WANI ALAMARI CHAPTER 3

WANI ALAMARI CHAPTER 3
Koda suka ƙaraso ƙofar shiga turakar ta Fulani kasancewar maimartaba na gefenta daga nan bakin ƙof suka dakata,sannan suka aikata tare da bayi mata da suka tarar a farfajiyar gurin masu yiwa fulani hidima da suke tsimayin fitowar maimartaba,shigar su cikin turakar ta Fulani suka iske maimartaba kishingiɗe gefe guda kuma Fulani tana masa fira,yayin da shi ɗin yake cin ƴaƴan itatuwan da aka kawo masa,da shigowarsu suka zube tare da kai gaisuwa ga sarki sannan suka gabatar da jeeddah a matsayinsu na ƴan saƙon da aka aiko,izinin fita maimartaba ya basu,sai bayan fitar bayin ne sarki ya juya ga jeeddah da kanta yake a ƙasa lokacin data cire niƙab en dake fuskarta saboda girmamawa ga sarki,ta sake miƙa gaisuwa cike da ladabi tana jiran jin me zai fito daga bakin maimartaba. "Jeeddatu mahaifiyar kowa..Shin yaya mahaifanki suke..?" Cikin sake yin ƙasa da kai ta amsa "Suna lafiya ranka ya daɗe.." "Masha Allah,haka muke fata a ko wane lokaci..." Sai da ya sake ɗaukan lokaci kafin ya sake yin magana "Shin kin san dalilin da yasa muka aika kiranki..??" "A'a ranka ya daɗe... Sai dai idan har ka sanar dani,sannan ne zan san dalilinku na kirana..Allah ya baka tsawon rai.." Murmushi maimartaba yayi irin nasu na manya masu ji da mulki,kafin ya jinjina kai "Haƙiƙa dalilin da yasa muka tura a kirawoki yana da girma a gurin mu,ba don komai muke da buƙatar ganinki ba face jin irin ƙoƙari da gudun mawar da kika bamu game da matsalar data kunno mana kai cikin wannan zuri'a tamu da kuma masarautarmu,lallai ne kin cancanci a yaba miki,sannan daga yau ke ɗin muna fatan ki kasance ɗaya daga cikin amintattun mu,kuma ɗaya daga cikin waɗanda zasu dunga yiwa yarima hidima.." Wata irin faɗuwa gabanta yayi da tunda take bata taɓa jin irinta ba a tsawon rayuwar ta,nan take ta fara jin jikinta ya ɗauki tsuma har tana jin yahun bakinta na ƙafewa,maganar da maimartaba yayi ita ta taimaka wajen dawo da ita hayyacinta "Muna fata zaki amince da wannan ƙuduri namu,sannan duk wani abu da zai faru baza ki taɓa ƙin duk wani umarnin muba.." "In sha Allah ranka ya daɗe bazan taɓa ƙin yi muku biyayya ba a duk abunda zaku umarceni nayi,a ko wane lokaci cikin jiran umarninku muke,mu bayinku ne a kullum umarnin ku shi ne abun binmu.." "Madallah..! Da waɗannan kalamai naki,wannan ya sake nuna mana ke en hadima ce mai biyayya ga duk wani umarnin mu,wannan dalilin yasa muka zaɓw ki muka baki wannan matsayi,ba don komai ba sai dan mun san zaki yi mana biyayya kuma kin cancanci matsayin...Abu na gaba da muke so daga gare ki shi ne muna so ki duba duk abunda kike so na daga dukiya ko na duk abunda kikaga kina so ki sanar damu,wannan alkƙawarinmu ne muyi miki shi abisa tukuicin kyautatawar da kika mana.." Shiru jeeddah tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa ba tare data furta komai ba,cikin zuciyar ta kuwa taradaddin abunda zata faɗa take,dan yadda zuciyar ta ke ƙiyasta mata abunda zata faɗa "Kawai tunda maimartaba yace ki zaɓa me zai hanaki ki zab'a..? AI tunda shi yayi alƙawari bazai ƙi yi miki duk abunda kika amtaba..." Wata zuciyar ta bata damar yin hakan,can daga wani gefen na zuciyarta kuwa saurin kwaɓarta tayi "To shin idan kin faɗa abunda kike so anyi miki ke kaɗai fa,iyayenki kuma fa..??? Shin mene ne amfanin ki nemi a ƴanta ki,alhalin mahaifanki na cikin ƙangin bauta..???" Jikin tane yayi sanyi saboda yadda zuciyarta take tunatar da ita abunda take ƙoƙarin mantawa a dai lokacin da bai kamata ace ta manta ɗin ba. "Tabbas babu amfanin a ƴantani alhalin mahaifana suna a halin bauta....zanyi ƙoƙarin jure duk halin da zan shiga indai har baza mu samu ƴanci tare da iyayena ba,to kuwa nima ya zama dole na haƙura da samun sa..Daga nan har zuwa lokacin da zan cancanci haka daga gurin iyayen gijina.." Jin yadda tayi shiru na tsawon wasu lokaci yasa maimartaba yin murmushi sannan yaci gaba da magana "Uwata naga alama kina jin kunya,amma mun baki lokaci kiyi tunani akan duk abunda kike buƙata daga garemu,saboda haka mun sallame ki zaki iya tafiya,mu kuma muna nan sauraron abunda zaki yanke.." Jiki babu ƙwari tayi godiya ga maimartaba sannan tayi godiya ga Fulani tayi sallama dasu ta miƙe da niyyar fita tana tafe tana ɗaura niƙab ɗinta har ta iso bakin ƙofa zata fita... ^^^^^ Haka nan yaji babu daɗi a abunda Yaseer ya masa,shi yana tambayarsa wace ce yarinyar ne ba don komai ba sai don tunawa da sunan da yaji Matawalle ya ambata a fada a matsayin wacce ta taimaka aka fito da shi daga ƙangin wahalar daya faɗa tsawon shekaru,duk da a zuciyarsa yana jin haushi tare da jin tsanar Aisha da Ladidi a matsayin su na waɗanda suka ƙulla masa makircin da yake jin haushinsu,itan kam yana jinta musamman a cikin ransa,tunaninsa da zuciyarsa duka suna bashi duk daga inda ta fito lallai ne itan ta musamman ce,yana jin a duniyarsa ta cancanci mutuntawarsa da darajtawa a duk yadda ta kasance,haka nan yake jin zuciyarsa na son ganinta ba don komai ba sai dan ra'ayin kansa. Fitowarsa daga gefen nasu direct gefen Fulani ya nufa cikin sauri kamar zai tashi sama,dai² ƙofar shiga turakar ta mahaifiyarsa ya ɗage curtains en zai shiga bakinsa ɗauke da sallama yaji ya bangaji abu,da sauri ya juya idanunsa zuwa gurin yana riƙo abun da yake niyyar jefarwa. Ita kanta jeeddah lokacin da take tafiya sam bata yi tunanin yadda take tafe tana ɗaura niƙab ɗin nata za'a samu matsala ba,haka bata taɓa kawowa a ranta wani zai iya shigowa ba shi yasa take tafe kanta tsaye,yadda taji an turota da ƙarfi har yayi sanadiyyar tafiyarta baya zata faɗi,riƙota da taji anyi shi ya bata damar haɗiyar wani wahalallen yahu da ƙyar sannan ta shiga buɗe runtsatstsun idanunta data kulle a sanadiyyar saddaƙarwar da tayi saita sha ƙasa,ba tare da tayi tunanin riƙe wani abu da zai tallafa mata ba,ƙuri ta masa da ido tana haɗiyan yahun wahala,shi ɗinma kallonta yayi yadda tayi covering jikinta duka banda ƙwayar idonta babu abunda ake iya gani,tayi shigar nan nata kamar wata fatalwa kuma duka da baƙaƙen kaya yasa shi sake kallonta kafin ya miƙar da ita tsaye yana faɗin "Sorry..!" Mamaki ne ya kama jeeddah dan ita yafi cancanta ta bashi haƙuri dan kuwa ita hadima ce kuma ita ke ƙasa da shi,ko kafin ta gama mamakinta tuni shi kam har ya bar wajen ya nufi gurin Fulani,juyawa tayi ta raka shi da ido sannan ta juya a hankali ta bar gurin... Shi kam a gefen yarima yazeed ko daya bar gurin yana zuwa ya tarar da maimartaba zaune,cikin sanyin jiki ya juyo zai bar wajen dan sam baiyi tunanin maimartaba yana wajen ba shi yasa har ya ƙaraso cikin turakar,kuma ko daya shigo sam hankalinsa bai kai kan maimartaba ba,sai yanzun da yayi ƙoƙarin zama sannan ya ganshi,nan take ganinsa a gurin yasa shi fasa zaman da yayi niyyan yi ya juya zai fice, cike da rashin jin daɗin abunda ya gani ya juya yana ƙoƙarin ficewa. Rashin jin daɗin da Fulani ta hango a fuskar maimartaba ahima yasa ta saurin kiran yazeed tun kafin ya kaiga ficewa "Yazeed dawo ka zauna za muyi magana da kai.." Jikinsa a sanyaye ya waiwayo idanunsa har sun sauya launi saboda ganin maimartaba tuni ya taɓa masa zuciya kuma hakan ya haddasa masa tuna abunda ya faru a shekaru biyar da suka wuce,yadda yaga Fulani ta jefe shi da wani irin kallo yasa shi sauke kai ƙasa sannan ya dawo ya zauna a ƙasa idanunsa suna kallon ƙasa "Yazeed me yasa kake aikata irin wannan abun..? Shin ina iliminka da tunani suka tafi..mufa mahaifanka ne me yasa dan mun yanke hukunci akanka zaka ɗauki abun da zafi haka..? Idan har kai da kake namu kayi mana haka,su kuma sauran al'ummah me zasu ɗauke mu ko wane irin kallo zasu mana dan mun zartar musu da hukunci..Wannan abun da kayiwa mahaifinka sam ba dai² bane kuma ina son lallai yanzun ka durƙusa ka bawa mahaifinka haƙurin ka kuma nemi afuwar abunda kayi.." Ɗagowa yayi da sauri idanunsa taf da hawaye ya kalli Fulani kana ya buɗe baki da niyyar yin magana "Bana son kayi min musu Yazeed,kamar yadda na faɗa nafi son ka aikata abunda nace da kai kawai ba tare da kayi jayayya da magana ta ba.." "Dan Allah Ummah ki gafarce ni,tabbas nasan na aikata ba dai² ba amma a halin da nake jin zuciyata,da irin ƙuncin da nake ji a duk lokacin dana tuna cewa mahaifina shi ya bada goyon bayan a tafi dani a tsare ba tare daya bada damar ayi bincike ba,duk da yasan halayena a matsayinsa na mahaifina dana tabbata kaf faɗin duniya bayan ku mahaifana da ɗan uwana babu wanda yasan halaye na da duk wani abu da zan iya aikatawa dama wanda bazan iya ba,amma kash sai gashi mahaifina ya zamo mutum na farko daya bada tsammani akan zan aikata abunda ya jima da sanin ba bazan taɓa iya aikatawa ba..." "Ya isa haka Yazeed,daga wannan bana son ka sake cewa komai kawai kayi abunda nace maka..Umarnine nake baka a matsayina na mahaifiyarka.." "Ummah kiyi haƙuri amma bazan iya aikata abunda kike umartata nayi ba a wannan halin..!" Bai ƙarasa ba yaji saukar mari a kumatunsa ɗaya daya sashi saurin yin shiru yana sauke kai ƙasa,cikin ɓacin rai Fulani ta kalli Yazeed tana magana "Irin ɗabi'un daka koyo kenan a gidan yarin..? Shin wannan shi ne irin halayen waɗanda kake tare dasu..? Mene ne ya baka sha'awa har haka Yazeed da har kayi ƙoƙarin koyo waɗannan mugayen ɗabi'un...??" "Ya isa haka Fulani.." Maimartaba ya dakatar da ita yana lumshe idanunsa "Amma Yallaɓai taya zan ƙyale shi yana faɗin irin waɗannan maganaganun agaban idanuna,ko da ace bakai ka haifeshi ba aurena kawai kake nazo da shi matsayin agola,taya zai kalli tsabar idonka ya faɗa maka irin wannan maganar sannan kuma kace na rabu da shi..Koda bama wannan ba kai ɗinfa matsayin shugabansa kake..." "Tunda nace ki bari kiyi shiru haka nan.." Maimartaba ya sake yin maganar ba tare daya kalleta ba,shiru tayi dan bin umarninsa amma ba don ta rabu da Yazeed ɗinba,a hankali ya juya ya kalli yazeed ya ajiye numfashi kana ya fara da cewa "Tabbas Yazeed duka abunda ka faɗa banga laifin ka ba,dalili kuwa ni da kaina na haifar da wannan matsalar,da na bari anyi bincike tun farko tabbas da babu yadda za'ayi haka ya faru tsakanina da yarona,wannan duk laifi nane kuma na amaa,sam a matsayina na shugaba kuma mahaifi wannan ba shi ne adalcin da nake tsammanin nayi ba,ni kaina sai bayan da al'amuran suka faru nayi nadamar abunda na aikata,amma a dalilin rashin hujjar da zata sa a sakeka shi yasa naci gaba da danne damuwata na abunda nasa aka aikata maka,sam ba don son raina na aikata hakan ba...Ka gaface ni yarona,nasan ban kyauta maka ba ko kaɗan amma kamin afuwa abisa kuskuren dana aikata.." Shiru duka suka yi suna sauraren maimartaba har ya kai aya,ko da Yazeed ya ɗago kansa ya kalleshi sai yaga yana goge hawayen da suka sauko masa,saurin jan jiki yayi ya koma kusa da maimartaba yana riƙe hannunsa dan baiyi tsammanin haka daga gareshi ba "Dan Allah Abiiy kayi haƙuri.. Wollahi na fahimci uzurinka,amma dan Allah kada ka zubarmin da hawaye a dalilin hukuncin daka sa aka aikatamin,nasan kai mahaifina ne duk hukuncin da zaka zartar akaina dai² ne,sai dai wasu lokutan nakanji zafin abunda ya faru a wannan lokacin da za'a tafi dani,daya janyo har ka kasa ɗaga ido ka kalleni,amma yanzun na fahimci komai..Dan Allah Abiiy kada ka sake zubarmin da hawaye,matuƙar kuwa zaka ci gaba to na tabbata babu ni babu rahama..." Saurin rufe masa baki maimartaba yayi yana girgiza masa kai alamun yayi shiru,amma ina Yazeed kam ya kasa yin shiru "Tabbas zubar hawayen iyaye akan yayansu hakan baya ƙarar su da komai face azaba da gamuwa da bala'ai.." Jinjina masa kai maimartaba yayi sannan yayi murmushi yana goge fuskarsa "Shi kenan yarona in sha Allah bazan sake kamantawa ba bare na aikata..Hawayena kuwa idan akanka ne baza su taɓa zubaba da yardar Allah.." Murmushi Yarima Yazeed yayi sannan suka rungume juna,dukansu suna masu jin farin cikin fahimtar juna da sukayi,a hankali Yazeed ya ɗago kansa daga jikin maimartaba yana shirin yin magana sai dai ya rasa ta yadda zaiyi wa maimartaba bayanin abunda ke ransa,nan ya tsinkayo muryar Umma'nsa tana masa magana "Ehmm! Yazeed ai kuwa da akwai wani albishir dana so yi maka,sai dai abunda kayi yanzun yasa na fasa sanar da kai.." Fuskarsa ya juyar zuwa gareta sannan ya ɗan marairaice mata fuska kamar ƙaramin Yaro "Haba mana Ummanah,idan baki faɗa minba waye ne zai sanar dani..?" "Rabu da ita ni zan sanar da kai komai tunda bazata faɗa maka ba.." "Ohoo! Wai haɗemin kai za kuyi...To ai shi kenan nima dai saukin ƙawayena suna hanyan dawowa cikin satin nan.." "Amma dai Ummah kafin su dawo ai mune dake,kuma ko sun dawoma zasu koma ne,tunda ba zama suka dawo dayi a gida ba.." "Koma dai me zaku ce ai zasu dawo ne kuma zasu ɗebemin kewa kafin su koma,makarantar da duka saura kaɗan su kammala.." Sun jima suna hira tsakanin su irin hira ta tsakanin ɗa da iyaye,irin wacc suka jima rabonsu da irinta,sannan Yazeed ya musu sallama ya fita dan komawa gurin Yaseer cox lokacin kam yana jinsa cikin sauƙi da nutsuwar da ya ɗauki tsawon lokaci baiyi irinta ba. Can a ɓangarensu ya iske YASEER sai safa da marwa yake ya kasa zama,kallonsa kawai yayi sannan ya wuce zai shige bedroom,da sauri Yaseer ya tare shi yana ɓata fuska "Wai kai wannan wane irin hali ne ka koyo daga tambaya ban baka amsa ba saika fice ka barni nan inata gadi.." Yamutsa fuska Yazeed yayi kafin ya janyeshi gefe zai wuce,da sauri Yaseer ya riƙo hannunsa "Me yasa ne kam kake min haka..? Ka faɗa min abunda na maka kafin ka wuce.." "Dillah sake ni..Banda ka rainawa kanka hankali na maka magana kawai ka tsaya kana nunamin wani abu daban ba dole na maka haka ba.." Dafe kai Yaseer yayi sannan yaja hannun yazeed suka zauna "Shi kenan bro kayi haƙuri.. Naji laifina ne amma kayi haƙuri.." "Nifa malam kaga ba haƙurin ka na damu dashi ba kawai ka faɗa min abunda na tambayeka tun farko shi ne haƙurin da zan iyayi.." "Okey..! Ok! Naji zan faɗa maka..amma before ina son ka faɗa min dalilin da yasa kake son saninta..?" Dan murmushi yayi sannan ya furta "Haka nan nake jin son sanin wace ce itan..??" "Ƙarya ne wollahi ba haka nan bane..Kaga malam kada ma ka soma tunanin ɓoyemin,kasan ko zaka ɓoyewa kowa babu ni a cikin irin waɗannan mutanen ko..?" Tsayawa YAZEED yayi kawai yana kallonsa yadda ya haƙiƙance akan maganar sai kace wani babba "Sannu Babanah..." "Malam babu wani baba da zaka cemin kawai dai ka sanar dani dalilin.." "To idan bance maka baba ba me kake so nace..?" Yar dariya YASEER en yayi kafin ya kalleshi up to down "Kai wollahi ka cika matsaloli wai zamanka acan ne yasa ka koma wani matsalalle ne haka..?" "Ban sani ba..idan zaka faɗa min ne to kawai ka faɗa idan kuma baza ka faɗa ba to kaja bakinta kayi min shiru.." "To bazan faɗa ba ɗin shugaban masu matsala..." Har ya juya zai tafi yayi saurin juyowa "Faɗi ka ƙara matsala ba a cikin ta na rayuwa har tsawon shekaru biyar..." Daskarewa Yaseer yayi jin maganar data fito a bakin Yazeed,haka nan sai duk yaji baiji daɗin kalmar ba,kuma ga yadda yazeed en fuskarsa ta koma dalilin ambaton maganar da yayi ne yasa "Dan Allah bro kayi haƙuri kada ka sake faɗan irin wannan maganar." "Kaifa ka fara shin kaga laifina dan na ƙarasa..??" "Pardon me bro..dan Allah kayi haƙuri.." Wucewa yazeed yayi ya barshi nan jikinsa da zuciyarsa duk babu daɗi,rasa abunda zaiyi ya dakatar da yazeed ɗin yayi kawai saiya buɗe murya da ɗan ƙarfi ya furta "Ba kowa bace face ƴar gidan SARKIN KASUWA................" Saurin waiwayowa Yazeed yayi,a hankali kuma ya dawo ya tsaya gaban Yaseer yana kallonsa kawai,rasa abun yi Yaseer yayi saboda yadda yaga fuskar yazeed har lokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa,ko da ganin haka kawai sai shima ya zubawa yazeed en ido kamar yadda ya masa,a hankali yazeed ya saki fuskarsa zuwa yanayin murmushi,mamakin murmushin Yaseer ya fara,sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya fara magana "Heeyy! Mr man..what this smile intends...??" Bai kula shi ba saima sake sakin wani murmushin da yayi sannan ya juya ya bar wajen,cikin d'aga murya Yaseer ya furta "Ya Allah..! Ya shirya min kai..ya fidda kai daga halin daka shiga.." Wata dariya ce ta sub'ucewa Yazeed lokacin da yake k'ok'arin shigewa bedroom en nasu,har bai san sanda ya waigo ba "Kai me kake nufi ne wai..?"+ "Ohoo! Abunda kake nufi nima shi nake nufi.." Yana daga inda yake ya girgiza kai had'e da cewa "Uhmm! Da kasan abunda nake da baka fad'i haka ba.." "Kai dai ka sani kuma,ni kaga nayi waje zani naga Ummi.." "Heeyy! Mr man ka jira na fito mu tafi tare mana nima ai ban shiga gurinta ba.." Komawa Yaseer yayi ya zauna yana jingina bayansa a jikin seat en daya zauna ba tare da yayi magana ba,shi kuma yazeed nan ya shige ya bar Yaseer yana jiran fitowarsa. A tare suka fito suka jera,duk da ba hira suke ba a tafiyar tasu haka nan suke cikin farin ciki dukansu,a haka suka nufi gefen Ummi'n Yaseer,nan suka yada zango Ummi sai jimamin yadda taga yazeed en ya koma take,haka nan duk inda ya motsa idanunta na kansa.Sun jima sosai a gefen ta,dan sai da suka ji kiran sallah sannan suka fito suka nufi masallaci. ^^^^^ Bayan fitar jeeddah daga gefen Fulani direct gida ta koma dan yin wasu aikace²n da Inno ta bari kafin ta fita,har ta koma gida zuciyar ta bata bar sak'a mata abunda ya wakana ba zuwanta kiran da maimartaba yake mata,ko data dawo gidanma tunanin dai taci gaba da yi kamar wacce ta rasa abun yi,a haka taita y'an aikace²nta har zuwa ta kammala. Tana zaune cikin kitchen ensu ta d'ora musu girkin dare,wayan dake mak'ale a jikinta ya shiga vibrating,jin haka yasa tayi saurin ciro shi daga jikinta tana dubawa,ko da taga ansa UNKNOWN NUMBER sai kawai ta tsaya ta zubawa screen en wayan ido kamar mai son nazartar wani abu a jikin fuskar wayan,sai da kiran ya katse sannan ta dawo cikin nutsuwarta tana k'ok'arin amsa kiran,ganin da tayi kiran ya katse yasa ta mayar da wayan inda ta ciro sannan ta ci gaba da abunda take,mintuna biyu tsakani mayar da wayan ta sake jin ta sake yin vibrate da sauri ta ciro tana dubawa sai dai wannan karon alamar shigowar sak'o ne,haka nan ta bud'e akwatin sak'on nata da niyyar duba abunda sak'on ke d'auke da shi "Lallai ke yarinya ce mara tunani...Taya za kiyi k'ok'arin taimakon ahalinsu mutanen da kullum basu da burin daya wuce su bautar daku..?? Ki nutsu kisan inda kanki yake,sannan muna gargad'inki da cewa wannan ya zama karo na k'arshe da zaki jefa kanki cikin matsalar da bata shafe kiba,haka duk wani abu da zaki ga ya faru kada ki sake yunk'urin shiga,idan kuwa kika kuskura kika tsoma kanki cikin abunda bai shafe ki ba,ko kika sake tunanin shiga hurumin mu,lallaifa ki tabbata kin jefa kanki a cikin masifar da baza ki tab'a iya fita ba....!" Shiru tayi tana sake bin harufan da sak'on yake d'auke da su,tafi minti biyar tana sake maimaita karantawa duk da ko kad'an bata fahimci ma'anar da sak'on ke d'auke da ita ba,haka taita faman juya kalmomin a cikin ranta,tana fad'ar su amma sam ta kasa fuskantar komai,ko da kuwa tambayarta za ayi a lokacin adadin yanda ta karanta ba lallaine ita da kanta ta iya fad'a ba,nan zuciyarta ta shiga tunanin inda sak'on ya fito da wanda ya turo mata,ta jima tana sak'a da warwara,ganin tunani na neman yi mata yawa yasa ta hak'ura ta maida wayan ta ajiye saman window sannan ta ci gaba da sabgogin gabanta ba tare data samu nutsuwa a cikin ranta ba... ^^^^^ Fitowarsu daga masallaci bayan an idar da sallah suka d'an zaga cikin gidan,ba don komai ba sai duk dan hakan ya d'ebema yarima yazeed kewa da y'ar damuwar dake cikin ransa,basu wani yi tafiya mai nisa ba sosai ya waiwayo ya kalli Yaseer "Ehenn! Mr man kace y'ar gidan waye ma Yarinyar nan..??" Sai daya waiwayo shima ya kalli yazeed en kafin ya d'auke kai yana sakin murmushi "Cewa nayi y'ar gidan Sarkin kasuwa ce...akwai wani abu dana fad'a bayan wannan ne..??" "No..! Kawai dai na manta ne shi yasa na tambayeka." "Uhmm! Kana buk'atar wani abu bayan sunan nata da sanin ko y'ar gidan waye itan..??" Kallon rashin fahimta ya bishi da shi yana squeezing face ensa "Nace maka haka ne..???" "Noo!! Na sani ko kana buk'atar saninta fiye da haka..??" "Me sanin nata zai amfaneni da shi..?" "Na sani..??" "Ohh! God.! Baka sani ba kake d'ora kanka akan zato..?? Kai wollahi ka cika sa ido,nifa duka ba wani abu yasa na tambaya ba,kawai naji an ambaci sunan ne a fada a matsayin ta na wacce ta bada gudunmawa aka sake ni,ya cancanta ace na neme ta nasan wace ce itan da dalilin ta nayin hakan,amma bayan haka fa..?" "Sorry bro...let us this chapter insulate..okay..?" Kai ya kad'a masa alamun shi kenan,daga haka kuwa babu wanda ya sake magana suka ci gaba da tafiya kowa da abunda yake sak'awa a ransa,suna daf da zasu wuce ta wani hanya da suka ratso kunnen yazeed ya kwaso masa sunan jeeddah da aka kira,saurin waiwayawa yayi da niyyar ganin wacce zata amsa,idanunsa ne suka sauka akan wata y'ar k'aramar yarinya da duka bazata wuce shekaru biyar ba,a hankali ya girgiza kai ya juya dan dai yasan wannan yarinyar babu yadda za'ayima ta kasance waccan jeeddan da yake tunani. Tsaf suka gama zagayen da zasu iya sannan suka kama hanyar komawa gida dan a lokacin tuni Yazeed ya fara yiwa Yaseer k'orafin ya gaji,shigarsu cikin parlor babu jimawa,wayan Yaseer tayi k'ara alamun shigowar sak'o,sai da yayi d'an jimm dan yasan duka a kwanakin nan sak'o d'aya ne yake iya shigo masa,haka ko wane lokaci yasan shi d'in ne zai iya shigowa wayarsa a duk lokacin da mai turowar yaso,kuma sak'on baya rasa samun nasaba da wannan b'oyayyiyar lambar,a hankali ya d'auki wayan ya shiga dubawa duk da jikinta da ya d'anyi sanyi "Little sister" ya gani,da sauri ya bud'e ya shiga duba sak'on dan yasan daga inda sak'on yake,sak'on da aka turo mata ne na d'azun ta b'oyayyiyar lambar tayi masa forward nasa,cikin tsananin mamaki ya gama duba sak'on kafin ya murza fuskarsa ya shiga neman line nata,sai dai har wayan ya katse bata d'auka ba,sake kira yayi can wayan yana daf da katsewa ta d'auka da sallama tana fad'in "Allah ya taimaki Babban yaya..?" Saurin katseta yayi da fad'in "Yaushe aka turo miki wannan sak'on..??" "Yanzun ne babu jimawa..amma naga alamun number babu suna,kuma nayi k'ok'arin tambayan waye sai dai text ena yak'i tafiya." "Na sani bazai tafi ba,yanzun abunda nake so dake shi ne..Ko da za'a kira ki da number ko aci gaba da turo miki sak'o kada ki kuskura ki d'auka,nd duk text en da za'a turo miki kada ya baki tsoro kin gane ko..??" "Ehh! Na fahimta.." "Ok..! Shi kenan sai munyi magana.." Cikin sanyi ta amsa da to sannan suka yi hanging kiran,juyowan da Yaseer zai yi idanunsa karaf suka sauka akan yazeed daya kafe shi da ido,iska ya shak'a sannan ya juya zai bar wajen,saurin rik'o shi yazeed yayi yana kallonsa "Mene kake magana akansa a waya..??" "Nothing bro..!" "Wollahi k'arya ne akwai wani abu.." "Noo! Bro Bafa wani abu ne mai muhimmanci ba,ka dena damuwa mana.." "Ohh!! Koh..? Ba shi da muhimmanci kake cewa kada a damu.?? Look Yaseer ya kamata ka sanar dani abunda ke faruwa.?? Ka san bazan iya juran naga ka shiga matsala ba ko.??" "Haba mana..! Ka yarda dani babu komai na fad'a maka.." "Shi kenan na yarda babu,amma ita wannan yarinyar wace ce..? Kuma mene ne alak'arka da ita da take kiranka,shima zaka cemin babu ne.." "Dan Allah bro ka bar maganar nan,na fad'a maka babu³ me yasa bazaka yarda ba..??" Shiru yazeed en yayi kawai yana kallon yadda Yaseer yake magana,a hankali ya jinjina kai sannan ya furta "It's ok ..na yarda babu,shi kenan...???" Komawa Yaseer yayi kan one seater ya zauna yana yin baya ya kwantar da bayansa a jikin seat en had'e da rufe idanu,fuskarsa da zuciyarsa duka d'auke da damuwa... ^^^^^ *PRISON...* Yadda captain ta gama mulke musu jiki da gishiri haka ta tusasu a gaba suka duk'ufa kan aiki babu ji bare gani,tun suna kukan gajiya da azaba,har suka zage suka dumfari aiki babu ji bare gani,da ganin yadda suke aikin kasan ba don suna yin aikin da k'warewa bane,a'a sai dan kawai ya zama dole ne akansu kuma su d'in ne za suyi shi,suna aiki Aisha naci gaba da sharar kwalla saboda rashin sabo da irin wannan aiki amma a haka sukayi ta fama dan gudun janyowa kansu jarfar captain.... Kwanakin su Aisha sun fara gangarawa a cikin gidan,haka kullum rana da zata fito ta fad'i suke cikin wahala da aikatawa tamkar bayi,kimanin watansu guda da zuwa gidan amma ko kad'an basu tab'a ganin wani ba bare suyi tunanin cewa yau ga wani ya tuna da su ya kawo musu ziyara,kullum iya abincin gidan shi ne abunda suke iya samu,zuwa wannan lokaci rayuwa gaba d'aya ta juya musu baya,zamansu a gidan ya dad'a sawa jikin su da duk wani lamari da suka bari a baya ya zama tarihi a garesu. Captain ce ta shigo cikin d'akin da ganinta kasan ba zuwan mutunci tayi ba,nan take ganinta yasa jikin Aisha ya fara kyarma tamkar taga wani sabon muridi,tsaye ta mik'e tana goya hannunta a baya,dan ta riga ta san ganin captain a gurinta ba alkhairi bane a iya tsohon wannan lokacin,harara captain ta watsa mata kafin ta kalli Ladidi tana fad'in "Kunyi bak'uwa..." Cike da mamaki ita kanta Ladidin ta kalleta tana tambayar captain "Captain mu kuma ake nema..?" "To dafa...?? Idan baku nake nufi ba uban waye nake nufi..??" "Kiyi hak'uri Aunty..." Waigawa tayi ga Aisha data k'ame kamar gunki "Ke wollahi ki shiga hankalinki,shegiya mai zubin makirai..." Kan Aisha a k'asa tana k'ifta idanu dan yadda take tsoron captain a rayuwarta sam bata tab'a jin tsoron wata halitta fiye da haka ba "Ni dallah ku wuce muje kuna b'atan lokaci.." Sum² suka mik'e suka bita,har zuwa inda ake ganawa da masu kawo ziyaran,sai da suka zauna sannan captain ta fita ta barsu su biyu a cikin gurin kowannensu zuciya cike da rauni da damuwa,suna nan zaune sunyi jugum² suna jiran ganin wanda zai shigo,aka turo k'ofar aka shigo,k'aran takalmin da yake tashi yasa su d'agowa suka juya dan ganin waye mai shigowar,ai a firgice Ladidi ta mik'e tsaye zumbur tana fad'in "Ke ce................???" *"ADDA* Kece...??" Abunda ya fito daga bakin Ladidi kenan tana sake kallon matar data kira da Addan,kafin ta fashe da kuka,a yanayi na mai sunan da ladidi ta ambata daka kalleta zaka tabbatar ba k'aramar mace bace,ilahirin jiki da fuskarta d'auke yake da ado,ko ina a jikinta zallar jan k'arfe ne (gold) sai shek'i yake da d'aukan ido,sam matar a yanayinta da zubinta bata yi kama da talaka ba,yadda suka zuba mata ido suna kallonta cike da sha'awa haka itama ta kafesu da ido tana kallon ikon Allah da mamakin yadda taga sun koma,hakan sai yasa ta tsayawa kawai tana sake binsu da kallo mai kama dana tausayi,a hankali ta kama Ladidi dake neman zubewa k'asa ta zaunar sannan ta rik'o Aisha tana kallonta kamar zata mata kuka itama ta zaunar,sannan ne itama ta iya d'osana nata mazaunan akan stool en,ta jima tana kallonsu kafin ta iya jan dogon numfashi "Yanzun Ladidi meya kaiki aikata wannan al'amarin..? Shin biyan ku za'ayi ko akayi..??" Sunkuyar da kai Ladidi tayi k'asa ta kasa magana,ko da ganin haka sai yasa adda girgiza kai,cike da takaici taci gaba da magana cikin wata irin murya "Gaskiya banji dad'in faruwar wannan lamarin ba gaba d'aya,shin yanzun waye gari ya waya..? Fisabilillahi banda kawai kin rasa mafad'i shi yasa kika biyewa son zuciyar ki,da shegen son kud'in ki na masifa yasa kika jefa rayuwar yarinya k'arama cikin masifa..duka Aisha shekarunta nawa ne da har zata aikata laifi makamancin wannan har ya janyo mata d'auri.." Kan Ladidi a k'asa idanun nan nata sun dad'a fitowa ta san yau kam saita Allah tunda Adda taji maganar nan,babu abunda zai hana bata mata wankin babban bargo ba,Aisha kuwa tunda Adda ta zaunar da ita banda kuka babu abunda take dan yadda Adda ke yiwa Ladidi fad'an jefata a uku da tayi "Dan Allah adda kiyi hak'uri, wollahi duka al'amarin nan ya faru ne ta yadda idan har ba bayani nayi miki ba baza ki tab'a fahimta ta ba,mu kanmu wollahi wannan al'amarin ba muyu zaton zai zo mana a haka ba,sam ba yadda kike zato bane,ki yarda dani Adda wollahi babu laifinmu.."1 "Haba Ladidi taya za'ayi na yarda dake bayan nafi kowa sanin halinki,nifa nan nina raineki,shin akwai wani abu da zaki b'oye min..?? Yadda nasanki bana tunanin akwai wani da zai iya bayyana fiye da abunda na sani a kanki..yanzun ma duk ba wannan ba,tunda al'amarin ya faru wa kika sanarwa..??" Shiru tayi tana sauraron me Ladidi zata fad'a amma itanma sai tayi mata shiru "Tambayar kifa nake kin sani a gaba kinmin shiru.." "Ban fad'awa kowa ba Adda..!" "Kin gani ba..irin wannan halin naki na nunk'ufurci,abu na damunki amma baza ki tab'a iya fad'awa kowa ba...yanzun da ban samu labari ba yaya kenan..?? Haka zaku yita zama a wannan gidan cikin azaba,kalli yadda kuka koma cikin wata guda duk wahala na neman maida ku iyayena,ni da na fiku jimawa a duniyar banyi tsofan da kuke neman yi ba..." "Kiyi hak'uri Adda in sha Allah haka ba zai kuma faruwa ba da yardar Allah.." "Ai zancen kicema bazai kuma faruwa ba bai taso ba,tunda dai wannan ya faru idan har kina da hankali zaki kiyaye faruwar haka nan gaba...Tun ba yanzun ba nasha gargad'inki da shiga abunda babu ruwanki amma kika k'i ji,yanzun da bana duniyar ma ban san me zai faru daku ba kuma...Allah ya kiyaye gaba ni kam shi ne zan iya fad'a.." Shigowar captain a dai² lokacin yasa Adda mik'ewa ta d'auki jakarta ta sab'a sannan ta kalli captain tana mata murmushi "Captain zamuyi magana ta waya in sha Allah, amma ina so a dunga kula min da su,wannan y'ata ce,ita kuma wannan y'arta ce..bana son wani abu ya samesu.." Dariya captain tayi mata tana fad'in "Hajiya Adda in sha Allah kamar yadda kika fad'a za ayi miki hakan,ai ke ce,kin fi k'arfin hakka a gurin mu,ke en ta daban ce kuma kinfi k'arfin a wulak'anta ki...Daga yau kam babu wani abu da zai sake faruwa da su.." "Godiya nake captain sai kinga aiken ki.." "Hajiya Adda nima ina matuk'ar godiya..ai tun farkoma dan ban san jininki bane da tuni na sanar dake.." Mamaki ne ya cika Ladidi da Aisha ganin yadda captain ta saki fuska har tana iya dariya a gaban su,bayan sunyi sallama da Adda ta shaida musu sai ta sake dawowa ganinsu,tare suka fita da captain saboda sak'on su Ladidi da zata bata,su kuma captain en tasa wata abokiyar aikinta ta maida su ciki,haka suka yi ta bin Adda da idanu yayin da suke jin zuciyoyinsu kamar zasu fashe dan damuwa da k'uncin daya cika su. Bayan komawarsu cikin d'aki da tafiyar Adda,captain ta shigo ta iske su a d'akin bakinta har kunne ta kallesu "Muje ku karb'i kayan ku da aka kawo muku ko..??" Amsawa suka yi sannan suka mik'e jiki babu k'wari suka bi bayanta har zuwa inda aka ajiye kayan,sanda suka isa gurin ganin irin adadin abunda Adda ta kawo musu nan take Ladidi ta fashe da kuka,Niko dai ina gefe nace ko kukan me take haka Ohoo mata... ^^^^^ Tun daga wannan rana da sak'on ya fad'o wayar jeeddah bayan ta turawa Yaseer sai ba'a sake tura mata makamancin sak'on ba,haka ba'a sake nemanta ba kamar yadda Yaseer en yayi zaton za'a ci gaba da turowar ba,haka shima tun daga sak'on na k'arshe da aka turo masa bayan fitowar yazeed ba'a sake tura masa ba,wannan yasa hankalinsa yake kwance ko dan dama can abun bai wani tada masa da hankali sosai ba,sai dai a duk lokacin daya tuna bai san mai turowar bane yakan ji rashin nutsuwa coz yasan tunda ake iya aiko masa da irin wannan sak'on mai turowar a shirye yake da ako wane lokaci ya cutar da shi.Babu wanda ya sanarwa da matsalar da yake fuskanta,haka yaja bakinsa yayi shiru har zuwa tsawon wannan lokaci. Kamar kullum suna zaune tare da Yazeed en a parlor cikin b'angarensu akayi knocking k'ofar shigowa,batare da damuwa ba YASEER ya bada izinin shigowa,drink ne saman plate a cikin cup guda d'aya bawan ya shigo da shi,tun kafin ya k'arasa ajiyewa YASEER ya zuba masa idoko da ganin ya ajiye kusa da YAZEED tun kafin ya kaiga yin magana YAZEED en ya mik'e ya fita da waya a hannunsa yana sata a kunne,haka nan yaji bai aminta da lemon da aka kawo ba,yadda aka kawo shi guda d'aya bayan ansan su biyu ne a gurin,yasan matuk'ar YAZEED en ne ya bada order akawo bazai tab'a sawa a kawo masa shi d'aya ba alhalin suna tare,kuma koda daga cikin gida aka aiko babu yadda za'ayi a kawo guda d'aya coz ansan dole ne suna tare,saurin kallon bawan yayi dai² lokacin da yake k'ok'arin fita "Waye ya baka order kawo drinks...??" Shiru yayi yana daga tsaye a inda yake ya juyo had'e da sauke kansa k'asa saboda rashin sanin takamaiman abunda zai fad'a,yadda YASEER yake kula da motsin bawan nan take ya shiga hakaito wani lamari a tattare da shi,da sauri ya mik'e zaune yana masa tsawa da tambayar waya sashi ya kawo,jin yadda yake masa magana yasa shi yin magana "Afuwaan..! Yallab'ai YAZEED ne yace a kawo masa.." Wani kallon rainin wayo yayi masa maganrsa cike da rainin hankali ya furta "Yaushe kenan..??" In-ina bawan ya fara sai kame ² yake,yace d'azu yace yanzun,sam ya rasa kalmar kamawa,a fusace YASEER ya mik'e tsaye ya kalleshi yana kama waist da nufi inda yake tsaye yana cewa "Zaka min bayanin wanda yasa ka kawo ko kuwa saina sa an d'aureka zaka fad'a..??" Jikinsa ne ya d'auki tsuma jin an ambaci d'auri nan take murya na b'ari ya shiga bashi hak'uri "Dan Allah Yallab'ai kayi min rai wollahi sani aka yi na kawo..." "Uban waye ya turoka ka kawo mana nan..kuma wa akace ka kawowa..??" "Wollahi Yallab'ai zan fad'a maka gaskiya..Wani ne ya bani shi yanzun a hanyan zuwa nan yace na kawowa yarima YAZEED kuma na tabbatar ya sha kafin na bar gurin.." Ai jin wannan batu nan take ran YASEER ya sake b'aci,nan ya auno wata uwar ashar da baima san ya akayi yayi saving enta ba "Kai kuma saboda gaka wawa baka yi tunanin me zai faru ba ka karb'a ka taho kawo masa ko...?? Shin baka yi tunanin waye ya aikoka ba..? Ko kuwa baka san za'a iya cutar dashi ba.? An baka abu kawai ka karb'a ka kawo..." "Dan Allah Yallab'ai kayi min rai wollahi bani da masaniya akan komai..Ni ban san shi ba Yallab'ai, nayi zaton cikin sababbun ma'aikatan da aka kawo ne.." Yadda ya zube guiwoyinsa a k'asa duk ya had'a zufa yana yiwa YASEER magiya abun sai ya so baku tausayi,amma ga YASEER kuwa sake had'e girar sama data k'asa yayi ya kalleshi "Wannan ba abune da zaisa na d'aga maka k'afa na rabu da kai ba,laifi ne gagarumi ka aikata da yake dai² da a had'a baki da kai a cutar damu,shin dama aikin wasu kake yi a gidan nan ko kuwa...??" "Wollahi Yallab'ai ban tab'a aikata makamancin irin wannan ba,yau d'inma sab'ani aka samu,kuma ni harga Allah banyi tunanin komai ba akai shi yasa daya bani banyi zaton komai ba na karb'a.." Iya cika YASEER ya gama zuwa wuya saboda fusata,magana yake k'ok'arin yi amma kafin ya kaiga furta abunda zai fad'a k'arar shigowar sak'on ya katse shi,saurin d'auko wayan yayi dan yasan ko daga ina sak'on ya fito ya wara idanunsa akan wayan "Ka kyale wannan bawan ya tafi,bashi da masaniya akan komai,kuma ko da kasheshi zaka sa ayi babu abunda zai iya fad'a maka..idan har kai kanka kana son kwanciyar hankali ka tabbata ka karb'a ka bawa YAZEED ya sha wannan ruwan lemon da hannuna.....!" Shiru YASEER ya d'iba na tsawon wasu dak'ik'u ba tare daya iya cewa komai ba,har sai da shi kansa bawan yayi zaton idan YASEER ya juyo kansa zai iya sawa a kasheshi,ga mamakinsa kuwa lokacin da YASEER ya juyo gareshi gani yayi kawai yayi masa alama da hannu akan ya tafi,nan ya zube gaban YASEER kamar zai kwanta dan godiya,hakan da YASEER ya gani sai jikinsa ya sake yin sanyi,nan ya koma ya zauna yana goge gumin daya fara tsatstsafo masa dan tsabar damuwa akan wannan sabon tashin hankalin dake neman kunno musu kai,ya jima shiru shi kad'ai kafin YAZEED ya dawo,shigowarsa babu jimawa ga shi yariman kasancewar baisan abunda ya wakana ba,da zuwansa kawai sai ya nufi inda cup en yake ajiye ya d'auka lemon ba tare da tunanin komai ba yakai bakinsa.... ^^^^^ Tun data fito daga wanka take ta sauri tana son shiryawa ta nufi cikin gida,musamman yadda taga lokaci yaja mata sosai yau tana gida bata tatafi da wuri ba,shigartan nan dai kamar fatalwa haka tayi duka komai bak'i,sannan ta kawo nik'ab enta ta d'aura,duka shirin komai yinsa take cikin hanzari tana yi tana kallon agogo,dai² k'arfe 3:30pm ta fice a gidan ta d'auki hanyan cikin gida,sai data fara shiga gefen Fulani ta taya inno wasu aikace²n sannan ta k'arasa gefen Ummi'n YASEER,a can ta yada zango dan tasan ita ce da hadimar gefen gaba d'aya,tunda maimartaba ya d'auke ta a matsayin mai kula da YAZEED take hidima da su duka,wannan yasa tun lokacin ragamar girkin b'angaren Ummi'n ya dawo hannunta kasancewar ta mai amana da tsafta,sai data gama shirya duk wani abu da zata mata na girki da misalin k'arfe 5pm,sannan ta shirya komai a turakar ta Ummi ta gyara mata gefen sannan tayi haramar komawa gida,gurin Ummi ta nufa cike da son yi mata sallama,a nan ne Ummi take bata sak'on ta shiryawa su YASEER abincinsu sannan ta kai gefensu yau baza suzo nan ba,amsawa kawai tayi sannan ta fita tabar Ummi'n a nan cikin d'aki,bayan fitarta kitchen ta koma ta shirya komai cikin basket sannan ta d'auka ta fita ta nufi hanyan da zai kaita side en nasu,da zuwanta ko kula da door bell bata yi ba tayi knocking k'ofan da hannunta,YASEER dake zaune yaji anyi knocked dama lokacin duka ya gama shiga cikin coma dan yadda yaga YAZEED ya d'aga cup en bilhak'k'i ya dumfari bakinsa zai sha drink en,yi yayi kamar zai yunk'ura ya mik'e YAZEED en yayi saurin yi masa alama da hannu yana nufin ya zauna,cup en hannunsa ya fasa kaiwa bakinsa,ba tare daya ajiye shiba ya nufi k'ofar yana niyyan bud'ewa. Itama can a gefen jeeddah koda tayi knocked taji shiru ba'a yi magana ba,kawai sai zuciyarta ta bata ko basa nan,saboda haka ta yanke shawaran shiga kawai ta ajiye musu tasan duk inda suka je idan sun dawo zasu gani,bata gama tunanin ba tabi umarnin zuciyarta tasa hannunta jikin handle en ta murd'a k'ofar had'e da turawa ciki,bud'e k'ofan yayi dai² da isowar YAZEED gurin,har yakai hannunsa zai bud'e ita kuma jeeddah ta rigashi turo k'ofar,cikin sa'a tana turo k'ofar ta daki hannunsa da yake d'auke da cup en lemon,nan ya sub'uce daga hannunsa ya fad'i k'asa gaba d'aya ya tarwatse,daga cup en har lemon nan suka samu damar bajewa nan a bakin k'ofar. Wani kallo YAZEED yayi mata daga ita har fasashen cup en,sannan ya jaa da baya ya bar wajen,ga jeeddah kuwa ba tare data iya yin magana ba ta shiga bin wajen da kallo,jikinta duk yayi sanyi musamman yadda taga ya watso mata kallon sannan kuma ya juya ya bar wajen fuskarsa a d'aure ya shige ya barsu nan a parlour, basket en hannunta tayi saurin fara ajiyewa ta durk'usa a wajen tana shirin sa hannu a cikin fasashen kwalban,YASEER dake zaune yana kallonta kuma yaga duk abunda ya faru ya saki wani mugun murmushi had'e da cewa "Karki soma sa hannun ki a cikin wannan kwalban.." Sam bata yi zaton yana gurin ba sai maganarsa data ji,a hankali ta d'ago kanta dake sunkuye ta shiga waige²n inda zata ganshi,yana daga gurin da yake ba tare daya bari ta ganshi ba yaci gaba da magana "Ki wuce kitchen ki samo abu ki share da shi..ke naga ko gudun ki yanke hannu bakya yi,kike k'ok'arin sawa ciki salon kijiwa kanki ciwo..??" Sai lokacin ta fahimci daga inda yake magana,nan ta mik'e tana yin d'an murmushi had'e da d'age nik'ab enta tayi baya da shi,har ta shiga ta d'auko abunda zata d'auko ta dawo ta gyara gurin YAZEED bai fito ba,tsaiwa taci gaba d'ayi zuciyar ta cike da son taga fitowarsa ta bashi hak'uri dan taga yadda yanayinsa ya koma lokacin data masa ta'adin "Idan kin gama kije kawai abunki..." YASEER yayi maganar yana kallonta,a hankali itama ta d'ago ta kalleshi dan lokacin tana tsaye ne kuma tana iya ganinsa "Ina son bashi hak'uri ne,na masa laifi bai kamata na tafi ba..." "Kije kawai kada ki damu zan wakilceki idan yazo.." "Amma Babban yaya idan na tafi ai nayi rashin kunyafa..!" "A'a..! Baki yiba je abunki ni zan masa magana idan ya zo.." "Toh.." Tace sannan tayi masa godiya ta wuce ta fita jikinta duk a sab'ule dan yadda taji rashin dad'in bashi hak'uri da kanta da bata yi ba,tana fita babu jimawa shima ya dawo,ba tare daya kalli gurin da YASEER yake ba ya furta "Me kace mata ne...?" 'Dagowa yayi ya kalleshi sannan ya maida kansa akan abunda yake "Cewa nayi ta tafi.." "No..! Bashi nake nufi ba.." "Wani abu zata maka ne..??" "Tambaya kake..??" "A'a...idan ba magana nayi ba kana tsammanin mene da..??" Banza YAZEED ya masa sannan ya nemi guri ya zauna yana hararar YASEER en,ko da YASEER yaga abunda yayi k'in tanka masa yayi,zuciyar sa shi dai cike da farin ciki mara misaltuwa,shi kad'ai idan ya tuna yadda ruwan juice en ya salwanta sai yayi murmushi, zuciyar sa cike da addu'ah yana godewa Allah daya kub'utar da YAZEED daga shiga mugun tarkon da aka d'ana masa.... ^^^^^ Jeeddah kuwa bayan fitarta kasa komawa cikin gida tayi gurin Ummi'n YASEER en,haka duk take jin babu dad'i,musamman idan ta tuna da fuskarsa lokacin daya bar wajen,sai duk taji ta dad'a zargi kanta,tana tafiya tana tunane² wayanta dake mak'ale jikinta tayi vibrate,bata iya kulawa ba dan tana kan zaton ko company suka aiko mata da sak'on,dan haka har taje gida bata damu da dubawa ba dalilin zuciyarta dake nata babu dad'i,haka ta k'arashe yinin ta haka sukuku ba tare da wani cikakken kuzariba,ko Inno ma a haka ta dawo ta iske ta,sai dai bata kaiga tambayarta me yake faruwa ba ta yi mata sallama had'e da shigewa d'aki ta kwanta,sai a lokacin ne ta d'auka wayanta cike da son yin game ko zata koma dai²,tana cire key en wayan tayi arba da akwatin sak'on ganin har lokacin yana kicking yasa harta danna masa delete haka nan kuma sai tak'i bin option en da suka bata na "yes" da "no",a hankali ta bud'e duk da bata san ko sak'on na mene ne ba,tana shiga kuwa idanunta suka sauka kan wata kalma data so tada mata da hankali,cikin sauri ta zaro ido waje tana maimaita kalmar,tamkar wacce aka biyawa darasin da aka tursasata haddarsa haka ta shiga maimaitawa.............. "Ki jira ganin sakamakon abunda kika aikata mana....." Tsayawa tayi a kan kalmar ta zuba madaidaitan idanunta akai,ta maimaita kalmar ya kusa sau biyar kafin ta dawo farkon sak'on kamar yadda ta tsallake tun farko "Kin tafka babban kuskure...kin yi mana asara mafi girma,wacce baza mu iya yafe miki itaba,kamar yadda kika aikata mana ya wuce mu kirashi da kuskure,sai dai wannan karon shi ne na k'arshe da zamu ja kunnen ki..Ki jira ganin sakamakon abunda kika aikata mana...!" Idanunta ta ware akan wayar sosai,tabbas sai yanzun ta kula da b'oyayyiyar lambar da a baya aka tab'a turo mata sak'on tsoratarwar,sam ta manta da batun lambar haka tun lokacin bata ko kad'an bata tab'a kawowa ko a ranta wani abu zai sake had'ata da su a karo na biyu ba,shawaran da zuciyarta tabi inda tayi copying text en ta turawa YASEER,saboda tun wancan lokacin ya sanar da ita matuk'ar aka sake turo mata sak'on ko kiran waya to tayi hanzarin sanar da shi,mintuna biyar tsakanin tura masa sak'on kiransa ya shigo wayan nata,a hankali ta d'auka wayan ta karata a kunnenta bakinta cike da sallama,bayan ya amsata duka sai suka yima juna shiru,ko da yaji tayi shiru bata ce komai ba shima enma kuma rashin sanin dame zai fara saboda yadda jikinsa yake a sanyaye sai kawai ya furta "Wannan sak'on fa..??" Dogon numfashi ta saki kafin ta furta "Nima ban sani ba,kawai dai na ganshi a wayan yanzun dana zo bacci..." Shiru ya d'anyi yana tunani,zuwa wasu y'an dak'ik'u ya furta "Kin san dalilin da yasa aka turo sak'on..??"+ "Wollahi Babban Yaya ban sani ba,hasalima ni ban ko san su waye ne suke son shiga rayuwata ba...!" "Ba rayuwarki ke kad'ai ba,har muma ba'a bari ba,yadda ake turo miki sak'on muma gare mu haka yake..." Mamaki ne yaso kamata jin ya ambaci har suma "Yanzun Babban Yaya kana son cewa kaima ana turo maka irin wad'annan sak'onnin.??" "K'warai kuwa k'anwata,ni kaina ba'a barni ba,babban dalilin turo sak'on nasan ya samo asali ne tun daga kan matsalar YAZEED,dole ne wannan shine babban hujjar da masu turowar suke amfani da shi na son cutar damu,tarayyar da muka yi wajen bincike shi ne ya janyo miki fuskantar wannan matsala,sai dai ina tunanin kan wannan matsalar haka ina hakaito cewa duk mai turo sak'on yana yi ne badon komai ba sai dan niyyar *FANSA..."* "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Allahumma ajirna fii musibatiin wa'aklufna khairan minha...! Amma Babban Yaya nifa ina wani tunani akan matsalar.." "Ehhhenn! Fad'i abunda kike son cewa..ina sauraronki.." "Dama akan matsalar ne babban yaya,ina tunanin gaskiya anya kuwa babu sa hannun wanda yasan sirrin cikin gida kuwa...??" Dogon numfashi ya sauke,sannan ya d'an yi murmushi mai ciwo "Tabbas hakan zai iya kasancewa,sai dai rashin k'wak'wk'waran hujja dole zaisa baza muyi saurin zargin kowa ba a ciki..." "Haka ne..Addu'ah a wannan bigiren shine mafitarmu,in sha Allah koma su waye ne suke da sa hannu ciki Allah zai bayyana su mu sansu.." "In sha Allah.. Muna nan muna yi sai dai ko mu sake jajircewa.." Sun jima suna maganganu akan matsalar har ta kai ga YASEER ya kasa b'oyewa jeeddah matsalar da shima yake fuskanta,nan ya fayyacewa jeeddan komai daya danganci inda aka samo matsalar da sak'onnin da ake aiko masa tun daga ranar farko,har zuwa kan matsalar data kusa faruwa a yau,a nan ne yake cewa "Naji matuk'ar farin ciki da Allah yasa kika yi gaggawar zuwa a yau da ban san mene ne zai faru damu ba...Nayiwa Allah godiya kuma ina kanyi a dalilin zuwanki Allah ya kub'utar da ni daga fad'awa cikin wannan gagarumin matsala da aka so jefani..." Yadda yake mata maganar da duk wani damuwarsa daya warware mata ya sanar da ita sai ya bata tausayi,duka sai taga ita natama nafila akan nasa,sai da suka shafe ak'alla sama da awa biyu suna tattauna ta yadda zasu b'illowa matsalar sannan suka yi sallama suka ajiye wayan,lokacin da jeeddah ta ajiye wayan ta gyara kwanciyarta zuwa rigingine tana kallon saman roof en d'akin,nan ta fad'a duniyar tunanin matsalar dake neman kunnowa YASEER dama ita kanta kai kafin ta samu yin bacci... ^^^^^ Tun da safiyar ranar maimartaba yayi aike gefen su YASEER haka zuwa gefen Ummi akan duka yana nemansu su hallara a babban parlour,jin kiran yasa su shiga tunanin dalilin kiran na maimartaba,sai dai sam sun kasa hakaito dalilinsa nayin haka,musamman duba da yadda akan d'auki lokaci mai tsaho kafin irin haka ta faru,dalili sun riga da sun san matuk'ar ba wani abu ne mai muhimmanci ya taso ba ko kad'an maimartaba baya tab'a had'a irin wannan meeting en,haka dai duka suka hallara a parlour'n tun kafin fitowar maimartaba suka zazzauna jigum² suna sauraren fitowarsa da taradaddin abunda kunnuwansu zasu ji,sai wajen misalin k'arfe goma na safe sannan maimartaba ya k'araso cikin parlour'n,d'aya bayan d'aya suka kai gaisuwa sannan parlour'n ya d'auki shiru na wani lokaci inda duk suka tattara hankulansu suka dank'a zuwa ga maimartaba,binsu da kallo maimartaba yayi ya jinjina kai kafin yayi sallama ya fara magana da cewa "Shin ko akwai wani d'aya cikiku da zai iya bayyana min dalilin da yasa muka nemi ganinku a wannan rana...??" Amsa d'aya ce ta fito daga bakunansu,inda suka tabbatarwa maimartaba babu wanda ya sani cikinsu,cikin nutauwa da izzar mulki maimartaba ya juya ga gefen da yaseer yake ya d'an kalleshi,sannan yaci gaba da magana "Mun sani kamar yadda muke a matsayinmu na ahali guda,ba ko wabe lokaci muke irin wannan taro ba,sai lokaci zuwa lokaci a dalilin afkuwar wani al'amari da muke ganin zai kawo mana ci gaba a rayuwarmu baki d'aya...To alhamdulillah..! A wannan karon ma muna fatan wad'annan al'amura su kasance mana kamar yadda wad'ancan suka kasance mana masu dad'i..Muna son yin amfani da wannan damar wajen shaida muku Babban dalilin da yasa muka taru a wannan rana kamar yadda muka sani kowa cikinku bashi da burin daya wuce ya saurari abunda zamu bayyana muku,alal hak'ik'a kuma abisa faruwar wasu al'amura masu kyaui,duk da munsan za kuyi zaton wani abu da ban,alal hak'ik'a ba wani dalili bane daban kamar yadda kuka sani sai don sauraren ra'ayoyinku game da yaranmu akan karatu...!" YASEER ne ya d'ago kansa ya kalli YAZEED suna had'a ido YASEER en ya jinjina masa kai yana murmushi dan yasan yau kam dole ne sai maimartaba ya taso da maganar da suka tab'a yi a baya lokacin YAZEED na gidan yari,bai Ankara ba yaji maimartaba ya kama sunan sa "YASEER shin a wancan lokacin da muka yi maganar makaranta da kai kace sai kayi tunani,shin tunanin ne har yanzun baka kammala ba,ko kuwa akwai wani uzuri da kake da shi akan hakan..??" Sunkuyar da kai YASEER yayi yana sakin d'an murmushi ba tare daya iya magana ba,jin yadda maimartaba yayi shiru baice da shi komai ba ya fahimci shi yake saurare yaji abunda zai fad'a nan ya bud'e baki da kyar ya fara magana "Ina neman afuwar maimartaba akan wannan matsala da aka samu daga gare ni...!" Kafin ya kai k'arshe tuni maimartaba ya katse shi da cewa "Kai muke saurare muji hujjarka ta k'in bin umarnin mu da kayi..." Sai daya jaa numfashi sannan ya furta "Allah ya taimaki maimartaba...Gaskiya bani da wani dalili daya wuce na jiran d'an uwana...!" "Jira kumaa..??" Sauran iyayen suka ambata suna zuba idanunsu akan YASEER daya sake sunkuyar da kai k'asa "Wane irin jira ne kake masa..??" "Allah ya baka tsawon rai..kamar yadda ya kasance tun tasowarmu wani abu bai tab'a zuwa ya bambanta muba,wannan dalilin yasa ko daka min maganar karatu a baya yasa ban maida hankali akansa ba,nak'i maida hankali ne a saboda ganin cewa d'an uwana yana wani hali..wannan yasa naji bazan iya aiwatar da wani ci gaba a rayuwata ba matuk'ar bama tare,tun tasowarmu ranka ya dad'e wannan ya jima da zama burinmu,haka wanban alk'awarinmu ne da muka jima da yiwa juna alk'awarin wani abu bazai tab'a bambanta muba,shi yasa ko a lokacin da kayi maganar ranka ya dad'e na kasa bada amsa akan maganar sannan na nemi da a bani lokaci isashshe da zai bani damar yanke duk wani hukunci...Wannan shi ne dalilin Allah ya baka tsawon rai kuma ina sake neman afuwa abisa wannan kuskuren nawa..!" Murmushi kawai maimartaba yayi yana jinjina kai,dan ko kad'an baiyi tunanin haka abun yake ba sai yanzun "Amma YASEER banda shirme irin naku na yara wannan dalilin shi zai hanaka yin karatu a tun wancan lokacin..?? Matsalar yarinta kenan sam bakwa tsayawa kuyi tunanin gaba da abunda zai farj,shi kenan rashin tunani sai yasa ku kasa kawo tunanin kunyi ba dai² ba..Komai da kuka aikata kuna ganinsa dai²..." Sunkuyar da kai ya sake yi k'asa ba tare daya iya d'aga kansa ya kalli maimartaba ba har ya gama musu nasihar daya fara musu akan muhimmancin lokaci,nan a k'arshe ba Tate daya nemi shawaran suba ya yanke hukunci akan ci gaban karatun su nan bada jimawa ba. Y'an surutai ne suka fara tashi suna shawarwari tsakanin iyaye da y'ay'an akan inda yafi dacewa a turasu karatun,kafin daga bisani maimartaba ya sake yin gyaran murya alamun dake nuna musu yana buk'atar suyi shiru,shiru ne ya ratsa parlour'n cikin k'ank'anin lokaci sannan maimartaba ya sake kallonsu yana murmushi "Albishir na gaba da muke fatan sanar daku shi ne,a jiya munyi magana da HAJIYA ta kuma sanar damu in sha Allah idan har Allah ya ara mana lokaci cikin satin nan tana kan hanyar dawowa,saboda haka sai ku fara shirin dawowarta....Na sanar daku wannan nauyin ne tun yanzun saboda kada wani abu ya gifta na kasa sanar da ku abunda ya kamata ku sani...Muna fatan zaku kiyaye hakan..." Murna sosai ahalin suka fara da jin wad'annan labari daga bakin maimartaba,kafin yasa akayi addu'ah ya sallame su gaba d'aya. Haka taron ya tashi kowa na farin ciki musamman ga YAZEED dan tunda aka fara maganar da yaji abunda YASEER ya fad'a yake jin wani yanayi a tattare da shi sai dai ko bayan nan bai yi masa maganar ba saboda yasan halin YASEER en yanzun sai ya raina masa hankali har maganar ta salwanta ba zai taba tsayawa su fuskanci juna akan maganar ba,sai dai kawai ya zuba masa ido lokuta da dama dan tun a bayan fitowarsa daga gidan yarin YASEER yake ta masa abubuwan al'ajabi,dalilin da yasa k'imarsa da k'aunarsa ta sake k'aruwa a gurinsa kenan,har ma idan wani abu ya had'a su da YASEER en ya masa badaidaiba bayan al'amarin ya lafa sai yaji rashin dad'in abunda yayi masa... Kwanaki uku tsakanin maganar maimartaba da ahalin nasu sak'on isowar HAJIYA ya riskesu daga k'asa mai tsarki,yadda gidan ya kacame da shirye²n dawowarta sai mutum yayi zaton wani gagarumin biki za'ayi,ko ina na gidan an chanja masa tsari da fasali sai shek'i da d'aukan ido yake,girke² kuwa tamkar ana wani mashahurin taron da dubunan mutane zasu halarta,cikin haka Allah ya sauk'i HAJIYA a k'asar ta nigeria lafiya cike da jin dad'i da farin cikin kasancewar ta a cikin ahalinta,gefe guda aka gyara mata tare da bayin da zasu ci gaba da mata hidima,wanda a washe garin ranar dawowarta kuma maimartaba ya shirya gagarumar liyafar murna duka ta dawowarta. Kasancewarta Babbar mace dattijuwa da kowa ya kalleta zai san tana da nasaba da gidan sarautar,yasa manya da dama ak'asar suka samu damar halartar taron,cikin shiga ta alfarma kuwa ahalin suka shiga shige da fice a cikin al'ummah,ko ita kanta hajiya duk inda ta gifta banda k'arar k'arafa babu abunda mutum zai dunga ji saboda yadda sautinsu ko kad'an baya b'uya,duk da girmanta da kasancewarta mai manyan shekaru hakan sam baisa ta maida kanta tsohuwa ba kamar yadda al'ummarmu hausawa kanyi da zaran shekaru sun fara ja musu,sam hajiya bata had'a hanya da irin wadannan jama'ar ba,y'ar gayu ce itan da ko wata budurwar ba lallai ne ta nuna mata sanin me duniyar ke ciki ba. Bayan dawowar Hajiya daga k'asa mai tsarki da y'an kwanaki al'amarin tafiyar su YAZEED karatu ya taso kamar yadda maimartaba ya tsara kuma ya sanar dasu su kasance cikin shiri dan a ko wane lokaci za'a iya kiransu,haka har sanda lokaci ya gabato ko yaushe cikin shiri ake,shiri sosai maimartaba yasa aka musu,cikin hukuncin Allah kuwa a satin jirginsu ya d'aga daga 9ja zuwa k'asar ta India,inda basu sauka ko ina ba sai a birnin na BANGALORE da makarantar da zasu yi karatu take can,haka garin ya kasance daga b'angaren kudu maso yammacin k'asar ta india,a cikin wani gari da ake kira da KARNATAKA. Gida guda maimartaba yasa aka sama musu da zasu zauna dan gudanar da al'amuran da suka shafi karatun nasu ba tare da fuskantar matsala ba,a wani estate dake cikin arean HUBLI wanda aka fi sani da HUBBALI,haka maimartaba yasa aka had'a su da bayi masu yi musu hidima zuwa masu kula da al'amuransu daga nan har zuwa lokacin da zasu kammala karatun. Duk da a b'angarensu Yaseer en basu so tafiyarsu da bayin ba sai don kasancewar hakan umarni daga maimartaba yasa dole suka ja bakunansu ba tare da sun ko iya nunawa a fili ba bare su furta aji,coz sun san matuk'ar maganar ta koma ga maimartaba abunda zai biyo baya bazai musu kyau ba. Ko da saukarsu sai da suka shade ak'alla sati guda da saukarsu ba tare da sun fita ko ina ba,a cikin sati na biyu ne da zuwansu sannan suka d'auki hanyar INDIAN INSTITUTE OF SCIENCE BANGALORE,tun daga zuwansu garin cikin y'an kwanakin da suka yi yasa tuni suka fahimci yadda al'amuransu zasu kaya a k'asar dama cikin makarantar. Haka tun bayan tafiyarsu babu wani matsala ko wani abu daya sake giftawa da wasa bare ya shafi rayuwarsu ko rayuwarsu imma a cikin k'asar ko a k'asarsu ta haihuwa,cakin sha'awa da burgewa haka harkar karatunsu ta soma tafiya cike da nasarori cikin hukuncin ubangiji suka maida hankali sosai akan duk wani abu da zai kawo muau ci gaba ba tare da samun wata damuwa da zata gifta musu ba bare ta hanasu karatun ko ta tab'a rayuwarsu... ^^^^^ *A GURGUJE....* Rayuwar su Aisha a gidan yari kam ba'a iya cewa komai,izuwa wannan lokaci tuni ta d'an sauya zani,duk da bawai captain ta sawwak'e musu wahalar da suke fuskarta ba,amma zuwan Adda gurinsu ya kawo musu ci gaba,kasancewar a wannan lokaci sun d'an samu sassauci daya rage musu wani kaso cikin irin bautuwar da suke da bin duk wani doka da aka shimfid'a musu a gidan,har ta kai yanzun captain kan sakar musu fuska batun hantara zagi ko cin fuska duk babu shi,tun suna aiki cikin rashin sabo da gogewa har abun ya dawo ya zame musu jiki,ta ko wane gefe kam sun gama k'warewa da duk wani aikin wahala na gidan da za'a sasu yinsa. Kimanin watanninsu shida a gidan wanda yayi dai² da watanni biyar da y'an kwanaki da tafiyar su YASEER k'asar ta India aka sallamesu bayan Adda ta shiga lamarin nasu ta biya duk wani tarar da aka gindaya musu,nan ta kwashesu suka nufi hanyar katafaren gidan da ya kasance mallakinta a unguwar ta Lamid'o crescent,lokacin da Ladidi da Aisha suka yi arba da gidan tuni ta'adin gurin ya haddasa musu susucewa dan ko cikin mafarki basu tab'a tsammani ko hakaito rayuwarsu da kasancewar su a irin wannan gida ba bare kuma har ta kaiga sun ga hakan a zahiri.Tun a bayan Fitowarsu kuwa daga gidan kason nan Adda ta zage ta shiga basu kulawa ta musamman ba don komai ba sai dan tana buk'atar su koma cikin hayyacinsu cikin k'ank'anin lokaci............ *BAYAN SHEKARU BIYAR DA TAFIYAR SU YASEER ZUWA K'ASAR INDIA......... A gefen jeeddah kuwa tun bayan dasu YASEER suka bar k'asar take cikin yanayin kwanciyar hankali,tsakanin ta da iyayen gijinta babu wani abu na badai²ba,kullum cikin bawa kowa girma da mutuntawa take,hatta kuwa da tsakanin su bayi bata yarda ta raina wani ba,duk wanda ke sama da ita a shekaru tana k'ok'arin bashi girmansa yadda ya dace,a b'angaren aikintama haka abun yake babu wani sab'ani da suka tab'a samu da kowa,kullum cikin hidimtawa iyayen gijin nata take cike da sabo da mutuntawa,kamar yadda take jin dad'in aiki dasu haka suma kowa yake jin dad'in kasancewa da ita. Al'amarin dawowar su YASEER kuwa tun da labarin ya riski kunnuwan duka bayin gidan kowa yake nan²,a kullum rana tunda watan dawowar su ya kama cikin hidima ake a gidan,babu wani mai samun cikakken lokacin zama,haka ko wane lokaci basu suke samun lokacin komawa gida ba sai dare,yauma hakan take domin kuwa tun asubar fari bayan sun idar da sallar Asubah suka fito daga gida ita da Inno suka nufi cikin gidan,saboda k'arasa shirye²n da ba'a k'arasa ba... ^^^^^ Fitowar Adda cikin ado daga bedroom enta tana sauri yasa ni sakin baki na bita da kallo,shiga ta alfarma tun daga sama har k'asa haka ta zubata,zallar jan k'arfe kuwa kad'ai data baza a jikinta kamar idan ka kira shi zai tako da k'afarsa ya kawo kansa,a cikin katafaren parlour'n ta tsaya turus tana waige² kamar tana neman wani abu,zuwa can kuma a hankali ta saki tsaki sannan ta juya zuwa hanyan staircase, jikin reeler en ta kama tana d'an d'aga kanta sama cikin muryar k'osawa ta shiga fad'in "Aisha..! Wai kam bazaki sauko bane haka nan,kin sanfa ke nake jira ko..??" Daga can sama cikin sanyayyar muryarta ta amsa "Please..! Adda gani nan saukowa ina k'arasa shirin ne.." Siririn tsaki Adda ta kuma sannan ta juya zuwa saman cuition tana mita "Ni matsalata daku kenan ke da uwarki,duk sanda mutum ke sauri sai kun nemi b'ata masa rai da lokaci,fisabilillahi yanzun k'arfe nawa nema kuma tun yaushe na sanar dake tafiyar nan..?" Tayi maganar tana d'ago tsintsiyar hannunta dake d'aure da wani agogon sark'a k'irar Gucci "Wollahi idan baki sauko yanzun ba zaki fito ki tarar da bana nan,wannan ai iskanci ne,tun yaushe nace ki shirya amma saboda tsabar nuk'u² da yayi miki yawa kin hau sama kinyi shiru keba tsuntsuwa ba bare nace dama gadonku ne zaman sama.." K'arar takalminta yasa Adda d'agowa daga mitar da take zubawa tabi hanyar da kallo,a hankali cikin nutsuwa y'ar matashiyar budurwar da adadin shekarunta baza su wuce ashirin da uku ba take takawa tamkar bata son tafiyar,nan kuwa tsabar mamakin abunda idanunsa suka gani yasa nabita da kallo cike da son gane inda nasan mai wannan kammanin,cike da tantamar inda nasan mai wannan kamannin na bita da kallo har zuwa sanda ta tsaya a kusa da Adda,sosai na k'ureta da ido fuska cike da tsantsar mamakin gano ko wace ce itan,a fili na furta *"AISHA..!"* Waiwayowar Adda da Aisha a lokaci guda yasa ni saurin b'uya k'asan staircase gudun kada su hango ni su antaya ni waje na shiga lek'en su ta k'asa,juyawa naga sunyi a hanakali suka kama hanyar ficewa yayin da Adda ta bud'e murya da d'an k'arfi tana fad'in "Ladidi mun tafi sai mun dawo...!" Cikin sauri ta fito daga d'aki tana amsawa da fad'in "To Adda a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya.." Daga haka suka fice a gidan cikin motar da Aisha ke driven,ni dai gaba d'aya al'amuransu sun d'auremin kai musamman yadda naga Aisha da Ladidi sun koma wasu y'an gayu na ban mamaki,nasan ko ku kuka gansu a wannan lokacin dole ne kuyi mamakin yadda cikin y'an tak'aitattun shekaru suka koma,a hankali Aisha dake driven motan,cikin nutsuwa ta d'an waiwaya ta kalli Adda tana fad'in "Adda ina muka nufa...??" Ba tare da Adda ta kalleta ba saboda wayan da take pressing a hannunta ta furta *"ROYAL PALACE....!"* Wani uban brake Aisha ta taka a sakamakon jin maganar da Adda tayi,hakan kuwa ya haddasawa Adda yin gaba da baya,cikin takaici da b'acin rai bayan ta dai²ta zamanta ta kalleta "Anya Aisha kina cikin hayyacinki kuwa yau..?? Duba yada kika kusa sawa muyi hatsari daga tambaya na baki amsa.." "Sorry..! Adda." Tsaki Adda ta saki kafin ta juya tana maida wayan cikin jaka tana mita,ga Aisha kuwa tunda taji an ambaci *ROYAL PALACE* tuni ta gama sukurkucewa,nutsuwar ta tayi tsallen albarka daga jikinta ta fice ta window,suna tafe tana tunanin abunda zai kaisu masarauta bayan tunda suke da Adda bata tab'a mata maganar masarautar ba,zuciyar ta ce ta kasa nutsuwa da yawan tunane²n da take,a hankali ta sake waiwayowa ta kalli gefen Adda,muryar ta cuke da sanyi ta furta "Adda me zamu yi ne a can en..??" Ba tare da Adda ta kalleta ba ta furta "Me nace miki da zai kaimu...??" Shiru Aisha tayi ba tare data iya bawa Adda amsa ba,tunawa da abunda Adda'n tace mata za'ayi masarautar a safiyar ranar,driven take amma har lokacin ta rasa da yadda zata fassara AL'AMARIN,a haka har suka yanko takan titin da zai sada mutum da ainihin cikin gidan sarautar. Koda suka samu waje nan cikin harabar gidan suka yi parking motansu,nan suka ci gaba da takowa da k'afarsu inda suka shiga wuce manyan sorayen gidan sarautar,jikin Aisha har lokacin bai daina zikirin da yake yiba,a haka har suka k'arasa wucewa,b'angaren Hajiya suka nufa direct,tun kafin su k'arasa shiga cikin parlour'n da HAJIYA ta hango Adda ta fara bud'e baki da fara'a tana fad'in "Lale marhabun da y'ar uwa rabin jiki Adda...!" Ba Aisha kad'ai ba hatta da ni kaina da nake a bayan su sai da maganar hajiya ta daskarar dani lokaci guda naji ina neman gagara tsayawa da k'afafuna.Ga Aisha kuwa jin wannan magana ta HAJIYA nan itama ta k'ame ta kasa gaba bare baya,tsabar mamaki da zallar fargabar yadda akayi wannan dattijuwa tasan Adda shi ya hana mata samun nutsuwa,nan take wani irin zafi da gumi suka had'un mata a lokaci guda. Har Adda ta nemi guri ta zauna Aisha bata shiga cikin parlour'n ba,sai da k'yar bayan tayi yak'i da zuciyar ta da hangar jikinta sannan ta iya shiga cikin parlour'n ta nemi guri nan k'asa saman shimfid'a ta zauna,cikin ladabin da ban san lokacin data koyo shi ba ta duk'ar da kai k'asa tana fad'in "HAJIYA Barka da yamma..!" Cike da nutsuwa dattijuwar ta juyo fuskarta ta zuwa gefen da Aisha take kallo ta amsata da fad'in "Barka ka dai..Masha Allah..! Adda ina kika samo budurwa ban sani ba...??" Tayi furucin tana bin Aisha da kallo,y'ar dariya Adda tayi kafin ta kalli Aisha tana bawa HAJIYA amsa "Haba HAJIYA Aisha cefa y'ar wajen Ladidi tawa.." "Ya salaam..! Yanzun Aishar ce ta zama haka .?? Ai kam dole na kasa ganeta,dubifa yadda tayi girma..Masha Allah! Girman d'an mutum babu wuya.." Ita dai Aisha har lokacin kanta na k'asa bata d'ago ba,haka maganganunsu sai sake d'aure mata kai suke,sam ta gaza fahimtar matsayin su a wannan gidan,haka nan ta gaza fuskantar yadda akayi wannan dattijuwa ta santa... ^^^^^ *4:00pm @Malam Aminu Kano airport.* Da misalin k'arfe 4:00pm na yammacin ranar ta asabar jingin masarauta dake d'auke dasu yarima YAZEED da YASEER had'e da bayin su daya taso daga can k'asar ta India yayi dirar mikiya a k'asar tamu ta 9ja,a katafaren filin nan na tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano,tun kafin isowarsu k'asar kuwa tuni manyan motoci daga masarautar suke tsaye suna jiransu,har wasu daga cikin y'an uwama sun samu damar halartar wurin yayin da wasu ke can gida suna jiran isowarsu.Fara bayyana da bayin masarautar sukayi shi ya tabbatarmin kuma ya tabbatarwa da y'an uwa cewa suna daf da bayyana,cikin shiga ta alfarma duk da kasancewar su wad'anda suka fito daga gidan mutunci kuma mai cike da al'ada,sai dai a wannan rana kam kusan sai nace sun ajiye al'adar gefe,dan kuwa a maimakon naga sun bayyana cikin shigar al'ada kuma ta masarautar kamar sauran y'an uwa,sam sai hakan ya gagara dan kuwa a wannan rana sanye na hangosu cikin suit wacce ta amsa sunanta y'ar asali,cikin nutsuwa suka fara tako matakalar jirgin cike da nishad'i gami da shauk'i mai tattare da nutsuwar rai data hangar jiki mai cike da samun nasarori suke tafe,har suka k'arasa sakkowa murmushin dake kan fuskokinsu bai b'ace ba,yadda gurin yake shak'e da al'ummar masarauta sai yaso basu mamaki,da haka dai samu suka shige motocin dake Parke suna jiran isowarsu bayan gaggaisawa da wasu daga cikin y'an uwa,daga nan akayo musu convoy aka d'ungumo zuwa gidan sarautar. Tun daga ainihin k'ofar farko ta gidan sarautar mutum zai tabbatar da lallaifa wad'annan samari maimartaba na matuk'ar ji dasu a wannan fada,yadda aka sake k'awata fada abun har ba'a magana,su da kansu yadda suka fara ganin sauye² a gidan har sai da abun yaso basu mamaki,amma tunawa da ko waye maimartaba da yadda matsayin su yake a wajensa nan yasa mamakinsu kaucewa.Tun kafin motocin su fara tsaiwa tuni har y'an uwa da suka zo taya su murnar dawowa sun fara hallara,tsayawarsu babu jimawa aka bud'e murfin motan suka fito,nan fa y'an uwa kowa ya fara nufio su ana san barka da taya su murnan samun wannan gagarumar nasara. Da k'yar suka samu hanya suka nufi b'angaren Fulani,nan suka tarar da ita a cikin y'an uwa turakar tata babu masaka tsinke,wannan tasa koda suka gaisa basu samu damar zama mai tsayi da ita ba,suka fice suka kama hanyar b'angaren Ummi'n YASEER,can enma dai bata sauya zani ba dan yadda suka tarar da turakar Fulani haka itama nata gefen yake,koda ganin haka sai yasa su ficewa suka nufi gefen Hajiya,a can ne kad'ai suka d'an samu rangwamen al'ummah,sai kuma y'an k'annensu mata da suka samu damar kammala karatun secondry su uku,da maza mutum biyu,nan suka d'an tab'a hira kafin daga bisani suka fice zuwa sashinsu dan su samu su huta gajiya..misalin k'arfe bakwai na daren ranar kuwa,gagarumin dinner da aka shirya na murna dawowar su da tarba dake cike da zallar nuna k'auna daga maimartaba har zuwa kan sauran ilahirin ahalin nasu dole ne ya sa mutum tunani saboda yadda wannan tarba ta sha bamban da sauran irin tarbar da ni kaina na saba jin labari a gari ya faru. Katafaren d'akin taron dake cikin gidan na gwamnati,cike yake mak'il da y'an uwa da abokan arziki,kama daga masu mulki har zuwa kan masu sarauta,y'an boko gami da masu ji da kud'i duk babu wanda wannan k'ayatacciyar dinner bata tara ba,haka kowannesu yana cikin shiga ta alfarma,yadda gurin yake a tsare haka ma al'ummar gurin suke,abunku da taron masu da shi,babu wani da yake a tsaye kowa ya samu guri ya zauna abun gwanin sha'awa,ciki da wajen gurin kuwa duka tsare yake da dakarun sojoji da bayi wad'anda suka yo rakiya. Tunda aka fara gabatar da taron ake ta neman su YASEER a wajen amma abun mamakin sam babu su a gurin,haka aka ci gaba da gudanar da taron walimar amma har kimanin k'arfe takwas basu samu damar isowa ba,wannan tasa aka fara neman line su amma abun takaicin shiru duka wayoyinsu a kashe,dole tasa aka hak'ura aka zubawa sarautar Allah ido aga kuma ta inda zasu b'illo. ^^^^^ Can a masarauta kuwa abunda ya faru tun bayan isowarsu k'asar bayan da suka shige gefensu,Ummi ta bawa jeeddah izinin shirya musu abinci mai rai da lafiya ta kai musu can,dan nan en tasan bazai zaunu ba a gurinsu daga lokacin har zuwa dare lokacin daya kamata ace an tafi gurin walimar,haka jeeddah ta amsa sak'on uwar gijiyar tata sannan ta nufi hanyar kitchen en dake nan cikin b'angaren,sanda ta kammala shirya komai kamar yadda aka bata umarni ta zuzzuba cikin manyan cooler's sannan ta d'auka ta nufi hanyar kaiwa sashen nasu,cikin sa'a kuwa harta kammala shirya komai ta fito a gefen bata had'u da kowa ba,a haka ta fice ta kulle musu gurin sannan ta koma ta sanarwa da Ummi ta shirya komai kamar yadda ta umarta,sannu ta mata sannan ta bata izinin tafiya gida ta shirya itama coz tana son ta halarci gurin taron kamar kowa na ahalinsu,amsawa tayi bayan tama Ummi'n sallama ta kama hanyar gida abunta. ^^^^^ Tsabar nemansu da neman wayoyinsu da ake ba'a samu yasa ran maimartaba da mahaifin YASEER b'aci,maimartaba cikin takaicin rashin halartar taron da wuri dasu YASEER basu yiba ya kalli d'an uwan nasa yana masa magana k'asa² "Shin mene ne labari game da rashin halartar yarannan wannan taron da basu yiba..??" Cikin girmamawa Abban na YASEER ya bawa sarki amsa "Allah ya baka tsawon rai..ko kad'an bani da masaniyar dalilin daya hanasu isowa har yanzun.." Jinjina kai maimartaba yayi kafin ya furta "A kirasu a waya a tambayesu hujjar da tasa zasu ajiye mu anan muna jiransu,shin mune iyayen ko kuwa su ne..??"2 "Ayi musu afuwa ranka ya dad'e bada nufi suka yiba...In sha Allah kuma hakan bazai sake faruwa ba.." Ba tare da maimartaba ya sake yin magana ba ya jinjina kai,ga Abban YASEER wato GALADIMA kenan,ba tare daya sake yin magana ba shima,ya shiga k'ok'arin bin line YASEER,jin line a rufe yasa shi ya gwada kiran na YAZEED amma abun k'arin haushin shine shi enma nasa line a rufen yake,har yayi niyyan sanar da maimartaba halin da ake ciki sai kawai ya fasa ya shiga neman line Ummi kasancewar ita da Fulani suna gida ransa a mugun b'ace,tana d'auka kuwa taji muryansa cikin b'acin rai yana tambayar ta su YASEER,rashin sanin takamaiman amsar da zata bayar yasa tayi shiru,ai kuwa nan GALADIMA yayi ta fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba tamkar ita tayi laifin haka yayita mata fad'a,hak'uri tayita bashi tunda taji fad'an yayi yawa,da k'yar ya hak'ura yayi shiru sannan ya kashe wayan shima sai da tace masa zata sa a duba side ensu a gano ko lafiya sannan ya kashe wayan,lokacin daya kashe tana ajiye wayan ta saki wani ajiyar zuciya,nan tasa aka kira mata wani cikin bayin dake gefen ta,lokacin daya iso ta juyo da niyyar aiken su je su duba mata ko su YASEER en suna can,sai ga jeeddah ta shigo fuskar nan sakaye cikin nik'ab tayi sallama,fasawa Ummi'n tayi ta sallame su sannan ta juya ga jeeddan ta kirata ta bata umarnin taje ta dubo mata sashen nasu YAZEED ko lafiya aketa kiransu wayoyinsu a kashe kuma ba'a san a wane hali suke ba.Amsawa tayi cike da ladabi sannan ta fice ta kama hanyar gefen nasu cikin sauri ganin yadda gidan yake babu mutane sosai sai dakaru masu tsaron gidan ta kowane lungu da sak'o. Har ta k'araso bakin sashen nasu bata ji alamun motsin mutum a cikiba,har ta juya zata koma ta hangi haske a cikin parlour'n ta tsakanin curtains da sauri ta koma ta shiga knocking k'ofar tana jiran a bud'e ta isar da sak'on Ummi,ta d'auki kimanin mintuna goma tsaye a gurin ba tare da an bud'e mata k'ofar ba,hakan yasa ta fara tunanin ko lafiya hakan ya faru..?? Sake juyawa tayi zata koma nan take wata zuciyar ta bata shawarar shiga ta duba halin da ake ciki,da saurinta ta dawo zuciyar ta na skipping ta kama handle en k'ofar ta tura ciki,koda k'ofar ta bud'e nan tabi sahun k'ofar zuwa ciki bakinta d'auke da sallama kafin ta shiga kiransu "Babban Yaya...! Yallab'ai..!!" Shirun data ji yasa ta tunanin anya kuwa suna nan..!? Zuciyarta ce ta bata amsa "Shin idan basa nan me zaisa wutan side en ya kasance a kunne..??" Shiru tayi tana daga tsaye a bakin k'ofar kafin taci gaba da takowa cikin parlour'n tana fad'in "Akwai wani anan da yake jina..??" Nanma shiru taji,tad'an d'ebi wasu dak'ik'u a wajen,ko da jin shirun ya soma yawa sai kawai taci gaba da waige² tana nemansu,can daga tsakiyar cuitions en parlour'n idanunta suka hango mata su a baje a k'asa kan carpet suna kwasar bacci abun su,hakan yasa ta dafe kai tana sakin ajiyar zuciya sannan ta k'arasa kusa da YASEER tana kiran sunansa,cikin magagin bacci ya d'ago murya na season ya kalleta yana sakin murmushi da fad'in "K'anwata kece...??" "Ehh! Babban Yaya nice..Ummi na son ganinku yanzun.." Komawa yayi ya sake kwantar da kansa cikin muryar bacci ya furta "Kice mata ba yanzun ba.." "Amma fa Babban Yaya tace yanzun take son ganinku Maimartaba yayo aiken a duba lafiya baku samu halartar taron ba.." "Ke..! Kije kice mata ba yanzun ba..!" Yadda yayi maganar cikin d'an d'aga murya yasa ta marairaicewa "Ammafa Babban Yaya sak'on na maimartaba ne.." "Heeyyy!! Young lady aje ace masa shima nace ya bari ba yanzun ba..!" Zaro ido jeeddah tayi waje tana fad'in "Babban Yaya maimartaba fa nace maka.." "Shi en nake nufi nima..ko aka ce miki ban san me nake fad'a ba...??" Yadda ya juyo saitinta yana magana yasa tayi saurin mik'ewa tana ja da baya musamman taji jikinta ya shiga bada wani yanayi da bata tab'a jin makamancin irin sa ba,haka nan maganar daya fad'a yace a fad'awa maimartaba sai ta shiga kai kawo a cikin zuciyarta,kallonsa ta sake yi sannan ta shiga maimaita ta har a fili................

0 Comments