata ganshi ba abinda ta rasa amma batajin dad'in rayuwarta sam!!! Ganin ya Shigo da sauri ta miqe taje gunshi "Yaa Abdul lapia kuwa? Kwana biyu bana ganinka?" Hannunshi ya sanya ya tureta yace cikin maye "Zaman uwarki nake a garinnan dazakice Sekin ganni kullum,wlhy ki Shiga taitayinki" zaro ido waje tayi jin muryarshi se a sannan ta kula da yanayinshi sarkace k'atuwa a wuyanshi da wando iya gwiwa daka ganshi kaga zararre kuma a buge yake,kafin tayi wani yunkuri ya fad'o ajikinta,tare shi tayi sannan cike da k'arfin hali taje ta kwantar dashi a d'akin shi,wannan ne karo na farko data fara Shiga d'akin kuma ya tsoratar da ita, ko ina kwalaben giya ne da kwalayen sigari,bata tab'a zato cewar yana aikata wannan mugun abin ba,tausayin momy ne ya kamata tace a sarari murya na rawa "Wlhy nikan nashiga uku na,ya Allah ka kawo mun agaji" anan ta durqushe ta rushe da kuka me ban tausayi,kome yasa takejin tausayin Abdul oho...Tunawa tayi da yanda akeyi cikin films idan mutum yasha giya da sauri ta Shiga toilet nashi ta dauko towel da ruwan sanyi masu ice tazo tana Shafa masa akai a hankali,sanda ta kula yafara sound and safe sleep sannan ta kwanta a kusa dashi taci gaba da kukanta,bata masan me take wa kukan ba,wani abu takeji me d'aci har cikin ranta a wannan lokacin,a haka bacci ya kwasheta,se yamma ya farka tsoron abinda yayi ne ya dawo masa akai ganinta ajikinshi ya tariyo masa komai,dafe kanshi yayi yana kuka me sauti wanda kukanne ya tasheta,k'ura masa ido tayi sanda yayi me isarsa sannan ta dafa kafadar shi tace "Yaa Abdul dan Allah ka dena kuka" jiyowa yayi ya kalleta da jajayen idonshi yace "Hafsat dan Allah ki yi hakuri kuma ki rufamun asiri karki gayawa Su momy,wlhy bana neman mata giyar ce kawai kuma zan dena I promise" k'ura masa idonta tayi se hawaye kasa cewa tayi da shi komai,ta zauna zaman kuka awurin,janyo ta yayi ajikinshi yace "Hafsat ki tallafi rayuwata na dena shan giya,wlhy ba laifi na bane,nace dasu banson sarautar nan nafi buk'atar rayuwata cikin kwanciyar hankali amma sun kasa ganewa wlhy Hafsat bana so,zumunci yaqi saidai tuwa sabida sarauta,d'an uwa na neman ran d'an uwansa sabida sarauta,inaso na auri Humaira sun hanani sabida munafuncin sarauta,yanzu sun k'ara rabani da Raihan sabida nasu ra'ayin,Elham ki yarda dani banida burin tarwatsa rayuwar ki shiya san ya na gujewa aurenki bansan kalar muguntar dazasu miki ba, karkema Su rabaki da farin ciki na har abada,Hafsat wlhy na rantse miki banaso ki Shiga damuwa akaina,Banso ko kad'an kika zama cikin wayanda zasu d'and'ana muguntar gidan sarautaba" kasa magana tayi ya d'ago kanta ya sanya duka hannayenshi ya d'ago kanta ta hanyar Saka lasu a cheeks nata ta fuskance shi

"Hafsat ki yarda da zancena nafi shekaru biyar ina d'awainiya da sanki cikin raina,wlhy Humaira da Raihan duk badan sun zamemin dole nake san auren suba, sabida kurun sud'in yan gidana,I really don't wannan drag u and ur family in to this mess,naso sosai kiyi aurenki inda zaki huta,momy ta kasa fahimta na,akanki kisane kawai bazan iya ba wlhy bazan juri ana neman tab'ar b'are rayuwar ki ba,ki sani ina sane nake zaginki nacin zarafi sabida kawai ki ce bazaki aure niba dan kisamu freedom me dorewa,ko bayan auren mu danake zaginki dan kawai ki kasa daure wa ne kice bazaki zauna daniba ki huta,ban tab'a zaginki Nayi bacci ba wlhy Hafsat duk sanda naci zarafinki bana iya bacci, sabida bakin ciki ni kanji natsani kaina amma ya zanyi.Tsakanina dan iyayenki biyayya ce me tsafta ki binci kesu kiji,tun ranar da muka taho yau gobe nakejin wasu maganganu daga gida wayanda bazan jura ba,Hafsat zan sauwaqe miki sabida inasan ki dauwa ma a farin ciki badan komai ba,idan ba wannan hukuncin na yanke mana ba wlhy bazasu barki ba Hafsat,sannan kuma bazan tab'a yin bankwana da giya ba idan nace zan rayu dake kina shan wahala,kuma soyayyar kice Zata halla kar dani idan har ban rayu dake amma na sani bakya sona ni kuwa farin cikinki shine nawa,sabida haka zamu rabu Hafsat ki guji yan gidan sarauta,anmiki asara mafi muni a yanzu haka,zuwa next week zan maidaki gida" k'ura masa ido kurin tayi takasa koda k"wak'waran motsi,Mik'ewa yayi yaje ya bud'e wardrobe d'in sa ya d'auko takarda ya miqa mata takardar yace "karanta kigani Hafsat,kuma kar kiga laifina koku zargeni wlhy k'aunace sila,kuma koda kin koma gida dan Allah ki guji faruk wlhy har cikin raina nakejin wannan tab'in dayake wa jikinki" Mik'ewa tayi jikinta se rawa yakeyi ta kasa bud'e takardar illah kallonshi kawai da takeyi cikin rashin fahimtar zancensa, janyota yayi jikinshi ya rungumeta sosai ya saka wani razanannen kuka daya tayar mata da hankali......
Hmmm to wai jama'a meyake damun Abdul,abin zantuttukan hankali yakeyi kuwa? Anya tun farko bamu kasa fahimtar Abdul ba kuwa? Muje zuwa dai kuna tare da alkalamin momZare rungumar daya mata tayi ta tallafi fuskarsa da tafin hannunta tace cikin sassauta murya da sigar rarrashi+


"Com down yaa Abdul,ur a man plss try to look as one mana" k'ura mata ido yayi duk da hawayen basu dena tsiyaya daga idon shiba,tace tana me k'ara saisaita fuskarshi da hannunta


"Yaa Abdul plss be like a man kaji,kalle ni plss dena kukan haka" zaunar dashi tayi sannan ta sakashi jikin kafadarta a hankali take Shafa bayanshi tamkar wani jinjiri,dagowa yayi yace "Hafsat yau zan sanar abubuwa da dama wayanda baki san dasuba arayuwa ta" gyad'a masa kanta tayi alamar yaci gaba.....


"Koda na taso naganni a gidan me girman gaske,a labarin danaji Kakanmu wanda ya haifi mahaifina kashe shi akayi ta hanyar yi masa yankan rago, yanada mata Su hudu da kuma yara manya maza Su takwas,se kuma mata Su goma sha uku....Akwai k'aninshi Muhammad shine kadai gareshi dan uwa mahaifinsu Su biyu kad'ai ya haifa,bayan rasuwar sa kasancewar Kakanmu shine Babba se aka bashi sarkin garin,wannan abin ba k'aramin tayarwa mahaifiyar Su Muhammad hankali yayi daga nan ta k'walla fa ranta akan se Muhammad yayi sarauta.....Kakanmu a cikin y'ay'anshi takwas dinnan maza mahaifina shine na shida mahaifin Su faruk shine na biyar, kafin rasuwar kakanmu kuwa ansha fama da Baba Muhammad da mahaifiyarshi daga k'arshe dai sukayi nasarar yi masa yankan rago wanda agaban idon mahaifina hakan ta faru shida kanshi ya sanar dani,bayan rasuwar sa aka gane Sune amma se mutane suka k'aryata hakan,daganan aka bashi sarautar,sauran kishiyoyin kakata kuwa suka d'auki masifar san sarauta suka d'aurawa akan yayan su,daganan me martaba kakana yabar baya da k'ura sabida sune suka kashe Baba Muhammad da Kansu, a wannan lokacin se abin yazama rigima domin kuwa duk wanda yahau sarautar se an kasheshi haka yayyun mahaifina sukayita rasuwa har akazo akan Baban faruk,shine ma ya jima akan sarautar domin kuwa tun muna yara shina taso na gani akan sarautar,zancen da nake miki wayanda fa ake kashewa har matansu da y'ay'ayensu bawai barinsu akeyiba indai kin haifi yaro namiji sedai kiji ance guba yasha idan mace tace Zata motsa ita d'inma a kasheta mututus.....gidan sarauta yazama wani iri domin yayyuna maza guda biyu sace su akayi haryau ba labarin su mahaifiyata duk sanda kikaga tana kunannan dakike damuwa idan tana yinsa yaranta take tunawa,an halakasu duk dan sabida Karsu tasa su gaji sarauta, Ana haka muna aji shida a secondary akayi murdering mahaifin su faruk ta hanyar poisoning d'in sa,wanda haryau ya haddasa rud'ani akan cewa mahaifina shine ya kashe shi,da kunnena naji mamansu faruk na cewa lallai idan nayi aure sedai duk sanda matata tayi ciki su zubar dashi ta hanyar tsafi bazasu tab'a bari na haihuba,sedai ko na gaji sarautar yayan faruk su gada,wannan dalilin ne yasanya na nemi auren Humaira yayar Raihan aka hanani daga baya kuma na nemi auren Raihan ita d'inma ban samu ba,Karfa ki Zata sabida ina sansu ne wlhy kurun sabida nasani bata yanda za'ayi uwa ta cutar da 'yar ta hasalima wlhy banasan tarbiyar yaran,nafara sanki ne tun kina jss 1,Nakuma t'aba sanar da momy ki binci keta kiji amma duk sanda na tuna cewar zasu lahantamun ke su wurgaki cikin halin da ba nakiba senaji bazan iya ba,ahaka na koyawa kaina yi miki kallo iri d'aya da feenah sabida haka na fara jin sassauci,dazaki tariyo farko kece babbr k'awata banida Aboki yar hira seke,tun sanda na fara ganinki da faruk na d'aura aure da giya sosai,nasani rashin ki masifa ne a gareni, Naso Raihan bazan miki k'aryaba amma wannan a rashin kine nasoma sabawa da ita, bayan rashin ki kuma yanzu me martaba ya matsa akan rashin lapiyarshi wai ze sauka ya bani ragamar mulki,Hafsat ko kinsan hallakaki zasuyi bazasu bari kiga k'wanki a duniya ba,bayan nasani Baba Hashim yasha wahala kafin samuwarki Harma ya cire rai da haihuwa kuma bayanki seda suka shekara biyar basu samu wata haihuwar ba,sunci ganin jikokinsu sannan kuma kece zaki basu kulawa,idan kika Shiga damuwa yaushe zaki kula da kanki ma bare su,a yanzu haka an shaida mun tun dawowarmu nan da kwana d'aya an kashe Amir k'anina kuma labari ya riskeni ance saura ni dake!!!!! Hafsat ki yarda da k'addara wannan takardar saki d'aya ne aciki dana miki sabida na tserar da rayuwar ki daga halla ka plss ki fahimceni" shiru tayi ta k'ura masa ido nakusan minti biyar wanda shima d'in ita yake kallo,hannunta ya riqo ta warce da sauri ta mik'e tsaye ta juya masa baya yau kukanma ta kasa yi,cikin d'acin murya tafara magana


"Dukkanin hujjojinka ababen dubawa ne,amma anya ka tausa yamun daka mayar dani k'aramar bazawara? Da kasan kanaso kan kareki daga hannun su aiba seka wulank'anta mun rayuwa ba,akwai wulakncin dayafi ka mayar dani k'aramar bazawara? Baka da labarin idan Kayi imanin da Allah cewar babu wanda ya isa yamaka abinda Allah be makaba kuma kanada adua ba wanda ya isa ya maka wannan mugun abin,wlhy na yarda da dukkanin abinda ka fad'a amma wannan sakin dakamun ya nunamun cewar tsantsar k'iyayyace ba wani so dakake mun se shirin tarwatsa rayuwata,nakuma gode k'warai" tasowa yayi a rud'e ya riqo ta ta kwace kanta da sauri

"Bakada labarin cewar ni ba matarka bace? Kuma banida iddar ka ayau na wanke tsaf daga kanka,idan gobe naso aure na zanyi,sabida haka wlhy kaji na rantse maka wlhy karka kuma tab'ani,kuma yanzunnan zan kira momy na sanar mata" da sauri ya kalleta yace "ki rufamun asiri Elham karki sanar mata,amma ki kirata kimata gaisuwar Ameer,dan Allah dan annabi karki sanar wa kowa" hararar tayi tana me jin tsantsar tsanar sa


"So kakeyi na k'urawa kaina ido a gida koso kakeyi na tabbata ban sanar wa kowaba,kana nufin cewar banaso nayi aure,aure zanyi dama ai acikin d'inbin masoya ka d'aukoni Ba maqiya ba,so namaka alkawarin acikin watanni biyu kacal zanyi aurena kuma kowa sena sanarwa ka sakeni" magiya yashiga mata ita kuwa ta saka wani kuka me ban tausayi,tanajin zafin mutuwar Ameer sun shaqu sosai kwanciya tayi tana ambaton sunan Ameer tana kuka......Abdul kamma kuka ya saka ya zauna yana ta bata hakuri,dakinta ta koma ta k'ulle kanta,ta zauna tanata rusan uban kuka,tama rasa me zatayi,kiran momy tayi tayita kuka tamata ta'aziyar Ameer amma ta kasa gaya mata sakin da Abdul ya mata,bayan sun gama ta share hawayenta ta kira Aunty husna,komai sanda ta sanar mata,nisawa Aunty husna tayi tace+


"Kinga Elham,bazamu bari aurenki ya lalace haka a banza ba,karki kuskura kowa yaji wannan zancen, koda yace ze dawo dake karki yarda amma ki Barshi wlhy ze kawo kanshi ne,hujjojinshi basuyi karfin da zeyi wasa da saki har Hakaba,duk da yake yanada ban tausayi amma wlhy bazamu aminta ya lalata rayuwar kiba,yanzu ki nutsu Elham saki akwai ciwo ba kad'an ba, kuyita hakuri Koda yace ki dawo Nigeria karki yadda,ki roqa a sama miki makaranta anan" shiru tayi sabida tanaji wannan karon bazata bi zancen Aunty Husna ba kuma sam tama tsani ganin Abdul,se can tace


"Aunty Husna nifa wlhy na tsaneshi bana san a gyara auren,ni sena sanar wa momy" sassauta murya husna tayi cikeda rarrashi


"Haba Elham Karki yiwa momy haka mana,kinsan yanda take k'aunarki d'innan Zata iya yanke jiki ta fad'i ga kuma an mata mutuwar Ameer na damunta,dan Allah na rok'eki ki gyara aurenki da kanki batare da sanin kowa ba" nisawa tayi tace "Idan haka ne Aunty ina da shawara"

"To ina jinki Hafsat" daga nan ta zayyane mata komai yanda take ganin za'ayi dashi,ta k'ara da cewar "Aunty wannan ne kad'ai hanyar danike ganin zamu bi,Abdul be kyauta wa kanshi ba aganina kuma beyi jarumta ba amaimakon yayi jarumta ya nemi mafita seya sakarwa yan uwansa ragamar rayuwar sa gaba d'aya"

"To Elham ina fatan Allah ya sanya wannan tsarin namu yayi working kinji" sallama sukayi ta ajiye wayar cike da bacin rai,har kusan kwana ki biyar bata k'ara ganin Abdul a gidan ba da wannan take tunanin bata yanda za'ayi plan nasu yayi working,a maimakon ta kira Husnah,kurun se fushin zuciya ya d'ebeta ta kira momy ta saka mata kuka,cikeda wauta ta gaya mata komai tsaf daya faru,B'acin rai me tsanani ya ziyarci momy,rayuwarta ta b'aci,bak'in ciki ya lullub'e ta hankalinta ya tashi,kuka kawai ta saka ta kashe wayar,a fusace ta kira Number d'inshi.....


Yana office zaune yana tunanin yanda zeyi da Elham so yakeyi yace ze maida aurenta amma yasani bazata aminta dashiba,yana tunanin yanda zeyi rayuwa batare da Elham ba,yanzu ya haqiqancewa kansa rayuwarshi batada wani amfani idan ba Elham,Mema zesa yayi wannan tunanin har ya biyewa san zuciyarsa ya saketa,yana tsakiya da wannan tunanin wayarsa ya soma ringing, gabanshi ne yayi mummunan fad'uwa ganin sunan momy domin kuwa basufi awanni biyu da gama wayar ba,yakuma sani banza bata kai zomo kasuwa,jiki a mace ya d'aga wayar....


"Baba na na gode da abinda ka sakamun dashi na sakar mun mama na da Kayi, ka mayar mun da ita k'aramar bazawara,ka tozar tar dani,baka dubi halin rashin Ameer danake ciki ba ka sakar mun yarinya,me kake so nace da iyayenta? Wlhy ka wulakanta ni fiye da tunaninka,kuma ka sani sena rama da yardar Allah Mamana Zata auri miji wanda ya fika lallai ka Turo mun ita as soon as possible sabida ta sanar dani ba iddar ka a kanta zamanku tare yanzu had'arine Babba ba k'arami ba" kafin yayi magana ta kashe wayar koda ya kuma kira wayarta a kashe gashi feenah bata gida yanzu bare ya kira ta bata,dafe kanshi yayi yata kuka tamkar k'aramin yaro,seda yayi me isarsa sannan ya tashi zuwa gida,d'akin Elham ya wuce kai tsaye ya tarar ta idar da sallah tana adua zama yayi harta idar,juyowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta


"Hafsat mesa kika mun haka? Mesa zaki zab'i had'ani da mahaifiyata? Menene ban miki ba a rayuwa? Sabida kawai ki dauwama a farin ciki na sadaukar da nawa farin cikin,Ashe ban cancanci ki rufa min asiriba? Bayaga haka na gama yanke hukuncin zan kama aure na,Mesa bazaki fara tambaya na tsarin dana mana ba" wani mugun kallo ta wurga masa tace a fusace


STORY CONTINUES BELOW

"Wlhy Kayi kad'an na kuma zama matar har abada,da kake zancen kama aurenka sekace wata tinkiya kokuma dabba,bakada labarin cewar Na gama idda,dole ne se an sake daura mana aure,kuma bana buk'atar k'arasa rayuwata da ragon namiji,mutumin daze bar ragamar gidansu ta lalace sabida rashin lissafi,aure na ya kare dakai har abada,banida iddar ka kuma Baba me gadi ya kaini islamiyyah,an sanar dani cewar idan idda ta yanke baza'a k'ara komawa aure ba se an d'aura kuma da waninka zan d'aura bada kaiba,na gama dakai har abada" duk girma irin na Abdul kasa daure wa yayi ya saka kuka


"Elham wlhy bazan iya rayuwa batare dake ba,kuskure ne nayi kuma na gane kuskurene plss give me a second chance" dariya ta kwashe dashi "Off course I can give u one big another chance to destroy my life" matsawa yayi kusa da ita yace

"Ba haka bane Elham,wlhy kece rayuwata gaba d'aya, banajin zan iya rayuwa baki" ka tayi magana wayarta ya soma ringing, dauka tayi taga yaa Ibrahim ne,d'agawa kurin tayi,t wani shagwabe murya


"Yaa Ibrahim dan Allah fa tun yaushe na kiraka shine se yanzu kake kirana?" Daga d'aya bangaren kuma Murmushi yayi najin dad'i yace

"Kiyi hakuri Rose kinji,inata aiki ne yanzunnan na shigo gida go lunch ban ciba" K'ara langwab'e murya tayi tace "Yaa Ibrahim kai kuwa seka riqa wani tunamun da yaa faruk na,shine yake kirana da Rose" Murmushi yayi shi yakasa gane kan Elham yanzu kuma tace dashi wai aurenta ya mutu,kuma batada Idda dama auren dole akayiwa dukkansu1


"Ehn love one tintin Kodai yanzu da yaa faruk za'ayi aurenne?" Dukda tasan cewar Abdul bawai yana jiyo me Ibrahim ke cewa bane,amma seta tsinci bakinta da furta Kalmar "Bazan kuma aure a gidan sarauta ba,indai yaa faruk ne na hak'ura gaba d'aya, kawai dai sunanne yake zuwarmun da good memories damuka kasance a tare,he's such a nice person,nasan da ace Shina aura,da Banyi zaman zawarcin k'uruciya ba a yanzu,baze tab'a saki naba sabida yana sona sosai"

"To kiyi hakuri wata rana se labari,idan na kammala abinda nake zanyi kiranki" sallama sukayi ta wuce bathroom kai tsaye tana me jin zafin yanda zuciyarta keso ta bata kunya akan Abdul,mesa takejin tausayin sa ne?" Wannan itace tambayar data kasa samun amsarta tuni.....


Juyin duniya Abdul yayi amma Elham takasa bashi fuska,hasalima zagine ke Shiga tsakaninsu,a haka a rikice ya dakatar da duk abinda yakeyi ya kwaso ta suka dawo Niger.......


Zagi na wulakanci momy ta masa,yashiga magiya amma fir taqi saura rarsa,iyayenta sunyi bak'in cikin wannan wulakncin sedai wannan karon a wurin momy ta dawo da zama gaba d'aya,d'akin feenah shine ya zama nata,hankalin Abdul be kara tashiba seda yaga har me martaba Fushi yake dashi, shirya wa yayi yaje fadar me martaba,a durk'ushe yake agaban me martaba yana kwasar gaisuwa,daga gaisuwar kuwa me martaba yamata banza,seda ya raina kanshi sannan yace


"Abba dama nazone akan zancen Hafsat,dan Allah a taimaka a dawo mun da ita,tunda saki daya ne,Inshaa Allah,wannan kuskuren baze sake faruwa ba" yafi mintuna sha biyar da gama magana me martaba be kulashiba,ga bahalin cewa komai,se can yace


"Ina so kasani,mahaifiyata Hafsat ta kasance me rauni tun kafin zuwan tsufanta kasancewar batada lapia ko kadan,mahaifiyar Elham itace ke d'awainiya da ita kasancewar a b'angarenmu bamuda macen dazata kula da ita,bata tab'a gaji yawa da kulawa da itaba kazalika bata tab'a karb'ar sisin kwabon mu na ladan d'awainiyar da take da ita ba, alokacin datake fama da matsananciyar rashin lapiya Asabe baro mijinta take ta dawo ta kwana a wurinta,itace da kanta ta samo mata maganin hausan datayi ta sha harta samu lapiya,tafara tafiya bayan tayi shekaru takwas bata taka k'afafuwanta,sabida yaa d'aukar Mahaifiya ta matsayin mahaifiyarta tana haihuwa ta sakawa yarta suna Hafsat!!! Yarinyar da shekara da shekaru Allah be basu haihuwaba se daga bisani suka haifeta,soyayya me tsanani mahaifiyata keyiwa Elham wanda wannan shaida ne kowa yasani" "shiru yayi yad'anja fasali sannan yaci gaba


" Anya Abdurrahman kayiwa Mamana adalci daka saketa da k'uruciya? Bakada labarin matsalar da wannan sakin ya jamun awurin Mahaifiyata akan na bada auren takwararta akan mijin dabe dace da ita ba? To ka sani gangan cin danayi abaya bazan k'ara maimaita irinshi ba har abada,Elham ta kawo mana yaron dazata aura me suna Ibrahim kuma mun bashi aurenta nanda sati biyu masu zuwa" zabura yayi tamkar wanda aka tsikara ya saka kuka agaban mahaifinshi

"Dan Allah Abba kamun rai,na rokeku kubani wata damar nayi alkawarin zan gyara kura kuraina,na baya,zan kula da ita zan rayu da ita cikin Aminci" Murmushi me martaba yayi irinna manya yace


"Abdurrahman ka rigada kafara haduwa da darasin rayuwa, da wannan zakasan muhimmancin tunani me zurfi kafin yanke ko wane irin hukunci" da kuka yabar wurin..... Sanye take da doguwar rigar less ash color tayi rolling da red d'in mayafi,fuskar nan tasha makeup tamkar babu abinda ke damunta,nan kuwa tunanin Abdul ya tayar mata da hankali matuka,tarasa nutsuwar ta gashi sam ta gayya ta gayyato Ibrahim a rayuwar ta bata taba zaton cewar ze gabatar da kanshi da sauri har hakaba, Dukda bata sonshi, amma a yanda Abdul ya wulakanta ta Zata koyawa kanta san Ibrahim ko yaya ne......kamar wanda k'wai ya fashewa aciki haka yake tafiya,a garden yazo ya sameta zauna kusa da ita,waigowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta gaba d'aya,cikin sanyi murya ya furta


"Hafsat zuwa nayi muyi magana akan zancen aurenki da naji,dan Allah ki taimakamun karki barni" wani malala cin Murmushi tayi tace


"Kamar yanda Kayi dogon nazari akan sakina kafin ka sakeni,haka nayi dogon nazari akan auren masoyina Na haqiqa,Abdul bakada hurumin dazakace wai na fasa auren shaqiqina na dawo hannun wanda bema san darajar iyaye na ba,inaso idan mafarki kakeyi toka farka,sabida bazan tab'a auren kaba" k'ura mata idonshi yayi da suka sauya launi zuwa jajaye yace murya na rawa


"Hafsat nasani ban miki adalci ba ko kadan,kuma ban isa in hanaki komaiba,nasani wannan hukuncin dakika yankemun Na cancanci wanda yafishi,zan miki fatan alkhairi idan har kika zab'i yin hakan amma wlhy duk halin dana Shiga kece sila,mutuwa zanyi ada na hakura dakene sabida wasu yan dalilai,yanzu kuwa bayan munyi aure mun rabu na fahimci kece rayuwata tsaf zan mutu idan nayi rashin ki my Elly,ina miki....se kuma tari ya sarqeshi janyo handkerchief yayi ya tare wanda atake ya soma aman jini,gigicewa Elham tayi ganin wannan tashin hankali tazo ta riqeshi " Yaa Abdul Sannu,meke faruwa da kaine? Aman jini na Shiga uku " ganin fa be kulata ba kuma gashi se aman yakeyi ya matukar tayar da hankalinta,a rikice taje part d'in momy ta sanar mata,a tare sukazo aka kwashe shi zuwa asibiti Elham se kuka takeyi wanda ita kanta bata san kona meye ba,tsoro takeji karta rasa yaa Abdul d'inta wannan aman jini idan yayi irin shi so biyu toko tabbas tsaf mutuwa zeyi dominnko ba abinda ze hana wa jininshi tsiyayewa ta tas.....abin mamakin kuwa shine yanda doctors suka tabbatar musu cewar lallai daga zuciyarshi har b'angaren ulcer lapiyarshi qalau,me martaba be yadda ba yasanya aka masa general check up nan ma Lapiyar shi qalau.....haka ya shafe kwana ki goma cur besan inda kanshi yake ba idan kuma yasoma aman jini baya tsayawa seya kusa amayar da yayayen hanjinshi,Elham ita kad'ai setaje d'akinta tayita kuka daba tasan dalilin shiba,Gashi me martaba yace aurenta ba fashi sora kwana ki 4 tunda ba biki za'ayiba daurin aurena kawai kuma Abdul bashi bane angon kazalika ba waliyinta bane da har za'ace ajira warkewarsa,a yanzu an dawo dashi gida sabida likitoci basu gane komai ba,inda ake zargin asiri aka masa,momy dukta ya mutse ba itaba ba Elham ba,a haka ranar d'aurin aure tazo ba amarshi haka aka gangama daurin auren......Dangin Ibrahim kad'ai ake jira amma basu isoba,me martaba da kanshi yayi kiran sheikh Muhammad Adam,mahaifin Ibrahim amma abin mamaki se cewa yayi dashi+


"Ranka ya dade me martaba amin afuwar rashin kira,Allah yayiwa Ibrahim rasuwa yanzunnan,akan hanyar mu ta zuwa,kawai aman jini ya fara juyawar dazamuyi zuwa asibiti mafi kusa akace damu Allah ya karb'i abinsa,hankali nane ya d'auku dan Allah amana afuwa"

Innalillahi wa Innah ilaihirraji'un" itace Kalmar da me martaba ya furta,"Ina rokon Allah ya jikanshi dan rahamarsa,inshaa Allah gobe zamu zo" godiya ya masa sukayi sallama,koda me martaba ya sanarwa mutane se al'ajabi ya kamasu,mahaifin Hafsat ne yace,Dan Allah tunda anrigada an tara mutane kuma dama mijinta na farko ya buk'aci koma warta dan Allah a d'aura dashi,k'anin me martaba ne yayi zumut yace


"Da d'ina dakai Baba magadi haka iya had'iye kwad'a yinka,sarautar nan tunda ba gadar ta kayiba ai ka dena cusa jininka aciki ko?" Rayuwar me martaba ne yayi matukar b'aci dajin wannan zancen,mutane sun d'auki mutuwa ba'a bakin komaiba yanzunnan wani ya mutu amma basu da asara,lallai karshen duniya ne yazo,kallon Mahaifin Elham yayi yace "Ka wakilci ango nine wakilin Mamana" batare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren.....kamar saukar aradu haka Elham taji sanda labarin mutuwar Ibrahim ya riske ta, Kuka kam ta shashi,amma tarasa dalilin daya sanya bataji zafi ba da aka mayarda aurenta da Yaa Yarima,da ita akaje gaisuwa har garin abj,yan uwan Ibrahim se kuka sukeyi musamman daya kasance mutuwar huji'a ce kamar daga sama,sosai suka bata tausayi ba kadan ba.


   *Bayan sati d'aya*


Har akayi sati d'aya da d'aurin aure baisan inda kanshi yakeba,Elham kuwa duk tabi ta rame duk sanda aka barsu su biyu seta zauna tayita rusa uban kuka gani takeyi tamkar ze mutu ya barta ne,ranar wata alhamis ya fara kwara amai najini tamkar ranshi ze fita,ita kad'ai ce atare dashi tunawa tayi da yanda yan uwan Ibrahim ke bada labarin irin Amman dayazo masa nanjini nonstop kuma be tsayaba har sanda ya dauke sheda,rasa abinyi tayi da sauri taje ta d'auko alqur ani tafara karanta wa da k'arfi lokaci d'aya kuwa ya fara tsagaita aman,bata daka taba taci gaba da karatun sanda taga ya dena aman kwata kwata sannan ta ajiye alquranin tazo kusa dashi ta dafe k'irjinshi tafara tofa masa adu'o i kala kala na tsari,a hankali taga yana bud'e idonshi da sauri ta matsa kusa dashi tace "Sannu yaa Abdul ya jikinka?" Binta da ido yayi yana mata kallon rashin sani,adu'ar taci gaba da tofa masa har taga ya soma bacci cikin nutsuwar da tunda yafara wannan ciwon Bata gani a tare da shiba Mik'ewa tayi taje ta sanar da momy ta k'ara da cewar "momy me za'a hana akira malam uthman na meduguri se nakega abin kamar da iska aciki,dogon nazari momy tayi kan taje ta sanar wa me martaba,hakan kuwa akayi koda malamin yazo aljanai aka turowa Abdul a haka a haka akaso harya mutu,a binciken da malamin yayi wancen ma wanda ya mutu Wato Ibrahim shime same abune ya kashe shi kuma samu ne aka musu,amma Allah be bashi ikon gano wanda yayi wannan aikinba sedai ya bada adu'o I da kuma ruwan adu'a daze riqa sha kullum da du'oin da za'a masa dakuma wanda zena yiwa kanshi,Elham ce ta karb'i wayanda za'a na masa yayinda Abdul aka baiwa wayanda zeyiwa kanshi,gidansu aka maidasu na ainahin wanda tun farkon auren can suka fara zama.....


   Zaune yake tana bashi coffee abaki kasancewar har yanzu jikinshi be gama k'wariba yace yana kallon ta " Hafsat na gode sosai,na gode sosai Allah ya miki albarka,wlhy da baki dawo gareni ba nasani mutuwa zanyi" har Wannan lokacin hafsa bata gane komai ba game da son datakewa Abdul, kasancewar har gobe tanason faruk,wanna ya sanya ta sauya akalar  zancen


"Zakaci wani abinne?" Coffee dake hannunta ya karb'a ya a jiye sannan ya janyota jikinsa ya d'ago kanta ta fuskanceshi sannan yace "Ellyn yaa moris fushin ne haka har yanzu plss kiyi hakuri mana" k'uramasa ido kurun tayi batayi magana ba, batayi auneba taji bakinshi cikin nata taso sosai ta k'wace kanta amma ta kasa dole ta haqura,yafi minti biyu yana tsotsar bakinta,seda dan kanshi ya gaji ya saketa,da sauri ta sadda kanta k'asa sabida haka kurun taji wata kunya ta lullub'e ta,hannunshi yasa ya d'ago hab'arta yace yana Murmushi "Elham na kalle ni mana" duk'e kanta ta k'ara yi yana Murmushi yace "Kaddai kunya Elham na? Kiyi hakuri na dena miki I just couldn't take my ice off this fine lips of urs" batace komai ba ta tamik'e cikeda kunya ta bar wurin Murmushi yayi yana mamakin yanda yakewa Elham kallon wacce ta saba da maza amma wannan kiss kawai ta wani ji kunya Allah karya sanya zargin shi ya tabbata a kanta" zuwa tayi ta kwanta a bedroom nata,tarasa dalilin daya sanya ta kasa cire wannan moment d'in a ranta,da zaran ta tuna da yanayin da taji lokacin daya kama harshenta setaji wani Yarr har cikin ribs nata takejin wani feelings na shigarta,ba ita tabar cikin d'akin ba se la'asar kai tsaye kitchen ta wuce da sauri ta daura macaronie paper soup da beef souce, tana tsakiya da kwashewa yashigo bata saniba ta bayanta ya rungumeta ya daura hab'arsa sama wuyanta yace cikin wata siririyar murya "Elham na me kike girka mana,kika bar patient da yunwa har yamma Waike kunya ko? soon enough zanyi maganin wannan kunyar taki" kasa bashi ansa tayi ta lumshe ido ta bud'e su a hankali,janye jikinta tayi a hankali ta juyo amma bata bari sun had'a ido ba tace 'Kayi hakuri bacci ne ya sace ni" zagaye hannayenshi yayi a waist nata yace "Gwara daya dawo mun da Elham na,ba wanda ya isa ya sacemun ke" dariya maganar shi ta bata tayi Murmushi har hak'waranta suka bayyana gaba d'aya, d'an gyaran tsayuwa yayi still yana rik'e da waist nata yace "Elham na I'm hungry fa" hannayenta ta d'aura asaman nashi dake zagaye da waist nata ta langwab'e kai tace "To ka bani mintuna goma sha biyar yanzunnan zan kawo maka abincinka" saketa yayi ya juya bece ko maiba, a dining tayi serving nashi kuma tayi serving kanta,amma ga mamakinta yaqiyin koda loma d'aya ne da mamaki ta kalleshi duk yunwar dayake kira ya tasa abinci agaba yaqici


"Yaa Abdul mesa bakacin abincinka ko baka son wannan naje na girka ma wani daban" kamar wani k'ank'anin yaro haka ya shagwabe "Ni bazan iya ci da kaina bafa" wani takaicin shi taji ya kamata amma a zahiri setayi Murmushi tace


"Kona baka da kaina ne?" Murmushi yamata "Dama mana to waye ze bani?" Tasowa tayi ta zauna kujerar dake kusa dashi ta dinga ebar abincin tana bashi a baki cikeda nutsuwa dama mana maza ba kunya  yakuwa hankad'e yayi narkar abinshi sanda ya k'oshi sannan ta koma taci nata... Da dare bayan ta shirya cikin rigar bacci mara nauyi tazo ta sameshi yana adu'a Sosa kanta ta d'anyi ta tsaya sanda ya idar,tasowa yayi ha zauna a bakin gadon tace dashi


"Yaa Abdul ina so zanje na kwanta idan baka buqatar komai,na rigada na rufe ko ina na gidan" hannunshi ya saka ya janyota ta fad'a jikinshi kwantar da ita yayi akan gadon yaje daidai saitin kunnenta yace "Bana tunanin ina buqatar komai seke Elham na,yaya zaki tafi Kibarni ni kad'ai kin manta banida lapia?" Wani irin kasala ya saukar mata kasa cewa komai tayi har cikin b'argon ta takejin wani abu dabaza ta iya fassara ko meye ba,hannun shi yakai ya shafi mararta lokaci d'aya numfashin ta ya soma barazanar d'aukewa da sauri ta d'aura hannunta saman nashi se kuma ta soma kuka tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri" hancinshi ya saka a saman nata yana gogawa a hankali batare daya janye hannunshi a saman marar tata ba,ita ma kuma ta kasa d'auke nata,sannan ya kai bakinshi wurin kunnenta yace "Menene yake sakaki kuka Elham na? Bakyaso nake zuwa kusa dakene ko me?" Cikin kukan tace "Nidai Kayi hakuri tsoro nake ji" sakinta yayi yaje kashe fitilar d'akin ya d'are kan gadon,janyota yayi sosai jikinshi ya lalubo bakinta yafara kissing nata passionately, kasa tureshi tayi kurin dai bata dena kukan ba,seda yagaji dan kanshi sannan ya pulling out,yace cikin sigar rarrashi hannunshi na saman kanta "Elham na menene? Bakyaso?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,janyota sosai yayi ya rad'a mata a kunne

"To kiyi baccinki Na dena kinji,ko bakyason ki kwanta ajikin mijinki?" Banza ta masa yace "Ean Elham na bakyaso?" Cura fuskarta tayi acikin k'irjinshi duk da suna cikin duhu,cikeda shagwaba tace "To nidai ban ceba" Murmushi yayi ya k'ara k'ank'ameta a haka bacci me dad'in gaske yayi awon gaba da Dukkansu.Tun asuba ta farka taga baya nan,ga alama ma sallaci yaje ita d'inma sallah taje tayi,ta wuce kitchen kai tsaye ta d'aura musu egeg yam with beef paper soup, ba jimawa ta kammala ta hada masa coffee ita kuma ta had'a kayan tea nata ,a dining ta Jere komai ta wuce toilet kai tsaye tana idar wa ta fito ta shafe jikinta da mai tafara sanya sure spray follewed by body splash nata,ta bayanta ya rungumota ta na tsaye ajikin mirror d'in rufe idonta tayi jin saukar hannunshi saman breast nata, dukda a saman towel ne seda taji wani yarrrr,bata gane menene yake mata yawo a duk sanda ya rab'eta irin haka,jikinta ta janye da sauri ta sadda kanta k'asa,hannunta ya janyo ta dawo jikinshi ya manna mata hot kiss a wuya yace "Elham na,ina kika Shiga ina ta nemanki?" Murmushi tamasa


"Ina kitchen ne ina had'a breakfast"

"Dama yunwa ya addabeni oya saka kaya da sauri muje muyi break fast d'in" yaudai Hafsatu kasa koda motsi tayi bazata iya saka kaya a gabanshi ba,kallonta yayi ganin tayi tsaye ta sunkuyar dakai

"Bakiji ba nace ki shirya mu tafi ko" d'an ya tsanta ta saka a baki tace "Yaa Abdul ka bani wuri to mana,zan sameka a dining d'in" Murmushi yayi ya fice batare da yayi magana ba,yau ma sanda ta bashi abincin yaci sannan suka dawo parlor a saman cin yarta ya d'aura kanshi shi adole wai ga mara lapia, ita kuwa kunyarshi take ji matuka yanzu......


Tun da safe Hafsat ke fama da wani matsanan cin ciwon kai amma bata sanar masa ba da rana ma haka ta daure ta girka masu spaghetti da miyar Hanta kurun se ice tea, zuwa yamma kam Hafsat jiki ya tsananta domin kuwa kasa yin girki tayi,Shikuwa baya gidan yaje ya gaisa da mahaifanshi kasancewar jikinshi yayi k'wari.....sosai momy taji dad'in ganinshi agidan Ras da shi tace


"Mamana fa? Ina fatar tana lapia?" D'an Sosa kunne yayi yace "Tana nan lapia lau momy tace ma na gaidaki ai" Murmushi tayi "To Babana kadaiji tsoron Allah ka kula da yar mutane tsakanin ka da Allah dan Allah na rokeka karka kuskura ka wula kanta musu 'ya,sunmaka halacci sosai"

"Inshaa Allah momy zan kiyaye komai da kika ce zan kula da ita" al Barka ta zabga masa ya tashi ya fita......Koda ya dawo Elham bata parlor kuma yaje kitchen bata nan,kai tsaye bedroom nata wuce ya tarar ta k'udundune a bargo se rawar sanyi takeyi,da sauri ya Hau saman gadon ya d'an yaye duvet d'in

"Hafsat lapia dai meya sameki?" Kasa bashi ansa tayi kurin dai taci gaba da zubar da zafafan hawaye,dagota yayi ya d'aura ta saman cinyarshi yaji jikinta zafi rau "Hafsat plss Sanar dani meyake damunki haka,jikinki zafi fa sosai" dak'yar ta iya cewa "Kainane yakemun masifar ciwo sarawa yakeyi tamkar ze rab'e gida biyu" kan ya kama yaji zafi rau yace "subhanallah Elly tashi muje asibiti,bazan barki gida da zazzabi haka ba gaskia" kasa cewa dashi komai tayi da kanshi ya saka mata doguwar riga ya kinkimeta se asibiti, zazzab'in cizon sauro ne ke damunta aka mata aluurai aka bata magunguna suka dawo gida abinsu,salar isha ma dak'yar tayi tayita ya samu tasha tea kawai suka koma d'aki suka kwanta,janyota sosai ajikinshi ya rungumeta yanata rarrashi nta se hawaye kurun takeyi sabida ita kad'ai tasan yanda kanta ke masifar Sara mata,har bacci ya d'aukeshi ita bata rutsa ba,can Wuraren karfe ukun dare kukanta ya tasheshi,"Hafsat har yanzu kanne?" Cikin kuka tace "yaa Abdul dan Allah ka k'ananun kaina ciwo yakemun sosai wlhy,kuma ka matsamun k'afana suma suna mun nauyi saramun komai yakeyi" haka ya tashi yamata kamun kai yashiga mata tausa sosai har jikinta ya sauka atake ta fara had'a gumi se bacci me nauyi yayi awon gaba da ita,adu'a yashiga yi mata seda yaji ana kiran Sallar asuba sannan fa yaje yayi alwala a d'akin yayi sallah sannan yaje ya soya kwai da plantain ya hada ruwan zafi,koda ya dawo d'akin ta farka amma bata tashi ba,hawa saman gadon yayi ya tab'a jikinta yaji ba zafi "Sannu Hafsat Kindai ji sauqi ko?" Murmushi ta sakar masa tace


"Naji sauki sosai,amma daga kwance ina ganin jiri"

"So nake namiki wanka sekici breakfast naki" zaro ido tayi waje tace "Allah ni zanyi da kaina" cikeda shagwab'a tayi wannan furucin har tana shura k'afa,be tsaya wani gaddama da itaba ya fara cire mata kaya jikinta yanayin yanda take jujjuya jikinta ne yafi tafiya da imaninsa tsirara ya mata sannan ya d'aga ta cak ya nufi ban d'akin da ita,acikin bahon wankan ya tsunduma ta ya sab'e ta tatas,se sussune kanta takeyi,da kanshi ya Shafa mata mai ya saka mata kaya ya daga ta se dining,shine ya bata abincin sanda ta k'oshi sannan ya ci Nasa,bayan sun dawo parlor se tausa yake mata tun tana lumshe ido har bacci b'arawo ya saceta se farkawa tayi ta ganta a cikin faffad'an girjinshi me cike da gargasa suna baccin a tare,kasa motsi tayi karta tada shi ta koma ta kwanta.....


*Bayan sati Biyu*

Jikin hafsat ya tsananta matuka,tasha maganin malaria kala kala amma duk a banza ciwon kai ne ya sakata a gaba babu k'auk'utawa,ganin haka momy ta kaita private hospital, duk ta rame tayi bak'i sabida azabar ciwon kai ko idonta bata iya d'agawa gwajin farko suka gano tana d'auke da cikin sati uku!!!!!! Agaban momy suka zo sukace da Abdul"Congratulations sir,ur wife is 3 weeks pregnant, Baza kuga daidai ajikinta ba se ta wuce trimester d'inta so se hakuri zamu bata magungunan dazasu taima kawa ita kanta da cikin dake jikinta" mutuwar tsaye Abdul yayi dagashi had Elham d'in yayinda momy se murna takeyi 'yarta nada ciki,Zata samu jika dama gashi feenah haryau shiru!!!!!!! Kai tsaye gidansu yace a amai dasu ze kula da ita,hakan kuwa akayi can aka sau kesu, Elham har lokacin kuka takeyi magungunan da aka bata ma watsar wa tayi, tarasa Inda Zata saka rayuwarta taji sauqi,a take ma taji ta tsani kanta tama kasa tunanin daya dace tayi, a d'akinshi taje ta taraddashi a zaune tana kuka ta duqa kusa dashi tace


"Yaa Abdul wlhy summa tallahi ka yarda dani ba namijin daya tab'a sanina a 'ya mace,dan Allah Kayi hakuri" wata muguwar harara ya fara sakar mata sannan yace "A ruwa kika sha cikin dan kutmar uba? Wannan shine sakayyar soyayyar danake miki Hafsat? K'iyayyar daki kemun har takai matsayin da Zakije kiyi zina da aurena akanki? Wato sanda aka daura auren mu banida lapiya maza kikaje kina bi ko? Dukdan sabida bakya sona,cikinki sati uku ya nnuna cewar kinada igiyoyina akanki kikaje kina watsewarki da wanina,Allah ya isa ban yafe miki ba wlhy" kukan tane ya tsananta tace murya na rawa


"Wlhy na rantse maka yaa Abdul bansan komai ba game da wannan cikin,ban tab'a aikata zinaba tun ina gidanmu balanta na kuma da aurena" shaqo wuyanta yayi yace "Baki tab'a zinaba a ina kika samo wannan d'an shegen? Wlhy Sekin sanar mun waye ubansa,sabida kinsan bazan iya gayawa momy da duniya abinda Ki kayiba shine yasanya kika zabi tozartar dani har haka Elham?" Sakinta yayi ta fadi cikin d'acin rai ya soma kukan shima,yana sambatu


"Wlhy Hafsat ina masifar sanki,mutuwa zanyi idan ban rayu dakeba amma ya zanyi da wannan bak'in cikin da kika sakani? Allah ya isa wlhy bazan tab'a yafe miki ba" da gudu tabar sashinsa tana rusa uban kuka....


*Bayan sati uku*

Hafsat har wannan lokacin bata samu lapiya ba,ciwon kai yaqi ci yaqi cinyewa,gashi batashan koda paracetamol ne,ta d'auki damuwa me tsanani ta saka a ranta,a d'akinta yashigo ya sameta tana aikin kukan data saba,kusan kwana ki biyu bata ganinshi,zama yayi kusa da ita yace "Hafsat ki sassauta wa rayuwar ki wannan kukan dakikeyi dazaki sanar dani waye uban d'annan data fiye miki" cikin d'acin rai ta d'ago ta kalleshi tace "shed'an shine uban d'annan ni banida bakin dazan iya kare kaina dashi awurinka amma ina rokonka dan Allah karka ce zakayi ta shan giya yanda naga kanayi wlhy zaka illata Lapiyar ka ne yaa Abdul,nfa daka gannin nan wlhy mutuwa zanyi,babu wanda ze yadda dani to meye amfanin rayuwata a yanzu?" K'ura mata ido yayi na y'an dak'ik'u kan ya tashi yabar wurin gaba daya..... A buge yashigo cikin gidan yana tafe yana maye,tareshi tayi tace dashi

"Yaa Abdul wai dan Allah bazaka dena shan giyar nan haka nan ba? Haramun ne fa,kuma sarai ka sani wlhy" wanketa yayi da wani kyakyawan mari sannan ya Hau jibgarta baji Ba gani,tun tana iya motsi harta kasa,shurinta yakeyi tamkar ba gobe,dukya fasa mata baki da hanci se jini sukeyi sanda ya gaji sannan ya qyaleta ya wuce d'akinshi.... Dakyar ta rarrafa d'akinta takira momy,tana dagawa tace da ita


"Momy dan Allah Kizo ki taimakeni yaa Abdul ze kashe ni?" Cikin rudu momy tace "ze kashe ki kamarya Elham?" Tana k'ok'arin yin magana kawai taji bata iya numfashi Athma d'inta ya taso mata gadan gadan,anan ta zube a sume....Dashi suka fara cin ka fito daga bed room d'inshi cikin halin maye,cikeda rud'u tace dashi "kai Babana Lapiyar ka kuwa? Meka wa yar mutane kuma meye haka kamar wanda yasha giya" dariya yayi irinta wanda yasha ya bugu yace "Momy ke bakya ganine Yarinyar nan tunda na aureta ban taba kwanciyar aure da itaba,yama za'ayi tace wai tana da ciki uban waye ma uban d'an?" Momy bata gare inda ya dosa ba,ta d'aura maganga nunshi a mizanin wanda yake cikin maye,tasan yanashan giya amma sam batayi tsamanin har yanzu be dena ba,wuceshi tai zuwa d'akin Elham acan ta tadda ta bata numfashi,aikam kinki mota tayi zuwa mota,ado driver yaja suka tai bata k'ara komawa takan Abdul ba abin duniya ya isheta yaronta ya daura aure da giya kuma kana kallon Elham kasan cewar dukan tsiya tasha abinma da kunya taje tana fada, A asibitin data kaita farko yauma can suka nufa,da sauri suka k'arbeta daura mata oxygen sukayi sanda ta farfado sannan suka bata test kala kala,ganin yanda duk tayi rama,bin cikensu ya nuna masu cewar typhoid ce tayi mata mummunan kamu,kuma itace take sakata wannan ciwon kan me tsanani,magunguna suka rubuta,suna zuwa zasu bata momy ta dakatar da doctor d'in tace


"Dr magungunan nan basu mata k'arfi ba kuwa naga cikin nata beje ko ina ba k'arami ne" da mamaki doctor d'in ya kalleta yace "Ai dukkanin test sanda mukayi da muka dauki sample na blood nata,batada ciki fa" wani kallo da bazaka fassara wane iri bane momy tawa doctor din "wane irin zance ne wanan doctor sid? Baku bane last week bin ci kenku ya nuna tana da cikin sati uku?" Mik'ewa tsayi yayi ya duba file d'inta,abinda ya fad'o masa arai shine case dasuka gama solving jiya jiyannan akan wata Hafsat Elham Hashim, dafe kanshi yayi yamayar da dubanshi zuwaga khabbab yace "Dr khabbab I think she's the one,zo kaga sunan Hafsat Elham Hashim" matsowa Dr yayi yace "off course she's the one" mayarda dubanshi yayi zuwaga momy yace


"Yaune muke shirin bin bayanku ta hanyar address dinku kasancewar tun jiya muke kiran wayar mijinta bama samu,wlhy wrong result aka baku,an samu kuskuren sunane yazo iri d'aya sak dana wata ita tana fama da matsalar ciki yayinda wannan ke fama da typhoid a matakinta na karshe a cutar da mutum,kunsan nan asibitin private ne lab d'inmu d'ayane dan Allah Kuyi mana afuwa,ita kanta waccen wlhy zuwa akayi da ita ta samu miscarriage seda mukayi bincike muka gano cewar magungunan typhoid ne suka mata nauyi,dan Allah kumana afuwa,ita d'inma se jiya tazo,kuma muna ganewa mu kaita neman layin mijin wannan amma be jeba" kuka Hafsat ta saka jin wannan maganar wanda shi ya hana momy zazzagawa drs d'in masifa iya son ranta,ta juyo ta rungume Hafsat tace "kiyi hakuri Hafsat inshaa Allah zaki samu wani me albarka" momy batasan Hafsat kukan dad'i takeyiba Allah ya wanketa,amma bata ce da ita komaiba,anan asibitin ta kwana yayinda momy ta koma gida ta Turo kanwar Hafsat d'in domin ta zauna da ita a asibitin.....da safe da kanta tayi kiran Abdul yaje ya sameta gida,cikeda nutsuwa ta kalleshi sannan ta kurb'i fresh milk dake hannunta tace


"Babana na sani yaqi da rayuwa abune me matukar wahala amma shin kanada tabbacin wannan abin daka d'aukar wa kanka shine mafita? Baka ganin cewar idan kana sab'awa ubangijin ka har haka baze karb'i adu'ar kaba,kaida nake kallon Kaine zaka kawo sauyi a wannan masarautar shine zaka b'ige da aikata wannan mummunan barnar to Babana bazan maka fad'aba Nasiha ce nake maka akan kaji tsoron Allah abu na gaba kuma shine ina so ka d'auki k'addara,matarka daka narkewa k'oshi tana asibiti a kwance batada lapia typhoid ne ya matukar ci zarafin ta,wannan cikin damukewa murna da d'auki Ashe batada ciki,mistk din result din sukayi,suka bamu na wata Hafsat daban banita kasance war sure name nasu da sunan yazo iri d'aya,ita kuwa waccen suka bata na Hafsat wanda magungunan sukayi sanadiyar barar ma waccen baiwar Allah da ciki,anbata magungunan typhoid alhalin ciki ne da ita,kuma sse jiya suka sani,suce sunyita neman wayarka basu samu ba sunso sanar maka tun jiya" da sauri ya d'ago ya kalleta,lokaci d'aya k'irjinshi ya bala'in dokawa idonshi suka sauya launi zuwa ja sosai,ita uwa jin yayi shiru ta qara da cewar

."Abu na karshe da zan fad'a maka shine ko bayan Hafsat idan ka k'ara auren wata mata nan gaba ban yafe maka ba idan har ka daketa,karka kuma dukan mace wannan haline na la'antattun maza be kama cekaba wlhy ko kad'an se'a kiyaye,maza katashi kaje ka dubata ga abincin su can na break fast ka wuce musu dashi " kasa magana yayi sam, a haka ya mik'e jiki ba k'wari yabar gidan koda ya Shiga mota zama yayi ya dinga tariyo zan tuttukan momy se kurun ya fashe da kuka sanda yayi me isarsa sannan ya zaro wayarsa yakira zayyan, fayyace masa komai yayi ya qara da cewar "Zayyan ya zanyi? Wlhy masifar kunyar Elham nakeji na rasa meke damun kaina,mesa Banyi tunanin kaita wani asibitin ba,mesa kuma ban yadda da itaba sanda take ta mun ranstuwa? Yanzu yaya zanyi ina zan tsoma rayuwata? Da wane ido zan kalleta?" Nisawa zayyan yayi


STORY CONTINUES BELOW

"Lallai wanna al'amarin akwai rud'u a cikinsa watak'il dabaka biyewa wannan bak'ar zuciyar takaba da tun a wancan lokacin kun cimma mafita,ni banida abinda zance maka yanzu,kawai dai ka bata hakuri Allah hasa Zata hakuran dts all" godiya yayiwa Zayyan ya kama hanyar asibitin,gwiwa a sab'ule ya Shiga d'akin da sallamar sa,sister d'in ta gaidashi ya ansata yaje ya zauna yace da Elham


"Sannu Elham ya jikinki?" D'auke kanta tayi daga dubanshi gaba d'aya ta mayarda dubanta zuwaga d'ayan b'arin daban,lokaci d'aya hawaye masu d'imi suka gangaro daga idonta,Kallonta Asiya yayi yace "Asiya ko Zakije gida ne kiyi wanka ki dawo sena zauna da ita" bata masa musuba ta mik'e yace "ungo ki Hau adaidaita kinji" dubu d'aya ya bata ta k'arba ta wuce......tashi yayi yaje ya zauna a saman gadon da take ya riqo hannayenta duka biyu da sauri ta warce abinta har wani azaba taji a d'ayan hannunta me cannula, muryarshi na rawa yace

"I knw I have wronged u Elham,but could u plss find a place in ur heart to forgive me? Wlhy wannan kuskure aka samu nasani ban kyauta ba daban zurfafa bincike ba amma kema kin sani akwai rud'u dan Allah kiyi hakuri my life partner" yanda ta rufe idonta harya k'araci maganarsa bata bud'esu ba,yafi awa d'aya yana bafa hakuri amma fir yaqi ce masa koda ci kanka,abinci ma yayi juyin duniyarnan taci amma taqi dukya bi ya rud'e matuk'a kuka kurun ya saka mata,har aka kira azahar shi da itane kurun a d'akin,momy ce dasu feenah sukayi sallama sukazo kallon shi momy tayi


"Babana badai kana nufin cewar sabida kawai angano Ba Hafsat bace da cikin shine ka sakata agaba kana dirzar kuka,wannan wane irin haline wai? Su wayancen da k'addarar rashin yaronsu ta afka musu sabida rashin bada result daidai suce me? Sekai da bawai cikin bane ya zube dama babu shi? Dudu yaushe akayi aurenku ? Kasan tsarin Allah akanku? Danla ni matsa ka bani wuri ka wani zo haye gadon tamkar zaka maidata ciki" bece komai ba yatashi ya zauna akan k'aramar sallayar dake d'akin,se yamma su momy suka tafi.....


Sanda Hafsat tayi kwana biyar sannan akayi discharging nata,har aka sallameta bata kulashi,kullum Awurinta yake wuni amma harya k'araci surutunshi da ban hakuri bata cewa dashi ci kanka,koda aka sallameta yace zasu wuce gida kuka ta saka ita lallai momy zatabi seta k'ara jin sauqi,hakan kuwa akayi momy ta wuce da ita gidan su.......


A d'akin momy bayan yan dubiya sun watse dare yayi momy ta kalli Hafsat tace "Mamana don Allah sanar dani menene ya had'aki da Babana harta kai ga duka,dukda na ganshi acikin halina maye sanda naje gidan" Murmushi ta kakalo sannan tace "Ba komai momy".

" kinga Hafsat tun kina k'ara marki nake tare dake I knw very wen ur telling the Truth,Karki mun k'arya sanar dani gaskiyar komai" se kawai ta saka kuka,kyar momy ta lallasheta tayi shiru,sannan tace


"Dama fa momy ni tunda mukayi aure da Yaa Yarima ba abinda ya tab'a Shiga tsakanina dashi na auratayya shine kawai akace inada ciki.....daga nan kuma kuka ya k'wace mata,dak'yar ya tsagaita ta kwashe komai ta gayawa momy, nisawa momy tace " wannan abu kam sam beyi dad'i ba kuma Yarima ya tafka kuskure sabida komai yanada buqatar bincike,yayinda ke kuwa kikayi zurfin ciki,ai kamata yayi tun a asibiti kiyi magana semu k'arayin test kinga kin wanke wa kowa zargi amma ta yaya zamu gane gaskiyar lamarin bayan kinyi shiru? Kinga mijin kima zaton zeyi kin aikata ba saidai ba,amma shd'inma ya rafka kuskure sabida a yanda kike d'innan ni kaina zan iya shedarki,kiyi hakuri ki dena kuka kuma ki koma gidan mijinki ki yarda haka Allah ya tsaro miki taki rayuwar,kuma karkiji kunyar duk wani abu dazan gaya miki yanzu danake taqama dasu ake cewa na asirce mijina na hanashi aure.....sosai momy ta zayyane mata komai na yanda Zata kula da mijinta se sussune kanta takeyi.


washe ta kira Abdul ta zazzaga masa wandon masifa sannan daga bisani ta had'asu duka tamusu Nasiha sannan ta hanesu gayawa wani wannan zancen kana sukaje suka gaisa da mahaifiyar Elham Abdul yamusu shatara na arziqi sannan wuce gida....


Love wan tintin...


Ranar gaba d'aya Abdul kasa nutsuwa yayi shi harga Allah so yake ya angwance da matarsa,sallah ya saka sukayi sannan sukayi shirin kwanciya,Elham duk wani d'ari d'ari takeyi da Abdul,kallonta yayi ta wani takure a hijab yace


"Yan matan moris yau baza'a mun kwalli yar bacci bane?" Tafukan hannayen ta saka ta rufe fuskarta sannan a shagwab'e tace "yaa Abdul nifa sam banajin bacci wlhy" Murmushi yayi yace aranshi ina ganin Yarinyar ta tsorata dani barin barta harta saba da wasanni na"

"To muje parlor muyi kallo mana ehn" yafad'a yana kallonta da alamar wasa


"To muje mana" Tafad'a bayan ta mik'e tsaye...takowa yayi yace yana k'ok'arin cire mata hijab "shi kuma wannan hijab d'in fa, kishiya tane?" Wani narkewa tayi Tafad'a jikinshi tana buga qafa a qasa cikeda shagwaba "Allah ni yaa Abdul karka cire mun bafa komai a jikina" sosai ta sungume hankalinshi sukayi habuja,d'aga hijab d'in nata yayi ya cura hannunshi ciki ya d'aura a saman waist nata,wani Yarr taji lokaci d'aya ta lumshe ido,hannunshi yasa ya zare hijab d'in wasu hatsabiban kayan bacci ya gani a jikinta riga k'arama da guntun wando Heeps d'innan sun zauna cas dasu ga dukiyar fulanin nan sun ciko sunyi sama,kasa d'auke dubanshi yayi daga nonuwanta, jefar da hijab d'in yayi ya riqo k'ugunta da kyau tazo jikinshi yakai bakinshi asaman breast d'in yabasu hot kiss wanda atake ya bata kunya,ta rufe idonta Shafa gashin kanta yayi yace

"Haba y'an matan yaa moris ya zaki b'oye mun wannan kyakyawar shigar,ina ni Ki kayiwa? " sadda kanta tayi qasa tana Murmushi daga nan ya sanya hannunshi ya dagata cak zuwa parlor,a saman cinyarshi yayi mata matashin kai,ya cura hannunshi a cikin gashin kanta yana mata tafiyar tsutsa,gaba d'aya ya gama kashe mata jiki se lumshe ido takeyi a haka har bacci ya sureta.....mamakine ya kamata ganinta ajikinshi kuma ga haske ya mamaye d'akin alamar gari ya waye sannan dukkaninsu ba kaya ajikinsu,da sauri ta lalubo duvet ta rufe jikinta,wannan zaburar datayi ne ya farkar dashi,rufe idonta tayi ganin shiko ajikinshi be damu ta ganshi a hakaba,matsawa yayi daf da ita ya rungumota yace "Ke kintashi shine bazaki tashi kiyi salla ba,nifa tun asuba nayi sallah na" cikeda shagwab'a tace har lokacin idonta a rufe yake "shine ni baka tashe niba?" Murmushi yayi yace "ked'ince dason jikin tsiya kin kama kin wani qanqameni sekace za'a sace miki ni,dak'yar na samu na zare jikina kuma ma Aina tashe ki so biyu kene baki tashi ba" cura fuskar ta tayi a k'irjinshi cikeda kunya domin batasan me tayi ba acikin bacci,kamar zatayi kuka tace "shine kuma ka cire mun kaya nika tashi zanyi sallah ne" matse bakinta yayi yace "Zakiyi sallah d'in sena tashi,Kedai zaki tashi kije kiyi alwala rana na kallonki sakiyi salla" maqe kafad'a tayi "yaa Abdul bafa kaya ajikina dan Allah ka fita sena saka" bushewa yayi da dariya yace "kinga yan mata kayanki ma yana parlor naga kinata had'a gumi Shiyasa na ciresu,barima kiga" zare duvet din yayi ya sungumeta be dire ta ba se ban d'aki se yarfe k'afafuwanta takeyi tana shagwaba ga idonta a rufe ruf.....shi se dari yarta yakeyi kun yarta na bashi mamaki da dariya...

Sanda ya wanke ta tatas sannan ya barta tayi alwala,ta dauro towel ta fito se wani kunya takeji a haka ta zura jallabiya tayi sallah,kai tsaye kitchen ta wuce ta musu samosa bread da spaghetti bolognese ta had'a masa coffee sannan ta dawo d'aki light makeup tasaka sannan ta sanya less ruwan Zuma ta murza d'auri ta feshe jikinta da turaruka sannan ta fito kai tsaye d'ankinsa ta wuce,a gaban mirror ta sameshi yana taje sumar kanshi,d'auke kanta tayi daga dubanshi sannan a hankali tace "Yaa Abdul Barka da kwana" ajiye brush d'in yayi ya juyo yana Murmushi sosai ya mata kyau,Sanye yake da jeans black da rigar sa asalin fara qal kirar kamfanin mk ya dirza agogon gold a hannunshi se tashin k'amshi yakeyi,matsowa yayi kusa da ita ya rungumo ta jikinshi sannan ya kalli kyakyawar fuskarta yace "Blossom kullum k'ara kyau kikeyi,narasa wane kalar kaya ne yafi miki kyau,kinga idan kika saka k'ananun kaya seki fito kamar wata baturiya,idan kuma kika saka Jallabiya seki dawomun balarabiya sak idan kuma kika saka kayanmu na hausawa sena kasa wai hausa Fulani nake gani kokuma kanuri" tsura masa ido tayi harya gama wannan rattaben sannan a hankali ta sauke idonta k'asa tace
"Yaa Abdul breakfast is ready" hannunshi ya saka ya d'ago hab'arta yace "Blossom bakya san kallona,har yanzu fushin kike dani?" Batayi magana ba Murmushi kurin tayi be saki hab'ar tata ba yace "Blossom dan Allah kiyi hakuri komai ya wuce Allah bana cikin nutsuwa ganin wannan halin da kike ciki,kalli fa na miki kwalliya bakice namiki kyau ba ko sabida ban saka takalmi bane?" Dariya ta masa har haqwaran ta suka bayyana tace "Kayi kyau mana yaa Yarima nifa dana shigo banma gane kaba,na Zata wani balarabe ne Ashe miji nane?" Dariya yayi yace+

"Kin iya tsoka na faa blossom, kuma kinga nifa bana so kike laqabamun wani yaa Yarima yaa Abdul, ki sama mun suna me dad'i daza kina riqa kira na dashi" Murmushi tayi sosai tace " yaa Abdul ni bansan me zan ce ba fa,wane suna kake so na kiraka dashi"
"Kece da kanki zaki nemo nima ban saniba" dariyar dai tamasa "Muje kaci breakfast mana" bece komai ba ya saqala hannunshi a nata suka wuce,shine da kanshi ya bata taci sannan yaci,daga nan suka dawo parlor suna kallon wani film na hausa.

      Da dare ma wanka tayi ta caba kwalliya cikin doguwar rigar dress red color bata saka d'an kwaliba tufke kanta kurun tayi da Jan ribon,bayan ta gama dafa musu tuwon semo da had'addiyar miyar egusi taji ganda kifi da nama,se tashin k'amshi takeyi ta had'a mu sugar cane and lemon zest drink se tashin k'amshin dadi yakeyi,lomar sa ta farko ya lumshe ido yace "Blossom idan kinsan irin wannan dad'in zaki riqa girka wa ki dena kawoni dining kurun ki ajiyeni a qasa,idan ba haka ba kuwa Allah fad'owa zanyi " sosai maganarshi ta bata dariya,dariyar kuwa tashiga yi har tana riqe ciki,shi kuwa yana dariyar yana kallonta ba k'aramin burgeshi takeyi ba tana dariyar,sanda yace "Au dariya ma kike mun,zan rama ne nine zan mana lunch Allah idan kika kuskura kikaci daddad'an girkina sumewa kurin zakiyi" dariya ya qara bata jin zancensa aikam tafara mar dariya har tana durqushewa take lomar datakai bakinta ya sarqeta nan take ta soma tari ba k'ak'autawa idonta yayi jajir,tasowa yayi ya tallafeta yana bata ruwa dak'yar ta samu ya tsaya mana,ama abin da ya bashi haushi still suna cin abinci tana masa dariya kuma taqi magana

"Blossom dama haka kike da dariyar k'eta? Allah yau zan shayar dake mamaki zaki tabbatar sunana Mr.chef" tana dariyar tace "Tom yau kuwa zanga Mr. chef meze dafa mana" Murmushi yayi yace

"Shawarma da hand sandwiches zan miki plus mango and milk shake,yau d'innan zan tabbatar miki ban zauna turai a banza ba" dariyar taci gaba dayi "idan ina bacci na karka tasheni se idan ka tabbatar ka kammala mana lunch" shidai banza ya mata,daganan zuka wuce bed room bacci....... Ba ita ta farka ba se Wuraren karfe d'aya sallah tayi tawuce parlor kai tsaye se sauri takeyi tamakara girki a tunaninta wasa Abdul keyi,aikam tana zuwa kitchen ta tarar yama kammala girka komai se tashin k'amshi gidan keyi, Juyowa yagi ya wara hannayenshi yace "common sleeping beauty" Murmushi tamasa amma kunya ta hanata k'ara sawa jikinshi dakanshi ya tako yazo ya rungumeta,ya rad'a mata a kunne "Blossom nagama fa,yau zakici best girki ever" Murmushi tamasa kurun seta tsinci kanta da lafewa ajikinshi ta saka hannayenta bayan waist nashi "Yaa Yarima I'm so hungry" Tafad'a har tana doka k'afanta a k'asa cikeda shagwab'a, d'ago habarta yayi da hannunshi yace "Look blossom taimako d'aya zaki mun ki bani 15 mnt nayi sallah ke kuma ki had'a table kinji" Murmushi tamasa tace

STORY CONTINUES BELOW

"Alright u go and pray and I will set d table" sakinta yayi bayan ya manna mata kiss a kumatu yabar kitchen din.....mamakine ya kamata ganin yanda ya had'a Shawarma da hand sandwiches d'in ga kuma mango and milk shake a manyan cups guda 4 saka biyu tayi fridge sannan ta gyara sauran a dining, kan ya fito kuma taje tayi wanka da ruwan miski ta feshe jikinta da manya manyan turaruka ta saka doguwar rigar jallabiya kalar wine color ta d'aura d'an kwalin ta kalar sararin samaniya tayi kyau matuk'a,a yanga ce take tafiya harta iso dining d'in k'amshin turaren ta ne ya sanar masa da zuwanta, da sauri ya  juyo lokaci d'aya ya mik'e yaje ya rungumeta sauke ajiyar zuciya yayi yace a hankali "blossom kina kashe ni da wannan wankan naki me d'aukar hankali,wlhy ki yarda dani lada kike samu kuma ina matukar jin dad'in haka,k'amshin turarenki banajin kalarshi ko ina se a wurinki sanar sani Wanne irine zanje nawa CEO na campanin babbar kyauta" Murmushin ta me sanyi tamasa,sannan cikeda shagwaba tace "Yaa Abdul zanji shawarma yawuna se tsinkewa yakeyi" saketa yayi yana dariya "yanzunnan sekice zaki mun kuka,muje na Kici" bata masa musuba kurun sukaje sanda taci guda biyu sannan taci sandwiches d'in ta shanye mango and milk shake duka sannan tace

"Man wane shop ka siyo Wannan shawarmar? Murmushi yayi yace " Moris Shawarma shop" kwashe wa tayi da dariya sannan yace "ki shirya da yamma zamuje yawo kinji" A green color suka je yawo se hirar su suke suna dariya,tana ganin Shawarma tace Zata ci,yace "Blossom ki bari Kici wani abun daban da akwai agida fa" maqe kafad'a tayi "Noo ni wannan zanci yanzu idan kuma naje gida Senayi warming wancen naci"  aikam koda ta fara ci setace bataso wai nashi yafi dad'i, sanda suka gama shan iskar duniya gab da magrib zuga biya ice cream shop suka siya sannan suka wuce gida direct.....

    Bayan sallar isha,suka dawo parlor suna hira abinsu,Elham ta saka wani wando iya cin yarta sannan kuma ga bingilalliyar riga gashi batada bra niples nata sun gama tayarwa gogan da hankali, gashi ta baje yalwa  taciyar sumarta se tashin kamshi takeyi,kasa hakuri yayi ya dawo kusa da ita,hannunshi ya sanya ya janyota ta kwanta a saman k'irjinshi ya cura hannunshi acikin sumarta yana mata wasa dashi a hankali,kasa hanashi tayi zuwa wannan lokacin idan ba cikin jikinshi tajita ba batajin daidai,yau d'in ma bacci taketa so tayi har goma ta gota amma a yan kwanaki biyunnan ta soma sabawa da kwanciya a jikinshi seta kasa,ganin zatayi bacci a haka ya sanya ya sauketa yaje ya rife ko ina yazo parlor ya kashe kayan kallo ya dagata se bedroom nasa....Kwantar da ita yayi bayan ya kashe fitinar d'akin lokaci d'aya ya sanya hannun shi ya zare mata guntun wando,gaban tane ya fad'i tace murya na rawa "yaa Abdul dan Allah ka dena" bakinshi yakai daidai kunnerigarnan  "Haba blossom bakyason kiji dad'in bacci,kayan nan taku raki kurun zeyi" ta bud'e baki Zata magana ya cura bakinci a nata harshenta ya janyo ya dinga tsotsa tamkar ze tsinkashi yakai minti biyar yana saukar mata da kasala sannan ya janye bakinshi daga nata yace "Ki tashi zaune mana ki cire rigarnan na sakaki a jikina kiyi bacci" cikeda shagwab'a tace "yaa Abdul ni ka bani wandona plss" hannunshi ya d'aura aka lips nashi yace "shhhhhhh blossom bana san gadda ma fa" shura k'afa tasoma yi cikeda shagwab'a "yaa Abdul dan Allah fa" cikin y'ar tsawa kad'an yace "Blossom if there say a word again I will slap you fa,just sit down and raise up ur hands" tashi tayi zaune tana kallonshi acikin wannan d'an hasken na deem light,zunb'uro baki tayi tana yamutsa fuska ta daga hannunbya zare yar muna fukar rigar dake jikinta,gaba d'aya kunya ce ta gama da matsalar ta musamman dataga yana cire kayanshi mayarda idonta tayi ta rufe,sannan ta kwanta rigingina cikeda kunya, kashe deem light d'in yayi sannan batare da tayi auneba taji lallausan harshensa da lips d'inshi a saman breast d'inta,d'imau cewa  tayi gashi lokaci d'aya ya saukar mata da kasala wani irin masifaffen dad'i ne ya ziyarceta da bazata iya fasssara yanda take jinshi ba wani abune yake fizgarta tun daga kan d'an yatsanta na k'afa har saman kanta,dak'yar ta iya bud'e bakinta tace "Yaa Abdul zaka kashe ni" sake mata breast d'in yayi ya matso da kanshi wurin kunnenta yace "Kashe ki kuma blossom dame zan kashe ki?" Cikeda rad'a yace haka mik'a tayi daba tasan dalilin taba tace "Dan Allah kadaina mun magana a kunne" be kula taba ya kuma kai bakinshi wuyanta yarfe hannayenta tayi duka biyu tace "Nashiga uku" nanma be kula taba yaci gaba da lasarta dukta inda yaso Elham,se murk'ususu takeyi tarasa dalilin dayasa ta nemi nutsuwar ta ta rasa, bakinshi ya kuma kaiwa kan breast dinta ya dan na musu kyakyawar tsotsa lokaci d'aya numfashin ta yafara up and down,d'ayan hannunshi kuma ya d'aura asaman d'ayan breast d'in ba shiri ta d'aura hannunta saman kanshi tana Shafa, Allah Sarki Abdul cikeda k'warewa ya sarrafa Elham da wasanni masu sanya nishad'i dajin dad'i mara misaltuwa,a hankali yazo ze saukewa kanshi wahala kuma yar garin bata yi masa musu ba,lapiya lau be cutar da ita ba cikeda sanin darajar 'ya mace ya kuma duba kasancewar ta k'aramar yarinya ya lallab'a abarsa har ya cimma burinsa,sedai fa yasha raki Elly kuka tayita masa tana magiya,koda ya dawo nutsuwarsa albarka ya d'inga zuba mata,ganin ya sameta cikakkiyar mace me gard'in gaske,koda ya haske d'akin da fitila rufe fuskarta tayi da tafukan hannayenta,ganin duk ya b'ata wurin da jini ya sanya ya d'aura towel ya zauna yace
"Hafsatul Elham ina roqon Allah yayi miki albarka ba adadi,Allah ya albarkaci rayuwar ki da rayuwar zuriyarki,yanda kika faranta raina Allah ya faranta rayuwar ki daga yau har abada,Hafsat kin burgeni a wannan zamanin d'aid'aikun matane kurin za'a samu da kare Kansu irinki,yau na k'ara tabbatar wa kaina ina d'aya daga cikin mazaje mafi Sa'a a rayuwa,Allah ya  barmu tare blossom" batace komai ba saida ta gaji kuma harga Allah kunyar abinda yashiga tsakaninta dashi takeyi "Blossom ki tashi na gasa miki jiki kinji?" Cikeda shagwab'a tace
"Yaa Abdul zanyi da kaina plss" sarai ya sani gaddama Zata tsaya masa,wannan ya sanya ya d'agata zuwa bathroom a bahon yadireta acikin warm water sannan ya wanke ta shima yayi wankan yasanyata tsarkake kanta agabanshi domin ganin iyawarta,yane zanin gadon yayi sannan ya wuce d'akinta suka kwana acan cike da farin ciki.....

  *Bayan sati d'aya*

     Cikeda zumud'in kasancewa tare da juna suke tare,yau fitar yamma sukayi Sunje gida,lapiya lau suke hira a mota,suna isowa k'ofar gidan Elham taga wata qatuwar halitta dabazata iya tantance meye ba tayo kanta,da sauri ta kwallah k'ara tayi bayan Abdul ta koma tace "Nashiga uku yaa Abdul wlhy ga wani abunan ze kasheni a k'ofar gida" dubawa yayi bega komai ba yace "Blossom ki nutsu nifa banga komai ba" dagowar dazatyi takuma ganin abin aikam ta ruga seda ya riqota,wasa wasa fa gaba d'aya ta haukace sekace me shafar aljanai waya yayi momy tazo anfi awanni biyu amma taqi Shiga ciki,dole suka koma da ita gidansu name Marta ba,duk sanda Abdul yazo kusa da ita seta saka masa ihu kamar wacce taga wani abin tsoro gaba daya ta fita hayyacinta....

Post a Comment for "HAFSAT CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...