YARDA DA KAI CHAPTER 6

YARDA DA KAI CHAPTER 6
Bayan shekara ɗaya A cikin wanan shekarar nasara ta ƙara bunƙasa a dukiyar Audu Kallah, wanda bayan gonar da yake da ita sai da ya ƙara siyan wata wadda a ƙalla ta kai guda biyar, noma yake ba rani ba damina, ga kuma gidan gonarsa da Allah ya sanya ma Albarka, sosai ya ke samun abokanan cinikayya daga birni kasancewar kasuwancinsa yafi yawa a can.+ Ana haka ya haɗu da wasu abokanan cinikayya na kirki, ɗaya a ciki mazaunin Gombe ne wanda harkar fata da kuma kamfanin sarrafa nono na jarka da leda ya kan kawoshi neman wadataccan nono a garin, sosai amintarsu ta kan-kama da Audu Kallah wanda shima yake da lafiyayyun shanun da ko yaushe basu rabo da samun nono. Haɗuwarsu da Mukhtar ta ƙara wayar masa da kai a harkar kasuwancinsa, wanda da shawararsa ya buɗe kamfani mai zaman kansa wanda ya masa suna da *ANA FASHION DESIGNED COMPANY* saboda cuɗanyar da Mukhtar ke yi yasa bai sha wahala ba, ya sama masa ma'aikatan turawa, su suka fara kafa kamfanin ya samu matsayi da ɗaukaka kasancewar ƙasarmu tana son duk wani abu da za'a ce turawa ne suke sarrafa shi. Da dukkanin zuciyarsa Audu ya sakar da akalar kasuwancin nasa ga aminin nasa, ganin ko mi ya ke ciki yakan tsaya kai da fata a yi shi, haka kuma ya jinginar da nasa kasuwancin ya ke tsaye ƙyam a kan nasa. Lokacin da su Iro suka ga wanan ci gaban ya samu ɗan uwansu, sosai zukatansu suka ƙara faɗaɗa da jin kai, ko ina suka zauna labari ne akan Yayansu shine mutum guda na farkon da ya fara yin kamfani da kuma aiki da turawa. Sai dai a baki suke yayata hakan, zuciyarsu na zafi na ganin har yanzu su ba abin da suka cimma, ga dai karatu sun durfafa suna yinsa ka'in da na'in. Shekara bata ƙara zagayowa ba sai da Audu Kallah ya kwashi iyayensa da surukansa Malam Jauro da Innar Fatitiya da ita kanta fatitiya ɗin ya kaisu ƙasa mai tsarki. Yayin da ya bar Iro da Mammadu suna kula masa da kasuwancinsa da gidan gonar a zuwan wata shekarar su sa je. Hakan ba baƙanta musu zuciya yayi ba, musamman ganin yanda ya ɗauki surukansa ya tafi da su, su kuma da ke basu da wani amfani sai jiran dukiyarsa shine ya barsu anan. Sun ƙullaci abun a ransu ƙwarai da gaske, hakan ya sa suka rinƙa bushasha da dukiyarsa da kuma yanka kaji a ko wata rana su ci abinsu. Gefe guda mutanen Bamaina sun cika da mamaki halaccin Audun ga surukan nasa, duk da malam Jauro na da kuɗi amma bai taɓa biyama kansa zuwa aikin hajji ba, sai gashi yau rana tsaka mutumin da suka fi kowa ganin ƙas-ƙancinsa shine ya kwashi rayuka har shida ya biya musu. Duk dama su yanzu Audu mamaki da shakkarsa suke, Idan akace yana gari gidansa bai rabuwa da mutanen da suke neman taimakonsa, haka kullum Kallah ke fama da masu neman taimakonsa, girmamawar da ake masa ka ɗauka Mai garin Bamaina ne da kansa. Wani lokacin yakan rufe kansa a ɗaki yayi ta hawaye yana godiya ga Allah da ya bashi tsawon rayuwa yaga wannan lokacin, bai taɓa tsammani da hasashen sunansa zai sauya daga cikon gari ba, kamar yanda ko a mafarkinsa baya hasashen ganin girmamawar wani daga cikin garin. Tabbas duk wanda yace ƙaƙa-na-ƙayi to ya manta da Allah ne. Acan ya haɗu da abokinsa Izadden wanda shima suka je da nasa iyalin gaba ɗaya sauƙe farali, sai dai shi kusan kasuwancinsu sunyi kamancacceniya da na Audu, dan kuwa shima kayan masarufin ya ke fiddawa zuwa ƙasashen ƙetare, musamman alkama da yake kaita ake sarrafata ta koma biskit, sosai kasuwancin ya karɓeshi, haɗuwarsa da Audu yasa yaji yana kwaɗaita masa akan shima ya kamata ya shigo ya gwada irin wanan kasuwancin, kasancewar komi ya zama sai ana raba hannu, haka harka da turawa akwai alheri ba kaɗanba a cikinta. STORY CONTINUES BELOW  A yanda ya ga mutumin da kuma yanda bai rufe masa komiba, yasa ya yi na'am da kasuwancin da ya masa tayin yi, wanda yake yinta acan ƙasar Spain. A cikin watanni biyu suka saba sosai, haka kuma Izadden kan ƙara buɗa masa yanda kasuwancin ya ke, harma yakan sanar da shi zai iya sanya hannun jari a kamfanin koda ba zaina musu safara alkama a can ɗinba. Wanan ne dama-dama kam a wajan Audu dan ba zai iya raba hankalinsa waje da yawa ba, amma shi hannun jari kamar wata buɗaɗɗiyar ƙoface a gareshi, duk da ba'a tsammanin asara sai dai koya asara take tana nan a sunanta, haka ba'a tanadinta zuwa kawai ta ke kwatsam. Suna daga can ya bama Mukhtar kwangilar gina masa ƙaton gida mai ɗauke da ɓangare huɗu a birnin Dutse, ya kuma buƙaci da a hanzarta aikin kafin su dawo. Abunka da kayan kuɗi lokacin da suka sauƙa har an kammala ginin gidan wanda tarewa ce ta rage kawai, gidan da ya amsa sunansa na gida, wanda kowa ya gani yasan naira ta koka a wanan lokacin. Kai tsaye gidan suka nufa iyayensa na tambayarsa amma ya musu shiru, lokacin da suka zo unguwa tun anan suka san babbar unguwa ce da ke ɗauke da manyan masu kuɗi, musamman da ginin unguwar ya ke fallasa haɓakar mazauna cikinsa, wani ƙaton gida suka ma ham masu gadi har guda biyu suka buɗe musu ƙofar, kasancewar dama Mukhtar ne ya kwasosu daga airpot ɗin. Tun daga harabar gidan fulawoyi kema wajan ƙawanya ga kuma manyan fitulon da suka haska ko ina a gidan. Ko wani ɓangare ɗaya iri ɗaya ne, ban-banci bai wuce launin fantin da aka ma ko wani sashi ba, amma tsaruwarsa da kayan da ke ciki komi iri ɗaya ne. Baki buɗe su Malam Kallah ke ganin gidan, wanda aka shiga zagayawa da su ko wani saƙo da lungu na gidan. "Nan kuma ina ne Abdussalam?" Malam Jauro ya tambaya yana kallonsa. "Murmushi yayi yana sunkuyar da kai "Nan shine sabon gidan da zamu zauna ni da iyayena da ƙannena, suma ko wanne a cikinsu akwai gefensa da na matarsa idan ya aura, sai na iyayena da kuma namu ni da Fatima." "Allahu Akbar! Allah mai hikima da iko, sannu kaji Audussalam, Allah ya maka albarka ya ƙara sanya albarka a cikin dukiyarka, lallai kai na daban ne, kamar yanda aiyukanka suke na daban a garemu. Kai babbar kyauta ce da aka aiko garemu, ta yanda ka jiƙa mu da alkhairainka, ka kuma nuna mana hanyoyin da ake ribatarsa. A yanzu ba ni ke da Arziƙin bamaina ba, kai ne kake da shi Audussalam." Murmushi ya yi yana sunkuyar da kansa ƙasa, yana jin nauyin kalaman surukin nasa akansa "Baba har abada wanan sunan naka ne, ni ban taɓa ɗaukan wanan abun da na ke da shi a matsayin arziƙiba, dan gani nake kamar wata ƙofa ce da kan fiddo da hucin zafi a gareni, ba lallai kowa ya ji abin da na ke ji ba, amma na sani wanan ba arziƙin da za'a kirashi da sunansa ba ne, face mabuɗin haɓakar ɓoyayyiyar inuwar da ido bai ganinta, ka min addu'ar samun sauƙin sauƙe nauyin da aka aza abisa wuya na, wata ƙila zafin ya ragu a gareni." Kai Malam Jauro ya jinjina yana yaba kaifin basirar Audu, da kuma tarin tausayinsa, wanda yasan dama hakan zata iya kasancewa, shafa kafaɗunsa yayi yana murmushin da ke ƙarfafa masa gwuiwa "Ba ko wani zafi bane ya ke da ƙuna Audussalam, wani zafin na tafiya ne da hanzarin bada kariya, ka tsammaci kariya ke gareka ba wai ingizawar raunatawa ba. Allah ya albarkaci rayuwarka da ta ahalinka baki ɗaya." "Ameen duka wajan suka amsa" Su dai su Lahla mamaki ya hanasu magana, gani suke kamar mafarki, wai sune zasu yi rayuwa a wanan ƙatoton gidan, lallai komi na Allah sauƙi gareshi, ba kuma acewa ba zai kasanceba. Anan dai suka zazzauna Mukhtar ya nemo musu abinci da abinsha suka ci suka rama sallolin da ke kansu, kana Audu ya roƙi alfarma da su kwana kafin gobe ya nuna musu wajan kasuwancinsa, idan yaso bayan kwana biyu sai su koma Bamaina. To basu musa ɗinba, dan dama a gajiye suke, hakan yasa suka kwana a washegari kuma suka fita da shiri, sosai suka rinƙa mamakin tafkeken kamfanin da Audu ya ke da shi, ga kuma ma'aikatan turawan da suke ta kai-kawo w cikimsa. Haka kuma shagonsa na farko na kasuwa shima yana nan ya ƙara haɓaka, kama dana suturu zuwa na kayan masarufi, mutanen da yawa ke layin siya, kasancewar kayansa ne yafi ko wanne sauƙin farashi a kasuwar. Sun sanya masa albarka da fatan kariya agareshi sanan suka nufi garin Bamaina a tare gaba ɗaya, har lokacin Mukhtar ke jigila da su, kasancewar gajiyar da ke ɗawainiya da Audu a wanan lokacin. Daga bayansu kuma wata ƙatuwar motar tirela ce da ke cike da kayan masarufi na abinci, sai yadika da atamfofin da suma aka haɗa dasu,wanan duk daga kamfanin Audu suke suka nufi garin Bamaina. ******* BAMAINA Tun shigowarsu Audu mutanen garin suka fara yi ma motarsa ƙawanya, ganin basu tsaya ba yasa suka ruga da gudu suka bisu, har ƙofar gidan Alhaji Jauro (Wanda yanzu sunayensu suka sauya." Wanan kuwa yana cikin tsarin Alh. Kallah wanda yace su sauƙa a gidan kasancewarsa babba kuma mai yalwa fiye da nasa. Sosai garin ya cika da kiɗe-kiɗe da bushe-bushe wanda sai ka rantse akan wani sarki ne ya dira a garin. Daga sassan gidaje kuwa sai rububin kawo musu abinci ake ta ko ina, lallai arziƙi yayi idan akayi duba da yanda mutanen bamaina ke ta risinawa suna washe baki da kiran "Maraba da sauƙa alhazawan Bamaina na farko a tarihi." Abin zai baka dariya idan kaga yanda ƙofar gidan Malam Jauro ta cika da matasa dattijai da kuma yara, iyaye mata ma basu yi ƙasa a gwuiwa ba suka rufo gyalensu suka tasamma gidan. Ba buƙatar sai sun huta hakan yasa suka shiga musu rabon kayan abincin da kuma tufafin sawa. Anan fa kida ya ƙara ninka na da, ihu da ahuwon mutane yasa har mutanen fadar mai gari suka rugo, dan dama tun zuwan motarsu labari ya riskesu, amma jin tsoron Mai gari yasa suka kasa tashi, to amma wanan tashin kiɗan da sowar mutane ya hanasu bin doka, wanda ya sasu kwasawa a guje dan kada ma mai garin ya dakatar da su. Ashe kuwa sunyi farar tafiya, suma suna zuwa aka haɗasu da nasu tagomashin alkhairin wanda ya sasu takawa da baza rigunansu, abinci ne da sai gidan wane da wane, sai gashi yau ko wani gida an bashi lasisin da zai girka tukunya ya sha. "Allah ya yiwa rayuwar ANA albarka, ya bashi tsawon kwana da kariya." Kalaman da mutanen bamaina suke ta yi kenan saboda nuna farin cikinsu. Haihuwa-haihuwa ce sai dai wata tafe fake da farar saƙar fa kan haska waje ko ba fitila, shi yasa zuwan ANA ga zamai musu kamar tsintaccen zinaren da ke wadata mabiyansa da komi na rayuwa. A cikin shekara biyun da akayi da haifar ANA ba zasu iya fayyace tarin alkhairai da nasarar da suka samu ba, kamar yanda mahaifinsa shima ya ke ganin kyakkyawan musali daga dukiyarsa da kuma nasararsa. Buhu kusan goma da tarin tufafi Audu ya bada akaiwa mai gari, wanda fadawansa har kamar sa kifa dan murna. Tun kafin su isa wajansa suka fara washe baki suna kiran "Lallai ba ruwan arziƙi da mugun gashi, yau ga ɗan gidan Kallah cikon gari ya kece sa'a, ko kasan har kamfanin sarrafa kaya gareshi da kuma na kayan masarufi na 'yan gayun da sai a radio muke jin labarinsu? To dai maganin tankiya gani da ido ga shi nan moto shaƙe da kayan abincin da yace a kawo ma, gaskiya yaron nan yayi nisa da baya da ƙyashi balle a samu hassada a tare da shi." Wani mai azababban surutu ya ke ta rattabo bayani ba tare da ya yi la'akari da ganin yanayin Mai gariba. Sai jin faɗuwarsa sukayi yana ta faman tari hannunsa dafe akan ƙirjinsa, kafin su ankare ya fara fidda guda-gudan jini ya bakinsa, hancinsa kuma yana zubar da jini. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 A hankali ya ke sauƙowa daga matattakalar jirgin, ido ya ɗaga ya kalli sama kana ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali. "Ƙasata" Ya faɗa da wata sassanyar muryarsa, wanan shine karo na uku zuwansa ƙasarsa wanda baya daɗewa tun bayan kai shi ƙasar Spain da karatu. Yaro ne ɗan shekara goma sha uku a duniya, amma a zahirance sai ka ɗauka shekarunsa sunfi haka, saboda girman jiki da kuma murɗaɗɗan jikin da yake da shi, kalar fatarsa fara ce da dogon ido sai lumsassun idonsa da suke cike da gashin ido, wanda girarsa ta ƙara taimaka masa wajan wadatuwarsa. Sumar kansa kuwa a murɗe take, wanda bata da maraba da ta turawa, sai dai a zahirance zubin fulani gareta idan ka wara ido. Cikekken bafullatanin da ya samu tsawon rayuwa a ƙasar waje, ya haɗu da rayuwar jin daɗin da ya ƙara tsatso da kyansa.+ Ido ya fara warawa yana kallon mutane da ke wajan suna ɗaga alamar da ke nuna sun zo ɗaukan wani ne. Ji yayi an ƙan-ƙameshi ta ƙasa, kafin kuma a kwatsa wani ihun da ya sashi Yin ƙasa da kansa, karo yayi da kyakkyawar yarinyar da bata da maraba da shi, wanda shekarunta ba zasu wuce biyar ba, ɗagata yayi yana jujjuyata fuskarsa ɗauke da murmushin da ya fidda jerarrun haƙoransa, da kuma lotsawar kumatunsa. "MAIMUNATU NAH!" Ya faɗa yana karata akan ƙirjinsa "Sosai nayi kewarki ba 'yar kaɗan ba." "Akhy! Kullum sai Abbu da Ummu sunce min za su kaini wajanka, amma basa kaini." Ta faɗa cikin muryar yarinta. Shafa gashinta yayi da ya sha gyara "Ƙyalesu ai gashi nan na zo ni ko." Kai ta gyaɗa kafin tayi magana suka ji anyi gyaran murya "To idan kun gama shanyamun sai ku zo mu tafi gida." Da sauri ya juyo yana kallon iyayen nasa da suke harɗe da hannayensu akan ƙirjinsu, baki ya buɗe yana kiran "Lah Abu dama tare kuka zo? Kaga harda wata mai kama da Ummu kuwa." Kunnensa ta ja tana kiran "Ƙara dubawa dai da kyau." "Auchhh! Abu kace ta sakar min kunnena, gani nayi ta dawo ɗagwas da ita. kamar ba ta ajiye ni ba. Ni gani nake ma kamar ta fini yarinta Abu." Ya ƙarasa maganar yana maƙe murya alamar raɗa. Dariya duka suka sa, harda Ummu da ta sakar masa kunne "Kaji da shi, har yanzun halinka na nan bai barka ba." Dariya yayi ya rungumeta yana kiran "Ina da kyakkyawar uwar da ke kular min da Abu wani sauyi zan gani? Ga kuma haɗaɗɗiyar ƙanwar da zan samu daloli da ita." Kai suka girgiza atare sanan suka nufi wajan motarsu da ke cike a harabar filin jirgin, ga kuma masu tsaron lafiyar Abu kasancewar a wanan shekarar ya taka matsayi da mataki mai yawa. Wanda har a wanan lokacin yana jerin sahun mutanen da suke da arziƙi a ƙasar Nigeria, matashin mai kuɗin da ke faɗi ta shi da kuma ɗaukar ɗawainiyar matasa galihu da guminsa da aljihunsa. Wanda ya janyo hankalin 'yan siyasa da yawa kansa, a matsayin su zo ya sa musu hannu ko bai fito takaraba, ya ɗaga hannunsa a matsayin shi nasu ne, hakan zai sa mutane su zaɓeshi. Kai yake girgiza musu yana murmushi akan siyasa ba ra'ayinsa bane, ba kuma ya fatan ya yita. Wanan kalmar na baƙanta ran su, hakan yasa suka biyo ta hannun ƙannensa Iro da Mammadu, wnda suma yanzu sun zama manyan mutane, haka kuma sun tara iyalai ko wannensu na da yara da aƙalla huɗu. Kasancewar Fatitiya ita bata haihuwa dan tazarar da ke tsakanin ANA da MAIMUNATU shekara takwass, gashi tun daga kanta shuru haihuwa ta tsaya mata. Shi yasa suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗora akan Maimunatu, musamman Ana da komi nasa Maimunatu, hatta a wajan karatu bai da labari sai nata. Duk da baya ƙasar amma kusan ko yaushe cikin video call suke, tun bata ganeshi har ta masa kyakkyawar sanayya. Duk kuwa lokacin da ya zo hutu Fatitiya kan zaunarshi ta masa nasiha akan ya kula da Maimunatu, ya bata kariya ko bayan basa nan. Musamman da ta je dubai tasa aka ƙera mata zobe guda biyu mai ɗauke da harafin sunayensu, ta sa ma Ana nasa, ta ɗaurema Maimunatu nata a wuta, da zare wanda sai ya zama kamar ado ne. Gargaɗi ta musu akan su kula, ko wata rana zai iya musu amfani. STORY CONTINUES BELOW  Lokacin da suka ƙaraso gida, ba ƙaramin mamaki ne ya kama Audu ba ganin yanda ƙofar gidan nasa ta ke cike taf da motoci. Ɗan tsaki yayi a hankali cike da jin haushi, dan yasan ko su waye ba zai rasa nasaba da 'yan siyasa ba. "Ku shige gida, zan gana da baƙi." Ya faɗa yana kallonsu, kana ya buɗe motar ya nufi wajan mutanen. Da fara'a suka tarbeshi, yayin da ya tsuke fuskarsa. "Nikam sau nawa zance muku bana buƙatar siyasa a rayuwata, Alh. Mukhtar? Yanzu kaima Alh.Izadden har ka bi sahunsu ka fara min jele? Ni har ga Allah kasuwancine ya isheni, haka bazan iya sanya hannu wajan cutar da talakawa ba." Tafi Mukhtar yayi yana kallon Audu "Da kyau Alh. Abdussalam Bamaina. Yau har kai ke nuna mana hannu da yatsa akan muna neman alfarma a gareka, kada ka manta duk wata gwagwarmaya da faɗi tashi na dukiyarka da mu aka yita, amma da yake kai butulu ne shine har zaka ƙi bamu dama mu samu wani abu muma." Kai ya Jinjina yana murmushi "Ka yi kuskure mukhtar, lokacin da ka ganni da arziƙina ka ganni, haka babu ko sisi naka a ciki da zaka ce da guminka na sameta." Dafashi yaji anyi ya ɗago, Izadden ne ya kafe shi da ido fuskar nan babu fara'a "Amma ko wani abu akwai mafari da sila ko Audu Kallah? Wanan shine karo na ƙarshe da zamu zo gidanka a matsayin neman alfarma, dan haka ka bamu amsa ɗaya da zata gamsar da mu, zaka shigo jam'iyarmu ko a'a." Hannun Izadden ya buge "Ba zan shigo ba har abada." Kafaɗa Izaddeen ya ɗaga "To ai shikenan, sai mu tafi ko?" Miƙewa duka sukayi mutanen dai-dai lokacin da su Iro suka kalli yayan nasu "Amma yaya baka kyauta ba gaskiya, abokananka tun da ƙurar kai kama haka?" "Ku min shuru! Ina ruwanku da rayuwata?" Kai suka girgiza suna wara hannu "Ba ruwanmu kam, mu dai ko yaya ne ba zamu yi asara ba." Harara ya bisu da shi, duk farin cikin da yake ji ya neme shi ya rasa. Hakan ya sa ya shiga gira rai a jagule, da sauri suka tare shi suna tambayarsa ko lafiya. Baki ya ciza yana girgiza kai "Wai ni su Mukhtar suke ma bore akan wata banzar siyasa. Har su Iro na faɗa min ba zasu yi asara ba." Kai ya jinjina yana dafe kansa da ke barazanar fashewa "Ba komi." Dafashi Fatitiya tayi yana bashi haƙuri akan ya manta da komi, shi kansa Ana jikinsa yayi sanyi da yanayin mahaifin nasa. Madadin Farin ciki ranar gidan komawa yayi na alhini. ******* ƘARFE BIYU NA DARE 2:00AM Wasu manyan mutane ne majiya ƙafi kewaye a gidan Audu tun daga katangar gidan har zuwa harabar gidan, gaba ɗaya sun buɗe masu tsaron lafiyarsa da hodar sumarwa. Haka kuma ko wannensu na ɗauke da mugun makamai a hannunsa, Fuskokinsu sun cika su da shunu ta yanda ba za'a gane kamarsu ba. Kai tsaye sashen Audu suka nufa suka zura wani mukilli suka buɗe mangaran, Zama wani jirɗeɗen mutum yayi akan kujera mai ɗaukan mutum uku, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana jijjigawa. "Ku shiga ku fiddo min ko wani abu mai rai anan." Nan suka ruga da gudu suka fara buɗe ɗakunan suna rufewa har suka shiga ɗakin Audu suka tuso ƙeyarsa shi da Fatitiya, wanda tsoro da furgici ga sata rafka salati da rawar jiki. watsasu sukayi a gaban murjejen mutumin, anan ya fara kallon mutanen wajan "Ina yaran nasu." Da sauri suka koma suka fara bincike sai gasu da Maimunatu a hannunsu "Ita ɗaya muka gani Oga" "Ku ƙara bincikawa ance babban ɗan nasa ya dawo yau ɗin nan." Komawa sukayi suka ci gaba da bincike amma basu ga ANA ba kasancewarsa a wani keɓaɓɓan ɗakin karatu, wanda ba kowa ne ya san wajanba daga shi sai mahaifinsa, dan ƙofar wajan kamar loka take, sai an buɗe an danna wani abu kana akega ɗakin, duk wani abu nasu mai muhimmanci na sirri kama daga dukiya ko wani docments anan suke ajiyewa. Sosai Audu ya gargaɗi Ana akan ko mahaifiyarsa kada ya nunawa, dan ɗakin a cikin ɗakinsa akayi shi, haka kuma ya sanar da shi wanan shine duk abun da ya mallaka da kuma shedara abun mallakinsa ne. STORY CONTINUES BELOW  Kai Ogan ya jinjina sanan ya kalli AUDU "Bamu da lokacin ɓatawa Alh.Abdussalam, mun zo ne akan ka bamu ko wani docmnets naka da dukiyarka, tunda ka ƙi ka sanya hannu akan siyasa, da ci gaban 'yan uwanka." Murmushi Audu Yayi "Ta nan kuma suka biyo, to ka koma ka sanar da su, dukiyar ƊAN BAMAINA ta sa ce, haka ta yarana ce, sile ba zan bawa ko wani ƙato ba." Kai ɗan daban ya jinjina "Sai dai ni ba iya ɗan aike bane Audu, ni mai cika aiki ne." Yana gama faɗar haka ya ɗana kunamar bindigarsa ya harbama Fatitiya a tsakiyar kanta. Nan take ta faɗi ƙasa ba numfashi.2 Wani ihu Audu ya ƙwalla da ƙarfi, wanda ya firgita dukkanin mutanen wajan, sanan ya nufi kan gawarta yana jijjigata, tuni jini ya yi ambaliya awajan, yan zuba. Dariya suka kwashe da shi "Ka makara, saura yarinyarka kuma." A zabure ya miƙe ya cakumo wuyan Mutumin jijiyar kansa duk ta firfito saboda tsantsar ɓacin rai, take mutumin ya saita hannunsa ya harbeshi, ƙara Audu ya ƙara saki, kafin ya ankara an ƙara masa harbi akan ƙafarsa. Wani wahalallan ihu ya saki, wanda yasa ANA fitowa a ruɗe ganin, mutanen da ke kewaye da falon gidan nasu, ga kuma iyayensa cikin jini ya sashi haukacewa da sakin wani ƙara. "Abu! Ummu" ya faɗa cikin firgici. Hannu Audu ya ɗaga masa cikin wahalalliyar murya "Kada ka ƙaraso nan ANA, ka gudu ka ceci rayuwarka, ka kula 'yar uwarka, kada ka bari su cutar da ita." Kai ya shiga girgizawa yana ƙarasawa wajan iyayen nasa, wanda Abu ke numfashi da ƙyar, ga kuma Maimunatu ahannunsu "Kada ka damu, ba zamu kashe ɗiyarka ba, dan ance itama kadara ce mai zaman kanta." Sanan ya juya ga mutanen ya musu inkiya da su kama ANA. Rirriƙeshi sukayi wanda yasa Abu zubar hawaye "Ahmad kada ka bari suyi nasara akanka, ka gudu ka ceci rayuwarka." "Ba zan iya tafiya na barkaba Abu! kaga Ummu bata numfashi Abu!" Ya faɗa muryarsa na shaƙewa. Ido Audu ya lumshe wani hawaye na bin kuncinsa "Yana da kyau ka rayu Ahmad ko dan ƙanwarka." Ya ƙarasa maganar yana lumshe ido saboda jinin da ya fara ɗaukarsa, ƙara ANA ya saki, wanda yasa ya watsar da mutanen biyun da suke riƙe da shi. Bindigar ɗaya a cikinsu ya wurce ya fara harba musu ta ko ina, ba shiri suka bashi hanya ya ruga da gudu, ga Maimunatu da ke ta faman kiransa tana AKHY! muryanta bai fita da kyau, saboda ruɗewar da tayi, ganin yanayin ɗan uwan nata ya sa ta faɗi sumammiya. Ɗaukanta shugaban 'yan dabar yayi suka fito harabar gidan, anan ya bada umarnin wasu subi ANA wasu kuma su ƙone gidan. Daga can nesa ANA ke hango gidansu na ci da wuta ga iyayensa na ƙonewa, hawaye ke bin idonsa yana jin ɗaci da bushewar zuciya na bijiro masa. Ganin mutane yayi sun iyo caaa akansa suna biyo shi, hakan yasa ya wullar da fankon bindigar da ke hannunsa ya ruga da gudu. Wata mota tilori yaga ta zo giftawa yayi saurin ɗaneta ba tare da ya san ina zasu ba, haka kuma mutanen basu fasa binsa a motarsu suna harbinsa ba. Ganin haka ya sa direban motar ya ƙara mata wuta, tsammaninsa 'yan fashi ne suka biyo bayansa, dan yayi lodin dabbobi zai kai su JOS kasancewar bikin kirismati da ya kawo kai. Sai da rana ta fito gari yayi haske mutanen basu bar binsa ba, anan ya hango wani jeji mai duhuwar gaske ya duro akan motar, duk da gudu da take, ya jima kansa ciwo sosai, dan saida ƙafar tayi ƙara, wanda ko shakka baya yi, karaya ce ya samu. Da jarumta ya take ƙafar yana jin ƙaranta ya kutsa kai jejin yana mugun gudu, ganin inda ya nufa yasa mutanen juyawa suna dariya a matsayin ruwa ta sha, ya kai kansa ga halaka. JEJIN YANKARI, nan na yima kaina iso na zamar da shi gidana, duk da tarin halittu mugwaye da manya da yara, haka kuma gefe masu farautar rayuwata basu fasa zuwa suna shawagi dan duna ina raye ko na mutu ba. Tun ina jure yunwa har na gagara na koma cin ganyayyakin bishiya da kuma ruwanta, ina tsoron namin jejin da ke kewaye da jejin, amma sai gashi Allah ya kareni suma ya sanya musu shakka a kaina, ganin yanda nake kwaikwayon rayuwa da ɗabi'arsu, ɗacin mutuwar iyayen da fuskar mutanen da suka kashesu ta gaza ɓacewa akan idona, gefe ɗaya kuma ina neman amsar silar rasuwarsa. A raina nasan ba dan siyasa bane, kawai yasa makusantan Abu suka kashe sa, sai dan wani abu da bai rasa nasaba da dukiya. Ka faɗa min TA YAYA NE ZAN SAKE YARDA DA WANI MUTUM A DUNIYA? TA YA ZAN YADDA AKAN ANA SAMUN MUTANEN KIRKI HAR YANZU? Shekara biyu na ɓata ina rayuwa a jeji ina yin rayuwar da dabbobi keyi, na manta haske da jin daɗin da na taɓa ji. Duk saboda YARDA DA KOWA NAGARI NE DA ABU NA YAYI. YA YARDA AKAN KO WANI MUTUM TSAGINSA NE BA ZAI CUTAR DA SHI BA, SABODA KALMAR MUSULUNCIN DA TA HAƊA MU." Hawaye ya biyo bayan maganar AKHY. Wanda kowa a wajan ya kasa koda motsa yatsansa, yana jinjina kai da al'ajabin wanan rayuwa. MUN DAWO LABARI Sosai hankalin jama'ar mai gari ya tashi, wanda suka kin-kimeshi suka shiga da shi gida, dai-dai lokacin da Lurwani ya rugo gidan a guje, hannu mai gari ya ɗagawa jama'arsa alamun su bashi waje zai yi magana da Lurwanu.+ Da hanzari suka futa yayin da wasu a ciki kuma suka tafi neman mai magani da ƙyar ya yafito Lurwanu ya ƙarasa kusa da shi, muryarsa na fita da ƙyar, ya riƙe hannun Lurwanun "Ajali ya cimmani ba tare da na cika burina akan Audu Kallah ba, ko wata rana nakan wayeta akan buri da son ganin faɗuwarsa, wanda kamar ina ƙara masa wutar haɓaka ce da ci gaba a gareshi. Ko bayan raina kayi ƙoƙarin cika min burina, ka nesanta da garin nan da mulkin mutanen bamaina, domin ba zasu soka ba, ba kuma zasu ma biyayya ba, ko ni ma gaf suke da min bore saboda bani da dukiyar da zan gamsar da su."4 Hawaye ne ya zuba akan idon Lurwanu "A'a Baba, kada ka ce zaka tafi ka barmu. Idan har ban karɓi mulkin bamaina ba wa ye zai karɓa? Bayan ni gadarta nayi." Shafa fuskarsa mai gari yayi, sanan tari ya sake taso masa, wanan karon jinin ya fi ko yaushe zuba da yawa "Saboda ka cimma nasara ɗana! Sai ka kawar da kanka daga zama mai garin bamaina sanan zaka yi nasara akan Audu Kallah." Hannunsa ya ƙara damƙewa da ƙarfi. "Ka cika min wanan burin nawa ko bayan raina." Girgiza kai Lurwanu ya ke yana sharar hawaye "Ni bani da gaba da Audu Baba, ba zan iya cutar da shi ba, dan zuciyata babu hassadar wani ko ƙyashi a tare da ita, ina roƙar maka rahama da sassauci daga abin da kake ji wanda kai ne ka siyama kanka shi. Audu mutum ne ɗaya da ɗaya, wanda ke maida alkhairi da sharri, na san na so Fatitiya a rayuwata, amma rasata da nayi ba yana nufin zan ƙulaci gaba da wanda ya kasance mijinta ba ne Baba. Ko yaushe takan sanar da ni bana jerin mazajan da kan tsayu da ƙafafuwansu, haka ban can-canta da zama tsani na rayuwarta ba. Tayi gaskiya Baba, mu da dukiyarku muke tunƙaho yayin da Audu ke bada labarin kansa da alfahari akan shi waye da matsayin da ya taka. Zan roƙa maka gafara daga gareshi, ina kuma fatan mutuwarka ta zama hutu a gareka." Yana gama faɗar haka ya tashi yana share hawayen da ke zuba akan fuskarsa. 'Tabbas ya ƙara yin karatu a yanzu, ya kuka fahimci illar da ke tattare da hassada, mahaifinsa ya fi ƙarfin komi a garin, sai gashi ya kasa godiya da abin da ya samu, har yake tunanin ganin bayan wani, waninma talakan da ke ƙarƙashin ikonsa.' Bai kai ga barin gidan ba, yaji ana ruga masa kira akan ya dawo rai yayi halinsa, mahaifinsa ya mutu. Wani zazzafan hawaye ne ya zuba akan idonsa, yana jin ciwo da kuma ɗacin rashin mahaifinsa da ya yi, tsawon rayuwarsa ya nuna masa gata da kuma soyayya, bai taɓa neman abu ya rasa a wajansa ba, mutuƙar yana da iko. Cikin ƙan-ƙanin lokaci labarin rasuwar Mai garin Bamaina ta karaɗe garin, kafin wani lokaci mutane sun cika ƙofar gidansa, da yawa tsoro ya kamasu, dan a yau ɗai-ɗaikun mutane ne basu ga mai gari zaune akan kujerarsa ba. Mutuwar da ta girgiza Malam Jauro da Audu Kallah, musamman da ya tuno tarin alkhairan Mai garin, wanda har tattaki yayi yama ANA kyauta. Lallai duk wanda mutuwa ba ta zama wa'azi a gareshi ba tofa babu wani abun da zai zama izna a gareshi. Bayan anyi jana'izarsa zuwa kwana bakwai, anan aka shiga batun naɗin sabon Mai gari, wanda sunan Lurwanu shi ke yawo a bakunan mutanen garin. Miƙewa Lurwanu yayi ya kalli dattawan garin da suke shirin naɗa shi a matsayin sabon Mai garinsu. Gefe guda kuma tarin mutanen garin ne suke baza nasu idanuwan dan ganin yanda naɗin zai kaya. Gyaran murya yayi gami da sallama da gaisuwa a garesu, wanda suka amsa cikin haɗuwar baki, suna kuma mamakin abun da zai faɗa wanda ya dakatar da naɗin nasa. STORY CONTINUES BELOW  "Tabbas na gode ƙwarai da karar da kukayi na zaman ta'aziyyar mahaifina, haka kuma zanyi amfani da wanan damar na roƙawa mahaifina yafiya a gareku. Sha'anin mulki abu ne mai mutƙar wahala da kuma nauyi, wata ƙila mahaifina ya taɓa aikata wa wani kuskure ko kuma zalinci da iko akan mulkinsa, akan hakan nake haɗa hannayena duka biyu nake baku haƙuri, daga talakawa zuwa masu wadata, yara da kuma manya, ku yafema mahaifina." Ya ƙarasa maganar yana haɗe hannunsa alamun roƙonsu da kuma neman yafiyar da ya ke. Anan aka shiga hayaniya, wanda da yawa kalmar "Mun yafe, mun yafe." Ita ke tashi a wajan. Murmushi Lurwanu yayi yana jinjina kai "Abu na gaba kuma, ni bana da ra'ayin Mulkin gari, haka kuma shekaruna sun gaza wajan sauƙe nauyi da hakkinku da zai hau kaina, kasancewar ban san ya ake tafiyar da mulki da kuma mutanen gariba. Sai dai a madadina na bada wanan mulkin ga Alhaji Kallah cikon garin Bamaina, ina fatan zai gudanar da mulkinsa cikin adalci da kuma kyautatawa fiye da ko wani mai garin da ya shuɗai." Hayaniya ce ta cika fadar, wanda har ba'a jin abun da wani ke faɗa, hannu Lurwanu ya ɗaga musu alamun su yi shuru wanda yasa wajan yayi tsit "Kun san mi yasa na ce na bar masa wanan mulkin?" Kai suka shiga jin-jinawa suna kiran "A'a" Murmushi yayi kana ya ɗora da cewa "Kasancewarsa talalan da yafi masu arziƙi wadatar zuciya, wanda ya ke kawar da kansa daga roƙo da kuma kwaɗayi a wajan wanda ya fishi, ba dan yana da akwaiba ko kuma ba shi da damar roƙon ba, sai dan zuciyarsa da ta ke cike taf da yadda da ƙaddara. Sunansa kawai na ke ji ana kira a matsayin cikon gari, amma a zahirance shi ne gundarin jigon garin bamaina, talakan da baya ƙyashin bayar da abin da ya mallaka, wanda ya ke fafutukar rayuwa a kewayawar maƙiyansa, ya kuma mayar da ɗansa ya zama jarumi jigo a garin Bamaina, duk da cizgunawar rayuwar da suka faɗa a wancan lokacin, hakan bai hanashi tunƙaho da kyautatawa mutanen garin nan ba, ya kuma mayar da matsalar mutane ta koma tasa fiye da wanda ke matsayin Mai garin. Shin kuna ganin akwai wanda ya fi cancanta da mulkarku fiye da wanan mutumin?" Kai suka shiga girgizawa suna kuma yin kabbara "Allahu Akbar!" Shine abun da mutanen wajan suke faɗi, tabbas babu wanda yafi cancanta fiye da Kallah cikon gari. Sai dai a wanan lokacin shi kuma Kallah mamaki ke daskarar da shi da kuma al'ajabi, kamar yanda da yawan mutanen wajan suka cika da jinjinawa Lurwanu. Take Alh. Jauro ya miƙe yana jinjina ga Lurwanu kana ya haɗa da bashi auren ɗiyarsa bara'atu wadda ke bin fatitiya. Lamarin da ya yima mutanen Bamaina daɗi kenan, gefe guda kuma Audu ke faman murmushi da jin-jinawa ga Lurwanu, ya kuma yi fatan ace ya zama daga ahalinsa na har abada. A yayin da alfahari da ɗagawa ya shiga zukatan IRO DA MAMMADU dan wanan nasarar gani su ke wata dama ce ta ƙara kusantowa garesu. Bayan naɗin sarauta dubbanin mutane suka shekada ɗaurin auren Bara'atu malam jauro da kuma Lurwanu Halilu. Anan Audu ya ja hannun Lurwanu suka keɓe a gefe "Ban san ya zan faɗa maka na nuna godiyata a gareka ba, sai dai ina fatan zuciyarka ke ɗawainiya da al'amuranka ba wai kanka ba." Murmushi Lurwanu yayi "Wanan shine karo na farko da naji araina alkhairi yana saurin kewayowa ga mai yinsa, ban taɓa ji araina zan samu mata a kurkusa ba sai a dalilin sadaukarwa. Shin kasan mi ake kira da hakan? Bayar da abin da ka fi komi so a rayuwa, naji araina mulkin Bamaina gado na ne, sai daga baya na fahimci gado bai fiya zama can-canta ba, zan iya aika kuskure masu yawa, wata ƙila su zama tsanin halaka a gareni kamar yanda suka zama ga mahaifina. Yin rayuwa kamar ko wani mutumin gari na nuna kana da damar yalwatawa ba tare da an tauyeka ba, akan hakan nake farin ciki da kuma bayar da abin da ya fi dacewa ga wanda ya can-canta. Zanyi amfani da wanan damar na roƙama mahaifina yafiya a gareka, wata ƙila baka saniba amma a zahirance hassadar da kan cinye zuciya da rayuwa ita ta zama silar mutuwarsa, dan Allah ka yafe masa." Ya ƙarasa maganar hawaye na zuba akan idonsa. Rungume shi Audu yayi yana share masa hawaye "Ban taɓa kwana da mutum a rainaba koda ya ɓata min akan idona, balle wanda ban saniba, na daɗe da yafema duk wanda suka cuceni da kuma wanda ke shirin cutar da ni a gaba. Mulkin Bamaina dole zai kawo tsaiko ga komawar Lahla birni, amma a madadinsa kazo ka zauna tare da ni da ƙannena, ka zauna kamar ahalina kaima." Sosai farin ciki ya kama Lurwanu, wanda hawaye suka sauƙa akan fuskarsa, anya akwai wani mutumin kirki a wanan duniyar bayan Audu Kallah? Gaskiya zai iya cewa babu, dan idan akwai ma basu da yawa. Ananfa labari ya kewaya gari da kewayansa na sabon shugaban da aka samu, haka mahaifiyar Lurwanu taji daɗin abun da yaron nata yayi, wanda ya zame masa alkhairi. ***** Bayan mako guda Anan su Audu suka tattara suka koma Dutse da zama shi da iyalinsa da kuma Lurwanu da matarsa, wanda da yawa 'yan garin suka musu rakiya suka kuma ga irin dukiyar da aka kashe. Gefe guda kuma Audu yasa an ƙawata gidan mahaifin nasa, da ginin da ke nuna tamabarin sarauta na zamani, haka aka gyara tsohon gidan mai gari wanda matansa ke zaune, yake kuma ɗaukan duk wata ɗawainiya ta su. ***** Bayan shekara ɗaya A wanan shekarar Audu ya zuba hannun jarin dukiyarsa a ƙasar Spain wanda ya ja kaso mafi rinjaye akan ko wani mai hannun Jari, kamar ko yaushe sunan ANA shine ya maye wajan kasuwanci, da kuma tambarin hannunsa da yayi tattaki ya zo da shi. Komi na turawa akwai tsari mai kyau, wanda ko ya ka gusa a abu to dole kai ke da damar yinsa komin shekara. A wanan lokacin kuma ya danƙama ƙannensa shagonsa da ke kasuwa na atamfofi da kuma na kayan masarufi, a matsayin mallakinsu halak malak. Haka kuma ya buɗe ma Lurwanu wani shagon kamar wanan, sai dai shi a garin Haɗejia ya buɗe masa, kusan guda uku ɗaya na atamfofi da kayan sawa dangin su shadda da less. Yayin da ɗaya ke na Takalma da jaka da kuma kayan kwalliya na mata, sai wanda ke na kayan masarufi, a ciki ya bashi ɗaya ya zama halaliyarsa, sauran kuma ya bashi a matsayin jiro da kuma amana a gareshi. Lamarin da ya baƙanta ran su iro, ganin yanda komi yanzu suke kafaɗa-kafaɗa da Lurwanu, haka ko a wajan Lahla, kafin ya tarbesu ya tarbi Lurwanu da matsalarsa da kuma fara'arsa, komi yanzu da akema Lurwanu ba'a musu koda rabinsa ne. Lallai dole su ƙara shiri mai tsayi.4 Kasancewar kasuwancinsa da ya ƙara ƙarfi a ƙasar spain hakan ya sa ya ɗauki ANA ya sanya shi a makarata a ƙasar, wadda har ɓangaren addini akwai. Matakin karatu tun daga nusry har zuwa scandry. Fuskar kowa da ke falon cike take da hawaye, baka jin komi sai kaɗawar fanka da ƙarar masuburbuɗar sanyin da ke tashi. Abban Jiddah ne yayi ƙarfin halin share hawayen da ke fuskarsa, kana yayi gyaran murya, yana dai-daita zamansa da dafa kafaɗar Akhy. "Ko kaɗan ba kayi laifi ba idan kaƙi yarda da mutane Ahmad. Sai dai a cikin mutanen banza akan samu koda guda ne na kirki.+ Shekaru biyun da ka ɓata kana fafutuka da rayuwa sun siya maka jarumta da ƙarfin zuciya. Ta iyu akwai wani dalili babba da Allah yasa ya barka a raye maƙiyanku basu cimmaka ba, lallai ya kamata ka cika fatan mahaifinka na ƙarshe, ka tsaya kayi fafutukar rayuwa da mu'amalantar mutane mabam-banta. Ka kuma ɓadda kama ta hanyar rikiɗewa Sabon mutum, ka fara shiga fagen fafatawa da neman ilimi, daga nan sai ka waiwayi rayuwar da ta gifta akan idonka. Lallai dukiyarka ta kasance taka ce kai da 'yar uwarka, dole ka nemeta a duk inda take ka zame mata inuwa ko daga nesa ne, har zuwa lokacin da zaka cika burinka." Rinannun idanuwansa ya ɗaga yana kallon Abba, muryarsa tayi zurfi sosai da rauni "Ta ina zan fara duk waɗan nan abubuwan Abba?" Murmushi Abba yayi kana ya ce "Ka sauya, ka koma kamar mayunwacin zakin da ke farauta a jeji, ka ɗauki maƙiyanka kamar karnukan da basu rabo da suɗar ƙashi. Ka wara idanuwanka wajan hango ma komi a matsayin babba, haka koda shuru ne kunnuwanka su ankare da abin da ya ke nufi." Murmushin gefen baki yayi yana shafa sumar kansa da bata da yawa "Abba ba buƙatar nayi sauri har haka, zan bari maƙiyana su manta da labarina, ta yanda zan zo musu a lokacin da basu tsammaci zuwana ba. Sai dai zan yi ƙoƙarin neman Maimunatu, saboda ban san a wajan wa take ba, da kuma halin da take ciki, duk da jikina yana bani tana cikin ƙoshin lafiya." Kai Abba ya jinjina yana shafa kansa "Allah ya albarkaci rayuwarka, ya ji ƙan iyayenka. Dole mu fara neman labarin Maimunatun, ko ta wata hanya ce daban. Ya kakega maganar karatunka? Zamu karɓo takardunka daga spain idan ya so mu sauya maka wata ƙasar da zaka ƙarasa karatunka acan ba tare da kowa ya sani ba." Kai ya jinjina yana goge fuskarsa da tafikan hannunsa "Idan akayi hakan baka ga maƙiyana zasu samu labari akan ina raye?" Kai Abba ya girgiza masa "Bana jin hakan, saboda su suna da ban-banci da ƙasarmu, basa bada bayani akan ko wani ɗalibi nasu, a taƙaice hankalin maƙiyanka ba zai taɓa kaiwa zaka samu damar komawa wata ƙasar karatu ba, saboda sun daɗe da ma kallon matacce." Ajiyar zuciya ya sauƙe, sai yanzu kuma ya fahimci abin da Abban ke nufi, godiya yama Abban sosai. Sai a lokacin Umma ta samu ƙarfin halin yin magana "Ina mutƙar maka ta'aziyyar rashin iyayenka. Haƙiƙa kaga rayuwa mai ban al'ajabi, ina kuma fatan zaka ɗauke mu a matsayin iyayenka na halak, ta yanda zamu samu damar kyautata maka kwatankwacin yanda mahaifanka suke maka." Kai ya gyaɗa saboda a zuwa yanzu ya gajiya da magana sosai, dan ba zai iya tuna yaushe rabonsa da yayi magana mai tsayi ba. "Na gode Ummah." Ya faɗa yana miƙewa daga falon, saboda gajiya da yayi da zama, harabar gidan ya fito yana kallon bishoyoyin da suka ma gidan ado da kuma bada kyakkyawar iska. Ji yayi an dafashi wanda ya sashi juyowa da sauri, ganin Kamalu ne yasa shi yin murmushi yana ɗaga masa gira alamar tambaya. Kai Kamalu ya kawar gefe saboda idanuwan Akhy da ke masa yawo suna sanyaya masa ko wata kusurwa ta jikinsa. "Ban taɓa jin labari makamancin naka ba tunda na ke a duniya. Nasha jin labari na cin amana, butulci da kuma zalinci, amma ban ci karo da wanda yayi kusa da wanan ba. Lallai kana da babbar zuciya mai kyau, shi yasa Allah ya barka da lafiyarka ya kareka a cikin manyan dawan da ko sunansu kan bada tsoro. Ka ɗauke ni a matsayin ɗan uwa aboki da kuma amini, ni kuma zan zama kamar sawun bayanka da kan maida ƙafarsa a duk inda ka ɗauke taka." Murmushi Akhy yayi ya rungume Kamalu "Ku bani komi na rayuwa a lokacin da na fidda ran samunsa, hakanma ya isheni Kamalu, ba sai na haɗa ma da wani nauyinba." Kai ya girgiza masa "Ban taɓa jin soyayyar ɗan uwa ba sai a yanzu da na haɗu da kai, ban taɓa jin zafi da ƙuna idan wani abu ya samu wani ba sai a kanka. Na ji a raina idan hakan da ni ya faru ban san ya zan kwatanta yin rayuwa ba. Dan Allah ka bani damar shiga cikin rayuwarka mu nemi fansa a tare." Sakin Kamalu yayi daga rungumar da ga masa, kana ya harɗe hannunsa yana kafe shi da idanuwansa "Ka cike ramin ɗaukan fansa a ranka Kamalu, kamar yanda nake ƙoƙarin cike ramin da ke zuciyata. A yanzu muna buƙatar yin rayuwa kamar ko wani mutum, muna kuma buƙatar fara gwagwarmaya da fafatuka a cikin ko wani yanayi. A cikin wanan shekarun namu zamu haƙa mu binne da ramin da ke da zurfi, har sai ya fallatsu ya haƙe da kansa, ka maida hankali akan karatunka, lokaci zai zo da zai kiramu da kansa ba tare da mun haɓako sa ba." Yana gama faɗar haka ya juya yana tattaki akan ƙafafuwansa, da mamaki Kamalu ya bishi da kallo, yana jin ƙaunarsa na ratsa ko wani sashi na zuciyarsa da tausayinsa. Numfashi yaja ya sauƙe a jiyar zuciya, kana ya juya da zummar shiga gidan, anan yayi tozali da Jidda da idanuwanta suka yi shaɓe-shaɓe da hawaye. Da mamaki yake kallonta, dan bai san da wanzuwarta a wajanba.. _Alhamdulillahi, a cikin rayuwa akan samu motsuwa da kuma zunguri na wasu sassan jiki, kamar yadda rayuwa ba ta cika bada abu guda ba, dole sai an samu kishiyarta. Cikin ikon Allah na samu sauƙi, duk da ba mai yawa bace, amma zanyi ƙoƙari na sauƙe nauyin da kai kaina kafin wani lokacin._ ********* Mamakinsa ya ɓoye ya raɓa ta kusa da ita zai wuce "Yaya Kamal ina so ka zame masa idon bayan da ke kare farmakin maƙiya. Zuciyarsa mai kyau ce, amma akwai ƙuna da duhun da ya hana ido ganinsa, yana buƙatar abotar da zata sanar da shi ba ko wani mutum bane mugu. Dan Allah ko sau ɗaya ne kada ka barshi ya tafi cikin lalume da yima mutane kuɗin goro akan mummunan ɗabi'a." Tunda ta fara maganar ya tsaya yana kallonta da mamaki, a shekarun da ke gareta wayonta da sarrafa kalamanta sukan bashi mamaki. Harshenta na da kaifi ƙwarai faɗar abu mai kyau. Shafa kanta yayi yana murmushi "Jiddah! Mutum da kike gani baya iya sauya ƙaddarar wani, bani da tsayin hannun da zan wara wanda zasu ruski Ahmad akan ɗabi'arsa. Amma zamu iya taimaka masa wajan gyara walwalarsa ko ba duka ba ce, ba lallai ki fahimci ƙunar da ke zuciyarsa ba, kamar yanda ni ma kintace nake akan abun da yake ji a nasa ran. Mu taya shi da Addu'a kawai, mu kuma bi abun da ya ke so mutƙar babu kasada da hatsari a cikinsa." Yana gama faɗar haka ya raɓa ta kusa da ita ya wuce, yayin da ta masa rakiya da ido. 'Ni zan sauya masa rayuwa Yaya kamalu, zan dawo da shi kamar ANA da ya shuɗe a shekara ukun da ta wuce.' Ta faɗa a ƙasan ranta kana ta share hawayen da ke zuba a kan idonta. Gidan ta shiga, inda ta tadda Ahmad yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun da ke falo, idonsa na kallon labaran da ake a tv, a zahiri ne ya ke kallon amma a baɗini zuciyarsa ta lula wata duniyar daban. Hannu Jiddah ta ɗaga tana fifita masa fuskarsa saitin idonsa, shurun da ta ji bai tanka mata ba haka bai ƙifta idonba ya sata jin yana wata duniyar daban ne. Gyaran murya tayi ta kai bakinta saitin kunnensa, anan ta kwaɗa ihu da ƙarfi wanda ya sashi furgita da rikicewa. Dariyar da yaji ana yi a gefensa ya sashi juyawa yaga JIddah har riƙe ciki take saboda dariya, tana kuma hantsilawa ƙasa daga kan kujerar da take, hannunta na kan cikinta. Murmushi yayi yana kallonta ya lumshe idanuwansa, baya buƙatar ƙarin bayani dan ya san ita ce silar tsoratarsa. Saida tayi dariyarta mai isarta kana ta sake zama a kusa da shi tana murmushi, duk da idanuwansa a lumshe suke amma yana ji a jikinsa ana kallonsa. Idonsa ya buɗe ya kalleta sanan ya mayar da su ya rufe "A irin wanan nisan zangon tunanin, mutane da yawa akan sace su. Rayuwar da ta gifta akan idonka tayi tsaurin da zata iya wanzar da raunin zuciya. Amma ga irinka ƙarfin zuciya ake buƙata, akwai nauyi da yawa da ya rataya akanka. Shin bayan Maimunatu ka taɓa tunanin Kakanninka kuwa?" Juyowa yayi yana kallonta da duka idanuwansa, kai ta gyaɗa tana ƙara fuskantarsa "A zuciyarka ƙuna ce da tanadin fansa da kuma lalime a cikin duhu, amma ya kamata koda sau ɗaya ne kaji aranka kana son sanin labarin halin da kakanininka suke ciki bayan rasuwar iyayenka. Kada ka tsayar da komi ka tsammaci zuwansa, abubuwa da yawa suna buƙatar hanzari da kuma zaburarwa. Kayi amfani da bugawar zuciyarka ba agogon da ke ɗaure a hannunka ba, ita kaɗai ce zata ankarar da kai lokuta masu muhimmanci na rayuwarka." Tana faɗar haka ta miƙe tsaye tana kallonsa, kamar yanda shima yake kallota da tsantsar mamakin maganarta yake, yanda ta iya tsaro zance kamar wata uwar mata. Murmushi ta masa ta gyaɗa masa kai "Kana buƙatar abokin rakiya saboda yin ɓadda kama, wanda zai nemo maka labarin halin da ahalinka suke ciki. Kafin ka bar ƙasar nan ya kamata ka san labarinsu, ta iyu ka samu wani hasken da zai haska abin da ya shige maka duhu." Daga nan ta tafi ta barshi da bin bayanta da kallo. Murmushi yayi yana auna maganarta da tayi, gefe guda kuma yana jinjina kaifin azancinta. Tabbas yana buƙatar sanin wani abu bayan labarin Maimunatu, haka kuma yana buƙatar yin waiwaye dan jin ababen da suka wanzu a bayan babu su. STORY CONTINUES BELOW  'Amma ta ina zai fara? Wa yake da shi a yanzu da zai zame masa idanuwa da kunnuwansa kafin ya tona kansa? KAMALU! shine mutum guda da zai iya kare ma sirrinka, wanda a idanuwansa babu komi sai Zallahr ƙauna da kuma tausasawa ta 'yan uwantaka.' 'Ina jin tsoron MUTANE da abin da suke ɓoyewa a ƙasan ransu. Ina jin tsoron fuskar da suke ɗorawa akan ta zahirinsu, bani da tabbacin KAMALU baya daga cikin mutanen nan. Ba zan yi wanan sakacin ba kamar yanda ABEY yayi a baya.' Tarin tunanin zucin da ya ke kenan yana kuma tufka da warwara akan abin da zai ɓulle da shi. Sai dai har a wanan lokacin bai samu matsaya guda ɗayaba wadda ta wuce Kamalu, dan zuciyarsa na ingizashi akan yayi amfani da shi ko da sau ɗaya ne, sauran shirin da zaiyi agaba ya barwa kansa shi. Tashi yayi ya samu Kamalun yana zaune a ɗakinsa, ya zauna kusa da shi yana kallonsa "Ina so zaka min rakiya Jigawa gobe, zamu dawo a kwana biyu idan mun samu labarin halin da su Lahla suke ci." "Da gaske?" Kamalu ya faɗa cikin zaƙuwa da ɗokanta da jin labarin. Kai ANA ya gyaɗa yana murmushi "Idan har Abba ya amince amma. Sanan muna buƙatar sabuwar fuska da sauya kamanni wanda ba za'a gane mu ba har mu shiga mu fito." Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa da ɗokin maganar ANA ɗin "Tashi tun yanzu mu sanar da Abba, dan mu samu muyi sammako gobe idan Allah ya kaimu." Tashi sukayi a tare Kamalu na gaba Ana na bin bayansa, har gaban Abba, Kai tsaye Kamalu ya sanar da Abba abin da ya kawo su. Kallon Ana yayi yana murmushi "Wai haka Ahmad?" Kai ya gyaɗa yana shafa kansa "Ina son nasan halin da suke ciki ne Abba, kafin na bar ƙasar, wata ƙila na iya samun labarin MAIMUNATU, duk da ba wai a kamata ta zahiri zan je musu ba, zan yi ɓadda kama a matsayin matafiyin da hanya ta ɓace musu, ina so muje da Kamalu muyi kwana biyu sai mu dawo." Kai Abba ya jinjina cikin gamsuwa da maganar tasu "Shikenan sai kuje da direba idan ya so sai ya ajiye ku ko a dutse ne, ku kuma ku ƙarasa a motar haya gudun kada a gane ku wasu ne, ku je a matsayin talakawa inaga zai fi muku sauƙin samun yardarsu, duk da mutane yanzu sunfi gane wa da yaren da kuɗi ke badawa, amma bana so kuje a hakan gara kuje kamar kowa. Ƙila Lahla ya fi karɓanku fiye da masu kuɗi." Kai suka gyaɗa cikin gamsuwa da maganarsa, suka risina suna masa godiya. Washe gari tun ƙarfe bakwai na safe suka fito da shirin tafiya, Abba da Umma da Jidda na musu rakiya da fatan sauƙa lafiya akan Allah ya kare su. Sai da suka ga ɓacewarsu kana suka koma cikin gidan, cike da kewarsu a zukatansu. **** Gombe, Nigeria. Shuru ne ya karaɗe falon, sai ƙaran fanka da masuburbuɗan sanyin da ke tashi. Can ya ɗago da wasu takardu ya watsa akan fuskar ɗan nasa "Wanan shine shirmen da ka aikata a wanan shekarar Zayd, ba Ƙwandala guda ba, zunzurutun maƙudan kuɗaɗe na na kashe, dan kawai na sama maka kyakkyawan karatu da kuma mafakar da zaka tsaya da ƙafafuwanka. Amma duba nan banda fail da fass ba abun da ka samo min, anya kana ma kanka da ni adalci kuwa Zayd? Ga 'yar uwarka nan duk sakamakon jarabawarta ba wanda ta samu good ma balle aje matakin fail, itace zaƙwaƙurar da ta kere ko wacce samun makin jarabawa a makarantar. Gashi dai idan ta fuskar shekaru ne ka fita, amma ba komi akanka sai zallar ƙura da hayaƙi. To ka jini da kyau ko baka so ya zame maka dole kayi karatu, dan ina buƙatar kafuwarka da kuma ganin ka tsaya wajan kula min da kasuwanci na." Tunda ya fara maganar bai tsaya, yayin da gefe guda Zayd ke cika yana batsewa, yana aikawa da Yumna da harara kamar idanuwansa zasu faɗo. Ita dai murmushi take jin yabon da Dady ya ke mata, ga kuma tarin ƙuncin da take hangowa akan fuskar Zayd ɗin da ya kasance dodonta kuma mai cin zalinta. Momy ce tayi tagumi tana kallon Zayd ɗin da har jijiyar kansa ta tashi saboda tsabar ɓacin rai da jin haushin maganar mahaifin nasa. "Dady sau nawa kake so na faɗa maka ni babu karatu a tsarin rayuwata, asalima ni ban ɗauke shi a wani tsani da zai kafani ko kuma silar taimakon kasuwancinka ba. Mutane nawa na sani da karatu ya zame musu silar naƙasu na rayuwarsu, wasu ma kamar almajirai suke da ɗai ba za'a ce sunyi shi ba. A yayin da gefe guda wasu suke zama masu babakere da handama ga abin da ba nasu ba, dan kawai sun zama wani abu daga karatun da suka koya. Dady ni ba zanyi karatu dan kasuwanci ba, idan har akwai abin da zan yi to zanyi ne dan amfanin mutanen da zasu girmama ni da dukkanin zuciyarsu, ba wai waɗanda zasu girmamani dan sulalan da ke gareni ba. Ina so na tsaya da ƙafafuwana ba wai na ƙare rayuwata ƙarƙashin kula da dukiyar da ba ni ne na zama silar taruwarta ba." Da mutuƙar mamaki suke kallonsa, ciki kuwa harda Yumnah da ta kasa ɓoye al'ajabinta akan ɗan uwan nata. Kai Dady ya riƙe yana ji yana mutƙar sara masa, kana ya lumshe idanuwansa yana ji kamar zai faɗo ƙasa. Shikam wani zunubi ya aikata haka da aka jarrabe shi da Zayd, ta ko ina ya biyo da shi yana zamewa ya kauce akan ko wani buri nasa da yake hararo ƙarshensa da Zayd ɗin zai iya kawowa. Sai dai ashe hasashe yake da tsammani amma ko kaɗan hakan ba mai iyuwa bane. "Haba mana Zayd ! Mi yasa kake so ko yaushe ka ɓatawa mahaifinka rai? Minene dan ka ajiye burinka ka cika muradin mahaifinka? Da mi hakan zai rageka Zayd?" "Momy ni ina son yin rayuwa mai sauƙi ne kamar ko wani mutum. Ina da burin zama wani abu a karan kaina ba wai a matsayin ɗan wani ba. Mutane suna cewa masu tsayuwa a bayan wasu raunatattu ne, haka kuma kasassu ne da ko yaushe lissafin rayuwarsa kan iya komawa sufuli. Zai iya yiyuwa na zama silar daƙusar da ci gaban arziƙin Dady idan na karɓi abin da ba ni da tsari a kansa. Da ko wata rana soyayyar Yumnah nake gani a idanuwansa, tausasawarsa duk a kanta yake ƙarewa, to taya zan ƙarfafa gaɓɓain jikina na wahaltu da ƙwarewata ƙarshe ta fini samun matsayi da kuma amfana da abun da ni nasha wahalar tara shi." Kai Momy ta iya gyaɗawa ba tare da ta iya magana ba, sai Dady da ya gama sarewa da al'amuran yaron nasa, ba shakkah Zayd zakkah ne a wajansa, haka kuma jarrabawar rayuwarsa, amma idan banda haka a lokacin da kowa ke fafa da tunƙaho da iyayensa, shi ƙoƙarin gudun wanan matsayin yake. "Shikenan, kaje kayi duk abin da kake son yi Zayd, ni kuma zan tsayawa Jiddah da dukkanin abin da nake da shi, akan ta faɗaɗa karatunta, ta kuma cika min burina da kai ka kasa cika min shi. Nagode Allah da ba kai kaɗai ne ɗana ba, da na tabbata zuciyata yau sai ta buga, amma ba zan taɓa bari ta buga a sanadinka ba, dan ina da tarin mafarkan da ban gama cika su ba. Ku fara yima Jiddah shiri dan daga yau zuwa ko wani lokaci zan samar mata wajan karatu a ƙasar Germany." Yana gama faɗar haka ya tashi ya barsu, da rakiyar ido.

0 Comments