WANI ALAMARI CHAPTER 4

WANI ALAMARI CHAPTER 4
Can kuwa a b'angarensu YASEER lokacin da jeeddah ta shiga ta shirya musu table,duk kansu basa cikin parlour'n,dan haka har tayi zagayenta a wajen ta gama ta fita basu san da shigowar taba,haka itama harta fitan bata yi tunanin suna nan ba,fitarta babu jimawa sosai suka fito dan bawa uwar hanjinsu hakkinta kamar yadda Ummi ta shaida musu an shirya musu table en,koda bayyanarsu cikin parlour'n bayan sun watsawa jikinsu ruwa sun d'an rage gajiya sai duk suka nufi hanyan table da suka hanga da kayan abinci a kai,zamansu babu jumawa suka fara kai hannayensu kan lemon dake cikin cup's da aka d'ora abu an rufe a tare,koda d'aukan cup's en ba tare da wata² ba suka shiga tultulewa uwar cikinsu,bayan nan kuma kowannesu ya shiga d'iban abunda ransa ke buk'ata. Duka da zaman su a gurin baifi mintuna ashirin ba,suka fara neman b'ingirewa,YAZEED ne ya fara d'ago kansa a hankali jin yadda jikinsa yayi nauyi ya kalli YASEER yana bud'e idonsa da k'yar da yayi masa wani mugun nauyi yana shirin yin magana "Bro..ss...! Wai wane irin abinci ne wannan..??" Cikin murya kamar ta mutumin daya sha wani abu ya bugu YASEER ya d'ora kansa akan table en yana sakin dariyar mugunta da cewa "Kaji wani rainin hankali..yo nima ina na sani nida nake shirin tambayar ka..ko ance maka na zama Mr chief ne da zaka tambaye ni kalolin abinci..?" Tsaki YAZEED yaja kafin ya gallawa YASEER en harara cike da jin haushin amsar daya bashi ya furta "Kai matsalar ka rainin wayo...Baka tashi yin abu sai kaga wani yayi sannan ne zaka nufi hanyar aikatawa..'Dan rainin sense kawai..Daga tambayarka abu kana wani bani wata banzar amsarka can..dillah ja jiki...!" Yana fad'ar haka ya yunk'ura zai tashi ya bar wajen dan yadda yake ji alokacin,haka da ganinsa kasan tuni ya jima da manta abunda yake yi a gurin,d'agowa YASEER ya sake yi ya kalleshi yana masa murmushi "Bro..ss..! Where u dey go ne..??"+ "Kaiii kada ka takurani wanka zanyi.." Murmushin dai YASEER ya kuma yi masa yana d'aga masa hannu da fad'in "Sai ka dawo...nima yanzun zan motsa.." Yana shirin ci gaba da magana idanunsa na rufewa da bud'ewa yaga alamar mutum ya wuce,saurin lek'awa bayan YAZEED dake tafiya yayi yana masa inkiya da hannu ya matsa kamar wanda akace masa yana kallon abunda yake yi,coz a time en shi YAZEED en ya bawa YASEER baya,dan haka sam bai san me yake yi ba,shi en kuma da yake masa hakan bawai yayi masa magana bane,koda ganin haka sai yasa YASEER d'aga murya cikin muryar maye ya furta "Waye nan ne...??" Tuntsurewa da dariya YAZEED yayi dake neman kifawa saman cuition yana fad'in "Kai amma kwai gara,waye kuwa idan bani ba..??" Ga YASEER kuwa koda yaji abunda YAZEED en ya fad'a kawai sai ya kalleshi da narkakkun idanunsa yaja tsaki,duk da a buge yake a lokacin hakan bawai yana nufin baiga giftawar da akayi ba,mik'ewa yayi cike da tangad'i ya nufo hanyar tsakiyar parlour'n da niyyar bincikawa,yana daf da zuwa gurin kawai sai yaga mutum ya fice da gudu.Bin bayan wanda ya fita yayi yana kira da tambayar waye,sai dai ko kafin ya k'araso tuni har yayi masa nisa saboda tafiyar su babu yadda za'ayi tayi dai²,dawowa yayi da baya yana d'aga kafad'a sama alamun ko a jikinsa,zuciyarsa da tunanin abunda ya gani shin gaske ne ko kuwa zatone yake,ko kuma dai shi ne baiga dai² ba,girgiza kai yayi yana sake d'aga kafad'a sama kafin ya dawo kusa da YAZEED shima ya baje. *Cikin wannan yanayin ne jeeddah ta zo ta tarar da su.* →→→ Mik'ewa tayi tsaye zuciyar ta cike da fargabar sak'on da YASEER ya bata ta sanar da Ummi'n nasa,har ta juya zata bar side en nasu ta fasa,a hankali cikin rashin nutsuwa ta dawo kusa da su ta tsuguna a kusa da YAZEED tana cire nik'ab en dake fuskarta kamar wata jami'ar bincike,cikin muryanta mai sanyi ta shiga kiransa "Yallab'ai..! Ka tashi.." Ta kirashi ya kusa sau goma kafin ya iya d'agowa yana licking lips ensa kamar mutumin dake shan sweet,hoton shadow enta daya gani cikin idanunsa ne yasa shi sakin d'an murmushi sannan ya shiga k'ok'arin bud'e idanunsa duka da k'yar,akanta ya sauke sexy eyes ensa dake cike da maye yana sake sakar mata murmushin sa mai tsada,ko da ganin haka sai jeeddah tayi masa murmushin itama tana cewa "Yallab'ai Ummi na son ganinku...!" Ba tare daya iya tantance me tace ba ya maida kansa ya kwantar yana d'aga mata hannu alamun ta tafi karta dame shi,mamaki ne ya cikata da ganin abunda suke mata kamar wad'anda ke cikin yanayin hauka,sake kiransa tayi tana maimaita masa sak'on na Ummi,ga mamakinta wannan karon koda ya d'ago ya kalleta sai kawai ya mirgino da k'yar ya jata zuwa jikinsa cikin muryar maye ya furta "Hiii..! Young lady..!" K'ok'arin k'wace jikinta ta shiga yi daga nasa cikin rikicewa,cikin abunda baifi minti d'aya ba gaba d'aya ilahirin jikinta harya hau rawa saboda tsabar firgicin dake tattare da ita,kasancewar jikinsa babu wani k'wari sosai yasa bata sha wahala ba tayi nasarar kub'utar da kanta,shi kuwa gogan koda yaji yadda suke kokawa da ita sanda take son kwacewa daga rik'on daya mata,sai kawai ya shiga kyalkyala mata dariya,ita kuwa jeeddah koda ta samu ta tsira bayan ta gama maida numfashi sai ta juyo ta kallesu duka,haka nan taji zuciyarta tak'i nutsuwa da yanayin su a lokacin,tunaninta ne yayi nisa kan warin data jiyo yana tashi daga bakin YAZEED lokacin da yake mata dariya,nan ta tsaya tana sake binsu da kallon tsantsar mamaki,yadda suka sheme suna irin wannan bacci cikin dak'ik'u tuni ta gama fahimtar babu lafiya,haka nan ko kallonsa kayi daga yanayin shigar dake jikinsu dole ne duk mai hankali ya fahimci basa cikin yanayin da zai tabbatar da lafiya,juyawa tayi ta nufi table en data gani a warwatse cike da son bincika ainihin abunda ya faru,yadda ta iske table en da abinci cikin plate's ba'a ko ci rabin ko wane plate ba yasa ta juyawa ta kallesu tana nazari,haka nan tsarin table enma kad'ai sai daya sata share gumi,tabbas tasan itace ta shirya komai,ta yaya za'ayi ta ganshi a haka yanzun a hargitse kuma tayi zaton lafiya..?? Kasuwa zuciyarta tayi saboda tsabar tunanin dake neman yi mata yawa,amma kuma sam ta kasa tantance abunda take zargi,cups en data gani a kwance maimakon su kasance a zaune ta mik'a hannu ta d'auka tana juyasu a hannunta kafin ta kaishi saitin hancinta da nufin shanshana su,tun kafin ta k'arasa kai hancinta kusa da cup en tayi saurin janye shi tana ajiyewa gami da to she hancin,saurin dawowa tayi ta tsaya a kansu ba tare data yanke shawaran abunda ya kamata tayi ba kawai ta zuba musu idanu zuciyar ta duk ta cunkushe saboda rashin madafa. Ta d'auki lokaci a tsaye ba tare data gama yanke shawaran abunda ya dace tayi ba na daga taimakon daya dace ta fara basu,tana nan tsaye ba tare da tayi yunk'urin aikata komai ba doorbells yayi k'ara,a firgice ta juya ta kalli k'ofar sannan ta sake kallonsu zuciyar ta na daka,knocking en k'ofar da aka sake yi a dai² lokacin shi ya dad'a tayar mata da hankali,har ta kama hanya zata shige ta nemi gurin b'uya zuciyar ta ta gargad'eta da sauri ta tsaya duk a rikece ta rasa abunda ya dace tayi,hawayen firgici na sakkowa saman fuskarta,motsin k'ofar da taji ana tab'awa alamun ana daf da shigowa tuni ya dad'a jefata cikin zullumi da fargabar abunda zai je ya dawo a wannan fada,tabbas tasan matuk'ar aka ce wani yasan halin da ake ciki tofa lallai ne kashinta ya gama bushewa,hanzarin katse tunanin tayi cikin sand'a ta matsa jikin k'ofar da kyau ta tokareta,dai² sanda take k'ok'arin kai hannunta saman handle en daga can waje taji an rik'e ana murd'awa,cikin tsantsar tsoro da damuwa tayi azamar d'ora nata itama akai ta rik'e iya k'arfinta,iya murd'awa mai son bud'ewar yayi k'ok'arin sa wajen ganin ya samu nasara amma ina jeeddah ta hana shi wannan damar dan kuwa itama ta rik'e gam ba tare data saki ba,murya cike da jin haushi wanda ke k'ok'arin bud'ewar ya saki handle en gami da yin tsaki mai sauti yana fad'in "Kaiii! Nanfa bana tunanin akwai mutum a ciki...!" Ya fad'a yana sake lellek'awa kamar ance masa zai ga wani idan yayi hakan,zuwa can kuma ya juya ya bar wajen cike da mita,bayan barinsa wajen koda jeeddah ta tabbatar babu kowa a gurin nan tayi saurin rufe side en ta ciki sannan taja mugun numfashi tana sharce mugun gumin daya keto mata,gaba d'aya k'wak'walwarta tayi duhu duk wani mafita da take tunanin tana da shi a dai² wannan lokacin kam ya b'ace,haka nan take jinta tamkar bata tab'a sanin komai ba a rayuwarta,idea ne ya fad'o mata na kashe fitilun parlour'n,nan kuwa tabi shawaran zuciyarta duka ta kashe sannan ne ta dawo inda ta barsu ta zauna cikin duhun tana fashewa da kuka mai tsanani ba tare da sa ran samun mafita ba... ^^^^^ Can kuwa a b'angaren GALADIMA koda yaji shirun yayi yawa Ummi bata neme shi ta sanar masa halin da ake ciki ba,nan ransa ya sake kaiwa matuk'a wajen b'aci,ba tare daya sake nemanta ba akaci gaba da gudanar da taron dinner,cikin zuciyar GALADIMA kuwa lissafa irin hukuncin da zai yiwa su YASEER yake ba tare da sanin maimartaba ba saboda yadda suka wulak'anta su a gaban dubban al'ummah,haka nan ita kanta Ummi ya gama yanke shawaran abunda zai mata dan yadda yaji shiru zuwa wannan lokacin gani yake har da laifin ta yasa basu zoba har yanzun,ba tare da ganin kyallinsu ko sa ran zasu samu damar halartar taron ba aka ci gaba da gudanar da shagalin. Misalin k'arfe tara na daren da wasu y'an mintuna,bak'ar motar k'irar Benz sabuwa fil da ita ta shigo harabar gidan gwamnatin aguje,dai² bakin coronation hall en ta paker,a dai² lokacin ne kuma na jiyo karad'in MC en yana sanarwa,sake saurarawa nayi dan jin mene ne zai fad'a haka mai muhimmanci,nan kuwa na tsinkayo muryarsa yana fad'in "ALHAMDULILLAH..! Alaa kulli haliin...! Bayan dukkan jinkirin da muka samu da tsaiko na jiran da mukayi,y'an uwa da abokai da suka samu damar halartar wannan taro mai albarka..A dai² wannan lokacin ne nake fatan sanar daku k'arasowar masu gayya..Wad'anda Ni,Ku dama dukkanmu nan muka taru dominsu a dai² wannan lokaci....! Saboda haka muke fatan al'ummah zasu sake bawa wad'annan shahararrun matasa hannu...! Domin karramawa..." K'aran tafi ne ya cika gurin,cike da fara'a da murnar isowarsu ga sauran y'an uwa da basu samu damar ganinsu lokacin da suka iso k'asar ba,yadda al'ummah suka cika d'akin taron abun gwanin sha'awa da mamaki,garesu kuwa tunda suka shigo cikin gurin da suka hangi yadda fuskar GALADIMA nan take yasa su shan jinin jikinsu,haka dai jiki a sab'ule suka nemi guri suka zauna,duk wani yanayi dake fuskar iyayen nasu babu wanda basu karanta ba,hakan tasa cikin rad'a YASEER ya kalli YAZEED yana fad'in "Broh..! Yau kam mun tafka laifi..kaga irin kallon da Abba yake mana kuwa..??" Murmushin yak'e YAZEED yayi sannan ya d'an juyo ta yadda yasan YASEER en zai jishi ya bashi amsa "Ka bari kawai d'an uwa.. Nifa duk ba kallon da Abba yake mana yafi tayarmin da hankali ba,yadda akayi muka yi sake har muka b'ata lokaci nake...shin wane irin bacci ne muka yi haka...Ni wannan duk yafi damuna ya kuma fi d'aure min kai sama da komai a yau.." "Haka ne ni kaina wannan abun yasa ni damuwa sosai,sai dai kasan dole ne mu danne duk wata damuwa yanzun har zuwa mu koma gida gudun kada mu sake yin laifi.." Jinjina kai YAZEED yayi sannan suka maida hankalinsu kan MC,haka taron dinner yaci gaba da gudana inda daga Biyani kuma MC ya nemi kowanne cikinsu daya gabatar da jawabin godiya tare da bayyana kad'an daga cikin irin nasarorin da suka samu a tak'aice,haka ko sanda YAZEED ya bayyana a gaban jama'a tun kafin ya kaiga bayyana ko shi en waye tuni ruwan flasher ya soma d'aukan idonsa,shi abunma tun yana bashi mamaki har ya daina,sai dai abun d'auren kan dalilin da yasa hakan ya faru daya shiga yi musamman ganin yadda fiye da rabin masu d'aukan nasa suka kasance mata,a hankali ya tab'e baki sannan yaci gaba da abunda ya tsaida shi cikin dakiya da d'aure fuska. Kamar an ce masa ya kalli side ensa na dama daga can ensa,ai kuwa nan idanunsa suka sauka kanta nan zuciyar sa tace dawa Allah ya gamamu,farace amma ba canba,mai madaidaitan idanu,haka nan hanci da bakinta duka ba wasu masu girma ba,kyau kam tana dashi dai² nata,sanye take da bak'ar riga haka nan Vail en kanta shima bak'in ne,tana zaune ita kad'ai tayi shiru abunta ba tare da damuwa da komai ba,ya d'auki lokaci yana kallonta kafin ya iya janye idanunsa akanta da k'yar sanda ya kawo k'arshen speech en nasa,sanda ya koma kusa da YASEER ya zauna ya sake wulga idanunsa inda ya ganta saboda son bawa YASEER en labarin abunda idanunsa suka gani sai kawai ya nemeta ya rasa tamkar fatalwa. Mamaki ne ya cika shi dan yadda ya ga gurin da take zaune d'azun yanzun babu ko kyallinta,sake juyawa yayi yana baza idanu cikin taron jama'ar amma ko mai kama da ita bai hango ba,haushi ne ya kama shi cikin takaici ya furta "Wace ce ita.....??" Wani kallon rashin fahimta YASEER ya bishi da shi kafin ya furta "A ina kenan.??" Juyowa YAZEED yayi ya kalleshi fuska duk b'acin rai ya furta "Ban sani ba nima.." Tsaki YASEER ya saki kafin ya juya yana kallon wani side daban,har aka tashi a gurin dinner en YAZEED bai daina hangen inda ya ganta ba ko Allah zaisa ya sake yin gam da katar,a haka kowa ya watse su kuma suka kamo hanyar komawa gida,har lokacin zuciyarsa cike da jin haushin rashin ganinta da bai samu damar sake yi ba bare yasan daga inda ta fito,da wannan tarin haushin suka nufi gida,bayan isowarsu gida basu yi gangancin bin ta side en iyayen nasu ba,direct nasu side en suka nufa,koda shigansu babu wanda ya iya magana da d'an uwansa suka nemi guri kowa da abunda ke sak'awa a zuciyar sa. Sun d'auka lokaci a haka zaune shiru,zuwa can idanun YASEER suka koma kan table a hankali ya mik'e ya nufi gurin yana dube²,yadda komai yake haka yake yanzunma,komai nakai a hargitse kamar wanda akayi wani shahararren artabu akansa,gurin ya k'ute da kallo zuciyar sa cike da tunanin yadda akayi suka maida gurin haka........ _Tambayar anan itace shin yaya akayi wai su YASEER suka samu damar halartar taron...??_ _Mene ne ya faru da su har suka yi irin wannan buguwa...???_ ^^^^^^^^ Duk iya tunaninsa akan yadda hakan tafaru sam ya gaza kaiwa kan abunda yake tsammanin,takura kansa da k'wak'walwarsa yayi akan lallai sai ya gano gaskiya amma ina abu ya gagara,ko da ganin haka kawai sai ya hak'ura zuciyarsa cike da niyyan barin wajen,har ya juya zai bar gurin idanunsa suka sauka kan tuntsirarrun cup's en,saurin waigowa yayi cikin azama ya suri guda d'aya yana juya shi a hannunsa,haka nan yake jin sam bai yarda da zaman cup's enba,ya jima yana nazari da jujjuya shi kafin ya ajiye,yana dafa table en da hannayensa biyu,d'an ruwan da yaji ya tab'a a dai² gurin daya ajiye hannunsa na dama yasa shi d'ago hannun kana ya shiga yarfewa,seat yaja ya zauna had'e da yin baya yana shafa fuskarsa da hannunsa,tsamin da yaji ya bugi hancinsa ne yasa shi saurin d'agowa yana sake bin gurin da kallo cike da son gano inda yaji tsamin daya ji ya bugi hancinsa haka nan cikin rud'ewa "Veer...?? Me ya kawo ta nan..?? Mene ne ya had'a mu da ita...??" Yayi furucin yana sake kai hannunsa kan fuskarsa saboda yaji yadda cikin k'ank'anin lokaci gumi ya fara biyo fuskarsa saboda tsananin firgita,wannan karon kam ko daya kai hannunsa dai² saitin hancinsa yana goge gumin daya tsatstsafo masa a gurin,take warin ya addabeshi sama da karon farko daya fara ji,mamaki ne ya matuk'ar kamashi musamman ta yadda akayi yanzun ya fara zargin daga inda warin yake fitowa,not believing ya d'ago hannunsa yana juyawa,kafin daga bisani kuma ya kaishi hancinsa,saurin janyeshi yayi saboda yadda yaji tsamin ya dameshi har yana niyyan yin amai,mamaki ne gami da tsoro ya cikashi,zuciyarsa cike da tsantsar mamaki na yadda akayi ya samo giya a jikinsa ya koma ya zauna dab'as yana sharce gumi. Ga YAZEED kuwa tunda yaga YASEER ya nufi table en a tunaninsa ko abinci zai ci shi yasa bai yi magana ba,jin shirun yayi yawa kuma sam baiji alamun motsin spoon da plate ba sai ya waigo ya d'an kalleshi "Heeyy!! Mr man idan ba abunda kake anan ka taso muyi magana.." Cikin rashin nutsuwa YASEER ya d'ago kansa dake sunkuye yana girgizawa,cikin wani irin murya mai cike da fargaba ya furta "No..! Bro yanzun ba wannan lokacin bane.." A hankali YAZEED en ya mik'e ya zauna sosai ta yadda yana iya hango YASEER dake dinning area "Kace babu wannan lokacin..Sai name kenan..?? Shin kasan ma dalilin da yasa nace haka..?? Ko kuma kasan akan abunda zanyi maka magana ne..??" Kai ya girgiza masa har lokacin baya cikin nutsuwar sa kana ya bud'e baki da k'yar ya furta "Noo!! Bro...!" Cike da rashin fahimta YAZEED ya kalleshi "Baka sani ba amma kayi saurin dakatar dani..??" "A'a bro..! Kada kayi saurin yanke hukunci mana,ka fahimci dalilina nima,kasan dai ai bazan fad'i haka ba dan kawai na b'ata maka rai..." "Shi kenan ya isa haka kawai mubar maganar na fasa..!" "Haba mana ka fahimceni shin kasan me yasa nace maka haka ne nima?? Ko kuwa kana tunanin akan matsalar da muka fuskanta kafin mu fita...?? Ba tare daya kalli inda yake ba kawai ya d'aga masa hannu alamun ya k'yale shi haka nan baya buk'atar jin abunda zai fad'a,yadda yayi masa yasa shi jin haushi,cikin wani irin yanayi ya mik'e a gurin,duk jikin YASEER en yayi sanyi zuwa lokacin saboda samuwar giya a gurinsu ya gama firgita shi,muddin kuma wani ya sani har zancen ya koma kunnen maimartaba ko GALADIMA to tabbas yasan baza suji da dad'i ba,wannan abun duk shi ne yafi komai bashi ciwon kai,cike da takaici ya suri cup guda a gurin sannan ya dumfari inda YAZEED en yake kwance saman cuition,da zuwansa ba tare da yayi magana ba ya shiga mik'a masa empty cup en,kallon rashin fahimta YAZEED ya bishi da shi kafin yayi magana "Me zanyi da shi da kake bani..??" "Ka karb'a dai zaka san me zaka yi da shi later..." "Ka maida shi inda ka d'auka kawai ni ban ce maka zanyi amfani da shi ba.." "Ka dai karb'a en zaifi..." "Dan Allah YASEER ka kyaleni haka nan naji da abunda ke damuna,me yasa wai wani lokacin kake son takurani ne..?? Nace maka bana so amma kak'i yarda,shin idan na karb'a nayi me da shi ne kam..??" Murmushin takaici YASEER ya saki before ya d'aga masa gira d'aya yana cewa "Karb'a ka shanshana cikinsa zaka fahimci abunda nake nufi.." Kallon rashin fahimta yaci gaba da binsa da shi,kafin ya amsa cup en yana kaishi dai² hancinsa yana sunsunawa kamar yadda YASEER en yayi masa izinin yi,mugun tsamin daya daki hancinsa ne yasa shi saurin cilli da cup en gefe cike da masifa ya furta "Meye ne wannan en ka bani...?? Me yasa kasan ko mene ne zaka bani kace na duba maka...??? Me hakan yake nufi..???" "Calm down Mr man..!" "Ank'i ayi down en,me yasa zaka sani duba abunda bai dangance ni ba..?? Wato ka fara shaye² shi ne nima kake so na fara ko..?? Haba YASEER me yasa zaka yi haka,da can baka sha ba sai yanzun da kake cikin hankalinka,me kake so iyayen mu suce daga lokacin da suka sani..??" Shiru YASEER en yayi masa yana binsa da kallon mamaki,koda yaga YASEER ya kasa tanka shi,shi kuma YAZEED en nan yaci gaba da magana cikin d'aga harshe sai ruwan bala'i yake zazzagawa YASEER en,cike da jin haushin gurum en daya masa ya furta "Wannan ba dai² bane,kuma sam baka kamanci ta'ammali da kwayoyi ba,amma dan Allah rok'ona da kai d'aya shi kad'ai nake son kayi min alk'awari baza ka sake aikata makamancin wannan kuskuren ba,kasan bazan tab'a iya jura ba na ganka cikin damuwa,shin me kake tunani idan wani abu ya sameka..su waye zasu yi asarar rashin ka..?" "Haba mana Malam taya zaka yi tunanin ni zanyi ta'ammali da k'wayoyi,kamar ni na aikata haka bayan ina cikin nutsuwata..?? How comes..?? Kai kanka kasan abune da bazai tab'a faruwa ba na aikata wannan kuskuren..." Yadda YASEER yayi maganar cikin jin zafin abunda YAZEED en ya fad'a yasa nan da nan temperature en YAZEED sake hawa cike da masifa ya kalli YASEER en yana sake fad'in "To idan baka fara shaye² ba taya akayi muka samu veer a nan..?? Waye ne ya kawota idan ba kana sha ba..??" Cikin jin haushin maganar YAZEED ya sake kallon shi yana fad'in "Nake sha ko kuma muke sha..??" Wani kallo YAZEED ya bishi da shi kafin ya tambaya "Ka ce mene...??" "Abunda dai kunnanka yaji shina fad'a...Idan har zaka yi zargina akan abunda baka da iliminsa what about you..?? Ko kuwa shin kai baka san tare muka sha ba sai yanzun da nake fad'a maka..??" Tsawa YAZEED ya bugawa YASEER cikin k'araji kamar zai dake shi ya furta "Don't rehearses these drastic to me...Ko da wasa..! I warned u..!" Yayi magannar yana karkad'awa YASEER yatsa cike da fushi,dariyar yake mai cike da rainin hankali YASEER yayi wacce ake cewa tafi kuka ciwo kafin ya kalli YAZEED from head to toe ya jinjina kai "Kana d'auka da d'in da wasa nayi maka ne?? Ko kuwa tunanin ka na fara samun matsala a cikin k'wak'walwata da har wani banzan tunani zai sani ta'ammali da wine..?? Idan baka sani ba bari na fayyace maka abunda nake zargin faru duk da bani da tabbas,nd kai kanka yana da kyau ka maida tunanin ka baya kad'an,daga lokacin da muka fito da shirin fita,zuwa dawowar mu,shin zaka iya tuna wani abu da muka yi before these time around...??" Shiru YAZEED yayi yana bin YASEER da kallon rashin fahimta,koda YASEER en ya fahimci irin kallon da yake masa sai kawai ya jinjina masa kai dan yadda yaga yayi ya tabbatar masa babu abunda zai iya tunawa "Ba shiru za kayi ba,amsa nake buk'atan ka bani da kanka.." "Bazan iya tunawa ba..Kawai dai kamin bayanin abunda kake nufi.." Jinjina kai YASEER yayi sannan ya nemi guri ya zauna yana sakin ajiyar zuciya "Idan har baka manta ba,daga kan lokacin da Ummi ta kiramu zuwa time en da muka fito cikin parlour'n nan zamu yi dinner,idan har zaka iya tuna wani abu daya faru da kai har ya janyo mana yin mugun baccin daya kusa janyo mana fushin maimartaba da har yasa bamu samu damar halartar taron da wuriba,shin kayi tunani akan wannan..?? Ko kuwa anan baka yi zargin wani abu ya faru damu a wannan lokacin ba...???" Shiru YAZEED yayi yana kallon parlour'n zuciyarsa cike da son tuna wani abu da zai iya bada shaida akan tambayoyin da YASEER en ya jefe shi dasu,sun d'auki tsawon wasu y'an mintuna shiru,YAZEED kuwa sai k'ok'arin tunawa yake amma sam hakan ya gagara,cike da damuwa ya kalli YASEER yana girgiza masa kai "Brohh!! Na kasa tuna komai..Ni sam ma bana tunanin wani abu ya faru makamancin haka.." "Tabbas ya faru kuma ni na tabbatar.." "Ta yaya kenan kake tunanin hakan..??" Ba tare daya kalleshi ba ya shiga koro masa jawabi tun daga fitowarsu bayan amsa kiran Ummi kafin susha drinks en,har zuwa sanda suka sha lemon,da abunda ya faru da su bayan sun sha na daga mugun baccin da sukayi,nan ya ci gaba da fad'in "Daga kan wannan bana tunanin na san kuma meya sake faruwa,da yadda akayi muka dawo hayyacinmu..amma dole ne ka yarda duk abunda na fad'a ya faru.." "Tabbas...! Ya faru..kuma nima na tabbatar yanzun,sai dai abun mamakin anan shi ne ya akayi giya yazo mana nan..?? Nd waye ne ya kawo mana muka sha..??" Shiru dukansu suka sake yi,zuwa wani lokaci YAZEED ya kalli YASEER ransa a mugun b'ace "Waye ne aka sa ya shirya abinci yau.??" A bazata tambayar ta zowa YASEER saboda shi sam hankalinsa bai kai kan tunanin wanda ya shirya abinci ba,ko da jin abunda yariman ya fad'a take yasa YASEER girgiza kai alamun dake nuni da lallai ne shima bai sani ba,nd duk wanda ya shirya musu abincin ko tantama babu shi ne abun zarginsu,shi ne kuma mutumin daya shayar dasu giya,ba tare daya samu damar bawa YAZEED amsa ba ya d'auka phone had'e da soma neman line Ummi,cikin abunda bai wuce minti biyu ba tayi picking,ba tare daya tsaya wani dogon sharhin ba ya fara tambayarta "Ummi waye ne kika sa ya had'a mana dinner...??" Sai da tayi murmushi kafin ta furta "Haba YASEER kaima ai kasan duk fadin ginan,haka duk adadin masu hidiman gidan nan,da mutum d'aya kawai na aminta ta had'a muku abinci bayan ni kaina,ita ce dai wacce ka sani tun kafin tafiyarku ban sauya wata ba...." Mamaki ne ya cika shi dan kuwa take ya fahimci kowa Ummi'n take nufi,sai dai abun tambayar anan idan har ita ta had'a abincin ya akayi haka ta faru...?? Tabbas a iya sanin daya mata ya jima da saninta haka nan abunda zata iya aikatawa da wanda ma bazata yu,ya riga da ya jima da sanin babu yadda za'ayi ta aikata haka,gefen Ummi kuwa jin yadda yayi shiru daga tambayar bai sake cewa komai ba kuma bai ajiye wayyan ba yasa Ummi'n cewa "Akwai wani matsala daya faru ne..? Naji kayi shiru..." Saurin danne damuwar da yake ciki yayi sannan ya k'irk'iro murmushi da cewa "Noo!! Ummi shi kenanma kawai..." Yana niyyan kashe wayan Ummi'n ta sake dakatar dashi da maganar da take yi "YASEER ya akayi yau kuka k'i zuwa wajen taron nan ne...!? Shin kun kuwa san yadda kuka b'atawa iyayen ku rai...??" "Afuwaan Ummi,mun makara ne sakamakon uzuri daya gifta mana,amma munje gurin bamu jima da dawowa bama..." "Shi kenan to Allah kiyaye gaba,amma dai ya kamata ku gyara ko dan gaba,ko da ace ba iyayen ku ba wasu a waje suka gayya ce ku to yana da kyau ku halarta da wuri ba don komai ba sai dan cika alk'awari da kuma mutunta lokaci..." "In sha Allah Ummi zamu kiyaye..." Daga haka suka ajiye wayan,ga YASEER ko bayan da suka gama wayan damuwar daya b'oye ce ta dawo kan fuskarsa,nan take zuciyar sa ta shiga kaikawo akan wacce Ummi tace ta shirya musu abincin "Shin me hakan yake nufi..??" Yayiwa kansa tambayar ba tare da sa ran yana da amsar taba,ga YAZEED kuwa koda yaga YASEER yayi masa shiru bai ce komai ba,sai kawai ya kalleshi cike da son yin magana "Me kacema da Ummi ne..??" Sai lokacin YASEER ya kalleshi cike da rashin k'warin guiwa ya furta "Na tambaya ne waye tasa ya shirya mana abinci.." "Eheenn! Waye tace..??" *"JEEDDAH.....! "* Wani kallo YAZEED en ya masa,haka nan yanayin sama da yadda jikinsa ya koma tamkar wanda bai tab'a jin sunan ba sai yau,cike da mamaki ya ce da YASEER "Ka kuwa ji abunda ka fad'a..??" "K'warai nasan me nace,kamar yadda kaji haka nima naji,sai dai gaskiya zuciyata tana bani wani abu daban bayan wannan,na tabbata jeeddah ba zata tab'a aikata haka garemu ba..there must be something hidden da muka kasa fahimta..." "Kana nufin baka yarda ba kome..??" YAZEED yayi masa tambayar,cike da k'warin guiwa YASEER ya girgiza masa kai "K'warai ban amince ba,kuma babu ta yadda za'ayi na amince da zata aikata haka,tilas ne akwai wani da yake bibiyar sahunta damu baki d'aya.." Kallon mamaki YAZEED yayi masa kafin ya mik'e ya bar YASEER a wajen da sunan yana zuwa,bayan barinsa a gurin,tunani ne iri² YASEER en ya dunga yi,daga wannan ya koma wannan,haka nan gaba d'aya ya hana kansa sukuni,k'ofar shigowa parlour'n nasu ya tsaya kawai ya zubawa ido tamkar wanda ke neman amsan duka tambayoyinsa a jikinta,picture en inuwar daya gani a baya ne ya dawo masa,a hankali yaci gaba da takura kansa da son binciko shin da gaske ne kuwa abunda yake zargin ya faru,yana daf da tunawa YAZEED ya dawo yana tambayarsa "Broh! Wai wace jeeddah kake nufi nema..??" 'Dagowa YASEER yayi yana sakin gwauron numfashi kafin ya bashi amsa "Wacce dai ka sani ta asalin ita nake nufi..??" Mamaki ne ya sake bayyana akan fuskar YAZEED kafin yayi magana "Kana nufin wai dama tana cikin gidan nan..kuma duk tsayin wannan lokacin tana tare damu amma ban sani ba..??" Da kai ya iya amsa masa ba tare da yayi magana ba,tsantsar mamaki ne ya sake bayyana a fuskarsa a fili ya furta "Babu yadda za'ayi wacce tayi sadaukarwa akaina a wancan lokacin ta iya aikata wannan kuskuren..!" 'Dagowa YASEER yayi ya d'an kalleshi yana jinjina kai "Ni kaina zargin da nake yi kenan,sai dai kuma idan har ba ita bace to waye ne mai wannan d'anyen aikin...??" Shirun da suka sake yi shiya bawa yarima YAZEED damar yin tunanin wani abu,yadda yake squeezing face kamar wanda yaga wani abu da baya so duk kuma cikin salon son ya tuna en,da sauri ya kalli YASEER yana fad'in "Noo!! Broh...! Tabbas kayi gaskiya akwai wani da ban daya aikata wannan kuskuren.. Shin me zaisa ta aikata haka gare mu..?? Sannan me zaisa itama wannan d'aya yarinyar ta taimaka mana lokacin da muke cikin tsaka mai wuya..? Kenan kaga bama ita kad'ai ke k'ok'arin bamu kariya ba akwai wata daban..!" Yadda YASEER ya k'ure shi da kallo har ya gama fad'ar abunda zai fad'a yasa shi jinjina masa kai alamun tabbaci,murmushi YASEER ya saki sannan ya furta *"ITA KAD'AI CE.....babu wani ko wata..Jeeddan dai itace a wannan karonma.............!" Tsantsar mamaki YAZEED ya shiga ba don komai ba sai dan jin maganar data fito daga bakin YASEER,zuciyarsa cike da son sake gasgata abunda yaji ya furta "Ita kad'ai fa kace...Kana nufin yanzunma ita jeeddan ce tayi wannan k'ok'arin akanmu..??"+ "K'warai kuwa itance dai,babu wata a bayanta kuma babu taimakawar wani..." Shiru yayi ba tare daya sake cewa komai ba,yanayin shirun da yayi yasa shi lulawa cikin duniyar tunani,nan take kuwa wasu daga cikin abubuwan da suka faru a d'azun kuma tsakanin su suka shiga fara gilma masa a cikin idanunsa,a hanakali picture en abunda ya faru a d'azun ya shiga dawo masa cikin idanunsa da k'wak'walwarsa,duk da a lokacin baya cikin hayyacinsa amma tsaf a dai² wannan lokacin a shirye yake daya takura kansa badon komai ba sai dan ganin ya tuna en,sai tunaninsa yayi nisa yana shirin tuna wani abu sai abu ya nemi gagararsa,sam ya kasa kai kansa inda yake da buk'atar zuwa,abunda kad'ai yake iya tunawa har yanzun shi ne sanda ya fara dawowa cikin nutsuwarsa,tabbas ya ganta fuska da fuska sai dai a hakan daya ganta akwai nik'ab a nata fuskar daya hana shi ganinta gaba d'aya,hakan tasa bazai iya tuna kamanninta ba,abunda dai kawai ya sani itan bak'ace nd bak'i kuma bana wasa ba,haka zalika yanayinta ba wata Babba bace ko a shekaruma,cikin zuciyar sa yake ta mamakinta da yiwa kansa tambayar "Shin taya za'ayi mai k'arancin shekaru kamar nata ta iya yin tunani makamancin haka...??" Bai wani sha wahala na neman wanda zai bashi amsa ba,d'ayar zuciyar tasa ta bashi amsa da "Wannan ai ba wani abu bane kasan ko wane bawa da yake rayuwa ai yana da tasa kalar baiwar,ba duka halittun Allah suke dai² ba,kowa da akwai ta inda ya sab'a da d'an uwansa,koda kuwa hakan na nufin tare kuka zo duniyar,lallai ne sai an samu wani abu da kuka yi sab'ani da juna akansa...!" Jinjina kai yayi cike da gasgata maganar da zuciyar tasa ta fad'a masa,haka nan tunawa da wannan maganar tasa shi tunowa da wani abu daya faru tsakanin sa da ita a d'azun sanda take shirin fita daya biyota yana son tambayarta,tun kafin ya kai ga yi mata magana sai kawai yaga ta zabura ta fice kamar wacce akace idan ta sake ya k'araso zai mata wani abu,yadda ta fita a cikin parlourn nasu a d'azun kafin su tafi gurin dinner da gudu shi ne abu mafi dad'i a gurinsa da tunawarsa tasa har ya ita sakin murmushi duk da a lokacin da abun ya faru ta b'ata masa rai,amma a yanzun bayan sanin wani abu daya faru sai yaji duk ya dena jin haushin duk da bawai dama jin haushin nata ya d'ora ba,cike da wani irin k'warin guiwa ya juyo ya kalli YASEER ya fara yi masa magana "Amma broh..! Mene ne dalilin yarinyar nan na guduwa a d'azun ne...?? Naga ko kad'an bata tsaya ba kuma nasan tana jin irin kiran da nayi mata.." "Bazata tab'a tsayawa ba.." Da mamaki a fuskarsa ya kalleshi yana maimaita abunda ya fad'a sannan ya d'ora da fad'in "Me yasa kace haka..?? Itan ba khadimar mahaifina bace..?? Ko kuwa bani da damar dakatar da ita idan ina buk'atar hakan..??" "Ko kadan ba yadda kake zato bane,na tabbata tayi haka ne saboda bata son wani abu ya shiga tsakani,nd musamman duba da irin abunda ya faru,tabbas zata yi tunanin ko zamu zargeta da aikata wannan kuskuren ne,na rigaka sanin wace ce itan shi yasa na fad'a maka haka,amma bawai dan ina son kareta ba kamar yadda tayi akanka ba,ni na sani babu yadda za'ayi ta tsaya coz ban taba ganinta tsaye da wani ba ko da acikin hadiman gidan nan,sannan kuma idan kayi duba da yanayinka kai kanka lokacin daka tunkareta dole ne yasa ta kasa nutsuwa dan bata san me zai faru ba idan ka kusanceta,dan haka kawai ka d'auka hakan ya faru ne bisa kuskure..." Shiru yarima yayi yana juya maganar a ransa,shi kuma YASEER bayan ya gama karanta masa abunda ya sani game da itan yaci gaba da sabgoginsa.Waiwayowar YASEER inda yarima YAZEED en yake jin yayi shiru,yayi dai² da k'arar shigowar text message a wayar YASEER en,murmushi yayi kafin ya shiga k'ok'arin duba inda sak'on ya fito kasancewar a time en babu damuwar komai a ransa,koda ya bud'e duk iya adadin yadda fuskarsa ta kai ga sakewa take cikin abunda baifi y'an dak'ik'u ba annurin fuskarsa ya disashe,haka nan tun bai kai ga gama karanta sak'on ba tuni har ya mik'e tsaye yana tsuke fuskar sa mai cike da rashin nutsuwa.A hankali ya shiga sake bibiyar sak'on cikin rashin nutsuwa _"Shin kuna tunanin ku wasu masu wayo ne...Ko kuna tsammanin duk wani shirin mu akanku zaku iya dakatar da shi..?? Mun d'aga muku k'afa ne kawai ba don mun gaza ba,sai don rabuwa daku na wani lokaci..Wannan lokacin mun shirya tsaf domin k'addamar da duk wani shirinmu akanku ba tare da saurarawa ba,tabbas a yau kun tsallake troop na farko a sanadiyyar taimakon da kuka samu daga wannan yarinyar,sai dai a wannan karon shirin mu dole ne yayi tasiri akanku,ba kuma iya ku kad'ai ba,hatta da ita kanta tunda tayi k'ok'arin shiga abunda babu ruwanta sai fushinmu ya sauka akanta......!"_ 'Daure masa kai sak'on yayi sam ya gaza fahimtar komai,a hankali kuma kamar mai tunanin wani abu ya juya ya kalli YAZEED dake zaune ya zuba masa ido,saurin juyawa yayi dan baya son ko kad'an ace ya fahimci halin da yake ciki,yasan gaba d'aya had'uwa za suyi cikin damuwa,shi kuma hakan ne baya so ya faru,yafi son ace shi kad'ai yake fuskantar duk wata damuwa da zata b'illo musu.Wani tunani ne ya fad'o masa nan take ya juya da sauri yayi yana tafiya,saurin kallonsa YAZEED ya sake yana girgiza kai kafin yayi masa magana "Ina kuma zaka da kake k'ok'arin fita a wannan lokacin..??" Ba tare daya waigo ba kasancewar yasan halin YAZEED da saurin b'aro jirgin mutum,duk yanda ka kai da b'oye damuwa matuk'ar ya kalleka yanzun zai iya fahimtar halin da kake ciki,yasa shima yak'i yarda su had'a ido,yana a yadda yake ya shiga bashi amsa still kuma yana ci gaba tafiya "Yanzun zan dawo zanje gefen Ummi ne.." Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya d'ago ya kalla,ba tare da damuwa ba ya furta "By this time around zaka je gefen Ummi'n..?? Kayi mene a can a irin wannan lokacin da ka riga kasan a rufe yake..??" Saurin d'ago hannunsa shima yayi ya kalla sam baiyi tunanin lokaci ya tafi har haka ba shi yasa yaso shashantar da damuwarsa a nan idan ya fita,sai dai kuma kash lokaci ya masa tsiya,nd yana da tabbacin matuk'ar ya koma kusa da YAZEED yanzun tabbas ne saiya fahimci halin da yake ciki,d'an dakatawa yayi a inda yake yana tunanin abunda ya kamata yayi,ko kafin ya kaiga juyawa tuni YAZEED en ya cillo masa tambayar da tasa shi yunk'urin barin wajen babu shiri "Kana cikin damuwa...Amma saboda ka koyo zurfin ciki shi yasa bazaka iya fad'awa kowa ba,mene kake tunani da zaisa ka b'oye min..!?" Ba tare daya kalli inda yake ba shi enma ya bashi amsa "A'a malam ni ban fad'a maka ina da damuwa ba,shi kenan mutum bashi da damar yin wahami akan abu sai yasa ka zargin ko ina b'oye maka wani abu ne.." Murmushi YAZEED yayi mai sauti kafin ya furta "Ka rainawa wanda bai sanka ba hankali..amma ni kam ka san ko me zaka fad'a ba yarda zanba.." Shiru YASEER yayi dan baya so maganar tayi nisa,matuk'ar kuwa zai ci gaba da fad'a shima yana yi tofa dole ne sai YAZEED ya rafko shi,dan haka kawai sai yaja bakinsa ya tsuke ba tare daya sake tankawa ba,haka shima YAZEED ko da yaga YASEER en yayi haka k'arshe ma ya juya ya bar wajen kawai sai ya girgiza kai had'e da d'an d'aga murya,cikin sautin da yasan YASEER en zai jishi ya furta "Shi dai duk mutumin dake zama cikin damuwa Allah yaso ya san makomar yin hakan...Ni kuma bazan gaji ba da tambaya sai dai in mutum yak'i fad'a saboda tunanin an takura masa,hakama addu'ar neman shiriya ba fasawa za muyi ba.." Yana jinsa yasan da shi yake,ko da jin haka sai ya girgiza kai kawai had'e da sakin murmushi ya shige ciki abunsa. ^^^^^ A can b'angaren Jeeddah kuwa,tun daga sanda ta zauna tasa kukan nan,ta jima tana aikin abu d'aya cikin kuka ta shiga addu'ah,sai da tayi kirari ga ubangiji sannan taci gaba da addu'ah "Ya Allah ka taimakeni ka fidda ni a cikin wanna damuwar...Na tabbata a yau matuk'ar aka san abunda ya faru babu wanda zai yarda da bani da laifi..Ya Allah ga baiwarka tana neman agajinka,Allah ka tallafi rayuwata ka kawomin mafita cikin sauk'i...!" Ire²n addu'o'in da tayi ta yi kenan,haka addu'o'in da ta dinga yi har ita kanta bata san adadinsu ba,kuma ko ta fara bata kaiwa k'arshe take datsewa take kama wata,saurin mik'ewa tayi tana share hawayen fuskarta had'e da yin murmushi mai cike da godiya ga Allah,da sauri ta bar wajen ta nufi hanyan kitchen en dake cikin apartment en saboda wani tunani daya fad'o mata,dube² ta shiga yi zuciyar ta cike da fatan samun abunda take da burin gani a wajen,cikin sa'a kuwa tana bud'e freezer en idanunta suka sauka kan tarin lemon tsamin,hamdala tayi ga Allah kafin ta juya ta d'auka wani cup mai kyau ta shiga aikin yankawa da matse ruwan a ciki,sai data tara ruwan da d'an yawa,haka nan iya yadda take tunanin zai kai mata adadin da take nema kafin ta bari tana sake goge fuskarta da har lokacin gumi bai daina tsatstsafowa a jikinta ba,haka nan duka jikinta har lokacin bai bar b'arin da yake ba,a haka ta dawo cikin parlour'n tana haskawa da y'ar wayarta da kullum take mak'ale da ita,sanda ta iso gurin da suke saboda rashin tantance abun yi sai kawai ta tsaya tana raba idanu dan saboda rashin sanin ta yadda za'ayi ta aiwatar da abunda zuciyarta ke sak'a mata,ko da ganin tana dad'a b'ata lokaci a haka tuni wata zuciyar ta shiga bata shawara kan abunda yafi dacewa tayi,nan kuwa ta nemi guri ta ajiye cup en sannan ta matsa kusa da YASEER ta shiga masa magana,ta d'auki lokaci tana kiransa kafin ya iya amsawa,cikin tausasa murya ta furta "Babban yaya ga ruwan ka sha..." Murya na rawa tayi maganar "Bazan sha ba..ko na ce miki ki kawo min ne..??" Yadda yayi maganar cike da gadara,yasa ta yin Jim ba tare da tayi magana ba saboda tsabar fargaba,haka nan sam bata yi zaton hakan zai iya faruwa ba,duk a tunanin ta da tace masa gashi zaiyi obeying nata cikin sanyi ba tare data sha wahala ba amma kuma ga mamakinta saita ga sab'anin abunda tayi zato,har tayi niyyan rabuwa da su tayi tafiyar ta saboda maganar sam bata ji dad'in taba,sai dai ko data tuna cewar duk wanda yazo ya gansu a haka dole ne itace zata kasance mutum ta farko da za'a fara zargi,k'arshe kuma bata san mene ne zai faru da rayuwarta da ita kanta ba ta sanadin wannan kuskuren da take shirin yi,wannan tunani shi yayi tasiri akanta har taji dole ne akanta ta fasa tafiya,haka nan tana jin idan har ba tayi nasara ba na ceton su daga wannan mugun yanayin ba bazata iya tafiya ko nan da can ba,saurin katse tunanin ta tayi sannan ta ci gaba da lallab'a shi,a haka tun yana turjewa tana bashi hak'uri yana gayan magana son ransa,itanma a nata gefen tun tana jin haushin maganganun har ta dawo kuma abun ya daina b'ata mata,da k'yar ta samu ya karb'a ya kafa kai zai sha,ko da ruwan ya shiga bakinsa nan yayi yunk'urin dawo da shi,ai koda ganin haka da jeeddah tayi bata san sanda ta rik'e hannunsa ba tana bashi hak'uri akan ya sha,wata uwar harara ya galla mata cikin maye mai d'auke da b'acin rai ya kalleta "Ke...! wannan ne ruwa.??" "Ehh! Babban Yaya ruwan lemon ba,ai kai kace na kawo maka kana son sa a haka.." K'wafa yayi jin abunda tace,sannan ya maida kansa yaci gaba da sha badon komai ba sai don kawai tace shi ne yace ta kawo masa,yana zuwa geji ya ajiye mata cup en ba tare daya mata magana ba ya koma ya sake kwanciya,hamdala ta yiwa Allah fuskar ta cike da fara'a mai cike da fara samun sukuni ta masa godiya shima sannan ta mik'e ta bar wajen,wani ruwan lemon ta koma ta sake tarawa saboda kaf na ciki YASEER ya shanye,sannan ta dawo kan YAZEED en shima,rikicin da suka yi da shi har sai da yaso ya wuce na wanda suka yi da YASEER,sun jima suna tak'addama da juna saboda tsabar k'afewa da yayi kafin da k'yar ta samu ta sha kansa ya yarda ya karb'a ya sha,yana gama sha ta mik'e a gurin ta bar su,zuciyarta cike da murna ta shiga tattare duk wani abu kama daga cikin parlour'n har zuwa kitchen da tayi amfani da shi dama wanda suka yi ta tsaftacesu a nan,duk bayan mintuna tna aikin sai ta dawo ta duba su,ba don komai ba sai duk dan kada a samu matsala,sun d'an jima a cikin yanayin kafin mayen ya fara sakin su,sanda ta dawo da niyyar sake dubawa a karo na k'arshe,tana kawo jiki zata fito daga ciki ta hangi wutan parlour'n a kunne,a d'ari da tamanin ta fito ta shiga dubawa zuciyar ta da fargabar Allah yasa ba wani ya shigo gurin ba,sanda ta gama fitowa ne ta iske YASEER zaune saman cuition ya b'alle duka botiran rigarsa saboda yadda ya had'a zufa,haka nan idanunsa a runtse ya jingina bayansa da seat en,koda taga haka a zatonta wani abune ya sake faruwa dan yadda ta tarar da shi,a hankali ta lallab'a ta fito har sanda ta kusa zuwa daf da shi sannan ta dakata tana kiran sunansa cikin k'asa da murya,a hankali ya shiga k'ok'arin bud'e idanunsa da suka masa nauyi har sanda ya gama ware jajaye lumsassun idanun a kanta ya kafeta da su,ganin irin kallon da yake mata yasa ta yin baya kad'an had'e da tambayarsa "Babban Yaya akwai abunda kake buk'ata a kawo maka ne..??" Ci gaba yayi da kallonta har saida ta sake maimaitawa sannan ne ya iya d'aga mata kai da fad'in "Bani ruwa na sha...!" Amsawa tayi cike da k'warin guiwan samun nasara,sannan ta tafi don kawo masa ruwan kamar yadda ya buk'ata,wannan karon ma kam koda ta d'ebo ruwan bata yarda ta kawo masa shi a haka ba,saboda tuna cewar zak'i na tafiyar da maye,shi yasa tayi k'ok'arin duba zuma ganin bata samu ba yasa tayi amfani da abunda ta samu kawai ma'ana tasa masa sugar a ciki sannan ta dawo tana mik'a masa ruwan cikin girmamawa,ko daya shanye nan ya neman k'ari itan kuwa nan ta shiga aikin k'ara masa ruwan mai d'auke da sinadarin sugar,gare shi kuwa YASEER tun a karon farko da yasha ruwan d'an test en zak'in da yaji a cikin ruwan shi ne ya jashi har yayita sawa tana k'ara masa,suna nan a wannan halin YAZEED en shima ya soma dawowa dai²,kwatankwacin yadda suka yi da YASEER haka ce tayita faruwa tsakaninta da YAZEED en har Allah ya taimaketa suka d'an sauka daga halin mayem da suka tsunduma,ko data tabbatar a lokacin sun gama saituwa nan tayi musu sallama tana bin hanyar ficewa da niyyan tafiya inda zai fishsheta tunda dai burinta ta cika a lokacin,dai² tana daf da fita YAZEED ya mata magana,tsayawa tayi a dai² inda take kana ta juyo tana kallonsa sai k'ifta idanu take,cikin rashin wadataccen kuzari ya taso ya shiga nufo ta,yadda taga yana yi ne da irin mugun kallon k'urillar da yake mata ya kasa bata nutsuwa,take ta hau ja da baya saboda rashin takamaiman abunda zaije ya dawo,biyota yaci gaba dayi har sai da suka kusa danganawa da k'ofa koda taga idan sun kai nan babu kuma sauran gurin da zata nufa ai take ta faki idonsa cikin sauri ta bud'e k'ofar ta fice a guje. Koda ganin fitarta haka nan kawai sai yayi murmushin da bai san dalili ba,seconni a tsakani kuma ya tsuke fuska yana tambayar kansa "Shin me nake yiwa dariya ne..??" Rashin amsa yasa shi d'age shoulders sannan ya koma ya zauna yana sakin jikin nan nasa mai kamar an nad'a masa na jaki,cike da jin haushin abunda ta aikata masa. Ita kuwa jeeddah lokacin data samu ta gudu bayan fitarta a cikin apartment en nasu bata iya biyawa ta gefen uwar gijiyar tata ba dan a lokacin koda ace taje tofa bata da takamaiman amsan da zata iya bata idan har ta tambayeta game da labarin abunda ya faru tayi irin wannan jimawar daga aike,haka nan idan ace tak'i zuwa shima kuma bata san me zai faru ba idan suka had'u goben,wani tunanin ne ya sake dawo mata a ranta nan take ta shiga taradaddin wanda ya kamata ta d'auka cikin biyu,shin taje gurin Ummi'n ta sanar da ita gaskiyar abunda ya wakana ko kuwa ta wuce ta tafi ba tare data je ba idan yaso duk sanda suka had'u ta shirya mata k'arya..............???^^^^^^^^ Shawaran tafiya gida kawai ta yanke dan tana jin kaf fad'in duniyar babu da wanda zata iya yin wannan maganar,hatta kuwa da Ummi'n Yaseer en,haka nan take ji aranta ba iya Ummi kad'ai ba koda ma ace Inno'n ta ce bazata tab'a fad'a mata ba,duk iya adadin yadda za'a takurata babu yadda za'ayi ta iya fidda wannan sirrin,haka nan koda ace gobe matuk'ar taje kawai zata san abunda duk ta hanyar daya dace ta sanar sanar da Ummi abunda ya kamata,da wannan tunanin ta kama hanyarta ta komawa gida taci gaba da tafiya abunta,tana daf da isa gida ta tuna maganar Ummi akan zuwa taron da tace mata tana son ta halarta,duk da bawai itan har ranta take jin sha'awar zuwan ba,haka nan taji har ranta bazata iya k'in zuwan ba,dan tasan matuk'ar tak'i zuwa kuwa tofa kamar bata yiwa uwar gijiyar tata adalci ba,yadda taji har ranta hakanma ya zama kamar dole ne akanta ta halarta ko ba dan komai sai dan amsa gayyata kamar yadda ta amsata,har ta juya zata koma ko me ta tuna kuma ta dawo a hankali ta shiga gida ta sake gyara jikinta sannan ta fice a gidan,ita kad'ai tayi tafiyar dan ko da acema sai lallai da wani zasu je wajen to ita kam bata san da waye ya dace ta tafi ba,har ta isa d'akin taron ta gama duk kalle²n mutane ko Allah zaisa taga wani data sani amma shiru babu fuskar wani mutum d'aya data gani data mata kama dawanda ta sani,tana nan zaune shiru ita d'aya ta hangi Aisha tana shirin giftawa ta kusa da ita,tun kafin ta k'araso da idon jeeddah ya sauka a kanta ta gama ganeta sai dai itan da hankalinta sam bai kai kan jeeddan ba,haka itama kuma koda ta ganta bata mata magana ba,sai dai wani abu guda d'aya daya d'aurewa jeeddah kai,wanda ba komai bane face ganin Aisha a wannan taron,mamakinta da tarin tambayoyin da suka addabi zuciyarta a lokacin baya wuce son sanin alak'ar Aisha da taron,ta jima tana tunani da son gano wace irin alak'a ce ke tsakani amma sam tunaninta ya gaza kai mata kan amsar data dace dan haka kawai saita hak'urewa ranta taci gaba da baza ido,duka da zuwanta baifi minti goma ba suma su YASEER suka k'araso,ko da ta samu tabbacin akan halartar su taron ba tare data b'ata lokaci ba ta bar gurin ta kama hanyarta ta komawa gida zuciyarta wasai cike da farin ciki marar misaltuwa babban gurinta kenan dama taga sun isa gurin kuma gurinta ya cika,tun tana hanya take jin yadda wayanta ke vibrate amma ko kad'an tak'i kulawa har sanda ta isa bakin gidan sarautar ta sauka,ko bayan ta sallami mai napep ci gaba da tafiya tayi da k'afarta a haka ta isa cikin gidan tana tafe zuciya cike da nishad'i. Koda ta shiga gida ta gama duk wasu uzurorinta da duk lokacin data b'ata,har lokaci. Inno bata dawo daga cikin gida ba,d'an k'aramin agogon dake mak'ale a cikin d'akin ta kalla nan take idanunta suka hasko mata nine minutes to ten,shiru tayi tana tunani dan tunda suke aiki gidan,daya kasance ba can suke kwana ba yasa basa kaiwa irin wannan lokacin basu dawo ba,amma yau ganin irin wannan shirun yasa hankalinta sam ya gaza kwanciya duk da k'ok'arin da take yi na ganin hakan ya faru,harta cire kayanta zata kwanta taji hakan bai mata ba,a hankali ta tashi ta maida kayan sannan ta fice ta kama hanyan cikin gida,hanyan shiru babu mutane sosai tana tafe tana tunanin mene ne yasa Inno yau tayi Lattin dawowa haka..Gashi dare sai dad'a jaa yake..? Dai² tana daf da fitowa daga wani line dake gaban nasu,kawai taga mutum ya tsaya a gabanta,mamaki ne ya kamata ko da taga haka sai dai bata kuka shi ba tayi niyyar canja hanya,a hankali tayi k'ok'arin matsawa zata bi ta gefe,amma nan enma sai taga ya biyo ta yayi blocking hanyan,kallonsa tayi tun daga sama har k'asa ta d'an saki dariya,kafin ta sake chanja hanya zata wuce,ga mamakinta nan enma sao gani tayi ya sake biyota,still tayi kawai a gurin tana nad'e hannayenta a k'irji gami da zubawa mutumin dake tsaye idanu,ta d'an b'ata a k'alla mintuna biyu tana nazarin sa kafin ta girgiza kai tana sakin murmushi,cikin muryar ta mai sanyi ta furta "Yi hak'uri malam ka bani hanya na wuce,ina da abunda yafi min wannan tsayuwar muhimmanci.." A maimakon taga ya matsa ya bata hanya kamar yadda tayi magana,sai taga ya ci gaba da tsaiwa yana kallonta,sake kallonsa tayi tun daga sama har k'asa,yadda ya rawane fuskarsa kamar wani buzu ko irin mutanen agadaz ennan yasa ta fara tunani akansa a hankali ta sauke numfashi tana d'an runtse danunta saboda bata yi zaton ganinsa ba tana fad'in "Babba Yaya..! Kai ne a irin wannan lokacin..??" K'in amsa mata da taji yayi,ta fara zaton ko yayi mata haka ne don yayi surprise nata,amma har lokacin sai taga yak'i yayi magana,jikinta ne ya fara bata a kwai matsala,sake zuba masa ido tayi cikin hikima da nazari ta fara fahimtar wani abu a tattare da mutumin,koda ta gama hakaitowa a ranta game da YASEER ta kuma tsaya tsaki ta kalli wannan sai yasa ta gano BAMBANCIN dake tsakanin su,koda ta gama fahimtar abunda take tunani akai,kawai sai ta juya da baya zata koma tana tafiya cikin sauri ta mik'i hanyar komawa gida,har tayi nisa zuciyarta ta sak'a mata wani abu,take kuwa ta waiwayo a tunaninta zuwa lokacin ta jima da baroshi a can nesa,ko data juyo en dan ganewa idanunta nan ta hange shi biye da ita,tsorata ta fara yi da lamarin mutumin,dan haka ba tare da jiran komai ba take ta k'arawa k'afafunta sauri,koda taga ta kusa da gida kuma tana juyawa taga ya kusa tarar da ita nan take ta take k'afafunta a d'ari da tamanin,ba ita ta tsaya ba sau data dangana da gida,tana shiga soron gidan nasu kuwa ta maida k'ofar ta kulle kana tayi ciki da sauri sai haki take saboda gudun daya sa tayi mai cike da mugun tsoro.Bata iya tsayawa nan a tsakar gida ba sai data danganta da d'aki sannan ta zauna tana maida numfashi,zuciyarta cike da zallar mamakin abunda ya faru yanzun,a fili ta shiga tambayar kanta abunda ya had'a ta da wannan mutum cikin damuwa "Shin waye ne wannan en daya tsorata ta haka kawai..??" Rashin samun wanda zai bata amsa yasa ta hak'ura,ta d'an d'auki lokaci tana maida numfashi sannan daga bisani ta mik'e ta cire kayan jikinta zuciyarta cike da tunanuka iri² ta kwanta,tana nan cikin wannan hali Baba ya dawo kasancewar bai cika zama sosai ba kuma koda yana gari mafi yawan cin lokaci baya dawowa gidan da wuri,da safe kuma kafin ma ace sun tashi tuni za'a iske shi har ya fita,ya jima yana bugun gidan kafin jeeddah ta jiyo ta fito tana nufan hanyar soron,koda ta zo soron kafin ta bud'e saida ta saurar tukun ta tsaya daga baya² saboda bata san da waye zata yi gami ba idan har ta bud'e,k'asa² ta fara tsinkayo muryar Baba yana mitar rufe gidan da akayi tun a wannan lokacin,koda jin haka sai yasa tayi saurin bud'ewa tana masa barka da dawowa kana ta amshi kayan hannunsa tayi ciki,a cikin y'ar rumfa tayi masa shimfid'a ta kawo masa ruwa da abinci sannan ta gaisheshi tana sake masa barka da dawowa,yadda yaji gidan shiru yasa bai ko tambaya ba dan daga dukkan alamu yasan Inno bata nan,ita kuwa jeeddah koda haka ta faru nan ta mik'e tayiwa baba sallama ta shige d'aki ta k'ule can k'uryar d'akin tana ci gaba da sakin ajiyar zuciya na samun nutsuwa,saboda dawowar baba a lokacin ba k'aramin taimako ya bata ba dan ko motsinsa da b'ab'atun radio ensa daya kunna yana sauraron taskar mako kad'ai ma hakan yayi mata dad'i,tana nan kwance tana y'an tunanikanta itama Inno ta dawo,tashi tayi tana niyyar fita daga d'akin,har taje bakin k'ofa ta hango wayarta dake saman y'ar locker enta ta kaya tayi Haske,da kamar zata duba kuma ta fasa,sharewa tayi abunta ta fice kanta tsaye ba tare data kula ba,bayan taje gurin Inno ta mata sannu da dawowa ta sake komawa d'akin,inda ta ajiye wayar ta fara nufa bayan ta d'auka kuma ta koma saman d'an gadon nata ta kwanta tana bud'e wayar,da miss call's ta fara cin karo a fuskar wayar,cikin tsananin mamaki ta shiga dubawa dan tasan babu mai kiranta a wannan wayan,bata gama tunanin da take ba da mamakinta k'arar shigowar sak'o ya ratsa kunnenta,a hankali ta bud'e ta shiga karantawa cikin kwanciyar hankali dan bata san ko na ina baane,irin sak'on da aka turawa YASEER itama shi en aka turo mata,koda ta gama karantawa bata tsaya b'atawa kanta lokaci akansa ba ta maida wayar ta ajiye had'e da mirginawa ta kwanta tana karanta addu'o'in kwanciya bacci zuciyarta babu damuwar komai... ^^^^^ A nasa gefen shima YASEER tunda ya samu ya bar YAZEED zaune a parlour'n,koda ya shiga bedroom soma raba jikinsa da kayan daya sa yaje dinner yayi,daga nan kuma ya fad'a bathroom yayi taking shower,sanda ya fito kayan da yasan zasu bawa gangar jikinsa damar samun wadatacciyar iska ya sanya sannan ya kwanta yana karanta addu'o'in bacci coz a lokacin sam baya son duk wani abu da zai takura shi ko sawa ransa damuwa da zata iya janyo masa kwana da ciwon kai,dai² yana juyawa YAZEED ya shigdad'iima,alamun shigowar sa da yaji yasa shi saurin rufe ido dan a lokacin sam bai shirya yin ko wace irin magana da shiba,ta gefe shima YAZEED en ya kalleshi had'e da tab'e baki dalilin kuwa yasan ko kad'an yasan YASEER ba baccin yake ba a lokacin,haka nan kallo d'aya zaka masa ka fahimci akwai abunda yake b'oyewa,shima har ya gama abunda zaiyi ya kwanta YASEER en yana a yadda yake ba tare da bacci ya d'auke shi ba haka nan kuma idanunsa har lokacin a kulle suke ta yadda babu yadda za'ayi ayi saurin gane hakan... ^^^^^ A b'angaren maimartaba kuwa tun daga lokacin da yasa akayi kiransu amma shiru har zuwa tsawon wucewar wasu sa'o'i basu halarci gurin ba yasa suka fara shirin barin gurin,suna daf da niyyan nasu ne Allah ya kawo su YASEER gurin,wannan yasa koda ganin haka sai suka fasa tafiya har sai da suka jira har zuwa lokacin da aka gabatar dasu a lokacin da suke yin tsokaci game sa irin nasarorin da suka samu a harar karatun su dama rayuwarsu,iya kar abunda suka iya saurarawa kenan saboda wucewa lokaci yasa maimartaba bada umarnin su kama hanyar komawa gida saboda dare ya fara tafiya. Lokacin da suka dawo gida kuwa tun kafin suyi sallama maimartaba ya dakatar sa d'an uwan nasa inda yayi masa tuni game da meeting en k'arshen shekara da zasu gudanar a family'n nasu cikin sati mai kamawa,daga nan suka yi sallama kana fadawa suka rakashi har b'angaren Fulani,shima GALADIMA yayi nasa gefen saboda huta gajiya.+ Tun daga shigowar GALADIMA da yadda ya d'an had'e fuska Ummi ta fara shan jinin jikinta,dalili kuwa tasan yau kam tsakaninta da mai gidan nata sai ta Allah akan abunda su YASEER suka aikata,tsaf yanayin sa ya gama bayyana mata itan mai laifi ce,sai dai koda ganin haka sai yasa ta k'udurce a ranta da duk iya fad'an da zai mata a wannan lokacin bazata tab'a tankawa ba,zata tank'washi kanta ta bashi hak'uri ne duk da ba ita takar zomon ba,tana wannan tunanin kawai sai yayi abunda ya matuk'ar bata mamaki duk da sanda ya shigo fuskarsa babu wata wadatacciyar walwala,har tayi masa barka da dawowa ya amsa,haka har sanda suka yiwa juna sallama suka kwanta bai tada mata maganar ba,sai bayan data kwanta ne wayarta tayi k'ara,sunan YASEER data gani ya bayyana shi ne yasa tayi hanzarin d'auka kana ta bar kusa da Abba GALADIMA,dan yadda yakeennan bata san me zai faru ba,tsaf suka gama maganar duk da zasu yi ta dawo,amma duka har lokacin bai ce mata komai ba,ko da ganin haka sai itama ta tattara komai ta ajiye shi gefe sannan ta kwantar da hak'ark'arinta... *One week later...* Kimanin kwanaki bakwai da dawowarsu k'asar,taron na family taso gadan²,a b'angaren YASEER kuwa tun daga dawowarsu k'asar har kawo yau ko kad'an tsakanin shi da jeeddah ba'a barsu sun huta ba,kullum rana da zata fito ta gabas ta fad'i a Yamma da kalar sak'on da za'a turo musu,haka ko wane sak'o akwai irin razanin da yake d'auke da shi,sai dai garesu duk da sun tabbata mai turowar a shirye yake da aiwatar da duk abunda ya fad'a hakan ko kad'an baisa sun nuna a fili ba,dalili kuwa shine sun jima da sanin matuk'ar za'a dunga turo musu irin wad'annan sak'onni tofa dole ne mai aikata hakan yana kallonsa a ko wane lokaci haka zalika a duk wani motsinsu,wannan tasa su b'oyewa dan dole saboda basa son ko kad'an su nunawa b'oyayyan mak'iyin nasu gazawarsu. Kasancewar yau en ta kama ranar taron family'n gidan sarautar,yasa tun daga kan iyaye kama har zuwa y'ay'a da jikoki na wannan ahalin duk sun halarci taron,family ne Babba da ko cikin garin na kano babu wanda zai ce bai sansu ba,sai dai kasancewar wasun su ba mazauna k'asar ba da aiki ya rarrabasu garuruwa zuwa k'ashashe yasa ba'a cika ganin yawan nasu ba,sai ko a irin wannan lokacin da suke gudanar da bikin k'arshen shekara ko wata hidima itan ta taso,shi ne kad'ai yake iya bayyanar da asalin yawan su.Harabar gurin a cike yake taf da jama'ar family'n kwansu da k'wark'wata duk suna gurin zaune cikin manyan rumfuna da aka sa masu d'auke da shimfid'u na alfarma,gurin yayi shiru saboda jawabin da Matawalle yake gabatarwa na game da nasaba ta wannan family,a cikin batunsa na k'addamar da littafin zuri'ar mai d'auke da sunan kakan maimartaba Alh Abdullah Muhammad jibirillah wanda shi ne asalin zuri'ar tasu,ma'ana dai ta kansa ne chain en zuri'ar ya faro,har zuwa kan iyayen su zuwa kansu da y'ay'a,sai jawabi na gaba da zai gabatar da k'addamar da wad'anda basu tab'a samun damar halartar taron ba ko sau d'aya (marasa zumunci kenan),a k'arshe kuma Matawalle ya rufe da sanarwa ta sa ranar auren wasu y'ay'a nan a cikin family'n,kana aka yi addu'ar rufe taron baki d'aya. Sanda YAZEED ya tabbatar an tashi a taron,ya mik'e saboda gajiyar zama gurin da yayi,yana yiwa YASEER magana akan su bar gurin saboda yadda ya fahimci idanun y'an matan family'n nasu na kansu,basu jima da barin gurin ba kuwa,suma Adda da HAJIYA suka keb'e a b'angaren hajiyar na nan cikin gidan,hira suka dasa sosai irin wacce suka kwana biyu basu yiba a matsayinsu na y'an uwan juna,sai ga Aisha sun shigo tare da y'ar gidan Matawalle mai suna Sajida,ko kad'an basu yi tsammanin kakannin nasu suna zaune a b'angaren ba,tun kafin su kai ga shigowa Sajida ta kalli Aisha cike da zumud'i ta shiga labarta mata irin yadda ta jima tana dakon son YASEER,yadda tayi maganar yasa Aisha tayi mata dariya kafin ta furta "Kai y'ar uwa gaskiya ina miki murna sosai,yadda kike son nan nasa ina miki fatan ya soki fiye da haka,sannan na tabbata matuk'ar kika same shi a matsayin mijin aure kinyi dace wollahi sosai.." "Thank yuh y'ar uwa da wannan yabi naki..Gaskiya naji dadi sosai,kuma na gode miki da kika min wannan hasashen..Ammafa kema ko gaskiya na miki sha'awar wani handsome a gurin nan..Ba don komai ba sai dan yadda idan kuka zama makusantan juna abun zai bada colors tamkar rainbow..." Murmushi Aisha tayi ba tare data bata amsa ba,can Sajidar ta sake kallonta itama tana mata murmushi,kafin cikin zumud'i ta furta "Kinyi dariya bayan baki tambayeni ko waye na gano miki ba,bare ki bani tukuici...Kumafa ko Allah nasan ko ke kika ji abunda zan fad'a na tabbatar sai kin susuce dan nasan shu en ba irin k'ananun yaran nan bane,mutum ne shi mai aji..!" "Kaii! Sajee kin cika damuwa wollahi,banda abunki taya kike tsammanin ni zan kai kaina gare shi..?? Bakya tunanin ni en na fishi aji ne da had'uwa..?? Karfa ki manta da adadin samarin dana baki labari suna bibiyata,bama nan ba hatta cikin family ke kanki shaida ce akan yadda mutane da dama ke son suyi min magana ba don komai ba sai don kawai suna so na saurare su amma nak'i,shin toma taya zaki had'a ni da wani kiyi tunanin class enmu zai kai dai²..??" "Wahh..! Sisto gaskiya nasan haka wannan batun naki yake,sai dai ko ina son ki ture batun class enki gefe,domin kuwa shi wannan en na musamman ne,duk inda kika kai ga aji da dukma wani abu ina fad'a miki a samanki yake,dan yayi miki nisa mai girma indai ta wannan fannin ne,ke bama iya nan ba hatta da ko ina ta miki sharrr...!" Had'e fuska Aisha tayi saboda yadda maganar ta Sajida ta d'an sosa mata rai,a fusace ta mik'e zata bar wajen,saurin rik'o hannunta Sajidar tayi tana mata d'an murmushi kafin ta furta "Haba y'ar uwa fushifa ba naki bane a yanzun, kuma dai ai ko ba komai kafin kiyi zuciya dan na fad'a haka ya kamata ki tsaya kiji ko akan waye nake magana..." Kallonta Aisha tayi kawai tana sakin numfashi cikin siririyar muryarta ta furta "Dan Allah Sajee ki kyaleni da wannan maganar dan baki san yadda nake ji bane saboda kin gama cimin fuska akan wani can da ko matsayinsa ban sani ba bare nasan waye...Ina mai tabbatar miki tunda har a yanzun nan kika gayamin wannan maganar da tunda nake babu wanda ya tab'a fad'a min makamanciyarta yasa naji duk duniyata bani da wanda nake gaba dashi sama da wannan da kike magana akansa,sai dai abu na k'arshe da zan iya fad'a miki shi ne,ina so ki banu nan da kwanaki,ni kuma kafin cikarsu ina son tabbatar miki da dole ne saina zo miki da labarin na sashi ya fad'a tarkon soyayyata,dole duk girman kai da tak'amar da yake ji da shi na maisheshi ya zama tamkar bawana,matuk'ar na amsa suna na kuma na haifu cikin mahaifiyata alk'awari ne wannan nayi tsakanina dake,kuma saina tabbatar daya cika...!" Tana gama fad'an abunda yazo bakinta tayi hanyar ficewa a parlour'n,tana daf da fita ne Sajidar ta furta "Kinyi alk'awari..! Sannan kinci alwashi akan sai kin sa shi ya soki,har kika ce ko wane ne shi en ko...?? Amma abunda ban tambayeki ba shi ne,shin da kika fad'i haka kina nufin ko da ace ni en ina nufin *YARIMA YAZEED* ne....................??? Saurin juyowa tayi tana kallon Sajida fuskarta d'auke da matsanancin mamaki,ta d'ebi y'an mintuna a haka ba tare data iya aikata komai ba tamkar wacce aka dannama pause sannan a hankali ta matsa kusa da Sajidar tana cewa "Me kika ce ne Sajee...??" Kallonta sajida ta tsaya yi kawai tana murmushi,koda Aisha taga haka take fuskarta ta rikid'e zuwa wani irin mugun yanayi mai wuyar fassara kafin ta sake tambayar sajidar "Dan Allah ina son ki maimaita abunda kika fad'a yanzun.." Fari sajida tayi mata,cikin kwarkwasa tamkar wacce ke gaban saurayi ta furta "Dallah ni kada ki rainamin hankali,nasan kinji abunda na fad'a,dalilin baki san shi zan ambata bane yasa kika gama cika min baki ba...?? Haba y'an mata ai na fad'a miki tun farko kada kice zaki ja da lamarinsa domin kuwa shi en ne ba tsaranki ba,bawai kece ba tsaransa ba,amma da yake kina son mai dani wata bahaguwa shi ne zaki zauna ki shirya min shirmenki tamkar shirin jigida..Huh.! Yanzunma dai duk ba wannan ba ni abunda nake so dake kawai shi ne ki tsaya kiyi tunani akansa,idan har kika ce abunda kika saba yiwa sauran samari zaki masa wata k'ila a maimakon shi ya fad'a tarkonki ke kya kai kanki cikin komarsa...Amma fa shawara ce na baki,kina iya canjawa idan kin so,sai dai kafin kice zaki yi gaggawa ki sani,matuk'ar kika yi wasa da damar samun yarima,tofa ki tabbata babu ke babu wata dama ta alkhairi da zata sake samunki,dan wannan shine mafi k'ololuwar alkhairinki a rayuwa....!" Yadda Aisha ta kafeta da idanu gami da kunnuwa saiku rantse wani darasi sajida ke biya mata,nutsuwa ce ta dole ta shiga jikinta da ni kaina sai da nayi mamakin inda ta samota,kallonta Sajida tayi tana girgiza mata kai kafin tayi magana "Mene ne kike min irin wannan kallon haka..?? Ko na fad'i wani abu ba dai² ba.??" Cikin sanyin jiki Aisha ta girgiza mata kai "A'a babu komai..amma dai naga alamun a na damunki,da har kika iya yin wannan tunanin,shawarata gare ki shi ne ko dan gaba kafin kiyi tunanin faruwar abu ko zartar da hukuncin k'i akansa,ina so ki fara bincike ki tabbatar shin idan kinyi abun babu matsala ko kuwa,haka nan idan wasa kike ne to ina ganin gaskiya ki san irin wanda ya dace kiyi,dan ina ganin garin irin wannan wasan naki wata rana sai wani ya rasa ransa,idan kuma ba haka ba to lallai ne da irin wad'annan zantukan shirmen naki wani saiya kifa miki mari dan takaici..."+ "Kamar yaya kenan kike nufi..? Shin kina tunanin wannan maganar da wasa nake yinta nima..?? Bari kiji Aisha idan har ke kin d'auka da wasa to ki canja tunani,kamar yadda na fad'a miki sirrin zuciyata,nima sam bada wasa nayi ba,abun duk dana fad'a shi nake nufi.." Kallon kin cika Mara hankali Aisha tayi mata kafin tayi shigewarta zuwa waje ta bar sajida zaune a nan ba tare data sake tanka mata ba,bayan fitarta a parlour'n da sajida ta raka ta da kallo ta tab'e baki,cikin takaicin rashin bata had'in kai da Aisha tayi ta fara mita "Gaskiya a duniya ban tab'a ganin bagidajiya irinki ba Aisha,taya alkhairi zai kiraki amma ki dunga gudun sa..? Wollahi matuk'ar yarima ya kub'uce miki kinyi asara a rayuwarki ta duniya gaba d'aya,na tabbata bazaki tab'a samun mijin daya kaishi ba,kai in bandama rashin rabo irin naki taya zaki d'auki wannan maganar a wasa,ni da ace ni ce a matakin nan ai wollahi duk wanda yazo min da wannan batun har kyauta zan masa dan k'arshe ya gama burgeni saboda zaton alkhairi da yamin...Mtttsssss..!" Taja uban tsaki saboda tsabar takaicin da Aisha ta k'unsa mata,kafin daga bisani itama ta mik'e tayi waje,tana bin bayan Aishar.. Can a k'uryar d'akin hajiya kuwa itace da Adda suke nasu k'us² en game da wasu al'amura nasu na family da kuma wasu abubuwa da suke faruwa a kwanakin a gari,a cikin hiran ne sunyi nisa sosai suka fara jiyo shewar su Aisha sanda suke shigowa,wannan yasa su dakatawa dan basa son kowa yasan suna nan bare kuma a san mene ne suke magana akansa,hiran dasu Aisha dake gudana tsakanin sajidar da Aisha suka kasa kunne suna sauraro,duk abunda suke tattaunawa babu wanda basu saurara ba,a b'angaren Adda koda taji sanda sajida ke yiwa Aisha maganar yarima YAZEED take hankalinta ya karkata zuwa tunanin akan hakan,ta shiga fasalta duk yadda al'amura zasu zama idan hakan ta kasance,ai kuwa nan ta fara sakin murmushin jin dad'i,kafin ta juya ga hajiya za tayi magana,ko kafin ta kaiga yin magana tuni hajiyar ta mata alama da tayi shiru tukun,nan take kuwa tabi umarnin data bata,saboda lokacin maganar tasu aisha ya koma kamar fad'a,har tak'addamar da suka yi akan maganar duk a kunnuwansu har zuwa lokacin da suka fice,sai a nan ne hajiya ta juyo ta kalli Adda tana sakin murmushi "Gaskiya yarinyar nan ba dai tunani ba .Duba fa yadda take wannan magana kamar Babba,ni da har inayi mata kallon sha³ ashema tafi Aishar hankali,dubafa yadda take nusar da ita alkhairi amma tana guduwa,irinsu Aisha ne alkhairi ke binsu a baya suna guje masa,banda haka har kamar Sajida tayi wannan tunanin amma itan ta tsaya karanta fankon wasik'a..." Cikin jin haushi Adda ta gyad'a kai tana cewa "Ki bari kawai HAJIYA,ai wollahi dan dai kin ce kada nayi magana ne lokacin,amma da so nayi na kirasu nan su maimaita abunda suka fad'a,a inda suka fad'a ni kuma zan d'ora nawa sharhin,irin wannan dama haka data samu amma take k'ok'arin b'arar da ita,kai Allah ya mana maganin irin wannan asarar,wannan ai asara ce kana ji kana kana gani kasa hannun hagu ka tankwab'ar da damarka..Amma zan sameta ne dan ubanta,dama ai irin mijin da nake fatan ta samu kenan tuni ta tsaya shirme ita saita zab'a,garin ruwan ido kuwa taje ta samo wanda tafi k'arfi..." "A'a fa Adda wannan abun bana gaggawa bane,ya kamata ki lallab'ata har ta amince,amma idan kika ce zaki tursasata kan dole tofa zata iya k'in yin biyayya,amma ya kike ganin shawara ta..??" "Haka ne HAJIYA amma dai gaskiya wannan ba abune da zanyi sanya da shiba,irin su yarima dake wahalar samu ita ta same shi a sama ta ka zata ce bata so,ai wollahi bata isaba,haka kawai zata mana bak'in ciki.!" 'Dan murmushi hajiya tayi kafin ta furta "Allah yasa mu dace to,amma kam yau na farko dana ga wautar Aisha,banda haka yariman nan ai jininta ne,mene ne a ciki dan wannan alkhairi ya k'ullu,ina ganin ai zumunci ne zai dad'a k'arfi ko..??" "Wollahi kuwa Adda,kuma banda abunta yanzun ko cikin y'an matan nan data gani a family,bata ganin yadda ko wacce budurwa ke rububin taga ta samu damar tsayawa da shi,dana dai shi en yana d'auke musu kai,ai da tuni wata ta samu guri.." K'wafa Adda tayi tana jinjina kai cikin b'acin rai ta ci gaba da magana "Ki kyaleni da ita hajiya,ai a yau zata had'u da fushi na wollahi,yo ko uwarta idan taji wannan danyen aikin da take niyyar yi mana na asarar yarima ai bazata kyaleta ba...Ke dai kawai ki bari hajiya babu wani d'aukan lokaci da zan wajen yi mata magana,da gaske zan mata idanma auren ne bata so ni zanci mata uwa.." Dariya hajiya tayi kana taci gaba da magana "A'a ayi dai hak'uri Adda kada acinye mata Ladidin,ya kamata ki bita ta yadda komai kika ce tayi zata amsa,amma kiyi mata yadda zata koma cikin nutsuwarta tasan me duniyar ke ciki.." "Ai HAJIYA babu batun saurarawa,gara na bud'e mata wuta shi ne zata yi hankali,idan ba haka ba kuwa wannan ai sake shiga dawa za tayi..To tun yanzunma kina ganin k'aulin da take zuwa da shi bare anyi mata da sauk'i..??" Sun jima suna maganar inda duk bayan mintuna idan abun ya addabi Adda a cikin zuciyarta saita hau mita,yinin ranar abunda ta wuni yi kenan,gashi Aisha kuma sam tak'i ganuwa,dan tunda suka fice tare da sajida basu sake shigowa ba.. ^^^^^ Ko da YAZEED yayiwa YASEER magana akan su bar gurin maimakon su kama hanyar cikin gida b'angarensu,ina sai kawai suka d'auka mota suka fice a gidanma gaba d'aya dalili kuwa sun san yau gidan nasu ba wani dad'in zama zaiyi ba a gurinsu,suka kama hanyar gidan sarki na Nassarawa G.R.A,har sun kusa da gidan suka tuna da batun abinci kasancewar sun san baza su dawo a lokacin ba,tsayawa suka yi a dai² get en AUDU BAK'O SECRETARIAT da tunanin abun yi,yadda YASEER ya tsaya yana tunani yasa YAZEED kallonsa,ko kafin yakai ga yin magana tuni YASEER en ya riga shi da cewa "Malam ya dai ka juya kan mota mu koma mana,ko kuwa zamu rayuwa anan ne ba tare da abinci ba..??" Kallonsa ya juyo yayi kafin ya harareshi "Kasan Allah in dai ni zanyi driven ennan to babu inda zan koma,matuk'ar kuwa ya zama dole sai mun koma to sai dai kai ka maida mu,amma ni yadda na fito babu yadda za'ayi na koma yanzun.." "Haba malam shi kuma abincin fa..?? Zamu rayuwa ne a haka.??" "Oho! Wannan kuma kai ka sani,Amma ni na riga na fad'a maka matuk'ar zan koma to babu dalilin da zaisa ni dawowa nanma gaba d'aya..!" "Kada Allah sa ka koma en,amma ni dai kasan bazaka sani yinin yunwa ba,dan kai ka saba zaman haka nima sai aka ce maka zan zaunane..?" "Sannu acici...! Wai da kake wannan dagewan akan sai mun koma shin dole aka maka sai lallai abincin gida..?? Ina cewa ga restaurant nan a gari kaje mana kaci idan ka damu..??" Hararar sa shima yayi yana d'age kai "Kasan Allah nima babu dalilin da zaisa ni cin abincin restaurant,kawai idan zaka maidani gida na d'auko to idan kuma bazaka ba ni ka bani motan na koma fak'at.." "Ko..?? Ni kuma na zauna a ina kenan..?? Anan kan street kake so na tsaya jiranka..??" "Ina na sani nima..Kawai ka bani guri ni na juya.." Kallonsa YAZEED yayi ya zabga masa harara kafin yaja motan yaci gaba da tafiya,a tunanin YASEER koda yaji bai sake magana ba sai yayi zaton ya hak'ura ne akan zasu koma en,sai dai koda yaje dai² junction zai juya su koma gidan kamar yadda ya fad'a sai gani yayi ya wuce abunsa,saurin kallonsa yayi zaiyi magana yaga ya had'e girar sama data k'asa,cikin jin haushi ya girgiza kai had'e da yin k'wafa yana cewa "Kasan Allah bashi kaci...Tunda kayi min haka babu abunda zaisa ban rama ba.." Bai bari ya kai k'arshe ba YAZEED ya tari numfashin sa da cewa "Ka dad'e baka rama ba,banda rainin wayo kasan kana son abu ka kasa magana har saida muka kusa zuwa sannan ka wani ce sai mun koma.." "To tunda baka koma ba en ai saika min shiru ko..!" "Kanka ake ji...Ina ganin za ka iya yin waya ai ka fad'awa Ummi ta aiko maka da abinci nan,amma taya banda rigima kace mu koma cikin wannan jama'ar..??" "Dillah malam ni ka rabu dani,ina ruwanka dani da zaka bani wani shawara..Ka rik'e kayanka zai maka amfani a gaba.." Kallonsa YAZEED yayi dai² sanda suka iso bakin get en shiga gidan ya saki murmushi mai sauti,k'wafa YASEER ya sake yi yana juya kansa gefe ba tare daya sake tankawa abunda YAZEED en yake cewa ba. Bayan shigar su harabar gidan ko da YAZEED yayi parking tuni ya fice ya barshi man cikin motan,tsabar mugunta kuma irinta YAZEED koda ya fita sai ya zare key en yayi tafiyarsa da shi yana wasa da shi,haushi ne ya sake kama YASEER,nan ya fito a motan yana girgiza kai cike da son yi masa muguntar da zata wanke masa haushin daya k'unsa masa yaci gaba da bin bayansa.Lokacin da YASEER ya iske shi a cikin k'aton parlour'n zaune ya iskesa ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya da waya a kunnensa yana magana,duk da baisan dawa yake wayarba hakan bai hanashi kallonsa ba dan yadda yaga yana wayan sai yasa mutum rantsuwa akan babu wata waya da yake,kawai dai yasa tane a kunne,saboda babu abunda ake iya ji,cikin lokaci kad'an ya gama abunda yake ya ajiye wayan, ba tare daya kalleshi ba,ya furta "Ka nemo wani ka aika shi ya karb'o abincin munyi magana da Ummi yanzun.." K'in kula shi yayi kana shima ya nemi guri ya zauna yana muzurai... ^^^^^ A b'angaren jeeddah kuwa tunda safe data shigo cikin gidan bata samu damar zama ba saboda aikace²n dake kansu ranar musamman kuma daya kasance a ranar akwai wannan taron,tun safe data shiga b'angaren Ummi ko kad'an bata fito ba sai aiki take,sai wajen gabanin sallar azhur ta fito a kitchen en da niyyan zuwa tayi sallah,dai² ta fito tana shirin wucewa ta sanarma Ummi ta gama aikin da take yi,saiga Aisha ta shigo gefen cikin b'acin rai,d'agowa jeeddah tayi jin yadda aka bangajeta aka wuce da niyyar ganin ko waye,nan take idonta ya sauka akan Aisha da ita ko kulama ta buge mutum bata yiba,maganar da tayi niyyan yi ta fasa,kawai saita koma kitchen en da baya dan bata son wani abu ya sake had'a ta da ita yanzun,komawarta babu jimawa Ummi ta fito tana nemanta,a kitchen en ta tarar da ita tsaye ta jinjina bayanta jikin cabinet tana tunani,har shigowarta duk bata sani ba sai lokacin da Ummi'n ta fara mata magana "Yawwa uwata ke nake nema kuwa yanzun.." Saurin juyowa tayi tana sakin ajiyar zuciya,kana ta d'an rusuna tana yin d'an murmushi "Idan kin kammala aikin da kike yi,ina so yanzun kiyi k'ok'ari ki had'awa su YASEER abinci,YAZEED ya sanar min zasu turo wanda zai kai musu chan gidan sarki na nassarawa.." Amsawa tayi cike da girmamawa,nan itama Ummi'n ta juya da nufin komawa,itama jeeddah ta koma bakin aikin nata,bayan fitar Ummi baifi da mintuna ba,sai ga sajida ta shigo kitchen en,tun daga bakin k'ofan shigowa ta tsaya kawai tana kallon yadda jeeddan ke aikinta cikin nutsuwa da hanzari,a hankali ta tab'e baki sannan ta shigo ta bud'e freezer tana duba ruwa mai sanyi,can gefe ta koma ta tsaya taci gaba da kallonta tana jinjina kai,kafin ta gama shan ruwan ta fice ta barta tana ci gaba da aikinta. Kimanin awa guda da y'an nintua jeddah ta shafe kafin ta kammala shirya musu abincin ta d'auka kimai ta jera komai cikin basket,nan a kitchen ta barsu sannan ta fita don zuwa ta sanar ma da Ummi ta gama,bayan fitarta da y'an mintuna ta ta sake dawowa da niyyar d'auka ta fita dasu gurin driver'n da zai kai musu kamar yadda Ummi'n ta sanar mata ya zo tuni ita yake jira,shigowarta babu jimawa kawai saita tarar da su Aisha tsaye akan basket en sun bud'e flask's en suna niyyan d'iba,da saurinta ta k'arasa inda suke,ba tare data yi musu magana ba ta janye basket en sannan ta kinkima zata fita da shi,cikin jin haushin abunda tayi musu sajida ta taso kanta gadan² kamar zata daketa tana mata magana cike da gadara "Keee..! Dak'ik'iyar ina ce da kina ganin zamu d'iba ki wani zo ki d'auke..?? Dallah can dawo ki ajiye mana kucaka kawai.." Kalmar data ambata ita tasa jeeddah tsayawa a inda take ba tare data juyo ba,bare susa ran zata dawo en kamar yadda suka fad'a,sai dai ranta yayi matuk'ar b'aci da kalmar da aka kirata da ita,a hankali Aisha ta juya ta kalli sajida kafin itama ta samu damar yin magana "Ke wai ba dake ake bane,kina jin mutane amma kin mana shiru..ke wawuyar ina ce..???" Koda jin muryar Aisha take yasa ta juyowa tana sakin murmushin mugunta ta kalleta ido cikin ido,cikin wani salo ta sake sakar mata murmushi tana karkata kanta kafin ta fara mata magana "Hi..! Aisha ya kike..?? Ya bayan rabuwa...??" Wani mummunar fad'awa gaban Aisha yayi lokaci guda duka annurin fuskarta ya dusashe saboda tsabar fargaba,cikin rashin sanin makamar abunda ya dace tayi ta shiga had'iyar yahu,ganin jeeddah a wannan lokaci tuni yasa ta kasa sake yin magana,kallonta sajida tayi da mamakin jin yadda jeeddan ta kirata tana fad'in "Yane sis kin san wannan ne..??" Bata iya bata amsa da baki ba sai d'aga mata kai kawai da tayi,koda ganin yadda Aisha ta koma a sanadiyyar ganinta kad'ai yasa jeeddan ta juya abunta ta fice hannunta d'auke da basket en,tana fita itama Aisha bata iya ci gaba da tsaiwa a side enba tabi bayanta,sai dai bata ko yarda sun sake had'a hanya ba,direct bayan fitowarta gefen hajiya ta nufa nan ta nemi tadawa Adda hankali akan lallai saita tashi sun tafi a dalilin lak'anawa kanta rashin jin dad'i. Ita kuwa jeeddah lokacin data fito bayan ta nemi driver'n da zata bawa sak'on bata ganshi ba,duk inda take zaton ya tsaya da kuma wanda ya dace ta tambaya duk tayi,sai dai duk wanda ta tambaya sai yace mata ai bai jima da barin gurina,hakan yasa ta d'an dakata tana jira taga ko zai dawo amma har kusan mintuna a k'alla talatin babu shu bare labarinsa,hankalinta ne yak'i kwanciya da jin shirun,nan take tunanin abunda ya dace tayi ya fad'o mata,har tayi niyyan neman wani driver'n ta bashi ya kai musu kuma sai ta fasa saboda tunanin kada taje garin neman gira ta janyo a rasa ido,wannan tunanin yasa ta kama hanyar fita kawai da niyyan kaiwa da kanta duk da bata tab'a zuwa gidan ba amma tasan duk mai napep en data tsayar bazai kasa sani ba,har ta fita bakin titi ta tare napep bata ko sake ganin kyallin driver'n ba,dan haka kawai sai ta hau kanta tsaye suka d'auki hanyan state road,a dai² k'ofar gidan ya ajiye ta,bayan ta fito ta sallame shi ta d'auki kayan tana kama hanyar k'ofar shiga gidan gadan² k'irjinta sai tsananta bugu yake,ko da zuwanta nan fadawa suka tareta da tambayar inda zata da abunda ya kawota,bayani ta musu na gurin wad'anda tazo da kuma sak'on data kawo musu,ai tun kafin ta gama fad'a suka dakatar da ita akan ta koma,duk iya bayani ta musu ta kuma basu hujjanta na zuwa amma fir suka hanata shiga,kuma abun takaicin gareta shi ne,ta samu ma su karb'i kayan su kai shima sunk'i wai lallai sai dai ta koma da shi dan basu san wane irin abune a k'ulle a ciki ba,rasa abun yi tayi dan haka kawai sai ta koma gefe ta tsaya zuciyarta cike da tunanin mafita daya dace tayi amfani da shi a wannan gurin,tana nan tsaye ta b'ata kusan awa guda ba tare da sun barta ta shiga ba ko su karb'i sak'on ba motarsu ta fito,a lokacin kuwa tuni jeeddah ta gama gajiya saboda tsananin shan ranar da tayi hatta da idanun nan nata tuni har sun fara sauya color,daga dukkan kana kallonta zaka gane ta wahala,har sun gota ta YASEER ya hangota kawai sai ya tsaya da motan kasancewar a lokacin shi ke driven,ta side mirror ya d'an sake kallo inda take sannan yayi baya kad'an,a center en inda take tsaye ya parker,mamaki ne ya kama shi lokacin daya tabbatar itan ce dan da fari baiyi zaton hakan ba,kawai dai ta masa yanayi ne da itan shi yasa ya kasa wucewa har sai da yaji yana son dubawa,a hankali ya fito a motan fuskarsa na bayyanar da mamaki ya furta "K'anwata..! Kece a nan,me kuma kika zo yi nan..........??"

0 Comments