Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

FARA YAR SHEHU CHAPTER D KARSHE

FARA YAR SHEHU CHAPTER D KARSHE

- - Post a Comment

 FARA YAR SHEHU CHAPTER D KARSHETantama na shiga yi akan abinda naji ya fito daga bakinshi, favor yace nayi mishi na aureshi ko kuma auditory hallucination ne ya sameni lokaci guda. Idanuna na dago na sauke cikin nashi wanda ya tsareni dasu, zaku rantse da Allah kuce amsar tambayar tashi cikin idanuwan shi take.

"Can you do me a favor of marrying a bachelor like me?"


Ya kara maimaitawa, haka kowa yake ji idan akai masa proposing. Yanayi ne sabo da ban taba jin makamancin irinshi ba, to ta ina zanji tunda babu mahalukin daya taba cewa zai aureni? Kowa sede yazo ya gama wasa da zuciyata sannan ya wullar da ita inda yaga dama.


"Asmau, ba se kin amsa ni yanzun ba, sede kin ganni bana da hakurin jira, waiting really sucks kingane?"1


A hankali na gyada kaina kamar wata sokuwa shi kuma ya cigaba da fadin


"Ni ba yaro bane, kema you don't look like a teenager, gaba dayanmu adult ne mu. To ya kamata dukkan approach dinmu ya zama very matured. Dan Allah Asmau don't make me wait!"


Kasa nayi da kaina inajin wani sashe na zuciyata na fadin kice kin yadda, kice kin amince amma bazan iya ba shima ba lokaci daya yaji yana sona zai aureni ba, it took him time kafin ya fahimci me yake bukata. Shirun da mukai yafi na mintina biyar kafin yayi breaking silence din da fadin


"Ashe dubiya nazo fa, ya jikin naki?"


Dan murmushi nayi a raina ina fadin jinya kam ai ta tafi sede wata amma ka rigada ka wanke duk wani dafi da tsatsa dake kanta. A zahiri nace


"Jiki yayi sauki Alhmdllh. Nagode......."


Mikewa yayi yana hararata yace


"Ki cigaba da godiyar nan dana hana"


Mikewa nima nayi ina murmushi nace


"Idan akai maka abin arxiki, is not bad when you show your gratitude right?"


Bansan ya expression din fuskata yake ba da nayi maganar, abu daya na sani nadan daga girata. To yadda ya tsaya yana kallona da bakinshi da hancinshi ya shagala sosae har seda na rufe fuskata da gefen veil dina kafin ya girgiza kanshi yana wani irin murmushi wanda idan zai kwana yanayi bana tunanin zan gaji da kallonshi, he looked so charming and loving.


"Hakane kam, why not ki adana mana hakan se right time yayi"


Dan murmushi nayi bance komai ba Shima se yace zai tafi yana son sallama da Abba, kallon snacks din da aka kawo mishi dadu lemu nayi amma bai taba komai ba hakan yasa nace


"Ummaah zatayi magana baka ci komai ba"


Kallon gurin yayi sannan ya kalleni yace


"Bake bace kinzo kinata kallona ta yaya zanci abu na kware"


His funny side na ayyana a raina ina dariya, karshe se packaging akai musu, su su Raudha sunci nasu. Seda yaje ya gaida Inna tana ce masa


"Kai yanzun Abbas ka rasa wa kake so se wannan kodaddadiyar, ina laifin ni?"


Yayi dariya yace


"Ai karki damu kece uwargida kuma mowa, ita zata shigo a yar aiki ne."


Gaba daya mukai dariya inata kallon shi ban taba tunanin he has this side ba, farkon ganina dashi kawai naga serious mutum da bai san bata lokaci ko wasa ba, shidai foremost thing shi ne kayi aikinka kada ya kama ka da laifi. Na yadda da mutane sukace never judge a book by its own cover!


"Ko kada Na tafi ne, naga se kallona ake?"


Hararshi nayi ina mita cikin raina akan dalilin da yasa nake ta kallonshi. Nan yaje gurin Ummaah nan babu wasa se girmamawa da darajawa kafin su Raudha suka tashi bayan Abba da Ummaah sunyi mata kyauta nima na duba dakina na samo chocolate da sweet na bata, suka aje min kayan dubiya inata mitar hakan na rakasu har bakin mota. Ina saitin Maman Raudha tace min


STORY CONTINUES BELOW

"Se munji magana me dadi"


Dan murmushi nayi cikeda kunya ina shafa fusakar Raudha, kallona yayi daga dayan gefen yace


"Kiyi bacci da wuri very early zamu wuce"


Kaina na gyada masa suka tafi ni kuma na koma gida, tamkar bani nake kukan nan da nayi dazun ba, i was so so happy har dana shiga daki kawai kan gado na fada tareda rungumo pillow a kirjina ina jin kamar zan maida shi cikin jikina, farin cikin da nake ciki kasa misaltuwa yayi, mikewa nayi na dauro alwala nazo nayi raka'o'i biyu na godiya ga Allah inajin a jikina komai yazo karshe. Jin Ummaah na kirani yasa na cire hijabin tareda wullar dashi na daidaita kaina na fito sede fuskata betrayed me dan wani kyakyawan murmushi ne yaki barinta, dukkan dimples dina a lotse suke.

Kallona Ummaah tayi sannan tace


"Yar fara wannan murmushi haka?"


Rufe fuskata nayi nace


"Kai Ummaah"


Jikinta na kwanto ta shafa bayana tace


"Allah ya zaba mafi alkhairi, kiyi istikhara ki nutsu sosae. Duk wanda yasa Allah a lamarinshi bazai taba dana sani zabin shi ba. Ok?"


Kaina na gyada na tafi gurin Abba shikam tambayoyi yayi tayi min akan Dr Abbas wanda na sani na fada idan ban sani ba kuma nayi shiru. Nasiha sosae yayimin se naji kamar auren gobe ne, harda kwalla ta.

Washegari sunday muka tashi da mummunan labarin sakin da yaya Suleiman yayiwa Nadia, ni gaba daya na manta da abinda ya faru kwatkwata. Inna ta dinga murna tace gwara taje ta koyo tarbiyya Ummaah ta korashi akan indai ya dauketa kamar ta haifeshi to ya mayar da Nadia, saki ba koda yaushe yake gyara ba kuma Nadia tayi rashin hankali amma se ya barta da kunyar haduwa damu ma nan gaba. Abba daya ji kamar zai daki yaya Suleiman yace ya wuce ya dawo da ita.  Wajen laasar ina zaune a parlor da system dina ina kara harhada presentation din da zanyi akan Spinal Bifida, dake duk monday akeyi kuma wannan turn dinmu ne.


Kamar daga sama naji sallamar Yaya Suleiman ko dagowa banyi ba amma na amsa sallamar, zama yayi se lokacin na dago naga shida Nadia ne, tayi zuru zuru idanunta sunyi jawur, dan murmushi na kirkiro na musu sannu da zuwa tareda kwalla kiran Asiya akan ta kira Ummaah nikuwa na cigaba da aikina. Ummaah na zuwa na tattara kayana na koma daki dan nasan hakuri aka zo bayarwa ni kam meye nawa a ciki. Ta rigada ta nuna min matsayina gurinta so ko komai ya koma normal alwai abinda har abada an wuce gurin.


Ina karasa kallon love in the moonlight se naji ta turo kofar ta shigo, pausing episode din nayi har ta zauna ta kasa magana haka nima tunda ni banida abin ce mata. Hannuna ta kama tace


"Kiyi hakuri"


Kaina na gyada nace


"Ya wuce"


Se mukai shiru nikam na cigaba da kallona har ta gaji da kanta tayi min sallama. Kamar jira ake ta fita sega kira ya shigo, seda nayi murmushi kafin na daga kiran


"Sir barka da yamma"


"Barka dai Asmau, kin gama compiling presentation din?"


Kaina na gyada nace


"Eh na gama"


"Nice of you, turo min na gani"


Kaina na sake gyadawa nace


"Sure Sir"


Daga haka mukai hanging na tura masa ta mail sannan na tafi nayi sallah se wajen tara na dare ya turon na duba naga corrections din da yayi.

Washegari karfe shida da rabi na gama shiryawa, tea kadai nasha yazo muka tafi. Tunda muka gaisa bai kara cemin komai ba seda muka wuce mariri sannan yace


"Asmau ya maganar mu?"


Da sauri na kalleshi bama kallona yake ba idanunshi yana kan titi hakan yasa na janye idanuna slowly ina tuna maganar Adda Sa'ada data cemin yanzun babu jira, babu sanya kawai i should let things flow naturally kawai.


"Can i blow the winds up for you? Can i treat you like the most precious lady that ever existed in this world? Can you do me the favor of marrying me?"


Ya fada yana kallona bayan yayi parking gefen titi, bazan iya daurewa ba, ba zan iya ja ba kuma words din are so sincere yadda suke fitowa daga bakinshi. Kawai ce mishi nayi


"You most welcome!"1


Kallona ya dinga yi da wani kwantaccen murmushi daya kara kayatar da fuskarshi yayi kyau, ga rana data ratso ta window ta sauka kan fuskokin mu. Dauke idona nayi ina murmushi tateda jin wata nutsuwa ta mamaye ni kamar wani puzzle ya kamata na jera kuma na jera din.


"Naso ace ke din halaliya tace , i would have hug you kiji yadda zuciyata take bugawa. Babu damuwa soon, very soon zan cika mana burinmu. Inshaaa Allah bazkiyi dana sanin amincewa da aurena ba"1


I was emotionless ban ma dago ba ganin bazanyi magana ba yasa ya fara driving muka koma hanya har lokacin kaina yana kasa ina wasa da zoben dake hannuna. Cikin wannan yanayin na tsinkayi muryar shi yana fadin


"Sunana Abbas Aliyu Kwaccido, mu asalinmu fulanin sokoto ne. Kwaccido family name dinmu ne. Mahaifina shi ne dan sokoto, mahaifyata yar kebbi ce a arugungu. So kinga dukkan su dai kusa da kusa suke. Mahaifina dan kasuwa ne wasu dalilai yasa ya koma hadejia gaba daya da zama. Babban yayana Umar shi kadai aka haifa a sokoto suna zuwa hadejia babu jimawa ya rasu. Ni ne dansu na biyu a yanzun ni ne babba a gidan daga ni se Maman Raudha wadda mukazo dubaki da ita. Se autar mu hajara ita ce kamar zakuyi sa'anni da ita kuma tana sokoto tana aure. Bayan barin Alhaji sokoto se ya samu wasu yan uwanshi suka biyo shi shi ne muka tada wani familyn anan. Se ya zaman mu mun tashi a matsayin yan jigawa tunda mun samu indigene by birth. A hadejia nayi primary school dina, seda na gama sannan aka kaini unity school a kwara anan nayi secondary dina baki daya har na kammalla. Allah ya taimakeni sciences nayi, kuma WAEC dina tayi kyau so da aka tashi bada scholarship harda ni anan naje russia nayi medicine and surgery, duk shekara ina dawowa hutu haka dana gama nazo nayi internship dina na koma nayi Family medicine se suka rikeni nayi musu aiki na shekara biyu a haka ina kara fadada karatu na har na samu na dawo. A Aminu kano na fara aiki kafin na koma murtala muhd daga nan na tafi germany nayi wani course akan dialysis. Ina dawowa aka bani MD a hadejia bayan na koma Kazaure se kuma na dawo nan only to meet the love of my life"2


Murmushi mukai dukka a tare sede na gamsu da bayanan sa amma akwai abinda nake bukatar ji daga bakinshi kamar yasan me nake tunani yace


"Izzatu, cousin dita ce. Mahaifinta shi ne babban yayan su Hajiya. Itada Maman Raudha sa'anni suke dukda Maman Raudha ta gurmeta da akalla shekara daya amma duka same boat suke. A lokacin suna Abuja da sauran yan uwanta daga baya mahaifinta aka bashi Ambassador a Russia so kusan duk karatun da nayi a embassy dinsu na zauna. Dukkansu maza ne a gidan ita daya ce mace kuma basu jituwa da ita saboda been the only female child se ta zama over pampered child. Kusan ko da yaushe muna tare da ita ni nake kaita makaranta kuma na dakko ta. Bazan iya cewa ga lokacin dana fara sonta ba na dai san wannan shakuwar ita ta rikeda mana ta zama zazzafar soyayya. Ban taba son wani abu kamar yadda na so Izzy ba, she was everything I ever wanted Asmau amma Allah is the best planner. Muna haka na gama karatuna, lokacinda zan taho tayi kuka a ganinta mun rabu kenan shi ne dalilin da yasa na dawo na karba aikin da aka bani a lokacin tana year 2 a nursing son sena jira ta gama muyi aure amma Abban Abuja yace da zarar zan koma nigeria da matata zan tafi. Hakan ba karamin dadi yayi mana ba, aka shiga shiru mudai kullum a shiriritar soyayya muke. Haka lokaci yazo muka dawo nigeria dan ayi aure. Sede tunda aka fara bikin Izzy ke wasu irin weird maganganu kamar Allah sarki naso na zama matarka da maganganu iri iri wanda sede nayi dariya har aka daura aure...."


Se yayi shiru tareda parking motarshi a gefe, dagowa nayi na kalleshi he looked disturbed, idanunshi har sun canja, se naji jikina yayi sanyi hakan yasa na bude baki zanyi magana amma yace


"I'm sorry it's still hurting zan karasa miki wani time din"


Kaina na gyada muka cigaba da tafiya cikin wani yanayi me zafi, atmosphere was tensed shi yana tunanin Izzatunshi yayinda nake tunain me ya faru suka rabu da izzatu?

Cikin nutsuwa na maida hankalina wajen presenting spinal bifida, condition ne dayake affecting yara, mukan kirashi "congenital defect" tun lokacin yaro yana ciki spine dinsa "laka" bata rufu ba, hakan is a very rare cases da yafi affecting whites amma anan dinma ana samu. Cause dinshi dai takamaimai baa sani ba sede hankali yafi karkata a rashin sinadarin folic acid a jikin uwa lokacinda tana dauke da ciki.+

Ina kamallawa hannun daya fara clapping na MD ne, se kuma sauran suka dauka aka cigaba. Nayi murmushi ina jin dadi sannan na fara amsa questions da kuma consultants da suke kara min wasu points din. Se wajen tara kowa ya nufi office dinshi ready to start the work of the day. Dakina na koma dan na canja kaya saboda ba wears din aiki bane a jikina, seda Na kammalla shirina tsaf na nemo powder cikin wani kit na shafa, na murza kohl nasa lip balm sannan na kalli kaina, nayi tsaf dani se wani murmushi da yake kwance kan fuskata da yaki ya bar kanta, ni kaina na manta lokacin da na fito cikin nutsuwa ta haka, wanka dai bana fasa shi amma fuskata kullum maiko take tun Dr fadima na mita hakan har ta tattara ta kyaleni.

Kulle dakin nayi na nufi lounge dan nasan house officers din da zamui rounds dasu suna can kamar yadda na umarcesu su jirani. Ina shiga dukkansu suka mike tareda gaisheni. Da murmushi nace

"Are we ready?"

Dukkansu suka amsa sannan muka fito, tamkar wata sabuwar halitta haka nake jin kaina yadda nake jin jikina light like a feather, se nake jin sassanyar iskar dake kadawa tamkar zata daga ni sama. Ina jinsu suna kuskus din abinda ya sani nake wannan farin cikin hakan abinda wasu dagacikinsu basu taba katarin gani ba.

Ina stepping kafata cikin labor ward naji ana fadin

"Kira Dr Shahada matar nan so take tayi parking!"

Ni kaina gaba na seda ya fadi, is it a welcome? Na tambaya kaina kafin na cire stethoscope din dake wuyana na mikawa Dr Ruwaida nayi ciki da sauri suka biyo bayana, tana ganina Sister Naima ta saki ajiyar zuciya, gloves na dauka na zura a hannuna sannan na karaso gurin ina fadin

"Sister me ya faru?"

Tana ta kokarin securing second line tace min

"PPH 2• home delivery. Sunce tayi bleeding sosae on their way coming, jikinta ya nuna though on arrival babu active bleeding sede she's paper white kuma mata kadai suka zo babu maza"

Kaina na gyada ina kallon ta nace

"Shock zata shiga anytime from now, NASG fa?"

Tace

"Ana hadowa"

Muna tsaye muna jira sega kakarta ce ko babarta no can tell, irin fulanin kauyen nan ne, tana tsayawa tareda kama hannun matar tana mata fullanci nace mata

"Baba har yanzun mazan babu wanda yazo"

Kai ta girgiza tace
"Basu zo ba malama"

Na danyi tsaki nace

"Mijinta baisan kun taho bane ko ko?"

Dariyar yake matar tayi wanda kana kallo is painful tace

"Rayuwa ce kawai"

Ban kara cewa komai ba tunda Na fahimci abinda take nufi. Baa fi minti biyu ba se gashi an kawo NASG muka shimfuda akan wani vacant bed sannan aka ciccibo ta muka daura ta, tana ta shure shure a haka muka fara kokarin daura mata amma wannan tsohuwar taxo ta rike hannuna tace
"'Yata ki kyaleta da wannan abin kawai bana so"

Kallonta nayi nace
"Baba wannan shi ne taimakon da zamuyu mata kafin mu samu jini"

Matar nan fir taki, muna haka Metron ta shigo nayi mata bayani tace

"Kun manta ethics dinku, patient's right, idan kuma kuna gama sawa ta rasu fa, zata iya cewa abin ya kasheta allow her"

Se lokacin na tuna hakan, aikuwa muka kyalleta se mukai waya lab a ara mana jini amma kafin a kawo jinin matar ta rasu, it was touching dan babar tace dalilin da yasa mijin yaki zuwa yace jininta wahala yake kuma shi baisan inda zai samu ba. Mazan kauye kenan basu masan meye amfanin aure ba balle su san darajar auren ko dalilin da yasa ake yinshi.
Gaba daya ranar sukuku nayi ta babu wani walwala a tare dani, bawai ban taba ganin mutuwa ba, no amma akwai mutuwar da will stick in your mind forever. Office na wuce dan lokacin da zanyi assignment dina yayi dake ina course na IMCI (Integrated Management of Childhood Illnesses). Glasses dina na saka na bude system dita na fara shigarwa. Wani soft knock naji a jikin kofar hakan yasa na dago tare da kallon kofar, se na tuna cewar ai nayi locking kofar. Dan tsaki na saki tareda mikewa na nufi kofar, ina budewa nayi kyakyawan gani. Yeah kyakyawan gani mana tunda kuwan naga sanyin idaniya ta, naga abinda yasa na saki murmushi a take a gurin.

Tsayawa nayi ina maida masa martanin murmushin da yake min. Seda yace min

"Rowar office din kike min? Kin tsaya a kofa as if I'm not welcome"

Dariya nayi kadan tareda matsawa se ya dage kafadarshi yace

"I was passing by nace bari naga yadda kike"

Cikin jin dadi nace

"Thank you"

Kanshi ya girgiza ni kuma na koma ciki bayan naga tafiyarshi. Tunda na zauna na kasa tabuka komai ina tunanin labarin da Doctor ya bani dazun, I'm so curious nasan me ya faru da Izzy, aure tayi ko kuma hanata auren shi akai. Tunani kalakala babu wanda bai zo min ba har tunani nayi kodai Raudha yar shi ce kuma ita ce fruit of love dinsu. Gaba daya na rasa tunanin me zanyi kuma dan kuwa wannan puzzle ne dana kasa solving.

🎶Can't you see? He's my everything, I'll wait on him all the days of my life! Can't you hear? This sweet song he gave? Like cool rain drops falling on a sunny day🎵

+
Kwanaki a hankali suke shudewa suna wucewa ba tareda saka ran zasu kara dawowa ba, sun tafi tafiya ta har abada. Rayuwar gaba daya is too short wasu abubuwan suna faruwa Amma kwatkwata bamu fahimta, we're so much engrossed da son kyalekyalen duniya not knowing rayuwar gaba daya ta kusan karewa.

A kalla tafiya tsakanina da Dr Abbas tayi nisa mutane da yawa cikin asibiti sun fahimci meke tsakanin ni dashi. We barely hold giggling and grinning idan muka hadu. Akwai wani lokacin banma san me ya faru ba, kawai an kirani naje OT akan wani aiki da zamuyi. Tun daga kofar OT nasan yana ciki saboda bambamin fadan da yake tayi babu kakkautawa, muryar shi was at it's highest pitch haka. Tamkar kada na shiga dan ni ban taba ganin fadan shi ba hakan yasa naji gaba daya I'm weak. Na juya zan fita kenan naji muryar Dr Lamin yace

"Asmau!"

Juyawa nayi fuskata looking dull na karkaro murmushi nace

"Abban Afeeyya, ina kwana?"

"Lafiya lau"

Ya bani amsa sannan yace

"Dan Allah shiga ciki, a patient died on couch, may be idan ya ganki fadan zai ragu"

Baki na bude da niyyar protesting se ya riga ni da fadin

"Just save them please"

Ba yadda na iya haka na shiga ciki, suna tsatsaye a clean area, dukkansu idonsu ya raina fata shi kuma se kumfar baki yake. Banyiwa kowa magana ba kawai na nufi cikin lounge din bayan na tabbatar mun hada ido dashi, kamar minti biyu naji muryarshi yana fadin

"All of you should get out of my sight"

Ajiyar zauciya na sauke, bayan wasu mintina na fito shi dinma baya nan se chief anesthetist na samu yana ta dariya na zauna kujerar dake facing tashi nace

"Me ya faru?"

Dariya ya kara yi yace

"Kin ceci mutane fa, shigowa office nayi na kiraki nasan ke kadai zai gani wannan temper ta sauka"

Kaina Na girgiza dan shikam ya rigada ya san meye tsakanin mu, gashi MD is making it obvious to everyone cewar nidin ni ce farin cikin shi da nutsuwar shi. Mikewa nayi nace

"Ba haka bane, kawai na shigo daidai lokacin da zai gama fadan ne. I guess it's a coincidence"

Wani kallo yayi min yace

"No, ni ba haka na gani ba, kina shigowa duk wannan fadan dake idanunshi sukai melting especially kin shigo baki kula shi ba."

Dan dariya nayi kadan nace

"Oga baka da dama"

Yace

"Of course, Inata adduar idan mijinki yazo Allah ya baki miji na gari wanda zaki zama sanyin idaniyar shi. Kinsan there's a great wisdom akan hakuri amma mutane kalilan ke fahimta, kede a rayuwarki kinci ribar hakuri. Ya fada min har manya sunyi magana ko?"

Se lokacin na tuna MD ya taba fada min Chief abokin shi ne, like ko sunyi school daya ne i don't remember gaskiya. A idona Chief yanada matsayi saboda duk lokacin da zanzo OT bai bari na fita bai nuna min cewar aure lokaci bane, no way sede idan aiki yayi mana yawa. Godiya nayi mishi nace
"Gobe munada Dialysis so wannan surgery bazaiyi taking place ba se jibi"

Kanshi ya gyada tareda min fatan alkhairi na fita, tamkar jirana yake ina fita yana kirana, seda nayi murmushi sannan na kara wayar a kunnena ina fadin
STORY CONTINUES BELOW
"Allah ya huci zuciyarka"

Dariya yayi kadan yace

"Me yasa kika shigo lokacin, baki bari nayi knocking senses into their head ba."

Nima dariyar nayi nace

"Saboda bana son naji wani abu ya taba maka muryarka, that's why"

"Can i see you? Ko kina aiki ne?"

Kaina Na girgiza tamkar yana gaba na nace
"Zanzo inshaaa Allah"

Daga haka mukai sallama na nufi can a hanya naga anata nuna ni inajin ana cewa ita ce budurwar MD, murmushi kawai nayi na wuce zuwa office dinshi, shi kadai na samu yana zaune akan kujerarshi, idanunshi cikin farin medical glasses wanda ya fito da tsayin hancinshi, dukkan hankali shi  yana kan system dan sallamata kawai ya amsa amma bai dago ba balle ya kalleni, zama nayi na maida hankalina kan plasma dake aiki, MBC 2 ce takeyi ana wani program na The Doctor, zamana na gyara dan bana bari ya wuceni ko online ne se na kalla. Ranar akan hyperlipidemia akeyi so yadda na bada attention dina sosae bansan har ya kammalla aikin ba seji nayi dif an kashe socket din, dagowa nayi na ganshi tsaye yana kallona, mikewa nayi nace

"Shi ne ka kashe?"

Kujerar dake facing dina ya zauna yace

"I can't help naga dukkan hanklainki ya tattara acan kinga dole na kashe."

Bakina na tabe irin nayi fushi dinnan se ya gyara zaman shi tareda daidaita fuskarshi shi wadda ta tabbatar min serious magana zamuyi, na zauna tareda bashi dukkan hankalina. Yace

"Asmau kinsan me yake kara miki daraja a gurina?"

Kaina na langwabar ina kallonshi with so much love in my eyes Na girgiza kai, murmushi me kyau yayimin yace

"Kinada hakuri, ni banida hakura most especially if it's for me to wait. Kin bani lokaci da yawa kin daga min kafa dukda kullum ina gani kina son na karasa maganar Izzy a idanunki amma kinki tambaya"

Na kagu naji amma bana son takura mishi, bance komai ba ya cigaba da fadin

"Seda aka daura aure, ban taba ganin ranar da nayi farin ciki irin wannan ranar ba, nayi murna kamar zan tashi sama saboda I've got what i waited for all my life. Kinsan me...."

Ina kallnshi Na girgiza kai yace cikin rauni

"...Kafin na baro inda aka daura aure zuwa family house dinmu aka kiramu Izzy ta rasu..."

Mikewa nayi hannuna akan kirjina idanuna a warwaje nace

"Innalillahi wa inna ilahil rajiun,! Sorry please, I'm so sorry ya Allah!"

Murmushi yayi amma i can clearly see the pain he's hiding, yace

"Wannan shi ne mummunan labarin da ya taba riskata a cikin rayuwata, i felt it dan a take akai asibiti dani, soyayya ta kayar dani na rasa inda kaina yake, meke damuna ? Me ke min ciwo? Me nake bukata. Asmau nasha wahala kafin nayi fighting zuciyata na kara tashi. Nayi kukan rashin izzatu haka tamkar ta tafi da zuciyata se hoto ta bari. Na zama mafadaci very hostile gaba daya na canja, naki nayi aure, soyayyar na tattara na watsar da ita gaba daya. Hajiya kullum nasihar ta nayi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa amna na kasa fahimta gani nake babu mace kamar izzatu kuma ban samu ba tunda na sawa raina hakan. A hankali aka fara hada ni da yaran abokan alhaji ko na hajiya amma ko kallo basu isheni ba se suka kyaleni, a cewar su dan kaina zan sakko and here I'm about to go crazy akanki."

Dan dariya nayi tareda zama nayi masa gaisuwa da jaje amma nasan he's just faking the smiles, hakan yasa nace

"Haka rayuwar yake it's so unfortunate. Allah ya jikanta"

Murmushi yayi yace

"Amin. So ina jinki fada min taki side of story din naji. Your love"

Kaina Na girgiza komai yana dawo min ina picturing dinsa cikin kwakwalwata sede babu wani labari me dadi ciki amma haka nan zan fada masa especially akan yaya Suleiman.

"Taka soyayyar is more enticing than tawa, babu wani jin dadi dana samu se heartbreaks dana samu..."

A hankali daki daki na bashi labarin yaya mukhtar down to yaya Suleiman, sede bansan meye dalilin wani rauni da yazo min ba lokacin da nake fada masa ni nayi hooking Suleiman da Nadia, kawai se naji kuka ya kwace min. Kaina na kifar ina kuka a hankali wanda baki daya ya rikita shi fadi yake

"I'm sorry, bansan haka kike ji ba , da ban tambaya ba"

Seda nasha kukana har fuskata ta canja launi sannan nace
"It pains yadda yayi wasa da tunani na Amma it's all in the past"

Hirar kuma duk se babu wani dadi hakan yasa yace naje na huta.

Kamar hadin baki weekend din da muka tafi dashi yana sauke ni, Yaya Suleiman na parking, hakan yasa na leka nace ya fito su gaisa dashi, seda ya harare ni kafin ya fito. Yaya Suleiman cikin sakin jiki da sakin fuska ya mika masa hannu shikam Oga ranshi a bace ya bashi suka gaisa ya koma mota Yaya Suleiman ya shiga ciki. Tsayawa nayi nace

"What was that face for? You barely smile"

Yana bude baki se cemin yayi

"I don't like him!"

Da sauri nace

"Why? Is not as if kasanshi ko kun taba haduwa"

Dariya ya danyi yace

"Saboda yasa min wannan idanun sunyi kuka kinga laifina? He played with your heart baby"

Rufe fuskata nayi ina murmushi wanda ke ratsa raina nace

"Se munyi waya!"

Shoulder dinshi yayi shrugging sannan yayimin sallama na wuce ciki ya tafi tamkar na bishi!
Washegari da daddare Abba ya kirani dakin Inna, ina kallo sakon ya sameni daga bakin Ikhramar Adda Meeyna da tazo mana hutu, mikewa nayi na dauki wani plain veil na dauka ash na yafa a kaina sannan na fita bayan nayi kashedi da babbar murya akan kada a taba min system din. Ina zuwa na same shi yana zaune kan carpet gefenshi Ummaah se Inna akan katifa da yaya halifa shima a zaune.+
A sanyaye Na zauna dan na san it must be something serious. Seda na kara gaishesu suka amsa inna ta nuna min gefenta na zauna sannan Abba ya fara da fadin

"Na taraku anan saboda ke Asmau, ina cikin matukar farin ciki da Allah ya bani iko na sauke nauyin da ke kaina. Last week da kikazo na tambayeki akan maganar Abbas kin amince kin yadda fully zaki aureshi, hakan yasa cikin satinan na zauna da magabatansa na kuma basu aurenki. Alhamdulillah! Kowacce 'yata haka na mata amd kema hakan na miki sede it's a condition on no account should you tell me kin fasa aurenshi sede idan babban abu ne wanda ni ne zanyi deciding hakan, there's no going back. Ina fata kinsan watanni uku kawai aka saka saboda haka sukai requesting. Allah ya tabbatar da alkhairi ya bada fahimtar juna"

Gaba daya nasan maganar nan kwwai daga bakinshi ne ban ji ba, inshaaa Allah kawai nace sanoda ji nayi tamkar an zuba min ruwan kankara yadda jikina yayi balain sanyi. Koda yaushe ina fatan ranar da zan budu idanu naga aurena amma yanzun se nake jin I'm loving the house more and more. Idanuna se suka cicciko da kwalla inna na tayimin dariyar wai da girmana meye na kuka? Tasan idan nayi auren mantawa da ita zanyi ai fadar haka se na bare baki na fara kukan da baya min wahala, Ummaah ce ta janyo ni jikinta tana rarrashina Abba yana cemin it's a normal pace for every lady, so su kyaleni nayi kukana.

Koda na koma daki gaba daya se na kalli wannan na kalla wancan, na shafa gadon na bude wardrobe na kalla dressing mirror dina filled with kayan shafe shafe a lokacin naji wani irin missing gudan nake. Wayata na dauka na fara dialing "Jewel" kamar yadda nayi saving mishi number nake kuma kiranshi dashi, saboda a ganina yafi karfin silver, darajar sa tafi ta gold haka ta diamond, he's a priceless gemstone. Yana dauka yace
"Cara mia!"

Haka yake kirana dashi, at first banma san menene sunan yake nufi ba se wata rana yake cemin it's means My beloved in russian language. Duk lokacin da ya fada se naji kamar kara min son shi ake.

"Jewel!"

Na fada muryata cikeda rauni,
"Yaya akai? Me ya faru? Muryarki says it all"

Kamar yana gabana na turo bakina, dole Abbas ya sami zuciyata saboda kallona idan yayi yasan idan akwai matsala haka idan muna waya kuma bazai taba kyaleni ba se ya tabbatar nayi dariya.
"Ni ban gaji da gida ba fa!"

Dan dariya yayi yace

"Ma'u love! So dama yaya halifa ya fadamin wai na shirya rocking baby, se yanzun Na fahimci  menene auren auta! Gidana ma ai is home menene abin damuwa"

Kamar yana gabana na fara bubbuga kafata a kasa kamar me kuka nace

"Kullum sede ba zan kalla Ummaah ba"

"Asmau ai yanzun ma ba kullum kike ganinta ba, ki dauka kamar zakije dutse ne"

Kawai se naji hawaye ya fara zuba min, inajin wani irin damuwa a raina. Nasha kuka dakinnan akan banyi aure ba amma see me crying saboda zan bar gidan. Da tsananin mamaki yace
"Cara mia are you crying? Menene abin kuka, is not like auren dole zaayi miki, i love you so much and you feel the same. Bawai kuma zakije detentions bane, kinsan duk lokacin da kike son ganin Ummaah I'll grant you that request. Cara mia dan Allah ki bar kukannan haka, kinsan yadda nake ji haba mana baby? Kiyi hakuri I'll be everything you need ok?"

STORY CONTINUES BELOW
"Mhm"

Na fada ina share hawayena dan murmushi yayi yace

"Smile kinji"

And i smiled like a baby daga haka hirar tamu ta cigaba kusan dukkanta akan yadda zamu kasance ne in 3 months dinnan. Daf da zamui sallama nace

"Jewel na manta ban fada maka zan tafi minna ba next week"

"Minna? Me zakiyi"

Gyara kwanciya ta nayi nace
"Ka manta can nayi secondary school dina, New horizon?"

"Yes?"

Ya fada wanting to hear the details"

"So zamuje old students reunion"

Shiru yayi kamar bai ji ba nima nayi shiru dan na tabbatar yaji abinda nace alamun anya zakije kuwa? Dan tsaki yayi yace

"Flight zaki bi, kin sani ko?"

Murmushi nayi nace

"Awnnnn I love you! Nayi booking ni da Nadia da Rayhana"

"Seems good, alright ban gaji da jin muryar ki ba, but kiyi bacci kinji"

Kaina na gyada nace
"Alright sleep well"

🎵Baby I'm yours I love you much!🎶

Bayan sati daya ranar Wednesday na fara off, tun monday bamu hadu dashi ba and it feels so bad haka nan, bana jin dadi. Gaba daya aiki ya rike shi bashida wani free time haka nima se dan interval da zai samu ya kirani to check on me. Tun dare na hada kayana so muna gama rounds na koma daki nayi wanka na canja kayana zuwa wata loose English gown me kyau color royal blue se touches Na turquoise blue a jiki so se nayi amfani da veil da wani flat clowse half cover me kyau. Fuskata like usual daga kwalli se balm se powder da na shafa. Wayata na ciro nayi dialing number Jewel dan nace masa zan tafi, yana picking yace na sameshi a OT yana can. Mota ta na dauka na tafi bayan nayi parking na shiga ciki inajin kamar na shiga da gudu na ganshi na fada masa how much i missed looking at that handsome face of his. Yana zaune a reception shida Chief gabansu da mug din coffee, bana don wannan coffee din tsakar ranar da yake sha, he's already addicted to it.
Seda na gaida Chief ya dan tsokane ni wai suna missing dina a OT dake na jima banyi surgery ba. Murmushi nayi shikuma yacemun

"Let's go"

Bayan shi na bi ya tsaya a inda mota ta take yace

"So se tafiya kenan?"

Kaina na gyada nace

"Yes zan tafi se next week inshaaa Allah"

Kanshi ya gyada yace

"Safe journey, Allah ya kiyaye se munyi waya"

"Amin" na amsa masa na shiga drivers seat tareda fastening belt dina sannan Na kalleshi nayi masa wink, kanshi ya zuro cikin motar yace

"Tsokana ko?"

Dariya nayi ya zuro envelope gefen seat dina yace
"Take care of yourself for me. I love you!"

Akwai lokuta da dama da repetition of abubuwa ko magana se ya saka ka gaji, kaji haushi amma banda wannan kalmar ta "I love you" kullum tamkar sabuwa haka take kullum jin ta nake kamar yau aka taba fada min, it's enticing....

Karfe uku jirginmu ya tashi zuwa niger state, tunda muka boarding flight din muke hira dasu gaba daya secondary school life muke tunawa munata hira so bamu ga lokaci ya ja ba. A school accommodation dinmu yake aikuwa acan muka sauka, muna zama na fara kokarin kiranshi se gashi ya kira, rayhana tace

"Tab Ma'u this your Doctor oooo"

Hararta nayi na dauki wayar muka fara hira akan tafiyar har suka gama wanka ban gama ba se da Nadia tace

"Doctor zatayi wanka"

Sannan muka rabu inata mita. Munsha hira kafin washegari akai grand reunion kusan dukkan yan class dinmu sunzo da yayansu baifi mu hudu ne bamuyi aure ba. Se naji dadi saboda bani daya bace kuma gwara ni ina aiki na kama kuma dahir amma ita daya daga cikinsu ma babu aikin babu mijin babu komai a haka take rayuwar. So ka dinga kallon rayuwar wasu nan zaka gane kana cikin niima sosae.

Taro ya tashi lafiya washegari muka dauka hanya zuwa airport anan naji message ya shigo min, duk tuannina ya tafi akan may be mtn ne seda na kira Jewel sannan naga wata bakuwar number ce, i didn't check on the message har seda naje gida nayi wanka na gama wayata sannan na tuna dashi. Wannan message din almost gave me a heart attack ban taba ganin dare me tsayi irin wannan daren ba.

I heard zaki aura Dr Kwaccido, do you ever taught of abinda ya hanashi aure. Bari na fada miki he's a WOMANIZER!

Gyara kwanciyata nayi tareda sake bude text message din ina karantawa a iya adadin da bazan iya tunawa ba. Lokaci daya naji wata zufa ta rufeni, makoshina ya bushe se gaba na da ya dinga faduwa kamar zai balla kirjina ya fito. Kallon wayar na karayi na kara nanata message din "A womanizer?" Na tambayi kaina for the nth of time. Kwalkwalwata taki aminta da abinda ta gani haka zuciyata fada min take is not possible, he can never ba amma sede na kasa gaskata su dukka saboda ina cikin wani irin rudani da ban taba shiga irinsa ba. Wayar na ajiye a gefe tareda runtse idanuna a raina ina ayyana me yasa haka ke faruwa dani? Me yasa rayuwa take min haka? Me yasa kaddarata take zuwa a haka? Seda na fara son shi, na gina dukkan mafarkaina tare dashi sannan wannan abin zai kunno kai? Se kawai naji kuka ya kwace min, i was helpless tsoro sosae ya kamani, tsoron kada na rasa shi saboda nasan zuciyata will be shattered jinina se ya kai koluluwan hawa. To amma ai anyi bincike, kuma na tabbatar Abba bazai overlooking wannan abin ba saboda yana son nayi aure, kaina Na girgiza. Ni da kaina na bincika iya yadda zan iya amma me yasa se daga baya naji wannan muguwar maganar, ina zan saka kaina. Haka nayi ta tunani har da wanda bashida amfani na rasa me zanyi a wannan daren ga bacci yace bai san zancen ba.+

Na jima ina kwance, numfashi ne kawai nake fitar dashi a dadin rai amma ko hannuna jinshi nake yayi min nauyin gaske, so a haka dai nake kwance hawaye ya wanke min fuskata. Da kyar na kara mika hannuna na janyo wayar na kara duba message din, se lokacin idanuna yakai kan number, it's a strange 9mobile number not in my contact, hannuna yana rawa nayi dialing number amma se a cemin my call has been forwarded, bansan iya lokacin da na dauka ina gwada saata ba amma wayar nan bata shiga ba. Jefar da wayar nayi ina nanata innalillahi wa Inna ilaihil rajiun! With the hope akan zuciyata zata rage zafin da tske min zanji afuwa a cikin raina.
Kafin gari ya waye idanuna sun tashi saboda rashin bacci da kuma kuka, jikina was very weak da na tada sallah ma nayi tunanin bazan iya ba amma haka na daure nayi sannnan Na kwanta akan carpet dun aikuwa bacci ya daukeni. Bacci marar dadi me cikeda mafarke mafarke duk akan maganar, wai na sameshi akan maganar yace min wai to se me? Da gaske ne haka dai abubuwa iri iri. Amma a haka nayi baccin ban masan ummaah ta shigo ba haka Asiya balle kiran Jewel da yayi tayi se karfe goma Asiya ta shigo ta tasheni da sauri na mike ina fadin

"Ya ilahi! Rana haka ta fito?"

Da sauri nayi bandaki nayi wanka ina fitowa na shirya cikin lace maroon da blue zani da peplum riga. Veil na yafa na dakko komai sannan na fito, jikina duk a mace komai inayu ne dan ya zama min dole nayi shi. A parlon Abba nayi breakfast pancake da tea shima kawai sha nake da korawa amma it was tasteless gaba daya message din ya tafi da dukkan kuzari na, dukkan farin ciki na and it's left and empty and emotional Asmau. Sallama nayi dasu na dauki hanya na tafi cikeda kewar su. I zeroed my mind yadda zan samu nayi concentrating akan tukin amma i hardly do that. Haka dai na samu na isa lafiya, tun a hanya ina kallon Jewel nata kirana amma na kasa dauka saboda ina jin kamar a muryata zai fahimci halin da nake ciki, it breaks my heart to see yana kira ban dauka ba.

A office na aje kayana, na bude wani shelf na dauka abubuwan amfani sannan na zura lab coat dita na fito, ina fitowa naga Messenger MD yazo akan nazo yana kirana, wannan nasan bazan iya tsallakewa ba, haka na bishi inajin gabana yana wani irin faduwa inajin tsoron haduwa dashi nake all in all. A hankali na tura kofar bakina dauke da sallama na shiga ciki, yana jin muryata ya mike daga kan kujerarshi fuskarshi cike da damuwa yace

"Asmau are you ok? Ina wayrki?"

Saukar da idanuna nayi cikeda rashin jin dadi, he looks disturbed he was looking at me with so much tension a idanunshi. Kallona yayi yace

"Zauna Asmau"

Zama nayi babu wani kuzari a jikina sede kallonshi nake ina hasaso how possible will it be for this soul to be a womanizer, Aniya! Na fada cikin raina I doubt so much hakan bamai yiwuwa bane ba.
Gefena ya zauna yace

"Ina jinki me ya faru?"

Nafi mintina biyar ina hesitating na nuna masa ko kada nayi amma zuciyata ta nuna min gwara na fada amsa ayi shi lokaci daya once for all komai ta fanjama fanjamjam! Wayata na ciro daga lab coat pocket dina na bude message din na bashi, tunda ya karba na tsira mishi idona inga wanne yanayi fuskarshi zata yi, babu wani guilt se tashin hankali da mamaki, ban taba ganin yana stammering ba se a lokacin yace

"As....Ma'u....fr....om where?....ina kika samu wannan waye ya turo miki?"

Kuka na fara me daci saboda i can see his innocence a idanunshi, shiru yayi har seda na daina kukan yace
"Is ok, tell me"

Cikin sanyin jiki na bude baki na fara masa bayani tareda nuna masa yadda nayi ta kiran number ban samu ba. Ranshi yayi masifar baci yace

"Cara mia, idan ina neman mata ke zaki fara fahimta da tuni in any way possible na nuna miki, I've never done such wallahil azim, believe me"

Hawayena na share nace
"Ayya na sani Jewel i trust you"

Mun jima yana nuna min bashi bane and se naji hankalina ya kwanta naji nutsuwa tazo min, a haka ya kira wani friend dinsa akan a tracking number. Na fahimci no way ka nemi aure ba tareda yan bakin ciki sun shiga dansu watsa abin Amma Allah yafi su.

Ranar banyu aiki ba daga office dinshi kawai fivewa nayi na tafi gidan kyaftun se dare muka rabu. A kwana a tashi babu wuya wajen ubangiji kafin wani lokaci biki ya gaba to sosae banda shiri babu abinda nake.
Ina zaune a tsakar dakina a dutse mun gama waya dashi ranar ya tafi kwalam gaisuwar surikai, flour na debo cikin wata bowl na kwaba da ruwa yayi kamar batter sannan na cire kayana se wani short da half vest dana bari, dining mat na baza a kai na zauna sannan na fara shafawa ina murzar jikina, seda na gama na fitar da ita tas sannan dakko manja na mulke jikina tas na barshi dan jikina yayi absorbing da kyau shima na murje daga baya, na maida lallae wanda na kwaba da madarar turare me kamshi, seda ya bushe na murje sannan na daura kwababbiyar madara and i did same kafin na tafi bayi nayi wanka babu soso da warm water wanda aka zuba tarare a ciki. Gaba daya na kaure da kamshi me sanyu dama kwanakinnann tunda na fara wannan skin therapy din na kara haske jikina yayi laushi haka Adda tace nayi kafin a kaini gun asalin skin pamper din. Da wannan ruwan na wanka na shafe jikina da humra sannan na tsugunna a garwashi tareda lullube jikina da quilt.

Tafiya ta tafi kamar cikin mafarki ranar da aka saka biki ta karato, shirye shirye ko ina yinshi ake dukda dai na rigada nayi making clear to everyone akan I'm not for a grand wedding, babu abinda nake bukata banda kowa ya tayani addua, wani mugun kallo Adda Sa'ada tayimin itada Anty Bintu ranar munje yiwa Anty Bintu yini.+

"Lallai ai se munyi bikin da a fadin nigeria se yayi wata guda yana ringing kunnen jamaa, a YouTube kam shi ne a saman search engine."

Dariya nayi nace
"Kai haba Adda, we just need a bless full marriage ba wani abu ba"

Anty Bintu tace

"Aa fara kinsan dole zaayi kamu dolen dole ne, kuma Anty (Ummaah) zatayi yini. Me kike daukar kanki bazawara ko me?"

Dariya nayi jin abinda tace, Adda Sa'ada tayi caraf tace

"Dallah can, zawarawan yanzun kina kallon yadda suke grand wedding sannan ke kice ba haka ba, baki isa ba kinga I'll talk to him myself"

Nidai dariya kawai nayi ina ganin kamar a mafarki abubuwan ke faruwa wai da gaske ni Asmau ni ce zanyi aure bayan shudewar shekarunnan. Bayan na rigada na cire tsamannin zuwan wannan ranar amma gashi dake Allah shi ne Allah I'll be hitched soon. Dukkan shirye shiryen da suke ina jinsu nidai nawa dariya ne kawai nawa dan dama ba wani sani suke a ciki ba. Se yamma lis muka mawa Anty sallama, wasu kulle kullen cikin leather wasu rubber ko wanne da directives kan yadda zanyi amfani dashi ni dai har na kosa ma wallahi, dan na gaji da shaye shayen nan kamar wata 'yar ganye. Seda na kai Adda gida kafin na wuce namu so lokacin da na isa already an idar da sallar maghrib ana kokarin yin isha, i was on my period so babu wata damuwa kawai shigewa ciki nayi na sheka wanka na fito parlor inda Ummaah ke zaune Abba yaje Kwalam shi da Inna Ade.

"Asmau akwai event din da kike son kiyi ne?"

Ta tambayeni idanunta a kaina, girgiza kai na nayi nace

"Ummaah kawai dai zaayi normal traditional kamu, sede idan ke zakiyi wani abin?"

Itama kai ta girgiza tace

"Shi dinma is ok, Abbanku yace da kanshi zai kaiki kinga babu wani taro kenan"

Kaina na gyada ban kara cewa komai ba, se lumshe ido da nayi inajin irin wasu bakin yanayi suna dabaibaye ni. Gyaran murya Ummaah tayi hakan yasa na bude idona ina kallonta, itama dukkan hankalinta a kaina yake tace

"Gajen hakuri bashi da amfani, a cikin rayuwarki I've learnt a great lesson. Duk yadda ka kai ga son abu ya kasance indai Allah bai yadda ba hakan bazai faru ba. Na sani na cutar dake Asmau, i wasn't a good mother actually ban kyauta ba, idanuna sun rufe na kasa lallashinki lokacin da kika fi bukatar hakan se kara miki matsaloli da nayi tayi. Ki yafe min dan akwai hisabi tsakanin da da uwarshi tunda kuwa mu din kamar care takers dinku ne da Allah ya bamu. I'm sorry fara"

Kaina na girgiza mata inajin raunin dake saukar min cikin zuciyata, rungumeta nayi nace
"Ummaah, maganar ta wuce ko a lahira bazaa tada ita ba, ke Ummaah tace fa wannan shi ne kulawar ki, baki zlince ne ba you just wanted me to do it. Ummaah Allah ya kara lafiya"

Hawaye a hankali ya dinga bin kuncina, sosae nayi kuka lokacin saboda nasan na kusa barin gidan na kusa tafiya na bar Ummaah, a lokacin ji nake kamar zanyi hauka, I don't want to leave!

Na koma Dutse dan se na kara sati biyu kafin na dawo gaba daya, da kaina naje danshi baya gari yaje wani Workshop a ikeja. Kwana na biyu da dawowa ya dawo ina tsakiyar aiki a SCBU an kawo wani neonate me neonatal tetanus muna attending dinsa, wayata ta fara ringing, ko ban ciro ba nasan Jewel ne he got a unique ringing tone a wayata. Murmushin da nayi yasa Dr halima karbar folder daga hannuna tace

STORY CONTINUES BELOW
"Jeki you are excused"

Kaina na girgiza da sauri ina fadin

"Aa ma'am, fada zaiyi ai na bar aiki. I'll tell him aiki nake"

Kanta Ta gyada tareda mika min folder na cigaba sede fiye da rabin hankalina baya jikina, kina kallona zaki san I'm super excited abin mamaki Allah Allah nake na gama na tafi. Crap muna gamawa kuma se ga wani admission din shikam sepsis ne babu yadda zanyi haka na gama dashi na jira suka kawo drugs dinsu nayi setting line kafin na koma gurin Metron naji ko akwai wani abu tace babu, sallama na mata bayan nace mata duk abinda ya tashi a kirani, tana dariya tace

"Jeki kede nasan wannan murmushi da ake na ganin oga ne"

Fuskata na rufe ina dariya a hankali cikeda kunya sannan na fita tareda ciro wayata na fara kiranshi
"Cara mia! Na dawo"

Har cikin raina sunan nan yake shigar min, inajin farin ciki whenever he calls me Cara mia, yana nuna min da gaske I'm his beloved.
"Jewel sannu da zuwa, ya hanya?"

"Ina OT ina jiranki"

Kaina na gyada kamar wata wawiya haka na tafi inata suppressing ihun da nake son nayi, kamar nayi flying naje na sameshi amma babu dama, kamar mutane sunsan me nake yiwa akai ta tsayar da ni ana min Allah ya sanya alkhairi wai dama sunata zargin hakan se gashi ya tabbata. Nidai nawa smiles ne kawai nawa dan bansan me zance ba.
Yana zaune bansan abinda yake yi a OT ba a wannan time din, most times idan zamu hadu zai ce min na sameshi a OT bansan wanne bond ke tsakanin su ba. Ina shiga OT was calm so straight inda nasan zan sameshi na wuce bayan na gama gaisawa da nurses din gurin sunata tsokanata da amarya nidai sede nayi murmushi inajin kunya tana kama ni. Seda nayi knocking softly kafin naji manly muryar shi yace

"Come In please"

Da murmushi na shiga yana zaune shi da Chief na zauna ina gaishesu, Chief yace min

"Ya gajiya? Jiya nan was hectic"

Kaina na gyada nace

"Gaskiya kam, it was Amma Alhamdulillah gajiya ta tafi"

Murmushi yayi yace
"Hakane"

Se ya mike ya mana sallama, zama ya gyara yace

"Cara murnar nan taki boyuwa fa, anya kuwa zaa dinga bari na ina zuwa assignment kuwa"

Dariya nayi nace

"I was just happy ka dawo lafiya"

Cikeda jin dadi yace

"Yeah i see, I'm so happy seeing you, babu ruwanki your face is glowing ki kalla duk na kode"

Dariya nayi nace
Babu wani fa

"Sadiq yace wai zai hada mana walima or not really walima something like luncheon, gashi kince ke baki san taro sosae I don't want to disturb you"

Kaina na rausaayr gefe nace

"It's ok, ai babu dadi nayi turning gayyata. Mun gode mishi"

Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace

"That simplicity of you makes me fall for you often."

Fuskata na rufe inajin kamar I'm immersed in a cool water.
"Yace wai soyayyar tamu a nan OT ta fara so dole ya zama yayi mana something memorable"

Kallonshi nayi nace

STORY CONTINUES BELOW
"Da gaske anan ta fara"

Slamming system din dake gabanahi yayi tareda tsira min idonshi wanda yasa nayi saurin kawar da nawa gefe yace

"Of course my lady, a OT komai ya fara. I started liking your skills ranar da muka fara aiki dake, i dunno nayi ta cewa Dr halima ta kara mana booking aiki tare, i just feel safe working with you and bansan yadda akai your love unfreeze that froze heart of mine, yayi penetrating hakan. Baby I love you"

Da kyar na samu banyi shouting I love you too ba, saboda yadda naji ni on top of the cloud, wani sanyi na ratsa ni. Mun kusan hour muna hira sannan muka fito shi ya fita zuwa office dinshi ni kuma naje nayiwa Chief godiyar luncheon sannan na tafi.

Biki saura sati daya aka kawo lefe, imagine lefe na. Kuyi tunanin all those super dutch, super ABC, exclusives, laces, voiles, materials, shaddas,Abayas. Da na zauna gani kasa irgawa nayi saboda yawa tsada da kyau. Nayi godiya har seda yayi fushi. Bayan an nitsa se shirye shirye suka kara kankama kamar me na gaji likis. Ana saura kwana biyu a fara biki yazo gida akan zamuje zaayi visa ta tafiya honeymoon. Bakina kamar ya yage dan I remembered kamar wasa ya taba tambayata a duniya akwai famous gurin da nake son suwa? Bazaa rasa ba i had them da yawa. Ban kawo komai ba na zauna nace
"Ina son naje naga leaning tower of Pisa, italy. Colosseum of Rome, Italy. Twin towers of malaysia, the sphinx of egypt se the golden gate of San Francisco of USA"

Seda ya gama jina yace

"Duk ina kika sansu haka"

Nayi dariya nace

"I checked on wani littafi tun ina secondary school shi ne naji tun lokacin ina son naje"

Daga nan bamu kara maganar ba koda mukaje yin visas din karshe har Abuja mukaje na samu rakiyar Ikhrama, Baby da Raudha dinshi. Abin manya babu jimawa aka ciku ciku sede ta egypt ce bamu samu ba yace kilan ma zamuyi trans in indai hours din zai isa babu matsala.
Muna dawowa me kunshi na jirana akayi aka gama me gyaran jki tayi nata na karshe ta wuce, da daddare Adda Habiba mukaje salon da ita aka gama komai na dawo a matukar gajiye. Aure yakin mata i said. Da asuba bayan an idar da sallah ina zaune ko tashi akan sallayar banyi ba inata karatun qurani, zuciyata tayimin nauyi inajin wani irin yanayi wanda ni kadai da victims dinne zasuyi bayani amma banda su Shatutu. Na jima ina karatun naji wayata tayi ringing. Seda nakai aya kafin na katse na dauka jikina a sanyaye ganin Abba ne. Ina dauka yace na sameshi a dakinshi. Mikewa nayi bayan na damkawa Kyaftun wayar wadda tun jiya taxo itada Afeeyya se wani cikin dake jikinta, dake mutane sun fara zuwa sannan na fita, tunda na sameshi shi daya nasan abinda nake ta gudu shi ne zai faru wato nasihan auren nan da bana so, tunda Ummaah ta mini last week nafi awa uku ina kuka. Aikam nasha nasiha shiaysa a rayuwata ban taba mantawa da nasihar Abba Ummaah, metron dinsu kyaftun ba. Matar nan ta zaunar dani kafin na tafi ta nuna min yadda zan tafiyar da aure socially, financially, physically, psychologically, sexually and stuffs.
Inata kuka na fito daga dakin nashi saboda maganganun daya fada min tabbas na fahimci aure is not all what it seems to be, hakurinnan da saa ta cewa kayi ba a banza ba, ya nuna min wannan zaman is a boring zama wanda babu wata soyayya da zata kaika, the only thing shi ne mutuncin junanmu da wannan affection din, understanding junanmu da approach na zamantakewa shi ne komai. Same abinda ta cemin aure ba hakuri yake bukata ba juriya, uzuri, kawar da kai, tattali da daraja juna shi ne komai. Metron ta cemin aure shi ne gaskiya da gaskiya duk abinda kake boyewa se an ganshi, idan hali ne lokaci zaiyi da se halin ya fito kowa ya fahimta kuma hakane se bayan da naje na fahimci hakan.

Adda Maryam ta kalleni tace

"To ke kuma kukan me kike kamar zaa miki auren dole? Allah ya kyauta"

STORY CONTINUES BELOW
Ko kulata banyi ba na cigaba da kukana, ita rana irin haka ihu haka ta dinga yi har seda tasa nayi kuka amma see her saying this nonsense.
Tun twelve na tafi kwaliyya saboda karfe biyu ne luncheon din, nasan babu wani babban mutum da zai zo kuma ya jiramu shima seda ya nanatawa Adda Sa'ada da kyaftun akan hakan, muna zuwa aka kaini bridal room, ceo din da kanta ta yimin kwalliyar, lace dina na ranar was Milk with coffee touches so komai da nasa was coffee nayi kyau ni kaina na sani ban taba make up ko bikin kyaftun banyi ba, yanzun ma seea tayi counselling dina sosae kafin na samu kwarin gwiwa and naji dadin ganin kudin daya biya bai tafi a iska ba. Aka kakkashe ni da flashes after much canja style, unlooking styles and stuffs haka nan dai na jure aka gama.

Da kanshi yazo daukata shikadai cikin motar da sanyi da kamshi kawai ke tashi a ciki, yana cikin wani lafiyayyen yadi, milk aikinshi coffee same as mine, nice fara shi baki ne so milk din yayi aiki a fatarshi sosae, yayi kyau babu karya, i was mesmerized by the lovely look in his eyes, yana kallona kamar bai taba ganina ba seda Adda tace

"Ina nan fa"

Dariya yayi yace

"Ke 'yar sa ido ce fa"

Bata rai tayi dama sun saba fadansu shi da ita kamar ba surukai ba. Seda na shiga aka kakkashe mana flashes kafin yaja suma suka shiga motarsu suka bi bayanmu. A cool music was playing
It's the way she fill my senses,
Its perfume thet she wears
I feel I'm loosing my defenses,
To the color of her hair
And every little of her is right,
Just thinking about her takes me through the night.

Every time we meet the picture is complete ,
Every time we touch the feeling is too much,
She's all i need to fall in love with again,
I knew it from the very start ,
She's the puzzle of my heart!
It was cool, one thing da muke dashi in common shi ne son wakokin west life. Har mukaje gurin sannan yayi waya akan mun iso, kallona yayi na lumshe ido se kawai ya fara min hotuna yace

"Cara mia!"

Dagowa nayi na kalleshi kamar me tsoron kallon nashi se kuma na kara maida idanuna kasa, kafin ya kara magana akai knocking hakan yasa yayi wining glass din kasa se lokacin naga motoci da yawa kusan talatin sunyi parking, Adda Sa'ada ce da Uncle Mamman mijinta, suka gaisa dan ina tunanin first time da suka hadu kenan, se Maman Raudha da mijinta shima. tare muka fito ina jin wani irin bakon yanayi, yana mamaye jikina, Adda Sa'ada da uncle mamman a gaba se Maman Raudha Anty Zainab da mijinta Uncle Labaran a bayan mu. Na tuna lokacinda na tambaya kyaftun yadda ango da amarya ke tafiyarsu tayu dariya tace idan time yayi babu me koya min, I'll do it unconsciously and here I'm doing it.

Wani soft music ke tashi cikin gurin, decoration din yayi kyau kana kallo kasan medics zasui aure dan harda stethoscope da syringes a decoration din. Anyi hoto kafin muka shiga. A table of four kowanne couples ne, se namu acan sama yayi kyau kamar ba gobe. Kowa ya mike mutanen duka basu fi sixty ba, tare muka zauna babu wanda yazo yimin hoto saboda anyi hiring photographer dan haka mc direct ya fara aikinshi.  Dr. Hannafi shi yayi opening prayers, kyaftun da tazo da Lamin ta bada tarihi na, wani friend dinsa Dr Imran ya bada nashi. Halfway mukaje muka gaggaisa da mutane akai mana hoto har na gaji, kawayena sunmin kara, su Amina Aminu, rayhana, Nadia, Dr fadima, da wasu kukma and abin dadin kowacce da mijinta. Harda friends dina nurses na shekoni dana potuskum inda nayi service se sisters dina, a nashi bangaren manyan medical doctors abokanshi wajen goma kowanne da matarshi suka zo, se cousins dinsa.

Chief shi ya bada tarihin soyayyar mu, wai shi ya hada daga mika scarpel next shi ne, Dr Shahada I'm waiting for you in the OT, mukai ta dariya sannan muna dan hira dukda nawa gyada kai ne but trust me, photographer  baiyi missing capturing moments din da mukai dariya ba ko kallon juna haka. Daga karshe akai closing da addua bayan Adda Sa'ada ta bamu marital advices ita kuma Maman Raudha addua tayi. Muka mike dan sallama da guest dinmu anan wani soft music
Just a smile and d rain is gone
Can hardly believe it , yeah
There's an angel standing next to me reaching for my hand
Just a smile and theres no going back
But there's an angel calling me reaching for my hand
Yes, I'll be ok because this time is real!

I lay my love on you, it's all i wanna do
Every time I breathe I feel brand new
You open up my heart, show me how you love and walk right through.
I believe it's ok, cuz this time it's real!
I lay may love on you , is only i wanna do
Every time I breathe I feel brand new.

Har gida ya maida ni lokacin ana laasar ina shiga aka rikeni mukai pictures sannan na tafi nayi sallah. Ranar gaba daya bamuyi waya sosae ba kowa yana ta bakinsa. Washegari kamu ne, lace dina yellow ne not wannan lousy yellow. Yolk yellow gaba daya zaren da akai designs a jiki black ne me kyau. Munje kwaliyya da nasa aka min ado da accessories bakake se naga i was breathtaking nafi jiya kyau. Maman Raudha ta dinga daukata tana turawa doctor shi kuma yana exclaiming.

A compound din gida akai niyyar yin kamun amma ina bazai yiwu ba saboda baki dole se hall aka kama muka tafi. Anmin kara daga friends din Ummaah, nawa yan kwalam, yan uwan Ummaah, friends dina, yan potuskum, ya shekoni musamman my hearty nurses, yan shatuuu kingdom, Maman Mamaa da zeenert group da group din da shatuuu bata ciki amma labarina ya isa garesu sunyi kokari sosae. Naji dadi haka wata yayar babanshi ta kama ni aka min naira spray sannan se picture session aka tashi lafiya.

I was super tired kamar zan fadi haka naji da muka dawo so ranar da wurwuri nayi bacci shima seda na masa text dan kada ya kira. Friday ce washegari ranar da bazamu taba mantawa da ita ba cikin rayuwar mu daga ni har shi, ranar da Allah ya cika mana burin mu  muka zama officially mata da miji, na zama Mrs Abbas Kwaccido.
Amina Aminu na daura min zani, Dr fadima ta miko wayata, ganin sunan seda naji wata faduwar gaba ta ziyarce ni babu wanda ya kula dani haka na dauki wayar, cikin sanyin murya nayi masa sallama, da kyar naji amsawar da yayai saboda yadda background din ke cike da hayaniya alamun basu bar wajen daurin auren ba. Kamar whisper haka ya sanar min ni yanzun tashi ce, he's completely mine also, yana mana fatan alkhairi. Wani farin ciki ne ya mamaye ni, instead naji tsoro se naji wani irin safety yayi clouding dina tamkar shield aka rufe ni dashi. Kafin na sauke wayar gidan ya dauki buda alamar zancen ya iso, sadakina da gold ya biya. Adda tasa nayi sujudus shukr sannan nayi sallah rakaa biyu lokacin angwaye suka iso. Suka gaishesu hotunan kadan akai saboda yana sauri ya shirya baifi 3 hours ya rage flight dinmu ya tashi ba. So nima yana tafiya aka sake murje ni da taurarruka, dura wancan sha wancan haka har aka gama nayi wanka aka min turare sannan na shirya cikin wata farar soft abaya, free ce kamar zubun bubu, anyi mata ado da wasu flowers da palse masu kyau. Komai fari nasa. Tunda akace yazo na fara kuka har da Ummaah a kukan balle Asiya. Inna ta saka ni ciki bayan munyi sallama da Abba. Inaji driver yaja muka tafi har lokacin kuka nake, ko rarrashina baiyi ba hakan ya kara tunzura ni, seda driver yayi parking sannan ya matso kusa dani ya shafa bayana bayan yayi hugging dina yace1

"It's ok, stop crying. You're safe!"

Dif kukan ya dauke, yanayi bazai fadu ba amma that's the first closest body contact we had, shima kanshi seda yaji a jikinshi. Tare muka fito bayan ya goge min fuska, akai screening da weighing hand luggage dinmu muka tafi.
You got that smile
That only heavens can make,
I pray to God everyday that you keep that smile.
You're my dreams
There's no a thing i won't do,
I'll give my life all for you,
Cux you're my dreams.
And baby, everything that I've is yours,
You'll never go cold or hungry,
I'll be there when you're insecure,
Let you know that you always lovely,
Bcux you're d only thing i got right now.
Tunda muka boarding jirgin baccin gajiya ya fara dauka ta, ni ce jikin window shi kuma a gefena. Ganin yadda nake ta lumshe idona yasa ya daura min kaina akan kafadarshi, hakan da yayi min ba karamin dadi naji ba, se bacci ya dauke ni so peaceful dukda ban samu na ware kafata ba amma wannan body contact din is so loving. Daga karshe kaina cinyar shi ya mayar min hakan yasa na kara sakin jikina, idanunshi gaba daya suna kan fuskata ni ban masan yana kallon ba all i know I'm cuddled. Hannunsa yasa yana shafa hancina zuwa lips dina da nayi musu damping lip balm akai. Bansan iya lokacinda ya dauka yana surveying fuskar tawa ba, nasan dai ni ban tashi ba se da aka fara announcement akan kowa yayi fastening seat belt dinsa, the plane is about to land, shi ne yasa ya tashe ni a hanakali. Idanuna na bude na kalleshi sannan na gyara zamana , da kanshi ya saka min belt din yace+

"Kinsha bacci?"

Dan murmushi kawai nayi bance komai ba, saboda normally idan na tashi a bacci bana son magana se naga kamar zaaji bakina yana wari hakan yasa nayi shiru bance uffan ba. Shima bai kara cemin komai ba se hannuna da ya riko yana tracing lallen da nashi hannun, wani irin electrical waves na dinga ji suna shiga jikina, kafin wani lokaci jikina ya mutu kuma bazan iya janye hannun nawa ba. Ana gama komai muka fito akai screening da komai sannan muka bar Riyadh, dama nasan umra zamu fara yi kafin muje states. Kafin ya samo mana cab din da zata kaimu yasa na zauna kan wani bench da luggage dinmu sannna ya tafi. Ina zaune inata kallon mutanen dake ta hada hadarsu not minding harkar kowa.

Numfashi na shaka a karo na babu adadi ina kara yiwa Allah kirari, ni kaina inajin kamar mafarki nakeyi ba gaske bane, ni ce nayi aure ni ce nake da miji har na taho honeymoon? Idanuna na lumshe ina jin komai a rayuwa Allah ya tsara anad timing matters alot, no matter how badly you want something idan Allah bai yarda lokacin abun bane sede ka takura kanka kawai. Aure ba farilla bane, sunna ce me karfin gaske sede you can't be accountable of what you've not done, Allah alhakim ne, yafi kowa HIKMAH yafi kowa sanin menene ya dace da wannan bawan nawa, a rayuwar nan saboda matsin da ake ciki na takurawa akan rashin aure mutane da yawa are into bad marriage, wasu sun bar gida gaba daya.

Mun rigada munsan aure is a mutual agreement between souls, zama ne wanda ake adduar ya zama har abada, what if baka shirya ba ka shiga? Baka san me zaka tarar ba ka shiga? Wannan su ne abunda ke leading to broken homes..... Tabani yayi hakan yasa na juyo da sauri yana tsaye hannunsa da bottled water, se wata leda kuma a dayan hannun. Mika min ruwan yayi na kuskure bakina sannan nasha, se muka dauka kayan wanda shi ya dinga kaiwa ya hanani dauka muka zauna bayan motar, driver ya tada muka dau hanya.

"Tunanin ke kikeyi?"

Kallonshi nayi sannan na dan langwabar da kaina nace

"Rayuwa!"

Kanshi ya gyada tareda kara kamo hannuna yace

"I see, tamu ta rigada ta canja. Munyi addua neman alkhairi se Allah ya mallaka mana junanmu, kinsan me yake ce mana, ni dake we're perfect for each other. I'll do everything possible within my reach to make it possible. Inshaaa Allah bazakiyi dana sanin zabin da kikayi ba, I'll make you the most happiest queen in her kingdom, it will only be possible if you are willing to"

Hannunshi dake cikin nawa na damke inajin wasu irin mixed feelings suna flooding cikin jikina. Kamar mai koyon magana ko kuma me tsoron abinda zata fada nace

"I'm willing to, I'll be submissive Inshaaa Allah"

Wani bone crushing hug ya bani kamar zai maidani cikin jikin shi, hannuna nasa na rungume shi nima inajin wani sanyi na ratsa zuciyata.

Muna zuwa muka isa masaukinmu, ba suite bane daki ne guda daya hade da bayi a ciki. Shi ya fara wanka sannan na shiga nayi, seda na gama sannan na fara tunanin yadda zan fara fitowa gabanshi a haka. Se naji muryar shi yana cemin ya sauka kasa zai karbo sako, ajiyar zuciya na sauke sannan na fito bayan naji ya rufe kofar, da sauri na saka kaya bayan na shafe jikina da soft scented perfume. Ina zura hijabi yana shigowa hannunsa rikeda tray ashe ba inda yaje, he gave me space na shirya, da sauri na karba na aje a kasa akan rug din dake shimfude. Seda mukai sallar da mukai missing sannan muka ci abinci. Yana cikin farar jallabiyya ni kuma baka se hijab dana daura akai muka tafi harami tareda daura niyyar umra. Seda muka gama abinda zamuyi akai sallar ishai sannan muka fara walk yana nuna min abubuwa wasu nayi dariya wasu na harareshi. A karshe mukaje wani ice cream parlor ya saya min na sha a gurin, shi dama yace min shi bai taba sha ba ai abin yara ne. Ban kula shi ba seda ya sake jiki yana bani labari kawai na ciko scoop din hannuna nasa mishi a baki ina dariya, a zabure ya mike kamar wanda aka saka mishi flagyl a baki, kallonshi nayi ganin ya tsotse tas yana wani yamutsa fuska. Dariya nayi nace

"You like it?"

Kanshi ya gyada kamar wani me zance, cikowa na karayi tareda kai masa bakinsa and babu musu ya karba, karshe dai tare muka shanye. Se ya cemin wai dama haka yake da dadi bai sani ba, nace all thanks to me yanzun ka sani.

Bazan taba manta zaman sati daya da mukai a saudia ba, bai min komai ba a cewar shi se mun fara neman albarkar auren kuma saudiyya ai ibada mukaxo yi. Believe me munyi ibada, munyi yawo ya nuna min duk kulawar da ya kamata ace an nuna min.
Da daddare jirginmu ya tashi zuwa italy instead of states. An canja saboda akwai wani official assignment da zaiyi acan kuma time baiyi ba so shiyasa. Rome urbe airport anan jirginmu ya sauka. A gajiye nake likis dan kayan ma se shi ya dakko, karku manta ni a son jiki har yanzun bawai na daina bane kawai na rage ne. Hotel din da yayi mana booking muka wuce. Tabbas Rome ta hadu it's an ancient city of historical significance.
Muna tafiya driver da Allah yasa yana jin turanci yana mana bayanin gurare, iyakar building dinsu ma abin kallo ne. Se na ware duk wannan kukan gajiyar da nake ya tafi. Hotel dinmu ya kaimu bayan Jewel ya karba digit dinsa akan zai zama idonmu a Rome. Wannan ma dakinne kamar wancan, ina ganin gadon na fada saboda yadda yayi kyau ya sha gyara Kamar babu gobe. Kwanciya nayi yazo daidai kafata ya zauna yace
"Cara Mia! Kiyi wanka se kiyi baccin"

Kafadata na girgiza ina zumbura baki nace

"Ka fara ni na gaji"

Kanshi ya gyada tareda mikewa yace

"Nidai ban bada gajiya ba amma kullum zancen gajiya kike, I'll give you the gajiya you crying for"

Bansan na tashi ba se gani na nayi kawai a toilet na fara watsa ruwa abin ma se ya bani dariya, daidai toilet din yazo yace
"Kiyi sauri kinji wasa nake yi"

Turo baki na nayi kamar yana ganina na cigaba da wankan. Ina fitowa na shirya cikin simple skirt da riga na wani bakin material da na taho dashi. Hijab na saka na leka balcony yana tsaye yana kallon gari. A hankali ya juyo yana kallona se na karasa gefenshi na tsaya ina kallon yadda motoci ke ta gewayen su.

"The view is breathtaking isn't it?"

Kaina na gyada ina murmushi nace

"Sure, kaje kayi wanka to mana"

"Ina wari ne?"

Da sauri na girgiza kaina nace
"Kai, ni ban fada ba fa kawai kayi ko kaji dadi"

Barina yayi a gurin bayan ya min peck a kumatuna, gaba daya na rike gurin ina wani smiling foolishly inajin kamar bai dauke lips dinsa daga gurin ba. Haka ya fito ya taddani tsaye ina sake sake, mukaci abinci sannan muka dan fara hira kadan kadan dukda yawanci hurar ba maganar baki bace, its a soul conversation dan tunda ya ciren hijab din jikina hannunshi ya fara roaming zuwa sashen da ban ma taba expecting bayan hannuna akwai wanda zai iya tabawa, jiki da jini shekaru sunja, ga aikin hormones take naji dukkan jikina ya amsa, kowacce gaba ta jikina was accepting and welcoming that sensation da maraba. Karshe cushion din da muke kai se ya gagara daukar mu haka ya Jani passionately muka koma gado. He gave me something that taste as sweet as honey!

Something as sweet as honey!+

Gajiyar da nake kukan ta tun a nigeria, ita ya daura min, danma yace shi a idanunshi nothing is as fragile as I am, hakkinshi ne yayi duk yadda zaiyi yayi protecting dina. Ban taba kawowa ko cikin daydream dina akwai irin wannan kulawar, da Jewel ya bani ba. Tamkar zai tsaga jikinshi ya maida ni ko kuma ya min numfashi haka yayi. Tabbas Jewel worth the wait.

Ranar babu inda muka leka har washegari muna daki daga kan sofa se kan gado se kan rug. Se dare ya fita karbo min pizza anan mukai whatsapp video call dasu Ummaah, tana ta tambayata ko akwai abinda yake damuna nace mata babu amma dukka hankalina se naji yayi gida, naji babu abinda nake so illa na ganni gaban Ummaah, so tun kafin muyi sallama na fara kuka. Cikeda damuwa tace

"Menene Asmau?"

Kaina na gurgiza nace

"Babu komai"

"To ki daina kuka kinji? Kowacce mace da kike gani da haka ta saba. Kowacce seda ta bi wannan process din. Ki kwantar da hankalinki kinji kar ki daga masa hankali"

Aikuwa dai na kasa tsayar da hawayen se sallama kawai tayi min, tana kashewa kuwa na hada kaina da gwiwa na fara wani sabon kukan, wani abu naji ya tokare min makoshi na. Ina wannan halin Jewel ya dawo, bakin shi da sallama ya shigo. A zabure na mike zanyi toilet amma ina ya rigada ya ganni, aje kayan hannunshi yayi ya karaso inda nake tsaye nasa tafin hannuna na rufe fuskata ina wata sheshekar kukan. Baice min komai ba kawai ya jawo hannuna ya kaini bakin gado na zauna, shi kuma ya dakko min ruwa me sanyi da ya tsiyayo daga dispenser ya kawo min , babu musu na karba saboda many are contemplating on where the soul is, Believe me cold and chilled water knows its location. Inasha naji a hankali wannan kululun na wuyana yana melting down, na saki ajiyar zuciya tareda aje cup din na karba tissue daya miko min na goge fuskata. Shi bai cemin ba se ya wuce toilet sannan ya fito yace

"Je kiyi wanka"

Banyi musu ba nayi stripping kayan jikina se towel na daura na shiga a ciki inata bawa kaina hakuri saboda i can read damuwar da yake ciki kuma na tabbatar gani na a hakan ne. To ya zanyi? Nima I can't help it I'm missing home kuma normal ne ga kowacce amarya irrespective of age. Yana zaune na sameshi hannunshi yana danna waya, murmushi na sakar mishi wanda yasa dole ya mayar min da martani tareda tasowa ya amsa towel din dake hannuna yana gogen jikina, kunyar  nan ba duka ta tafi ba wata dai ta wuce amma still akwai ta. Da kyar na yarda ya shafa min soft lotion shima da gangan yake tsokanata, kafin na gama shiryawa gaba daya mood dina ya canja se dariya nakeyi. Wani pallazo pant na saka maroon da free shirt me dogon sleeve peach na saka sannan nayi rolling, seda yayi surveying da kyau sannan mukai hoto saboda babu inda shigata ta fitar da surar jikina.
Hannunshi cikin nawa muka fita zuwa ground floor kafin mukai exiting gaba daya daga hotel din, wannan driver na gani a tsaye yana jiranmu. Da murmushi ya gaisheni na amsa sannan muka shiga muka dauki hanya. Na kalli Jewel da suke ta hira da mutumin nace

"Colosseum din zamu je?"

Kanshi ya girgiza yace

"Surprise"

Bakina na tura nace

"Bana son surprises fa"

Girarshi ya dage min yana yar dariya da tasa na shagala hanci baki da ido ina kallonshi, a hankali na kai hannuna kan side burns dinsa da suke kawatar da fuskarshi, Allah ya sani i always admire maza masu side burns se gashi na samu se nyi yadda nake so. Yadda nake ta wasa da hannuna a gurin yasa ya kasa concentrating kan maganar da suke kawai se yayi shiru tare dashi lumshe idanunshi, nayi murmushi na kwanto a jikinshi babu bata lokaci yasahannunsa yayi enveloping dina into a hug.

Trevi fountain mukaje naga water fall, mukai hotuna inata jin dadi kamar zan tashi sama, shikam se murmushi yake yana jin ddin ya sani farin ciki, hannuna cikin nashi munata strolling a gurin inda yamin kyau na tsayar dashi muyi hoto a haka har show din ya kare muka tafi. Muna kwance ni dashi mun gama shirin bacci, ya kawo hannunshi ya kama nawa yace

STORY CONTINUES BELOW
"Tell me me yasa kike kuka dazun? Ni ne? Nayi miki laifi Cara mia?"

Kaina na girgiza nace
"Ummaah ce mukai waya da ita, i was missing her"

Sosae yayi dariya tareda kissing bakina da nayi pouting lips din yace

"Auta, shagwabar ta tashi kenan?"

Hannuna na kwace ina kara zumbura baki, a haka muka shiririce ya cikani da soyayya and i gave him something he'll never forget. Washegari gaba daya ranar yawo mukai, se ranar mukaje colosseum din, gurin yayi bama yadda nake expecting ganinshi ba. Ancient building ne sosae , mutumin yana ta bamu labarin yadda akai colosseum din haka. A daren muka koma pisa, kwanan mu daya mukaje naga leaning tower, mamaki sosae nake ta kasa a daidai take amma daga can ta karkace wai saboda tsayin ta da ground softness, daga baya tsoro na dinga ji kada ta fadao amma ga mutane nan nata harkokinsu babu wani wanda ke da damuwa.

America ita ce inda mukaje bayan mun bar italy, tunda mukaje bama ya zama saboda wannan seminar din se yamma yake dawowa, so kawai se nake fita zuwa ground floor wajen wani pool ina kallon mutane ko kuma daga balcony inyi tsaye inata kallon gari. Seda yayi sati kafin ya kammalla aikin. Nayi wanka nasa wata off shoulder top thigh length. Gahina dana taje nayi parking dinsa in a bun na kwanta saboda bacci da nake ji. Cikin baccin naji massage with those soft palms of his. Idanuna da suka canja color na bude ina mitsitsika idanu nace

"Ka tashe ni"

Shima yadda nake turo bakin haka ya turo nashi yace

"Inata sauri nazo shi ne kike bacci"

Dariya nayi nace
"Tohm na tashi anything for me?"

Kanshi ya gyada yace

"Sosae ma, lemme bath and come"

Mikewa nayi na bi bayan shi nace

"I'll help"

Murmushi yayi min muka wuce tare, it was enticing. A sweet moment actually! Munje famous golden gate of San Francisco, brigde din da ya hada Pacific Ocean da francisco peninsula. Ta mota mukaje naga brigde din da gate din. It was a wow mashaa Allah, kana tafiya ruwa a kasanka. Washegari muka koma mukai riding boat na kankameshi kamar zan fadar dashi, nan kuma kana kallon motoci nata wucewa akan bridge din. Kwana biyu muka kara se malaysia anan naga Twin tower gaba daya mun gaji musamman ni so kawai nake na ganni a nigeria. Seda muka huta sosae sannan muka taho nigeria cikeda farin ciki marar misaltuwa.

A Abuja muka kwana sannan da safe muka taho kano, a farawa layout anan gidan yake, yaya halifa shi ya dakko mu daga airport, tunda muka fito daga gurin screening na hangoshi dasu Addas da Maman Raudha tazo harda Hajara sister shi dake sokoto tana aure, dama ba taxo biki ba saboda basu kasar. Har seda na gaji da rungumar da ake min kowa se zuzuta yadda nayi kyau nayi fresh dani kana kallona kaga ta gaban goshin Kwaccido! 😆.
Motar Yaya halifa muka shiga akai sabon convoy na rakiyar amarya. Gidan bayan Ibrahim kunya yake, amma se an shiga ciki. Flat duplex ne me kyau. Dukkansu a waje sukai parking me gadin ya bude yana ta gaishe mu, ban manta adduar da Ummaah tace ba, nayi idan zan shiga. Ko ina ka kalla flowers ne wasu a cikin pot wasu a cikin pits. Ga motata anyi parking ga tashi guda biyu sun saka tawa a tsakiya. Anty hajara ta bude kofar parlon muka shiga . Awnnnnn Allah ya sakawa Abba da alkhairi, tabbas komai yayi. Parlon yayi kyau anan muka zazzauna anata wasa da dariya sunfi awa kafin kamar hadin baki suka tafi. Kowa na mana fatan alkhairi. Muna dawowa na cire mayafin jikina na nufi dining area inda Adda tace akwai abinci. Biyoni yayi yace

"Se ace bana baki abinci ai"

Murmushi nayi nace

"I missed Nigerian dishes"

STORY CONTINUES BELOW
"I see"

Ya fada yana zama gefena, masa na zuba masa da miyar taushe ni kuma na zuba dambu amma ya barni naci se hadewa akai. Gurin na gyara na wuce kitchen yana bayana kamar wani bita zai zai, nanma kitchen din subhannallah! Dakuna hudu ne, uku akai furnishing kowanne da kayan gado dayan kuma aka barshi aka saka kanan sofas da round center carpet, shelves da study table da lamps akai, se books dina da nashi a ciki. Ajiyar zuciya na sauke ina kara yiwa Allah godiya.

Washegari na samu na kira duk wanda yazo bikina, nasha tsokana kyaftun harda cewa zata kawo PT strip bata san lokacin period ma nake, shima da na fada masa yayi ta mita

"Yanzun Cara mia you're telling me I'm not a good shooter"

Bakina na rufe ina dariya ya girgiza kai yace zaki sani. Kwana uku da dawowar mu ya kaini gida na yini. Dake mostly idan ina period se nayi ta kwadayi so kowa yayi tunanin ciki ne dani aikiwa nasha gata gurin Ummaah da inna wadda tsufa ya kara kamata. Da daddare yazo daukata Abba ya kara mana nasiha akan zaman aure sannan ummaah ma haka. Har mun shiga mota Asiya ta kawo min guntuwar fish sauce din da tunda nazo Ummaah ta min nake ci tace, wai Ummaah tace idan mun dawo zaayi min. Kallona yayi yace

"Me kikace musu?"

"Nothing sunyi tunanin inada ciki ne"

Na fada ina dariya, kanshi ya girgiza yace
"I'll give you don't worry, enjoy while it still last"

Sun comes up on this new morning,
Shifting shadows sunbird sings,
If this words couldn't keep you happy,
I'll do anything.
When you feel alone I'll be your shoulders,
With the tender touch, you know so well,
Somebody once said it's the soul that matters,
Baby who can really tell? when two hearts belong so well,
May be the walls will tumble,
Sun may refuse to shine,
When i say I love you, baby you gotta know.......

Muna idar da sallar asuba na hada mana pancake da tea muka sha muka dauki hanyar hadejia, kusan shi ne lokaci na na farko dana fara zuwa hadejia. Tun ina taya shi hira har bacci ya daukeni dan daga Gujungu bana tunanin na kara gaba, seda ya wuce yan leman sannan ya tasheni wai naga hanya, ni haushi naji ma shima bai kulani ba. A haka ya dinga nuna min wasu garuruwan har muka shigo hadejia ginsau birnin doki masu ruwan atafi kogin..... A GRA gidansu yake babban gida ne haka, an gyara shi, parking yayi muka fito muka shiga ciki, ko me zan tarar shi ne abinda nake ayyanawa.

Masu musu hidima sunata gaishe mu da murmushi a fuskata ina amsawa har yayi leading dinmu wani katon parlor da babu kujera ko daya se wani katon rug a malale a kasan, se kanana a me circle, me square an shimfida a guraren parlon. Wasu dattawa su biyu kana kallonsu kaga iyayen mijina a zaune se Raudha da wasu yara guda uku an zuzzuba musu tea a cups. Raudha na jin sallamar mu ta sheko da gudunta tana fadin

"Uncle Anty oyoyo!"

Hannunta na riko muka shigo kaina a kasa inata murmushi, matar ta mike da ta dan girma Ummaah kadan, shikam datijjon sanye da glasses yafi Abba. Da murnarta tana  fadin
"Yau ga 'yata tazo"

Rungumeni tayi inata kokarin tsugunnawa tana dariya tace

"Sannu da zuwa ASMA'U FARA'YAR SHEHU"

Zama mukai nace

"Ina kwana Baba"

Yayi dariyar yace

"Alhaji ake cemin, idan kikace Baba se naji kamar ba yar dana haifa ba"

Kaina na gyada ko a iya haka aka tsaya naji dadi. Kafin wani lokaci an kawo mana abinci irin na asalin gargajiya, yan matan da suke riko suka zo ganina duk na kasa sakewa naci abincin seda Hajiya ta lura tace masa

"Yaya Asmau ba ta ci fa"

Kallona yayi yace
"To duk sun makalkale ta ta ina zata ci abinci, come on ku saketa hakanan"

Hararshi nayi su kuma kowa ya baje amma dukda haka se daki aka kaini naci Hajiya na fadin a ina aka taba ganin barebari da kunya. Nace tazo Kwalam ta gani😃.

Satina daya a nan shi kwana biyu yayi ya koma aiki se friday yazo muka tafi inata kewar su Hajiya da muka saba dasu sosae. Mun biya ta kwalam sannan muka wuce sokoto nayi kwana daya a gidan Anty hajara muka dawo kano. Kwanakin hutuna sun kare muka koma aiki.

Ranar monday da sassafe muka karaso, dama tuni kyauftun ta kwadhe min kayana daga dakina an maida shi gidanshi na cikin quaters din. Shi yayi furnishing gidan yayi kyua. Shiryawa mukai sannan muka fito gaba daya kunya nakeji wai ni ce me aure, se nayi dariya ya kalleni ya girgiza kai baice komai ba. Saboda yace wai har yanzun ni yarinya ce nidai jinshi kawai nake.

Ina parking kowa ya nufi office dinshi, ina shiga na cire hijab din jikina na saka lab coat nayi rolling mayafin abayar dake jikina. Glasses dina nasa na dauki ruwa nasha sannan na fito daga office din zuwa ward round. Ranar har gajiya nayi da amsa gaisuwar mutane kowa fatan alkhairi kawai yake min a haka ranar ta tashi na wuce gida danshi ya shiga cabinet meeting.


Aure ba abu ne me sauki ba, duk yadda na kwaso gajiya daga clinic ina shigowa gidan ko zama banyi ba na shiga daki na rage kayan jikina. Agogo na kalla naga uku harda kwata, wanka kadai zan iya yi na samu sallah a daidai. So kawai se na fada toilet nayi wanka yadda ya kamata. Ina fitowa nayi turare bayan na shafe jikina da humra. Atamfa na dakko wata English wax dinkin kimolly tamkar a jikina aka dinka ta saboda yadda ta yi min gyangyan. Sallah nayi hade da azhkhar lokacin hudu har tayi, Kitchen na wuce bayan na daura dankwalin wadda ba iyawa nayi ba seda Ikhrama da Suad sukazo gidanmu a kano suka kokoya min hade da turan tutorial videos shi ne nake dan catching kadan kadan. Na jima a tsaye ina tunanin abinda zan dafa amma na rasa, yanzun da ni daya ce da sede kawai na dafa noodles. Karshe kawai nayi irish porridge se na soya plantain. Ina cikin gyara kitchen din naji sallamar shi a parlor, hannuna na wanke a sink sannan na tsane da hand towel na fito yana zaune kan sofa looking all exhausted. Komawa nayi na dakko bottled water hade da tumbler na kawo masa tareda zama gefen shi ina massaging kafadarshi. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya aje tumbler din yace min

"Allah will bless you Ma'u ta, Kinyi kyau ta gurina"

Far nayi da idanuna tareda mikewa nayi juyi sannan nayi masa wink, hannunsa yasa ya kamo ni na fado jikinsa yace
"Baby!"

Peck nayi masa a kumatu nace
"Kayi wanka muci abinci ko?"

Kanshi ya gyada yayi daki ni kuma na koma kitchen dan karasa aiki na. Daki naje na dakko masa kaya, wani three quarter pant ne da kuma armless top red. A gefen gado na aje masa sannan na kara komawa dan aje abinci.
Seda nayi wata biyar da aure kamar bazan samu ciki ba, period dina smoothly yake zuwa yadda ya nunamin bai damu ba se na kwantar da hankalina tunda nasan auren ma ba karfi na bane ya bani Allah yayi lokaci ne yayi to hakan ma dai cikin da haihuwar shi ma lokaci ne. Ranar monday ce watana na bakwai kenan da yin aure. Da sassafe kamar yadda muka saba muka taho daga kano, gaba daya bana wani jin dadi kawai sede karfin hali saboda bana son ya fahimta. Muna daukar hanya bacci ya daukeni bani na farka ba seda muka zo Fanisau sannan na tashi. Zama na gyara tareda kallonshi nace

"Well done Sir!"

Dan kallona yayi yace

"Sleepy head."

Sunan kenan na kullum indai nayi bacci. Kamar yadda muka saba a office dinshi mukai breakfast na saka lab coat dita na fita dan ranar surgery zamui ni dashi. Da sauri na hada kan yan team dina muka tafi ward round. Muna zuwa komai set kawai farawa mukai, kafin mu gama nayi matukar gajiya kuma it's unlike me, dan se na jima ina aiki ban gaji ba, I'm the workaholic Shahada! Ina gamawa kaina kamar zai tsage saboda ciwo kwana biyunnan abinda ke damuna kenan ciwon kai. Nayi tunanin stress ne amma it seems kamar akwai wani abu.

Fanta nasa aka karbo min na zauna a station ina sha, anan na lura da kafata ta fara kumbura, kallon Metron nayi nace mata a gwada min BP na. Da kanta ta gwada min, na kalleta da mamaki kamar yadda take kallona with amazement tace

"Kin gani?"

Da damuwa a fuskata nace

"I can't believe it, ya BPna haka?"

Kara gwadawa tayi amma reading is still very high, no wonder nake ciwon kai wani lokacin har ina ganin dishi dishi nayi tunanin ciki ne da nake tunanin ya shige ni yasa hakan. Wayata na ciro daga aljihu na jin tana ringing na dauka , Jewel ne

"Cara Mia ke muke jira"

A sanyaye nace masa ganinan haka na mike babu wani karsashi a tare dani na tafi OT, dukkansu sun shirya so ina shiga nayi changing muka fara aiki. Sosae na daure dan kada ya lura and God so kind bai fahimta ba har muka gama. A ciki na barshi naje na zauna nayi documenting komai sannan na fito daidai lokacin shima ya fito yana gyara hannunsa. Kallona yayi yace
STORY CONTINUES BELOW

"Ya dai?"

Kaina na langwabar nace

"Tired"

Kanshi ya girgiza yace
"You look worried muje"

Bayan shi nabi muka tafi office dinshi, seda na zauna sannan ya zauna gefena yace

"Ya akai"

"BPna ne yayi shooting"

Idanunshi ya ware yace

"Haba? How comes? Nawa yake reading"

"180/110 fa"

Mikewa yayi yana girgiza kai ya sake gwada min, glasses dinshi ya cire ya zauna gefe na tareda cuddling dina jikinshi yace

"Baby, me yake damunki?"

Kaina na girgiza inajin wani rauni a raina nace
"Allah babu komai. I dunno!"

Se hawaye ya fara saukar min, rungumeni yayi yana bubbuga min baya har Seda nayi shiru dan kaina sannan yace

"To meye abin kukan kuma? Kiyi shiru kinji."

Hawayena ya share min sannan ya dinga kwantar min da hankali a haka na hakura. Bai daura ni akan drugs ba kawai se yace bari a fara gano sudden rise din. Da muka koma gida ko girki banyi ba se kyaftun ce ta kawo mana dan da kanshi ya fadawa Lamin.

"To kiyi pt mana ki gani ko ciki ne"

Kyaftun ta fada min ina cin abinci, kaina na girgiza nace

"So nake se lokacin period din yayi idan banyi ba se nayi"

Shikenan muka cigaba da hira har dare seda ya dawo sannan ta tafi ita kuma yinin ymin dadi sosae dan na jima banyi irinshi ba. A hankali kuma se yau ya hau gobe ya sauka munata monitoring se daddare yace ya kamata muje ayi pt a gani yana tunanin matsalar daga ni ne. A gida mukayi abinmu and it was positive sede dukkan mu babu wanda yayi murna tunda kuwa yazo da matsala. Bayan munyi sallar ishai muka shiga cikin asibiti don yayimin scanning aikuwa ana yi, ya cemin

"Cara mia molar ne"

Kallon screen din nayi dama jikina ya bani shinkadai ne zai saka BP ya tashi at early pregnancy bayan munsan normally first trimester ana samun low BP. Tissue yasa ya goge min cikina yace

"Sannu kinji"

Kaina na gyada kawai na kasa cewa komai, molar gestation? Ni kuma da abinda zan fara kenan. A haka yana ta kwantar min da hankali mukaje gida. Yana ajeni ya fita se gashi ya dawo da ice cream. Kallon shi nayi nace

"Is that a bribe?"

Kanshi ya girgiza yace
"Not at all, inason naga kina murmushi ne"

Dariya nayi nace

"Gobe se naga Dr halima se ayi booking dina"

Kanshi ya gyada yace

"Nayi mamaki da kika samu molar bayan yafi zuwa mutane below 20years da kuma above 35years"

"A book kenan, Allah a gurinshi it doesn't matter"

Kanshi ya gyada min yace

"Yeah!"

Molar gestation kamar ciki yake amma tumor ne but non cancerous sede idan baayi da gaske ba zai iya zama cancer din. Mostly yana faruwa saboda anyi fertilizing empty ovum ko kuma sperm cells biyu sunyi fertilizing ovum daya, yaron memakon 46 normal chromosomes zai samu 96 saboda an samu duplicate copy. Scanning ke nuna cewar wannan molar ne. Se terminating dinshi akeyi da zarar ansan shi dinne. Washegari bamu fita da wuri ba se wajen 9am muka tafi, office din Dr halima muka fara zuwa tana ganinmu ta mike tareda bamu guri muka zauna. Seda muka gaisa ya mika mata scanning dina , kamar patient haka tayi counselling dinmu sannan tayi admitting dina a Amenity. Kafin wani lokaci har yan dubiya sun cika na rasa inda zan tsoma raina. Da yamma tazo ita dashi aka kaini OT akamun suction evacuation. Lokacinda muka dawo anesthesia bata sake ni ba inata bacci. Se bayan isha sannan na farka lokacin shi daya ke zaune a gefena. Tashi nayi na zauna bayan ya taimaka min yana ta faman jera min sannu. Abinci ya kawo min bayan nayi brush naci sannan nayi wanka aka shigo serving drugs nurse din tayi sannan tayi mana sallama ta tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Ban tashi da wuri ba se wajen tara na safe, ko ina neat dana tashi so wanka na shiga na fito na shirya cikin abayar da ya aje min sea green se maroon dankwali na daura na zauna tareda daukar wayata na kirashi, yana dauka yace

"Kisa hijabi gamu nan zuwa"

Ya kashe hijab na janyo na saka tareda daidaita nutsuwata. Sallamar shi ta katse ni ya shigo fuskarshi da murmushi bayan shi duk manyan asibitin ne. Cikin nutsuwa na gaishesu sunata amsawa sannan suka dubani, my God kyauta dai na sha ta. Nayi musu godiya suka tafi sannan ya dawo tareda zama gefe na yace

"Na gaji Asmau"

"Ka huta kafin ka tafi"

Hannunshi ya kai jikina danjin temperature sede all normal se ya mike yace

"Bari na tafi kada na hana mutane dubiya"

"Aikuwa dai dan kowa yasan kana nan ba zuwa zaayi ba."

Dariya yyai ya fice nasha dubiya kuwan, da yamma akai discharging dina hade da bed rest kawai se muka tafi kano. Se lokacin su Ummaah suka sani, washegari se gata tazo ranar kamar bakina zai yage dan murna bata jima ba sega Hajiya daga hadejia, i was super excited.
A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, kamar yadda Allah ya tsara mana. Rayuwa mukeyi cikin aminci da mutunta juna. Na fahimci sosae me rayuwa take nufi me aurenn shi kanshi yake nufi. Akwai lokuta da dama da nake jin kamar na bar gidan, musamman idan muka sami sabani naji kamar wuta ake zazzaga min but dake ni dashi are all matured minds haka muke hakuri mu dangana. Dadin a nawa yafi rashin dadin yawa, so babu abinda zance se godiyar Allah.

Shekara biyu nayi inata bari seda nayi planning na five months jikina ya huta sannan na samu ciki. Zo kuga tattalli dama lokacin na gama course dina akan family medicine so kawai se na zama a consultation room nake. Munyi rainon ciki babu kakkautawa wayaga dan Doctor da Doctor? Yasha kulawa scan dinmu na farko ya bani mamaki, it shows triplets yayi ta murna ni kuma ina kuka saboda ina tunanin ta ina zan fara wannan rainon, seda ya gama murnarshi kafin ya zauna yana ta bani baki da nuna min CS ne ba wani abin ba. Aikuwa dake Allah shi ne Allah, babu wani pregnancy complications banda kumburi shi kenan, ina seven months inna ta rasu. Nayi kuka kamar me seda nayi sati a kwalam kafin na dawo, to rayuwar duka nawa ce ma.

Da kyar na kai 36 weeks babu pain ko daya aka ce mana kawai ayi CS din zaifi, tare dashi aka shiga aka kaimin sede yana gefe na saboda ba GA bace idona biyu. Ana cirowa ana weighing ana miko masa, first one din namiji ne se mata biyu. Mashaaa Allah kawai. Ana kaini na huta kamar kasa mutane naga soyayya ko nace triplets dina sun gani. Kyaututtuka kam har seda na daina gane wannan na waye. Ranar suna ya saka musu Muhammad, Khadija da A'isha. Ba sunan kowa bane se gidan annabi da ahalinsa.

Bayan shekara uku sun girma, duk wanda ya gansu yana shaawarsu not knowing ni irin wahalar dana sha. Shekararsu biyu na dage seda aka kaisu school saboda na gaji, kullum kaina kamar zai tsage ga na patient ga nasu, shidai sede ya kalleni yace I'm his everything, he can't imagine life without me.

Shekararsu biyar muka tafi Ukraine, dukkanmu karatu ya kaimu. Tun daga kansu ban kara samun ciki ba saboda nasan uterus dina is very weak idan na matsa mata zaa samu matsala gwara na huta da kyau. Asabar ce weekend ne, tun sassafe na tashi na shiga kitchen, it's Saturday kowa yana da damar da zai zabi abinda yake son yaci, wannan shi ne yancin dana basu dukda I'm a very strict mother amma kuma ina wasa dasu dan idan muna wasa bazaka ce ni ke fada ba. List din na duba, Muhammad nasan noodles, Khadija na son strawberry pancake ita kuma A'isha tace scramble egg da bread zataci. In a jiffy na harhada komai, Daddy dani we always have same choice saboda our hearts and soul are connected komai hakan ke so.

Gyara gidan nayi sannan nayi wanka har lokacin tara da rabi basu tashi ba, seda na shirya sannan na tada daddy ko ta kansa ban bi ba na tafi gurin yarana, yana ta mitar wai na daina kula dashi nidai bance komai ba se dariya naje, ina zaune sukai wanka na shiryasu muka fito daidai lokacin shima ya fito, da gudu suka karasa suna fadin
"Daddy!"
"Kiddos"

Dariya nayi tateda daukarsu hoto sannan mukai breakfast, muna gamawa aka assignment seda suka gama sannnan na kunnna musu cartoon muka fara namu assignment din. Mun kammallla na kalleshi kamar yadda yake kallona, i imagined him a matsayin mijina, idanuna na lumshe ina tuna rayuwata from lokacinda ta rikice bayan kammalla preclinicals dina, nayi hakuri gashi kuma naci riba, yaran na kalla sunata dariya so peaceful hakan ya kara kwantar min da hankali. A wannan gabar ina kira ga duk wacce batayi aure ba kada ta damu lokaci ne, idan yazo se anyi. We all believe aure habo ne haka wasu kance layin markade ne idan yazo kanka se an markada. Nawa suka aje bucket dinsu aka barar, wasu aka sace, wasu aka saka musu gwalagwaji but still seda aka markada. Ina fatan dukkan yanmata zasui koyu da rayuwata su saka ransu the biggest thing will happen, the patient dog eats the fattest bone!

Da daddare muna tsaye ni dashi a gaban balcony, yaran sunyi bacci bayan mun gama video call da yan nigeria, idanuna na daga na kalla sama yadda taurari suka cika sunata haskawa yasa nace subhannallah tareda tabo shi nace

"Come on ina son daya"

Kalla yayi sannan ya kalleni yayi murmushi nace

"Ka kamo min mana"

Kallona yayi cikin idanu, wasu molecules suka samu damar ratsa lens din har retina inda ya tafi kwakwalwata ya tarwatsa komai, shi kadai ne a duniyata no one exist again se shi.

"I've already got my star here"

Ya fada yana nuna ni, rungumeshi nayi na fara bashi wani sensual and seductive kiss, da kyar muka koma daki and he gave me something as sweet as honey!

Alhamdulillah!!!

This piece of work is dedicated to any unmarried lady or a spinster, Allah will make it happen so don't lose hope my dearies. Wanda Allah ya kaddara naku ne suna nan zuwa and they will for sure take you.


Post a Comment for "FARA YAR SHEHU CHAPTER D KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...