Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BANSAN LAIFINA BA CHAPTER A

BANSAN LAIFINA BA CHAPTER A

- - Post a Comment

 BANSAN LAIFINA BA CHAPTER A

Cikin kuka take cewa " Danial ka fad'a min abinda na maka bayan ka raba ni da iyaye na da y'an uwa yanzu kuma kace zaka sake ni ka fad'a min laifi na" duk wannan maganar da take cikin yarabancin take yinta.+


Cikin yarabanci shima ya fara bata amsa cikin masifa "Sisiliya nace bana son ki ki tashi ki barmin gida na tsane ki."

Cikin kuka tace "Naji zan bar maka gida amma ka bani Eleina na tafi da ita ".

Wani banzan kallo Danial yayi mata yace " ba'a baki ita d'in ba ai daman bada ita kika zo ba , Sisiliya I say get out" ya fad'a yana tunkud'o ta waje ya maida k'ofar ya kulle.

Durk'ushewa tayi a wajan ta fashe da kuka mai tab'a zuciya , d'aga kai tayi ta kalli sama taga yadda hadari ya had'o sai walk'iya ake alamun ruwa yana daf da sauka.

Zama tayi a wajan tana tunanin inda zata nufa yanzu itadai tasan ko giyar wake tasha baza ta koma gidan iyayen ta ba tunda ba son auren ta suke da Danial ba guduwa tayi aka d'aura musu aure bata tare da yarda su ba.

Saukar ruwan da taji ya kashe Mata tunani kafin tayi aune an fara ruwa mai k'arfin gaske.

Cikin sauri ta mik'e tana kalle-kalle tana furta "Jesus help me , help me my lord."

Tafiya take amma ba tare da tasan inda zata ba ga dare ga kuma ruwan sama dan haka unguwar ta zama shiru babu kowa , tasha ta nufa taga wata mota guda d'aya cal ana ta kiran Abuja state , cikin sauri ta shige bayan boot d'in motar ta b'uya , da yake babu mutane da yawa a lokacin mutum biyu suka samu mota ta tashi suka nufi garin Abuja.

Kallan garin Lagos take tana hawaye masu zafin gaske tun tana tunani har bacci yayi gaba da ita.


⚡⚡⚡⚡


Tunda Danial ya rufe k'ofa Eleina take kuka tana kira Momy , yarinya ce y'ar shekara biyar zuwa shida ba amma Danial baiji tausayin ta ba ya kifa tama mari yana fad'in "In kika kuma yi min kuka sai na kashe ki shegiya mai halin uwar ta".


Cak ta tsayar da kukan tana ajiyar zuciya , Jan hannun ta yayi suka shiga cikin gidan wani d'aki ya shiga ya zauna yana faman ajiyar zuciya .

Wata siririyar mata ce ta shigo d'akin tana zauna kusa dashi ta rik'e fuskar tace " Ka kwantar da hankalin ka nawan in ba irin halin Sisiliya ne dani ba zan aure ka in zauna da kai bazan tab'a cin amanar ka ba" ta fad'a cikin yaroban ci.

Ido ya zuba mata yace "ina jin tsoro kar kema kiyi min abinda Sisiliya tayi min" . cikin kissa tace "Haba dear hakan bazai tab'a faruwa ba , yanzu yaushe za'a daura mana aure?".

" Gobe a Church " ya bata amsa yana kwanciya a kan gadon.

Wani farin ciki ne ya Lullub'e Merry cikin murna tace "naji dad'i sosai my husband, ko zan iya taya ka baccin?".

Bai mata magana ba sai lumshe ido da yayi yana jin haushin Sisiliya a har cikin ransa , sai a lokacin Merry ta lura da Eleina a gefe tana faman Kuka .

Wani bak'in ciki ya taso mata ta kalli Danial tace "daman bata tafi da y'ar ta ba? Meyasa baka taba ita ba in itama ta irin halin tane fa ita fa?".


Shiru Danail yayi yana gasgata maganar Merry da ya sani ya bata tsiyar ta amma sai yayi shiru bai magana ba.

Kwafa tayi a ranta tace " sai kin gudu da k'afar ki yarinya bana son kowa ya rab'i Danial ni bani ba sai na azaftar dake."

Bata kuma magana ba sai kallon Eleina da tayi ta daka mata tsawa tace " fita ki koma parlour ki kwanta shegiya mai kyaun aljanu".

Tsabar tsoratar da Eleina tayi kawai sai ta fashe da kuka ta fito parlour tana kuka sosai.

Tsaki Danial yayi ya koma ya kwanta yana jin haushin ta har cikin ransa.

A kan kujera Eleina ta zauna tana kuka tana tsotsar hannu ,mik'ewa tayi ta shiga d'akin Momyn ta ta kwanta kan katifar ta tana faman kiran Momy har bacci ya d'auke ta.

Merry kuwa ganin Eleina ta fita sai ta taso ta dawo kan gadon ta zauna tana shafa fuskar Danial tana jin kaunar sa na ratsa ta.


Kafin tayi aune taji ya had'e bakin sa da nata ya shiga kissing , Merry kuwa daman abin nema ne ya samu ta kuwa cafke tana taya shi .


K'ok'arin cire masa kaya take ya dakatar da ita da fad'in "is ok" yana fad'in hakan ya juya mata baya.

Babu yarda zata yi haka ta kwanta a bayan sa ta rungume shi har bacci ya d'auke ta.


Washe gari ya kama Sunday dan haka da huri suka tashi aka fara shirye-shiryen zuwa church ,suna zaune a parlour suna break fast Eleina ta fito tana kiran Momy .

Tsawa Danial ya daka mata cikin b'acin rai yace "in kika kuma kiran min wannan matar a gidan nan saina kashe ki stupid."


Shiru tayi dan yanzu tsoron Dadyn nata take yi , cikin muryar yara tace "Dady am Hungry" ta fad'a tana rik'e cikin ta.


Wani banzan Kallo Merry tayi mata tace "baza'a baki ba sai kinje kin Wanke min wannan kwanikan dana yi Girki dasu yanzu sannan za'a baki, zoki wuce kitchen ki fara aikin dana saki."

Tafiya take a hankali tana kallon Dadyn ta ko zaice ta dawo amma sai taga ko kallo bata ishe shi ba ya wani d'auke kai yana shan tea.

Kamar yadda taga Momyn ta nayi haka ta zauna ta fara wasa da ruwa tana d'ibar kumfar tana busawa tana dariya , bata yi aune ba taji an shara mata ruwa mai sanyin gaske.

Tsabar gigicewa bata San time d'in da ta bud'e fridge tana k'ok'arin shiga ba , jayo wa Merry ta kifa mata mari tace " daman wasa kika tsaya yi ba aikin Dana saki ba? Ashe kuwa zaki ci uban ki yau" ta fad'a tana yajo ta .


Ita kuwa Eleina ban da rawar sanyi babu abinda take yi hak'oran ta sai had'uwa suke da juna , nan da nan numfashin ta ya fara d'aukewa ai kuwa ta zube a wajan tana wani irin nishi da k'arfi.

Ba k'aramin tsorata Merry tayi ba ganin yadda numfashin ta yake sama kamar zai fita , da gudu ta fito ta kira Danial ta sanar da shi tana haki.

Tsaki Danial yayi yace " Asthma d'in tane ya tashi kuma ni bansan inda inyeler dinta yake ba ,kinga ni bai dame ni zo mu tafi church" ya fad'a yana rik'o hannun ta.

Zaro ido tayi tace "Daman tana da Asthma ne?."

Tsaki yayi yace "Gashi na fad'a miki kinga in baza kizo mu tafi ba zanyi tafiya ta."

Duk rashin tausayin Merry sai da tausayawa Eleina amma ganin babban ta bai damu ba ita ta share ta bishi suka tafi church suka bar  a kwance a kitchen tana Eleina sama-sama.
*D'AND'ANO*😎

Ya kuka ji a tsaya ko a cigaba? Ya kuka ji salon labarin ? A ko da yaushe Neat Lady da wani sabon salon take zuwar muku😉😉

Fita suka yi daga gidan suka nufi church suna tafiya suna hira.

+

Tun fitowar su akan idon  Bitris tana ganin fitowar su tayi sauri ta fad'a cikin gidan dan taga halin da Eleina take ciki dan akan idon ta ya Kore ta jiya mijin tane ya hana ta taimakawa Sisiliya, Bitris mak'ociyar suce suna shiri sosai ita da Sisiliya kuma tana k'aunar Eleina sosai.

Tayi sa'a kuwa gidan a bud'e da yake unguwar da suke babu mutane hakan yasa wayancin su suka barin gida a bud'e , da azama ta shiga gidan tana faman kiran Eleina.

Jin shiru babu motsin ta yasa ta kutsa kai cikin parlourn tana kiran ta shiru taji bata amsa ba , a hankali ta k'arasa kitchen d'in tana fad'in "Eleina where are..." Kasa k'arasa maganar tayi sakamakon ganin Eleina da tayi a kwance tana numfashi sama-sama .

Cikin tashin hankali ta isa wajan ta tana jijjigata tana fad'in "Wake up my daughter".

D'auko ta tayi ta fito da ita parlour ta kwantar da ita , kalle-kalle take tana so taga inda inyeler d'in take amma bata gani ba , cikin sauri ta fita daga gidan ta nufi wani pharmacy da yake kusa dasu ta siyo sabuwar inyeler ta dawo.

D'ago tayi ta bud'e bakin ta ta fesa mata tana d'an jijjigata , a hankali tayi ajiyar zuciya numfashi ta ya dawo dai-dai sai zazzab'i da ya rufe ta banda rawar sanyi babu abinda take yi.

Mik'ewa Bitris tayi ta shiga d'akin Sisiliya ta d'auko kaya ta canja mata sannan ta kalle tace " my daughter kinci Abinci? ".

Girgiza mata kai tayi alamu A'a , da sauri ta mik'e ta shiga gidan ta ta had'o mata tea mai kaurin gaske tare da chips ta kawo mata.

Ci Eleina take hannu baka hannu kwarya da rabon ta da abinci tun lunch d'in jiya , tana gama ci ta bata paracetamol tasha .

Fashewa tayi da kuka tana fad'in " ki kaini wajan Momy na kinji Mama ki kaini".

Share hawaye Bitris tayi ta rungume ta jikin ta tana shafa bayan ta.

Cikin k'ank'anin lokaci bacci yayi gaba da ita , kallon agogon d'akin tayi dan tasan yanzu an kusa fitowa daga church , tana zaune su Danial suka shigo parlourn.

Had'e rai Merry tayi tace "ke kuma daga ina ? Wa ya baki ikon shigo min gida?".

Cikin kuka Bitris ta kalli Danial tace " Amma ka bani mamaki wallahi banyi tunanin zaka yi haka ba to komai Sisiliya tayi maka ai bai kamata laifin ta ya shafi Eleina ba dan babu abinda ta sani yarinya ce k'arama , kuma....."

STORY CONTINUES BELOW

Cikin tsawa yace "shut up Eleina y'a tace ko kashe ta nayi babu abinda ya dame ki , daga yau kar ki k'ara shigo min gida kar kuma ki k'ara yink'urin tab'a y'a in ba haka ba alk'ali ne zai raba ni dake, get out for my house" ya fad'a yana nuna mata hanya da hannu.

Bata kuma wata maganar ba ta juya ta fita daga gidan cike da tausayin Eleina.


Cikin fushi Merry ta kalli Eleina tace "Tashi ki koma tsakar gida kona Zane ki yanzu".

Cikin rawar jiki ta mik'e ta fita tana tunanin ina Momy ta tafi ta barta?.

Zama Danial yayi yana tsaki dan shi gabad'aya baya son duk wani Abu da ya shagi Sisiliya shiyasa yake jin haushin Eleina.

Kusa dashi Merry ta zauna tace " My groom ina cikin farin ciki yau".

Kiss yayi mata a goshi yace "Me too" daga haka bai kuma cewa komai ba ya mik'e ya shiga d'aki.

Ganin ya shiga d'aki yasa tayi saurin fitowa inda Eleina take zaune tana hawaye , tsugunawa tayi a gaban ta ya rik'e kunne ta da k'arfi ta murd'e tace "Zaki ci uban kine yarinya badai yanzu na dawo gidan ba sai kin gudu da k'afar ki" tana gama fad'ar hakan ta mik'e har takai bakin k'ofa sai ta dawo ta kalli Elein dake faman hawaye tace "kar ki sake ki shigo parlourn nan sai da daddare" ya fad'a tana shigewa ciki.


Eleina kuwa kunne ta ta rik'e tana kuka sosai .

D'akin Danial ta shiga basu suka fito ba sai bayan k'arfe biyar na yamma a lokacin tuni Eleina tayi baccin yunwa a tsakar gida.

Koda suka fito basu kalli inda Eleina take ba kitchen Merry ta shiga ta had'a lunch suka zauna suka ci .

Shigowa Eleina tayi tana sosa ido alamu daga bacci ta tashi , kallan Dadyn ta tayi sai ta fara kuka tana tsoron zuwa kusa dashi.

Tausayi ta bashi hakan yasa ya mik'e ya rik'o hannun ta ya zaunar da ita ya ajjiye mata abinci a gaban ta , aikuwa kamar jira take ta fara cin Abincin tama murnar Dadyn ta ya kula ta.

Merry kuwa ta fusata Sosai akan wane dalili zai wani bata abinci Ashe kenan yana son Sisiliya har yanzu tunda gashi yana son y'arta, zama tayi a kusa dashi tace "kalle ta kamar ba y'ar Sisiliya ba haka itama wata rana zata ci amanar ka tunda gado tayi."

Nan take yaji wata irin tsanar Eleina ta taso masa cikin zafin nama ya mik'e yaja gashin Eleina ya cilla ta d'aki ya rufe yana wuci.

Murmushi nasara tayi ta matso kusa dashi tana shafa shi alamun rarrashi.

Eleina kuwa tun tana kukan har ta daina ta shiga wasan ta , da yake akwai toilet a d'akin in taji fitsari sai ta shiga tayi ta fito ta cigaba da abinda take yi , tana cikin wasan in ta tuno da abinda Dady yayi mata itada Momy sai ta fashe da kuka mai tsanani.


⚡⚡⚡⚡


Tunda ta sauka a garin Abuja gaban ta yake fad'uwa bayan motar su ta tsaya aka bud'e boot a fito da kayan ciki  , ganin sun bud'e yasa ta dad'a b'oye wa a cikin wani buhu , juyawa Wanda ya bud'e motar yayi cikin sauri ta diro daga cikin motar ta bar wajan da sauri , babu Wanda ya lura da ita Dan kowa tunanin sa fasinja ce ita, mota ta hau ta nufi unguwar su.

Bakin wani k'aton gida ta  tsaya Cikin fargaba ta tura gate d'in gidan ta shiga , cikin sauri mai ya taso cikin harshen yarabanci yake fad'in "Waye ?" Duk da dad'ewa da tayi bai bai ganta ba hakan baisa ya kasa gane ta ba .


Murmushi ya k'ak'alo tace "Sannu fa su Momy suna nan kuwa?".

Cikin girmamawa ya d'aga mata kai alamun eh , Tace " Please in kana da dari biyu d'an bawa mai mota a waje."


STORY CONTINUES BELOW

Cikin girmamawa ya juya ya fita.

Cikin gidan ta shiga a parlour ta tarar dasu suna hira , Momyn ce ta mik'e tsaye tace "Sisiliya are u?".


Fashewa tayi da kuka tayi knee down jikin ta na rawa tace " Please Momy forgive me please" ta fad'a tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

Cikin masifa Dadyn ya mik'e yace "Ba'a yafe miki d'in ba ki tashi ki koma wajan Danial tunda shi kika zab'a akan mu ki tashi ki Fitar min daga gida!" Ya fad'a cikin tsawa.


Kwanciya tayi ta rik'e k'afar sa tana kuka sosai tace "please Dady nasan nayi Kuskure amma Ku yafe min hakan bazai k'ara faruwa kayi Hak'uri."


Jikin Momy yayi sanyi ta d'ago ta ta share mata hawaye tace "Kiyi mana bayanin abinda ya faru tsakanin ki da Danial ina Eleina take?".

" Momy ban San me nayi masa ba yace kori ni daga gidan jiya ana ruwa kuma yace bazan tawo da Eleina ba yanzu haka tana can".

Dady yace "gwara ma da baki tawo da ita ba yaje ya rik'e y'arsa muma mu rik'e tamu y'ar , is okay my daughter stop crying" ya jayo ta jikin sa ya rungume ta yana jin dad'in dawowar ta.

Shiru tayi itama tana farin cikin shiryawar da tayi dasu .


*ASALIN LABARIN*

Mr Deynis Ola shine cikakken sunan mahaifin Sisiliya , asalin su Yoruban Abia state ne aiki ne ya kawo Ola Abuja har shine suka zauna a nan, kyawawa ne sosai da idan ka gansu baza kayi zaton yarabawa ne ba sabida kyaun da Allah yayi musu.

mahaifin su Ola hamshak'in mai kud'i ne sosai hakan yasa duk y'ay'an sa babu wanda bashi da kud'i, Ola yana da y'ay'a biyar duka maza tun suna yara suke mutuwa yanzu sai Danial da k'anwar Christy , Jecholia wato mahaifiyar Sisiliya kenan ita kuma a Abuja aka haife ta kowa nata yana garin Abuja .

Sun had'uDeynis ne a wani super market tunda lokacin suke soyayya har akayi aure , Jecoliya ita kad'ai ce wajan iyayen ta sun d'auki son duniya sun d'ora mata dan lokacin bikin ta sunyi wasa da kud'i kamar basa so.

Bayan Aure Jecolia da Deynis da shekara uku suka haifi Goluria bayan shekara biyu suka haifi Sisiliya tun daga kanta basu kama haifuwa ba.

Duk wani so sun tattara su d'aura akan Goloria da Sisiliya, Goloria tana shekara biyar a duniya ta mutu sosai suka ji mutuwar ta suka dinga kuka suna kiran Jesus, tunda ta mutu so ya dawo kan Sisiliya Duk abinda take so shi ake mata.

Sisiliya tana da shekara ashirin a duniya suka had'u da Danial a makaranta , tun suna soyayya a b'oye har suka fito suka baiyana, Danial Danial d'an garin Lagos ne yazo karatu a Abuja shine suka had'u da Sisiliya.

Koda Sisiliya ta gabatar da shi a matsayin Wanda zata Aura mahaifin ta mr Deynis yayi tsalle ya dire yace baza ta aure shi ba sai in ta zab'a kosu ko shi.

Danial ya dinga hure mata kunne har ta amince ta bishi suka gudu daga garin suka je can Lagos aka d'aura musu aure suka zauna.


Jecolia tayi kuka sosai na rashin y'ar ta k'arshe ta Hak'ura , Jecolia itace pastor d'in duk church d'in dake garin Abuja.


Zaman lafiya ake tsakanin Danial da Sisiliya har zuwa lokacin da ta d'auki cikin Eleina , yayi farin ciki sosai dan har kyautar sark'ar gold yayi mata mai tsadar gaske.

Lokacin da aka haifi Debora babu irin murnar da baiyi ba kowa shigowa yake yana kallon Eleina sabida kyau ta.

Eleina na Shekara hud'u  amma akwai yawo ga basira ana yin Abu ko aka fad'a mata zata rik'e shi, Eleina ta d'an iya Hausa sabida akwai hausawa a unguwar da suke kuma suna shigowa gidan su to yau da gobe ita da Sisiliya yasa suke d'an jin Hausa.


Tunda Merry ta shigo rayuwar Danial Sisiliya ta fara fuskantar matsala har zuwa ranar da ya Kore ta Wanda bata San dalilin hakan ba a lokacin Eleina tana shekara shida.


Wannan kenan.


⚡⚡⚡⚡


Washe gari Danial ya bud'e Eleina ya bata abinci kamar gaske , duk abinda yake yi Merry na kallan sa tayi kwafa tace "sai nasan yadda nayi yarinyar nan tabar gidan nan."


Bayan Danial ya fita Merry ta kalli Eleina tayi murmushi tana girgiza kai , jin k'arar motar Danial alamu ya dawo yasa tayi sauri ta d'auki Eleina ta shigar da ita d'akin Danial ta d'auki kud'i masu yawa ta saka mata a riga ta fito ta kyale ta.

Eleina kuwa fito da kud'in tayi ta rik'e a hannun ta tana wasa dai-dai lokacin Danial ya shigo d'akin.

Kallon Eleina yayi yace "ke a ina kika d'auki wannan kud'in?".


Zata yi magana Merry tayi saurin cewa " Eleina sata kika koma? Kema kin d'auko halin uwar ki Gaskiya bazan zauna da ita a cikin gidan nan ba sata bazai yu ba."

Ran Danial ya b'aci ba tare da yayi bincike ba ya nufi Eleina da take wasan ta ya kifa mata mari sannan ya zare belt ya shiga Zane ta , tun tana kuka tana bashi Hak'uri Har har ta kasa magana numfashin ta ya tsaya cak.

Tsayawa yayi da dukan yana huci ransa a b'ace , juyowa yayi ya kalli Merry da take ta faman tsalle tana murna harara ya sakar mata ba shiru ta nutsu tana kallan sa .

+

Tsaki yayi ya cillar da belt d'in ya fita daga gidan , wani wawan tsalle Merry tayi tace "Kai amma fa naji dad'in dukan nan da yayiwa wannan shegiyar , bara na bata magani Dan bana so ta mutu ban gama azabtar da ita ba" ta fad'a tana shiga toilet d'in da yake d'akin.

Ruwan sanyi da d'ebo ta sharawa Eleina da take kwance jikin ta duk ya fashe , cikin gigicewa ta mik'e tana numfashi dak'yar.

Wata banzar harara ta sakar mata ta bud'e drower ta d'auko magani ta bata tasha tana ajiyar zuciya, komawa tayi wajan ta kwanta har bacci ya d'auke ta.

Tsaki Merry tayi ta fice daga gidan , Bitris ta ganin Fitar ta shigo gidan a guje dan tana jiyo ihun Eleina , d'ago tayi ta fashe da kuka tana kallon yadda jikin ta ya fashe ga kayan ta a jik'e , mik'ewa tayi da sauri ta shiga toilet ta kunna heater ta ruwan yayi zafi , d'aukar tayi cak tayi mata wanka ta gasa mata jikin ta ta saka mata kaya ta kalle ta tace "My daughter me yake damun ki Yanzu?".

Cikin kuka tace " Mama wajan Momy nake so zuwa Dady kashe ni zaiyi ki kaini wajan ta , *BAN SAN LAIFIN* dana yi masa ba yanzu baya sona".


Cike da tausayi take kallon ta da ace mijin ta zai amince ai wallahi d'auke ta zata yi to tasan ko a mafarki bazai yarda ba Dan basa shiri da Danial, kwantar da ita tayi akan cinyar ta tana shafa mata kai har bacci ya d'auke ta.


Cikin sand'a ta mik'e ta fice daga gidan Dan bata so Danial yazo ya same ta , fitar ta da minti biyar Danial ya shigo gidan yana zama Merry ta shigo , d'akin da Eleina take ta shiga da mamaki take kallon ta ganin yadda akayi mata wanka aka canja mata kaya , fitowa tayi ta kalli Danial tace "Dear Kaine ta shirya Eleina haka?".

D'agowa yayi ya kalle ta yace " Ban gane ba me kike nufi?".


Tace "Naga anyi mata wanka an sake mata kaya kuma ni ban yi mata wanka ba magani kawai na bata."

Cikin b'acin rai yace "Bitris " yana furta hakan ya mik'e ya nufi gidan Bitris .

Masifa ya dinga zazzagawa mijin ta akan kar ya k'ara barin ta ta shigar masa gida , Mijin Bitris yace "Calm down Danial Dan Matata tana son y'ar ka shine kike wannan fad'an ? Yau zamuyi tafiya kuma baza mu dawo ba sai nan da shekara biyu ko uku kaje ka kashe y'ar taka ai ba ta wani bace" yana gama fad'ar hakan yayi tsaki ya bar masa wajan.

A fusace ya koma gida ko kallan Merry baiyi ma ya shiga d'aki ya ficiko Eleina ya fito da ita parlour ya kalle ta yace "In kika k'ara yiwa waccan Bitris d'in magana saina kashe ki, babu ruwan ki da ita in kin ganta kinji ko?".

Ita dai Eleina banda rawar jiki babu abinda takeyi Dan gabad'aya tsoron Dadyn nata take.

Tsaki yayi ya mik'e ya shiga d'aki  Merry tabi bayan sa .

STORY CONTINUES BELOW

Tsakar gida Eleina ta fito tana kukan yunwa kuma tasan Merry baza ta bata Abinci ba , k'arar bud'e k'ofa taji tana d'ago kai taga Bitris ta shigo cikin sand'a , zata yi magana tayi sauri dakatar da ita jakar ta ta bud'e ta d'auko dubu d'aya ta kalle tace " My daughter yau zamuyi tafiya ki rik'e wannan kar ki nunawa kowa ga inyeler dinki ma ki rik'e a hannun ki ".

Karb'a Eleina tayi tace " Mama zan biki".


Bitris ta share hawaye tace " bazai yu na tafi dake ba amma zan dinga dawowa ina ganin ki ki dinga cin abinci kinji?" Tana gama fad'ar hakan tayi waje da sauri.


Mik'ewa tayi ta shiga d'akin Momyn ta ta bud'e wata yar jakar ta ta saka kud'in da inyeler d'in , tana cikin bincike a cikin jakar ta gano hoton ta ita da Momyn ta sai kuwa ta fashe da kuka tana kiran Momy , tun tana kukan har ta daina ta fara wasa.

Bayan kwana biyu.

Da daddare misalin k'arfe bakwai na dare hadari ya had'o sosai garin yayi shiru , Merry ce zaune a parlour ita kad'ai da alama Danial baya nan, kallon Eleina tayi tace "ke come here".

Cikin rawar jiki tazo ta durk'usa a gaban ta , Merry tace " Maza tashi kije waje wajan mai provision d'in can kice ya baki cingom ki kawo min saura kuma ki dad'e."

D'ago kai tayi ta kalli Merry tace "Momy an fara ruwa fa kuma Momyna ta hanani fita da daddare" ta fad'a taba wasa da y'ar jakar ta data rataya a wuyan ta.

Cikin mamaki Merry ta kalle tace "ni kike fad'awa wannan maganar? Lallai to bara Dadyn naki yazo".

" Meya faru naji ana bara nazo?" Danial ya fad'a yana shigowa parlour.

Merry ta fashe da kuka tace "wai ni ce zan aiki Eleina nace taje provision d'in can tace a bani cingom shine tace wai baza ta ba Momyn ta ta hana fita da dare ni ba Momyn ta bace Dan haka baza ta ba."

Cikin tsoro Eleina tace "Bafa haka nace ba Dady cewa nayi....." Bata rife baki ba yayi ball da ita ta fad'i a kan hannun ta ya bada sautin k'asss , wata mahaukaciyar k'asa ta saki tana rik'e hannun ta .

Ba tare da ya kula da hannun nata ba yace "Tashi kije ki karb'o cingom d'in in kika dawo Babu shi saina kashe ki".

Dak'yar Eleina ta mik'e ta fita daga gidan tana kuka sabida yadda hannun ta yake bala'in ciwo.

Yawo take a unguwar amma bata ga wani provision a bud'e ba Dan har an fara yayyafi , har zata dawo sai tanu maganar Dadyn ta cikin sauri ta cigaba da tafiya tana kuka .

Tafiya take bata San inda zata ba tun bata gaji ba har ta kasa tafiya ga hannun ta na mata ciwo , juyawa tayi da niyar komawa gida amma sam ta manta hanyar da zata kaita gida , duk da haka bata Hak'ura ba ta cigaba da tafiya a gari babu kowa ko ina a kulle balle tayi tambaya , Wata mota ta gani a ajjiye irin ta d'ibar kayan nan zuciyar tace ta bata umarnin kawai ta hau bayan motar irin motar mak'ocin suce yanzu zai kaita gida.

Cikin murna ta d'afe bayan motar dak'yar ta zauna , babu jimawa mai motar ya shiga yaja motar yayi gaba abinsa.


Danial ya kasa zaune ya kasa tsaya kusan two hours da Fitar Eleina amma har yanzu bata dawo ba , Ganin haka Merry ta kalle shi tace " Haba Dadyn Eleina kaima fa kasan babu yadda za'a yi ace Eleina ta b'ata a garin nan ka kwantar da hankalin ka Zata dawo ".

Haka Merry ta dinga yaudarar sa har hankalin sa ya kwanta duk dai cikin zuciyar cike take da fargaba amma haka ya daure ya kwanta.

Ita kuwa Merry rufe ido tayi tana addu'a kar Eleina ta dawo.


Eleina kuwa tun tana wasa da jakar ta har bacci ya d'auke ta ta lullub'a da buhu tayi bacci a bayan mota , tun tana bacci cikin dad'in rai har ta mik'e bacci ya ishe ta har lokacin tafiya suke basu daina ba ga fitsari ya matse ta ga hannun ta yayi tsami ya kumbura sosai .


STORY CONTINUES BELOW

Gari yayi haske sosai har zuwa lokacin driver bai tsaya ba tafiya yake , Eleina yunwa ta dame ta sai rik'e ciki take .


Basu yi wata tafiya mai yawa suka iso tasha , fitowa drive yayi ya shiga cikin tasha ba tare da yasan da mutum a bayan motar sa ba , ganin ya fita yasa Eleina ta diro daga motar tayi cikin tasha tana fita kayan ta duk jirwayen fitsari tana tafiya tana kuka tana kiran Momy , horn ake a bayan ta amma sam bata ji Ashe har yazo tsakiyar titi bata sani ba , drivern yayi k'ok'arin taka burki amma ya kasa sai da ya kad'e Eleina.


Da sauri drivern ba fito ya d'auke ta yasa a bayan mota da gudu ya nufi asibitin Aminu Kano teaching hospital.


Sosai mutanen tashar unguwa uku suka tausayawa Eleina gani yadda jini ke zuba a kanta kamar an yanka akuya , masu raunin zuciya yadda yi mata kuka .


Isar su asibitin aka karb'e ta da gaggawa aka kaita emergency aka fara treatment d'in ta , mota drivern ya koma ya d'auko ya waya ya kira Hajiyar da yake yiwa aiki ya sanar da ita , babu jimawa ta iso da saurin ta ta kalli shi tace "Musa ya akayi haka ta faru?".


Yace " Wallahi Hajiya babu irin horn d'in da ban yiwa yarinyar nan ba amma Kar mai tunani ko kad'an bata ji ba ."


"Mudai fatan mu Allah ya bata lafiya".


Ya amsa da Ameen.


Ciki suka koma bakin d'akin da aka kwantar da ita , Dr ya fito ya kalli ta yace " Ku biyo mi muje office ".


Cikin sauri suka mik'e suka bi bayan sa , bayan sun zauna ya kalli matar yace " bata ji wani ciwo sosai ba ta samu buguwa a kanta sosai sai kuma hannun ta Dana kula kamar ba ciwon yau bane  amma insha Allah zuwa anjima zata yi farkawa cikin koshin lafiya."


Ajiyar zuciya tayi tace "Alhamdulilah mun gode likita " suka fito daga office d'in suka shiga d'akin da aka kwantar da ita suka zauna.

K'arewa fuskar ta kallo matar take nan take taji so yarinyar ya shigar ta sosai , bud'e k'ofar da akayi ne yasa ta juya tana kallon Wanda ya shigo .


Maza ne biyu sai mace d'aya kana gannin su kasan uba ne da y'ay'an sa, yarinyar tace "Momcy ya jikin yarinyar?".


Tace " da sauki ance zuwa anjima zata iya farkawa ."


Momy ta kalli mijin nata tace "Wallahi yarinyar tausayi take bani sosai gata kyakykyawa."

Yace "Ai da tausayi Allah ya bata lafiya."

Namijin ne ya kalli macen suka tab'e baki suna hararar Eleina.

Har akayi sallar La'asar Eleina bata farka ba , suna zaune kowa da abinda yake sak'awa a ransa .


Eleina ta fara motsa hannun ta alamun ta farka , Momy ce ta lura da hakan cikin sauri ta k'arasa wajan ta tana fad'in "Dady Suhail ta farka fa" da sauri suka k'araso baki gadon suna kallon yadda take motsa ido , a hankali ta bud'e idon tana k'are musu kallo.


Dady ya kalli namijin yace "Suhail maza jeka ka kira Dr".


Wanda aka kira Suhail ya fita yana kwafa zuciyar sa cike da jin haushin Eleina.

Tare suka shigo da Dr ne ya kalli Eleina yace " Sannu ko me yake damun ki Yanzu?".


Shiru tayi babu amsa sai kallon su da take yi , likita ya kuma maimaita tambayar amma ta Kuma yin shiru.


Dady ya kalli likitan cike da damuwa yace "kodai ta samu matsala ne?".

Likita yace " bana jin haka Gaskiya sai in bata jin hausa".

Dr ya kalle ta yace "What is ur name?".

A hankali ta furta " Eleina Danial ".


Suhail ya kalli k'anwar sa Shukra suka k'yalk'yale da dariya tare da fad'in " Ashe k'yadara ce ".

STORY CONTINUES BELOW

Tsawa Dady yayi musu yace " Baku da hankali ne meye abin dariya a nan ni na rasa ranar da zakayi hankali Wallahi , Ku fita Ku bamu waje sha-sha-shai kawai."


Dady ya kalli Dr yace "yi Hak'uri likita cigaba da aikin ka".


Kafin likita yayi magana Eleina ta fara kuka cikin yarabanci take fad'in " Kar Ku maida ni wajan Dady na zai kashe ni baya sona wajan Momy zaku ni".


Babu Wanda ya fahimci abinda take cewa , likitan ya kalle ta yace "Speak  English we don't understand what u said."


Rik'e hannun Momy tayi da d'aya hannun da baya ciwo ta cigaba da kuka tana maimaita abinda ta fad'a da turanci.


Cikin turanci Momy tace "ina Momyn taki ta tafi?".


Eleina tace " Ban sani ba nima Dady ne ya Kore ta ana ruwan sa da daddare , kullum sai ya Zane ni kar Ku maida ni please."

Dady yace "A wanne gari kike?".


" Lagos" ta bashi amsa tana rik'e cikin ta .

Likita ya kalle ta yace "kina jin yunwa ne?".


D'aga masa kai tayi alamun eh , Cikin sauri Momy ta goge hawayen ta ta d'ebo mata abinci ta kawo mata , kallan ta tayi tace "Momy banyi brush ba".


Cikin jin dad'in sunan da ta kira ta dashi Momy ta mik'e ta fita waje ta siyo brush ta dawo tayi mata sannan ta bata abincin da kanta.

Office d'in Dr Dady ya shiga likitan ya kalli Dady yace " Ga magunguna mun rubuta mata kuma Gaskiya ba zamu Sallame ta yanzu ba sai taji sauki sosai. "


Godiya Dady yayi masa ya koma d'akin .

Suhail da Shukara suna zaune a d'akin suna k'us-k'us d'in su , Momy tace "Dadyn Shukara yanzu ya kake ganin zamuyi da wannan yarinyar?".


Dady yace " Na yanke hukuncin zamu rik'e ta tamkar y'ar da muka haifa dan ni yarinyar ta shiga raina sosai Wallahi , zamu musulintar da ita ko babu komai ma samu ladan hakan , ina tausayawa yarinyar sosai yarinya k'arama ace tana fuskan tar wannan matsalar  ai da tausayi ."

Ajiyar zuciya Momy tayi tace "Kamar kasan abinda yake raina kenan wallahi tunda nagan ta naji ina k'aunar ta sosai , naji dad'in wannan hukuncin Allah ya bamu ikon rik'e ta."

"Wai Yanzu Dady sai Ku rik'e wannan K'yadarar Baku San daga inda take ba , kila ma y'ar boko haram ce haka kawai muna zaune Ku d'auko mata jaraba Ku kawo mana ita cikin gida , Gaskiya da sake baza mu zauna da sabon tuba ba ko ba haka ba Sister?."

Shukra tace "Wallahi kuwa kila ma mayya ce  Baku sani ba , Momy da ace Baku da y'ay'a sai Ku d'auke ta amma fa kuna da y'ay'a har guda biyu amma kuke harin wannan sabon tuba......." Marin da ya sauka a fuskokin su ya hana ta k'arasawa .


Cikin mamaki Suhail ya kalli Dady yace "Dady akan wannan k'abilar ka mare ni?".

Shukra tace " Momy akan wannan sabon tubar kike mare ni? Ke nan kinfi sonta damu ko?."

Cikin tsawa Dady yace "na rantse da Allah duk Wanda ya kuma kiran ta da wannan sunan sai ransa yayi mummunan b'aci, Ku Yanzu ba abin alfaharin Ku bane ace iyayen Ku sun rik'e yarinyar da rayuwar ta take cikin hatsari da yake Baku da hankali shine kuke fad'a mana wannan maganar banzar , babu kamar kai Suhail ka girma amma baka San ka girma ba kana biyewa k'anwar ka kuna sha-shanci to Ku shiga hankalin Ku daga yau wannan yarinyar ta zama k'anwar Ku , Ku tashi Ku bani waje."


Jikin sauri suka mik'e suka fita daga d'akin.


Momy ta kalli Dady tace "ni bansan inda yaran nan suka d'auko wannan halin banzan ba Wallahi."

Dady ya kalli Eleina da take kallan su ta d'azu yace "My daughter daga yau sunan ki FATEEMAH ba Eleina ba kinji."


FATEEMAH ta maimaita sunan a ranta , murmushi tayi tace "Nice name my Dady."


Shima murmushi yayi suka cigaba fa hira da ita.

Suhail da Shukra kuwa mota suka shiga da gudu Suhail ya bar asibitin suka nufi gida kowa ransa a b'ace.


wani tangamemen gida suka shiga dake unguwar state Road , ko kulle motar basu yi suka shiga parlour suka zauna suna huci.


Iya tsaruwa parlourn ya tsaru babu abinda babu a ciki.


Shukra ta kalli Suhail tace "Yanzu Yaya haka zamu bari mana ji muna gani wannan sabon tubar ta fimu matsayi wajan iyayen mu? Kana ganin kanta suka mare mu abinda basu tab'a yi ba kenan ."


Suhail ya mik'e tsaye ya kalli Shukra yace "ki rabu da ita badai gidan nan zata dawo ba sai ta gane kuran ta wallahi wannan murgud'ad'd'en hannun ta sai mun karya shi Wallahi zata gani" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita daga parlourn yana bala'i.


Su Dady kuwa a d'an k'aramin lokaci sunyi mutuk'ar sabo da Eleina wacce take amsa sunan FATEEMAH yanzu, ta saki jiki dasu kamar dama can  sansu.


Dady da kansa ya lak'aba mata Kalmar shada ta fad'a itama , kabbara Momy tayi tana faman zuba murmushi cikin hikima Momy take sanar da ita addinin musulci , tunda Fateemah ta karb'i Musulunci take jin wani farin ciki na ratsa ta ita kad'ai ta dinga murmushi tana jin dad'in sunan da ake kiran ta dashi.

Fateemah akwai wayo da saurin fahimtar Abu nan da nan take d'auke abinda Momy take ce mata.

Danial kuwa......Danial yana tashi daga bacci ya mik'e da sauri ya shiga d'akin da Eleina take  , dube-dube yake amma bai ganta ba gaban sa ya fad'i badai har yanzu bata dawo ba , a fusace ya fito cikin k'araji yake k'wallawa Merry kira , da gudu ta fito ta tsaya a gaban sa tana fad'in "Dear lafiya kake kira na haka?".

B'ata rai yayi yace " Ina Eleina?".


Dafe kirji tayi tace "Daman bata dawo ba? To yanzu ya zamuyi kenan?".

Shak'e mata wuya yayi ya zaro ido waje yace " Baza ki  min inda kika kai min daughter ba ? In baki fad'a min ba yau sai na Zane ki a gidan nan. "


Numfashi take dak'yar idon ta yayi ja ya firfito sosai dak'yar tace "Nima ban sani ba kaje ka dubo ta".


Cillar da ita yayi ya nuna ta da yatsa yace "in na fita ban ganta ba I swear sai jikin ki ya fad'a miki" ya fad'a yana fita daga gidan da sauri , bai tsaya d'aukar mota ba ya fita a k'asa yana tafiya yana kalle-kalle.

Lungu da sak'o yake bi yana kiran Eleina , sai da ya kwashe awa uku yana wayon Neman ta amma ko mai kama da ita bai gani ba , haka ya dawo jikin sa gabad'aya yayi weak dak'yar yake tafiya zuciyar cike da nadamar abinda ya aikata mata.


Koda ya dawo bai kalli inda Merry take ba kaya ya canja ya d'au makullin mota ya fita daga gidan.

Bai wuce ko ina ba sai gidan radio da gidan Tvn dake Lagos cigiya ya bayar ko wani ya ganta , gida ya dawo jikin sa yayi bala'in sanyi zuciyar cike take da kewar y'ar sa .

Merry kuwa tunda ya fita take Neman yadda zata yi tasa ya manta da Eleina take , har ya shigo tana zaune tana tunani ta kasa samun mafita.

Zama yayi ya kwantar da kansa a jikin kujera ya lumshe ido yana tunanin Eleina , cikin dauriya Merry ta mik'e ta zauna kusa dashi tace "Calm down sweet ni San wannan yarinyar tana sane ta gudu ba b'ata tayi ba guduwa tayi ka daina tayar da........" Saukar Marin da taji a fuskar ta ya hana ta k'arasawa , cikin zafin rai ya mik'e ya nuna ta da d'an tsaya yace "in na k'ara jin kin fad'in wannan maganar sai na kashe ki rubbish" yana fad'ar hakan ya shige d'aki yana huci.

Ita kuwa Merry tana dafe da kuncin ta zuciyar cike da tsanar Eleina , a fili tace "sai nasan yadda nayi nasa ya manta da wannan y'ar tasa bazan tab'a kyale ta ba" tana fad'a tana ficewa daga gidan da sauri.


⚡⚡⚡⚡


*BAYAN KWANA BIYU*


Jikin Fateemah yayi sauki sosai ta saba sosai da Dady da Momy , drivern da ya kad'e ta ya kawo mata y'ar jakar ta kullum cikin kallon hoton Momyn ta take.

Ganin yadda ta samu sauki aka basu sallama suka tawo gida, tunda suka shiga gidan Fateemah take kallon sa Dan iya had'uwa gidan ya had'u.

Da sallama suka shiga parlourn gidan da gudu Shukra ta taso tana fad'in "Ga Momy ga Momy".


Tunda ta had'a ido da Fateemah ta had'e rai kamar bata tab'a dariya ba , Momy ta kalli Shukra tace " Shukra maza kawo mana abinci."

Hararar Fateemah tayi ta shiga kitchen tana kwafa , kawo musu abincin tayi ta juya ta shiga d'aki tana shirya irin muguntar da zata yiwa Fateemah.

Bayan sun ci abinci Momy ta kira Driver ta bashi kud'i yaje kanti ya siyowa Fateemah kayan sawa kafin a d'inka mata .

Wanka tayi mata aka kawo kayan ta sa mata , parlour suka dawo Momy ta kira Suhail da Shukra suka zauna suna sauraren abinda zata ce.

"Suhail ,Shukra" d'ago wa suka yi suka kalle ta suka ce "Momy muna jinki".

Momy tace " ga k'anwar Ku nan ina so Ku rik'e ta kamar k'anwar Ku bana so Ku dinga muzguna mata kunga yarinya ce , ba y'ar aiki na kawo muku ba y'a ce Dan dai-dai take daku a waje na, kar naji kar na gani in ba haka ba ranku zaiyi bala'in b'aci , ke Shukra Fateemah a d'akin ki zata dinga kwana sabida tayi k'ank'anta da kwana ita kad'ai Shukra kar kiga dare yayi babu kowa a d'akin daga ke sai ita ki dinga wulak'anta ta Allah yana kallon ki kuma duk ranar da na gane gaskiya sai ranki ya b'aci in kunne yaji jiki ya tsira" ta fad'a tana mik'ewa daga wajan ta saura sama .


Cikin b'acin rai Suhail ya kalli Fateemah da take game a wayar Momy yace "Shukra kinji abinda Momy tace fa , akan wannan banzar zata takura mana yarda kafa mana sharud'a Wallahi baza ta sab'u ba wai ta d'auke ta kamar yadda ta d'auke mu mtswww."

Shukra tace "ai gwara kai nifa kana ji wai a d'aki d'aya zamu dinga kwana , amma ni hakan yayi min ta haka zan samu dama naci uban shegiya mayya" ta fad'a tana hararar Fateemah.

Suhail yayi murmushi mugunta yayi kwafa ta mik'e ya bar wajan zuciyar sa cike da haushin Faty.

 ita kuwa Fateemah ko a jikin ta Dan ba fahimtar abinda suke cewa take ba ,hararar ta Shukra tayi komai ta tuna sai tayi murmushi ta shige d'aki.

Da daddare suna zaune a parlour Dady ya kalli Fateemah yayi murmushi yana jin dad'i a ransa , Fateemah kuwa abincin ta take ci cikin kwanciyar hankali.

Bayan sun gama cin abincin Momy tayi mata wanka ta saka mata kayan bacci , da kanta ta kaita d'akin Shukra ta kwantar da ita tayi mata addu'a sannan ta fito.

Shiga d'akin Shukra tayi ganin Fateemah akan gadon ta yasa tace "kan bala'i Wallahi baza ta kwana a gado ba sai dai ta dawo k'asa".


A fusace ta nufi kan gado ta d'akawa Fateemah duka a cinya , cikin firgici ta Mik'e tana fad'in " Sorry Dady bazan k'ara ba".

Tsaki Shukra tayi tace "Bayarabiyar banza kawai zaki tashin min a gado ko saina Zane ki?".


Duk da bata fahimci abinda tace sosai ba amma ta gane fad'a take mata , da sauri ta mik'e ta sauka a kan gadon tana kallon Shukra.

Tab'e baki Shukra tayi ta kwanta abinta , Cikin turanci Fateemah tace " sister ni a ina zan kwanta?".

"Kutumar uba kar na k'ara ji kin kira ni da wani Sister Dan uwarki ni ba y'ar uwar ki bace Dan kaf dangin mu babu arna , in zaki kwanta kan carpet ki kwanta in baza ki kwanta ba kuma ki koma garin Ku shegiya mayya".

Tsoro Fateemah taji sosai cikin rawar jiki ta kwanta a carpet tana k'ok'arin yin kuka.

Cike da mugunta Shukra ta mik'e ta d'auki remote d'in Ac ta k'ure mata gudu , komawa tayi ta kwanta tare da Jan blanket ta rufa .

Rawar sanyi Fateemah ta fara hak'oran ta suna had'uwa da juna , hancin ta ya toshe dak'yar  take Fitar da numfashi , nan take numfashin ta ya fara sama alamun Asthma d'inta na gab da tashi .

Numfashi da take yi ne yasa Shukra kallo inda take , ganin yadda take numfashi yasa ta tsorata kar ta mutu Cikin sauri ta mik'e ta kashe Ac sannan ta d'auki barko mai dauyin gaske ta rufa mata.

A hankali taga numfashin ta yana dawo wa dai-dai har bacci ya d'auke ta , zama tayi kan kujerar dake d'akin tayi tsaki tace " ko me yasa ma na taimaka mata oho " cikin jin haushi ta mik'e ta fice daga d'akin.

Bata wuce ko ina ba sai d'akin Suhail Dan tasan baiyi bacci ba , ko sallama babu ta afka cikin d'akin yana zaune yana danna waya alamun charting yake .

D'ago kai yayi ya kalle ta ya had'e rai yace "ke kuma lafiya kika shigowa mutane d'aki  ko sallama babu?".

Cikin da takaici tace " Wallahi Yaya Suhail Momy sun kawo mana jaraba cikin gida , kaga wani numfashi da yarinyar can take yi ? Wai daga na k'ure Ac sai ta fara wani irin numfashi kamar wacce zata mutu."

Tsaki yayi yace "daman ai Momy tace min tana da Asthma , kema kuma laifin kine meye zaki kashe Ac basai ki barta ta mutu ba shegiya kawai."


"Wai Yanzu ya zamuyi da itane?".

STORY CONTINUES BELOW

Numfashi Suhail ya sauke yace " Bama kisan abin haushin ba kin San har Momy ta siyowa wannan arniyar form d'in Nigerian tokish".


Zaro ido tayi tace "Yaya Nigerian tokish fa kace? Tab lallai ma makarantar da tafi ko wacce tsada a Kano ita za'a kaita ? Da sake Wallahi."

Suhail yace "Kar ki damu da sannu zamuyi maganin ta soon Wallahi zata San ta shigo gonar mu, jeki ki kwanta gobe zamuyi maganar."

Juyawa tayi ta fita daga d'akin a ranta tana maimaita makarantar da Momy zata kai Fateemah .

Da asuba tana jin bugun Momy tayi saurin d'auko Fateemah ta d'ora ta kan gado sannan ta bud'e d'akin , shiga d'akin Momy tayi tana fad'in "kedai naga ranar za kiyi hankali ki dinga tashi sallah da kanki".

Kusa da Fateemah ta zauna ta d'an jijjaga ta tana fad'in " Fateemah ! Tashi kiyi sallah kinji. "

Da yake bata da nauyin bacci yasa ta bud'e ido ta kalli Momy , Momy tayi murmushi tace "Maza tashi daughter kiyi sallah."

Mik'ewa tayi cikin hausar da bata fita sosai tace " Momy zo muje kiga yadda kika kowa min alwala."


Cikin rud'ewa Momy tace "Subahanallah daughter yaushe mura ta kama ki haka? Muje kiyi sallah sai mu sai na baki magani."

Kallan Shukra tayi tace " Ac kika kunna ko? Bayan ta fad'a miki yarinyar nan tana da Asthma amma da yake kunne k'ashi ne dake sai da kika kunna ko? Kin kyauta zamu gamu ne. "

Jan hannun ta tayi suka fita daga d'akin .

Tsaki Shukra tayi tace "haka kawai yarinya ta had'a mu da uwar mu".

Koda suka koma d'akin alwala Fateemah tayi , sosai ta burge Momy ganin yadda ta iya alwala sai d'an cin gyaran ta da ake kad'an.

Cikin nutsuwa tayi sallah bayan ta idar ta Kali Momy tace " Ina kwana Momy".

Murmushi Momy tayi tace "lafiya lau daughter , sannu mura ta kamaki sosai, zo muje ki gaida Dadyn Ku".

Tare suka shiga d'akin suka tarar ya dawo daga masallaci , gaishe Fateemah tayi cikin farin ciki ya amsa yana murmushi.

Da sallama Suhail ya shigo ta tsuguna ya gaida iyayen nasa sannan suka zauna sukayi lazimi kamar yadda suka saba , sai da gari yayi haske sannan kowa ya mik'e ya , Momy tace " Yauwa Suhail in anjima zaka kai Daughter Fateemah makaranta ta zatayi interview , k'arfe goma zaku tafi saura kuma kak'i fitowa da huri."

Cikin takaici yace "Yanzu Momy interview d'in ma ni zan kaita ? Ina Musa basai ya mik'a ta ba."

Cikin tsawa Dady yace "Wallahi kaji na rantse kai zaka kaita , wai ka mai yasa baka da kirki ne? Allah yasa kak'i kaita ko kak'i fitowa sa huri ka gani."

Cikin b'acin rai ya fita daga d'akin yana mita.
*WANNE DADY?*


Alhaji Habibu Audu Harisu Wanda aka fi sani da (H.A.H) hamshak'in mai kud'i ne na azo a gani , haifaffen garin Kano ne a unguwar janbulo , su hud'u iyayen su suka Haifa , duk inda kaje a garin Kano indai kace Family H.A.H babu Wanda bai San su ba Dan yayi suna sosai ta b'angaren kasuwan ci.

Alhaji Habibu yana da mata d'aya Hajiya Mardiya wato Momy auren saurayi da budurwa , suna mutuk'ar k'aunar junan su sosai , Momy ta kasance mace mai tausayi da son taimakon jama'a hakan yasa kowa a dangin su Dady yake son Momy , Momy ita kad'ai ce mace a wajan iyayen ta sai yayyata maza guda uku da k'anne maza biyu , tunda tayi aure take son haihuwar y'a mace da Allah ya zuba mata son y'ay'a mata .

Shekarar d'aya da aure ta haifo kyakykyawan d'inta Suhail , Suhail kyakykyawa ne sai da ba fari bane ya d'auko fatar mahaifiyar sa da Momy ba fara bace amma kuma baza'a sata a layin bak'ake ba amma Dady ya fita fari sosai.

Bayan haihuwar Suhail da shekara uku ta haifo Shukra , Shukra taci sunan mahaifiyar Dady wato Rashida , sabida farin cikin da Momy tayi na haifar y'a mace yasa ta saka mata suna Shukra.


Kulawa sosai yaran suke samu daga wajan iyayen su da kuma kakannin su , Shukra ta taso tana da girma jiki amma hakan yasa da kad'an Suhail ya d'ara ta.


Tun daga lokacin haihuwa ta tsaya musu cak , ko b'atan wata Momy bata k'ara yi ba .


Tun tasowar Suhail Da Shukra sosai basa so suga wani ya rab'i mahaifan su musamman ma Suhail Dan yafi Shukra rashin son ganin mutane.

Suhail yanzu yana da shekara goma sha bakwai Shukra kuma sha biyar , Suhail yana B.U.K yana karantar Agricultural inda Shukra tayi candy yanzu result take jira .


*Wannan kenan.*Bayan gari yayi haske da wajan k'arfe tara na safe Momy ta kalli Shukra da take break fast tace "Shukra in kin gama kiji ki kira min Suhail lokacin zuwa interview d'in Fateemah ya kusa."

+

A ciki ta amsa ta cigaba da cin abincin ta , ganin Momy tana zaune a wajan yasa ta mik'e rai a b'ace ta nufi d'akin Suhail.

A kwance ta ganshi sai sharar bacci yake da alama bashi da niyar tashi yanzu , murmushi tayi tace "yauwa haka nake so gwara da Allah yasa bacci yake yanzu zama na zanyi bazan koma ba in ba haka ba ina komawa Momy sai tace ina yake."

Parlourn sa ta koma ta zauna ta cigaba da danna waya .


Momy kuwa tana can ta saka y'ar aikin gidan shirya Fateemah ita kuma tana d'aki tana gyara kaya , kallon agogo tayi taga minti talatin kenan da Aiken Shukra amma babu ita babu alamar ta .


Tsaki ta mik'e ta nufi part d'in Suhail , tana shiga ta ganta zaune tana charting tana dariya , cikin tsawa Momy tace "Aiken da nayi miki kenan!?".

Cikin firgicewa ta mik'e tana Neman wajan b'uya dan tasan Abu ne mai sauki Momy ta mare ta , Momy tace " Ba magana nake miki ba kin tsaya kina zare min ido?".

Cikin rawar murya tace "Wallahi... Momy Yah Suhail d'in ne yake bacci shine ban tashe ba dan yace in yana bacci kar na kuma tashin sa."

"Ki cigaba da abinda kike yi Shukra Tara ki kawai nake Wallahi , ki guji had'uwar mu dake " tana gama fad'ar hakan ta shiga bedroom d'in Suhail.


A zaune ta ganshi a kan Kujerar mirror yana shafa mai da alama daga wanka ya fito , ganin Momy yasa ya mik'e yace "Momy na lafiya na ga ranki a b'ace?".

" Ban sani ba , haka muka yi da kai? Ba ce maka nayi zaka kai Fateemah interview ba k'arfe goma , Yanzu k'arfe nawa ?" Ta fad'a cikin fad'a.

Kallan agogon d'akin yayi ya ga k'arfe 9:36 kallan Momy  yayi yace "kiyi Hak'uri zan kaita kafin goman tayi".

Tsaki tayi tace " kace ma baza ka kaita ba mana , sha-shan banza kawai " tana gama fad'ar hakan ta juya ta fita daga d'akin.

Cikin b'acin Shukra ta kalle shi tace "kaji ko akan yarinyar nan Momy tace mana sha-sha-shai Wallahi bro in ba muyi da gaske muna gani zata kwace mana iyaye zaman gidan nan ya gagare mu."


Kallan ta yayi ya had'e rai yace "zamu yi maganin ta amma ba yanzu ba sabida in muka yi mata wani Abu yanzu Momy tasan mune , kin ishe ni da magana fita ki ban waje."


Ba musu ta juya ta fita daga d'akin.


Fateemah kuwa tana zaune a parlour kusa da Momy Dan ita ta gama shiryawa Suhail kawai take jira , Bai wani d'au lokaci ba ya shigo ya kalli Fateemah yayi murmushi da shi kad'ai yasan ma'anar sa yace "little Sis har an shirya ? To maza taso muje kar ki makara ko? " cikin turanci yake mata magana hakan yasa tayi murmushi ita ta mik'e d'in kamar yadda yace.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi Momy tayi tace "Ko kaifa Suhail maza kuje to."


Rik'e hannun ta yayi suka fita daga parlourn , mota suka shiga suka d'au hanyar Makaranta.

Tunda suka shiga motar ya had'e rai yana faman banka mata harara , ita kuwa Fateemah bata ma San abinda yake ba kallon taga kawai take.

Tsaki yayi Wanda yasa Fateemah juyowa ta kalle shi , zare mata ido yayi yace "to mayya cinye ni zakiyi kin kafe ni da Wannan idon naki mai kama Dana mage."


Saurin juyar da kanta tayi idon ta ya cicciko da k'wallah , tsayar da motar yayi ya kalle ta yace "Dan uwar uban ki mai na miki da zaki min kuka eye? Shegiya mai ruwan aljanu wallahi badan Momy da Dady ba saina b'alla ki."

Goge hawayen ta tayi tana ajiyar zuciya , tsaki yayi yaja motar suka cigaba da tafiya.


Goma saura minti uku motar Suhail ta shiga cikin makarantar , cike da kasaita ya fito daga motar yana wani shan k'amshi, juyawa yayi ya kalli Fateemah da ke zaune a cikin motar tana jin tsoron fitowa yayi mata fad'a , yace "Au baza ki fito ba? Shikenan cigaba da zama ke kika huta."

Duk da bata gane mai yake nufi sosai ba ta bud'e motar ta fito bai kula taba ya nufi cikin makarantar , ganin ya tafi yasa itama ta bishi a baya .

Tare suka shiga ajin Interview d'in tana shiga aka kulle k'ofa lokaci yayi , babu b'ata lokaci aka fara gabatar da interview har aka zo kan Faty , Sosai take amsa duk abinda aka tambaye ta kowa mamakin basirar ta yake , cike da burgewa baturen yake kallon yadda take koro bayani kamar a Brain d'inta akayi abun .

Babu Wanda bata burge ba a wajan banda Suhail da yake ta shan k'amshi yana jin haushin ta , bayan an gama akace su zauna zuwa one hour za'a kafe result.

Mota ya koma ya zauna cike da takaici.


Ita kuwa Fateemah tana cikin class d'in ko wanne Malami sai nan-nan yake da ita.

Bayan an kafe result d'in wani Malami yaja hannun ta suka je wajan , a hankali yake duba sunan ta har ya gano sunan ta a Y'an primary 5 , cikin burgewa ya kalle ta cikin turanci yake fad'a mata Dan gabad'ayan su sun d'auka baturiya ce .


Sosai Fateemah tayi murna tana jin dad'i a ranta , office d'in principal aka nufa aka bata uniform da id card da littafai sannan malamin ya rako ta mota .

Ya kalli Suhail fuskar da murmushi yace "k'anwar ka akwai basira sosai yanzu haka taci interview d'in ranar Monday zata fara zuwa makaranta."


Yak'e Suhail yayi yace "Haka ake so, little Sis shiga mota mu tafi."

Shiga motar tayi hannun ta rik'e da kayan ta .


Bai kula ta har suka isa gida , cike da farin ciki take fad'awa Momy yadda akayi , sosai Momy tayi murna a take aka kira Tela aka bashi dinkin uniform.

Suhail yana zaune yana kallan su zuciyar sa kamar ta fashe , Momy ta kalle shi tace "yauwa Suhail yanzu abinda ya gare shine gobe zaka kaita islamiyya kafin asoma mata driver ."

Yak'e yayi yace "to Momy Allah ya kaimu".

Bayan wasu kwanaki.

Fateemah ta fara zuwa makaranta kuma tana fahimtar duk abinda ake musu, a islamiyya ma haka tana gane komai Dan yanzu basai ance taje tayi sallah ba da kanta take zuwa tayi .


Zuwa yanzu Shukra da Suhail sun canja salo in Momy da Dady suna nan kamar su cinye Fateemah sabida so amma in a bayan idon su ne Zane ta suke babu kamar ma Suhail.

Allah sarki Fateemah in sun Zane ta tasha kukan ta ta mik'e ta koma ciki Dan ba yarinya bace mai surutu, kullum wajan kwanciyar ta shine kan carpet in kuma bata kwanta ba sai dai tasan inda zata kwana .

Ko assignment aka bata bata zuwa wajan su wajan Momy take zuwa ta koya mata .

Bayan an tashi daga makaranta tana zaune a parlour Suhail ya shigo , cikin sauri ta mik'e zata bar wajan ya daka mata tsawa yace " dawo ki zauna dodo ni da zaki gudu?".

Jikin ta banda rawa babu abinda yake gashi Momy bata nan ta fita , bata yi aune ba taji d'auke ta da Mari tsabar gigicewa ba tasan lokacin data rik'e shi tana kuka ba .

Hankad'e ta yayi kanta ya bugu da kujera ta saki wata k'ara mai ban tausayi , gashin kanta ya damk'o yace "gobe ma in kika ganni ki kuma guduwa " yana fad'ar hakan ya cillar da ita ya fita daga parlourn.

"Bayarabiya kina ina ?" Shukra take kwalla mata kira .


Cikin kuka ta mik'e kanta na juyawa Dan tasan sunan da take kiran ta dashi kenan in Momy bata nan , ganin tana kuka yasa Shukra sakin dariya tace "to makira uban me akayi miki ? Koda yake bai dame ni ba maza kije ki Wanke min kayana a toilet."

Ba musu ta juya ta shiga d'akin band'akin ta shiga ta shiga anan tayi tozali da bra dasu pant da alama su zata Wanke.

Bata b'ata lokaci ba ta fara yin jik'a-jik'ar ta Dan babu abinda ta iya , kumfa sosai ta had'a ta dinga d'iba tana wasa da ita tana faman dariya.

"Abinda na saki kenan?" Shukra ta fad'a cikin tsawa. "

Rawar jiki Fateemah ta fara tana Dan jujjuya kayan , kwafa Shukra tayi ta fita daga toilet d'in , parlour ta koma ta bud'e fridge ta d'auko ruwa mai sanyin gaske ta nufi toilet d'in.

Fateemah tana tsugune a toilet bata yi aune ba taji saukar ruwan sanyi a jikin ta , wata k'ara ta saki gashi ranar ana bala'in sanyi , sai da ta juye mata ruwan kaf sannan ta jayo ta suka dawo d'akin tace "gobe ma Dan uban ki kya kuma yin wasa in na saki aiki."

Ita dai Fateemah banda rawar sanyi babu abinda take gashi ta ware Ac a d'akin , tsaki Shukra tayi ta koma kan gado ta zauna tana danna laptop.


Kusan minti uku da yin hakan taji shiru ko numfashin Fateemah ta daina ji , d'ago kai tayi ta ganta a kwance a k'asa kamar matatciya .


Da sauri ta diro daga kan gado tana fad'in "shegiya makira daga watsa miki ruwan sanyi dai ki wani sume ? To Wallahi wani zan k'ara miki yanzu" ta fad'a tana niyar bud'e fridge d'in d'akin.


"Wallahi kika watsa mata ruwan nan sai na yi miki dukan tsiya" Suhail ya fad'a yana shigowa shida Momy da Dady.

Cike da tsoro ta juyo tana kallon Suhail da yake banka mata harara , Momy bata kula taba sai wajan Fateemah da ta nufa ita da Dady , babu alamun numfashi a jikin Fateemah cikin sauri Momy ta d'auke ta suka fita dan tasan Asthma d'inta ne ya tashi.


Suna fita Suhail ya kalli Shukra yayi murmushi yace "matsoraciya kin yi min dai-dai amma fa zaki ci uban ki wajan su Dady yanzu ma Dan hankalin su baya wajan ki ne, ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana fita daga d'akin.

Shiru Shukra tayi gaban ta na fad'uwa amma wani b'angare na zuciyar ta mamakin Suhail take lallai ya cika cikakken Makiri ji yadda ya wani b'ata rai a gaban su Dady amma suna fita ya saki murmushi yadda cewa ta burge shi, a fili tace "dole nima na hau kan Wannan hanyar ta Yaya Suhail."


Su Dady kuwa kuwa basu huce ko ina ba sai wani private hospital dake kusa dasu , cikin gaggawa aka amshi Fateemah aka fara duba ta .

+

Su Momy suna zaune suna kallon yadda numfashin ta ya fara dawowa a hankali , kallon su Dr yace "A Gaskiya Asthma tayiwa yarinyar nan mugun kamu bai kamata Ku dinga bata aikin ruwa ba da har zata dinga jik'a jikin ta haka , badan kunyi saurin kawo ta asibiti bama da bamu San abinda abinda zai faru ba , ga magani nan da inyeler an rubuta mata amma gaskiya in bakuyi da gaske ba wajan hana ta aiki da ruwan sanyi da shiga k'ura ba komai zai iya faruwa, zuwa nan da anjima zata farka" yana gama   fad'ar hakan ya fita daga d'akin.


Babu Wanda yayi magana tsakanin Dady sa Momy kowa da abinda yake sak'awa a ransa ,bayan Fateemah ta farka aka basu sallama suka tawo gida.

Suna shiga parlour lokacin Shukra tana zaune tana fargabar dawowar su taji saukar lafiyayyen mari a fuskar ta , kafin ta dawo daga duniyar data shiga taji an k'ara mata wani.

Iya rud'ewa Shukra ta rud'e sai ihu take Dan tunda take da Momy bata tab'a dukan taba sai yau , cikin b'acin rai Momy tace "So kike ki kashe ta ko? Da tsabar mugunta zaki samu yarinya k'arama mai d'auke da Wannan cutar ki zuba mata ruwan sanyi sabida ba ke kika haife ta ba ko? To bara kiji kinyi na farko kin na k'arshe Wallahi tallahi in kika kuma saina sab'a miki kamamni stupid girl" Momy ta ja hannun Fateemah suka shiga d'aki.

Zama Shukra tayi akan kujera tana kuka kamar ranta zai fita zuciyar ta cike da tsanar Fateemah dan yanzu ji take ko wuk'a aka bata sai ta iya kashe Fateemah.


A nan Suhail yazo ya same ta tana kuka ko bai tambaya ba yasan abinda akayi mata, nan take shima yaji duk duniya babu wacce ya tsana sama da Faty, kwantar da kanta yayi a kafad'ar sa yace "Sorry sister ki kwantar sa hankalin zamu samo hanyar da zamu Fitar da yarinyar nan daga cikin gidan nan amma fa ba yanzu ba zamu bata wasu y'an lokuta yadda su Dady basa su b'ata ganewa cewa mu muka aikata hakan ba, ki yi shiru kinji nasan abinda zanyi."

Share hawayen ta tayi tace "na amince da shawarar ka Yaya." Murmushi yayi mai sauti mai kuma cewa komai ba ya mik'e ya fita daga parlourn.

Shukra kuwa d'akin Momy ta nufa a hankali ta shiga d'akin tana tsoron k'arasawa ciki, "In baza ki shigo ba ki fice min daga d'aki" Momy ta fad'a tana kauda kai gefe.

A hankali ta k'arasa ciki ta durk'usa tace "Dan girman Allah Momy kiyi Hak'uri insha Allah hakan bazai kuma faruwa ba daga yau na d'auki Fateemah kamar k'anwa ta kiyi Hak'uri ki yafe min."


Sosai ta bawa Momy tausayi Momy tayi murmushi tace "haka nake so ai Shukra bawai na fison Fateemah daku bane A'a kawai ina la'akari da bata da kowa sai mu shiyasa nake mutuk'ar tausayin ta, babu komai na yafe miki Shukra."

Murmushi Shukra tayi ta mik'e ta fice daga d'akin zuciyar ta cike da haushin Fateemah.*BAYAN SHEKARA BIYU.*

"Nifa Wallahi Bro na k'agu ka dawo kodan muyi maganin wannan aljanar" Shukra ta fad'a tana rik'e da waya a hannun ta.

A can b'angaren Suhail yace "Kar ki damu Shukra karatu ya tsayar dani a k'asar nan amma da tuni na mu kori shegiya ni kaina zaman America ya ishe ni ji nake kamar nayi tsuntsuwa na dawo shekara d'aya har da watanni ai da gajiya."

STORY CONTINUES BELOW

"Ai yanzu soyayyar dasu Momy suke mata ya ninka na da sabida yarinyar akwai d'an banzar k'ok'ari duk term ita take d'aukar ta d'aya islamiyya da boko shiyasa Momy suke dad'a sonta kamar y'ar su."

Suhail yace "Kar ki damu na kusa dawowa ai nasan abinda zanyi, ke ko ban dawo ba zan shirya miki yadda komai zai faru amma ba Yanzu sai nan gaba."

"Shukra tace " to Shikenan sai anjima ni zan tafi makaranta ina da lecture 2 to 4."

Suhail yace "yayi kyau ayi karatun lawyer dakyau banda kula samari".


Dariya tayi ta kashe wayar .


Zaune take a harabar makarantar kowa ya tafi ita kad'ai ce a zaune tana jiran driver.


Wani saurayi d'an kimanin shekara goma sha tara  yazo wucewa yana sauri da alama akwai inda yake son zuwa, wallet d'insa ce ta fad'o daga aljihun rigar sa amma tsabar sauri bai kula ba ya cigaba da tafiya.


Ganin har ya shiga cikin  makarantar yasa Fateemah ta mik'e ta d'auki jakar ta koma ta zauna tana jiran fitowar sa.

Babu jimawa ya fito yana dube-dube da alama wallet d'in yake nema, ganin babu yasa ya dafe kai cikin muryar sa mai dad'in sauraro yace "Oh my God yanzu ina na yar da wannan wallet d'in?".

" Wannan kake nema?" Fateemah ta fad'a tana nuna masa Wallet d'in.

Murmushi yayi na nuna farin ciki har dimple d'insa suka lob'a, da sauri ya k'araso inda Fateemah take ta ya tsuguna a gaban ta yace "ita nake nema y'ar beauty a ina kika ganta.?"

Mik'a masa wallet d'in tayi tace "D'azu kana sauri baka sani ba ta fad'o daga aljihun ka shine na d'auka na ajjiye maka."

Hannu yasa a ajihu yaji aljihun a b'ule, d'ago kai yayi ya kalle ta yace "Gaskiya Nagode sosai k'anwata, meye sunan ki.?"


Murmushi itama tayi tace "Sunana Fateemah amma ana cemin Fatyn Momy."

Murmushi yayi mai sauti yace "Nice name Fateemah au sorry Fatyn Momy, me kike yi anan baki tafi gida ba har yanzu.?"

Shagwab'e fuska tayi tace "Har Yanzu ba'a zo d'auka ta ba kuma yunwa nake ji."

"Ayya little Sis zo muje na sauke ki" ya fad'a yana rik'e mata hannu.

K'in tafiya tayi ya juyo yana kallon ta yace "kizo mu tafi mana."

K'ok'arin kwace hannun tayi ta b'ata fuska tace "A islamiyyar mu ance babu kyau namiji inba ba yayan ka ba ya rik'e maka hannu kuma Momy ta hanani."


Ba k'aramin burge shi tayi ba ya koma ya tsuguna kusa da ita yace "Haka ne mana babu kyau amma kema ai kince banda Yayan ki kuma kinga ni yayan ki ko ba shi bane.?"

Murmushi tayi har ya wushiyar ta baiyana tace "Yaya nane mana."


Yace "Good zo muje na sauke ki sai na shiga da kaina nacewa Momyn ni na kawo ki, a wacce unguwa kike.?"

"State road" ta bashi amsa tana wasa da jakar ta.

Yace " oya muje to" bata yi musu ba ta bishi a baya suka tafi.

Mota suka shiga suna tafiya tace "Yaya nah kana da kyau."

Lumshe ido yayi sabida a rayuwar sa yana so a kira shi da Yaya yana son k'anne amma Allah bai bashi ba, Yace "tab ai kin fini kyau sosai kin ganni kuwa?."

B'ata fuska tayi tace "ni bani da kyau bayan kullum sai Aunty Shukra tace min mai kyaun aljanu."

Dariya yayi yace " Ah ah wasa take min amma kina da kyau sosai."

Murmushi tayi bata kuma magana ba har suka k'arasa inda tayi masa kwatance.

Tare suka fito daga motar ka kalle shi tace "Yaya nah mu shiga ka fad'awa Momyn in ba haka ba fad'a zata yi min."

Bai musa ba yabi bayan ta suka shiga cikin gidan.


Da gudu ta shiga parlour ta fad'a kan Momy tana fad'in "Momy na na dawo."


Murmushi tayi tace "Fatyn Momy yau kin dad'e baki dawo ba lafiya.?"


Nan ta bawa Momy labarin ba'a zo d'aukar ta ba, Momy tace "To yanzu ame kika dawo?".

Bata bata amsa ba sai d'aga labule da tayi tana fad'in " Yaya ka shigo mana."


Da sallama ya shiga ya zauna a kan carpet ya gaida Momy cikin girmamawa, cikin fara'a Momy ta amsa tana yi masa godiya.

Murmushi yayi yace "Ai babu komai k'anwa tace" ya fad'a yana kallon Fateemah.


Murmushi tayi tace "Momy sunan sa Yaya fa."


Dariya Momy tayi tace "to Yayan Fateemah."

"Momy ina kika ajjiye jakar ban......" Maganar ta mak'ale sakamakon arba da kyakykyawan saurayi da tayi a zaune a parlourn su.

Momy ta juya ta kalle ta tace "Yauwa Shukra kawo masa ruwa bara na d'auko waya ta nasan anata kira" ta fad'a tana mik'ewa ta bar wajan.

Zuba masa ido tayi tace "Sannu da zuwa."


Ganin yadda take kallon sa yasa ya had'e rai Yace "sannu."


Ruwa ta kawo masa da lemo ta zauna a wajan tana satar kallon sa, kallon Fateemah tayi ta harare ta tace "au mayya an dawo" ta fad'a Dan ta burge Shi.

Sunkuyar da Kai tayi tana shirin yin kuka, Cikin b'acin rai ya d'ago tabbas yaso ya fahimci wani Abu tsakanin Fateemah da Shukra tunda ta fito take hararar ta, tsaki yayi ya kalli Fateemah yace "Sweet k'anwa zo ni zan tafi zan dawo gobe mu gaisa ki cewa Momy na tafi."

Murmushi tayi ta d'aga masa kai.


Shima murmushi yayi mata ya juya ya fita daga parlourn.


Cike da jin haushi Shukra ta mik'e ta bar wajan zuciyar ta cike da kewar saurayin.


D'akin Momy Fateemah ta wuce taje ta fad'a mata Sannan ta fara cire uniform.

Tunda ya bar gidan yake faman tunanin Fateemah yana murmushi , tsaki na kusa dashi yayi yace "Wai kai meye yake damun Kane? Kamar Wanda ya samu cutar murmushi tun da ka shigo kake aikin murmushi kodai kayi kamu ne.?"

+

Ajiyar zuciya yayi yace "wata kyakykyawar yarinya na had'u da ita har gidan su ma na kaita."

Dariya yayi yace "Kace ka fad'a tarkon sonta."


Tsaki yayi yace "kaifa baka da hankali da baka da magana sai ta soyayya to Wannan yarinya ce kuma ni a k'anwa na d'auke ta , baza ta wuce Shekaru takwas a duniya ba amma kake wannan zancen."

Dariya abokin nasa yayi yace "Lallai kaga mai k'anwa daga k'anwar za'a zarce munga irin Ku yafi sau dubu."


"Ka gane Amir yarinyar kamar tana fuskantar matsala daga wajan wata yarinya a gida Dan baka irin kallon da take mata ba."


Amir yace "Kaga Malam ni ba wannan ya same ni ba Fitar ka Mamy ta kira tace in ka dawo ka kira ta."

Wayar ya d'auka ya danna number Mamy ya kara a kunne, daga can b'angaren aka ce "ina ka shiga ne tun d'azu nake kiran ka?."

Yace "na d'an fita ne Wallahi, ina fatan dai lafiya ko Mamy na.?"

"Lafiya lau, yaushe zaka dawo Abuja ne? kaga tafiyar mu England tana matsowa kuma fa sabida kai zamuyi tafiyar nan."

"Mamy ba wannan bara na baki wani labari, yau na had'u da wata yarinya kyakykyawar gaske gata da kirki wallet d'ina na yar da nazo ina nema ta bani kuma wallahi yarinya ce k'arama."

Dariya Mamy tayi tace "Kodai anyo mana sirika ne?".

Murmushi yayi yace " haba Mamy kwata-kwata nawa nake da zanyi budurwa yanzu? Itama fa yarinya ce Dan baza ta wuce 8yrs ba amma tsakani da Allah ta shiga raina sosai."

Mamy tace "kaga kenan ka samu k'anwa a Kano."

"Wallahi kuwa Mamy kuma Yaya take cemin baki ji yadda take burge ni ba."

Mamy tace "to mai k'anwa sai anjima na daka ta taka makai gobe muna wannan hirar sai anjima, ka kuma yi k'ok'ari ka dawo ka koma England ka cigaba da karatun ka ziyarar ta isa haka."

Yace "To Mamy na zan dawo insha Allah."


Suka yi sallama ya kashe wayar.


Bai ajjiye wayar ba ya danna wata number ya kuma kira.

"Assalamu Alaikum".


Daga can b'angaren aka amsa sannan yace " Umma an huni lafiya? ".


" Lafiya lau ya Kano? ".

" Lafiya lau Umma, na kusa dawowa ma."

"To masha Allah Allah ya dawo da kai lafiya, ina fatan babu matsala ko?".

STORY CONTINUES BELOW

" babu komai Umma daman kira nayi mu gaisa" sallama sukayi ya kashe wayar .

Kallon wayar yayi yace "Hajiya Umma kenan mai jin kunyar d'anta."

Dariya Amir yayi yace "Gaskiya dai Umma bata sakewa da kai kamar ba ita ta haife kaba, koda yake haka Fulani suke da kunyar d'an fari."

Tab'e baki yayi yace "to ko meye abin kunyar oho, kofa waje naje indai Umma na wajan ina zama zata mik'e ta bar wajan shiyasa yawancin mutane suke cewa Mamy ce ta haife ni, ai naji dad'in aurar Mamy da Abba yayi gashi yanzu na samu uwa mai saurare na bata jin kunya ta."

Dariya Amir yayi bai kuma cewa komai ba.


BAYAN KWANA BIYU.

Tunda saurayin nan ya had'u da Fateemah bai tab'a yin minti d'aya ba ba tare da ya tuno taba gashi bashi da lafiya cikin kwana biyun balle yaje ya dubo ta, haka yake huni kullum cikin tunanin Fateemah yana yi yana murmushi.


Shukra kuwa cikin kwanakin ta tabbatar da son D'an saurayi take, kullum cikin tunanin sa take gashi bata San inda zata same shi ba.

A haka Momy ta fito ta same ta zaune ta jinginar da kanta a jikin kujera, tsaki Momy tayi tace "Wai ke meye yake damun ki cikin kwanakin nan?".

D'ago kai tayi ta kalli Momy tace " Babu komai Momy kawai kaina ke min ciwo. "

"Kullum maganar kenan kanki na ciwo, zan d'an fita ba jimawa zanyi ba zan dawo ki tabbatar kafin na dawo kin tanadi abinda zaki gaya min" ta fad'ar hakan ta fita daga parlourn.

Ajiyar zuciya Shukra tayi a fili tace "Na shiga uku na Rashida meyasa so zaiyi min haka? Ban San mutum ba ban San daga ina yake ba amma kawai zuciya ta ta kamu da sonsa, Gashi kwata-kwata bazai wuce shekarun Yaya Suhail ba, Ya Allah na rok'e ka ka kawo min mafita cikin gaggawa."

Tama rife baki Fateemah ta shigo parlourn tana cire jakar bayan ta, wani banzan kallo Shukra ta aika mata dashi cikin sauri Fateemah ta d'auki jakar ta ta bar wajan.

Kwafa tayi tace "shegiya duk akan ki Wannan abubuwan suke faruwa amma zanyi maganin ki nan kusa wallahi."

Bayan kamar minti goma Shukra ta mik'e ta nufi d'akin Momy Dan tasan yanzu haka Fateemah tana can, tana shiga ta ganta a zaune tayi shiru, cikin tsawa tace "Ke zonan!".

Cikin rawar jiki Fateemah ta mik'e ta k'araso wajan ta, kud'i ta d'auko ta mik'a mata tace " maza kije wannan provision d'in da yake baya kice a baki Chocolate kuma wallahi kika dad'e saina b'alla ki kuma kika sake kika yar da kud'in nan sai na lahira ya fiki jin dad'i."

Ba musu ta karb'i kud'in ta fito daga d'akin, bakin gate ta fito mai gadi yace "A'a Fatyn Momy ina zuwa haka?".

Tace " Aunty Shukra ce ta aike ni tace na siyo mata chocolate a kantin baya."

"Ah Ah baza ki fita ba kawo naje na siyo mata" ya fad'a yana k'ok'arin karb'ar kud'in hannun ta.

"Wallahi ka sake ka karb'i kud'in nan a bakin aikin ka" Shukra ta fad'a daga jikin tagar parlourn.

Bai kuma cewa komai ba ya Bud'ewa Fateemah k'ofa ta fita daga gidan.

Kallon k'ofar gidan tayi dan tunda take bata tab'a fitowa ita kad'ai ba, rasa inda zata bi tayi sai kawai ta fara tsakani-tsakani, canke-canken ta ya nuna mata tayi hannun dama aikuwa babu musu tabi hanyar tana d'an tsalle-tsalle.

Y'ar tafiya kad'an ta tsaya tana kallon hanya itadai bata ga wani katin hanyar ba, duba hannun ta tayi taga babu kud'i, bata San lokacin da ta fara kuka ba da gudu ta koma baya tana duba hanya ko zata ga kud'in amma babu 1k babu alamar ta.

Tsugunawa tayi a wajena tana kuka sosai Dan tasan yau sai Shukra ta kashe ta.

Kusan ten min ta d'auka a wajan kafin ta yanke shawarar mik'ewa ta tafi gida, tafiya take tana goge fuska da hijjabin ta.

"K'anwa ta" taji an fad'a daga bayan ta.

Ko bata ga fuska ba ta gane muryar waye, da sauri ta juyo ta ganshi tsaye jikin mota yana murmushi.

Da gudu ta k'arasa wajan sa ta rungume shi tare da fashewa da kuka, d'ago ta yayi daga jikin sa yace "Subahanallah Beauty Lafiya kake kuka haka?".

" Aunty Shukra ce ta aike ni na siyo mata chocolate shine na yar da kud'in kuma tace in na yar mata da Kud'i sai na lahira ya fini jin dad'i. "

Tsaki yayi cike da tsanar Shukra yace "Nawa ne kud'in?".

Tace " Dubu d'aya ce."

"Ok muje na baki kud'in ki kai mata kice kinje babu chocolate d'in."

Mak'ale kafad'a tayi tace "Nidai A'a kawai ka bani na siyo in ba haka ba Zane ni zata yi ko na bata ta watsa min ruwan sanyi."

Cike da tausayin ta yace "Kar ki damu sai mu shiga tare ai in dani baza ta dake ki ba."

Cikin farin ciki ta amsa, mota suka shiga suka k'arasa gidan.


Kud'in ya bata sannan yace ta fara shiga zai biyo ta, cikin fad'uwar gaba Fateemah ta shiga parlourn.


Tana ganin ta ta mik'a mata hannu tace "Ina chocolate d'in?".

Cikin rawar murya tace " Aunty Shukra kud'in sun fad'i kiyi Hak'uri Dan Allah kar ki dake..... " bata k'arasa ba ta d'auke ta da Mari har sai da tayi baya ta fad'i akan carpet.

Bata Hak'ura ba ta mik'ar da ita ta k'ara kifa mata Mari tare da d'aka mata duka a baya Wanda bata San lokacin data k'wallah k'ara mai k'arfin gaske ba.

"Shegiya mai halin shaid'anu Dan rashin mutunci na aike ki kice min kud'in sun fad'i, to wallahi yau sai na ci uban ki shegiya Bayarabiya."

Fincike Fateemah taji anyi tare da d'auke ta da mari itama, d'ago kai tayi Dan ita duk a tunanin ta Momy ce amma sai taga sab'anin hakan.


Duk zafin Marin da taji tana yin tozali dashi taji gabad'aya wani dad'i ya mamaye ta kawai ta zuba masa ido tana kallon sa.

Kud'in ya bata sannan yace ta fara shiga zai biyo ta, cikin fad'uwar gaba Fateemah ta shiga parlourn.


Tana ganin ta ta mik'a mata hannu tace "Ina chocolate d'in?".


Cikin rawar murya tace " Aunty Shukra kud'in sun fad'i kiyi Hak'uri Dan Allah kar ki dake..... " bata k'arasa ba ta d'auke ta da Mari har sai da tayi baya ta fad'i akan carpet.


Tsabar Firgicewa ta ma manta an bata kud'in da zata bata.


Bata Hak'ura ba ta mik'ar da ita ta k'ara kifa mata Mari tare da d'aka mata duka a baya Wanda bata San lokacin data k'wallah k'ara mai k'arfin gaske ba.

"Shegiya mai halin shaid'anu Dan rashin mutunci na aike ki kice min kud'in sun fad'i, to wallahi yau sai na ci uban ki shegiya Bayarabiya."

Fincike Fateemah taji anyi tare da d'auke ta da mari itama, d'ago kai tayi Dan ita duk a tunanin ta Momy ce amma sai taga sab'anin hakan.


Duk zafin Marin da taji tana yin tozali dashi taji gabad'aya wani dad'i ya mamaye ta kawai ta zuba masa ido tana kallon sa.

Zaiyi magana kenan Momy dake tsaye a bakin k'ofa tace "Kayi min dai-dai Wallahi daka sani ka k'ara mata, sha-sha-sha Mara hankali."+


Nan ya bawa Momy labarin duk abinda ya faru, Momy ta kalli Fateemah da take ta faman kuka tace "Nagode kaji Allah yayi maka albarka, ke kuma zakiga abinda zan miki."


Hannun Fateemah ta rik'e suka shiga ciki, kallon Shukra yayi yace "Allah ya baki ikon k'ara dukan ta a gaba na wallahi saina nuna miki baki da wayo, kamar ba k'anwar ki ba ki dinga yi mata Wannan dukan? Kodan kinga ta fiki kyau ta fiki hankali, kar kiga ni ba d'an uwan Ku bane Wallahi akan Fateemah babu abinda bazan iya yi ba mtsw" yana gama fad'ar hakan ya watsa mata harara ya fita daga gidan.


Maimakon taji haushin sa sai wani burge ta da taji ya k'ara yi, lumshe ido tayi tare da shafo inda ya mare tana jin wani farin ciki a ranta.

Had'e rai tayi tace "Wannan Fateemah ita zata hanani rawar gaban hantsi tunda naga yafi sonta dani to wallahi bata ta sab'u dole Yaya Suhail yasan yadda zamuyi da ita" ta fad'a tana mik'ewa fuuu ta shiga d'aki.


Washe gari an tashi daga islamiyya Fateemah tana zaune tana jiran a zo a d'auke ta tana d'agowa suka had'a ido da Yayan ta yana faman yi mata murmushi.


Da gudu ta k'arasa wajan sa tace "Yaya na sannu da zuwa ina wuni."

"Lafiya lau k'anwa ta, zo mu tafi tunda ba'a zo d'aukar ki ba" ba musu ta bishi suka shiga mota.

Suna tafiya suna hira har suka zo k'ofar gidan, zata bud'e k'ofar yace "tsaya Beauty na ina so zan tambaye ki wani Abu amma fi ki fad'a min tsakanin ki da Allah bana son k'arya."


Gyara zama tayi tace "Toh Yaya ina jinka."


"Wannan matar sa ta dake jiya Yayar d'aya uwa d'aya uba d'aya?".

Sunkuyar da kai tayi ta fara hawaye, yace " Subahanallah beauty abinda na tambaye kine ya b'ata miki rai? To shikenan goge hawayen ki basai kin fad'a min ba."

Cikin kuka tace "bafa su Momy ne suka haifi ba kawai dai sun d'auke nine kamar y'ar su, shekara biyu kenan da d'auka ta."

Cike da mamaki ya kalle ta yace "ban gane mai kike nufi?".


Bata b'oye masa komai ba ta bashi labarin duk abinda ya faru, ta d'ora da cewa " Haka su Aunty Shukra suke wahalar dani ita da Yaya Suhail ba tare da sanin Momy da Dady ba dan su suna sona Sosai."

Ba k'aramin tausayin ta ji ba zuba mata ido kawai yayi yana kallon ta zuciyar sa nayi masa zafi Sosai yace "Shikenan ki kwantar da hankalin ki komai ya kusa zuwa k'arshe tunda na shigo rayuwar ki, bazan d'auki a dinga wulak'anta ta ki ba, share hawayen ki ki shiga ciki in gobe zan dawo."


Goge fuskar ta tayi ta fito daga motar tana d'aga masa hannu.


Har ta shige gida yana kallon ta fuskar sa da murmushi, ajiyar zuciya yayi yaja motar ya bar wajan.


Tun daga ranar kullum sai Yazo wajan Fateemah kowa ya saba dashi a gidan hatta Dady yasan shi, shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin sa Fateemah Dan ko abinci bata iya ci indai yayi kwana d'aya baizo ba, ta b'angaren sa shima haka in har bai ganta ba sai yayi zazzab'i, Yayan Fateemah ya gama gano cewar ya fad'a tarkon son Fateemah ba tare da ya sani ba so kuma irin mai k'arfin nan.

B'angaren Shukra kuwa babu ranar da zata b'ullo da koma bata yi tunanin sa ba, gabad'aya ta kori samarin ta sabida shi, shi kuwa ko kallon arzuk'i bata samu daga wajan dan duk duniya babu Wanda ya tsana kamar ta.


Chocolate, biscuit da kayan ciye-ciye kullum sai ya kawo mata, Fateemah yanzu bata da wani damuwa tunda yanzu Shukra ta daina takura mata sosai sabida shi.


Shi kuwa Suhail bashi da burin da ya wuce ya dawo gida su had'a plan d'in da zasu Kore ta, kullum cikin shirya plan suke shida Shukra.

Yau Shukra tayi niyar baiyana wa Yayan Fateemah son da take masa koda kuwa zai kashe ta, shiryawa tayi cikin kaya na alfarma ta zauna jiran zuwan sa.


Yana mota a zaune ya aika aka kira masa Fateemah, babu jimawa ta k'araso ta bud'e motar ta shiga tace "Yaya na sannu da zuwa."


Murmushi yayi yace "Yauwa beauty na ya makaranta?."

"Lafiya lau Yaya na".

Murmushi yayi ya kalle ta yace " Har yanzu baki tab'a tambaya ta Yaya sunana ba."

Y'ar dariya tayi tace "tab ai Momy ta hanani fad'ar sunan manya shiyasa ban tambaye ka kuma a ko ina in na ganka sunan ka Yaya."

Murmushi yayi yace "Ina son ki Faty nah."

Murmushi itama tayi tace "Nima haka Yaya na inason ka."

Zaiyi magana Shukra ta k'araso wajan cikin takun alfarma sai zuba k'amshi take, a saitin tagar inda yake ta tsaya tace "sannu fa".

Tsaki yayi ba tare da ya amsa ba ya cigaba da hira da Fateemah, Yak'e tayi ta kuma cewa " Haba Yayan Fateemah bai kamata ace ina yi maka magana kayi min banza ba kamar baka ji abinda nace, wallahi tun ranar Dana d'ora ido a kanka naji duk duniya babu Wanda nake so sama da kai," tsugunawa tayi tana hawaye ta cigaba da fad'in "in ban aure kaba zan iya rasa raina dan Allah ka daure ka amince dani kaji."

Ajiyar zuciya Yayi yace ...........


Post a Comment for "BANSAN LAIFINA BA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...