-->
olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

FARA YAR SHEHU CHAPTER A

 FARA YAR SHEHU CHAPTER A


Sunana Asma'u Shahada, Mahaifina Dan sanda ne Wanda ya taka Har matsayin CP that's commissioner of police, sede yayi retire a halin Yanzun. Amma dukda haka baya zama saboda shi mutum ne me kazar kazar, he's a patriotic citizen, never believe in zaman banza. yana da gonaki inda shi ne invest dinsa, to kusan kullum se yaje, hakan yasa koda yayi yayi retire amma bai huta ba.+
Asalinmu Yan Taura ne ta Jigawa, cikin garin Kwalam, kakanni  na a Kwalam suke. Malam Aminu shi ne kakana da ya haifi Mahaifina, manomi ne sosae, if I can say Abba anan yayi gadon noma, Don idan kaje kofar kudu kace gidan Sarkin Noma, don't be amaze amma kowa ya sanshi. Inna Ade ita ce mahaifiyar Abba, sunanta Sa'adatu, so se aka cire karshen Sa'ade ake kiranta Ade. Nasha ayyanawa da kuma tunanin yadda akai har zaman Alhaji da Inna Ade Yayi wannan doruwar. Alhaji mutum ne me hakuri da kauda kai, bazaka taba fahimtar fadanshi Ko Maganar shi ba cuz the tone is always same. Inna Ade kam! Jarabar duniya, matar tana da fada na bugawa a Jarida, so far, zan iya cewa akwai possibility din Tasha ruwan Atafi da ake fada saboda sunyi zaman hadejia. Lol. Amma duk wannan hayaniyar tata, bana gani saboda muna mugun good time da ita, Tana sona kuma tana fito na fito da duk Wanda ya nemi takurawa rayuwata, koda Abba ne ko Ummaah, Yanzu Yanzu zata wanke su tas tas, su da suka haifeni kenan balle kuma yan uwana da ba ganinsu take da gashin Kai ba, wannan ai sede dan kansu su bar mata gurin. I knew her Best side so far.


'Ya'yansu takwas, Hajiya Uwani ita ce babbar yayarsu Abba, Tana aure a Majia ta Taura garinsu Nanaye. Tana da Yara wajen goma, kuma baki daya matar photocopy din Inna Ade ce plus Wasu mugayen halayenta Wanda basuda asali bare kuma tushe. Daga ita se Abba shi ne Shahada, kuma Mahaifina, na yadda partially da mutane su kace ana inheriting Uwar miji a gurin haihuwa, yeah akanmu Hakane. Abba shi daya Shi ne namiji, surrounded by sisters, haka nan Ummaah, kuma haka muke a gurinta.
Daga Abba se Umma Falmata, Tana can Adamawa anan take aure, dake Inna Ade asalinta daga can take. Asalin bafullatana ce, bansan yadda akai ta aura Alhaji ba, har ya dakko ta tun daga Uwa duniya Har Kwalam. Mabiyar ta Anty Hauwa ce, boss kenan, se Anty Shamsiyya , Anty Mero sai Anty Rakiya da Adda Ummiey wadda ita ce autarsu, kuma a gidanmu ta tashi, Dan Saar Adda Habiba ce, Tare akai musu aure abinsu.

Sauda Ummaah bakanuwa ce 'yar koki, mahaifanta dukkansu yan nan cikin kanon ne. Ummaah ita kadai ce mace a gidansu, dukkan Yan uwanta maza ne, amma Dayake Allah shi yake tsarinsa bakwai daga cikinmu Duka mata ne se namiji daya tal. Babbar yayarmu Adda, Tana aure anan Kano, wani yaron Abba ta aura, me bi mata Yaya Halifa, sunan Alhajin Kwalam ne dashi shiyasa sunanshi yake a boye. Shidai baiyi aure ba se Karatu kamar zai cinye Boko, Yayi degree, Yayi Msc, banda PgD da yayi, da courses kanana kanana. Yanzun Haka PhD yakeyi. Duk gidanmu ni ce nafi shiri dashi saboda Ina son Karatu, I find joy and happiness in studying. Wannan yasa na zama Kamar kawarshi, I enjoyed been with him. Adda Sa'ada ita ce takwarar Inna Ade, as we all know a gida idan kana da takwara you seems to be in the most goodest relationship da ita, wannan karya ne when it comes to Inna Ade and Adda Sa'ada basu shiri Ko na mintina daya, hardly ka gansu tare. Tana aure a Niger state, Adda Habiba Saar Adda Ummiey ita ce a dutse, se Adda Meeyna, Adda Salma da Adda Maryam se ni kuma auta Kare nono as they always call me.
1995 aka haifeni, Ummaah da Inna Ade, sun bani labarin ranar da zaa haifeni, ranar kawar Inna Ade wadda ita ce Asma'u. Kawarta ce sosae, tun suna Yanmata Har seda akai musu aure. Kunsan aikin police federal aiki ne, so transfer Ko da yaushe ana cikinta. Amma lokacinda Ummaah ta samu cikina, shi ne lokacin da Abba yake ASP a kano, I was lucky baayi tafiye tafiya da cikina ba.
Ranar Alhamis ce, dake Inna Ade, in har Ummaah Nada ciki to duk sati se Tazo, Har Se Ummaah ta haihu kafin zata tattara ta tafi, wannan zaman an dinga balai da ita, musamman itada Adda Sa'ada, wani lokacin Abba ke raba fadan. Ile kuwa ranar sun gama yinta, Adda Sa'ada tayi girki Inna Ade tace Allah ya kasheta, ita tuwo zataci, Adda tace ita kuwa kitchen ta gama shigarshi a wannan ranar sede Inna tayi da kanta.
"Saude Saude! Ki fito Ki raba Dani da wannan shedaniyar yar taki"

Ummaah na daki, ita kadai tasan halinda take ciki, ta jiyo kiran da Inna Ade ke yi mata, Ta sani Ko Baa fada ba, Adda Sa'ada ce kawai Inna zata dinga ihu akanta. Gaba daya ta jike da gumi sharkaf, ta fito da kyar, daidai karasowar Inna Ade, Tana mitar rashin amsata da Ummaah tayi, kicibis sukai, abinka da Manya tana kallon fuskar Ummaah, tasan nakuda take, babu bata lokaci ta saka wani cousin din Abba, kawu balarabe wanda ke zaune gidanmu Ya dakko Mota suka wuce asibiti.
Ana karbar ta, Inna ta saka a sanar da Abba, Allah Ya taimaka ya tashi a aiki, hakan yasa ya nufo asibitin, Babu jimawa aka fito Dani cikin zani an haifeni, Inna Ade tace min kwatakwata da karbata baifi mintina uku ba, sakon rasuwar kawarta Asma'u ya iske ta. Ta shiga Tashin hankali marar misaltuwa, Inna Ade tayi ta kuka Abba yana lallashinta. Duk yadda akai ta hakura amma taki, se fadin

"Shahada, idan zaka saka a kaini Jimeta ka saka, idan baka sawa ka barni na tafi! "

Babu yadda ya iya haka yasa a ranar aka tafi da ita Jimeta. Seda akai kwana uku sannan ta dawo. Tana dawowa kuwa tace lallai sunan aminiyarta Zaa maida min. Ranar da na cika kwanaki bakwai aka rada min sunan Asma'u, Inna Ade tana cemin FARA 'YAR SHEHU!

Na tabbatar once a rayuwar Abba da Ummaah, Sunyi regretting saka min wannan sunan, ba Dan komai ba se Dan Inna Ade. Duk weekend din duniya tana kano Tare dani, as I heard, bakina da sunanta Ya Fara budewa, sunanta na Fara kira.
Nayi shekaru biyu aka bawa Abba commissioner of police, sannan aka masa transfer zuwa Taraba state, inda anan ne Zaiyi commissioner din. Aka kammalla dukkan shirin tafiya, amma Inna Ade tayi tsalle tace babu me tafiya Dani, a gurinta zan zauna. Inna Ade yar daru ce ta gaske, waye Zaiyi musu Abba ko Ummaah? Babu. Haka aka tattara ta tafi Dani Kwalam su kuma suka wuce Taraba abinsu.
Da wannan rayuwar na tashi, babu Wanda na sani se Innata, a Haka Har na Fara Wayo nakai shekara hudu, duk lokacinda Abba yazo da niyyar tafiya Dani Dan Ya sani a makaranta, Se Inna ta Fara kuka,
"Shahada akan yarka zaka nuna min iyakata? "

Ummaah ta lallabashi Badan ransu yaso ba, suka kyaleni a gurinta, amma seda aka kaini central primary school dinsu. Ni mutum ce me wasa da kiriniya, I pay attention to nothing, so ko da mukai exams, it was beyond comment, ni na dakko ajin. Abba Kamar Zaiyi kuka Dan takaici, Yaya Halifa kam Kirirkiri Ya fito sukai ba dadi shida Inna Ade, bata kulashi ba saboda Tana yawan cewa, ita tasan darajar miji, so shi yana cin darajar sunanshi Aminu.
A Haka rayuwa ta cigaba da gungurawa, kullum hankalin iyayena yana kaina, as for me duk tunanina Inna ta haifeni, su ina daukarsu kawai yan uwanmu, Kamar yadda naga Sauran na zuwa. Seda nayi shekara bakwai sannan nayi wata rashin lafiya wadda seda muka kwanta a Aminu Kano. Munfi wata sannan na samu sauki, wannan shi ne asalin dawowata gidanmu, Inna ta hakura a cewarta kada mayu su lashe mata kurwata. God so kind!

Surprised? Ooooo

Bayan dawowata abinda aka Fara kokarin yimin, shi ne makaranta. Dayake lokacin Ummaah ta gaji da binshi, se sukai settling baki daya a kano, shi kuma Yana zuwa ya koma. Adda Maryam kadai ke primary lokacin, itama kuma Tana Basic 5, a excel college. Spring aka kaini duk dan na dan farfado daga asarar da akai, Basic 1 aka kaini, amma matsalar ko two letter words ban iya ba. Bazan taba manta wannan abin ba.1

Ranar da aka Fara kaini school din, Inata murna abuna, saboda uniform din kawai birgeni yake, ga lunch box dina, Ummaah ta shake shi da chips, ga Caprisonne. Oolala! Yaya Halifa ne ya Fara kaini, seda ya rakani Har class sannan Yayi min kashedi, tareda fadawa uncle din ya saka min ido sosae, Aikuwa Ya saka, dan na amshi wuya hannun bawan Allah nan.

Abinda ya Fara sakawa na karaya nafi kowa girma a ajin, saboda Inada Girman jiki, ga yawanci duk sun iya turanci ni kuwa daga come and go babu abinda na sani, gashi Baa vernacular a school din. Se ya zamana idan na shiga har a tashi bana magana, saboda na taba gwada surutu da Hausa, aka fadawa uncle Ya zaneni. Tun daga lokacin na daddara bana taba gigin yin surutu.

Idan na dawo gida bayan an tashi lesson, islamiyya ce zamu tafi nida su Adda, bazamu dawo ba se 5:30. Da anyi Sallar Maghrib, Yaya Halifa zaizo da Belt in dakko books dina, ina kuka Haka Zamui homework dina sannan ya koya min sabon abu, wannan belt din na gefe, bawai dukana Zaiyi ba amma ita ta barazana ce. Karshen dukan shi ne rankwashi. Duk yadda nake son kallo musamman cartoon banayi, ana gamawa zanyi Sallar ishai na kwanta. Cikin sati biyu gaba daya na fita a hayyacina saboda ban saba irin wannan rayuwar ba. Rayuwar Kwalam babu sawa bare takurawa, kullum se nayi kukan zan koma gurin Inna amma babu me kulani, se idan Boss din gidan tana nan Adda Salma ta bubbuge ni, so shirina da ita kadan ne.

Ana haka aka kawo wani new student, Emma a class dinmu, Shi duk yafi mu, gashi azzalumi babu hasken musulinci tattare da yaron nan, tunda yazo shikenan Sauran walwalar da nake da ita ta tafi. Ya rigada ya gane ban iya turanci ba kuma ko yayi min abu I can't express myself hakan yasa yake cin zalina shida gang dinsa. Ranar duka gida aka makara, so ko breakfast bamuyi ba haka muka taho se daga baya Ummaah ta aiko driver ya kawo min Abinci, Inata murna saboda azabar yunwar da nake ji, amma ina karbowa Emma da mutanenshi suka karbe abincin, Ina kallo suka cinye, Aikuwa Na dinga kuka na tafi gurin uncle, it was embarrassing. Ina zuwa yace min


"Asma'u what happened? "


Gaba daya na diririce saboda bazan iya cewa "He ate my food" ba haka na gaji da tsayuwa na koma na zauna. Shikenan suka gane lagona Har dukana suke, gashi ni kuma a gida haushin kowa nakeji, ina ganin duk su suka jawo min, da ace Ina Kwalam waye zaimin haka? Ai babu shi idanba so yake yaga kaddamarwar Inna Ade ba.

Da sassafe Adda Meeyna na shirya ni, Inata kuka, kallona tayi tace

"Menene Wai? Yau kwana uku kenan kullum se Kinyi kuka. Makarantar ce baki so? "


Kaina na gyada, Wasu hawayen na sakko min nace


"Ni bazanje ba Adda zazzabi nake"


Wuyana ta taba sannan tayi dariya tace

"Yar gidan Inna, babu wani zazzabi fa, kede kawai kin zama yar baci"


Muna haka Adda Sa'ada, service take anan Kano, kuma mijinta ya tafi wani official assignment a Urk, ta shigo tana fadin

"To! Autar Ummaah me ya faru? "


Nan Adda Meeyna ta fada mata yadda mukai da ita. At this stage, iyaye ya kamata ku lura da wani abu, bullying yafi karkata a primary school, sosae Wanda suka fi karfinsu suke zaluntar su. Shiyasa yaro zai dinga kukan makaranta, saboda Wasu lokutan Yaran Zaa iya threatening dinsu su kasa fada, ya kamata kowacce Uwa ta zama alert.2

Shiru Adda Sa'ada tayi sannan ta kama hannuna muka fito, Ummaah ta fito dauke da bag pack dita, ganin fuskata kacekace da hawaye yasa taja ta tsaya, fuskarta da damuwa tace

Story continues below

"Uwata" Kamar yadda take kiran Adda Sa'ada, da yake Baa boye mata sunanta, "Me Ya sameta? "


Inajin tayi wannan tambayar na kara kwabe fuska, Inata kuka, Inaji Adda Sa'ada nayi mata bayani, dake Ummaah classroom teacher ce, take ta fahimci abinda yake faruwa. A ranar tare dukka mukaje school akai complain, haka a gaban class aka Zane Emma, shikenan na samu sauki, kuma na dage na Fara turanci, idan nayi ai tayumin dariya amma a hankali da taimakon family na, na samu nake iya hada sentence.

Har term din ya kare babu Inna Ade babu dalilinta, haka muma bamu samu Munje Kwalam ba, in banda Ummaah da Abba, nayi mitar nayi kukan har na hakura abuna. Ranar da akai Hutu na dawo Inata murna Dan zan dan huta at least, Tundaga tsakar gida nake jiyo muryar Inna Ade, matar is very lousy, inhar tana guri some miles away zaka dinga jiyo muryarta, bansan lokacinda na sake lunch box dina da school bag ba nayi parlor a guje ina fadin

"Inna Ade! "


Kanta na fada nayi mata wata runguma me karfi, itama rungumeni tayi tana shafa jikina tareda fadin

"Fara 'yar shehu, Asma'u Sannu "


Sakinta nayi na dawo gefenta na zauna nace


"Inna Ina yini? "


"Lafiya lau, "


Tana magana Tana assessing jikina, se naga ta bata fuska ta kalla sashen da Ummaah take, zuwa lokacin na fahimci har Abba dasu Adda suna zazzaune Kamar Wanda ake wani karamin meeting.

"Saude amma Kinsan ba haka na kawo 'yar shehu ba Ko? Ta Yaya na baku yarinya da kibarta Yanzun Nazo Naga kashi da rai? "


Ni Kaina seda nayi dariya, balle kuma su Adda, amma Ummaah tsakani da Allah Ta Fara kokarin kare kanta. Nanfa Inna ta hau sababi, ita kafata kafarta bazata barni anan ana cuta ta ba, Abba da Ummaah se hakuri suke bata. Se ka rantse da Allah ita ta haifeni, basu suka haifeni ba. Inajin wannan Maganar na Fara murna Dan tabbas a lokacin babu abinda nake adawa dashi kamar zaman gidanmu.1

Halayena Wanda na aje a kofar gida lokacinda zan dawo daga Kwalam su na bude, sabon shafin rashin mutunci, saboda I'm sure babu Wanda ya isa Ya taba ni tunda Inna Ade na nan, islamiyya na tattara na aje, Da daddare nayi ta rigima se nayi kallo, sannan da safe se eleven nake tashi. Babu Wanda ya cemin ci Kanki, se ana gobe Inna zata tafi, mun kammalla breakfast tace da Abba Wanda ke kokarin fita

"Shahada, gobe zan tafi Maganar Asma'u Fara da ita zan tafi."


Abba ya bude baki Zaiyi magana yaga har ta tashi ta tafi, Nima gudun abinda zai biyo baya na take mata baya zuwa dakin da yake nata, Dan tun zuwanta na tare a can.

Adda Sa'ada ce ta mike ranta a mugun bace ta nufi dakin Yaya Halifa bansan abinda tace mishi ba, all I know ina kwance naji sallamar Adda Maryam, amsawa nayi sannan ta shigo, tareda tambayata inda Inna Ade take, bandaki na nuna ba tareda na furta komai ba, kanta ta gyada sannan tace min Yaya Halifa na nemana. Wata muguwar faduwar gaba naji, saboda babu Wanda nake Tsoro, har cikin raina kamar shi da Adda Salma. Mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na nufi dakinshi.

Da sallama bakina na isa, yana zaune gabanshi Wasu manyan text books ne, se wata dorina me Baki biyu a gefe. Jikina Se ya Fara rawa, naji tamkar na ruga gurin Innata amma who born me? Da kuwa Yayi min dukan mutuwa. Tsugunnawa nayi a gabanshi bakina na rawa nace

"Yaya gani"


"Na ganki" ya furta ko kallona baiyi ba, nafi mintina goma a Haka kafin ya daura kafafunshi akan table din yana kallona yace


"Idan Inna zata tafi gobe zaki bita? "


Shiru nayi saboda bansan right reply ba, zuciyata kowa yasan Inna Ade take son bi, amma wannan Zakin dake gabana, I don't think zan iya fadar son raina. Ina tunani Ashe har ya dauki dorinar, sede jinta nayi a kafafuna dana mikar, wani tsalle na buga saboda azabar radadin da naji tareda bude baki zanyi ihu,

"Idan kika bari naji Kinyi Ko tari ne, se na karkarya ki na zubar anan. Dawo ki zauna"2


Its funny gaskiya, jiki na rawa na dawo na zauna inajin yadda kafafuna ke zugi, yaye skirt dina nayi, abinka da fara tuni gurin ya tashi Yayi jawur, hawaye tamkar an bude famfo haka ya dinga zubowa, kafin wani lokaci fuskata tayi jawur. Sakkowa yayi ya zauna gefena yace

"Kinsan idan na kara jin kince zaki koma Kwalam, wannan bulalar se ta karye a jikinki, kuma Yanzunnan kije Kicewa Inna bazaki bita ba"


Kaina na gyada cikin sauri sannan na mike, kamar haske har na isa kofa Ya dawo Dani akan na wanke fuskata. Ina Naga ta musu, toilet dinshi naje na wanke amma kana kallona zaka San nayi kuka, nasan idan Inna Ade ta ganni a Haka, kilan kashe Yaya Halifa zatayi hakan yasa na wuce dakin Ummaah na kwanta, ranar anan na kwana.


So you guys where truly waiting for me! I got it. Thank you so much for the comments and prayers! I got youAyshatuuuA ka'ida tafiyar Inna da sassafe take yinta, duk inda goma take to ta kama hanya, Haka idan zuwa zatayi da sassafe take zuwa. Tunda mukai Sallar asuba, Ummaah ke harhada min kayana, ranta a mugun bace, I can swear cewar ban taba ganin fuskar ta a Haka ba, saboda ta kasance mutum ce me faraa, hardly kaga ranta a bace.+

Ina kwance ni kuwa Bance mata komai ba, seda ta gama sannan ta dubeni tace

"Tashi kiyi wanka"


Ban Musa ba, na tafi bandaki nayi jika jika Kamar yadda na saba na fito. Da kanta ta shafa min Mai ta shirya ni sannan muka fita zuwa parlor, Har an hada breakfast, Yana aje an baza katuwar dining mat anan parlor, komai an kawo se ci Ya rage. Zama nayi gefen Inna da ta gama amsa gaisuwar Ummaah dukda an rigada an gaisa Tun asuba. Tana ta bani labarin kawayena na Kwalam, da yadda suke dokin dawowata amma ni jinta kawai nake, muna nan Sega su Adda sun fito kusan lokaci daya gaba dayansu, se Yaya Halifa fuskarshi a murtuke ya samu guri ya zauna yana wurga min harara, cikin rashin saa Inna ta lura da hararar, kawai gani nayi ta dada mishi Duka a bayanshi tareda fadin

"Dan banza kawai, uban me tayi maka da safiyar nan zaka kafa hararar ta? Dole yarinya tabi ta lalace, kun saka ta a gaba kamar mayu"


Idaanuna sukai raurau alamar kuka, su kuwa banda dariya babu abinda suke, a Haka Abba da Ummaah suka iske mu, abincin duka babu wani armashi haka mukaci, ana gamawa Inna ta dubeni tace


"Maza Kawata tashi dakko kayanki kizo mu tafi"


Kowa a parlon zuba min idanu yayi, suna jiran ganin abinda zanyi. To everyone utmost amazement kallonta nayi nace

"A'a Inna Ade, kije ni bazanje ba"


Wani mugun kallo Tayi min zatayi magana se kuma ta juyar da kanta zuwa inda Adda Sa'ada ke zaune hannunta da tea mug tana kurba,

"Ahaf! Ni nasan zaayi Haka, wannan yayan suna gidannan ai na daina ganin daidai. Sa'adatu da Aminu ba. Nagode sosae Kunyi kokari. Amma ku sani Fara 'yar shehu Ko kunso Ko kun ki tawa ce, barazanar ku babu abinda zatayi mata! "


Tana gamawa ta Mike tareda kallon Abba tace

"Zan wuce Shahada"


Abba da Ummaah Wanda suka rasa bakin magana suka mike tareda bin bayanta, Nikam dakin Ummaah na koma Inata kuka, wayaga samu da rashi.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya na hakura da zancen zuwa Kwalam na rungumi sabuwar rayuwar dake gabana. A wannan hutun sosae nayi Karatu, Yaya Halifa ba karamin kokari Yayi a Kaina ba. Babu Wanda yake min magana da Hausa seda turanci. Kafin Hutun ya kare har na Fara mayarwa. A bangaren islamiyya shima sosae nake abin kirki, hakan ba karamin dadawa su Abba yayi ba, shikenan aka daina takura min, tunda na riga nayi blending da yadda suke son na zama.

Duk Hutu idan akai Zaa kaini Kwalam nayi sati daya sannan na dawo. A Haka shekaru sukai ta ja har nakai shekaru goma sha biyu, lokacin ake ta cukwukun kaini secondary school. Matsalata daya ce wadda kusan kullum se anjini da Ummaah da Sauran sisters dina, bana Aikuwa, I'm very lazy, laziness dina Har ya saka jikina kanshi na gyara se ya zama abu, wanka se Ummaah tace min naje nayi, balle gashina, se nayi sati biu ban taje shi ba, idan aka samu nayi kitso zan iya 3 months ban tsefe ba. Kuma nafi kowa Baki idan akace Ni kazama ce, kuma deep down inside me nasan ni kazama ce, kuma san jiki shi ne ummul aba'isin kazantar.

Wani yammaci mun dawo daga islamiyya nida Adda Salma da Adda Maryam, tunda muka taho bakina yake a cunne Kamar Karin kunama, saboda Adda Salma tace kaina yana wari, Bance komai ba Har muka isa gida. Ina shiga dakinmu na tarar da kayana duka na cikin wardrobe an fito dasu an watsar a tsakiyar dakin.

Takaici kamar zanyi me, ciki na karasa Ina bin kayan da kallo, gaba daya an cakuda wankakku, gogaggu da masu datti. Idanuna taf da kwalla nayi kofa zan Kai Kara naji an bude kofar toilet an bude, komawa nayi, Adda Meeyna ce hannunta rikeda face towel tana goge wet face dinta.

"Yawwa kwashe kayannan ki fitar dasu, yarinya kamar 'yar daji se shegiyar kazanta"


Tura bakina nayi na juya na tafi gurin Ummaah, Tana kitchen tana kada miyar dare,

"Ummaah kinga Adda Meeyna Gabaki daya ta Watson da kayana waje ko? "


Seda ta kashe Gas din sannan ta kalleni tace

"Ba kazanta kike ba Asma'u? Shekara goma sha biyu ace wanka se nace miki kiyi? Wallahi dama kisani ba NTIC kike so ba? Allah Bazaa kaiki ba, Gwaram zaki tafi, yadda ko sunana kikaji se Kinyi kuka, se seniors sun miki dukan da ko cewa akai kiyi kazanta bazakiyi marmarin hakan ba"


Ai daga jin hakan na Fara kuka ina bata hakuri amma ko kulani Batayi ba ta tafi daki, komawa nayi dakin Inata kuka, na tsugunna na Fara tsitsince kayan, Adda Maryam ce Tazo ta tayani muka gyara kayan, Wanda basuda guga na kaisu inda ake Tara kayan guga. Marasa wankin kuma na kaisu cikin laundry bin, ni Kaina dana kalla wardrobe din seda naji dadi, saboda yyai kyau. Sallah mukai sannan muka zauna ta tsefe min Kaina Dama kitson guda goma ne, ana cikin combing Adda Sa'ada ta shigo, gefenmu ta zauna bayan ta dage curtains sannan ta kura fanka tace


"Wannan se mutum Yayi suffocating saboda warin da Kanki yake"


Ni magana Tana min wahala, amma da ina magana nasan tabbas rashin kunya zanyi, so instead of rashin Kunyar sede na murguda Baki, bakin na murguda daidai shigowar Adda Salma, hannunta tasa ta gwabe min bakina tace

"Zaki sani, sena fasa fitsararren bakin nan naki"


Adda Meeyna dake kwance tayi saurin cewa

"Ku kyaleta Dan Allah, kada taji Kamar an takura mata"


Dage kafada Adda Salma tayi ta kara Ficewa, wata Uwar harara nabi bayanta dashi, ribbon nasa na tufke kan in a bun, inajin Adda Maryam na mitar gashina baida zuciya. Adda Sa'ada ta wanke min shi tas, tayimin drying sannan tayi min kalba Manya, ta saka nayi wanka ai ji nayi kamar an sakeni, wata fresh air tana shigata ta ko ina a Haka bacci ya daukeni.

Duk tunanina zancen zuwa Gwaram wasa Ummaah take, amma bayan sati uku lokacin Zaa shiga sabon session Naga anata shiri, tunda naji Ni Zaa kai nake ta kuka, saboda har ga Allah bana son zuwa. Hatta Abba dake bani goyon baya wannan Karon ban samu ba. The only person that stands for me was Yaya Halifa, shima dalilinshi kada background dina ya lalace amma yadda Ummaah ta dage nasan babu me juyata.

Da daddare naje dakin Abba na gaisheshi, Yana ta tsokanata yar boarding, kiran Inna Ade ya katse mana hirar, katsewa yayi ya kira suka gaisa sannan yace mata gani a kusa. Da murnata na karba sannan na mike na fito waje, cikeda murna na gaisheta, Tana tambayata yadda nake, nan kuma na Fara kuka ina fada mata Ummaah bata sona, ta takura min tace Abba ya kaini Gwaram. Dariya Inna tayi tace kada na damu karshen sati tana hanya.

Ranar asabar kuwa da sassafe se mukaji isowar ta, lokacin Inata bacci ban tashi ba, Maganar ta yasa na fito, gaba daya ta hade gidan da sababi da kuma fada. Gashi Abba da Ummaah basa nan so babu Wanda ya kulata a cikinsu. Tana zaune naje na zauna kusa da ita nace


"Inna kinzo? Sannu ya hanya?"


kaina ta shafa tace


"Lafiya kalau yar albarka"


Mikewa nayi na tafi kitchen na dakko abincin da aka riga aka hada mata na kawo mata, Tana ta saka min albarka, jin dadin hakan yasa duk wannan laziness din nawa naje na bude dakinta na share har da mopping lokacin ta gama cin Abinci, muka koma dakinta ina tayi mata complain akan zaman gidan. Nan kuwa ta hau Tana ta masifa har su Abba suka dawo.

Can Ina kwance Tun kayan Dana tashi daga bacci shi ne a jikina, ko wanka banyi ba, ga zafi da ake a gari, jikina Har stinky yake yana bashi amma ina kwance Kamar sarauniya, su kuma sisters dina suna can suna aiki. Sallamar Inna naji hakan yasa na tashi na zauna ina Mata Murmushi Dan nasan zancen zuwa Gwaram ya rushe. Gefena ta zauna tace

"Kawata, Ashe kazanta kikeyi? Nidai Allah Ya sani ban tashe ki da kazanta ba, Haka zalika bansan Saude da kazanta ba. Dan Haka ni bana goyon bayan rashin gaskiya, Gwaram zakije ta kodan kiyi hankali"


Hannunta na kama ina fadin

"Inna Allah zan dinga yin tsafta, Dan Allah Kice Ummaah tayi hakuri"


Kanta ta girgiza, wannan shi ne karo na farko da Inna ta juyamin baya, shine sanadin tafiyata GGSS Gwaram!

AyshatuuuBayan sati biyu duk wani shiri ya kammalla, I was tired of crying Dan Haka na hakura na zubawa sarautar Allah idanu, Ina ganin ta yadda zaa Fara. Saura kwana biyu na tafi, duk Yan gidanmu suka zo. Adda (Babbar yayarmu) ita ta hada min kayana, kana kallon kayan zai Baka insight din daga gidan Dana fito. Duk fadan da akai min akan tsafta ne, Adda tace min Ummaah tace indai ina tsafta to Zaa canza min makaranta naje dreamy NTIC dina.+

Ranar Monday very early, Adda Sa'ada da Yaya Halifa suka rakani, Garin Yayi min nisa sosae amma its all sightseeing. Tunda muka shiga na Fara kuka, kuma na lura suma duk jikinsu Yayi sanyi. A office din principal muka shiga, Dama ta rigada tasan da zuwanmu, ina shiga na gaisheta suma suka gaisheta, ta zagayo inda nake ta tsaya tareda shafa kaina tace

"Asma'u how are you? "


"I'm fine"  na bata amsa da dasashiyar murya, Dan Murmushi tayi ganin ina kuka, zama mukai bayan tayi mana tayin seat, seda tayi cikecike sannan ta tura aka kira VP academic ta hada ni dashi. Nan sukai mata godiya, Har naje kofa tace


"I wish you a nice stay kinji"


Kaina na gyada kawai, a raina Ina ayyana Wanne nice stay kuma a wannan uban dajin. A lokacin ji nake gaba daya rayuwata an gama tarwatsa min ita. Office din VP academic mukaje ya buden student file sannan ya tura SS3 aka kira masa head Girl, Nidai ina zaune babu uhm babu uhmm uhmm, Haka Tazo ta gaisheshi sannan ta gaida su Yaya Halifa fuskarta a sake.

"Ga Sister na baki, Dan Allah ki kula da ita"


Kai ta gyada tareda nufo inda nake tsaye ta riken hannuna, daga nan mukai sallama bayan su Yaya Halifa Sunyi mata alkhairi sannan aka bata amanata. Tunda naga fitar motarsu nake kuka, tana ta rarrashina ji nayi kamar nayi tsuntsunwa na koma Kano amma babu halin hakan. Haka na bita ta kaini class, gashi makarantar unity school ce, so you got to see different people from different places having different religion, what makes us united is that we're Nigerians. Kamar munafuka haka na shiga ajin na zauna, se surutu ake, amma wannan head girl din na shigowa sukai Shiru. Seda nayi settling sannan ta koma nata class din.  Tunda na zauna ban tashi ba haka kuma bance uffan ba Har aka fita break, kuma Kamar sun hada Baki babu Wanda ya kulani, ina nan zaune duk suka fice se baifi kadan suka rage ba. Durkusar da kaina nayi nayi ta kuka Kamar raina zai fita, na jima a Haka sannan wata Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, ni bansan Wacece Anty Rashida ba but I guess wannan head girl dince. Binta nayi muka tafi, fuskata tayi jawur saboda yadda nayi kuka, ina wucewa anata nuna ni Wai new comer ce.

Ana tashi a class muka tafi zuwa hostel nabi ayari, Dutse hostel aka kaini kwanar Anty Rashida, ruwan wanka tasa aka kaimin nayi, ta gyaran kayana, nayi sallah sannan na bita dining, ana Fara zubawa aka zubamin wata taliya, masifar yunwar da nake ji tasa na daure naci, daga nan se prep na yamma, wannan slow slow din da nake har seda aka tareni ban samu sallar ishai ba, aka zanemu kuwa. Har na kwanta ranar kuka nake.

A hankali kuma na Fara warewa, sede kafin na ware a kalla nafi sati biyu a Haka, amma daga baya se na Fara yiwa mutane magana Kamar yadda Nima naga suna shiga harkata, ko ina na wuce se Anyi maganata saboda kwatakwata I don't match with that environment. Zancen tsafta kuwa, ba koda yaushe muke samun ruwa ba, ni a Haka ma Inada Uwar kwana amma dukda haka se nayi kwana uku banda alwala babu ruwan dake zuba a jikina, tunda ba wani amfani take min ba, se nice ma take amfaniwa dani. ga Rana ga wuya da dealing a makarantar da kuma azabar aike. Kafin wata daya farar fatar da duk gidanmu mu biyu muke da ita ta Fara dafewa, na rame Kamar marar lafiya. Lokuta da dama idan naje class banida aiki idan ba kuka ba, na kasa sabawa da rayuwar. Ga duk yammaci da safe se nayi zazzabi to banida Wanda xan fadawa Dan Haka ni daya nake abuna, idanba wata Rumasa'u ba, to Anty Rashida kawai Wayo takeyi min.

Ana haka ranar visiting tazo, ana gobe visiting Anty Rashida ta tsefen Kaina ta wankemin tayi min Sabin kitso, Washegari tasa nayi wanka Wanda duk nasan na ganin ido ne. Ta dakko min sababbin check Wanda ban taba sawa ba, na saka take kuma se nayi kyau, idanun nan nawa Kamar na mujiya, Dama girma ne dasu to gashi na rame, hancina ya Kara tsawo, idan aka kalleni abinda ake gani kenan.

Muna zaune nida Rumasa'u, class dinmu daya haka dakinmu, so ita ina sakin jiki sosae da ita mun kuma saba.


"Asma'u ban taba ganin dariyarki ba irin ta yau, kodan visiting day ne"


Dariya nayi Ina rufe fuskata data dashe, kamar banida jini, Haka tafukan Hannayena suma duk Sunyi fayau dasu.

"Bazaki gane irin farin cikin da nake ciki ba Rumasa'u"


Kanta ta gyada tace


"Ai naga alama kam, amma..... "


Bata karasa Maganar tata ba, wata yar SS1 Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, babu yadda banyi ba akan Rumasa'u Tazo muje amma taki, haka na hakura na tafi abuna. Tundaga Nesa na hango Ikhram yarinyar Adda, da wani irin gudu na kwasa, su basu ganni ba Dan Haka babu sanarwa na fada jikin Adda Meeyna, gaba daya suka jiyo suna fadin


"Yar boarding, Iyeee! "


Zama nayi gefen Adda Inata Murmushi amma na kasa magana. Duk se naga yanayinsu ya canja gaba daya se bina da kallo suke Kamar irin it's the first time of them seeing me.

"Ummaaah bata zo ba? "


Kafin a bani amsa Sega motar su tayi parking, Yaya Halifa, Ummaah, Abba. Muna hada ido kawai na rufe fuskata Inata kuka, from nowhere naji wata irin karaya ta saukar min. Dukkansu sukai Shiru har nayi me isata na gama, sannann naja Adda Maryam muka Kira Anty Rashida. Ina dawoa na sauka Kan Abinci, duk yadda nake dauki amma haka na kasa cin abincin, su dai basu ce komai ba amma yanayinsu kadai ya nuna min they're not happy da yadda suka Tarar Dani.

Har akai Sallar laasar sannan suka Fara shirin tafiya, Inata daurewa saboda kada nayi breaking, amma seda nayi kuka. Lokacin Abba ya dawo daga office din principal, kallona Yayi yace

"Akwai abinda kike bukata a hostel zaki dakko? "


Cikin rashin fahimta nace

"Abba? "


Kallon Yaya Halifa yayi yace

"Gobe kaje ka samo mata wani admission din, Bazan iya barinta a Haka ba"


Maimakon naji farin cikin da nake tuanin ji, se naji zanyu missing makarantar, gaba daya kayana na tattara na bawa Rumasa'u. Muka tafi gida, shima asibiti muka fara tsayawa Naga Likita sannan muka dawo gida. Ina shiga dakinmu toilet na wuce na dinga wanka Kamar zan cire fatar jikina, na fito na kwanta se bacci peacefully and calm.Washegari ana Fara kiran Sallar farko na tashi, na jima a zaune ina karewa dakin kallo ina kuma godewa Allah, da tuni ina can daji ga sanyin asuba Kamar zai kwashe ka. Kaina na girgiza tareda sakin murmushi na sakko daga gadon na nufi toilet. Nayi alwala sannan na dawo Ina karewa dakin kallo, yadda Adda Salma da Adda Maryam ke baccinsu hankali kwance, a raina na ayyana basu san irin abinda na gani ba, basu san yadda boarding take ba saboda ni daya tal nayi boarding a gidanmu. So I gat the best and weird experience.+

Seda aka Fara iqamah sannan nasa hannuna na tashi Adda Maryam, ni kuma na tada sallah abuna. Kowa a gidanmu yasan ni da kaunar baccin bayan asuba amma tunda aka kaini Gwaram bana tunanin nayi baccin bayan Sallar asuba sau uku, so har na rigada na saba da hakan. Suna idarwa ko magana bamui dasu ba, suka wuce gado suka sake kudunduna, Nikam Shiru nayi a raina Ina jin tamkar an canja ni, I'm not that lazy Asma'u again, I'm a new person.

Kafin bakwai na safe nayi wanka na saka kaya sannan na fito parlor, babu kowa, gidan Shiru kowa baccinsa yake. Se can cleaners dinmu suka zo, kowa ya ganni se Yayi mamakin ganina a gida, sannan Tashin da nayi da wurwuri. Kitchen na tafi dan taya Baba Zulai me yi mana girki aiki. Ina shiga ta juyo da mamaki tace


"Asma'u yaushe kika dawo? "


Dan Murmushi nayi nace

"Jiya, aiki zan tayaki"


Seda ta kalleni for some seconds kafin ta amsa min da to, haka Inata tayata tana koya min abubuwa, Dan babu abinda na iya, idan kaganni a kitchen to aiko ni akayi. Wajen Tara naji mutanen gidan sun Fara fitowa, ban leko ba, ina juya Irish din dake cikin mai. Muryar Ummaah naji tana fadin to ina Asma'u zataje da sassafen nan? Kun duba ko ina kuwa? Dan dariya nayi sannan na saki leak spoon din nace da Baba Zulai, bari naje gurin Ummaah, Dan da alamun ita bataji abinda naji ba.

Ina lekowa naga Sunyi cirkocirko harda Abba, karasa fitowa nayi Ina gaishesu, kowanne mamaki ne a fuskarshi, Abba yace

"Asma'u me kikeyi a kitchen? Kin tsoarata mu, yan uwanki basu ganki ba"


Dan Murmushi nayi nace

"Abba ina taya Baba aiki ne, bansan zaa nemeni ba"


Kanshi Ya gyada yace

"If that's the case, naji dadi "


Daga Haka ya juya zuwa dakinshi, hannuna Ummaah ta kama tace

"Ya kika tashi da wurwuri? Keda bakida lafiya "


"Ummaaah ai na samu sauki, kuma a school Baa komawa bacci, so na rigada na saba"


"At least, yarinya ta gyaru ko Ba komi"


Adda Sa'ada ta fada, kafin muka zazzauna ana ta hira, yawanci su suke abinsu dan ni kawai jinsu nake. Da yammacin ranar Sega Inna tazo, Ashe Abba ne ya kirata, Tana ganina tace Bazan koma ba, Ummaah tace Dama wata makarantar Zaa canja min. Kwananta biyu ta koma Kwalam.

Satina biyu na warware gaba daya, babu wani abinda yake min ciwo, da Adda zata tafi tace zata tafi Dani Ummaah ta hana, a cewarta nema min admission ake. Wannan zaman da nayi kowa seda ya lura da transformation din da aka samu a tattare dani. Dukda ko aikin nake amma bana sauri, zan jima ban gama ba amma zanyi, Haka halitta take banida sauri.

New horizon college dake Minna nan aka samo min admission, wannan karan babu Wanda Yayi protesting haka aka kaini, nida cousin dita Rayhana amma ita tun Farkon term din aka kaita, so se nayi joining dinta.1

Naji dadin zaman makarantar, Dan aljanna ce compared to inda na baro, ga Karatu both western and Islamic, saboda dama Islamic union suka kafata.

Hutuna na farko Daddyn Rayhana ne yazo, munata murna zamu tafi gida, dayazo Ya dauketa ita kadai yace Abbana zai zo ya daukeni, tafiyarsu kuwa ba dadewa Abba da Ummaah sukazo tare, Ashe basa Kano, an tura Abba Delta state wani official assignment na wata daya, shi ne ya taho da Ummaah. Dukkansu sunji dadin ganina da kuma result dina, Haka muka dauki hanya wadda banda bacci babu abinda nakeyi, saboda Daren jiya bamuyi bacci ba, munata hada kayanmu da murnar zuwa gida.

A Mobile Base accommodation din yake, flat gida ne da two bedrooms se parlor, toilet da kuma kitchen. Ni na dauki daya su kuma suna daya. Idan ya tafi aiki se nida Ummaah mu danyi hira, muyi aiki Haka muke zama abinmu.

Satina daya amma zan iya irga sau nawa na leka kofar gida, ranar Ummaah Kamar an saukar mata da bacci, se bacci take, ni kuma na gaji da zama, kallon ya isheni kawai se na fito na zauna kofar gida, time to time Ina ganin wucewar mutane mazauna Base din. Na jima a zaune naji an kwado min ball a Kaina, da sauri na mike ina sosa gurin saboda ta shigeni bugun. Bakina na turo Ina jujjuyawa dan naga wanene. Wasu maza su biyu suka karaso se haki suke dukkansu sanye da jersey, Babban baifi saan Adda Habiba ba se karamin da baifi saan Adda Maryam ba. Suna zuwa karamin yace


" Ina ball din? "


Ya tambaya yana waigawa alamun nemanta yake, harara na wurga mishi tareda dauke ball din na nufi kofa zan shige gida, saboda rainin Wayo ne, by mere looking sunsan sun buga min tunda gashi ina sosa Kaina amma su ta ball din suke.

"Ina zaki Kai mana ball dinne? Bakyaji ne? "


Babban ya fada yana Hararata, wani haushi naji na dauki ball din na wulla mishi, take kuwa ta sauka a kirjinshi nace


"Feel the pain! "


Daga Haka na wuce gida na buga kofar tareda jingina a jiki ina maida numfashi, did I seriously hit him? Na tambayi Kaina, kafadata na girgiza na wuce zuwa kitchen na dakko ruwa nasha sannan na zauna ina maida numfashi. Ban kara fita ba Tundaga ranar saboda Ina ganin Kamar idan na fita to zamu hadu dasu.

"Ummaah Wai Haka zamuyi ta zama, ba zamu fita ba?"


Aje kayan hannunta tayi tace

"kin gaji da zama ne?"


Kaina na gyada nace

"Muje ko cikin gari ne mana"


Kanta ta gyada, daga nan ban kara cewa komai ba na maida hankalina kan kallon da nake, da daddare Abba ya dawo yace zamuje gidan abokinshi a cikin Base din, nafi kowa murna, Dan ni na Fara shiryawa na zauna jiransu, a Mota mukaje, gidan sak irin namu. Tun a kofa nake jin muryar maza sunata hayaniya, hannun Ummaah na rike Har muka shiga ciki, Maza ne guda uku suna game ta Chisel, ga board din a gabansu, saboda ihunsu ko sallamar da mukai I'm not sure idan sunji, wata mata wadda bata Kai Saar Ummaah ba, Ta fito daga dayan bedroom din tana fadin

"Wai Meye Haka duk kun cika gida da ihu, Iyeee! "


Take duka suka shiga taitayinsu, Se lokacin ta hango mu nida Ummaah a tsaye, yadda ta karbe mu fuskarta a sake ta karaso tana fadin

"Ihunsu bai barni naji sallamar ku ba, Dan Allah ku shigo"


A take naji ta birgeni, saboda na yadda da bahaushe da yace shimfudar fuska tafi ta tabarma. Bayanta muka bi, Ummaah ta zauna saman cushion ni kuma na zauna Kan carpet nace

"Anty Ina yini? "


Kanta ta girgiza tace

"Call me Ummiey, ya sunanki? "


"Asma'u" na bata amsa Ina Dan Murmushi, lokacin ne na fuskanci su waye 'ya'yanta, sune Wanda na bugawa ball last week, bata rai nayi Inaji suna gaida Ummaah, Babansu ya fita ya shigo da Abba, nan aka kafa hira Se ni daya a gefe, su kuwa sun cigaba da game dinsu. Abbansu yace su matsa min nayi nima. A dadare na zauna gefen Babban, na tsakiyan shi ne Wanda ban gani ba ranar, Yana gwada min yadda ake chisel, dashi muka buga Ya cinye ni, aka kara yi yayi winning. Aje king din nayi kan board din nace

"Wayo kake min ko? "


Dariya yayi, Juyawa nayi na Kalli Babban yayansu, ya matsa gefe amma idonshi a Kaina. I can say ban taba saurin Sabo da mutane ba irin yadda nayi dasu ba. Matsowa yayi ya dauki king din yasa min a hannuna, dagowa nayi na kalleshi cikin ido shima kallona yake cikin ido and I can swear time stuck, saurin kasa nayi da idona inajin wani discomfort a tare dani, a hankali cikin nutsuwa ya gwada min and take na fahimta, dashi mukayi na cinye dukda nasan he gave me that chance. Kafin lokacin tafiyarmu yayi na ware Duka na saba dasu amma Abu daya na manta shi ne sunayansu, the only name that ring in my head sunan Mamansu UMMIEY!


Bamu Kara komawa wannan gidan ba, kamar Hadin baki suma basu zo gidanmu ba, sede naji Abba yace da Ummaah, Ummiey na gaisheta, su Assignment dinsu ya kare sun tafi, duk se naji babu dadi cikin zuciyata, the least thing I should do is to know their names, amma ta Yaya? Babu wata hanya, dan koda mukaje gidan Banji an ambaci sunan kowa ba a cikknsu.


Muma a Haka hutuna ya kare aka maida ni Minna, nan muka cigaba da Karatu. Duk Hutu xaazo a dauke mu, sannan visiting sau daya ake zuwa mana a term, so har mun rigada mun saba hakan. A Haka naje SS1, Adda Habiba, Adda Meeyna Da Adda Ummiey Sunyi aure, Adda Salma ma tayi aure dukda bata gama university ba amma Ance ta karasa a gidanta.

Gidan Ya rage daga ni se Adda Maryam da Yaya Halifa, Adda Maryam tana Kuwait Tana Karatu, so ko Nazo Hutu sede mu, zauna da Yaya Halifa, muyi Karatu Wanda a gurinshi baya karewa, Har ya samin mugun son karatun, na rigada na saba, hobby dina Karatu ne.

"Rayhana Kinsan na kasa karasa Haddar last page din suratul Nisa'i"


Na fadawa Rayhana, ina rikeda qurani ita kuma tana zura uniform zamu tafi Quran class dinmu.


"Bansan me yasa take baki wahala ba, ki Kara maimaitawa kafin time ya cika"


Idanuna na runtse sannan na bude, na tattara dukkan hankalina akan karatun, seda time Yayi ta gama shiryawa sannan muka tafi, gabana se faduwa yake, dan na tsana embarrassment, Allah Ya taimaka ina shiga akace Anyi mishi rasuwa he can't make it, naji dadi hakan na wuce can extreme din class din nayi ta bita Har ta zauna sannan na dawo gefen Rayhana.

Lokacinda muka shiga final year, ni nayi applying medicine and surgery, ita kuma Rayhana tayi applying Biochemistry, Kaf class dinmu Rayhana batada na biyu a chemistry, ita ce overall best chemistry student a duka set dinmu, bana jin ba zata iya ba.

Munyi graduation gaba daya daga secondary, Yaya Halifa ne yazo ya daukemu daga Minna, Kamar zanyi flying Haka nake ji, ko babu komai nasan at least na taka wani mataki a rayuwata.

Straight daga Minna Kwalam muka wuce saboda akwai bikin cousin dinmu da akeyi kuma Duka family dinmu sun hadu. A cikin gida muka sauka, ko Rayhana ban jira ba nayi ciki abuna, da Adda Meeyna na Fara haduwa hannunta dauke da Aarif, rungumeta nayi itama cikeda murna ta rungumeni sannan na karba Aarif nayi ciki. A dakin Inna na tarar dasu Ummaah, kowa yana tayi mana murna, muka gaisa sannan na shige cikin uwardakin Inna, bata cikin dakin hakan yasa na fada gadon Ina Murmushi tuna yarinta da yadda na rayu a dakin, irin bacin da nayi. Ina kwance idanuna a lumshe naji shigowar ta tana fadin

"Kawata, kina ina? "


Dagowa nayi tareda riko hannunta nace

"Ganinan Kawata, na sameku lafiya? "


"Lafiya lau, ya hanya? "


Fuskata na shafa Dan tun eight muka dakko hanya amma Se Yanzun laasar muka karaso, na gaji sosae.

"A gajiye nake Inna"


Hannuna dake cikin nata ta saki, tace


"Maza sakko kije kiyi wanka, kizo kici abinci. Se Ki huta"


"Fauziyya! Fauziyya!! Fauziyya!!! "


Inna ta kwalla mata kira, Se gata ta shigo da ciki a gaba, cousin dinmu ce sannan yayar Rayhana ce tare akai aurensu da Adda Salma, kuma kusan sa'anni ne Dan dai Adda Fauziyya ta bata watanni biyu.

"Maza jeki Ki hadawa Fara 'yar shehu ruwan wanka"


Nasan halin Inna Ade, so banyi mamaki ba amma Adda Fauziyya da mamaki tace

"Haba Inna Ade, Wanne irin ruwan wanka kuma? "


Kugu Inna Ade ta kama kamar me shirin fada tace

"Ruwan wanka nawa ne? Ki wuce kije kiyi abinda na saki, yarinya ta dawo daga makaranta ko tausayinta bakwaji"


"Inna wallahi ina fama da kaina Bazan hadawa Asma'u ruwa ba, sede kada tayi wankan. Muma ai 'ya'ya ne kuma jikoki, amma sede ki ware bi..... "


Bakinta Inna ta buge tana huci tareda fadin

"Eh lallai, ni Fauziyya ke yadawa magana, to idan bazaki hada ruwan ba, Uwarki ta hada"


Jin hakan yasa nayi saurin cewa

"Inna, ni bana jin wanka Yanzun, bani Abinci naci tukunna"


Allah Ya taimaka se ta fita kawo min Abinci, Itakuma Adda Fauziyya tasa hannunta ta dada min duka a cinya Sannnan ta fice, bakina na turo Ina sosa gurin, se kuma nayi dariya. Inna Ade Tashin hankali, Yanzu fa tsaf zata iya kiran Anty Hauwa ta hada ruwan, Aikuwa da na fadawa aya zakinta.

Ina nan kwance Sega Nu'aimah ta shigo da kwanukan Abinci, a gabana ta aje ta gaida ni sannan tace


"Adda Asma'u, Inna tace Wai ki fada idan kina son wani abu"


Kaina na girgiza nace

"I'm ok da hakan, kirawo min Rayhana muci"


Kanta ta gyada ta fita, kwanukan na bude Abinci Kala uku, kwadon rama da first, ga sachet water me sanyi da Fanta. Rayhana Tazo muka fara ci naji isowar mutanen Adamawa, Umma Falmata da tawagar ta. Babu Wanda ya tashi cikinmu seda muka gama sannan muka je muka gaida ta. Wajen shida muka shirya mukaje gurin kamu.


"A Ina zaki kwana? "


Ummaah ta tambayeni bayan an gama kamun, Adda Sa'ada tace


"Kiji Ummaah da bata Baki Kema kin sani ai"


Dariya nayi nace

"Allah Ya bamu alkhairi "


Daga Haka na koma gidan Inna Ade, parlonta duk Anyi shimfida, da yawa mutane sun Fara kwanciya, tsatsallake su nayi cikin dakin, ina zuwa na tarar Inna na sallah babu kowa kan gadonta, kwabe kayana nayi na canja sannan na kwanta akan gadon, ni nasan ba bacci nakeji ba kawai dai hutawa nake sonyi ga Inna idan ta Fara sallah har Se mutum ya gaji da jiranta. A hankali bacci ya Fara cin karfin idona, ban jima da baccin ba naji muryar Adda Fauziyya tana tashina, tashi nayi na zauna raina ya baci nace


"Adda na Fara bacci fa"


Harara ta tayi tace


"Na sani ai, sakkowa zakiyi ki wuce ki samu wani gurin ki kwanta"


"Saboda?"


Inna ta fada, Ashe ta idar da sallah, Juyawa Adda Fauziyya tayi tace

"Inna wallahi bana iya kwana a kasa dole se a gado, idan ba Haka ba da kyar nake tashi"


Tsaki Inna tayi tace

"Shashanci kenan, ke Kawata koma Ki kwanta, ke kuma Fauziyya kiyi ta tsayuwa amma gadonnan bazaki haushi ba"


Kawai se ta Fara kuka Wai Inna bata sonsu, ni take so to itama jika ce, Kaina na girgiza Dan halayen Adda Fauziyya basida kyau. Komawa nayi na kwanta, zuciyata babu dadin abinda ya faru.


Washegari aka daura aure, wajen laasar na shigo dakin Inata mika saboda gajiya, wata Hamma na buga daidai shigata dakin Inna, cak hammar ta tsaya saboda abinda na gani a gabana, Yaya Mukhtar yana zaune ya baje yana cin Abinci. Dagowa yayi ya kalleni sannan ya saki Murmushi tareda kallon Inna yace


"Inna Fara yar shehu ce haka, Aah yarinya ta girma"


Bata rai nayi na karasa shigowa ciki na zauna saman gado nace

"Kaima ai ka girma"


Dariya yayi yace

"Still with the futsara, Ashe baki canja Hali ba"


Se kuma nayi dariya na gaisheshi, ya tambayeni Ya makaranta, Inata jin dadi nace na gama secondary dina. Se kuma mukai Shiru, na kwanta inajin yana ta cewa Inna yadda na girma, na zama Yan mata.

"Ko dai kana ciki ne Mukhtar? "


Dariya yayi ya mike yana fadin

"Inna kenan! "


Ko kwakkwaran motsi kasa yi nayi, zuciyata ta Fara ayyana Ko dai Yana sona da gaske ne? Se nayi Murmushi saboda wani excitement da naji Ya lullube ni lokaci daya. Yaya Mukhtar sa'an Yaya Halifa ne, shi ne Babban yaron Umma Falmata, so a Adamawa suke shiyasa Haduwa dasu ba sosae ba, musamman shi da bai dade da dawowa daga Estonia ba. Mikewa nayi na zauna dan naji fitar Inna, kallon gurin da ya zauna nayi sannan na sake wani murmushin na canja kaya na Kara fita.Ana gama biki muka koma Kano, Abba yasa Yaya Halifa yayi min registration a gateway computers inda zanyi certificate, saboda kada na zauna bana komai. Babu laifi naji dadin wannan shawarar. Ya zamana morning classes ne, 9am to 12noon, da yamma kuma naje islamiyya, so I'm always kind of busy hakanan.+

Ranar jumaa ina ciwon ciki ko makaranta banje ba, Ummaah ta shigo ta kawo min magani da ruwa nasha, ban wani jima ba bacci yayi gaba dani bani na farka ba se bayan Sallar laasar. Ina tashi nayi wanka na canja kaya sannan na fito parlor. Da mamaki a fuskata ganin Yaya Mukhtar a zaune shi da Yaya Halifa suna hira.

Basu lura dani ba seda na zauna Kan cushion din dake gefen Yaya Halifa sannan yace


"Asma'u rikici"


Dan Murmushi nayi nace

"Yaya Ina wuni? Yaushe kazo? "


Kanshi Ya Dan shafa se Murmushi yake yace

"Lafiya lau, dazun nan"


Kaina na gyada tareda tambayarshi su umma Falmata, sannan Yaya Halifa ya tambayeni saukin jiki.

Da daddare Ummaah tana parlon Abba, Se ni daya a parlor, na kudundune kafafuna, dukkan hankalina yana kan kallon da nake, naji sallamar Yaya Mukhtar, dagowa nayi na kalleshi, murmushin nan nashi Yayi min, nima na mayar mishi inajin yadda Wasu knot ke kulluwa cikin cikina, kasa nayi da kaina har ya zauna gefen kujerar da nake, ya aje mug din hannunshi akan center table din yace


"Me kika kalla haka?"


Kallon allon TV din nayi, Kamar ban San me nake kalla ba nace

"Uhmmmm! Korean drama ne "


Kanshi Ya gyada yace

"I see, amma how do you differentiate between cast din?"


"It's simple " na fada Ina gyara zamana nace " Basu kama fa as long as you continue to watch film dinsu zaka gane each of them"


Kanshi Ya girgiza yace

"I doubt much, saboda komai nasu iri daya ne fa"


Murmushi nayi bance komai ba, saboda idan na biye shi I'll miss some important scenarios. Shima kamar yasan thought din dake running cikin raina bai sake magana ba, Se maida hankalinshi da yayi akan kurbar only God knows what dake cikin mug din. Nima duk se hankalina ya rabu biyu, rabi yana ayyana abinda yazo yi gidanmu, Dan dazun naji Ummaah tana fadawa Baba Zulai zancen zuwanshi, akan a Kara Abinci dashi. Rabin hankalina yana kan kallon da nake.

So ba komai na fahimta ba, har episode din ya kare, Se kawai na mayar Aljazira Dan na Kalli news, wannan yana daya daga cikin horon Yaya Halifa a Kaina. Shirun da mukai se yasa atmosphere din ta zama so dull and tense, gashi ina jin idanunshi a Kaina so se na Fara wasa da fingers dina, at least I want to break the silence. But how? Na tambayi Kaina,


"Ehn... Yaya Mukhtar so Hutu kazo yi kenan?"


Kanshi Ya girgiza yace

"I've been employed ne"


Take faraa ta, ta karu nace

"Oh! Congratulations, amma nayi maka murna "


Wink yayimin, Idan da yasan yadda wink dinnan ya taba ni, bana tunanin zai Kara min, ji nayi kamar zanyi melting cikin kujerar, na fada muku how Charming Yaya Mukhtar yake? Kyanshi kadai will make someone fall for him over and over again. Jinin Fulani Dan Mahaifinshi asalin 0 Adamawa ne, so kana kallonshi kaga hakan.

"So ya makarantar, medicine dinne? "


Kaina na gyada nace

"Shi ne, nayi passing Post UTME kuma score din yayi tallying "


"Mashaaa Allah what a great news, so mun kusa samun Doctor in the family kenan? "


Dan blushing nayi sannan na kalla agogon dake kafe a parlor, idanuna na dan zaro nace


"Bari naje na kwanta, its late"


Hannunshi ya watsar cikin iska yace,

"Oh nima bari naje na kwanta"


Daga Haka na juya zuwa daki amma ban kai ga shiga ba naji yace


"Asma'u! "


Juyawa nayi na kalleshi, Murmushi yayi min sannan Yayi min waving yace


"Sweetest of dreams"


Take naji wani blood rush gaba daya jikina, hannuna nasa na dafe cheeks dina saboda wani Hot da naji Sunyi, ban bashi amsa ba na shige ciki, kofar na mayar na rufe sannan na jingina da ita, ji nake kamar faduwa zanyi, tamkar kafafuna bazasu dauki jikina ba, na jima a tsaye a gurin Inata Murmushi sannan na janye jikina Na fada gado, ranar tsabar farin ciki da annashuwa ko addua banyi ba nayi bacci balle canja kaya. Se wajen past two na farka a gigice, seda nayi yadda na saba sannan bacci ya daukeni.

Washegari kamar yadda na saba, bayan nayi sallah, wanka nayi na Nemo kaya Marasa nauyi saboda yanayin zafi Ya Fara shigowa. Kitchen na wuce na kwaba batter Banana pancake na Yaya Halifa, baifi 4 pieces nayi ba se abincin su Abba da Ummaah, babu wani Yawa abincin amma har Yaya Halifa yazo cin nashi ban gama ba.

"I wonder how you will become a doctor, Dan nasan watarana tabbas kafin Ki yunkura patient zai mutu"


Tura bakina nayi Dan wannan furucin kullum se najishi, sede idan banyi wani abu slow ba. Zama yayi ya ci sannan Yayi min sallama Ya tafi office. Ina kammalla breakfast dinsu Abba nayi parlonshi dashi, fitowarsu kenan, na gaishesu sannan na aje komai na koma kitchen Dan dafa noodles, Ina cikin duba wayata naji kamshin Elope, Wanda nasan mammallakin kamshin nan Yaya Mukhtar ne, se na samu Kaina da kasa Juyawa balle mu hada ido. Kaina na gefe nace


"Yaya Mukhtar an tashi lafiya? "


"Lafiya lau Princess"


Da sauri na kalleshi sede to my utmost amazement Bama kallona yake ba, hankalinshi yana Kan lemun daya shigo dashi, I was kind of disappointed. Amma Se nake ganin Anya ban zake ba, anya am I on the actual and right path? Allah kadai ya sani amma nasan one thing, akwai wani abu da nakeji a gameda Yaya Mukhtar, Wanda a hankali ya Fara gina kanshi cikin zuciyata. Ban taba tunanin ni sokuwa bace Ko kuma nace wawiya Se akan Yaya Mukhtar. Shidai bai taba cewa yana sona ba, sede yadda yake shiga al'amurana is different than any other.

Daga ranar tare muke fita, office dinshi a cikin Depot yake amma Se ya kaini har school sannan ya wuce abinshi. Wannan yasa muka saba sosae dashi, indai muna tare kuma mutane suna tare damu to tabbas se Kasan Inada wani special feelings akanshi.

Ranar da admission list Ya fito, nayi murna Kamar zan zauce,duk wani me sona seda ya tayani murna na samu Medicine , Rayhana ta samo biochemistry dukka a Bayero. A ranar ina kwance a dakina, nida Adda Meeyna Tazo, Sega Luba me mana Shara Tazo tace Nazo Inji Yaya Mukhtar, ko amsata banyi ba na mike zan tafi, wani fizgowa Adda Meeyna tayimin tace


"ke dallah zo, daga ya kiraki ke kuma busy body kin wani tashi, at least take your time mana, kija class dinki. "


Dariya nayi nace

"Kaji Adda Meeyna, is not as if saurayina ne fa"


Dariya itama tayi sosae tace

"Lallai yarinyar nan, wa zaku mayar Yara daga ke har Yaya Mukhtar din, ko makaho ya shafa yasan akwai magana "


Zamana na gyara nace

"Dan Allah sona yake? "


Se tayi sakale tana kallona, sannan tace


"To Dama baiyi proposing ba amma har kike wannan zakewar. Lallai Asma'u, ki maida hankalinki fa. Ba ayiwa maza haka"


Tabe Baki nayi jikina Yayi sanyi, nace

"Nifa kawai mutunci muke dashi babu wani abu"


"Mutunci ba, ni ban taba ganinki kin saki jiki da mutane kamarshi ba, to ki saurareni Dan abinda jikinki da idanunki ke fada you're deeply in love with him, ki zauna kiyi sorting out kafin dare yayi miki. "


Bance komai ba na fita kiran amma Kamar an zare min laka haka naji, duk yadda nake daukin abin se naji Ya fita akaina and I found myself questioning myself me nakeyi? Da gaske sonshi nake? Bansani ba tunda gaba daya na shiga rudani.

Congratulations Asma'u! Nayi matukar farin ciki da jin kin samu admission. Ina fatan zakiyi amfani da damarki, kiyi kokari dan Kinsan irin hard journey dake gabanki, I'm sure Kinsan Medicine ba wasa bane"

Kaina na gyada nace
"Na sani Abba, Inshaaa Allah bazan Baka kunya ba"

Murmushi yayi yace
"Idan kikayi haka zanfi kowa farin ciki, kuma kin taimaki Kanki, saboda duk abinda kika zama may be bana nan balle na Mora, amma nasan nayi miki Gata, inason kisa a ranki Dan Kanki zakiyi Karatu bawai ni zakiyiwa alfarma ba"

Kanshi Ya girgiza yace
"No! Ni na rigada nayi nawa, na riga na taka matsayin dazan taka, Yanzun filin naku ne. Allah Ya bada saa "

Ya fada yana daukar remote, Amin na amsa mishi sannan nayi masa sallama Dan naje na kwanta, Har na kai bakin kofar parlon, naji yace

"Asma'u "

Dawowa nayi tareda zama inda na tashi,
"Ahaf kinga na manta, shiga bedroom dina Ki dakko min wata jaka"

Tashi nayi na shiga ciki, abinka da Ajiyar wani Se ban gani ba, karshe da kanshi yazo Ya dakko Jakar yana tsokanata Wai na Fara tsufa. Nidai Murmushi kawai nakeyi, sabuwar Apple system da sabuwar Samsung ya bani a matsayin gift. Nafi mintina biyar Ina mishi godiya, saboda Ina son surprise yana kayatar dani.
"Se last thing dazan fada miki shi ne Maganar aure, zakiyi aure amma ban yadda ki kawo min wani namiji ba Har Se kin kammalla pre-clinicals dinki, a lokacin I can marry you out in peace. Is that OK? "

Dukda ba haka Naso ba, Dan a lokacin babu wani abu dake birgeni irin naga nayi aure, akwai Wanda muka gama secondary dasu su hudu duk Sunyi aure so I always feel like inama fate dina irin tasu ce. Kuma koda Zaa kashe ni akan dalilin da yasa nake son aure bansani ba, ni dai kawai nayi aure.
Bayan sati uku, na gama registration da komai Se Fara attending lecture, Ummaah tayimin sababbin dunkuna, Yaya Halifa ya siyo min dukkan Wasu stationery da nake bukata, in fact kowa supporting dina yake a gidanmu, kowa seda yayi participating in one way or d other.
Na gama hada noodles Kamar yadda ya zame min jiki, duk dare ita nake ci as dinner, Ummaah Har ta gaji da fada, Har seda tace Yaya Halifa idan yaje shopping din groceries ya daina hadowa da ita, amma haka zan aika a siyo min a shago, Dan Dama bawai inason in dinga cin brand daya, nafi son Yau naci Cherie, gobe indomie jibi Dangote. Different taste you know!
Kan kitchen island din na aje plate din sannan na janyo wata stool na zauna akai na Fara ci, nayi rabi naji isowar Yaya Mukhtar, wani irin race Ya Fara ziyartar jikina, zuciyata tana ta murna jin kamshin turarenshi, idanuna wide open saboda daukin ganinshi, haka kunnuwana sun kagu suji ya furta wani abu. Duk hakan ya faru saboda Yayi sati daya baya gida yaje Adamawa ganin gida, Se yau ya dawo kuma bamu hadu ba, saboda ban wuni a gidan ba naje gurin Adda Maryam acan na yini.
Takunshi a nutse ya shigo, amma bai karaso inda nake ba, Se ya tsaya, dukda son kallonshi da nakeyi Naki daga Kaina amma nasan a tsaye yake kuma kallona yake, I can feel his eyes all over me. Ga kamshin turarenshi dake kokarin zautar dani. Spoon dina na aje tareda tura plate din na mike hannuna na rikeda Hot lime juice.
STORY CONTINUES BELOW

"Asma'u! "

Dagowa nayi a nutse na kalleshi kafin na sake Murmushi nace

"Yaushe ka shigo? Yaushe ka dawo?? "

Gyara tsayuwarshi Yayi yace
"Na amsa daya bayan daya? "

More like a question, hakan yasa na gyada Kaina ina Murmushi Kamar wata sokuwa.
"Dazu da safe Kinje gidan Maryam. Sannan na jima da shigowa amma banyi magana ba"

Kaina na gyada nace
"Ohhhhhh! I see, ya ka baro kowa da kowa? "

"Dukkansu lafiya"

Ya bani amsa a takaice, ko me yayi tunanin kawai se ya fice, so tunanina zai dawo se na koma na zauna, amma nafi mintina goma babu shi babu dalilinshi. Dan Tsaki nayi na fito na tafi daki Inata mita a raina, Raina Ya baci saboda Ina ganin dan me yasa zai fice ba tareda Yayi min sallama ba. Se dana kwanta se naji Kamar anya Inada ounce of hankali a tareda ni? Is not as if Mukhtar yace yana sona ne amma ni me yasa nake wannan abin. Juyi nayi tayi akan gado Inata jin haushin Kaina, tareda tuhumar Kaina akan rashin sanin darajata. Inda kuka ga yadda nayi sorting abin zakuyi tunanin Bazan kara kallonshi ta fuskar so ba amma da safe muna Haduwa wajen gaida Ummaah naji Bazan iya resisting ba, tamkar me zuba min charm a jikina hakan nake ji.
~BUK~

Sabuwar rayuwa kenan dana Fara, level one Dama kowa yasan basics ne, abinda aka koya maka a secondary school ne, though Malaman mu a secondary zasuce, if you go to university, you will go deep. A university ace, this has already been taught during your Olevel no need to go deep. Kunga Kamar kowa yana gudun responsibility dinsa ne.
First week dinmu duk ya kare a introduction ne, seda muka shiga second week sannan na Fara karbar citta, kowanne course Se ka cinyeshi tas babu wani compromise, idan ba Haka ba it's either you change department or you get withdrawn. Shi ne abinda nafi Tsoro a rayuwata, bana son failure bana kaunarta.
"Ummaah hostel zan koma"

Na fada mata lokacinda na dawo da yamma a gajiye, ga Yunwa Dana kwaso.
"Me yasa? "

Kaina na dafe nace

"Ummaah wallahi wahala nake sha, kuma na dawo a gajiye Zaiyi wahala nayi Karatu sosae"

Kanta ta Jinjina tace
"Zanyiwa Abbanki da Halifa magana idan yaso se naji yadda zaayi"

Se naji wani sanyi ya ratsa ni at least gwara ayi hakan. Ban kara sati Ina day ba, gaba daya aka tattara na koma hostel, to hakan se yafi min sauki, ga muna tare da Rayhana se na jini safe.
Wani yammaci ina kwance a daki, babu lecture din yamma so Karatu nayi, na solving Wasu equation na 1301 sannan na dan kwanta na huta, at least kwalkwalwata ta Dan huta daga wannan charge data dauka. Nayi Shiru Ina bin yan dakin da kallo kowacce tana abinda ya dace. Wayata ta Fara ringing, janyota nayi inajin waye zai takura min ne? Amma ganin sunan Yaya Mukhtar na yawo a sama yasa babu shiri na tashi na zauna ina daidaita kaina,
"Assalamu alaikum "

Na fada Ina tabbatar da muryata tayi yadda ya dace, shima amsa ni yayi, se naji tamkar wannan ne Karo na farko dana Fara jin muryar shi
"Ina bakin hostel dinku"

Ya fada yana katse min tunanina, mikewa nayi zaune nace mishi I'll be out In a jiffy. Kashe wayar nayi na janyo wani blue black skirt na zura, Dama akwai long sleeve top Fara a jikina, Se kawai na hijab kato na saka sannan nayi waje. Amma zuciyata se kwabata ta take, Tana tuna min da how reckless nake acting. Sede mafi rinjayen Zuciyar hakan yake so sannan Sauran sashen jikina sun amince da hakan. Kuma kowa yasan idan zuciya na son Abu to Tana acting kafin kwalkwalwa ta ankare, to anawa case din Hakane, Se nayi abu se daga baya inxo Inta jin haushin Kaina.

A waje Kamar yadda ya fada na iskeshi, yana zaune kan motarshi yana danne danne a wayarshi, Yayi kyau sosae, Dayake shi ba ma'abocin saka kananan kaya bane, yafi ga manyan Kaya, Dan kullum a cikin kaftan yake, ko Dan yasan suna mishi kyau ne Oho!
Fuskata dauke da Murmushi na iso inda nake nace
"Yaya, Sannu da zuwa"

Aje wayar yayi ya kalleni sannan yace
"Yawwa, ya lecture din? "

"Alhamdulillah! "

Na fada sannan mukai Shiru, Raina Ina ayyana se yaushe zai ce yana sona ne? Se yaushe, na gaji I can't wait any longer kuma. Muna ta taba hira har Rayhana ta dawo, dakinmu taje anan akace mata na fita, tasan tabbas ina tareda Yaya Mukhtar hakan yasa ta fito. Tundaga Nesa take tafa hannunta har ta karaso tace
"Ikon Allah! Wai ku Meye tsakaninku ne? "

"Me idonki ya gane miki? "

Na fada Ina kauda Kaina amma kafin kalaman su gama sinking cikin kanta ya ce

"Babu komai tsakaninmu, we're just cousins.... "

Bansan nace
"Cousins!?"

Na fada muryata da rauni a ciki, Murmushi yayi tareda dirowa daga saman motar yace

"Zan wuce, akwai sako gurin Ummaah? "

Da kyar na iya girgiza kaina Dan ko amsa balle sallama kasa bashi nayi, na wuce inajin tamkar zuciyata zatayi gobara Haka naji.
"Yaya Mukhtar tsakaninka da Allah me Kakeji akan Asma'u? "

Aje wayarshi yayi a vacant seat din gefenshi sannan ya kalla Rayhana yace

"Kinsan kina damuna Ko? "

Lumshe idonta tayi tace
"Yaya Mukhtar, be serious Dan Allah, kana sonta ko kuwa? "

Kanshi Ya shafa yana Murmushi yace
"Amma Kinsan tambayar nan tanada wahalar amsawa Ko? "

"Ka bani amsa, ina maka magana ba Yaya da kanwa ba, ina maka magana matsayin kawar Asma'u "

Dan Murmushi yayi yace
"I see, I'm flirting with her, shikenan? "

Kasa Matsawa tayi Kawai tana kallonshi sannan tana nazarin abinda ya fada, can tace

"Baka kyauta ba, kuma kusan how reckless wasa da Zuciyar mutum take Kamar kana wasa da ranta ne. Kafi kowa sanin dai Asma'u na sonka, Da har bata iya fahimtar inda kasa a gaba, Dan Haka idan kasan manufarka bata alkhairi bace then allow her and let her be. Kadai tuna Kanada kannai mata! "

Tana gama fadar Haka ta wuce shi a gurin, yayi shiru yana tunanin karfin Hali irin na Rayhana, amma wannan shi ne least abinda zata iya!

....So let me be the one and only, can I be your friend and honey, I'll be your better man.........If you're my girl I'll take you round the world, I'll take you places where you've never ever been before, so give me your...... 🎶3

Wakar da kullum Lubna se ta jita a dakinmu, amma da yake I'm not a fan of Nigerian music, ban taba fuskantar abinda Psquare  ke fada ba se yau, may be hakan yana da nasaba da zafin da zuciyata keyi min, amma jin wakar se naji wani bakon yanayi yana mamaye min jikina, tamkar ana fizgata Ina jin wani tsumammen abu ya karade dukkan zuciyata. That's Love, a hankali na karasa gadona na kwanta Ina kara nutsuwa da bude kunnuwana inajin wakar, har ta kare. Ta kara maida ita, tanayi tana miming dinta cikeda nishadi.
Anty Zubaida itama roommate muke, tana zaune gefen gado tacr

"Nikam Lubna shi wannan Hayaty yaushe zai tura ne? Wannan ban taba ganin irin soyayyar ku ba"

Idanuna na mayar kan Lubna da ke ta Murmushi amma ta kasa magana, I'm sure tuna shi take. Se naji Kamar nayi kuka, ko se yaushe zanji abinda ake ji? Ko se yaushe zaa furta min, a so ni kamar yadda nake so? It might never happen Kila?
Shigowar Rayhana a hargitse yasa na dago ina kallonta, zama tayi gefena tace
"Zo ki rakani"

Mikewa nayi na dauki hijab din dana aje muka fita bayan nayiwa su Anty Zubaida sallama, a kofar hostel muka tsaya, hannunta cikin nawa amma jikinta rawa yake, hakan yasa na dubeta nace
"Me yake damunki, jikinki rawa yake fa? "

Kanta ta girgiza ba tareda ta furta komai ba, amma har lokacin jikinta bai daina rawa ba, gaba daya se naji jikina Yayi sanyi, tunda baifi two hours muka rabu ba, amma bansan me ya kada ta haka ba, it's unlike her saboda ita mutum ce me taurin zuciya, kafin kaga abu ya saka ta cikin Haka zaka dade. Na bude baki da niyyar kara tambayarta se naga motar Abdul saurayinta Yayi parking a gidanmu, hannunta na saki daidai fitowarshi, Ko tsokanar da ya saba min baiyi min ba Illa, bude mata front seat da yayi ta shiga sannan ya bude min yace

"Bismillah"

Kallonshi nayi Amma Se yayi saurin zagayawa Ya koma seat dinshi, baki daya Kaina ya kulle na kasa tunanin abinda yake faruwa. Shiga nayi na zauna, ina jinshi suna magana kasakasa shida Rayhana, bana jin su hakan yasa na rike wayata gyam a hannuna, and na rigada nayi concluding cewar nothing is right, nothing is in place, dole akwai abinda ke faruwa. Jin anyi parking yasa na dago, se ganinmu nayi a kofar gidan mu, cikin sauri na bude kofar saboda yadda naji wani mugun Tsoro ya shige ni, Ashe banga komai ba saboda kofar gidan iya ganinka motoci ne Anyi parking dinsu, ta karamar kofa na shiga seda jiri Ya kusa yar Dani saboda gawa dana gani cikin makara, a ajje. Waye ya rasu? Na tambayi Kaina Sabida Abba da Yaya Halifa na tsaye sede kallonsu kadai ya isa yasa Kasan cewa suna cikin Tashin hankali. Tsayawa nayi na kasa gaba balle nata, se bin mutane nake da kallo kamar yadda ake kallona, mafi yawancin mutanen basu lura Dani ba.
Tattausan hannu naji cikin nawa, hakan yasa nayi saurin dago idanuna, fes cikin na Yaya Suleiman, idanunshi Sunyi jawur, ga jijiyoyin kanshi sun firfito waje, baice min komai ba haka zalika Nima Bance komai ba, se cikin gida, da Adda Salma na Fara Karo, Tana zaune a kofar parlor Tana waya, ba kuka take ba amma kallonta kawai zai saka mutum yaji ya karaya, inda take na nufa da sauri, tamkar duk wani kuzarina ya dawo nace

STORY CONTINUES BELOW

"Adda waye ya rasu? "

Hannuna ta rike tace cikin lallashi
"Kiyi hakuri....."

Hannuna na kwace bansan me ya fusata ni ba, amma a lokacin gani nake idan banyi ihu ba, Adda Salma bazata jini ba, tamkar we're miles apart Haka nake gani, nace

"Ki sakeni! Ki fada min waye ya rasu? "

A hankali naji abu me dumi Wanda babu ko tantama hawaye ne, ya fara zarya akan kumatunshi. Banyi Ko kokarin gogewa ba, se naji an dafa kafadata hakan yasa na juya da sauri, Ummaah ce, Idanunta Sunyi ja, sun cicciko da kwalla tace

"Mukhtar ya rasu! "

Tamkar saukar aradu, haka naji saukar Maganar nan cikin dodon kunnuwana, lokaci daya ganina, jina baki daya suka dauke bansan iya adadin lokacin Dana shafe ba, all I know bayan na nutsu na ganni a dakin Inna Ade, tana zaune da carbi hannunta tana ja, hawaye na diga mata.
"Inna Wai da gaske Yaya Mukhtar ya rasu? Ya tafi gaba daya? "

Bata amsa ni ba, se rungumoni da tayi hakan yasa na saki kuka me ciwo, babu abinda nake maimaitawa Se conversation dinmu da ko awanni uku bamui da rabuwa ba. To me ya sameshi? Ashe rabuwar kenan? Ashe shi kenan mun rabu? Ashe bazan kara ganinshi ba? Kukan da nake se naji is insufficient, wani kululun abu ya tokare min makoshina, sakin Inna nayi na kwanta a dandanyar tiles, may be hakan zaisa na rage jin abinda nake ji amma tamkar ana babbaka wuta cikin zuciyata Haka nake ji, duk yadda Inna taso na daina kuka abin ya gagara.

Bayan mun rabu nida Yaya Mukhtar, kuma bayan sun gama magana da Rayhana se ya tafi, tunda dama yace mata tafiya Zaiyi, yana fita daga cikin campus dinmu Ko kofar famfo bai je ba ya bugi wata Mota dake fitowa daga cikin wani layi. Da yake a karar kwana abin yazo, kafin azo rescuing dinshi Har ya rasu shi kuma Wanda sukai Karon kafarshi ta karye. Shi ne aka kira Abba saboda shi ne last call dinshi kuma akai saa Umma Falmata da Abba Imam sunzo gida, so tare sukaje asibiti aka dakko gawarshi, aka Kira mutanen Kwalam da yan uwan kusa!
Hawaye kam bai Ko tsaya ba, zuciyata ta kasa sukuni, ni nasan baa wasa da mutuwa amma da tabbas zan karyata rasuwar Yaya Mukhtar. Da kyar da sudin goshi aka samu nayi shiri, ko kanneshi da sukeuba daya bazasu nuna min jin rasuwar Mukhtar ba, I can't believe cewar komai ya zama tarihi, his smile, his laughter, his caring. So komai na karshe ne.
Zuciyata bata karye ba seda naga Umma Falmata, se naji wani reason nake dashi na yin kukan rashinshi, abinda ta mallaka kwaya daya tak, ya tafi ya rasu lokacin da ake tsananin bukatarshi, haka rayuwar take.1
🎶Show me the meaning of been lonely, is this the feeling I need to walk with? Tell me why I can't be there where you are? There's something happening in my heart 💖

Washegari se lokacin na hadu da Rayhana, tun safe nayi wanka saboda Inada test din 1301, babu Wanda ya sani ma, amma ni nayiwa Kaina fadan na tafi, dan idan banyi test din ba, nasan nida medicine sede na Tara wata Shekarar. Dakin Ummaah naje na samu Umma Falmata da kishiyarta, tayi kuka marar har ta gaji, Har kasa na tsuggunna na gaisheta sannan na musu gaisuwa saboda a jiya babu wannan halin, Numa tausar nake so, kuma na samu Dan su Adda kusan a Kaina suka kwana Har nayi bacci, Dan kowa har ita Umma Falmata Sunyi tunanin soyayya muke basu San one sided feelings bane.

A kitchen na tarar da Ummaah nayi mata sallama tayi mamakin ganina a Haka amma fuskarta ta nuna jin dadi. Yaya Halifa ne ya kaini nida Rayhana bisa umarnin Abba. Duk wata nutsuwa da nasan Inada ita tattara ta nayi guri daya saboda nasan my future relies on each thing I wrote on that paper, Hakanan nayi sannan muka gama, naje hostel na kwaso abinda ya kamata, ban Tarar da kowa ba kasancewar sun tafi class. Se a bakin hostel ne naga Anty Zubaida, Tana kallona tace

"Asma'u me ya samu fuskarki? "

Tamkar an bude famfo na fashe da kuka, rikeni tayi tace
"Kiyi Shiru Kinji? "

Kaina na gyada sannan na fada mata abinda ya faru, ta jajanta min dukda bata sanshi ba, kuma ni ban sake dasu ba balle suji cikina. Kuma tunaninta muna tareda Rayhana shiyasa bata kirani ba.
A Napep Rayhana ke cemin

"Fara 'yar shehu, kin yafewa Yaya Mukhtar? "

Kallonta nayi sannan nace

"Me Yayi min? "

Hawayenta ta share tace
"Ki yafe masa ko zai samu gafarar Allah saboda niyyarshi akanki Bamai kyau bace. Naji mutuwarshi kasancewata mutum ta karshe da tayi magana dashi. Ina fata zaki lura da darsain da Allah Yayi a rasuwarshi"

Nidai Bance da ita komai ba amma maganarta Se echo take min, niyyarshi bamai kyau bace? How comes? Nidai abinda na sani har zuciyata na yafe masa!Walking down the street of Nothing ville, where our love is young and free, can't believe what an empty place it has to come to be, I'll give my life away, if it only be the same! Cuz I can hear a voice inside of me, that's calling out your name..... 🎶+


Wannan wakar mistakenly naji ta a wayar Yaya Halifa, shikenan na tura ta, se naji tamkar danni da Mukhtar Westlife sukai wannan wakar. Kullum naji ta Se nayi kuka, kuma naki na daina jinta, harseda Lubna ta fadawa Rayhana sannan tayi deleting dinta daga wayata, amma a banza it already stuck in my upstairs!

A Haka na cigaba da rayuwata, dukda tabon rasuwar Mukhtar yana cikin zuciyata, ban kuma ga abinda zaiyi nasarar goge shi ba. Amma Allah yafi kowa sanin me zai faru, me kuma zai kasance, kuma shi daya ya tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance.

Watan shi daya da rasuwa na Fara semester exams, na maida hankalina sosae wajen Karatu, ga kuma nasihar Ummaah da Abba da suke min akan it's now or never, Haka Yaya Halifa kullum mukai waya se yace min, idan na Bari damuwa ta saka na fadi exams na sani na gama da rayuwata, ga Adda Sa'ada sun dawo Kano baki daya, kullum se ta aiko min da Abinci, dukdan nayi Karatu. To idan na tuna hakan se naji Kamar ya tafi karatun kawai nake son nayi.


Sati biyu muka dauka muna Exams, Dama nafi gane Karatu cikin dare hakan yasa ranar da aka gama exams, kamar zan fadi saboda baccin da nakeji, hakan yasa nayi deciding tafiya gidan Adda Sa'ada nasan anan zanyi bacci son raina, Dan Ummaah tace min jikokin duka suna gida, Nikam I can't be that reckless.

Wajen Karfe biyar na yamma na isa gidan, kofar a bude take hakan yasa na tura na shiga, a parking lot na tadda Mijinta Yaya Bilyaminu da wani abokinshi, dukkansu Juyawa sukai suna kallona, gurin na isa na gaishe da bakon sannan na gaida Yaya Bilyaminu.

"Young Doctor, Ya exams"


Hamma nayi, cikin sauri na rufe bakina ina A'uziyya tareda yin murmushin nace


"It's over Alhamdulillah! "


Kanshi Ya gyada, hakan yasa na dan saci kallon abokin nashi, kwatakwata hankalinshi baya kanmu, se naji Banji dadi ba, at least I deserve a second glance, tunda ni mace ce, Fara ce nasan kuma abinda maza suke rubibi kenan, amma ni me yasa bana samun hakan. Se na fita fin a kirga amma ko kallo ban ishi maza ba, na rasa Wanne irin jini gareni. Kuma most mutanen da basu kaini ba, a kyau din, nutsuwa da komai zakusha mamakin yadda ake rubibinsu amma ni ko Oho!

Wucewa nayi ciki saboda idan na kara dadewa akwai matsala. Allah Sarki Addata ta kaina, Ina tunanin na manta ban fada muku Adda Sa'ada ita ce favorite sister dita ba, she's the best I can ever ask for. Tana zaune akan cushion, Idanunta sanye cikin farin medical glasses dinta, ko ban Kalli karamin glass table din dake gabanta ba nasan aiki take, Architecture ce.

Tana jin sallama ta, ta aje HB pencil din dake hannun ta, ta taho inda nake a tsaye, tasan me nake nufi I need a hug. Rungumeni tayi nima Haka tace


"Oyoyo Lil Sis, Ya Exams din? Oh kinga yadda kika kode kuwa? "


Dariya nayi na saketa Ina tattaba kumatuna, nace


"Kai Adda, ina wuni "


"Lafiya "


Ta amsa ni sannan muka wuce dakinta spare din, gado na fada Ina fadin

"Its been a while gaskiya"


Dariya tayi ta shige toilet nasan ruwan wanka take hada min, hakan yasa na tashi na cire kayana, Tana fitowa na shiga, na jima ina wanka kafin na fito, Har Kaina seda na wanke, dukda bawai opinion dina bane, Adda tace na wanke Dan akwai barbushin kazantar in store.

STORY CONTINUES BELOW

Bankai 30 minutes ba na gama shiryawa, wata carbon color gown na saka, irinta na Bubu ne, so babu inda ya kamani, bakin veil na yafa akai har ya sakko kirjina sannan na tsaya gaban dressing mirror ina kallon fuskata wadda ta zama pale tsabar yadda nash wahala kwana biyunnan. Chappette din dake aje kan Vanity Table na goga a tattausan siraran labbana, numfashi naja me karfi inajin wani sanyi a raina saboda kamshin vanilla da ya bugeni.

A parlor na zauna, Har lokacin mijinta bai dawo ba, Abinci naci muna Dan hira jefijefi, Har muka gangaro kan hirar Mukhtar, tace

"Amma Yanzun you're over that ko? "

Dan Murmushi nayi nace

"Adda, Mukhtar bai taba cewa yana sona ba da. Kawai yana nuna min alamar Yana sona"

Glasses dinta ta cire, tamkar cirewar zaisa ta gaskata abinda nace. Kaina na gyada mata irin na tabbatarwa dinnan. Kai ta girgiza tace

"Tab, ban taba tunanin hakan ba, amma ke kina sonshi Ko? "

Dan dariya nayi, se naji ruwa ya Fara tarar min a idona, Kaina na girgiza nace

"Babu amfani Yanzun, tunda ko ina sonshi babu abinda zai canza cewar shi din ya rasu"

Kaina ta shafa tace

"Abinda nake son naji kenan. Ina son kisan, ke din me daraja ce, ke mace ce a priceless and uncut diamond, Wanda ya aureki shi daya yasan worth dinki. Kiyi hakuri da hukuncin Allah, rabonki yana nan zuwa. Dama Mukhtar is just a passerby. Kin gane? "

Kaina na gyada, ina share hawayen da ya Fara zubamin saman fuskata, Bance komai ba amma zuciyata ta nutsu, idan da ace victims Irina Zaa dinga tuna musu Allah yana sane dasu kuma yanada plan ga rayuwarsu, tabbas da basu zama abinda suke Yau ba.

🎶.....When you worry the most, there's no easy way out, when you ready to go and your heart left in doubt, don't give up on your faith. Love comes to those who believe it! And that's the way it's!  🎶1

Karfe takwas tuntuni bacci yayi gaba dani, bani na farka ba seda akai assalatu, nayi sallah Ko azkhar Se a gado na karasa, shima ban tabbatar ba Ko na kai karshe, bacci ya daukeni. Ban tashi ba se goma da rabi, wanka na farayi inajin tamkar wata sabuwar halitta ce Ni din, duk wannan gajiyar ta tafi, se wani karfi da nake ji, fuskata normal wannan paleness din da nake hangowa babu shi. Haka na kara kwana daya sannan na tafi gidan Ummaah . Ashe rabon zanyi tsintuwa ne, tsintuwa Babba kuwa sede a lokacin is insignificant a gurina.

A kofar gate Naga Abba shida wani mutum da ban taba manta fuskarshi ba, suna tsaye se hira suke, kuma alamun sun nuna cewar sun jima basu hadu ba. Da sallama na karasa Inda suke na gaishesu, Abba farin ciki sosae a fuskarshi, Mutumin yace

"Badai Asma'u bace ta girma haka ba? "

Dariya Abba yayi, yayinda na rufe fuskata da hijab din jikina ina Murmushi, naji Abba yace

"Ita ce fa, Yanzun level 2 zata shiga tana Medicine "

"Mashaaa Allah, amma naji dadi sosae. Kasan Abdujjabbar shima medicine Yayi, Yanzun Haka residency yake. "

Kai Abba ya gyada yana ta san barka, wucewa nayi inajin hirar ta koma ta Abdujjabbar da yawa, amma a raina tunani nake cikin su ukun waye Abdujjabbar???

Tunda na tashi Kaina ke ciwo, da kyar na fito zuwa kitchen, na bude emergency kit dinmu na balla Pcm guda biu na kora da ruwan dana taro daga sink din kitchen. Zama nayi kan stool tareda daura kaina kan kitchen island din dan naga Inada Sauran time daya rage na daura abinci. Ina nan kwance naji shigowar Ummaah, ban masan ta shigo ba seda naji hannunta a wuyana, hakan yasa na dubeta da sauri, tace

"Zazzabi kike ai Asma'u, tashi kije daki, kamar dole? "

Dukda azabar da gabban jikina sukeyi, kuma nasan zazzabi ne tun ina daki, but to me rashin lafiya is the worst enemy, na tsani na ganni ina jinya.

"Ummaah ki bari zan iya, kinga idan na kwanta dada rufeni zaiyi"

Kanta ta gyada, kamar ta amince se ta dawo tace

"Kin tabbatar? Nifa hankalina bai kwanta ba "

Faint smile nayi mata nace

"Ummaah ni ce fa"

Kaina ta shafa sannan ta fita, a hankali na Fara aiki amma mainmakon ya ragu se karuwa da yake, hakan yasa na bar abincin halfway, nasa Amal din Adda ta fadawa Ummaah Bazan iya karasawa ba.

Ina zuwa na kudunduna cikin bargo, hakorana Har karkarwa suke saboda sanyin da nake ji. Ummaah data zo seda ta tsorata, can se gata ta dawo da Yaya Suleiman Wanda da alamun zuwanshi kenan, naji dai last week ana cewa zai fara Internship a Nassarawa kuma anan gida zai zauna. Ban wani ji dadi ba.

Ummaah fita tayi ta barmu, se Aleeya yarinyar Adda Sa'ada, bude bargon yayi yace

"I'll feel the temperature? "

Kamar tambaya amma kafin na bashi amsa se hannunsa me taushi naji a dokin wuyana, banida karfi amma dukda haka seda nayi kokarin ture hannunshi. Ficewa Yayi a raina Ina mitar wannan abu. Har bacci ya Fara daukata naji sallamar Adda Sa'ada data Yaya Suleiman. Se naji dadin zuwanta. Bude Kaina nayi Ina mata Sannu da zuwa, hannuna ta kama tana ta yimin Sannu, se lokacin naga syringe hannunshi yana hada allura gaba daya se naji raina Ya baci, kada dai ace allura zaimin? Ban gama tunanin hakan ba naji yace

"Sa'adatu gyara ta nayi mata allura"

"Sule bazaka daina cemin Sa'adatu ba right? "

Dariya yayi yace

"Tit for Tat! Gyarata Dan Allah "

Mutsu mutsu na Fara amma hakan bai hana Adda Sa'ada yaye min doguwar rigar dake jikina ba, Allah yasa akwai under skirt a ciki da naji kunya, da kanshi ya saukar da skirt din da pant dina ya caka. A take naji wata muguwar kunya ta lullubeni, ga haushinshi, ai yana cire Allurar na Fara kuka. A'a Se ya Fara lallashina Har da cewa1

"Sa'ada duk kun bata yarinyar nan, Har kukan allura take. "


Naji haushin furucinshi sosae, se na bata fuska ina share hawayen fuskata. Dariya yayi sannan yace+

"Kawo asaka canula"


Wanne musu zanyi, Dan hannu ai bazai hada fada ba, haka na mika yasa canular, Yayi allurai sannan yasa min infusion. Wani dadi naji a jikina, Tun Ina jin hirarsu Ko ince musunshi shida Adda Sa'ada Har nannauyen bacci yayi gaba dani. Bansan iyakar time din dana dauka Ina bacci ba. Amma nasan se da aka idar da Maghrib sannan na tashi. God so kind ba sallah zanyi ba. Koda na tashi, babu inda yake min ciwo se jikina da babu karfi. Amma haka na daure na sakko daga gadon, Amal na zaune da wayata a hannu Tana game. Kallonta nayi nace

"Amaly!"


Dagowa tayi, tana ganin yanayina ta saki Murmushi, se kuma ta aje wayar tayi waje. Kaina na girgiza na wuce bandaki Dan nayi wanka. Koda na fito yan dubiya sun cika dakin, kowanne na fadin Anty Sannu, ya jiki? Lafiya nayi ta fada sannan nace suje waje na saka kaya, dukkansu suka fice a hakan na samu na shirya Sannnan ya fito. Dakin Ummaah naje suna tareda Adda Sa'ada, dukkansu Sunyi farin cikin ganin na warware. Zama nayi ina cin Abinci munata hira.

Ban jima ba, Ikhram Tazo akan naje Yaya Suleiman yana kirana. Bansan na zunbura Baki ba seda naji dariyar Adda Sa'ada tace


"Meye hakan ke kuwa? Ki wuce kije mana"


Mikewa nayi ina gunguni, Inaji tana bawa Ummaah labarin allura Yayi min shiyasa. Banji abinda Ummaah tace ba nayi gaba abina. A parlor na tadda shi Yara sun baibayeshi. Zama nayi fuskata a murtuke nace


"Gani Yaya Suleiman"


"To ku daga ni, Se da safe Zamui wasan"


Basu Musa ba suka daga shi, daya bayan daya suka wuce dining Dan tun fiwota naji ana fama dasu akan Anyi serving dinner, amma da yake wasa ne a ransu basu lura ba. Bana takura musu saboda duk ranar da suka tafi se naji na zama so empty tamkar Anyi min mutuwa. They're company gaskiya.

"Na zata idan patient ya tashi, Doctor dinsa yake fada nema? See you "


Dauke kaina nayi bance komai ba, saboda bansan abinda zan ce dinba. Kafadarshi yayi shrugging yace

"Ya kikeji Yanzun? "


"Alhamdulillah "


Kanshi Ya gyada sannan ya mukamin Leda yace magunguna ne, godiya nayi mishi na koma dakina.

Bayan sati biyu ko barbushin zazzabi babu kuma na warke tas, babu wani abu dake damuna. Shima kuma baifi sau daya muke Haduwa a rana ba, kullum he's busy a asibiti. Da sassafe ina kitchen Ina daka barkono zan zuba cikin Naman kai, inason Adan saka kadan saboda yadda yake fito da flavor din. Banji sallamar shi ba se ji nayi yace


"Haba early morning kinzo kina daka, bakuda grinder ne? "


Dagowa nayi na kalleshi from head to toe, babu karya jinin Inna Ade ne, zancen bazaiyi kyau ba wannan wasa ne.

"Bamuda ita amma tunda Kaima gidanku ne, idan ka siyo Bakayi shishigi ba"


Na zata zaiji haushi, Se naji yayi dariya sannan yace

"I'll try, zansha coffee "


Yadda ya fadi coffee dinma daban ne, tamkar mace Haka yake da kakale kakale, kallonshi nayi sannan na juya Naman nace


"Bamu shan coffee, amma Munada Tea."


Ban jira abinda zaice ba, na shige store saboda turarenshi gaba daya Ya dameni, bansan zama kusa dashi. Ina fitowa na samu ya zubar min da gyadar Dana Dama baki daya ta malale a Kasan kitchen, kawai tsayawa nayi ina kallonshi raina a jagule.

STORY CONTINUES BELOW

"Biyani Sweetheart, naxo janyo cup ya bare"


Bance komai ba na kashe Gas sannan na dakko cup cikin wani rack dake a rufe, ba lalle ka gani ba in ba kasan gurin ajiyarsu kenan ba. Mika mishi nayi sannan na bashi Tea bag nace


"Komai yana kan dining, don't stress yourself"


Hannunsa Ya hade guri daya yace


"Kumaya"


Se nayi Murmushi hakan ya tabbatar masa na fahimci abinda yace. Da yamma na samu bakuncin Nadia, friend dita ce da mukai New Horizon tare, muna jimawa bamu hadu ba, dukda unguwarmu daya amma dake ita Tana Karatu a wannan Private University dake Yola yasa haduwarmu Se lokaci zuwa lokaci.

Lokacinda ta shigo Ina daki, Yaya Suleiman kuma yana parlour shida Yara, so seda suka gaisa sannan ya nuna mata dakina Wanda ta rigada ta sanshi tuntuni. Ina ninke kaya naji sallamar ta, rigarda ke hannuna na wullar Inata Murmushi na nufi inda take tsaye Tana kare min kallo.

"Oh Nadia, Oyoyo..... Is this a surprise? "


Hararata tayi tace


"Kinfi kowa dadin baki idan aka zo gurinki, amma Kira a waya ya gagara, and you always brag of I been your friend ko? "


Rufe bakina nayi ina Dan dariya kasakasa, idan da Sabo na saba da korafin Nadia, tanada zumunci Ina tunanin ba dan ita ba inaga da tuni we're separated tuntuni amma ta rike abin.

Janyota ciki nayi na ture himilin kayan dake gefen gado nace


"Zauna mana, se magana kike"


Kanta ta gyada tace

"Bari na gaida Ummaah se na dawo"


Hannunta na kama nace

"Ummaah sunje Abuja zasuyi visa zuwa Hungary"


Kanta ta gyada tace

"Dan Allah su sani a jaka"


Dariya nayi sannan na fice na dakko mata juice da cake da fish pie. Na kawo mata, tanaci munata hira, Dan banida kamar ta, ko islamiyya ma class dinmu daya. A mutanen dana zauna dasu Wanda bamu hada komai dasu ba, tafi kowa tolerating halayena.


"Ya ake ciki, kuma karkice min babu wani motsi "


Langwabar da kaina nayi irin abin tausayi dinnan nace


"Nads karya kike so nayi miki? wallahi har Yanzun Ina nan as single as me zance miki? "


Dariya tayi sosae sannan tace

"Kiga yadda kike kwabe fuska Kamar wata marainiya"


Daidaita fuskata nayi nace

"To Ya zanyi, I'm lonely I need a partner"


Numfashi taja me karfi tace

"Dama loneliness dole ne, tunda shekaru sun kai, amma Kinsan me? Lokaci ne fa, kuma har kyayi karatunki a nutse babu takura. "


Kaina na gyada nace

"An Kai kudin Rayhana da Abdul "


Wani ihu Nadia ta buga tace

"Shegu ce Rayhana, Kice an kusa? "


Dariya nayi nace

"Ke Kina ganin idan Baa saka ranar nan bazasu samu matsala ba. Ya jira da yawa ai, tun muna Js2 fa"


Daga nan muka wuce kitchen Dan ta tayani mu hada dinner, a parlor har lokacin Yaya Suleiman na zaune, kallo yake cikin system dinshi, yana jin fitowar mu ya dago muka hada ido, dauke kaina nayi inajin Nadia suna Kara gaisawa, ni kuwa ko ta kanshi banbi ba na wuce kitchen, seda ta shigo sannan tace


"Ke wannan handsome din fa? "


Tabe Baki nayi nace

"Handsome kam, Dan Anty Shamsiyya ne kanwar Abba. Internship yake a Nasarawa. "


Kanta ta gyada tace

"Yayi miki laifi ne? Naga Kamar kuna fada "


Kaina na girgiza Ina kokarin kuna gas nace


"Ko daya wallahi, in fact he's nice. Kawai dai bana son mu saba dashi yazo Ya mutu"


"Mutu kuma? Haba ke kuwa, kowa ai se lokacin shi Yayi, Mukhtar da ya rasu lokacin shi ne. To ya zaayi? "


Na amince da abinda tace amma haka kurum nake jin bana son sabawa dashi, a rayuwata na tsani rabuwa da mutane, I'm selfish nafi son idan na samu Abu to ya zama nawa, kada abinnan ya tafi, to a wannan rayuwar ta Yaya, ai bazai yiwu ba.

Nadia bata bar gidanmu ba se wajen Karfe Tara na dare akaxo aka dauke ta tafi, Se naji inama ta zauna dan naji dadin yinin ranar. Ban bar parlon ba se wajen twelve, muna ta kallo nida Yaya Halifa, can kuma Yaya Suleiman yayi joining dinmu, anan na sake dashi for the first time Tun zuwanshi gidanmu.Hutuna Ya Kare na koma school, big lady na zama yar level 200, tunda naje registering courses dina Naga babu su basics dinnan da nayi a level 1 na Fara jin wani shaukin dadi. Community based medical education, physiology, Anatomy, pharmacology and many da zaisa naji yeah I'm a medical student. Koda muka koma, first week ne kadai nayi day amma second week na tattara kayana na koma hostel, Dan na lura the higher we go, the hotter it becomes.

Ranar Friday na fito daga lecture din Biochemistry, wayata a hannu na, sauri nake Zanje hostel na dakko jakata saboda na wuce gida kafin a shiga sallah. wayata ringing tayi, na dakko na duba, Yaya Suleiman ne,

"Ajhumma! "


Ya fada Ina picking, dariya nayi nace

"Ajhussi! "


Se muka kara kwashewa dariya, sannan yace

"Nazo wucewa ta school dinku nace bari na dakko Sweetheart"


Cikin jin dadi nace

"Kai Yaya Suleiman, naji dadi, ka jirani kofar hostel dinmu, jakata kawai Zan dakko"


"At your service Ma'am "


Ko bana kusa nasan saluting dina Yayi, nayi Murmushi na katse wayar. Na tuna ranar da ya Fara cemin Ajhumma, naji haushi sosae, saboda ni nasan I'm not Ajhumma. Ina school ranar ya kirani da daddare lokacin mundan Fara sakewa da juna, yace min Ajhumma, I was like Kasan me kake fada kuwa, se yayi ta dariya, so ni kuma se nace mishi Ajhussi. Shikenan mukai naming kanmu, dake gaba dayanmu die hard fans din Korean dramas ne. Munada abubuwa sosae that are related ni dashi. I can even say, hakan ya karawa relationship dinmu karfi.

Wani sanyi naji cikin raina, I'm sure kowacce mace ta samu Yaya Suleiman tabbas ta gama morewa, halayenshi sunada kyau, kuma kowa zaiji dadin zama dashi. Books dina na dauka sannan na fito kafadata sabe da handbag dita na wuce dakin su Rayhana. Tana kwance da waya a kunnenta, na tabbatar Maganar daya ce, Abdul ne.

"Ke Baki jiya da waya ne, kullum ace kuna Abu daya. Haba Dan Allah! "


Na fada bayan na tsaya a kanta, Allah su Rayhana are irritating, kauda wayar tayi daga kunnenta tace min


"Duk ranar da kika Fara soyayya, soyayya da right man dinki, se kin fini sannan zaki gane abinda nake ji. So ya ake ciki? "


Harara na wurga mata tareda sakin Tsaki nace


"Zan tafi, kin fasa zuwan? "


Maida wayar tayi kunnenta, tayi mishi sallama, sannan tace


"Oh Asma'u, Karatu zanyi kije kawai. "


Kaina na gyada na wuce, har naje kofar fita a dakinsu naji ta kwalla min kira, Juyawa nayi nace


"Sauri nake fa"


"Haushi kika ji ne?"


Kaina na girgiza nace

"Ke Wanne haushi, nasan bawai Karatu zakiyi ba, Abdul ne kawai zaizo. Allah yasa nanda 2 weeks kina gidanshi ma huta muma. Amma...."


Tsaki nayi na fice, na rasa wannan jarababbiyar soyayyar tsakanin Abdul da Rayhana, kamar mayu kullum suna waya, abin haushi yake bani, kuma bansan me yasa nake jin hakan ba. Yaya Suleiman na zaune a drivers seat, ya kurawa kofar hostel ido, da dukkan alamu jirana yake yi. Straight inda yake na nufa, fuskata se Murmushi ne akanta, kamar bakina zai yage, is this what I've been missing, dama Haka akeji a soyayyar?

"Yaya kayi ta jirana Ko? Sorry "


Murmushi yayi yace

"Anything for Princess, nasan an tsaya yin girls stuff ne ko? "


STORY CONTINUES BELOW

Murmushi na kuma saki nace


"Kamar ka sani, muje Ko?"


Kanshi Ya gyada tareda yiwa motar key muka dauki hanya, seda muka fita wajen mun hau titi yake tambayata Baiga Rayhana ba, nace Rayhana ta zauna yin ayyuka. Kanshi Ya gyada dan naga shi da ita ba wani good time suke ba, unlike itada Yaya Mukhtar marigayi. A gida muna shiga nasan Yau Inada Babbar Bakuwa, Inna Ade, tamkar yadda na saba haka na shiga a guje Tana parlor tayi daidai, gabanta an cikashi da abubuwa, Abinci ne nama ne and stuffs. Rungumeta nayi nace


"Kawata! Sannu da zuwa"


Itama bakinta ta bude Wanda hakora suka Fara Ficewa sannan ga yadda goro ya rinar dasu. Tace


"Kawata, Karatu ya boye min ke"


Dariya nayi Ina gyara zamana nace

"Ya zanyi kawaliyya? Nasan Kema zakiji dadi ace kawarki Likita ce ko? "


Kanta ta gyada Tana kare min kallo tace


"Wannan haka yake amma se naga kin yi rama, Ina fata babu matsala"


Kaina na girgiza Ina tauna Apple din dana dauka akan table din gabanta nace

"Ko daya, kawai Karatu ne. "


Kanta ta gyada tace

"Allah Ya bada saa, kije kiyi wanka. "


Tura bakina nayi nace


"Kai Inna, wari nakeyi? "


Harara ta tayi tace Hali Zanen dutse. Nayi dariya sannan na tafi na Kai kaina wajen Ummaah, tunda na ganta, naji jikina Yayi sanyi, saboda yanayunta kawai ya nuna min babu lafiya. Zama nayi nace


"Ummaah, Menene? "


Murmushi tayi Wanda ko makoshi bai kai ba, balle ace daga zuciya yake. Tace


"Babu komai, kin dawo? Ya Naga baku taho da Rayhanar ba? "


Kaina na girgiza nace

"Zatayi aiki shiyasa"


Daga Haka na mike na tafi dakina. Inna kwananta biyu amma ni bansan dalilin zuwanta ba Dan babu Wanda ya fada min, sede ni din ba yarinya bace, nasan definitely akwai abinda ke faruwa, amma tunda kowa boyewa yake, Meye nawa na bincike. Se naji Dama ban dawo ba, saboda yanayinsu duka ba cikin jin dadi suke ba.

Ranar Monday mukai sallama da Inna Ade, Dan zata wuce Kwalam, Haka nima zan wuce school. Na tafi abuna. Wajen Karfe biyar na yamma Adda Sa'ada ta kirani akan gata ta shigo cikin school dinmu, Nazo wani eatery mu hadu. Haka na Mike da duk Gajiyata na tafi, ita tayi mana order chilled Fanta, Danni inason Fanta babu ruwana da kakale kakale. Yadda ta tsira min idanu yasa gaba daya na kasa sakewa balle na sha lemun.

"Asma'u kisha mana"


Langwabar da kaina nayi nace

"Adda nasan dole wani abu ya kawoku, Ki fada min Bazan iya sha ba. "


Hannuna ta kama tace

"Ki saurareni da kyau kinji"


Ban bata amsa ba na gyada Kaina, se ta cigaba da fadin


"Kinada saurayi? "


OK, to me tambayar Tazo min a bazata, Abu ne daban yi expecting ba, amma ya zanyi dole na bada amsa. Kaina na girgiza nace

"A'a Adda, wani abu ne? "


Kanta ta gyada tace

"Suleiman fa? "


Shiru nayi bansan yadda zan Fara mata bayani ba, nida Suleiman babu Wanda yace yana son wani amma kuma dukkanmu muna son junanmu, balle ni ai kada wani yaji labari, ina sonshi sosae, son abinda ban taba yiwa wani abu ba. Kuma duk yadda muka zauna da mutum Ko awa ne se ya fahimci shakuwar mu nida shi.

"Kinyi Shiru Asma'u "


Kaina na girgiza nace

"Adda, baice yana sona ba amma.... "


"Amma me? Mistake din da kikayi akan Mukhtar shi kike son kara maimaitawa. Me yake damunki ne Wai? "


Tura bakina nayi nace


"Kai Adda, yana sona ne fa, kawai nasan zai fada idan time Yayi "


Idanunta ta kafeni dasu sannan tace


"Bakida hankali dama Har Yanzun? Wa yace miki ana haka. Ki daina kulashi kina jina ko"


Juyar da kaina nayi bansan yadda zanyi ba, ta Yaya Adda zatace na rabu da only source of happiness dina, kaina na girgiza Se kuma tace


"Kinsan Inna tazo weekend dinnan. Baki San me ya kawota ba right?"


Kaina na girgiza, gabana yana faduwa nace

"Me ya kawota? "


"Zancen aurenki!"


Da mamaki sosae nace


"Ni? Aurena? Haba dai "


Dariya tayi tace

"Saboda Sajida, Nabila da Rayhana dukka sa'anninki ne kuma zasuyi aure, shi ne tazo ta bawa Ummaah da Abba notice. Idan Kinada wani saurayi Ki turashi yayi gaisuwa idan yaso ayi Maganar daga baya. "


Raina a mugun bace nace


"Lallai! Nifa banda saurayi banda Yaya Suleiman sede idan shi zan tura"


Duka ta kaimin Tana fadin

"Dallah rufe min bakinki a gurin, Suleiman ai yafi kowa sanin halin da ake ciki, idan da yana sonki kinsan da tuni yayi magana. Abinda nakeso dake Kiyiwa Allah ki daina grumping fuskarki, ko a samu mashinshini"


Nidai Bance komai ba, Raina Ya baci sosae amma ko daya hankalina bai tashi ba, saboda nasa a raina, aure da mutuwa lokaci ne.

Related Posts

Related Posts

Post a Comment