YARDA DA KAI CHAPTER 7

YARDA DA KAI CHAPTER 7
Tafiya mabuɗin ilimi, shine abun da Kamalu yake faɗa a yayin da yake ƙara wara idanuwansa yana bin ko wani gari da zasu gifta da ido. Ko kaɗan bakinsa bai huta ba, balle ya giya, ko wani gari suka gifta zai yayi tambaya akan ina ne suka zo? Isah direba shima ya biye masa, sanin wanan shine karo na farko da ya taɓa tsallake ƙafarsa ya bar jaharsa.+ Akwai tazara sosai tsakanin Bauchi da Jigawa, wanda a ƙallah sai da suka shefe awanni bakwai suna tafiya, wanda a lokacin har Kamalu ya gaji da magana yayi shuru. Gefan ANA kam banda fargaba da tunanin halin da zai riski garinsu ba abin da yake, duk da ya sauya sosai amma jini ba wasa ba, asalima kamarsa da ta Mahaifinsa na ƙara fitowa, fatarsa da tayi duhu yanzu ta haska wadda kuma dama can hasken fatar mamansa ya biyo, manyan idanuwansa sun koma masu buɗewa, saɓanin a baya da suke yawan lumshewa akai akai, sai dai miskilancinsa da ya ƙaru, wanda magana ke masa wahala saboda sabo da zama shurun da yayi a jeji tsawon shekaru uku. Kamar yadda Abba ya tsara musu a birnin Dutse suka tsaya, suka kamawa Isah direba ɗaki a hotel, kana suka ci abinci suka yi sallah, suma suka shiga suka yi wanka. Wani mai sufa shafa a fuskarsu wanda yasa fiskarsu ta surka duhu, haka ma jikinsu, sanan suka ɗauko wata riga ganjangara, da wandonta daban, sai hula irin ta tashi karka dameni ɗin nan, wani takalmi sosa suka sa ruwan hoda tsar da shi. Suka fito waje da 'yan kayansu a leda, suna fitowa Isah direba ya kwashe da dariya yana nuna su "Aradun Allah babu wanda zai ganku ya ce kun taɓa zama a wani birni ko wani gari. Taɓɗijam waima kun ganku?" Kallon juna sukayi kowa yana ma ɗan uwansa dariya, saboda kamar da suka sauya, ƙarshe dai Isah direba ya karɓi wayarsu ya musu hoto a tare, nan suka rinƙa dariya. Tare suka fito da shi ya ɗaukesu a mota ya kaisu har tasha, ya nema musu motar da zata kaisu har Bamaina, sanan suka yi masa sallama suna ɗaga masa hannu. "Garin nan ya sauya sosai Kamalu, a cikin shekara ukun da nayi bana cikinsa komi ya sauya, an samu ci gaba ta fannoni da dama. Haka tsarin gine-ginensu ya bunƙasa saɓanin lokacin da na barshi." Ana ya faɗa yana murmushi. Kai Kamalu ya gyaɗa cikin gamsuwa da maganar Ana "Kasan zamani abokin tafiya ne, haka yanzu hankalin mutane yana ga kan samun ɗaukaka, kamar yanda ake tsere na ganin nine nafi kowa, shi yasa komi ya koma kamar gasa." Murmushi Ana ya yi cikin gamsuwa da maganar Kamalu. Daga nan suka ci gaba da wara idanuwansu har suka shiga cikin garin Bamaina. Motar har garin ta shiga, saboda suma ba laifi sun samu ci gaba sosai, hanyar tayi kyau, kamar yanda aka samu yawaitar motocin haya a garin. "Alhamdulillah!" Abin da Ana ya faɗa kenan, lokacin da motarsu ta tsaya, hakan yasa Kamalu shima yin hamdala ɗin. Tunda suka sauƙo a garin mutane suke binsu da kallo, musamman ganin yanayin shigarsu, da fuskokinsu, wanda da gani basu da wata kama da 'yan asalin garin. Suma bin mutanen suke da kallo, da yawansu kowa na hada-hadar gabansa, wasu kuma suna zaman gindin bishiya suna hira, yawanci dattijan garin ke ta faman kai kawo, wanda da gani suna neman na kansu ne, yayin da yaransu ke gefe suna shan iska da zaman kashe wando. Murmushi Ana yayi yana kallon Kamalu "Kaga har yanzu ɗabi'ar matasan garin nan bata sauya ba. dan har yanzu iyayensu ke zirga-zirga yayin da su suke zaune a ƙarƙashin inuwa ana labarin ƙanzon kurege." Murmushi Kamalu ya yi, yana ƙara kallon dabar da suke wucewa da matasa a cikinta. "Ba'a taɓa raba mutane da ɗabi'arsu, musamman abin da suka ɗauka a matsayin al'ada da kuma ratsawar jini a tsakaninsu. Bana jin zasu iya yin wani yunƙuri bayan suna da ɗabi'a irin ta iyayensu, ga kuma zagayawar jinin da ke tafasa a jikinsu." Dariya ANA ya yi sanan ya tare wani dattijon mutum da ya zo wucewa ta kusa da su. "Sannu Baba." "Yauwa sannunku dai samari." Ya ɗaga ƙafa da zummar ci gaba da tafiyarsa. "Baba dan Allah tambaya muke da ita." "Allah ya sa na sani yaro!" "Mu baƙi ne muka zo wucewa, muna tambayar gidan Mai gari." Kallonsu yayi sai a lokacin ya kula da shigarsu, wanda ba suyi kama da 'yan asalin garinba, duk da sun sa kaya daban-daban amma da ganinsu wuya bata kama jikinsu ba. "Kunyi sa'a kuwa, dan nima hanyar da na nufa ce, sai ku biyo bayana." "Yauwa mun gode sosai." Ana ya faɗa yana wara bakinsa. Yayin da Kamalu ya ke binsa da kallon mamaki, dan bai ɗauka zai manta hanyar gidan ba. Murmushi Ana ya masa, yana riƙe hannunsa "Mu je kar ya ɓace mana." Binsa sukayi cikin tafiyar da bata gaza mintuna goma ba suka isa fadar mai gari, wanda ta ke zagaye da mutane wanda ba zasu haura shida ba, sai mai garin da ke kan kujerarsa a kishin giɗe. Sallama mutumin ya yi sanan ya zauna akan tabarmar da ke shimfiɗe a wajan, yana miƙa gaisuwarsa ga mai gari da sauran mutanensa. Amsawa ya yi yana kallon matasan da ke biye da shi, suma suka gaida shi kamar yanda suka ga yayi. "Malam Ilu ina ka samo baƙi haka?" Mai gari ya faɗa yana ƙara binsu da kallo. Kamar yanda suma suke kallonsa, zuciyar Ana tuni ta karye da ganin dattijon kakan nasa, wanda ya ƙara tsufa da kuma rama a tare da shi. "Ina tafiya ne suka tsayar da ni, suna tambaya ta fadarka rankai daɗe, shi ne nace su zo mu tafi dan nima hanya ta ce." Kai Mai gari ya jinjina yana ƙara kallonsu "Samari daga ina? Mi ke tafe da ku?" Shuru dukkaninsu sukayi suna kallonsa, shi dai Kamalu mamakin Kamar su da Ana yake, wanda shekaru kawai ya rarraba tsakaninsu da Mai garin, sai magana da hasken fatar da shi Ana ɗin ya fi shi. Shi kuma Ana zuciyarsa ce ta tsinke ganin Kakan nasa, wanda ya nuna masa tsantsar soyayya a duk lokacin da ya zo garin ko suke tare, sai dai babu halin ya bayyana masa ko shi waye.Ku nake sauraro samari. " Mai gari ya faɗa yana kallonsu. Wanda sautin muryarsa ta dawo da su daga duniyar tunanin da suka tafi dukansu, risinar da kai Ana yayi sanan ya ce "Mu mutanen Kauyen Kadimai ne, wani ƙauye a kusa da Haɗejia, muna zuwa neman kuɗi gari-gari da kuma koyan sana'ar da tafi yawa a cikin wanan garin, a cikin tafiyarmu ne sai hanya ta kawo mu wanan garin naku mai albarka, shine mukace zamu tsaya ko na kwana biyu ne. Warhaka mu samu wani ƙarin ilimi ta fuskar sana'ar da kuke, ta zame mana abun da zamu riƙe a gaba, har mu moreta."+ Tunda ya fara magana Mai gari yake kallonsa, wani abu ke caccakar kunnuwansa da kuma zuciyarsa, kallonsa yake da jin sautinsa kamar mutumin da ya sani, sai dai a ina ya sanshi? Amsar da bai da ita kenan, dan wanan sunyi hannun riga da wajan zama. Amma maganarsa ta taɓa zuciyarsa, ya kuma ji ƙaunarsa ta shige shi a lokaci ɗaya. Musamman da ya tuno masa da ɗansa abun alfaharinsa, wadda ko gawarsa bai samu damar sallata ba, sai tokarsa da ya gani. Hawaye ke barazanar zubo masa a kan idonsa, yayi saurin maida shi saboda mutanen da ke wajan, suna kallonsa, da yawansa sun fahimci damuwar da ya shiga a lokacin, wanda kuma ba sabuwa ce a garesu ba. Murmushi ya yi mai sauti kana ya gyara zamansa "Yaro gashi mu anan bamu da wata wararriyar sana'a wadda zata iya zama baƙuwa ko kuma abar ƙaruwa a wajanku. Daga kiwo sai noman da muke shima mafiya yawa munfi yinsa a damina, kaga kenan ba sabon abu bane a wajanku." Murmushi Ana ya yi sanan ya shafa kansa "Rankai daɗe ai noma tushen arziƙi ne, haka kuma ababen da ake nomawa a ƙasa suna da yawan gaske, ta iyu abun da muke nomawa ba lalle ya zama shine kuke nomawa a yankinku ba. Haka kuma kiwo, a cikinsa akwai abubuwan ƙaruwa da kuma ƙara sanin mahimmancin da dabba ke da ita a wajan mai ita, ta wata fuskar yanda rayuwarsu da ta mutane take cuɗanya da zama abar sabo a garesu. Haka a wata fuskar daban akwai hanyoyin sarrafa sinadarin da ke tare da su, kamar nonon da ake tatsa a sarrafa shi, a kuma ware man shanu a cikinsa, kaga mu bamu da ilimi akan yanda kuke sarrafasu, dan noma kawai muka sani, sai kuma sauran ababen da mukan tsinka a ɗan gajeran fataucin da muke yi a wani garin." Ba iya Mai gari ba, ɗaukacin jama'ar da ke wajan kowa hankalinsa na ga Ana, suna kuma jinjina kai cikin gamsuwa da maganarsa, da yawansu kuma sun ji zuciyoyinsu sun buɗe da ƙaunar baƙin matasan a yau. STORY CONTINUES BELOW  "Gaskiyarka yaro! A wanan lokacin ba ko wani yaro ake samu mai tunani irin naku ba. Dan gashi mu dai yaranmu basa maida hankali akan waɗan nan abubuwan, saima shiga burane da suke da zummar neman wani aikin da zai ƙawata musu zamaninsu. Wasu kuma muna tare da su amma basu damu su bimu su ga yanda muke tafiyar da rayuwarmu ba, balle su gajemu. Samari Mi ne ne sunayenku?" Wani dattijo ya faɗa, kansa sarƙe da rawani, wanda ko da jin muryarsa da kuma yanayin shigarsa ta nuna shine babban malami a garin, wanda ba'a zaman fada babu shi. "Ni sunana NASURU, shi kuma abokin tafiyata sunansa KAMALU." "Masha Allah. Sunayenku sun dace da kyakkyawar ɗabi'a irin taku, sai dai ina fatan ba zaku cutar damu ba, kasancewar yanzu zamani ya zama abin tsoro, wanda ka YARDA da shi kan cuceka, balle kuma baƙin da bamu sansu ba, balle garin da suka fito, a labari kawai muke jin sunayen garinku idan hanya ta kaimu." "In sha Allahu bama daga cikin irin waɗan nan mutanen, dan muma zuciyarmu na cike da fargaba da tsoron inda wata rana zamu samu kanmu, a irin wanan tafiye-tafiyen namu. Sai dai abun da muka fi YARDA dashi a ranmu shine Allah yana kare bawansa, mutuƙar yana bin dokokinsa, haka kuma shi yake kiyaye su ba tare da wayo ko danararsu ba." Ajiyar zuciya duka mutanen wajan suka sauƙe, sai mai gari da yake ta faman kallon Yaron da jin ƙaunarsa, akwai tarin nutsuwa sosai a tare da shi, ga kuma iya sarrafa harshe. Juyar da kallonsa ya yi gefe guda yana kallon ɗaya daga cikin mutanen fadan, "Surajo a shigar da su gidana ayima uwargida bayani akan baƙina ne, ta basu abinci da kuma ɗakin da ANA yake sauƙa idan ya zo hutu. Idan na shigo zan mata bayani akansu." "To Rankai daɗe." Wanda aka kira da sunan Surajo ya faɗa yana jinjina matsayin da Mai gari ya bawa waɗan nan baƙin da bai sansu ba, dan asaninsa baya haɗa ƙaunar jikansa da da kowa, kamar yanda bai iya ɓoye soyayyarsa a matsayinsa na jikansa na farko a duniya. Sai gashi waɗan nan matasan har sun samu matsayin da zasu zauna a ɗakinsa, wanda ko yaushe cikin gyara shi ake da tsammani akan zai zo. "Ku zo muje ko Yara?" Ya faɗa yana baza babbar rigar da ke jikinsa. Risinawa suka ƙarayi a tare suna godiya, kana suka juyar da kallonsu ga Malam Ilu shima suna masa godiyar. Murmushi ya musu, dan shima ya so ace shi ya karɓi baƙunci waɗan nan yaran masu cike da hikima da kuma abubuwan birgewa, sai dai sawun giwa ya take na raƙumi. Amma a ransa ya ƙudiri shima zai kyautata musu. Bayan shigarsu gida mutanen fada suka ci gaba da aika musu yabo da kuma tattauna muhimmancinsu. Gyaran murya Liman ya yi yana jinjina kansa da son yin maganar da ke bakinsa, duk da cewa yana tsoron halin da zai sa shugaban nasu, amma kuma ba zai iya barwa zuciyarsa ba, musamman da yaga abun a buɗe a hannunsa. "Bayan shuɗewar Audu Kallah a garin nan ban taɓa ganin matasan da suke da zummar neman abin da za su dogara da kansu ba. Sai zuwan waɗan nan yaran, wanda ina ganinsu naji zuciyata ta nutsu da su, na tabbata a duk inda ANA namu yake shima zai kai dai-dai da girman waɗan nan matasan." "Ƙwarai kuwa Liman. Ashe bani ɗaya ne nake ganin hakan a idona ba? Wallahi ina ganinsu Ana ya faɗo min, haka kuma da suka yi magana akan gundarin abin da ya kawo su babu wanda ya faɗo min a ƙasan raina Sai marigayi Audu. Allah kaji ƙan mazan jiya masu dogaro da kansu, masu maida alkhairi da sharri, wanda ya sabunta rayuwa da duniyar mafiya yawan attajiran garin nan." "Ameen Kallamu." Ɗaukacin jama'ar fadan suka amsa, idan aka ɗauke mai gari da yake faman murmushi, wanda kana gani kasan na ƙarfin zuciya ne da kuma nuna dakiya. Duk da a baɗini zuciyarsa na cike da begen ɗansa da iyalinsa, amma jin kyakkyawan yabon da kullum sai anyi masa a garin, yasa zuciyarsa ta nutsu, yake kuma kyautata musu kyakkyawar makoma, musamman da yasan abin da ya zama silar mutuwarsa, ta gobara ce wanda tana ɗaya daga cikin ababen da ake kira da mutuwar shahada. ***** Lokacin da Surajo ya gabatar wa da Inna bayanin baƙin mai gari, da kuma abin da ya ce, tayi mamaki ƙwarai, amma ganin yanda suka risuna har ƙasa suna gaidata, sai taji zuciyarta ta nutsu da su, Mukullin ɗakin ta shiga ta ɗauko mu Surajo tana cewa ya kai su ɗakin, za'a biyo su da abinci. Shikam Kamalu banda kallon ANA ba abin da yake, mamakinsa ne ya kamashi sosai, tun lokacin da ya iya tsara maganar abin da ke tafe da su. Har suka shiga ɗakin yana cike da mamaki, sai dai mamakinsa ya so ya fi haka, lokacin da idonsa ya yi tozali da kayan alatun da suka cika ɗakin, ga kuma ƙamshi turaren da bai taɓa sanin akwai irinsa ba. Gefe guda wata ƙatotuwar katifa ce malale a ɗakin, wadda bata hawa gado, sai kayan kallo da kuma manyan kujerun da suka zagaye ɗakin. A sama kuma hotuna ne na wasu larabawan yara mace da namiji, ɗaya kuma family ne na mace da namiji da yaran dai, duk da ɗaya yaron ya data, amma haka suka ƙan-ƙame iyayen suna dariya, suma suna dariya, haka akayi hoton wanda ko wanne a cikinsu kumatunsa ya lotsa idan aka ɗauke Uwar da nata bai fito sosai ba, ɗaya gefen kuma hotunansu ne duka har mai gari da Inna, da kuma larabawan, sai wasu mutum biyu matasa da su, fuskarsu na ɗauke da wani murmushi, saɓanin sauran da suke dariya. "Nan shine masauƙin da Mai gari yace a baku." Surajo ya faɗa yana murmushi. "To mungode sosai Baba." Ana ya faɗa yana mayar masa da martanin murmushin nasa. Juyawa ya yi yana jin ƙaunar yaron a zuciyarsa, gefe guda kuma yana mamakin rashin maganar abokin nasa. "ANA wanan larabawan kuma su waye?" Kamalu ya faɗa yana nuna masa hoton da yafi jan hankalinsa, na iyalin larabawan nan su huɗu. Kallon Hoton Ana ya yi yana murmushi "Family!" kalmar da ya faɗa kenan yana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin. "Family wani iri?" Dai- dai shugowar wata yarinya da ƙaton ture wanda yake ɗauke da kwanika sabbi guda biyu sai kuma dogon kofin ruwa da ƙanana guda biyu. Sallama ɗauke a bakinta suka amsa a tare ta ajiye musu kwanon ta na gaida su da kuma sanar da su abinci ne daga wajan Innah tace a kawo musu. Godiya suka mata ta juya ta tafi tana gaba girman da baƙin suke da shi a idon mai gari da matarsa. "MY FAMILY!" Ana ya faɗa hawaye na bin kuncinsa. Tsantsar mamaki ce ta kama Kamalu yana kallon Ana yana kallon mutanen da ke jikin hoton, wanda ko kaɗan basu yi kama da shi ba, asalima yaro da ke jikin hoton ya zarta wanan ANA ɗin da ke gabansa da haske da kuma kyau, ga zallar wayewa da jin daɗin da ya bi jikinsa. Kai yake girgizawa yana ƙara kallon ANA ɗin.....Kana so kace min wanan wanan matashin saurayin kai ne Ana?" Kamalu ya faɗa da mamakin da ya gaza ɓoyuwa akan fuskarsa. "Har yanzu zuciyarka na kokonto akan gaskiyar da idanuwanka suka gane maka ne Kamalu? Ka riƙe ko wata tambayar da zuciyarka ba zata gaskata amsarta ba Kamalu, Ka jira ɗan lokaci da kanka zaka samu duka amsar ba tare da ka tambaya ba." Yana gama faɗar haka ya shige wata ƙofar da ke jikin wani labile. Ashe toilet ne mai mutƙar kyau, wanda aka kashe masa tarin kuɗaɗe, kai kace ba a ƙauye yake ba, kamar yanda komi na gidan yake da ban-banci da sauran gidajan da ke waje. Da kallo kamalu ya bisa yana jin ba daɗi akan gaza fahimtarsa da Ana ya yi. Bai wani ɗauki lokaci ba ya fito jikinsa da alamun ruwa wanda ke tabbatarma da Kamalu alwala ya yi "Ka tashi ka ɗauro alwala mu rama sallahr da aka biyo mu, kafin a kira Magrib, dan kaga garin ya fara surka kala daga haske." Tashi Kamalu ya yi yana kallon Ana "Ka yi haƙuri Ana ba wai na gaza gaskata maganarka ba ne. Kawai abin ne ya bani mamaki sosai, ganin ban-bancin kamar da ke gareka da wanan hoton da ke liƙe. Amma komi da ke gareka ban taɓa ƙaryata shi ba balle har nayi shakka akansa. Ka yarda da ni Ana, ko kai ne kake a irin matsayin da nake a yanzu dole mamakinka ya gaza ɓuya." Murmushi Ana ya yi "Na yarda da kai Kamalu. Ban kuma faɗi haka ba dan ina jin haushin maganarka ba ne, ka je ka iyo alwalar muyi sallah cikina na kiran ciroman yunwa." Ya ƙarasa maganar yana shafa cikinsa, wanda hakan ya sa Kamalu dariya, ya kuma tabbatar Ana ba fushi ya yi da shi ba. Bayan Awanni biyu: A wanan lokacin sun kammala komi da suke yi, sun kuma zauna a ɗakin suna hira sama-sama wanda a yanzu hirar gajiya da wahalar doguwar hanyar da suka biyo ce, wanda kamalu yake ta nanatawa. Dariya Ana ya yi wanda bai fiya yinta ba "Anya kuwa kai namiji ne KAMALU?" ya faɗa yana murmushi a fuskarsa. Fuska Kamalu ya haɗe yana kallon Ana "Ban gane ni namiji ba ne? Da kallabi ka ganki ko kuma da zurmemen hijab da zani?" Ya faɗa yana ƙara tsuke fuskarsa. Kai Ana ya girgiza "Naga kana ta mitar gajiya da kuma hanyar da ka kwaso, duk da mun tsaya mun huta a hotel amma hakan bai gamsar da kai ba. Shine nake kokonto akan ko dai da mace za'ayi ne sai kuma kazo a suffar maza?" Yanzu kam dariya shima Kamalun ya yi kafin ya ɗauki wani tsinke ya fara sakatar haƙoransa "To ba'ace komi ba." Ya bashi amsa yana kanne masa ido guda ɗaya. Dariya suka sa atare wanda hakan ya yi dai-dai da shigowar Mai gari da kuma matarsa da ke biye da shi. Sallama suka musu suka amsa cikin haɗuwar baki, kana mai gari ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke ɗakin, haka ma Innah ta yi, ita dai har yanzu mamakin YARDA da yaran da mai gari ya yi take yi. Bayan sun ƙara wata sabuwar gaisuwar ne mai gari ya yi gyaran murya yana fuskantar matasan "DA fari dai ina muku maraba da zuwa wanan ƙauye namu mai albarka, da kuma ban gajiyar hanyar da kuka sha a yau." Kai suka risina suna kiran "Mun amsa rankai daɗe, muna kuma godiya da karramawar da muka samu daga gareka, da iyalinka." Kai mai gari ya gyaɗa cikin murmushi da jin daɗin godiyar da suka masa, sanan ya yi nuni da Inna da ke kusa da shi "Wanan matata ce da muka ɗauki tsawon lokaci muna zaman amana da jin daɗi tare da ita. Haka kuma duk wani abu da ya fito a gareni takan girmamashi kamar yanda nima nake girmama nata buƙatuni. Wani abu guda zan faɗa muku mai muhimmanci a zuwanku nan garin da kuma sauƙarku da nayi a gidana a kuma waje mafi soyuwa a gareni da iyalina." Kai suka gyaɗa suna gyara zamansu, shi dai kamalu mamakin dattijon yake da baya iya ɓoye matsayin matarsa da girmanta a wajan baƙinsa. "Nan ɗakin da kuke gani, ɗakin babban jikana ne da bana haɗa soyayyarsa da kowa. Kamar yanda nake ƙaunarsa haka shima yake mutƙar ƙaunarmu ni da iyalina, duk satin duniya idan yana gari anan yake hutun ƙarshen makonsa, haka kuma ko wani aiki na gida da kuma na waje yakan sa mana hannu ya taimaka mana. Duk da rayuwa ta ɗagashi da fifiko na jin daɗi da dukiyar mahaifinsa, amma ko yaushe abu ɗaya yake faɗa mana "Ba'a taɓa raina mafari kaka, abun da ke gareni shine lafiyata, wanda babana ya bani tallafi ne na kyautatawa da kuma jin ƙansa gareni. Ni bani da wadatar da zan baku, amma ina da lafiyar da zan iya taimakonku na kuma tallafa muku." Wanan shine maganar da Jikana ya ke mana a duk lokacin da muka so dakatar da shi daga wani aikin wahala." Babbar rigarsa ya sa yana goge fuskarsa, wanda ko ba'a faɗa musu ba sun san kuka yake yi, yayin da Inna ke ta faman jan hanci, dan tuna mata da ƙaton mikin da yaƙi barin zuciyarta. Kai Kamalu ya sunkuyar yana share hawayen da ya zuba a kan idonsa, kamar yanda Ana ya ke ƙoƙarin tsayar da nasa hawayen. Maganarsa ce ta ƙara katse su daga tunanin da suka faɗa a tare "Wani iftila'in rayuwa ne ya faru da shi da iyayensa, a ranar da ya dawo daga ƙasar waje makaranta. Ba zance ga ainahin abin da ya faru ba, sai labarin da ya riskeni cewar gidansu ya yi gobara, duka sun mutu. Sai dai ni har yanzu na gaza yarda akan hujjar da aka bani na wutar lantarki ce ta haddasa musu gobarrar, haka kuma na gaza gaskata cewa jikana ya ƙone a cikin gobarar, ko wata rana ni da iyalina mukan zo mu gyara ɗakin da komi, kamar yanda muke sa rai da tsammani akan dawowarsa, sauran kuma mun barwa Allah iyawarsa. Musamman da 'yan uwansa sukayi fatali da maganar, suka ja mana dogon layi akan ƙaddara ko yaushe tana sabunta mana tunaninmu, kamar yanda hanyoyin mutuwa suke da yawa, babu wanda yasan mi zai zama ajalinsa har sai mutuwar ta riskeshi kana mutane su ankare da ita. Wanan maganar ita ta zama salama a zuciyata na kuma bi su da fatan alkhairi shi da iyalinsa Fatima. Haka mahaifinta ya bama kowa mamaki yanda ya iya jure rashin fatima, duk da itace ɗiya mafi soyuwa a gareshi. Sai dai ramin da ya haƙa ya binne na soyayyarta har yanzu shi ke caccakar zuciyarsa, da dare yakan kwana yana kuka, hakan ya haddasa masa ƙarancin gani, sai da taimakon madubin ido. Kana ƙafafuwansa sun yi taushi baya iya doguwar tafiya ba tare da taimakawar sanda ba, a hakanma yana yi yana hutawa." Yanzu kam zuciyoyinsu sun ƙi tsayawa akan iya hawaye, kuka suke da dukkanin sautinsu, kukan tausayawa dattijan da suka dogara da abu, kukan raunin jiki da na zuciya da ya tasamma su a lokacin da basu tsammata ba. Dafa kafaɗarsu Mai gari ya yi yana murmushi mai sauti, wanda kana ganinsa ba na daɗi ba ne"Na baku labarin nan ne dan ku fahimci muhimmancin da kuke da shi a gareni, ban san mi Allah ke nufi da ni akanku ba, amma ina ganinku naji zuciyata ta aminta da ku kamar yanda ta so ku a kallon farko. Ku zauna damu kamar kakanninku, ku kuma saki jiki da mu a zaman da zakuyi a wanan garin tamkar kuna garinku." Tashi Mai gari ya yi yana kallon Innah "Zamu tafi masallaci da su dan su yi sallah a jam'i, haka kuma idonsu ya fara buɗewa da baƙin abubuwa. Ku tashi ka ɗauro alwala ina jiranku a waje." Tashi suka cikin mutuwar jiki suka Kamalu ya shige ya fara ɗaura alwala, ya fito kana Ana ya shiga shima ya iyo tasa alwalwar. Har ƙofar gida Inna ta takosu tana musu fatan dawowa lafiya, da kuma ɗaga musu hannu, itama ji take kamar jikokinta da suka kuskure mata a shekara ukun da ta gabata. Lokacin da aka idar da sallah Magrib basu dawo gida ba, zama su kayi mai gari ya ci gaba da gabatar da su a wajan mutanen da ke garin. Har sai da aka yi sallah issha'i sanan suka dawo gida, sosai suka sake da Mai gari da Innar yanda suke haba-haba da su, da kuma basu labarin ababen da suka shafi garin. Abincima kwano guda aka zubo musu da mai garin, Itama Innar cewa tayi ba zasu wareta ita ɗaya kamar mujiya ba, dan haka ta saka hannu suka ci tare ana ta barkwanci da ban dare. Shi dai Kamalu mamakin karamcin mutanen ya ke, duk da yana samun labarin mutanen ƙauye suna da kara da kuma girmama baƙinsu, amma bai ɗauka wannan ɗabi'ar hadda fulanin da suke da tsantsar aƙida akan yarensu da kuma al'adarsu ba. Sai dai Lahla ya shayar da shi mamaki, kasancewarsa mai garin Bamaina hakan bai ɗaɗa shi da ƙasa ya ji alfahari a tare da shi ba. "Lokacin da ina kamar ku, ban samu damar da zan fita na nemi kuɗi haka ba. Fafutukata da neman na kaina sun ƙare ne a iya garin nan, duk kuwa da cewar ina ganin kara da tsangwama daga mutanen garinmu. KALLAH CIKON GARI, shine sunana a wancan lokacin, sunan da mutane ke dariya a yayin kirana da shi, suna min izgili." Maganar Lahla ta dawo da kamalu daga tunanin da ya lula, yana kallon dattijon da fuskarsa ke ɗauke da fara'a. "Babu wanda ya taɓa tsammanin wanan Kallah ɗin zai zama wani abu, kamar yanda ko a mafarkina ban taɓa hasashen ganina cikin jerin masu faɗa a ji a garin nan ba. Sai gashi sunan Cikon gari da tambarin da ya bani ya siyo min kima, da ɗaukaka. Haƙiƙa Allah shi ke tsarawa bawa rayuwarsa, ya kuma ɗaukaka shi daga maƙasƙanci zuwa mai wadata, kamar yanda yake maida mai arziƙi ya koma talaka." Kai suke gyaɗawa cikin gamsuwa da kalaman nasa, da kuma jin ƙaunar tsohon a ransu "Kun san wani abu da zan faɗa muku mai muhimmanci a rayuwarku kuwa?" Kai suka girgiza suna miƙa duk hankalinsu a gareshi, murmushi ya yi sanan ya kurɓi ruwa a kofi "A rayuwa kada ku taɓa nuna damuwarku akan abin da wani ya mallaka, komi wahala da ƙasƙancin da za ku shiga kada ku roƙi wani mutum face Allah. Kada ku fallasa halin ƙuncin da kuke ciki, madadin haka ko yaushe ku kasance masu godiya ga Allah da abin da kuka samu. Idan hankalin mutane ya koma kanku, za su tsaya suna jiran ka kai kukanka garesu, ta yanda zasu samu damar da zasu goranta ma wata rana. Amma idan ka iya killace yunwar cikinka, ka ɓoye ƙuncin da ke addabar rayuwarka, sai a gaban mahaliccinka hakan zai siya ma kima, wata rana za'a faɗi alkhairinka ta hanyar da ka bi ka siyama kanka kima." Numfashi ya ja ya fuzgar da iska mai ƙarfi a bakinsa, kana ya kai kallonsa ga Inna "Kunga ni da matata ba zamu iya faɗa muku adadin kwanakin da muka sha yini da kwana da yunwa ba, amma a hakan babu wanda zai ce mun je wajansa koda da cin bashi ne balle kyauta. Bashi halal ne, sai dai wani lokacin halaka ne, musamman idan baka da hanyar da zaka bi ka biya shi, haka idan ya shiga rayuwarka baka taɓa daina cinsa komi matsayin da ka samu. Ina mai muku nasiha da ku guji cin bashi da kuma roƙo abin hannun mutane, idan kuka kiyaye wanan zaku samu albarka a cikin rayuwarku da kuma neman na kanku. Bashi fitina ne, baka sanin fitinarsa sai lokaci da mutuwa ta ɗaukeka, idan ba'ayi dace ansani da wuri ba sai ya hana mutum kwanciyar kabari, ga dai rayuwar da mutuwa bata sallama balle ta ƙwan-ƙwasa ƙofa." Kai suka gyaɗa cikin haɗuwar baki "In sha Allah zamu kiyaye Yallaɓai, mun gode sosai." Daga nan suka tashi suka nufi makwancinsu kasancewar dare ya raba sosai. "Gaskiya Kakanka mutumin kirki ne ANA, ban taɓa ganin dattijo mai hankali da nisan tunani a irin shekarunsa ba sai Lahla. Sai nake ji inama ace nawa kakan ne haka." Kamalu ya faɗa yana share hawayen da ke idonsa, saboda tasirin da maganar Lahla tayi a tare da shi. STORY CONTINUES BELOW  "Saima ka zauna da shi sosai zaka fahimci hakan Kamalu. Kaga dai talaka ne amma yana da wadatar zuci." "Ni banga alamu talauci a tare da shi ba ko kaɗan Nasuru." Ya faɗa yana dariyar kiran sunansa da yayi. Shima dariyar yayi bai ƙara magana ba, daga haka suka kwanta kowa na saƙa abin da ke ransa, har barci ya ɗauke su. ******** Bayan kwana biyu. A cikin waɗan nan kwanakin babu inda su Ana basu zazzaga ba, haka kuma mutane da yawa sun sansu a garin, dan ko ina mai gari za shi yakan sanya su a gaba su tafi tare ne. Har gidan Malam Jauro ya kaisu suka duba shi, ganin yanda ya koma saida Ana ya zubar da hawaye, saboda soyayyar da ke tsakaninsu da shaƙuwa. Tun da suka je kullum sai sun je gidan sun taya shi hira, hakan ba ƙaramin daɗi ya ke masa ba, kamar Lahla shima ko yaushe bakinsa na ɗauke da labarin jikansa da ɗiyarsa Fatitiya, hakan ya zame masa bege na sosai a tare da shi. Sai dai sukan kwantar masa da hankali akan wata rana jikansa zai dawo dan ba lallai ace ya mutu ba. Hakan na kwantar masa da hankali, a zaman da suka yi da shi hankalinsa ya kwanta sosai, ya kuma rage yawan damuwa da tunanin da ke ransa. A cikin kwana biyun da suka yi, Lurwanu ya zo garin, da kayan masarufu shaƙe a motarsa, ya jibgesu a gidan Lahla, da kana ya yini suna hira, anan ya gabatar masa da su ANA da fara'a ya karɓe su, ya zama wani babban mutum da shi, kana ganinsa kaga jin daɗi ya zauna a tare da shi. Katin addireshinsa ya basu, yana jaddada musu akan idan sun koma gida su nemeshi dan shima har yanzu a Haɗejia yake da zama, kasuwancinsa ya ƙara haɓaka, fiye da kima, yana ɗaya daga cikin manyan 'yan kasuwar da ake ji da su a garin. Haka matarsa ƙanwar Fatitiya yanzu yaranta biyar duk sun tasa sun zama matasa. Hawaye ya share a kan fuskarsa lokacin da ya ƙurama ANA ido ya jijjiga kai kawai ba tare da yayi magana ba, sai kafaɗarsa da ya bibbiga, a aljihunsa ya zaro musu rafar 'yan 500 guda ɗaya ya miƙa musu, yana ƙara jaddada musu yana zuba idon zuwansu. Har wajan mota suka rakoshi shi da su Lahla suna ɗaga masa hannu har ya ɓace a ganinsa. "Kaka wanan shima yaronka ne?" Kamalu ya tambaya yana kallon Lahla da ya ƙurama hanyarsa ido. Murmushi Yayi yana girgiza kai "Ba ɗana ba ne, sai dai a yanzu bani da wani yaron da ya wuce min shi. Asalin sarautar garin nan ta mahaifinsa ne, ya bar min yace ba shi da lokacin yin sarauta kuɗi zai nema, anan yarona ya buɗe masa shago a Haɗejia sai Allah ya sama kasuwancin albarka, yanzu ya haɓaka. kun san abin mamaki? sun haɗa neman aure da nawa yaron, wanda baƙin cikin hana shi yasa mahaifinsa mai gari ya haɗiyi zuciya. Amma shi sai Allah ya sa masa dangana ya haƙura wanda ya zame masa alkhairi a rayuwarsa. Duk sati yakan ziyarce ni nida iyayensa, amma zamansa anan yafi yawa, yana sauƙe nauyin da ko wani ɗa yake sauƙewa a wajan iyayensa. Har gobe yana kuka akan rashin yayansa Audu da kuma ɓatan yaransa, babu neman da bai yi ba, ko zai gansu har yau shuru, kunga kamar yanda ya tafi da hawaye haka ko yaushe yake tafiya da hawaye idan ya zo ya ganni." "Allah sarki! Dama AUDU ne kawai yaronka ne Lahla?" Murmushi yayi ya bigi kafaɗar ANA "Su uku gareni, amma yanzu sai nafi wata uku banga sauran yaran nawa ba, tun bayan mutuwar yayansu, komi na sa su suke juyawa, ko sun zo basa zaman rabin awa suke tafiya, haka watar salula ba ko yaushe suke kiranmu ba. Muma mantawa muke da su, ko wata matsalarmu munfi gane mu kira Lurwanu mu faɗa masa, shine ko mi yake zai fatsar ya zo. Amma su suna can da iyalansu, wani yana dutse wani kuma yana can ƙasar waje, adai tsakaninsu suke sabunta wajan zaman, nima sai dai naji labarin a bakin mutanena." "To Allah ya kyauta." Suka faɗa cikin haɗuwar baki, sai ANA da kansa ya ɗauki zafi sosai, ya shiga tunani. **** Bayan mako guda: Duk wani abu da ya kamata su Ana su samu sun same shi, ciki kuwa harda fakewa da koyan aikin da suka yi. Dan haka suka haɗa kayansu suka fito suna masu yin sallama da mutanen garin, sosai suka saba da su, haka kuma suka haɗa musu sha tara ta arziƙi, dan sun ji daɗin zama da su ba kaɗan ba. Basu da ƙiwa basu kuma da ganda, duk wani abu da ya taso tare ake da su a garin, sunyi abokai sunyi iyaye. Haka aka haɗa musu kayan amfani da yawa, malam jauro ma ya haɗa musu harda su zabbi da kaji da kuma ƙwai, yana mai jaddada musu lallai su sake halartarsu, kada su daɗe. Haka ma a ɓangaran mai gari ya basu sabbin yadika da shadda wanda bai ɗinka ba, dan ko yaushe Lurwanu kan ajiye musu kaya masu ɗinki da kuma marasa ɗinki ko buƙatarsu zata taso. Shatar mota mai gari yasa aka basu, ya biya kuɗin motar zuwa birnin dutse. Sai da suka cika bayan motar da kayan amfanin mutanen garin da suka basu. Kana suka rungume mai gari suna hawayen sabo da shi, suma haka 'yan garin suna hawaye suna ɗaga musu hannu har motarsu ta ɓace ma ganinsu. A tashar dutse aka sauƙe su da kayansu, kana direban ya ƙara gaba, waya Kamalu ya ɗauka ya kira direbansu, wanda shima ya zama ɗan gari. Bai wuce minti sha biyar ba sai gashi ya zo, ya kwashesu suka tafi hotel ɗin da suka sauƙa. Wanka suka yi suka sauya kaya, suka ɗauki hanya, dan dama cikinsu a ƙoshe yake. Ko wannensu zuciyarsa cike da kewar mutanen ƙauyen. Yini suka yi cirr a tafe sanan suka shiga garin bauchi, murna sosai su Umma suka sha da ganinsu, Abba kam sai tsiya yake musu wai ƙauye yasa sun haɗa uban tumbi da kumatuna. Su kansu sun san sunyi ƙiba dan abinci suke girka ba na wasa ba, Jidda kam baki har kunne sai maƙale musu take su bata labarin garin. "Jidda mana ki bari suyi wanka su ci abinci, muma muna son jin labarin tumbin nan nasu da suka haɗa." Dariya suka yi suka shige ɗakinsu, wanka su kayi suka sauya kaya mai sauƙi, sanan suka rama sallolin da ke kansu. Anan suka fito suka kwashi abinci, aka shiga labarin ƙauye tun tafiyarsu har dawowarsu, da kuma kyakkyawar tarbar da suka samu a ƙauyen. Anan direba ya yi ta jido musu da kayan tsarabar da suka samo, ikon Allah kawai shine abin da su Umma suke faɗa, cike da yaba hallacin mutanen ƙauyen da alkhairinsu. Abba kam kai ya ke ta jinjinawa "Wai a haka ma basu san ko su waye ku ba." "Wallahi fa Abba." "To masha Allah sai ku fara shiri nan da kwana biyu zaku tafi makaranta, dan na gama komi na fitarku ƙasar Germany." Murna suka yi suka rungume Abba a tare "Kai karku karya ni kun ci tuwon ƙauye ya huraku." Dariya suka sa duk a tare sai Jidda da ke zumɓura baki "Abba daga dawowarsu sai tafiya, su ƙara barina ni ɗaya." Gwalo Kamalu ya yi mata "Dama zaman gida ai na mata ne yarinya." Baki ta ɓaye zata yi kuka Abba ya ma Kamalu dunguri "Ka fita idona Kamalu. Jiddah nah ga Umma ga ni muyi ta cin daɗinmu babu su." Sai a lokacin ta sa dariya tana tsalle, shi kam Ana da ido ya ke binta yana murmushi. ***** A cikin kwana biyu duk wani shigi da fice da shirin tafiyarsu ya kamalla. Har air port Ummah da Jidda suka rakasu suna ɗaga musu hannu har jirginsu ya tashi, sai da suka biya ta Spain Abba ya shiga ya fita ya karɓo takaddun Ana na secondry kana suka tafi Germany. Sai da ya kamalla musu komi suka samu shedar zama cikakkun ɗalibai a makarantar, hatta accnt na banki ya buɗe musu ya loda musu kuɗi, faɗa sosai ya musu akan tsayawa suyi karatu su kuma guji abin da zai hallakar da su, su guji abokanai su yi abota da kansu kawai. Da kuka suka rabu da Abba shima yana hawaye da kewar rabuwa da su, dan karatu ne zasu yi shi har na tsawon shekara takwass, haɗuwarsu kuma sai kwana. Tafiyar su Ana ba ƙaramin kewa ta sa ma jidda da su Umma ba, kasancewar sabon da sukayi da su da kuma zama a tare. Yanzu gidan ya rage sai Umma sai 'yan aikinta, dan Jidda idan ta tafi makaranta tun 7 sai 6 Na yamma take dawowa, saboda ana musu lesson idan an gama kuma su wuce islamiyya, a taƙaice dai bata da lokacin kanta sai dare, shima kuma tana bitar karatunta. Sosai Umma ta shiga kewar rashin yaran, gidan ya mata faɗi sosai, har mita take ma Abba yana mata dariya.+ ***** Gombe, Nigeria Ko ina a gidan a hargitse yake, kowa kaga a lokacin sai kai kawo kake, motoci ne birjik masu launi iri ɗaya. Daga cikin gidan Mommy ce cikin shiga ta alfarma cikin wani rantsattsen leshi da kuma mayafi, gefe ɗaya kuma Dady ne shima fuskarsa ƙunshe da fara'a hannunsa na riƙe da na Yumnah. A jere suka fito hannunsa sarƙafe da na Yumnah ɗin. Tun kafin su zo aka wangale musu ƙofar motar suka shiga, daga nan sauran direbobin suma suka shiga motocinsu. Da mamakinsu sai ga Zayd ya shige mutar shima cikin shirinsa, ƙananan kaya ne a jikinsa wanda suka fito da zatin sa. Ba wanda ya masa magana har suka bar gidan, ko ina suka wuce sai an bi gwanon motocin nasu da kallo, da yawa suna kallonsu cikin sha'awa da birgewa, wasu kuma suna tirr da arziƙin da talaka bai mora. Ko yaya dai ɗan adam ba'a iya masa, dole ta wani wajan ya yabeka wani wajan kuma ya aibantaka. Basu tsaya a ko ina ba sai a Airpot anan suka fito suka buɗe musu motocin suka fito. Anan kuma jikin iyayen yayi sanyi, musamman ganin an fara kiran sunayen mutanen da jirgi zai tashi da su. "Ba a son raina bane zan barki kiyi nisa da ni Yumnah! Sai dai ina fatan zaki cika min burina wanda yayanki ya gagara cika min shi, ki maida hankali kiyi karatu. Shine abin da ya kaiki." Kai ta gyaɗa cikin raunin muryarta, kana ta rungume Dady ɗin "Zanyi kewarku da yawa Dady. Amma na maka alƙawali in sha Allah sai ka yi alfahari da ni." Murmushi yayi ya shafa kanta "Na sani ɗiyata, na san ba zaki taɓa bani kunya ba." Ƙarasawa kusa da Momy ta yi itama ta rungumeta "Momy rayuwa a nesa ba tare da ahali ba abune da ban taɓa hararowa kaina yinta ba, sai dai ina fatan addu'arki ta ci gaba da riskata a duk inda nake." Bayanta Momy ta bibbiga hawaye na taruwa a idanuwanta, tabbas tana son Yumnah so bana wasa ba, itace kuma 'ya ɗaya tilo da ke damuwa da ko wani lammuranta. "Rayuwa zata min faɗi a gidan da babu ke Yumnah. Sai dai na sani wata nasarar bata samuwa har sai an gusa gefe, Addu'ata a gareki abace wanzazziya da ba zata taɓa tsayawa ba har sai numfashina ya bar jikina. Ina miki fatan alkhairi da nasara a cikin karatun da za kiyi, ina kuma fatan zaki kare martabarki kasancewarki ɗiya mace musulma haka jinsi biyu hausa fulani." Kai ta gyaɗa tana share hawayen da ke zuba akan fuskarta "In sha Allah momy zan kula da kaina kamar yanda kike kula da ni." Tana ƙarasa faɗar haka ta matsa kusa da Zayd wanda ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa, fuskar nan tasa dunkum babu fara'a, asalima haushin biyo su da yake yi yayi. Dafa hannunsa tayi tana kallonsa, wanda shima kallonta yake ba tare da wanan hantarar ko hararba "Yaya Zayd kaga rayuwa zata sabunta mana muhallin zama na ɗan lokaci. Yumnah ɗin da baka son buɗe ido ka ganta a gabanka zata nisanceka na wasu shekaru. Sai dai ni a zuciyata kewa ce da ƙuna na nisantar ahalina da zanyi na wasu lokuta, haka kuma zanji kewar hantararka da tsanar da ko yaushe nake gani akan fuskarka." Murmushi tayi tana kallon yanayinsa na kadaran-kadaham. "Kace kana da naka burin saɓanin na Dady, ka yi ƙoƙari ka cikama kanka wanan kyakkyawan burin. Kace kana buƙatar samun mutuntaka daga mutane ba ta dalilin Dady ba, amma kasan hakan ba zai faru ba har sai ka fara mutunta kanka, ka sauya rayuwarka, mutane na kimanta mutanen da suke ganin zamani bai yi tafiyar ungulu da su ba. Wata girmamawar kana samunta ne a lokacin da aka fahimci ka girmama kanka. Ka daure ka ajiye komi da yake marar kyau, ka tsayu a matsayinka na musulmi bahaushen da ke kare kimarsa. Kada ka tsaya kana juya ababen da ke da ƙunci da munin haɗiyewa a zuciya, ka yi komi dan kanka ba dan iyayen da kake musu kallon wanda basa ƙaunarka ba, da kanka zakayi alfahari da sabuwar rayuwar da zaka fara ba tare da muyagun abokai ba. Idan ka rasa aboki na gari ka tsaya ka abokanci kanka." Tana gama faɗar haka ta saki hannunsa ta ja jakar kayanta, ta tafi, hannu iyayenta suke ɗaga mata itama tana ɗaga musu nata hannun, ga kuma shimfiɗaɗɗen murmushin da ya ƙi barin fuskarta. Da kallo Zayd ya ke binta, yana jujjuya maganar da ta faɗa masa, mamaki da al'ajabin sarrafa harshen Yumnah ya cika masa zuciya, tabbas yayi ganganci da yayi tunanin mahaifinsa ya fifita soyayyarta ne akansa, ashe shi a suna ne ya amsa sunan namiji haka kuma babba, amma a zahiri shi famkon da bai amfanar da kansa ne balle wani. Kai ya gyaɗa ya shiga cikin motar, dole shima ya shiga filin fafatawa a tare da nagartattu, ba zai ci gaba da rayuwa da lusaran da suke biye da ɗaukakarsa ba. Haka suka juyo gida ko wanne jikinsa a sanyaye, ga tarin kewar Yumnah da ta cika musu zuciya. Suna shiga gidan kowa ya yi sashinsa, Zayd banda kaiwa da kawowa ba abin da ya ke yi, ga tarin damuwar da bai san ko ta miye ba. Can kamar an mintsine shi ya tashi ya nufi ɗakin Momy, samunta ya yi tana ninke kayanta, zama ya yi yana tayata gyara ninkin kayan, wanda ya sa Momy tsayawa tana kallonsa da mamaki. Murmushi ya yi yana ci gaba da Ninke kayan "Daga yanzu zan ke tayaki aikin da Yumnah ta ke yi har zuwa lokacin da nima zan tafi makaranta." "Wata makaranta kuma?" Momy ta tambaya fuskarta ƙunshe da mamaki. "Madina." Ya faɗa a taƙaice fuskarsa na faɗaɗa da murmushi. "Ban gane maka ba Zayd? Ina nan mahaifinka ya sameka akan batun tafiyarka karatu ka ƙi, sai Yumnah ce aka maye wajanka da ita." Kai ya gyaɗa "Momy ai mun gama wanan maganar da daɗewa, ra'ayina baya tare da na Dady, shi kasuwanci ya ke so na koya, ni kuma bana son sa, na riga da na tura saƙon neman wajen karatu a madina, kuma har sun bani gurbin karatu, zan karanci ɓangaran shari'a a addinance. Wanan shine burina Momy, kuma ke nake so ki min komi na karatun ba wai Dady ba." Kai Momy ta ke gyaɗawa cikin gamsuwa da maganar ɗan nata, shafa kansa tayi tana murmushi "In sha Allah zan tsaya maka har sai burinka ya cika, ina fatan za ka ajiye ko wata shiririta ka fuskanci karatun da ya kaika." Kai ya gyaɗa yana murmushi "In sha Allah Momy, ai an wuce wanan wajan." "Masha Allah! Yaushe ne tafiyar taka." "Nan da wata ɗaya in sha Allah." "To Allah ya kaimu." "Ameen" "Lallai za ku min tawaye kenan, ga rashin Yumnah kaima kuma zaka bi bayanta." "Momy ai akwai waya, ba wai mun tafi bane." "Kayya ZAYD! Waya bata kai min ku ba a rayuwata." Dariya yayi anan suka ci gaba da hirar Yumnah tun baya amsawa sosai har ya ware yana amsawa, shi kansa yasan yana kewarta, dan bata taɓa yin fushi da shi. ******* Dutse Nigeria Kamar ko yaushe yauma su huɗu ne suke zaune a ƙayataccan palon da ya zame musu wajan tattaunawar su. Haka kuma yau fuskokinsu ɗauke suke da fara'a saɓanin ko yaushe "Burunmu na gaf da cika, dan mun ɗora tsanin da zai kai mu ga gaci." "Ƙwarai kuwa, sai yanzu na yadda da maganar da kake ta faɗa kullum, akan mu ƙara haƙuri akwai lokaci, ashe kai ka riga da ka gama sanin ta kan tsiyar." Dariya suka bushe a tare sanan suka ɗaga kofunan da ke cike da lemo suka kara a tare suna kiran "SHAGALI" a tare.

0 Comments