Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAFSAT CHAPTER A

HAFSAT CHAPTER A

- - Post a Comment

 HAFSAT CHAPTER ASosai ran Elham yake b'ace ba kad'an ba,ji take tamkar ta juya ta wanke yaron daya taka mata farar socks d'inta tayi datti tunkan tashiga school ma da mari,aranta se mita take tana kyankyamin kanta sabi da tsabar tsanda da kyankyamin da Allah ya halicce ta dashi, a class sam kasa zama tayi da socks d'in,gashi sam ba'a bari Su zauna haka,tissue ta zaro a jakarta fara kal ta nade ilahirin kafafunta dashi sannan ta zura sandal dinta,wunin ranar gabaki daya a jaguje tayishi,driver din gidan sarkin fulanin Adamawa ne yazo daukarsu a school ita da feenah, ko kallon juna basuyiba a haka suka Shiga mota,suna isowa gida feenah tayi gaba zuwa cikin babban gidan,yayinda Elham tanufi b'angaren Masu gadin gidan tana tafiya tana dan saka hanky tana karkad'e kasan wandon uniform dinta tana guntun tsaki dagowar dazatyi ta hango yaa Abdul ya kura mata ido ya hard'e hannayenshi a k'irji se wani shan kamshi yakeyi,wani yamutsa fuska taja d'an siririn tsaki aranta tana mamakin yanda za'ace mutum kullum yana cikin dawaki ko k'yank'yamin Su bayaji ita sam bazata iyaba wlhy,se mayan kallo sekace wani d'an kauye......A d'aya bagaren kuwa na Abdul mamakin iyayi da kuri da k'yank'ya mi irin na Elham yakeyi yarinya ba kowa ba kuma ba yar kowa ba amma se kafirin iyayi da shegen gulman tsiya,banda gulma kaje skul ka dawo ai sauri zakayi ka raba jikinka da uniform amma ita tsabar kazanta wai hanky nata datake share fuskarta dashi kuma dashi take karkad'e dattin wando shi aganinshi Wannan babbar k'azan tace....da sallama tashiga gidan nasu mahaifiyar ta dake kokarin gyarawa akuya daurin da aka mata ta kalla yanda ta dage taketa damkar akuyar girgiza kanta tayi tace tana yank'wane fuska "Sannu Innah,ina wuni?" Dagowa uwar tayi taga yanda tayi kichi kitchen da fuska,ita abinma dariya ya bata tasani Wannan akuyar ne datake damk'a kuma wunin ranar bazataci abinda ma ta girka ba tace


"Lapia lau Hafsatu harkun taso?" A tak'aice tace da ita
"Ea Inna" tashige d'akin dayake mallakinta a gidan...duk da yake gidansu ba wani me muni bane amma sam bazakayi tsammanin cewar d'akin Elham yakai had'uwar hakanba,komai naciki pink & white har labulaye da gado closet nata center carpet tiles na dakin da komai ma,a kofar toilet dinta akwai towel shid'inma pink&white ne,ajiye jakar skul nata ta farayi sannan ta zauna kan kujerar k'walli d'aya dake cikin dakin ta zare takalmin skul nata ta cire Wannan tissue data nad'e kafanta dashi ta wurga a dustbin dake gefen kofar shigowa dakin wanda yake pink&white ne shima,mik'ewa tayi ta cire uniform nata ta daura towel d'inta na wanka zarar Su tashiga bathroom d'in dan karamin washing machine nata ta budesu ta wurgasu har inner wear's d'inta ma ta barsu anan sabida yana drying bayan ya wanke a tsanake tayi wanka wanda ankai 40 mnt ana yinshi sannan ta kai dubanta zuwaga dan mitsitsin agogon bangon dake toilet me kalar pink& white taga biyu ta gota da sauri ta dauro alwala tafito daga ban d'akin,wurin dazayi Sallah ma wani tashin kanshin turaruka yakeyi ga almiski ma kamshin shi se tashi yakeyi a haka ta janyo hijab fari k'al me kamshi ta tada Sallah tajima awurin tana addu'o inta har aka kira sallar la'asar sanda tayi Sallah sannan ta tashi,cikeda yanga ta zura wata doguwar rigar jallabiya baqa me adon duwatsu jajaye ta dauko red mini veil ta yane kanta dashi gaban mirror taje ta watsa turaruka na asalin masu kamshin gaske, sedai ba masu tashi bane masu sanyin kamshi ne se kazo daf da ita zakaji numfashin ka na shirin dauke wa ya mata rakiya,wasu takalmi ta saka masu d'an tudu suma black & red sannan ta janyo wayarta kiran iPhone 6+ ta kunna ta,tafito tsakar gidan,kallon ta maman tayi tace

STORY CONTINUES BELOW

"Hafsat se ina haka?" Murmushi tayi tace "Zani gun momy Fulani ne,dasafe ban jeba"
"To zancen abin ci fa Hafsat?" Yamutsa fuska tayi wanda Wannan ya zame mata d'abi'a tace " Innah na k'oshi" ,girgiza kai Innah tai tana jinjina k'yank'yami irin na Hafsat,sam abin baya mata dad'i yarinya sekace me shafar aljanai.....Dannan wayarta take tana tafiya a yangace status take dubawa kasancewar yau through out bata hauba, a hanyar dazata sadata da sashen momy Fulani taci karo da yaa Abdul,dan yamutsa fuska tayi tace dak'yar
"Yaa Abdul ina wuni?" Ko kallon inda take beyiba yace "lapia" atakaice, haushi ne ya tarnak'e ta taja d'an guntun tsaki batare da sanin taba,Ashe ya jiyota,cike da dakakkiyar yace
"Elham zo nan" rai a bace tazo kusa dashi ta sadda kanta a kasa tace "Gani yaa Abdul" yafi minti biyu yana Kallonta beyi magana ba,harta fara tsarguwa gashi iya k'uluwa ta k'ulu a ganin ta wani salon wulakncine yake shirin tsirowa dashi,se can har kwalla ya taru a idonta yace cikin izzah da isa
"Wakike wa tsaki Elham?" Dago manya manyan fararen Idanuwan ta tayi dasuka Cika da kwallah ta saukesu a kanshi amma ta kasa magana,a tsawace yace
"Dake nake magana wa kikewa tsaki?" Kwallar datake kokarin tarewa ne ya silalo a idonta da sauri ta sadda kanta k'asa manya manyan eye lashes d'inta lokaci daya suka jike suka kara bak'i da shek'i,ta kasa magana
"Idan yanayin amsa gaisuwa tane bakyaso Na sauke miki ki huta karki kara gaidani,amma kinsani koba komai nafi karfin irinki tamun tsaki,balanta ina matsayin yayan ki" ta tsinkayi muryarsa yana fada, murya na rawa tace
"Dan Allah Kayi hakuri yaa Abdul wlhy baran karaba" bece da ita komai ba ya wuce abinshi ya barta gun a tsaye, harga Allah taji kunyar abinta tamasa batai tsammanin zeji ba,hankalinta ya tashi ainun,gwiwa a sace ta juya zuwa cikin gidan
"Da sallama ta Shiga parlor din bakowa se feenah dake shan romon kan rago,fuskarta ba Yabo ba fallasa suka gaisa tace
" feenah momy fa?" Kallon raini feenah ta mata tace "wace Momyn?" Idan da sabo Elham ta saba bata biye taba tace "Momyn ki" dariya feenah tayi "Au momy na nazata bacin inna kinada wata momy bansaniba,aida tun farko sabida rage kokwanto sekice momyna" Murmushi tayi wanda ya kasance na yak'e ta nemi wuri ta zauna ta kurawa TV ido batare da ta ce kalaba,se can momy tafito, da fara'a dauke a fuskarta tace
"Au Mamana dama kin shigo,yanzu nake cewa yau d'innan baki leqo minba sam ko lapia"
"Lapia lau momy na tashi makarene kuma yanzu na dawo bansamu nayi Sallah a school ba" Murmushi tayi
"Lallai kam nasan da babban dalili,kinmaci abinci kuwa?" Girgiza mata kai kurun tayi alamun a'a Momyn ta tashiga ciki batare da tayi magana ita kuwa feenah tace
"Yana dai da kyau mutum ya godewa Allah da kalar cimar gidan ubansa,ace mutum se tsabar kwadayi baka cin abinda aka girka gidanku tsabar had'ama" ran Elham ya baci matuka sedai batace da ita kalaba,kasancewar ta dama bame yawan san magana ba,kawai mikewa tayi tabar sashen gaba daya zuwa swimming pool na gidan,cire ta kalmin kafarta tayi ta kwashe rigarta ta zura kafafuwanta aciki tana wasa da ruwan a hankali....kuka me karfi ya kwace mata ta zauna tayi abinta ma'ishi koda taji an dafa ta ta dago se ganin yaa faruk tayi yana kallonta,nad'e kafar wandonshi shima yayi ya zura kafafunshi acikin ruwan yace
"Elham mesa ne bakya gajiya da kuka,ke sam abin kuka baya miki k'ank'anta,yanzu sanar dani menene nasani yanzu zakice ba komai" kallon shi tayi amma batayi magana ba kawai dai ta tsagaita kukan nata,rike mata hannu yayi yace
"Ba kasafai nake san tsoma kana a personal life nakiba,amma kisani ina damuwa aduk lokacin da naganki a damuwa kema,dan Allah kirage yawan kukannan har zaki bata kya wawan idanuwanki my swt sis" Murmushi tayi sannan ta sanya hannu ta share hawayenta tace "karka damu yaa faruk zan dena Inshaa Allah" Murmushi ya sakar mata aka wuce wurin.....
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari tun 7 ta shirya ta wuce gidan momy Fulani,akan hanya ta hadu da yaa Abdul,dan durkuso tayi "Yaa Abdul ina Kwana?" Ko Kallonta beba balanta na ya amsa gaisuwarta,bata wani damuba ita tama matsu yabar kasar kowa ya huta,mutum se mugun girman kan tsiya,tana saqe saqen ta se ga yaa faruk a gabanta
"Good morning beautiful" ya fada yana me sakar mata lallausan murmushin sa" murmushin itama tayi

"Good morn sweetest bro ever and how was ur night?" Tsayawa Abdul yayi ya juyo ya kallesu se fara'a suke

"It was sweet dear and u?"

"Splendid" tabashi amsa tana kokarin barin wurin,hannun ta yariko,Shikuwa Abdul ya dauke kanshi daga dubansu yayi gaba abinshi......"Bazaki tsaya mu gaisa da kyau ba pretty?" Agogon dayan hannunta ta kalla tace "I'm going be late sweetest bro, w'll do that when I come back from skul" sake mata hannun yayi "OK cutee all the best" Murmushi tamasa tajuya kurun,Raihan dake tsaye daga garden tana kallonsu tace a ranta "Zakaci k'aniyarka wlhy yaa faruk,sena gayawa ummah abinda kake shirin yi" ta juya zuwa b'angarensu kallonsu Haj Fati tayi tace "Raihan Yaya kin gama shiri nki? " Sosa kanta tayi tace

"Harma nafita na dawo?"" Mantuwa kika yine hala?" Zama tayi ta fuskanci ta

"Ummah kinga yaa faruk bayajin maganar ki ko? Kinganshi can ko yanzu yana wa yar me gadi magana,baze taba iya rabuwa da itaba inhar ba tsaye kika tashi masa ba" nisawa tayi tace "Raihan ki barni dashi ze ganene wlhy dani yake zancen,tashi kiyi tafi yarki" mikewa tayi domin batasan tayi fashi jiyama ciwon ciki be barta tafi skul,dukkanin Su a wurin mota suka hadu susu hudu,ba wanda yayiwa dan uwansa magana haka suka d'unguma zuwa school,Raihan ce bayan sun sauka ta kalli feenah tace

"Feenah muyi nan plss,ke kullum bakya taba raba hanya da talaka,talakan ma d'an masu gadi bakida labarin cewa annabi da kanshi yace munemi tsari da talauci,had'a hanya da talaka ma ni gani nake zunubi ne" feenah bata ce kanzil ba kasancewar itadin ma ba barinta Raihan tayi ba,Elham kuwa Idan da sabo ta saba da tsangwamar dukkansu,kazalika ire iren wayannan zantutuukan basa damunta, SS3 A take itada feenah yayinda Raihan take 3C, suna iska class yan class suka fara mss neat ta iso, yanzu zakuga iyayi cike da zolaya suke maganar Murmushi kurun ta musu ta zaro duster ta goge sit nata na zama da table sannan ta dauko wani fari se sheqi yakeyi ta shinfida sannan ta zauna,ihu suka saka suna dariya wasu na mamakin tsafta irin tata,Sune wayanda ba'a taba musu gwaninta.

Yau bayan sun iso gida hanky d'in ta zaro tafara aikin karkad'e kafar wandonta,hanky dinne ya sub'uce mata adaidai lokacin data d'a goshi domin karkad'e wa,a daidai Wannan lokacin yaa Abdul yashigo ya zo wucewa hanky d'in ya saukar masa akan fuskarsa,cireshi yayi ya juyo a fusace wurgar dashi yayi akasa yad'ago yana Kallonta ita d'inma shi take kallo,rikicewa tayi ganin yanayin fuskarsa tace murya na rawa

"Yaa Abdoul, dan Allah Kayi hakuri wlhy sub'uce mun yayi ban kuma san yanda akai yaje kan fuskar kaba" matsowa yayi daf da ita

"Karyane Elham,tunda kika iya mun tsaki to my face komai ma zaki iya yimun,nasani sarai kinsani kika wurgomun Wannan kazanta ajikin,an gaya miki kowa k'azamine irinki,wlhy na tsaneki bakida kirki ko kad'an ko ganinki ma bana sanyi dalilinki zanbar kasar nan inkoma inda nafi wayo,and this should be the last concrete warning dazan baki akan Shiga sabgogina daki keyi, next time ko kallon inda nake kikayi wlhy se kinsha mamaki,now get out from my sight" tana kuka tabar wurin Sa'a taci bakowa agidansu hakan ya sanya kai tsaye tawuce dakinta ta rufoshi acan tasha kuka sannan tayi wanka ta gabatar da sallah ta kwanta lamo baccin ya dauketa.......

Yaa Abdul yana tsaye yana Shafa jikin dokinshi Raihan tazo ta same shi, Murmushi me sanyi ya sakar mata yace "hii dear how r u?" Murmushin itama tayi

"I'm fine yaa Abdul u?" Be amsa mata ba yace "ya akayi Raihan?" Dan Shafa fuskarta tayi tace

"Yaa Abdul bakaga message nawa bane?" Murmushi ya sakar mata ya riko hannunta suka fitowar gidan dawakan yace "Raihan kiyi hakuri tafiyar nan tawa tazama dole ba yanda zanyi,kinsani company nakewa aiki kuma sun buqaceni yanzu,amma kin sani kullum zanna rika miki Waya so biyar arana kuma chat ma haka" sadda kanta tayi kasa tace "Allah yasa shine mafi alkhairi"
"That's my beautiful wife,Allah ya miki albarka,momy ta aikeni anjima bayan magrib so ki shirya muje tare keda feenah zan muku siyayya....

Bayan isha ya shigo part din momy anan ya taradda Elham,gaida momy yayi cikeda girmamawai,Elham ma ta gaidashi ya amsa a dak'ile,yace " Momy list d'inkifa?" Murmushi tayi tace "Yana wurin Mamana tare da ita zakuje" murtuke fuska yayi yace "momy Idan zaki aika driver ya kaita mana" bata fuska tayi itama tace

"Kaga Babana nafa kula kana takura mamana dayawa ka dauki karan tsana ka dora mata ji yanda ka ansa gaisuwar ta sekace ba kanwar kaba,yanda fa kuka dauki duniyar nan bafa haka take bafa tam,aiko dan darajata ka sota,itada feenah nace suje tare dakai Idan kuma bazakaje da Mamana ba Kayi tafiyar ka da kudinka banaso" durkusa wa yayi yashiga ban baki,arayuwar ya tsani yaga ya bata ran mahaifiyarshi,sassauta fushinta tayi tace "ke Elham jeki d'aki bamu wuri" bayan tafita ta kalleshi tace cikin taushin murya

"Babana ya kamata ka fahimci Elham yarinya ce me hankali kuma sanin kankace agidan nan aka haifeta ta cancanci duk wani matsayi daga wurinka kodan kasancewar iyayenta masu nagarta,ina sone danni kawai kadauketa matsayin kanwarka kamar yanda ka dauki feenah kuma duk wani abu dazaka was feenah itaama kamata,kai mata wasa da dariya kuma ka saurari matsalolinta daidai gwargwadon yanda kakeyi wa feenah,Babana Wannan ita kadaice alfarmar danake nema a wurinka ina sone konbayan raina ka tallafi yarin yarnan Banso tashiga wata damuwa kabata dama ta kusance ka ta hakane kadai zaka san wacece Elham,Allah shine shaidata ina yowa ilham soyayya me tsanani Wannan rarrabewar kan naku da rashin jituwa,se inaga kamar uwarku daya ubanku daya kuke Wannan,wlhy Babana idanbhar kamun Wannan zan dinga zabga maka albarka daga nan har ranar mutuwa,kuma aljannah dakake nema awurina Idan har ka dena wannann kiyayyar wlhy namaka alkawarin daga ma kafar ka shige tun yanzu" nisawa yayi yace "kiyi hakuri momy ni dama ba kinta nakeyi ba kawai dai Yarinyar komai seta riqa nuna wa mutum k'yama sam bata ajiye kanta kusaba wlhy,amma duk da zan jata ajiki zan kuma nuna mata rashin dacewar hakan" godiya momy tamasa daganan taki rasu suka bar gidan,a hanya Raihan se yada magana takeyi ba wanda ya kulata,bayan sun isa mall din ya baiwa kowa 30k yace Su siya abinda suke so,ya kalli Elham yayi da sauri ta sauke kwayar idon ta kasa yace "Kizo muje kina kwasar kayan momy kina had'awa da naki " bin bayanshi kurun tayi batayi maganaba,Su kuwa Su Raihan sun zare suna can suna kwasar kayan maku lashe abinsu,ita kuwa seda ta gama siyawa momy duk abinda ta rubuta,tabaki wurin biya kud'i sannan tajuya wa nata,mamaki ne ya kama Abdul ganin takalmi kurun ta dauka me tudu se turaruka na 10 10k guda biyu,se kuma ta dauko clips na 4800 kwalli d'aya,kasa hakuri yayi yace " Elly Wannan abin kurun zaki siya?" Yamutsa fuska tayi wanda hakan ya zame mata d'abi'a tace " Yaa Abdul turaruka ne fa masu kamshi ina matukar sonsu dama nawa sun kusa karewa duk na damu" takarashe maganar tana yarfe hannaye nta ,Murmushi yayi yace "To clip's d'imfa me zakiyi dashi?" Ya tambaya yana me hard'e hannayenshi a kirji ya sanya Murmushi a fuskar sa wani langwabe kai tayi ta yamutsa fuska tace "to ai yaa Abdul Kaine baka siyawa kanka komai ba shine na siya maka" mamakin Yarinyar yakeyi duk da yake can kasan zuciyar sa yanajin tsananin tsanarta amma ta burgeshi godiya ya mata suka gama abinda suke suka bar mall d'in, kallon Raihan yayi yace "Bara muje wurin amadu me kajin hausa karna bar kasar ban Ciba" a haka sukaje yab siyawa kowa tasa,kallon kazar Elham tayi tace "Ayyah yaa Abdul ai da baka siyamun ba bana cin kazar hausa" wani dogon tsaki Raihan tayi tace "kaji jaka,ko ranar naji tana gayawa yaa faruk batacin kazar Hausa wai kwata takesha,ina agidan ubanki har kiwonsu ake seki kaiwa tsofaffi Su suci tunda ana kiwo tsabar maqo ba'a iyaci,yanzu gata Banza nan saci" tsawa yaa Abdul ya daka mata

"Bakida hankaline Raihan? Ina komai ra'ayine? Tunda bata ra'ayi meye naki aciki,tsabar hauka seki sako iyayenta kina zagi,wlhy karna kuma ji ko ganikin zagi iyayen wata ma ba itaba,wannan ba tarbiyar damuka daura ku akai bane,and to be Frank I'm so very disappointed in you,Elham u should take hrt plss don't be angry,and do not take what she says to hrt,do forgive her,zan siya miki na turawa yanzunnan" Murmushi ta kakalo tace "Don't worry yaa Abdul its fine with me" kuka Raihan ta saka amma ba wanda ya kulata har sukaje gida,suna isa ta tattare kayanta tabar motar a fusace,ba wanda yabi ta kanta suka kwasa sukayi part na momy,acan Elham ta gayawa momy abinda yaa Abdul yaa basu kuma tamasa godiya da adu'a me yawa ta bashi clips data siya masa,momy taji dadi sosai...

Tana baro sashen momy Fulani taci karo da yaa faruk,hannayen shi yasa duka biyu ya daga ta yace "Kingan ki ba nayi se tsawo" d'an bata fuskarta tayi kasancewar batasan irin Wannan wasan daya ke mata hasalima batasan koda hannunta yake tab'awa gashi ta kula shi sam be dauki abin wani abin ba,tana yunkurin sauka tana wuntsila kafa yaa Abdul yafito daga part d'in,kallon mamaki yabisu dashi aranshi yana mamakin iskanci irinna Hafsat,sam bazakayi tunanin koda yatsa ka saka mata abaki zata ciza ba,d'an tab'e bakinshi yayi ya wuce Su,yayinda tana ganinshi taji wata irin kunya ta lullub'eta lokaci d'aya kuma ta dena yunkurin sauka daga jikinshi,sauketa yayi ganin yaa Abdul, b'ata fuska sosai tayi tace "yaa faruk dan manzan Allah kadena kokarin kai hannu jikina ko wane lokaci,nafa sanar maka banaso yanzu sabida Allah me kake so yaa Abdul yace?" Dariya yayi yace "Nadena princes Ni nasaba rayuwar turai wanna ba komai bane awurinmu"

"To ai nan ba turai bane so seka maintaining kanka gaskia nidai Banaso" takarashe maganar cike da shagwaba,wanda ba karamin burgeshi tayi ba. yace yana kallonta "Elham bakice mun komaiba I'm sure kinga message nawa since morning" Murmushi tamasa tace "yaa faruk kenan,kasani sarai bana bud'e phone nawa se 4 kullum,da yamma nagani trust me,and bansan me zance maka ba" kwai kwayar maganar ta yayi "kice Nima ina sanka yaa faruk mana" tufakan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta sannan tace "Yaa faruk dan Allah ka dena kana bani kunya wlhy"

"Naji yanzu jeki u ttxt me plss,and make sure u do that before going to bed" dan Murmushi tamasa tace+


"I'm not even sleepy @ all let's chat" Murmushi shima yamata yace "Fine then ping me if ur free" tafiya take tana Murmushi harga Allah tana kaunar yaa faruk,yafi kowa Santa agidannan me maraba ne da Fulani kurun suke nuna mta kauna fiye da shi,sun d'auketa tamkar yar uwarsu kuma jininsu kokuma Sune suka haifeta duk kuwa dayake itad'in ba kowa bace face 'ya awurin hadiminsu,a hadiman ma me gadi......bayan tayi wanka ta shirya cikin rigar bacci fara k'al ta tufke gashin kanta a tsakiya sannan ta saka hula a kanta ta kwanta,wayar ta ta dauka ta turawa faruk message


"Sweetest I'm done" Murmushi ya turo mata yace "fine,that's good rose yanzu sanar dani menene amsarki zaki aureni?" Murmushi ita ma ta aika masa,sannan ta tura masa da hoton hrt,batai magana ba,hrt yakuma aika mata shima sannan yace "Rose mana sanar dani plss,I'm telling Idan kin amince gobe zanje na sanar da me Martaba kina kammala Wannan makarantar Abani matana muje gidana" Murmushi tayi tace


"Zan aureka mana yaa faruk koda gobene na shirya wlhy" tsallah ya daka tamkar yana ganinta yace "I'm so much happy miss Rose,thanks a lot for loving me I really appreciate ur love"

"I thank you too,charming" murna ce ta kama faruk yata mata hira da wasanni......


*Bayan sati biyu*


Fushi sosai Elham ta dauka da faruk sabida yayi kokarin tab'a jikinta kota karfin tuwo,ko hanya basa hadawa domin kuwa dasun hadu take sake hanya,Abdul kuwa wani abu ya tsare shi a Niger be koma ba sam satinnan dai yake shirin komawa,faruk ya damu ganin ko wayarshi bata d'agawa,yauma kamar da damuwar rashin faruk d'inta tashigo pool na gidan,harga Allah tana missing na faruk,kurun tana sone ta nuna masa kuskurensa Shiyasa take ta faman azabtar da har kanta ma,kamar daga sama taganshi akanta hannunta ya finciko ya juyota ta fuskance sa a bango yaje ya mannata ya daga hannayenta duka biyu ya manna a bangon ya riqe gagam yace "Tell me miss Rose? Why are punishing me like?" What the fuch did I do to you?" Kasa magana tayi kuma bata wani yi yunkurin kwace kanta ba,zuba masa manya manyan fararen Idan uwan ta tayi cike da tsoro,wanda shima din ita yake kallo....a haka yaa Abdul ya shigo ya samesu mamaki suke bashi shikam sam ba kunya a idonsu,ita ce ta ganshi kasan cewar shi faruk ya baiwa kofar shigowa baya,daga nan tafara cuku cukun kwace kanta

STORY CONTINUES BELOW

"Yaa faruk plss let go of me" be sake taba illah ma ya kare riketa tamau ya zuba mata ido, a tunanin yaa Abdul sabida sun ganshi ne take kokarin basarwa ,tana hango sanda ya girgiza kai ya juya kurun, a fusace tace "Wannan mugun halin yasa kake kara nisanta kanka dani,na sanar maka haramunne abinda kake,niba muharra marka bace,ban riga na zama mallakinnka ba mene na tabamun jikina" a fusace ya saketa yafara banbami


"Idan sabida wanna kike mun ihu zaki zama mallakina Hafsat,kullum magana d'aya bakida zance sena jikinki sekace kece kikafi kowa a duniya,wlhy nasan maganin ki,yanzunnan zanje na fadawa me martaba ina sone ya daura mun aure dake faqat shikenan?" Ya kura mata yana jira yaji cewarta,cikeda warning tace


"Hakane bazan hanaka aikata Wannan ba,sedai fa ka sani karka kuskura na kuma ganin hannunka a saman jikina harsai ranar da aka daura auren namu,baka majin tausayina yaa faruk baka ganin yanda na rame duk sabida ina missing naka,simple abu ya gagareka" sassauta murya yayi "kiyi hauri miss Rose bazan karaba" daganan dai suka shirya Kansu yamata alkawarin baze kara tab'a taba.


Zabura Umma tayi dajin zancen faruk tace "Au Wato dama faruku duk gargad'in nan danake maka baka saurara ta? Ina kataba ganin Sarki me jiran gado ya auri yar talakawa ,yar talawan ma yar me gadi! Wlhy faruk kobana numfashi kan auri Elham ban yafe maka ba" gigicewa yayi ya Hau ban baki da ban hakuri amma sam Umma bata sakko ba kara hawa ma takeyi tamkar wata farashi,wasa wasa fa kusan Kwana uku yana rokarta taki aminta,dolece ta sanya yaje wurin momy, ba karamin dadi momy tajiba mamanta zatayi auren Hutu dajin dad'i ,tace "Karka damu umarul faruk zanje da kaina gunta na mata magana da yardar Allah zata a mince,kaga dama na yayanka da Raihan muna jirane nan da watanni shida Su kammala skul inyaso se a hada gaba daya" godiya yayi yatashi yabar wurin cikeda murna,washe gari kuwan momy ta shirya zuwa bangaren Umma,gaisawa sukayi cikeda girmama juna tamkar ba komai a kasan rayukansu game da juna sannan ,gyaran zama Fulani tayi tace


"Fulani Babba dama nazone in roki Alfarma awurinki akan zancen faruk da Mamana,dan Allah ki janye furu cinki ki barsu suyi auren Su,tunda addini da al'ada duk basu hana ba" wani mugun kallo ta wurga mata sannan tace


"Kinga Fulani wlhy ko ubanwa zaki gayawa bazan sauya Wannan maganar ba,ke gani kike kamar bansan tuggun dakike kullawa ba? Kome nawa Kinbi kin kwace mun yatashi daga nawa ya dawo naki,bayan kin hade kai da mijinki kun kashe nawa mijin sabida ya Hau sarauta,yanzu kinzo kinaso ku daura Abdurrahman har dan munafurci wasu na kiranshi Yarima ,shine zaki zo sabida ki kara batawa faruk suna zaki hada shi da wata shegiyar talaka wai ya aura,a zatonki bansan me nake ba kokuma banida hankaline,duk muna funcinku ina kalonshi wlhy, kuma da yardar Allah bazakuci nasaraba faruk shine ze gaji sarautar ubansa,ko Raihan sabida banaso tashiga damuwa ne kasancewar ta mace kurun ya sanya na yarje mata auren Abdul" kura mata ido kurun momy tayi sanda ta kai aya sannan tace


"Kinga Yaya habiba ba zwa nayi Kici mun mutunci ba,zancen kashe margayi me martaba dakike kuma kije mun barki da hukuncin Allah,zancen kuma sarauta dakike keta Shafa ni kina sane yarona bata shafeshi ba,Idan kuma har Allah ya zabeshi keda iyayi nki baku isa ku hana ba,auren Raihan da Abdul dakike magana ita Elham malama ba 'ya bace daki kece Raihan macece ai itama macence bakya duba damuwar dazata Shiga? Tsabar sonkai musulunci da kanshi yamana nuni a sassa daban daban,kuma hadisin ya inganta cewa imanin dayanku baya taba Cika Harse Idan ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa,kekuwa taki yar kawai kika sani,wlhy kiji tsoron Allah" mikewa tayi a fusace


"Kinga Nana barmun sashen na,borin kunya kikeyi Allah ya Toni asirin ku da wuri Wannan karon,wlhy inhar muddin ina numfashi bazaki taba cin nasaraba,nakara fada ko bayan raina faruk ya auri Elham dashi wayanda suka daure masa gindi Allah ya isa ban yafe ba,Idan gaskiyane ba mugunta kike shirin masaba ki baiwa Abdul Elham d'in ya aura mana" mikewa itama tayi


"Naji Yaya habiba Abu daya nakeso ki rubuta ki ajiye wlhy Nima ko bayan raina ban yarjewa Abdul auren Raihan ba,dukkanin Su suyi asarar ababen kaunar Su,zan kuma tabbatar miki cewar ba mugun nufi araina domin kuwa aure ne Elham da Abdul anyishi an gama,ke kuwa Idan kin isa ki hada auren faruk da Raihan kema din kiyi auren huce haushi" zage juna sukayi tatas wanda da faruk da Raihan duk suna jiyosu, aikam hankalin dukkaninsu ya tashi,bayan Fulani ta wuce suka yita baiwa ummansu hakuri amma bata hakura ba....


"Koda momy takira Abdul dake birnin London tafada masa kasa yi mata musu yayi kasancewar sa me tsananin biyayya....gashi kuma bashida wacce ya tsana arayuwa sama da Elham" kuka sosai ya saka shikadai tamkar wani karamin yaro a ranshi yace "Ina zankai Wannan kazamar? Ina zan iya da yarinyar da faruk ya gama lalatawa gaba daya,kai wlhy gobe dolene nakira momy na bata hakuri,idan ta rabani da Raihan mutuwa zanyi".....

1

Kasancewar yau weekends yasanya Elham ke kitchen tana girki asaman risho,taba tsakiya da aikin tajuyo sallamr su Raihan itada uwarta,mahaifiyarta inna ma fitowa tayi dauke da mamaki a fuskarta tana musu Barka da zuwa , sheqeqe Umma ta kallesu tace1


" ke Asabe gunki nazo,wato sabida kinaso yarki dole setayi kud'i shine kiketa faman qaqa bawa faruk itako,kuma kunga bakuci nasaraba bazan taba bari me jiran gado ya auri yar matsi yataba shine kuka zago kuka koma gun Abdul mijin da kowa yasani Raihan dina ze aura,kuka asirce uwarsa tace yanzu Elham ze aura? To ban hana kuba amma wlhy ku kuka da kanku da abinda zan muku Idan kuka wa y'ata kwacen miji,faruk kuma baze taba auren yar masu Kwana a kofar gida bba".....ba karamin ,baci ran innah yayi ba da Wannan cin kashin bayan sun wuce tayita yowa Elham fada akan shishigin ta da samarin,amma ba ruwanta da zancen aurenta da Abdul domin kuwa uwarshibce ta nemi alfarma, ita kanma bataji Wannan labarin ba se yanzu,ga shi Innah tace ko wayar faruk ta kuma dagawa Allah ya isa,wunin ranar a daki tayishi tana kuka,bazata taba musawa momy ba kodan halaccinta agareta,kazalika bazata taba kaunar Abdul ba kamar yanda bazata taba iya dena san faruk ba.


Washe momy na tsakiya da breakfast Abdul ya kirata,k'aidane Awurinta idan tana cin abinci bata magana,Wannan yasanya sam bata d'aga ba,se bayan data kammala sannan tayi kiransa back....gaisawa sukayi cikeda girmama wa,sannan cikin sanyin murya yace

"Momy dama akan zancen Elham ne damukayi jiya,dan Allah momy ki yi hakuri,wlhy narigada na gama tsara rayuwata zanyine tane da Raihan,Idan akaimun haka ba'a mun adalciba" gyrana zaman ta tayi ta daura kafarta daya kan d'aya sannan tace

"Babana Ashe kam kacika me hikima,kuma zuwanka a kasar turawa yayi matukar tasiri akanka,Ashe dai mutum da kanshi shine yake tsarawa kanshi rayuwar dayake so yakuma ga ta dace dashi banida Wannan karatun kuma agidan mu ba'a koyar dani irin shiba,wanda na sani shine Allah wanda ya halicci komai da kowa shine yake karawa bayinsa rayuwar data dace dasu ba wai Su bane suke tsarawa kansu,amma nagode daka sanar dani yanzu....zancen Mamana kuma Idan baka manta ba aiba tilastaka nayi ba,rokarka kurun nayi nace ka fitar dani kunya dacin zarafin da akamun,amma tunda tsarin rayuwar ka a hannunka yake,nagode maka kaje ka ci gaba da tsarin yanda kaso....abu na gaba kuma kaje na janye maka auren Elham sedai fa ko bayan raina ban yarje maka auren Raihan ba,seka shirya tsara wata rayuwar da wata ba itaba me tsari" kit ta kashe wayar gaba d'aya,jikinshi ne ya mace koda yakuma kiranta ta kashe wayarta.....Faruk duk ya gama kad'uwa shida Raihan yayinda Fulani Babba ta dauki k'iyayya me tsanani ta d'aura wa Elham da iyayenta,bata tsammanin zata iya bari faruk ya tab'a auren Elham,kazalika bazata taba iya barin rayuwar Raihan ya tagayyara ba beside koda faruk ze rasa sarauta ai Idan Raihan ta auri Abdul sarauta tamkar a hannunsu take,zasu Shiga malamai su mallakeshi kuma jikokinta su gaji sarautar daga baya,shirya wa tayi taje fadar me martaba....

Durkusa wa tayi har kasa ta kwashi gaisuwa,me matarba ya bukaci a basu wuri,bayan kowa ya fashe tayi gyaran zaman tamatelarta tace "Ranka ya dade me martaba dama nazone akan wata muhimmiyar magana,dangane da,zancen auren Abdul da Raihan, Haj Nana ce tace wai bazata tab'a bari Yaronta ya auri Raihan sabida wani dalili nata da ban sanshi ba,nikuwa a ganina da Abdul da Raihan duk abu d'aya ne abin beyi zafi har haka ba" jin tayi shiru ya sanya yafara magana
Da daddaya tamkar baya sanyi

"Habiba dukkanin abinda kika zomin dashi yanzu ina sane dashi,ki sani shi Allah ba'a masa wayo,ko kad'an abinda kikayi be kyau tuba,ai kodan darajar mahaifiyata kya duba ki bar faruk ya auri Elham,nine me yanke wa yarana hukunci akan wayanda zasu aura amma fa ki sani wlhy muddin kika hana faruk ya auri Mamana bazan bari Abdul ya auri Raihan ba,sabida Elham tafita bukatar taimako,kisani wanna umarnine na mahaifiyata akan inganta rayuwar Elham ko bayan Ranta,nasani cewar Idan na kuskura na had'a su kishi bazaki tab'a bari Elham ta zauna lapiya ba Wannan dalilin yasanya na ce shi Abdul ko yana so ko baya so ya auri Elham,Raihan kuma Baba karami na zab'a mata,Idan baki manta ba tun farkon dashi suka shirya Kansu kece kika hana kike turawa Abdul,nasani tunaninki Abdul shine ze gaji sarauta Shiyasa kikeso ki Aura wa Raihan shi toki sani ba sankai alamurana kazalika Abdul baya san sarauta sabida haka bazaki b'ata mana zumuncinmu ba sam,ko Nana,na sanar mata tuni bawai dan yanzu zancen faruk ya taso ba,na dade da sanar mata bazan bari akan Raihan zumuncin Baba karami da Abdul ya lalace ba labari yazo min cewar basa koda gaisawa kuma Abdul bashida gaskia tun farko yasani sun daidaita kansu,abin haushin ma har mu iyaye mun Shiga ciki daga zuwan shi ya b'ata komai kekuma habiba kika zuge yarki akan kwadayin mulkin da dukkaninmu a duniya zamu mutu mu barshi,ki sani wlhy Wannan karon bazan saurara miki ba,karna kuma jin zancen Abdul da Raihan,kuma lallai ne ta auri Baba karami,kusan shekaru 4 tana bashi wahala baku isaba" jin yayi shiru ya sanya tayi godiya kurun ta wuce abinta, rayuwarta ta baci,tsakani da Allah bataji dadin Wannan abin ba,dama kuma Raihan ba itace take san Abdul ba kwad'ai ta mata san duniya uwar tayi....jiki a sanyaye tashige part d'inta abin haushi kuma seta taradda Baba karami da Raihan suna zance ga dukkan alamu kiran dame martaba ya musu dukkansu yayi tasiri akan su,dama ga soyayya.

STORY CONTINUES BELOW

Abdul na zaune yana mamakin dalilin daya sanya momy ta dauki zafi har haka kusan kwanaki biyar bata daga wayar sa,ga d'ayan bangaren Raihan ma bata daga wayarsa,kullum cikin kiran Feenah yake,akan ta bashi momy amma sam momy bata karbar wayar,jin karar shigowar message yayi a wayarshi koda ya duba Raihan ce

"Salam yaa Abdul plss Kayi hakuri dani kamar yanda Nima na hakura dakai arayuwa,abubuwa ne iri iri daba kasan dasu ba,banajin dadin rashin daga wayarka amma nasani hakan shine daidai,ban guje ka sabida bana sankaba,wlhy ko kadan ba haka bane na dai gane kuskure na,sam ban kyautawa Baba karami ba,ina fata zaka fahimceni kuma Wannan baze taba mana zumun cin muba.Nagode Raihan." Nisawa yayi bayan ha karasa karanta message din yace a sarari..."Bazan taba dena sanki ba Raihan abu daya na sani tunda kika iya jin zaki rabu dani cikin lokaci kankani haka tofawa Nima zan hakura dake, Elham kuwa bazan taba Santa ba,zande aureta kurun sabida biyayya....

Yau Kusan kwanaki goma sha d'aya fa momy bata d'aukar wayar Abdul,ya damu matuka,Wannan dalilin yasanya ya kira friend d'inshi zayyan ya sanar masa komai,gyaran murya zayyan yayi yace

"Zancen gaskia moris maganar iyaye ba abin wasa bane,nifa iya gaskiya Na nake gaya maka ka daure wa kanka ka aure yarinyar,kasani Kaima momy tafisan ka fiye da kowa a yaranta mesa d'an wannan abin ze gagareka,macece fa a hankali zaka koyi santa insha Allah" dan nisawa yayi yace "Zandai aureta zayyan amma sam bazan tab'a Santa ba wlhy,kuma yazanyi da san Raihan ? Wlhy ina kaunarta" dan guntun tsaki zayyan yayi yace

"Kaga nifa moris bana sanka da rigima,kaida kanka fa kace dani tajuya wa first love d'inta beside haka zaka bari ran momy yata b'aci mahaifiya uwa fa ? Kasani wlhy ka gyara tunanin ka tawa shawarar kenan" nisawa Abdul yayi yace

"Yanzu ya zanyi zayyan?"
"Zuwa zakayi ka fara kiran Yarinyar a Waya,kuma ka daure kace ta hadaka da mahaifiyarka ka bata hakuri,ka sani fushin mahaifa wlhy Masifa ne moris"
"Tayaya zan kirata ince tabani momy zayyan?, girmana ze fadi a gunta fa" tsaki zayyan yayi "kaje wurin tariyar girma ka b'atawa mahaifiyar ka rai,bawai nace ne kace ta baka momy kai tsaye ba,kurun kamata dabara,misali bayan kun gaisa ya skul,waye waye Idan kun dan taba hira se kace kana gaida momy kuma ta tabbatar ta sanar mata"

"Zayyan tayaya zanyi hira da Elham dan Allah, ni harga Allah kazantar Yarinyar nakeji Wlhy"
"Kaika sani ni kaga ina kan aiki se an jima" datse wayar yayi kan yace wani abin,shi kuwa yayi sororro yana kallon wayar,ya dade yana nazarin maganga nun zayyan kan daga bisani yakira Safeenah,lokacin ita da Elham ne zauna sunawa momy tausa,domin agunta Abdul ya gado k'yank'yami sam bata huldarta da hadimai,shiya sanya Fulani Babba ke cewa dan bata gada bane. Dagawa tayi cikeda girmamawa ta gaidashi sannan yace "ki sending mun Number din Elham yanzunnan kinji ko?" D'an kallon momy tayi kasance war ita sam bata san meke faruwa ba kuma dama tasu bazuwa tayi d'ai data Raihan ba sannan tace "To Yaya Yarima yanzu zan turo" momy ce ta bude idonta dasuke a lumshe tun sanda suka fara mata tausar tace

"Me zaki tura masa kuma?"
"Number din Elham yake so wai" gaban Elham ne ya fadi yayinda zuciyar momy tamata sanyi ganinta takusa cimma burinta....a d'aya bangaren kuwa Abdul ya baiwa Elham msd col har biyu bata dauka ba kasancewar wayanta nacikin gidansu ita kamma bata gidan tana gun momy,se bayan isha tashigo wanda bata mabi takan phone d'imba,tana gama wanka tabi lafiyar gado,can acikin bacci taji wayarta na ringing janyota kurun tayi ta daga ta kara a kunne,a tunaninta samra Ce tasani ita kadai ke mata Wannan iskancin,cikin muryan bacci tace

"Samrah wai meye haka ne,kina yawan san takura ni wlhy,bacci fa nake" dan gyaran kwanciyar sa yayi sam be fahimceta ba yace

"Hafsat ya gida?" Zabura tayi jin muryar Abdul tace "yaa Abdul ina Kwana ya aiki?" Murmushi rikicewar ta ha sakashi yace batare daya shirya zuwan furucinba "Hafsat ina Kwana fa? Sabida kurun ke kina bacci seki ce dani ina kwana, Toni ban ma kwanta ba balanta na gari ya waye" kasa sakewa tayi da dogon surutunsa tace "kuskure ne Kayi hakuri yaa Abdul" shiru dukkansu sukayi sannan yace "seda safe,gobe Idan kinje wurin yarki kice ina gaidata" Murmushi tayi itama tace "zan fada mata inshaa Allah nagode sosai"
"Kinyi Alkawarin zaki fad'a d'in?" Ita dai binshi tayi da to a ranta tana tunanin yanda za'ayi ta sanar wa momy Wannan zancen, ahaka ta ajiye wayar tana nazarin dalilin kiran,ba wata kwakwarar dalili neman magana ne kurun.

Da safe ya kasance asabar dan haka da wayarta ta tsala ado ta tafi part d'in momy,suna gaisawa tafara gyaran d'akin momy ko ina yayi kalkal sannan ta dawo gyaran parlor tana tsakiya da gyaran wayarta yafara ruri,dagawa tayi takara a kunne da sallamar ta,amsa ta yayi cikeda isa yace "ki ajiye duk abinda kikeyi kije part d'in momy ki kaimata Waya zanyi magana da ita" d'an wai gawa tayi ta kalli momy dake cin breakfast,tace masa tana me shigewa cikin dakin "yaa Abdul inajin nauyi fa mezan ce da ita,dan Allah ka kira yanzu phone nata yana kusa da ita" shiru yamata tayita hello hello,ba amsa can taji ya katse wayar,kiransa tayi back yaki dagawa har kusan so biyu,Sekuma taji ba dadi ganin cewar sam yaqi daga wayar kuma ta fahimceahi yana da saurin Fushi ta sani Fushi yayi,dawowa tayi parlor din taje dakyar tace "Momy dama yaa Abdul ne jiya yace na gaidaki,yanzu kuma yace na baki wayar kanna zo nan ya yanke ko zaki kirashi da wayanki dan Allah" momy gani tayi tamkar Abdul ya sanarwa Elham bata daga kiransa,kuma seta kula tamkar Elham ta damu Wannan ya sanya ta,dauki wayarta tayi kiranshi,jikin shi har rawa yake ganin ta kirashi ya daga,ko gaisawa basui ba yace

"Momy dan manzan Allah kiyi hakuri, wlhy na gane kuskure na,na tuba momy wlhy zan auri Elham din dan Allah kimun gafara" nisawa tayi sannan ta tashi tashige dayan sashen daba kowa tace

"Zan gafarta maka Idan kamun alkawarin zaka rika kiranta so uku a rana,zaka mata yanda kakewa Raihan sanda kake neman aurenta,zaka biya mata bukatunta Idan basufi karfin taba kuma zaka shigo next month" nisawa yayi yace "zan yi momy,wlhy zanyi nanda sati biyu ma Zanso inshaa Allah" sallama tamasa ta sauke qayataccen Murmushi cikeda nishadi ta koma parlor......

Hankalin Fulani Babba sam baya jikinta ganin fa dagaske me martaba yake kuma kowa ya goyo bayan hukuncin ta,ga faruk ya koma paris abinshi baya ma kiran Waya gida, gashi kuma Raihan da Baba karami sun kara d'inkewa Yarinyar taqi bata hadin kai tai bori tace dole se Abdul,duk tashige damuwa sosai.

Wanin ranar Rabin shi Elham a wurin momy ta yishi,se bayan la'asar tabar gidan zuwa gidansu,Innah ta gaida inna ta ansata cikeda kauna tana kallonta ,ta yabawa yar yanda tayi jarumtar cire faruk a ranta gaba d'aya, takuma sani badan bata sansa ba,kurun dai Hafsat ne bata daukar wulakanci tasani wulakancin da Fulani Babba ta musu ne ya sanya ta fitar dashi aranta.....wuraren shidan yamma yakirata,da sauri kuwa ta d'aga wayar
"Yaa Abdul Barka da yamma" seda yadanja fasali sannan yace "Lapia,karki karamun abinda kikamun d'azu bana so" shagwabe wa tayi tamkar zatayi kuka,wanda ita bata dauka komai ba tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri wlhy bazan kara ba" wani yarrrr yaji ajikinshi lokaci daya abubuwan dake kai saqonni na fahimta acikin kwalwarsa suka dena aiki na na 1 mnt,dakyar ya tattaro nutsuwar sa yace "Naji" a takaice,gani tayi tamkar be aminta ba tace cikin wata shagwabar "Yaa Abdul plss mana,trust me bazan kara ba" kasala ce dabesan dalilin taba ta saukar masa ya kasa koda motsi bale yayi magana takuma cewa "yaa Abdul Allah fa nace" cikin muryar kuka,d'if ya kashe wayar yarasa dalilin dakesa kirjinsa ke dokawa dazaran tayi magana,yace aranshi "nifa momy tabani aiki Wannan kazamar jakar zata rainani ko ubanwa take wa shagwaba oho" ita kuwa tsaki taja tana share kwallar data sakko mata tace "Allah yaa Abdul bazan taba sanka ba,na tsaneka Nakuma tsani halayenka na jiji dakai,zan aureka kurun sabida iyaye nka".


Wuraren karfe 9 na daren ranar ya kuma kiranta amma sabida hafsa tafishi zuciya ga kuma rashin daukar raini ya sanya taki dagawa,msd col biyu ya bata,ranshi yaji ya sosu ba bad'an ba, daba dan momy bace wlhy Wannan Yarinyar da tayi kadan yasani sarai tana ganin col nashi tamasa banza,amma zata fahimci baya daukar raini Idan tashigo hannun shi....a bangaren Elham kuwa ta kudiri niyyan bazata kara daukar wayar saba,tunda kullum burin shi ya bata mata rai,ita banda munafurci ma batasan meye na kiran taba,washe gari kuwa bata ma tafi da wayarta sashen momy ba haka taje saddan,ayyukanta tayi tazo ta zauna cin abinci tare da momy da feenah,wayar feenah ya soma ringing, dagawa tayi ganin yaa Abdul ne


"Yaa Abdul ina Kwana" be amsata ba yace kije gidan su Elham ki kai mata Waya Kokuma kice da ita nace lallai ta kirani yanzu" tana kokarin sanar masa Elham na kusa kurun ya datse wayar tabe baki tayi ta kalli Elham tace


"Elly ina wayan kine?"" Kallonta sukayi har momy,sannan tace


"Tana sashen mu,agida na barta" dan yake tayi tace "Gwaramun me martaba ya kirani ban dauka ba nasan ze fahimci bana kusa akan yaa Abdul ya bani ko half msd c ne Idan akwai,ya tsani ya kira mutum yaqi d'agawa ko alama,yanzu kinga masifa yake wai na sanar dake ki kirashi yanzunnan" batayi magana ba shiru kurun tayi momy ce tace "ki tashi kije ki kirashi yanzu" mikewa tayi jiki ba kwari taje gidan msd col hudu ta tarar Nasa ,seta tsinci kanta da kasa kiranshi tsoro me tsanani ya shige ta,ta sani bazata iya gaya mai bakar magana ba amma fa batada juriyar wulakanci,tsaf zata kashe masa Waya Idan yanemi gaya mata ba daidai,daga karshe dai phone nata ta kashe gaba d'aya.... Ba ita ta koma part d'in momy ba se bayan isha sannan ta Shiga, suna wa momy tausa wayar feenah ta fara ringing tana dubawa taga Abdul ne,tana daga wa yace "Idan Elham tana kusa ki bata yanzu" batare da tayi magana ba ta mikawa Elham waya,tana karba tabar wurin seda tashiga d'akin momy sannan tace cikeda faduwar gaba


"Assalamu Alaikum" cikin tsawa yafara masifa


"Ke Elham me kika dauki kanki ne? Tun yaushe kike ganin col dina bakya dagawa kuma bakya kira back,kuma tsabar raini seki kashe wayar gaba daya,me kike tagama dashi kazama dake,ke badan umarnin iyaye ba da kin isa na rab'i hanyar dakika bima,iyayena naso su miki gata amma kina wulakanta musu yaro,ke bakisan halacci ba ko,dama mana tsinatacciyar mage ai bata mage,kisani wlhy talaka irin ki nafi karfin wulakanci daga wurinta,alkawrine nayiwa momy zan kiraki kullum so uku arana,dabadan uwa na uwa ba wlhy bazan kara kiran kiba,jaka kawai dabata san girman na gaba da itaba,kuma Idan kin isa Nakuma kiranki kimun banza,zan miki uzurin bakya kusa amma wlhy bazan miki uzurin rashin kirana back ba,idan katin wayane bakida zan miki VTU yanzunnan" kukane ya kwace mata,jin tana sheshekar kuka yasanya ya kashe wayar dak'yar ta iya saisaita kanta ta koma parlor d'in, momy ta zata wayar arziqi sukayi se washe baki taki,a daddafe ta gama abinda take ta koma gidansu,wanka tayi sannan ta kunna wayarta tayi adu'o in Kwanciya Sekuma ta kasa baccin ta soma kuka me tsuma zuciya,a haka ranar ta Kwana kuka tana mejin zafin zagin wulakncin da yamata,a rayuwar ta ta tsani a Rena mata iyaye da talaucinsu ko sabida kurun suna karkashin inuwarsu bashi ze basu damar wulakan tasu ba,mijin da zaka yana maka zagin na tozarci tunkan ayi auren hmmm...washe gari da ciwon kai ta tashi dama kuma sn fara final exam na kammala secondary skul,ranar ba skul basuda Exam kasa yin komai tayi,Wuraren 9 wayanta yafara ruri janyo wa tayi a wahalce,ta kara da kunne "Assalamu Alaikum" "Alaikissalama" ya fada cike sa isa


STORY CONTINUES BELOW

"Yaa Abdul ina Kwana?"


"Lapia kin tashi lapia?"


"Alhamdulillah" tabashi amsa a takaice "meyake damunki Elham,muryanki wani iri?" haushi ne ya tarnake ta tace "Ba komai qalau nake" shiru yayi itama hakan kusan minti biyu,daga bisani ya datse call din, tsaki taja tace aranta kadaiji da rainin wayonka d'an masu kud'i.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya sam Elham batajin dad'in rayuwar ta, ta tsani Abdul ta tsani kalar wulakancin shi,ta tsani jin koda muryar sane,ta tsani tunawa da zancen auren sa gaba daya,duk sanda ta tuna cewar sun kammala exams gaba d'aya gashi taji ance me martaba ya saka bikin nanda watanni biyu setaji tamkar ta daura hannunta asaman kai ta zunduma ihu,ba karamin dad'i tajiba sanda akace zezo kuma ya fasa zuwa sabida aiki yamasa yawa sabida bata bukatar ganinsa....


Tafe take cikin doguwar bakar jallabiya me adon yellow stones, ga rigar tasha shape,d'an karamin cikinta daya lafe tamkar ba'a saka masa ko loma d'aya aciki,ga wadaccen kugunta daya ke kad'awa batare da tasaka shiba,tafiya takeyi tamkar tanajin tausayin kasa,fuskarta tayi fayau ba komai a cikinta se powder da lipbalm, kallo d'aya zaka mata ka gano sam bata cikin walwala,dadana wayarta take tana faking murmushin.....shi d'inma wayarsa yake dannawa hankalin shi yana wurin abinda yake se karo sukayi da juna take wayarta ta sub'uce a hannunta tafad'i a kasan interlock dake shinfide a wurin tare sukabi wayar har suna gwara kai,hannun tane yariga nashi kaiwa yayinda nashi ya sauka akan nata,lokaci d'aya wani shock ya sauka musu dukkansu atare suka d'ago suka kalli juna,a haka suka k'urawa juna ido tamkar wasu statues,itane tafara dauke kanta,yayinda shi kuwa da sauri ya dauke hannunshi daga nata,atare suka mik'e batare da kowa ya dauko wayar ba,Kawar da kanta tayi akaro na biyu tace "yaa Abdul Kayi hakuri ban kula kana zuwa ba" dukawa yayi ya dauko wayar ya mata kallon tsafta yace cikin gadara


"Duk lokacin da kuke tafiya kuna maida hankalinku akan hanya kina jina?" Kai kurun ta gyad'a masa tana tunanin what on earth was he doing dabe mayarda hankalinshi akan hanyar ba shima,tana tsakiya da tunanin ta tsinkayi murya sa yana cewa


"Wayar kinnan kai tsaye ta lashe screen Elham,ki shirya karfe 8 daidai ki sameni mota zamu fita" batare daya jiyo cewarta ba ya wuce abinshi kazalika be bata wayar taba dashi ya wuce, tab'e baki tayi itama ta wuce part din momy,a ranta tana mejin zafin lashewar wayar ta,harga Allah bataji dadi ba....feenah ce tace da ita "D'an bani aron wayarki Elham inaso nakira Ashraf ntwrk nawa ya dauke d'if MTN basuyi ba Allah" dan rausayar da kanta tayi tace "Yanzunnan nayi karo da yaa Abdul wayar ta cinye screen wlhy,tanama hannunshi"

"Subhanallah wayar nan ko 9 month tayi kuwa? Amma banji miki dadi ba sam,yanzu me yace?"

"Bafa abinda yace,kurun yace na shirya mu tafi wani gu anjima" dan Murmushi tayi tace "Allah sanya wata wayar ze siya miki,nasan shi da kyauta inba hakaba aike da irinta har abada" sarai ta gano abinda take nufi cewar iyayenta bazasu iyaba,bayaga laifin taba kasancewar tasani komai momy ce ke mata.......gidansu ta koma ta tsala wanka ta saka hadaddiyar atamfarta dinkin riga da skirt ja ya amsheta sosai,sosai ta murza dauri yasha steps ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshin,light makeup tayi ta yafa dan mitsitsin mayafinta a kafada,ta dauko yar cloche bag dinta da uban takalmi me tsini tafito cikeda yanga,karfe 7:56 tana wurin motar tsaye yayinda Shikuwa 8 dinnan ya karaso shi d'inma se tashin kamshi yakeyi,turarukansu suka hade suka bada wani kamshi me sanyin dad'i, dukkan ninsu sun shagala da kallon junansu,itane tayi saurin sadda kanta kasa tace "Yaa Abdul Barka fa fitowa" kallon ta ya d'anyi yace "yauwa" motar dayake komai nata is computerized kirar 508 ya bude da remote key nata suka shige,hanyar Hamdan phones ya dauka da ita suna isa yace ta fito,a yangace take tafi yarta ta catwalk ,shi harga Allah mamakinta yake yanda ta dauki kanta,kalli shigar datayi sekace wata yar Sarki,se yauk'i takeyi tamkar zata karye,d'an guntun tsaki yaja yabi bayanta,suna isa suka hadu da samrah da mijin dazata aura kamal,d'an gudu tayi wanda ya qayatar da dashi ta daka tsallah ta rungume samrah, "saam dazu muna chat wayana ya sub'uce mun ya lashe screen nayi bakin cikin baki kara samun hirarba" dariya sukayi tace "akwai gobe zan shigo gidanku saam dolene naji kanun labarai" yana daga nesa kusa da wasu samari yaji dayan cikinsu yace "Baba kalli inda Allah yayi yalwar kugu agun chic dincan me jar atamfa, tsinanniyar yanzu zamu zamuce munasan mud'an latsa ta nuna ita ta manya ce" rayuwar shi ce yaji ta masifar baci,barin wurin yayi yazo ya gasa da kamal da samrah yace "Elham akwai wanda ke jirana muje muyi abinda ya kawo mu,mutafi" sallama tawa qawar tata,sukaje wurin phones ya zaro mata iPhone 7 kurun yace muje" biyan kudin yayi,suka bar shop d'in, duk daba hira sukayi ba sanda zasu zo seta kula ya sauya fuskar sa zuwa bacin rai,gyaran zama tayi tace "yaa Abdul dan Allah ruwa nakeso" ko Kallonta beyiba har suka isa gida,kallonshi tayi tace " yaa Abdul nagode sosai Allah ya kar'a girma da budi" Binta kawai yayi da ido ya zaro wayarta ta dazu,yaciro sim card nata ya bata,karb'a kurun tayi tabar cikin motar,da sauri yafito yace " zonan Hafsat" zuwa tayi kusa dashi ta tsaya yace "Ba'a sanar miki anbiya sadak'in ki bane" shiru tayi rai abace yakuma cewa "Daga yau duk inda zakiji Sekin nemi izinina kuma Wannan guntun mayafin bana sanshi,lallai kiyi Shiga ta mutunci koda bazaki saka hijabi ba" batace komaiba ta juya,hannun ta ya damko ya juya da ita gaba daya ya daura dayan hannunshi asaman kugunta yace "Bakiji abinda nace bane zaki juya kiyi tafi yarki sekace ina magana da iska" numfashin tane taji yana zarya yana barazanar daukewa dakyar ta iya cewa "yaa Abdul dan Allah ka sakeni ba kyau fa wlhy" sakinta yayi ya riko hannunta gagam ya matso daf da ita har suna jiyo bugun zuciyar juna yace

"Ohh Wato sabida niba faruk bane ko? Shi daidai ne ya murza ya kuma shade dukkanin jikinki yanda yaso, kisani wlhy badan najin komai na taba kiba,ke kinmun kazanta na yi Wannan dake ,kisani Kinyi gangan cin shigowa rayuwa ta,kazama kawai" ya sake hannun da karfi anan ta sake kwalin wayar da sim card din ta juya gida da gudu tana kuka....


Tana zuwa tayi Sa'a ba kowa kai tsaye dakinta ta wuce,fadawa tayi kan gado a rigin gine ta saka kuka me tsuma zuciya....duk'awa yayi ya dauki kwalin wayar da sim card d'in yabi bayanta dashi,da sallama ya isa gidan bakowa se k'anwarta Halima,tana ganinshi ta mik'e tsaye daga wanke kwanukan datake tace

"Yaya Yarima Barka da zuwa ina wuni?" D'an kallon yanayin gidan yayi ba laifi Ba kazanta sedai warin dabbobin dasuke kiwo a gefe d'aya, yace "lapia ina Elham?" Dan Sosa kai tayi tace "Ni kadaice agidan amma inaga sanda nashiga Sallah kamar naji shigowarta bara na duba d'akinta" batare data jira cewar saba ta juya zuwa d'akin, dage labulen kofar tayi tace "Aunty Hafsat ga Yaya Yarima yana magana dake" d'an saisaita kanta tayi batare data juyo ba ta ce,banasan tsayuwa a waje,ki kawoshi cikin d'a kinnan" juyawa kurun tayi domin tasan da matsala taje ta kawo shi har kofar dakin tace ya Shiga.....A yanda ta kwanta kife haka yazo ya sameta still kukan takeyi mara sauti sosai,sosai yaji ba dad'i,harga Allah kukan mace na karyar masa da zuciya ya sani kuma sam be kyauta ba yanda ya sakar mata maganganu,Shifa Wannan kurin da nuna cewar ita watace shine yake bashi haushi dashi,dakin yafara bi da kallo komai k'al k'al,gashi bazakace d'akin acikin gidan yakeba se tashin kamshi yake ya hade da Air conditioner dake dakin,kai dubanshi yayi zuwa ga mirror nata,mamakin manya manyan turarukan dake kai yakeyi,albashin ubanta baze siye daya daga cikin suba,lallai momy ta sangartar da Yarinyar nan,a hankali ya tako yazo daf da ita zama yayi kan gadon ya sanya hannunshi ya d'ago ta,batayi musu ba ya dauki kafarshi ya daura har saman gadon ya juyota ta fuskance shi ya sanya hannunshi ya tallafo kanta ya sanya hannunshi ya share mata hawayenta,so yakeyi yace mata tayi hakuri amma girman kai ya hana,tausayinta yakeji amma yanajin kiyayyarta can kasan zuciyar sa,yayi iya yinsa harshen sa ya furta Kalmar hakuri amma ya kasa,ganin haka ya sanya yanjanyota zuwa kirjinsa,a hankali yake patting bayanta,shida ita bazasu fad'i tsawon lokacin da suka dauka a haka,kawai dai gani yayi jikinta duk ya mace dagotan dazeyi yaga tana bacci,mayar da ita yayi kirjinshi yana mamakin kanshi bayaso ya motsa yakasance bacci nta beyi nisa ba ta farka,yakusa 30 mnt tana jikinshi yana jin yanda har lokacin take shasheka tana sauke ajiyar zuciya, ganin baccin nata yayi nisa ya sanya ya kwantar da ita da kyau ya mik'e tsaye yana kura mata manya manyan dara daran inuwanshi,lumshe ido yayi yana mamakin dalilin dayasa yake Kallonta, waige waige ya soma yi a d'akin can ya hango sckool bag nata ya dakko ta ya zaro paper da pen ya rubuta dakyar "I'm sorry Elly,plss call me as soon as u wake up" ya dakko wayar ya zura mata layinta ya kunna sannan ya jona caji ya bar gidan gaba d'aya..+


Wanka yayi ya shirya kwanciya,har ya Hau gado ya kwanta yayi adu'o insa Amma ya kasa bacci, duk motsi d'aya tunano yanayin da suka kasance atare dazu yake,dogon tsaki yaja yace a sarari "Wannan er iskar Yarinyar ta gama sabawa da maza,har ta samu damar yin bacci a jikina muna fukar banza,tagama nuna wa momy itadin ta kwarai ce" har bacci ya daukeshi yana mamakin kanshi yanda ya kasa manta Wannan moment din,dakuma yanda kwalwarsa keta tariyo masa uban tsallen da ta doka a shop dasukaje dazu,yarasa dalilin daya sanya tsallen ke bala'in bugeshi.


Elham ba ita ta farka ba se asuba da mamakin kanta ta duba agogo,tayi mamakin baccin datayi iya saninta bazata tunano sanda tayi bacci sanye da kaya ajikinta ba,ga kuma fitila a kunne,tunano abinda ya faru tayi jiki a san yaye ta tashi taje tayi wanka ta daura alwala tazo tayi sallah,nan ta zauna tana ta adu'a, Idan aurenta da Abdul ba alkhairi bane kar Allah ya tabbatar dashi,tana aduar neman gafarar kwanciya da tayi ajikinshi har tayi bacci alhalin hakan ya haramta a tsakanin su,nan dai ta ga saqon shi,taga wayarta,banza ta mishi se Wuraren karfe bakwai da Rabi ta fito ta gaisa da mahaifiyarta ta daura musu breakfast soyayyen dankalin hausa da kwai,ta hada ruwan shayi ta kai dakin Innah sannan ta dauko nata tazo tadan tsakura,ta ajiye....wayar tane tana yana ringing tana dubawa taga Abdul ne,d'agawa tayi tamkar bata san magana tace "Yaa Abdul ina Kwana" gyaran muryarsa yayi "lapia lau kin tashi lapia elly?" Shiru tamasa yace "karfe tara ki shirya zamuje Kano dake da feenah da Raihan,se bayan sati d'aya zamu dawo Idan munje,zan koma ne nanda wani satin kuma da siyayyar da zamuyi" langwabe kai tayi tace


"Yaa Abdul banida wanakken kaya fa,mafi akasarin dogawen riguna suna gun wanki plss Abari gobe mana,Idan na karbo" sosai ta bashi haushi yace

"Kinga nifa ba laifi na bane,momy ce ta ce lallai yau zamu tafi so kije da kanki ki sanar mata uzurinki" da sauri tace


"Kayi hakuri yaa Abdul bara kurin na ebi laces da atmfa,momy ta hana ni tara wanki fa,kuma kaga jiya na kammala exams ban samu na kaiba"

"Karfe 9 ya miki a mota kinji bana san Wannan African time na kau yanci" kantayi magana ya kashe wayar sa ya kama hanyar part din momy,a gurguje taje ta sanar da Innah da Baba anan takejin seda aka tambayi baban ta ma,har hada ka yanta tayi ta fito waje kai tsaye part din momy ta nufa taje kusa da ita ta zauna tace " momy na shirya" Shafa kanta tayi tace "Allah ya kiyaye Mamana,dan Allah ki kula da kanki sosai ki tsare mutun cinki kamar yanda nasan kinayi,kuma ki kula da mijinki daidai gwargwado,kai kuma Babana lallai ka kular mun da Mamana amana ce na baka kakuma san yanda amana take ko" girgiza kai yayi,ta zaro wayar daya siya mata tace tana kallon momy tana Murmushi "Momy kinga wayar da yaa Abdul ya siyamun jiya,momy ki tayani godiya dan Allah jiya jiyannan tawa ta fadi ta cinye screen d'in" Murmushi momy tayi,har ranta taji dad'i tace "Angode Babana Allah ya saka da alkhairi ya kara bud'i" shima yaji dadin adu'ar ta matuka,a haka sukazo wurin mota dukkansu,Abdul ne ya kalli kannenshi Baba karami da Ashraf gasu feenah yace "Baba karami,Ashraf,feenah da Raihan ku karbi key din range dinnan ku biyo ni abaya,da mota biyu zamu tafi ni zan tafi da Elham" yana fad'a tamkar yayi kuka,Wannan tsarin momy ne,su kuwa masoyan dama haka sukeso se murna sukeyi zasusha hira soyayyah,Ashraf d'ane wurin yayan momy daya rasu kuma a hannunta yatashi, shine ze auri Feenah a yanzu haka yana aikine da kamfanin MTN,kayan lefe ne akace suje hadowa shine zasuje.....


Yamma likis suka isa Kano,a Tahir guests palace hotel sukayi masauki,kallon Baba karami yayi yace"k'arami wayannan matan a kama musu suit Babba,ku kuma kujewa d'aki d'aya " kallon shi yayi yace "Yaya Abdul kaifa?" Wrist watch nashi ya kalla yace "Ba anan zan sauka ba ku dai ku zauna anan,kuma dan Allah banda shishirta,kusan wayannan yaran matsayin kannen ku suke ku kula da mutuncin su" haka kawai Elham taji ba dad'i tace tana shagwabe wa "yaa Abdul dan Allah kaima ka zauna anan" kura mata ido yayi nay'an dak'ik'u yace yana mayarda kallon shi ga Baba karami "Zan muku waya goben ku shirya early,zamu fita da range dukkanin mu" Da sauri ta sake jakarta tazo ta rike masa hannu "yaa Abdul dan Allah ka zauna anan hotel d'in" cikin fad'a ya warce hannunshi yace "ke Wannan wane irin rashin hankaline,kece zaki gayamun inda zan zauna kokuwa,bakida hankali" take idonta ya ciko da k'wallah su feenah suka kwashe da dariya sosai Wannan ba karamin bata ran Elham yayi ba,har ranta taji zafi.....bece komaiba ya ja motar shi yabar harabar hotel d'in, dakin da aka saukesu kowa tayi wanka aka kawo musu abinci suka ci banda Elham yoghurt kurun tasha tace ta koshi,silent ta saka wayarta ta fito waje,tasamu wurin flower bed dake zagaye wurin ta sadda kanta tana kuka me ban tausayi,kyakyawan saurayin datun fitowarta ita yake kallo yazo ya zauna wurin yace,cikeda iya tsara kalamai


"K'anwata duk abinda yayi zafi magani nsa Allah,da Wannan kukan dakike dama zuwa kikayi kika daura alwala kika nafila ki mikawa Allah kukanki,kuka baya maganin kowace irin damuwa a rayuwa dan Allah ki sassauta kukannan my sister" a hankali ta d'ago ta kalleshi tana Murmushi tace "Nagode da kulawarka dan uwa,Allah yabar zumunci zan gwada inshaa Allah" Murmushi yamata yace, ko zaki taimakamun da phone number dinki,ina tare da mahaifina Munzo wa'azin kasa da akene kuma yanzu zamu tafi" batayi musu ba ta bashi number yabar wurin yana mata Murmushi, bata saniba komai daya faru akan idon Abdul ne. Cikin dare tasha kuka ba ka danba,washe gari kuwa kowa yashirya fita banda ita,sukace da ita tazo suje tace bazata ba,mamaki sukayi Raihan tace "wa kikeso ya zab'a miki kayan to? Banza ta musu sukayi tafiyarsu,koda sukazo mota yaga Batanan,yace dasu tana na? Wai tace bazata ba,bece komai ba ya nufi d'akin,kwance ya sameta yaje ya zauna kusa da ita yace " Elham I'm sorry kinji" kallonshi tayi tace what for" dakyar yace "about yesterday mana" juya masa baya kurun tayi ta soma.Kara matsawa yayi kusa da ita yace cikin sanyin murya "Hafsat dan Allah ki tashi muje,koso kikeyi kowa seya fahimci halin damuke ciki" dakyar ya iya furta kalaman ban hakurinnan,tunawa yayi da maganar momy datace karya kuskura ya b'ata ran mamanta,Shiyasa kurun yake rarrashinta kuma sarai ya sani feena seta gayawa momy cewar ga abinda ya faru,banza ta masa ya sanya hannun sa ya dagota,da sauri ta kwace hannun nata ta kara matsawa cikeda fusata,beta ba ganin ta harzuqa irin haka ba,d'an tattaro hakurin daya rage masa wuri daya yayi yace cikin d'acin murya


"Hafsat kin sani ni d'innan ba sa'anki bane ko? Kuma sarai kin sani yarannan rainani zasuyi Idan har sukaga namiki magana kin k'i ji,plss mana hafsan momy Fulani,tashi ki shirya muje" murya na rawa cikin shagwabar daba ta ma san tanayi ba harda kwallanta tace

"Allah ni yaa Abdul bazan biku ba,yanzunnan zaka disgani su feenah kuma sumin dariya,ni ba wanda yake sona kowa ma ya tsaneni" fashewa tayi da kuka shi abinma dariya ya so bashi,zuwa ya mikar da ita tsaye yace hannayenshi biyu duka a kafad'un ta "Bazan disgaski ba I promise,jiya d'in ma Aina ce dake sorry,kuma yau ma nan zan kama dakin Nima,waye ma yace dake ba me sanki? Kowa ma yana sanki Elly, baga momy ba dasu Inna?,plss kije ki shirya muje kinji?" D'an tsukakken bakinta ta turo takuma yamutse fuska dama wanan dabi at tace tace "kaje waje yanzunnan zan watsa ruwa na shirya mu tafi" Kallonta yayi yana dan kasalallen Murmushi yace "zan jiraki a parlor and plss karki wuce 10 mnt" daga nan ya bar d'akin a gurguje ta shirya cikin doguwar riga me santsi kalar sararin samani ya,ta yane kanta da guntun mayafi pink color, jakar ta yar k'arama kalar pink takalmi nta masu uban tudu ma pink ne,powder kurun tasaka da lipstick pink and purple dan tsukakken ba kinnan ya had'e karshe,kwalli ta saka take manya manyan fararen Ida nuwanta suka k'ara girma hasken su yakara bayyana,tasowa yayi domin yaga abinda ya tsaidata kusan 30 mnt,yasani su Ashraf ma sun gaji sabida kurun suna tsoron sane suka k'i kiransa,a daidai lokacin daze Shiga d'akin ita kuwa lokacin take kokarin fitowa,karo sukayi take  ya bangajeta taje taga taga zata fad'i da sauri ya tarota jikinshi,kasa magana yayi ya k'urawa tsukakken mitsitsin bakinta ido,ita kuwa ta tsare shi da manyan idanuwanta yana kallon su kuwa ta lumshe su wanda hakan ba karamin saukar masa da kasala yayi ba,take kuma kamshin turaren ta ya gama rud'ashi,saurin saketa yayi yace "I'm sorry Elly, bansan kina zuwa ba" wara manyan idanu Wanga tayi akan nashi tace "Ba komai Nima ban kula kana zuwa ba I'm sorry" janye wa yayi ta wuce yabi k'ugunta da kallo gani yake tamkar danshi take Wannan rausayar,Murmushi yayi aranshi yace " yarinya bazaki rud'ani da Wannan rangwadar da shagwabar muna funcin dakike ba wlhy" koda suka fito kowa ya gama k'osawa Raihan ce sarkin baki tace a fusace "Wai mutum shiba kowa ba galadiman tsumma,yariqa d'aukar kansa wata tsiya,kawai zaki mana iko a karin banza ki barmu anan for more than an hour" batace komai ba,Ashraf ne me tuki,baba k'arami yana dayan gefen,yan matan susu uku suka Shiga baya,yayinda Abdul ya zaga gefen da Elham take ya zauna,lura yayi da yanda tsukakken tommy d'inta ya lafe ya kulleta yace "Elham have you eating?" D'an lagwabe kai tayi batace komai ba,Raihan ce yar iyayi tace " yaa Abdul bafa abinda Wannan taci tun zuwan mu anan,kasan halinta da k'yank'yamin masifa,yoghurt tasha jiya yauma haka" d'an Kallonta yayi ta d'auke kanta daga dubanshi yace,yana meso ya b'atawa Raihan rai karta gane baya san Elham,ko basason juna

"Elham mesa? Ban hanaki zama da yunwa ba? Kalli fa yanda flat tommy naki ya k'ara shigewa ciki,Ashraf plss take us to a near by restaurant" d'an narkewa tayi harga Allah ita batasan cin abincin wani restaurant arna ne fa sukeyi kuma ba tsarki sukeyi ba tace


"Noo plss yaa Abdul,zansha yoghurt I'm sure it will be OK" d'an mayarda dubanshi yayi kan hanya yace "Ashraf muje restaurant kawai" shiru ta masa ita harga Allah batasan cin komai na wuri,Mr Biggs ya kaisu kowa yafita shikuma ya riko hannunta haushi duk ya gama kashe Raihan,har k'arami ya fahimci hakan,shima hannun nata ya kama yace "kema zakici abinci ne habibty?" Da sauri tace zataci,koda sukaje suka zauna waiter yazo Elham se cewa tayi wai popcorn da ice cream takeso se fayrouz,hannunta Abdul ya riko yace murya k'asa2 "menene haka kike zama da yunwa? Sanar dani me Wannan k'walamar zasu miki' zuba mishi idonta tayi tace


" I'm sure zasu k'osaddani,so worry not plss" kallon waiter din yayi yace "fried rice with fried chicken plss" juyawa yayi aka Wadata su da abinda suke buqata d'in,cikeda yanga Elham kecin popcorn d'in kai kace tilastata akayi,tana wani yamutsa fuska,itafa wannan abin dake baiwa mutane haushi akanta bata masan tana yin shiba,hasalima haka Allah ya halicceta,matsa kujerar sa yayi kusa da tata ya sanya hannu ya kwace kwalin popcorn d'in yace "Hafsat bazaki bari momy tace nazo dake Kano na bari yunwa ze halla ka ki ba,so maza bud'e baki shinkafa zakici" spoon din ta kaiwa kallo taga cewar na roba ne alamar dispose one ne,tamkar zatayi kuka ta wara bakin ya saka mata,tana tauna shinkafar tamkar mecin magani,shidai bebi ta kanta ba,haka yayita bata sanda taci kusan Rabi ya kara ebo wa ze bata ta janye kanta,kallonta yayi alamar me hakan yake nufi,ta langwabe kai kurun,kara matsawa yayi da spoon din bakinta ta karayi baya "Elham Sefa kin cinye shinkafar nan tatas" bata fuska tayi tace "yaa Abdul Allah na k'oshi kuma fa kagan inaso zanci popcorn na da ice cream" Murmushi ya sub'uce masa aranshi yace"kini babbiya kyadaiji dashi kike wani mun karairaya sekace anga ya miki ni Wannan yana tasiri ne akaina" ita kuwa aranta se cewa tayi


"Mugu Wato sabida kurun suyi tsammanin yana kulawa dani,ta yanda ko aure mukayi nace yanamun wani mugun abin ba wanda ze yadda dani"bece komaiba,kurun ya mike yabar wurin Raihan se cab'e fuska takeyi,amota suka taddashi ya zauna inda yake zaune d'azu,tun daga nesa ya kurawa flat tommy d'inta ido,sosai yake mamakin duk abin cinnan data ci Tommy d'in nanan yanda yake dazu tamkar ba abinci aka zuba masa ba yanzu,Idan kaga tsukakken cikin bazaka yadda ka sanshi ke dauke da wayannan manya manyan Heeps da duwawun ba,dukta yanda ta cira kafarta tana tafiya ilahirin bayanta da gefen cinyoyinta motsi sukeyi,shi wasu lokutanma tsoro take bashi wlhy,a hankali ya d'aga idonshi zuwa dukiyar fulanin ta, yaa ilahi ya furta adaidai lokacin da suke kokarin shigowa motar ganin Raihan ta zago gefenshi yasanya yafito da sauri ya nufi shagon tamkar yayi mantuwa yaje ya dawo,ya zauna gefen Elham ya riko hannuta,wayarta yake kallo k'aya taccen pics nata data saka wall paper ya kurawa ido harga Allah yana san hoton,ba karamin kyawu hoton ya masaba,a haka suka isa shop na sammanin fatihu,mamakin yanda su feenah suka dage sunata kwasar kaya yakeyi ita kuwa ya kula she's too materialistic,and tana da high test ba komai bane yake burgeta sedai batada zalama, ta ebi  jallabi yu masu kyau da tsada black ones dakuma coloured one's sunfi kala talatin,kawai taje ta zauna,kallonta Abdul yayi yace "Elham kin gaji ne?" D'an yamutsa fuska tayi tace "yaa Abdul ba gajiya bane ina wayannan sun isa" harara ya wurga mata yace sauran su Lace's fa da atamfa material,shaddoji?" Murmushi tayi "bana saka shadda sam,Lace's kuma da atamfa,hmmm aikawa nadan duba suma sun isheni" haushin tane ya cikasa yace "kinga bazaki hadani da momy ba wlhy,dukkanin kayan da kika eva sunfi kala hamsin ne? Kuma acewarta 150 set za'a miki nikuwa anawa ra'ayin 200 zanyi so maza muje har abinda be mikiba ki Zara,naga wasu dresses a shop na friend d'ina jiya suma muje ki kwasa" kallonsa kurun ta tsayayi,a haka yaja hannunta ya dinga jibagar kaya tamkar besan darajar kudaden sa ba,haka kowa ya siya kayan ba laifi,saura aka barwa gobe kurun...... Yamma sosai suka dawo masauki,Elham ce tafara yin wanka da Sallah sannan sauran ma sukayi,batare da sun sanar mata inda zasu ba, suka caba ado suka fice,bata wani damuba tayi kwanciyar a dakin tana dannan wayar ta,kira ne yashigo,taga bak'uwar lamba,d'agawa tayi da salkamarta,shi d'inma ya masa,suka gaisa yace "sunana Ibrahim,nine wanda namiki katsalandan jiya,ma ina sone muyi sallama,karna bar gari bamuyi sallama gobe asubar fari zamu juya zuwa abuja,Idan bazaki damuba mu hadu a inda na ganki jiya" batayi masa musuba ta saka dress ta roba da siririn mayafi sosai surarta ta bayyana a hakan tafito,zama tayi abinda ta sameshi suka kara gaisawa,yace dama ze mata sallama ne,yayi mata wa'azin yanayin shigarta a kaikaice sannan yace "Hafsat inasan sanin menene yakawo ki Wannan wurin ke kadai hotel ne fa" Murmushi tayi tace

"Yaa Ibrahim ban t'aba zuwa hotel ba sam,Wannan ma daka ganni nida yayyu na maza nazo,dakuma yan mata irina susu biyu Munzo hada  kayan lefene daga Adamawa muke,yan gidan sarkin Adamawa ne yayin da Nike yar me gadin gidan sarkin tuni,babban d'ansa zan aura,shine mukazo da kannensa maza da mata dayake auren gida Zakuyi dukkansu hadin kayan lefe" gyad'a kanshi yayi alamar gamsuwa da baya ninta yace


"Se yanzu nakejin saukar nutsuwa akaina,da farko harga Allah na tsorata nazata cewar wani abinne yasanya kike gudo daga Allah ya albarkaci auren da Zakuyi, ina fatan zumun cinmun baze yanke daga nan ba" gyad'a masa kanta alamun ba abinda ze tsinka musu igiyar zumunci,ya zaro wani kwalin har guda biyu ya mik'a mata,godiya sosai ta masa,sukaci gaba da hira tamkar dama can sun saba,se dariya yake sakata,can ta hango Abdul ajikin mitarshi ya hard'e hannayenshi a k'irji yana kallonsu ya murtuk'e fuskarnan tamau,ta abin ma tsoro ya bata, sauri tayiwa Ibrahim sallama tajuya dakinsu....bayanta yabi yana zuwa ya banke kofar d'akin ya shiga,bata nan tana bedroom, kai tsaye yabita can fin cikota yayi yace a fusace. Uban waye kike zance dashi kullum a waje? A ina kika sanshi? Kuma ya akayi yasan kin zonan?" Rikicewa tayi gashi ya mata rikon da bazata iya daurewa ba,take ta fara zubar da k'wallah,+


"Yaa Abdul Kayi hakuri dan Allah wlhy anan muka hadu kuma gaisawa kurun mukeyi" wurgar da ita yayi yace "Anan kika sanshi dakika tafi ina kuka had'u? Wato iskancin naki na kula ba akan faruk kadai ya tsaya ba har wasu kartin banzan ko" kukan tane ya tsananta jin furucin shi, janyo ledar yayi yace yana bud'eta "har agogo ma yake baki da turare,shiya sanya kike mu'amala da turarukan dasuka fi karfin talakan ubanki, kin daukar wa kanki rayuwar datafi karfinki ,dole sekinyi abinda wasu masu kudin sukeyi shine kike bin maza ko,wlhy Wannan kaddararren auren da banka d'ad'd'iya irinki asarane,dabadan nayiwa momy alkawarin aurenki ko bayan rantaba ba ba kaddarar dazata sanya na aureki,kuma ki shirya wa kanki zaman kunci a gidana,banza kwad'a yayyiya Wama ya sani ko asircemun iyaye kukayi keda talakawan iyayenki dabasu san halacciba,banza jaka kalli shigar ki menene marabar da yar tasha haihuwar bakin kasuwa,wane me hankalin ne ze ganki ya zaci cewar ked'innan musulma ce? Wlhy an cuceni had'ani dake Hafsat Allah ya isa tsakanina dake, Sekin d'an d'ana kud'arki a hannuna wlhy" fusata tayi yanzu kam tamik'e tsaye tace tana me k'ank'ance idonta cikeda masifa


"I have had enough now yaa Abdul! Nagaji! Nagaji! Kuma wlhy Nagaji! Duk iyakar abinda zakamun zan d'auka amma wlhy karka kuma sako mun iyayena,ba kinnan nawa dakake gani bashida ragowa,ni ba yar iska bace ba,kuma ban gada ba,jikina be taba haduwa dana wani ba dasunan zina kuma duk wanda kemun kallon mazinaciya na Barshi da Allah ciki kuwa harda kai,kasani wlhy badan ina sanka kodan wani abinka zan aureka ba,sabida darajar momy ne kawai dame martaba,naga alama abin naka nasan ya wuce gona da iri kana zagarmun iyaye to my face,ni ka sani iyayenka har abada iyayena ne, kuma duk wanda ya zagesu agabana se inda karfina ya k'are,sabida nasan darajar manya na,zancen zaman k'unci dakake cewa zanyi a gidanka Ai tunba Yauba na shirya wa hakan,bakada wani farin ciki karan kanka dazaka bani da har zanyi mafarkin zaman farin ciki agidanka,zancen yanayin Shiga I will admit it nayi laifi,kuma ina fatan kasan cewar Allah nawa laifin bakaiba so awurinshi nake neman gafara Ba kaiba,so na gode da tunatarwa,dan Allah karka k'ara zuwa inda nake,karka k'ara kirana awaya,kullum kamun d'aya daga ciki da bakin ciki nake kwana,dashi kuma nake tashi,ba abinda yafi mun ciwo irin wai ace mijin dazaka aura shine yake zargin ka....." Kasa karasa wa tayi ta durkushe awurin tana kuka me ban tausayi, Shikuwa jikinsane yayi sanyi,seyake ga koda hakane mazina ciyar ce cin zarafin yayi yawa,beside wane tsautsayinne yakaishi zagin iyayenta,shida kanshi yasani Baba hasan dattijo ne me kirkin gaske,sam bashida hayaniya shekaru kusan talatin yake gagi agidan,tun yana dan shekara 5 aka kawoshi gadi gidan kuma amana ta sanya haryau ba'a sauya wani ba,take yaji ya tsani kanshi kuma se wata zuciyar ke bashi watakil ma ba wani abin Elham keyi itada faruk ko wanin shiba,gwiwa asace ya juya ya bar d'akin gaba daga kansa ya kunce,basu feenah suka dawo ba se shad'a yan dare,zuwa lokacin zazzb'i me zafi yagama rufeta,kanta ba kad'an ba yake Sara mata,zuci yarta zafi takeyi sosai duk sanda ta tuna da maganganun Moris setaji tamkar kasa ta bud'e tashige sabida tsanar kanta da tayi,sosai wutar qiyayyar moris ta k'ara huruwa a birnin zuci yarta, ji take tamkar ta kurma ihu sabida tsananin zafin da kalamnshi ke mata a rai,kwanciyar sukayi batare da sun san meke damun taba,cikin dare Wuraren karfe hudu ta farka da wani razannanen ciwon kai,ga rawar sanyi tanayi jikinta yayi zafi rau tamkar gaushin wuta,dakyar tamatsa kusa da feenah ta d'an bubbuga bayanta,tsaki feenah taja tace dan La Elly rabu dani,bacci nakeji" haka tayita tashinsu basu tashiba,da asubar fari ta mike domin yin Sallah tana matukar ganin jiri,kasawa tayi taje ta kwata,Raihan ce ta tashi ta kunna fitilar d'akin ta dawo ta tashesu itama tashiga ban d'akin tai alwala,tana fitowa taga basu tashiba,ta kara tashin Elham aikam tana mikewa ta sulale wurin ta fad'i,da sauri Raihan ta tareta,jitayi jikinta zafi sosai ,tace "subhanallah Elham dama bakida lapia har haka baki sanar wa kowa ba?" Kasa ansata tayi,dakyar tace "Raihan ku kaini wurin Innah mutuwa zanyi kaina ze rabe gida biyu" feenah ma tasowa tayi tazo ta na tattab'a jikinta rikicewa sukayi ganinta galala,da sauri feenah ta janyo wayarta takira Abdul,yana d'agawa tace " yaa Yarima mun Shiga uku Elham zata mutu wlhy bata da lapia sosai, bata ma iya tashi faa" beyi magana ba ya kashe wayar dama yana d'akin kusa dasu daya kama jiya,aikam da gudun shi ya nufo dakin yayi knocking Raihan ta bud'e masa, yana zuwa ya dauketa ya dora kan gadon,sosai ya rikice jin jikinta tamkar wuta,yace da sauri feenah ta kira masa Ashraf Raihan kuma ta dakko masa ruwa me sanyi da towel,take yafara bata tapinsponge se rirrik'e sa takeyi abinda ya kula ma sambatu takeyi,Ashraf na zuzuwa da kanshi ya kwashe ta zuwa mota suka kaita wata alfijir hospital,likitan yace damuwa ce tamata yawa,jininta ke kokarin hawa amma dai be Hau d'inba,se an bata injection da k'arin ruwa,Abdul ya tsorata dajin Wannan zancen,kaddai maganganun shi na jiya neke daga mata hankali har haka!!! Koda akazo amata allura kasa Tsayawa tayi seda Abdul ya riketa, drip na karewa ta samu karfin jikinta aka sallamesu,Abdul da kanshi yake jinyar ta,Shifa arayuwa yanzu bala'in tausayin Elham yakeji ga masifar kunyar ta dayake ji,ita kuwa duk ta bud'i idonta ta ganshi tsanar sace ke kara ruruwa a cikin zuciyarta.

*Bayan kwana d'aya*


     Yana zaune kusa da ita yana bata ayaba dakyar takeci amma ko kallonahi Bata sanyi yakuma kula da hakan,kallonta yayi cikin sanyin jiki yace "Elham dan Allah kiyi hakuri akan abinda na fada miki 2  back wlhy bacin Raine,abinda na fada bawai har raina bane" banza tamishi ta k'ara dauke kanta,yace "Dan Allah Hafsat kice dani kin hakura mana,nasani kalamai na ne suka jefaki a Wannan halin dakike ciki,dan Allah kiyi hakuri kinji" kuka tasaka masa,Shikuwa ayan kwana kinnan tausayin ta yakeji yarasa dalili wlhy gashi kuma bata bashi fuska,cikin rudu yace "kinga Idan zancen ne bakyaso kiyi hakuri na dena wlhy kinji Hafsat" kukan tane ya tsanan ta,harga Allah bata koda sanjin muryar Abdul wlhy ta tsaneshi.....


Tir qashi ga alamafa Abdul ma ya jajibowa kanshi qiyayyar Elham matuqa,gashi shi kuwa yafara yin laushi,muje zuwa dai kuna tare da alk'amin mom Nu'aiym....Zuwa yayi ya durk'usa daidai inda take zaune ya kamo hannunta ya rike,ta kwace hannun ta ta dauke kanta sannan ta rufe idanuwanta rufe,dafe kanshi yayi yana mejin zafin abinda ya aikata agareta,Shifa bawai yana Santa baneba,kurun dai tausayi take bashi kuma ya sani be kyauta mata ba sam iyaye ba abin wasa bane,matsawa yayi kusa da ita ya zauna yace cikin sigar rarrashi


"Elham mana ki sassauta Wannan fushin dakike dan Allah,Idan muka koma gida kina haka momy zatayi zaton wani abin,ki sassauta wa kanki kinji,kumafa doctor yace damuwa ke damunki" cikin kuka tace


"Yaa Abdul Idan ka fice mun daga rayuwa wlhy zan daina kuka,Idan kadena zuwa wurina,kadena kirana,ka dena damuwa da tawa damuwar,ka manta dani arayuwar ka wlhy zanji sauqi,dan Allah yaa Abdul ka taimakeni kace dasu me martaba bazaka aureni ba,wlhy banasan auren nan dakai,gwaramun na mutu ba aure dana auri wanda besan darajar iyayena ba yake mun kallon fasik'a yake wa iyayena dani kallon matsafa kuma masu kwad'ayi wlhy Yaya Abdul Idan aka daura mun aure dakai mutuwa zanyi,bazan tab'a manta muggan kalaman ka agareniba,Karfa ka manta har cewa Kayi wlhy ka tsaneni,dan Allah yaa Abdul.....kukane ya k'wace mata sosai,Abdul ya rasa ina ze tsoma ransa,tunda yake arayuwar sa be tab'ajin kunyar dayaji ba a yanzu,se yanzu yake gano d'imbin kuskuren daya tafka na kallon Tsakiyar idonta ya gaggasa mata maganganun marasa dad'i, musammamn tafuskar zagin iyayenta dakuma tsanar ta daya furta mata kanshi tsaye,menene ma ya aikeshi cewa ya tsaneta? Ko makiyinka na gaskia bazaka cewa haka agabanshiba,kallonta yayi idonshi har ya kad'a yayi jajir ita d'inma ta tsagaita kukanta shi take kallo, take ya hango tsanarsa k'arara acikin idonta,tashi yayi yabar d'akin  batare dayace kanzil ba,har wani duhu yake gani,yana zuwa d'akinshi ya kwanta se hawaye,gaba d'aya rayuwarsa ta masa k'unci shidai harga Allah bayasan Hafsat amma ya kasa gane tsakanin tausayinta da kuma kunyar ta Wanne yafi sakashi a k'unci a ce da girmansa da komai ya aikata abinda ko d'an shekaru baze aikata ba,wayarshi ya janyo ya dannawa Zayyan kira,suka gaisa sannan be b'oye masa komaiba ya masa bayani ya kara da cewar

"A k'alla ni a ganina be dace na sako iyayen ta ba akoma menene,wlhy zayyan kunya nakeji,kuma na kula Yarinyar ta tsaneni matuka kofa kallona bata iyayi,zayyan koda bana san Yarinyar nan aure fa zamuyi? Kuma fa kaga banida tsarin mata biyu,bayaga haka ba saki tsakanina da Elham haka zamu yita zama?" Nisawa zayyan yayi yace


"Moris Kaine kana da matsala wasu lokutan,nasha fad'a maka cewar yanda kake yi ba'a haka,nafasan Elham ba tun yauba,zan yadda da zancenka na iyayinta da kad'ifirin tsiya amma sam ni bana kawowa raina wai tana wanna abin,yanzu dai ka ajiye zancen Wannan k'iyayyar gefe ka rik'a rarrashinta kana bata hakuri,ninake gaya maka a hankali zaka koyi santa Ba kad'an ba" shimad'in nisawa yayi yace


"Zanyi yanda kace,amma kam zancen soyayya tsakanina da Elham har abada,Bance ma kuma tana zinaba amma dai idona ya ganemin suna wasanni mara kyau da faruk wanda har abada bazan manta Wannan ba,kazalika baze barni na iya had'a makwancina da nata ba,kasancewar ina kyamar ta wlhy" tsaki zayyan yayi yace


"Kanka akeji dai moris mace daice,wlhy tsaf zata rikita maka lissafi,a yanda na lura ma ta fara gigita mun kai" tsakin shima yayi yace "D'an rainin hankali kanka dai akeji wlhy" daga nan sukayi sallama ya koma ya kwata yana nazarin kalaman zayyan.....da yamma su feenah suka fita suda su Ashraf shi kuwa yazo d'akin wurinta,a zaune ya taddata saman sallaya tana adu'a  ta idar da sallah,zama akan gadon yana jiranta,tana idarwa ta Kawar da kanta gefe d'aya tace "yaa Abdul ina wuni" da k'yar, d'an Murmushi yamata yace "Lapia lau Elly ya jikinki?"

"Da sauqi" ta ansashi a tak'aice,nuna mata kusa dashi yayi yace "zoki zauna anan Hafsat" bata Musa masa ba taje ta zauna,ya ja hannunta ya riqe yace yana Murmushi

"Nifa banga kina shirin Wannan bikin ba fa,duk gayunnan naki bazaki hada mana wani abinba" bataso ta bada shi ta kula hirar yakeso kuma duk dan ha Kawar mata da damuwa ne,Murmushi tayi tace

"Yaa Abdul nifa banasan wani bidi'an yanzunnan zakaga ance nacika iyayi,walima kurun zanyi" hannunta dake rike da nashi ya matse sanda tayi k'ara kadan yayi dariya yace "kin Cika raki d'an wannan abin kikewa ihu haka,Nakuma sani bakyaso k'awayenki Su ganni fine fine bobo Su mak'alemun shiya sanya bakyason bikin" tafa kula so yakeyi ya mantar da ita abinda ya faru,bashida labarin cewa har abada bazata dena jin zafinsa da kiyayyar sa ba,kallonshi tayi tace " Ea mana Kaima kasan ai koda auren akayi Idan Nayi bak'i a d'aki zaka zauna" yaji dad'in yanda tad'an sake masa,hannu yakai daidai wuyan ta yatab'a yace yana kallonta ita d'inma shi take kallo

"Har yanzu da sauran zafi jikinki Hafsat,dan Allah ki rage damuwa kinji" Murmushi tamasa itafa harga Allah yanacin albarkacin momy ne tace "Naji sauqi fa,kurun dai kwad'ayi nakeji wlhy" murmushin sa ya fad'a d'a yace "me kikeso Kici to?" Langwabe kai tayi tace "popcorn da ice cream" hancinta yaja cikin wasa yace "kwad'ayin kenan oya dress well mu tafi" mikewa tayi ta zare hijabin jikinta ta yane kanta da yalolon mayafi,kallonta yayi dress dake jikinta ya d'ameta da yawa ga heeps sun bala'in fito,wani iri yaji ajikinshi yace murya k'asa k'asa "Hafsat plss mana,yanzu Idan na barki seki fita a haka dan Allah? kowa fa ze gama kalleki" d'an Murmushi tayi tace a shagwabe "Yaa Abdul meye aciki dan Allah nafa saka mayafi" komawa yayi ya zauna yace " ki saka hijab kokuma mu fasa fita gaba d'aya " komawa tayi ta d'auki hijab d'inta ta saka tace "to muje na saka"

"Yauwa  ko Kefa? Kinma fi kyau ahaka Allah kuwa" a haka sukaje suka dawo tun a hanya ta shanye roba biyu na ice cream se kallonta yakeyi ko ajikinta,anan fa ta fara fyace hanci lokaci d'aya mura ya taso mata amma bata dena shaba,suna Shiga d'akin suka tarar dukkansu sun dawo har mazan suna kallo, har lokacin ice cream d'inta takesha,wara ido feenah tayi tace " na Shiga uku,yaa Abdul hope dai Elly batasha ice cream d'innan da yawaba momy fa ta hana,ranar damu kazo ma naga kinsha namiki shiru ne sabida d'ayane kurun" kallonta yayi yace

"Bata shan ice cream sabida me to?" Kallon shi taku mayi tace "she's Asthmatic fa,kuma ire iren wayannan qanqarar sam basa bata lapia agida ma ko ruwa me sanyi ba'a bari tanasha" mayar da dubanshi yayi zuwa gareta yace "Hafsat hakane? Wannan fa rofa na ukune kinada hankali kuwa?" Turo baki tayi tana me fyace majina da tissue dake hannunta "kurun ni se'a riqa takurani,koma waye yana jin dadi bandani" nan take ya murtuke fuska dama Abdul akwai saurin Fushi1


"Danla can rufawa mutane baki,ke d'innan yar rainin wayau ce wlhy kinsan bakida lapia kike shan abinda ze cutar dake tsabar rashin sanin ciwon kai,maza bani ice cream d'in yanzu" tana shagwaba hadda doka kafa a kasa  da k'un k'uni  tabar wurin "Allah ni anbi duk an takura ni ice cream dinne bazan shaba kuma bayan kowa ma abinda yake so yake sha" galala ya saki baki yana kallonta harta bacewa ganinsa,kurun seyaji ta bala'in bashi Sha'awa,Binta baya yayi,ya zauna kusa da ita yace "Elham ni kuma kikewa k'un k'uni? Lapiyar ki fa nake dubawa" d'an rausayar da kanta harda kwallah "To Kayi hakuri bazan k'araba,amma plss ka bani na karasa shanye wa" Murmushi yayi yace "Zan dai hakura amma bazan baki ba gaskiya" kan wani cikinsu yayi magana har wayan ta ya soma ringing, Murmushi tayi ganin yaa Ibrahim a rubuce, da sauri ta daga wayar ta kwanta tana duban roof na d'akin a shagwabe tace "Lallai ma yaa Ibrahim,Wato se yau kake tunani,Allah ni Nayi Fushi bazan ma maka magana ba" wani d'aci ne ya tunkaro k'irjin Abdul tun daga kan dan yatsan sa har zuwa zuciyar sa da kwanyar sa,yana tsakiya da tunani yaji tana cewa "Ea mana Nayi bala'in missing hirar ka tun juya fa,Banyi dariya ba" da sauri ya mike yabar d'akin zuciyarsa she zafi take,wanda be san dalilin hakanba.Koda ta kammala wayanta ta juyo ya tafi,kwanciyar ta tayi bata kawo komai aranta ba,harga Allah ita be wani dameta ba,shi kuwa moris kasa koda kwanciyar yayi aranshi yana tunanin wanene Ibrahim? Hankalin shi ya tashi matuka,ya kasa gane mesa ya damu haka,wani barin na zuciyar sa yace dashi,kishi kishi ke damunka Abdul,yayin da d'ayan sashen na zuciyar sa yace dashi,kurun sabida zaka aureta ne bakajin dadin ganin tana huld'a da wasu mazan, "that's all" ya fad'a a sarari "Mema ze saka Nayi kishinta tunda ba santa nakeyi ba nikam" wanka yashiga ya fito ya saka jallabiya ya kwanta amma ya kasa bacci har karfe biyu na daren ranar idon sa biyu....cikin bacci Elham tasoma jin bata iya numfashi da kyau,dama kuma da mura sosai ta kwanta har tari takeyi,feenah ta tayar tace da ita "Feenah I'm sick,I cnt breath well,could u plss help me with my inhaler?" Mik'ewa tayi da sauri ta kunna side lamp d'in d'akin tace "Where d u keep it then,seda nace karki sha Wannan kayan sanyi amma bakyaji" kasa ansata tayi sabida abin ya taso mata sosai,ko ina feenah ta duba bata ga inhaler d'in ba,wayar ta,ta janyo takira Ashraf yana d'agawa tace dashi "Kazo yanzu plss Athsma d'in Hafsat ya tashi kuma gashi na duba ba inhaler d'inta" tashin baba karami yayi yace "Plss ka tashi muje gunsu feenah Waifa er matsalar nan Elham Athma d'inta ya tashi,shine zamuje muga halin datake ciki,zuwa sukayi suka yi cirko cirko akanta,se neman inhaler akeyi ita kuma tana fama da kanta, Ashraf ne yace " kaga K'arami kira yaa Abdul....." Yana zaune yana salati ya idarda da nafila kasance wa ya kasa bacci sabida tunanin Wannan Ibrahim da Elham ke waya dashi,yaji phone nashi na ringing,harta katse be tashi ba,harga Allah be kawo komai aranshi ba haka call d'in ya k'ara shigo yayi banza dashi,a tunaninshi wani balarabe ne dasuke huld'a dashi kasan cewar Su yanzu gari ya dade da wayewa,ganin fa Elham na shirin shrqewa ya sanya Baba karami ya soma danna mata k'irji,feenah ce tace "kunga dan Allah Kuzo mu kaita asibiti, Wannan athsma d'infa Idan ta tashi mata dole se anmata allura,da d'azu ne ma akaga inhaler ze sauka amma yanzu yayi nisa aminipilin injection kurun za'a mata ya sauka" Raihan ce tace "Hakane amma Inaga mu fara sanarwa Yaa Abdul koda ta zuwa d'akin sane tunda yana kusa" Ashraf ne yaje ya masa knocking,da mamakin sa ya bud'e ya k'urawa Ashraf ido,a rud'e Ashraf yace


"Zata mutu wlhy yaya mutuwa zatayi" kallon shi yayi da mamaki dauke a fuskar "kai ka nutsu mana wacece Zata mutu?"

"Yaa Elham ce fa Athma ya tasarwa,munyi kiran wayarka baka..." Ai bankeshi kurun Abdul yayi be tsaya ya karasa jin zancen ba,da gudu ya Shiga d'akin ganin k'arami na dannan mata k'irji ya sanya yaji wani bakin ciki ya taso masa,hawa kan gadon yayi ya dagota saman cinyar sa,gani yayi sam bata numfashi bata ma motsi rikicewa yayi lokaci daya ya kwasheta suka rufa masa baya seda ya sakata a mota sannan ya tuna da key,dagudu yaje d'akin ya had'o da wayanshi da ku d'ad'e,asibitin dasuka kaita ranar ya nufa,da sauri suka karb'eta aka danna mata ox da komai da injections,Abdul se zirga zirga yakeyi dawowa wurin Su Ashraf lokacin sun dawo sallar asuba yace "Waiku kuwa wane iskancinne ya hanaku kirana tun d'azu Idan da wani abin ya samu Yarinyar mutane me zakuce?"

"Yaa munfa kiraka baka d'aga ba,ka duba wayarka" kan wani yayi magana doctor d'in yace "Patient naku ta farfad'o,dama kunsan case na athsma yana sauka da Wannan injection da sauri,sedai ku kiyaye abubuwan dake saurin tayar mata da asthma" da sauri yaje d'akin, yana zuwa yaje wurinta ya riko mata hannu "Sannu Hafsat ya jikin?" Murmushi tamasa tace yaa Abdul zansha ruwa dan Allah" da sauri ya bude robar ruwan dake gefenta ya daga ta,asaman jikinshi ya kara ta ya bata tasha,gani yaye ta lafe ajikinshi ya sanya be d'aga taba yace cikin sanyin murya


STORY CONTINUES BELOW

"Elly bansan meyasa ba Idan bakida lapiya hankalina gaba d'aya yakan tashi,dan Allah na rokeki ki guje wa duk wani abinda ze kawo miki rashin lapia musamman irin Wannan,nafa Zata mutuwa zakiyi ki barni hankalina ba k'aramin tashi yayiba plss ki dena shan sanyinnan" mamakin kala manshi ne ya sanya ta d'ago ta kalleshi k'wallan datake kokarin tarewa ya sulalo,hannu ya saka ya share mata k'walar ya mayar mata da kanta saman k'irjin sa yana patting bayanta a hankali "Noo plss Elham banasan kina yawan kukannan Alhamdulillah kinji sauqi,koda inda yake miki ciwo ne?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,da sauri yace "sanar mun inane gayamun kinji,ina yake miki ciwo" janye jikinta tayi daga nata,ta kwanta tace "k'irji nane yakemun zafi,kuma se ina jin ribs nawa tamkar iska me sanyi tana Shiga cikin ribs d'in" kurawa dan tsukakken bakin ta ido yayi yanda take magana tana yamutsa fuska dukya gama burgeshi yace "zan sanar wa doctor yanzu I just cnt leave u in pain" Murmushi ta masa tace "Thank you" b'ata fuska yayi da wasa "Sabida na kula da Lapiyar matana kike wani cemun thank you bana so" Murmushi kurun tayi batayi magana ba.


A daddafe suka karasa kwanakin biyu da suka rage musu suka dawo gida da yola,daga kaga Hafsat kasan batada lapia ta d'an rame,ba laipi Abdul yana kula da ita sosai,suna dawowa da kwana biyu ya wuce London......


Abdurrahman Allah yayishi da ilimin Zane tun yana karami,kuma Allah ya daukakashi har girmanshi Zane ba irin wanda bayayi,a London kampanonin dake k'era motoci yake zanawa mota,yayinda har kampanonin builder's yake zanawa gida,a yanzu haka yanada kampanin sa na kansa Abdul builder's  dake birnin London,ba k'ananun kud'ad'e yake samu a harkar ba,ya kasance yaro ne d'an k'walisa meji da kansa ga tsananin k'yank'yamin masifa komai nashi CA's dashi.......

   

     Satinsa uku ga dawo,a parlorn sa yake yana kallo tayi sallama ta shigo kasancewar ya sanarwa feenah Idan tazo part din momy ta Turo masa ita phone nata a kashe yake,har qasa ta durk'usa ta gaidashi,da Murmushi d'auke a fuskarsa ya ce "Zonan ki zauna kusa dani Elham" batayi musuba taje a kujerar da yake ta zauna ya kalleta sosai ya janyo hannunta na dama ya rike yace

"Elham mesa kika mun haka?" D'auke kanta tayi zuwa d'ayan side d'in tace cikin wata murya me sanyi

"Yaa Abdul me na maka" karkatowa yayi gefenta ya daura kafafuwan sa gaba d'aya saman gadon yace "Yanzu ke baki masan me kika munba? sati na uku bana k'asar seki kama wayarki ki kashe gaba d'aya,abin takaicin ma nacewa feenah ta baki waya wai kin tafi gidan k'anwar mamanki,dagaske kin kyauta kenan Elham?" Sosai ta juyo ta k'ura masa ido,tana mamakin yanda yake rero kalamai tamkar da gaske,mutumin dayace ya tsaneta ina ruwansa da damuwa da inda taje" iska ya hura mata a ido,ta gyara zaman ta,sannan ta kalleshi ta k'ara ya mutsa fuskarta tace "kaga nifa sauqi namaka,ina dama ko tafiyar damukayi akan momy kake kulawa dani,yanzu baka gari menene ze dameka danna kashe Wayata beside ni a ganina wanda ka tsaneshi ai sauqin kane idan ya janye jikinshi daga naka" Hannunshi d'aya ya saka ya dafe kanshi yace "yaa salaam,Haba Hafsat wayene yace dake na tsaneki?" Murmushin yak'e ta masa tace "Yaa Abdul kenan,kasani matsalar furuci kenan ka furta akan idona kuma idanuwa na suna kallon naka sanda ka furta hakan na hango tsanar tawa k'arara a idonka da zuciyarka gaba d'aya" hannunta dake riqe a nashi ya matse sanda ta kwallah k'ara yace "Haba mana Hafsat,dan Allah ki dena furta irin wayannan kalaman kinji" kallonshi tayi tace "Ka gani ko yanzu fa ka kasa furta cewar ba k'iyayya ta aranka,kurun kace na dena zancen,naji Kayi hakuri bazan k'araba" juna suka k'urawa ido na yan dak'iku yayinda Abdul ya kasa gane ainahin meyakeji game da Wannan baiwar Allah ita kuwa tsanarsa fall a ranta sunan sa ma bata san ana anbata,shine ya Kawar da shirun dacewa

"An sanar dani kince ke kurun a daura aure bakyasan wani bikin mesa ?" Kallonshi tayi dama taci d'amarar gaggasa masa magana tace "Ba bikin bane banaso  auren nakane yake batamun rai wlhy banaso yaa Abdul,zargi na fa kake kuma kace ka tsaneni Wannan wane irin zama zamuyi,yaa Abdul bansan wazan sanarwa ba amma wlhy gabana fad'uwa yakeyi,tsoro nakeji" matsawa yayi kusa da ita ganin tana kuka,ya tallafo ta jikinshi,ita kanta mamaki takeyi yanda bata iya tureshi idan yazo jikinta. yace cikin rad'a "ki dena jin tsoro Elham,kuma gaban ki ya dena fad'uwa I promise to always be by ur side,dan Allah karki badani kowa fa jiran ranar aurena yakeyi,ki saki jikinki muyi bidirin mu kinji?" Bata yi magana ba kamar yanda bata bar jikinshi ba dan kanshi ya janye jikinshi daga nata........ba laifi Elham ta saki jikinta an cashe kuma na narke dukiya a Wannan bikin,sunsha gyara na musamman taciki data waje ba inda basusha gyara ba,fatar Yar fulanin yola se sheqi takeyi, komai iri d'aya aka saka musu ita da Su feenah.....


*Bayan ankai Amare*


      Yan matan Amarya sun watse,ya rage Amarya kurun,Abdul ya daukar wa kansa alkawarin baze tab'a barin ya rab'i Elham ba,shi harga Allah kazantar ta yakeji,sannan kuma batada matsuguni acikin zuciyarsa sam,kazar Amarci yashigo da ita a hannu,ya mata sallama,batare da wata kulawa ba yace

"Kici abinci kafin ki kwanta seda safe" daganan be jira cewar taba tafice daga d'akin,kuka sosai Elham tayi a Wannan daren,a ranta tace Wato dama ya kyalenine sabida agama bikin,yanzu nazo gidan na zama banza ko,daga nan ta kudiri niyyar cin ubanshi,kazalika ta dauki alkawarin baze taba ganin bacin rai a fuskar taba.....Abdul se zirga zirga yakeyi a d'akinshi ya kwasa bacci,ya rasa dalilin daya sanya zuciyar sa keta faman azalzalarsa akan yaje gun Hafsat,yanaga koba komai zataji sanyi,betab'a jin abokanshi sunce sun kwana d'aki daban daban da matansu ba musamman sabuwar Amarya, haka dai ya hakura ya kwanta dukda a wannan bacci sam be dauke shiba, da safe ma yaso Shiga d'akinta amma seyaji nauyin yin hakan....a b'angaren Elham kuwa Wannan rashin shigowar da safe ba k'aramin b'ata mata ranta yayiba,kuma ya kara nuna mata cewar ita da banza basuda maraba ko kad'an,sosai kuma taji ta qara sanarsa,tasani da faruk d'inta ne baze tab'a yi mata haka ba,wata k'ila ma sam zumud'i baze bari yabar kusa da itaba,kuka ta zauna ta saka ita kad'ai bame rarrashinta,tana Tsakiyar kukan wayanta ya soma bulayin neman agaji,dagawa tayi taga saam ce aminiyar ta da kukan ta d'aga bata boye mata komaiba,saam cewa tayi mata "Kinga ina gidan Aunty Husnah dama tace Zata baki tips na horar dashi sabida haka bara na bata,idan kina kuka kinma damu kenan" wayar aka baiwa Aunty Husna suka gaisa tace+


"Kinga Hafsatul Elham share hawayenki,yanzunnan zan saving digit naki a waya zanna riqa d'auraki akan service wlhy se yamiki magiya akan gwiwowinsa kekuwa alokacin zamu nuna masa cewar tabbas shayi ruwane,zamu tauna tsakuwa sabida aya taji tsoro kazalika zamu jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya jal,Abu na farko danakeso dake shine ki cirewa rayuwar ki qiyayyar sa sabida mijinki ne zawarci masifa ne,sannan kuma qiyayya jafa'i ne wlhy, komai zece da iyayenki kansa yayiwa Allah ne masani,yanzu sanar dani kina da k'ananun kaya?" Tana share majina tace "Ea dama ni nafi shiri dasu da dogwayen riguna" Murmushi Husna tayi tace "Yauwa yar gari,inaso ki cire abinda yake halla ka matan hausawa Wato kunya,ki rataye a kwandon shara,mijinki Ne ba haramci ko tsirara kika fito masa,Ki fara dannan guntayen riguna da wanduna da d'amammun kaya kina rafka uwar kwalliya,na sanki da yalwar gashi ga jiki me daukar hankali,lallai ne ki rama wulakancin daya miki idan ya kawo kanshi domin dolenshi ma yazo,karki kuskura ya gane kinci ciwo,kuma ki masa girki na wuce sa'a,ina fatan dai kin koya agida kosai nazone?" Dan Murmushi ya sub'uce mata tace "A wurin momy Fulani ba kalar girkin daban koyaba,har na turawa ma sanda take a k'asar waje tana koyamun,kuma Alhamdulillah na dauke Su tsaf,sanda mukaje Kano Hutu ma da ita ta sakamu catering school na kusan 3 weeks har snacks muka koya,a school kuma Nayi food and nutrition da home economics" dariya ta bushe dashi tace "Kai Wannan zancen yamun dad'i yanzu dai dan Allah ki riqa wanka da ruwan miski,kuma had'in magarya da bagaruwa na tsarki ma ba dole se kanada aure ba,kurun ki daure kina had'awa zan aiko miki da  butar k'arfe kina saka karan fari a  ruwan da Jan miski Harma da farin kisaka ganyen d'od'oya idan baki dasu duk zan aiko miki,karkuma naji kina tsarkin ruwan sanyi wlhy,ruwan d'imi Sune ruwan tsarkin ki,kuma kina yawan wurga karan fari a bakinki seyayi laushi yana hana warin baki kinji?" Godiya sosai tayiwa Aunty husnah sannan tana Ajiya wayar ta yi dariyar mugunta sosai ta gano yanda Aunty Husna keso suci uban Yarima me jiran gado cikin ruwan lolxxx....


   Tashi tayi tashige cikin toilet ta watsa ruwa abinta dama tanada farin miski momy ce ta bata kusan kwali uku,ta tsiyaya a ruwan se tashin kamshin miski takeyi tako ina,wata bingilallaiyar riga ta saka pure red me adon red stones agabanta,rigar iya karta gwiwa,gashi ta dameta ta d'ago da dukiyar fulaninta sun leqo waje ta baje gashinta batare data tufke shiba gashi bak'i wuluk se sheqi yake abinka da yar fulanin usul,ya sauka har gadon bayanta,a karonka na farko da ita zaka rantse cewar ba indiya ka gani,wani hula wanda bata rufe tsakiyar kai ta tsakiya ta zagaye kanta dashi ta sako gashin ta baya,janbaki me taken rubiwu ta saka a lips nata ta sanya kwalli me fito da blue color a take ta fara shanawa a fuska ma,kwanar turaren turarenta Na slim girl ta Shafa da sauran Su tomphord woman da daddy's girl ta saka sannan ta fito,a parlor ta taddashi yana zaune yana shan hot coffee yana kallo,cike da takun katsaita ta tinkaro inda yake,kamshin turaren tane ya shaida masa iso warta wurin,cup na coffee dazekai bakinsa ya dakatar yabita da ido,harga Allah be gane taba,murmushin ta me laushi ta sakar masa tace cikin wata hatsabibiyar murya "Ina kwana yaa Abdul dafatar ka tashi lapia" dak'yar ya saisaita tunaninsa sabida seda ma tayi magana ya tabbatar ita d'ince yace "Good morninh wify how was ur night" yafad'a yana kallonta wani wal tayi da ido tace "splendid yaa Abdul,kaifa?" D'an Murmushi yayi yace "Same as urs,u looking so wow" wani far tayi da ido "thank you yaa Yarima,me kake sha?"

STORY CONTINUES BELOW

"Coffee,will u like some?" Yabata amsa yana kuma tambayar ta, Mik'ewa tayi daga zaman tace "No thank you,lemme prepare something for u to eat" wani Murmushi yayi "for me or for us?" Ya tambaya D'auke da Murmushi a fuskarsa,ita d'inma Murmushi tayi,tace "sure for the both us"

"That's very good of u" bata kulashiba ta wuce se mazaya mazaunan ta takeyi,da kallo yabi Heeps nata,seda ya had'iya wani yawu me d'aci,sannan ya kawdda kanshi a daidai lokacin da ta b'acewa ganinshi,yace aranshi "Kinada diri Elham sedai bazaki dulmiyar dani ba,Wannan kad'ifirin naki a banza kikeynshi" A gurguje ta feraye dankali ta soye ta had'a kidney sauce ta soya k'wai,ta had'a ruwan tea,ta d'auka taje ta Jere Su a dining, ta zo ta zauna kusa dashi tace "Breakfast is ready" Mik'ewa yayi ba tare da ya kalleta ba yace "Shall we" shi adole ze D'auke idonshi daga kallonta,sabida Shifa ba wai yana santa  bane kuma yaga alama so take ta d'aga masa hankali da Wannan k'ayatacciyar halitta me d'aukar hankali,kamar yanda be kalleta ba haka itama ta Kawar da kanta tace "sure" zaman cin abincin bameyin magana harsu ka kammala,dukkaninsu suna tafiya ne da tarbiyar momy ta rashin magana idan anacin abinci,yarigata kammala wa ya kalleta yace "Thank you so much,its soo delicious" Murmushi kurun tamasa ta bar wurin zuwa,parlour d'inta,acan ta baje tana cin kwakwa da dabino data gani a kitchen ta ebo dama cimar tane acewar Sophie G vitamin.....karfe d'aya ta tashiga  kitchen koda ma ta duba yabar gidan be sanar mata ba Murmushi kurun tayi tace "A iya sanina dai duk wani namiji me mutunci idan ze fita ko Allah ya kiyaye ze nema agun matarsa amma banda Wannan,tunawa tayi da momy ta d'auki wayarta ta kirata,gaisawa sosai sukayi tace " Ina me gidan naki? " d'an Murmushi tayi cikeda kunya tace "yanzunnan ya fita momy" Murmushi itama Momyn tayi

"Kuyi ta hakuri mamana,kiriqe mijinki hannu bibbiyu na sani dukkanku biyayya kikamun amma da yardar Allah zakuga sakamakon yiwa iyaye biyayya kuma zaku k'aunaci junanku ba kad'anba" godiya tawa momy,Momyn tace "ke Mamana kina da nutsuwa kinga yar uwarki feenah da masifa ta isheni wai aika musu da abinci ba nace aiba wacce ban koyawa girki acikin kuba so bazan wahalar da kaina ba" dariya tayi "momy se hakuri kinsan halin feenah akwai shagwaba" ahaka dai suka sha hira kan suyi sallama.

Fried rice me yawa tayi da meat balls tayi salad na potatoes ta had'a zob'o se tashin kamshin karan fari yake da cucumbers, gidan gaba d'aya ya had'e da k'amshin girkinta,se Wuraren karfe  uku ta kammala girkin,wanka tayi ta dauro alwala,tana nan har akayi la'asar ta tashi tayi salla sannan tashirya cikin wani rantsatsen lace pink colour me flowers red aciki,ba k'aramin karbarta yayi ba ya fito da figure 8 d'in tannan CA's da ita ta tufke gashin kanta tsakiya ta fito dashi ta baya,fuskar arna tasha makeup idan ka ganta tamkar ka sace ta ka gudu,uban takalminta me tsini ta saka red ta fito tana tauna chewing gum dake bakinta,sanda tazo tsakiyar parlor d'in takula da Abdul moris da friends d'inshi Su hudu, d'anja da baya tayi sannan ta gaidasu,kafe ta da ido yayi sanda take magana dasu,d'an mitsitsin bakinta yake kallo ga fuskarnan tasha makeup tamkar ta ziyarci wani makeup studio,tace dasu


"Bismillah kuci abinci mana" zayyan ne cikeda zolaya yace "Dama mana kin isa muzo ki hanamu abinci aikinyi kad'an inba haka gobe zamu kara auro wata" dariya tayi har fararen haqoran ta suka bayyana tace "Aini kishiya se idan Anayi a lahira honey da kake gani ba kishiya a tsakanin mu ko ya kace honey?" Tafad'a tana me k'urawa Abdul ido tana dariya, yawunshi ya had'iya yace "Hakane sweery bazan miki kishiya ba har abada" cikin takunta na kasaita tajuya zuwa kitchen wani abokinsu yace da sauri batare dayasan tana jinsa ba"kai yanzu moris tsabar kai d'an iskane Wannan zangad'ediyar zakace bakaso shegen banza kawai" kawai moris seyaji haushi jin ancewa Elham zankad'ed'iya aranshi yace "data saka hijab da bazega surartaba har yace hakan,dining suka nufa Dukkansu ita kuwa koda ta karasa kitchen idonta ya Cika da kwallah aranta tace " Wato Harma friends nashi sunsan ni fankon ashana yafini daraja baya sona,ni ina kokarin nuna musu ana tare shi kuwa ba Wannan a tsarinsa ko?" Da k'yar ta iya saisaita kanta tafito tafara serving nasu tana dan Murmushi, lura Abdul yayi Wannan friend d'in nashi khamis ya matsawa Elham da kallo take yaji wani takaici dabesan dalilin saba,yabi heeps nata da kallo yaga tamkar ita ta dasawa kanta,yace "ki Barshi mana zan saka musu" Murmushi tamasa "Honey lemme just do it,its nothing ai" Noo u go and get us some fresh fruit's for me now" sake masa serving spoon d'in tayi tawuce cikin yangarta,Zayyan ya mikawa spoon din yabi bayanta,janyo hannunta yayi yana Shiga kitchen d'in ya rungumota ta hanyar rik'o k'ugunta ya sanya d'ayan hannunshi ya tallafo kanta ta bayan wuyanta,suka k'urawa juna ido na kusan second talatin itace ta fara d'an yamutsa fuska tana kokarin barin jikinshi,k'ara k'ank'ameta da kyau yayi yace "Elham me haka kikeyi?" D'an wara ido cikeda mamaki ta k'ara yamutsa fuska tace cikin shagwaba "Yanzu kuma yaa menayi" kara matseta yayi jikinshi yace

"Kinganki kuwa,kalli jikinki Elham mesa baki saka hijabi ba? Kinga mazancen fa se kallonki suke" tsuke bakinta tayi sannan tace "Yaa Abdul to yanzu kuma baza'a kalleniba,kurun sabida kai ka tsaneni kowama so kake ya tsaneni?" Shiru yayi kuma be saketa ba yana nazarin kalamnta,cikin sigar rarrashi yace

"Elham ki dena cewar wai na tsaneki,ba kyaufa kina cewa wai na tsaneki nifa mijinki ne" kara tsuke fuska tayi tace "kaga bafa ni bace nace haka Kaine da kanka kafad'a so yanzu me kakeso nace? Ni plss ka sakeni" sassauta riqon daya mata yayi yace cikin sigar rarrashi "Amma dai kin sani cewar ai ke matar aurece,dan Allah ko mayafi ne kisaka mana" gyad'a masa kai tayi alamun to,tama Zata sakinta zeyi se kurun ya kasa danne kwad'ayinnsa ya manna mata Sumba a kunci sannan ya saketa....juyawa kurun tayi tana mazaya masa k'ugu tana rangwa d'a anan ya tsaya amace......Koda dare yayi a parlor ta sako riga da wando na bacci gajeren wandon me aljihu ya fito da Heeps dinnan,ta baje gashinta me kyau kwantacce tazo ta zauna suna kallo tanashan fura daya kawonmata ba mewa wani magana,se Wuraren sha d'aya tamike tace "yaa Abdul I'm Danma sleepy,off to bed good night" Murmushi yamata "Bazaki bari film dinnan ya kare ba mu tashi tare?" Murmushi tayi ta cura hannunta cikin gashin kanta,tayi wata tsayuwa ta Turo k'afarta d'aya gaba tace tana yamutsa fuska"karka damu yaa Abdul bancinnan da gaske yake,idan ka tsayar dani wlhy anan zan maka bacci,kuma na tsani a tashe ni ina bacci" gyara kishingidar sa yayi "Bazanma tashe kiba cak zan d'a gaki zuwa room naki" tab'e baki takumayi ta  yamutsa fuska tace "I will not like that either, so just lemme go,good night" bata jira cewar saba ta juya,tun a parlor d'inta ta rufe da key,beji dad'in hakan ba yaso tayata bacci yau,yayinda a d'ayan bangaren ta kudirta baze tab'a Shiga sashinta da sunan bacci ba"


Tir k'ashi  muje zuwa to,koya Wannan zaman ze zama,kuci gaba da kasancewa da alkalamin mom Nu'aiym.

Post a Comment for "HAFSAT CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...