Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

 A DUNIYARMU CHAPTER A

A DUNIYARMU CHAPTER A

- - Post a Comment

 A DUNIYARMU CHAPTER A


*S*unana ayshat abbakar amma tun ina qarama ake kirana da shukrah bayan na girma wasu nakirana da *A2*.+


Mahaifina da mahaifiyata asalin fulanin yola ne a wani 'dan qaramin qauyensu mai suna ja'a.

Gobara ta kama qauyesu a wani dare Wanda mutanen dasuka fito qauyen a raye qalilan ne ciki harda iyayena bayan sun rasa kowa nasu a gobarar.


A garin Kaduna suka sauka gurin wani aminin babana  yasamo musu hayar gida da aikin gadi ga babana anan kusa dasu gidan wani babban 'dan kasuwa dake unguwar.


Shekararsu tara agarin zuwa lokacin sunada 'Yaya uku duka mata.


Ni *ayshat* nice babba,

Sai *mufeeda* itake bina tsakaninmu akwai shekara shida tukuna autarmu *ameerah* dake shan nono.

Shekarar ameerah 'daya aduniya Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa.


Nataso cikin rayuwar fuska biyu da garari tareda rashin gata da fargabar rayuwar dana tsinci kaina aciki.


Rayuwar danayi batada suna,

Tana 'daukeda darasi,al ajabi da Dana sani tareda axabtacciyar soyayya.

Shiru tayi sbd jikinta daya farayin sanyi takalli 'yan jaridar dake zaune gabanta su uku 'daya na recording biyu na rubutawa.


Saita tuno da wani lokaci acan baya daya shude tasaki wani murmushi mai ciwo daidai nan 'yan jaridar suka kuma jeho mata wata tambayar.


Kallon mai tambayar tayi da sauri sbd sosai ta ka'du dajin tambayar ta miqe da sauri tabar gurin cikin dan sauri sauri.

Idan ba Wanda yasantaba zai 'dauka gasar tafiyace takeyi sbd yanda take karyewa jikinta na juyawa duk da masifaffun heels 'din dake qafarta.


Bodyguards 'dinta ne sukayi saurin mara mata baya.

Qofar dazata kaita palonta direct daga garden 'din ta nufa da saurinta tana dannu hawayen dake qoqarin gangaro mata.


Wasu jibga jibgan sojoji guda biyu sukai saurin bu'de mata qofar ta shige.

Tana shiga palon yan aikita dake hidimar polon sukai saurin xubewa qasa suna mata barka da dawowa amma ko kallonsu bataiba ta haye sama da gudu sbd kukan dayazo mata gaba 'daya.

*******************


*SHEKARUN DASUKA GABATA* .


Tsuke take cikin wani tsinannen mini skirt da iyakacinsa cinyarta ya zauna cif cif a dirarren hips 'dinta,

Farine tas mini skirt 'din sai 'yar siriyar sarqa blue 'daure daga samansa.

Sai Riga blue kalar sarqar mai hannu 'daya mai kama da babu sbd sirantakarsa.

Heels ne aqafarya masu maseefar tsini da tsada ga kuma gashinta data zubo har bayanta sai qyalli yake sbd gyaran dayasha.


Farace sosai ga kuma diri mai kyau balle 'yar kwalliyar dataiwa fuskarta ta qara mata kyau sosai.


Ahaqiqanin gaskia bazaka kalleta kace musulma bace bare Hausa Fulani.


Cikeda yanga da karairaya tareda tafiyar fizgar hankalin duk mai kallonta ta nufi qofar babban bct club ta shige qawayenta biyu suka Mara mata baya cikin tasu qyamatacciyar shigar.


'Daya sunanta meenah abdl ganiyu 'ya 'daya tak ga deputy governor.


Ta biyun sunanta raheena,heena kenan itama 'ya ta biyu kuma 'yar autar  former governor.


Suna shiga suka nufi permanent gurin zamansu suka zauna.


Tray babbba daukeda tsadaddun kwalaben barasa aka kawo aka Jere musu Wanda kullum haka akeyi sbd meena da ita kadai keshan giya acikinsu.


Reena kuwa miqewa tayi ta fada rawa.


A2 kuwa gyara zama tayi tareda crossing legs tahau daddana tsadaddiyar wayarta.


Four hours kenan da zuwansu gurin.

Dan qaramin tsaki taja dan ita ta tsani jira da 6ata lokaci.


Maida kallonta tayi ga meena dake gefenta taga sai kora ruwan kwalba take tana lumshe idanu.


Tsaki takuma ja tareda qara kallon time taga asuba takusa amma baixoba

Wayarta ta 'daga ta danna kira ana 'dagawa cikin qoasawa tace,

        Anty kubby wllh haryanxu gayen nan baixoba kuma kinsan na tsani jira sbd inason nadawo da wuri sbd gobe tunda safe nakeson zuwa gurin momma.Easy A2.,nasani but hkr zakiyi tunda kinga wannan babbane kobayan haka wannan aikin is different sbd idan buqata ta biyane alh manga zai biyawa qannenki ku'din exams dakuma ku'din aikin mommanki dan haka wainan abubuwan zaki duba kiyi hkr da duk abinda zaki gani gurin gudanar da wannan task 'din kuma sanin kece ka'dai zaki iya da gayen yasa manga ya dage saike zakiyi.+


Kashe wayarta tayi batareda ta tsaya sauraren sauran dogon zancenba.

Tsaki taja tareda wurga wayar kan table 'din gabanta.


Tun tana duba time harta daina,iya 6acin rai ranta ya 6aci amma yata iya..

Kiran sallar asuba tafara jiyowa ta miqe tsaye tareda 'daukar wayoyinta da key motarta ta juya gefen meenah taganta abuge takira reeha a waya tace,

      Ki fito ki kamo meena Ku sameni a mota idan kuma kuka tsaya tafiyata zanyi.


Tana shiga motar suna fitowa ko qarasa rufe motar reeha bataiba shukrah ta figi motar a guje tabar gurin.


Idan da sabo sun saba da tuqin shukrah sbd kwata kwata bata tuqi ahankali sai masifaffen gudu akoda yaushe,

Ba tuqi kadaiba akoda yaushe shukrah bata son 6ata lokaci a gaggauce take komai.

Shukrah batasan hayaniya da yawan magana,miskilace ta qarshe duk da basusan waye mahaifintaba amma sunsan dole mai kudine sosai sbd matsiyatan motocin datake hawa tareda tsadaddun situru.


Meena da reeha friends ne tun daga primary haryanxu dasuke a university,

Sun taso a lalace sbd gata da rashin kwa6a da dukiya da iyayensu suka sakar musu..

Tun secondary school suka saba da yawan clubs.

Meenah itake shan ruwan kwalba da kayan maye.,itakuma reeha uwar rawa da son sex ce.


Sun ha'du da shukrah ne a wani babban bikin cika sherarun 'dan wani ambassador a Germany Wanda shukrah itace budurwarsa alokacin.

Haduwarta da burgewarta yasa suka fara shishige mata duk da basusan komai dangane da itaba saidai suna haduwa a club hardai suka saba suka zama friends daganan tafara zuwa dasu babban club din basu taba zuwaba duk yawace yawacensu.


Sunso qwarai Susan  wacece ita,inane gidansu waye babanta amma sun kasa dan babu dama daga A2.


***********

Bayan ta sauke kowaccensu gida ta nufi gida tun kan ta qarasa gate tafara dannawa maigadi horn ya bude tashiga tayi parking ta fito.


Babban palon gidan ta nufa bata tsaya ko inaba sai 'dakinta tayi watsi da wayoyinta kan gado tareda key ta tu6e ta fada toilet tayo wanka tareda alwala tazo ta fara gabatarda sallah.


Har gari yayi tas tana zaune tana istigifar kafin ta miqe 'dauko doguwar rigar jar atampha da hijab dogo har qasa tasa.


Wayoyinta ta kashe tasakasu a drawer gaban mirror dinta ta 'dau wata tsohuwar wayar Nokia na'de da robali ta rufo 'dakin ta fito.


'Dakin dake gefen nata tashiga tareda sallama.


A2 tun yanxu zaki wuce bazaki tsaya ko breakfast kiyiba kuma kinsan manga zaizo danjin Yaya ta kama.


No Anty kubby idan yazo kimai bayanin gayen baijeba gurinba jiya kuma gskia yau inason naje gida da wuri sbd momma kawai nakeson gani dan nasan tanacan tana aiki kuma kinga ba isashiyar lpia ne da itaba.


Kallonta Anty kubrah ke yi tana jaddada qaunarda shukran kewa mommanta da qannenta.


Tana fita daga makeken gidan ta nufi babban titi ta tari adaidaita sahu ta fada.


Wata tsohuwar matacciyar anguwa mai cikeda kwatoci tasauka tabiyasa tareda gangarawa ta shige wani lungu.


Kwatocine birjik a lungun ga yara qanana da manya daketa shigeda ficensu ga qarin wata 'yar bola da'aka qirqira a lungun.


Tsallake kwatocin taita yi harta isa qofar gidansu mai 'dan girma ka'dan tashige.


Sallama tayi agajiye tana zare hijab.


Bafulatanar asali farar mace tas mai dogon hanci da kyau ta 'dago daga tsintar shinkafar datakeyi tasaki murmushin farin cikin ganin 'yarta tace,

     Shukurah tunda safe haka.


Murmushi tayi tana zama kusada ita tace,

     Momma ina kwana.

Lpia klau,ince dai lpia kikayo sammako haka ko hajiyar tayi tafiyane.


Kwantawa tayi a cinyarta tana cewa,

     Lpia klau momma kawaidai na gamo ayyukana da wuri ne.


Shafa kanta tayi tana cewa,

     Allah yayi miki albarka ayshat,

Kin sadaukarda rayuwarki gurin aikatau sbd qannenki suyi karatu kuma musamu rufin asiri..Allah yabaki miji da 'Yaya masu tausayinki.


Wash hawayen tausayin mommanta suka ciko mata ido sbd kullum adduar mommanta kenan akanta.


Momma bakisan mai shukuranki take aikatawa bane,bakisan ba aikatau nakeyiba,

Momma Ina cikin tsoro da fargabar ranar dazaki gane me shukuranki tazama.

Tashi tayi jiki a sanyaye ta kar6i tsintar shinkafar tana gamawa ta kunna itace ta 'Dora girkin sannan ta 'dau tsintsiya ta share gidan tas tukunna ta fiddo wankinta dana mommanta danasu mufeeda tahau wanki.+

Qarfe biyu su mufeeda suka dawo  daga makaranta
Da gudu ameerah ta rungumeta tana fadin,
       Adda shukrah yau a gida zaki kwana ko?

Kamo hannunta ameerar tayi suka shiga 'dakin momma ita kuwa mufeeda 'dakinsu itada shukrah ta fa'da dan cire uniform itama taje gurin adda shukrah.

Bayan sungama komai sun zauna cin abinci mufeeda takalli shukrah tace,
     Addah shukrah saura wata biyu mufara exams 'din gama school itama ameerah suyi exam 'din shiga senior class amma gashi ankusa rufewa haryanxu bamu biy.....

Katseta momma tayi da fadin,
     Mufeeda so nawa zanfada miki ki daina gaggawa a alamari,
Ko tausayin addarku bakyaji kullum gurin aikatau dan kawai kuyi karatu kusamu Rayuwa mai kyau amma ke kullum cikin mitar kudin makaranta kike.,to ai inga kunyi karatun ya isa haka itama abarta ta huta angama karatun dag...

     A.a momma kiyi hkr tunda saura kadan su qarasa insha Allah zan roqi hajiya taban albashina harna watannin gaba sai naje nabiya musu kudin.
Kallon mufeeda tayi tareda dafata tace,
      Kuyi hkr mufeeda insha Allah zaku rubuta jarabawa kamar kowa.

Rungumeta mufeeda tayi da sauri tana hawaye tace,
     Mungode addah.

Itama ruwa idonta ya kawo wannan ke nuna mata lallai tabbas ta tsaya tayi qoqarin cika alqawarin cika aikin alh manga kodan karatun qannenta da aikin momma dan ko a 'dazu ta lura da kakin momma akwai jini aciki alamun ciwonta na nan yana cinta 6oyewa take kadata 'daga musu hnkali.

Qarfe hudu su mufeeda suka shirya sukai islamiyya ita kuma tsintsiya ta 'dauka ta qara share gidan ta 'dora musu abincin dare.

Saidatai sallar magrib kafin ta shirya cikin 'yar tsohuwar atampharta da dogon hijab ta zauna kusada momma tace,
Momma zani.

To shukrah Allah ya tsare kuma ki kula sosai shukrah ki kama mutuncinki.

To..tace jiki a sanyaye kafin tayi bankwana dasu mufeeda ta fice.
************

Kodata isa gidan alh manga na gidan da escort dinshi suna jiran isowarta.

Kai tsaye kujera tazauna kafin ta 'dago kai takalli alh manga tace,
      Barka da zuwa alhaji.

Kallonta yayi da kyau batareda ya amsa gaisuwartaba yace,
       Kaman da magana abakinki?

Ajiyar zuciya ta sauke tace,
      Alhaji ina Neman alfarmar daka biyawa su mufeeda kudin exams kafin nagama wannan aikin dan Ina matuqar buqatar cigaban karatunsu sbd....

No A2,mezaisa ayi hakan bayan ko farawa bakiyiba bare gamawa.

Nayi maka alqawarin cika maka aikin nan muddin kafara biyan kudin kasa aranka angama komai kawai dai yanxu ina buqatar hoton 'dan nasa dakuma wuraren dayake zuwa bayan wannan club 'din.

Wandake tareda alhajin yayi saurin bude briefcase ya miqo mata envelope    yace,
    Duk wani information akansa yananan ciki hadda photonsa,
    Sannan anbawa kubrah ku'di taqaro miki kaya da duk sauran kayan buqata sbd bincike ya tabbatar manada  yaron masiffafen 'dan qwalisane,
Miskili ne,
Kyakkyawa ne dan haka da wuya kyau ya ru'desa,

Yayi first and second degree 'dinsa a Vegas yanzu qwararren doctor ne mai zaman kansa.

Duk inda yake yake yana tareda friend 'dinsa mai suna asheer.

Story continues below

Baya shan alcohol amma ya qware gurin neman mata,

Duk macen datakai masa kanta baya sonta Zai tsaneta dan haka ki kula da takunki.

A2 munsan duk kyansa da 'dagawarsa zaki iya dashi sbd kinada kyau da qirar daukar hankali.

Babban aikin dai kamar yanda kika sani shine kisan yanda zakiyi ki'dau hankinsa ya fa'da tarkon soyayyarki mai ftsanani saiki gabatar masa da alh manga a matsayin mahaifinki dakikeso yasa mahaifinsa yasa Ai masa gwamna ammafa ki kula sosai kada kibasa damar dazai gano wani Abu sai aiki ya kammala buqata ta biya.

Bashi take kalloba amma bayanansa take sauraro cikin qure tunaninta.

Harsun miqe alh manga ya kalleta yace,
    Za'a kawo miki sabbin motoci biyu dan ki riqa canxawa idan xaku hadu.
Mamuh💋
[1/22, 5:50 PM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄

🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

          *7-8*
Bayan fitarsu alh manga ta jima cikin tunani,
Tunda tahadu da alh manga take masa irin wainnan aiyukan bata tabajin fargaba ko shakku ba sai a wannan karon.
Wannan ya banbanta da sauran ayyukan sbd sauran yaudararsu takeyi asamu abinda ake buqata amma yanxu so ake ta saka wani fa'dawa zazzafar soyayyarta,

How? Ta ina zata fara,
Batasan soyayyaba,batasan ma ya akeyintaba bare tasaka wani fa'dawa soyayyarta.

Ajiyar zuciya mai qarfi ta sake tareda maida kallonta ga Anty kubrah cikin kasalalliyar murya tace,

Anty kubby ko kinsan mai yasa alh manga keson zama Governor.

A2 nima abinda nakeson sani kenan sbd kudin dayake kashewa a wannan karon sunyi yawa alamun yana harin manyan daloli a gurin.

Anty kubby bansan ta ina zanfaraba sbd ana magana ne akan soyayya nikuma ban iyataba.

Kadaki damu shukrah zaki iya sbd kin kai inda akeson mace takai,
Duk kyawun da ake iqirarin yanadashi nasan bazai kalleki ya 'dauke idoba.

Jikintane yakumayin sanyi tace,
   
    Ance ya qware a harkar neman mata Anty kubby ina tsoron hakan.

Allah zai cigaba da tsareki shukrah insha Allah.

Miqewa tayi ta haye stairs ta bude 'dakinta ta fada toilet tayo wanka tana fitowa tayi sallar isha tana gamawa ta zauna gaban mirror ta fara tsara fitinanniyar kwalliyar 'daukar hankali.

****************
*JIGON LABARI*
*T* un bayan rasuwar mahaifinsu sun shiga matsi da tsanani na rayuwa uwa uba ciwon zucuyar dayayiwa mammansu mugun kamo sakamakon damuwar data saka aranta na rashin mijinta da makomarta data 'yayanta.

Shukrah ke 'dawainiyar kula dasu sbd itace mai wayo acikinsu.

Matsalar farko dasuka fara fuskanta itace rashin abinci gashi 'dan karatun secondary 'din da shukrah ta fara ta daina sbd 'dawainiyar qannenta da jinyar mommansu.
Wankinsu da tsaftar gidan tareda wahalar komai na kanta.
Rashin mafita yasa ta fara wanke wanke a gidan dake kusa dasu ana bata abinci tana kawowa sunaci.

Sannu ahankali momma taji sauqi hartana 'dan kamawa shukrah aikin daba'a rasaba.

Ahaka harsuka fara wankau ana biyansu suka tara kudin harsaida suka kai dubu biyu shukrah taje kasuwa tasiyo musu quli quli suka fara saidawa.

Da sannu sanaar ta kar6u harsuka qara da saida haddasu omo da sauransu maggi,da kayan miya ahaka harsu mufeeda suka fara girma.

Shukrah da kanta taje tasakasu mufeeda a makarantar islamiyyar bayan layinsu.

Story continues below

Lokaci yaja sosai dan mamma yanxu hadda surfe ake kawo mata ga wahalar aikin wanki bata dainaba har lokacin.

Wahala tayiwa shukrah yawa ta koma sai asabar da lahadi kawai take samun zuwa islamiyya.

Ciwon mommansu yafara tashi sbd ayyukan wahala dan haka shukrah ta hanata aikin komai itakeyi.

Tashin hnkli yafara sako shukrah gaba sbd ciwon momma daya taso haiqan dan har tarin jini takeyi yanxu gasu mufeeda da kullum suke mata kukan sunason suyi karatun boko gashi jarinsu duk ya karye.

A safiyar wata talata suka wayi gari cikin tashin hankalin momma datake ta aman Jini tana somewa.

Rungumeta shukrah tayi tana kuka sosai tareda sambatu gasu mufeeda da ameerah ma kukan sukeyi na ganin momma cikin wani hali mai ban tsoro.

Da gudu tashiga maqwaftansu tana roqonsu amma dakyar suka Ciro 'dari uku suka bata.

Asibitin gwamnati suka tafi aka kar6i momma cikin gaggawa aka fara dubata tareda 'daura mata ruwa.

         Kallonta Dr yayi bayan komai ya lafa momma tasamu bacci yace mata,
    Mahaifiyarki ce?

Eh,mamana ce.

Kozan iya sanin ina mahaifinki.

Ya rasu ta fada kai tsaye dan ta matsu taji meye matsalar.

Babu wani babba ko namiji a gidanku dazan iya magana dash..

Babu,tafada dasauri.

To matsalar itace mamanki na buqatar aikin idan har kinason taci gaba da Rayuwa.

Mamuh💋
[1/22, 8:30 PM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄

🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

           *9-10*
Takarda ya miqa mata tareda fadi,
       Ga kudin dazaki biya nan arubuce zuwa gobe ko jibi dubu 'dari biyar ne,idan kin biya ta rayu idan baki biyaba kuma am sorry.

Wucewa yayi yabarta tsaye tsaye riqeda takarda kamar  photo tana fidda wani irin gumi ga qafafunta dasuka dau rawa.

Jan jiki tayi ta qarasa gaban gadon momma ta rushe da wani irin kuka tana fadin,

Momma ya zanyi?
Ya zanyi da rayuwata idan kika tafi,
Ya zanyi da rayuwarsu ameerah,
Wayyo ni Aysha ya zanyi na tallafi rayuwarsu mufeeda da tawa idan bakyanan momma.

Ahankali momman ta bude ido cikeda azabar ciwo ahankali tace,
     Aysha ki daina kuka Allah zai duba alamarinku.

Cikin tsananin kuka tace,
    Momma dan...

Shihhhh shukrah,ki riqe Allah kinji..
Kuma ki koma gida kizo dasu ameerah tunda ba kowa.

Momma bazan iya barinki ke 'dayaba.

Kadaki damu shukrah zaki dawo ki sameni insha Allah.

Juyawa tayi tana waiwayen mommanta harta fita.

Sauri take sosai danta 'daukosu tadawo gashi maraice yayi sosai dan gaf akeda kiran magriba.

Zaucewa ne kawai batayiba data isa gidan ta tarar da basanan.

Maqwafta ta riqa shiga tana nemansu amma bata gansuba,
Neman kuka tayi ta rasa tsabar tashin hankali dan labarin 6atansu kawai ya isa ya qarasar da mommanta ga mutuwa.

Can bakin titi ta hango anyi dandazo gabanta yai mugun faduwa da gudu ta nufi gurin tana tsananta faduwar gaba.

Wani mahaukacin ihu tasaki ganin ameerah kwance cikin jini anka'deta mufeeda na rungume da ita tana kuka itama duk jinin ameerar ya 6atata.

Story continues below

Mufeeda na ganinta ta zabura da gudu ta rungumeta tana kuka mai tsanani gashi Wanda ya ka'denta ya gudu.

Bata tsaya sauraran wani bayaniba ta duqa ta cicci6i ameerah dake sume ta tari acha6a sukai wani mugun overload itada mufeeda da ameerah ga mai mashin.

Likitan daya kar6i mommanta shiya kar6i ameerah akayi emergency da ita cikin gaggawa.

Hannun mufeeda takama takaita gurin mommansu,
Bacci suka tarar tanayi cikin azabar ciwo sbd yanayinta daya nuna.
      Mufeeda ki zauna nan gurin momma ni zanje gurin ameerah idan momma ta tashi sai kixo ki kirani.
Zama tayi bakin gadon da ameerah take kwance anyi dressing din raunikanta amma har lokacin bata farfadoba.

Hawaye ta share masu zafi,tabbas dazaga mutuwa ta zatakai mata runguma sbd halin qaqa nikayi datake ciki.

Momma na buqatar aiki,
Ameerah ma na buqatar aiki kota rasa qafafunta dan su mai motar ya taka ashe.

Kuka ta darza mai isarta ta miqe cikin jiri ta koma 'dakinsu momma.

Kodata shiga momma ta 'dan farka har mufeeda ta fada mata abinda yasamu ameerah.

Ahankali tace,
      Shukrah ya ameerah take yanxu?

Cikin hawaye tace,
    Mommah taji sauqi rauni kawai taji a goshi.

Addah qafafunta fa mo.....

Kallonda shukrah tai mata yasa ta ha'diye sauran zancenta
Kallonta momma tayi da kyau ta hango tashin hankali a fuskar shukrah 'din amma  saitayi shiru tanajin tausayin shukrah dakuma jin ciwo da damuwar halinda suke ciki.

Washe gari tun asuba ciwon momma ya tsananta banda aman jini ta hanci da baki babu abinda  takeyi dan tuni ta fice hayyacinta.,
Ga ameerah har lokacin vata farfadoba mufeeda kuwa kuka tashin hankali taketa zurmawa.

Gigicewa tai ta fito waje tana neman kuka amma ya gudu  sai qoqarin fita asibitin take tsabar tashin hankali.

_ZAN BIYA KUDIN AIKIN MAHAIFIYARKI DANA QANWARKI_ .

Da mugun sauri ta juyo hartana neman kifewa.

Wata mace ce fara doguwa mai masifar kyau taci ado cikin sutura ta alfarma ga jin da'di da kwanciyar hankali tareda dukiya dasuka bayyana ajikinta.
Zatayi shekaru kimanin ashirin da takwas zuwa da tara.

Kamo hannun shukrah tayi suka nufi wata ha'daddyar Jeep suna isa ta jingina da motar takalli shukrah sama har qasa tace,

     Zan biya ku'din aikin mahaifiyarki dana qanwarki amma da sharadin zakiyiwa maigidana aiki.

Jikinta har rawa yakeyi tace,
     Allah zanyi masa aiki komai wahalarsa zanyi indai zaku taimaki mommana da ameerah.

Kadaki damu ku'din aiki ba matsala bane zamuyi magana da likitocin.

*********

Sallamarsu akayi bayan kwana biyu sbd jikin momma da yayi sauqi akan tsadaddun magungunan da'aka fara bata cikin kudin dasu macen ta biya.

Ameerah madai haka amma bata tafiya dan ba'ai aikinba.

Har zasu fice asibitin ta hangota tayi saurin sauke ameerah data goyo a benci ta nufeta tana cewa,
        Momma kujira ina zuwa.

Bayan mota suka tsaya tace,
      Nagode haj Allah yasaka da alheri.

Kadakiyi saurin godemin tunda ba'ai aikinba sai idan kin amince da buqatarmu.

Ko wane irine insha Allah zan iya idan har zaku biya musu kudin aikin.

To ni sunana *KUBRAH*,
Maigidana kuma *ALH MANGA*,
Idan nace maigidana ba ina nufin mijina ba ina nufin boss 'dina.

Story continues below

Alh manga ya da'de yana neman kyakkyawar mace irinki,
Yarinya,
Mai kyau,
Mai diri,
Mai nutsuwa dakuma sanyi.

Tun shekaran jiya naganki kuma nasan kin kai bai 6ata lokaciba nakirasa nafada masa yace indai zakiyi a biya komai nasu mamarki.

Ba wani aiki bane face ki zama mukullin cimma buqatunsa,

Ma'ana zai sakaki makaranta ya sakar miki dukiya,
Rayuwarki ta canxa,

Kizama babbar yarinya duk dan ki riqa yaudarar masa manyan masu daloli su riqa basa dukiyoyinsu da kadarorinsu da kamfunnansu.

Alh manga nada dukiya mai tarin yawa sbd h....

*KARUWA*,
*KARUWA* kukeson nazama.
Mamuh💋
[1/23, 10:40 AM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄

🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

         *13-14*
Mafarin da shukrah ta zama mai fuska biyu kenan,

Anyiwa mommanta aiki hakama ameerah dan yanxa tafiya take da qafafunta.

Gidama ansiya saidai gudun momma tayi zargin wani Abu sai aka siya 'dan madaidaicin flat a wannan anguwar.

An saka su mufeeda makaranta.

Anty kubby ta gabatarwa da momma amatsayin wadda ta taimakesu ta biya komai tareda basu gida da sakasu ameerah makaranta sannan ta 'dauketa aikin aikatau a gidanta saidai da daddare zata riqa zuwa sbd kular mata da yaranta dan ita likita ce a asibiti take kwana.

Wannan qaryar a shimfidawa momma duk da haka daqyar ta yarda harsaida aka 'dauketa aka kaita gidan kubrah ta gaisa da alh 'dahiru amatsayin mijin kubrah harda su godiyart.

Sosai momma tayiwa shukrah nasiha da jan kunne kafin tafara zuwa aikin.

Abinci saida aka cika musu store dashi babu abinda ba siya musuba a gidan har abin yafara ba momma tsoro saikuma ta duba kamalar kubrah da kirkinta saita cire komai aranta.
Kafin afara komai saida kubrah taje tayiwa momma qaryar zatai tafiya yanaso shukrah takoma gidanta ta kula da yaranta har ranar data dawo.

Hakadai momma ta yarda batareda tunanin komai arantaba.

Sukuwa qasar dubai suka Lula da shukrah inda aka wanketa aka koyo mata makeup da iya tafiyar 'daukar hankali da duk wani salo dazai fizgi hankalin namiji akanta.

Miliyoyan ku'di alh manga ya kashe akanta,

Set 'din akwati biyu aka ciko mata da situru na banza dana alfarma.

Satinsu biyu ta iya duk wani abinda aka koya mata ga wani irin canxawa datai kyau da dirinta ya qara fitowa Wanda ko su alh manga sai yanxu suke qara tabbatar da kyawunta.

Bayan dawowarsu kullum a gida take yininta sai bayan magrib take zuwa gun aikin.

Mommah ta yarda da kubrah sosai shiyasa hankalinta ya kwanta suke rayuwarsu.

**************
Nasarori sun samu fiyeda zato ga alh manga dan tun zuwan A2 sunan dasuke kiranta dashi kenan.

Tun zuwanta dukiyarsa ta nin ninku dan tuni ta qware a yaudarar manyan qasa,

Zatai shigar 'daukar hankali ta riqa kwadaita musu kanta harsai sun saka hannu a takardai mallakar wani 6angare na dukiyarsu saita warewarta batareda ta baka abinda kake kwadayiba.

Sannu ahankali alh manga yasata university amma part-time harta gama.
Sosai rayuwarta ta canxa da hutu qwarewa a aiki,

Story continues below
Ga motocin data hawa kullum cikin siya mata abubuwa ake,

Komai iskanci kaya bata kunyar sakasu dan tanajin 'dadinsu sosai.

Clubs kuwa manyan take zuwa bare data hadu dasu meenah.

Momma,mufeeda da ameerah kuwa Rayuwa tai musu 'dadi babu abinda suka nema suka rasa dan ko makarantarsu mufeeda mai shegiyar tsada ce.

Hakama duk wata tana kawowa momma dubu goma tace,
     Albashinta ne.

Sosai alh manga ke bata dukiya da kadarori saidai tace,
Ya riqe kawai.

_WANNAN KENAN_

*****************
*DAWOWA LABARI*

Yau tsuke take cikin wani fitinannen bums short na black jins da red spaghetti top.

Takalmin qafarta red ne masu tudu sosai.

Kamar ko yaushe bata saka sarqa sai manyan earings.

Yau kam club 'din acike yake da 'yayan banza ta fada a ranta lokacin datake nufar gurin zamansu.

Yau ko zama heena bataiba ta fa'da gurin rawa meenah kuwa tuni tabada odar kayan kwalba.

Wani ke6antaccen guri ta hango da security 'daya a tsaye.

Qurawa gurin ido tai tana son ta hango target 'dinta.

Tsaki taja ahankali sbd ita takasa hango fuskar.

Miqewa tayi ta nufi garden 'din club 'din dan kiran Anty kubby tace ta turo mata hotonsa yanxu a waya dan ita ta manta bata duba hotonsa dasu manga suka bata.

Mamuh💋
[1/23, 9:21 PM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄

🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

           *14-15*
qoqarin kiran Anty kubby take tafara jiyo wata muryar data fara sanyaya mata jiki tunkan tagai mai ita.

Juyowa tai takalli inda muryar ke fitowa
Idonta ne ya sauka kan wani handsome  kyakkyawa ajin qarshe.

Qananan kayane ajikinsa da silipas din maza masu tsada na kamfanin CBGB.

Gashin kansa kuwa ya sha gyara i rin na larabawa.

Waya yake cikin nutsuwa wanda ga alama shima hayaniyar ya baro dan yasamu wayar cikin nutsuwa.

Neman rikicewa take sbd kwarjininsa da zuciyarta datahau bugawa da sauri.

Kasa kuran anty kubby tayi ta koma jiki a sanyaye ta zauna tana tunanin ta inda zata fara.

Wani siririn tsaki taja tana cewa da gani saiyayi girman kai.

Abun farko datayi tunani shine tana hango ya gama wayar ta miqe ta nufi gurin.

Dai dai zai fito ita kuma zata Shiga.
Lanqwasa qafarta tayi tai luuu zata fadi
Harta cire ran zai riqota taji ya riqota ta fado jikinsa.

Shock 'din gaske ya kamasu lokaci 'daya.

Lumshe ido yayi sbd taushin fatarta da futinannen qamshin dake fita daga jikinta.

Rawa jikinta yafara sbd jin yana qoqarin qanqameta.

Qwacewa tayi da sauri tace,
Sorry.

Da sassarfa ta juya tabar gurin gaba 'daya batareda ta tsaya nemansu meenah ba.

Tana isa gida ta zube a gado tana sauke ajiyar zuciya.
    Ya salam..ta fada tana rintse idanu.

Kwata kwata ta manta da abinda yakaita gashi tayi missing wannan chance 'din.

Tu6ewa tayi tayo wanka tazo ta kwanta.

*****************
Gidane babba daza'a kira da mansion sbd girmansa da kyansa.

Securities ne sosai ke gadin gidan sunkai biyar.

A hankali ya fito daga part 'dinsa ya nufi na iyayensa.

Agogon hannunsa yakalla yana shiga palon.

Gaidasu yayi yana zama tareda 'daukar ruwan dake gaban daddynsa ya 'dan kurba.

Dad kakirani hp all is fine.

I hope so son,
But you mother here said she has sumtin very important to tell us.

Kallon mum 'dinsa yayi da kyau kafin yataso yazauna kusada ita ya riqo hannuwanta cikin kulawa yace,
     
       Mum you seems very worried pls tell me meye ne?.

Damuwarta yaga ta tsananta a fuskarta
Rudewa yayi ya raqa ruqota yana fadin,
      Mum dan Allah ki fadamin damuwarki idan zamu iya insha Allah zamu magance miki ita.

Dad 'dinsane ya miqe tsaye yace,
      
    *EMRAN* ina tunanin tofa kaine damuwar mahaifiyarka.

Dad..
   
  Yes emran sbd haka ka lallaba kaji wat is problem.

Juyawa yayi ya hayewarsa stairs yabarsu palon.
Murya na rawa cikin ru'du yace,

    Mum nine damuwarki?

Kai ta 'daga alamar eh.

Ru'dewar daya kumayi tafi ta farko ya zube gabanta yana cewa,
      Mum nayi miki alqawarin yaye damuwarki idan har bata sa6awa addini ba.,just tell me mum what is da problem.

       Kayi aure,..

Sakinta yayi tareda miqewa tsaye yace,

      Mum pls kadaki dawo da wannan zancen sbd Haryanxu banga irin wadda nakeso ba.

Katsesa tai da fadin,

to kabari ni na za6a maka.

No mum duk wa'inda kike za6owa basada tarbiya duk sun waye sosai sunyi yawon turai and you know I dont like girls like that.

Nafison 'yar data fito from low class family sbd zatafi bin dokokina da ra'ayina.
Dan haka pls mum kibar maganar auren nan yanxu ki qara bani time.

Wannan shine alqawarin dakaimin na yayemin damuwata,for god sake emran baka tausayamin inaso naga jikokina amma sai qoqarin zuban qasa a ido kake.

Cikin sanyin jiki yace,
     OK mum kiyi hkr ki qaramin time insha Allah zanyi idan banyiba na yarda ki za6amin da kanki.

Cikin farin ciki tace,
     Yauwa my boy Allah yai maka albarka kaje nabaka wata 'daya.

A tsorace yace,
     Mum wata 'daya yayi kadan saidai wata biyar.

Aa biyar kuma yayi yawa na qarama wata 'daya idan kuma suka cika baka fitarba ka shirya a watan za'a 'daurama aure da duk wadda ta kwantamin.

Baiji da'din zancenba ko ka'dan dan haka yana zuwa 'daki wanka yayi ya shirya ya nufi club.

Motar asheer daya gani ya tabbatar da yana gurin.

Sosai yake cikin zafi sbd maganar mum ta kunnosa shiyasa bai ankaraba yaji yayi karo da mutum harsaida wayoyinsa da nata suka zube qasa.

A hasale ya 'dago yakalleta tun daga samanta har qasanta
Yaji wani baqin cikinta ya tsayamai a maqoshi.

Doguwar rigace iya cinya ajikinta gashi rigar batada hannu ko 'daya
Ga gashinta yau pakesa tayi tsakiyar kai yana lilo ga uban heels 'din dake qafarta..
Iya kyau dai tayi abinta.

fa'di sbd mugun kallon daya fara aiko mata jikinta ya 'dau rawa dan satinta biyu a kwance tana jinyar mugayen maganganun daya sakar mata last time.

Ganin gurinsu ya nufo yasata miqewa da sauri tabar gurin tayi can baya inda ba mutane ta boye.

Fisgota taji anyi da qarfi harsaidata fa'da jikinsa ya tureta da qarfi cikin tsana yace,
         Ban wayata.

Jikintane yakuma 'daukar rawa tana masa kallon wace waya.

Ganin zata 6atamai lokaci fizgi wayar hannunta tareda wurga mata tata.

Na kar6i wayata ne sbd kawai contacts 'dina masu mahimmanci dake ciki badan hakaba da babu abinda zanyi da wayar datai kwanaki gurin karuwa.
   Sannan daga yau karki kuma bari na ha'du dake irin wa'inan gurin dan saina karya miki wuya,wawuya kawai.

Durqushewa tayi agurin tareda sakin kuka cikin tsananin jin ciwo da tarin dana sani sbd yau qiri qiri ankalli cikin idonta ankirata da karuwa.

Tabbas yau taji baqin cikin dayafi na rayuwarta ta baya,

Miqewa tayi ta bar gurin da matsiyacin gudu
Ko agidanma kwana tayi tana kuka.
Hardai idan ta tuno mommanta zata iya rasa ranta duk ranar data gano gaskia.

Lokaci yayi dazata bar wannan muguwar rayuwar zata koma gida ta zauna taredasu mommanta da qannenta.

Mamuh💋
[1/25, 1:56 PM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄

🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

            *18-19*
Yau akasalance ta shirya cikin pencil jins da jar riga mara hannuwa ta 'dau keys 'din motarta da wayoyinta ta fice.

'Daya daga cikin motocinta ta nufa ta shiga tabata huta tareda yin ribas ta fuskanci gate zata fita.

Wani mahaukacin burki taja saura qiris motar ta qwace mata sakamakon ido hudu datai da mufeeda tana kallonta hawaye na fita fuskarta sosai.

A rikice ta fito ko kashe motar bataiba ta nufeta amma kan ta qarasa mufeedar tai saurin ja da baya fuskarta cikeda mamaki da tarin tambayoyi.

Qasqantacciyar Shigarta take kallo tun daga sama har qasa.

Hawayenta suka qaru a hankali tace,
    Momma batada lpia sosai shinazo nafada miki.

Tana gama fada ta juya da gudu tabar gidan.

Sosai take cikin furgici da tashin hnklin ganin da mufeeda tai mata a irin wannan yanayin ga tuqa motar dataga tayi.

Da sauri takoma cikin gida ta canxo kaya tareda dogon hijab ta fito ganin tana a rikice sosai yasa Anty kubby ta fidda mota takaita gidan.

Koda suka isa ciwon ya qara tsananta dan tuni momma ta fice hayyacinta.

Kamata sukai a gigice sukai wani sabon babban private hospital.
Da gaggawa aka kar6eta aka shige emergency da ita.

'Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalli mufeeda data koma gefe ta rungume ameerah tana wurgo mata wani irin kallo.

Matsawa tayi jiki a mace ta kamo hannun ameerah tana cewa,
     Kuzo Anty kubby takaiku gida gobe kuje school tundake mufeeda kuna final exams.

Cikin idonta mufeeda takalla tace,

   Ni mufeeda daga yau nagama zuwa makaranta harsai nasan ta hanyar da ake samo kudin biyan makarantar.

For god sake mufeeda kadaki qaramin damuwa,kinsan kudin aikina ne ake biyan makarantarku dashi kawai ki ja ameerah kuje nizan kwana anan tunda kinaji nurse tace sai gobe Dr zai shigo so pls will you just go and stop giving me that look.

Qara waro ido mufeeda tai sbd jin shukrah tai turanci alhalin sunsan bata iyaba sbd batai karatu ba.

Rintse ido shukrah tayi sbd tasan ta qara bawa mufeeda dalilin wani zargin.

Juyawa tayi zata bar gurin da sauri.

Adda ki daina wani 6oye 6oye kawai ki fito ki fa'dan me kika zama idan kuma kinqi idan momma ta tashi ita saiki mata bayani.

Cikin 6acin rai ta katseta da fadin,
     Momma batada lpia idan kikai kuskuran fada mata abinda zai 'daga hanklinta to zakiga cikakken 6acin raina.

Kenan tunani yazama gaskia tsawon lokaci ha'intar momma kikeyi kina ciyar damu da ku'din ka......

Tassssssss ta wanketa dayasata zubewa qasa dafe da kumatu tana hawaye.

Anty kubby tai saurin riqe shukrah tana cewa,
      A2 pls kadaki biyewa maganganunta.

Ke kuma mufeeda kisan abinda zaki ringa fadawa shukrah sbd addarki ce kuma gaba 'daya abunda kike tunani ba haka yakeba.

Anty kubrah dan Allah kidaina kareta kibari ta fada da bakinta sbd batun yau na ta6a ganinta a irin wannan qazamin yanayinba amma saina qi yarda da itace  amma yau nagani na tabbatarda ita 'dince canzawa tai takoma mai...

Hannu shukrah takuma 'dagawa zata kuma bata wani marin Anty kubby tai saurin riqeta.

Kuka ya kufce mata tace,
    Anty kubby kinaji duk abinda mufeeda take fada,
Mufeeda ni kike fadawa magana irin haka?1

Cikin tsananin kuka itama mufeeda tace,
       Idan qarya nake ki qaryata da bakinki ki fadi gaskia da kanki
Kozakita dukana bazan fasa fadaba dan ayau inason nasan gskiyar halinda muke ciki.

Wani gigitaccen marin shukrah ta sakar mata tareda fadin,
    Idan kin manta na tunamiki ni yayarkice ina kuma da damar yin komai akanki and one more thing idan kika fadawa momma wata maganar dazata iya halakata to ki tabbatarda kinshirya shari'a dani.

Jansu mufeeda Anty kubby tayi daqyar takaisu gida dan hatta ameerah kuka takeyi sbd ganin yayunta na fada.

Shukrah kuwa kwana tayi a zaune tana kuka sbd ganin komai na Neman ca6e mata.

****************

Qarfe goma na safe Dr yashigo duba momma lokacin shukrah na toilet.

Tana fitowa nurse tace yanxu Dr yafita  amma kije office 'dinsa dan yanason ganin masu patient 'din.
But kiyi sauri dan Dr emran bayason wasa da lokaci dan anytime zaki iya zuwa ki tararda bayanan.

Ahankali take tafiya sbd rashin kuzari na rashin kwanciyar hankali.

Hannu tasa ta goge hawayen dasuke gangaro mata

Karon datai da mutum yasa tayi saurin dawowa daga duniyar tunanin data fada tana tafiya.

Ja da baya tayi da sauri lokacin datai ido hudu dashi yana  watsa mata kallon tsana da wulaqanci.

A iya sanina nanba asibitin masu awon HIV bane sbd irinku awon hiv ne kawai Ke kawoku asibiti and that's wat girls like you truly deserve and....

Cikin tsananin kuka ta katsesa da fadin,
    Niba karuwa bace kadaka Ku...

Shut up idan Ke ba ita bace mecece
macen datake yawon dare cikin shigar banxa mecece stupid kawai.

Tsaki yaja da qarfi tareda juyawa ya bar asibitinma gaba 'daya ko office 'dinsa bai shigaba.Baqin cikin maganganunsa yasata fashewa da wani sabon kuka ta juya da sauri zata bar gurin sukai ido hudu da mufeeda a tsaye tana hawaye itama alamar taji komai da emran ya fadawa shukrah.+


Mufeeda is not wat you're thinking I.......


Da gudu mufeeda tabar gun vatareda ta tsaya sauraran shukrah ba.


Jan qafa tayi da qyar na nufi office din Dr saita tarar shima bayanan batareda tasan emran ne Dr dinba.


Koda takoma 'daki momma ta farko su mufeeda da ameerah na zazzaune kusada ita Anty kubby ma tazo tana tsaye tana ha'dawa momma tea 'din datazo mata dashi.


A darare ta zauna kusada momma tana hawaye

Ita kuwa mufeeda shukrah na zama ta miqe tabar 'dakin.


Anty kubby tabita wajen tace, 

      Mufeeda abinda kike tunani Sam ba haka...


Anty kubrah kiyi hkr a yanxu zaiyi wuya na yarda da abinda zaku fada sbd tunanina akanku yayi nauyi kibarni tunanina yadawo daidai tukuna.


Tafiyarta tayi tabar Anty kubby a gun  bayan tagama fadar hakan.


    Shukrah dake tsaye tana sauraronsu ta matso gun Anty kubby jiki a sanyaye tace,

   

     Kibarta Anty kubby zuwa gaba zata gane.,

    Sannan Anty kubby result din momma ya fito sai ankuma yi mata aiki  

Wannan karon idan anyi bata warkeba to bazata taba warkewaba.


Kamata Anty kubby tayi sbd ganin tana Neman faduwa sbd kuka tace,,


      Shukrah dole muyiwa alh manga maganar kudin aikin.


Cikin kuka tace,

Anty kubby alh manga ba biya zaiyiba idan harba cika masa wannan aikin ba sbd kudin Nada yawa sosai.


Nasawa raina na daina wannan rayuwar sbd babu abundata kawomin sai baqin ciki da fargabar yaushe momma zata gano halinda nake ciki.


Kuma Wanda akeson nayi aikin akansa ina saka ran babu Wanda ya tsana yake qyama a dunia sama dani amma nayi alqawarin cika masa aikinsa a kwanan nan akaro na qarshe,


Dazaran nayi wannan shikenan bazaku sake ganinaba zan koma na rungumi 'yan uwana da talaucinmu.

*************


Kwanan momma biyu aka sallamesu da nufin next week za Ai mata aiki.


Tunda suka dawo momma ta fahimci akwai rashin jituwa sosai tsakanin shukrah da mufeeda.


Ta tabayi shukrah tace mata babu komai,


Mufeeda kuwa data yambayeta cewa tayi kawai karatun jarabawane.


Shukrah takoma aikinta amma tsoron emran 'din ko yaushe Ke kashe mata jiki takasa fita ko ina.


Emran kuwa lokacin da mum tabasa yakusa qarewa amma babu wadda ya fitar saima qoqarin burin qasar dayakesonyi.


Yau da daddare shukrah na fita mufeeda ta lalla6a tabita bayan tayiwa momma qaryar maqwaftansu zata shiga gun nanah qawarta.


Mashin ta tara tahau suka nufi gidan Anty kubby.


Nesa kadan da gidan tacewa mai mashin ya tsaya.


Sun kusan Rabin awa agun kafin ta hango magadin gidan ya bude gate tayi saurin hawa mashin 'din tana cemasa subi motar.


A guje tafito daga gidan tahau titi cikin wani matsiyacin gudu


Suma suka mara mata baya a gujen da mashin.


Daidai gidan su meenah ta tsaya suka fito cikin tasu waxamiyar shigar suna shiga taja suka wuce.


Ba qaramin mamaki da fargaba tashigaba lokacin dataga sun shige wani hotel mai hawa hudu.


Story continues below

Hanasu shiga akai da mashin dole ta sauko tana cewa mai mashin din yajirata.


Lalla6awa tayi ta boye bayan wata mota dake gefen ta shukrah.


Duk da dare ne tana iya ganin yawan 'yan matan dake gurin cikin qazamiyar shiga.


Qirin ya rage numfashinta yabar jikinta lokacin da shukrah ta fito motarta.


Shigar jikinta tayi muni matuqa sbd mini party dress ne ajikinta pink colour.


Kuka take qoqarin yi amma yaqi zuwa sbd tsoron ganin shukrah a wannan yanayin.


Shigewa sukai club 'din suna wata karairaya.


Ganin kaman bata hayyacinta yasa mai mashin Jan hijab 'dinta har gurin mashin tahau jiki na rawa sukabar gun.


Suna isa ta biyasa ta nufi gida jikinta na makyar kyatan sanyi dan zazza6ine ya rufeta nan take.


'Dakinsu ta shiga tareda zubewa qasa ta saki kuka mai 'dan qarfi.


Kuka ta darza da kyau har bacci yadauketa agurin.


**********


Mufeeda kiyi sauri mana kifito muje asibitin nan na dubo iya mairo tunda kinga dare yafarayi muyi sauri mudubota mudawo kafin sallar isha.


To momma banace muje da ranaba kikace gwara da daddare yafi 'dadin zuwa.


To nidai fito muje,


Ahanya firarsu suke suna tafiya dan dama da qafa zasu sbd ba nisa sosai.


Sunkai asibitin suna gab da shiga wata mota ta Parker gabansu tareda zuge glass.


Yawu ta hade da sauri sbd ganin 'yan matan nan biyu data gani tareda addarta a club.


Wadda ke tuqin tace,


A2 lapia naganki haka kuwa?


Cikin rawar murya tace,

        Ba ita bace.


Meena takalli Reena tace,

    Heena kalleta dakyau ba shukrah bace,

Shukrah 'yar qwalisa ce ba kamar wannanba.


Jawo mufeeda momma tayi tana mamakin ina shukranta tasan wainnan marasa tarbiyar,


Lallai ba shukrahta suke nufiba qara kallonsu tai tace,


      Wannan ba wadda kuke nema bace.


Harsun fara tafiya meena tayi saurin fitowa tana cewa,


     Yi hkr mama amma bari na nuna miki hoton wadda muke nufi zakisan sunyi kama sosai.


Cikeda 'dokin son sanin wani bayani gameda A2 ta 'dauko wayarta a mota ta nemo photunan shukrah cikin shiga Mara kyan gani.


Saurin katseta mufeeda tayi da fadin,

     Kibarshi bamason gani,

Momma muje.1


Mamuh💋

[1/27, 6:14 PM] Real Mamuhgeee: © _*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*_ 🐄


🌍 *_~A DUNIYARMU~_* 🌍


© _*MAMUH GEEE*_


*Dedicated to*

_Ummy Aisha_

_Mammy wambai_


                  *22*

Ganin mufeeda ta hade rai tareda daburcewa yasa mommah tsareta da ido cikin zargi kafin tamaida kallonta gun su meenah tace,


       Shukran da kuke nufi tayi kama da wannan ne?


Da sauri sukace eh,,

Sudai burinsu su san wani Abu dangane da A2 dan suna tsananin kwadayin son sanin ko ita 'yar waye.


Suna kama sosai kuwa kinmaga hotonta.


Kallon hoton dakyau  momma tayi cikin tantama tace,


     Mufeeda dubamin hoton nan dakyau kamar shukrah ko?


Ko kallon hoton mufeeda bataiba tace,

    Momma ba ita bace muje dan Allah.


Ameerah tayi saurin cewa,

     Adda shukrah ce wannan adda mufeeda ki kalla da kyau zakigama abinda kuke magana aranar keda ita har kukai fada ta marek.....


Buge mata baki mufeeda tayi da qarfi harsaida bakin ya fashe.


Girgixa sosai momma tayi cikin tsananin zargi da fargaba kafin ta kama hannun ameerah suka juya gida batareda sunma shiga asibitinba.


Ta jima qofar gida tana saqa da warwara sbd ta hango maseefa a idon momma dama ga momma ta iya hukunta mutum cikin tsanani.


Shahada tayi tashiga tanabin bango ahankali zata lallaba tashige daki har takai qofa taga an haskota da fitilar hannu kasancewar ba NEPA.


Cak ta tsaya jikinta babu inda baya 6ari ga hawaye da tuni suka fara saukowa sbd tsoro.


Sosai momma ta kalleta kafin tace,

    Mufeeda maiya hadaki da addarku har ranta ya 6aci ta mareki?


   Cikin rawar murya da rawar jiki tace,

     Babu komai momma dan Allah kiyi hakuri.


Wata tsawa ta daka mata saidata kusa sakin fitsari tace,


     Kunsani cikin wasi wasi da fargaba,

Bazan iya kwana a yauba batareda nasan abinda ke Neman raba kankuba,,

Sannan ayau basai gobeba zakibawa addarku hkr dan haka wuce muje gidan haj kubrah yanxunan.


Riqeta mufeeda tayi da sauri tana hawaye tace,

      Momma dan Allah kibari sai gobe idan tazo wlh zan bata hkr amma dan Allah kar muje gidan yanxu.


Kuka takeyi sosai tana roqon kar suje yanxu Wanda yaqara jefa momma cikin zargi da mamaki.


Cikin tsananin rudani da fargabar amsar dazataji tace,


    Mufeeda idan yau bakifadamin abinda ke tsakaninki da shukrah ba ma'ana laifin dakikai mata haryakai ga mari to wlh na cireki cikin jerin 'yayana.


Wani irin fitsarine mai zafi ya kubce mata jikinta ya'dau rawa..

    Momma dan Allah ki janye kalamanki.


Cikin sanyin jiki tace,

    Bazaki fadaba kenan.


Juyawa tayi zata wuce mufeeda tayi saurin riqota tana cewa,


Zan fada,zan fada momma.


Tsareta momma tayi da ido tana jiran taji abinda zata fada.


Momma adda..adda um am adda karu..am karuwanci tak......


Tasss tasss taji momma ta sakar mata marukan dasuka gigitata tayi hanyar 'dakinsu a kidime momma ta fixgota da qarfi tareda ingixata gaba tace,


Wuce muje gurin shukrah yanxu dan sai acan gabanta zan hukuntaki butulu.


Momma dan Allah kiyi hkr gobe idan tazo na yarda ko wane irin hukunci kutaru kumin amma dan Allah momma kadamuje yanxu.


Janta momma tahauyi cikin 6acin rai daya rufe idanuwanta.


Ameerah ta rufe gida tabi bayan itama tana hawaye.


Tunda suka samu napep suka shiga mufeeda ke kuka tana adduar Allah yasa su tarar da shukrah a gida kuma cikin shigar kamala batareda momma tagano komaiba.


Sosai itama momma ke cikin fargaba sbd gabanta dake tsananta faduwa.


O qofar gidan aka ajesu

Ameerah ta tsaya biyan mai adaidaita.


Motar data fitoce daga cikin gate din gidan taja hnklin mufeeda sbd taga idanba shukrah bace.


Momma gani mufeeda na kallon motar saita maida kallonta a motar.


Atareda ameerah suka kira sunanta.


       Shukrahhhh😳

      Addahhhh😳


Maido kallonta tayi da ga mufeeda taga tayi saurin sunkuyar dakai babu alamun mamaki a tattareda ita.


Komawa cikin napep 'din tayi da sauri sukabi bayan motar.

Post a Comment for " A DUNIYARMU CHAPTER A"