Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BANSAN LAIFINA BA CHAPTER B

BANSAN LAIFINA BA CHAPTER B

- - Post a Comment

 BANSAN LAIFINA BA CHAPTER B KARSHE

Ajiyar zuciya yayi yace "Kin gama? To bara kiji in gaya miki baki cikin tsarin matan da nake son aura, to koma kina cikin su ai kinyi min girma in baki girme ni ba to saura kad'an ki kamo ni, kina muzgunawa Fateemah amma kice kina so na so ki Lallai ma baki da hankali ai duk mai sona to yaso Fateemah in ba haka ba babu ni babu shi, kinje kin wani zanbad'o turare ke a tunanin ki zaki ja hankali na da turare ne? Baki San na tsani macen da zata saka turare mai k'arfi kuma ta fita dashi ba, ko da yake baki San illar hakan ba shiyasa, ki rubuta ki ajjiye bazan tab'a son ki ba har Abada Fateemah kad'ai nake so kuma ita Zan cigaba da so har k'arshe rayuwa ta, zaki iya tafiya" ya fad'a yana d'auke kai daga kanta.+


A guje ta shiga gida tana kuka kamar ranta zai fita.


Tab'e baki yayi ya juyo da kallon sa ga Fateemah da ta sunkuyar da kai tana sauraran duk abinda suke cewa, murmushi yayi yace "Beauty na ya akayi ne naga kin sunkuyar da kai kamar mai laifi?".


D'ago kai tayi tace " Babu komai kawai ji nayi Aunty Shukra ta bani Tausayi."


Kai da zancen yayi da cewa "Yanzu i'zufinkin nawa a hadda.?"


Jinginar da kanta  tayi jikin kujera tace "Izu na talatin da biyar yanzu."


Zaro ido yayi yace "cikin shekara biyu har kin kai haka, Lallai a gaishe ki my wife."


"Ur wife" ta maimaita tana kallon sa, murmushi yayi yace "my k'anwa ina sonki sosai."


Murmushi tayi tace "Nima ina sonka Yaya na, bara na koma gida zanyi Assignment."


"Okie hakan yayi kyau maza ayi Assignment da kyau kar a tsaya wasa."


Dariya tayi tace "insha Allah Yaya na, wai Yaya na mai kake karanta ne?".


" Ina karanta medical doctor yanzu haka huta nazo nan da wasu kwanaki zan koma".


B'ata fuska tayi tace "yanzu in ka koma bazan kuma ganin ka bako" ta fad'a idon ta ya ciki da k'wallah.


"Haba dai ai in kinga kin daina ganina to mutuwa nayi in ba haka ba banga abinda zai saka ki daina ganin ba, sai dai in na koma makaranta zaki jima baki ganni ba Gaskiya."


Shiru tayi tana tunanin, ganin hakan yasa yace "kinga jeki kiyi Assignment d'in kar anjima ki kasa yi."


Ta amsa da to suka yi sallama ta shiga gida.


Shukra kuwa tana shiga gida kamar mahaukaciya ta shiga d'akin ta ta kullo k'ofa ta fara watsi da kayan wajan ta fad'in "Wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan a kanta yau akayi min wulak'anci, duk hanyar da zanbi Dan ganin na Kore ta Wallahi sai nayi zan iya kashe ta akan sa, bazan iya jurewa ba dole na kashe ta in yaso kowa ma ya huta".


Zama tayi a bakin gado tana faman huci kamar zakanya, zuciyar ta sai d'arsa Mata munanan Abu take.


Da daddare bayan kowa ya kwanta Fateemah tana kwance a kan kujerar parlour tun ana kallo bacci ya d'auke ta har kowa ya tashi ya barta a wajen Dan baccin nata yayi nisa sosai.


STORY CONTINUES BELOW

Cikin sand'a Shukra ta fito parlourn ta tsaya a kan Fateemah tana wuci, bata tsaya yanke hukunci ba kawai ta d'aga rigar ta ta d'auko wata zabgegiyar wuk'a, d'aga wuk'ar da niyar caka mata Fateemah ta farka suka yi ido biyu da ita tana niyar kashe ta.


Saurin mik'ewa Fateemah tayi tana ja da baya tace " Aunty Shukra me kike yi da wuk'a yanzu?."


"Kashe ki zanyi" ta bata amsa tana binta inda tayi.


Zaro ido tayi tace "Aunty Shukra me nayi miki zaki kashe ni? Dan Allah kiyi Hak'uri ki barni da raina inaso na nemo inda Momy na take bana so na mutu ban k'ara ganin ta ba" ta fad'a tana hawaye.


"Baki isa ba wallahi akan ki saurayin nan ya ci mun mutunci duk da tsananin son da nake masa, a kansa zan iya kashe kowa ciki harda ke."


Cikin kuka tace "Dan Allah Kiyi Hak'uri karki kashe ni Dan.........." K'ara ta saki sakamakon yankar ta da tayi a hannu.


Dai-dai lokacin Momy ta fito zata d'auki ruwa taji ihun Fateemah tayo wajan da gudu har tuntub'e take.


Jini ne yake fita daga hannun Fateemah inda Shukra idon ta rufe ta d'aga wuk'a zata caka mata a ciki Momy tayi saurin rik'e hannun ta tana fad'in "Ke lafiya kike? Shukra meye haka kina da hankali kuwa, me kike yine kashe y'ar mutane kike son yi?".


A rud'e Momy take maganar tana rik'e hannun ta, saukar mari taje a fuskar ta tayi saurin juyowa tana kallon Dady da ransa yayi bala'in b'aci.


Cikin kuka take cewa " Babu Wanda zai hana yau na kashe Wannan anbobar, zaman ta ba alkairi bane a gidan nan, Momy Wanda nake mutuk'ar so akan ta ya wulak'antani yaci mun mutunci ya tozar dani, yace min ita kad'ai yake so gwara na kashe ta nasan babu ita a duniya yadda nima na rasa itama ta rasa."


Rik'e ta Momy tayi cikin tsawa tace "ke Shukra ki dawo cikin hankalin ki in ba haka ba zanyi mugun sab'a miki, akan wani zaki kashe Fateemah Dan baki da hankali."


Wajan Fateemah Dady ya nufa sai kuka take hannun ta rik'e da d'aya hannun banda zubar jini babu abinda hannun yake, rik'e Mata hannun yayi suka fita daga parlourn.


Zama Shukra tayi tana fad'in "Wallahi saina kashe ta ko ba yau ba saina hallaka ta".


Mari Momy ta bata a fuska kafin ta dawo dai-dai ta k'ara kifa mata mari tana fad'in " in zaki dawo hankalin ki ki dawo hankalin ki malama, kina tunanin in kika kashe ta kema barin ki za'a yi? Dole kema ki bita Allah yasa bake kad'ai muka Haifa ba balle abin ya dame mu, banza wacce bata da tunani."


Ajiyar zuciya kawai Shukra take tana had'e rai, yarda wuk'ar tayi ta shiga d'aki da gudu ta kulle kanta.


Dady kuwa Chemist suka wuce aka Wanke wajan da ta yake ta aka d'aure sannan aka yi mata allurar TT suka tawo gida.


Momy na zaune a parlour suka shigo ta mik'e da sauri tana kallon Fateemah, cikin rawar murya Fateemah tace "Dan Allah Momy ki bawa Aunty Shukra Hak'uri karta kashe ni inaso na k'ara ganin Momy na kafin na mutu ".


Rungume ta Momy tayi tana share hawaye zuciya ta cike da tausayin Fateemah.


D'akin Momyn suka shiga Momy ta kwantar da ita tana shafa kanta har bacci yayi gaba da ita.


Kallon Dady Momy tayi dake zaune akan bed side tace "ya kake ganin lamarin Shukra anya aljanu basu tab'a ta ba?".


Tsaki Dady yayi yace " babu wasu aljanu iskanci ne kawai da tsabar tsanar da sukewa Fateemah ita da Suhail ya jawo haka, amma Allah ya kaimu gobe Zan San yadda zanyi Ku kwanta tare da Fateemah Dan ta tsorata sosai."


Momy ta amsa da to sannan ya juya ya fita daga d'akin.


Washe gari Fateemah ta tashi da wani ciwon ka da zazzab'i mai zafin gaske, banda rawar sanyi babu abinda take.


Kiran Dr akayi yayi mata allura sannan bacci ya d'auke ta.


Kiran Shukra Dady yayi ya kalle ta yace "Shukra a ina kika koyi kisa ban sani ba? A ina kika koyo rashin imani da tausayi, yanzu kina y'ar k'aramar ki dake har kinsan ki d'auki wuk'a kiyi k'ok'arin kashe wacce take kamar k'anwa a wajan ki? Zama da k'awaye banza ya kawo hakan kenan ko kuma a makaranta kika koyo Dan dai wannan ba tarbiyar zuri'ar mu bace gabad'aya."


Banda share hawaye babu abinda Shukra take amma har lokacin bata yi Dana sanin abinda ta aikata ba, tace "Dan Allah Dady kuyi Hak'uri sharrin zuciya ne ya ja ni na aikata hakan kuyi Hak'uri bazan sake ba."


"Kima sake mana na Riga na gama yanke hukunci, babu ke babu zuwa makaranta na farko kenan, na biyu babu ke babu rik'e waya, na uku babu ke babu fita daga gidan nan sai dai in da wani, na hud'u cikin samarin ki ki Fitar da d'aya a d'aura muku aure in kuma kika 'ki zan aura miki Wanda naga dama, tashi ki bani waje."


Mik'ewa tayi ta shiga d'aki zuciyar ta sai k'ara zuga ta take akan Fateemah.


Kallon Dady Momy tayi tace "Gaskiya Wannan hukuncin da ka yanke yayi mata tsauri ya kamata a sassauta mata, ko babu komai mu muka haife ta bai kamata muyi mata haka ba."


Dady yace "na Riga na gama yanke hukunci."


Cikin fad'a-fad'a Momy tace "haba Dan Allah wannan hukuncin yayi tsauri nifa mahaifiyar tace bawai Dan bana sonta yasa nake mata haka ba inayi ne kawai Dan ina tausayin Fateemah amma bawai Dan nafi son Fateemah ba, Dan haka baza a fifita bare akan y'ata ba Wallahi" tana gama fad'ar hakan ta mik'e ta shiga d'akin ta.murmushi Dady yayi yace "y'a da uwa sai Allah in badan haka ba yarinyar da tayi yunk'urin kisa ai abinda yafi haka ma ayi mata."+


Da yamma kamar kullum Yayan Fateemah ya iso cikin gidan a parking space d'in gidan ya tsaya aka kira masa ita.


Tun daga yadda ta fito yasan bata da lafiya, bai bari ta k'araso ba ya fito daga motar a rud'e ya k'arasa wajan ta ya rik'e yana fad'in "Beauty na lafiya meya same ki?."


Kuka ta fashe dashi tare da fad'in " Aunty Shukra ce jiya da daddare ta d'auko wuk'a tace Sai ta kashe ni."


"What!!! Kina nufin ita taji miki Wannan ciwon?".


Tace " Eh itace amma Dady yayi mata fad'a sosai."


"Fad'an banza fad'an hofi wallahi bazan bar Wannan ba sai yarinyar nan tayi prison zan nuna mata koni waye a garin nan, nan gaba baza ta sake ko gangancin tab'a ki balle tace zata kashe ki" cikin b'acin rai yake maganar idon ya ya koma red colour.


Zaro ido Fateemah tayi tace "Dan Allah Yaya kayi Hak'uri bana so ka kaita prison sabida badan su Momy ba da yanzu ban San a duniyar da nake na Dan Allah inaso taci darajar su."


Cike da mamaki yake kallon ta shi tun wayo Fateemah da hankalin ta na bashi mamaki har ya koma bashi shawa'a yarinyar y'ar k'ara sai babban tunani.


Baice komai ba yaja hannun ta suka k'arasa mota ya kalle ta yace "to wai akan wane dalili tace zata kashe ki?".


"Wai sabida kace baka sonta ni kake so shiyasa zata kashe in yaso kowa ya huta."


Zai yi magana kenan ya hango fitowar ta da alama wajan su zata k'araso.


Haka kuwa akayi tana zuwa wajan ta kalle shi tace "Dady ya sanar dani akan na Fitar da miji ni kuma kai nake so Dan hakan zan sanar dashi."


Maimakon ya kalle ta sai ya kalli Fateemah yace "Beauty na anya wannan banzar Yayar taki bata da tab'in hankali?" Da sauri Fateemah ta d'ago ta shi, gira d'aya ya d'aga Mata yace,


"Yes mana to in ba mahaukaciya ba waye zai zo waje babu sallama ya fara zuba kamar ruwan sama, in ba sha-sha-sha ba wace zata zo wajan namijin da yace ba yayi baya so tazo tana yi masa maganar aure, in ba banza wace zata yi yuk'urin kashewa min k'anwa kuma sannan tazo tana fad'a min wai ni take so Dan kwakwalwar ta toshe da dusa" juyowa yayi ya kalli Shukra ya cigaba da fad'in,


"Bana son ki kuma bazan tab'a sonki ba har abada, Fateemah itace burin raina itace Matata Dan haka zaki iya d'ibar k'azaman k'afafuwan ki ki bar min nan kuma in kin cika mai sona in kin cika y'ar halak daga yau ki manta dani a rayuwar ki" yana gama fad'ar hakan ya rife motar sa yaja suka fita shiga Fateemah .


STORY CONTINUES BELOW

Ko motsin kirki kasawa tayi a wajan dak'yar taja k'afar ta ta shiga ciki.


Tunda ya bar gidan ya had'e rai sai faman mita yake shi kad'ai yana zazzaga bala'i, itadai Fateemah shiru tayi Dan tsoro ya bata bata tab'a ganin ran sa ya b'aci irin haka ba.


Bai wuce ko ina ba sai zoo road suka shiga sahad store, siyayya yayi mata sosai kamar baya son kud'in, bayan sun gama suka dawo mota suka d'au hanyar gida.


Kallan sa Fateemah tayi tace "Yaya nah kayi Hak'uri naga ranka ya b'aci sosai."


Sakin fuska yayi yace "Beauty na ina sonki sosai" ya fad'a yana rik'e hannun ta.


Ganin ya saki fuska yasa itama tayi murmushi suka cigaba da hirar su.


A k'ofar gidan yayi parking ya kalle ta yace "Beauty na gobe jirgin asuba zan hau zan koma England in cigaba da karatu, amma duk daran dad'ewa zan dawo gare ki ki rubuta ki ajjiye."


Hawaye ne ya fara zarya a idon ta tun tana kukan a hankali har ya fara fita, dafe kai yayi cikin tsananin tashin hankali yace "Dan Allah beauty ki daina kuka na fad'a miki zan dawo badan karatu na babu abinda zaisa na tafi na barki kiyi shiru bana son ganin hawayen ki ko kad'an."


Share hawayen tayi tace "Yanzu shikenan in ka tafi bani da Wanda zamu dinga hira, Yaya na Wallahi bana son ka tafi wani Abu nake ji yana min yawo a jikin Dan Allah kar ka tafi ka barni Dan Allah" ta fad'a tana rungume shi tare da fashewa da kuka mai tsanani.


Rasa yadda zaiyi yayi kawai sai ya lumshe ido yana shafa bayan ta yana jin kamar ya tafi da ita, da ace ba tare zasu tafi da Mamy da Umma ba da d'auke ta zaiyi kawai su koma Abuja, amma ina zai kai Fateemah? Shine tunanin da yake.


Katse masa tunani tayi da fad'in "Yanzu in ka tafi yaushe zaka dawo?".


D'ago kai yayi ya d'ago ta daga jikin ya rik'e fuskar ta yace " Ni kaina ban San time d'in da zan dawo ba sabida Abba yace bazan kuma dawowa hutu ba har sai nayi masters d'ina, amma zan San yadda zanyi na dawo kodan nazo na tafi dake, beauty na kar ki dinga kula samari ko ba yanzu ba bana so kiyi min Wannan alfarmar."


Ajiyar zuciya tayi tace "Kayi min alk'awari zaka dawo ko?".


Murmushi yayi shima yace " I promise u zan dawo."


Dariya tayi tace "To nima nayi maka alk'awari bazan dinga kula kowa ba ko y'an school d'in mune."


Hannu ya bata ta suka tafa ya saka hannu a aljihu ya d'auko wani ring mai kyaun gaske ya kamo hannun ta na dama ya zura mata ya kalle ta yace "Beauty duk tsanani duk wuya kar ki rabu da Wannan zoben koda kin k'ara girma bud'e shi kawai zakiyi zai miki dai-dai, ina sonki beauty insha Allah saina aure ki."


Ita kuwa da taji ya ambaci aure sai taji wani iri duk da da bata komai a ranta tunda tana da karancin shekaru, murmushi tayi tare da shafa zoben tace "Yaya na yayi kyau sosai Nagode sosai."


Zaiyi magana kenan wayar sa tayi k'ara dubawa yayi bai d'aga ba ya juyo ya kalle ta yace "to beauty suna yi min waya Wanda zamu tafi dasu nasan jirana suke, ki rik'e min alk'awari da kika d'auka."


Jikin ta ne yayi sanyi ta fashe da kuka ta fita daga motar a guje tayi cikin gida, share idon sa yayi shima sannan ya bawa mai gadin gidan yace ya shigar mata da kayan ya shiga mota ya bar k'ofar gidan zuciyar sa kamar ta fito tsabar dukan da take yi.


Ita kuwa Fateemah tana zuwa ta fad'a jikin Momy ta fashe da kuka mai tsuma jiki, cikin tashin hankali Momy tace daughter Lafiya me ya faru?".


Cikin kuka take cewa "Momy Yaya nah, Yaya nah" ta k'ara fashewa da kuka.


"Meye ya same shi? Yana ina Yanzu?" Momy ta fad'a a rud'e.


"Momy gobe zai koma England makaranta shikenan Yanzu bazan kuma ganin sa ba".


Ajiyar zuciya Momy tayi Dan ita har ga Allah ta zata wani mummunan Abu ne ya same shi, shafa kanta ta dinga yi tana bata Hak'uri.


Mai gadi ne ya shigo da kaya ya bawa Momy ya juya ya fita.


Tun tana kukan har bacci ya d'auke ta.

Bayan kwana uku.


Babu ranar da zata fito ta koma Fateemah bata yi zancen Yayan ta ba, tun tana bawa mutane dariya har ta koma basu tausayi daman haka sabo yake akwai dad'i rabuwa kuma babu dad'i.

Tana zaune a d'aki tana kallon zoben da ya bata, k'ara kallon zoben tayi a fili tace "daman wai da rubuta a jikin zoben nan, gashi an saka F&F kenan shima Yaya na sunan sa daga F ya fara".


Haka ta dinga surutun ta har lokacin islamiyya yayi ta tafi.


⚡⚡⚡⚡


"Merry kin kika sake kika zubar da cikin jikin ki saina sake ki" Daniel ya fad'a yana huci.


Tsaki tayi cikin masifa itama tace "I swear to God sai na zubar dashi haka kawai Dan in ya ta taso cikin bak'in ciki kamar yadda Eleina ta taso impossible."


Cike da takaici ya kalle ta yace "ni kike fad'awa Wannan maganar? Koda yake ba laifin ki bane laifi nane da kika zuga ni na kori Matata kuma kika b'atar min da daughter, to bara kiji in har kika zubar da cikin nan police ne zai rabu dake."


Yana gama fad'a mata haka ya shige d'aki, d'akin Sisiliya ya shiga yana k'arewa d'akin kallon zuciyar sa cike da kewar Eleina dan har Yanzu bai fara nadamar rabuwar sa da Sisiliya sosai ba.


Hoton Eleina ya d'auka ya rungume a k'irjinsa yana fad'in "ina kika shige ne daughter? Baki San nayi missing dinki sosai ba, a ina zan ganki, oh god Jesus help me to find my daughter, two years kenan barona Dana ganki I really love u my daughter."


Haka ya dinga magana shi kad'ai har ya gaji ya mik'e ya fita.


Merry kuwa jin ya ambaci police yasa duk ta tsora Dan a duniya ta tsani had'uwar ta dasu, cikin fargaba tace "Gwara na bar cikin in ba haka ba ya kaini wajan su kashe ni zasu yi."


Cikin sanyin jiki ta ja k'afar ta ta shiga parlour.


*BAYAN SHEKARU GOMA.*

Kyakykyawar budurwa ce ajin farko zaune a harabar makarantar B.U.K tana kallon zoben dake hannun ta tana goge hawaye.
+
"Fateemah wai yaushe zaki daina Wannan tunanin ne? Na fad'a miki addu'a zaki dinga yi in yana raye Allah ya baiyana shi in kuma baya Raye Allah ya jik'an sa amma Wannan tunanin babu inda zai kaiki Wallahi" wata budurwa kamar ta ta fad'a tana zama a kusa da ita.
Kyawawan idanuwan ta ta d'ago ta kalli k'awar tata cikin muryar ta mai dad'in sauraro tace "Lubna kar ki manta tun ina yarinya Allah ya dasa min k'aunar wannan bawan nasa yanzu shekara goma kenan rabon Dana ganshi kinga ai dole na shiga damuwa, in kinji yadda k'irjina yake bugawa a duk lokacin Dana tuna shi Wallahi sai kin tausaya min."
Dafa ta Lubna tayi cikin tausayawa tace "ki cigaba da Hak'uri Bestie in Allah ya yarda zaku had'u, amma fa zanso naga ranar da zaku had'u dashi wai waya ga washa."

Dariya Fateemah tayi tace "baki San wani abu bama kin san ba lallai na gane kammanin sa ba sabida lokacin da tsaho sosai."
Dariya Lubna tayi tace "To ai kema ba lallai ya gane ki ba sabida kamannin ki sunyi bala'in canjawa, in mutum ya sanki kina yarinya in ya Dad'e bai ganki ba ba lallai ya gane ki ba sabida kin canja gabad'aya."
Murmushi tayi har wushiryar ta ta baiyana tace "Allah dai ya kaimu lokacin da zamu had'u, kinga tashi mu tafi yau banzo da mota ba" ta fad'a tana mik'ewa.
Lubna tayi dariya tace "kinga sai mu taka a k'asa har gaban alpen store kinga kya rage Wannan hips din naki da yake baki haushi."
Tsaki Fateemah tayi tace "Aida tafiyar k'asa na sawa hips ya ragu da tuni na zama babu komai nifa da badan Momy ba da tuni na sha maganin rage hips wallahi, babu abinda yafi b'ata min rai dashi sai kowa kiga siket d'insa d'an k'arami amma nawa kamar za'a saka duniya" ta fad'a tana shagwab'e fuska.
Dariya sosai Lubna tayi tace "wallahi Fateemah har yanzu yarinya ke damun ki wallahi, muje yamma tana dad'a yi " jerawa suka yi suna tafiya har suka fito daga makarantar.
A bakin Alpen Lubna taja ta tsaya tace "ke wallahi na gaji mu hau mota mu tafi."
Tsaki Fateemah tayi tace "Ke wallahi raguwa ce y'ar Wannan tafiyar kikewa haki? Ya kamata ma ki dinga yin wacce ta fita sabida ki rage Wannan lipid d'in da yayi miki yawa".

"Ke ni wallahi bazan cigaba da tafiya ba mota zamu hau yawon Dana ke a makaranta bai ishe ni ba ke kanki shaida ce" ta fad'a tana tsaida adaidaita sahu.
STORY CONTINUES BELOW

Kwatance tayi masa suka hau suka tafi.

⚡⚡⚡⚡
"Wai Fa'iz tunanin me kake yi ne tun d'azu ina yi maka magana kayi shiru kamar baka jini ba."
Ajiyar zuciya Yayi yace "Amir bani da burin da ya wuce na koma Nigeria naje Kano wajan Beauty na nayi kewar ta Sosai."
Tab'e baki Amir yayi yace "Ahaf ai na sani daman kai kullum baka da magana sai ta waccan yarinyar, anya kuwa Fa'iz ba gano kayi ba? Tunda muka dawo k'asar baka da sukuni yau shekara goma kenan Allah yasa ma ta gane ka in kaje kai bama wannan ba Allah yasa ma bata yi Aure ba kazo kana wahalar da kanka kila ma yanzu ci....."
Cakumar wuyan sa da yayi ya hana shi k'arasa abinda yayi niyar fad'a, zaro ido Amir yayi ganin yadda kamannin Abokin nasa suka canja lokaci d'aya.
Cikin d'aga murya Fa'iz yace "Fateemah ka kira da aljana? Kuma ka kalli cikin idona kace wai Fateemah tayi aure a gidan uwar ka tayi auran? Amir in kana son kanka da zaman lafiya karka k'ara bud'e baki ka zagi Fateemah in ba haka ba zan iya yi maka duk abinda zuciya ta ta fad'a min, ka shiga hankalin ka" hankad'a shi yayi ya juya ya fita daga d'akin kamar iska.

Shafa wuya Amir yayi yace "Wai haka Wannan d'an fulanin yake da k'arfi? Tab da tuni na bak'unci lahira yau, bara na bishi naga ina yayi" da gudu ya mik'e ya bi bayan sa.

Fa'iz kuwa direct wani tafkeken parlour ya shiga yana wuci kamar zaki, Abban sa ya kalli Mamy dake zaune kusa dashi alamun meya sami d'an nata .

Umma tace "Wai lafiya kake kuwa ka shigo mana parlour ko sallama babu?".
Wata y'ar yarinya da baza ta wuce shekara Tara ba ta taso tazo wajan sa tace " Yaya na meya same ka?".
Amir ne ya shigo parlourn yana dariya kamar mahaukaci, Abba ya kalle shi yace "yau Amir meya sami d'an uwan naka ne?".

Nan Amir ya kwashe komai ya fad'awa musu.
Murmushi Mamy tayi tace " kayi Hak'uri kaji son insha Allah ka kusa Mallakar Fateemah kar ka damu."
Sai a lokacin yayi murmushi yace "Ameen Mamy na Allah ya amsa bakin ki."
Kauda kai Umma tayi ta mik'e ta shige d'aki.
Yana ganin ta shiga d'aki ya dawo kusa da Mamy yana murmushi yace "Ai Wallahi Mamy muna komawa daman ni jirgin Kano zan hau bazan je Abuja ba sai naje ka gano ta hankali na ya kwanta."
Dariya Abba yayi yace "kaikam Fa'iz baka da kunya a gabana kake fad'ar wannan maganar? Kana gani Yanzu Dan dole kasa Umman ka ta tashi."
"Ai Abba ko banyi Wannan zancen ba ina zuwa waje Umma zata mik'e ta shiga d'aki ko kunyar me take ji oho."

Abba yace "Ai kasan Fulani basa iya sakewa da d'an fari shiyasa, idan ka koma ka gano yarinyar sai kamar bayan sati biyu sai muje nida Abban Amir muyi magana da iyayen ta amma fa in nayi bincike na samu yarinya da wani bad behavior ko iyayen ta ta ka sani babu kai babu ita."
Cikin rashin damuwa yace "na amince Abba Allah ya kaimu lokacin."
"Little sister ya naga kin wani b'ata rai?".
Cikin shagwab'a yarinyar tace " to ba kai bane tun d'azu ina yi maka magana kayi min banza."
"Sorry kinji my k'anwa ban jiki bane, zo ki zauna ki bani labari."

Murmushi Mamy tayi tare da lumshe ido tana tunanin da ita kad'ai ta sanshi.

*WANENE FA'IZ?*.

STORY CONTINUES BELOW

Alhaji Usman Adamu shine mahaifin Fa'iz haifaffun garin Abuja ne tun Abuja na k'auye suke zaune a cikin ta har ta zama abinda ta zama Yanzu, Alhaji Usman su biyu ne rak a wajan iyayen su daga Yayan sa Alhaji Nuhu wato mahaifin Amir sai Abba, Allah ya bawa iyayen su haihuwa amma ana haihuwar yaran ko kwana goma basa yi suke komawa, lokacin da aka haifi Alhaji Nuhu mahaifiyar su wato Baba Ladi Sam bata sa ran zai rayu ba haka ma lokacin da ta haifi mahaifin Fa'iz.

Allah ya bawa familyn mu kyau kamar jinin labarawa haka suke ko wanne a cikin su kamar ka tab'a jini ya fito haka suke.
Alhaji Nuhu yana da mata guda biyu y'ay'a hud'u babban shine Amir sai k'anin sa Abdullah sai Haleema da Jamila.
Hajiya Hindu wato Umma Cikakkiyar bafulatana ce itace uwar gidan Alhaji Usman, d'an su d'aya da ita wato Fa'iz tun daga kansa basu kuma samun wata haihuwar ba tun suna sa rai har suka daina .

Lokacin da Abba ya gano Mamy a garin Abuja koda yazowa Umma da maganar bata yi musu ba ta amince tare da bashi koyan baya duk dai cikin zuciyar ta tana jin zafin hakan amma bata nuna ba, koda aka auro Mamy zaman lafiya suke yi Sosai da Mamy Sam bata da hayaniya, shekarar ta biyu a gida ta haifi y'ar ta mace mai suna Amina .
Alhaji Usman yana da kud'i kud'i irin Wanda ake kira kud'i, Allah ya bashi arzuki fiye da tunanin masu karatu, yana da taimako sosai Dan kaf garin Abuja babu Wanda bai San shi ba indai wajan taimako ne duk shekara sai ya kai mutane saudiya fiye da mutum d'ari, ga kyau da Fitar da hakk'in Allah akan lokaci shiyasa kullum Allah yake dad'a bud'a masa.

Alhaji Usman yana mutuk'ar k'aunar Fa'iz duk abinda yake so yana bashi ko kad'an baya son ganin b'acin ran sa amma duk da haka bai bar tarbiyar ta lalace ba.
Ta b'angaren kakanni ma babu irin son da basa nunawa Fa'iz especially ma Hajiya Ladi da Baba Adamu, duk abinda yake so shi suke masa, tunda aka haifi Amina soyayya dawo kanta babu Wanda baya nuna mata k'auna, Umma kuwa ji take kamar ita ta haifi Amina kullum tana wajan ta.
Wannan dalili yasa Fa'iz ya taso cikin gata da farin ciki, Abu d'aya ne baya samu shine soyayyar mahaifiya sabida kunya Umma watan banda gaisuwa babu abinda yake had'a da Fa'iz, shigowar Mamy rayuwar su yasa ya sake Sosai Dan Mamy taja shi a jiki kamar itace mahaifiyar sa duk dai ya girma lokacin da aka auro ta.
Suna zaune tare dashi a England sai dai su suzo su gaida dangi su koma dan Abba yace Fa'iz bazai koma ba har sai ya gama master d'insa.
WANNAN KENAN.

⚡⚡⚡⚡

Tun daga k'ofar gidan Fateemah tasa yau anyi manyan bak'i a gidan, shiga cikin gidan tayi ta tarar da Momy tana d'aukar ruwa a fridge.
"Momy yau bak'i akayi a gidan ne haka?".
Murmushi Momy tayi tace " inafa bak'i yayan Ku Suhail ne ya dawo yanzu nan ya bar nan ya tafi part d'in sa."

Gaban Fateemah ya fad'i amma sai bata nuna tayi murmushi tace "lallai yau muna da manyan bak'i kice mutanen America ne."
"Lallai kam maza kije ki Ku gaisa dashi in kin huta."
"Toh Momy bara nayi wanka sai naje."
Cikin fad'uwar gaba ta shiga d'akin ta dan tana ji a jikin ta dawowar Suhail ba alkairi bane a rayuwar ta.

*COMMENTS & SHARE.*

*© NEAT LADY.*
[3/4, 22:36] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa ce._❤

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 13πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Suhail kuwa suna zaune a part d'insa shida Shukra suna hira , Suhail yace "Wai ke Shukra baza kiyi aure bane kome?".
Yatsine fuska tayi tace " Ina so nayi amma Wanda na baka labarin har yanzu bai dawo ba."
"Mtsw kefa baki da hankali wallahi ta Yaya zaki d'auki son wani ki d'ora a ranki bayan kuma yace miki baya sonki? Malama in zaki nutsu ki nutsu kinga girma yanzu kuma mazan yanzu basu cika son Mace mai manyan shekaru ba, kisan abinyi tun huri."
Had'e rai tayi tana turo baki, kallan ta yayi yace "ke ni ba Wannan bama ina mayyar gidan nan ne? Tunda na dawo ban ganta ba."
"Tana makaranta kasan yanzu Bsc Nursing take yi a BUK tana can amma kila ta dawo yanzu."
Murmushi yayi yace "yanzu ne dai-dai time d'in da zamuyi maganin shegiya, d'akin ta daban ko?".
" Eh d'akin ta ita kad'ai ne yanzu, mai za'a yi mata?".
"Yauwa haka nake so daga gobe zamu fara aiwatar da komai, matso kiji abinda zamuyi mata."
Matsowa tayi suka fara magana k'asa-k'asa.

Bayan awa d'aya.
Fateemah ta fito daga part d'in Momy ta nufi part d'in Suhail gaban ta na fad'uwa, a hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga cikin sallama.
D'ago kai yayi Dan ganin wacece Wannan, kanta a sunkuye ta durk'usa tace "Yaya Suhail sannu da dawowa, ya hanya?".
Samun kansa yayi da zuba mata ido ya kasa magana yana kallon fuskar ta, jin shiru yasa Fateemah ta fara k'ok'arin mik'ewa Dan tasan halin sa a lallai ya amsa ba.

"Lafiya lau yakike?".

Kamar daga sama taji ya amsa cikin sauri ta d'ago taga kodai bata ita yake ba, tana d'ago wa suka had'a ido yana sakar mata murmushi.

Saurin sunkuyar da Kai tayi ganin yana yi mata wani irin kallo mai cike da abubuwa masu yawa.
A hankali ta mik'e  har ta kai bakin k'ofa taji yace " banfa gane ki ba gashi zaki fita baki fad'a min wace ba."
A hankali ta juyo tace "Fateemah ce k'anwar ka" tana gama fad'ar hakan ta juya ta fita da sauri.
Cike da mamaki yabi bayan ta da kallo, tsaki yayi yace "wai daman Wannan banzar yarinyar ce ta koma haka? Daman haka take da kyau kamar aljana?" Saurin kawar da zancen yayi yana tsaki.
Washe gari da huri Fateemah tayiwa Momy sallama ta hau motar ta ta nufi makaranta.
Suhail kuwa duk yadda yaso ya kawar da tunanin Fateemah a ransa kasawa yayi, ko Yaya ya rife ido ita yake gani lokacin data juyo zata bashi amsa, mik'ewa yayi daga kwanciyar da tayi yace "wai meyasa na kasa daina tunanin Wannan yarinyar? Mtsw ko meye da ita ma oho" cike da takaici ya shiga toilet.

Har ya fito daga wanka tsaki yake, yana gama shiryawa ya fito main parlour ya zauna.
Bayan sun gaisa dasu Dady sunci abinci Dady ya kalle su yace "Suhail Alhamdulilah ka gama karatun ka lafiya daga kai har Shukra, to yanzu Abu na gaba shine aure musamman ma ke Shukra na gaji da Wannan shashancin naki Dan haka na baki nan da sati biyu ko ki fito da miji ko na zab'a miki Wanda naga dama, kai kuma Suhail kayi k'ok'ari ka nemo mata in ba haka kaima zan had'a ka da wacce naga dama."
STORY CONTINUES BELOW

Shiru suka yi babu Wanda yace wani abu, Momy tace "Amma naji dad'in Wannan maganar wallahi Allah ya kaimu lokacin."
Suka amsa da ameen suka cigaba da hirar su, mik'ewa Momy tayi ta shiga d'aki.
Suna zaune ta fito cikin tashin hankali tana fad'in "Shukra kin d'auki sark'a ne?".
Zaro ido Shukra tayi tace " me zanyi da ita? Wallahi ban d'aukar miki ba."
"Yanzu fa na ajjiye ta akan drower kuma yanzu na shiga naga ban ganta ba."
Dady yace "kuma kin duba ko ina ko ta fad'a wani gurin?".
" Babu inda ban duba wallahi, babu wani y'ar aikin da ta shigar min d'aki Dan Fateemah ce ma ta gyara min d'aki tunda ta fito kuma ban shiga d'akin ba."
Dady yace "to ki bari ta dawo ko ta b'oye miki."
Ajiyar zuciya tayi tace "kuma fa haka ne, har naji dad'i wallahi Dan duk cikin gwalagwalai na tafi su tsada."
Da yamma suna zaune kamar yadda suka saba Fateemah ta shigo bakin ta d'auke da sallama.

"Momy sannu da gida na dawo."
Momy tayi murmushi tace "sannu daughter ya lectures?".
" Alhamdulilah Momy ta yau kam tayi dad'i."
Kallan Suhail tayi tace "Sannu da aiki" tana gama fad'ar hakan tayi hanyar shiga d'aki.
Bayan tayi wanka ta shirya ta fito taci abinci, Momy ta kalle ta tace "yauwa daughter d'azu da kika shiga d'aki na baki ga sark'ar gold d'ina ba akan drower?".
"Na ganta amma ban canja mata waje ba anan na barta."

Cike da mamaki Momy tace "A'a to ai ni ban ganta ba, kodai kin manta kin b'oye ta?".
" Wallahi Momy ban d'auke taba anan na barta".
Shukra ce ta fito daga d'akin Shukra tana fad'in "Momy daman Fateemah tana da irin sark'ar da kike nema?".

D'ago kai Momy tayi tace " ban gane ba me kike nufi?".
Yatsine fuska tayi tace "Na shiga d'akin ta ina neman wani littafi na Dana ajjiye jiya shine naga sark'ar a cikin bedsite d'inta, na zata ma ke kika bata wallahi."
Cikin tashin hankali Fateemah tace "haba Yaya Shukra ki k'ara dubawa kila baki kula ba, wallahi Momy Dan d'aukar miki sark'a ba."
"Kinji ko Momy ta tona kanta to daman wayace ki kika d'auka? Gashi nan ta fad'a da bakin ta" Shukra ta fad'a tana zama akan kujera.
Momy kallon Shukra tayi tace "ke bana son iskanci ki fad'a min Gaskiya".
"Wallahi Momy na ganta da cikin bedside d'inta, d'azun ma naga time d'in data fito da ita a rigar ta ta b'oye sabida bata so a gani dalilin da yasa ban fad'a miki ba sabida nasan baza ki yarda ba, amma ai ita tasan tayi."
Cikin fushi Momy tace "muje ki nuna min" tare suka mik'e suka shiga d'akin Fateemah.
Suhail yana zaune amma baice kala ba sai danna wayar sa sa yake yi.

Bud'e drower tayi tace "kin ganta Wallahi naga lokacin data fito da ita, daman naji jiya tana waya wai tana so ta siyi iPhone 11pro tunda kinga yanzu ba pro bace a hannun ta wai baza ta iya rok'ar ki ba amma tasan abinda zata yi shine ta d'aukar miki sark'a kenan."
Cike da b'acin rai Momy ta juyo ta kalli Fateemah da ta shigo d'akin tana kuka kafin tayi magana Momy ta d'auke ta da mari, kafin ta d'ago ta k'ara kifa mata wani baya tayi ta fad'i kanta ya bugu da bango.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin kuka tace "Wallahi tallahi Momy ban d'aukar miki gold ba Wallahi ban d'auka ba."
"To ya akayi tazo d'akin ki?" Momy ta fad'a cikin fushi.

"Wallahi Momy ban sani ba amma Wallahi bani na d'auka ba."
"To uban kine ya d'auka?".

Hannu tasa ta toshe bakin ta tana kuka Sosai.
Muryar Dady suka ji daga bakin k'ofa yana fad'in "Ya isa haka ki karb'i sark'ar ki ki koma d'aki".
Cikin fushi Momy ta fice daga d'akin tana kwafa.
Dady kallan Fateemah yayi yace " daina kuka daughter kinji nasan baza ki aikata hakan ba sai dai in had'a miki akayi."
Kallan-kallo aka fara tsakanin Shukra da Suhail, wani kifta mata ido yayi ita kuma tayi murmushi Wanda ba lallai mutum ya gane murmushi tayi ba, juyawa Suhail yayi suka fita daga d'akin Shukra ma tabi bayan sa.

Dady yace "ki ki bar wannan kukan na fad'a miki" ya fad'a yana fita daga d'akin.
Bai wuce ko ina ba sai d'akin Momy, a zaune ya same ta akan gado tana faman Fitar da numfashi.
Zama yayi kusa da ita ya kalle ta yace "ban sanki da haka ba Momyn Suhail iya zaman Ku da yarinyar nan yau shekaru goma sha biyu kenan ta tab'a yi miki sata?".
Girgiza kai Momy tayi tace " bata b'ata ba amma ai gashi yau an kama da dumu-dumu."
"Da idon ki kiga lokacin data d'auka?".
"Ko ban ganta da idona ba ai naga sark'ar a d'akin ta in ba ita ta d'auka ba mai zai kai sark'ar d'akin ta."
"To naji kin ganta da d'akin ta amma ai bakiga lokacin data d'auka ba, kika sani ko wani ne yakai sark'ar d'akin ta duk Dan a kulla mata sharri? Zato fa zunubi koda ya kasance gaskiya banyi tunanin zakiyi saurin yanke hukunci cikin fushi haka ba" dafa ta yayi ya cigaba da cewa,
"Ki nutsu ki shiga hankalin ki bana so nan gaba kizo kina Dana sani, da Fateemah tana sata da tuni an gane ta tun kafin ta Kai haka, akan waya Fateemah baza ta yi miki sata ba kwata-kwata nawa ce 11pro d'in? Ko Suhail ta fad'awa zai siya mata balle ni dake, kiyi tunani akan abinda na fad'a miki" yana gama fad'ar hakan ya tashi ya fita daga d'akin.

Shiru Momy tayi a ranta tace _tabbas abinda Dady ya fad'a haka ne, amma meyasa naga sark'ar a d'akin ta? Wannan amsar babu mai bani ita sai Ladi mai aiki gashi kuma d'azu ta tafi gida kuma kafin ta dawo za'a jima Sosai_.

A fili tace "Allah sarki daughter ko wanne hali take ciki yanzu? Bara naje na dubo ta" ta fad'a tana tashi da sauri.
Fateemah kuwa a inda suka barta anan ta kwanta tana kuka kamar ranta zai fita tana fad'in "Haba Momy ya zaki yi min haka Wallahi bani na d'aukar miki ba me na nema na rasa a gidan nan da zanyi sata? Wallahi bani bace" ta fad'a tana rushewa da kuka.
Da sauri Momy ta k'arasa wajan ta d'ago ta tana share mata hawaye tana jin zafin abinda ta aikata mata.

"Yi Hak'uri daughter nasan ban kyauta miki ba ki amma abin ne ya d'aure min kai amma komai ya wuce kiyi Hak'uri kinji".
Rungume Momy tayi tana kuka Sosai.
Dak'yar Momy ta rarrashe ta ta shiga band'aki ita kuma Momy ta fito daga d'akin.

Shukra dake lab'e a k'ofar d'akin tana ganin Momy ta fito tayi sauri ta bar wajan cikin sauri ta nufi part d'in Suhail.

Tana shiga babu sallama babu komai tace "Yaya Suhail komai ya lalace ga Momy can har sun shirya da Mayyar can."
STORY CONTINUES BELOW

Tsaki yayi yace "to shine zaki shigo min d'aki ko sallama babu" ya fad'a yana hararar ta.

"Kayi Hak'uri na rud'e ne wallahi."
"Kar ki damu Dan sun shirya akwai plan B ai zuwa nan da wasu y'an kwanaki zamu gabatar dashi."
Haka suka cigaba da had'a plan d'in su har aka yi kiran sallah suka tashi.

Bayan kwana uku.
Komai ya wuce Dan kowa ya saki jiki kamar komai bai faru ba.
Momy tana zaune a d'akin ta tana ninkin kaya Shukra ta shigo jiki a sanyaye ta zauna kusa da.
Momy ta kalle tace "ke kuma Lafiya na ganki kamar kwai ya fashe miki a ciki?".
" hmm wallahi Momy wani Abu ne yake damuna kuma kema ya shafe ki amma ban jin zaki amince dani."
"Fad'i mana mai zai saka nak'i amincewa dake."
"Wallahi Momy Fateemah so take ta auri Dady."
"Ke bana son iskanci banza dallah malama kiyi min bayanin abinda ke faruwa."
"D'azu naji Fateemah tana waya da k'awar ta tana cewa ai ita taga mijin aure a gidan da take wai wallahi duk yadda zata yi ta auri Dady sai tayi kuma tana shigowa gidan nan a matsayin matar Dady sai ta saka an sake ki, ni da farko wallahi Momy na zata Yaya Suhail take nufi sai da naji hirar Sosai sannan na fahimta, wai yau ma akwai abinda zata zubawa Dady a abinci kafin yayi Wannan tafiyar yana dawowa zaiji duk duniya babu wacce yake so sai ita, Momy baki ji yadda gabana ya dinga fad'uwa ba jikina ya fara ra......"
"Ya isa!" Momy ta fad'a cikin tsawa, "Shukra in kinsan Wannan abun sa kika fad'a min k'arya kike ki sanar dani."
"Wallahi Momy ba k'arya nake ba ki lura mana ranar da tayi miki sata baki ga irin kallon da Dadyn yake mata? Ni na fahimci shima sonta yake."

Mik'ewa Momy tayi tana huci cikin sauri ta fita daga d'akin.
Gab da zata shiga parlourn ta hango Fateemah tana barbad'e akan abincin da ke kan dining.
Wani taji kamar kibiya ya tawo mata tun daga brain ya tsaya cak a mak'ogaron ta.
Cikin tsawa ta furta "Ke Fateemah!!!."*COMMENTS &SHARE*

*© NEAT LADY.*
[3/4, 22:37] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa ce._😊

_ina mutuk'ar godiya da kulawar ku gare ni Allah ya bar k'auna._😍πŸ₯°

*SHAFI NA 14πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Cikin firgici Fateemah ta yarda maganin hannun ta ta juyo tana kallon Momy cike da tsoro.
Cikin sauri Momy ta k'araso wajan tana zuwa ta d'auke ta da mari tace "munafuka algunguma an miki rana kina neman kiyi mana dare, uban me kike zubawa a abincin Dady.?"
STORY CONTINUES BELOW

D'ago kai Fateemah tayi tace "Wallahi Momy Aunty Shukra ce ta bani tace in jiki na zubawa Dady a abinci wai maganin basir ne, wallahi tallahi itace ta bani."
"Kinji munafuka nida tun d'azu ina d'akin Momy yaushe na baki magani? Kawai da yau asirin kine ya tonu kuma duk bala'in ki wallahi baki isa ki auri Dady ba."
Kwafa Momy ta kalli Fateemah tace "Wallahi zaman ki yazo k'arshe a gidan nan bara kiga" ta fad'a tana fita daga parlourn da sauri.

Dady ne zaune a parlourn yana waya yana fad'in "kaima dai ka fad'a Alhaji Ado, shifa Alhaji Sabo bashi da magana sai ta na auri Fateemah ni bai San a matsayin y'a na d'auke ta ba."
Shiru yayi yana saurarar wayar sannan ya cigaba da cewa "wai fa da yazo gidan na sai yake min ai wallahi auran zanyi wannan kyakykyawar yarinyar ga iya girki ai Wallahi aure ta zanyi."
Dai-dai lokacin Momy tazo wajan ba tare da taji farkon maganar ba, ji take kamar zuciyar ta fito a ranta tace _Ashe dai da gaske Dady son yarinyar nan yake? Wallahi tallahi dole ta bar gidan nan._
Cikin fushi ta juya ta bar wajan kamar zata tashi sama.
Bayan Dady ya gama waya ya kira Momy a waya tazo suka yi sallama ya d'age Lagos ba tare da ta nuna masa komai ba.
Parlour Momy ta zauna ta kira Suhail a waya suka zauna a parlour suna kallon Fateemah da take kuka kamar ranta zai fita.
Momy ta kalle tace "Fateemah kin bani mutuk'ar mamaki banyi tunanin zaki yi min haka ba, daman hausawa sunce tsintacciyar mage bata mage, ni Fateemah ni zaki ci amana? Me nayi miki, to nima bazan kyale ki ba wallahi dole yau ki bar gidan nan Dan haka ki tashi ki tattara inaki inaki ki bar min gida tunda bada kud'in uban ki aka Gina ba shegiya bayarabiyar banza."
"Na rantse da Wanda raina yake hannun sa Shukra ce ta bani wannan maganin, Momy in kika Kore ni ina zani Dan girma Allah kiyi Hak'uri ban San komai akan abinda kike zargina ba" Fateemah ta fad'a tana kuka harda majina.
Tun daga babban d'an yatsa Suhail wani Abu yake masa yawo har zuwa brain d'in sa, baisan lokacin da yace "kiyi Hak'uri Momy ki kyale ta tunda tace bata San komai ba."
"Rife min baki koma mare ka baza'a barta d'in ba wallahi sai ta bar gidan nan yanzu ko tana so ko bata so."
"To yanzu Momy in kika Kore ta ina zataje? bata da kowa sai mu."
"Ta shiga duniya ma ni bai dame niba amma dai wallahi dole yau ta bar gidan nan."
Mik'ewa Momy tayi cikin zafin nama ta finciki hannun Fateemah ta jefa ta d'aki tace "ki tattara komai da kika San naki ne ki bar min gida yanzu."
Zata yi magana ta d'aga mata hannu tace "bana buk'atar jin komai daga bakin ki akan mijina babu abinda bazan iya yi ba."

Cikin kuka Fateemah take d'eb'o kaya tana zubawa a trolley kaya kad'an ta bud'e ta rife gwabar, bedside ta bud'e ta d'auko takardun makarantar ta saka ta d'auki y'ar k'aramar jakar ta ta saka a trolley tana kuka ta jayo ta ta fito parlourn.
A gaban Momy ta durk'usa tace "bani da bakin da zan miki godiya daga ke har Dady kun rik'e ni tamkar y'ar da kuka haifa, kun ganar dani addini na kun sani a makaranta duk wani jin dad'in rayuwa kun bani shi Wallahi Momy ko yankar naman jikina zaki yi bazan tab'a daina gode miki ba har abada, wallahi Momy ko kad'an ban kulla ce ki a raina ba har yanzu kallon uwa nake miki ba kuma zan daina yi miki wannan kallon ba,"

Juyawa tayi ta kalli Suhail da Shukra tace "na gode Sosai kuma da irin zaman da mukayi daku, amma fa kun sani duk Wanda ya cutar da wani ba tare da laifin komai Allah sai yayi masa saka masa, Nagode sosai."
Mik'ewa tayi ta ajjiye mukullin motar da aka bata ta nufi hanyar fita, cikin azama Suhail ya mik'e ya rik'e hannun ta ya kalli Momy yace " babu inda zata Momy ki kyale ta zauna."
Cikin masifa Momy tace "wallahi tallahi baza ta zauna ba ka sake ta tafi indai ka d'auki a matsayin uwa."
Sakin hannun ta yayi Fateemah ta bud'e k'ofar parlourn ta fita ta share hawaye.
Hanyar fita shima yayi yaba kira sunan ta Momy tace "kana fita daga parlourn nan sai na tsine kama sha-sha-sha Mara hankali kawai."
Komawa yayi ya zauna zuciyar sa kamar zata fito waje.

Fateemah kuwa a wajan mai gadi ta tsaya suka yi sallama daga nan ta fita daga gidan tana kuka sosai.

⚡⚡⚡⚡

Zaune suke a airport suna jiran zuwan jirgin da zai kawo su Abuja, Fa'iz yana zaune yaji gaban sa yana fad'uwa cikin sauri ya damk'e hannun Amir yace "Amir Fateemah tana cikin wani hali naji hakan a jiki na, kaga Ku hau jirgin Abuja Ku tafi ni zanbi jirgin Kano bara naje na siyi ticket kayiwa su Umma baya ni" yana gama fad'ar hakan bai jira abinda zaice ba ya mik'e da sauri ya abar wajan.

Girgiza kai Amir yayi Dan shi yanzu Fa'iz tausayi yake bashi ya lura so yayi masa mugun kamu.
Koda ya sanar dasu Dady murmushi yayi yace "Shikenan in kaima Kanon zaka fara zuwa sai Ku tafi gabad'aya."
Murmushi Amir yayi ya Sosa keya Dan har ga Allah so yake ya fara zuwa kano yaga Umman sa da Abie, amma kunyar idon Abban yasa ya kasa furta hakan.

Cikin sauri ya bi bayan sa tare suka siyi ticket suka yi sa'a akwai jirgin da zai tashi a lokacin ba'a fi minti goma ba suka tashi.

⚡⚡⚡⚡
Fateemah kuwa tana tafiya tana kuka tana jin tsanar Shukra da Suhail na ratsa ta Dan tasan duka wannan shirin sune dan lokacin da suke had'a plan d'in Momy ta aike ta ta kira mata Suhail anan taji suna maganar.
Tsayawa tayi tana tunanin inda zata nufa, zuciyar ta ta bata amsa da _ki tafi Lagos kawai_ saurin girgiza kai tayi tace "A'a ban shirya had'uwa da Dady yanzu ba, kawai na wuce Abuja kila a can na had'u da Yaya na tunda garin su ne."

Da wannan shawarar ta shiga kano line ta sami motar Abuja har ta kusa cika daman saura mutum d'aya tana shiga mota ta tashi.
Har suka fara tafiya bata daina kuka ba, har sai da wata mata a kusa da ita ta dafa tace "kiyi Hak'uri yarinya haka mutuwar aure yake da ciwo, amma wannan miji naki ya cuce ki yarinya kamar ki ya sake ki Allah ya saka miki."
Ita dai bata tanka mata ba sai rage kukan da da tayi tana ajiyar zuciya.

Arba'in ta kawo Amir da Fa'iz Kano bai jira azo a d'auke su ba suka tari abin hawa suka tawo.
+
Dak'yar Amir ya lallab'a Fa'iz suka nufi gida Dan shi niyar sa gidan su, wanka suka yi suka ci abinci kowa na gidan ya murnar ganin su.
Mahaifin Amir Wanda ake kira da Abie ba k'aramin farin ciki yayi da ganin su ba sai nan da yake dasu yana murmushi.
Suna zaune a parlourn Fa'iz ya mik'e ya kalli Amir yace "Malam in baza ka raka ni ba zanyi tafiya ta."
Murmushi Abie yayi yace "wai Fa'iz ina kake son zuwa? Na lura da kai tun d'azu kake sauri."
Sosa kai yayi ya sunkuyar da kai yana murmushi, dariya Amir yayi yace "zan baka labari Abie bara mu dawo."
"To Shikenan a dawo lafiya" Aunty mahaifiyar Amir ta fad'a tana kallon su.
Da sauri ya fice kafin Amir ya fito har ya shiga mota, yana shiga ya finciki motar ya bar gidan.
Gudu yake sosai ya k'agu ya k'arasa ya ga Fateemah, tsaki Amir yayi yace "wai Malam kashe mu kake son yi kome? Wannan gudu haka sai kace zamu bar gari."
Ko kallan sa baiyi ba ya cigaba da farara gudun sa, bai tsaya ba sai a k'ofar gidan su Fateemah yana tsayawa ya saki ajiyar zuciya tare da dafe kirji yana numfashi.
Kallon sa Amir yayi yace "Meye kuma haka bayan gashi munzo gidan, ka fita ka tura mai gadin ya kira ta."

Bud'e motar yayi ya k'arasa wajan mai gadin yace "Baba sannu da aiki."
Murmushi yayi yace Yauwa sannu d'an samari daga ina ban gane ka ba?".
"Nasan daman baza ka gane ni ba amma Dan Allah Baba ka shiga ciki kace wa Fateemah ana sallama da ita."
Rik'e baki Mai gadin yayi yace "wacce Fateemah ai Fateemah ko cikakken Awa d'aya bata yi da barin gidan nan ba."
"Ina taje Aiken ta akayi kome?".
"Eh to bana ce ba amma nidai na ga ta fito da jakar ta tana tafiya tana hawaye yadda na fahimta kamar korar ta mutanen gidan suka yi."
Zuba masa ido Fa'iz yayi dan shi Sam bai yarda da abinda yake cewa ba, bai tsaya tunani ba ya shiga cikin gidan da saurin gaske.
Suhail da Momy ne zaune a parlour kowa yayi shiru da alama kowa da tunanin da yake yi, sallamar sace ta katse musu tunani Suhail ya d'ago idon sa da suka koma ja ya amsa yana d'an sakin fuska.
Gaida Momy yayi yace "Nasan baki gane ni ba Momy, nine Fa'iz Wanda kuka fi sani da Yayan Fateemah shekaru goma kenan da suka wuce."
Murmushi Momy tayi tace "Kai Kai kai sannu da zuwa ai ban gane ka ba ka girma ka zama saurayi, ya hanya?".
STORY CONTINUES BELOW

"Lafiya lau Momy, ina mutuniyar?".
Had'e fuska Momy tayi tare da tab'e baki tace " wai Fateemah kake nufi?".
D'aga kai yayi alamun Eh.

Tsaki tayi tace "Fateemah bata jima da barin gidan nan ba na Kore ta kora ta har abada Dan bazan zauna da maciyar amana ba."

Da sauri ya d'ago kai ya kalli Momy yace "ban fa gane me kike nufi ba kiyi min bayani Sosai."

Cikin rashin damuwa Momy ta gyara zama tace "Fateemah taci amana ta na d'auke ta kamar y'ata amma ita so take ta cuce ni, daman ance tsintatciyar mage bata mage nima na gasgata hakan sai akan Fateemah, d'azun nan nace ta bar min gida ta d'ibi kayan ta ta fita."
Cikin fushi da b'acin rai Fa'iz ya mik'e yace "Anma ke kam anyi cikakkiyar azzaluma ko nace azalumai, Dan kunga da Ku kad'ai ta dogara bata da wani gata sai ku bata da Wanda zata kalla a garin nan tace nata ne sai Ku, yanzu Ku kanku Baku zan inda ta nufa ba, to bara kuji wallahi tallahi in wani abun ya sami Fateemah sai nayi Shari'a daku kar kiga wai  ke kika rik'e Fateemah har tsawon shekaru bazan kalli wannan ba zan manta da komai akan abinda kuka yiwa mata yanzu, kun zobe ladan Ku kuma Ku sani indai bata da laifi sai Allah ya saka mata zakuga sakaiyya a kanku."
Shiru suka yi suna sauraran sa Dan Suhail Sam bai ji haushin abinda Fa'iz yayi ba Dan shima da dama wallahi sai ya fad'awa Momy abinda yafi hakan duk da yasan sune silar komai.
Kallon sa Fa'iz yayi yace "na gane Kaine Suhail d'in da Fateemah take bani labari Kaine azzalumin da kake wahalar da ita, kunji dad'i kun saka an Kore ta sai Ku baza ruwa a k'asa kusha, insha Allah sai nago inda Fateemah take, Allah na tare da ita a duk inda take kuma duk bak'in cikin Ku sai na auri Fateemah."

Yana gama fad'ar hakan ya fito da sauri ya k'araso wajan mai gadi yace "Baba Dan Allah Fateemah bata fad'a maka inda ta nufa ba?".
Mai gadi yace " wallahi bata fad'a min ba tazo dai tayi min sallama ta fita daga gidan. "
Sallama yayi masa ya fito kalle-kalle kamar Mara hankali, ganin halin da yake ciki yasa Amir ya fito daga mota yana fad'in "kai kuma lafiya ka fito a firgice haka?".
Wasu zafafan hawaye ne suka fara sauka daga idon Fa'iz, kasa magana yayi sai tafiya da ya fara yana dube-dube, cikin sauri ya k'arasa wajan wani mutum yace " Dan Allah Baba baka wata yarinya da jaka a hannun ta ba tana tafiya tana kuka.?"
Mutumin yace "Gaskiya ban ganta ba Dan ban dad'e da zama a nan ba."
Baya Fa'iz yayi zai fad'i cikin sauri Amir da mutumin suka rik'e shi suna faman yi masa Sannu.

Hannu yasa ya dafe kai Dan jin yake kamar kansa zai fashe sabida yadda yake Sara masa, rik'e shi suka yi aka saka shi a mota, godiya Amir yayiwa mutumin sannan ya shiga motar yaja ta da sauri.
Bai wuce ko ina ba sai asibiti kafin su k'arasa asibitin zazzab'i mai zafi ya rufe shi, a wani d'aki aka kwantar dashi aka yi masa allura tare da saka masa drip, cikin minti na kad'an bacci ya d'auke shi.
Waya Amir yayi ya sanar dasu Abie, babu jimawa suka iso cikin tashin hankali suka nufi office d'in likitan.
Abie ya kalli likitan yace "Huzaifa me yake damun Fa'iz haka lokaci d'aya?".
Ajiyar zuciya yayi yace " Hak'ik'a akwai wani Abu da yake damunsa a cikin ransa, ko kuma an fad'a masa abinda ya firgita shi Sosai Dan Gaskiya jinin sa yayi bala'in hawa."
Dafe kirji Amir yayi yace "Hawan jini kuma Dr? Yanzu meye abin yi?".
Dr yace " dole a samu ya rage wannan damuwar in ba haka ba irin wannan cutar da ya samu lokaci d'aya tsaf zai iya samu heart attack."
STORY CONTINUES BELOW

Innalillahi wa'inna i'laihir raji'un shine abinda suka fad'a gabad'ayan su.
Jikin sanyi jiki suka fito daga office d'in suka koma d'akin da aka kwantar dashi.
Kallon fuskar sa sukayi ganin lokaci guda ya rame kamar bashi ba, suna zaune wajan mintina arba'in ya farka ya kallon d'akin.
Babu Wanda ya kula da farkwar sa kowa da abinda yake sak'awa a ransa, a hankali suka ji yace "Amir sun kori Fateemah ban San inda zan ganta ba Shikenan yanzu Fateemah ta barni."
Saurin juyowa suka yi suna kallon sa, Dr aka kira yazo ya duba shi ya fita.
Rik'e hannun sa Amir yayi yace "duk da baka sanar dani abinda ya faru ba na lura da yadda ka fito daga gidan nasan babu lafiya, ka kwantar da hankalin ka Brother insha Allah Fateemah matar kace ko ina taje zata dawo."

Girgiza kai yayi yana cize baki yace "ban San inda taje ba Amir in ban auri Beauty ba wallahi Zan iya rasa raina, Ku taimaka min Ku nemo ta."
Abie kallon Amir yayi alamun yana buk'atar k'arin bayani, shiru Amir yayi bai bashi amsa ba dan shi kansa bai San dalilin faruwar hakan ba.

Rufe ido Fa'iz yayi zuciyar sa nayi masa suya kamar zata k'one, shigowar su Mamy yasa ya d'ago kai yana kallon su.
Da sauri Mamy ta k'arasa wajan sa tana fad'in "Amir meye ya same shi haka?."
Nan Amir ya kwashe abinda ya sani ya sanar dasu,Mamy cikin damuwa tace "me ya same ta? Mutuwa tayi kome?".
Girgiza kai ya fara yana fad'in " Ba mutuwa tayi ba Mamy nazo na tarar bata gidan, sun Kore ta sun Kore ta."

Dady yace "kamar ya sun Kore ta daman iyaye suna korar y'ar su?"

"Zan Baku labarin komai amma ba yanzu nidai burina isan ida ta nufa."
Dafa shi Dady yayi yace "kar ka damu insha Allah matar kace za'a ganta."
Kallan su yayi yace "ina Umma Dady?".
" Bata zo ba muna shiga gida fa bamu Dad'e ba akace baka da lafiya shine mu muka tawo muka barta a can."
Murmushi yayi kawai bai ce komai ba.

⚡⚡⚡⚡

Fateemah bata sauka a Abuja ba sai bayan sallar magariba, a tasha suka rabu da matar ita Dan kowa sauri yake ya bar wajan sabida hadari da yayi bala'in had'owa, rasa inda zata je tayi kawai sai ta samu wani waje a can k'arshe tashar babu kowa ta zauna ta zabga uban tagumi.
Babu jimawa ruwa mai k'arfi ya sauka wajan ya zama babu kowa sai ita kad'ai a zaune, banda rawar sanyi babu abinda take yi ta rik'e jiki tana kuka.
"Wow kaga wata beautiful can a zaune ita kad'ai" wani dan shaye-shaye ya fad'a yana nunawa y'an uwan sa Fateemah.
D'ago kai d'aya yayi ya kalli wajan da aka nuna yace "kaiii da alama wannan ta muce muje kawai mu k'addamar mata."
Su uku suka nufi inda Fateemah take suna layi.Am sorry da rashin ganin posting kwana biyu mkrnt tasa hakan.πŸ‘πŸ»


*COMMENTS & SHARE.*


© *NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _hausawa sunce babbar Yaya ma uwa_

*TUKWICI GA:-*
*MY AUNTY JANAFY.*😍

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

_Last page nayi mistake a layin farkoπŸ˜‚ zan saka mintina arba'in sai na saka arba'in d'in, Allah yasa dai kun gane abinda nake nufi._

*SHAFI NA 16πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Har suka k'araso Fateemah bata sani ba hankalin ta yana wani wajan daban, babban nasu ne ya mik'a hannu zai tab'a suka ga ana hasko su da fitila alamun y'an sanda ne a wajan.
Ai basu tsaya shawara ba suka arce a guje, gudun da taji yasa ta d'ago tana kallon wajan tana tunanin to gudun me akayi haka?.
Y'an sandan suka k'araso wajan ta suka kalle ta d'aya yace "ke kuwa baiwar Allah me ya zaunar dake anan kin kuwa San hatsarin dake wajan nan? Yanzu daban muzo ba wallahi wad'ancan samarin sai sunyi nasarar yi miki fyad'e dan halin sune."
Gaban ta ya fad'i cikin rawar jiki ta Mik'e tace "kuyi Hak'uri wallahi bansan haka wajan yake ba ni bakuwa ce shiyasa".
" Ai ba zancen Hak'uri bane sauri zakiyi ki bar wajan nan in ba haka kuma duk abinda ya faru dake ke kika jawa kanki" yana gama fad'ar haka suka juya suka bar wajan.

Jan jakar ta tayi ta fito ta tsaya bakin titi, ita dai bata San idan zata ba gashi babu kud'i da yawa a hannun ta balle ta samu hotel ta kwana .
Wata mata ta gani tana kwashe kayan ta ta gama wuyar wainar masa, da sauri Fateemah ta k'arasa wajan ta tace "Baba sannu da aiki".

Murmushi matar tayi tace " yauwa y'ar nan, ke kuwa me ya fito dake cikin ruwa kinga yadda jikin ki ya jik'e? Haba y'ata kamar k'aramar yarinya. "
Marairaice fuska Fateemah tayi tace "Dan Allah Baba taimako nake nema."
"Fad'i Allah yasa zan iya yi miki."
"Yadda Allah ya taimake ki nake so ki taimaka min nima ki bani wajan kwana koda soro ne."
Zaro ido matar tayi tace "wajan kwana? Tab haka kawai ban sanki ba sai na d'auke ki na kaiki gidan da nake Har ki kwana a ciki a'a Gaskiya bazan iya ba."

Durk'usa Fateemah tayi ta rik'e k'afar matar tace "wallahi bazan cutar dake ba ni ba irin wacce kike tunani bace Dan Allah ki taimaka min ba Dan ni ba."

Ajiyar zuciya tayi tace "to mik'e ki taya ni d'aukar kayan muje".

Ba musu Fateemah ta mik'e cike da farin ciki suka tafi.

Basu yi wata tafiya ba suka isa wani d'an k'aramin gida Bud'ewa matar tayi suka shiga ciki, a d'an k'aramin parlourn suka zauna Wanda ke d'auke da leda shinfid'e.
Matar ta kalli Fateemah haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata, ragowar masar ta d'auko ta zuba mata miya ta mik'a mata.

Kamar kuwa tasan Fateemah wuya take ji nan ta fara cin wainar kamar babu gobe, bayan taci tasha ruwa matar ta kalle tace "Yarinya kinga inda nake da zama in zaki rik'e amana zamu zauna tsakani da Allah dake duk dai nasan ba lallai ki iya zama a nan ba sabida daga ganin ki daga gidan kud'i kika fito Hutu ya baiyana a jikin ki sosai, Yaya sunan ki?".
Sakin fuska Fateemah tayi tace " Sunana Fateemah. "
"Kice uwata ce ma, baba ta ni na d'auke ki kamar y'a ta Wallahi ina ganin ki naji kin kwanta min a rai nidai fatana kar ki cutar dani."
STORY CONTINUES BELOW

"Wallahi bani da niyar cutar da musulmi d'an uwana balle kuma Wanda ya taimake ni ki kwantar da hankalin ki Baba bazan tab'a cutar dake."
"Allah yasa hakan, ko ban tambaye ki ba nasan wani abun ne ya rabo ki daga gida bance sai kin sanar dani ba amma ina mai baki shawara idan irin yaran nan ne da suke Bari gaban iyayen su suke tawowa wayon karuwan cine ina mai baki shawara ki koma gida Ku fasa niyar ki, in kuma ba haka bane ina yi miki fatan Allah ya warware miki matsalar ki cikin gaggawa."
Share hawayen ta tayi tace "Wallahi ko d'aya ba haka ne ya fito dani daga gida ba, zuwa gobe zan baki labari na Baba."
"Allah ya kaimu goben, yanzu ki tashi kije ki canja wannan kayan sai kizo ki kwanta."
Mik'ewa Fateemah tayi tayi wanka tayi sallah sannan Baba ta shinfid'a mata wani kod'ad'den bargon ta ta kwanta.
Bayan kwana uku
⚡⚡⚡⚡
Jikin Fa'iz yayi sauki sosai dan har sun dawo garin Abuja, kullum Fa'iz yana d'aki a zaune yana aikin tunanin Fateemah tun ana yi masa magana Har aka gaji aka zuba masa ido.

Da yamma yana zaune a parlourn Mamy ya zubawa waje d'aya ido kana gani kasan tunani yake har Mamy ta zauna kusa dashi bai sani ba sai da ta kira sunan sa sannan ya d'ago ya kalle ta.
Tace "Wai Fa'iz baza ka daina wannan tunanin naka ba? In kaje ka jawowa kanka wani sabon ciwon fa, tunda kayi rashin lafiyar nan Shikenan ka zama shiru-shiru magana Sam bata dame ka ba ga fad'a Abu kad'an aka yi maka sai ka fara fad'a, Fa'iz in Allah ya rubuta Fateemah matar kace duk inda take zata dawo gare ka amma ka kasa ganewa kana ganin Wannan tunanin shi zai saka ta dawo gare ka, bama Wannan ba wai meye ya bara Fateemah daga gidan su?".

D'ago kai Fa'iz yayi ya sauke ajiyar zuciya yace " Mamy ban tab'a so ba sai akan Fateemah ban San meye so ba sai akan Fateemah, Mamy shekara goma ina dakon sonta tun ban San sonta nake ba har nazo na gane kinga kuwa Ashe in ina tunanin ta kamar banyi laifi ba."
Mamy tace "haka ne amma ai addu'a zaka dinga yi har Allah ya baiyana ta."
Murmushi yayi yace "Mamy ina auta ne?".
" tana islamiyya amma yanzu zaka ganta. "
Shiru yayi baice komai ba.
Mamy tace "ina jiran ka ka bani labarin Wannan Fateeman."
Gyara zama yayi yace "Wato Mamy ita Fateemah inda take basu ne suka haife ta ba."
"Kamar Yaya ban gane ba."
Zaiyi magana kenan wayar Mamy tayi k'ara ra d'auka tana amsawa.
Ganin wayar taki k'arewa yasa ya mik'e ya bar parlourn.
Mota ya hau bai wuce ko ina sai asibitin da yake aiki Dan tun d'azu ake masa waya.

Fateemah kuwa tana zaune ita da Baba sun dawo daga suyar waina Dan cikin kwanakin tare suke zuwa Dan zaman nasu gwanin sha'awa kamar daman can sun San juna.
Baba ta kalli Fateemah tace "Y'ata bawai na gaji da ciyar dake ko wani abun ba a'a kema kina buk'atar ki rik'e kud'i sabida buk'atar yau da kullum, akwai wani mai gidan mai a nan baya yana d'aukar ma'aikata sosai mai zai hana kije yanzu ki nema in Allah yaso sai kiga an dace."
"Wallahi Baba kamar kinsan abinda yake raina kenan ni kaina bana so naga kina aiki ni bana yi, ina so nima na dinga taimaka miki koda da siyan ashana ne, bara na saka hijjabi na naje."
Mik'ewa tayi ta saka hijjabi Baba tayi mata kwatance ta tafi.

Wajan babu wuyar ganewa tana zuwa ta gane wajan, d'aga kai tayi tana gan rubuta Fa'iz petroleum, Fa'iz ta maimaita sunan a ranta sosai gidan man ya burge ta Dan ya tsaru iya tsaruwa.
STORY CONTINUES BELOW

Ta tambaya ta isa office d'in manajan, da sallama ta shiga yana zaune a kan kujera yana rubuce-rubuce ya amsa ba tare da ya d'ago kai ba.
Gaishe shi tayi ya amsa dak'yar yana shan k'amshi.
Fateemah tace "Dan Allah taimako nazo nema yadda Allah ya taimaka ke ka nima ka taimaka min ka bani aiki koda na goge-goge ne."
D'ago kai yayi ya kalle ta, zaro ido yayi tare da lashe baki yace "Y'an mata kar ki damu zan baki aiki a gidan man nan ai bansan haka kike da kyau ba."
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta sunkuyar da kai tana wasa da zoben hannun ta, yace "kije an baki aiki gobe kizo da safe Dan ke zaki dinga share office d'in nan Dana Oga amma fa da huri zaki zo, zamu dinga biyan ki dubu goma a duk wata."
Cikin farin ciki Fateemah ta amsa tare da yi masa godiya ta taso ta fito, duk da tayi murnar samun aikin ta amma kuma zuciyar ta na fad'a mata wani Abu game da Wannan mutumin.
Haka ta koma gida ta sanar da Baba bata b'oye mata har yadda manager yake kallan ta.
Baba tace "Alhamdulillah Fateemah tunda Allah yasa an dace kin samu aiki ina mai baki shawara ki rik'e mutuncin ki a duk inda kike kada kiga bakya gaban iyayen ki hakan yasa ki watsar da darajar ki ta y'a mace, ki dubi girman Allah ki karewa kanki mutunci."
Jikin Fateemah yayi sanyi tayi na'am da shawarar Baba ta kuma yi mata alk'awari hakan bazai faru ba.
Washe gari da huri Fateemah ta shirya cikin doguwar Riga ta saka dogon hijjabi wanda k'afar ta kawai ake gani tare da d'ora nikab akai ta nufi wajan aiki.

*COMMENTS & SHARE.*

© *NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*Ummu Nabil & Aunty Maryamuu.*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 17πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Isar ta wajan ta tarar da mata da maza kowa yana harkar sa, wani yana zubawa customers mai wasu kuma suna kaikawo a wajan.
"Baiwar Allah wa kike nema?" Wata budurwa ta fad'a tana kallan Fateemah.
Juyowa Fateemah tayi tace "office din manager zani jiya yace ya d'auke ni aiki nazo yau shine zan tafi office d'in nasa,Dan Allah yazo kuwa?".
Zare ido matar tayi tare da girgiza kai tace " au kece wacce yace mana zaki zo yau kenan, sannun ki da zuwa jeki ki fito su mu San juna."

Murmushi Fateemah tayi tace "Hakan yana da kyau bara na dawo d'in" ta fad'a tana yin hanyar office d'in.
Bin bayan ta budurwa tayi da kallo tace "Allah ya kare ki daga sharrin manager yadda kike da kyau d'in nan kin shiga uku."
A can k'arshe gidan man office d'in yake wajan babu kowa Dan ba kasa fai ake biyowa wajan ba.
STORY CONTINUES BELOW

Gaban ta na fad'uwa ta tura k'ofar office d'in ta shiga cikin sallama.
Yana jin muryar ta ya d'ago yana washe baki ko sallamar ya kasa amsawa, zama tayi a kan kujerun da aka ta Dana tace "ina kwana."
Washe baki yayi yana yi mata wani irin kallo yace "lafiya lau Fateemah har kinzo aikin kenan?".
" Eh nazo" ta fad'a tana sunkuyar da kai.
Mukulli ya d'auko ya mik'o Mata yace "karb'i key d'in office d'in ogan dashi zaki fara."
Hannu ta mik'a zata karb'a ya rik'e hannun ta yana murmushi tare da saka mata key d'in a hannun.
Fizge hannun tayi ta zabga masa harara tayi tsaki, baice komai ba sai murmushi da yake yi.
"Ki fita waje kice ina Jamila tazo ta nuna miki office d'in oga" ai bata bari ya k'arasa ba tayi huf ta mik'e ta fito da sauri.

Da kallo ya bita yayi dariya sosai sannan yace "yarinya zamu gamu ne ai wallahi saina d'and'ani zumar ki Wannan uban hips haka".
Ita kuwa tana fita  ta tambaya wace Jamila aka nuna Mata wacce suka gaisa ita, murmushi Fateemah tayi tare da cewa " Ashe sunan ki Jamila?".
"Wallahi ke ya sunan ki?."

"Fateemah" ta bara amsa a takaice.
"Wow nice name ina son suna Fateemah wallahi, ko zamu iya zama k'awaye?".
Dariya Fateemah tayi tace " Me zai hana, yanzu dai kizo muje ance ki nuna min office d'in oga".
Jamila tace "to muje" tare suka jera suna tafiya har suka k'araso wajan.
Wata k'ofa suka bud'e suka shiga, parlour ne k'ayatatce da alama na saukar bak'i ne koma meeting, sakin baki Fateemah tayi tana kallon parlourn Dan yayi bala'in tafiya da ita.
Jamila tace "yauwa to tun daga nan zaki fara aikin naki in kin gama sai ki bud'e waccan k'ofar a cikin office d'in yake da kuma toilet, nidai burina Allah yasa kiyi aikin da zai burge oga."

Kallon ta Fateemah tayi alamun tana buk'atar Karin bayani.

Murmushi Jamila tayi tace "An kawo y'an aiki sunfi ashirin Wanda zasu dinga share office d'in nan da kuma Wannan meeting room d'in amma in akayi yana zuwa zaice baiyi masa ba dole a canja masa wata, Dan haka kiyi aiki da kyau da baya k'aunar k'azanta."
Dafe kirji Fateemah tayi tace "to shi kuma haka yake? To Allah ya d'aura ni akan sa, yana ciki yanzu?".
" Wah tab ogan zaki gani yanzu da sassafen nan? Ai oga sai ya kwashe sati ba tare da shigo gidan man nan ba balle ma yanzu da ya dawo daga tafiya, nifa wani lokacin har tunani nake anya kuwa Oga yana son kud'i?".
"Banda abinki Jamila waye baya son kud'i?".
" to ai naga Sam bai damu da gidajen man ba, gidan man sa uku amma babu Wanda zai jera kwana uku yana zuwa."
Fateemah tayi murmushi tace "Allah ya kyauta bara na fara kar lokaci ya k'ure" Dan ta lura Jamila akwai surutu in ta biye mata baza tayi aikin ba.
Jamila tace "to nima bara na koma" ta fad'a tana fita daga wajan.
Babu b'ata lokaci Fateemah ta share meeting room d'in yayi tas ta kunna turare wuta na tsinke sannan ta nufi office d'in.
Tana bud'ewa wani k'amshi mai dad'in gaske ya bugi hancin ta har sai da ta lumshe ido, zubawa office d'in ido tayi a ranta tace,

_ikon Allah Wannan office kamar wani office din President? Lallai bawan Allah nan yana da kud'i masha Allah, Ko meye abin shara ana nan oho._

Dad'a kallon office d'in tayi Dan ya burge ta shima.
STORY CONTINUES BELOW

Sharewa ta fara bayan ta gama tayi goge-goge ta shiga toilet d'in ta Wanke sannan ta fito, agogon office d'in ta kalla taga awa d'aya ta d'auka tana gyara wajan.
Tace "Daman Wannan waje mai girma ai dole nayi awa ban gama ba".
Idon tane ya kai kan wani k'aton hoto dake saman office d'in, a hankali ta k'arasa wajan tana karewa mutumin kallo.
A hankali ta furta" Wow Gaskiya Allah yayi hallita anan wajan".
Hoton Fa'iz ne yana zaune a wani waje fuskar d'auke da bak'in glass ya d'aura hannun sa a sajen fuskar sa.
Kallon pic d'in take zuciyar ta na wani irin bugawa da sauri tana ji kamar tasan mai kama da Wannan mutumin, iya tunanin ta tayi amma ta kasa tuno fuskar sai kawai ta d'auki mayafin ta ta yafa ta kulle office d'in ta fito.
Office d'in Manager ta koma tana shiga ta tarar baya nan cikin farin ciki ta ajjiye kullin ta fito da sauri.

A hanya suka had'u da Jamila, tace "Fateemah har kin gama ashe ?".
" Na gama wallahi Daman nima wajan ki zan zo mu zauna naga manager baya nan balle nasan ko zan iya tafiya."
"Haka ne muje mu zauna" waje suka samu suka zauna suna d'an tab'a hira kad'an.

Bata jima da zama ba Manager ya dawo anan tayi masa sallama ta nufi hanyar fita.
Tana fita daga gate d'in motar Fa'iz tana kunno kai cikin gidan man.
Da sauri ma'aikatan wajan kowa ya shiga hankalin sa Dan sun San halin oga baya k'aunar kin yin aiki haka kawai.
A hankali ya fito daga motar ya sha ado cikin manyan kaya Wanda suka amshe shi sosai, gashin kansa ya sha gyara sai kyalli yake sajen nan ya kwanata yayi luf.
Da sauri maganer ya iso ya karb'i jakar hannun sa yana yi masa barka da zuwa.
Cikin sauri kowa ya iso ya kwashi gaisuwa , shi kuwa kamar an masa dole haka yake amsawa, su Kansu sunyi mamaki Dan sun San ba haka yake yi musu ba sai dai in akwai abinda yake damun sa.
Gaba yayi manager ya bin sa baya har suka isa bakin office d'in, mukulli yasa ya bud'e ya shiga.

Turus yayi ya zare glass d'in fuskar sa yana kallon meeting room d'in.

Baiyi magana ba yayi gaba tare da bud'e office d'in, nan ma kallon sa ya tsaya yi tare da mamaki.
Cikin cool voice d'insa yace "D'ayyabu waye ya gyara office d'in nan da meeting room?."

Sosa kai yayi yace "Kayi Hak'uri Oga na d'au ma'aikaciya ba tare da izinin kaba amma nasan ko....."
"Shut up Malam, ni ba surutu na tambaye ka ba ce maka nayi waye ya gyara?".
" Oga ai wacce nake so nayi maka bayanin na d'auke tan itace ta gyara."

Juyowa yayi cike da mamaki yace "kana nufin kace ba order kuka d'auka aka zo aka gyara ba?".
" Eh Oga ba order aka d'auka ba yarinya ce budurwa tayi hakan, in kana so ma bara na kira ta."
D'aga masa hannu yayi yace "A'a bance ba kyale ta wata rana ma had'u" ya fad'a yana yatsine fuska.
Shiru manager yayi yana mamakin ogan nasa Dan yaga gabad'aya ya canja kamar bashi ba ko wasa da dariyar da ake yau baya yi sai had'e rai yake.
Katse masa tunani yayi da fad'in "to ni daman ba zama ya kawo ni ba Dan nayi tafiya ne ma yasa na zo naga yadda aikin yake tafiya, alhamdulillah naga kowa yana k'ok'ari yadda ya kamata ni zan koma sai na k'ara b'ullowa kuma" yana gama fad'ar hakan ya maida glass d'insa ya fita daga office d'in.

STORY CONTINUES BELOW

Tun daga ranar bai k'ara dawowa gidan man ba yau sati biyu kenan, Fateemah kuwa ta saba Sosai da mutanen wajan babu kamar ma Jamila Dan suna hira da ita Sosai Dan wata ran ba aikin take ba zama take suyi hira Dan office d'in babu abinda zata share.

Fa'iz ne kwance akan k'aton gadon sa ya zubawa waje d'aya ido yana hawaye, ba komai yake tunawa ba sai Fateemah lokacin da take kuka ranar da zai tafi.
Share hawayen sa yayi a fili yace "ya Allah na rok'e da kyawawan sunayen ka ka baiyana min Fateemah cikin gaggawa ya Allah kai ka d'aura min sonta a cikin raina ya arhamar rahimina ka baiya ta cikin aminci" kuka ne taci k'arfin sa Sosai baiyi k'ok'arin yin shiru ba yayi kukan sa ya k'oshi .

Umma dake tsaya a k'ofar d'akin itama hawayen ta goge tana jin tausayin sa na ratsa ta, badan kunyar sa da take ji ba yau da ta nuna masa soyayyar da yake mafarki samu.

Juyawa tayi ta Dan baza ta iya shiga ba.
Mik'ewa yayi jikin sa yayi sanyi haka kawai yau yake jin gaban sa na fad'uwa ya rasa dalilin hakan, wanka yayi ya shirya ya d'au key d'in mota ya fita.
Shiga motar yayi amma ba tare da ya San inda ya nufa ba, zuciyar ta umarce shi da kawai ya tafi d'aya daga cikin gidan man sa ya zauna, kunna motar yayi ya bata huta ya bar gidan da gudun gaske.

Fateemah kuwa yau tayi yamma Dan ta taya Jamila aiki suna gamawa kuma manager yace ta gyara masa office, tun Jamila na jiran ta har ta tafi dan bata jin dad'i.
Cikin sauri-sauri take aikin Dan so take ta koma tayi abinci kafin Baba ta dawo, shigowar mutum taji da kuma k'arar murd'a makulli.

Juyowa tayi taga manager ya zuba mata ido yana lashr baki, gaban ta ya fad'i cikin rawar murya tace "Manager na gama aiki Zan tafi gida."
Zare makullin yayi ya d'an daga wandon sa ya jefa makullin a ciki yace "zo ki d'auko" ya fad'a cikin wata irin murya.
Rawar jiki ta fara tana ja baya yana matsowa har ta kai bango, matse ta yayi har tana jin numfashin sa yace "Fateemah na dad'e ina jiran Wannan rana tazo amma taki zuwa sai yau, tunda na d'ora ido a kanki naji duk duniya babu macen da nake sha'awa sama dake yau dole na biya kaina buk'ata Dan in banyi ba sha'awar ki kashe ni zata yi" ya fad'a yana d'aura hannun sa a kirjin ta.
Runtse ido tayi ta hankad'e shi tace "ni ba fasik'a bace wallahi bazan amince dakai ba, Dan Allah kayi Hak'uri ka barni na tafi Dan Allah" ta fad'a tana fashewa da kuka.
Dariya yayi Sosai yace "ai daman nima ba amincewar ki nake so ba, ko kina so ko bakya so yau dole na d'and'ana zumar ki" ya fad'a yana cire kayan jikin sa.
Waje d'aya ta cure ta rufe ido jikin ta na rawa sosai, bai bar komai a jikin sa ba ko kunya babu ya matso musa da ita ya tsuguna ya kad'a mata makullin yace "kinga makullin nan in kina so na baki to ki amince Dani cikin sauki zanyi na gama in ba haka ba kuma bazan baki makulli ba kuma sai nayi abinda nake ao dake."
Itadai banda kuka babu abinda take idon ta a rife, murmushi yayi yace "bud'e idon ki na baki mukullin ki tafi."
Cikin sauri ta bud'e ido tana ganin halin da yake ciki ya saki wata k'ara tare da rife idon ta gam jikin ta na rawa.
Kokawa suka fara da ita yana k'ok'arin zuge mata zip d'in riga .

Ganin in ya tsaya kallon ta zata b'ata masa lokaci yasa ya d'auke ta da wani marin da yasa ta rud'e ta kwanta a wajan.
Kwanciyar da tayi ya bashi damar zuge zip d'in rigar har ya cire ta ya cillar , hannu yasa ya balle k'arfen bra d'in ta ta bud'e sai dai bai cire ta ba Dan ta kwanta a kai.
STORY CONTINUES BELOW

Jin ya fara shafa bayan ta yasa ta dawo hankalin ta ta mik'e tana rik'e bra din Dan kar ta fad'i tana kuka tana ja ba.
Cafke ta yayi ya had'e bakin su waje d'aya .
Fa'iz kuwa koda ya iso sai yaga office d'in maganer a kulle, tsaki yayi yace "kila yana ciki yana Wannan baccin nasa " ya fad'a yana saka safaya key d'in ya bud'e office d'in a dai-dai lokacin da yake kissing Fateemah.


*COMMENTS & SHARE.*


*© NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*D'auka cin masoyan wnn littafi.*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 18πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Manager yayi nisa Dan bai San lokacin da aka bud'e k'ofar ba, Fateemah kuwa jin an bud'e k'ofar yasa ta cigaba da k'ok'arin kwace kanta tana ture shi da hannu d'aya d'ayan kuma yana bayan ta ta dafe brezia d'in Dan kar ta fad'i.
Cikin sa'a kuwa ta kwace kanta tayi gefe kusa da k'ofar duk da ba taga ko waye ba tana kuka.
Cikin tsawa taji ance "Munafuka da ai da baki ji an shigo ba tsaya kika yi cak ana kissing dinki waye yasan abinda kuka yi kafin nazo, da yake ke makira ce sai da kika ji motsi zaki wani kwace kanki kina kuka shegiya karuwar banza, wallahi Dana San abinda kuke yi kenan babu dalilin da zai saka na katse ku sai na bar Ku kusha sha'anin Ku" Fa'iz ya fad'a rai a b'ace.

Sai a lokacin manager ya kula dashi jikin sa ya hau rawar yana laluben inda ya cillar da wandon sa.
Cikin b'acin rai Fa'iz ya kalle shi yace "Kai kuma na dawo kanka kalle ka da girman ka da hankali kayi tsirara a gaban wata, ko da yake ban San iya lokacin da kuka d'auka kuna aikata hakana ba, naga alama itace sabuwar ma'aikaciyar daman Shiyasa kake ta yabon ta Ashe ban gishiri na baka manda kuke ko? To daga kai har ita aikin Ku ya kare anan Wallahi gwara ita akan ka sai kayi Dana sanin aikata hakan" ya fad'a yana ficewa daga office d'in ransa a b'ace Sosai.
Fateemah data had'a kai da guiwa tana kuka sosai tana Dana sanin kawo kanta wannan ma'aikata, duk da bata cikin haiyacin ta kuma bata ga fuskar sa ba amma muryar sa yawo take mata a cikin zuciya tana jin kamar tasan mai irin ta.
Ganin tana b'ata lokaci yasa ta mik'e ta saka rigar ta ta d'au mayafin ta ta yafa sannan tace "Nagodewa Allah da bai baka dama ka aikata abinda kake so dani ba, amma duk da haka ka sani Allah ya isa tsakanina dakai bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e" tana gama fad'ar hakan ta fita a guje tana kuka.
Tafiya take tana kuka kamar wacce ta haukace har ta isa gida, tana shiga ta fad'a jikin Baba ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Cikin tashin hankali Baba tace "Uwa ta lafiya meya same ki? Meyasa yau baki dawo da huri ba? Ki fad'a min ko hankali na zai kwanta."

STORY CONTINUES BELOW

"Baba wai sai yaushe zanji dad'in duniya nima na zama y'a kamar kowa? Ban San dad'in iyaye ba tun ina k'arama na rabu dasu ina zanga mahaifiya ta wacce nake mutuk'ar buk'ataa rayuwa ta? Na tabbata da ina wajan ta yanzu duk da wannan abun bai faru dani ba" ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka.
Rarrashin ta Baba tayi Sosai har tayi shiru tana ajiyar zuciya, Baba tace "sanar dani abinda ya faru."
Fateemah bata b'oye mata ta fad'a mata komai har korar da akayi musu a wajan aiki.
Baba tace "Duk abinda ya faru da bawa Allah ne ya k'addara Dan haka bana so ki saka komai a ranki tunda Allah bai bashi damar b'ata miki rayuwa ba, sai me Dan kin bar aikin Allah zai baki Wanda yafi shi ni Wallahi Ogan naku ne yafi bani haushi bai tsaya yayi bincike ba ya yanke hukunci Dan yasa shine mai wajan, to su rik'e abinda su da Allah muka dogara, maza tashi kije kici abinci ki kuma daina wannan kuka."
Mik'ewa tayi tana share hawaye ta shiga d'aki.

⚡⚡⚡⚡
Cikin bala'i Merry take cewa "nifa na gaji bazan zauna da kai baka da kud'i ba bazai yuwa dole ka sake ni ko kuma na bar maka gidan."
Da mamaki Mr Danial yake kallon ta yau shi Merry take yiwa wannan rashin mutumin akan ya talauce? Cikin takaici yace "Bazan sake ki ba kuma baki isa ki bar gidan bab in ba haka ba kuwa saina had'a ki da police kin biya ni duk abinda kika San na kashe miki, ya zanyi da raina ne Merry kin bara ni da first wife d'in ta kin rabani da daughter ta, ki zubar da cikin unborn d'ina kin kwashe dukiya ta kince zaki yi business kika zo kika cemin ai kinyi asara daga kud'in har biran babu yanzu kuma kizo kice na sake ki impossible."
"Yes ni na raba ka da Sisiliya I know sabida a wancan time d'in kafi son ta dani baka ganin kowa sai ita da Eleina, Shiyasa ranar da ta fita muka saka sani ya bita a hanya ba tare da ta sani ba yayi hugging d'inta ba tare da ta lura ba, mu kuma mana gefe muka dinga yi mata hotona na turo maka, kai kuma da yake Rubbish ne sai kawai ka yarda dani ka kore ta ka Kore ta ni kuma yanzu bazan zauna ba" tana gama fad'ar hakan ta juya da sauri ta fita daga parlour.

Tagumi Danial yayi hawaye na zuba a idon sa, yanzu ina zaiga Sisiliya da Eleina? Goge hawayen sa yayi yace "in naje gidan su Sisiliya yanzu babu abinda zai hana Dadyn ta ya kashe ni balle ma in suka San ban San inda Eleina take ba, oh Jesus help me to solve this" ya fad'a yana k'ara fashewa da kuka sosai.
Merry ta gudu da dukiyar sa ta barshi bayan ta raba shi da matar sa da kuma y'ar sa, da wannan tunanin ya mik'e ya koma d'aki yana hawaye.

⚡⚡⚡⚡
"Kai Suhail bana son maganar banza ina Fateemah take?".
" Wallahi Dady Momy ce ta Kore ta wai tace so take ta aure ka".
Kallon Momy Dady yayi Cikin b'acin rai yace "haka ne?".
Cikin masifa Momy tace " Eh haka ne kuma bana nadamar yin hakan wallahi, kaima ai son nata kake tunda naji kana waya kana fad'a."
Girgiza kai Dady yayi ya kalli Shukra yace "ko Ku fad'a min gaskiyar abinda kuka had'awa Fateemah ko kuma ranku ya b'aci."
Cikin masifa Momy tace "me suka had'a mata? Duk laifin tane da batayi ba ai da har yanzu tana nan kawai dai kace daman kaima da shirin auran tana a ranka."
Tsaki Dady yayi yace "Ban tab'a sanin baki da hankali ba sai yau yarinyar Dana rene ta tun tana k'arama na d'auke ta matsayin y'a ita kike cewa zan aura?".
" Nawa akayi a su nan sa yawa a gari".

Suhail ne ya katse su da cewa "Momy kiyi Hak'uri wallahi Fateemah bata da laifin komai duk abinda ya faru nida Shukra muka had'a shi tun daga kan sark'ar ki har zuwa lokacin da kika Kore ta."

STORY CONTINUES BELOW

"Lallai Suhail nuna min kafi k'aunar mahaifin ka a kaina dan ka akare ta shine kake cewa wani kuka had'a to komai me zaku ce nidai bazan yarda ba."

Dady ya kalli Suhail yace "cigaba da bayanin ka."
Suhail bai b'oye musu komai ya sanar dasu duk abinda suka k'ullawa Fateemah sannan ya d'aura da cewa "Dady ban tab'a nadama a rayuwa ta ba sama da wacce nayi lokacin da aka kore Fateemah, sai bayan tafiyar ta na tabbatar wa kaina da son Fateemah nake, Wallahi Dady ji nake in ban auri Fateemah ba zan iya mutuwa."
Momy da jikin ta yayi sanyi bata San lokacin da hawayen nadama suka fara zubowa daga idon ta ba tayi shiru tana sauraran abinda suke cewa.
Dady yace "to kinji Babu laifin da yarinyar nan tayi gabad'aya makircin y'ay'an kine sai kiyi tunani yanzu da kika Kore ta kin San inda take? Kin San halin da ta shiga yanzu? Baki sani ba sabida bake kika haife ta ba, tabbas nasan kinyi k'ok'arin rik'e ta tun tana yarinya amma daga k'arshe sai kika zobe ladan ki maimakon ki k'arasa, Yanzu me gari ya waya uhum."
Suhail yace "Dady kuyi min izini naje na nemo ta Dan Allah."
Tsaki Dady yayi yace "kaida baka k'aunar ta ina kai ina zuwa Neman ta? Tunda har kuka yi sanadiyar Fitar ta daga gidan ku Yanzu kuma kazo kace wai kana sonta k'arya kake wallahi, ke kuma Shukra na baki dama akan ki fito da miji kinki ko? To bara kiji sati mai zuwa zan aurar dake kamar yadda na fad'a miki in baki fito da miji ba zan baki Wanda naga dama in kinga dama ki zauna in baki ga dama ba ki kashe auran ki fito" Dady na gama fad'ar hakan ya mik'e ya shige d'akin sa.

Momy dai ta kasa cewa komai sai girgiza kai taje cike da Dana sani.

⚡⚡⚡⚡⚡
After 3 day's.

Fateemah ta saki ranta harkar gaban ta kawai take, bayan sun dawo daga wajan suya wata mata mai suna inna Harira ta shigo gidan.
Bayan sun gaisa ta kalli Fateemah tace "A'a Faty yau baki je wajan aikin da kika samu bane?".
Baba tace " ke dai bari Harira ai ta daina Wannan aiki tun kwana uku da suka huce."
"Me yasa ta daina?".
Baba ta kwashe komai ta sanar da ita.
Inna Harira tace " Nima na goyi bayan karta koma d'in akan wani banza aiki akayi k'ok'arin yi mata fyad'e, amma zama hakan bazai yu ba sabida a matsayin ta na budurwa tana buk'atar Dan rik'e kud'i na siyan kayan yau da kullum."
Baba tace "Nima haka nake tunani wallahi Harira da ace inada kud'i ko babu dalilin da zai saka nasa Uwa ta tayi aiki sabida ni kallon y'a nake mata."

"Na sani ai basai kin fad'a ba, akwai wata mata wacce nake aiki da safe a gidan ta kafin na fara wuya tace min tana son y'ar aiki wacce zata dinga dafa mata abinci in samo mata, to sai naga mai zai hana muje Fateemah ta dinga yin aikin? Tana da kirki matar fiye da tunanin ki."
Baba tace "to gata nan ai in zata yi to in baza tayi ba in bazan tilasta mata ba."
Harira ta kalli Fateemah tace "y'a ta zaki iya?".
Fateemah ta kalli su baza ta iya watsa musu k'asa a ido ba duk abinda suke so shi zata yi, d'aga kai tayi alamun eh.
Inna Harira tace " to maza tashi ki shirya muje yanzu amma fa ina jin sai dai kin dinga kwana a can sai kin bushi iska kizo ki gaida Baba. "

Mik'ewa tayi zuciya ta a cunkushe ta saka hijjabi suka fita ita da inna Harira.

Basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani k'ato gida Wanda kana ganin sa kasan an kashe kud'i wajan Gina shi.
STORY CONTINUES BELOW

Da yake masu gadin duk sun Santa bata sha wahala baa suka shiga gidan.
Umma na zaune a parlour taji sallamar su, cikin sakin fuska ta masa suka zauna.
Bayan Inna Harira ta gaishe ta itama Fateemah ta gaishe ta tana sunkuyar dakai, amsawa tayi cikin fara'a.
Inna Harira tace "Hajiya ga mai miki yidimar da kika ce nasamo miki."
Murmushi Umma tayi tace "Yaya sunan ki y'an mata?".

Fateemah tayi murmushi Dan matar ta burge ta tace " Fateemah".
"Kai kice babban suna gare ki, kinji aikin da zakiyi Girki ne sai kuma d'an gyaran d'aki da baza su wuce biyu ba."
D'aga kai Fateemah tayi alamun ta sani.
Umma tace "Masha Allah to amma dai kinzo kenan ko? Dan anan zaki inga kwana bana son aikin jeka ka dawo d'in nan."
Kafin tayi magana Inna Harira tace "Eh tazo kenan bata yanzu naje na tawo mata da kayan ta" ta fad'a tana mik'ewa.
Umma tace "yauwa hakan yayi duk wata za'a dinga biyan ki dubu ashirin da biyar insha Allah, sai dai bana son k'azanta duk da yanayin ki ya nuna min ke ba k'azama bace, sai kuma ki rik'e amma Dan ban zama inuwa d'aya da naci amana a duk inda yake."
Fateemah tace "insha Allah Zaki same ni yadda kike so bazan tab'a sab'a miki ba."
Fa'iz ne ya shigo yana waya da alama da Mamy yake yi yadda yake maganar zaka tabbatar da ita yake .
Zama yayi akan kujera ba tare da ya kalli inda Fateemah take har ya gama wayar.
Umma ta kalle shi tace "ka sabuwar ma'aikaciya mun samu zata dinga Girki da kuma gyara maka d'aki."
Ba tare da ya d'ago ba yace "is ok Allah yasa dai ba k'azama bace Allah yasa ta iya girkin da sharar da wallahi daga kanta na daina cin abincin y'an aiki restaurant zan fara shiga."
Tsaki Umma tayi tace "kaji da iyayin ka, Fateemah kinga lemo can d'auko min."
Jin an ambaci sunan Fateemah yasa ya d'ago amma baiga fuskar taba Dan ta juya baya .

Maida kansa yayi ya cigaba da danna wayar sa.
Fateemah kuwa tunda taji muryar sa jikin ta yayi sanyi da tsaf ta gane muryar waye gaban ta sai fad'uwa yake Allah yasa shi bazai gane wace ba.
A hankali ta juyo da lemo a hannun ta ta kawo wa Umma ta ajjiye, Kofi Umma ta d'auka ta zuba lemon tana sha.
"Umma Nima zan sha zob'on naki."
"Mtsw to rik'e hannun ka nayi da baza ka zuba kasha ba? Faty zuba masa."
Zubawa tayi a kofin ta k'arasa kusa dashi ta mik'a masa, bai karb'a ba sai cigaba da danna wayar sa da yake Dan sauke hannun ta yayi shi kuma lokacin ya d'ago hannu zai karb'a ya tankad'e zob'on ya kusa zube masa a jiki.

Cike da masifa ya d'ago ya sauke idon sa a kanta wacce kanta yake sunkuye .
Cike da mamaki ya mik'e tare da fad'in "Umma daman wannan karuwar kika d'auka aiki? Har ta dafa abinci naci? Wallahi baza ta sab'u baza ta zauna a gidan nan ba."
*COMMENTS & SHARE.*

*© NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*Gaskiya writers Association.*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 19πŸ“‘*
*__________πŸ“–* rawar jiki Fateemah take hawaye na yawo a idon ta zuciyar ta cike da Dana sanin zuwa gidan.
Umma ce ta daka masa tsawa tace "Kai wai Lafiyar ka? Tunda ka rasa wannan yarinyar ka koma kamar sabon kamu, to bara kaji ido ba mudu ba amma yasan kima karya kake ka kalli yarinyar nan ka kira ta da wannan kalmar kuma zama a gidan nan ai ni na kawo ta baka isa kasa ta bar gidan nan ba."
Cize Baki yayi ya d'au wayar sa da gudu ya haura sama.
Umma kallan Fateemah tayi sai taji ta bata tausayi dan tunda ta ganta taji ta kwanta mata a rai, tace, "kiyi Hak'uri kinji y'ar ta karki saka komai a ranki."

D'aga kai Fateemah tayi Dan dai kawai taji tane amma ba yarda tayi ba.
Babu jimawa Inna Harira ta kawo mata kayan ta kira ta gefe tayi mata nasiha Sosai tare da sak'on da Baba ta bata ta, bayan ta gama ta tafi ta bar .
Fa'iz kuwa d'aki ya shiga yana huci cike da jin haushin abinda Umma tayi masa gaban karuwar nan, wayar sa tayi k'ara ya d'auka yana fad'in "Yaushe zaku dawo Mamy? Wallahi Umma ta daina sona gabad'aya tunda Gashi Yanzu ta fifita y'ar aiki a kaina."

Dady dake zaune gefen Mamy yana sauraran abinda yake cewa yace "y'ar aiki fa kace Fa'iz, to akan me?".
"Nidai kawai Ku dawo Dady wallahi gidan gabad'aya ya fita daga raina, na rasa me nayiwa Umma kamar ba ita ta haife ni ba."
Mamy tace, "kwantar sa hankalin ka Son zamu dawo very soon insha Allah, ka cigaba da kwantar da hankalin ka."

Bai tsaya sauraran me zata kuma cewa ba ya kashe wayar, zama yayi a bakin gado yana tunanin hukuncin da ya dace da Fateemah.

Tsaki yayi yace, "Dan ma taci sa'a sunan beauty ne da ita shiyasa kawai na kyale ta yanzu, koda yake ma ai gurbin ido ba idon bane zata gane kuran ta zata san wanene ni."
Kwanciya yayi yana kallan sama nan take tunanin beautyn ta ya fad'o masa a rai, murmushi yayi yace "Ya Allah ka baiyana min beauty na cikin gaggawa."
Dak'yar ya mik'e ya shiga toilet Dan yaji an fara kiran sallah.

Fateemah kuwa danne zuciyar ta tayi ta tayi wanka a d'akin da aka nuna mata, bayan ta gama ta saka doguwar Riga ta fito Dan tacewa Umma yau zata fara aikin ta.
Kitchen ta shiga ta d'aura jellop rice wacce taji kayan lambu, cikin mintina kad'an ta gama ta jera kan dining kamar yadda aka fad'a mata ta koma d'aki.
Fa'iz kuwa yana shigowa dining ya nufa ya zauna ya fara cin abincin sa, anan Umma ta tarar dashi tace "wato kai har ka Riga kowa ko?".
" Wallahi Umma abincin ne yayi bala'in dad'i kamar kar na daina ci haka nake ji."
Murmushi tayi bata ce komai ba ta zauna ta fara cin abincin.
Tunda tayi loma d'aya ta girgiza kai tana yaba iya Girki irin na Fateemah.
STORY CONTINUES BELOW

Auta ce ta fito suka cigaba da cin abincin tare.

Haka Fateemah ta cigaba da yin aiki a gidan su Fa'iz, tunda suka had'u sau d'aya bata kuma bari sun had'u ba Dan ko d'akin sa zata gyara sai ta tabbatar baya nan take shiga shima tana gamawa zata fito.

A haka har ta kwashe kwana goma a cikin gidan.

Sosai take jin dad'in zama da Umma da mace ce mai fara'a gashi yadda take Jan Fateemah a jiki kamar ba y'ar aiki ba.
Shi kuwa Fa'iz tuni yama manta da wata hallita Fateemah a gidan, Dan ko abinci yake ci ya dinga tambayar Umma wacce tayi amma tayi masa banza a cewar sai ta k'uri k'arshe iyayin sa.

Ranar Tuesday da rana Fa'iz ya dawo daga asibiti duk ya gaji dan mata biyar yayiwa operation yana kwance a kan gado ya rufe ido yana tunanin da ya saba.
Tunanin Fateeman da ya gani tare da manager ne kawai ya fad'o masa, mik'ewa yayi zaune ya runtse ido tare dare da cize baki yace, "Wai meyasa na kasa mantawa da wannan yarinyar ne? Meyasa yadda na same su yake min yawo a zuciya ta da idona? Meyasa ko da yaushe ina tuno su sai naji gabana ya fad'i?".
Tsaki yayi tare da mik'ewa yana cewa " haka kawai na saka damuwa a raina ita wacce ta aikata hankalin ta kwance tunda gashi har aiki take a gidan mu, shi kuma na Kore shu na saka wani meyasa to na kasa mantawa?".
_Kila Dan sunan su d'aya da beautyn ka,_ zuciyar sa ta bashi amsa, ajiyar zuciya yayi tare da tab'e baki ya shiga toilet.
Fateemah suna zaune da Umma a parlour Umma tace, "Faty yau kin kuwa sharewa wancan yaron d'aki?".
Murmushi Fateemah tayi Dan tasan indai Umma tace wancan yaron to Fa'iz take nufi, tace " ban gyara ba amma yanzu nasan baya nan bara naje na gyara" ta fad'a tana mik'ewa.
"To dakya sai kin dawo" Umma ta fad'a tana cigaba da kallon TV.
Cikin kwarin guiwa Fateemah ta hau sama ta tura k'ofar d'akin sa ta shiga Dan ita a tunanin ta baya nan.
A parlour ta cire hijjabin ta ta gama gyara parlourn tas sannun ta shiga d'akin.
Gyarawa ta fara cikin sauri Dan ko kad'an bata k'aunar abinda zai had'a ta dashi.

Shi kuwa Fa'iz yana fitowa daga toilet towel d'aure a k'ugun sa d'aya kuma ya rife fuskar sa da ita, bud'e towel d'in yayi yana k'ok'arin cirewa.
"Na shiga uku" Fateemah ta fad'a tana juya fuska tare da runtse ido.
Bud'e fuska yayi ya ganta tsaye amma ta juya baya, ko ba'a fad'a ba yasan karuwa ce cike da takaici yace "ohhh wato kin saba bin maza shiyasa kika shigo min d'aki babu izini ko? I hope dai kinga abinda kike so ki gani, to wallahi nima bazan bar idon naki ba saina bashi punishment" ya fad'a yana komawa toilet d'in.
Cikin tsoro Fateemah ta juyo tace "Dan girman Allah kayi Hak'uri wallahi Umma ce ta sani tace nazo na gyara maka d'aki."
Sarai yaji abinda take amma ko kad'an baiji tausayin ta ba saima haushin ta da ya dad'a ji, Rambo (insecticide) ya d'auko a ya girgiza yaji akwai sannun ya fito.
Fateemah kuwa ta had'e da bango ta runtse ido tana jiran hukunci, a hankali taji yace "bud'e idon ki".
Jin yadda yayi maganar yasa ta zata ya Hak'ura, cikin sauri ta bud'e ido, tana Bud'ewa ya fara fesa mata Rambo a ido.
Wata k'ara ta saki tana saka hannun ta tana karewa amma ina ya Riga ya shiga cikin idon ta, sai da ya k'arar dashi tas a fuskar ta sannun ya jefar da gwangwanin ya nuna ta yace " gobe naga da idon da zaki k'ara kallon maza, k'aramar karuwa kawai. "

STORY CONTINUES BELOW

Ita kuwa Fateemah ta rasa abinda zata yi sabida azabar dake ratsa idon ta, ko kad'an kuma yak'i Bud'ewa balle ta samu hanyar fita.
Shiryawa sa yayi ba tare da damuwa ba Dan yasan babu abinda ta isa ta gani a yanzu dai in ma taci sa'a bai lalata mata ido ba, yana gama shiryawa ya d'auki key d'in sa ya sauko daga saman.

Umma dake zaune ta mik'e tare da fad'in "daman kana nan ina Fateeman to?".
Tab'e baki yayi yace " tana cikin Wanke toilet garin ya fesawa kyankyaso Rambo ta fesa a idon ta gata can a bedroom d'ina ko bud'e idon bata iya......" Ai kafin ya k'arasa fad'a Umma ta hau saman da sauri.
Ficewar sa yayi ya hau motar ya bar gidan ba tare da wata damuwa ba.

Da gudu Umma ta shiga d'akin ta tarar da ita a kwance tsabar azaba ko kukan ta kasa.
Auta Umma ta kwallawa kira tazo suka kama Fateemah wacce ko tafin hannun ta bata gani suka fito daga d'akin.
Kuka sosai Auta take Dan ba k'aramar shak'uwa suka yi da Fateema jinta take kamar yayar ta.
Da taimakon masu aikin gidan akana kama Fateemah aka saka ta a mota aka tafi asibiti.
Da yake asibitin da suke zuwa ne kuma private ne suna zuwa aka karb'e sao emergency, cikin sauri-sauri likitocin suke aiwatar da abun sabida yadda suka San illar abinda ya shigar mata ido.
Umma dai ta kasa zaune ta kasa tsaye, tunanin ta d'aya in Fateemah ta rasa ido ya zata yi tunda itace silar komai? Da bata dauke ta aiki ba da kila babu abinda ya faru da ita yanzu.
Tana cikin wannan tunanin likitan ya fito, da sauri Umma ta nufe shi tana tambayar sa idon Fateemah.
Ajiyar zuciya yayi yace "Umman Dr yarinyar nan kuwa taje makarantar secondary?".
"Ban sani ba gaskiya amma ina tunanin ta huce secondary ma."
"To indai taje makaranta tasan illar duk wani insecticide sabida su Kansu a jikin gwangwanin zaki ga sun rubuta kar ka saka a ido, da fuska, in takaice miki labari Umma Fa'iz ba lallai wannan yarinya ta cigaba da gani ba."
Dafe kirji Umma tayi tare dayi salati tace "kana nufin ta zama makauniya?".
" Eh to bama ce ba baza mu tabbatar da hakan ba sai ta farka, amma in yayi mata da kyau shine ta daina gani Sosai infa yayi mata da kyau kenan."

Shiru Umma tayi tama rasa abinda zata ce sai sautin Auta da yake tashi.


*COMMENTS & SHARE.*

© *NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*Gaskiya Writers Association fan's grps.*πŸ˜‰
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

STORY CONTINUES BELOW

*SHAFI NA 20πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Zama Umma tayi tana tunanin halin da Fateemah ta shiga, sai da ta kwashe awa uku a kwance sannan   Fateemah ta farka.
A hankali take bud'e idona ta har ya bud'e gabad'aya, a hankali take kallon d'akin sabida gani take komai yana juya mata.

Cikin sauri Auta ta fita ta kira likita suka shigo tare.
Kusa da ita likitan ya zauna tare da fad'in "Sannu Fateemah ya idon naki?".
A hankali tace " Da sauki amma har Yanzu yana min zafi".
"Kar ki damu insha Allah shima zai daina, kina gani na?".
" Eh ina ganin ka amma kayi min nisa da yawa ka d'an matso sai nafi ganin ka."
Kallan ta Umma tayi tace "Ai yana kusa dake Faty ko hannu kika mik'a yanzu sai kin tab'o shi."
Mirza idon ta tayi Sosai ta bud'e tace "ni kuma a nesa nake ganin sa."
Likitan yace "kar ki damu ai matsalar tazo miki da sauki Sosai ma," ya kalli Umma ya cigaba da cewa "Ba abin damuwa bane medical glass zamu bata Wanda yayi dai-dai da ciwon ta za kuma mu d'ora ta akan magunguna da insha Allah wata rana ba sai tayi amfani da glass d'in ba, amma a kiyaye gaba in har hakan ta kuma faruwa to idon ta zai iya mutuwa gabad'aya".
Ajiyar zuciya Umma tayi tace " Insha Allah hakan ma bazai kara faruwa ba, mun gode."
Murmushi yayi yace "haba Umma ki daina min godiya kefa mahaifiyar Ogana ce Dr Fa'iz duk abinda nayi miki bazan tab'a rama alkairi da yayi min ba, na bar Ku Lafiya" ya fad'a yana fita daga d'aki.

Auta ce ta k'arasa wajan Fateemah ta zauna kusa da ita ta rik'e hannun ta tace "Sannu Aunty Fateemah Allah ya baki lafiya."
Itama rik'e hannun ta tayi Dan ba k'aramin so take yiwa Amina Auta ba.
Umma tana kallan su sai tayi murmushi tace "nifa wallahi ba k'aramar kamar Ku nake gani da Amina ba, Dan yadda kuke kama koda wancan yaron basa yi."
Cikin murna ance suna kama da Fateemah Auta tace "Allah Umma na? Ashe nu kyakykyawa ce tunda muke kama da ita."

Ita dai Fateemah murmushi take tana jin kaunar ta har cikin zuciyar ta.
Tare da Auta suka kwana a asibitin tunda dai Fateemah na gani sai dai kawai ta taimaka mata sabida yanayin ganin nata.
Washe gari da huri aka zo aka tafi da Fateemah d'akin bada glass, bata akayi tana gwadawa tana fad'ar yadda take ganin mutanen har aka samu Wanda ya dace da ita in ta saka glass d'in tana ganin komai dai-dai kamar da.

Lokacin da aka dawo da ita Auta tana band'aki tana fitowa tayi arba da ita, sakin baki tayi tana kallon ta.

Fateemah tace "ke kuma Lafiya kin zuba min ido?".
" Tab Aunty Fateemah kinga yadda glass d'in nan yayi miki kyau? Dan Allah ki kalli madubi ki gani."
"Ban da abinki Auta ina kyau a abin lalura? Dan dole na saka shi amma ni bana k'aunar saka glass ko kad'an."
Dariya Auta tayi tace "Dan baki ga kanki bane da ke kanki sai kinji kin burge kanki."
Umma ce tayi sallama suka shigo ita da Inna Harira da Baba mai waina, k'arasawa suka yi ska zauna, Baba tace "Uwa ta ya jikin naki?".
Murmushi Fateemah tayi cike da jin dad'in ganin ta tace " Da sauki Baba wallahi ya aiki naki?".
"Wanne aiki y'ar nan ai tunda Harira take jiya da daddare ta sanar dani baki da Lafiya ko kasko yau bazan d'ora ba."
Dariya Fateemah tayi wushiryar ta ta baiyana tace "Ai naji sauki Baba komai ina gani Yanzu."
"Allah ya k'ara sauki, amma Uwa ta ki dinga kula da irin abinda zakiyi amfani dashi kinga gashi garin ki kashe abinda kika fi tsoro kin fesa a idon ki."
Yak'e tayi tana tunani a zuciyar ta _kenan haka yace musu ni na fesa a idona kamar wata wacce bata son boko ba,_ tsaki tayi zuciyar ta cike da jin haushin sa.
Bayan sallar Azhar aka basu sallama bayan an d'ora ta kan magunguna.
⚡⚡⚡⚡

Yau satin Shukra biyu da tarewa a gidan Habib tana zaune a parlour tana charting yayi sallama ya shigo.
Mik'ewa tayi tare da yi masa sannu da zuwa ta karb'i jakar sa takai d'aki.

A zaune ta dawo ta same shi yana kad'a k'afa kamar yadda ya saba.
Kafin ta zauna ya dakatar da ita da fad'in "ke wai baki iya tarbar miji da ruwan sanyi ba ne?".
Marairaice fuska tayi alamun gajiya tayi hanyar kitchen ta d'auko ruwa da lemo ta ajjiye masa a kan center table.

Zaune ya mik'e Sosai ya kalle ta yace " kewai baki da tarbiya ne? Haka ake kawo ruwa babu Kofi?".
Tab'e baki tayi ta juya ta d'auko Kofi ta ajjiye ta koma ta zauna.
"Ke wai wace irin banza ce? Kina nufin ni zan zubawa kaina ruwan da hauka."
"Kai kai kai wallahi ni na gaji da wannan mulkin naka zuba lemon ma baza ka iya ba ni zanyi haba ka dinga saurarawa mana" ta fad'a tana zuba masa a Kofi.
D'auka yayi ya sha yana wani cin magani.
Yana gama shan lemon ya Mik'e ya shiga d'aki.
Da harara ta bishi tace "aikin banza komai sai anyi maka kamar wani sarki mtsw."
Yana shiga d'akin ya ganshi kamar yadda ya tafi ya barshi, rik'e k'ugu yayi tare da kwalla mata k'ira.
Cike sa fusata ta taso ta shigo d'akin tana fad'in "wai me zan maka ne?".
" Wai ke wacce irin k'arama ce Yanzu haka kika bar d'akin nan ko gyara babu?".
"To ya zan maka yau Dije bata da lafiya shiyasa bata gyara maka d'akin Ba."
"Ke Meye Anfanin ki da baza ki gyara ba sai dai wata mai aiki ta gyara? Ki shiga hankalin ki wallahi in ba haka ba zaki gane kuran ki, nizo ki cire min kaya zan yi wanka."
Wani banzan kallo tayi masa tace "Haba Malam dakata mana kayan ma ni zan cire maka kamar wani jariri to bazan iya ba."
"Ke kiyi hankali kar ki manta sadaka aka bani ke Dan haka duk abinda nake so sai kinyi min, ko ki cire min kaya kiyi min wanka ko kuma yanzu jikin ki ya fad'a miki."
Cike da b'acin rai ta yi abinda ya sata tana yi tana tsaki.
Tun a band'akin ya fara shafa ta yana wani murmushi, banza tayi masa kamar bata ji abinda yake yi, ganin yana k'ok'arin cire mata Riga yasa tace "kai wai in ba jaraba ba babu abinda ka iya ne?".
" kutumar uba ni kike kira jarababbe? Good zan nuna miki jaraba ganin idon ki wallahi yau sai kin kasa tafiya."
Bai jira mai zata ce fa ya fara romancing d'inta cikin zafi-zafi.
Ita kuwa zuciyar ta banda zafi babu abinda take mata, kawai sai ta fashe da kuka.
Bai kyale taba sai da yaga ko motsin kirki bata yi sannan ya kyale ta, kallan ta yayi yaja tsaki yace "ki kuma tashi ki dafa min abinci anjima abokaina zasu zo wallahi in kika yi mistake sai na Zane ki kuma wallahi yau da daddare kin shiga uku" yana gama fad'ar hakan ya shiga toilet.

Dak'yar ta mik'e tana hawaye ta koma d'akin.
⚡⚡⚡⚡

Fateemah kuwa koda suka koma gida  hana ta aiki Umma tayi tace sai ta samu sauki.
Shi kuwa Fa'iz koda ya fita ticket ya siya ya dawo gida ya had'a kayan sa ya wuce Dubai wajan Mamy Dan suna can itada Dady aiki ya rik'e shi.
Bayan sati biyu.

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_
    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_
*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.
*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»
*TUKWICI GA:-*
*Ummu Hanash, Innahoro, jikar Hajiya, maman Adnan, Sumy, Queen Abidat.*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.+

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
_kuyi hak'uri inajin korafin Ku Sosai akan na k'ara yawan typing,🀦🏻‍♀ insha Allah zanyi k'ok'arin ganin na k'ara din._

*SHAFI NA 21πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Fateemah taji sauki Sosai Dan har ta cigaba da aikin ta, sai dai duk inda take glass d'inta yana mak'ale a idon ta sabida in babu shi bata iya gani Sosai.

Cikin kwana kin taje gidan Baba sun jima suna hira kana tayi sallama ta dawo gida.

Shak'uwa mai k'arfi ta k'ara shiga tsakanin ta da Auta, makaranta ce kawai ke saka Auta ta bar wajan Fateemah.

Ranar Tuesday tana zaune a parlour ita kad'ai dan Umma na d'akin ta Auta kuma tana makaranta, Sam baji shigowar mutum ba sabida tayi nisa sosai wajan tunani.

Hard'e hannu yayi a kirji ya zuba mata ido, ji yake a jikin sa kamar ya tab'a sanin mai wannan fuskar, ajiyar zuciya yayi tare da lumshe ido yana tuno fuskar Fateeman sa.

K'arar wayar sace ta saka ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi, d'auko wayar yayi ya kashe kiran yana mai da ita aljihu.

D'ago ido Fateemah tayi ai kuwa cikin sa'a suka had'a ido dashi, saurin sunkuyar da kai tayi Dan ko kad'an bata k'aunar ganin fuskar sa duk da fad'uwar gaban da taji a duk lokacin da ta kalle shi.

Tsaki yayi tare da banka mata harara, cikin takun k'asaita ya hau sama zuciyar sa a cunkushe.

Yana bud'e d'akin wani daddad'an k'amshi ya bugi hancin sa, bai San time d'in da ya lumshe ido ba yana shak'ar k'amshi d'akin.

Ajjiye jakar hannun sa yayi ya fara cire kaya alamun wanka zai shiga, fasawa yayi ya zauna tare da Jan tsaki yace "ko uban me yasa na kasa mantawa da abinda nayi karuwar can oho, shegiya yarinya kamar aljana medical glass d'in ma kyau ya k'ara mata," tab'e baki yayi tare da fad'in, "duk dai kyaun ta nasan baza ta kama k'afar beauty na ba, Allah sarki beauty ko tana ina yanzu? Allah na rok'e ka kasa tana cikin k'oshin lafiya" jikin sanyi jiki ya mik'e ya shiga toilet.

Fateemah kuwa ya ta fashe da kukan rashin gata, yanzu da ace tana da gata ya aikata mata haka? Duk da dai iyayen sa basu San shi ya aikata hakan ba amma koda sun sani bazasu fifita ni ba sama da d'an su.

Cikin kuka take fad'in "Momy na kina ina? Ina zan ganki, Ina kake Yaya na mai sona da ace kana nan da duk wannan abun bai faru dani ba, Ku kad'ai ne gata na gashi kuma yanzu na rasa ku, bazan tab'a yafewa Suhail da Shukra ba duk sune silar rabuwa ta da Yaya na, ko yanzu wane hali yake ciki?" Ta fad'a tana fashewa da kuka Sosai.

Cire glass d'inta tayi ta goge idon ta tana fad'in "duk Wanda yayi rashin uwa a kusa dashi yayi babban rashi a rayuwar sa, ina sonki Momy na, ina sonka Yaya na nasan da sonku zan mutu".

STORY CONTINUES BELOW

Sosai kuka yaci k'arfin ta har muryar ta dashe, dafa ta Umma tayi daga baya ta zauna kusa da ita cikin tausayi tace " Mahaifiyar ki da Yayan ki sun rasu ne?".

Rasa me zata ce mata tayi kawai sai ta d'aga mata kai alamun Eh.

"Ayya Allah ya jikan su, amma ba kuka ya dace kiyi musu ba addu'a ce ta kamace su kinji?".

D'aga kai tayi alamun to, Umma tace " maza tashi kije ki Wanke fuskar ki ki kwanta ki huta."

Mik'ewa Fateemah tayi cikin sanyi jiki ta shiga d'akin da take kwana.

Da kallo Umma ta bita, ta rasa meyasa haka kawai take jin k'aunar Fateemah ba.

K'arar takun da taji ne yasa ta juya ta kalli wajan, cike da mamaki take kallon sa har mamakin nata yak'i b'oyuwa tace, "toh masu gudun hijira yaushe ka dawo?".

Sunan da ta kira shi dashi ya bashi dariya yace, " ko one hour banyi ba wanka kawai nayi na sakko, na shiga d'akin ki naga bakya nan" ya fad'a yana k'arasa inda take.

"Yanzu na fito nima sautin kukan Fateemah ne ya fito dani, ya su Mamyn naka?".

Dariya yayi Sosai yace, " Haba Hajiya Umma ki fad'i kawai abinda ke ranki, nasan Dady kike so ki tambaya ba Mamy ba, to ya nan kalau yace na fad'a miki ya kusa dawowa tunda dai kink'i ki bisu, wai Umma meyasa kika k'i binsu ne?".

"Karb'i nan" ta fad'a tana yi masa dakuwa, tace, "Kaji min yaro Mara kunya ina ruwan ka da dalilin zuwana Dubai? Wannan yaro ka maida dani uwa wata kakar ka."

Dariya yayi Sosai harda rik'e ciki har yaso bawa Umman haushi, dak'yar ya tsayar da dariyar yace, "To ki kwantar da hankalin ki Umma ta Dady na nan tafe zuwa jibi insha Allah, da dai yace zasu wuce Saudiyya amma sabida wannan cutar baza su ba sai komai ya lafa."

Rik'e baki Umma tayi yace "Ni jikar mutum hud'u wannan cuta sai dai mu dage da addu'a Allah ya kare al'umar musulmai, naji ance ko d'awafi ma ba'a yi kuma wai cikin alamomin ta harda ciwon ciki shiyasa jiya da Auta take ciwon ciki hankali na ya tashi Sosai."
"Injiwa yace miki ba'a d'awafi Umma? Anayi Sosai madina ne ba'a shiga ziyara sai lokaci zuwa lokaci, amma ka'aba ko ba'a d'awafi a k'asa to anayi a sama balle ma anayi a k'asan, ranar da ba'a yi a kasan ba wallahi Umma tsuntsaye ne suka dinga zage ta a Jere abin gwanin sha'awa Wallahi."

"Allah ya kyauta amma ni dai ina in tsoron ta Sosai."

"Yauwa babu ciwon ciki a cikin symptoms din coronavirus, abubuwan da ake gane itace na farko dai akwai zazzab'i mai zafin gaske da ciwon kai, mura, yawan atishawa, yawan gajiya, tari, zubar majina daga hanci, wani lokacin ma yarda ciwon kirji amma babu ciwon ciki a ciki."

Rik'e baki Umma tayi tana girgiza kai alamun gamsuwa da maganar sa, ya cigaba da fad'in,

"Kuma Umma ana so mutuma ya yawaita Wanke hannun sa da sinadari mai kumfa, ya killace kansa a gida a duk lokacin da bashi da lafiya, ya dinga amfani da mask lokacin da yake fama da tari ko mura, kada ya shiga kasuwa ko wani waje Wanda ya Tara mutane da yawa, kada mutum ya yawaita musabaha sabida In ya gaisa da mai cutar tsaf zai iya d'auka."

"Kai dallah tafi can kace likitancin naku har sunna Annabi Muhammad (S.A.W) yake son hanawa? Yo duk Wanda yace kar ayi musbaha ai ya haramta sunana kenan, wannan ai yahudanci ne".
Murmushi yayi yace " To ya za'a yi Umma duk cikin kare lafiya ne fa, amma duk da haka nima nasan wad'an nan turawan suna son su dak'ile masa sunna wani lokacin, amma dai wannan cutar ana d'aukar ta ta hanyar gaisawa sa mutane."

Umma tayi ajiyar zuciya tace "Allah ya kyauta ya kuma kare Al'umar Annabi baki d'aya."

Ya amsa da Ameen yana sunkuyar da kai, nan take yanayin fuskar sa ya canja ya koma alamun damuwa.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin kulawa Umma ta kalle shi tace, "Lafiya naga fuskar ka ta canja lokaci d'aya haka?".

Ajiyar zuciya yayi yace, " Umma dan Allah ki dinga taya ni da addu'a Allah ya baiyana min Fateemah ta, Wallahi Umma zuwa nan da wani lokaci indai banga Fateemah ba komai zai iya faruwa dani, Umma na rasa wanne irin so nake mata kawai daurewa nake nake harkokina."

Shafa kansa tayi tace, "Ka kwantar da hankalin ka Fa'iz bana so kana shiga damuwa haka, insha Allah za'a ga Fateeman ka har ma ka aure ta."

Murmushi yayi yace, "Allah yasa hakan, yau Umma na ta kira ni da sunan da aka rad'a min" ya fad'a yana y'ar dariya.

Itama Umma dariyar tayi ta mik'e ta hau sama.

Fateemah ma kuwa wani wahalallan bacci ne ya d'auke ta a d'akin, shigowar Auta d'akin da gudu ne yasa ta mik'e tana dafe kai.

Fad'awa kan gadon tayi tace, "Aunty Fateemah baki da lafiya ne?".

" A'a Auta kaina ke min ciwo amma shima yanzu zan sha magani."

"A'a ban yarda ba bara na sanar da Umma ta fad'awa Yaya na yazo ya duba ki ya baki magani" ta fad'a tana mik'ewa.

"A'a Auta bara in nasha p.c ma ya ishe ni basai an bani magani ba, zo ki bani labarin makaranta yau."

Zama tayi ta fara zuba tana bata labari Fateemah na dariya.

Washe gari.
Wani b'angaren garden ne mai kyau Sosai ko ina korayen grasses ne a wajan, banda iskar bishiya da kukan tsuntsaye babu abinda ake ji a wajan.

Fa'iz ne zaune a wajan yana danna laptop, sautin kuka ya dinga ji daga nesa dashi, mik'ewa yayi da sauri yana bin hanyar da yake jin wannan kukan har ya k'arasa inda ake yi.

Wata budurwa ce a zaune a wajan ta had'a kai da guiwa tana kuka, tsugunawa yayi a gaban ta yace, "Yarinya lafiya kike kuka haka?".

Cikin murya mai dad'in gaske amma cikin kuka tace, "Ban San inda Momy take ba, kuma Yaya na da nake so shima na rasa shi."

Da kallo ya bita yana so ta d'ago fuskar ta amma taki, hannun ta yabi da kallon nan idon sa ya sauka akan zoben hannun ta.

Zaro ido yayi ya rik'e hannun ta cikin rawar murya yace, "Su..nan..ki Fateemah? A k..ano kike?".

D'aga masa kai tayi amma still bata d'ago kanta ba, rik'e kafad'ar ta yayi yana fad'in, Beauty ki d'ago ki kalle ni nine Yayan ki gani a gaban Dan Allah ki d'ago naga fuskar ki" duk a rud'e yake wannan maganar.

A hankali ta fara d'ago fuskar ta, shi kuma ya zuba mata ido so yake kawai yaga ta d'ago.

A guje Auta ta shiga d'akin ta fad'a kan gadon tana fad'in, "Yaya na kazo ka kaini makaranta."

A firgice ya mik'e yana kallon d'akin zuciyar sa na bugawa da sauri, cikin masifa yace, "Baki da hankali ne da zaki shigowa mutane d'aki ko sallama babu? Haka kawai kinzo ki katse min bacci."

Jikin tane ya fara rawa da bata saba da tsawa ba, cikin sanyi jiki ta mik'e tana share hawaye ta fita daga d'akin.

Tsaki yayi yace "wannan yarinyar ta Katse min mafarki na da tuni naga fuskar Fateemah ta," ya fad'a yana dafe kai.

"Ni ba masanin fassarar mafarki bane amma duk da haka zan iya gane wani Abu a cikin Wannan mafarki, hakan na nufi Fateemah na cikin wahala kuma tana kusa dani, ya salam ina zan ganki Faty na?".

Tunani kala-kala yake tayi dole yau ya fita Neman Fateemah ko inane indai ba so yake ya kashe kansa ba.

Da Wannan shawarar ya d'auki waya ya kira ya kara a kunne, " Amir ka daure yau ka shigo Abuja Dan Allah. "

STORY CONTINUES BELOW

Shiru yayi alamun ana bashi amsa, yace "Ok Allah ya kawo ka".

Yana kashe wayar ya mik'e ya shiga toilet Dan yau ko asibiti bazai shiga ba.

Bayan ya fito ya shirya cikin k'ananun kaya Wanda suka amshi jikin sa Sosai ya zaune a d'aki.

Umma ce take k'wallawa Fateemah kira, da sauri ta fito tana gyara zaman glass d'inta.

" Yauwa maza d'auki abincin nan ki kaiwa Fa'iz kila dai fad'a suka yi da Auta naga sai kuka take."

Murmushi Fateemah tayi tace "ita da Yayan ta yau akayi fad'a lallai" ta fad'a tana d'aukar tire d'in.

Umma tace, "kema kya fad'a ina mamaki abin ya bani Dan ko harara baya so ayi mata."

Bata ce komai ba sai hawa saman da ta fara gaban ta na fad'uwa.

Da sallama ta tura k'ofar parlourn ta shiga, yana zaune a parlourn remote ne a hannun sa yana canja tasha.

Amsawa yayi ba tare da ya d'ago kansa ba, ajjiyewa tayi ba tare da tayi magana ba ta juya zata koma.

"Ke baki iya gaisuwa bane?" Ya fad'a kamar bashi yayi maganar ba.

D'an tsaki tayi Dan ita bata k'aunar abinda zai had'a ta dashi, tace "ina kwana."

"Rik'e kayar ki karuwa kawai."

Cikin takaici tace "ni Wallahi ba karuwa bace kar ka k'ara cemin karuwa."

Sai a lokacin ya d'ago kai tare da d'age gira d'aya yace "Really?".

Tsaki tayi tace "oho."

Cikin b'acin rai ya mik'e yana nuna ta da yatsa yace "ni kike yiwa tsaki? Iskancin  har ya kai haka kenan, baki daddara da abinda ya faru bako? Shikenan naga da abinda zaki fita daga d'akin" ya fad'a yana cire glass d'in fuskar ta.

Saurin rife ido tayi tana ja baya a hankali, komawa yayi ya zauna ya kallon ta yana so yaga ta yarda zata fita daga d'akin babu glass tunda a cewar sa ta zama makauniya.

Fateemah kuwa k'ofar ta kalla taga tayi mata nisa sosai, haka ta shafa wajan har taji handle d'in ta bud'e ta fita daga parlourn duk da hanyar ta canja mata gabad'aya, gashi Auta bata nan balle tace ta d'auko mata wani a d'aki.

A hankali take bin wajan duk inda taga yayi mata nisa sai ta dinga shafawa da hannu, wajan matattakala ta k'araso ta kalli wajan, can nesa ta hango wacce zata taka Dan rage Nisan wajan tayi ta hanyar saka k'afar ta a tunanin ta ta taka dai-dai.

Tana takawa ta tafi gabad'aya ta dinga gangarowa daga saman tana ihu, Umma take zaune a parlour taga yadda take fad'owa daga sama cikin tashin hankali ta mik'e mma kafin ta k'arasa har tazo k'arshe.

Da gudu Umma ta k'arasa wajan tana kiran sunan ta amma ina Fateemah ko motsi bata yi sai jini dake zuba daga kanta kamar an yanka akuya.

Fa'iz dake zaune a parlour yaji ihun ta da sauri ya mik'e ya fito, tana lek'o kansa yagan ta a kwance a k'asa jini na zuba Umma na kusa da ita tana hawaye.

*COMMENTS & SHARE.*

*© NEAT LADY.*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_
    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_
*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.
STORY CONTINUES BELOW

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
Allah ya sani har cikin raina ina jin dad'in comment's dinku😍 Allah ya saka da alkairi❤.

*SHAFI NA 22πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Bai tab'a jin yayi nadamar abinda ya ke aikata mata ba sai yau, da sauri ya sakko bai tsaya sauraran Umma ba ya d'auke ta cak sai mota ya bar gidan a guje.

Auta ta kalli Umma tace, "Umma wallahi Yaya ne ya kwace mata glass d'inta yace yaga da abinda zata iya tafiya."

Juyowa Umma tayi tace "ya akayi kika sani?."

"Umma lokacin da ta hau saman bana fita ta baya ba? To ai ta step din baya na hau waini iso naje kila a gaban Aunty Fateemah mu shirya shine naji yana fad'ar hakan."

Ran Umma ya b'aci ta tace, "D'auko hijjabin ki muje asibitin nasan bazai wuce asibitin sa ba."

D'aki ta shiga ta d'auko hijjabi driver ya d'auke su suka tafi asibitin.

Fa'iz kuwa gudu yake Sosai kamar zai tashi sama sabida Fateemah ko numfashin kirki bata yi, hankalin sa ya k'ara tashi tunanin sa kar ya kashe yarinyar mutane.

Koda suka isa asibitin da sauri suka amshe ta sabida yadda suka ga halin da take ciki, taimakon gaggawa aka shiga bata k'ok'arin tsaida jinin aka yi sannan aka shiga duba inda ya samu matsala a jikin ta.

Koda su Umma suka iso a k'ofar d'akin suka zauna suna tunanin halin da take ci, Auta kuwa kuka take Sosai tana jin haushin Fa'iz sabida duk shi yasa Fateemah halin da take ciki.

"Waye bashi da Lafiya ne?" Muryar Dady suka ji yana tambayar likitan.

Da sauri Auta ta mik'e taje ta rungume shi tana kuka, d'ago kanta yayi yace, "Amina fad'a min waye bashi da Lafiya ne?".

" Dady Aunty Fateemah ce baka ga yadda jini yake zuba a kanta ba."

Da alamun son k'arin bayani ya kalli Umma yace, "wace kuma Fateemah? Dawowa ta kenan ina zuwa akace min kun tawo asibiti."

"Dady ina Mamy?".

"Ta wuce gidan granny dinki Dadyn tane bashi da lafiya itama, wai yanzu wai wacece Fateemah?."
Kafin su bashi amsa Fa'iz ya fito yana cire hand glove's, da mamaki yake kallon Dady yace, "Dady daukar yaushe?".

"Ba Wannan ne ya same ni ba Fa'iz wacece Fateemah? Meye ya same ta?."

"Dady muje office sai ayi maganar a can".

Tare suka tafi office d'insa suka zauna, Dady yace " ina jinku."

Umma ta kwashe labarin komai ta fad'a har samun matsalar idon ta, Kafin wani yayi magana Auta tace, "Kuma fa Dady duk Wannan abun Yaya Fa'iz ne yayi mata kuma yana sane."

Cike da mamaki Dady yace, "Haba Amina ya za'a yi Fa'iz ya aikata hakan yana sane?".

" Wallahi Dady shi yayi mata kuma shima ya sani da bakin sa naji yana fad'a mata."

Kallan sa Dady yayi yaga ya sunkuyar dakai alamun rashin gaskiya, Dady yace, "Haka ne?".

K'arya bata cikin halin Fa'iz hakan yasa ya amsa da eh.

Sai kuwa Umma ta mik'e ta inda ta shiga bata nan take fita ba fad'a kawai take.

Ran Dady ya b'aci sosai yace, " Kawai sabida mugunta da zalinci sai ka aikatawa yarinya wannan mummunan aikin? Kuma da ace Amina bata fad'a shikenan kayiwa banza ko?, dan kaga bata da gata kai yanzu in wani yayiwa Amina haka zaka ji dad'i? Da yake ita kaga housemaid ce shiyasa kake yi mata Wannan wulak'ancin? Yayi kyau ka kyauta " Dady yana gama fad'ar hakan ya mik'e ya fita daga office d'in.

STORY CONTINUES BELOW

Umma ma mik'ewa tayi tabi bayan Dady ranta a b'ace Sosai.

Wajan abokin Fa'iz suka shiga Wanda suka fito daga d'akin tare, Dady yace, "Fad'a min halin da yarinyar take ciki".

Dr ya kalli Dady yace, " A Gaskiya Dady tana cikin sauri wani hali domin maganar da nake muku yanzu jini ya shiga cikin brain d'inta Sosai, Allah yasa Fa'iz yana gari tunda yafi kowa kwarewa yace gobe za'a yi mata aiki a kwashe jinin, matsalar d'aya ce in an kwashe bamu da tabbacin zata dawo dai-dai kila tayi losing memory, ko kuma brain d'inta zata iya tab'uwa ma'ana dai baza dawowa ita ba mai hankali ba ita kuma ba Mara hankali ba, ko kuma ta dawo normal cikin ukun nan Dole ayi d'aya amma guda biyu farko sunfi faruwa ga irin Wanda ya samu irin ciwon ta gaskiya, addu'a zamu dage da ita insha Allah zata dawo normal. "

Ajiyar zuciya Dady yayi cike da tausayin Fateemah duk da bai tab'a ganin ta ba, Umma tayi shiru hawaye ya taru a idon ta sabida tausayin Fateemah.

Jikin sanyi jiki suka fito daga office d'in suka shiga d'akin da Fateemah take kwance.

Kwance take a kan gado an d'aure mata kai da bandage tana saukar da numfashi a hankali.

Dady ya kalli Umma yace, Ashe ma yarinya ce k'arama. "

Umma dai ta kasa magana sai dai kawai ta daga kai.

Baba mai waina ce ta shigo d'akin Ita da Inna Harira, gaisawa suka yi dasu Dady ta kalli inda Fateemah take a kwance ta share hawayen ta bace komai ba.

Umma tayi k'arfin halin cewa "Kiyi Hak'uri Baba insha Allah zata samu sauki ta dawo kamar ba ita ba."

Baba tace "Allah yasa, amma Hajiya in ta warke zata daina Wannan aikin ta dawo gabana da zama mun yafe aikin, yarinyar nan tun tana k'arama take shan wahala a rayuwar ta bazan jure ganin ta cikin damuwa ba gaskiya."

Inna Harira tace "Gaskiya dai gwara ta dawo tunda dai aikin gidan bai amshe ta ba."

Umma dai tana yi shiru bata ce komai ba, Dady yace "Allah ya kaimu ta samu lafiya komai ma ya biyo baya."

Fa'iz kuwa suna fita ya kifa kansa akan table, kallan sa Auta tayi duk da son da take yi masa Yanzu ji take tafi k'aunar Fateemah akan sa.

Mik'ewa itama tayi zata fita taji muryar sa yace, "Yaushe kika k'ware wajan gulma ban sani ba Auta?".

Gaban ta ya fad'i Dan ba k'aramin tsoron sa take ji ba, shiru tayi bata amsa ba.

D'ago kansa yayi ya zuba mata ido yace "Dake nake magana."

Cikin rawar murya tace, "Kayi Hak'uri bazan sake ba". Tsaki yayi ya mik'e yazo inda take ya zare mata ido yace, " Yayi miki kyau tunda kin fifita y'ar aiki a kaina jeki wajan ta."

"Dan Allah Yaya kayi Hak'uri b....."

"Nace ki fita ko?" Cikin sauri ta fita daga office d'in.

Tana fita ya jinginar da kansa da bango yana tunani, bai San meyasa ya damu da halin da Fateemah take ciki ba, ji yake yana jin haushin kansa Dan gane da abinda ya aikata mata.

Ajiyar zuciya yayi ya koma ya zauna komai ya jagule masa ya rasa inda zai saka ransa.

Dady kuwa waya ya d'auka ya kira Mamy inda take shaida masa zasu wuce Sokkoto ita dasu Dadyn ta sabida jikin sa yayi zafi kuma a can likitan sa yake aiki kafin ace ya tsallake aikin sa yazo Abuja komai zai iya faruwa gwara suje can d'in, izinin zuwa ya bata suka gaisa da Umma tayi mata ya mai jiki suka yi sallama.

Mik'ewa Dady yayi ya tafi gida Dan yana so ya d'an huta .

Umma bata tafi ba sai bayan sallar i'sha inda ta bar Inna Harira da Baba wajan ta .
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari da wuri aka fara shirin yi mata aiki Fa'iz kawai ake jira, duk Wanda ya kalli Fateemah sai ya tausayawa mata sabida yadda kanta ya kumbura.

Fa'iz kuwa duk wani irin haka yake jin sa Daren jiya bai samu wani baccin kirki ba, ciki a sanyaye yake komai gashi Umma da Dady haushin sa suke ji ko kula sa ma basa yi.

Shiryawa yayi ya d'au key d'in mota ya fita daga gidan.

Koda ya isa asibitin har an shigar da ita shi kawai ake jira, yana zuwa kuwa ko office bai shiga ba ya wuce d'akin, shi kansa lokacin da yayi arba da ita sai da gaban sa ya fad'i tausayin ta da Dana sani suka taru suka yi masa yawa, babu b'ata lokaci aka fara.

Basu fito ba sai da suka d'auki ki manin awa biyu sannan suka fito, a bakin d'akin suka yaga su Umma a zaune da alama tun jima da zuwa.

Umma tace "Ya akayi ya jikin nata?".

Fa'iz yace " Anyi aiki lafiya sai jiran farkawar ta, addu'a take buk'ata dan zata iya farkawa cikin hali uku, ko ta manta komai nata ta dawo kamar jaririn da aka Haifa yanzu, ko kuma ta dawo..."
Umma ta d'aga mata hannu tace "duk nasan da Wannan Allah yasa ta farka Lafiya, nan da awa nawa zata farka?".

" Nan da kamar awa d'aya insha Allah."

Komawa Umma tayi ta zauna kusa dasu Baba.

Tun safe har akayi sallar azahar shiru Fateemah ko motsi bata yi ba, hankalin su Baba ya tashi tsoro ya cika musu zuciya.

Umma da kanta ta fito ta shiga office d'in Fa'iz shima lokacin yana k'ok'arin fitowa.

"Umma lafiya na ganki haka?".

"Ina fa lafiya kace yarinya awa d'aya zata farka gashi tun k'arfe goma na safe har uku tayi amma ko motsi bata yi ba."

"Kada ki damu Umma zata farka da yardar Allah, muje d'akin na ganta."

Tare suka d'akin dai-dai lokacin da Fateemah ta fara motsa idon ta.

Fa'iz ne kawai ya lura da hakan da sauri ya k'arasa wajan ya tsaya yana jiran farkawar ta.

A hankali take bud'e idon ta har ya bud'e gabad'aya, da yake babu glass a fuskar ta bata ganin su waye a cikin d'akin.

Ganin ta bud'e ido yasa Umma tayi hamdala ta bud'e jakar ta ta d'auko glass ta k'arasa wajan ta ta saka mata.

Da Fa'iz ta fara had'a ido a hankali komai yake dawo mata, juyawa tayi ga kalli Umma tace, "Umma zan sha ruwa."

Gabad'aya d'akin aka furta Alhamdulillah.

Lumshe ido yayi shima tare da sauke Ajiyar zuciya, da sauri kuwa Umma ta Mik'e aka bata ta kuskure bakin ta sannan tasha.

Baba ta k'arasa wajan ta tana yi mata sannu.

Da taimakon Baba ta mik'e zaune tana dafe kai sabida yadda take ji yana Sara mata.

Kallan Baba tayi tace "inaso nayi wanka bana jin dad'in jiki na Yanzu" ta fad'a tana cize baki.

Kallan sa Baba tayi tace likita ta iya yin wanka yanzu?".

Idon sa ya mayar kan Fateemah da idon ta yake a lumshe yace, "A'a badai yanzu sabida yanzu ko ance ta tsaya a tsaye baza ta iya ba sabida ciwon dake kanta".

Bud'e ido tayi ta kalle shi kawai sai hawaye suka fara zuba daga idon ta.

Jikin sa yayi sanyi dak'yar yaja k'afar sa ya fita daga d'akin.

Baba ce ta share mata hawayen tace, " Kiyi Hak'uri kinji Uwa ta daga rana mai irin ta yau baza ki kuma aiki a ko ina ba gwara ki dawo gida da zama Wanda kika yima Allah ya bada lada.

STORY CONTINUES BELOW

Abinci Umma ta zuba mata dak'yar taci kad'an tace ya ishe ta.

Fa'iz kuwa abin duniya yayi masa zafi gabad'aya ya rasa tunanin ma me zaiyi.

Bayan kwana d'aya.

Babu laifi dai jikin Fateemah ya d'an yi sauki amma ba Sosai ba tunda Yanzu takan iya mik'ewa ta zauna ba tare da an taimaka mata ba.

B'angaren Mamy kuwa jikin Dadyn ta yayi sauki Sosai dan har sun kusa dawowa.

Fateemah ce zaune a kan gado ta da hijjabi a jikin ta, Umma tayi tsaki tace, "bara kawai na kira Fa'iz tunda yana gida ya shiga d'akin ki ya d'auko miki kayan da zaki saka" ta fad'a tana kara waya a kunne.

Tana gama sanar dashi ta kashe wayar, bin wayar yayi da kallo tare da fad'in, "Ban da abin Umma ni ina nasan d'akin nata ba balle nasan inda kayan ta suke?".

Haka ya fito daga d'aki ya sauko k'asa, d'aya daga cikin y'an aikin ya tambaya ta nuna masa ya shiga.

Tunda ya bud'e k'ofar k'amshi mai dad'i ya bugi hanci sa bai San lokacin da ya lumshe ido ba.

Bin d'akin yayi da kallo, d'aki ne mai d'auke da gado irin na y'an boarding sai wadrop mai biyu sai d'an k'aramin mirror, ko ina tsaf kamar ba'a kwana a d'akin.

A hankali ya taka ya bud'e wadrop d'in, k'amshi tararen wuta ya bugi hancin sa Dan Fateemah akwai turara kayan ta da turare mai k'amshi, kayan ta ne a shirye a ciki rasa Wanda zai d'auka yayi kawai sai ya hango wata atampa a can k'asa, bai tsaya tunanin komai ba kawai ya jayo ta.

Wani d'an k'aramin littafi ya ne ya fad'o daga k'asan Atampar, d'auke littafin yayi har zai mayar sai yaji yana sha'awar bud'ewa.

Ajjiye kayan yayi ya koma bakin gado ya zauna tare da bud'e shafin farko na littafin inda yayi tozali da pic d'inta tana k'arama kamar yadda ya Santa.

Kurawa pic d'in ido yayi zaro ido yayi tare da saka hannu ya murza idon sa, tabbas abinda ya gani gaskiya ne beautyn sace.

Jikin rawar jiki yake bud'e sauran Page's d'in yana karantawa zuciyar sa sai harbawa take da sauri, kafin kace me hawaye ya fara zarya a idon sa dai-dai lokacin Ya bud'e tsakiyar littafin inda yayi tozali da zoben da ya bata da kuma abinda ta rubuta kamar haka,

_Ina ka shige ne ka daure ka dawo gare ni Yaya na duniya tayi min zafi bani da Wanda nake so na gani sama da kai, I love u too Yaya._

Jefar da littafin yayi jikin sa na rawa Sosai ya fita daga d'akin da gudun tsiya.

*TOFA*πŸ€”πŸ€”

*COMMENTS SHARE.*

*© NEAT LADY.*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

STORY CONTINUES BELOW

_Aradul Allah kuna burge ni masoya na._πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

_Ban tab'a sanin inda masoya ba sai da aka gabatar da Wannan zab'e na fidda gwani, Neat Lady taga masoya kamar ita kad'ai ce writer😊 da Wannan dama zanyi amfani na gode muku duk da bani da bakin godiya gare Ku, Allah ya bar k'auna😍 Allah y bar zumunci, nagode Sosai.❤πŸ’ƒπŸ»_

*SHAFI NA 23πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Mugun gudu yake zubawa a kan titi sai over talking yake kowa ya ganshi kauce masa yake Dan tunanin su bashi da hankali.

Bai tsari kulle motar ba yana tsayawa ya fito da gudu yayi ciki, kowa sai mamakin sa yake Dan ba'a tab'a ganin sa cikin Wannan hali ba.

Da k'arfin gaske ya bud'e k'ofar Fateemah na zaune kan sallaya da alama sallah ta idar.
Bai tsaya b'ata lokaci ba iya wajan ta da sauri yana zuwa ya zube guiwowinsa ya zuba mata ido, ba k'aramin tsoro ya bata ba sai ja baya take a hankali.

Kasa magana yayi sai girgiza kai da yake yana cije baki hawaye na zuba a idon sa.

Ganin abun nasa bana k'are bane yasa Umma ta daka masa tsayawa tace, "kai wai lafiyar ka ina Aiken da nayi maka?".

Dafe kirjin sa yayi ya zauna a k'asa yana numfashi sama-sama yace, " Beauty."

Yadda ya fad'i beauty d'in yasa tayi sauri d'ago wa tana kallon sa, had'a ido suka yi tayi saurin d'auke idon ta gaban ta na fad'uwa.

Cikin wata irin murya yace, "Beauty na ko baki gane ni bane? Meyasa kika tafi kika barni meyasa Fateemah, kin San halin Dana shiga kuwa? Meye dalilin ki nak'in sanar dani kece Fateemah ta!" Ya fad'a cikin k'ara ji tare da rik'e kafad'ar ta.

Ido ta zuba masa zuciyar tana son k'arya ta abinda taji yana fad'a, ganin kamar Yanzu bata gane abinda take nufi ba yasa yace,

"Beauty kar kice kin manta da yayan ki na kano, beauty kada kice kin manta da masoyin ki tun kina k'arama, beauty kada kice kin manta da Wanda ya baki zobe shekara goma sha d'aya da suka wuce, kalle ni Fateemah nine nan Yayan ki nine ba mafarki kike ba nine" ya fad'a yana jijjiga ta.

Zuba masa ido tayi nan take kamanin sa suka fara dawo mata cikin kwakwalwa, tabbas shine Yayan ta, cikin rawar murya tace, "Yaya nah Kaine?".
" Eh nine beauty ki yarda dani" ya fad'a yana rungume ta a jikin sa.

Jikin ta yayi sanyi ji take kamar mafarki take, rik'e shi itama tayi gam ta fashe da kuka mai tsuma rai tace, "Me yasa kaki dawowa gare ni? Kasan halin Dana shiga kuwa bayan barin ka kusa dani me yasa."

Ba tare da ya d'ago ba yace, "Na dawo beauty lokacin Dana koma akace min ko awa biyu baki yi da barin gidan ba, Fateemah nayi kukan rashin ki Wanda ban San adadin sa ba ina son ki Fateemah in ban same ki ba zan iya rasa rayuwa ta."

Umma da Baba mai waina sunyi shiru suna kallon ikon Allah babu abinda ake ji a d'akin sai sautin kukan Fateemah dana Fa'iz.
Had'iye kukan ta tayi tare dasa iya k'arfin ta ture shi daga jikin ta, mik'ewa tsaye tayi tana kallon sa tare da tab'e baki tace,

"Wannan shine son da kake cewa kana yi min? Na farko kayi min k'azafin zina na biyu kayi k'ok'arin makantar dani na uku kayi k'ok'arin kashe ni har lahira, Wannan shine son? Banga so ba anan da dai nasan kana sona amma yanzu bazan tab'a yarda dakai ba."
"Da kyau kin burge ni kin nuna min ke y'a mace ce mai aji, ai ko kin amince bazan tab'a bari ya aure ki ba tunda ba sonki yake ba, zo ka fita ka bawa mutane waje" Umma ta fad'a tana nuna masa hanyar fita.
Bai kula Umma ba ya yayi kneel down tare da had'e hannun sa waje d'aya yace, "ki yafe min Fateemah Wallahi tallahi ban son ke bace da nasan kece ko k'uda ba zan bari ya hau kanki ba, Fateemah kullum sai nayi kukan rashin ki bani da tunanin kowa sai naki, kada ki juya min baya a lokacin da nake buk'atar ki, kada kisa zuciyar dake k'aunar ki tun kina yarinya cikin wani hali, wallahi zuciya ta zata iya fashewa in kika yi nesa dani a yanzu bazan tab'a iya jure rashin ki ba, dan Allah ki yafe min nasan ni mai laifi ne a wajan ki, ki yafe min" ya k'arasa maganar da kuka mai k'arfin gaske.

STORY CONTINUES BELOW

Jikin ta yayi sanyi k'alau ta kasa furta Kalmar da take son furtawa, kafin Fateemah tayi magana Umma tace,

"Fa'iz in har ka d'auke ni a matsayin mahaifiyar ka kazo ka fice ka bamu waje" ta fad'a cikin b'acin rai.
Babu yadda ya iya haka ya mik'e yana dafe kai sabida yadda yake masa ciwo ya fita daga d'akin yana waigen ta.
Tsaki Umma tayi ta dugawa Dady waya ta sanar dashi duk abinda ke faruwa, Dady yace da Umma ta karb'i sallama su tawo maganar baza ta yu a asibiti ba.

Haka kuwa akayi ta Dole likitocin suka bada sallama badan Fateemah ta warke ba sabida kawai mahaifiyar ogan su ce ta so hakan .
Fa'iz kuwa kamar wani d'an maye haka yake tafiya yana dafe kai, baya yayi kamar zai fad'i yaji an taro shi.
Amir yace "Subahanallah Fa'iz lafiya Me ya same ka?" Ya fad'a yana rik'e shi.

Babu abinsa yake furtawa sai Fateemah yana nuna masa hanyar d'akin.

"Me Fateeman tayi? A ina ka ganta?" Amir ya tambaya a rud'e.

Babu inda yake nunawa sai d'akin, hakan yasa Amir rik'e shi suka shiga mota ya bar cikin asibitin.

Koda suka isa gidan ta lifter suka hau saman Dan Fa'iz d'in ya koma kamar wani sabon kamu.
Zaunar dashi yayi tare da fita daga d'akin, Jim kad'an ya dawo shida wani akayiwa Fa'iz allurar bacci.

Kallon sa Amir yayi cike da tausayi ya kalli Dr yace, "Soyayya tana Neman mayar da Fa'iz mahaukaci."

Dr ya girgiza kai cike da tausayin sa yace, "So sai a hankali in ya kama mutum kafin ya barshi sai an jima, Allah ya bashi wacce yake so sai anjima" ya fad'a yana fita daga d'akin.

Zama yayi a bakin gadon yana kallon fuskar abokin nasa zuciyar sa cike da tausayin sa.

⚡⚡⚡⚡
"Yanzu Suhail baza ka rage Wannan damuwar akan Fateemah ba? In Allah yayi rabon kace sai kaga duk inda take ta dawo gare ka in kuma ba rabon ka bace Duk abinda za'a yi baza ka aure ta ba."
Runtse ido yayi zuciyar sa nayi masa zafi yace "Momy da ace nasan inda ake cire so dana cire na Fateemah na huta, Momy bana iya bacci sai da hoton ta a kirjina, zuciya ta a koda yaushe zata iya bugawa."
Ajiyar zuciya tayi cike da tausayin Suhail tace, "kar ka damu insha Allah rabon kace."
Likitan dake tsaye yace "Hajiya in baza ki damu ba inaso na Baku shawara."
"Ina jinka".
" Akwai wani likita a Abuja masanine Sosai akan aikin sa kamata yayi Ku d'auki Suhail Ku kaishi can domin a magance matsalar da zuciyar sa ke k'ok'arin kamuwa, in kuka je zai bashi magungunan da ya dace wajan yak'i da Wannan ciwo dake son kama shi, bance ya kamu da ciwon zuciya ba amma yana gab da kamuwa, in kuje Abuja kuje Fa'iz special hospital me asibitin shine zai duba shi Hajiya yasan aikin sa Sosai, amma shawara ce."
Momy tace " Ai dole ma Dr dole yanzu bara Dadyn su ya dawo a siyo mana ticket gobe ko jibi Sai mu wuce can Allah yasa dai ya kula mu ko kuma muje baya nan."
"Bashi da wulak'anci ko kad'an Hajiya kuma yana gari ko jiya munyi waya da P.A d'insa, Allah ya k'ara Lafiya" ya fad'a yana had'a kayan sa ya fita.

Koda Dady ya dawo tayi masa bayani ba'a tsaya b'ata time ba aka tafi siyo ticket.
Shukra kuwa banda wahala babu abinda take fuskanta a gidan mijin ta Habib, gashin dangin mijin ta ko kad'an basa son ta kullum cikin zagin ta suke, haka ce ta faru tana zaune a parlour tana cin abinci wata budurwar yarinya ta bankad'o labuben d'akin ta shigo tana taunar cingom.
STORY CONTINUES BELOW

Kallan sama da k'asa tayiwa Shukra tace, "Ke banza ina Yaya nah yake?".

Tsaki Shukra tayi tace " Ajiyar sa kika bani da zaki kina min surutu a ka."
"Kut ni kike fad'awa haka Dan uwar ki? Kin manta lik'a masa ke akayi kinyi kwantai babu mashinshini shine zaki zo kina fad'a min wannan maganar."
"An fad'a miki d'in kiyi duk abinda zakiyi Dan uwar ki shegiya gadon matsiyata."
Bud'e baki yarinya tayi cikin d'aga murya tace "Maman tamu kike fad'awa haka Dan baki da kunya? Maman mu fa?".
Ba tare da fargabar komai ba Shukra tace " Maman naku fa uwa tafi uwa ne?."

"Tabbas uwa bata fi uwa amma zan nuna miki nid'in dangin matsiyata ne" Habib ya fad'a yana fitowa daga d'akin.

Juyowa Shukra tayi tace "ka tsaya ka fuskanci maganar kafin ka yanke hukunci, itafa ta fara zagin tawa uwar k........" Kafin ta k'arasa ya d'auke ta da mari har sai da ta kifa, kafin ta d'ago ya fara jibgar ta sa belt.

Sai da yayi mata lis a gaban k'awar sa sannan ya kyale ta suka fita shida k'anwar sa suka barta a wajan.

Kuka Shukra take Sosai tama rasa abinda ke damun ta, dak'yar ta Mik'e ta shiga d'aki.

⚡⚡⚡⚡
Su Umma kuwa koda suka dawo gida d'aki Fateemah ta shiga a nan ta tarar da diary d'in ta, tsugunawa tayi dak'yar ta d'auke tana hawaye.

Tabbas in tace bata son Fa'iz tayiwa kanta k'arya kuma ta cuci kanta amma baza ta iya auran Wannan sam bai San mutuncin d'an Adam ba, a wajan ta zauna tana kuka Sosai kamar ranta zai fita.
Wajan shud'ewar minti talatin Dady ya shigo parlourn, zama yayi ya kalli Umma yace, "ina Fa'iz d'in da Fateeman suke?".
Mik'ewa Umma tayi ta shiga d'akin Fateemah, a zaune ta ganta ta jinginar da kanta a jikin gado hawaye na zuba a idon ta, cike da tausayi Umma ta kalle tace, " Faty kizo parlour ana jiran ki" tana gama fad'ar hakan ta juya Dan ita ta cigaba da kallon Fateemah zata iya yin kuka.
A hankali ta mik'e ta fito parlourn tana dafe kai, a kan carpet ta zauna tana sunkuyar da kai, Amir ne ya taimakawa Fa'iz suka sauko k'asan suka samu waje suka zauna.
Dady ya kalli Fa'iz cikin tausayawa yace "Fa'iz Wannan itace Fateeman da kake kuka akan ta kullum?".

D'aga kai yayi tare da zuba mata ido.
Dady ya kalli Fateemah yace " Fateemah Wannan shine Wanda kuka baru tun kina yarinya?".

D'aga kai tayi alamun eh, Dady yace "to tashi kije zan kira ki."

Mik'ewa Fateemah tayi ta shiga d'aki.
Dady ya kalle shi yace, "Fa'iz kaga illar wulak'anta mutum ko? Gashi kazo ka wulak'anta wacce kake so har da yunk'urin hallaka ta Yanzu me gari ya waya? Kana ganin duk son da yarinyar take maka in ta tuno Wannan abun da kayi mata zata iya jin ta tsane ka, yanzu ya kake so ayi."
Shiru yayi baice komai ba ya sunkuyar da kai hawaye na zuba a idon sa, Dady yace "da kai nake magana fa".
Nan ma babu amsa sai sunkuyar da Kai da yayi, Amir ne yayi k'arfin halin cewa "Hak'uri za'a Dady kaga bai San ita bace."
"Ok sai kasan mutum daman kake girmama shi? A takaice ma ita Fateeman y'ar inace?".
Gyara zama Fa'iz yayi bai b'oyewa Dady komai ba akan Fateemah ya sanar dashi, sai dai Dady ya gama saurara yayi murmushi yace, " Yaro man kaza Yanzu kai daman akan Wannan y'ar yarabawan kake wahalar da kanka haka? To abinda zai fi maka sauki shine ya cire ta a ranka dan ni ban zan laminici ka auri wacce bata da asali ba kuma sabon buta bazai yu ba."
STORY CONTINUES BELOW

Cikin shak'ewar murya yace "Dady tana da asali wallahi mahaifin ta....."
"Dakata Fa'iz kome zaka fad'a min bazan tab'a harda ba," cikin kakkausar murya Dady ya mik'e yace, " Umarni nake baka ba shawara ba ka cire wannan yarinyar a ranka da Baku dace ba kota asali balle kuma ta ....."
"Haba Dadyn Auta bai kamata ka dinga fad'ar Wannan maganar ba, kada ka manta talaka da mai kud'i Allah ne yayi su, bayarabe bahaushe, duka suna hallitar Allah ne, kuma dai tunda Allah yasa yarinyar nan musulmace ai banga aibun hakan ba."
"Dakata bana so ki k'ara yi min wata magana hukunci ne na Riga na yanke babu Wanda ya isa yasa na canja."

Da sauri Fa'iz ya rik'e k'afar Dady yana fad'in, "Dady ka ceci rayuwa ta ka amince na auri Fateemah Wallahi rasa ta dai-dai yake da rasa raina Dady, Dan Allah ka tausayawa min."
Auta dake zaune a gefe tace "Dan Allah Dady ya kyale sa ya aure ta d'in."
Cikin tsawa Dady yace "Baza ka aure ta ba indai har ni na haife ka, in kuma ka canja mi a matsayin uba zan gani kaga yaro Mara kishin kai, kai yanzu in an barka sai ka aure ta da yake baka da tunani."

Amir ya bud'e baki zaiyi magana Dady ya d'aga masa hannu yace, "bana buk'atar maganar ka na Riga na yanke hukunci babu shi babu yarinyar nan har abada."
Tafiya Dady ya fara zai bar wajan, cikin sarkewar numfashi Fa'iz ya fara fad'in "D..ad.y ka..ka... Tausayawa rayuwa ta Dan Allah......" Bai k'arasa maganar ba ya fad'i a wajan sumamme babu ko numfashi a tare dashi.

A rud'e su Amir suka yi kansa amma in ko mosti baya yi, d'ago kai Umma tayi ranta a b'ace tace, "Ka gani ko kana Neman hallaka d'an ka da kanka akan wata hujjar ka da musulunci bai haramta haka ba, koda ace Faty arniya ce addini bai haramta aure ta ba, ban tab'a magana akan abinda ya shafi Fa'iz ba amma a yau ina nema masa alfarma ka amince ta auri Fateemah" tana gama fad'ar hakan ya d'au mayafi tabi bayan su Amir da aka fita da Fa'iz.

Lokacin da motar su ta tsaya dai-dai lokacin motar su Suhail ta tsaya.
Da saurin gaske aka fito da Fa'iz aka shiga dashi emergency da saurin gaske.

Da mamaki Dadyn Shukra ke kallon yadda mutanen asibitin sabida yadda yaga hankalin kowa a tashe, d'aya daga ciki ya tsayar ya tambaya nan ya tsaida masa abinda ke faruwa.

Kallon Momy yayi yace, "ko kinji fa Wanda muka zo wajan nasa ma bashi da lafiya sai mu koma".
Kafin ya bud'e motar Suhail ya fara wani tari kafin wani lokaci ya fita daga haiyacin sa, cikin rud'ewa Dady yayi cikin asibitin aka zo aka shiga da Suhail.
A bakin d'akin suka zauna tare za zabga tagumi, a lokacin Abban Fa'iz yazo da mamaki ya kalli Dadyn Shukra yace " Alhaji Habibu".

Da sauri ya d'ago yace, "Alhaji Usman, kaine ?".
Gaisawa suka yi cike da mamakin ganin juna, Dady yace, " Alhaji Habibu Lafiya na ganku anan waye babu lafiya?".
"Suhail ne wallahi mu munzo da niyar ganin wani wai shi Dr Fa'iz sai kuma muna shigowa akace ai shine bashi da Lafiya, har zamu juya sai Suhail d'in ya fara wani irin tari shiyasa muka shigo dashi."
"To ai Fa'iz d'in danka ne, shine d'an wajena."
Da mamaki yace, "ikon Allah Ashe rabon mu gana ne yasa muka shigo garin, meya same shi?".
" Wannan maganar sai mun zauna Alhaji Habibu mu shiga muga jikin Suhail d'in. "
Dady yace "Ai likitocin basu fito ba sai dai in wajen Fa'iz d'in zamu je".
STORY CONTINUES BELOW

" A to babu damuwa muje can d'in" tare suka shiga d'akin Momy na biye a bayan su.
Mamy kuwa saukar ta kenan Amir yayi mata waya ya sanar da ita ko gida bata Je ba ta tawo asibitin cikin tashin hankali.
Ana zaune a d'akin babu mai yiwa wani magana, Momy dai sai kallon fuskar Fa'iz take tabbas tasan shi kuma sarai ta gane shi, bata so ta furta sabida Kar wani abun ya faru.
Kuka Sosai Mamy take tana sabida tausayawa Fa'iz, suna zaune Abie da Ummee suka shigo d'akin.
Da mamaki kowa yake kallon su, Dady ya bud'e baki zaiyi magana kenan Abie ya d'aga masa hannu yace "kar kace komai mun San kai ka haifi Fa'iz zaka iya yanke masa duk hukuncin da kaga dama, amma ka sani indai na isa da Fa'iz dole mu aurawa Fa'iz Fateemah indai matsayin uba nake a wajan sa."
Shiru Dady yayi baice komai ba.
Dadyn Shukra ne ya dinga bashi Hak'uri, shi kuwa Abie kamar dad'a zuga shi ake a haka ya bawa Dadyn Shukra labarin soyayyar Fateemah da Fa'iz amma bai sanar dashi dalilin hana auren ba.
Rik'e baki Dadyn Shukra yayi in ya fahimci labarin tabbas Fateeman da ta zauna a gidan suce, shiru yayi baice musu dalilin cutar Suhail ba kenan.
Suna zaune a haka har dare yayi Sosai, Su Dady ne suka yi musu sallama suka tafi zuciyar su cike da fargabar fad'a musu cewa a wajan su Fateemah ta zauna.
Washe gari da sassafe  Baba Ladi ta sauka a garin Abuja ranta a b'ace Sosai.
A asibitin ta zauna tana tana jiran isowar Dady.
Suhail kuwa jikin sa yayi zafi Sosai bashi da magana sai ta in anga Fateemah ace ta yafe masa.
Koda su Dadyn Fa'iz suka halin da yake ciki ba k'aramin tausaya masa suka yi ba jikin kowa yayi sanyi.
Fa'iz kuwa bai ma San Wanda ke kansa ba a halin da ake ciki zuciyar sa ta fara kumbura kiris take jira da ta fashe.
A bakin d'akin Dady suka had'u da Baba Ladi wato mahaifiyar sa, tana ganin sa tace "to me d'a duk naji abinda ya faru da kuma dalilin sa ya saka kaki amincewa da auren, Bara kaji baka isa ba har kana da bakin da zaka ce bayarabiya ce ka manta matar ka ta biyu wacece? In ka manta ni ban manta ba ina shekarar ta d'aya da musulunta ka aure ta, bara kaji baka isa ba dole ayi Wannan auren."
Umma da Mamy dake tsaye a wajan sunyi shiru babu Wanda yace komai babu ma kamar Mamy.
Haka Baba Ladi ta cigaba da fad'a ta inda ta shiga bata nan take fita ba, dak'yar tayi shiru suka shiga d'akin da Fa'iz yake Dan ba'a son hayaniya tayi yawa.
A bakin d'akin Mamy ta tambayi Umma wacece Fateemah, babu b'ata lokaci Umma tayi mata bayanin komai .
Kawai sa aka ga Mamy ta fashe da kuka tana fad'in "Dadyn Fa'iz wannan yarinyar ba kowa bace face y'ata wacce nake baka labari, itace Eleina ta.....!!"
Da sauri Dady ya kalle ta yace "kina nufin fa Fateemah y'ar kice?".
"Tabbas bana tantama Wannan itace Eleina ta labarin yayi dai-dai sa nawa, sunan mahaifiyar ta Dana mahaifin ta yayi dai-dai da komai nawa, wallahi itace Eleina ta.!!!"


Tirk'ashiπŸ€” Ana wata ga wata
*COMMENTS & SHARE.*

*© NEAT LADY.*

[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

STORY CONTINUES BELOW

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*Masoyan Neat Lady😍😍*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 24πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Cike da mamaki kowa na wajan yake kallon ta tare da tausayawa, Dadyn Shukra da ido wajan a lokacin yace, "Ikon Allah to ai ni kuma nine na rik'e Fateemah tun tana shekara shida wata matsala ce tasa ta bar gidan."
Da saurin gaske Mamy ta mik'e tace, "Ku fad'a min inda Fateemah take Dan Allah inaso na ganta, rabona da ita tun tana shekara shida a duniya Ku kaini wajan ta".
Cikin sanyin jiki Dady ya kalli Amir yace, " Jeka gida ka tawo da Fateema yanzu."
Ba musu Amir ya juya ya tafi, Umma ta rik'e Mamy tace "Ki kwantar da hankalin kin yanzu Fateemah zata zo zaki ganta Dan Allah Ki daina Wannan kukan."

Dak'yar aka rarrashi Mamy suka koma cikin d'akin da Fa'iz yake, zaunar da Mamy aka yi a kan kujera, Umma ta d'auko ruwa ta bata tasha kad'an.
Ajiyar zuciya Mamy take yi irin ta wacce taci kukan nan, d'akin yayi shiru kowa da abinda yake sak'awa a ransa,  Share hawaye Mamy tayi ta kalli Momy da gaban ta ke fad'uwa tace, "Ki sanar dani ya akayi kuka rik'e Fateemah? Bayan nasan a Lagos na barta wajena mahaifin ta."
Gyara zama Momy tayi a hankali ta bata labarin komai cikin sanyin murya Dan gudun kar Fa'iz ya farka, kaf ta kwashe komai ta fad'a mata ba tare da ta b'oye ba har dalilin barin gidan ta da Fateemah tayi.

Sauke numfashi Momy tayi tana goge hawaye ta durk'usa k'asa tace, "Kuyi Hak'uri Ku yafe min sharrin shaid'an da kuma rashin binkice yasa na aikata hakan, duk kuma silar y'ay'an Dana haifa Dan sune suka had'a komai ni kuma na kasa nage hakan, Dan Allah Ku yafe min nasan nayi laifi mai girma."
Girgiza kai Mamy tayi tace "Baki laifin komai ba Dan badan ta bar gidan ki ba da hakan bai faru ba, ni farin ciki nayi da hakan kuma ai daman d'an Adam baya wuce Kuskure, in akayi la'akari da yadda kika rik'e ta mu ya kamata muyi miki Godiya Allah ya saka da alkairi ba dan Ku ba da har yanzu ban San halin da take ciki ba, Allah ya bani ikon fatan ta muku kuma" duk Wannan maganar da Mamy take cikin sanyin murya take yin ta.
Murmushi Momy tayi tace "ina Fateeman take yanzu? Ta zo na nemi yafiyar ta ga Suhail can ma a kwance shima banda a cewa Fateemah ta yafe masa babu abinda yake furtawa."
Umma tace "to muje muga yadda jikin nasa yake" ta fad'a tana mik'ewa, tare suka fita daga d'akin suka shiga d'akin da Suhail yake.
Idon sa a bud'e yana kallon masu shigowa, sannu kowa yayi masa duk da baya iya magana sai dai ya d'aga kai, cikin muryar marasa Lafiya yace, "Momy ba'a Fateeman bako? Shikenan nasan daman da k'aunar ta zan koma ga Allah, Momy ina son Fateemah son da bana yiwa kaina in kun ganta kuce ta yafe min" ya fad'a muryar sa na sark'ewa.
Share hawaye Momy tayi zuciyar ta cike da tausayin sa, rik'e hannun sa tayi tace "Kayi Hak'uri in Allah ya rubuta  Fateemah matar kace babu makawa sai ka aure ta ka kwantar da hankalin ka Dan Allah Suhail."
STORY CONTINUES BELOW

"Momy baki ji yadda nake ji bane zuciya ta kamar zata fito haka nake ji."
Kuka ne yafi k'arfin Momy tayi saurin fita daga d'akin, kallon Dadyn sa yayi yace "Dady da son Fateemah zan mutu."
Dady kallon Dadyn Fa'iz yayi ya kalli Umma da Mamy yace, "Suhail kayi Hak'uri kaji, bara na turo Momyn taka" tare suka fita kowa zuciyar sa cike da tausayin Suhail.
A zaune suka tarar da Momy a zaune, tana ganin su Mamy ta mik'e ta isa wajan Mamy ta rik'e hannun ta tace, "Dan Allah ki taimakamin kiyi min wata alfarma."
"Haba babu abinda zaki nema a waja na na kasa yi miki, fad'i indai ina da ikon kin samu".
" Dab girman Allah ki taimaka ki aurawa Suhail Fateemah badan ni ba badan halin mu ba" ta fad'a tana fashewa da kuka.

Mamy kallan Umma tayi ta rasa abinda zata ce mata, kafin tayi magana Dadyn Fa'iz yace, "Nima matsayin uba nake a wajan Fateemah, kar ki damu insha Allah Fateemah matar Suhail ce."
Da sauri su Mamy suka kalle shi da mamakin furucin sa, godiya Momy tayi Sosai kamar wacce aka bawa kyautar aikin hajji.
Momy d'akin Suhail ta koma cike da farin ciki, Su Umma kuwa d'akin Fa'iz suka koma kowa zuciyar sa cike da sak'e-sak'e.

Umma ta kalli Dady tace "nifa ban gane abinda kake nufi ba, me kake so kace ne wai? Kana nufin fa...." Katse ta yayi ta hanyar d'aga mata hannu tare da fad'in,
"Ki bari mu zauna mayi maganar amma ba Yanzu ba."
Shiru tayi ba Dan taso ba, da mukullin mota Mamy ta fito da saurin gaske, Dady ya kalle ta yace "Ina zaki je kike Wannan saurin?".

" kayi Hak'uri bazan iya jira har Amir ya dawo ba zanje mu tawo tare hankali na ya ki kwanciya kayi Hak'uri " tana gama fad'ar hakan ta fice da sauri tana sharar k'wallah.
Umma ta kalli Dady tace "Bai kamata a bar ta fa ta tafi ita kad'ai ba,kana ganin ba a cikin hankalin ta take ba."

"Haka ne Gaskiya, ki shiga ciki Ku zauna da Ummen Amir bara naje na fad'awa Yaya Nuhu na tafi".

Fita yayi ya sami Abie ya fad'a masa ya tafi shi kuma ya dawo ciki suka zauna tare da Fa'iz.
Zubawa Fa'iz ido Umma tayi cike da tausayi ko motsi baya yi baka jin komai sai k'arar computer, ya rame Sosai yayi farin ciwo.
D'auke ido tayi daga kansa zuciyar ta na mata zafi akan Abinda Dady ya fadawa mahaifiyar Suhail, kenan yana nufin ya bawa Suhail Fateemah ko? Wato d'an wani yafi d'an sa.
Mamy kuwa tana shiga gida a bakin gate ta ga Amir sai zagaye yake, da sauri ya kalli motar da aka shigo da ita gaban sa na fad'uwa yana fatan Allah yasa ba Mamy bace Dan bai San me zaice Mata ba.

Ko tsayar da motar bata gama yi ba ta fito daga motar da sauri ya nufo inda Ami yake, ta k'arasowa tace, " Amie ina Fateeman? Tana ina Amir, tana ina?" Ta fad'a hawaye na zuba a idon ta.

Kasa magana yayi sabinda bai San abinda zaice mata ba, yace "Mamy tana... Uhum... "
"Wai me yasa ka kasa magana ne? Ka fad'a min ina Fateemah."
"Gaskiya Mamy tun jiya Fateemah ta bar gidan nan kuma babu Wanda yasan inda ta tafi."

"Ami bana son wasa ka sanar dani Gaskiya, ina Fateemah?".
Kafin ya bata Amsa Dady ya shigo da motar sa cikin gidan, da sauri ya bar inda take ya nufi inda Dady yake.
Dady ya fito daga motar ya kalle shi yace, " Amir ina Fateemah take?".
STORY CONTINUES BELOW

"Dady mutanen gidan nan sun sanar dani tun jiya aka ga Fateemah ta fito da trolley a hannun ta ta fita daga gidan kuma babu Wanda yasan inda ta nufa."
"Subahanallah to ina Inna Harira ai itace ta kawo ta."
"Dady na tambayi sauran y'an aikin gidan sunce Inna Harira jiya tace musu ta tafi k'auye, kuma babu Wanda yasan inda Fateemah take da zama a cikin su."
Mamy kuwa tana tsaye ta kasa magana sai girgiza kai kawai take hawaye na anbaliya daga idon ta.
Ganin kamar ba'a hankalin ta take ba yasa Dady ya rik'o ta suka shiga parlour ya zaunar da ita akan kujera yace, "Ki kwantar da hankalin insha Allahu za'a Fateemah kiyi mata addu'a Allah yasa tana cikin k'oshin lafiya."
Kai kawai ta d'aga ba tace masa komai ba.
Dady ya kalli Amir yace, "Amir ya sa yanzu a fita a nemo Fateemah nasan dai baza ta wuce cikin garin nan ba a binkito gidan da Inna Harira take da zama kafin ta tafi k'auyen."
Amir ya amsa ya fita da sauri.

Abu kamar wasa har gari ya waye babu Fateemah babu dalilin ta, in kaga Mamy a sai ka tausaya mata sabinda yadda take a rud'e na rashin y'ar ta.
Umma ma kanta hankalin ta ya tashi sosai kawai tana daurewa ne, har lokacin Fa'iz baiyi motsi ba yana kwance kamar gawa in kaje kusa dashi har sautin bugun zuciyar sa kana ji.
Suhail kuwa yaji sauki Sosai tunda Momy ta sanar dashi yadda suka yi da Dady hankalin sa ya kwanta ya fara hango Fateemah a matsayin matar sa.
Koda aka sallame su gidan su na Abuja suka zauna da Suhail yace bazai koma Kano ba sai sun had'u da Fateemah.
Umma na zaune a d'akin da Fa'iz yake Abie ya kalle ta yace, "me zai hana a mayar da Fa'iz gida sai a samo likitocin da zasu dinga kula dashi har ya farfad'o, kinga nan kowa hankalin sa ya rabu biyu ana tunanin b'atan Fateemah ga kuma rashin lafiyar Fa'iz kinga in aka maida shi gida komai zai da sauki."
Umma tace "Hakan ma yafi amma a ina za'a samu Wannan computer's d'in da suke taimaka sama wajan numfashi?".
" haba Wannan ai mai sauki ne, nan fa asibitin sane na kansa."

"Haka ne amma baka ganin anan sai yafi samun kulawa?".
" Eh to da Wannan a barshi a nan d'in Allah ya bashi Lafiya. "

Suna zaune a d'akin Fa'iz ya fara bud'e ido a hankali har ido ya bud'e gabad'aya, kallon selling d'in d'akin yayi ya juya bayan sa yaga Umma zaune tana Jan jarbi da alama bata kula da ya farka ba.
Tarin da yayi ne yasa kowa ya juyo yana kallon sa cike da farin ciki, Abie ne ya mik'e da sauri ya k'arasa wajan sa yana fad'in, "Sannu Fa'iz".
Kai kawai ya d'aga masa ya fara k'ok'arin mik'ewa, saurin komawa yayi ya kwanta tare da tafe saitin zuciyar sa.
Cikin tausayawa Abie yace " kwanta kaji bara a kira likita yazo yaga jikin naka."
Da sauri aka kira likita ya shigo fuskar da alamun farin ciki, duba shi yayi ya kalli Fa'iz d'in yace, "Sannu oga".
Lumshe ido kawai yayi ba tare da ya amsa ba, bp d'in sa auna yana nn dai yadda yake amma ya d'an sauka kad'an.
Maida kallon sa yayi ga Umma wacce tayi banza kamar bata San ya farka ba, a bad'ini kuma ta gefen ido take kallon sa cike da farin ciki.
Murmushin k'arfin Hali Fa'iz d'in yayi yana mamakin hali irin na Umman sa.
Dr yace " Oga yanzu meye maka ciwo?".

A hankali ya d'aga ido ya kalle shi tare da nuna masa saitin zuciyar sa, jikin likitan yayi sanyi yace, "Shima zai daina da yarda Allah."
Can k'asan mak'oshi Fa'iz yace "Abie zan shiga toilet."
Taimaka masa akayi ya mik'e hannun sa na kirjin sa sabida yadda zuciyar sa ke harbawa da sauri, yana rik'e da Abie har cikin toilet d'in, a bakin bathtub ya zauna Abie ya fita tare da kullo masa k'ofa.

Bai wani jima ba Sosai ba ya fito dak'yar da alama har wanka yayi duk da ya maida kayan jikin sa, a bakin gado ya zaune tare da jinginar da kansa a jikin gadon ya lumshe ido babu abinda yake ganowa sai lokacin ya fara had'uwa da Fateemah.

Shigowar Dady yasa ya bud'e ido ya kalle shi yana ganinsa maganganun sa suka fara dawo masa cikin k'wakwalwa, saurin rife ido yayi sabida yadda zuciyar ke wani irin bugawa.
Da sauri Dady ya k'araso wajan ya rik'e hannun sa yace "Ya jikin naka Fa'iz?".
" Da sauki" ya bashi amsa yana runtse ido.
Auta ce ta shigo tana hawaye tana fad'in, "Umma Yaya bashi da Lafiya Mamy ma bata da Lafiya, ga Aunty Fateemah ta b'ata har yanzu ba'a san inda take ba kuma ace na daina kuka bazan iya ba."
Jin ta ambaci Fateemah yasa yayi saurin bud'e ido tare da fad'in, "Dady ba'a Fateemah ba? Dady ina ta tafi? Me yasa ba'a je an nemo ta ba?" Ya fad'a yana k'ok'arin sakkowa daga kan gadon.
Saurin rik'e shi Dady da Abie suka yi cike da tausayin sa Abie yace, "Ka kwantar da hankalin ka zaka ga Fateemah."

"Abie na kwantar da hankali na fa kace? Ka manta hankalin nawa akace ba'a gani ba, Abie in ba'a ga Fateemah ba dai-dai yake da mutuwa ta, ya zanyi ne Abie bafa ni na d'orawa kaina son Fateemah ba Allah ne ya d'ora min amma Dady ya kasa fahimtar hakan, in Dady ya raba ni da Fateemah dai-dai yake da ya raba ni da rayuwa ta gabad'aya, dole naje na nemo ta da kaina in ba so kuke na mutu ba" ya k'arasa Maganar da kuka mai k'arfi.
Nan take ya fara wani numfashi a kirji da saurin likitoci suka shigo, suna zuwa kusa dashi ya d'aga musu hannu yace, "Bana buk'atar taimakon kowa Ku kyale ni."
D'aya daga cikin likitocin ya kalli Abie yayi masa alama dasu fito, tare suka fita Dr ya kalli Abie yace, "Amma Abba ta Yaya aka bari ya k'ara shiga damuwa haka? Wallahi kaji na rantse rayuwar sa tana cikin hatsari indai ba'a daina bari ya shiga damuwa ba, Abba Dan Allah duk abinda ya nema Ku bashi kawai indai har kuna son rayuwar sa, Abba zuciyar sa a kunbure take a ko wanne lokaci in aka cigaba da sashi cikin wani hali Wallahi zata iya bugawa gabad'aya, Dan Allah Abba a kiyaye."
Godiya Abie yayi kasa ya koma ciki jikin sa sanyaye.
Fa'iz ya tayar da hankalin sa akan lallai sai ya bar asibitin, ala dole suka sallame shi aka tawo gida dashi.
Babu Wanda ya kula a gida yana dafa bango ya shiga d'akin Fateemah, k'arewa d'akin kallon yake yana jin sanyi a cikin ransa.
A bakin gadon ya zauna yana shak'ar k'amshin d'akin yana lumshe ido.

Tunowa da yayi ance ba'a ganta ba yasa ya Mik'e da sauri ya fito daga d'akin, A parlour ya same su a zaune Mamy na kwance akan doguwar kujera ta rife ido kamar mai bacci.
"Dady zanje Neman Fateemah, Amir taso ka muje" ya fad'a yana yin hanyar fita yana cize baki Dan ba k'aramin ciwo yake ji ba yana daurewa ne kawai.
Babu Wanda yayi magana sabida kowa yana gudun b'acin ransa, mota Amir ya shiga shima ya shiga suka fita daga gidan.
Sun d'an yi nisa Amir ya kalle shi cike da tausayi yace, "to yanzu ina muka nufa Fa'iz?".
" muje kawai Allah zai sa mu ganta ko a hanya ne" ya fad'a yana rufe ido.
STORY CONTINUES BELOW

Amir yace "kafin nan badan ni ba in akana so Allah ya had'a ka da Fateemah mu tsaya kaci abinci kaga rabon ka da abinci fa kwana uku kenan."
Jin addu'ar da yayi yasa yayi shiru baice komai ba, ganin yayi shiru yasa ya karkata motar sa suka bi hanyar masu sai da masa Dan yasan abincin da yafi so kenan.

Koda suka Je Amir yayi Neman duniya baiga wacce yake ciyan waina a wajan ta ba in yazo Abuja, babu b'ata lokaci ya tambaya aka yi masa kwatancen gidan ya tafi.
A k'ofar gidan Baba mai waina ya tsaya  tare da bud'e motar ya fita ya shiga cikin gidan, Fa'iz kuwa jin Amir ya fita ya bud'e ido yana kallon gidan da suka zo, gaban sa yaji yana fad'uwa hakan yasa ya bud'e motar ya fito shima ya nufi cikin gidan.
A zaune ya tarar da Amir suna ta hira da Baba ita kuma tana zuba masa waina a plat, ganin ya shigo yasa yayi sauri ya mik'e ya rik'o shi suka zauna a kan tabarmar.
Ko ba'a fad'a ba Baba ta gane waye hakan yasa take Allah-Allah ta sallame su, Inna Harira ce ta fito daga d'aki tana yafa mayafi, Sam bata lura da su a zaune ba sai ji tayi Fa'iz yace, "Inna Harira ina Fateemah?".
Damm gaban ta ya buga da sauri ya juyo ta kalle shi ita kanta sai da ta tsorata ganin yadda ya rame yayi fari kamar k'wara, kafe da ido yayi hakan yasa Inna Harira ta dabarbarce ta fara kame-kame.
Kafin tayi magana Baba tace, "Ai yau kwanan mu uku rabon damu da Fateemah, muma sai labarin tafiyar ta muka ji ko sallama muma bata yi mana ba, hakan yasa Inna Harira tace tayi tafiya sabida kar azo ana ce mata ina Fateemah tun da dai ita ta kaita aiki gidan Ku."
Cike da rashin yadda yake kallon su yana kallon d'akin da Inna Harira ta fito, Amir yace, "ikon Allah Ashe anan Fateemah take da ni ban ma sani ba."
Lumshe ido Fa'iz yayi Baba ta mik'o musu wainar su, a hankali Fa'iz ya mik'e har zai fita ya dawo ya durk'usa gaban Baba yace "Dan girman Allah in kun San inda Fateemah take Ku sanar da ita tana gab dayin kisa dan rashin Fateemah dai-dai ake da rasa rayuwa ta, nasan nayi Kuskure a baya Ku bata Hak'uri kuce ta dawo gare ni ko naji saukin abinda ke damu na in kuma so take na mutu shikenan ta cigaba da zama ma had'u a lahira amma ta sani itace sana din mutuwa ta" yana gama fad'ar hakan ya mik'e dak'yar ya fita, haka kawai yake ji a jikin sa sun San inda Fateemah take.
Mota suka koma Amir ya ja mota suka tafi Fa'iz kuwa kwantar da kujerar yayi ya rife ido.
Sai da suka ji tashin motar su Baba ta kalli Harira tace, "Yaron nan ya bani tausayi Sosai."
Inna Harira tayi shiru ta rasa abin cewa, Fateemah ce  ta fito daga d'akin tana goge ido da alama duk taji yadda aka yi.

Baba ta mik'e ta k'araso wajan ta tace "Fateemah nasan duk kinji yadda muka yi dasu yaron nan ba k'aramin sonki yake ba me yasa bazaki tausaya masa ba?".

Shiru tayi ta rasa abin cewa sai hawaye da take yi.

Fa'iz kuwa suna cikin tafiya ya kalli Amir yace, " mu koma gidan da muka baro yanzu. "
Cike da mamaki Amir ya kalle shi baiyi magana ba ya juya suka koma gidan.

Motar na tsayawa ya fito ya shiga gidan, ganin ya shiga yasa Amir yabi bayan sa shima.*COMMENTS & SHARE.*

© *NEAT LADY.*
[4/17, 22:49] Ukhtee Baby: *°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*MY DEAR ZEEY.*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
*SHAFI NA 25πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Ginjina yayi da bangon k'ofar ya zuba mata ido yana kallon ta cike da shauk'in k'auna.
Babu Wanda ya kula da shigowar su, Fateemah ta kalli Baba tace, "Haka ne Baba amma banjin Zan iya komawa gare badan wai bana son sa ba sai Dan mahaifin sa baya son tarayyar mu tare, bana son a dalilina na raba shi da mahaifin sa gwara nayi nisa da garin na koma inda babu Wanda ya sanni na na manta dashi."

"Idan kika yi haka kuwa kin ci amanar soyayya" Fa'iz ya fad'a yana k'araso wa cikin gidan.
Da sauri suka juya suna kallon sa cike da mamakin lokacin da ya dawo gidan, zuba masa ido Fateemah tayi nan tale zuciyar ta ta karye jikin ta yayi sanyi ganin yadda ya rame a cikin kwana uku kacal.
Sai da yazo daf da ita ya d'ago fuskar ta yana so su had'a ido amma Sam tak'i yarda sai kauda fuska da take yi, cikin sanyin murya yace, "Fateemah yaushe kika zama Mara tausayi ban sani ba? Ashe zaki iya tafiya ki barni cikin Wannan duniyar mai cike da kunci wacce  ke kad'ai ce zaki fitar dani daga halin da nake ciki, me yasa bakya yafiya ne?".
Gyara zaman glass d'inta tayi har lokacin akwai bandage a goshin ta, tace, " Babu abinda zan iya yi maka ko kana so kace zaka fifita soyayya sama da mahaifin ka? To in zaka yi hakan ni bazan iya bari hakan ta faru ba ta dalili na, kaje ka bi umarnin mahaifin ka ka manta dani a rayuwar ka gabad'aya nima zan manta da kai har abada kamar ban tab'a sanin wata hallita Fa'iz ba."
"Ashe har Yanzu baki yafe min laifin da nayi miki ba a rashin sani ko?".
" Ka daina Wannan tunanin ni ba abinda yasa zan barka ba kenan, inda har yanzu ina jin haushin ka ba zan tsaya muna magana ni dakai ba, shikenan ma muje a bana sonka d'in eh bana sonka ka koma wajan mahaifin ka shine yayi maka komai na rayuwa ni kuma a sama na same ka."

Matse mata hannu yayi da k'arfi ya had'e ta bango ya rik'e fuskar ta gam yace, "k'arya kike Fateemah kuna sona bayan ga zallar k'auna ta nan ina gani a cikin idon ki, Fateemah meyasa baza ki tausayawa zuciyar dake k'aunar ki ba? Fateemah bana gani kowa sai ke wallahi ko wacce mace a namiji nake kallon ta bayan iyaye na, Fateemah Kik ratsa cikin zuciya ta kin samu fada mai kyau kin fara sarauta wacce take cike da aminci, duk wata dak'ik'a bata wucewa ba tare Dana tuna ki ba, a hakan kike so ki barni? Wallahi Fateemah kika sake kiyayi nisa dani saina kashe kaina dan banga amfanin rayuwa ta ba babu ke, idan kuma kina musu ki gwada tafiya na tabbata zaki samu labarin mutuwa kuma ki sani kece sanadi."
Ajiyar zuciya yayi tare da k'ara rik'e ta Sosai, hannun ta sa saka a kirjin sa dai-dai saitin zuciyar sa yace, "Kinji yadda zuciya ta ke bugawa sabida ke ko? Me yasa baki yiwa zuciyar da ta kusa bugawa a kanki adalci ba Faty? Tun bayan rabuwar ban kuma kallon wata mace ba da zunmar so har sabida na Riga na mallaka miki zuciya ta har abada amma meyasa kike son juya min baya ne" durk'usa wa yayi gaban ta tare da rik'e hannun ta ya cigaba da fad'in " ki yafe min laifin da nayi miki, ki amince ki aure ni ni kuma nayi miki alk'awari zan baki gata Wanda babu wata y'a mace da ta tab'a samun sa, ki ajjiye maganar Dady a gefe yana magana ne akan rashin hujja tunda addini bai haramta auren mu ba banga Wanda ya isa ya hana ba, ki amince dani."
Zuba masa ido tayi Ita bace eh ba kuma bata ce a'a ba, in taki amincewa dashi tabbas tasan ta cuci kanta Dan itama zata iya kwanciya ciwon zuciyar, amma mahaifin sa fa?.

Katse mata tunani yayi ta da fad'in "kinyi shiru baki ce komai ba?".

Ajiyar zuciya tayi tace " Indan nace bana sonka nayi k'arya ina sonka kuma ina burin zama da kai, but mahaifin ka fa da yace bazai aura maka ni ba koda zaka mutu ya zakayi dashi?".

Mik'ewa yayi fuskar sa d'auke da murmushi yace, "Kada ki damu Wannan ba matsala bace Allah zai kawo mana sauki, Fateemah kin riga kin zama jinin Fa'iz babu ta yarda rayuwa zata yu ba tare da ke ba, kin zama ni na zama ke, ina sonki Fateemah sonda ban San iya adadin sa ba."
Murmushi tayi mai cike da so itama tace, "Nima ina k'aunar ka Yaya nah".
Dariya yayi har hak'oran sa suka baiyana, bai tsaya wani tunani ba ya had'a ta da kirjin sa ya rungume ta tsam yana sauke numfashi.
Itama rik'e shi tayi gam tana jin yadda zuciyar sa ke bugawa sa sauri, tausayi ya bata sosai kawai sai ta fara hawaye.
Saurin d'ago ta yayi yana share mata hawaye yana girgiza kai yana fad'in, " Kuka ya k'are a rayuwar ki Fateemah keda kiyi kuka sai dai in na farin ciki, bana son ganin hawayen ki ko kad'an ina jin zafin sa a raina, saukar hawayen ki d'aya dai-dai yake da saukar ruwan zafi a cikin zuciya ta ki daina Wannan kuka, d'auko hijjabin ki muje."
Amir dake tsaye shida su Baba ba k'aramin tausayi suka basu ba Amir yarda hawaye.
Fa'iz kuwa tuni ya manta da wasu Baba a wajan soyayyar sa kawai yake zubawa.
Kallan ta Baba tayi tace "Uwa ta kije ki d'auko hijjabin ki kuje ina ji a jikina kamar alkairi ne zuwan ki yau".
Fateemah dake tsaye ta shiga d'aki bata San dalilin da yasa gaban ta ke fad'uwa ba.
Hijjabi ta d'auko ta saka ta kalli Baba tace, " Baba ki taya ni da addu'a gabana sai fad'uwa yake na rasa dalili."
Baba ta dafa ta tace, "Alkairi ne insha Allah" kallon Fa'iz tayi ta rik'e hannun Fateemah ta rik'e na Fa'iz ta had'e waje d'aya tace, "Kada Ku bani kunya ko nan gaba Ku rik'e junan Ku da kyau Allah yayi muku albarka."
Suka amsa da amin suka fita daga gidan.
Tunda suka shiga mota Fa'iz ya kasa rife baki Sai kallon Fateemah yake yana murmushi, ciwo kuwa tuni ya neme shi ya rasa tunda yayi tozali da Fatyn sa.
Amir kuwa kallon Fateemah yake yana gasgata Maganar Mamy tabbas Wannan y'ar tace.
Tunda suka shiga gate d'in gidan gaban Fateemah ke fad'uwa, a hankali ta fito daga motar Fa'iz ya rik'e hannun ta suka shiga parlourn.
Kamar yarda suka barsu suna zaune anyi shiru kamar gidan mutuwa, sallamar suce tasa kowa ya d'ago banda Mamy da ta rife ido.
Fateemah kuwa kanta a k'asa ta shigo parlourn cike da tsoron abinda zai biyo baya, cikin rawar murya ta durk'usa tace, "Sannun Ku da hutawa".
Kamar a mafarki Mamy taji maganar Fateemah zunbur ta mik'e tana kallon ta, amsawa su Umma suka yi kowa ransa a sake.
D'ago kai Fateemah tayi zata yiwa Auta magana karaf idon ta ya fad'a cikin na Mamy, zaro ido tayi ta mik'e tana nuna ta tare da murza ido tace, Momy na ke nake gani ko mafarki nake?".
Cikin kuka Mamy ta taso tace, " Fateemah ba mafarki kike ba nice dai Momyn ki mahaifiyar....." Ai kafin ta k'arasa Fateemah ta fad'i sumammiya.

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
*SHAFI NA 26πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Da sauri Mamy ta zauna a wajan tana kuka ta d'ora kan Fateemah a cinyar ta tana girgiza ta tana fad'in, "Kada kiyi min haka daughter ki tashi dan Allah" ta fad'a tana fashewa da kuka.+

Da sauri Fa'iz ya bud'e fridge ya d'auko ruwa mai sanyin gaske ya zuba a hannun sa tare da zama a wajan ya tallafo kanta ya shafa mata a fuska cikin tashin hankali.

A dai-dai lokacin da yake shafa mata ruwa su Suhail suka yi sallama suka shigo parlour, Ummee ce kawai tayi k'arfin halin amsawa daga haka bata kuma cewa komai ba, tunda Suhail ya shigo idon sa ke kan Fateemah da kanta ke kwance a kirjin Fa'iz.

Wani irin kishi ne ya taso masa cikin sauri ya kauda kai duk da son ganin Fateemah da yake, ganin kamar Fateemah ba'a hankalin ta take ba yasa Suhail yayi saurin k'arasawa wajan ya tsuguna yana kiran sunan Fateemah.

Fa'iz kuwa bai ma kula da wani Suhail ba hankalim sa na kan Beautyn sa, ganin breathe d'in ta na sama-sama yasa hankalin sa ya kuma tashi mutuk'a.

Cikin kuka mai k'arfi Mamy tace "Fa'iz numfashin ta na sama Dan Allah ya ceci ranta".

Kamar jira yake ya saka bakin sa a cikin nata yana hura mata iska, Da sauri Suhail ya kalle shi ransa a b'ace duk da yasan taimakon ta yake amma hakan bai hana sa jin haushin Fa'iz ba.

Fa'iz kuwa iaya k'arfin sa yake bata taimakon gaggawa, a hankali numfashin ta ya fara dawowa normal duk da ya kula amma bai zare bakin sa daga nata ba.

Duk da cikin rashin lafiya Fateemah take hakan bai hana Umma taji kunya ba cikin sauri ta kauda kai.

Tari Fateemah ta fara hakan yasa Fa'iz ya zare bakin sa daga nata a hankali yana kallon fuskar ta, a hankali ta bud'e ido tana ajiyar zuciya.

Tashi tayi Daga jikin Fa'iz tana tafe kai sabida ciwon da yake mata, da sauri Mamy ta rungume ta tana shafa bayan ta.

Kuka Fateemah ra fashe dashi tana fad'in, " Momy na ina meyasa tafi kika barni eh Momy na? Me yasa baki neme ni ba duk tsahon Wannan shekarun?" Ta fad'a cikin kuka sosai.

"Babu yadda zanyi ne Daughter amma a kullum take nake kwana dake nake tashi, kiyi Hak'uri ki yafe min Dana tafi na barki a wajan waccan mugun mahaifin naki, ina jin haushin kaina a duk lokacin Dana tuna na hakan, na saka an duba min gidan sai aka kawo min labari Mara dad'i ji wai an neme ki an rasa daughter na shiga tashin hankalin da ban tab'a shiga ba a rayuwa ta, a da su Dady sunce kada na neme ki amma Daga baya dasu ake Neman ki daughter har zuwa lokacin da na auri mahaifin Fa'iz".

Fateemah ma kuwa kuka kawai take ta kasa cewa komai, share mata hawaye tayi tace, " Daughter na samu labarin irin wahalar da kika sha da irin taimakon da kika samu" ta fad'a tana k'ara rike ta gam.

Ajiyar zuciya Fateemah take bakin ta fal yake da tambayoyi amma ta kasa sabida kukan da take yi ga kuma ciwon kai.

Umma ce ta k'araso wajan ta kalle su tace, "Shikenan Safiyyah Ku daina Wannan kukan Dan Allah Ku tashi mu shiga ciki kiran sallah ake" ba suyi musu ba Mamy ta mik'e tare sa rik'e hannun Fateemah itama ta mik'e suka shiga daki.

STORY CONTINUES BELOW

Fa'iz kuwa mamaki yake Ashe daman Mamy itace mahaifiyar Fateemah? Haba shiyasa yake yawan fad'awa Mamy tana yi masa kama da wata Ashe Fateemah ce.

Dafa shin da Amir yayi yasa ya dawo daga tunanin da yake, Amir yace, "Tashi muje ana kiran sallah a masallaci."

Mik'ewa suka fita ba tare da yayi magana ba.

Da yake masallacin a gidan yake suna fita suka ga su Dady suna shirin shiga ciki, a bakin k'ofa suka had'a ido da Suhail tsaki Fa'iz yayi ta d'auke kai Dan har yanzu bai daina jin tsanar Suhail a zuciyar sa ba.

Shima Suhail d'in dauke kai yayi dan ba k'aramin kishi yake da Fa'iz ba.

Fateemah kuwa koda suka shiga d'aki alwala sukayi suka tayar da sallah, bayan sun idar Mamy ta zubawa Fateemah ido tana murmushi ji take kamar ta cinye ta sabida son da take mata.

Murmushi Fateemah tayi ta kalli Mamy tace, "Mamy na ya akayi kika shiga musulunci? duk da ina da karacin shekaru a baya  nasan ba musulmai bane mu."

Ajiyar zuciya tayi tace, "Bayan mun rabu da mahaifin ki na dawo gida ban b'oyewa iyaye na komai ba na fad'a musu, ransu ya b'aci sosai amma hakan bai hana sun yafe min laifina ba sune suka ce na manta dake ai daman bada ke naje ba, bayan wasu kwanaki munzo wucewa ta wani masallaci sai muka ji ana wa'azi mai ratsa jiki ana fad'ar azabar da Allah ya tanadarwa kafiri, jikin mu yayi sanyi especially Momy da Dady, Dady ya bud'e motar ya shiga cikin masallacin ya zauna yana cigaba da jin wa'azin mu kuma muna mota, da yake Allah yaso mu da rahamar sa gabad'ayan mu sai muka ji muna sha'awar shiga Wannan addini, Dady baiyi sanya ba ya sanar da malamin ya kuma yi mana bayanin addinin tare da sanar damu mahallicin mu, na takaice miki labari anan wajan dai muka karb'i musulunci, Fateemah tunda nayi Kalmar shahada naji wani farin ciki na ratsa ni haka ma Dady da Momy, shawara Malami ya bamu akan mu samu malamin da zai dinga nuna mana addinin mu, bamu yi sanya ba washe gari muka samu malamai mace da namiji suna koya mana addinin Allah, bayan wasu watanni muka had'u da mahaifin Fa'iz ya nuna yana son aure na, bincike sosai Dady na yayi aka gano bashi da wani bad behavior daga nan na amince dashi aka d'aura mana aure har kawo yanzu, kinji yadda abin ya kasance."

Ajiyar zuciya Fateemah tayi ta girgiza kai tana murmushi tace, "To Mamy ya akayi kuka iya Hausa?".

" Haba Fateemah indai zaka zauna cikin hausawa ai dole ka iya Hausa, kuma daman can muna ji amma ba sosai ba Gaskiya. "

"Mamy nasan kin San labari na basai na fad'a miki ba, amma bazan iya b'oye miki taimakon Baba mai waina da Inna Harira gare ni ba," nan ta kwashe komai ta sanar da ita.

Girgiza kai Mamy tayi tana hawaye tace, "Allah ya saka musu da alkairi Allah ya biya musu buk'atun su, Fateemah duk Wanda ya taimaka miki gani nake ko me zai tambaya a waje na zan iya bashi dole naje wajan Baba mai waina domin yaba kyauta tukwici."

"Haka ne Mamy na, Mamy gashi komai ya wuce kamar ba'a yi ba."

Mamy ta rik'e hannun ta tace "haka ne daughter gashi yanzu zancen auren ki za'a fara" ta fad'a tana murmushi.

"Mamy ni ba Wannan ya dame ni ba, Mamy ina so naje naga halin da Dady na yake ciki amma banjin zan iya ganewa da tuni naje gare shi, ina ji a jikina kamar yana cikin wani hali."

B'ata rai Mamy tayi Dan inda abinda ta tsana bai wuce zancen Danial ba, ganin yadda ta had'e rai yasa Fateemah tace, "kiyi Hak'uri Mamy in na b'ata miki rai."

Kafin Mamy tayi magana Auta ta shigo da gudu ta rungume Fateemah tana kuka, itama rungume ta tayi tana shafa bayan ta.

D'ago kanta tayi tace, "Mamy Ashe Aunty Fateemah yaya tace ta jini shiyasa nake jin ina sonta sosai Ashe yaya tace".

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ita Fateemah tayi tana jin k'aunar k'anwar tata na ratsa ta.

Hira suka dinga cikin farin ciki da k'aunar juna, Mamy ta kira iyayen ta ta sanar dasu sunyi murna sosai babu kamar mahaifiyar ta ma inda suka ce sunan zuwa suga jikar su.

Ko kad'an Fateemah da Mamy sun kasa rabuwa da juna koda yaushe suna zaune tare suna hira.

Zaune suke a k'aton parlour Dadyn Fa'iz da Umman sa, Mamy, Dadyn Suhail da Momy, Abie da Umme, suna ta hira ita dai Mamy ko kad'an ta kasa b'oye farin cikin ta dai murmushi take.

Momy ce ta gyara zama ta kalli Dadyn Fa'iz ba tare da wani tsoro ba tace, "Alfarma nake nema a wajan Ku gabad'aya, tunda dai ka gama maganar Suhail da Fateemah shine nace mai zai hana ba za'a saka lokacin biki ba?".

Da mamaki Abie mahaifin Amir yake kallon yace, " A'a Fateemah tace shi take so ne?".

Momy tace "A'a basu magana da Fateemah ba ina so ayi maganar ne sabida ya d'an samu relief."

Kallan ta Dadyn Shukra yayi cike da mamaki danshi yasan Fa'iz ke son Fateemah, yana mamakin k'arfin hali irin nata, yace, "Banda abin ki ayi maganar aure yarinya bata ce tana son Suhail ba? Ai sai munji daga bakin ta sannan sai ayi magana."

Dady yace "Haka ne maganar ka bara na kira Suhail da Fa'iz d'in da kuma Fateeman in yaso sai ta fad'i Wanda take so da bakin ta."

Abie yace "Hakan yayi a kira su."

Umma da Mamy dai babu abinda suka ce kowa yayi shiru, Mamy kuwa tana cikin tashin hankali tana San tabbas Fateema Fa'iz take so, amma kuma iyayen Suhail sunyi hallacin da ko abinda yafi y'a ne ya kamata a basu.

Shigowar Fa'iz da Suhail yasa ta dawo Daga tunanin da take yi, zama suka yi akan carpet ko wanne gaban sa na fad'uwa ba kamar Fa'iz ma.

Gyaran murya Abie yayi yace, "Suhail, " Suhail ya d'ago ya kalle shi, "Fa'iz", shima ya d'ago ya kalle shi tare da cewa "na'am Abie".

" Duk kan Ku y'ay'a ne a wajan mu dan mu d'aya muka d'auke Ku sabida kai Suhail Mahaifin ka Abokin mune tun a da wajan zama ne ya raba abotar tamu, Fa'iz kana son Fateema mun San da haka tunda tun tana k'arama kake son ta, haka kaima Suhail kana son Fateemah kuma kun San dai mace bata auren maza guda biyu dole ne a d'au d'aya a bar d'aya, to zamu kira Fateema zata zab'i Wanda take so da kanta amma Ku sani duk wanda ta d'auka ba hakan yana nufin munfi sonsa akan d'ayan ba A'a, sannan in ta d'au d'aya ta bar d'aya to ya sawa zuciyar sa salama kuma ya sani daman can wani baya auren matar wani, Wannan shine dalilin da yasa aka kira Ku."

Shiru suka yi babu Wanda ya amsa kowa da abinda yake sak'awa a ransa.

Cikin sallama Fateemah ta shigo kanta a k'asa gaban ta na fad'uwa ta zauna kusa da k'afar Mamy.

Abie ya kalli Fateema yace, "Fateemah", d'ago kai tayi tace, " Na'am ".

Ya cigaba da cewa "Fateema mun sa an kira ki ne badan komai ba sai dan a cikin wad'an nan samari guda biyu ki zab'i d'aya a cikin su Wanda yafi kwanta miki rai, kada kiga idon mu ki d'auki Wanda bakya so ki raba gardama ki d'auki Wanda kike so."

Gaban ta ya fad'i cikin zuciyar ta take tunanin to waye d'ayan? Ita dai Fa'iz ta sani bata San wani mai sonta ba, d'ago kai tayi ta kalli Abie tace,

"Ni ban gane abinda kake nufi ba ni mutum d'aya na sani bayan shi ban sani wani ba Gaskiya".

Abie yace " Au Ashe fa lokacin da ake ta abun bakya nan baki San da rashin lafiyar Suhail akan ki ba, Fateemah Suhail Wanda kika sani a baya shine yazo ya nuna yana sonki har a kanki ya kwanta rashin lafiya kamar yadda Fa'iz ya kwanta, duka su biyun suna sonki kuma suna burin auren ki baza mu bawa d'aya mu hana d'aya ba amma idan kike kika zab'a da kanki kinga dole d'aya ya Hak'ura ya barwa d'aya."

STORY CONTINUES BELOW

Fargaba da tsoro ne suka shiga Fateemah ta rasa abin cewa jikin ta yara rawa ta yaya zata ce ga zata d'au d'aya ta bar d'aya? Kwakwalwar ta kulle ta rasa tunanin me zata yi, muryar Abie ta katse mata tunanin da fad'in,

"Fateema ke muke sauraro?".

D'ago kai tayi suka had'a ido da Suhail da ya zuba mata ido, d'auke kai tayi ta maida kallon ga Fa'iz da ya lumshe ido yana sauke numfashi ya d'aura hannun sa a kirji da alama bashi da lafiya.

Kallon Abie tayi tace, " Abie a bani lokaci zanyi tunani."

Abie yace "To Shikenan tunda ki neme hakan an baki nan da sati kije kiyi tunani, tashi ki tafi Allah yayi miki albarka."

Ta amsa da Amin ta mik'e ta fita kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki.

Kowa yayi shiru a parlourn  sai sautin ajiyar zuciyar Fa'iz ke tashi a wajan, cike da tausayi Umma da Mamy ke kallan sa sudai da za'a bi ta tasu wallahi Fa'iz ne mijin Fateema.

Abie yace "to kunji yadda tace a bata lokaci kuma an bata, ko wanne ya kwantar da hankalin sa ya cigaba da addu'a."

Fa'iz bai kuma magana ba ya mik'e ya fice daga parlourn, haka ma Suhail din shima fita yayi.

Taro ya tashi Mamy ta shiga d'akin Fateema ta tarar da ita a zaune ta zuba uban tagumi, Kusa da ita ta zauna ta dafa ta tace, "Daughter lafiya meke damun ki?".

" Mamy an sani a duhu yanzu wa zan d'auka a ciki wa zan Bari? Iyayen Suhail sun yimin abinda bazan tab'a mantawa dashi ba kuma bani da hanyar da zan biya su har abada, Mamy tsakani da Allah Fa'iz shine zab'i na tun ina yarinya yake sona nima kuma haka tun ban San meye so ba, a kaina kina ganin halin da ya shiga yau din nan aka sallomo shi daga asibiti amma bai tsaya tunani ba ya fita nema na har ya samo inda nake, Mamy in nace bana son Fa'iz Wallahi zai iya rasa ransa bazan iya d'aukar Suhail na bar Fa'iz ba duk da abinda ya faru tsakanina dashi cikin rashin sani, haka in naki Suhail nayi butulci sabida iyayen sa ta Wannan hanyar xan d'an biya su abinda suka yi min amma babu son Suhail ko kad'an a zuciya ta sai zallar tsanar sa, duk da abinda Fa'iz yayi min a rashin sani hakan bai sa naji haushin sa kamar yadda nake jin haushin Suhail ba."

Ajiyar zuciya Mamy tayi ta rik'e hannun Fateemah tace, "Tsakani da Allah nima Fateema nafi sonki da Fa'iz sabida nafi mahaifiyar sa sanin wanene shi nasan halin sa fiye da yadda bakya tunani, nasan irin son da Fa'iz yake miki sabida kullum sai ya bani labarin ki da irin son da yake miki, in na tuna kuma irin taimakon da iyayen ta suka yi miki sai jiki na yayi sanyi na kasa cewa komai, amma ki cigaba da addu'a kina Neman zab'in Allah, Allah zai zab'a miki mafi alkairi."

"Ameen Mamy bara naje waje na gaji da zaman nan."

Mamy tace "A'a ki bari ayi sallar i'sha tunda an kusa".

Ta amsa sa toh ta shiga band'aki.

Mik'ewa Mamy tayi ta fito parlour, Fa'iz ta hango shida Amir a zaune ya ginjinar da kansa a jikin kujera.

A hankali Mamy ta k'arasa ta zauna a wajan tace, " Fa'iz lafiya meke damun ka?".

D'ago idon sa yayi da yayi ja ya kalli Mamy yace, "Mamy kina kallon za'a raba ni da farin ciki na ko? Wallahi Mamy rasa Fateemah dai-dai yake da rasa raina ki taimaka min Mamy ji nake kamar ana zuba min ruwan zafi a zuciya ta."

Rik'e hannun sa Mamy tayi tace "Ka kwantar da hankalin ka Fa'iz in Allah ya rubuta matar kace sai ka aure ta babu makawa, matar mutum kabarin sa."

Murmushi yayi ya runtse ido ya nuna dai-dai zuciyar sa yace, "Mamy kin San yadda nake ji anan? Ji nake kamar buga min wajan da guduma, amma zanyi yadda kika ce zan cigaba da addu'a."

Shiru tayi bata amsa ba sabida yadda take jin tausayin sa na ratsa ta, haka ma Amir dake gefe.

Mik'ewa yayi yace "Mamy bara nayi sallah na kwanta kicewa Beauty ina gaida ta nasan baza tazo inda nake ba" ya fad'a yana fita.

STORY CONTINUES BELOW

Fateemah dake lab'e a k'ofar d'akin kuka take sosai ta koma ciki da gudu ta fad'a kan gado tana kuka.

Cikin Daren tsakanin Fa'iz Fateema Suhail babu Wanda yayi wani baccin kirki.

Da safe ko wanne jikin sa a sab'ule, Fateema kuwa a d'aki daya suka kwana da Mamy da Auta.

Wajan k'arfe sha d'aya na safe motar Suhail rayi parking a cikin gidan, bayan sun gaisa da mutanen gidan ya fito zuciyar sa cike da son ganin Fateemah ya zauna a garden d'in gidan yana kallon pic d'in Fateema dake wayar sa.

Yana zaune Fateemah tazo wucewa, Sam bata kula da Suhail dake wajan ba.

"Fateemah" ya fad'a yana mik'ewa.

Cak ta tsaya ita bata juyo ba ita bata cigaba da tafiya ba, k'arasowa yayi yana murmushi yace, "Fateema an tashi lafiya."

A hankali ta amsa da lafiya.

Suhail yace "Fateemah nasan ni me laifi ni a wajan ki amma Dan Allah ki yafe min abinda ya faru a baya nayi nadama fiye da yadda bakya tunani."

Juyowa tayi ta zuba mata manya idanuwan ta tace " Kayi ka gama fad'ar abinda zaka fad'a inada abin yi."

Ganin yayi shiru yasa ta fara tafiya, caraf ya rik'e hannun ta hakan yasa tayi saurin juyowa tana kallon sa.

Fa'iz dake waya ya fito daga part d'in sa juyowar da zaiyi idon sa ya sauka akan su, ba k'aramin tashin hankali Fa'iz ya shiga ba ganin Suhail na rik'e da hannun Fateema.

Bai San time d'in da wayar hannun sa ta fad'i ba wani tari mai k'arfi ya sub'uce masa, tarin da yayi ya jayo hankalin Fateemah da Suhail dake tsaye.

Tari Fa'iz yake sosai har ya durk'usa yana dukan kirjin sa, nan take jini ya fara fita daga bakin sa.

Topa zab'i yana wajan Ku fan's shin waye ya dace da Fateemah tsakanin Fa'iz Da Suhail?πŸ€”

Nagode da addu'ar Ku gare ni I love u my fan's❤❤😍😍😍😍

*COMMENTS & SHARE.*

*© NEAT LADY.* *G.W.A Welfare*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*GASKIYA WRITERS FAN'S GROUPSπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»❤❤❤❤❤*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

_A'a Lallai Fa'iz yana da masoyaπŸ˜‚ Wannan ruwan comment's haka kuma duk akan Fa'iz shi kad'ai, gsky babu adalci a cikin Wannan abun kun nuna kunfi son Fa'iz akan Suhail fa kenanπŸ™„ tunda bashi da kowa ni na koma bayan sa🌝, nidai sai SuhailπŸ’ƒπŸ»._

20 read more🌚

*SHAFI NA 27πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Da k'arfin gaske ta kwace hannun ta daga rik'on da Suhail yayi mata ya nufi Fa'iz da gudu, kafin ta k'araso Amir ya zo wajan hankalin sa a tashe.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin tashin hankali Fateemah tace, "Amir mu kishi Asibiti kaga jini ke fita daga bakin sa."

D'aga musu hannun yayi alamun baya so a kaishi asibiti, d'aga shi Amir yayi amma ya kasa tsayawa sai da mai gadi ya taimaka aka shiga dashi ciki.

Bin bayan su Fateema tayi Dan ita har ga Allah ta manta da wani Suhail, shi kansa Suhail ya tausayawa Fa'iz nan take jikin sa yayi sanyi.

A parlourn sa aka kwantar dashi Amir yayi sauri ya d'auko maganin sa ya bashi tare da ruwa, Mamy da Umma ne suka shigo d'akin suna faman yi masa Sannu.

D'aga kai kawai yake sabida ya kasa magana, ganin kamar ya samu bacci yasa Mamy da Umma suka fita aka bar Amir da Fateema.

Kallon Fateemah Amir yayi yace, "Bara naje na dawo Yanzu" ya fad'a yana fita daga parlourn.
Juyawa tayi da niyar fita taji murya sa yace, "Daman nasan tafiya zaki ce zaki yi."

Juyowa tayi ta kalle shi sai dai har lokacin idon sa a rufe baza kace shine yayi magana Yanzu ba.

Bud'e ido yayi ya kalle ta tare da mik'ewa dak'yar yazo daf da ita cikin wata irin murya yace, "Fateemahhh."

Yadda ya fad'i sunan nasa yasa taji wani iri a jikin ta har ta lumshe ido ba tare da ta sani ba, a hankali tace, "Na'am" ta fad'a kanta a k'asa.

Zubawa fuskar ta ido yayi yace, "Kalli cikin ido na". A hankali ta d'ago kai suka had'a ido tayi sauri d'auke idon ta dan bata son had'a ido dashi.

Murmushi gefen baki yayi yace, " Ok nagane kin tsane ni bakya son ganina ko? Shikenan jeki hakan yayi kyau" ya fad'a yana had'e rai tare da komawa ya zauna.

Rife idon sa yayi babu abinda yake gani sai lokacin da Suhail ya rik'ewa Fateema hannu, wani irin zafi yake ji a ransa Dan Allah ya hallice shi mutum ne mai kishi bala'i lokaci d'aya yaji ita kanta Fateeman haushi take bashi.

Ita kuwa ko motsawa ta kasa yi Daga inda take tsaye, shawara take ji taje wajan sa ko kuma kawai ta fice daga d'akin.

Yi tayi kamar zata zo inda yake sai kuma ta juya tana k'ok'arin bud'e k'ofa, duk abinda take yana kallon ta hakan yasa ya fara tarin k'arya da, da sauri ta dawo ta zauna kusa dashi tare da rik'e shi tana yi masa sannu.

Tsayar da tarin yayi tare da jawo ta ta fad'a jikin sa yace, "Wash kin fama min ciwon Zuciya ta" ya fad'a tana dafe kirji.

Ita kuwa ta zata da gaske yake sai ta K'ara rud'e wa tana fad'in, "Sannu, ka sake ni na tashi tunda ina fama maka ciwo."

"Tashin ki shi zai saka ta cigada da ciwon, wayyo Allah" ya fad'a yana cize baki.

Sunkuyar da kai tayi tana jin wani iri a jikin ta, d'ago wa tayi zata yi masa magana suka had'a ido, kallan juna suke ko kifta ido basa yi har lokacin tana jikin sa.

Iska ya hura Mata a fuska ta lumshe ido yace, "I love u Fateema" ya fad'a yana kawo fuskar sa dai-dai fuskar ta har  numfashin na had'uwa da juna.

K'ara rik'e ta yayi yace, "Ki yafe min laifi na Fateema ki amince da aure na".

Shiru tayi ita dai bata amsa ba kuma bata tashi daga jikin sa, a hankali tace, " Ka sake ni babu kyau fa".

"Saki fa kika ce? Babu Wannan Kalmar tsakanina dake har abada, cewa zaki na kyale ki ba na sake ki ba, to laifi ne dan mata ta kwanta a jikin mijin ta?" Ya fad'a yana had'e fuskar su waje d'aya yana goga hancin sa jikin tana.

Wani iri ta fara ji a jikin ta hakan yasa ta fara k'ok'arin kwacewa tana fad'in, "Ka k'yale ni Dan Allah bana so."

Sakin ta yayi ta mik'e yace, "Tunda bakya so na kyale ki farin cikin ki shine nawa."

STORY CONTINUES BELOW

"Fateema baki ce komai ba kin yafe min?".

Rik'e k'ugu tayi tace, " Eh na yafe maka amma zab'i na Suhail ne ba kai ba" ta fad'a tana juyar da fuskar ta.

Mik'ewa yayi a hankali ya zo inda take bai tsaya b'ata lokaci ba ya had'e ta da bango ya matse ta sosai, nan take idon sa suka canja kala yace, "Naji kin zab'i Suhail tunda baki da tausayi baki da imani, amma kafin ki bar d'akin nan sai kin saka wuk'a kin kashe ni in ba haka ba bazan tab'a barin ki ki fita ba kuma bazan tab'a yafe miki ba har abada" ya fad'a cikin fad'a Sosai.

Hannu ta yaja suka k'arasa kan center table d'in d'akin ya d'auko wuk'a ya saka mata a hannu yace, "Kashe ni ki huta Fateema kashe ni".

Ganin tayi shiru ra kasa komai sai kai da take girgiza wa yace, " Baki San da ki fad'a min abinda kika fad'a ba gwara ki saka bindiga ki harbe ni ba? Na rasa abinda zan miki ki yafe min babu irin rok'on da ban miki ba amma kinki, ya kike so nayi da raina? Ina zaki kai hakkin na Fateemah? Kullum cikin ciwo nake amma ke ko a jikin ki sai ma wajan waccan kika je har yana rik'e miki hannu, ki kashe ni Fateemah ki huta".

Har da wuk'ar tayi ta fashe da kuka mai k'arfi, runtse ido yayi tare da rungume ta a jikin sa shima yana hawayen.

Cikin kuka Fateemah tace, "kaine zab'i na Yaya na tun ina k'arama kai nake so me yasa ka kasa fahimtar cewa soyayyar ka ta Riga ta zama jiki na ba? Na tabbata kaima ka mutu nima binka zanyi, kayi Hak'uri bazan k'ara fad'ar hakan ba".

Ajiyar zuciya yake yana shafa bayan ta yana lumshe ido, d'ago kai tayi ta gyara glass d'in ta tace, " Na yafe maka duk abinda ya faru nasan bisa rashin sani ka aikata hakan, Abu d'aya na kasa mantawa shine sunan karuwa da ka kira ni dashi, har gobe ina jin zafin Wannan kalma."

Bud'e ido yayi ya sake ta ya tsuguna a gaban ta yace, "Ki yafe min Dan Allah badan niba nasan nayi Kuskure amma ki yafe min dear."

Itama tsuguna tayi ta rik'e hannun sa tace, "ka daina rok'o na haka komai ya wuce, bazan iya rayuwa ba babu kai."

"Sonki Fateemah ya ratsa zuciya ta ya shiga cikin jini na ya tafi kwakwalwa, duk motsina bana yin sa sai na tuna ki, kin shiga zuciya ta kin zauna ki tare ko ina Baki bar wani waje ba balle wata ta samu inda zata rab'a, ki rik'e min alk'awari kada kici amanata Fateemah wallahi zan iya rasa raina akan ki, ina kishin ki fiye da yadda bakya tunani."

Rik'e hannun ta k'ara yi tace, "Baza ka tab'a samu na da cin amana ba ina fatan kai ma haka."

Murmushi yayi yace, "Nayi miki alk'awari Beauty na."

Sunkuyar da kai tayi tare da dariya tana jin farin ciki na ratsa ko ina na cikin ta, k'aramin bakin ta ya zubawa ido kome ya tuna sai kuma ya had'e rai tare da mik'ewa cikin fushi ya shiga bedroom.

Cike da mamaki Fateema ta bishi da kallo, mik'ewa tayi ta bi bayan sa tana shiga yayi saurin dakatar da ita da fad'in, "kada ki shigo Fateema" ya fad'a yana runtse ido babu abinda yake tunawa sai lokacin da Manager yake sunbatar bakin ta.

Zata yi magana ya D'aga mata hannu yace "kije kawai".

Cikin sanyin jiki Fateema ta juya ta fita zuciyar ta cike da tambayoyi.
Nasan wasu sun gyara zama ana jira aga 20 read more ko?πŸ˜‚. To kwalelen kuπŸ˜›πŸ˜›
*COMMENTS & SHARE.*

© *NEAT LADY.*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

STORY CONTINUES BELOW

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*Iyalan grp din MACE TA GARI.πŸ‘πŸ»πŸ˜*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

_Kai yasin a gurguje._πŸ˜ŽπŸ˜‚

*SHAFI NA 28πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Haka Fateema ta huni tana tunanin laifin da tayiwa Fa'iz lokaci d'aya haka ya canja kamar bashi ba.

Suhail kuwa tunda yaga halin da Fa'iz yake ciki jikin sa yayi sanyi haka ya koma gida jiki babu kwari.

*AFTER FIVE DAY'S.*

Cikin kwanakin Fateema da Fa'iz wata sabuwar shak'uwa ce ta shiga tsakanin su koda yaushe suna tare a garden suna hira cikin soyayya, hakan ba k'aramin farantawa Mamy da Umma yayi Dan basu da burin da ya wuce Fateema ta auri Fa'iz.

Zaune suke a parlour gabad'ayan su kan Fateema a sunkuye taba sauraran Abinda Dady zaice.

Gyaran murya Dady yayi yace, "Kamar yadda muka fad'a a kwanakin baya mun bawa Fateema sati d'aya ta zab'i Wanda yayi mata, to yau Allah ya kawo mu ranar Dan haka Fateema ke muke sauraro cikin Suhail da Fa'iz wanne kika zab'a a matsayin miji?".

Gaban ta ya fad'i tana d'ago kai suka had'a ido da Momy Suhail, saurin sunkuyar da kai tayi tace, " Dady ni YAYA FA'IZ NE ZAB'I NA, Tana gama fad'ar hakan ta mik'e da sauri zata bar parlourn.

Jin furuncin ta yasa hankalin Momyn Suhail ya tashi dashi kansa Suhail d'in, cikin sauri ya mik'e ya tare Fateema dake niyar fita yace, "Ki tausayawa rayuwa ta Fateema komai zai iya faruwa dani in kika bar ni ki taimaka ......." Maganar ta tsaya sakamakon baya da yayi ya fad'a jikin kujera.

Da gudu kowa ya taso yayi kan Suhail dake kwance a in unconsciously,kuka mai k'arfi mahaifiyar ta ta saki ta mik'e ta rik'e Fateema tana fad'in,

"Ki tausayawa masa Fateema badan halin mu ba, shi kad'ai da namiji da Allah ya bamu Dan Allah ki tausaya".

Fateemah kuwa ta kasa magana sabida kukan da ya ci k'arfin ta, babu Wanda bai tausayawa Suhail da iyayen sa ba Dan shi kansa mahaifin nasa daurewa kawai yake .

Fa'iz kuwa ko a jikin sa tunda dai Fateema ta zab'e shi baiga abinda zai saka hankalin sa ya tashi ba, Mamy ta kalle shi tace, "Fa'iz kazo ka bashi taimakon gaggawa mana."

Sai a time d'in ya mik'e ya d'auko ruwa ya shafa masa a fuska amma shiru bai farfado ba, kallan su yayi yace,"kawai muje asibiti shine Abu mafi sauki."

Ba tare da b'ata lokaci ba aka kinkimi Suhail sai asibiti,  gabad'ayan su suka tafi banda Fateema da Auta.

Ana zuwa aka karb'i Suhail tare da bashi taimakon gaggawa, bayan Minti sha biyar likitan ya fito yace su same shi a office.

Gabad'ayan su suka shiga banda Fa'iz dake zaune a gefe yana shirin kiran wayar Mamy Dan ya ganta hannun Fateemah.

A office d'in Dr ya kalle su yace, Gaskiya jinin d'an Ku ya hau Sosai fiye da yadda bakwa tunani, Allah ne ya rufa asiri da yadda ya fad'in nan zai iya kamuwa da cutar shanyewar b'arin jiki, bayan haka zuciyar sa tana k'ok'arin kamuwa da ciwo, shawarar da zan Baku shine Ku daure kuyi masa abinda yake so ko indai da hali in ba haka ba za'a iya rasa shi."

STORY CONTINUES BELOW

Kowa shiru yayi har Dr ya gama suka taso jikin sanyin jiki suka fito.

A zaune suka ga Fa'iz Dady ya kalle shi yace, "Fa'iz wanene ni a wajan ka?".

Cikin fad'uwar gaba yace, " Mahaifi mana Dady meyasa kake Wannan maganar?".

"Indai ka yarda ni baban Kane ina mai baka umarni da ka barwa Suhail Fateema ya aure ta, umarni ne ba shawara ba kuma na gama yanke hukunci Yanzu in an sakko daga masallaci za'a d'aura aure bana son wata magana" yana gama fad'ar hakan ya juya ya bar wajan.

Tashin hankali Wanda ba'a saka masa rana shi Fa'iz ya shiga, rasa ma abinda zaiyi yayi kawai sai ya mik'e ya bar wajan cikin sauri.

Da gudu Mamy ta bishi amma ina kafin ta cinmasa har ya shiga mota ya bar asibitin a guje.

Dawowa tayi ta kalli Umma tace, "Wallahi bazai yu ba akan farin cikin wani baza mu tauyewa d'an mu hakki ba, sai dai ya sake ni amma bazan tab'a bari hakan ta faru ba" ta fad'a cikin fushi.

Umma dai shiru tayi Allah yasa su Momy sun shiga wajan Suhail Mamy take fad'ar hakan, ita kanta taji haushin abinda yayi amma itama tana bayan Mamy.

Bayan minti biyar harabar asibitin ta cika da mutane sai yahaniya ake, da gudu wani Dr ya shigo yana hakki ya kalli Mamy yace, "Hajiya an kawo Fa'iz yanzu yayi accident bai San inda kansa yake ba."

Tirk'ashiπŸ€”πŸ€”
Sai Hak'uri fa nasan yau nayi muku long page d'in da kafin Ku gama karantawa idon Ku yayi ruwa.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜›

Kuyi Hak'uri da ciwon ciki na tashi yau wlh da bazan ma yi typing din ba.😟
*COMMENTS & SHARE.*

© *NEAT LADY.*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*TUKWICI GA:-*
*NEAT LADY NOVEL'S GRP.*πŸ₯°

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

I love u too dear Zeey😘

*SHAFI NA 29πŸ“‘*

*__________πŸ“–* Cikin tashin hankali suka mik'e ba tare da b'ata lokaci ba suka fita da sauri kowa yana salati, a bakin d'akin suka tsaya sabida an hana kowa shiga ciki, a nan suka tarar da Abie shima hankalin sa a tashe.

Babu Wanda ya kula wani kowa da abinda yake sak'awa a ransa.

Dady koda ya samu labari ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba da sauri ya dawo shima a nan ya tarar dasu a tsaye sunyi tagumi.

Kiran sallah ne yasa su Abie suka fita suka nufi masallacin juma'a, har aka idar da sallah babu labarin Fa'iz Dan ko likitocin basu fito ba balle a San halin da yake ciki.

Suhail kuwa ya farka yana zaune akan gadon ya zuba tagumi yana tunani, kusa dashi Momy ta dawo Dan ita bata San ma Fa'iz bashi da lafiya ba Dan Dady bai fad'a mata ba, zama tayi tace,

STORY CONTINUES BELOW

"Suhail ka kwantar da hankalin ka Fateema taka ce insha Allahu."

Ajiyar zuciya yayi yace, "Momy bazai yu ba sabida Fateemah bata sona Fa'iz take so bana so na takura mata, a kyale ta kawai kada ayi mata auren dole."

"Babu zance wani auren dole mahaifin Fa'iz d'in ne ya fad'a da bakin Dan haka ka kwantar da hankalin ka kaji".

Murmushi kawai yayi ya rufe ido.

Dadyn sane ya shigo ya kalli Suhail yace, " Sannu Ashe ka farka, ya jikin naka?".

"Da sauki Dady, lafiya naga hankalin ka a tashe?".

"Fa'iz ne yayi accident wallahi har yanzu bai San Wanda yake kansa ba kuwa awa uku kenan."

Zaro ido Momy tayi tace, "Subahanallah Wannan wacce irin masifa ce, Allah ya bashi lafiya."

Suhail kuwa ba k'aramin tausayin Fa'iz yaji tabbas yasan Fa'iz yafi shi son Fateemah kuma yasan shine ya dace ya aure ta, amma baya jin zai iya bar masa ita ba.

Fateemah kuwa tunda suka fita take kuka kamar ranta, Auta ce take ta rarrashin ta amma taki yin shiru sosai kuka take.

Sai da ta gaji Dan kanta Sannan ta mik'e ta shiga tayi alwala ta tayar da sallah.

Har yamma babu Wanda ya dawo a cikin su ganin hakan yasa Fateema ta shiga  kitchen Dan ta dafa musu abinci akai asibitin, jikin sanyi jiki take aiki gaban ta na fad'uwa, ta rasa dalilin fad'uwar gaban, babu b'ata lokaci ta dafa abinci ta zuba a kula ta fito harabar gidan.

Drive tayiwa magana ta bashi tace ya kai asibitin, Auta ce ta fito da gudu tana fad'in, "Ya tsaya ni muje tare."

Motar ta shiga suka tafi ita da drive aka bar Fateemah a gidan.

Lokacin da likitocin suka fito suka d'aya ya kalli Dady yace, "Alhaji har yanzu bai farfad'o ba amma an samu numfashin sa yayi dai-dai, ya samu karaya a hannu guda d'aya sannan bp d'insa ya hau sosai, kwanakin baya daku mukayi magana akan kada a dinga b'ata masa rai sabida ciwon sa amma aka tsallake doka har jinin sa ya hau haka, bazan b'oye muku ba daga nan zuwa gobe da safe indai bai farka ba zamu iya rasa shi Dan Gaskiya yana cikin matsala Sosai addu'ar Ku kawai yake buk'ata."

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abinda kowa yake maimaitawa, Mamy ce tayi k'arfin halin cewa, "Yanzu zamu iya ganin sa?".

"A'a ba yanzu ba Gaskiya sai zuwa anjima, amma mutum biyu su shiga in sun fito wasu su shiga amma banda surutu."

Suka amsa shi kuma ya bar wajan.

Mamy da Umma ne suka fara shiga, a kwance yake numfashi a kirji hannun sa d'aure k'afar sa ta dama ma an d'aure, kansa a d'aure da bandage idon sa a rife.

Da kuka Mamy ta fito sabida tausayin Fa'iz dake ratsa ta, Umma ma daurewa kawai tayi amma sai da tayi hawaye.

Kowa ya shiga haka yake fitowa jiki a salub'e, Umma dai na zaune tayi tagumi Dan ita har ga Allah ta Fitar da rai akan Fa'iz gani take bazai tashi ba.

Auta kuwa kuka take Sosai ta d'auki wayar Mamy ta kira Fateemah amma bata d'auka ba, text ta rubuta ta tura mata tana hawaye.

Suhail kuwa ya kasa sukuni so yake kawai yaje ya ga halin da Fa'iz yake ciki, mik'ewa yayi tare sa dafe kai yace, "Momy bara naje naga jikin Fa'iz hankali na ya kasa kwanciya."

"To in zaka iya muje tare nima so nake naje na gano shi, d'azu Shukra tayi min waya wai itama tana hanyar zuwa nan d'in."

Baice komai ba ya fita yana dafa bango, a bakin d'akin ya gansu da sauri Amir ya rik'e shi yana fad'in, "Haba Suhail me ya kaika fitowa yanzu? kai da baka da lafiya."

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi yayi yace, "So nake kawai nazo naga halin da Fa'iz yake hankali na ya kasa kwanciya."

Murmushi Amir yayi yace, "To mu shiga ga ganshi."

Tare suka shiga da Amir shi kuma ya tsaya a bakin k'ofa yana kallon sa, zama Suhail yayi a bakin gadon ya zubawa Fa'iz ido yace, "Kayi Hak'uri Fa'iz nasan duk a dalili na ka shiga Wannan halin ka yafe min, nayi tunani babu Wanda ya dace ya auri Fateemah sai kai, Kaine ka dace da ita bani ba nidai burina ka yafe min Dan Allah" ya fad'a yana share hawaye.

Dadyn Fa'iz ne yazo ya d'aga shi yana fad'in, "Haba Suhail ka kwantar da hankalin ka, ka share hawayen ka."

"Dady Dan Allah ko bayan raina ka bari Fa'iz ya auri Fateemah shine ya dace da ita, tun tana k'arama yake sonta ni na Hak'ura domin ni ban dace da Fateema ba."

Jikin kowa yayi sanyi a wajan zuciyar kowa cike da tausayi Suhail ya cika musu zuciya.

Cikin sark'ewar murya yace, "Dady Dan Allah a kira Fateemah na nemi yafiyar ta Dan Allah."

Kallon Amir Dady yayi yace, "jeka ka tawo da Fateemah Yanzu."

Ya amsa da toh ya juya ya tafi.

Fito dashi akayi aka zaunar dashi a kujerun dake wajan d'akin, Ajiyar zuciya yake yana runtse ido sabida shi kad'ai yasan halin da yake ciki.

Fateemah kuwa tunda Amir ya fad'a mata hankalin ta ya tashi duk da har lokacin bata San Fa'iz bashi da lafiya ba, jikin sanyi jiki ta saka hijjabi suka fito.

D'aki aka komar da Suhail Dan anga jikin nasa na Neman tashi, tunda Fateemah ta shiga d'akin gaban ta ke fad'uwa, a jikin bango ta tsaya hawaye ya cika mata ido.

Murmushi Suhail yayi yace, "Fateema Dan Allah kiyi Hak'uri ki yafe min laifin da nayi miki na yanzu dana baya."

Shiru bata ce komai ba  sai share hawaye da take yi, Suhail ya kuma cewa, "Kinyi shiru baki ce komai ba hakan yana nufin baki yafe min ba kenan?".

Girgiza kai tayi tace, " Na yafe maka komai ya wuce."

Ajiyar zuciya yayi tare da fad'in, "Alhamdulillah, Momy ta yafe min yanzu bani da nauyin kowa a kaina sai Fa'iz, in ya farka Dan Allah kuce ya yafe min nasan nine na sashi halin da yake ciki yanzu."

Momy ce tace, "Ka daina Wannan maganar Suhail."

"Momy ni Kad'ai nasan abinda nake ji bana jin zan tashi ina ji kamar rayuwa ta tazo k'arshe."

Kasa magana kowa yayi sai hawaye da wasu suke sharewa.

Likita ne ya shigo yace kowa ya fita zasu duba shi, juyawa suka yi cikin sanyi jiki suka fita.

Tunda Fateemah taji labarin halin da Fa'iz yake cikin take kuka, koda ta shiga d'akin kuka take kamar ranta zai fita sai kallon sa take tana kuka.

Mamy ce da kanta ta fito da ita tace Amir ya maida gida ita da Auta da Umma tunda dare ya fara ita zata kwana a wajan sa.

Umma tace, "Suje ni anjima na tawo."

Har suka je gida Fateema kuka take, Amir da Auta ba k'aramin tausayi ta basu ba sai bata baki suka amma taki yin shiru.

Bayan sallar i'sha su Umma dasu da Abie suka dawo gida aka bar su Mamy a can, kowa jikin sa sanyaye suka kwanta ranar babu Wanda ya kula abinci.

Misalin k'arfe biyu na dare aka yiwa Dady waya, d'aukar wayar yayi ba tare da ya duba ba yace, "Assalamu alaikum".

" Kazo asibiti yanzu Fa'iz ya farka amma yana cikin wani hali."

Bai tsaya ya k'arasa ji ba ya kashe wayar ya mik'e da sauri, Umma ta kalle shi tace, "Lafiya?".

STORY CONTINUES BELOW

" Babu lafiya tashi muje asibiti."

Mik'ewa tayi itama ta saka hijjabi suka fito.

A parlour suka ga Fateemah zaune tayi tagumi tana tunani, Umma ta kalli Dady ta kalli Fateemah tace, "Fateemah lafiya kike zaune a nan?".

Da sauri ta mik'e ta juyo tace, " Umma ina zakuje? Umma me ya samu Yaya na Dan Allah Ku fad'a min na kasa bacci jiki na yana bani wani Abu yana shirin faruwa" ta fad'a tana fashewa da kuka.

Kallan ta Dady yayi yace, "Jeki ki saka hijjabi kuzo muje asibitin."

Da sauri ta shiga d'aki ta saka hijjabi suka tafi.

A can asibiti kuwa Mamy kuka take Sosai sabida halin da Fa'iz yake ciki, gabad'ayan numfashin sa ya bar ciki ya dawo wuya da dak'yar yake sauka, da taimakon oxygen numfashin nasa yake sauka.

Likitoci ne a kan sa a suna k'ok'arin ceto rayuwar sa, duk dauriyar Umma sai da tayi kuka da taga halin da Fa'iz yake ciki, Fateemah kuwa a bakin tagar da ake ganin sa ta tsaya tana kuka Sosai.

A can b'angaren Suhail shima jikin nasa ya tashi amma bai kai na Fa'iz zafi ba, shima wani likita ne a kansa yana duba shi.

Bayan kamar minti goma wani likita ya fito daga d'akin da Suhail yake ya shiga d'akin da Fa'iz yake, babu jimawa ya fito yana cire mask d'in fuskar sa.

Da sauri Abie ya Mik'e yace, "Dr ya jikin nasu?".

Ajiyar zuciya yayi yace, " Kuyi Hak'uri Allah yayiwa d'aya daga cikin su rasuwa, d'aya kuma yana buk'atar addu'ar Ku."

Tun kafi ya fad'a kowa yasan Fa'iz ne Dan kowa ya Fitar da rashi sabida halin da yake ciki.

Dady ne yayi k'arfin halin cewa, "Wanne dafa ciki?".

Dr yace.............

Kuyi Hak'uri rashin Lafiya ke hanani typing.πŸ˜”

*COMMENTS & SHARE.*
© *NEAT LADY.*

*°πŸ”˜°BANSAN LAIFI NA BA°πŸ”˜°*
        _{RAYUWAR FATEEMAH}_
              *1441H/2020M.*
       
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata burin mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFEπŸ‡πŸΌ*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*•
πŸ…–πŸ…¦πŸ… ᎳᎬᏞfαŽ¬α’αŽ¬.

*SADAUKARWA GA:-*
*MISS XERKS.😍* _Hausawa sunce babbar Yaya ma uwa._πŸ’ƒπŸ»

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITTER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 30πŸ“‘*
*__________πŸ“–* Dr yace, "Allah ya karb'i rayuwar SUHAIL sai dai muyi Hak'uri muyi masa addu'a" yana gama fad'ar hakan ya juya ya tafi.

Baya Momy tayi zata fad'i Umma tayi saurin rik'e ta cikin sauri, kasa kukan Momy tayi sai girgiza kai da take tana runtse ido.
Babu Wanda baiji mutuwar Suhail ba a cikin su, kuka Sosai Fateemah take Dan in tace bata ji mutuwar sa ba tayi k'arya, babu Wanda yake magana a cikin su kowa yayi shiru cike da alhini.
Mazan ne suka shiga d'akin cikin k'arfin halin, k'arasawa suka yi gaban gadon suna kallon fuskar sa, Allah mai iko kamar bashi ne ya gama magana mintina kad'an da suka wuce ba, mahaifin sa ya d'aura hannun sa a fuskar sa yace, "Allah ya jik'an Suhail, Allah yasa can tafi nan a wajan ka."
STORY CONTINUES BELOW

Su Dady suka amsa da Amin, juyowa yayi ya kalle su yace, "kunga tunda mutuwar dare ce gwara mu d'auke shi aje ayi masa wanka a had'a shi gobe k'arfe takwas a kai shi."
Abie yace, "Hakan ne ya kamata, amma a sanar da mutane a waya."
"Eh in mun koma gida zan saka a tura musu text message."
Babu b'ata lokaci aka fito da Suhail aka zo aka wuce dashi ta gaban Su Mamy da suke rik'e da Momy da Fateemah, wasu hawaye ne masu zafi suka suka shiga zarya a idon Momy, babu Wanda yayi yink'urin hana ta dan babu Wanda ya San abinda take ji mutuwar d'a ba wasa bane.
Umma ce tayi k'arfin halin cewa, "Yanzu fa addu'a yake buk'ata ba kuka ba, Wanda ya halicce shi ya karb'i abinsa daman kuma ya fimu son sa tunda shi yayi shi, fatan mu shine Allah yasa ya had'u da haliccin sa lafiya."
Cikin tawakkali Momy tayi tana k'ok'arin tsayar da hawaye amma ta kasa.
Mamy tace, "Mu tashi muje can ayi gidan sai a bar Fateema a wajan Fa'iz d'in kafin da safe."
Girgiza kai Fateema tayi tace, "A'a Mamy nima zani can d'in."
Umma tace, "Shikenan Amir ka zauna dashi kafin safiya sai a San yadda za'a yi."
D'aga kai kawai Amir yayi Dan shima yaji mutuwar Suhail, d'akin Fa'iz ya koma shima har lokacin numfashin dai sai a hankali.
An yanke shawara kawai a tafi Kano ayi masa suttura a can tunda kakan nin sa sun ce a tawo.
Cikin Daren aka d'au hanyar Kano, amma an kira Amir an tafi dashi an bar Mamy da Fateema a wajan Fa'iz tunda baza bar shi kad'ai ba.
Bayan sallar asuba suka shiga Kano aka shiga gidan, babu Hutu sallah akayi aka d'aura ruwan wanka, babu b'ata lokaci aka had'a Suhail akayi masa sallah aka tafi kaishi gidan sa na Gaskiya.

Ana tafiya Shukra tazo gidan tana ihu da tumami, rarrashin ta aka dinga yi ana bata baki aka samu tayi shiru tana Ajiyar zuciya.
A can kuwa bayan tafiyar su tunda suka shiga d'akin da Fa'iz yake Fateema take kuka, Abu biyu ne ya tarar mata na farko ga rashin lafiyar habibin ta na biyu na mutuwar Suhail, Mamy ta matso kusa da ita ta dafa ta ita kuma ta kwanta a kafad'ar Mamy tana share hawaye.

Ana sallar Azahar su Umma suka d'auko hanyar Abuja, bayan sun sauka kuma Mamy da Fateema suka tafi Dan yi musu gaisuwa.
Tun daga k'ofar gidan Fateema ta fara kuka, gani take kamar in ta shiga zata ga Suhail d'in a ciki, koda suka shiga suka yiwa Momy gaisuwa zama suka yi suka yi shiru kowa yana sak'a da warwara.
Shukra ce ta fito daga d'akin hannun ta rik'e da cazbi, had'a ido suka yi da Fateema wacce ke kallon da cike da mamakin bak'i da ramar da tayi.
Ita kuwa Shukra mamakin ganin Fateemah take, gaisuwa suka yi mata ta zauna tana satar kallon Fateemah, wani b'angaren na zuciyar ta kuma haushin ta take ji sabida a dalilin ta Yayan ta ya mutu.
Jirgin k'arfe biyar suka biyo suka dawo Abuja.

*BAYAN KWANA UKU.*

Jikin Fa'iz dai yana nan yadda yake babu wani cigaba yana nan kwance kamar gawa.
Fateema kuwa taje gidan kakanninta daga can take zuwa asibitin Dan kullum sai tazo inda kuma tazo to da kuka take komawa.
Likitoci ne zaune su uku a wani d'an d'aki da alama tattaunawa suke, d'aya daga cikin su yace, "Wai Yanzu haka zamu zuba ido Fa'iz yana cikin Wannan halin mu kasa yin komai?."
Na gefen sa yace, "To ya kake so muyi? Ai bamu zamu bashi lafiya ba Allah ne mu munyi iya k'ok'arin mu amma abun yaci tura, ni kaina ina tausayin Oga duk a sanadin soyayya ya fad'a Wannan hali."
STORY CONTINUES BELOW

D'ayan yace, "Oga yayi mana koma a rayuwa ko bai bamu wani Abu ba yadda muke zama dashi ayi wasa da dariya ya ya kamata muyi wani abun."

"To me kuke so muyi?."

"Yauwa ina da shawara, me zai hana muje mu cewa mahaifin sa in da dama ayi masa aure da wacce yake so kafin ya farka ta haka ne kawai in ya farka zai dawo normal."
"Good idea mutumina dad'i ba dakai basira wallahi, hakan zamu yi kaga Dole su aura masa ita ko babu komai mun samu ladan ceto ran musulmi."
D'ayan yace, "to me kuke jira muje mana Yanzu muyi musu bayani tunda duk suna nan Yanzu."
Babu tab'a lokaci suka fito, a wani parlour suka gansu zaune gabad'ayan su har da Baba Ladi Fateema da Auta ce kawai babu.
Gaishe su suka yi Sannan d'aya ya fara cewa, "Wato Abba a Gaskiya Oga Fa'iz ciwon zuciya ya kama shi sosai in ya farka ma babu mu da tabbacin zai ji sauki lokaci d'aya, samun saukin sa yana wajan Allah yana wajan Ku bakin d'aya."
Kafin Dady yayi magana Baba Ladi tayi caraf tace, "Kamar ya kenan likita?".
Ya gyara tsayuwa yace, " Shawara zamu baku Wanda muke ganin zai amfane mu gabad'aya kuma mu ceto rayuwar Oga."
Abie yace, "Muna jin ka."
"Abinda nake so nace shine, kamar yadda kuka sani duk a sanadin soyayya ya fad'a Wannan hali to me zai hana indai an San wacce yake so kuma itama tana sonsa mai zai hana a d'aura musu aure kafin ya tashi, yana farkawa ya samu Wannan labarin tunda abinda yake so kenan tabbas zai samu lafiya fiye da tunanin Ku."
Baba Ladi tace, "To yaro Wannan ai Abu ne mai sauki hakan ma za'a yi wallahi, mun gode Sosai da Wannan shawarar Allah yayi maka albarka kaji d'an nan."
Murmushi yayi cike da farin ciki ya amsa da Amin suka fita daga d'akin.
Baba Ladi ta kalli Abie da Dady tace, "To me kuke jira a San abinda za'a yi tunda dai hakan zai saka ya samu sauki Sosai sai a d'aura, daman ni na k'agu naga auren Fa'izu."
Abie yace, " Ai hakan ma za'a yi Hajiya gobe in Allah ya kaimu bayan sallar asuba za'a gabatar da komai, shi ya zama wakilin Fateemah."
Dady dai yana jin su baice komai ba dan yasan yana cewa wani Abu Hajiya zata fara fad'a.
Mamy da Umma kuwa ba k'aramin farin ciki suka shiga ba har farin cikin su ya ka b'oyuwa suka dinga murmushi.
Baba Ladi tace, " Allah ya kaimu, har na k'agu goben ma tayi."
Suka yi dariya ba tare da sunce komai ba.
Fateemah kuwa bata San me ake yi ba tana can wajan Ganny.
_A gurgujeπŸƒπŸ»‍♀._
Washe gari

Da asuba mutanen masallaci suka shaida auren Fa'iz da Fateemah akan sadaki naira duba hamsin.
Fateema tana kwance akan gado taji wata irin iska na ratsa ko ina na jikin ta, bata San dalilin da yasa ta tsinci kanta a cikin farin ciki ba duk da tana jin kanta yayi mata nauyi, tashi tayi ta bud'e taga sanyin asubayi yana ratsa ta tana lumshe ido.
Sama take kalla tana murmushi.
Tsintar kanta tayi da shiga toilet tayi wanka ta zauna gaban mirror ta tsara k'walliyya ta gani ta fad'a, fitowa tayi daga d'aki ta shiga kitchen ta d'aura breakfast.
Ta had'a abinci ta jera kan dining Sannan ta zuba Wanda za'a tafi dashi asibiti, so take kawai mutan gidan su tashi dan ita ta danganta farin cikin da take ciki da samun lafiyar Fa'iz.Zama tayi a kan kujera so kawai take wani ya fito, Umma ce ta sakko cikin sauri tana so ta had'a abinci a kaiwa Amir dake asibiti.

+

Fateemah ta gani a zaune tana murza zoben hannun ta, murmushi Umma tayi tace, "Amarya yau da sassafe kika tashi?, A'a wannan kwalliyyar duk ta ganin ango ce?".

Murmushi tayi duk da bata gane maganar Umma ba tace, " Umma barka da asuba. "

"Kin tashi lafiya?".

" lafiya lau Umma " ta fad'a tana sunkuyar da kai.


Kallon dining Umma tayi cike da mamaki tace, "Wai har Girki kinyi da safiyar nan?".

" Wallahi Umma ji nayi kawai ina son yin aiki yau shine na tashi na girka. "

"Kin kyauta Allah yayi miki albarka, bara na zuwa anjima sai Ku tafi in driver ya fito" ta fad'a tana niyar komawa sama.

Da sauri Fateema tace, "Umma basai an kaini ba zan tafi ni kad'ai."

Rik'e baki Umma tayi tace, "Toh yau Faty da shauk'in angon kika tashi kenan?, A'a kin San dai bana son kina driving ki bari Yanzu zaizo Ku tafi" ta fad'a tana dariya.

Fateemah ta amsa da to, a zuciyar ta kuwa tunani take akan abinda Umma ta fad'a, Amarya da Ango ita dai tasan Umma bata yi mata wannan wasan.

Zuwa Iliya ta kashe mata tunani, hijjabi ta saka ta d'auki kai basket d'in mota, har ta juya zata je d'akin Mamy sai ta tuna jiya girkin tane tana d'akin Dady.

Da sallama ta tura k'ofar D'akin ta shiga, Amir ne ya amsa fuskar sa d'auke da murmushi yace, "A'a amarsu ta ango yau kece da kanki da safiyar nan?."

Y'ar dariya tayi tace, "Ina kwana?".

" Lafiya lau, ya me jiki?".

"Kai zan tambaya mai jiki ai."

Kallon inda Fa'iz tayi tagan shi kwance da alama numfashin sa ya dawo dai-dai, k'arasawa wajan tayi tana kallon fuskar sa.

Kallan ta Amir yayi ya d'

Saki dariya yace, "Amarya wannan kallo haka ai sai ki kwashe masa kyaun nasa."

Dariya tayi bata ce komai ba ta zauna a kujerar dake gefen gadon.

Amir yace, "To tunda kinzo bara naje gida na canja kaya na dawo nayi break."

Ta amsa da to ya juya ya fita daga d'akin cikin fara'a Dan har ga Allah soyayyar Fa'iz da Fateema burge shi take yi.


Hannun ta tasa cikin nasa ta rik'e tana murzawa a hankali, kamar almara idon sa ya fara motsi har ya fara bud'e idon a hankali.

Fateemah kuwa bata kula bama ta rufe ido amma har lokacin hannun ta na cikin hannun sa Mara ciwon, a hankali juyo ya sauke idon sa a kan Fateema da ta jingina kanta a kujera.

A dak'yar ya bud'e baki yace, Beauty ".


Kamar a mafarki haka taji tayi saurin d'ago kai suka had'a ido, murmushi ta fara tana fad'in, " Alhamdulillah ka farka ashe,? Bara naje na kira Dr " ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa.

Rik'e hannun ta yayi ya girgiza mata kai alamun A'a kar taje.

Komawa tayi ta zauna tana kallon sa, sun kasa d'auke ido daga kan juna sun zubawa juna ido ko kiftawa basa yi.

Sun d'auki mintina masu tsayi kafin ta fara d'auke idon ta tana murmushi ta sunkuyar da kai, matse hannun ta yayi yace, "Fateemah wanne abin alkairi ne ya faru naji ina farin cikin da ban tab'a yi ba?".

" Nima haka Yaya na amma ban zan dalili ba."


Murmushi yayi yace, "Tunda zuciyoyin mu suna cikin farin ciki nasan wani abin alkairi ya faru beauty."

Cize baki yayi yace, "Beauty ina son Wanke baki ya za'a yi?" Ya fad'a yana zuba mata ido.

Mik'ewa tayi tace, "Bara naga toilet d'in a kawai toothpaste."

Sakar mata hannu yayi ya ta shiga ta duba, abinka da private hospital komai akwai, d'auko wa tayi had'e da wani d'an Kofi ta fito.

Mik'a masa tayi tace, "Gashi to kayi."

Kallon ta yayi ya kalli hannun sa yace, "To da wanne hannun zanyi? Wannan ciwo ne a jiki Wannan kuma an sami drip duk ya kumbura" ya fad'a yana yamitse fuska kamar wani yaro.

Amir ne ya bud'e d'akin ya shigo cikin sallama.

Tsakin da Fa'iz yayi shi yaja hankalin sa gare shi da sauri ya k'arasa wajan yana fad'in, "Fa'iz Ashe ka farka, ya jikin? An fad'awa Dr?".

Cikin muryar da bata fita Sosai yace, " Ban sani ba haka kawai kazo ka b'ata min komai."

Fita Amir yayi ya kira Dr suka shigo tare, duba shi yayi ya kwance bandage d'in kansa tare da k'ok'arin Wanke ciwon wajan.

Wanke wa yayi Fa'iz kuwa sai wani b'ata rai yake yana kauda kai, drip yake niyar sa masa ya yayi saurin cewa,


"Me kake shirin yi wai?".

Dr yayi murmushi yace, Oga drip za'a saka ma Dan kaji kwarin jikin ka."


D'age gira d'aya yayi yace, "ce maka ayi bani da kwari, ni ji nake yanzu ma na fika Lafiya tunda gani ga beauty na, so kawai ka kyale bana needing wani drip."


Murmushi likitan yayi Dan ya San halin Fa'iz in yace baya so kawai baya so, yace, "Shikenan to bara na duba karayar hannun naka."

Bai kula shi ba ya kalli hannun ya d'an bud'e yace, Masha Allah Gaskiya komai yayi kyau Wallahi, nifa wallahi mamakin ka nake Oga daga farkawa haka ka samu Lafiya lokaci d'aya, Allah ya amshi addu'ar mu."

Murmushi shima yayi Dan baya son magana yanzu sabida kansa ya fara sarawa.


Kwance masa bandage din k'afa yayi Dan ciwon ya warke Yanzu saura na kansa kawai, yana gamawa ya juya ya fita.

K'ok'arin mik'ewa zaune ya farayi, cikin sauri Amir ya taimaka masa ya mik'e yana cize baki dan yana jin ciwo Sosai musamman ma a kirjin sa.

Taimaka masa Amir yayi ya Wanke bakin sa ya zuba masa tea, tunda ya karb'i tea d'in baiyi magana ba kuma bai sha ba.

Da mamaki suke kallon sa kamar bashi ne ya gama magana Yanzu ba, da sallama aka turo k'ofar d'akin aka shigo.

Dady ne da su Umma gabad'ayan su kowa baki a bud'e da alama sun San ya tashi.

K'araso suka yi kowa yana yi masa sannu, d'ago kai yayi ya amsa tare da gaida su.

Baba Ladi tace, "Fa'izu ya jikin naka?"

Kallon ta yayi yace, "A'a kakus saukar yaushe?".

" kadai bari d'an nan ai jiya nazo da yamma, ai tunda ka fara rashin lafiyar nan zuwan Abuja ya aure ni."

Murmushi kawai yayi bai kuma cewa komai ba.

Baba Ladi tace, "Oh ni y'asu wai duk akan soyayya Fa'izu ya shiga Wannan halin."

Kowa ya d'an yi dariya amma babu Wanda yayi magana.

Sai a lokacin Baba ta gano Fateema tace, "Au Ashe ga amaryar can shiyasa naga sai kallon gefen yake."

Bai shirya dariya ba amma sai da ya murmusa, kallon Abie Baba tayi tace, "Kunyi masa albishir din dai hala?".

"A'a Hajiya ko Fateemah ma bata sani ba da niya ta sai mun koma gida."

"Zancen banza in kuma kafin a koma gidan jikin nasa ya rikice fa? Ku sanar dashi Yanzu."

Abie yace, "To Hajiya," juyowa yayi ya kalli Fa'iz yace, "Fa'iz yau da asuba an d'aura muku aure kai da FateemaFateema."

Da sauri ya d'ago kai ya kalli Abie, Baba Ladi tace, "Eh yau kaida Fateema ma'aurata ne d'azu da asuba aka d'aura auren."

Wasu siraran hawaye ne suka fara zuba daga idon Fa'iz.

Tsaki Baba Ladi tayi tace, "kalli abin kunya yana kuka a gaban matar sa, in ta raina ka Kai ka jiyo ai."
+
Yadda tayi maganar ya bawa kowa dariya, Fa'iz kuwa juyawa yayi ya zubawa Fateemah data sunkuyar da kai.
Umma tace, "Yo Baku ga Amarya ba yau ta riga kowa tashi jira kawai take tazo taga angon ta."
Ummi tace, "Ga alama nan kuwa irin Wannan kwalliyya, nidai ban tab'a gani tayi Wannan kwalliyyar ba sai yau."
Abie yace, "Naga alama Ku bakwa sirika da Fateemah."
Wayyo Allah Fateemah kuwa kasa motsawa tayi sabida kunyar Su take ji, shi kuwa gogan sai murmushi ake Allah Allah yake su fita su bashi guri shida matar sa.
Abie ya kalli Dady yace, "Toh nufa yau sai Kano tunda jikin nasa yayi sauki, sai kuma biki ma dawo."
Dady yace, "Da wuri haka? Na zata sai gobe zaku wuce?".
" Yanzu zamu tafi  aiki yana can ya tarar min gwara naje na rage kafin lokacin bikin."
"Gaskiya ne, muje na d'an taka muku".
" Kuyi zaman ku basai kun fito ba," ya kalli Fa'iz ya cigaba da fad'in, "Allah ya k'ara sauki angon Fateemah, Fateemah gaki ga mijin ki kuka ya k'are" ya fad'a yana murmushi.
Sallama yayi musu suka tafi.
Cikin Tsokana Amir ya kalli Baba yace, "To ke yaushe zaki tafi?".
" Ban sani ba Dan uban ka gashi nan a tsaye, a kanka nake? Kaji min yaro da rashin kunya."
K'yalkyalewa da dariya yayi Dady ma dariyar yake yace, "Daman tsokanar ki yake son yi kuma yayi."
STORY CONTINUES BELOW
"Eh da yake mahaukaciya ce Niko?".
Rik'e baki Dady yayi yace, " A'a Allah ya baki Hak'uri. "

Haka suka dinga hira da dariya, Fa'iz ya kalli Amir yace, "jeka waje Dan Allah ka kira min Dr Bashir."
Fita yayi babu jimawa suka shigo tare, Ya kalle shi yace, "Na gaji da zaman asibitin nan gida nake son tafiya."
Dr yace, "To Oga yadda kace, Allah ya k'ara lafiya."
Mamy tace, "Haba Fa'iz ka Bari ka k'ara samun sauki mana."
Kallan ta yayi yace, "Mamy bazan iya zaman ba Gaskiya na gaji Wallahi."
Mamy tace "To ai Shikenan."

Babu jimawa suka had'a kayan su suka bar asibitin.

Bayan komawar su gida Fa'iz yayi wanka ya shirya duk da yana d'ingishi amma haka ya daure, kwanciya yayi amma ya kasa yin baccin, ko yaya ya rife idon sa fuskar Fateema yake gani lokacin da take murmushi.

Mik'ewa yayi ya fito daga d'akin da Yanzu garau yake jin sa kamar baiyi cuta ba, canke-canken inda zai ga Fateemah yake yasan tabbas Yanzu bata d'aki kodai d'akin Umma ko d'akin Mamy, d'akin Umma ya nufa ko tana can.
Da sallama ya tura k'ofar d'akin ya shiga, tana kan sallaya da alama walha tayi, zama yayi a bakin gado yace, "Sannu Umma."
Ba tare da ta kalle shi ba tace, "Yauwa ya jikin?".
" Jiki Alhamdulillah."

"To me ya shigo da kai?".
Bud'e baki yayi yace, " Yanzu sai da dalili zan shigo d'akin ki?, na gane Ashe daman duk kulawar da kika bani Dan bani da Lafiya ne yanzu naji sauki kin tattara ni kin watsa a bola."
Tsaki tayi ta kau da kanta.
"Wai ni kam Umma ina su Suhail ne? Ban gansu a asibiti ba kuma ban gansu a nan ba, suna ina?".
Ajiyar zuciya Umma tayi tace, " Sun koma Kano, Suhail Allah ya amshi rayuwar sa ya mutu jiya akayi uku ma, kafin rasuwar sa har d'akin da kake kwance yazo yana ta yi maka magana yana Neman gafarar ka."
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine abinda Fa'iz yake maimaitawa kawai.

Bai kuma cewa komai ba ya mik'e ya fita daga d'akin,  d'aki ya koma ya kwanta lamo yana tuno duk wani Abu da ya shiga tsakanin sa da Suhail.

Bai yi aune ba yaji hawaye na zuba a idon sa, tabbas sabo ake wa kuka, bai wani saba da Suhail Sosai ba amma yaji mutuwar sa Sosai.
Kasa fita yayi ya zauna a d'akin yana ta tunani har akayi sallar Azahar.

Bayan ya idar da sallah ya saka Suhail a addu'a Sannan ya mik'e ya fito daga d'akin, d'akin Mamy ya nufa yana tafiya a hankali sabida ciwon k'afar sa.
Da sallama ya shiga parlourn, amsawa tayi tana murmushi.
Zama yayi a kan kujera yace, "Sannu da huta wa Mamy."
"Yauwa sannu Fa'iz, ya jikin naka?".

" jiki Alhamdulillah da sauki."
"To Allah ya k'ara lafiya."
Ya amsa da Amin Sannan yace, "Mamy Ashe Suhail ya mutu? Gaskiya naji mutuwar bawan Allah nan Allah ya gafarta masa."
Girgiza kai Mamy tayi tace, "Amin ya Allah, nima baka ji yadda mutuwar sa ta dake ni ba Wallahi."
Kallon d'akin ta yayi yace, "Mamy wai ina k'annan nawa ne?".
Y'ar dariya Mamy tayi tace, "Auta tana parlourn k'asa wajan Hajiya."
STORY CONTINUES BELOW
Ba tare da kunya komai ba yace, "Mamy Beauty fa?".
D'agowa tayi ta kalle shi tayi murmushi tace, " ai muna dawowa ta tafi Asokoro wajan Granny. "
B'ata fuska yayi yace, "Lallai ma ta raina ni da izinin wa ta tafi?".

Umma dake bakin k'ofa tace, " Da izinin iyayen ta, kaji min yaro da iyayin banza kai ko kunyar Mamyn baka ji? Wato kai me mata ko? In ta dawo ka daka ta."
Dariya Mamy tayi Sosai tace, Haba Umma ai ba laifi bane in ya tambaya, ni Wallahi na zata ta sanar dashi kafin ta fita da bazan barta ta tafi ba, yi Hak'uri son in ta dawo zan turo maka ita."
Tsaki Umma tayi tace, "Ai daman ke kike Goya masa baya yake abinda yaga dama" ta fad'a tana hararar Fa'iz.
Mik'ewa yayi ya fita yana murmushi.
K'asa ya sakko yaga Granny da Auta suna hira, zama yayi a kusa da ita yace, "Kaka ta kina zaune kina hutawa kenan."

"Eh ina zaune Aminatu ta cika ni da surutu, ina Amaryar taka?."
"Mamy ta aike ta yanzu zata dawo."

"Eh ni zan fad'awa uban ka kaima za'a yi maka al'adar fulanin da tunda an d'aura aure Fateema baza ta tare ba sai bayan shekara d'aya, ka ganni nan haka aka yi min gashi kuma yanzu shekara da shekaru muna tare da Kakan Ku, to kaima haka za'a yi maka" ta fad'a tana washe baki.
Juyawa yayi yaga Auta ta bar wajan hakan yasa ta Mik'e yace, "Kai Kakata dad'i na dake basira, kin ga in ta zauna zaman shekara d'aya sai ta ta tare da d'anta kinga basai an sha wata wahala ba."
"D'anta kamar yaya kenan?".

Sunkuyuwa yayi dai-dai fuskar ta yace, " Banda abinki kina ganin Beauty zata zauna zaman shekara d'aya bayan tana matsayin Matata bata haihu ba? Ai da d'an mu zamu tafi kila ma akwai cikin na biyu" ya fad'a yana kashe mata ido.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ni Ladi naga ta kaina na had'u da fitsararran yaro, yanzu Fa'iz ni kake fad'awa haka? Lallai zamani ya lalace".
" To ai Gaskiya na fad'a miki, kwara ki samarwa kanki mafita kar kiyi wannan maganar in ba haka ba Wallahi mun samu me wankan jego a banza."
Pillow kujera ta d'auka ta jefa masa tare da fad'in, "Fita Mara kunya ka bani waje."
D'aki ya koma yana dariya Dan yasan yayi maganin ta.

Yana barin wajan Fateema ta shigo, har lokacin Baba Ladi tana ta mita ita kad'ai.
Murmushi tayi kawai ta gaishe ta nufi d'akin Mamy.
Zama tayi tace, "Mamy na gaji Wallahi."

"Mtsw ke komai kin gaji me kika yi? Nima ko sirfe?".

" Ba d'aya, gashi kinji momy tace nace miki tana gaishe ki, Dady kuma yace in kin samu time kije yana son magana dake. "
"To insha Allah zan lek'a in na samu lokaci, yauwa d'azu Ashe baki tambayi mijin ki ba kika fita? Wannan wacce irin d'abi'i ce Daughter? Tun yanzu zaki fara fita bada izinin mijin ki ba, kar ki sake kinji na fad'a miki, kuma kije ki bashi Hak'uri Dan baiji dad'in Fitar da kika yi baki fad'a masa ba."
"Insha Allah bazan sake ba Mamy, Mamy ina son magana dake amma Dan Allah kar ranki ya b'aci."
"Ina jinki fad'i abinda zaki fad'a."

Ajiyar zuciya Fateema tayi tace, "Mamy ina son naje Lagos Neman mahaifina cikin satin nan, Dan Allah kar kice A'a ki amince badan niba."

Kauda kai Mamy tayi tace, "Ni daman bazan hana ki zuwa wajan mahaifin ki ba kije."
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi tayi tace, "Yauwa Mamy na shiyasa nake sonki wallahi, ina Auta?."
"Tana d'aki tana bacci kila, nima kwanciya zanyi, yauwa bud'e fridge akwai wani Abu a roba ki d'auka ki shanye duka kar ki bar ko kad'an."
Mik'ewa tayi ta bud'e ta d'auko abun, tace, "Mamy meye wannan?".
" Magani ne, in kin fita ki kullo min k'ofar " ta fad'a tana kwanciya akan gado.
D'aga robar tayi ta shanye tas ta ajjiye ta fita daga d'akin.

D'akin Umma ta shiga da sallama a bakin ta, kafin a amsa Umma tace, "Yauwa kinga Amaryar nan ita za'a yiwa gyaran, nan da two week za ayi bikin."
Matar dake zaune kusa da Umma tayi murmushi tace, "Babu damuwa komai zaiyi kyau, yadda take da kyaun nan ai ba k'aramin karb'ar gyara zata yi ba" ta fad'a tana bud'e wata Leda.
Wani Abu ta d'auko a roba ta mik'awa Fateema tare da fad'in, "Bara mu fara tun Yanzu, karb'i Wannan ki sha."
Karb'i tayi Dan ita har ga Allah bata son wad'an nan magungunan, sha tayi tana yamitse fuska.

Fita tayi ta bar su tare suna tattaunawa.
Gaban ta na fad'uwa ta nufi d'akin Fa'iz Dan cika umarnin Mamy, a hankali ta tura k'ofar parlourn ta shiga da sallama.

Babu kowa a parlourn da alama yana cikin bedroom, ji tayi kamar ta juya sai kuma ta Hak'ura ta k'arasa wajan k'ofar d'akin ta fara kwankwasawa.
Duk a tunanin sa Amir ne hakan yasa yace, "Shigo mana."
A hankali ta tura k'ofar ta shiga kanta a k'asa.
Yana ganin ta ya mik'e yana murmushi da ya kasa b'oyewa, yace, "Welcome beauty k'araso mana."
"A'a nan d'in ma yayi, zuwa nayi na baka Hak'uri d'azu na fita bada izinin ka ba, kayi Hak'uri Momy ce tamin waya tace naz zata....." K'asa k'arasa maganar tayi ganin yadda yazo daf da ita har jikin ta na gugar nasa.

Hannu ya d'ora akan lips d'inta tare da fad'in, "Shihhhh bakya lefi a waje na ya wuce."
Sunkuyar da kai tayi ta kasa had'a ido dashi, wani b'angaren na zuciyar ta cike yake da tsoro d'aya b'angaren kuma farin ciki ne fal a cikin sa.
A hankali kamar me koyan magana tace, "Daman ina so na fad'a maka cikin week d'in nan nake son zuwa Lagos wajan Dady na, inaso na ganshi jiki na yana bani yana cikin wani hali."

Rik'e hannun ta yayi ya jata ya zaunar da ita a bakin gado yace, "Hakan yayi kyau gwara aje d'in, zuwa Yaushe kike son zuwa?."
"Ni ko gobe ne ma" ta fad'a tana d'ago kanta.
Lumshe ido yayi yace, " gobe yayi wuri bakya gani bani da lafiya, sai dai zuwa jibi in Allah ya nuna mana".
Cikin fara'a tace, "Jibin yayi Allah ya kaimu".
Ya amsa da amin yana kallon bakin ta.

Mik'ewa tayi tace, "Bara naje kar Mamy ta neme ni".

Rik'e Mata hannu yayi yace, " Ta yaya zata neme ki bayan tasan kina wajan mijin ki, ni naga kamar gudu na kike."
"A'a ba haka bane kawai dai."

"Kawai dai me?" Ya tambaya yaba kallon ta.
Shiru tayi bata amsa ba, "dawo ki zauna" ya fad'a yana zama shima.
Babu musu ta dawo ta zauna kusa dashi tana wasa da zoben hannun ta.
"Fateemahhhh" ya fad'a a hankali.
STORY CONTINUES BELOW
Tsigar jikin ta tayi yarrrr sabida yadda ya kira sunan ta har ta lumshe ido Sannan tace, "Na'am."
"Ya kika ji lokacin da akace kin zama tawa na zama naki? Wanne irin farin ciki kika shiga?."
Shiru tayi tana murmushi k'asa-k'asa.

Murza hannun ta yayi ta d'ago ta kalle shi yace, "Kinyi shiru, nifa kaga banbancewa nayi mafarki nake ko gaske ne, Beauty kin San yadda nake son to yadda nake sonki haka nake kishin ki, Fateema bazan tab'a iya rabuwa dake ba ina sonki ke JININ JIKI NACE, duk ranar da babu ke babu rayuwa ta, kece zuciya ta gabad'aya Dan Allah kiyi min alk'awari rik'e min kanki" ya fad'a yana kwantar da ta a kirjin sa.
Wani zallar madarar farin ciki ne yake ratsa Fateema, bata San time d'in da ta zagayo da hannun ta itama ta rik'e shi tace, "Nima ina sonka Yaya na, yadda kake kishi na haka nake kishin ka bazan iya jure naga wata mace a tare da kai, Dan Allah kada kayi min kishiya nayi alk'awari kome ka nema a wajena zan baka mutuk'ar baifi k'arfi na ba, ka zauna dani ni d'aya kaji" ta k'arasa maganar cikin shagwab'a.
A hankali yake shafa bayan ta yace, "Beauty na banda abinki ina da kamar ki ina ni ina Neman wata mace? In kinga nayi aure to daman haka Allah ya k'addaro min kuma kin san d'an Adam baya wucewa k"addarar sa, ina k'aunar ki Fateema kece rayuwa ta gabad'aya."

K'ara kwantar da kanta ta k'ara yi a jikin sa tace, "Nima ina sonka my happiness."
K'asa ya fara yi da zip d'in rigar ta hakan yasa tayi sauri ta d'ago tana kallon sa, karyar da kai yayi alamun kada ta hana shi, girgiza masa kai tayi alamun A'a.
Nuna kansa yayi yace, "Nidin".

Gara gira tayi alamun eh.

Yace, " babu Abinda zan miki fa."

"Eh naji ka kyale ni."

Bata rufe baki ba ta fara kissing Lip's d'inta.

Duk yadda tayi ta kwace kanta kasawa tayi hakan yasa itama ta saki jiki.
Sun kwashe lokaci me tsayi a haka kafin k'arar wayar sa ta katse su, kamar Mara sa Gaskiya haka suka tsorata juyawa yayi ya d'au wayar ita kuma ta Mik'e da gudu ta fita daga d'aki.
Tana zuwa d'aki ta fad'a gado tana haki, murmushi ta dinga yi tana tuno abinda ya faru tsakanin su.
Shi kuwa Fa'iz haushi ne ya kama shi sai tsaki yake an korar masa mata.
A ranar Mamy ta sanar dasu Umma zancen tafiyar Fateemah da Fa'iz Lagos, suka yi na'am da maganar suka nuna goyan bayan su.

*BAYAN KWANA BIYU.*
Fateemah ce zaune kusa da Mamy tana bata address d'in gidan Dan ita ta manta, sallama tayiwa Mamy tayi mata addu'a ta fito.
D'akin Umma ta shiga ta tayi mata sallama itama.

A cikin kwana biyun ba k'aramin kyau Fateema tayi ba sabida yadda ake bata kulawa daga b'angare biyu, Mamy tayi  Umma tayi, tayi wani fresh fatar ta har wani yellow take yi sabida kyau.
babu yarda ba'a yi da Mamy akan suje tare da Fateema amma Sam taki yarda tace ita dashi sai dai a lahira.
Fateemah trolley ta d'auka kawai ta zuba kayan ne Dan bata San kwana nawa zasu yi ba, d'akin Granny ta shiga zata yi mata sallama taga Fa'iz zaune a gaban ta yana dariya Sosai.
Cak ya tsaya tare da zuba mata ido, wutar k'aunar ta na k'ara huruwa a cikin zuciyar sa, tsugunawa tayi tace,
"Hajiya na shirya zamu tafi kiyi mana addu'a."
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi tayi tace, "Allah ya kaiku Lafiya kinji y'ar albarka, Sannan kada ki ganku Ku kad'ai ki manta da kashedin da nayi miki kinji?".

D'aga kai Fateema tayi tana sunkuyar da kai.

Fa'iz yace, " Kashedin me kika yi mata y'ar tsohuwa?".
"Kashedi nayi mata akan kada ta yarda da duk wani dad'in bakin ka kada ta baka kanta har sai kun tare Dan naga kanka rawa yake."
Baki bud'e Fa'iz yake kallon ta cike da mamaki yace, "Lallai ma Wannan matar, wato kina nunawa Matata hanya Mara kyau ko? Kina so ta shiga wuta da k'afar ta kin manta me Annabi yace akan wacce tak'i amsa kiran mijin ta?, Mala'iku zasu kwana auna tsine mata har sai ta wayi gari, tsinuwar mala'ikun kike son sata kenan ko? Akan wata banzar al'ada wacce ba addini ba, Shikenan maza kita zuga ta kuma wallahi zan baki mamaki" yana gama fad'ar hakan ya mik'e ya fita.
Tsaki Baba tayi tace, "Eh jeka kome zaka ce ba zata yarda ba, ke kuma ki rik'e abinda na fad'a miki".

Fateemah kai kawai ta d'aga ta mik'e ta fito daga d'akin itama.
A waje taga Auta tana jiran fitowar ta, rungume ta tayi suka yi sallama, bayan motar ta bud'e Dan tasan yana ciki tunda airport za'a kaisu.
Tunda ta shiga suka fita daga gidan bai kalli inda take ba har suka isa airport suka hau jirgi.

Gajiya tayi da shirun tace, "Wai me nayi maka ne tunda muka fito daga d'akin Hajiya kak'i kula ni?".
Juyowa yayi ya kalle ta yace, " Oh baki San abinda kika yi ba ko? Ke Yanzu da ilimin ki zaki biyewa waccan matar?, nema take ta kaiki wuta da k'afar ki wallahi. "
Ajiyar zuciya tayi tace, "Wai daman akan Wannan kake fushi, to ka kwantar da hankalin ka na San abinda nake yi, nasan hukuncin abinda take so nayi."
Murmushi jefen baki yayi yace, "Kin kyau tawa kanki."
D'ago ido tayi ta kalle shi sai wani kau da fuska yake, murmushi tayi kawai bata ce komai ba.
Koda suka sauka a garin Lagos gidan Dady dake Ikeja suka sauka.
Gida ne Babba na gaske mai kyau Sosai, bayan sun shiga Fateema tayi wuf ta fad'a toilet tayi wanka, har ta shirya bai shigo d'akin ba da alama shima wankan yayi a wani d'akin.
Shigowa d'akin yayi hannun sa rik'e da Leda ya zauna yace, "Matsoraciya meye na wani saurin shiga wanka? Hausawa sunce komai wayon Amarya sai ansha manta, badan gani gaki ba hmm" ya fad'a yana murmushi.
Ita kuwa ba k'aramar fad'uwar gaba take ji ba hakan yasa tayi shiru kawai.
Abinci suka ci bayan sun gama ta kalle shi tace, "Muje mu fara Neman nasa ko tunda dai shima a cikin unguwar nan yake."
"In baki gashi ba tashi muje mu fara kila a dace."
Tashi tayi ta yafa mayafi tace, "To muje."

Wani kallan up and down yayi mata yace, "Ashe baki shirya zuwa ba kenan" ya fad'a yana zama akan kujera.

B'ata fuska tayi tace, "Haba Dan Allah kana gani na saka mafayi kace ban shirya zuwa ba?."
"Wannan kayan sun kama ki Sosai kinga yadda hip's d'inki ya fito Sosai? Ko ki saka hijjabi ko a fasa zuwa."
Cikin shagwab'a tace, "Haba Dan Allah me kayan jikina suka yi?".
"Wallahi kinji na rantse in baki saka hijjabi ba baza ki fita ba, ni kaina kin tayar min da hankali da Wannan shigar taki balle kuma wani na waje."
Babu yarda ta iya haka ta saka hijjabin suka fita, wani ya kira a waya ya kawo musu mota suka shiga suka shiga cikin unguwa.
Yadda Mamy ta basu address din suka dinga bi duk da unguwar ta canja Sosai amma haka suka dinga bi suna k'ok'arin gano gidan.
A bakin wani gida suka tsaya Wanda yayi dai-dai da address d'in da Mamy ta basu, kallon gidan Fateemah take Sosai tabbas Wannan gidan sune.

Fita suka yi daga cikin motar ta tsaya ta kalle shi idon ta cike da hawaye tace, "Nan ne wallahi Yaya na."

Rik'e hannun ta yayi yace, "to meye na kukan kuma? Muje ciki" tare suka nufi k'ofar gidan, a waje ya tsaya ita kuma ta shiga ciki.
Knocking d'in gate d'in gidan tayi har sau uku Sannan taji an tawo alamun za'a bud'e, tana Bud'ewa taga wata mata cikin yarabanci take tambayar ta lafiya.
Cikin yaren itama Fateema tace, "Nazo Neman Mr Danial ne."
"Babu wani Danial a nan gidan, Dan haka ki juya ki bar nan" ta fad'a tana niyar rife k'ofar.
Mijin tane ya fito yana tambayar lafiya, bayani tayi masa ya kalli Fateemah yace, "Danial ya siyar da gidan nan sabida talauci da yayi masa yawa."
Cikin tashin hankali tace, "Ko zaku fad'a min inda ya koma please."
"Kinga Yarinya mu bamu San inda ya koma mun samu labarin dai bashi da lafiya Sosai, zaki iya bar mana gida" rife k'ofar yayi ya juya ya fita.

Hannu biyu tasa ta toshe bakin ta sabida wani kuka da ya tawo mata, a haka Fa'iz ya gano ta yayi saurin k'arasowa ya rik'e ta yana fad'in,
"Beauty Lafiya meye ya faru? Ina Dadyn?".
Cikin kuka ta fad'a masa abinda suka ce ta d'ora da cewa, " ina so naga Dady na Yaya Yanzu ina zan ganshi? " ta fad'a tana fashewa da kuka Sosai.
Rik'e ta yayi ya sata a mota yana bata Hak'uri, haka suka zaga gari har dare basu ga mai kama da dashi ba, Hak'ura suka yi suka koma gida da alk'awarin da safe zasu koma.
Koda suka koma gida Mamy suka yiwa waya suka fad'awa, dak'yar ya dinga lallashin ta har bacci ya d'auke ta.
A gefen ta ya kwanta tare da jawo ta jikin sa yana shafa kanta har bacci ya d'auke shi.

Da safe bayan sun yi breakfast suka shirya fita Neman Danail, fita sukayi suka shiga mota suka fara zaga garin Ikeja.
+
Tafiya suke basu San isa suka nufa ba tun tafiyar nayiwa Fateema dad'i har ta gaji ta kalle shi tace, "Anya kuwa Dady yana Raye? Jikina yana bani kamar baya yare" ta fad'a fuskar ta da damuwa Sosai.
"Kada kice haka Beauty insha Allah zamu ganshi ki kwantar da hankalin ki."

Numfashi ta sauke tare da jinginar da kai jikin kujera tayi shiru.
Tun safe suke Abu d'aya har Azahar tayi a lokacin gab suke da barin Ikeja, Fateemah tace, "Kaga kawai mu koma gida anjima ma dawo yanzu gaji yunwa ma nake ji."
Juya kan motar yayi suka dawo, Tafiya suke kowa yayi shiru babu maiyin magana, a dai-dai da wani d'an dattijo ya ya tsaya a tsakir titi, duk horn d'in da Fa'iz yake masa baiji ba sai rikicewa da yayi yana kalle-kalle har suka bige shi ya fad'i a wajan a sume.

Da gudu suka fito daga motar mutanen wajan suka taimaka masa aka sashi a mota sai asibiti.
Kallan mutumin kawai Fateema take tana kuka ganin halin da yake ciki ya tayar mata da hankali Sosai.
Asibiti mafi kusa suka nufa aka karb'e shi cikin sauri, tun a waje aka jona masa drip Dan jikin sa yayi weak Sosai.

Suna tsaye bakin d'akin suna zagaye hankalin su a tashe Sosai, Fa'iz ya dafa kafad'ar Fateema tare da zaunar da ita a kan table din bakin d'akin yana bata baki.
Sun kwashe a k'allah minti arba'in a wajan Sannan likitan ya fito ya kalle su yace, "Muje office."
Ba musu suka bi bayan sa suka shiga suka zauna.
Likitan yace, "Bai samu wani rauni Sosai ba sai fashewar da goshin sa yayi sai Dan kukkujewa, amma kafin Wannan daman Wannan bawan Allah yana cikin wani hali sabida yadda jinin sa ya hau ga rashin abinci, Gaskiya zan iya cewa gwara sa Allah yasa kuka bige shi da Yanzu ba'a San halin da yake ciki ba, amma Yanzu ya samu sauki mun sa masa drip mun bashi magani kuma ya samu sauki Sosai, sai abinci da yake buk'ata da gaggawa."
Fa'iz yace, "Alhamdulillah Dr mun gode Sosai, ko zamu iya ganin sa?".
" Eh bismillah Ku shiga."

STORY CONTINUES BELOW

Mik'ewa suka yi suka fito daga office d'in suka shiga d'akin, a zaune suka ga mutumin ya zabga tagumi yana tunani.
Zama sukayi Fa'iz yace, "Sannu Baba ya jikin naka?".

Juyowa yayi ya kalle su sa hausar sa wacce bata fita Sosai yace, " da Sauki, Nagode yaro."
D'ago kai Fateemah tayi ta kalli mutumin tace, "Sannu Allah ya kara sauki."

Abinci Fa'iz ya bayar aka siyo aka kawowa mutumin, kamar wani mayinwaci haka yake cin abincin hannu baka hannun kwarya, sai da ya k'oshi Sannan ya ajjiye yana Ajiyar zuciya.
Ganin ya dawo hankalin sa yasa Fa'iz ya gyara zama tare da cewa, "Baba ka fad'a mana inda zamu samu iyalin ka Dan mu sanar dasu halin da kake cikin, ko number waya zaka iya bamu Sai mu kira."
Tagumi yayi yace, "Bani da kowa iyaye na sun mutu, matata ta gudu ta barni gashi ban San inda daughter ta take ba."

Fa'iz kallon Fateemah yayi cike da mamakin maganar mutumin, Fa'iz yace, "To Yanzu Baba babu Wanda zamu sanarwa abinda ya same ka?."
"Babu Dan bani da kowa ni kad'ai nake rayuwa ta."
Fateemah tayi shiru tana girgiza kai.

Babu Wanda ya kuma cewa komai a cikin su, likita ya shigo da takarda a hannun sa ya mik'awa Fa'iz yace, "takardar sallama ce tunda baiji ciwo ba."

Karb'a yayi tare da yi masa godiya ya fita.

Takardar suka bawa mutumin suka ce masa an sallame shi zai iya tafiya gida, cikin yarshen yarabanci yake fad'in, "Yanzu ina na nufa? Bani da kowa bani da gida ina zani yanzu."
Kallan Fa'iz tayi ta kalli mutumin ta juya harshe tace, "Baba da a ina kake da zama?".

Jin tana jin yaren sa yasa ya saki jiki ya fara magana yace, " A soron wani gida nake da zama in sun rage abinci su bani in kuma babu sai dai na kwana haka babu ci babu sha."
Cikin tausayawa ta fad'awa Fa'iz abinda suka fad'a, rik'e hannun ta Fa'iz yayi suka fita daga d'akin.
A bakin k'ofar yace, "Yanzu ya kike ganin zamuyi da Wannan mutumin?."
"A gani na mu d'auke shi muje gida dashi kaga koshi zai taimaka mana wajan Neman Dady."
"A'a Beauty ta yaya bamu San halin mutum ba mu d'auko shi mu kawo shi gidan mu, bamu San shi ba bamu San halin sa ba, mutumin kirki ne ko akasin haka bamu sani ba, kada fa muzo muyi abinda zamu yi Dana sani fa."
"Eh da hakan amma insha Allah babu abinda zai faru, baka ganin taimako muka yi? Gashi naga alama ba musulmi bane kaga in ta hanyar mu ya musulunta kaga ai mun samu lada."
"Haka ne to, Allah ya bamu ikon kyautata masa, muje kar yaga mun barshi shi kad'ai."

Shiga suka yi suka yi masa bayani yayi murna Sosai tare da gode musu, Fa'iz yana rik'e dashi suka fita aka sashi a mota suka tafi.
Koda suka isa gida d'akin mai gadi suka bud'e masa suka ce ya shiga ya zauna, ciki suka yi inda Fateemah ta shiga kitchen ta fara k'ok'arin dafa abinci.
Bayan ta gama ta zuba a flask suka shiga d'akin ita da Fa'iz, a zaune suka same shi yana kallon wani hoto yana hawaye.
Zama suka yi cikin yaren su Fateema ke tambayar sa abinda ya sashi kuka.
Bai bata amsa ba sai mayar da hoton cikin aljihun sa da yayi yana goge hawaye.
Ganin yayi shiru yasa suka Mik'e suka yi masa sallama suka fita.
Fateemah tace, "anjima sai muje muyi masa bayanin Dady ko yasan inda yake ko?".
"Babu damuwa Allah ya kaimu, Yanzu dai mu barshi ya huta shima naga yana cikin damuwa Sosai."
STORY CONTINUES BELOW

"Nima na gani Allah yasa dai yasan inda Dady yake."
Ya amsa da Amin.

Da yamma misalin k'arfe biyar suka koma d'akin, kamar d'azu yana zaune yana kallon hoton yana hawaye.
Fateemah ta kalle shi tace, "Baba tambayar ka muke son yi, wani mutumi muke nema a nan garin Ikeja."
Bai ajjiye pic din ba yace, "Ina jinki".
" Mina Neman wani mutum mai suna Mr Danial, yana da y'a Eleina amma bai San inda take ba tun tana yarinya aka neme ta aka rasa, matar sa ta farko Sisiliya kafin su rabu, ta biyu kuma Merry."

Saurin d'agowa yayi yana kallon Fateemah hawaye na anbaliya a idon sa yace, "Na sanshi ke wacece a wajan sa?".
Murmushi jin dad'i Fateema tayi ta kalli Fa'iz Sannan tace, " Nice y'ar tasa Eleina da mijin ta."

Mik'ewa yayi hannun sa na karkarwa yana nuna Fateemah yana fad'in, "Da gaske kece Eleina daughter na? Nine Mr Danial Eleina nima Dadyn ki, kinga hoton mu tare lokacin da kina yarinya" ya fad'a yana nuna mata hoton da yake kalla.
Karb'a tayi hannun ta na rawa tana kuka-kuka dariya-dariya,  da gudu ta fad'a jikin sa tana kuka mai tsuma rai, shima rungume ta yayi yana hawaye sosai.

Fa'iz kuwa yana tsaye yana murmushi cike da farin ciki, fita yayi a d'akin tare da kira Mamy a waya, tana d'aga wa yace, "Alhamdulillah Mamy abin muka zo nema mun samu yau munga mahaifin Beauty."
Tsaki Mamy tayi tare da tab'e baki tace, "To ina ruwa na ni? Kuma kuyi gaggawa Ku dawo sabida a fara gabatar da biki" tana gama fad'ar hakan ta kashe wayar.
Bin wayar yayi da kallo yana mamakin Gaskiya ba k'aramin Abu mahaifin Fateemah yayiwa Mamy ba tunda har tayi haushi haka.

Fateemah kuwa tana jikin mahaifin ta tana kuka tace, "Dady me Mamy na tayi maka a lokacin da ka Kore ta? Kuma kasan Bata San laifin da tayi maka ba, nima kazo ka tsane ni dukka bazan iya tuna komai ba amma wani abun na rik'e, *BAN SAN LAIFINA BA* ka d'auke tsana ka d'ora min, Dady me yasa?".

Share mata hawaye yayi yana girgiza kai yace, "Daughter duk abinda ya faru ba laifi na bane laifin Merry ne itace ta dinga zuga ni har abinda nayiwa mahaifiyar ki, kiyi Hak'uri daughter nasan na b'ata muku keda Momyn ki, ina zanga Momyn ki ina so na bata Hak'uri itama."

"Momy na tana Abuja ta kuma yin aure har ta haifi Amina Yanzu shekarar ta goma ma."
Shiru yayi baice komai ba ya sunkuyar da kai.
"Eleina naji ana kiran ki da wani suna kin canja addini ne?".
" Eh Dady dani dasu Momy gabad'aya mun koma musulmai addinin Gaskiya, Dady kaima ina gayyatar ka zuwa Wannan addini mai girma, ka sani Annabi Isa ba d'an Allah bane manzon sane, Dady ka dawo hanyar gaskiya Wallahi tallahi a lokacin da ka karb'i Kalmar shahada a lokacin zaka ji duk duniya babu Wanda ya kaika farin ciki. "

Girgiza kai yayi cike da gamsuwa yace, "Daughter wani Malami yayi mana bayanin addinin nan Sosai lokacin da kuka kad'e ni ma wajan sa zani na karb'i Wannan addini, amma Yanzu a shirya nake zaki iya fad'awa abinda zan yi na zama musulmi."
Cikin farin ciki ta fita daga d'akin ta suka dawo tare da Fa'iz, babu b'ata time aka lak'aba masa Kalmar shahada ya karb'a suka yi kabbara.

Murmushi kawai Fateema take tace, "Yanzu Dady ka dawo kamar jaririn da aka Haifa yanzu duk wani zunubin ka na da Allah ya yafe maka, ina taya ka murna."
A cikin lokacin shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin su har Fa'iz yadda ya saki jiki dashi suna hira sosai kamar daman ya san shi, Fa'iz ya koya masa yadda zaiyi wanka shiga musulunci, abubuwa da dama a ranar Fa'iz ya fad'a masa sauran yace za'a samu Malamin da zai dinga koyar dashi, inda Dady ya tashi daga Danial ya koma Abdulk'adir.
STORY CONTINUES BELOW

A cikin Daren suka siyi ticket d'in komawa Abuja sabida Dady ya matsa sai yaje ya bawa Mamy Hak'uri.
Kafin su dawo sai da suka biya ta wani shagon da suke siyar da kayan hausawa manya a d'inke, siya suka yi suka tawo dasu gida akayi sa'a kuwa sun yiwa Dadyn dai-dai.
Washe gari kuwa da safe wani abokin Fa'iz ya kaisu airport ya dawo da motar, Fateemah na kusa da Dadyn ta ko kad'an bata San ta matsayin daga kusa dashi.
Suna sauka a airport Fa'iz yayi waya aka zo aka d'auke Su.
Suna zaune gabad'ayan su a parlourn har Alhaji wato mahaifin su Dady kenan, hira suke cikin nishad'i da shirye-shiryen yadda biki zai kasance.
Da sallama su Fateemah suka shigo parlourn kowa fuskar sa d'auke da murmushi, amsawa suka yi suna yi musu sannu da zuwa.
Shigowar Dadyn Fateemah yasa Mamy mik'ewa a fusace tana nuna shi da yatsa tana fad'in, "meye ya kawo ka inda nake? Ko nan ma kazo ka Kore ni d'in kaci min mutunci iye, Fateema me yasa kuka tawo min dashi nan Ku fad'a masa yayi gaggawar fita daga nan kafin nayi wani Abu akan sa Wallahi."

Umma ce ta mik'e ta zaunar da ita tare da fad'in, "Haba Bilkisu kamar bake ba, kiyi Hak'uri ki kwantar da hankalin ki kije meke tafe dashi, bai kamata kiyi masa haka a gaban Fateema ba ko babu komai mahaifin tane duk lalacewar sa, kiyi Hak'uri ki saurarare shi."
Ajiyar zuciya take tana faman wuci, shi kuwa bawan Allah Abdulk'adir ya sunkuyar da kai yana jiran duk hukuncin da zata yanke a kansa, cikin Hausar da bata fita yace, "Ba wani Abu ya kawo ni wajan ki ba sai Neman yafiyar ki, nasan nayi Kuskure a baya na Kore ki ba tare da kin San abinda kika yi min ba, ni kaina ba laifi na bane zuga ce irin ta Merry, ina Neman yafiyar ki Dan Allah ki yafe min badan ni ba" ya fad'a yana tsugunawa a k'asa.
Tsaki Mamy tayi tace, "in nak'i yafewa zaka dake ni ne? Ko kuma zaka Kore ni ana ruwan sama Sannan ka hana ni y'ar ta? *BAN SAN  LAIFINA BA* kayi min wulak'ancin da bazan tab'a mantawa dashi ba har duniya ta nad'e shine yanzu kake Neman gafara ta? To baka isa ba ka koma can wajan Merry."
"Haba Mamy kalli kiga ya durk'usa har k'asa yana baki Hak'uri me yasa zaki ki yafe masa? Allah da ya hallice mu muke masa laifi duk girman sa amma in mun rok'e ya yafe mana su waye mu to Dan wani yayi mana mu juya baya muce bamu San zance ba? Allah yana son me yafiya in kika yafe masa sai Allah ya yafe miki kema, ina taya shi Neman afuwar ki ki taimaka kiyi Hak'uri Dan Allah" ta fad'a tana durk'usawa ita.
"Mamy nima ina Neman masa alfarmar ki yafe masa badan mu ba" Fa'iz ma ya fad'a tare da tsugunawa gaban ta.
Umma tace, "Ki yafe masa Mamy nima na shiga cikin masu rok'on ki."
Ajiyar zuciya tayi tace, "Shikenan na yafe masa Allah ya yafe mana gabad'aya" tana gama fad'ar hakan ta juya da sauri ta shiga d'aki.

Dady ne ya bashi waje suka zauna suna y'ar hira kad'an.
A Ranar aka samarwa Dady d'an k'aramin gida a nan ya zauna, tare suka je gidan da Fateemah, ta jima a gidan Sannan ta dawo.

A d'aki ta samu Mamy ta zauna kusa da ita tace, "Mamy na sai b'ata rai kike wai lafiya?".
" Lafiya lau" ta bata amsa tana cigaba da abinda take yi.
Mik'ewa tayi ta fita Dan taga alamun yau Mamyn nata sai a slow.
D'akin Granny tayi tana shiga Granny ta fara k'are mata kallo tare da fad'in, "Da alama dai yarinya kinji nasiha ta na ganki garau dake."
Murmushi Fateema tayi kawai tace, "Barka da yamma Granny."
STORY CONTINUES BELOW

"Barkan ki y'ar albarka, na taya ki murnar ganin mahaifin ki Allah ya baki ikon yi masa biyayya."
"Amin Hajiya Nagode".

Fa'iz dake tsaye bakin k'ofar d'akin yayi kwafa yace, "hmm Granny kenan yau zan nuna miki basai miji ya tare da matar sa yake da ikon Neman ta ba, zaki gani ne" ya fad'a yana barin wajan da sauri Dan yaji alamun fitowar Fateemah.
D'akin Umma suka gaisa, Umma ta bata wani Abu a roba tace taje ta cinye shi, ba musu ta karb'a ta fito daga d'akin.

Ajjiye abin tayi a d'akin ta ta koma d'akin Mamy, Auta na zaune tana shan alewa Fateemah ta shigo d'akin.
Auta tace, "Yauwa Aunty na ga taki sweet d'in na ajjiye miki".
Karb'a tayi tana dariya ta fara sha, yare suke hira da Amina da Mamy taki kallon ta, sai da ta gaji da shariyar tace, " wai yanzu Mamy akan na nemo mahaifina kike fushi dani? Mamy kar ki manta da uba fa ake ado, amma in hakan ya b'ata miki rai kiyi Hak'uri. "
"Ko kad'an baki b'ata min rai ba Fateemah kawai ganin Danial ne yasa na tuna da duk abinda suka faru baya, har cikin raina kuma na yafe masa kawai dai inna tuno wani abun sai naji raina ya b'aci Wallahi."
"Hak'uri zakiyi Mamy yanzu baga shi komai ya wuce ba? Duk wahalar da kika sha Mamy baki kaini ba amma gashi na manta da komai."
"Haka ne, yauwa kije parlourn Dadyn Ku kiga kayan lefen ki an gama komai, kinga a dace Dadyn naki nada mata Yanzu da sai a kai can kawai."
"Ni Mamy basai na gani ba, mata kuma munyi magana da Dady zai Baba mai waina d'azu ma har gidan ta naje."
"Baba mai waina fa kika ce koma ya yarda?".
" Eh mana Mamy, bafa tsohuwa bace Dan bata fi sa'ar Umma ba kawai dai wahala ce tasa ta zama haka itama kuma ta amince Dady na ya sani yace cikin week din nan za'a yi komai a gama dan yace gobe zasu je suga magabatan ta."
Tab'e baki Mamy tayi tace, "Allah ya sanya alkairi".
Fateemah tace, " Amin."
Bayan sallar I'sha kowa yaci abinci kowa yana d'aki, Fateemah tana d'akin ta tana faman cin abinda Umma ta bata Dan har ta kusa cinye shi.

Fa'iz kuwa d'akin Granny ya shiga ya zauna ya kalle ta yace, "Tsohuwa zan nuna miki Fateemah Matata ce d'azu duk ina jin abinda kike cewa."
"Na fad'a d'in kuma baka isa kayi mata komai ba sai ta tare, jarababbe kawai."
"Haka kika ce?"
"Eh haka nace, tashi ka bani waje ni."
Mik'ewa yayi yana dariya ya fita daga d'akin.
Gida yayi shiru da misalin k'arfe sha d'aya na dare kowa ya kwanta banda Fateema da take zaune tana danna waya.
Kira Fa'iz ne ya shigo wayar ta d'auka cikin sallama.
"Wa'alaiki salam Matata, ki kawo min coffee Yanzu in babu damuwa."
"Babu damuwa bara na had'a maka."
"Yauwa beauty na Allah yayi miki albarka."
Ta amsa da amin tana kashe wayar.

Cikin minti biyar ta gama had'awa ta saka dogon hijjabi ta nufi d'akin nasa.

A d'aki ta same shi yana danna laptop, yana ganin ta ya kashe system d'in yana murmushi, a kan table ta ajjiye masa tare da fad'in, "To gashi nan, sai da safe" ta fad'a tana niyar barin wajan.
"Ji mana Hajiya, kya tsaya ai na gama ki tafi da kayan ko?".

" A'a da safe kawai nazo na d'auka."
STORY CONTINUES BELOW

"To zauna na gama kya tafi."
Babu yadda ta iya ta zauna a kan kujerar dake d'akin.
A hankali yake shan coffee d'in Dan ta jima a d'aki, gyagyad'i ta fara a zaune da alama bacci take ji, murmushi yayi ya cigaba da shan coffee d'in sa.
Bai tashi daga inda yake ba sai sha biyu dai-dai lokacin Fateema baccin ta yayi nisa Sosai.
Mik'ewa yayi tare da yin duk wani da yasan yana gabatarwa kafin ya kwanta, k'arasowa yayi gaban ta ya d'auke ta cak ya kwantar da ita a saman gado tare da cire mata hijjabin jikin ta.
Kallon ta yake yana murmushi ganin yadda take baccin ta hankali kwance, kashe hasken d'akin yayi tare da kwanciya kusa da ita.
A hankali ya matsa kusa da ita sabida tsoron kar ta tashi, zame hular kanta yayi ya fara shafa gashin ta kanta, cikin nutsuwa yake gabatar da komai har yayi nasarar raba ta da kayan jikin ta.
Ita kuwa Fateema cikin bacci take cin wani sabon lamari na ziyartatta, gyara kwanciya ta dad'a yi duk tunanin ta mafarki take.
Sai da taji abun ya wuce misali yasa ta bud'e ido, duk da duhu da d'akin ta fahimci inda take kuma ta gane yanayin da suke ciki daga ita har shi, bud'e baki tayi da niyar magana ya rife mata baki da nasa hannun sa na yawo a duk wani b'angare na jikin ta.

Iya wahala Fateemah ta wahala Dan bai barta ba sai sa bayan k'arfe biyu na dare Sannan ya kyale ta, gefe ya koma yana Ajiyar zuciya cikin farin ciki.
Ita kuwa Fateemah tun tana kukan har murnar ta ta dashe sai kukan kurame da take, ko d'an yatsan ta ta kasa motsawa sabida yadda ko ina na jikin ta ke mata ciwo kamar ana sarawa.
Mik'ewa Fa'iz yayi ya k'araso kusa da uta tare da kunna hasken d'akin, tana nan yadda ya barta sai ido dake faman ambaliyar hawaye, bai b'ata lokaci ba ya had'a mata ruwan zafi tayi ya gasa ta Sosai tare da wanka ya fito da ita.
Gyara wajan kwanciyar yayi ya saka mata doguwar rigar ta ya kwantar da ita, har lokacin bata ce k'ala ba kuma bata daina kuka ba.

Zama yayi tare da fad'in, "Sannu beauty Allah yayi miki albarka kinji."
Fashewa tayi da kuka Sosai tace, "Mara ta baya na, k'afa ta, k'uguna, duka ciwo suke min".
Ba k'aramin tausayin ta yaji ba yace, " Kiyi Hak'uri kinji beauty zasu daina Bara nayi miki allura."
Allura yayi mata tare da bata magani,cikin k'ank'anin lokaci bacci ya d'auke ta.
Gab da asuba ta farka ta mik'e zaune dak'yar duk da babu laifi ta d'an ji dad'i ba kamar d'azu ba.
Mik'ewa tsaye tayi tana cize baki cikin muryar Mara sa Lafiya ta kalle shi tace, "Bara na koma d'aki na bana so wani ya gane abinda ya faru ina jin kunya Sosai".
Mik'ewa yayi shima ya k'araso gaban ta yace, " Abun kunya kika yi? Mijin kine fa ba wani Abu ba."
Sunkuyar da kai Dan shi kanshi kunyar sa take ji balle kuma su Umma tace, "kawai ina so na koma can d'in ne."
"Ki Bari ayi sallah yanzu zaki ji kira in kin idar sai ki koma."
Babu yadda ta iya haka ta koma ta zauna.

Kallan ta yake ganin yadda ta rame lokaci d'aya kana kallon ta kasan bata da Lafiya.
Ranar ko Masallaci baije ba jira yayi aka yi sallah Sannan ya mik'e ya rik'e ta ya raka ta d'akin nata badan yaso ba, Dan in ta tashi ne baya so yayi nisa da ita sabida ya bata kulawa Sosai.
Tana shiga d'akin ta kwanta a kan gado tace, "to kaje d'akin ka kar wani ya ganka."
"Ni kina bani mamaki to meye in wani ya ganni? Zina nayi kome, Allah zaki sa na kwanta anan d'in naga abinda za'a yi."
STORY CONTINUES BELOW

"A'a yi Hak'uri Dan Allah kaje d'akin naka" ta fad'a tana k'ok'arin yin kuka.
K'arasawa yayi tare da yi mata kiss a goshi ya fita daga d'akin.
Ajiyar zuciya tayi tana tunanin me zata fad'awa Mamy da Umma da safe.
Gari yayi haske wajan k'arfe goma amma Fateema bata fito ba, kowa yayi mamaki Dan an San itace take had'a breakfast.

Umma ta kalli Aunta tace, "Auta maza jeki d'akin Fateema kiga lafiya take".

Da sauri ta nufi d'akin ta, a kwance ta ganta cikin bargo sai rawar sanyi take hak'oran ta na had'uwa da juna, da gudu ta k'arasa wajan ta tana fad'in, " Aunty Fateema Lafiya meye ya same ki" ta fad'a tana tab'a fuskar ta.
Saurin d'aukewa tayi sabida wani irin zafin da jikin ta yayi, da sauri ta sakko daga kan gado ta fito a guje.
"Mamy, Umma Aunty Fateemah bata da lafiya jikin ra yayi zafi Sosai sai rawar sanyi take" ta fad'a a rud'e, dai-dai lokacin da Fa'iz ya sako kai parlourn.
Da sauri suka shiga d'akin, Umma ce ta k'arasa wajan ta tana tambayar abinda yake damun ta.
Ta kasa magana sai rawar sanyi da take yi, da sauri Fa'iz ya k'araso wajan tare da yaye bargon ta tab'a wuyan ta.
Kai ya dafe tare da fad'in, "Ya salam har Yanzu zazzab'in nan bai sauka ba."
Umma tace, "Au daman kasan bata da lafiya ne?".
Diriricewa yayi yace, " Eh..daman...jiya da daddare tace min zazzab'i na damun ta har na bata paracetamol. "
"Uhum yayi" Umma ta fad'a tana kallon sa Dan bata yarda da abinda ya fad'a ba.
Mamy tace, "Ta tashi ta d'an watsa ruwa a jikinta ko ta d'an ji dad'i."
Da sauri Fa'iz yace, "A'a basai ta watsa ruwa ba bara na yi mata allura kawai zata ji dad'i" ya fad'a Dan yasan in ta mik'e asirin su ya tonu.

Kallon rashin gaskiya Umma tayi masa tace, "Shikenan yi mata allurar Allah ya kara Lafiya" ta fad'a tana fita daga d'akin.
Bin bayan ta suka yi ya rage daga Fa'iz sai Fateema, suna fita yayi ajiyar zuciya, mik'ewa yayi ya shiga toilet ya d'auko towel da ruwan sanyi a roba, zama yayi tare da kwantar da kanta a cinyar sa ya tsoma towel din a ruwa ya fara goge mata jikin ta.
Daga wuyan ta zuwa cikin ta yake gogewa har jikin ta ya d'an yi sanyi, paracetamol ya bata tasha a hankali ta fara gumi sabida zazzab'in ya sauka.
Ganin tana gumi yasa ya kunna mata Ac tare da yaye mata bargon da ta rife jiki dashi, mik'ewa zaune tayi Dan zafi take ji Yanzu.
Kallan ta yayi yace, "Sannu beauty, babu inda yake miki ciwo Yanzu?".
Girgiza kai tayi alamun akwai, yace, " ina ne yake miki ciwon fad'a min?".
Shiru kawai tayi Dan tana jin nauyin sanar dashi, ganin haka yasa ya gane abinda take nufi yace, "Sannu kinji shima zai daina ciwon."

Kai kawai ta d'aga masa tana k'ok'arin mik'ewa, Umma ce ta shigo d'akin tace, "Sai ka tashi ka fita ka bamu waje tunda baka da ta ido kai, wai har mu zaka yiwa wayo mtsw Allah ya kyauta, tashi kaje nace ko."
Sosa keya yayi ya fice cikin kunya Dan yasan ta fahimci komai.
Fateemah kuwa kamar ta shige k'asa haka take ji, Umma ta kalle ta sai ta bata dariya yadda take wani sunkuyar da kai kamar munafuka tace, "Daina sunkuyar da kai tunda kike ya koya miki rashin kunyar, duk zanyi maganin Ku daga ke har shi" ta fad'a tana shiga band'aki.
STORY CONTINUES BELOW

Jim kad'an ta fito ta kalle ta tace, "Tashi kije ki gasa jikin ki, ki samu more than 20min a cikin ruwan, in yayi sanyi ki k'ara had'a wani zaki ji dad'i Sosai."
Mik'ewa tayi ta tsaya tana so ta fita ta k'arasa band'akin dan bata so taga yadda take tafiya, ganin hakan yasa Umma ta fita ta bata waje.

Bayan ta fito daga wankan ita kanta tafi jin dad'i akan d'azu, tunda gashi yanzu tana iya tafiya Sosai duk dai in ka kula zaka gane ba dai-dai take tafiya ba.
Shiryawa tayi ta zauna a d'akin tana jin kunyar fitowa, shahada tayi ta fito kawai a hankali take takawa har ta isa d'akin Mamy.
Tana shiga Mamy ta kalle kawai ta d'auke kai ta cigaba da abinda take yi, zama tayi tace, "Mamy ina kwana".
" Lafiya lau, ya jikin naki?".
K'asa tayi da kanta Sannan tace, "da sauki."
"Allah ya k'ara Lafiya" Mamy ta fad'a ba tare da ta kalle ta ba.
A hankali Fateema tace, "Dan Allah Mamy kiyi Wallahi ba laifina bane....."
"Shihh kinji nace kinyi laifi ne? Tunda bance kinyi laifi ba kiyi shiru kawai."
Bata kuma cewa komai ba ta mik'e ta fice daga d'akin, a parlour suka had'u da Umma da Granny suna tsaye, ai tana gano ta tace, "Wato Ashe duk nasihar da nayi miki a banza ko? Kinje ki saki jiki ki bashi ya more ko? Shi kuma Dan rashin kunya wai har zuwa yayi yana fad'a min kema kin zama shi d'in ai."
Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba.
Granny tace, "to ki had'a kayan ki ki tafi gidan su Bilkisu har sai lokacin bikin yayi in ba haka ba Wallahi da cikin ta zata shiga gidan."
Umma tace, "Shikenan ma maza had'a kayan ki Auta ta raka ki."
Mamy na jiyo su sai dai tayi dariya kawai.
D'aki Fateema ta shiga Dan itama Wannan hukuncin yayi mata dad'i Sosai Dan Yanzu ko kusa da Fa'iz bata San zama.
Cikin lokaci kad'an ta had'a kayan ta suka tafi ita da Auta.
Fa'iz kuwa koda Granny ta fad'a masa ba ransa ya b'aci ya kira Fateema ya fara fad'a akan me zata tafi bata fad'a masa ba, ita kuma tace umarnin Umma ne ba nata ba ta dinga bashi Hak'uri har ya sakko.
_A gurguje._πŸƒπŸ»‍♀
*AFTER TWO WEEK'S.*

Tun daga lokacin da abin ya faru Fateemah bata kuma bari wani Abu ya shiga tsakanin su ba, ko yazo gidan Granny k'ark'ari su gaisa kawai Dan tsoron sa ma ita take ji.

Duk ya fahimce ta sai dai yayi murmushi kawai.
A cikin kwanakin Dadyn Fateema ya tare da Amaryar sa  Rabi wato Baba mai waina, zaman Lafiya suke Sosai ga hanyar arzuki da ta fara Bud'ewa masa.
Yau ta kama za'a yi lunching d'in su Fa'iz, kowa ka gani aiki yake a gida, da yamma aka tafi lunching, waje yayi waje amarya da ango sunyi kyau Sosai.
B'angaren iyaye suna ba'a barsu a baya ba Dan ko wacce Ashoke ta nad'a aka tsara mata kwalliyya, Baba mai waina har da ita a cikin su Dan yanzu Sosai suke mu'amala.
Anci ansha anyi guzuri, Dan MD, da innahoro, Ummu Nabil, Zeey, Abidat, sunyi guzurin abinci daman da ledar su a jaka, Ummu Hanash kuwa ai ba'a magana ta cika jaka dak'yar take iya d'aukar jakar.😝
Miss xerks kuwa ana gefe kamar baza'a ci ba Ashe jira take taga an juya ta cika cikin ta.
Shukra da Momyn ta ma ba'a barsu a baya ba Dan Shukra itace ta zama k'awar amarya Dan ta nemi yafiyar Fateema kuma ta yafe mata, kuma ta tabbatar Yanzu Fa'iz yafi k'arfin ta tunda itama tana da aure.
STORY CONTINUES BELOW

Anyi biki Lafiya an gama lafiya, ankai amraya Fateema gidan ta bayan anyi musu nashihohi Sosai.

Soyayya mai tsafta suke shimfid'awa kowa yaje gidan su Sai sun burge shi, kullum cikin tattalin juna suke suna gujewa abinda zai b'atawa wani rai a cikin su.
Shukra kuwa sun dai-daita da mijin ta Yanzu zaman lafiya suke babu sauran tashin hankali.
Ta b'angaren gidan su Fa'iz ma suna nan yadda suke da Dan in kazo baka gane mai Girki a cikin su sabida tare suke komai kuma ko wacce taci kwalliyya.
Haka ma gidan Dadyn Fateemah suna zaune lafiya babu rigima balle fad'a.

*Bayan shekara d'aya*
Fateemah ce a labour room Fa'iz tsaye a kusa da ita inda wata nurse ke karb'ar haihuwar tata, cikin ikon Allah ta haifo yaran ta biyu mace da namiji, murna kam ba'a magana kowa ya nuna farin cikin sa Sosai.
Ranar suna yara suka ci Umma da Dadyn Fateemah wato Hindatu da Abdulk'adir, inda ake ce musu Afif da Afifah.

Anyi suna na gani a fad'a Dan yan Gaskiya writer's fan's grps sun cashe sunci sun sha, haka y'an Neat Lady fan's su harda guzuri ma.
Shukra ma ta haifi d'an ta namiji inda yaci sunan Suhail.
Anyi bikin Amir shida Amaryar sa Khairat suna zaune lafiya lau suma.
Tana zaune a d'aki tana shayar da Afifah Fa'iz ya shigo ya zauna kusa da ita yace, Beauty na a duk lokacin da na kalli yaran nan na tuna nawa ne kuma daga jikin ki suka fito sai naji wani farin ciki na ratsa ni."
Murmushi itama tayi tace, "Baka kaini ba My happiness a duk lokacin da tuna ina tare da kai a matsayin miji sai naji nafi ko wacce mace sa'a a duniyar nan."
"To indai haka ne a ajjiye Afifah aji da mahaifin Afifah ko?".
Dariya tayi tace, "Yanzu kuwa kafin a samu Afifah ai mahaifin ta aka samu".
Dariya yayi ya rungume ta yana fad'in, " Ina mutuk'ar k'aunar ki Matata Allah ya bar mu tare. "
"Nima ina sonka mijina, rayuwa kenan yau gashi komai ya wuce RAYUWAR FATEEMAH ta fara da kunci da wahala yanzu kuma ta d'ore da jin dad'i da kwanciyar hankali musamman ma da ta samu abokin rayuwa kamar Ka."
"Haka ne shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah, Fateemah kece rayuwa ta."
Glass d'inta ta gyara tace, "Nima Kaine rayuwata."
"Ina sonki beauty".
" Nima haka my happiness. "

Neat Lady ma tace tana sonku masoyan ta.*ALHAMDULILLAH.*πŸ™πŸΌπŸ˜…

*A YAU TALATA  14/4/2020/ 21/sha'aban 1441H, na  kammala Wannan littafi mai suna BAN SAN LAIFINA BA.*


Post a Comment for "BANSAN LAIFINA BA CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...