AMJAD CHAPTER A

 AMJAD CHAPTER A


Canada,Mu'az resident

      Kid'a ne kawai yake tashi a gidan kai seka d'auka a club kake inba wai ka gane wa idonka ba.

       Amjad! wata mace ta kira bayan data shigo d'akin wanda tana da tabbacin kid'an daga nan yake.

      Saurayin data ke kiran sunan nashi ya juya baya sam ba jinta yake ba se miming wa'kar yake.Takawa tayi ta 'karasa inda yake tayi tapping kafad'arsa da 'karfi.

     Da sauri ya juya tare da yin 'yar 'kara "Aww!"

      "Will you please turn the music off?"

      "Mom am glad you are back"Abinda ya fad'a kenan kafin ya 'karasa ya kashe kid'an.


       " Amjad this is too much ".

      "Mom am just having some fun,it's awesome".

      " Where is Shaheed?"

       "He just left"        "To?"

         "I don't know".

         " What about Zakia?"

          "I guess she is in her room".
  
          " Well, have you eaten?"

         "No".

         " Why? are you not hungry?"

         "Of course I'm I just don't wanna eat"

          "Is something wrong?"

            "No". Ya amsa a taka'ice.

            " I hope so,let me prepare omelette for  you try a little son I don't want see  you starving just like that".

     Seda ya d'an d'age gira tukun yace "Ok".

       "That's my kid".Ta fad'a tare da jan kumatunsa tana murmushi.

      Shima murmushin yayi,daga haka ta fita daga d'akin shikam ya fad'a kan gado tare da d'aukan phone d'insa ya fara tapping.

        D'akinta ta koma tare da rage jacket d'inta da viel d'in data yafa shima ta cire  ta fito kitchen.

       Cikin d'an 'kan'kanin lokaci ta kammala ,dining ta jera sannan ta hau upstairs zuwa d'akin Zakia.

       " Come in"Aka fad'a bayan tayi knocking.

        "Mom so you are back?"

         "And you're here busy chatting"

         "Ohh" Ta fad'a tare da sosa kai tana rife laptop d'in.

        "Have you eaten?"

         "Yes Mom"

          "Ok then we enjoy our omelettes alone"

STORY CONTINUES BELOW

           "Omelettes? that's my favorite you know"

            "I made it for Amjad"

             "Come on Mom Amjad is not a kid you're spoiling him much, Dad is right".Ta fad'a cikin shagwa'ba.

         " Kema?"

          "Nima me?" Ta tambaya cikin rashin 'kwarewar hausa".

         "You're backing your dad"

        "Why not ? He's right"

          "Ok let's go" Ta fad'a tare da tallafo kafad'arta suka sauka 'kasa.

         "Amjad! Omelettes is ready"

          "Ok Mom"Ya amsa daga d'aki.

          "You see"

           "Zakia ?" Mom ta fad'a in between laughter.

            "Ehyi he's almost 26 but yet you're treating him like a 16"

            "What are you two discussing?Suka jiyo muryarsa yana sakkowa daga step.

           " She.."

            "Mom!" Cewar Zakia da 'karfi tana zaro ido signing take mata na tayi shiru.

         "Ok ,I gerrit" Tayi alamar zipping mouth da yatsa.

           "Are you guys hiding something?"Ya tambaya yana kallonsu.

         " No"Suka amsa a tare.

          "Lazy  I hope your hands didn't touch my Omelettes?"

          "What if it those?"Ta tambaya cikeda tsiwa.

          " R.I.P"Ya amsa yana gyara kujerar zama.

           "Really? Let.."

            "Shh! Guys let eat and stop chatting" Mom ta katse su dan yanzu sesu mayar mata da table upside down halinsu neh  kullum se sinyi fad'a shi tsokana ita kuma tsiwa.

       "Yau wani beyi sallah na Asr ba". Zakia ta fad'a bayan sinyi nisa da cin abincin.

          Karaf! Ya dire spoon dake hannunsa ,ya san inde zatai munafinci shine take jagulo hausa dukda kuwa ba 'kwarewa tayi ba amma de ta fishi dan a yanzun ma ba sosai ya fahimci abinda tace ba amma de ya ayyana dashi take.

       " Zakia are you serious? " Mom ta tambaya.

       "Yes Mom" Ta amsa.

        "What did you mean by that?" Ya tambaya fuskarsa a d'aure.

        "Amjad is that true?" Mom ta tambaya yanayin fuskarta ya sauya.

        "What?"
         "You didn't pray Asr" Ta amsa a takaice.

          Yanzu ne ya gano gulmar data fesa mata.A fusace ya mi'ke dama Zakia tasan za'a rina, a guje ta tashi daga kujerar ta fyalle hanyar sitting room dan ba damar hawa bene.Bata san ita kanta inda zata 'boye ba,'kofar fita ta nufa.Mom na kiransa amma ko sauraranta ya'ki yi.

       'Kiris be iske ta ba sega Dad ya shigo,da sauri ta la'be a bayansa.

        "Dad help me!" Ta fad'a da 'karfi.

         Ganin haka yasa Amjad yaci birki se huci yake.

      "Amjad what's going on?" Dad ya tambaya.

STORY CONTINUES BELOW

       Shiru yayi dan bashi da abin cewa yasan idan yaji maganar sallah ne seya santa a gun dad.

      Tana daga baya amma a haka take masa gwalo.

       "She took my ..my diary" Yayi 'karya.

       "Diary?" Waiwayawa yai ya kalli Zakia,da sauri ta saita kanta.

      "Where is it?"

        "In the locker".
        " Give him back ok?"

         Kai ta gida'a alamar toh,daga haka ya wuce ya barsu a gun.

        "I saved you"

         Galla mata harara yayi tukun ya wuce ,tana bin bayansa da gwalo.

       "Honey you're back". Cewar Mom lokacin daya 'karaso ta mi'ke tare da hugging d'insa.

         " Uhm,mey kuke ci haka?"

         "Omelettes" Ta amsa.

         Amjad jin da yaren da dad yayi magana yasa yace "disgusting" ba tare da sun jiyo ba,ko takan omelettes d'in be biba ya haye sama abinsa.

         "Shaheed?" Ya tambaya.

           "He went out am sure he's  on his way back home"

           "I hope so" Ya amsa.

            Spoon ya d'auka kan table d'in tare da d'iban omelettes d'in yayi tasting. "Uhhm yummy"

      "Really?" Take ta hau blushing.

       "Sure" Ya amsa.

        Zakia dake tsaye gun ta ta'be baki tana murmushi,koyaushe haka Mom take akwai son a yaba girkinta.Sometimes takan ce dad is so  lucky he has a loving and caring wife.

      Ita ma d'akin nata ta koma tsokana yasa ta tsiri ci dan ba wani yunwa da take ji.

      6:16pm Shaheed ya shigo lokacin kowa yana d'aki,be shiga nashi d'akin ba ya shiga na Amjad

     Sallah ya tarar dashi yanayi,ko ba'a fad'a ba yasan Asr yake dan aikin kenan a haka anci sa'a be had'a da Isha'i ba.Yana zaune har ya idar tukun ya soma magana.

      "Asr right?"

       "Mind your own business silly boy ,where have you been?

        "Do I have to explain? Look at how you're talking as if you're my dad"

         "Pillow ya d'auka ya cilla masa a fuska." Get out "

         "Easy,am going dude" Tashi yayi ya fita ya rabu dashi.

       
Nigeria, Kano.

      Sauri-sauri take tafiya hannunta ri'ke da jakar makarantarta kayanta kuwa uniform d'in islammiyya ne.

     "Assalamu Alaykum" Ta fad'a bayan ta 'karasa gida.

      "Waalaikissalam"Aka amsa mata.

    A tsakar gida ta tarar da Mahifiyarta tana gefen shinfid'ar mahaifinta daya ke kwance ana ganinsa ansan yana jin jiki.

      " Sannu Baba".Ta fad'a.

      Kai kawai ya iya gid'a mata dan ko magana ya kasa yi.

      "Ina kika baro su Maryam d'in?

       " Suna dawowa tafiyar tasu ba sauri shiyasa nayo gaba"Ta amsa.

        "Laila idan kin cire uniform d'in zaki je gidan kawunki ki kar'bo ruwan rubutu za'a bawa Babanku"

STORY CONTINUES BELOW

       "Mami wai wannan ji'ke-ji'ken baza a dena d'ura masa ba"Ta fad'a 'kasa-'kasa kar Mahaifin nata ya jiyo.

      " Toh ya za'ayi"Mami ta fad'a.

       Ba jimawa ta chanja cikin kayan gida tare da zira hijab ta fito.

      "Na tafi".Abinda tace da ita kenan tukun ta fad'a.

       Gidan kawun nata daya ke bayan layinsu ne ba dad'ewa ta dawo,a lokacin suma 'kannen nata suka dawowa.

      Dama Mami ta san ba iya ruwan rubutun bane hadda sauran ji'ke-ji'ken magunguna idan ta'ki bashi kuma suce bata son d'an uwan nasa ya warke shiyasa ta dena 'kin bashi dan wasu lokutan da kansa yake zuwa ya d'ura masa.

    
    LAILA itace d'iyar fari a gidansu se 'kannenta guda uku Maryam ,Nusaiba se auta Fauzan. Laila wannan shekarar ta kammala secondary school dan hatta jamb tayi admission take jira,tana da shekara 19 a duniya.

        Mustafa Mu'az sunan mahaifin Laila ,Fatima sunan mahaifiyarta.Mahaifin Laila yana da yayyi guda biyu Yunusa Mu'az na farko da Engr.Abdallah Mu'az na biyu se shi na uku.Mahaifin Laila ba mey kud'i bane yana de d'an sana'arsa,lokaci guda rashin lafiya ya kamashi ,koda suka je asibiti aka fad'a musu ya kamu da ciwon 'koda.Duk cikin su ukun Engr.Abdallah shi yayi karatun boko mey zirfi cikin ikon Allah ya samu d'aukaka har yakai wannan matakin sanda ya kammala karatunsa a 'kasar waje ya samu aiki.

     Rushda Lincoln data kasance haifarfiyar Italy business ya dawo da iyayenta Nigeria,haka yasa ta iya harshen hausa dan tun tana 'karama suka komo,Egr.Abdallah daya ta'ba yin aiki 'kasan Mahaifin ta a dalilin haka suka had'u da Rushda .Lokacin da yazo wa 'yan uwansa da maganar aurenta kowa ya'ki amincewa dan su a ganinsu ma ita Christian ce seda 'kyar suka fahimci musulma ce grandparents nata ne Christian amma iyayenta musulmai ne ,Lincoln kuwa sunan da family d'insu suke bearing ne.Bayan aurensu suka koma Canada da zama inda sukai 'ya'ya guda Uku watoh Amjad, Shaheed se Zakia.

     A yanzu haka Amjad ya kammala karatunsa yana da shekara 26 ,Shaheed yana da 23yrs shima yana gab da graduating ,Zakia tana da 19yrs ita bata dad'e da fara university ba.

      Engr.Abdallah lokuta-lokuta yana zuwa 'kasa Nigeria domin ziyartar 'yan uwansa dad'i da 'kari Company nasa (RAZAS),Amjad da tun befi 10 ba idan aka zo Nigeria baida buri a tafi company har yanzu sed kuma zaman Nigeria ne sam bayaso . Kusan yanzu 7yrs rabonsa da Nigeria last zuwa da akai harkar school tasa beje ba daga Mom se yaran guda biyu banda dad dayake tare dashi.
       
      Tunda Mahaifin Laila ya kwanta rashin lafiya Dad yana tura masa kud'i na asibiti ,yanzun ko ya turo Baba  seya ce Mami siyi siyayan abinci dan yana ji ajikinsa kamar baze tashi ba.Shikuwa dama Kawu Yunusa baya son zuwa asibiti haka kullum cikin had'o ji'ke-ji'ken gargajiya.Toh wannan kenan.

   8:30pm

       Bayan sun kammala cin tuwo suna zaune dukansu a tsakar gidan ,Mami se fifita take ma Baba abincin ma ya'ki ci se numfarfashi dayake.

      "Sannu,a had'a maka shayi tunda ka kasa cin abincin"

     Kai ya gurgiza mata alamar a'a.Shiru tayi daga haka ta cigaba dayi masa fiffitar.Yaran ma sinyi shiru basa ko hira,Fauzan ne ma mey yin magana shima ganin sinyi masa shiru ya dena,'kuruciya tasa baya fahimtar halin da ake ciki iya kaci yaji ance sannu Baba shima ya fad'a. A yanzu yaran nada shekara 7,Maryam nada 16 se Nusaiba 14.

       9:00pm nayi kamar koyaushe lokacin baccinsu yayi dan haka suka mi'ke zuwa d'akinsu.

     "Kada a mance ayi addu'a"
       "Toh Mami". Suka amsa sannan suka shige d'akin.

        Su duka ukun a shimfid'a d'aya suke kwana ,Fauzan daban.Basu kwanta bacci ba seda suka tabbatar sinyi addu'oinsu sannan suka kwanta,Laila da 'kyandas taji ko alamar bacci babu a tattare da ita.Ciwon Baba ba 'karamin damunta yake ba,gashi ita kanta Mami tana cikin damuwa kusan 2month ana jinya.

STORY CONTINUES BELOW

      Da'kyar ta samu ta rufe idanunta bayan 15min bacci yayi gaba da ita.

   Amjad,4:12am

       Kamar ba dare ne ba,earphone ne ma'kale a kunnensa ya d'ora laptop kan gado se chat d'insa yake hankali kwance gefensa kuwa Pepsi ne yana korawa.
   
      Kusan koyaushe haka yake baya wani isashshen bacci se kusan 4:30am ya kwanta   har lokacin subh yayi be farka wa inba Mom ce ta tashesa ba itan ma setayi fama kafin ya mi'ke.Dad ya rasa yadda zeyi da irin hali na Amjad sam ya banbanta da siblings d'insa ,ga yawo shine club shine parting tare da bad guys.

Washegari,Saturday

      Duka yaran suna makaranta kamar koyaushe basa d'ara 8:30am kowa take tashi daga bacci se kuma wani daren ,kowa ya shiga sabgarsa Laila kuwa tana kitchen tare da Mami suna had'a karin kumallo,Fauzan ma na wasanshi a tsakar gida su kuwa Maryam da Nusaiba suna wanke kwanuka.Baba kuwa yana d'aki kwance yana jiyo hayaniyar yaran.

        Kwan ! kwan! Suka jiyo bugun 'kofa daga waje,sallamar da akayi neh tasa suka sheda mey maganar.

      "Kawu ina kwana".Yaran suka fad'a bayan an bud'e 'kofar ya shigo ciki.

        " lafiya".Ya amsa.

          "Ina Baban  naku?" Ya tambaya.

            "Yana ciki ". Suka amsa.Da sauri ya 'karasa d'akin,Mami kamar yadda tayi tsammani hannunsa ri'ke 'kulli-'kullin magunguna.

    " Za'a sake kwankwad'a masa wasu kenan"Laila ta fad'a bayan ya shigesu.

      "Idan ya jiyoki ba ruwana ,kiyi aikin dake gabanki atoh". Cewar Mami tana cigaba da sakin fanke.

     " Fad'imatu!" Taji Kawu ya 'kwalo mata kira.A gigice ta tashi dan ta mugun razana tsoronta kar ko wani abu ne ya samu Baba amma tana zuwa taga ba haka ba."Jiya kin bashi maganin da Laila tazo ta amsa guna?"Yadda yake maganar cikeda tuhuma.

    "Ehyi Kawu an bashi"

     "Allah yasa dan naga jikin ba 'kwari ina 'ko'karin zaunar dashi ma abu ya gagara ko dama ya jima a hakan?"
 
        "Jiyane de be samu ya iya zaman ba"

           "Toh ga wani maganin na kawo yanzunnan za'a bashi yasha d'akko kofi a tsiyaya"

    Da "Toh" ta amsa ,bayan da aka kawo kofin ya tsiyaye maganin,tallafo shi yayi da 'kyar tukun ya kafa masa.

       "Ka daure kasha ko ka samu 'kwari"Kawu ya fad'a.Baba da ba yadda zeyi haka ya 'kwan'kwad'e.

         Maidashi yayi ya kwantar se nishi yake d'an mi'kewar da yayi yasa yake jin wata wahalar."Sannu" shine abinda suke fad'a,da'kyar yake gid'a kai.

   Canada

        8:20am,dukansu sun hallara a dinning table suna breakfast chair na Amjad kuwa empty ba shi babu batunsa.
       "Where is Amjad?" Dad ya tambaya yana kallon Shaheed.

      "Uhh..in his room"Mom ta amsa cikin in'ina

       "Sleeping right?"Yadda yayi maganar yasa dukansu sukai shiru ,  ta sunki da kanta 'kasa ba tare da ta sake cewa komai ba .

        A fusace ya mi'ke daga kujerar ya dire spoon d'in hannunsa,ko ba'a fad'a ba Mom tasan d'akin Amjad ya nufa.Itama tashi tayi tabi bayansa tana 'ko'karin tsayar dashi.

         " Honey stop! Honey listen to me"

      Banza yayi da ita ya cigaba da tafiyarsa har ya 'karasa 'kofar d'akin dede zeyi knocking wayarsa tayi ringing.

     Da alama kiran mey mahimmanci ne haka yasa ya sauka 'kasa.Dad'i taji ganin haka dan tasan da ya shiga d'akin rai ze 'baci kuwa.

       Da kanta ta Shiga d'akin,ya 'kudundune da blanket se sharar bacci yake.

      "Amjad,wake up it's almost 9am" Ta fad'a a hankali tana tapping shoulder d'insa.

       A hankali ya motsa memakon taga ya bud'e idanunsa a'a se ya juya fuskarsa d'ayan side d'in.

      "Amjad! Your dad is here"

       "Uhmm" Ya fad'a a ciki-ciki.

        "I said wake up"

         "Mom please,30min more.."

         "Amjad!" Ta kira da 'karfi.

         Da'kyar ya tashi yana mirza idanuwansa da suka 'kan'kance tsabar bacci daya taru yana kunbure- kunbure.

       "Ya tashi " Ta fad'a bayan ta sakko 'kasa.

        "Better" Daga haka ya koma d'aki.

    Sanda Amjad ya sauko Dad ya bar dinning d'in,hankalinsa kwance yayi breakfast d'insa kowa ya tashi ya barshi.A zuciyarsa yana jin dad'in tafiyar da Dad zeyi zuwa Paris yasan zey samu ya sarara ba takura zeyi abinda yake so.

    kano
    Wajajen 2:30pm Laila ta gama shirinta cikin uniform d'in islamiyya,fuskarta ba wani makeup amma hakan be hana kyawunta fitowa ba,eyelashes nata zara-zara da girarta me matu'kar had'uwa very thick ga curve ,lips nata dede ga dogon hanci ,ganshinta kuwa tayi parking ,ko powder bata sa ba amma farar fatanta bebar haskakawa ba(kwatancen laila zey ja lokaci shiyasa  kawai aka d'anyi description kad'an)
   Yawanci kullum tana riga su shiryawa shiyasa wasu lokutan bata jiransu.

      "Maryam!" Ta 'kwala mata kira.

      "Kinsan ba jiranku zanyi ba kuna gani uku ya kusa zanyi tafiyata idan bakuyi sauri kun shirya ba"

      "Yanzu fa zamu shirya"

       "Banga alamar hakan ba ai" Ta bita da harara."Seki je ki kirasu Nusaiban"

          Basu suka fito daga gida ba se 2:54pm,se dungure musu kai take tana balbalesu da masifa.Daba ace Mami ce ta takura su tafi tare ba da bata jira su ba.

Canada

      4pm Dad ya tafi zuwa Paris, Shaheed da Zakia  se Mom suka raka shi har airport banda Amjad da yana gida duniya tai  dad'i Dad is not home dukda kuwa ya sake ja masa kunne akan zuwa party da 'kin yin sallah akan lokaci.

Canada+

8:30pm,suna dining Mom,Zakia da Shaheed kowa kawai de cin abincinsa yake wannan kusan duk ranar da Dad yayi tafiya haka sike saboda yana da wasa da dariya cikin familyn nashi amma dukda haka Amjad besa ya dena ganin tsananta masa da Dad yake ba,shi a ganinsa ya takura masa.

Suna zaunen ne Amjad ya sakko ,ya ma'kala earphones a kunne se bin wa'kar yake hankalinsa kwance yaja kujera ya zauna.Gabad'aya kallo suka bishi dashi dan sun gano dalilin farincikinsa,jin kallon ya isheshi yace.

"Sorry guys ,I forgot to say hi to you is that it?"

Kai kawai Shaheed ya girgiza ya tashi,Zakia kam ta'be baki tayi ta cigaba da cin abincinta.

"Amjad you're happy Dad is not here right"Mom ta fad'a.

"Ahn?" Ya zare earpiece d'aya dan beji mey tace ba.

"I said you're happy Dad is not here right?"

"Why should I not, he's always harassing me ,am glad now he's not home no more harrasing I wish he could stay there for 6month"
Ya 'kare maganar a ciki-ciki

"Because you want to enjoy parting hanging around with silly boys like you " Zakia na gama fad'a tayi sauri ta gudu d'aki dan idan ta tsaya seya daki bakinta.

"Mom did you heard that? I can't tolerate nonsense!"

"Come on eat forget about what she just said,she's sad Dad is not home"

'Kwafa yayi ya cigaba da cin abincin tare da 'karo volume d'in wa'kar.Kowa d'akinsa ya wuce ,Amjad like always ya kunna laptop sede yau video call ya shiga yi da farko da wani friend d'inshi Sam ya fara bayan ya gama labarta masa Dad yayi tafiya kuma ya soma yi da wata beb.

"Hi Rosie" Ya kirata fuskarsa d'auke da murmushi.

"How you doing ?"

"Am ohk" Ta amsa.

"But you don't seems to be ok" Ya amsa cikin sanyin murya.

Cikeda iyayi irin tasu ta turawa tayi rolling eyes tare da sauke numfashi kafin tace."Am just having a hard time here in London am tired I need to come back to Canada " Ta 'kare maganar tana sa'kale gashinta bayan kunne.

"I knew it,you won't like staying there how could that even be so possible I know you missed me"

"Yeah I do,and you?"

"Do you have to ask ?"

Murmushi kawkawai yi ba tare da tace komai ba."Now what's your decision are you going to stay there or you have changed your mind?"

"Well,you know I can't live without you,why will you even expect me to stay there? It's not that easy" Ta 'kare maganar kamar zatai kuka.

"It's all over now,everything is gonna be ok"

"Yeah"

"Amjad"Ta kira sunanshi.

"Huh?"

"I'am sorry,i'am sorry for hurting you so bad for living without even saying goodbye"

"Shh! Stop apologizing, I know you won't left me it's just that you need to have some space at that time, I was also wrong to treated you like that,i'am also sorry"

Kai kawai take gid'awa dan a yanzun kuka yaci 'karfinta se gogewa take amma ya'ki 'karewa.

"Please stop crying everything is fine"

"Yeah I know,I just can't hold it"

"You can ,look at me "

A hankali ta d'ago kamar yana gabanta kuwa idanuwan sunyi jazir ga kumburi da sukai fuskar ma tayi red.

STORY CONTINUES BELOW

"I love you"Ya fad'a.

Wani farinciki taji ya shiga zuciyarta kukan ma ta nemeshi ta rasa duk da kuwa ba yaune first time daya fad'a mata hakan ba, kawai de tayi missing words d'in daga bakinsa.

" I love you too" Tayi 'ko'karin amsa wa,tuni ta mance da komai suka shiga hirarsu ta masoya.

Rosie, tare sukai makaranta da Amjad tun suna teens da farko friendship suke ba ala'kar soyayya amma daga baya soyayya mey 'karfi ta shiga tsakaninsu.Watarana suka samu sa'bani sakamakon wani saurayi daya ganta dashi,ko explaining be bari tayi masa ba ya hau fishi da ita hakan yasa tayi zuciya ta koma wajen mahaifiyarta da zama wadda take a London ,Amjad se ji yayi ta tafi ,1month da faruwar hakan du zaman ya isheta tayi missing d'inshi idan ta kirashi baya picking se yanzun taci sa'a ya nemeta.

Kano,9:15pm

Mami ce zaune kusa da Baba se fifita take masa,ga abinci a gefe ya kasa ko loma d'aya.

"Ina yaran?"Ya tambaya murya a dashe.

" Sun kwanta bacci".
"Taso su" Ya fad'a.

"A taso su" Ta nanata taji banbara'kwai dan shine me hanawa a tashi wani yana bacci.

Tashi tayi jiki a sanyaye ta shiga d'akin yaran d'aya bayan d'aya ta tashesu ,Nusaiba da nauyin bacci se rife ido take.

"Laila kuje babanku yana kiran ku"

"Kira?"

"Eh kuje yanzu"

Su biyu suna biye da ita a baya banda Nusaiba da tana ganin fitarsu ta koma baccin ta.Suna shiga suka zauna bisa shinfi'darsa.

"Au Nusaiba komawa baccin tayi?" Mami ta fad'a bayan data lura bata gun ,tashi tayi da niyyar kiranta Baba yace ta rabu da ita.

"Laila,Maryam" Ya kira sunansu.

"Na'am Baba" A tare suka amsa.

"Ina so ku kasance masu biyayya ga mahaifiyarku da 'yan uwana duk da nasan kuna yi amma zanso ace kun dad'a a kai" Dukansu jikinsu yayi sanyi jin irin kalamansa.

"Koda ace bana duniya kada ku d'auka cewa baku da mey fad'a kuji ,yayyina d'aya sike dani a gunku suma iyayenku neh kunji koh ?"

"Toh Baba" Maryam ta amsa.Ita kuwa Laila kuka ne yake nema ya ku'buce mata zuciyarta tayi matu'kar karaya.

"Laila kece babba a cikin yarana,'kannanki sune masu koyi dake ,kece abokiyar shawarar mahaifiyar ki .." Tari ne ya katsesa ya kasa cigaba da magana.

"Sannu Baba" Ruwan dake cikin jug Mami ta tsiyaya a cup ta bashi yasha kad'an.

"Kuyi ha'kuri" Suka ji ya fad'a.

Shiru d'akin bame magana har kusan 10min,ganin haka Mami tace su koma su kwanta. Laila tana fita daga d'akin ta koma gefen 'kofa tayi zaman dirshan Maryam ta shiga d'aki ta barta duk da ita ma ba barci ta koma ba.

"Sannu" Ta jiyo muryar Mami tana fad'a dan tarinsa ya tsananta.Zuciyarta sai dukan uku-uku take da tayi yun'kurin shiga d'akin seta kasa wani tsoro take ji yana sake shigarta.

"Baba" Take ta ambata a hankali.

Ganin yadda Mami ta fito a kid'ime yasa tayi saurin mi'kewa a firgice."Laila zanje na kira kawun ku"

Bata jira jin abinda zata ce ba ta fita daga gida ,Laila da sauri ta shiga d'akin ta tarar dashi yana ta numfarfashi.

"Baba" Ta zauna tare da ri'ko hannunsa ta had'a da nata tafin,hawaye ne kawai yake 'kwaranya a fuskarta ta rasa ina zata sa kanta itade tunda take bata ta'ba shiga tashin hankali kamar wannan ba.

STORY CONTINUES BELOW

Sunkui da kai tayi ta dafe goshinta da hannunsa had'e da nata,Maryam ce ta shigo itama ganin yanayin da Laila ta shiga tasa kuka."Ina Mami ta tafi?"

Ta kasa ko amsa mata har yanzu kanta a sunkuye yake,10min later sega Mami ta dawo tare da Kawu Yunusa.'Karasowa yayi inda yake ya du'ka a sanyaye.

"Mustafa" Ya kira sunansa.

Laila se lokacin ta d'ago ta dubi Baba tana jira ya amsa.Hannunsa data ri'ke taji yayi nauyi."Baba" Ta kira a raunane.Ta kira yafi sau uku amma shiru,kawu ne ya ri'ko hannunsa daga bisani kuma ya maida.

"Innalillahi wainna ialihi raji'un" Abinda ya furta kenan.

"Fad'imatu sede mi ha'kuri amma Yunusa Allah ya d'auki abinsa"

Jitai kunnuwanta ya toshe idanunta kuwa sun soma dena gani ko kukan ma ta dena ,tana kallo Mami tai zaman dirshan take ta soma kuka.Innalillahi wainna ilaihirraji'un.

Maryam ma kukan nata ne ya sake 'karuwa,Nusaiba daga d'aki tajiyo su kamar a mafarki ,zinbir ta tashi tayo waje.Wajen Mami tazo ta 'kan'kameta tasa kuka ganin Mami na kuka da Maryam.

"Kawu a tafi asibiti bafa mutuwa yayi ba" Suka jiyo muryar Laila, ba wanda ya tanka mata dan sunga zafin mutuwa ne ya doke ta.

Washegari
Duk cikinsu ba wanda ya iya bacci har gari ya waye,a jiyan dama Kawu ya kira wasu 'yan uwa ya sanar musu da rasuwar saboda haka da asuba suka fara zuwa.

Laila ba ita ta tabbatar da Baba ya rasu ba seda taga gida ya cika da jama'a,nan ta dasa nata kukan ta shige d'aki.Lokacin da aka zo fita da gawarshi seda kawu ya korata ita a lalle seta bisu an kaishi da ita.
'Yan uwan Mami sukai ta rarrashin yaran suna basu ha'kuri.
Kawu Yunusa ne ya samu ya kira Dad a waya ya sanar masa da rasuwar d'an uwan nasu.Yaji mutuwar sosai,Mami tana zaune aka kawo mata wayar sukai wa juna gaisuwa daga bisani sukai sallama,zuwa Nigeria ya kamashi gashi yayi tafiya dan a yanzun ya shiga busy akan aikinsa sosai.

Canada, 4pm

Yau Sam ya kawo ziyara wajen Amjad,Sam d'aya daga ciki abokansa ne na yarinta tare sike rashin jinsu da yawo he is one of his craziest friend.

Da Sam da Shaheed duka suna d'akin Amjad wai zasu gwada wrestling Amjad ne rep Sam da Shaheed sune players duk sun 'kwa'be rigar jikinsu.

Wani rectangular plane katako suka d'ora kan kujeru biyu at each end.Amjad ya tsaya daga gefe suna jira ya busa 'kusur.Fittt! Suka soma,kowa burinsa ya d'aga wani ya danfara a kan fence d'in,daga yadda 'kirar Sam take za'a gano cewa yafi Shaheed 'karfi.Chancharas ya d'aga Shaheed ,se wutsul -wutsul yake Amjad yana ta dariya hadda ri'ke ciki.Yana ji yana gani ya damfarasa akai hatta katakon seda ya ragargaje kujerun kwa suka fad'i ,Shaheed ko motsi da'kyar yake ya ri'ke 'kwan'kwaso se juyi yake.

"I caught that on camera" Amjad ya fad'a.

"Dude are you alright?" Sam ya tambaya yana dariya.

"Aghh,Mom!" Ya 'kwala mata kira.

Ba dad'ewa kuwa sega ta ta shigo,hannu ta d'ora a baki tana waro ido."Oh my god ,what did they do to you Shaheed ?"Ta 'karasa inda yake ta rasa ma ta ina zata soma taimaka masa ya mi'ke.

"Guys this is crazy,look at him he's hurt"

"Mom he's gonna be ok" Cewar Amjad.

Da'kyar ya samu ya mi'ke suna had'a ido dashi suka she'ke da dariya.

"Shut up! This is not funny,Amjad this is nonsense behave yourself don't let that happen again" Tana gama fad'ar haka ta fice, Shaheed yana biye da ita se dafe baya yake ,bayan yayi jazir.

STORY CONTINUES BELOW

Ganin Mom bata ji dad'in abinda sukai ba ya tsagaita da dariyar.

Seda ta daddana masa ice block shima tana yi tana dungure masa kai,da be kula su ba da hakan be faru ba.

"Don't ever try this again,this is stupid"

Shide ya sunkuyar da kai a zuciyarsa yana tsara ramuwar da zeyi musu shima,gashi sunyi video zasi yad'a shi.

Landline na sitting room da yayi ringing yasa ta mi'ke dan amsa kiran.

"Innalillahi wainna ilaihirraji'un"Ta furta bayan Dad ya sanar mata da rasuwan.

" Sorry for your lost,I felt sorry for his family may his soul rest in peace
May Allah grant him jannatul Firdausi.

"Ameen" Dad ya amsa daga d'ayan 'bangaren.

"Mom,what happened?" Zakia ta tambaya dede lokacin ta dawo daga school taji tana wayar.

"Your uncle, he's gone"

"Uncle mustafa?"

"Yes"

"Uhh,may his soul rest in peace, I will call Dad"

"Yes you have to, am gonna call his wife Fatima"

A take ta kirata aka ci sa'a wayar tana kusa,cikin harshen hausa ta soma mata gaisuwa.

"Allah yaji 'kanshi yasa ya huta"

"Ameen,nagode" Mami ta amsa murya a sanyaye.

"InshaAllah muna nan zuwa ,ki gaida yara a basu ha'kuri"

"Zasi ji,nagode "

Amjad da tunda ta fara wayar da Mami ya jingina a bango ya wani folding arms yana jiran ta gama wayar dan ba jin abinda take fad'a yake ba,when it comes to Mom wajen hausa to bafa ya tsintar komai amma idan Zakia ce ko Shaheed toh yakan tsinci kad'an shima da 'kyar.Rashin iya hausarshi ya samo asali ne dalilin boarding school da yayi,sukuwa sauran Suna gida duk sanda Dad da Mom suka juya magana da Hausa sukan tsinci wani abun kuma shima Dad yana 'ko'kari yaga sun koya.

"Where is he?"

"Who?"

"Sam"

"He just left"

"Amjad you have to be careful,this should be the last time ,don't let that happen again,Shaheed is your bro why do you like hurting him?

" Ok,ok it won't happen again "

"I hope so"

Har zata wuce ta tuna ta dawo."Your uncle is gone,you should call your Dad"

"He died, When?"

"Last night"

Kai ya jinjina tare da d'age gira."may Allah grant him Janna".

"Ameen".
Kano

Haka ranar Suka wuni duk cikinsu ba wanda yasa abu a bakinsa se Fauzan da be mallaki hankalinsa ba.Laila dan tsabar kuka har zazza'bi ne ya rife ta gashi ta'ki cin komai shiyasa ta galabaita tana kwance 'kuryar d'aki ,tunanin tsahon rayuwar da suka d'auke tare da mahaifinsu tayi -tayi da 'karshen maganar da yai musu.

Ko 'yan islamiyyarsu da suka zo gaisuwa da 'kyar ta samu ta iya fitowa tsakar gida,data lura da Mami taga yadda ta sake ramewa fiye da da.

2weeks later

11:23pm

Dad kwana biyu da dawowarsa Canada gobe zasi je Nigeria dukansu, shirye-shiryen tafiya suke yi ,d'akin Zakia Mom ta shiga dan dubawa ko ta gama nasu shirin dan jirgin safe ne dasu .Kamar yadda tayi tsammani taga ta gama shirya kayanta,koda ta duba Amjad shi video call d'inshi yake da Rosie.

STORY CONTINUES BELOW

Ganin shigowarta yasa ya katse kiran sukai sallama.

"Amjad,what are you doing you didn't park your things?"

"Are we really travelling?"Ya tambaya cikeda rainin wayo.

" Yes,you should have park your things our flight is 7am"

"What!" Ya mi'ke tsaye.

"I don't wanna go anymore"

"And you must,it's necessary put this in your head better park your sh*t now!"

"Mom!"Bata saurareshi ba tayi ficewarta ta barshi.

"F*ck up!"Ya daki cloth set dake jingine.

" Nigeria Nigeria ,hot! hot ! hot and that fucking little sh*t(mosquito😂),damn it! Shi kad'ai yake masife-masifensa kafin daga bisani ya bud'e cloth set d'in.

Kano

Yau su Laila suka koma makaranta ita da Maryam suko Nusaiba da Fauzan ana yin kwana ba'kwai washegari suka koma,suma su Laila saboda 'yan gaisuwa yasa Mami tace su bari yau.

Laila tayi mugun ramewa seda akai da gaske ta dena zama da yunwa ,fuskarta har yanzu da nuna damuwa a tattare da ita.

"Kun fito kenan?"

"Eh Mami" Suka amsa ta.

"Toh se kun dawo"Daga haka suka tafi.

★★★

Amjad bayan daya gama jera kayan daya ke bu'kata ya suri jacket a hankali ya salalla'ba ya fice daga d'akin, a sitting room ma da sand'a ya bud'e 'kofa ya fice.Wayarsa ya d'akko a aljihu ya danna was Sam kira yake fad'a masa ya fito dama sun had'a appointment.Mintina 'kalilan ya 'karaso daga can nesa yayi parking motarsa yadda bame jinsu,cikin sassarfa ya 'karasa wajen beyi wata-wata ba ya bud'e 'kofar ya shige abinsa.

"Man,where are we going?" Sam ya tambaya.

"Rosie"

"Then let's go to club first, later I drop you to Rosie's home"

"No,it's getting late it's 12am already"

"Come on we are not gonna spend much time there"

"Alright, then
get going"

A wani haukace ya suresu kafin daga bisani ya seseta tu'kin,Amjad ko jikinsa inde wannan ne ya saba.

Seda suka fara zuwa club kamar yadda Sam yace,nan suka had'u da abokanan shashancinsu sukai ta shirmensu,masu rawa nayi masu drinking nayi shide duk yadda yakai ga zuwa club ko sau d'aya be ta'ba shan wine ba rawa de za'ai iya son rai.

Basu suka fita ba se 1:30am,da'kyar ya samu ya janyo Sam suka fita dan already he's drunk suna fitowa kuwa ya soma she'ka amai,se tangali yake kamar sabon mahaukaci.Key ya kar'be daga hannunsa dan yasan a halin daya ke ciki baze iya tu'kasu ba.Direct gidansu Rosie yayi parking,bayan ya fito daga motar ya kirata a waya lokacin bacci take cikin magagi tayi picking.

"Hello" Muryarta 'kasa-'kasa.

"Am outside"

"Amjad,is that you?"

"Yeah"

"Seriously?"

"Don't you believed me? look outside the window"

Tashi tayi ta le'ko ta window d'in ta hango shi jingine da mota take ta saki murmushi, da sauri ta fito tana sanye da dogon wando wanda da kad'an ya wuce gwiwa se wata vest gashin kan a barbaje kan kafad'arta.Fuskarta d'auke da murmushi har ha'kwaranta suna bayyana.

STORY CONTINUES BELOW

Tana 'karasowa tai hugging d'insa ."Are you really travelling? "Ta fad'a bayan sunyi breaking hug d'in.

"Who told you?" Ya tambaya tare da furrowing eyes yana mey mamakin wanda ya fad'a mata.

Kallonta ta mayar kan Sam dake cikin mota yana shargar bacci."So he is the one"Ya fad'a bayan ya dawo da kallonsa gareta.

"Yeah"

"I won't take so long there"

"What about your family? are they gonna stay there for long"

"I think so"

Daga nan suka d'are kan mota hand in hand suka shiga hirarsu,se 2:14pm ya tafi gida Sam a haka ya 'karasa gida da rabin hankali.

Washegari

7am flight d'insu ya tashi ,kafin su 'karasa kowa ya gaji,Amjad tuni annurin fuskarsa ya d'auke ,driver Dad yayi kira a waya lokaci 'kalilan ya 'karaso.Yana jinsu suna 'yan maganganunsu ko tanka musu ya'ki yi har suka 'karasa mansion d'insu,Mom mamaki neh ya kamata ganin gidan tsaf.

"Honey how..?"

"Surprise right?" Cewar Dad d'auke da murmushi.

"Yeah"

Tun a jiya Dad yasa a gyara gidan dan yasha 'kura saboda tsahon lokacin da aka d'auka ba'a zauna ba.

D'akinsa ya wuce direct ga yunwa dayake ji amma bama ya sha'awar cin abincin.

Driver Dad yasa ya siyo musu abinci kafin siyi settling kuma,Shaheed, Zakia kowa ya shiga d'akinsa bayan sunci abincin shikuwa 'kinci yayi ya kwanta da yunwa.Da safe kuwa da wuri ya farka dan yunwa ,kitchen ya nufa direct Allah ya taimaka yaga fridge a cike da kayayyakin ci.Bowl ya d'auka ya had'a cornflakes stool yaja ya zauna ya soma sha.

"Son" Yaji Mom ta kira sunanshi sanda ta shigo kitchen.

"Morning" Ya gaisheta.

"Yunwa koh?" Seda ya d'an yi nazari tukun ya tuna mey hakan yake nufi.

"Uhmm" Ya amsa.

"I made you a toasted bread"Ta fad'a tana 'karasawa ta d'akko masa.

Se lokacin ya kalli clock d'in dake ma'kale a kitchen d'in yaga 8:34am.Su kuwa tun tuni sunyi breakfast d'insu ma,da sauri yaci ya koma d'aki yayo alwala ya tada sallah.

Se around 11am ya fito bayan yayi shower baccinsa ya koma,yana sakkowa 'kasa ya tarar dasu duka a sitting room.

" Morning Dad"Ya gaishesa.

"Morning" Ya amsa.

"Yaushe zamu je?" Mom ta tambayi Dad.

"Anjima zamu"

"Gidan late Uncle?" Zakia ta tambaya.

"Ehyi"

Shi sam ba son wannan hausar da sukeyi yake ba,sede yayi ta kallon bakinsu,tunanin yadda zey tsara tambayar mey suke cewa ya shiga yi amma fa da yaran Hausa,yafi minti uku yana tsara abin fad'e kafin yai gyaran murya.

"Mey cewa kukai?"Ya fad'a da confidence d'inshi.

Gabaki d'ayansu ba wanda beyi dariya ba,Zakia hadda ri'ke ciki dan dariya.Tuni ransa ya 'bace duk wannan tsare-tsaren shine zasi 'bige da dariya ,pillow na kan sofa d'in ya d'auka ya wurga wa Shaheed a fuska ya tashi ya koma d'aki.

Ganin haka Mom ta tsagaita da dariyar ta fara kiran sunanshi amma yayi burus.

" It's ok guys,enough please"

"Wani yasa ya kasa koya ,dole miyi masa dariya the next time yayi abinda yafi haka wani dariyan zamiyi +shame shame "Dad ya fad'a.

Tashi tayi ta nufi d'akin sa." Come in" Bayan tayi knocking.

"A zaune ta tarar dashi kan gadon yana tapping phone d'insa be ko kallo wajen ba.Zama tayi kusa dashi ta dafa kafad'arsa " Son we are sorry"

"You don't have to"

Ohh sweetheart ,you even try there is nothing wrong there it's just that you misplaced the words"

"Then you correct me not laugh"

"It won't happen again"

"Do you want learn the.."

"Not anymore" Ya katseta.

"No son it's good to ,what if you are to stay in Nigeria?"

"God forbid"Yayi saurin fad'a.

" Who knows if.." "

"Mom please stop it,I don't like talking about it,am not staying in any other country apart from were I was raised"

"Am joking ,don't worry" Ta fad'a tare da tallafoshi sekace 'karamin yaro.

4pm suka nufi gidansu Laila,aiko ranar an tashi da rana duk da a cikin mota suke Amjad be fasa complaining ba har suka isa gidan.Mami tana tsakar gida taji sallama,tana bud'e musu 'kofa wa zata gani.Iso tayi musu suka 'karaso har ciki ta sauke su a d'an 'karamin parlonsu inda aka ci sa'a ma daakwaia wuta ta kunna musu fanka,su Laila kuwa dukansu suna makarantar islamiyya.

Dijensy❤

Dukansu wuri suka samu suka zauna,Shaheed da Zakia suna zaune 2 seater se Mom da Dad da suke zaune kan 3 seater Amjad ya hakimce kan 1 seater daga can 'kuryar parlon se cin magani yake.+

      Cikin rissinawa yaran suka gaida Mami da yaran  Hausa shima yai koyi da abinda suka ce yayi mata gaisuwa,suma Mom da Dad suka sake mata gaisuwa bayan sun  gaisa.

     "Ina yaran suke?" Dad ya tambaya.

      "Dukansu sun tafi islamiyya nan da anjima zasu dawo"

      "Allah yayi albarka" Cewar Mom.

      Mami ta amsa da "Ameen".

    Hira kad'an suka d'an ta'ba wanda kusan duk akan yaran nasu ne ,nan Mami take fad'a masu Laila ta kammala karatun secondary.Sun kwashe kusan 1hr tukun suka je gidan  kawu Yunusa ,bayan sunyi kamar 40min Mom da yaran suka komo gidan su Laila Dad yana tare da Kawu yunusa suna tattaunawa.

      Kamar yadda sukai zaman farko haka sukai yanzunma ba wanda ya chanja position, Amjad da zafi ya fara isarshi se d'aga 'kasan T-shirt d'insa yake yana firfita sekace ba fan a d'akin.

     Zakia ce ta d'auki jug d'in da Mami ta kawo musu ruwa ta tsiyaya a cup ta sha,Shaheed ma ta ziba mishi sannan Mom.Mom da kanta ta ziba wa Amjad ta bashi,shide ya ri'ke a hannu amma ya'ki sha se danna phone d'insa yake.

     5:43pm su Laila suka dawo gida tun daga 'kofar gida suka gane anyi ba'ki sede basu san su waye ba.

     " Assalamu Alaykum"Sukai sallama.

    "Daga parlor Mami ta amsa ,Nusaiba da Fauzan ne suka le'ka cikin rissinawa suka gaishesu da sauri Nusaiba ta tashi shi kuwa yaje ya ma'kale da Mami yana sunkui da kai.

     " Suwaye suka zo?"Maryam ta tambayi Nusaiba.

      Laila da take cire hijab bayan ta ajje bag d'inta tace"Idan kin damu kije mana ki gani"

       Dama tun a islamiyya wani malaminsu ya bata haushi.

     "Daga tambaya"

      "Wa'annan d'innan 'yan uwan Baba ,'yan farare"Cewar Nusaiba.

     " Laa kawu Abdallah "

     Laila da ta gano suwa ake nufi amma tayi kamar bata sansu ba koda ta gama sauya kaya waje ta samu ta zauna 'karamar wayarta ta d'auka ta hau danne -danne.

    Maryam kuwa tana gama sauya kayanta ta tafi parlorn ta gaishesu,daga gefen Mami ta d'an raku'ba ta zauna Zakia se faman murmushi take wa yaran tana ji ina ma ace sun saba.

     Amjad tun shigowarsu be ko d'ago kai ba dan koda suka gaida su Shaheed ne da Zakia suka amsa hankalinsa na kan chat d'insa.

     "Ina Yayarku?" Mami ta tambayi Maryam a hankali.

      "Tana d'aki"

       "Toh kice mata tazo su gaisa mana"

        Tashi tayi taje ta fad'a mata ko uffan bata amsa ta ba.

      "Yaya baki jini ba?"

       "Naji karki takura min"

      Wucewarta tayi ta koma "Tana ina"Mami ta tambaya.

     " Wai karna dameta"

      "Bari naje na doko ta wannan halin bazata fasa ba  mutum ya shige 'kuryar d'aki yana miskilanci"

     Mami ce ta tashi ta tafi zuwa d'akin yaran ta isketa ma ta shingid'a kan katifa abinta.

     "Mey kike yi da baza ki taso ba ana kiranki?"

STORY CONTINUES BELOW

      "Mami yanzu zanzo"

       "A hakan kina kwance,tun d'azu ana tambayarku dan wula'kanci kuma seki kwanciyarki bakisan abinda ya dace kiyi ba"

      Sallamar Dad tasa Mami ta fita daga d'akin,se lokacin ita kuma ta ajje wayar ta mi'ke d'ankwalin ta yafa akanta dama doguwar rigar material ce sky blue a jikinta A shape ta fito.

     Daga bakin 'kofa ta tsuguna "Ina yini"

       "Lafiya lau" Mom suka amsa.

       "Ya 'karin ha'kuri"

        "Da godiya" Ta amsa.

        Zakia da Shaheed  ma ta gaisa dasu  banda Amjad da bata san da zamansa a d'akin ba saboda yana daga can gefe bata lura dashi ba inba wai ta shiga ciki ta zauna da kyau ba.

       "Wannan itace babba ko?" Dad ya tambayi Mami.

      "Eh itace Laila ,se 'kannenta " Tayi masa bayaninsu d'aya bayan d'aya.

        Laila da take jinta kamar akan 'kaya da sauri ta bar d'akin ta koma.Not more than 3min sega Mami ta shigo "Keda kika zo kika zauna anan  mey zami basu?"

     "Ga ruwa kin basu"Ta fad'a cikin rashin nuna damuwa.

       " Gidanku,ruwa abinci ne? tun d'azu fa suke nan har sunje gidan Kawunku sun dawo kuma shine zan zira musu ido"

     "Toh ga tuwo nan za'a d'ora idan zasu iya jira se a sa musu"

       "Waike lafiyarki lau? Idan su iyayen sunci yaran taya zasi iya ci kinsan de ba cimarsu bace" Mami ta fad'a.

     "Toh ya zami musu shi mike dashi"

     "A'a baza'ai haka ba,yanzu de dama miyar alayyahu zanyi kinga se'a sayo musu gurasa sauran chanji a siyo musu lemo"

    "Tohh"

    "Maghrib yana yi bari na aika Nusaiba ta siyo,ke kuma ki had'a miyar ina Maryam seta taya ki kuyi sauri" Mami ta fad'a daga haka ta fita.

     Nusaiba ba jimawa ta siyo kayan,Laila kuma suna had'a miya kafin su kammala maghrib tayi Fauzan ne ya zuba musu ruwa a buta bayan sinyi alwala ya rakasu masjid ,su Mom suma sukai tasu sallahr a gida.

    Kafin su dawo har abinci ya kammala ,komai da komai aka jero a tray Maryam ta dire a tsakkiyar parlorn.

      "Sannu"Zakia ta fad'a tana murmushi.

    Itama Maryam murmushin tayi ta amsa mata da" Yawwa"

       Sun dawo daga masjid Amjad be shigo ba ya tsaya a waje yana iyayi shi network yake searching.

      Mom ganin shigowarsu tayi serving d'insu"Amjad?"Ta tambayi Shaheed.

     "Yana waje yana ganin gari"Dad ya fad'a.

     D'an dariya tayi ta ziba musu juice d'in" Zakia"Ta kira sunanta tana mata nuni da ta sakko 'kasa,ba musu ta sakko shima haka Shaheed.

     Seda ya gama iyaye-iyayensa tukun ya tsiri d'aukan pic ,daga bisani ya d'akko camera d'insa a mota nan ma ya hau video na area d'in.

     Bata dad'e da zama ba a d'aki tajiyo knock."Mtchww! ko waye a wannan lokacin"Tana jin haushi ta tashi ta nufi 'kofar waje.

      Tana bud'ewa taga mutum a tsaye,tunani ta shigayi damage tare take d'azu,ganin zata 'bata lokaci ta matsa gefe  ya wuce.

     "To ko tare sike ?amma ba d'aya ne namijin ba?"

    Tana waiwayawa bayan ta rife 'kofar taga har ya shige parlorn.Ra'bawa yayi ya shige zuwa seater d'insa yana kallonsu suna cin abinci ya ta'be baki ,Mom data ce ya sakko yaci ya girgiza mata kai alamar a'a.

STORY CONTINUES BELOW

     Se 8:23pm suka tashi da zimmar tafiya kan lokacin tuni Amjad ya 'kosa su tafi saboda shi ba hirar ake dashi ba shi bada cin abincin ba su Zakia suna d'an hirarsu da Shaheed amma shi dinkim kamar bebe kawai kad'a 'kafa yake.

     Dad 50k ya direwa Mami bayan fitar yaran dama Mom ,Mami tayi ta godiya har 'kofar gida suka rakasu banda Laila da ta tsaya daga tsakar gida.

     "Kin wani ma'kale a ciki"Mami ta fad'a.

     " Toh mey zan musu?"

      "Bansani ba" Ta wuce ta barta anan.

               ★★★

       Amjad suna shiga gida ko d'aki be shiga ba ya wuce kitchen ya nemi abinda zeci,yunwa yake ji sosai amma tsantsami yasa ya'ki cin komai balle yasha.

   "Amjad ,so you're hungry" Ya jiyo muryar Mom ta fad'a.

    "Yeah"

     "But you refused to eat .."

      "I can't eat that". Ya katseta.

       " What wrong with the food?"

        "Nasty!"

         "Nop it's yummy ,you missed it boy"

         "No it's not"

           "Mom"

            "Yes"

             "When are we going back home"

          "This is home too"

           "Yes!" Ya jiyo muryar Zakia tana shigowa kitchen d'in.

       "This is non of your business" Amjad ya fad'a.

        "Am not here for trouble"

       "Gobe fa ina zami je?"

         "I don't know"Mom ta amsa ta.

           "Babu zuwa ko ina!" Ya fad'a bayan ya dire cup dake hannunsa ya wuce yana mata kallon banza.

    Ta'be baki tayi ta maimaita abinda ya fad'a "Babu zuwa ko ina" irin ba saban ba yau yayi Hausa.

     Tunda ya shige d'akinsa be sake fitowa ba yana jiyo hirarsu.

   
   Washegari

     Har 7am be tashi ba seda Mom tazo ta tashesa,suna kammala breakfast kuma Dad ya tafi dasu zuwa RAZAK Amjad se gyangyad'i yake a mota bacci be ishesa ba.Sanda suka shiga yaga komai ya sake sauyawa ya 'kara kyau building d'in komai an sake 'kawata shi ba 'karamin birgeshi yayi ba dan a take ya d'auko camera ya soma d'auka Dad yana kallonsa amma yayi kamar be kula ba,Amjad da gaske yana son RAZAK company sede fa Nigeria ce bayaso.

      "Do you like it?" Mom ta tambaya.

       "Yes I do it's really beautiful"

        "Do you wanna work here?"

         "Mom,actually No I don't like staying in Nigeria"

          "Son Nigeria is your country"

           "No no!"

           Suna tafiya suna hira da Mom,Dad suna can wani side d'in da sauran yaran yana nuna musu ,Manager ma ranar be shigo company d'in ba dan ya manyanta sosai kusan koyaushe cikin kar'bar treatment.

   Amjad  office na CEO ya d'are a kujerar Mom tana masa dariya.

      "Mom am the Boss"

      "It suits you my handsome"

       "I knew it"

        "Mr Amjad  Mu'az"

        "You're boosting my ego"
     
        Ganin shigowar Dad ya mi'ke yana scratching kai,shi wancan fa ko anan zamu barshi ne"Dad ya fad'a yana kallon Amjad.

     "Bayason Nigeria kuma ba"Mom ta fad'a.

      "Zeso ta wataran"

      "How?"

       "Idan na dawo dasu duka nan"

      Hakan ba 'karamin dariya ya bawa Mom ba dan a ganinta hakan bame yuwuwa bane ita kanta bazata so hakan ba.

    "Zakia do you wannan stay here in Nigeria, no Mom and Dad with you?"

    Gira ta d'age alamar "eh"tana dariya daga baya kuma tace "No".

     " I can't stay alone"

      "Shaheed?"

       "No,not anymore unless with Amjad"

      "God forbid" Yayi saurin fad'a.

       Shiru Dad yayi yana kallon yaran ba tare da ya sake cewa komai ba yana murmushi.

    Wajen 12:30 suka biya restaurant sukai lunch daga nan suka wuce mall suka yo siyayya suka komo gida,nan fa Amjad ya dasa video call da Rosie.

                 
Don't forget to vote, comment and share.✌💋

Dijensy❤

Yau  suncika 2weeks a Nigeria sun zazzagaye gidan sauran 'yan uwa har sun 'kosa su koma musamman Amjad da yake jinsa kamar a kan 'kaya, kullum mita yake ga mura da ta kamashi  se faman raki yake wa Mom tamkar d'an shekara 5 hakan ba 'karamin 'kular da Zakia yake ba ita da take 'karama bata abinda yake.Tissue kuwa duk inda yaga dama cillarwa yake sede Mom ta d'auke haka magani ma seya 'bata lokaci yake sha.+

     "Amjad wake up it's time to pray " Mom ta fad'a bayan data shigo d'akinsa.

    2:18pm beyi sallah ba se bacci yake tun bayan daya sha magani.

   "Amjad"

    "Mom I wanna sleep more"

      "I will let you sleep as much as you want but pray first"

    "I can't get up".
    Tana ji tana kallo ta rabi dashi har se wajen 3 tukun yaga dama ya tashi.Bayan yayi sallahr ya sakko downstairs,Zakia data had'a pancake d'inta dede cikinta dan tasan ba lalle sauran su ci ba.Amjad dashi ya fara cin karo a kitchen  aiko ba 'bata lokaci ya fara ci ,baki wangalau ta saki sanda ta shigo ta tarar yasa plate a gaba yana ci mata.

     Da sauri ta 'karaso ta sure plate d'in "It's mine"

      "You  better keep it or else"

       "Else what?"

        "I will hurt you the way you will regret doing what you just did now"

          "Allah I made it for my self not for you"

         Tashi yayi a fusace sekace ba shine mey langa'bewa Mom ba."What's going on?"Suka jiyo Mom.

     "Mom he took my pancake and I took it back"

     "You should have made more of it,let him eat it then I made you another"

       "What! I spent an hr preparing it and you're telling me to give him"

     "Zakia I said I will  make you another"

      Yadda Mom ta d'aga murya yasa Zakia taji kuka ya zo mata ,plate d'in ta dire ta tafi tana kuka.Amjad take ya hau murmushi ba tare da Mom ta gani ba ko a jikinsa ya d'auka ba ko kunya ya cigaba da ci.

               ★★★

    Duka yaran suna tsakar gida yau ba islamiyya Mami tana d'aki sega yaro ya shigo yake fad'a masu ana sallama a waje.Da Maryam ta le'ka taga driver nasu Dad ne,kaya me yawa taga yana cirowa a bayan mota.

     Mami tana zaune taji ana shigo da kayayyaki,buhunhunan  shinkafa ne da jarkokin mai da sauran stuffs lodi-lodi sun cika tsakar gida,farinciki a gun Mami baya misaltuwa,drivern be jima da tafiya ba ta kira Dad tayi masa godiya,nan yake fad'a mata sun kusa komawa Canada.

     Amjad ba 'karamin dad'i yaji ba sanda Mom ta fad'a masa saura 2days ya rage su tafi,a ranar ya kira Rosie ya sanar mata da dawowarsu.

   Mom da Zakia se Dad sune suka zo gidansu Laila sukai sallama ana gobe tafiyarsu ,washegari 9am flight nasu ya tashi.

       Yanzun yaji sa'ida a ransa yana tsarawa shida ya sake zuwa Nigeria kuma ...musamman idan aka ce ya fara aiki bashi ba zuwa Nigeria (A tunaninsa).

     Mami washegari ta kirasu tayi musu ban gajiya.Zakia basi ko kwana uku ba sukai resuming school komai ya cigaba da kasancewa kamar yadda yake Amjad ya d'ora inda ya tsaya tonight ya shirya wajen zuwa 11:pm   birthday partyn d'aya daga cikin friends d'insa.Bayan kowa ya kwanta ya salalla'ba ya fita a hanya friends suka d'auke shi suka wuce wajen partyn.
 
    
    Mom kamar ance tashi ta farka daga bacci 12:36am ,kitchen ta shiga ta sha ruwa bayan ta fito kuma ta nufi d'akin Amjad a zatan ta ko zata ganshi yana chat amma taga wayam,datai knocking bathroom taji shiru take zuciyarta ta bata ya fita.Bayan ta koma d'aki ta d'akko wayarta ta kirashi amma shiru beyi picking ba, ita damuwarta kar Dad ya duba ya gano baya nan.Haka ta kwanta tana ta addu'a a ranta kar Dad ya duba d'aki idan ya tashi.

STORY CONTINUES BELOW

      Amjad a wajen partyn ya manta wayarsa a mota ,wajen se hayaniya ne da kid'a yake tashi guys and ladies ana ta chashewa.

       "Hi Am" Yajiyo muryar wani classmate nashi da ya dad'e be had'u dashi ba,yana daga cikin trouble makers na school d'insu.

      "Hello" Ya amsa shi.

      "How have you been?"

       "Fine"

       "That's cool is good seeing you around"
    
        Yana daga zaune guy d'in yasa aka kawo masa 2 glass of beer .

      Guy d'in daya kar'bi d'aya ya mi'ka wa Amjad.

     "No" Ya fad'a yana girgiza kai.

      "Come on it taste good"

       "I don't drink"

        "Try a little dude"

        Nan ma kai ya girgiza,yana sake matsar da cup d'in gefe.

       D'an murmushi guy d'in yayi tare da d'aga cup d'in ya shanye tass,ba jimawa ya tashi ya bar gun Amjad daya dubi agogon hannunsa yaga 1:12am,koda ya duba wajen yaga bega Sam ba.

     "Hello" Yaji muryar mace.

     Yana d'ago kai yaga be santa ba ma."I'm Lucy "Ta fad'a tare da mi'ka masa hannu suka gaisa.

     Apple juice tasa aka kawo musu two  glass cup ,da farko beyi niyyar sha ba amma da ta takura yasha ganin Apple juice ne,kuma yaga yanayinta batai kama da bad girl ba.

     Kad'an -kad'an tana masa tambaya shikuma yana amsata,sede fa ya fara jinsa a gajimare wani irin yanayi yaji shi komai ya fara koma masa upside down.A hankali ya mi'ke yana dafa table.

   "Are you ok?" Ta tambaya tana masa wani shu'umin murmushi.

     Ko amsa mata ya kasa yi se tangali yake yana had'a hanya 'ko'kari yake ya fita amma ya kasa."Amjad "Ya jiyo  Sam ya kira shi.

     " Are you drunk?"Ya dafa kafad'arsa.

      "What did you do?" Ya tambayi yarinyar dake kusa da Amjad.

      "Hey she do nothing, your friend is drunk drag his ass and f*cking leave" Guy da ya zauna kusa da Amjad d'azu ne yake fad'in haka.

    Dariya suka saka wanda suke wajen dan da 'karfi yayi maganar.

     "You have something to do with this I know you fucking asshole"

      "You called me ashole who do you think you're?" Guy d'in ya fad'a yana bangazarsa kamar zey dokeshi.

     "Let's go" Cewar Amjad a cikin muryar maye.

     "This is his first time to drink" Guy d'in ya fad'a yana smirk smile.

    Dariya wajen ya d'auka wasu suna ihu Whoa!👎haka Sam ya jashi  suka fice daga wajen.Tsoron saukeshi ya shiga yi kar Dad yace dashi aka basa,hakannan ya samu ya kaishi gida.

   2am suka ji ringing na door bell,Dad da Mom suka farka a ranta tana tsoron abinda zey faru.

     Tana biye a bayansa ya bud'e dan shi kanshi yasan ba lafiya ba a wannan lokacin ayi knocking.

    "Amjad!" Ta fad'a tare da rife baki.

    "Sam what happened to him?" Ta tambaya.

     Dad dayai tsaye yana jiran amsarsa dan tuni zuciyarsa ta fara ayyana masa.

STORY CONTINUES BELOW

     "He ..he's drunk" Ya fad'a cikin stammering.

      "Oh god! Amjad, he don't used to.."

       "Quite please, how sure are you huh?"

     Be ko jira ta bashi amsa ba ya koma d'aki ya barta a nan,da taimakon Sam  suka kai shi har d'aki, bayan nan yayi mata bayanin duk abinda ya faru tukun ya tafi.

      Zama tayi daga gefen gadon ta cire nasa takalmin 'kafarsa da suit na jikinsa ta hau shafa gashin kansa mey she'ki "Amjad why do you have to,your Dad is mad at you now"

   Se wajen 2:40am ta koma d'aki ta tarar Dad ya kwanta."Honey you are not supposed to.."Be jira ta 'karasa ba ya juya mata baya.

    Hakannan ta kwanta da damuwa a ranta tana tunanin ta yadda zata 'bullo wa ala'amarin.

               ★★★

     7:30am ta farka bayan komawa baccin datai taga Dad har ya fice,wayarta ta d'akko ta kirashi amma shiru be d'aga ba se text ta tura masa.

      "Honey please pick my call"

        "I will pick your call but you have to promise me that you won't talk about him"

     Ba yadda ta iya haka tayi reply da "Yes I promised"

      Se lokacin ya amsa wayarta gaisawa kawai sukai ta katse wayar jikin a sanyaye dan tasan halinsa shi idan akai masa lefi shikenan kuma baya ta'ba bari a sake magana akan abin koda kuwa ya ha'kura.

     D'akin Amjad ta shiga taga ya tashi harma yayi sallah.

    "Morning" Ya gaisheta.

     "Morning, Son your Dad is   mad at you he won't allow me to talk to him about it"

     Kansa ya sunkuyar ya'ki cewa komai  yasan kome ya faru shi ya janyo.

    "Mom I really doesn't mean to do it"

     "You don't have to explain Sam told me everything,but you have to be very careful son"

     "It won't happen again"

      "I hope so"

       Hakan yana d'aya daga cikin abinda yasa yafi damuwa da Mom domin kuwa tana saurin fahimtarsa.
 
       Yau through out haka Amjad ya wuni be fita ba dan har yanzu baya jin 'kwarin jikinsa dan a yanzu ma da yasani yake na zuwa,wajejen 5:30pm Dad ya dawo sam be tambayi inda Amjad yake ba balle ma yayi maganar jiya.Koda lokacin dinner yayi Amjad se d'ar-d'ar yake dan kasa sakkowa yayi cin abincin seda Dad ya tashi.Haka the next day ma dan ya had'u dashi sanda ya shiga kitchen amma bece masa uffan ba,shi kanshi Amjad be zaci haka ba dan  a ganinsa babban laifine da be ta'ba yin irinsa ba wanda beci ace ya 'kyalesa ba be d'auka a iya shunning abin ze tsaya ba.

     An jera kwana hud'u ana haka idan ya gaisheshi baze amsa ba ya samu chance d'in bada ha'kuri ma ya kasa samu.

     8:23pm dukansu suna dinning, shiru wajen ya d'auka ba me cewa komai.Amjad yana sane ya soma amfani da hannun hagu yana cin abincin,Dad ko magana beba kuma ya kula dashi.Suna cikin cin abincin ne Amjad yasa Zakia ta mi'ke masa salt se yaga Dad ya bashi,bashi kad'ai ba hatta mom dasu Shaheed seda suka kallesu suna mey mamaki.A sanyaye ya kar'ba a ransa yana mey tunanin dalilin Dad na yin hakan.

      Ba Amjad ya tashi yin mamaki ba se sanda yaji alert na $500 gashi 'kiri-'kiri Dad ne ,shiko mey yayi wa Dad na kirki daya  saka masa da wannan shida yayi laifi.

      Da safe bayan sinyi breakfast ya samu Dad yayi masa godiya.

      "Don't worry you deserved more than this" Abinda ya fad'a kenan yana murmurshi.

     "Dad,am..am sorry"

      "Stop apologizing I understand everything"Yana gama fad'in haka ya bar Amjad a tsaye ya rasa abin yi .

     " We need to talk "Dad ya fad'awa Mom da take zaune a sitting room.

     A d'aki tana kan coach jira take ya fara magana,shikam yana daga tsaye saitin window yana nazarin ta inda ze fara.

     " Rushda ,you need to understand all I have to say and want am willing to do"

    Jitai jikinta yayi sanyi jin irin lafazinsa,daurewa tayi kawai ta gid'a kai tana jira ya fad'i abinda yake shirin fad'a.

     "He is no more child,he has to change he's almost 27 I can't keep eye's on him just like that I need to stop him I want him to stay away from those bad friends of his"

     "Tell me,what are you trying to do?" Ta tambaya cikeda 'kosawa.

      "Don't you think it's the right time for him to marry?"

      "Marry! To who?" Cikeda rasana tayi tambayar tare da mi'kewa tsaye.

      "Laila"Ya amsa a ta'kaice se lokacin ya juyo.

       "You want her to stay here with us?"

        "No,Amjad "

         "He is moving to Nigeria,I want him to run my Company"

       "He can't stay there" Bata ma san lokacin da ta fad'i haka ba gabaki d'aya ta rud'e.

     "No he can"

      "Amjad is too young to hold responsible for.." Bata 'kare maganar ba ya katse ta da fad'in."But he is too big to drank,is that it?"

     "Why won't you believe ?Amjad didn't drank someone forced him to"

     "Then I want him to avoid them"

    "By forcing him to marry?"

    "This is for our on good, he won't regret marrying her I'm telling you this or do you want your child to marry Christ,Rosie  is not the kind of woman you want your child to marry right?"

     Kai kawai ta girgiza a hankali.

    " Don't you like Laila ".
    "It's not that I don't like her,I just don't know how Amjad is gonna take this"
Yanda tayi maganar a hankali kamar rad'a dan nauyin zancen take ji.

     "You have to convince him,pray for him"

     "Amjad" Ta furta sunanshi a hankali tare da komawa kan coach d'in ta zauna ta dafe kai kamar mey jimami.
           
      "Can you talk to him?" Ya tambaye ta.

      Seda ta jima tana nazari kafin ta gid'a kai "yes".Tasan gwara ita tayi maganar da ace Dad wata'kila ko yafi fuskantar zancen.

     Kusan ranar wuni tayi ta kasa sukuni abinci ma ta kasa ci gashi ta  kasa yi masa maganar,tana kitchen ta ziba tagumu ga glass cup na juice da'kyar take kur'ba.

     " Mom"Ya kira sunanta.

     "Mom,are you ok?" Se lokacin ta dawo saga duniyar tunani.

    "Amjad, am ..am ok"

     "Are sure?"

     "Am fine" Ta fad'a,a ranta kuwa tana tunanin ko tayi masa maganar...

Amjad siblings at side

     Mom sam ta kasa fad'a masa har 9pm,seda ta gama tsare-tsarenta tukun ta nufi d'akinsa.Yana daga zaune  ta iskeshi bayan ta shiga d'akin.+

     "Mom" Ya kira sunanta fuskarsa d'auke da murmushi.

     Gefensa ta zauna tana masa murmushi daga bisani kuma tace.

    "Son"
    "Yes"

     "It's about the company, your Dad.. your Dad really need someone to run his company,Mr Yusuf(RAZAK's company manager) is too old to handle the company..."Bata 'karasa ba ta tsaya.

    "So what is he going to do now?" Ya tambaya ba tare da ya nuna wani damuwa ba.

   "Amjad you like the company, don't you want to..."

    "No no! This is bad idea beside it's not even possible I'm living in Canada how do you expect me to run the company"

    "Nothing wrong here,you're going to build a  better  life there and .."

   "Please stop all this jokes"

   "I'm not joking Amjad, you're not staying alone there,it's the right time for you to marry "

    "Mar..marry ? I ,for god sake ! Stop it please I am just 2..6 " Yadda ya fad'i 26 d'in a wani rarrabe.

   "What wrong with that ? It's not the matter of age ..."

    "I'am not ready,this is a fairy tale"

     "If you can't do this for me then do it for your Dad,please don't say no to him accept Laila even if  you're not going to move to Nigeria"

    "What! Did you just called Lai..wait Dad..he want me to marry what he has chosen for me and again he want me to run his company ,so this is the reason why he has been nice to me just because he want something in return"Wannan karan ya mi'ke daga zaunen dan yaga abin nayi ne.

  " You proved him wrong"

   "He has no right to force me marry who I don't even know"

    "No you're mistaken, Laila is your cousin sister you're familiar with each other"

    "No way,I just heard about them but I can't recognize them at all"

    "Laila, mustafa's daughter your late Uncle she is his first child"

    "I don't need any explanation please I want to be alone"

     "You're sending me away?"

      "Please Mom, I can't bear this it's too much this is not fair"

      "Amjad"

       "Please!"

        Daga haka bata sake cewa komai ba ta fice ta barshi da jimami,ya rasa inda zesa kansa daga ya zauna seya mi'ke daga baya ya zira jacket ya fice daga gidan.

                ★★★

    10:12am,su Maryam suna Makaranatar boko Laila ce kawai da Mami a gidan lokacin  ta gama aikin gida ta shigo sitting room ta zauna Mami na daga gefe.

     "Laila d'azu kinji ni ina waya koh?"

      "Eh"

       "Kawunki ne na waje, nide se naga kamar akwai maganar daya ke so yayi amma ya fasa"

     "Tohh,alamu kika gani?"

     "Ehyi bayan mun gaisa ne naji kamar zey sake wani maganar kuma ya fasa bande san dalili ba"

STORY CONTINUES BELOW

     "Koma meye de zakiji inde har ze fad'a d'in"

      "Uhmm"

    2days later,Amjad tun lokacin da Mom tayi masa maganar aure shikenan ya dena zama a dining cin abinci zaman living room ma ya dena yana d'aki koda yaushe inde ba fita yayi ba.Dad ma ko gaisawa basa yi dashi ,bayan da Mom tayi masa bayanin yadda ta kasance shima yayi nashi 'ko'karin dan yaga ya shawo kansa amma Amjad yayi kicin-kicin besan zance ba dan 'kiri-'kiri ya fad'a masa shi baze auri wacca baya so ba asali ma Rosie ce wadda ze aura.

Amjad

     Knock! Knock!
        
     "Come in" Ya fad'a kamar baya son yin magana.

       Waiwayowa yayi domin ganin mey shigowar ,ganin Shaheed ya maida kansa ya sunkuyar.

    Gefensa ya zauna tare da d'ora hannunsa kan kafad'arsa.

     "Bros ,everything is gonna be ok"

     "Ok? Really"

     "We are so worried about you,we missed having fun together it's boring "

     "Are you blaming me for that? he is trying to force me ,force me!"

     "No one can force you to marry you know, marrying Laila doesn't mean it's the end of the world,just do this for Dad ,Nigeria is not that worthy bad you're expecting .

     "What about Rosie? You want me to breakup with her just because I'm forced to marry someone"

     "No you're not going to breakup with her, if only you will accept to run Dad's company then you have nothing to worry about because you will get the chance to be with Rosie remember you're on your own Man! no one will  treat you like  a child again,do you gerrit?

    Bece komai ba sede fa zancen Shaheed yaso ya shige shi,yasan a lokacin da aka ce ya zama CEO  plus married man bame kuma sake controlling d'insa ze samu damar yin duk abunda yake so baya tare da Dad balle ya tsawata masa ,Rosie d'insa kuwa suna tare ita kuwa Laila oho by the time ta gaji ....

    " Amjad "Shaheed ya katse masa tunaninsa.

     " Huhhn"

     "What is your decision?"

     "Leave me  I wanna be alone"

      "Think about it"

       "Then you allow me"

       "Ok I 'm leaving,goodnight"Yai tapping shoulder d'insa tukun ya fice.

    Mom tana hangoshi sanda ya fito daga d'akin Amjad,dan tana ji kamar ta shiga d'akin sede kuma bata da courage.

   Daren ranar zancen Shaheed dashi yayi bacci ,washegari kuwa da wuri ya farka ba kamar koyaushe ba da seya yi sallah a makare.

      " Yes /No yes/no ... Shi kad'ai  yake zancen sa,daga baya ya tashi ya ciro paper da pen ya raba gida shida,uku ya rubuta yes uku ya rubuta No.A tafin hannu ya ziba su duka bayan ya nannad'esu seda ya gaurayasu tukun ya zibesu 'kasa.He has to choose one in 6 papers amma seda ya shafe 5min tukun ya d'auka d'aya.

     A hankali ya bud'e inda yayi tozali da "No" instead yaji sanyi a rai seya sake shiga confusion, wani idea d'inne ya sake zuwan masa. Rose flower ya tsinko dake a garden ya komo d'aki nan ma one by one yana cisge slide d'in Yes,No, yes ,No..haka yai tayi 'karshe de ya 'kare a Yes more confusion ya hau shi.

     Tattare tarkacen paper da flower d'in yayi ya zibar a dustbin ya komo ya kwanta kan gado.Gam ya rufe idanuwansa yana tunano sanda suka je gidansu Laila shi sam ya kasa tuna exact face d'inta be ma tabbatar da wace babbar ba shide yasan yaga yara sunzo sun gaidasu amma be sheda kowa ba ,tuna wacce ta bud'e masa 'kofa ya shiga yi nan ma de kad'an-kad'an ya tuna kamanninta."Is she the one?"Ya tambayi kansa.

STORY CONTINUES BELOW

       "What is about to happen? It's too early to marry,how could I even marry the person that I don't love, I don't recognize, we never had a word with her,did she agreed to marry me?" Haka ya 'karaci sambatunsa daga baya ya sakko zuwa kitchen dan yunwar data dameshi.

     Komai da sauri-sauri yake  ba nutsuwa a tattare dashi garin haka plate ya su'buce daga hannunsa tass! Mom da take d'aki tayi sauri ta sakko zuwa kitchen d'in.

    "Are you ok?" Ta 'karasa inda yake.

    "Yes" Ya amsa.

     "Amjad you're mad at me,you don't even want to talk to your Mom"

     Daya d'ago da idonsa ya kalleta sosai fuskarta ta nuna damuwa a 'yan kwana biyunnan hadda rama tayi.

     "Mom" Ya kira sunanta bayan ya 'karasa gab da ita.

    Hannunta ya ri'ko a nasa yana murzawa smoothly "I don't wanna see you in such condition"

     "Son I really care about you.."

      "And you want to send me away"

      "No we are not sending you away,we will be able to visit you and  same to you ,you're going to live a happy life there"

     "With the woman I don't love?"

      Mom ta zama speechless bata ce ko 'kala ba jin abinda ya fad'a.

                   ★★★

    2 month later

         Laila! Laila!
        "Mami gani fa" Ta fad'a tana 'ko'karin zipping hand bag d'inta.

       "Kina ji ina 'kwala   maki kira yanzu fa 5:30pmm ya kusa amma baku fita daga gidannan ba se 'karfe nawa kike so ku dawo?"

   "Bafa nisa daga min bada zamu komo"

    "Toh gidan Anty bilkin bazaki ba?"

    "Gobe..."
     "Kullum zancen kenan ,ki tabbata kinje zanyi mata waya ma idan baki je ba zata fad'amin"

    Tana chono baki suka fita daga gidan da'kyar ta iya fad'ar mun tafi,Maryam na biye da ita.

      Ba jimawa suka tsari d'an sahu zaman kurame suka yi bame cewa komai Laila da take gefe tana kallon waje amma hankalinta baya gun ta tafi duniyar tunani.
   
      Flashback★

       "Amjad ,d'an Kawu Abdallah"
       "Mami wallahi bana son shi,auren dole ne fa wannan dan Allah mami kice musu bana son shi"

     "Badan ni ba Laila,saboda mahaifinki kina ganin idan yana raye zai ji dad'in haka?d'an uwanki baze cutar dake ba.."

    " Kuka nake kamar raina ze fita amma bame saurarona ,na fad'a wa mami bana sonsa amma ta'ki fad'awa Kawu,auren dole shi suka za'bamin,auren wanda besan daraja ta ba,auren wanda baya sona,shin da gaske sena aure shi? "

STORY CONTINUES BELOW

       Kayan d'inki zata kai na biki shima seda Mami tayi da gaske tukun ,Anty bilki sister mami ce ta iya gyaran jiki har yanzu ta'ki fara zuwa idan ta fita setace zata biya seta dawo gida Mami taji ance bata je ba,4weeks ya rage biki duk daren duniya seta zubar da hawaye take bacci ga ramewa da tayi kamar mey rashin lafiya.

              ★★★
  
         Dawowarshi kenan daga gym ,be tsaya a ko ina ba ya shige d'akinsa.

    Ring! Ring ! Wayarshi yayi k'ara "Babie" ya gani a jikin screen.

     Ba tare da 'bata lokaci ba yayi picking, kwata-kwata Rosie bata san wani maganar aure da Amjad ze ba ko Sam be fad'awa ba ya hani Shaheed daya fad'awa wani wanda yasan shi saboda haka ba wani wanda yasan da maganar aurensa.

      Bayan ya gama wayar ne ya lura da Mom tsaye wadda besan da shigowarta ba.

  "Mom"
   "Did you talk to your Dad?"

    "Yes he told me"

      "Is't ok for you?"

        "Yeah ,what about you?'

         "Sure,were you able to talk to her?"

          "Ye..yes" Yayi 'karya.

           Anfi 3weeks da bashi number na Laila amma ya'ki kira,yanzun ma gajiya yayi da ce mata a'a shine yayi 'karya.Mom kuwa ba 'karamin dad'i taji ba daya ce ya kira.

     "Good"

      "If you need something let me know ,ok?"

       Kai kawai ya kad'a ba tare da yace komai ba.Tana fita ya d'auka phone d'insa,ya manta wani sunan yayi saving number d'in ma.

      "Nigeria" Ya gani lokacin da yake dubowa.Da yayi kamar zey kira seya fasa daga baya ma ajje wayar yayi gefe.

  
                ★★★

    Yau de anci sa'a ta biya gidan Anty bilkin,tana dawowa gida ta shige 'kuryar d'aki tasa kuka.Mami tana jiyota daga tsakar gida tayi banza da ita,har bayan isha'i tana d'aki sallah ce kawai take fito da ita.

    Itan ma idan Mami ta tambayeta sunyi waya da Amjad setai 'karya tace eh.
    Nusaiba da Fauzan basu da hira se bikin Yaya,ba wanda ta fad'awa maganar bikin hatta 'kawarta bata sani ba islamiyyar ma bata fiya zuwa ba yanzu.

      A kwana a tashi har an shafe 2weeks ,yau su Mom suka duro Nigeria Zakia se murna take wani abun ma da biyu take,shide ko 'kala baya ce mata dan yanzu seya wuni bece da wani komai ba balle har ya taya mutum ma siyi fad'a.

      Amarya Laila abu kad'an aka yi se tasa musu kuka Mami abin ya isheta taga da gaske take ,sam ba yin kanta bane tilasta wa Laila auren Amjad  kawai de bazata iya cewa Dad no ba banda Kawu yunusa da shi yazo da maganar ma tana ganin idan ta'ki kamar bata kyauta ba.Kuma tabbas Dad da aansa ya fad'a mata 'kw'k'kwaran dalilin yin hakan,yana ganin shi yayi nisa da danginsa wannan damar itace zata sa zumunci tsakaninsu ya sake 'kulluwa.

      Laila ta sake yin kyau sosai duk da ramar da tayi,tana ji mami tana waya dasu Mom suke fad'a mata sun iso Nigeria.

      Rabon invitation ma se Maryam ce tayi da Nusaiba dan gabad'aya Laila ta lanjare musu duk wata hada-hadar biki ba ita a ciki.Dad yasa an gyara musu gidansu yayi kyau sosai kamar sabo.Kud'i mey tsoka Dad ya bawa Mom ta bawa Amjad domin yiwa Laila siyayya a yadda suka tsara tare da Lailan zasu amma yayi burus shi beje ba kuma be kira ba.

      Mansion babban gaske Dad ya bashi kyauta duk dan ya faranta masa amma ko a 'kwalar rigarsa.

     Kaya na musamman Mom ta aikawa Laila na fitar dinner,fafur tayi ita bazata saka ba ai bata rasa kayan sawa ba seda mami ta tsawata mata.Sukad'ai suke rawarsu su taka Maryam ,Zakia da Nusaiba.Ana gobe dinner ya kira wayarta,tana cikin hayaniya 'Yan kwanan biki se surutu suke wayar ma bata san inda ta yar ba.Sau biyu ya kira ganin bata  d'aga ba besa ya damu ba dama haka yake so.

STORY CONTINUES BELOW

     "Ta zama ta zama d'akko hula" Suka hau yi mata wa'ka.

    "Mtcchww! Hular uban wa?"Fuu! ta wuce ta barsu da sakakken baki.

     Ba ita ta duba wayar ba se wajen 11:30pm taga 2missed call da ba'kon number haka yasa bata damu tai call back ba tayi kwanciyarta.

                ★★★

   6:00am hayaniyar Zakia ne ya tasheshi." Hey wake up it's you wedding day"

    "Get out!"

    "1..2..3 flash na camera ya haske masa ido." Shaheed,stop it"

    "It's your wedding day"

     "So what?"

      "Have a look at this" Ya nuna masa galleliyar shadda fara da aka d'inka  na dinner wanda besan da ita bama.

     "What is this?"

      "It's yours,dinner dress"

      "Babban riga"Cewar Zakia tana dariya.

     " Fools leave now!"

      "Don't you like it?"

       Be amsa su ba ya shige bathroom ya doko 'kofar,a wardrobe sika saka  tukun suka fita suna dariya.

      Ta 'bangaren Laila kuwa ko breakfast bata samu tayi ba 10am suka fita gidan 'kunshi ita da Maryam.Jan lalle akai mata shima d'in bata bari yayi ja sosai ba ta wanke ba yadda ba ai da ita ba amma ta'ki ji,ba'ki kuwa tace bata so Maryam tana ji tana gani aka hanata ba'ki se jan ta samu itama aka yi mata amma yafi na Laila turuwa.Daga gidan lalle suka juyo gida.

     "Ina 'kunshin yake?" Mami ta tambaya.

      "Gashi" Bako kunya ta mi'ko hannun.

      "Yanzu wannan shi kike kira da 'kunshi,shi kuma ba'kin fa?

     " Mami wallahi wankewa tayi kafin yayi,ba'kin kuma ta hana ayi mana "

    "'Karya take.."

     "Sena doka miki ta'baryarnan akanki idan baki rufen baki ba sakarya,ki nuna wa duniya cewa ba'kyason auren sesi maganin hakan kinji" Mami ta fad'a cikin 'bacin rai.

    Daga mami se wasu 'kannenta biyu a tsakar gidan sauran ba'kin suna d'aki."Ke Laila meyasa kike haka ne,so kike ki 'batawa mahaifiyarki rai?"Wata 'kanwar Mami ta fad'a.

     Kai ta girgiza alamar "a'a hawaye suna biyo kumatunta se murza yatsa take ta sunkuyar da kai.

     " Toh kidena irin haka kinji koh"

     A hankali ta gid'a kai dan bazata iya magana ba,d'aki ta shige ba mutane da yawa  ta juya bayanta ta dasa sabon kuka dad'i da yunwa da take addabarta rabonta da abinci tun jiya da rana taci abincin kuma ta'ki.

       9:12pm an gama tsara mata make-up tayi had'uwa iya had'uwa tasha farar gown se walwali take ga sar'karta mey farin stones ,tasa hill shoe tunda take bata ta'ba sa hill shoe kamar wannan ba se tsoron mi'kewa take,daga ita se Bahijja 'kawarta suna jiran ango.

        A wajen biki kuwa kowa ya hallara Zakia,Shaheed suna daga mota Maryam da Nusaiba duk sunyi kwalliya sun fito, Amarya da ango suke jira su iso su taka musu baya.Sun kwashe kusan 1hr a haka,Mom da Dad kuwa suna ciki dasu Mami.

    
       Mom fatan ta Allah yasa karya bata kunya dan sanda ta  fito daga gida ko kaya be ciro ba balle yasa.Ganin an sake shafe 30min basu ba alama ta kirashi shiru be d'aga ba.

      Driver dede wajen kwalliyar yayi parking kamar yadda Mom ta bashi address.Maimakon ya kirata da kansa a'a seya bawa driver wayar yayi mata magana.

      "Hello,madam gamu a waje da...da angon"

      Take bugun zuciyarta ya 'karu."Tir'kashi baze iya magana dani ba"Ta fad'a a ranta.

     "Ya?angon ne?" Bahijja ta tambayeta.
   
       "Eh" Ta amsa a sanyaye.

     Gwiwa ba 'kwari ta mi'ke,kafin su fita ta sauke mata net viel d'in a fuskarta,da'kyar take takawa saboda rashin sabo da takalmin me tsaho hakan kuma seyayi mata kyau  yanayin tafiyar.

      Driver ne ya bud'e mata gidan baya 'kawar kuma ta zauna a gaba ,shiru motar bame ko tari,ta kalli gefe ma ta kasa balle taganshi,'kamshin turare ne kawai yake tashi nata soft 'kamshi shikam 'karfin nashi tararen ya danne nata.Be d'ago ya kalleta ba dan wayarsa ce a hannunsa amma yana kallonta ta gefen ido fuskartace de baze iya gani ba,'kawa kuwa besan da zamanta a motar ba ma.

     Suna isa wajen Zakia suka fito se murmushi take ,ganin  Amjad sanye da babbar riga yasa su kallon juna da shaheed dan a zatonsu baze saka ba,basu san irin faman da Mom tayi dashi ba kafin ya yarda zey saka.

     "Handsome Amjad" Ta fad'a.

       Laila kuwa tana gefe separate da inda yake,Maryam da Nusaiba suma suka 'karaso wajen,se lokacin Zakia ta farga ashe fa ga amarya.Ri'ko hannunta tayi ta matso da ita gefensa daf,wata uwar harara ya galla mata amma tayi kamar bata gani ba Laila bata san ma yana yi ba.Shaheed a take ya Shiga yi musu pics kala-kala,seda suka tabbatar sinyi well arranged tukun Amarya da Ango suka shiga.

     "MashaAllah" Mom ta fad'a ta kasa dena murmushi.

       Mom dakanta ta d'age mayafin fuskar Laila ,nanfa akai ta pics  sede fa ba annuri a tattare da Amjad gara ma  Laila friends suna d'an sata murmushi,shi gabaki d'aya babbar rigarce yaji ta isheshi kamar ya 'kwa'be ga hula ma gumi ya tarar  masa a gashinsa.

      Taro anyi angama lafiya kowa ya tafi,driver ne ya kai amarya tare dasu Maryam Amjad kuwa su Shaheed ya bi Mom suka tafi da Dad.

     Yana isa gida ya yaye rigar tare da wurgar da hular gefe,yana yin shower ya kwanta sanda Mom ta shigo ta tarar har yayi bacci.

     Laila ko kayan bata gama cirewa ba  ta 'bingira bacci se cikin dare ta farka tukun ta cire.

       The next other day aka d'aura AMJAD da LAILA akan sadaki 100k,tun lokacin da aka ce an d'aura aure Laila take kuka har ta gaji da zubar ta hawaye se sheshshe'ka take,daga baya ma satar jiki tayi ta tafi gidan Kawu Yunus tayi kwanciyarta idan aka tambayi Nusaiba setace ta tafi chanja kaya.Seda Mami ta kirata a waya tukun ta dawo,nan yayyin mami suka yi mata nasu fad'a maimakon tayi kuka 'kandas dan hawayenta ya gaji da zuba sede kukan zuci.8:30pm aka kai Amarya kuka ba iya su Maryam ba hatta Mami ma,Laila (Taya za'a ce ita kada tayi,tell me how?)

Dijensy❤

Laila at side

      8:46pm,mutanen dasu ka kai amarya ba wani yawa ne dasu ba,cikin 'kan'kanin lokaci kowa ya kama hanya se Bahijja da Maryam su d'in ma ba zaman sukai ba 9:30pm nayi suka tashi zasi tafi,Laila se ro'konsu take kar su tafi dole ta ha'kura tana ji tana gani suka tafi.

       A take ta fara jin tsoro jin tsit,ganin da gaske ta bar gida ta sake saka wani kukan har seda ta gaji kanta ba abinda yake se ciwo.10:03pm ta gani lokacin da ta kalli agogon dake d'akin,se yanzu ta kalli ma irin d'akin ta waiwaya can ta waiwaya nan duk irin kyawun d'akin da kayan dake ciki ba birgeta yayi ba komai duhunsa take gani,ganin lokaci yana sake ja ta tashi.'Kofa data gani daga can side na d'akin ta nufa ,koda ta murd'a taga  bathroom ne 'kayatacce,seda ta dawo ta bud'e wardrobe ta dubi wata doguwar riga na bacci har 'kasa ta d'akko.

      Hijab ta soma lalubowa amma bata gani ba,wani mayafi ta samu mey d'an nauyi ta d'akko ta shiga bathroom, bayan data samu gu ta sa'kale kayan seta tsaya dube-duben bucket na wanka.Babu shi ba alamarsa haka buta ma balle kuma mod'a.

    "Mtchww!" Tayi tsaki.

   Jacuzzi ta tsirawa ido tana tunanin ta ina zata soma amfani dashi, bathtub d'in ta samu ta 'ko'karta ta had'a ruwan  tana la'kai-la'kai kamar bazata shiga ba,se can ta samu ta shiga ,d'aya daga cikin shower gel d'in ta d'akko da sponge tayi  using, se bayan 17min tukun ta fito already ta zira rigarta sauran kayan kuma ta ninke su tasa a wardrobe.

    Kan mirror ta duba wayam ba kayan shafawa,se can data duba drawer tagansu a jere.Mayukane wanda bata ta'ba shafasu ba,d'aya-bayan d'aya ta bisu tana karantawa yawanci lighten lotion ne da'kyar ta samu wani mey dama dama tukun ta shafa  ita wai bazatai bleaching ba😂 komai ta maidashi muhallinsa ta dawo kan gadon ta zauna tare da d'ora hannayenta kan gwiwoyinta.Se yanzu tunanin wayarta ya fad'o mata ,mi'kewa ta sake yi ta bud'e wardrobe d'in daga 'kasan kaya ta d'akko ta kamar inda Maryam ta ajje mata.

    "Toh wa zata ma kira?" Ta tambayi kanta.

   Wata zuciyar tace kiyi game,aiko snake ta hau yi lokaci yana taja.

  Amjad

       Mom da ta shigo d'akinsa dan tana da tabbacin be tafi ba ,baki ta saki tana kallonsa yana kwance abinsa bacci yake kamar ba gobe.Ba halinsa bane bacci da wuri amma dan wula'kanci yau shine tun 9:30pm ya kwanta har 10:36pm.

     "Amjad"

      Seda ta 'karasa tai tapping shoulder d'insa tukun ya d'anyi motsi.

    "Amjad,wake up!"

     "Mom what?"

      "Do I have to tell you?"

        Yana la'kai-la'kai yatashi zaune,yana wani mirza idanuwa.

    "Amjad, do I have to tell you what to do ,it's almost 11pm.."

     "Mom you're sending me away,can't believe it you're sending your own son"

     "No I'm not, how will I send m beloved son away ?"

     "I'm tired I need to rest"

      "Rest!" Ta maimaita ,dariya ma abin ya bata tana kallonsa.

    "Your Dad doesn't know you're here"

     "I gerrit ,don't worry I'm leaving now"Ya fad'a tare da mi'kewa.

     Kallo kawai ta bishi dashi tana girgiza kai,watsa ruwa yayi ya fito ya saka wata black T-shirt mara nauyi tare da black jeans.Dad yana d'aki besan abinda ake ba har Amjad ya fito,Mom har bakin mota ta rakoshi su Shaheed daga nesa bakin 'kofa suna waving hand yadda sikeyi za'asan cewa na tsokana ne shide banza yayi musu Mom a cikin ranta tana jin zafin rabuwa da d'anta kawai de daurewa take.2

STORY CONTINUES BELOW

      Yana ji tana cewa ya gaisheda Laila amma yayi kamar beji ba ya shiga motar driver ya jasu
     Be bari ma ya shigo dashi har ciki ba daga bakin gate yace ya ajjeshi,a parking space ya tarar da Marcedes Benz black da Dad ya saya masa ,kallo d'aya yayi mata ya wuce ciki.
       Se yanzu ya sake 'karewa katafaran gidan kallo,direct room d'insa ya wuce wanda  yake opposite da Laila.
     Yana shiga ya bud'e wardrobe yaga neat kayansa da sauran abubuwansa ,komowa yayi kan gadon ya d'auki wayarsa ya soma Zombie kill (game),laptop d'in nashi ma ya mance a gida se yanzun ya tuna.
     Laila kuwa bacci yayi gaba da ita wayar ma a gefe ta yasar.
               ★★★
     6:23am,a gigice ta tashi daga bacci sakamakon mafarki da tayi tana kuka.Agogon d'akin ta duba taga har subh ya shige ,a kasalance ta mi'ke ta fad'a bathroom tayo alwala ta tada sallah.Bayan ta idar tayi azkar sannan taja jiki ta jingina jikin gadon tana tunanin sabuwar rayuwar data tsindima."Koh ni kad'ai na kwana a gidannan?"Ta tambaya a ranta.
      Amjad  a 'bangarensa kuwa bacci yake cikin kwanciyar hankali babu mey tashinsa yau.
     Se 8:16am ya farka daga bacci, se bayan ya idar da sallah ya tuna da zaman wata Laila,tunani ya shiga yi yaje ya dubata ko kuwa.Daga baya de ya yanke shawarar sauka downstairs.
     Laila daga d'aki tana jiyo 'karar rufe 'kofarshi,sad'af-sad'af ta tashi kamar wata mara gaskiya ta la'be jikin 'kofa tana jiyo takunsa har ya sauka.Hakan ya tabbatar mata anan ya kwana.Kitchen ya shiga dan neman abinda zeci ,seda ya gama dube-dube 'karshe de ya 'bige da tea da toasted bread dan shi ba gwani bane wanjen wani yin abinci hakan ma ba 'karamin dagewa yayi ba ya saba sede Mom ta had'a masa.
     Daga kitchen kuma ya fito harabar gidan ya zauna daga kan kujera dake kewaye da flower plants ,wayarsa ya danna wa Rosie kira karo na farko bata d'aga ba se ana biyu.
     Ita a tunaninta aiki ne ya dawo dashi Nigeria kamar yadda ya fad'a mata dan be gaya mata asalin gaskiya ba.
     "I missed you" Ta fad'a daga d'aya 'bangaren.
      "I missed you too"Shima ya fad'a.
      Yanda yake fara'a za'a San cewa ya mance da duk wani damuwarsa ,best moment of his life yaga yana hira da love of his life Rosie.
        
     9:30am ,yunwa ta fara addabarta harta kasa daurewa se shawara take kota fito,sede ita ganinsa ma bata son yi balle har magana ta had'asu.
     " Toh a ina zan samu abinci ma?"
     "Kitchen mana" Zuciyarta ta amsata.
     Dama mayafinta a yafe yake dan haka fitowa kawai tayi se sand'a take batasan ko ina ba ,'kofa dake opposite da d'akinta ta kalla se gefe ta hangi steps dan haka ta sauka 'kasa nan d'inma ta gama kalle-kalleta tayi can ta yi can har ta samu kitchen.Sosai ya tsaru ita kanta ya birgeta mug ta gani empty data duba taga alamar ansha tea dashi."Tea yasha kenan,dame ya had'a?"
      Ta'be baki tayi ganin ba mey amsa mata ta nufi fridge inda taga kayayyaki birjik se wanda ta za'ba amma ba'kunta tasa taji bata sha'awar cin kayan ,cikin locker ta hangi cornflakes ta had'a abinta ba wani 'kosar da ita yayi ba.
       Ta fito daga kitchen tana shirin komawa sama sega Amjad yana shigowa.Tsayawa yayi yana kallonta itama hakan daga bisani ta soma hawa bene kanta a sunkuye.
     "Hey"
     Chak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.
      "What is your name?"Taji ya tambaya.
      "Kutt! Raini" Ta fad'a a ranta.
      'Kin juyowa tayi har seda ya 'karaso inda take tukun ta juyo."I'm asking you,what is your name?"
     "Laila" Ta amsa ciki-ciki ba tare da ta kalleshi ba.

      "Why are you here?"Ya sake wata tambayar.
      "Nima ban sani ba" Yadda tayi maganar da sauri.
      Anzo wajen wannan yaren da baya son ji shi zatayi masa?
     "Talk to me in English"
      Yitai kamar wata kurma tana tsaye batace komai ba.
     "I'am talking to you" Yanda yayi maganar cikeda 'kosawa.
      Anfi 2min batace komai ba kuma bata tafi d'akin ba.
    "She don't understand English? fuck up!"Yayi maganar a hankali.
     Taji sarai amma tayi kamar bata fuskanci mey yake fad'a ba.
    " Aiko inde turanci ne ka dena jinsa inde kana nan,Hausa ce ba fashi"Ta fad'a a ranta.
     Wucewa yayi ba tare da ya sake wata maganar ba tana ji ya doko 'kofa.Itama d'akinta ta shige ta zauna wayarta dake gefe ta d'auka ta kira Mami.
     "Mami ina kwana"
     "Lafiya lau"
      "Ina su Maryam? Anjima zasu zo?
       " A'a suzo siyi miki meh? bade yanzu ba"Mami ta fad'a .
       "Mami meye a ciki idan sunzo"
      "Bafa zasu zo ba,ki gaida Amjad d'in ba'kina zasi tafi se anjima"
    Bata kuma wani maganar ba mami ta katse wayar.Wata 'kwallar takaici ce ta zubo mata ganin ba ta ita ake ba basusan halin da take ciki bama.
    Kuka ta shiga yi harda sheshshe'ka cikin 'kan'kanin lokaci tayi bacci.
     Bata yi 20min da kwanciya ba taji 'karar kid'a a gigice ta farka kanta yayi mata wani mugun nauyi zuciyarta na bugu da sauri-da sauri.
       Amjad da gayya ya 'kure volume d'in so yake kawai ya takura mata.
     "Innalillahi wannan yana kuwa da hankali?" Ta fad'a a fili.
     Baccin da batai ba kenan,tayi game har charge d'inta ya 'kare.Zama tayi-tayi har 'karfe 1pm tukun ta tashi tayi sallah,'kugin da cikinta yake ne yasa ta kasa sukuni.
      Dole ta fito ta sakko 'kasa kitchen, dube-dube tayi tayi a  locker bata ga komai ba har ta d'akko bread ta lura da wani corridor koda ta duba taga 'kofa tana bud'ewa taga kayan abinci taff a ciki.
     Nan da nan ta d'ibo dankali  ta fere a take tayi blending pepper cikin 'kan'kanin lokaci ta had'a faten dankalinta se 'kamshi yake ta cika 'kasan da 'kamshi.
      Stool taja taci abinta a kitchen ta kora da juice yanzun taji normal ,'yan kwanukan datai amfani dashi ta d'auraye.Tana fitowa daga kitchen kanta a sunkuye taji tayi tuntu'be da mutum.


    Ko bata d'ago da idonta ta kalleshi ba tasan waye dan haka ta matsa gefe ba tare da ta d'ago kai ba.+

      "Blind, watch out!"

       Wucewa tayi ta barsa a gun a ranta tana mey jin zafin maganar da yayi mata.Shikuwa daya shiga kitchen warmer dake kan drawer ya fara gani ,ganin abinda ke ciki yasa yayi wani murmushin gefen fuska a take ya d'auka ya nufi d'akinta.

     Knock! Knock!

        Take hantar cikinta ta kad'a ba tare da tayi tunanin hakan ba,batasan dalilinta na tsorata ba.Tana bud'e 'kofar ta ra'be jikin 'kofar tana sunkui da kai.

     "Look up,madam chef"

      Tana d'agowa taga food warmer dake hannunsa."Who do you keep it for? "

     Shiru ba amsa"Me?"Yayi pointing kansa.

      Kai ta girgiza alamar a'a."Then who? Pets ?"

     "Ni ba wanda na ajje wa"

      "Oh god!"

      "Look at me" Ya fad'a.

      "I said look at me"Ya sake maimaitawa.

        Tana d'ago da kanta ta kawar dan bazata iya had'a ido dashi ba." I.. don't.. understand... your.. language.."Yanda yayi maganar dalla-dalla.

     "Nima bana gane naka" Ta turo baki.

     "Ke?" Taji ya fad'a tare da nunata da d'anyatsa.

      "Ashe kana ji " Ta fad'a a ranta.

     Matsawa tayi daga pointing d'in da yayi mata ta kalli gefe.

     Phone Ring!
      "Mom" Ya gani a jikin screen.

      "Hello"Ya fad'a bayan tayi picking.

       "You don't even mind to call me""

        "No Mom"

         "How you doing?"

         "I'm doing good" Ya amsa.

          Ita de Laila komawa tayi kan gado ta zauna ta juya gefe ba tare da ta kalli inda yake ba,shikuwa yana tsaye har lokacin flask d'in yana hannunsa d'ayan hannunsa ya ma'kala phone a kunne.

   "Laila?" Ta tambaya.

    Seda ya d'au kusan 2min kafin yayi magana."She is doing ok"

Tana zaune taga an mi'ko mata waya."Mom"Ya fad'a yana binta da kallonta banza

      Cikin girmamawa ta gaisheta  tana gama wayar ta mi'ka masa."Gashi"Ta fad'a.

     Harara ya watsa mata kafin ya fisge wayar har farcensa yana 'ko'karin cakar hannunta."'Kasami"Ta fad'a a ranta.

    Kan gadon ya d'ora mata abincin "Finish it" daga haka ya fita ko 'kofar be rufe ba.

     "Ca akai ma ni mayunwaciya ce?" Ta d'auki flask d'in ta dire a 'kasa bayan ta rufo 'kofarta ta koma ta cigaba da aikin zama.

  
      Haka ta cigaba da zama har maghrib bayan tayi sallah ta tuno wayarta ba  charge,drawer ta dudduba ba alamar charger nan ma hankalinta ya tashi,ita de tasan wannan mara kirkin ba sauraronta zey ba.Flask d'in data dire a kasan ta janyo ta soma ci ko chokali babu haka taci dan bason sauka 'kasa take ba, kad'an ta rage ta tashi wanke hannu daga nan ta d'auro alwalar  isha'i. Tunani ta fara yi ko taje ta tambayeshi sede kuma tana tsoron wula'kanci,hakannan ta ha'kura da charge d'in wajen 9:14pm tai kwanciyarta.

STORY CONTINUES BELOW

Washegari**

        Da asubahr fari ta tashi bayan ta idar tayi wanka tai shirinta cikin doguwar rigar atamfa blue me ratsin pink  tayi mata chif a jikinta d'ankwalin ma ba wani d'auri ta tsara ba ture kaga tsiya tayi ita kanta data kalli mudubi dariya ta shiga yi data kwance seta sake yi 'karshe de ta ha'kura ta barshi ,powder kawai ta shafa se kwalli data sa sosai tayi kyau ga humra data shafa mey 'kamshin gaske.

     Phone ce yanzu matsalarta game d'in da take d'ebe mata kewa babu,8:30am ta sauka zuwa kitchen.Store d'in ta duba tana shawarar abinda zata dafa,daga 'karshe de ta fere Irish potato ta d'ora frying pan ta fara suya.Jikin window ta koma tana jira ya soyu,tana hangen waje, garden ta gano yasha flowers masu kyawu luf-luf gwanin sha'awa sam ta shagala da kallon gurin musamman da taga tsintsaye na shawagi a gun.

     "Welldone madam Chef" Tajiyo muryar Amjad.

      Da sauri ta juyo har mayafinta yana fad'uwa da'kyar ta samu ta tattaroshi ta rufe jikinta tana sunkuyar dakai."Can't you smell?"

    Se lokacin ta gane dankali ne yake 'konewa,da sauri ta 'karasa gun tana 'ko'karin kwashewa a plate.Da sauri ya jata baya ganin mayafin ta na shirin shiga cikin man da take soya dankali "Watch out!"Ya cillar da mayafin gefe.

        " Toh shine kuma seka ciren mayafi!" Ta fad'a cikin fad'a cikeda tsoro.

     Sunkuyawa tayi ta d'auki mayafin ta yafa abinta ta koma gefe,dankali kuwa ya 'kone 'kurmus.

     "What are you waiting for?"

     Jin ya fad'i haka tayi sauri ta matso kusa ta kwashe dankalin,seda ta rage gas d'in tukun ta sake zuba wani, yana daga gefe yayi folding arms yana kallonta.

     "Nasty!"

      Banza tayi dashi a ranta tana fad'in"'Kwalelenka so kake kaci kuma baza ka ci ba"

     Fridge ya nufa ya ciro apple guda d'aya ya samu stool ya zauna daga nesa yana kallonta.

    "Why do you married me?" Ta jiyo tambayarsa.

     Ko 'kala batace ba tana juya dankalinta.How old are you?"
     Data gama kwashe dankalin seta tuna bata d'akko egg ba gashi yana kusa da fridge d'in amma hakannan ta daure ta 'karasa.Seda ta d'ebo guda biyu a d'an 'karamin bowl zata rife fridge d'in ya ri'ke mirfin.

    "Answer me"

     "Auren dole akai min"

     "Damn it!" Ya buga mirfin fridge d'in tare da mi'kewa tsaye,a take ta sunkui da kai ganin tsahonsa ya kere nata tana gudun karta ji saukar mari dan har yanzu taga ganin ba sanin halinsa tayi ba.

     "Look up"

     "Laila I'm talking to you"Ya fad'a da 'karfi ganin ta'ki amsa sa.

      A hankali ta d'ago amma har lokacin bata bari sun had'a ido ba."Speak in English"

     "Ni..ban ..iya ba" Ta fad'a dalla-dalla tana kallonsa cikin ido da ido.Ita kanta batai zaton zata iya ba.

    Ya d'an fahimci abinda take nufi sede be nuna ya gane ba harara kawai ya bita dashi yasa 'kafa ya fice.

     "D'an wahala,Alhamdulillah gwara da Allah yasa baka ganewa nima da hausar zanke ramawa"

     Nan da nan ta gama had'a breakfast d'inta, yau a dinning taci kayanta tana gamawa ta d'auraye kwanukan ta koma d'aki.

    "Ni ina zan sami charger?"

    Fitowa tayi ta sakko 'kasa living room ta duba ko zata samu charger nan ma babu.Ganin bata samu ba yasa ta fita ,nan taita kallon tsarin gidan,a haka har ta nufi garden data hango d'azu aiko ta samu kujera gun tayi zamanta se kalle wajen take.

       Yana kwance ya zira earpiece a kunne yana sauraron wa'ka yaji kamar 'kara,da farko ya share seda yaji da gaske de 'karar ce tasa ya zare earpiece d'in tare da mi'kewa ya sakko 'kasa jin 'karar daga waje ne yasa ya fito.Yana dube-dube a harabar gidan idonsa ya sauka a kan Laila da ta d'are saman mota kanta ko d'ankwali babu a kanta gashin kanta dake parke ya ware se 'kyarma take,mayafin kuwa yana 'kasa gefen tayar motar wanda bata san inda yake ba   se waige-waige take sam hankalinta baya jikinta, ba zato ba tsammani taga Amjad tsaye yana kallonta.

       "Mami"Sunan da take kira kenan idanuwanta ya cika da 'kwalla.

       " What is your problem? "
      "Lizard" Ta ta'be baki kamar zatai kuka.

     Dariya ce tazo masa amma seya basar ,ya zaci ko hausar zatai masa "So you can speak English clearly? Huh?"

     Har yanzu kyarma take,ita bata san lokacin da ta fad'i lizard ba ji tayi dama batai magana ba.

    Alamu yayi mata da hannu nata sakko daga kan motar amma tayi burus kamar bata gani ba.

    "Hey,don't spoil my car"

     "Toh matsa na sakko ,ko a kanka zan duro kana wani kallona sekace 'kadangaren" Ta fad'a a fili dan tasan ba ji zeyi ba.

    Maimakon ta sakko ta saitin daya ke a'a seta sauka ta d'aya side d'in ta zagayo ta d'auki mayafin se zazzageshi take.

      "what you just said in English"

      Da sauri ta d'ago taganshi ya tsaya a kanta "Toh d'an garin ga'ba-ga'ba"

      "Matsa min na wuce" Ta wani sha kunu.

      "You're sick" Ya harareta tare da barin gun.

Tana komawa d'aki ta cire kayan jikinta ta sauya wasu dan gani take kamar zata sake ganin 'kadangaren a jikinta.

      Da rana couscous tayi da miya yasha vegetables da nama tayi har dare iya cikinta .Shikuwa Amjad baya wani cin abinci mey nauyi daga madara seya d'ansha fruit ko cornflakes sam cimar ba dad'i take masa ba yayi missing girkin Mom girman kai bazesa yaci abincin Laila ba.

     9:04pm taji motsin 'kofarsa alamar ya fita daga d'akin,a hankali ta bud'e 'kofarta tare da fitowa.Handle d'in 'kofarshi ta murd'a ta shiga ,fasalin d'akinsa yayi mata kyau sosai ga wallpaper dake d'akin,se frames da pictures nashi dake manne jikin bango.Ganin zata shagala da kallo ta soma neman charger, drawer take ta dubawa na mirror daga baya ta dawo na gefen gado ,ba tare da tayi tsammani ba taji an murd'a handle d'in 'kofar.Kid'imewa tayi ta rasa yanda zatai,wani idea ne ya fad'o mata tayi sauri ta bud'e clothset ta shige ta rufo murfin tana tsima.

     Amjad daya shigo d'aki ganin duk abinda zeyi ya gama baze sake sauka 'kasa ba ya kulle 'kofar d'akinsa ,T-shirt  d'insa ya cire ya cilla su kan couch ya zauna daga shi se 3 quater.

Where did we stop? Laila..hihi!+

         Ring! Wayarsa tayi 'kara,koda ya duba yaga."Baby boo"

     Laila dake cloth set tana jiyoshi yana waya se soyayya yake sha da Rosie d'insa.An shafe kusan 40min har lokacin yana waya Laila ta soma gajiya ga bacci data fara ji.

       "Goodnight sweetheart"Daga haka yayi hanging.

       Wani munafikin tari ne ya turnu'ko a ma'kogoranta da sauri ta rife bakinta amma dukda haka seda ya ku'buce." Wayyo Allah"Ta fad'a a ranta.

     Jira take taji an bud'ota amma taji shiru sede ma duhu data sake gani ya lullu'be hakan ya tabbatar mata da kashe light d'in d'akin yayi,haka ta cigaba da zama lokaci yana sake shigewa a yanzu har 11:46pmpm shiru Amjad tuni yayi nisa a bacci.

     A tsorace ta bud'e 'kofar tana sand'a a daddafe take tafiyar dan ba gani take yi ba sosai tass! glass cup dake kan drawer hannunta ya ta'ba aiko ya fad'a 'kas.Amjad dake cikin bacci a firgice ya tashi tare da kunna light d'in d'akin.

      "You? What are you doing here?"Ya fad'a cikeda mamaki.

      Shiru tayi ta kasa cewa komai se waro idanuwa take gashi yana side d'in 'kofar fita.

     " When did you broke in my room just like that?"

     "I want to charge my phone " Ta fad'a tana sosa kai.

    "Charge?"

     "Uhm"

     "Find your way out"Ya nuna mata 'kofa.

     Sum,sum ta fita tana rufo 'kofar tace" Karka bayar".

    D'akinta ta shige disappointed, kayanta ta cire ta sauya da na bacci riga da wando wanda be kai ankle ba tayi kwanciyarta.
 
Washegari 10:23am

      "Kin sake kiran nata a kashe?" Mami ta tambayi Maryam.

      "Eh na sake kira a kashe"

       "Toh ko Amjad d'in za'a kira"

        "Toh ai baki da number shi"

       "Semi kira Mamanshi ta turo mini ko"

        "Eh"

       Mom ta kira bayan sun gaisa take tambayarta ta turo mata number shi.Kiran farko data kirashi be d'aga ba se karo na biyu."Hello"

      "Assalamu Alaykum" Tayi sallama.
  
      "Waalaikissalm"

      "Uh.m Mamin Laila ce" Ta fad'a.

       "I..ina..yi...ina kwana" Ya fad'a da 'kyar.

        "Lafiya lau,ya gida?"

        "Da lafiya" Ya 'kwa'ba hausarsa.

      Mami ganin ba iya Hausa yai ba yasa bata ja zancen ba ta tambayeshi Laila.D'akinta ya nufa ko knock beyi ba ya murd'a handle.Da sauri ta mi'ke daga kwancen da take "Your Mom" Ya bata wayar.

STORY CONTINUES BELOW

     Tana rawar jiki ta kar'ba tana fara'a."Hello Mami ina kwana"

    "Lafiya lau,ya gida"
     "Lafiya lau,yasu fauzan?"

       "Duk lafiya suke,meya sami wayarki?"

       "Uhn...charge ne babu"

       "Chaji? Toh ya haka?"

        "Eh babu irin nawa ne"

        "Kuma baki ko kira a wayar tashi ba"

        "Ina son na kira ,ina su Maryam yaushe zasu zo?" Ta chanja topic.

        "Tun yanzu,a'a se an d'an kwana biyu"

       "Mami dan Allah suzo ko gobe ne"

      " Zasu zo amma ba lalle goben ba"

     "Toh shikenan"Ta fad'a a ranta bata so haka ba.

     Hira kad'an sukai tukun sukai sallama,se bayan ta gama wayar ta lura ya fice.Wayar tabi da kallo kafin ta murd'a handle zata mayar ,Ring!Ring kira ya shigo.

       " Baby boo❤"

       "Baby boo" Ta maimaita sunan a ranta.Ganin kiran ze katse ta 'karasa 'kofar d'akinsa tana shirin murd'a handle ya riga ta bude'wa.

      "Gashi" Ta mi'ka masa tayi sauri ta koma.

     Ganin Rosie ce ta kira yasa ya saki murmushi ,dad'i yaji sosai dan ya tabbata ta ga sunan.

   Laila sam bata ji wani haushi ba kawai de takaicinta d'aya shine zama da take haka ita d'aya wanda batasan 'karshensa ba.Kwanciyarta tayi ta rufe idanuwanta dan bacci ya fiye mata wannan zaman shirun.

               ★★★

     Laila tsakaninta da Amjad har yanzu kallo ne ba wani abu dake had'asu,yau aurensu kwana takwas kenan ,Amjad yaje gida so d'aya driver da Dad ya kawo masa yace baya so da kansa yake driving motarsa dukda dama ba wani fita yake ba sede restaurant wani sa'in yana zuwa ya siyi abinci.

      Knock!knock! Ta jiyo tana kitchen."koh waye?"Ta tambayi kanta dan Amjad yana gida,ajje yankan carrot d'in da take yi tayi ta fita bud'ewa.

      "Maryam!" Tai hugging d'insu tare da Nusaiba tana tsalle.

      Lokaci guda farinciki ya dabaibayeta,ta kasa komawa kitchen d'in ma dama bata d'ora abincin ba.Ji take kamar ta cinyesu dan dad'i ,hira kawai sike ba 'ka'k'kautawa.

      Se wajen 1pm ta tashi dan yi musu girki,kusan tare dasu ma aka girka abincin.Fried rice sukai mey dad'in gaske ,a plate d'aya ta zubo musu suka zauna a parlour abinsu suka ci su ukun.Har lokacin Amjad be fito ba ita bata ko damu ba dan tun jiya rabon data sashi a ido .

      Suna kammala cin abincin sukai sallah su Maryam suka d'auraye kwanukan da aka 'bata."Maryam kunsan wani abu?"

     "A'a sekin fad'a"

STORY CONTINUES BELOW

     "Yanzunnan nake so ku tayani nayiwa Mami cake ku kai mata"

     "Toh" Maryam ta amsa.

      "Mami fa tace kar mu dad'e"Cewar Nusaiba.

       " Ke dalla can seku kwana"

        "Tabb bada mu ba" Maryam ta fad'a.

     "Meye idan kun kwanan?eyyi?"

    Shiru tayi Maryam tana munafikin murmushi tare da kad'a kai "a'a de".

     " Bazaki magana ba,nace meye idan kun kwanan?"

     Dariya ta shiga yi tana rufe fuska "Mtchww! Sakarya ni tashi muje kitchen d'in" Ta fad'a tana mi'kewa daga kan sofa dan ta fahimci inda ta nufa.

    A hankali suna had'a abinsu har sukai baking, sosai cake d'in yayi dad'i nan ta d'ibarwa Mami mey yawa ta rage kad'an.Wajajen 5:30pm suka tafi, pictures da suka kawo mata na biki tayi ta kalla.

     Amjad kuwa yana jiyo su daga d'akin yana sane ya'ki sakkowa dama ya shiga da abincin daya siya a waje d'aki harkokinsa yayi tayi a d'akinsa.

      Ita kuwa da dare cake d'inta taci tasha lemo tayi kwanciyarta.

11:35pm,  Knock! Knock! Tajiyo bugu  tana cikin bacci, tashi tayi duk jikinta yana shaking dan bugunshi yaso ya razana ta.

     "Mtchww! Ze tayar min da hankali ina bacci na" Seda ta yafa mayafi tukun ta bud'e masa.

    "Let me have your phone"Abinda ya fad'a kenan banyan ta bud'e.

     Seda ta d'an jinkirta kafin ta koma ta bud'e drawer ta d'akko."Gashi"Ta fad'a a ciki-ciki.

    "This?" Ya wani kalli wayar tare da nuna ta da yatsa.

     A wani wula'kance ya kar'beta bayan ya jujjuyata ya mi'ka mata abarta."This is useless "Ya fad'a.

     " Wacce ka siyamin?"Ta fad'a a ranta.
  
       Kamar yana so ya sake fad'ar wani abun amma de yayi shiru ya fita daga d'akin ta rifo 'kofarta.

    "Allah ze sakan tashi na dakai" Ta koma ta kwanta.

     
  ***

     Washegari tasha mamaki ganin ya siyo mata waya,bata yi tunanin yana da ragowar mutunci ba,IPhone 7+ silver colour.

       Tunda tayi waya ta rage damuwa da rashin mutane a kusa da ita,zatai chat d'inta tayi kiranta tayi karatun novel wani lokacin tayi kwalliya tayi ta selfie d'inta.

      Amjad kuwa kwana hud'u kenan da fara zuwa aiki.Ranar farko daya je company kowa kallonsa yake  a iya shekarunsa a matsayinsa na chief executive officer gashi dressing yake duk wanda yaga dama har 'yar shirt me gajeren hannu ma yake saka wa ya tsuke abinsa gashin kannan yasha style.

      12:14pm,taji motarsa yai parking tana daga d'aki,labulen window ta d'an bud'e tana ganin fitowarsa ta ta'be baki ta cigaba da danna wayarta.

      Tana jiyo shi ya shiga d'aki,wanka kawai yayi ya sauya kaya cikin farar T-shirt da black jeans ya shirya shirts, wayarsa da key kawai ya d'auka bayan  ya feshe jikinsa da turare ya fito.

STORY CONTINUES BELOW

      Knock! Knock! Taji ya bugo 'kofarta.

     "Follow me" Abinda kawai ya fad'a yawuce downstairs.

     "Follow you? To where?"

      Komawa tayi ta zauna amma kuma ta kasa ci gaba da dannan wayar,seda tayi kusan 8min a haka tukun ta mi'ke ta yafa mayafinta kan riga da skirt na atamfa dake jikinta ,flat shoe d'inta ta zira ta ajje wayarta ta sauka 'kasa.

       A living room taga bayanan,tana le'kawa waje ta ganshi ya jingina da pillar na varender.Yana jin motsinta ya waiwayo ,wata uwar harara ya watsa mata sannan ya nufi motar.

     "Toh ina kuma za'a? Toh wayata kuma na d'aki"

    Wata zuciyar ce tace "kika sani ko gida zey kaiki ,karki koma kuma ya fasa" A hankali ta 'karasa jikin mortar tana d'an ra'be-ra'be kanta a sunkuye.

     "Get in" Ya fad'a.

     Gidan gaba ta bud'e tana d'ar-d'ar ta shiga,har suka hau titi bame cewa komai tsit"Toh ina kuma zamu?"Ta fad'a ganinsa tayi ya kauce hanyar da zata sada ta da gida.

      Kasa tambaya tayi ta zira ido tana ganin ikon Allah.K'aton gida taga yayi horn an bud'e masa ya shiga.Har lokacin bata gane inda aka zo ba,seda taga Shaheed yana fitowa daga ciki.

      "Are you staying here forever?" Ta jiyo ya fad'a.

     Da kanta ta bud'e 'kofa ta fito tana d'an taka wa a hankali so take ya shige gaba."Ina wuni"Shaheed ya fad'a lokacin da suka 'karasa

     "Ina wuni" itama ta fad'a.

     Handshake taga sunyi suka jero suna 'kus-'kus wanda ba ji take ba.Suna tafe tana binsu a hanya har suka 'karasa ciki,ba kowa a parlourn ta samu ta zauna a sofa,tana kallo ya nufi wani sashen Shaheed kuma ya hau sama.Not more than 3min sega Mom da Zakia sun sakko fuskarsu d'auke da fara'a suka 'karaso.

      "Laila" Ta kira sunanta tana 'karasowa ta zauna daga gefenta tare da tallafo shoulder d'inta.Laila cikin jin kunya tayi 'kasa da kanta tare da du'kawa ta gaisheta.

    "Get up,feel free daughter"

    "Ya kike?"

      "Lafiya lau" Ta daure ta 'Kalo murmushi.

     "Ina yini" Cewar Zakia tana murmushi.

      "Ina yini"

       "My cutie sister please feel free,this is home"

     Itade murmushi kawai take musu Mom tasa mey aikinsu ta kawo mata abin sha.

     "Kada ki bari fa aiki yana miki yawa   kiyi magana kinji se'a sami mey aiki""

    Kai kawai ta kad'a ba tare da tace komai ba,tana hangoshi har ya 'karaso inda sike ko zama ya'ki yi kawai de ya gaisa da Mom ne Zakia se wani kallon gulma take masa yana harararta ji yake kamar ya mareta ganin Laila yasa ya 'kyaleta .

      "Amjad talk to her to  drink something" Mom tayi maganar dan ta gano ya zaman nasu yake.

     "She is fasting" Taji ya fad'a.

     D'ago idonta tayi har suna kallon juna yayi mata 'kiri gefen fuskarsa d'auke da murmushi.

     Mom jinjina kai kawai tayi , inda Allah ya taimaki Amjad  Monday ranar ta kasance.Daga bayan tashi yayi ya fita a mota ba tare da sunsan inda zashi ba,kad'an-kad'an Zakia tana janta da hira kawai amsata take dan yunwa ta gama kashe mata jiki rabonta da abinci tun 8:30am saboda yau da wuri tayi breakfast,addu'a take maghrib yayi tasan Mom zata had'a mata kayan shan ruwa har kusan maghrib Dad ya shigo suka gaisa,suna zaune Amjad ya shigo ko zama beyi ba yace ta tashi su tafi,Mom ba yadda ba tayi dashi ba ya bari tasha ruwa anan amma ya'ki dan har tasa an girka mata abinda zata ci,daga 'karshe de yace kawai tasa mata a food warmer se su tafi dashi.
     "Mugu azzalimi" Ta fad'a a ranta.

      Daga yadda yaga yanayinta ya gano tana cikin wani hali dan ya'ke kawai take."Let's go"Yayi mata murmushi.

    Har mota suka rakasu suna tsaye suka fita daga gidan.Food warmer d'in tayi ta d'an d'agen wuya ko zata gansa d baya amma ba alamarsa,hanyar daya kamata suyi taga sun kauce.

     "Where are we going to?" Ta tambaya.

     "Mall,madam chef" Ya bata amsa yana murmushin mugunta.

     Kai ta dafe ta kalli taga har wani duhu-duhu take gani,tana ji tana kallo yayi parking. "Let's go".

    Ac dake busawa taji ta isheta,ji take kamar mey zazza'bi,yana tafe tana binsa a bayan se wani kalle-kalle yake kafin ya d'auki abu d'aya seya shafe fin 5min.

      " Do you like this? " Ya d'akko wata doguwar riga iya gwiwa yana nuna mata.

     "My wife is eager to go home ,but her husband is not readyyy"

    Ji take kamar ta sha'keshi,haka ya gama d'age-d'agensa harda kara mata a jiki yaga wai yayi ko beba gabaki d'aya English wears yaita za'ba.8:42pm suka shiga gida ,ko kallonsa bata sake yi ba har suka shiga.kayan daya siyo  leda uku ciki ya mi'ka mata ta'ki kar'ba,kan kujerar ya dire mata ya koma mota ya d'akko abincin har lokacin da ya dawo tana parlour. Yadda ya rungumo warmer d'in zaka san cewa ya taki rashin mutunci.

     Need your comment,I'm really busy but I tried hard to update coz I don't want to keep you guys waiting, I don't know If I can be able to update tomorrow, I'm really really busy.Love ur💋

Binsa tayi da kallo tana jira taga mey zeyi da abincin,har kusa da ita yazo ya wuce ta gefenta yana rungume da flask d'in ya haye sama ya barta a tsaye tana had'iyar miyau.+

     Jitayi kamar ta bishi amma gudun karya wula'kantata ta nufi kitchen, seda ta fara had'a tea tasha tukun ta d'ora indomie sharp sharp ta gama da zafi-zafinta haka ta samu taci harda guntun hawayenta na takaici.Se bayan ta gama cin abincin ne ta tuna bata yi sallah ba maghrib da isha'i,shima Amjad d'in tunawa tayi beyi ba."Tabb! La'ilaha illallahu maimakon yaje masallaci ,toh ko dama haka yake wasa da sallah?"Ta tambayi kanta tana mey mamakinsa dan ita shaf ta mance yunwa ta rufe mata ido batai noticing ba.

     "Astaghfirillah" Abinda ta fad'a kenan ta koma d'akinta kayan kuwa ta barsu anan. Seda ta idar da sallolin da ake binta tukun ta samu nutsuwa,tana yin wanka tayi shirin kwanciyarta koh phone d'inta bata duba ba dan gajiya.

        Washegari da safe kafin ta fito taji fitar Amjad, 8:20am agogon d'akin ya nuna.Inda ta bar kayan jiya anan tazo ta tarar dasu,ta'be baki tayi tai wucewarta kitchen "Ka kaiwa budurwarka ba niba"

             ***
  Sati d'aya su Mom suka 'kara a Nigeria suka koma ,kafin su koma seda suka zo gidan Laila.Amjad ji yake kamar ya bisu ,tun lokacin da suka koma ya dena walwala ko kula Laila bayi yake ba balle magana ,kaya kuwa bata kwashesu ba se lokacin da Mami zata zo ta d'auke ta kaisu wani d'akin daban ta rife.A yanzu sun kwashe wata d'aya kenan da aure.

     Saturday 8:17am,ta gama shirinta cikin  lace black mey red torches,tasa sar'karta mey stones red color tayi matu'kar kyau ga d'aurinta da ya tsaru fuskarta tayi light makeup se 'kamshin turare take.Tana sauka 'kasa taga parlourn ma ba wani datti yayi ba dama jiya da yamma ta gyara shi,kitchen ta shiga dan had'a karin kumallo ,yau doya da 'kwai taji tana sha'awa ,tana d'ora doyan a pot ta nufi drawern dan  d'akko bowl ,kasancewar tsahonta baya kawai setayi d'age tana janyo bowl d'in ya su'buce ya fad'o kan babban yatsanta na 'kafa Tass! Ya fashe pieces a wajen ,take ta saki wata  'kara dan azaba.Fuskarta tuni tayi jazir gumi yana keto mata,zaman dirshan tayi tana ri'ke da 'kafarta d'anyatsan se jini yake.

        "What happ.." Be 'kare tambayar ba yayi shiru da bakinsa ganin yadda 'kafarta ke zubar jini.

    Kuka ta shiga yi sharaf-sharaf hawaye yana zuba.

     "Get up" Ya fad'a tare da d'ora hannu da niyyar mi'kar da ita.

     "Aghhh!" Ta 'kwallo 'kara.

      Jin 'karar da tayi yasa ya d'auke hannunsa,tana zaune ita bata tashi ba kuma bata dena kukan ba."Are you staying like this? "

    Banza tayi dashi kamar bata jiba,yana sake d'ora hannunsa a kafad'arta ta kuma tsala ihu fin da.Ita bama iya zafin yasa ta 'karar ba ta'bata ne bata so yayi.

      Tsaki yayi "It left for you" Ya fita daga kitchen d'in.Yana  fita ta tashi se d'ingishi take,ganin jinin yana d'iga a 'kasa ta zauna kan wani couch.Tana hangoshi ya sakko daga bene hannunsa ya ri'ko first aid.

      "Cabb! Zaka ga first aid"

       Bata ankare ba taga yaja wani guntun table ya zauna opposite da ita."Let me see"

    "Kaga mey? kai likita ne?"

     Ko bin ta tata beyi ba ya kama 'kafar se fisgewa take amma ta kasa "Aghh!"Se 'kara take yayi banza da ita yana goge jinin se kuka take, seda ya gama ya rife ciwon da bush tukun ya sake mata 'kafa.

     " Allah ya is a"Ta fad'a a fili tana share hawaye.

     "You have to be careful"

      "Ni matsa min na tashi" Ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa.

STORY CONTINUES BELOW

       Maimakon taga ya tashi seyai zamansa yana kallonta.

     Kasa balancing tsaiwarta tayi ta fad'a kan couch d'in.Ganin ya sake matso da kujerar yasa hanta cikinta ya soma kad'awa,ta sunkui da kai tana jin idonsa a kanta.

     "I need to know why,why did you agreed to married me?"

      Shiru tayi ta kasa cewa komai tana murza yatsa."I'm asking"Ya sake matsowa har takai baza ta iya mi'kewa tsaye ba."Please let me go"

     "Until you answer my question"

      "I never married you because I love you,they..they forced me to"Ta fad'a da 'kyar.

      "Wow! I hope what you're saying is true"

     "Now what is your plan? Run away?"

     "Please".

     Tashi yayi tsaye ya d'auke first aid d'in ya haye sama,tana gani ya tafi tayi sauri ta bar wajen ta koma kitchen tana d'inhisawa,wajen daya 'baci da jinin ta gyara a daddafe ta 'karasa had'a breakfast d'in taci kayanta.

     Tunda ta koma bata sake fitowa ba se bayan zuhr,tana ganinsa a parlour tai 'kasa da kai bata so ta had'a ido dashi.Shiko be sake yi mata maganar 'kafar ba balle yai mata sannu.

     Laila da daddare ta kira Mami tana ta shagwa'ba ita a lalle taji ciwo  Nusaiba tazo.Washegari Mami ta turosu da Nusaiba harda Fauzan amma basu kwana ba.
      Tun bayar tafiyarsu Laila ta soma jin sauyi game da ita,kad'an-kad'an mararta ta soma ciwo tun bey takura mata ba har ta kasa jurewa.Ta kwanta se mutsukka 'kafafuwa take tana dafe ciki,tunani ne ya fara zuwan mata na MP date nata data lissafa taga lokaci yayi." Tir'kashi!"
      "Ya zanyi?"Tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta ko zata samu mafita,8:18pm taga agogo ya nuna juyi kawai take ta rasa inda zata saka kanta gashi idan a gida ne magani take sha wani sa'in Mami ta had'a mata black tea ta kur'ba amma yanzu ba d'aya.Hawaye ne kawai yake tsiyaya daga idanunta tana tauaayin kanata na halin rayuwar data shiga.9:03pm a daddafe ta tashi ta sauka 'kasa ,a kitchen ta had'a tea kad'an ta samu ta daure ta kukkur'ba ga yunwa DAT me ji amma bata jin zata iya con komai.D'akinta ta koma ta cigaba da aikin juye-juye,gashi tana taoron gone monday tasan da wuri zey fita,idan kuwa ta bari ya fita tana cikin matsala dan bata da ko sisi balle tace zata fita suyo wani Pad dan duk 'Yan kud'ad'enta ta 'karar wajen saka credit last siyan ma shine sands su Fauzan suka zo ta aikesu suka suyo mata na 500 dan.Se can bayan 30min bacci ya kwasheta da ciwon ya lafa.

       5:46am ta farka taga har subh tayi,da 'kyar ta iya tashi dan a halin data tsinci kanta mey faruwa ta faru batsman kuma ya zatai ba yau.Wata zuciyar ce ta bata shawara ta fad'awa Amjad,tana jin kunya haka tayi knocking 'kofarsa lokacin 6am.

     Taci 6min kafin ya bud'e mata ,daga ganinsa ta gane lokacin ya tashi daga bacci.

    "Morning" Yaune lokaci na farko data ta'ba gaisheshi.

   Da'kyar yake bud'e idanuwansa "What?"

     Wayar hannunsa ta mi'ka masa bayan data gama danne-danne.

     Kamar baze kar'ba ba yasa hannunsa ya kar'ba"Read"Ta fad'a tana kallon gefe.

     "I want to use pad" Yaga ta rubuta ta note app.

       "So?"Ya fad'a ba tare da ya nuna damuwa ba.

         Hannunsa ta mi'ka alamar ya bata wayarta a lokacin kuwa idanuwanta sun cika da 'kwallo jira take kawai ta bar wajen.
  
    "Check in what you disposed the other day"Abinda ya tafa mata ya mi'ka mata dan yasan bata duba kayan ba dan da ta duba da bazata tambdaya ba.

      Tana gama karancewa ta tuna da India ta ajje kdyan,kunyace taullu'beta tana da tasani duk da ba haka ba.A kunyace ta jiya zuwa d'akin data yasar da kayan.

     Tana dubawa tagani kuwa se lokacin taji relief,da Saudi ta komo zuwa d'akinta da pad pack d'in a hannunsa ,mamaki ne da kunya ya sake lullu'beta lokacin da taga yana tsaye har lokacin a 'kofar d'akin kamar jiranta yake.Basar wa tayi ta wuce a hannun hagu ta ri'ke yadda baze gani ba tai sauri ta shiga.Shi dariya ma ta bashi (Gani na yaushe kuma).Tana shigewa shima ya rufo 'kofarshi,se lokacin yaje ya d'auke alwala.

              ★★★
   
    A kwana a tashi har sun shafe kusan 4month,sun saba da irin zamansu yanzu kowa baya damuwa da kowa wannan itace rayuwar da suka za'barwa junansu.Laila har ta samu admission a BUK ,kafin ta fad'a masa seda aka kwana biyu taci sa'a bece komai akai ba kud'i kawai ya bata na registration  shi a yanzu besan ma lokacin da zata fara zuwa ba be tambaya ba kuma bata fad'a masa ba.Ita kuwa ta 'bangaren ta ranar Monday kawai take jira dan shine sanda zata fara shiga lectures ita har ta 'kagu lokacin yayi ta huta da zama shiru.Mom lokaci-lokaci suna waya da ita ,shima ta 'bangaren Rosie ba abinda ya chanja har yanzu bata san wani abu game da auren Amjad ba.

       ***
   Monday

          Da asubar fari ta farka saboda d'okin makaranta,tana idar da sallah tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na material purple colour,powder kawai ta shafa se lip gloss ta shafa turare mey taushin 'kamshi.

     Hijab d'inta da tasa aka kawo mata daga gida ta d'akko d'aya daga cikin kalar kayanta ,zira abinta tayi se niqab d'in kuma ta ri'ke a hannunsa had'e da handbag d'in ta saki ta kalmi ta sauka 'kasa.

      Ba wani breakfast mey d'aukan lokaci ta had'a ba ,tea kawai tasha da toasted bread.Tana fitowa daga kitchen d'in ta d'aura niqab d'inta dede lokacin Amjad yake sakkowa daga bene cikin shirinsa na Blue suit ciki kuma  white shirt se black jeans ya rife idonsa da specs.

       
      *Short chapyy and boring I think.Akwai d'aya daga cikin littafina wanda shine na farko da na fara rubutawa sede Allah besa na kammala ba,a bisa complain da nake samu game da rashin 'karasawa inshaAllahu bayan na kammala wannnan zan cigaba da HASHIM ABDALLAH amma bata blog ba zan dawo dashi wattpad ina tunanin hakan zefi sau'ki.Masu son d'ayan littafin mey suna SON ZUCIYA zaku iya samunsa ta  wannanan  khadijasko.blogspot. com*
      
*Dijensy❤*

Ina godiya Amjad fans ,musamman 'yan whatapp ,one luv💋+

       
         Tana kallonshi ta cikin niqab d'in ta sunkui da kai,tana jinsa tsaye yana kallonta."Where are you going to?"

    "School" Ta amsa a ta'kaice.

     "Why did you dress this way?" Ya fad'a tare da nunata da yatsa daga sama har 'kasa.

     Shiru tayi bata amsa shi ba har lokacin bata d'ago da kanta ba."Are you a terrorist? "

      Jin abinda ya fad'a yasa tayi saurin d'ago da kanta tana kallonsa "Kana musulmi kake irin wannan maganar" Ta fad'a cikin ranta.

    "I'm asking you?"

     "Muslims are not terrorist" Ta fad'a tare da kawar da kanta gefe.

     "Whoa! so Amjad is not a Muslim, may be I'm Christ or jews right?"

       Ganin zey 'bata mata lokaci ta gyara handbag d'inta ta wuce."Do I ask you to go?"Taji ya fad'a.

     'Karasowa yayi inda take ya zagaya yanda zata ga fuskarsa dan ko juyowa batai ba."Answer me"

     "No"

      "Then why did you?"

      "Because I have to"

       "Now,did I ask you to stop"

        "Rainin hankali" Ta fad'a a ranta.

      Be sake wata maganar ba ya wuceta ya fita tana tsaye."Mtchww!"Taja tsa'ki itama ta nufi wajen bata ko kalli inda yake ba ta nufi bakin gate tayi ficewarta.Ba abinda ya 'kona masa rai irin yadda ta fita bata ko damu ta rufe 'kofa ba.Da kanshi ya koma ya rufe 'kofar tukun ya shiga motarsa ya fice.

     Tana tafiyarta taji horn mey uban takura ba 'ka'k'kautawa tana juyawa taga motarsa ce,seda yazo daf da ita kamar zey bigeta ya zuge glass d'in motar.Cikin suit d'insa ya zira hannu ya zaro 2k 'yan d'ari biyar ya mi'ko mata da hannun hagu a wani wula'kance.

      Ranta inyayi dubu ya 'baci,kawar da kanta tayi ta cigaba da tafiyarta ita kad'ai tasan mey take ji a ranta.Tana cikin wannan halin ne bata ankara ba taji an fisgo hannunta.

     "How dare you shun me like that?" Ya fad'a ransa a 'bace.

     A 'kufule ta d'ago da idanunta ta kalleshi cikin glasses d'insa suka had'a ido."Kai wawan ina ne ,ka sake min hannu! "Ta tsawata tana 'ko'karin fisgewa.

    " Come on fight back"

      Ri'kon da yayi mata ba 'karamin zafi yayi mata ba kuka ne yake son ku'buce mata amma hakannan ta daure dan a ganinta babbar asara ce yaga hawayenta.

     "Let me go"

     "Make me"

      Doke kafad'arshi ta shiga yi ba 'ka'k'kautawa tana fisge-fisge,da 'kyar ta samu ya cikata .Bata ko tsaya ba tayi sauri ta tari wani Napep dake shigowa street d'in,ta gwammace an bi da ita ta wani titin data bi ta hanyar da zata sake ganinsa.

     Tana barin gun ya koma motarsa cikin zafin rai ya fizgi motar ya bar wajen.Laila a d'an sahu bata ankara ba taji hawaye na bin 'kuncinta,kuka mara sauti ta shiga yi har ta kusa isa school tukun ta d'akko tissue a jakarta ta goge fuskarta,3k da sukai saura na registration d'inta a ciki ta d'auka N500 ta bawa mey d'an sahu ya mi'ka mata chanji ta wuce.Tana shiga school d'in daga kan wani bench ta zauna,tunanin irin abinda yayi mata ta shiga yi ji take kamar daga makarantar ta gudu gida,a ranta tana tunanin Baba ,da ace be rasu ba da tuni tana gidansu.

STORY CONTINUES BELOW

      "Assalamu Alaykum" Taji muryar mace.

     Tana d'ago da kanta taga ba'kuwar fuska"Waalaikissalm"Ta amsa tare da yin guntun murmushi.

     "Baiwar Allah kema sabuwar d'aliba ce?" Ta tambayeta.

     "Eh" Laila ta amsa muryarta kusan a dashe.

     "Wani course?"

      "Microbiology" Ta amsa.

       "Ashe course d'in namu d'aya"

        "Allah ya bamu sa'a" Laila ta fad'a.

        "Ga nan ki zauna" Laila ta matsa mata.

      "Ya sunanki?"

      "Laila" Ta amsa.

       "Ni kuma Aliya ta fad'a.

       Daga haka duka su biyun sukai shirun dan Aliya taga kamar Laila bame son surutu bace,ita kuwa Laila ba kasafai take sakin jiki da ba'kin fuska ba inba wai ta zauna ta fahimci halayyarka ba.

      An d'auki kusan 1½hr a haka kowa d'an danne-dannen wayarsa yake a hankali wasu students d'in na zuwa lokacin suka had'u da course mate d'insu.

   10:30am suka shiga first lecture, kowa yana jin ba'kunta class yayi shiru ana sauraron lecture Aliya tana kusa da Laila.Seda aka kwashe kusan 1⅓ suka fito daga class,tana jin yunwa amma sam bata jin zata iya cin abinci.

     Basu suka sake shiga wani lecture d'in b se bayan zuhr,se 4pm ta komo gida."Tir'kashi!"Ta fad'a ganin 'kofa a kulle,ita sam ta manta da batun wani key na gida balle har tayi tunanin fita dashi.Ga yunwa tana ji banda gajiyar data kwaso,kan steps na bakin 'kofa ta zauna tana addu'a Allah yasa ya dawo yanzu duk da kuwa ba son ganinsa take ba.Zama tayi-tayi shiru har ta gaji,se to 5:45pm ya shigo gidan ,tunda ta hangoshi ta kawar da kanta gefe tare da sakin niqab d'inta ta rufe fuskarsa ko idanunta baza a gani ba.

    Cikeda ta'kama ya 'karaso yiyai kamar be ga mutum ba.Gefe ta matsa masa karya bangaje ta,tana jin ya bud'e 'kofar ta mi'ke har ya shiga yana 'ko'karin rufewa ta ri'ke handle d'in.Ba tare da yace komai ba ya wuce ta shigo sannan ta rife ,ko d'aki bata je ba ta shiga kitchen.Wani ragowar donot da tayi tun shekaran jiya ta d'auko ta had'a da orange juice taci sannan ta koma d'aki.Seda tayi sallahr maghrib tukun ta watsa ruwa ta zira doguwar riga mara nauyi na material ta koma kitchen ,jollof d'in macaroni kawai tayi kad'an taci ta koma d'aki.

      Washegari ma da wuri ta tashi ta had'a breakfast mey nauyi-nauyi bayan data d'anyi gyara-gyaranta tai shirinta yauma bayan ta zira hijab ta d'aura niqab d'inta, tana rufo 'kofar d'akinta shima yana fitowa,waya ce ma'kale a kunnansa yayi shirinsa cikin black T-shirt da jeans ba'ki fuskarsa yau ba specs."Bye Darling "Ya fad'a ganin Laila tana kallonsa yana sane ya tsiri kiss ,wayar ya kara a bakinsa  yanda Rosie zata ji sautin kiss d'in,(Irin kiss da shaheed kapoor ya kewa Sonakshi a R..rajkumar ,lol). through phone.

     Kanta ta kawar ba tare da ta kallesa dukda kuwa taji shi,dama tasan da biyu yayi hakan kuma ko a jikinta." Jealous"Taji ya fad'a.

    Key taga ya mi'ko mata ta gefe,hannu tasa ta kar'ba ba tare da ta d'ago ba tayi wucewarta.Yau ma kamar jiya tana tafiya taji wucewar motarsa ,seda ta jima kafin ta samu d'an sahu dan sanda ta isa school ma har an shiga lecture,inda Allah ya taimaka ma Aliya ta samar mata seat.seda sukai 2hrs lecture cir suka fito ,ko 10min basi ba suka sake shiga wani lecture d'in se 12pm suka fito daga nan suka wuce cafeteria cin abinci. Kad'an-kad'an suna hira da Aliya,suna haka ne wayar Aliya tayi 'kara cikin fara'a ta amsa kiran.Ta d'au lokaci tana wayar kafin daga bisani ta katse."Sorry na zaunar dake"Aliya ta fad'a.

    "Babu komai" Laila tayi murmushi.

     "Ke gwara ke daga kin koma gida hutawa zaki,ni kuwa senayi girki" Aliya ta fad'a.

     "Uhnn..kina da aure?" Laila ta tambaya.

     "Au ban fad'a maki ba ko? Wata shida kenan" Ta amsa.

      Jinjina kai kawai Laila tayi tana mamakin hakan dan ta zaci Aliya budurwa ce ,dan ko a fuska tafi nuna yarinta a kan Laila.

      "Lalle kam hakane" Abinda ta fad'a kenan ta kawar da zancen.

      Lecture d'aya suka 'karayi  suka tafi,yau bata bi takan abinci ba wanka kawai tayi ta zauna tana hutawa abinta.

      Laila seda ta jera sati biyu tana zuwa school ba tare da ta nemi kud'i gunsa ba,a 'karshen satin seda ta koma tafiya da abinci school dan kud'inta yayi 'kasa,gobe Monday 50 Naira ce kawai ta rage bata san kuma ya za'ai ba.
       
       9:39pm,ta sakko 'kasa shan ruwa tana shiga kitchen d'in ta ganshi zaune kan stool yasa fruit salad a gaba yana sha,d'ayan hannunsa kuma ya ma'kala waya a kunnensa.Ko ba'a fad'a ba tasan da budurwarsa yake waya.Allah yasa ta yafa mayafi kan riga da wando na bacci data sa,wucewa tayi ta bud'e fridge ta d'akko bottle, glass cup dake jere a kitchen ware ta d'akko ta tsiyaya tasha kayanta.Tazo zata fita taji shi ya sake yin irin kiss na rannan a wayar kusan fiya dana rannan.

      "Are you jealous?" Taji ya fad'a.

     'Kwata-'kwata bata san ya biyota a baya ba se gani tayi yasha gabanta.

       "Do you wanna know about her?"

      Kauda kai tayi ta shige gefe zata hau sama taji ya ri'ko hannunta."You're jealous,I can see it through your eye's"

      Hannunta ta fisge "Never!" Bata jira ya sake wani maganar ba ta tafi.

      A duniya baida buri irin yaga ya ba'kanta mata dama farko na ba'kunta ne yanzun ya gaji da zaman lafiyar.

               ★★★

     7:38am ta gama shirinta tsaf tana dinning a zaune,tunanin yadda za'ai ta iya zuwa makaranatar kawai take gashi tana jin kunyar tambayarsa,shida ya mi'ko mata kud'i dukda bata San nawa bane ta'ki kar'ba taya zata iya ce masa yanzu ya bata?

      "What are you waiting for?" Tajiyo muryarsa yana sakkowa daga step.

    Shiru tayi ta'ki cewa komai fuskarta bata rife ba amma de ta d'aura niqab d'inta."May be this?"Taga ya ajje kud'i kan table d'in 'yan 1000 ne sede bata san nawa bane.

    "Take it" Ya fad'a.

     Shawara ta shiga yi ta d'auka ko karta d'auka? Ganin lokaci yana ja ta daure ta saka hannu ta d'auka.

     "Shame" Yana fad'ar haka ya fita.

       "Eh d'in ai ba sata nayi ba". Ta fad'a a ranta.

       Seda ta bari ya fita tukun ta fita,tana shiga school ta had'u da Aliya wanda dede lokacin mijinta ya sauketa a mota.Se 4:30pm ta dawo gida tana sigowa taga motarsa,hakan ya nuna ya dawo gida.Se bayan ta ajje handbag d'inta ta sakko kitchen daga bakin 'kofa ta tsaya saboda abinda ta gani.

Wani 'katon cake ta gani daya sha ado sosai pink and white rubutu akai masa akai "Happy birthday sweetheart" da candle jere a kai.
Sede ita bata ga abinda aka rubuta ba tunda bata 'karasa ba.Gefensa kuwa laptop d'insa ce yana video call,tana jiyo murya mace amma bazata iya ganin fuskarta ba,bata bari ya d'ago ya kalleta ba tayi saurin komawa d'aki.+

     "Happy birthday baby" Tare suka bushe candle d'in as if tana kusa da cake d'in.

     "Thank you Baby" Ta fad'a tana washe ha'kora dan ta kasa rufe baki saboda farinciki.Balloons manya daya sa'kala  jikin fridge ya ciro su."Do you like this baby?"

    "Yes I love it "

    Teddy bear dayai hiding a  bayan laptop d'insa ya ciro 'kato pink colour a tsakkiyar cikin an rubuta happy birthday beautiful "

    Nan ma wani sabon farincikin ne ya rufeta."Baby you're so sweet"

    "You deserved more than this baby"

      Hira suka shiga yi abinsu ,Laila kuwa jitai dama bata sauka 'kasan ba dan ma Allah yasa bai ganta ba.Dama ba wani yunwa take ji ba,gasasshen masarar data suyo a hanya ta d'akko a jaka ta soma gagayar kayanta, tana yi tana danna wayarta.

  Se wajajen 8:15pm ta sakko kitchen, balloons d'in duk nemansu tayi ta rasa seda ta bud'e fridge taga cake ,yaci iya wanda zeci ya bari .Rubutun da akai ta kalla ta ta'be baki ta d'auki abinda zata d'auka a fridge d'in ta rufe.

              ★★★
    
     Washegari da safe ta makara se sauri take ko living room bata gyara ba kitchen kawai tayi goge-gogenta bayan tayi breakfast ta koma d'aki ta shirya.Tana daf da fita taji ya kira sunan da yafi son gaya mata.

      "Madam chef"

       A hankali ta waiwayo fuskarta a rufe tana kallonsa ko shirin office beyi ba 3qtr ne da shirt a jikinsa.Ganin ya 'karaso ta sauke kanta 'kasa.

    "Remember you're now a  married woman don't tell me that you don't know your duties, I mean what you suppose to do here"

       "Mey kuma zanyi bayan wanda nake"Ta fad'a a ranta.

       " What?"
     
      "Prepare me a meal"Ya amsata.

      "It's getting late,it's almost 8 "

       "I don't care "

        "But.."

        "Just go on with your works and stop wasting much time"

       Har ya koma ya dawo "I forgot to tell you,I need omelette and  sandwiches"Daga haka ya koma d'akinsa.

    
       Tunani ta shiga yi ko tayi tafiyarta,amma kuma tana gudun abinda ze biyo baya.Haka tana ji tana gani ta cire hijab da niqab d'in ta fara ,tana yi tana mita."Da abincin kake cewa ai maka,ko dan kaga ka bani kud'i"

       "Kuma Allah ya kaimu gobe, baza ka san lokacin da zan tafi ba".
       Ba ita ta gama ba se 8:53am tana gama ajje masa a dinning ta saka hijab d'in ta ta fice.Yana daga d'aki ya hango fitarta,murmushin gefen fuska kawai yayi ya cigaba da harkokinsa.

       Lokacin data isa makarantar har an shiga lecture,seda tayi missing wannan lecture d'in.Se na 'karfe 12pm ta samu 2:30pm ta dawo gida.

      Motar sa da ta gani hakan ya tabbatar mata yana gida,lokacin da ta shiga a living room ta ajje jakarta ta nufi kitchen ganin plate na d'azu inda ta barsu yasa ta ci birki,'karasawa tayi table d'in ta bud'e ba abinda aka ci na ciki d'ayan ma haka ,ta rasa ma mey zatayi saboda tsabar takaici.

STORY CONTINUES BELOW

  " It's Nasty! It  smells bad"Tajiyo muryarsa.

   Kallo ta bishi dashi almost harara ta shiga kitchen, abinda take so tayi a kitchen d'in ma ta kasa saboda tsabar ba'kin ciki dan haka ta fasa girka komai ta komo living room ta d'auke handbag d'inta zuwa d'aki.

     "Allah ya isa" Ta fad'a a fili tana cilli da jakar.

      Ga yunwa tana ji amma haushi baze bari ta iya cin komai ba.Se bayan asr ta sakko ganin bata ga plates d'in ba yasa ta shiga tunani "Ko yaci?"

     Wainar fulawa ta had'a ta soya kayanta taci a kitchen d'in, wajen daya d'an 'baci a kitchen d'in ta share lokacin data bud'e dustbin tasha mamaki ganin sandwich a yashe a wula'kance.

     "Wannan ai almabazzaranci ne"

     Haushi de ranar tasha shi,bayan maghrib tayi plunging charge a wayarta ta sakko 'kasa,kan d'aya daga cikin sofa a living room ta zauna tare da d'aukan remote control ta kunna  TV.

    Chanja channel d'in tayi zuwa Bollywood aiko ta riska ana film d'in da take so "Veer zaara".Sosai ta bada attention a kai tana jin dad'in kalla dan har taji fishin da take ya tafi.

      1hr later sega Amjad yana sakkowa ,tana jin motsintsa amma tai kamar bata san dashi ba.Kitchen ya fara shiga ko mey ze d'auka oho ,koda ya fito har ya nufi upstair ya dawo.

     " She's enjoying it"Ya fad'a a ransa.

      "Excuse me!"

       Banza tayi dashi ta cigaba da kallonta,ganin ta'ki kulasa ya 'karaso yayi blocking d'inta yadda bazata iya ganin komai ba.

     "Are you deaf?"

      Maimakon yaga tayi magana se gani yayi ta mi'ke tsaye tayi tafiyarta d'aki.Har cikin ransa ba haka yaso ba se yanzu yake daya sanin barinta na tafiya.Laila kuwa a d'aki harda kukanta dan tsabar takaici ya katse mata kallonta tasan dama abinda yake so kenan kuma burinsa ya cika,a ranta kuwa ta 'kudura ba'kanta masa itama.

                 ★★★

     Washegari da asubar fari ta tashi da wuri tayi shirinta hatta breakfast datai a flask tasa ta zira a jaka.7:16am nayi ta fita daga gidan.

    Knock! Knock! Laila! Ya 'kwala mata kira amma shiru ,yana murd'a 'kofar yaga bata ciki.Da 'karfi yayi banging 'kofar ya koma d'aki ,a niyyarsa yau ma ya sake sata dafa masa abinci duk da ba cin zeyi ba.

     "Nigeria"Sunan da yayi saving number d'inta kenan. Daga yayi dialing seya kashe da 'kyar ya bari kiran ya shiga.Ya kirata sau biyu batai picking ba,wurgi yayi da wayar gefe sau biyu kenan yana kiranta bata ta'ba d'aga wa, lokacin bikinsu da yau.

     Laila kuwa tana shiga school tasa wayar a silent,tana zuwa ta samu gu taci abincinta ,a ranta tana mey jin dad'i dan tasan duk tsiya seya ji haushi.

      Koda aka tashi ba gida ta komo ba gidan Mami ta wuce dama ta dad'e tana planning yin hakan tunda tayi aure bata ta'ba zuwa ba.

      " Ga yaya!ga yaya!"Fauzan ya tafi da gudu yayi hugging d'inta.

      "Tohh,zuwa ba zato ba tsammani"Mami ta fad'a tana fitowa daga kitchen.

     " Daga makaranta nake"Ta  fad'a tare cire niqab d'in.

      Kowa murnar ganinta yake ,tuni ta mance da rayuwar gidanta.Kitso tasa Maryam tayi mata bayan sunci abinci,4pm taje gidan Kawu Yunus nan d'inma seda ta shafe kusan awa d'aya ta komo gida.

     Amjad 4:23 pm ya dawo gida be sameta ba,Mom ta dad'e tana masa maganar zuwa gidan Mami se yanzu  yaga dama shine ya dawo su tafi  tare amma be sameta ba,shiru-shiru har 5:15pm bega dawowarta ba dan haka yayi fitowarsa shi kad'ai.

   
       "Laila yanzu dubi hannunki sungul kamar taliya ba ko jan 'kunshi" Mami ta fad'a.

     "Mami makaranta ba lokaci"

     "Toh 'yar boko..." Bata 'karasa ba sega Fauzan ya shigo da uniform d'in islamiyya a jikinshi."Mami unnhh..yaya Amjat yazo"

     Laila dake shingid'e a wani razane ta mi'ke zaune."Kace mey?"

     "Baki ji ba,mijinki ne yazo dama shi zezo d'aukan ki?"

     "Uhmm..shi..shine" Ta amsa cikin in'ina.

     "Toh ki tashi ki shirya".

    "Mami zaku gaisa ai" Laila ta fad'a.

    "Fauzan kace ya shigo" Cewar Laila.

     Da'kyar ya fuskanci abinda Fauzan yace,lokacin da  Fauzan ya shigo Amjad yana biye dashi.Yana zaune kan kujera lokacin da Mami ta shigo ya d'an du'ka kad'an shima tuna yadda Laila tayi sanda taje gidansu ne yasa yayi haka.

      Laila kuwa a d'aki se fiffita take da hannunta tunanin yadda zata fita take."Shikam taya yasan ina nan?"

    "Laila ki fito toh har ya fita yana jiranki" Tajiyo muryar Mami.

     "Gani" Ta amsa 'kasa-'kasa.

       Jiki ba 'kwari ta shirya tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta.Har waje Nusaiba suka rakota jiki a sanyaye ta bud'e gidan gaba ta shiga.A nitse yake tu'kinsa har suka isa  bakin titi,daga gefe taga yayi parking.

     "Get out" Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba.

     "Naje ina ?" Ta fad'a a fili.

      "Dismiss from my eye's!" Ya tsawata.

      Shawara ta shiga yi ta fita ko ta zauna?

Zaman jakarta ta gyara tayi kamar bata jin yaran."I said get out"

     Tayi yun'kurin yin magana ya daka mata tsawa"Now!"

      Cikin sauri ta bud'e 'kofar ta rufe da 'karfi tayi gaba abinta.Shima cikin zafin rai ya figi motarsa ya bar wajen.Haka tayi ta jiran d'an sahu seda 'kyar ta samu,tana isa gida direct ta wuce d'aki.

     Knock! Knock taji bugu dede lokacin ta fito daga bathroom, towel ne iya gwiwa a jikinta.Cikin hanzari ta d'auki hijab ta zira,la'bewa tayi a bayan 'kofar ta bud'e kad'an ba ko ina za'a iya gani bama a d'akin.

     "What are you hiding?"

      'Sangalalen 'kafarta data ke karewa ya kalla ,se lokacin ya gano dalilinta na 'buyan.

     "What do you think you're doing? I knew this is not the first time.."

     Be 'karasa maganar ba ya saki atishawa ba zato ba tsammani har yana sunkuyawa,hakan ba 'karamin dariya ya bawa Laila ba amma ta basar."Cha'kwai'kwaiwa yanzu ai kayi shiru"Ta fad'a a ranta.

     "Don't you ever.." Wata atishawar ce ta sake zuwan masa a jere har uku,Laila harda kawar da fuska.Harara ya bita dashi ya bar wajen, yana shiga d'akinsa yayi banging 'kofar.

     Bayan sallahr maghrib lokaci guda zazza'bi ya rifeshi harda ciwon kai ga dukkan alamu yana ji mura ce ta kamashi.Tuni ya fara fita daga hayyacinsa,yana kwance shame-shame hanci se tsiyaya yake yayi jazir, kwalin tissue ya ajje gefe daga ya share seya cillar duk inda yaga dama.

      Da'kyar ya samu ya mi'ke daga kwance ya d'auko wayarsa ya kira Mom ya wani kwantar da murya yana mata complain.Ji tayi dama tana kusa dan tasan yanayin dayake shiga idan baida lafiya rakin tsiya komai se an mashi kamar za'a goya shi.

      "Please try and take your medicine"

       "Get well soon my dear"

        "Mom,my head chest every where is paining"

         "Sorry,wish you quick recovery my love"

      Haka ta dad'e suna waya dashi wai duk dan ya samu relief, da 'kyar ya samu yayi sallahr isha'i.Laila kuwa bata san halin da ake ciki ba tana d'aki abinta.

     Hancinsa a toshe ko bacci ya kasa yi gashi a lalle baze kashe AC ba shi karya ji zafi,banda yunwa dake addabarsa a yanzu ba abinda yake bu'kata irin black tea amma mey had'a masa ne ya rasa.

       Washegari da safe kamar koyaushe ta gama shirinta breakfast ne kawai ya rage.

     Laila! Laila! Tana daga kitchen tajiyo shi yana kiranta.Tea take had'awa seda ta gama tukun ta hau sama,'kofarsa tayi knocking shiru ba amsa a hankali ta tura kamar bazata shiga ba.

     Yana bathroom tajiyo kakarin amai ,data kalli flow d'in d'akin kuwa tissue ce fal ba adadi duk ya cillar. Ba iya 'kasa ba hatta kan gadon a birkice yake.

      Ganin ya fito a daddafe ta kawar da kai gefe,tana ji ya 'karaso tare da zama kan gado.

     " Why are you so evil?, do you want me to die here?"

      "Nina d'ora maka?"Ta kalleshi.

    
         "Allah ya 'kara alhaki na ne".

         "Make me tea"
    
           Juyawa tayi ba tare da tayi magana ba, bata  dad'e ba ta had'a masa ta kawo.Tazo ba'kin 'kofa fita ya tsayar da ita.

       "Are you living me like this?"

        "Mey zanyi ma?" Ta fad'a.

         "Speak in English"

STORY CONTINUES BELOW

          "I'm hungry"Taji ya fad'a.

        "Bring me water"

         Tana turo baki ta tafi kitchen, dankalin data soya ta zibo masa tare da soya masa egg ta kawo,se bottle of water da cup ta jero a plate.Tana direwa tasa 'kafa zata fita."Laila"Ya kira sunanta daga kwance.

     "Where are you going?"

      "School" Ta amsa.

       Kai kawai ya girgiza bece komai ba ya d'ora d'aya hannunsa a kai se squeezing yake.

     Tana sauri haka ta fice koh  a jikinta ciwonsa be d'aga mata hankali ba.Yauma bayan sun fito daga lecture na farko ita da Aliya suna zaune kan bench suna duba wani aiki.

     Ring!Ring!Taji kira ya shigo wayarta,unknown number ta gani seda ya kusan katsewa tayi picking.

     "Hello"

     "Laila come back home" Taji an fad'a daga d'aya 'bangaren.

      "Who am I talking to?"

      "It's me Amjad"
    
      "Why do I have to come back"

      "I'm dying Laila, I totally can't breath"

       "Then take your medicine"

        "I can't"

        "Naji gani" Ta fad'a tare da katsewa.

        "Mtchww!" Bata san tayi tsaki bama.

         "Tohh,keda wa?" Aliya ta tambaya.

         "Uhnm,tafiya zanyi" Ta fad'a rai a d'an 'bace.

       "Tafiya kuma? Sauran lectures fah?"

       "Ya zanyi? Wata'kila na dawo".

       " Ok,Allah yasa lafiya"

        "Hmm" Abinda ta fad'a kenan ta tashi
         Ita de Aliya kallo ta bita dashi dan har yanzu ta rasa gane kanta.

      10:45am ta koma gida,seda ta shiga d'akinta ta ajje jakar tukun tai knocking d'akinsa."Come in"Ya fad'a.

     Lokacin data shiga ma yana zaune ita sam bata ga alamar wani tsananin ciwo ba,basarwa yayi kamar ba shine wanda ya kirata ba."Why are you here? "

     "You called me"

       "I'm fine,you can go coz I don't need you now"

       "Tabd'ijan,wannan yana haukane?" Ta fad'a cinkin ranta.

      "'Kazami kawai" Tayi 'kun'kuni ta fita daga d'akin.

      Abincin data kawo masa ma be bud'e ba se yanzu,loman farko yayi ya ajje fork d'in bayaso yaci abincinta sam amma dad'in dayaji yayi yasa ya cigaba da ci.Kad'an ya rage badan ba dad'i ba sedan ya 'koshi,da'kyar ya samu yasha magani tukun ya kwanta.

      12:30pm haka ta tashi ta koma makaranta,lecture d'aya suka 'kara yi ta komo gida duk a gajiye dan ma seda taci abinci ta taho.Tana watsa ruwa ta kwanta bacci,se kusan maghrib ta tashi.Tunda ta sakko 'kasa d'aukan ruwa bata sake fitowa ba se wata washegarin.

      Yana 'kudundune cikin blanket yau ma da zazza'bin ya tashi da 'kyar a daddafe yayi sallah.Tana shiryawa wayarta tayi 'kara koda ta duba taga number da Amjad ya kirata jiya ne.

       "Hello" Ta amsa.

        "Make me ginger tea"

         "Uhum" Ta fad'a ciki bata bari ya sake wata maganar ba ta kashe.

        Seda ta gama abinda zatai tukun ta sauka zuwa kitchen,fara had'a nata breakfast d'in tayi kafin daga bisani ta had'a masa tea d'in."Come in"Ya fad'a bayan tayi knocking.

     Kan  drawer na gefen gado ta d'ire masa,bako sannu tayi fitowarta.Komawa tayi dinning tayi breakfast d'inta tukun ta dawo d'aki ta d'auki handbag d'inta tayi tafiyarta.

     Shikad'ai yayi ta fama da ciwonsa,yanzu daya ji wuya ya kashe Ac d'aki kuwa yana nan yadda yake kaca-kaca.

                 ★★★★

   Yau ta samu lecturen farko ba kamar jiya ba,seda sukai lecture biyu 12:15pm suka tafi cafeteria.Suna fitowa ne wani saurayi dake ciki ya soma biyo bayansu,yana daga side d'in Laila.

     "Assalamu Alaykum"

     Kamar bazata amsa ba ,ta amsa da "waalaikassalm" amma bata kallon inda yake.

    "Baiwar Allah ko zan iya jin sunan?" Ya tambaya yana murmushi.

    Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta, Aliya se bugin hannunta take "Ke baki ji ? Ki sallameshi ya dena bunmu"

     "Please ko zan iya samun number ki?" Ya sake wata tambaya.

       "Bawan Allah kai baka san matar aure bane" Laila ta fad'a rai a 'bace.

       "Ayi min afuwa amma dake matar aure ce nima zan gane hakan,dan Allah ki taimaka ko numbern ki ne ki bani".

     " Mtchww!"Taja tsuka tayi gaba tabar Aliya anan.

     Kai ta girgiza ta bita a bayan dan ita a tunaninta ta fad'i haka ne saboda ya rabu da ita.Ita kanta Laila mamaki ta shiga yi na 'bacin ranta bata zaci haka ba.

    "Haba Laila, shine kike yin 'karya da aure akan bakyaso ki kula wani?"
      "'Karya? akan mey zanyi 'karya shi baida tunani ze tare ni..." Laila bata 'kare maganar ba se ji tayi kuka ya ku'buce mata ,Aliya dake tsaye ta ri'ko kafad'arta ta zaunar kan bench.

     "Abin yakai ga haka?"

      "Aliya baza ki gane ba" Ta fad'a tana 'ko'karin share hawayenta da tissue.

     Shiru sukai na d'an lokaci kafin Aliya ta sake wata maganar."Laila na tambayeki?"

     Kai ta kad'a alamar "Eh".

     "Da gaske ne abinda kike fad'a ,kina da aure?"

      "Ina da aure Aliya.."

      "Kina nufin kice jiya wayar da kikai da mijinki kikai?"

      "Uhmm"

      "Amma  shine kike magana haka? Laila sekace a 'kauye"

      "Please mu bar maganar nan"

      "Keko dan Allah tun yaushe kikai aure?"

      "4month,ki tashi mu tafi ko an shiga lecture" Tayi 'ko'karin kawar da zancen.

     "Idan kince yanzu mu bar maganar ai gobe ma rana ce,idan kikai wasa ma har gidan naki zanzo"

    "Jibeki ni tashi kin fiya manyancen tsiya"

     "Naji,ke kuma babba dake amm..."

      "Amma mey?"

      "Abar kaza cikin gashinta" Tayi dariya tare da mi'kewa.

      "Oho miki" Suka  jera suna tafiya.

     Lecture da aka shiga yasa basi samu lokacin sake magana ba,ana fitowa kowa ya tafi gida.

    Tana shiga gida taga kiran su Aunty bilki ,nan take fad'a  mata suna hanyar zuwa gidanta ita da sauran sisters d'in Mami.

      Short and boring chappy I know,don't forget to comment,share and vote. Love ur❤

Dijensy❤