WANI ALAMARI CHAPTER 2

WANI ALAMARI CHAPTER 2
Shiganta gida bayan ta sanar da inno dawowarsu ta fad'a d'aki ta kwanta,take sababbin hawaye suka shiga sake tsere a fuskarta,sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta zauna tana gyara fuskarta zuciyarta cike da son zuwa wani waje,sake shiryawa tayi sannan ta fito tana cewa inno taje gidansu Aina'u amma ba jimawa za tayi ba yanzun zata dawo,amsa mata da to tayi nan tasa kai ta fice zuciyarta cike da taradaddin abunda zata tarar a inda zuciyarta ke k'iyasta mata taje. Fitowarta daga gidan ta d'an tsaya a soro tana mak'ale y'ar wayar da yarima ya kawo mata,sannan ta fice ta mik'i hanyar gidan su Aisha,tana tafiya tana tunano halin da yarima yazeed yake ciki da haka ta k'arasa,da sallama ta shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gida dan haka sai ta k'arasa bakin k'ofar d'akin su tana sake yin sallama,Ladidi dake kishingid'e daga ita sai d'aurin k'irji ta d'ago tana amsa mata,tana binta da kallon rashin sani,sakin fuska tayi bayan ta shiga cike da ladabin da bata yi niyyan yiwa ladidin ba saboda tsabar tsanarta da take ji aranta wacce take taso mata haka kawai daga can k'asan zuciyarta,ita kuwa ladidi yadda taga jeeddah ta sunkuya cikin ladabi tana gaisheta sai taji Yarinya ta burgeta,haka ta amsa tana ta bin jeeddan da kallo. "Aisha tana nan..?" Jeeddah tayi tambayar,da y'ar dariya Ladidi ta girgiza mata kai "Ayyahh! Wollahi na aiketa amma ba jimawa za tayiba zata dawo..ko zaki jirtaa..?" "To babu komai bari na jira tunda bata yi nisa ba.." Shiru suka yi na d'an wani lokaci ita kuwa jeeddah sai wasa take da yatsun hannunta,ga Ladidi kuwa tun da jeeddan tayi shiru lokaci zuwa lokaci sai ta d'ago ta d'an saci kallonta tayi murmushi kamar mai matsalar kai,can zuwa jimawa kamar wacce aka matsa ta ladidin ta sake kallonta tana cewa "Y'an nan mene ne sunan ki..?" Sai data d'ago tayi mata murmushi sannan ta bata amsa "Suna na Hawwa'u amma da jeeddah ake kirana.." "Allah sarki sunan manya gareki,ya mamarki take..?" "Tana nan lafiya.." Ta bata amsa a tak'aice tana juyar da kanta zuwa gefe,cikin zuciyarta ko fad'i take "Kuji mata da fi'ili sai kace tasan mamar tawa har da wani tambayata ya take.." A zahiri kuwa ko data waigo suka had'a ido sai tayi murmushin yak'e,daga haka babu wanda ya sake cewa komai,sun jima zaune shiru sannan Aisha ta dawo,tun kafin ta shigo d'akin Ladidi take ta faman rafka mata kira "Shatu maza kiyi sauri ga jeeddah tazo tun d'azun bakya nan.." Kallon Ladidi jeeddah ta tsaya yi jin yadda tayi caraf kamar wacce aka matsa ta fad'a,wani haushin Ladidin ne ya sake kamata har ta banka mata hararar da bata sanma tayi ba,itama Aishar kamar an cillota ta fad'o d'akin tana tambayar "Tana ina Baba..?" "Gata nan zaune sai jiranki take ke kuma daga aikenki kinje kinyi zamanki,kamar na aiki bawa garinsu..ni kawo min aiken nan.." "Kiyi hak'uri Baba wollahi shi ne mai shagon bashi da hanzari tun d'azun dana je sai yanzun nefa ya sallame ni.." "Iyyy! ai dama haka kullum na aikeki zaki dawo kice,mak'aryaciya kawai,ni dallah bani ki matsamin anan kafin na mangareki.." Kasak'e jeeddah tayi tana kallon yadda Ladidi ke zubawa Aishar masifa,haushin daya cika tane yasa ta mik'ewa tana fad'in "Aisha tafiya zanyi nacewa da inno bazan dad'e ba dama kuma tun d'azun nake ta jiranki.." "Kai dan Allah ke kuwa ki d'an zauna mana..sai na raka ki." "A'a wollahi idan taga ban komaba yanzun zata min fad'a shi yasa zan tafi.." "To shi kenan muje na rakaki.." Sallama ta yiwa Ladidi sannan ta fita ta zura takalminta,muryar Ladidin ta juyo tana bata sallahun ta gaida mamanta,ita kuwa tace to kawai tasa kai ta fice ita da Aisha, suna cikin tafiya dukansu sunyi shiru jeeddah ta saci kallom Aishar ta gefen ido,da sauri ta juyo ta kalleta fuskarta da d'an tsoro "Laaa! Aisha kin san kuwa jiya dana tafi gida wollahi wannan mahaukaci/aljanin sai daya biyo ni,ai in baki labari ni wollahi abunda yayi min ma har yafi naki,kin san wani abuma daya min ya k'ara min tsoro..? Wollahi har naje line gidan mu bansan yana bina ba sai dana je zan shiga gida naji an rik'eni...Ya matsemin wuya wai saina fad'a masa abunda na sani akan k'aryar da kikayi a fada,dana ce ban sani ba,shine ya cillani jikin bango karkiji yadda na bugu,wollahi ko dan bakiga yadda yamin ba amma da kin tausayamin a jiyan nan kin fad'a min abunda yake cewa kije ki fad'a,ai zaki fad'an ko..?" Shiru tayi tana turning fuskarta zuwa kalar tausayi,shiru Aishar tayi tana tunani fuskarta ta rikid'a zuwa wani irin yanayi,koda ganin haka ai da sauri jeeddah tasa hannu ta matsa wayar dama tana dai² b'angaren recorder "Gaskiya ko jeeddah ni bazan iya fad'a miki ba yanzun,kinga ko ki manta da wannan maganar dan ni babuma abunda na sani akan abun kawai wannan mahaukacin yanayin haka ne amma ni ban sanshi ba,ban tab'a ganinsa ba sai jiya,to wace gaskiyace zan fad'a muku,ni babu wani abu dana sani bare na fad'a miki...Ki gaida gida sai anjima kada baba taga na jima yanzunma tamin fad'a.." Tana fad'ar haka ta juya da sauri tabar wajen jikinta duk alamun tsoro ya bayyana a tattare da ita,binta jeeddah tayi da ido tana jinjina kai had'e da sakin wani murmushi mai ciwo,sai data daina hangenta sannan ta juya tana magana da kanta "Zan saki fad'ar gaskiya wata rana da izinin Allah ko kina so bakya so,imma kin amince ko baki amince ba,wannan alk'awari na ne saina tursasaki kin fad'a a gaban jama'ar da kika yi k'arya a wancan lokacin..." Hanyar gida ta kama itama tana tafiya tana tunanin hanyar daya kamata ta bi wajen tursasa Aishar ta fad'a mata duk abunda ta sani,yayin da a ko wane motsawar second take jin tayi loosing duk wani hope,karo na farko kenan da zuciyarta ta k'iyasta mata ta rasa duk wata dama... Tun daga wannan ranar da taje gidansu Aisha'n bayan rabuwarsu sai ta fara ganin sauyi daga gurin ita Aishar,haka alak'arsu da juna ta fara jaa baya,ko gaisawa ba sosai suke yinta ba,hasalima duk sanda Aishar zata ganta saita canja hanya,abun duniya duk ya taru yayiwa jeeddah yawa gashi kullum cikin sa rai take da fatan binciko gaskiyar da zata taimaka musu wajen ganin an fito da yarima daga gidan kangararrun yaran,amma abu yaci tura duk wata hanya da zasu kama sai ta nemi sub'uce musu,dama kuma akan Aishar suke da sa rai idan har ta fad'a musu abunda ta sani shi ne zai bada damar a sake shi,bayan wannan kuwa babu wata shaida da suke da ita,wannan yasa suka tattara komai suka mik'awa ubangiji dan sun san shi ne mai ikon yin komai,hakka addu'ah kullum cikin yinta suke akan Allah ya basu dama da zasu sake yin nasara,saboda yak'inin da suka gina zuk'atansu akai matuk'ar suka gabatar da ita a matsayin shaida da suke da ita sun san nasarar da suke nema ta samu,sai dai a yanzun suna ganin komai ya zama tarihi saboda ita Aishar ma ko zama inda jeeddah take ta daina yi,wannan rashin k'arfin guiwa yasa su tattara komai suka ajiye tare da sa ran wata rana ubangiji zai sake kawo musu mafita cikin sauk'i da tafi ta baya... *5 YEAR'S LATER...* Fitowarta daga d'akin girkinsu kenan tana ta sauri zata shiga wanka Aisha ta shigo gidan kamar an cillota tana ta haki,juyawa jeeddah tayi ta kalleta fuskarta cike da tsantsar mamaki dan rabon data ganta har ta manta bare kuma tazo gidansu,idan ko har bazata manta ba kuma zata iya tunawa rabo da su sake had'uwa tun ranar da suka rabu da juna a wani zuwa da tayi gurinta wanda ak'alla yau kimanin shekaru biyar kenan babu y'an watanni. Juyawa tayi ta sab'i bokitin data had'a ruwa zata shiga bayan gida ba tare data sake kallon inda take ba dan ta san tsakanin su kam a yanzun babu wani mutunci bare maganar arzik'i ta had'a su,muryar Aisha ta d'aki codon kunnenta dai² lokacin da take k'ok'arin shiga bayan gidan "Dan Allah jeeddah ki dakata kafin ki shiga kuyi magana,wollahi akwai wani muhimmin sak'o dana zo na sanar dake a yanzun..." Ba tare data juyo ba ta furta "Bani da lokacin sauraren k'arairayinki a yanzun,Aisha ke kanki ki san da haka,saboda haka zan iya cewa ki gaida gida..." "Wollahi jeeddah ba wasa ya kawoni gurin ki ba,muhimmiyar maganar dana ce miki ita ta kawoni kuma ita nazo muyi dake,amma ina so ki saurara yanzun kiji ko da kuwa hakan yana nufin baza ki sake saurarena ba har abada.." Waigowa jeeddan tayi cikin cushi ta kalleta tana dire bokitin hannunta,cike da masifa tana d'aga harshe ta furta "Na fad'a miki bani da lokacin da zan tsaya sauraren kalaman mutumin da yake mak'aryaci,macuci kuma maha'inci,azzalumi da babu abunda ke zuciyarsa illa zallar cutarwa...Shin Aisha kina ganin akwai wani abu daya rage ki sanar dani wanda ban riga na sani ba..? Uhmm.! Kawai kije abunki duk lokacin da kika ga dama kya iya zuwa ki bayyana gaskiya a inda kika yi k'arya a saki bawan Allah'n da bai jiba bai gani ba,tunda ku Allah baisa kuna tunawa da halin da kuka jefa bawan Allah ba.. Abun tausayi kun d'auki hakkinsa alhalin bai muku komai ba,na tabbata da ace kuna tunawa da mutuwa..Kwanciyar kabari da kuma hisabi..da ba'a kawo yanzun ba.. Sai dai na sani wannan duka ba abubuwane da zaku yi tunani akansu ba,haka ba abune da zaku yi saurin fahimtar kun aikata bisa kuskure ba,amma akwai lokaci,na tabbata lokaci zai zo da Allah zai bayyana gaskiya,abunda kuka jima kuna b'oyewa zai bayyana,amma yanzun abunda zan fad'a miki shine ina so kiyi gaggawar fita a nan gidan matuk'ar kina son kanki da lafiya,kafin na fusata na miki abunda baki tab'a tunanin zanyi ba..." "Jeeddah dan girman Allah kiyi hak'uri ki saurareni wollahi ban zo nan ba sai da nayi alk'awarin sanar miki da komai,a yau na k'udurce zan fad'a miki komai daya faru wanda har ya janyo mahaukacin nan ya dunga bina yana tsorata ni,duk da haka banjiba a lokacin nak'i fad'a,amma dan Allah ina so kiyi min alk'awarin babu wanda zaki fad'awa,sannan bazaki bari maganar ta koma kunnen Baba ba dan ina jin tsoro idan har ta san na fad'awa wani wollahi kashe ni zata yi..!" Zaro ido jeeddah tayi waje tana maimaitawa "Zata kashe kifa kika ce.? Me yasa zata kasheki..?" Hawaye Aisha ta fara cikin kuka taci gaba da magana "Saboda ta sha gayamin,ta kuma jima tana jamin kunne akan duk ranar dana bari wani yasan gaskiyar wannan Al'amarin saita kasheni ba tare da ta bar wata shaida da za'a san ita tayi hakan ba,na sani baba ba ita ta haifeni ba,amma yadda ta raineni ta kuma bani damar sake rayuwa a lokacin da aka sata ta kasheni yasa nake d'aukarta fiye da kowa dana sani nake kuma rayuwa da shi,itace uwa da ubana dana tashi na ganni tare da ita,itace komai nawa a duniyata,haka lokacin da ake k'ok'arin rabani da rayuwa ta ita tayi k'ok'arin bani kariya,wannan yasa nake jin tsoron bayyana abunda na sani gudun kada mu fad'a mugun hali daga ni har ita.Duk da ina tunanin ita kanta ba haka nan ta aikata wannan abunba,amma nasan halinta a duk lokacin da tayi niyyar aikata abu ko mene ne zata iya aikatawa,jeeddah duk yanda zan kwatanta miki mugayen halayenta wollahi ta wuce nan..." Wani sabon tashin hankalin jeeddah ta shiga jin wannan maganar daga bakin Aishar "To ke ina iyayenki suke..? Ko kuma sune suka bata ke sukace ta kashe ki..?" Girgiza kai tayi tana ci gaba da kuka "Nifa na fad'a miki bani da iyaye,hasalima ban sani ba ko ni en shegiya ce.." "Wa'iyazhu billah...! Kaii haba dan Allah ki daina fad'ar haka in sha Allah haka bazai faru ba,kema y'ace kamar kowa,ki daina cewa baki da iyaye..amma abunda ban fahimta ba idan har Ladidi zata karb'e ki ta raineki tun kina jinjira,akan me yasa su iyayen da suka haifeki basu raine ki ba,akan mene suka bata ke ta kaahe ki..? Shin duk akan mene wannan AL'AMARIN zai faru..? Me yasa iyayenki zasu aikata irin wannan kuskuren..??" "Wollahi ban sani ba nima jeeddah,tun dana taso ni dai na ganni a hannunta kuma ko sau d'aya bata tab'a nunamin wani tace shine dangina ba,hasalima kamar yadda na fad'a miki tace bata ni akayi akace ta kasheni,ganin baza ta iya ba yasa ta k'yale ni taci gaba da rainona,koma me yasa tayi haka ni ban san dalilin ta ba,haka suma wad'anda suka aikata min hakan ban san dalilin su ba...ban sani ba..!" Shiru duka suka yi zuciyoyinsu cike da tsantsar mamaki da al'ajabi "Shi kenan Aisha in sha Allah iyayenki zasu bayyana kema kinji,kada wannan ya sa kiyi tunanin aikata wani abu da zai iya janyo miki ciwo,amma ni ina da tabbacin Babarki tasan ko su waye iyayenki idan kuma har bata sani ba to wad'anda suka bata ke sun san inda iyayenki suke..." Kuka Aisha taci gaba dayi ita kuwa jeeddah sai bata baki take akan tayi hak'uri ta maida lamuranta gurin Allah shi zai bayyana mata iyayenta duk tsayin zamanin da za'a d'auka. "Kinga ko ki share hawayenki muje ciki mu zauna sai mu k'arasa maganar,in sha Allah na miki alk'awarin babu wanda zai san wannan labarin da kika bani,amma ina neman wani abu guda a gurinki.." Kallonta Aisha tayi sannan ta girgiza mata kai alamun tana jinta "Muje dai mu zauna tukuna saina sanar dake.." "Toh..!" Tace sannan suka shiga d'aki,sai data faki icon Aishar sannan ta d'auki wayarta ta kuna recording ta dawo kusa da ita ta zauna kana ta furta "Ina saurareni Aisha,idan har kina ganin aminta dani yasa kika yanke shawarar sanar dani abunda kike son fad'a na miki alk'awari babu wanda zaiji.." Kai Aishar ta girgiza cikin sanyi ta furta "Wollahi na yarda dake d'ari bisa d'ari,idan da ace ban yarda dake ba wollahi babu ta yadda za ayi yau nazo da niyyar fad'a miki wannan sirrin.." Kai itama jeeddan ta jinjina sannan ta kalleta "Idan har kin yarda dani da gaske kamar yadda kika fad'a to ina son ki fad'a min gaskiya da dalilin da yasa mahaukacin nan yake son ki fad'a yanzun.." Marairaicewa tayi kamar zata yi mata kuka hawaye kuwa har sun fara sintiri a kumatunta "Jeeddah na fad'a miki wollahi idan har na fad'a miki kasheni za tayi da gaske babu wasa..Amma na miki alk'awarin zan fad'a miki wani abu daga ciki..." "Shi kenan ki fad'a min wannan en ina sauraronki,amma ki tabbatar gaskiya zaki fad'a min kamar yadda kikayi alk'awari kin san shi alk'awari girma ne dashi da kuma had'ari muddin kika k'i cikawa to kada ki manta ubangiji bazai kyaleki ba matuk'ar baki cika ba zaki gamu da azaba na sab'a alk'awari da kika yi.." Share fuskarta tayi sannan ta girgiza kai "Kamar yadda nayi miki alk'awari tabbas zan fad'a miki gaskiya...Abunda ya faru a shekaru biyar da suka gabata,da dalilin da yasa wannan mahaukacin yake binta yana tsoratar dani naje na fad'a ba wani abu bane illah yana so naje fada na fad'a cewa duk abunda na fad'a akan yarima yazeed k'arya ne,kuma wollahi nima na tabbatar cewa a waccan ranar duk abunda baba ta fad'a k'arya ne,makamancin wannan bai faru ba,duk abubuwan data fad'a wollahi ba gaskiya bane,amma ina jin tsoron na fito na ce ba haka bane saboda na santa wollahi muguwa ce duk abunda ta fad'a zata iya aikatawa matuk'a.Gaskiya ne nayi k'arya kuma nayi shaidar abunda babu shi amma wollahi ki yarda dani dole ce tasa ni yin haka ba don son raina na aikata ba,ina rok'onki don Allah kada ki bari kowa ya san wannan sirrin,kamar yadda kika yimin alk" awari ki zama mai cikawa,kinga tun farko munyi alk'awari dake,kuma yarda ce tasa na fad'a miki wannan sirrin,dan Allah kema ki kasance mai cika naki alk'awarin..." Kai jeeddah ta jinjina kafin ta mik'e tsaye ta zare wayarta daga inda ta mak'aleta sannan ta kalli Aishar tana cewa "Gaskiya ne Aisha nayi miki alk'awari,amma a gaskiya wannan maganar ba irinta ce wacce ni jeeddah nake yin alk'awari akanta kuma na cika ba,shin bakya tunanin rayuwar bawan Allah'n da kuka jefa a masifa..? Ko kuwa saboda son kai da zuciya irin naki sai yasa bayan nasan gaskiya naci gaba da rufa miki asiri..? Shin nayi shiru na zuba ido ina gani ana cutar da shi bayan nasan gaskiya shi ne burinki..? Dole ne na fito na bayyana gaskiya ko da hakan na nufin faruwar komai,amma alk'awari d'aya zan iya yi miki,shi ne zan rok'a miki alfarma in sha Allah sunan ki bazai tab'a bayyana a matsayin wadda ta fad'a min ba,idan kuma har al'amarin ya wuce yadda muke tunani in sha Allah zanyi k'ok'arin ganin wata matsala bata same ki ba,zamu san yadda muka yi aka d'auke ki daga hannun Ladidi saboda kada ta samu damar cutar dake.." Tana fad'ar haka ta juya ta fice daga d'akin,duk kiran da Aishar ke mata ko d'aya bata amsa ba bare tasa ran zata juyo ta saurari abunda zata sake fad'a mata. Ita kuwa Aisha koda taga jeeddah ta fice daga d'akin nan tashin hankalinta ya sake k'aruwa saboda bata san ta wace hanya ce su jeeddah zasu bi su bayyana gaskiyar da suke fad'a ba........... ^ B'angaren jeeddah kuwa tunda ta shiga wanka take sakin murmushin jin dad'in da rabonta da tayi irinsa har ta kusan mantawa,cikin sauri tayi wankan ta fito cikin shirinta,a nan inda tabar Aisha zaune haka ta dawo ta isketa fuskarta cike da damuwa,ta buga tagumi da duka hannayenta biyu,bata bari sun had'u da Aishar ba sai data tabbatar ta kammala shirinta,duk shirin babu wanda ta tsaya b'ata lokaci akansa sannan ta fito cikin shiganta ta yau da kullum,kusa da Aishar ta zauna ta dafa kafad'arta,da sauri itama Aishar ta d'ago ta kalleta sannan ta marairaice mata fuska "Dan Allah jeeddah ki rufamin asiri,kamar yadda kika min alk'awari kema ki kasance mai cikawa,na miki alk'awari ni da kaina zanje fada na fad'i duk abunda kuke so,in dai zaisa a saki yarima..amma..!" "Amma me..? Ci gaba mana ina sauraronki.." "Amma ba yanzun ba..ina so ki bani lokaci,in sha Allah zanyi duk abunda kuka ce..Sai dai ina jin tsoron fitowa na fad'a a yanzun.." Wata dariyar rainin wayo jeeddah ta saki tana kallon Aisha "Aisha kenan..! Ni yanzun abunda kike so zanyi ko kuwa ni wanda nake so zanyi...? Wai ke anyama mutum ce kuwa..? Taya zan san gaskiya sannan kiyi tunanin naci gaba da b'oyewa? Shin idan na aikata haka nawa za'a biyani ko kuma nawa zan samu..?" "A'a jeeddah wannan fa ba maganar nawa za'a biyaki bane,magana ce ta salwantar rayuwa.." "Kinga Aisha bana son jin wannan maganar taki,akan taki rayuwar sai kuma muyi k'ok'arin salwantar data wani wanda baijiba bai gani ba...Kina jina koh abunda na fad'a miki kawai ki d'auke shi,na riga na fad'a miki sunan ki bazai bayyana a cikin maganar nan ba,amma kuma banyi miki alk'awarin zanyi shiru da wannan maganar ba,yanzun kawai ina son ki kama hanyar gida sannan kamar yadda muka fara ko da zamu had'u a hanya da duk inda kika san mutane za su iya zarginmu ina so ki nuna kamar baki sanni ba...wannan zai hana a zargeki a matsayin wacce ta sanarmin da wannan maganar..kin fahimta ai..?" Kai ta d'an rausayar idanunta kamar zasu fara zubar da hawaye "Shi kenan to...Amma ni dai jeeddah ina jin tsoro sosai wollahi.." 'Dan siririn tsaki jeeddan ta saki kafin ta dawo ta gabanta ta tsaya "Kinga Aisha ko kina jin tsoro ko bakya ji wannan gaskiyar dole ne ta bayyana,abu d'aya kawai zaki dage akansa kuma nima in sha Allah zan taya ki addu'ah na san ubangiji zai kub'utar dake daga dukkan wani tsananin da zaki fad'a ya kuma bayyana miki iyayenki..amma yanzun kije gida kawai sai mun sake yin magana." "Toh shi kenan jeeddah na gode... Kuma na fahimci abunda kike nufi,ni kaina ina bayani ki akan ki bayyana gaskiya ko da hakan zai yi sanadiyyar rasa tawa rayuwar,amma sak'o d'aya da zan baki shi ne..ko da ace bayan na rasa rayuwa ta,idan kuma har Allah ya bayyana mahaifana ina so ki sanar dasu cewa duk abunda suka min na yafe musu..Nima ina buk'atar su yafemin idan har nayi musu wani laifi da yasa su salwantar dani...." Tana fad'ar haka ta mik'e jikinta a sanyaye idanunta suna fidda hawaye ta fice da d'an gudunta...Binta jeeddah tayi da sauri tana son tsaida ita,amma kafin ta fito daga d'aki tuni har ta fice a gidan. Kasancewar babu kowa a gidan sai ita kad'ai hakan ya bata damar kintsawa ta fice itama bayan ta kulle gidan,sai data fito k'ofar gida ta tsaya ta k'arewa hanya kallo zuciyarta da tunanin inda ya kamata tabi,d'an tak'aitaccen tunani ta tsaya yi cikin zuciyarta take tambayar kanta "Shin yanzun ina ya kamata na nufa..? A ina zanga yarima Yaseer..?" Nan ta d'anyi shiru na wucin gadi sannan ta karkata akalarta zuwa hanyar da zata sada ta da cikin gida,tafiya kawai take tana tunanin anyama yanzun idan taje zata iya samun damar ganin yarima YASEER en kuwa..? Da wannan tunanin ta ci gaba da nausawa tana tafiya,har ta iso harabar gidan ta ratsa ta nufi hanyar da zata sadata da b'angaren mahaifiyarsa.. Har ta iso turakar Fulani tana tafe tana waiwaye ko Allah zaisa ta gamu da shi kafin ta iso amma ina ko mai kama da shi bata had'u da shi ba,d'an siririn tsaki ta saki sannan tayi sallama a bakin k'ofar shiga b'angaren,kamar kullum idan ta zo haka ta gaisheta cikin girmamawa,ita kuwa Fulani sai janta da hira take,amma ina ita jeeddan hankalinta duk baya kan abunda Fulani ke mata magana akansa,ta d'an jima a b'angaren nata har ta tambayeta ko akwai wani aiki da zata mata,shima har tayi ta gama amma bata ga ko kyallin yariman ba a gurin,sallama tayiwa Fulani akan zata tafi gida saboda yamma da tayi har ana neman fara kiraye²n sallar Maghreb,sallamarta tayi sannan ta fice tana tafiya duk guiwoyinta a sanyaye saboda damuwar rashin ganinsa. Cike da b'acin rai ta kamo hanyar dawowa gida,duk ranta tana jin babu dad'i,tana niyyan shiga soron gidansu taji an rik'o hijab enta ta baya,da sauri ta juyo dan ganin waye,fuskarsa a rufe yayi shigar nan tasa tamkar ta buzaye duk dan ya b'adda kama,wani murmushin jin dad'i ta saki sannan tayi saurin kallon hanya,yadda yaga tana lek'en bayansa yasa shi saurin sakinta tayi ciki yana biye da ita a baya,a soron suka tsaya kafin tayi magana ya rigata "Kina nemana ba..?" Mamaki maganar tasa ta bata dan bata tab'a zaton akwai wanda zai gano hakan ba "Babban Yaya ya akayi ka fahimci haka..?" "Yadda fuskarki ta nuna babu wanda bazai yi saurin fahimta ba ai..bare kuma tunda naganki a b'angaren Fulani nasan akwai maganar data kawo ki.." Fuskarta ta shiga tab'awa tana son gano abunda yake nufi,d'an murmushi yayi kafin yaci gaba "Neman me kike min ne...?" Sai da tayi d'an murmushi sannan ta furta "A k'arshe dai Allah ya nufa munyi nasara..." Kallon rashin fahimta yayi mata "Nasara akan me kenan..." "Case en yarima...." Wani kallo ya mata "case en yarima..? Wannan ai dad'ad'd'en labari ne da tun tuni muka manta da shi..." "A'a Yallab'ai bamu manta ba,mun dai hak'ura ne a dalilin rashin samun k'warin guiwa...mun hak'ura mun jingine shi a dalilin rashin shaida...Amma a yanzun zai tashi,Allah ya nufa lokacin k'ark'areshi yayi da izininsa..." Ta k'are maganar tana sakin murmushin jin dad'i,a hankali taci gaba da fad'in "Idan har kamin izini Yallab'ai zan bayyana maka dalilina na fad'ar haka a yanzun bada b'ata lokaci ba.." Kai ya iya girgiza mata ba tare daya iya yin magana ba,saboda mamakin maganar data zo masa da ita a wannan lokacin,wayar daya bata tun wancan lokacin ta ciro daga jikinta sannan ta shiga gefen data adana recording en data yi na maganarsu da Aisha tayi masa playing,duk yadda suka yi da Aisha babu abunda bai jiba,tsabar mamaki da murnar da yarima Yaseer ya tsinci kansa a ciki har baisan sanda ya zube a wajen yayi sujudush-shukur ba,bakinsa sam ya gaza rufuwa saboda tsantsar mamakin daya tsinci kansa aciki,idan ya d'ago zaiyi mata magana sai ya kasa,gaba d'aya kalmomin bakinsa sun d'auke ya gaza furta komai,tura recoding en yayi a nasa phone en sannan ya mik'a mata nata,cikin annashuwa ya furta "Ki jira kyautarki daga gareni wannan alk'awarina ne nayi miki kyauta ta musamman..." "Ranka shi dad'e ina neman afuwa a bisa abunda zan fad'a,idan har na fad'a ba daidaiba ko maganata zata b'ata maka rai ina neman afuwarka bisa hakan..." "Babu komai ki fad'a ina jinki,a yau kam kome za'a fad'a,kome za'ayimin ba lallai ne nasa shi a raina har ya b'ata min ba...saboda haka ki fad'i duk abunda kike son fad'a ina saurarenki..." "Yallab'ai dama ba akan komai nake son yin magana ba..ina nufin ina son cewa ne wannan kyautar da kace ka barshi ranka shi dad'e,ba don komai nayi wannan maganar ba sai don kawai ban cancanci hakan ba..." Wani kallo ya b'alla mata kafin ya saki murmushi "Idan na baki ki bayar ko ki yar kice bakya so.." "Afuwaan Yallab'ai..." "Babu komai ai nima ra'ayina na fad'a idan har kinji bai miki ba to ki bayar..." Kanta ta dad'a sunkuyarwa k'asa tana wasa da gefen hijab enta,ba tare data sake iya cewa komai ba.Godiya yayi mata wanda har ya janyo taji kunyar hakan,sannan ya fice ya barta nan tsaye jingine da bango tana sauke numfashi idanunta a kulle... ^^^^^ Tun daya saurari audios en zuciyarsa ke cikin matsanancin farin ciki,direct gefen su ya nufa ya shirya kana ya d'auki mota,bai zarce ko ina ba sai gidan Matawalle dan yasan shi kad'ai ne zai iya fahimtarsa a irin wannan lokacin,zuwansa gidan Matawalle ya iske shi da bak'i,dan haka sai kawai ya nemi komawa bayan sun gaisa da shi da sunan daman yazo ne ya gaisheshi,badan matawalle ya yarda da maganar ta Yaseer ba ya k'yale shi ya tafi. Ko daya dawo gida kasa zama yayi dan babban burinshi bai wuce yaga an saki d'an uwan nasa ba,amma yaya iya dole ne yabi komai a sannu idan ba haka ba komai zai iya lalacewa kamar yadda a lokacin baya da suke kan neman shaida komai ya lallace musu,dole yasan a yanzun gaggawa ba tasa bace. Cikin turakar mahaifiyarsa ya nufa dan yana jin ko zai iya boy'ewa kowa abunda ya sani tofa banda ita,yana shiga ya isketa da bayin dake mata hidima ciki kuwa harda Inno,juyawa yayi zai koma ta dakatar da shi,cikin nutsuwa ya dawo ya nemi guri ya zauna,yanayinsa kad'ai data Kalla tasan akwai dalilin daya kawo shi a irin wannan lokacin,dan haka kawai sai ta sallami bayin nata sannan ta fuskance shi "Yaseer me yake faruwa ne na canja cikin irin wannan murnar haka..?" 'Dagowa yayi yana sakin murmushi sannan ya bud'e bakinsa cikin farin ciki yana fad'in "Ummi a k'arshe dai komai zai zama tarihi.." "Tarihi kuma...? Wane irin tarihi ne wannan da kake fad'in k'arshensa yazo...?" "Ummi ina nufin k'arshen zaman d'an uwana a kurkuku,Allah ya nufa a yau gaskiyar da muka yita jira ta bayyana,dama nasha fad'a miki,ni nasan waye d'an uwana kuma nasan duk abunda zai aikata da wanda bazai iya ba,na tabbatar dama wasu ne suke shirya wad'annan abubuwan ba don komai ba sai don su b'atawa d'an uwana suna...amma alhamdulillah..! What is tossed upwards must falls back down...!" Wani murmushi ne ya sub'ucewa ita kanta fulanin da bata san lokacin da tayi shi ba,cikin zak'uwa ta furta "Yaseer me kake son cewa ne...? Kana nufin kun samu shaidar da zata iya sawa a saki YAZEED ko me kake nufi..?" "K'warai kuwa Ummi yau Allah ya nufa mun samu gamsashshiyar shaidar da ita kad'ai zata iya sawa a sake shi..Harma a wanke shi daga mugum k'azafin da aka masa.." Hamdala Fulani ta shiga yi tana yiwa Allah godiya bisa wannan ni'ima da Allah yayi musu a lokacin da suka riga suka gama fidda rai da samunta. "Amma Yaseer ta wace hanya kuka samo wannan shaidar...?" Murmushi ya saki kafin ya furta "Ummi sanin inda muka samo shaidar ba shi ne mai muhimmanci ba,abunda yafi kawai shi ne mu maida hankali akan a sake shi..." "Haka ne Yaseer amma sanin ainihin yadda aka samo shaidar shima yana da muhimmancii.." "Shi kenan Ummi zan fad'a miki komai da yadda akai muka samu shaidar...!" Yana niyyan yin magana wayansa dake ajiye a gabansa tayi k'ara,a hankali ya kalleta ganin *UNKNOWN NUMBER* yasa shi k'urawa wayar ido har kiran ya katse ba tare daya d'auka ba,juyawa yayi ya kalli Ummi da niyyan sake yin magana,k'aran shigowar sak'o ya katse shi,kamar bazai d'auka ya duba ba kuma can ya d'ago wayar ya bud'e sak'on,ga abunda sak'on ya k'unsa _"Shin kai kana tunanin kai wani mai wayo ne...? Ko kuwa kana ganin wannan y'ar shaidar daka samu zata isa sawa a saki wanda kake tak'amar d'an uwanka ne..? Me yasa kai baka tunani ne akan future enka,kullum kai kenan kaita maganar d'an uwanka kamar shi kad'ai kake da a fad'in duniyar...? Sarauta gadon kuce ya kamata ka tsaya kayi tunani,kai kanka wannan dama ce ka samu da idan har baka bayyana yarima a matsayin mara laifi ba,wata rana zata kaika ga zama *SARKI* dole mutane baza su tab'a yarda mutum mai irin halin yarima yazeed ya mulkesu ba,amma har sai ka b'oye wannan gaskiyar da kake tunanin bayyanawa...Idan kuwa har kaji zaka iya bayyana shaidar ka,tofa ka sani daga lokacin da aka saki yarima aka kuma wanke shi a matsayin mara laifi,kasa a ranka babu kai babu zama SARKIN GOBE........! Kamar yadda jama'a suka fara maka lak'abi da yarima..." Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci yarima Yaseer da bai san sanda wayan ta sub'uce daga hannunsa ta fad'o k'asa ba,saurin binta yayi ya d'auko yana sake duba sak'on data inda sak'on ya shigo wayarsa.K'ok'arin tura sak'o ya shiga yi sai dai sak'on nasa sam yak'i tafiya,idanunsa ne suka kai dai² inda yake tsammanin ganin suna da number da aka turo sak'on,sam babu lamba bare suna haka mad'aukin sak'on ya nuna masa,wannan ya nuna kenan ko zai shekara yana tura sak'o zuwa lambar bazai tab'a tafiya ba,dafe kansa yayi yana furzar da wani irin huci mai d'umi,Ummi kuwa sai binsa da kallo take kafin ta fara tambayarsa lafiya..? "Babu komai Ummi wani sak'o na gani ne yanzun..." Bai k'arasa ba kira ya sake shigowa da sauri ya kalla phone screen en a tunaninsa ko wancan number ne ta sake kiransa,sunan Abba Matawalle da yayi appearing a sama yasa shi sakin d'an murmushin k'arfin hali kana ya furta "Ina zuwa Ummi..." Wayan ya zara cikin sauri yayi hanyan fita daga d'akin,bai kai ga answering call en ba lokacin ya fito cikin parlor yaga inuwar mutum ta gifta da sauri,wayan yayi saurin mayarwa silent sannan ya tura ta a aljihunsa yabi hanyar da yaga inuwar tabi,cikin sand'a ya shiga bin hanyar amma iya bincikensa baiga kowa ba,dawowa yayi yama Ummi sallama da sunan zai je Abba Matawalle na nemansa duk dan ya k'are maganar da suka fara d'azun dan bai son ci gaba da yinta a nan,matuk'ar kuwa saiya fad'a mata to tabbas ya hak'ura ba yanzun ba dan ganin inuwar nan ya tuna masa da lokacin baya,haka kawai yanzunma yaji bai amince da ganinta ba.Da wannan tunanin ya bar b'angaren mahaifiyar tasa ya nufi nasa gefen,sai daya tabbatar duk ya sallami duka hadimansa sannan ya nemi guri ya zauna ya shiga kiran matawalle,bayan daya d'auka Yarima Yaseer ya gaisheshi cikin girmamawa da mutuntawa a matsayinsa na abokin maimartaba kuma d'an uwa ga iyayensu ta dangantaka. Nan yaci gaba da sauraren Matawalle inda yake masa magana "Yawwa Yaseer d'azun kazo ina tare da bak'i bisa ga alamu kuma dai akwai wani muhimmin abu daya kawoka,dan nasan ba haka kawai ake ganin kuba,sai dai kuma baka tsaya na sallami bak'in ba ka tafi..." Sai daya sosa kai saboda jin kunyar Matawallen sannan cikin girmamawa ya furta "Ehh! Wollahi Abba,dama akan matsalar yarima nazo..To kuma saina iske kana tare da bak'i shi yasa nace bari na tafi kawai na dawo daga baya.." "Allah sarki ai daka min wannan bayanin da na sallami bak'in da wuri saimu tattauna batun da kace,ina ganin shi en yafi muhimmanci akan ganawata da bak'in.." "A'a Abba ai kowa da irin uzurinsa,akan namu uzirin bai kamata mu hana sauran mutane ganinka ba.." "Ehh! To amma dai dole kuma suma mutanen suyi mana uzuri akan namu uzurin idan har suna son ganinmu da kuma neman biyan buk'atunsu.." 'Dan murmushi Yaseer yayi,sai da suka tab'a wasa da dariya tsakanin su bisa ga al'adar su,sannan ya nemi Yaseer en daya sanar da shi maganar daya fad'a ta kaishi. Jawabin komai Yaseer yayiwa Matawalle daya shafi case en yarima YAZEED,har ya kai k'arshe sannan ya k'ara da cewa "Amma Abba ina ganin wannan shaidar ita kad'ai bazata isa tasa a saki YAZEED ba..." "Zata isa Yaseer dan kuwa gamsashshiya ce ga duk wanda zai saurareta,sai dai inda gizo yake sak'a shi ne b'arin ita wannan yarinya daka fad'a min yanzun,lallai ne a duba nata lamarin itama,idan har muka ce zamu fito fili mu bayyanata a matsayin shaidar da muke da ita tofa kamar yadda ta fad'a d'in ne komai zai iya faruwa da rayuwarta,dole ne kafin a saki YAZEED sai munyi k'ok'arin ganin mun bata kariya ta yadda babu wani da zai iya samun damar cutar da ita..." "To amma Abba taya zamu bata kariya bayan tun farko ita ta fara jefa YAZEED a matsala..Ina ganin koma mene ne take fad'a zai faru da ita hakan zai zama BARAZANA ne da ake mata amma bawai dan hakan zai kasance ba.." Murmushi Matawalle yayi kafin ya furta "Yaseer kai yaro ne,wannan maganar ba irin tace wacce ake saurin yin sakaci da ita ba,dole ne kafin muyi komai sai mun bi shi a sannu,amma maganar fitowar yarima daga kurkuku ko a yanzun muna da damar da zamusa a sake shi,sai dai maimartaba yayi hani da hakan tun a wancan shekarun da suka gabata.." Shiru Yaseer yayi yana sauraren Matawalle da bayanin da yake masa har yakai aya,dogon numfashi ya saki kana cikin sanyi ya furta "Shi kenan Abba duk yadda kace hakan za ayi,in sha Allah kuma zan kiyaye duk abunda kace,Allah ya k'ara girma.." Daga haka suka yu sallama da juna sannan suka ajiye wayar a lokaci guda.......... _To nima dai na ajiye birona sai mu tara zuwa gobe da yardar Allah....._ Suna gama waya da Matawalle ya gyara zamansa a saman kujeran da yake yana lumshe idanunsa,zuciyarsa cike da tunanin sak'on da aka turo masa,haka ganin inuwar nan daya rasa dalilin da yasa take yawan giftawa duk ya tsaya masa a rai,knocking k'ofa akayi yana a yadda yake ba tare daya d'ago ya kalli gurin komai shigowar ba ya furta "Shigo...!" "Ranka ya dad'e gashi..." Bawan ya furta yana mik'o masa glass cup da ruwan lemo a ciki,a hankali ya bud'e idonsa ya kalleshi sannan ya furta "Ajiye ka fita.." Ajiyewa yayi sannan ya juya kamar wanda baya son tafiya,kallonsa Yaseer yayi cikin d'an d'aga harshe ya furta "Kaje mana ba na sallameka bane kake tsaye a nan.."+ "Afuwaan! Yallab'ai.." Yadda yake tafiya cikin sanyi yana waiwayensa yasa YASEER kallonsa yana buga tsaki "Idan baza ka tafi ba ka dawo ka nemi guri ka zauna,duk sanda kaga na sha sai ka tafi.." Yadda yaga yanayinsa ya fara sauyawa yasa shi saurin ficewa daga part en yana sunk'e kai k'asa,bayan fitarsa Yaseer ya juyo yana kallon cup en daya ajiye,k'urawa cup en ido yayi kamar mai nazarin wani abu,ko mai son gano wani abu a cikin lemon,haka nan yaji bazai iya shan lemon ba kamar yadda zuciyarsa bata aminta da shi ba gaba d'aya,wani tunani ne ya fad'o masa da sauri ya mik'e ya fita yana neman bawan daya kawo masa lemon,duka sai daya duba bayin da suke iya shiga gefensa amma babu wanda yake nema a cikin su,haka nan yayita dubawa amma baiga wanda ya kawo masa lemon ba,hankalinsa ne ya gaza kwanciya cikin sauri ya koma side ensa ya d'auka wayansa ya shiga kiran line Ummi yaji ko ita ce ta aiko masa da lemon,sai dai kash sam itanma ba ita ta aiko masa ba,hasalima ita bata fahimci abunda yake fad'a ba,da wanda yake nufi ya kai masa lemon,cup en ya zara cikin fusata ya nufi kitchen da shi sai juya shi yake a hannunsa yana sake k'are masa kallo,cikin sink ya watsashi sannan ya bar fasashshen cup en a nan ya fito ya koma ya zauna yana sake tuna maganganun da suke cikin text en da aka turo masa.Take mugun nama ta fara masa kaikawo cikin k'irjinsa,idan ya tuna maganar cewar daga zaran an saki yarima yazeed tofa babu shi babu mulki kenan,sai kuma yaji zuciya na masa hud'ubar kawai ya binne duk wata gaskiya da yake tare da ita,idan kuwa har zaiyi k'ok'arin fitowa yayi yak'i a saki yazeed en tofa gaskiya ne babu wata dama da zai sake samu da zata masa jagoranci zuwa ga mulkin garin kamar yadda zuciyarsa ta fara kwad'aita masa tare da k'awata masa mulkin,wannan tunani shi yayi tasiri a zuciyar Yaseer da yasa shi lokaci guda ya fara jin zuciyarsa na neman canja masa akalar tunani. Tunaninsa ne ya koma kan inuwar da take yawan gifta shi,a fili ya furta "Shin wane ne wannan inuwar...?? Mene ne dalilin ta na rab'ata a lokuta mabambanta...??" Shiru yayi saboda rashin amsa da wanda zai bashi amsan tambayoyin dake dank'are a cikin zuciyarsa daya rasa wanda ya kamata ya tunkara ya amsa masa,haka nan zuwan wannan bawan daya kawo masa lemo,duk da bai sha ba yana jin zuciyarsa na sanar da shi lallai ne akwai *WANI AL'AMARI* dake shirin faruwa koma yake kan faruwa,to amma taya zai fuskanci hakan...? Shin da gaskene wani ne yake shirya wad'annan abubuwan kamar yadda ya fara tunani ko kuwa dai zuciyarsa ce ke k'iyasta masa hakan zai iya faruwa..? Wannan tambaya ita tafi komai yi masa yawo acikin k'wak'walwarsa,cikin nutsuwa ya mik'e hannayensa a goye a bayansa ya shiga zarya a cikin parlor yana tunani akan abubuwa da dama. "Dole ne nayi wani abu,idan ba haka ba komai zai iya faruwa..." Ya furta a fili dai² lokacin da yake sake kiran line Ummi,bayan ta d'aga nan yayi mata bayanin komai daya sani daya shafi binciken da suka fara tun kafin yanzun,hatta maganar inuwar dake yawan wucewa da maganar bawan daya kawo masa lemo bada jimawa ba ya sanar da ita,ba tare daya iya b'oye mata komai ba,ita kanta Ummi'n tayi mamaki sosai dan tana da tabbacin ba kowa keda ikon shigowa cikin masarautar ba,bare kuma har ta kaishi ga yayi basaja ya shiga inda ransa ke so ba,amma to ta yaya har haka ta faru wani daban can ya shigo ya tsallake duka masu tsaron gidan ya nufi gefensa..? Lallai ne akwai wani abu dake kan faruwa da su.Katse tunanin da take yi tayi saurin yi,sannan ta shiga masa nasiha akan koda yaushe ya kasance mai jin tsoron Allah,sannan ya tsarkake zuciyarsa a koda yaushe,kada ya kuskura ya bari dai² da second d'aya shaid'an yayi nasara akansa,bare har yayi masa hud'uba ko k'awata masa sarauta,ko maganar sarautar daya fata matama sai dataa gargad'e shi daya d'auke idonsa akan mulkin masarautar,yadda ta nuna masa hatsarin dake cikin mulkin da halin da zai iya jefa kansa yasa shi jin mutuwar jiki,nan take sarautar ta fice masa akai,dama tun asali shi en bawai yana sha'awar zama mai mulkin ba,a'a lokaci guda sanadiyyar sak'on da aka turo masa aka so asa masa kwad'ayin zama sarkin.Nasiha sosai ta masa mai ratsa jiki wacce jinta kad'ai ya sake k'arfafa masa guiwa akan taimakon d'an uwan nasa daga halin daya tsinci kansa a ciki har na tsawon shekaru biyar,suna gama waya da Ummi ya shiga juya wayan a hannunsa,hamdala yayi ya kuma godewa Allah da baisa shi ya aikata abunda zai zo yana nadama ba,cikin sauri ya turawa matawalle duka recodings en daya turo sannan ya kashe wayan nasa gaba d'aya,dan yadda yake jin jikinsa tamkar zazzab'i na shirin kama shi,zuciyarsa kuwa ji yake tana neman yiwa k'irjinsa nauyi... ^^^^^ *B'ANGAREN YARIMA YAZEED...* A gefen yarima yazeed kuwa tun bayan da aka kaishi REMAND HOME en a lokacin yana d'an shekaru sha biyar a duniya dai² da sau d'aya bai tab'a kawowa a ransa zaiyi irin wannan zaman ba,dan ko a can lokacin yana gidan kangararrun yaran bai kawo zai haura y'an watanni ba tare daya fita ba,sai dai har ya shafe shekaru uku a gidan sannan aka sake masa chanjin guri daga nan zuwa PRISON en ta nan goron dutse,ko da chanja masa gurinma yanzun da zamansa a cikin prison en shekaru biyu kenan,haka tun zuwansa tsawon wad'annan shekarun ko sau d'aya bai tab'a ganin maimartaba ba,hakama mahaifiyarsa,y'an uwansa mata da duka wasu ahalinsu,kaf maimartaba ya hanasu zuwa gurinsa haka babu wanda yake gigin zuwa,sai ko idan aka d'auke yaseer da kusan ko wane lokaci idan yayi ra'ayi zaije ya ganshi,ta b'angaren iyayensa mata sai dai ko suyi aike a gano musu lafiyarsa,iya tsayin wannan lokacin gaba d'aya kamanninsa sun sauya yayi duhu haka ya tara uwar k'asumba duka ya zama kamar wani tsohon daya shekaru saba'in a duniya,tun shigarsa kawo wannan lokaci ko kad'an yak'i yarda ayi masa aski,kullum ka ganshi shi kad'ai yayi shiru ko yana karatu,haka kullum yana killace abunsa babu sabgar wanda yake shiga,haka ko zamanin da yake can a remand home bai yarda yayi aboki ba,hakama cikin prison en tun shigowar sa bai yarda ya had'a hannu da wani ba bare ace har yayi aboki,a kullum bashi da burin daya wuce ace maimartaba ya fahimci sharrin da aka masa,shi bama ta a sake shi yake ba,a'a gurinsa da fatana har kullum maimartaba ya fahimci AL'AMARIN,tunda yaga sa ran da yake akan kwanaki kad'an zasu d'auke shi a cikin gidan,a fidda shi har sun zo sun shud'e amma shiru kake ji,wannan tasa shi ya fidda rai dan zamansa a gurin tsawon wannan lokacin yasa shi sawa ransa hak'urin dole dan tabbacin daya samu akan tun daya kawo yanzun babu shi babu barin gurin har sai ya cika wa'adin da aka d'ibar masa. *BAYAN KWANAKI BIYU...* Yana zaune a d'aki da alk'ur'ani a hannunsa,yayi nisa wajen karatu inda yake cikin karanta suratu alii imraan,guard ne ya zo dan sanar masa yana da bak'o,kasancewar ya bawa k'ofa baya yasa shi girgiza masa kai kawai ya masa alamu,juyawa yayi ya fita sannan yazeed en ya tak'aice karatun da fad'in "Sadak'allahul aziiym...!" Waiwayowa yayi sannan ya sauke tashi ka fiya nacin daya kifa akansa,yana juyawa suka yi ido had'u da matawalle tsaye yana k'arewa d'akin dama shi kansa kallo,da sauri yazeed en ya mik'e ya nufe shi idonsa d'auke da hawayen farin ciki dake sauka daga idanunsa,yana niyyan tsugunawa matawalle ya rik'o shi ya rungumeshi cike da tausayawa rayuwarsa,sun d'auki lokaci a haka sannan Matawalle yayi masa bayanin dalilin zuwansa gare shi,kukan farin ciki yazeed yasa da tun zuwansa bai tab'a hawaye masu sanyi ba sai wannan ranar data zo masa da tarihin daya dad'e yana mafarki,bayan gama koke²n yazeed da tsantsar jimami daga gurin Matawalle bisa ga abunda maimartaba ya aikatawa d'an cikin nasa wanda shi kansa Matawalle'n dama wasu daga cikin y'an majalisar sarki suke ganin anyi rashin adalci wa yazeed en na k'in bada lokaci ayi bincike da maimartaba ya hana ayi tun farko,haka ajiye shi acikin mutane da akayi maimakon a killace shi kamar yadda ake yiwa wasu y'ay'an manyan da ake kamawa,amma gashi yazeed en sai maimartaba ya hana duk ayi masa haka,kuma yasan duka yayi hakan ne ba don komai ba sai don gujewa zagin mabiyansu,wanda yin hakan da yayi kuma ba zai rage ko ya k'ara abunda mutanen suka yi niyyar fad'a ba,kamar yadda shi en yake ganin hakan zai basu kariya daga gujewa zage²n. Sun jima a haka kafin Matawalle yayi umarnin ayiwa yazeed en aski wanda da kyar shi kansa yazeed en ya yarda aka masa,sai da yaga ya d'an fara samun nutsuwa har yana iya yin murmushi sannan yayi masa sallama akan ya jirayi dawowarsa bada jimawa ba,nan ya fice a d'akin ya barshi ransa a b'ace. Direct office en shugaban gidan ya nufa da zuwansa bai tsaya wata² ba ya fara masa fad'an wulak'anta d'ansu da akayi,taya zasu barshi cikin ko wane irin mutane..? Hak'uri ya bashi sannan ya fad'a masa shi kansa ba laifinsa bane,sak'on maimartaba ne hakan daya turo musu akan kada su kuskura su ware masa gurin zama shi kad'ai,yadda ya masa bayanin hakan yasa Matawalle fahimta duk da dai yaji babu dad'i,shi kam gaba d'aya ma ya rasa fahimtar halayen maimartaba akan wasu abubuwan da yake aikatawa,lokuta da dama idan yayi wani abun tamkar bashi ba,ko a fada wasu lokutan sai yayi abu amma su kasa fahimtar dalilinsa nayin hakan. Sunyi maganganu da shugaban gidan kafin ya gabatar masa da hujjojin dake tattare da shi akan case en na yazeed,shi kansa incharge en tun lokacin baya yaso yin wani abu akan matsalar yazeed en,dan dai kada ya shiga cikin case en ne da kuma jan kunnen da maimartaba ya musu akan kada wanda yasa hannu wajen fitar da yazeed en yasa baiyi k'ok'arin yin wani abu ba,amma kam da tuni ya jima da fitar dashi,sai dai kuma yakan gaza fahimtar dalilin maimartaba akan hukuncin da aka yankewa yazeed en ba tare da an tsananta bincike ba,sam shi halinsa ba irin na sauran jama'a bane,ya jima yana aiki a gurin kamar yadda yasan manyan mutane da dama idan aka ce yau an kama nasu yayi laifi sukan tsayawa iya yinsu na ganin ba'a hukunta shi ba,amma shi maimartaba sarki Abu yazeed nasa salon sai ya bambanta dana saura. Nan Matawalle ya nuna buk'atarsa ta son a saki yazeed en a lokacin,hak'uri incharged en ya bashi sannan ya k'ara masa da bayanin yayi hak'uri har zuwa washe gari idan aka zauna a court aka k'ark'are case en sai a sallame shi,a nasa ganin wannan hanyar ita yafi kamata dasu bi wajen tsarkake yariman daga mugun zargi sannan kuma hakan zai sa wad'anda suka masa k'ullin bazasu fahimci komaiba bare suyi yunk'urin guduwa. Haka ba don Matawalle yaso ba ya hak'ura suka tsaya akan washe garin,ma'ana dai kamar yadda aka fara a court en masarauta a k'are a can,da wannan jawabin matawalle yama yazeed sallama sannan ya kama hanyar komawa gida........... ^^^^^ Jeeddah kuwa a nata gefen tunda Yaseer ya sanar mata da sun kammala komai na dangane da case en yarima yazeed hankalinta sai ya kwanta dan tana da tabbacin wannan hujjar ta isa zama gamsashshiya da zata sa a sake shi bada b'ata lokaci ba,sai dai hankalinta har yanzun bai gama kwanciya ba,basin komai ba sai don matsalar da Aisha ta sanar mata zata iya fuskarta matuk'ar suka yi yunk'urin bayyana gaskiya game da case en na yarima yazeed,haka tun bayan rabuwarsu da Aishar take yawan jin fad'uwar gaba mai tsanani. Zama tayi ta buga tagumi zuciyarta cike da fargabar abunda zai iya biyowa baya,dan tunda Aisha ta shaida mata kad'an daga cikin halayen Ladidi take fargabar wani abu ya sameta,harta mik'e zata fita kuma kome ta tuna ta koma ta zauna tana d'aukan wayarta,d'an gajeran sak'on ta rubuta sannan ta turawa Yaseer en cikin sauri. A dai² lokacin da sak'on ta ya riski Yaseer kuwa suna tare da Matawalle yana masa tambayoyi game da yadda za'ayi a kamo Ladidi da ita kanta Aishar dan gudun kada su samu labarin za'a saki yazeed su gudu,tunda har ya zama yanzun akan samu siririn cikin gidan yana fita ba tare da sanin ahalin masarautar ba,yana gama dubawa kuwa ya saki murmushi sannan ya sanar da Matawalle abunda ke kan faruwa kamar yadda jeeddan ta tura masa sak'on,suna gama maganar Matawalle ya tashi wasu mutum biyar cikin amintattun bayinsa da sarki Abu yazeed ya bashi ya musu bayanin abunda yake buk'atar su aiwatar a lokacin na zuwa a kamo masa Ladidi da y'arta Aisha,sannan su kasance cikin taka tsantsan kada a samu matsala,bayan ya sallame su suka kama hanyar gidan Ladidin da niyyan k'wamusota kamar yadda aka basu umarni. Kamar yadda aka musu umarnin haka suka yi ba tare da sunyi wata² ba suka dak'umo Ladidi da Aisha suka nufi gidan Matawalle dasu dan dama abunda yace dasu kenan da zaran sun kamosu to su kai masa su gidan shi zai adana su har zuwa wayewar gari,koda suka cika umarnin bayan sun sanar masa hamdala yayiwa Allah sannan ya sallami Yaseer akan sai gobe idan Allah ya nuna mana lokacin zaman fada,da wannan shima YASEER en ya kama hanyar komawa gida zuciyarsa cike da taradaddin abunda zai wakana a zaman kotun.. *WASHE GARI..............…..*Yadda k'ofar fada ta d'inke ta cika mak'il da jama'a,abun sai ya so baku mamaki,duk inda ka duba jama'a ne iya ganinka,abun d'aure kan da mamakin kuwa bai wuce ganin babu wata sanarwa da akayi bisa hakan ba,amma jama'ar dake wajen tamkar idin yaumul-adhaa,tun kafin a zauna a fada maimartaba ya fito daga gida tuni har jami'an gidan yarin sun bayyana tare da Yarima YAZEED,wannan yasa sai jama'ar fadar basu kawo zargin ko wani ya sanar da jama'a abunda yake faruwa ba. Cikin farin ciki da samun y'anci a wannan ranar yarima ya fito daga cikin motar kurkukun,da Yaseer suka fara arba ko da ganinsa take suka rungume juna suna masu farin cikin sake kasancewa tare a lokacin,daga nan cikin gida suka nufa su duka Yaseer rik'e da hannun yazeed suka nufi b'angaren mahaifiyar yazeed en. Fulani na zaune cikin turakar ta suka yi sallama,ba tare da jiran izinin shiga ba suka kunna kai ciki suna masu sake yin sallama a karo na biyu,muryoyin da kunnenta ya kwaso mata su suka haddasa mata d'agowa daga duba littafin ADDU'A'U MIN KITABB WAS-SUNNAH da take cikin bincikenta na neman ayatur-ruk'yah,fuskarsa kad'ai ta Kalla tayi saurin mik'ewa tsaye tana binsa da kallon tsantsar mamaki,murmushin k'arfin hali yazeed yayi sannan ya nufeta da saurinsa,yana niyyan tsugunawa a gabanta tayi saurin rik'o shi tana fashewa da matsanancin kukan yadda taga d'an nata ya koma kamar wani dattijo saboda sauyawar da halittarsa tayi,cikin muryar kuka take fad'in "Yazeed kai ne...? Ko kuwa dai mafarkin dana saba yi ne yake neman sani na zauce...?? 'Dan nan kamin magana kona tabbatar ba a mafarkin dana saba ganin ka bane.." Kasa magana yazeed yayi sai murmushi mai cike da hawaye da yake sake mata saboda tsabar farin cikin da yake binsa a ciki,nan ya samu damar rungume mahaifiyarsa,yana sake shak'ar iskar y'anci,shi kansa Yaseer yadda yaga sun koma yau sai duk suka bashi tausayi,komawa yayi ya zauna sannan ya tankwashe k'afafunsa yana binsu da kallon da Allah kad'ai yasan ma'anarsa,ga Fulani kuwa yadda ta k'ank'ame yazeed en ji take idan har ta sake shi yanzun tofa zata iya bud'e ido taga duk abunda ya wakana a cikin bacci ta gansa,jin irin rik'on tsaurin da tayi masa yasa shi bud'e baki yana fad'in "Ummata nine fa YAZEED enki,gani gabanki a yau cikin hukuncin ubangiji da yardarsa,kuma da izininsa komai zai zama tarihi..." Jin muryarsa yasa Umman tasa d'agowa da sauri ta kalli fuskarsa tana k'ura masa ido had'e da tattab'ashi duk dan ta tabbatar gaske ne ba k'arya bane,sai da taji ta gamsu sannan ta furta "Yazeed kai ne...? Kai ne ka koma haka..??" Sai kuma ta sake fashewa da kuka,su kam dukansu nan suka tsaya kallon ikon ubangiji daga shi har Yaseer,yadda Umma'n tasa ta koma masa kamar wata wacce ta samu shafar jinnu "Yazeed yanzun kaine ka koma haka..?? Allah na gode maka daka fito min da d'ana abun alfahari na,Allah na gode bisa ni'imar da kayi a gareni na dawomin da yarona,Allah ina rik'onka daka gaggauta bayyana duk wani maisa hannu a cikin al'amarin nan...Allah ka tona musu asiri mu gansu mu kuma gane su dan alfarmarka..."+ "Nooo!!! Ummah banda cikin gaggawa..dan kuwa hadisi ya tabbata daga annabi (S.A.W) yana cewa: "Atta'anniiy minallah..wal'ajlatu minash-shaid'an.." Ma'ana jinkiri daga Allah yake..gaggawa kuma daga shaid'an take..saboda haka idan zaku rok'i ubangiji kada ku rok'i a gaggauta muku,la'allah abunda zaku rok'a ya kasance ba alkhairi bane a tare daku,amma idan aka jinkirta muku koda babu alkhairi a cikin abunda kuka rok'a sai Allah ya musanya muku shi da wanda yafi shi zama alkhairi a tare daku.." Fuskarsa ta shafa tana rausayar da kai sannan ta furta "Hakane yazeed amma ni a gare ni bani da burin daya wuce naga asirin duk wani mai hannu ya tonu,sam mutane zuk'atansu babu Allah,shin mene ne ka tsare musu da haka zai faru da kai tun kana yaronka...?" Murmushin dai ya sake yi mata sannan ya juya ya kalli Yaseer daya zuba musu ido yana ta sakin murmushi abunsa,yana goge hawayen dake saman fuskarsa "Koma mene ne Umma,kuma ko su waye suka yi wannan aikin ni bani da abunda zance dasu daya wuce nace *na barsu da Allah...* dan nasan shi zai karb'amin hakkina a hannun duk wanda ya zalunce ni,saboda haka kema ki daina sa wannan maganar a ranki coz ina tsoron wani abu ya sameki.." Jirkita kai tayi gefe tana kallonsa cike da tausayi,Yaseer ne ya kallesu duka cikin wani yanayi ya furta "Bross ka samu kayi wanka yanzun kafin a shiga fada...Dan lokacin halartar maimartaba ya kusa.." Amsawa yayi yana zaunar da Umma'nsa a saman shimfid'a sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa "Ummata bari na shirya sai na dawo.." "To yazeed amma ka wanke wannan fatar taka da kyau...kaji ko..? Allah ya saka maka,yabi maka hakkinka.." 'Dan yak'e ya sake yi mata sannan suka fice suka nufi gefensu,tun daga shigarsu yake bin ko'ina da kallo tamkar wani bak'o,har sai da yaja yaseer ya sake masa magana sannan ya shiga wankan,ko shigar sa toilet en sai daya b'ata lokaci a ciki kafin ya samu ya fito,lokacin kuwa tuni har an fara zuwa ana kiransu dan tuni har maimartaba ya halarci fadar,sauri yayi ya shirya cikin wata d'anyar shadda data amsheshi,duk da irin ramar da yayi,sannan suka kamo hanya da niyyar zuwa gefen mahaifiyar tasa suci abinci kamar yadda ta labarta musu,dai² lokacin da suka fito daga gefen zasu je yiwa Umma'nsa sallama akan zasu fada tukun yanzun idan yaso bayan fitowarsu a can sai su zauna cin abincin tunda har an fara turo y'an aiken,si suka sake cin karo da wasu bayin akan suzo su sake kiran su,hakan tasa dole suka hak'ura da zuwa gefen Fulani suka nufi hanyar fada dan bin umarnin maimartaba. Lokacin da suka iske k'ofar fada da k'yar suka samu hanyar wucewa suka isa cikin fadar saboda yadda jama'a suka sake yin cikar kwari,baga mata ba baga maza ba,hatta da k'ananan yara suma ba'a barsu a baya ba.Sai da suka mik'a gaisuwa ga maimartaba sannan suka koma gefe suka zauna kusa da juna suna jiran jin yadda zaman zai kasance. Maimartaba ne yayiwa Matawalle umarnin dasu fara gabatar da abunda ya tarasu a gurin ba tare da b'ata lokaci ba,ko kafin Matawalle ya kai ga yin magana sai da suka yi y'an maganganu da TALBA kasancewar shi matsayin wanda Alkalai suke k'ark'ashinsa kuma ta hannunsa suke ganin Sarki,Shi kuma MATAWALLE Shine mai kula da aikin dukkan Alkalai haka yana iya yin hukunci idan har abun ya shafi masarauta,bayan Matawalle ya mik'e yayi gaisuwa,sannan ya fara jawabin abunda ya tarasu,kamar yadda yayi jawabi a wad'ancan shekarun da suka gabata a ranar da aka kawo k'arar ta yarima yazeed,sai dai na yau ya bambanta dana wancan ranar kasancewar wannan ranar shaidu suke niyyar gabatarwa da zasu wanke yariman,bayan nan kuma yasa a shigo da Ladidi da Aisha da suma tuni aka zo da su cikin gidan. "Kamar yadda wannan fada ta shaida,kuma kamar yadda ya al'ummah ta shaida,a shekaru biyar da suka gabata,wannan Yarinya mai suna Aisha ta shigar da k'ara a wannan kotu ta fada da akan tana k'arar yarima yazeed bin abu yazeed,bisa laifin da suka yi ik'irarin da cewar yariman ya aikata na keta mata haddi kamar yadda suka ambatawa kotu a shekarun da suka gabata,sai dai bisa ga bincike da wasu a cikin wannan masarauta suka gabatar akan wannan case da idan fada ta bada dama zamu gabatar da shaidun da muka samu da suke kore tabbatatuwa akan cewa lallai ne yariman wannan masarauta bai aikata abunda aka zargeshi da aikatawa ba,hasalima a wannan ranar da abun ya faru yarima yana tare da mahaifiyarsa a wannan dare,haka kuma bayani gamsashshe ya riskemu kan cewa bayan barinsa a gefen Fulani suna tare da d'an uwansa kuma abokinsa wato YASEER kasancewar kamar yadda aka sani duk dare tare suke barci haka duk wasu al'amura nasuma k'asan tare suke gabatar dasu....." Sai da yad'an tsagaita sannan yaci gaba da magana "Sai dai abun tambaya a nan da kuma d'aure kan shi ne...A lokacin da ake maganar wannan AL'AMARI ya faru,Shin iya yarima yazeed ne ya aikata ko kuwa duka su biyu ne...? Idan kuwa har iya shi yarima ne shi kad'ai to a wannan lokacin shin shi YASEER yana ina hakan ta faru..? Ko kuwa dai ana nufin ace yariman ya fita daga gida ne ba tare da sanin YASEER ba haka ba tare da sanin wasu a cikin masu tsaron wannan masarauta ba,duk da kasancewar kowa yasani tun tasowarsu duk wanda ya sansu tare ya sansu...Ina neman afuwar wannan fada bisa wad'annan tambayoyi dana gabatar,amma idan har fada ta bada izini muna da buk'atar mu samu amsoshin wad'annan tambayoyi daga jama'a sannan daga su Kansu wad'anda suka kawo wannan k'ara..." Jinjina kai maimartaba yayi zuciyarsa cike da farin cikin wannan AL'AMARI duk da a baya sam baiyi tunani akan matsalar ba,haka kwata² baiyi tsammanin abunda ake zargin d'an nasa da aikatawar bai faru ba,sai yanzun daya fara jin yadda matawalle na bud'e bayanai,haka sai yanzun ne ya fara jin inama tun kafin wannan lokacin ya bada damar ayi binciken kamar yadda Matawalle ya nemi izinin daga gare shi,haka ko Mahaifiyar yazeed zuwa kan K'aninsa GALADIMA,WAMBAI dama Wazirinsa duk sai da suka same shi da maganar amma yak'i sauraren su,haka har zuwa kan y'an majalisarsa kusan babu wanda baiyi maganar ba,amma duka ya share su saboda a lokacin yana kan dokin zuciya na mugun Fushin da yayi da yariman. Shiru fada ta d'auka babu amsa,koda ganin haka sai Matawalle yayi d'an murmushi sannan yaci gaba "Ran maimartaba ya dad'e ubangiji ya k'ara tsawon rai yaja kwana,wannan shirun da al'ummarmu suka yi ya isa ya sake tabbatarwa da lallai nefa yarima bazai tab'a iya aikata abunda ake magana ba,idan kuwa har an samu wanda ya yarda da cewa ya aikata en to muna buk'ata daya hallara a gaban fada domin ya mana bayanin da zai gamsar damu akan faruwar hakan.." Nan ma shirun dai aka sake yi,babu wanda ya iya koda tari bare a samu wanda zaizo gaban fadar ya fad'i abunda ake buk'ata,ko da ganin haka sai yasa Maimartaba ya bashi damar ci gaba "Ina fata wannan abu daya faru a gaban fada zai zama shaida ta farko ga wannan laifi da ake ik'irarin yarima ya aikata..." Bayan shud'ewar wasu y'an min tuna,Matawalle ya sake kallon al'ummar fada cike da k'warin guiwa yana cewa "Idan har wannan fada mai alfarma ta bada izini ina son gabatar mata da shaida ta gaba,wato Aisha a matsayinta na wacce al'amarin ya faru akanta,sannan ina son yi mata tambayoyi.." Kafin ya gama magana tuni har an kawo Aishar gaban fada,duk wanda ya kalleta a wannan lokacin tsaf zai iya gano rashin gaskiyar dake tattare da ita,jikin ta duk sai tsuma yake musamman yadda taga idanun gaba d'aya al'umma akanta,kuma kowa su kad'ai yake saurare yaji me Matawalle zai ce sannan itan wace amsa zata bayar..? Irin kallon da taga Matawalle yayi mata fuskar nan babu alamun wasa aciki tuni ta dad'a firgita "Aisha muna so yanzun ki yiwa fada bayanin abunda ya faru a waccan ranar..." Shiru tayi ta kasa magana saboda tsabar firgicin dake tattare da ita,a hankali ta juya ta kalli Ladidi idanunta na tsatstsafo da ruwan hawayen da ita kad'ai tasan ma'anarsu,jin shirun nata yana neman yin yawa yasa Matawalle sake maimaita mata tambayar daya mata,duk da yayi hakan ne dan kawai ya tabbatar da ta fad'i gaskiya.Cike da in-ina ta fara magana tana yi tana tsayawa tana kuma kallon Ladidi,hakan yasa Matawalle yin magana "Aisha so muke ki bud'e baki sannan kiyi magana a nutse saboda nan a gaban fada kike kuma ita fada ki sani ba'a mata k'arya..Muna fatan zaki kiyaye harshenki da fad'in abunda yake ba daidaiba.." Hawayen daya ziraro mata ta goge sannan ta fara da fad'in "Yallab'ai ina neman afuwar fada amma ni babu abunda na sani game da abunda ake magana akansa.." Girgiza kai Matawalle yayi kafin yace "Shin kina nufin baki sani bane..? Ko kuwa kina son nunawa fada ke bama ki fahimci abunda ake magana akansa ba..?" "A'a Yallab'ai ni ina magana ne akan shaidan da ake magana.." "Toh..! Aisha ko zaki iya yiwa fada cikakken bayani akan abunda kike nufi,dan ina ganin dukanmu nan bamu fahimci abunda kike nufi ba.." "Ehh! Yallab'ai zan iya...Maganar da nake anan Yallab'ai shi ne,wannan abu daya faru dani shekarun da suka gabata babu k'arya a cikinsa,haka AL'AMARIN yake,duk wani abu da muka fad'a a wancan lokacin haka yake..." 'Dagowa yarima yazeed yayi ya kalli Yaseer, koda suka had'a ido sai Yaseer en ya masa alama da kada ya damu komai zai zama dai²,badan ya gamsu ba ya sake maida hankalinsa gaban fada don jin mai Matawalle zai fad'a shi kuma,nan ko ya tsinto Matawallen yana fad'in "Haka ne Aisha...Idan har ban manta ba kuma kema ina fatan baki manta ba,haka zalika idan al'ummar da suke sauraren mu basu manta ba,a waccan ranarma irin abunda kika fad'a kenan ko..?" "K'warai kuwa Yallab'ai haka ne..." "Shin har yanzun kina kan bakar ki akan yarima ya aikata miki hakan ko kuwa zaki chanja maganar ki kafin na bayyana wani sirri da baki san da shi ba,wanda kuma ke en dama mahaifiyarki kuka jima kuna b'oyewa..?" "A'a Yallab'ai babu abunda zan fad'a.." "Kin tabbata babu wani abu da zaki chanja ko ki k'ara,ma'ana kina nan kan abunda kika fad'a.. Ko da bayan bayyana wannan gaskiyar da nake fad'a..?" "Eehh! Yallab'ai babu.." Sai da suka yi haka da ita har sau uku tana tabbatar masa itafa tana nan kan k'udurinta kuma babu wani abu da zata chanja cikin maganar ta,nan take Matawalle ya juya ga Maimartaba da sauran al'ummah yana fad'in "Hak'ik'a wannan abu da Aisha ta fad'a ba gaskiya bane ya maimartaba.." Hannunsa ya d'ago da yake d'auke da wata y'ar k'aramara recorder yana cewa "Wannan na'ura dake d'auke a hannuna ya maimartaba d'auke take da shaidar sak'on murya na wannan Yarinya Aisha a inda sukayi wata maganar sirri da d'aya daga cikin masu binciken suka gabatar,ina neman izini da idan har maimartaba ya bada dama,kuma fada ta bada dama ina so yanzun a gabato mana da speaker dan sanyawa kotun fada shaidar da muke d'auke da ita a cikin wannan sak'on murya da muka samu,wacce muke ganin saurarenta kad'ai zai iya gamsar da fada dama ilahirin al'ummar data halarci wannan guri..." Cikin y'an mintuna tuni har an kawo k'atuwar speaker en da zata wadaci gurin,nan aka jona y'ar na'urar da Matawalle ya saka memory en daya d'ora voice recording en na Aisha,sannan akayi playing nasa,nan take muryar Aisha ta soma amsa kuwwa a cikin fadar da tayi tsit kowa na son shaida abunda zaiji daga sak'on muryoyin,cikin sheshshek'ar kuka take fad'in _"Dan Allah jeeddah ki dakata kafin ki shiga muyi magana,wollahi akwai wani muhimmin sak'o dana zo na sanar dake a yanzun..."_ Jin haka yasa jama'a sake nutsuwa suna sauraren maganar da take fitowa daga bakin ita kanta jeeddan...Duk yadda suka yi da jeeddah da kuma ita Aishar babu abunda recording en bai bayyana ba har zuwa k'arshen maganar tasu inda jeeddah ke kwantar mata da hankali bisa abunda ta fad'a mata na abunda zai iya faruwa da ita idan har aka san ta bayyana hakan,ana zuwa nan Matawalle ya tsayar da abun sannan ya juya ga ita Aishar fuskarsa d'auke da wani irin murmushi mai cike da nuna nasarar dake tattare da shaidar daya gabatar,nan ya sake kallon al'ummah da sai a lokacin ne suka samu bakin magana kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan matsalar tare da yiwa Ladidi da Aisha tofin ala tsine bisa ga wannan gagarumar k'arya da suka shirga a gaban fada,sai da sa jama'a suka yi shiru sannan yaci gaba "Aisha....! Shin kin saurari wannan sak'on..?" "Ehh! Yallab'ai na saurara.." Murya na cracking cike da rashin gaskiya ta amsa masa "Shin ko kina da wani abun fad'a game da hakan..?? Ina nufin ko zaki iya gane wannan muryar Waye...??" Nanma muryarta na kyarma ta furta "Ehh! Yallab'ai.." "To Aisha muna sauraronki muna kuma buk'atar ki fad'awa fada shin wannan muryar ta waye..? Sannan kuma da waye kika san kinyi wannan maganar.A kuma ina hakan ta faru.?" "Muryata ce Yallab'ai.. Kuma bada kowa muka yi wannan maganar ba face da jeeddah.." Girgiza kai Matawalle ya sake yi kafin ya furta "Yanzun kin tabbatar wannan en muryarki ce..? Kuma ako ina aka tambayeki zaki iya fad'ar cewar tak'i ce ba tare da tunanin komai ba..?" Shiru ne ya biyo baya dan gaba d'aya Aisha ta gama tsinkewa da lamarin,kamar yadda bata zata ba haka ko kad'an tunanin ta bai kawo mata cewa jeeddah zata iya recording maganar tasu ba,gumi ne mai tsanani yake ta keto mata saboda yadda gaba d'aya aka d'aureta da jijiyoyinta,ji take inama zata samu hanya da ko kad'an babu abunda zai hana bata take k'afafunta a gurin ba,amma ina duk inda ta wulga idanunta dakaru ne na fada haka jami'an tsaro da Matawalle ya kawo da suka sake bawa fadar kariya ta yadda duk k'ok'arin mutum bai isa ya nemi tserewa ba. Nan Matawalle yaci gaba da magana "Bisa ga wannan tak'aitattun shaidu da suka gabata a gaban fada da kuma al'ummah muke fatan wannan fada da kuma kotu zasu saurari hukunci da za'a gabatar ga wad'annan azzaluman mutane,bisa cutarwa da suka yi ga yarima na d'ora masa laifin da bai aikata ba,da kuma wannan ne kotu zata yi amfani wajen tsarkake wannan bawan Allah dan ya fita a cikin zargin da aka lik'a masa.." Komawa Matawalle yayi ya zauna a kusa da TALBA suka d'anyi magana kafin ya gabatar da hukuncin da za'a yankewa su Aisha kamar yadda shari'a da addini ya tanada,zuwa wasu y'an mintuna kowa ya d'anyi taking breath sannan Matawalle ya sake mik'ewa don zartar da hukuncin da daga shi,shi kenan zaman yazo k'arshe. Bayan tabbatarwa da aka samu daga bakin ita Aishar da fada ta saurara da kuma gabatar da shaidu wanda duka suka gudana a gaban idanun dubban al'ummah,tashin Matawalle a dai² lokacin yasa gaba d'aya surutan dake tashi a fadar ya dakata kowa yayi shiru yana jiran jin irin hukuncin da za'a yanke,dan hatta ni kaina shiru nayi na zubawa Matawalle ido ina sauraren naji mai zai ce,nan kuwa ya fara da yin sallama sannan ya d'ora da fadin "Bisa ga shaidu da muka shaida,fada ta shaida kuma al'ummah ma ta shaida gaba d'aya muke fatan al'ummah gaba d'aya zasu sake saurarawa don jin hukuncin da addini da kuma shari'a ta tanada ga wad'annan mutane..." Shiru ya d'an sake yi na wasu y'an dak'iku kafin yaci gaba "Da farko zamu fara da gabatar da hukuncin da addini ya tanada ga duk wani wanda aka samu da laifin K'AZAFI ga wani mutum....Bisa ga hukunci daya tabbata daga al'qur'ani mai girma,ya tabbatar cewa ga duk wani da aka samu da irin wannan laifin nayin k'azafi,tofa hukuncin sa ya ta'allak'a ne kamar yadda Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin suratun-nur,ayata hud'u zuwa ta biyar inda Allah mad'aukaki yake cewa:"WALLAZIIYNA YARMUNAL MUHSANATI THUMMA LAM YA'ATUU BI ARBA'ATI SHUHADA'A FAJLIDUHUM THAMANINA JALDATAN WALA TAK'BALUU LAHUM SHAHADATAN ABADA,WA'ULAA'IKA HUMUL FASIIK'UUN..ILLALLAZIIYNA TABUU MIN BA'ADI ZALIKA WA-ASLAHU FA'INNALLAHA GAFURUR-RAHIIYM..." _Ma'ana "Kuma wad'anda ke jifar mata masu kamun kai,sa'annan kuma ba su je da shaidu hud'u ba to ku yi musu bulala,bulala tamanin,kuma kada ku karb'i wata shaida tasu, har abada.Hak'ik'a wad'ancan su ne fasik'ai...Sai dai ga wad'anda suka tuba daga bayan wannan,kuma suka gyaru,to lallai ne Allah mai gafara ne,kuma mai jin k'ai..."_ "Bisa ga saukar wad'annan ayoyi hakan ya tabbatar da cewa duk wani wanda aka kama da laifin k'azafi ga wani bawa salihi,tofa lallai ne za'ayi masa bulala tamanin domin tsarkake shi da kuma kub'utar da shi daga halaka,a saboda haka ne suma wad'annan bayin Allah za'a gabatar musu da hukuncin bulala tamanin kamar yadda nassi ya tabbatar,kuma a gaban al'ummah dan su zama shaida akan cewar an zantar da hukuncin kamar yadda ubangiji yayi umarni.................. _Hhhhhh! Jama'a kada kuso kuga idon LADIDI da AISHA dan ni dai da nake gurin tsabar ganin yadda suka koma har ban san lokacin da hawayen mugunta suka fara biyo fuskata ba......😂😂😂_ Su Ladidi ido yayi tsilli² jin yadda aka ambaci bulala tamanin,kafin kuce kobo tuni ta zube a k'asa ta fara rusa kuka mai tsanani, wannan yasa gaba d'aya hankalin jama'ar fada ya koma kanta,nan wasu ciki suka shiga zaginta da jifanta da bak'ak'en maganganu na ita ta janyo faruwar hakan,kuma son zuciyarta shi yayi mata jagoranci ga aikata hakan,ga fadawa kuwa nan suka shiga mata tsawar ta shiga nutsuwarta sannan ta san a inda take wannan ihun kafin jikinta ya tsamama,shiru tayi tana damk'e bakinta idanun nan kuwa tamkar an matsa agwaluma. Shiru akayi umarnin mutane suyi a gama yanke hukunci kafin a tashi a zaman fadar,nan mutane kowa ya sake saurarawa yana jiran yaji me zai sake faruwa dasu Ladidi,Matawalle ne ya sake mik'ewa sa'annan yaci gaba da magana "Kamar yadda muka sanar da jama'ah hukuncin da addini ya tabbatar da za'a gabatar wa dasu Ladidin nan bada jimawa ba in sha Allah,bayan an zartar musu da wannan hukuncin kuma akwai k'arin hukunci da zasu karb'a wanda wannan kotu ta bada izinin ayi musu,abisa la'akari da irin lokacin da aka b'atawa yarima,haka nan b'ata masa suna da akayi bisa hakan,sannan ga tsare shi da akayi abisa laifin da bai aikata ba,wannan kotu ta zartarwa da wad'annan mutane hukunci kamar haka:Na farko zasu biya tara ta naira dubu d'ari biyar ga shi yariman,sa'annan na biyu kuma za'a tsare su a gidan yari na tsawon watanni shida tare da basu horo mai tsanani,ba tare da bada damar yin bailing nasu ba,sannan daga wannan lokaci wannan kotu ta wanke yarima akan laifin da aka zarge shi daya aikata,a bisa samun sa da akayi bashi da hannu a cikin wannan matsala,wannan kotu mai alfarma tana k'ara bashi hak'urin b'ata masa lokaci da suna da akayi,sa'annan kotun tayi watsi da wannan k'ara saboda rashin ingancinta,kuma ta gargad'in duk wata kotu da karb'ar case makamancin wannan har sai an tabbatar da mutum ya aikata kafin a yanke masa hukunci..." Sai daya d'an saurara sannan yaci gaba "Da wannan hukuncin muka kawo k'arshen wannan shari'a,muna fatan wannan hukunci zai zama izina ga y'an baya dama duk wani mai sha'awar aikata kwatankwacin wannan laifi,haka muna fatan wannan zai zama k'alubale gareku al'ummah baki d'aya....." Ihun da Ladidi taci gaba da zundumawa yasa gaba d'aya hankalin jama'a ya sake komawa kanta nan mutane suka ci gaba da zund'enta suna aibantata saboda munanan halayenta da suka bayyana a icon duniya,nan akayi addu'ah sarki ya sallami kowa,daga nan kuma aka tattara su Ladidi ita da Aisha akayi waje dasu harabar gidan inda ake hukunci dan gabatar musu da nasu hukuncin kamar yadda aka tabbatar,ga Yaseer da yazeed kuwa ana kammala yanke hukunci bayan zaman ya tashi nan suka fito daga fada da niyyan komawa gida,Aifa nan jama'a suka yi ta zuwa suna masa jajen abunda ya faru da Allah ya tsare saboda kasancewar sa tun asali mutum ne shi da bamai yawan shiga abubuwan daba nasa ba kuma ba'a sashi ba,sun jima suna karb'ar jaje daga mutane daban²,sai da k'yar suka samu hanya suka bar wajen suka nufi cikin gida gefen mahaifiyarsa,dan su kam dama tun kafin a tashi a fada suka k'udirce babu abunda zai kaisu gurin hukuncin tunda Allah ya bayyana gaskiya su wannan ma ya ishesu abun godiya ga Allah. Suna shigowa gefen na Fulani suka isketa ta idar da salatud-dhuha tana addu'ah,suna shigowa suka kalli juna suka yi mata murmushi, saurin idar da addu'o'in tayi sannan ta juyo garesu har lokacin yanayin damuwar da take ciki bai barta ba "Alhamdulillah..! Alaa kulli haliin..! Har kun dawo..??"+ "Ehh! Ummah mun dawo..sai gajiyar zama da muka sha.." "Alhamdulillah..! Tunda anyi nasara hakan ba wani abu bane..yanzun dai ku samu kuci abinci tunda Allah ya dawo da ku.." Maimakon su nufi abincin da tasa aka shirya musu kamar yadda take musu izini,saima taga YAZEED ya koma ya kwanta yana rufe idanu ya musu shiru,juyawa Fulani tayi ta kalleshi kafin tayi magana "Yazeed ka tashi ka samu kaci abinci saika kwanta ko..?" A hankali ya bud'e idanunsa yayi mata murmushi "Ummah ki bari na huta tuku,bama jin zan iya aiwatar da wani abu yanzun..." "Amma YAZEED ai daka samu kaci wani abu saika kwanta en,nima ba hanaka hutawan nayi ba..amma rabonka da cin abincin gida ka d'auki tsawon lokaci,saboda haka nake son ka fara cin abincin saika kwanta.." Yadda yayi shiru ya zuba mata ido kamar wanda baya cikin nutsuwar sa yasa ta yin magana,amma sai taji yayi shiru baice komai ba har sai data sake yin magana da d'an d'aga murya,hawayen da yake neman zubo masa yayi saurin mayarwa fuskarsa tana rikid'ewa zuwa yanayin damuwa,saurin tashi yayi ya nufi hanyar fita,da sauri ta kalleshi ta kuma juya ta kalli YASEER da shima ya bishi da kallo,ko kafin Fulani tayi magana tuni har ya fice da sauri,maganar ta mayar kan Yaseer cikin yanayin kid'ima "Yaseer maza kayi saurin binsa bamu san ina zai nufa ba a yadda ya fitan nan cikin damuwa,dan Allah kayi saurin binsa kada wani abu ya faru da shi..." Girgiza kai yayi sannan ya mik'e cikin hanzari yabi bayansa,b'angarensu ya nufa direct nan shima yaseer en ya iske shi har ya kwanta saman kujera idanunsa a rufe,ganin alamun yana cikin yanayin damuwa,sai yasa yaseer en k'arasowa cikin sanyin jiki,a kusa da shi ya zauna yana dafa shi,ba tare daya bud'e idoba ya furta "Dan Allah Yaseer ka kyaleni zuwa wasu lokaci,ina buk'atar na samu hutu da nutsuwar zuciya.." Cikin sanyi Yaseer ya girgiza kai da fad'in "Okay..! Amma dai kayi hak'uri kada ka sa wani abu a ranka har yazo ya haifar maka da wani ciwon..." Daga haka bai sake cewa komai ba ya mik'e yabar kusa dashi,can ya koma gefe ya zauna yana y'an tunane²nsa shima.... ^^^^^ *K'OFAR FADA* Yadda harabar gurin ya sake cika da al'ummah kai kace mutanen k'asar sin aka aro,wad'anda da dama basu samu damar halatar cikin fada ba a d'azun yanzun kam sun samu damar isowa dan ganewa idanusu abunda zai wakana,can daga sama cikin tanti sarki ne zaune sai manyan y'an majalisarsa,nan aka sake gabato dasu Aisha gaba kana mabugi ya halarto da zabgegiyar dorinarsa,ai koda Ladidi taga k'osashshiyar bulalar da aka d'auko nan take idanunta suka sake raina fata,jikinta ya sake d'aukan tsuma,in ina ta shiga yi tana magana cikin tsoro da fad'in "Yallab'ai dan Allah ayimin aikin gafara...amma wollahi zan fad'i gaskiya..." Nan jama'a suka d'auki dariya saboda kowa yasan k'arshen zancen nata bazai wuce ace wata sabuwar k'arya zata gindaya ba,wani kallo da madakin yayi mata yasa ta dad'a tsurewa dan haka ta shiga raba idanu tana kallon jama'a "Wollahi zan fad'a muku gaskiya...Allah yana kallo nima wollahi ba laifina bane...Ku saurareni kiji...!" Kamar an ce Ladidi ta d'aga idonta,can daga cikin jama'a ta hango shi sanye da bak'ak'en kaya tamkar fatalwa,babu abunda take iya hangowa a fuskar mutumin sai idanu kad'ai,ganin wannan mutum take ya sake rud'ata jikinta ya shiga kyarmar data fi ta farko,nan cikin zuciyarta ta furta "Wannan shi ne mugun gamo..Ya allah me yasa haka zata faru..?" Tana kuka take dad'a baza idanu dan tasan muddin ta sake yin magana tofa kashinta ne zai bushe,wannan mugun gamon da tayi ya sake haddasa mata tsoro nan take tayi shiru na dole,idanunta na fidda hawayen da Allah kad'ai ma'anar abunda suke nufi sannan kuma ita,cikin zuciyarta kuwa tarin damuwa ce data cika mata zuciya nan taci gaba da maganar zuci abunta "Wayyoo!! Allah na ni Ladidi yau mena aikata haka..? Son abun duniya da son zuciyata yana neman jefani a bala'in daya fi k'arfi na,me yasa baza ku kyaleni ba haka nan ba..!" Tana wannan suturun a zuci taji madakin ya fara tsaula mata bulala,wani ihun azaba data saki tuni yasa al'umamar wajen b'arkewa da dariya suna mata ihu,haka aka ci gaba da lafta mata bulalan tana kurma ihu,yayin da su kuma al'ummah suke ta lissafa mata adadin bulalunta tun daga d'aya har zuwa tamanin,koda aka cikata mata bulalanta nan ta zube a gurin ta shiga halin jinya,ihun kawai take amma hawaye sam yak'i fita daga idanunta,itama ga Aisha haka ce ta faru dan ita kam tsabar azaba har suma saida tayi saboda yadda taji saukar bulalun a jikinta,nadama kuwa da tarin Allah ya isa babu wanda bata aunawa Ladidi ba,haka kewar ahalinta da danginta da bata san ta inda zasu bayyana mata ba,tayi kuka sosai har sai da taji hawaye na neman fin k'arfin ta,daga nan kuwa aka tattara su akayi prison da su dan cika wa'adin da aka d'iba musu,koda suka isa bayan an aunasu zuwa d'akin da zasu zauna,ganin d'akin da aka kaisu ma kad'ai ya sake sawa nadamar Aisha ta dad'a ninkuwa bisa abunda aka ta aikata,haka ta kwanta nan a k'asa a ruf da ciki dan zama ma ji take ya gagareta,saboda yadda bayanta duk yake a farfashe,rigarta duk ta manne a jikinta sam tak'i fita,da k'yar ta rok'i alfarmar y'an d'akin nasu suka taimaka suka rabata da rigar jikinta,bayan nan kuma suka d'an taimaka mata suka goge mata jinin jikinta da ruwa. Isowar Captain Adama ma'aikaciyar gurin dake da alhakin kula dasu,wacce aka damk'a su a hannunta da zata dunga kula da duk al'amuransu a gidan har wa'adinsu ya cika,kuma ita zata basu duk wani aiki daya dace suyi a matsayin horon da zasu karba ta shigo ta tsaya can daga bakin k'ofa ta coge k'afa cikin muryar rashin mutunci ta furta "Wace ce Aisha da Ladidi anan.?" Cikin b'arin jiki da rashin kuzari Aisha tayi saurin furta "Gani Aunty...!" Wani kallon raini captain tabita da shi tana fad'in "Taso kizo muje..." Kasa motsawa tayi daga gurin jikinta duk yayi mata nauyi kamar yadda idanunta suka zama masu nauyin a gareta,cikin kalmar neman a tausayi mata ta furta "Dan Allah Aunty kiyi hak'uri wollahi bazan iya tashiba yanzun wollahi duka jikina ciwo yakemin..." "Keee! Dakata bana son rainin wayo,dan uwarki an fad'a miki hutawa kika zo yi..Nan gidan horo ne,idan kinsan kina buk'atar hutu uban waye yace kiyi laifin da za'a kawoki nan..? Dallah malama taso muje aiki na nan yana ji ranki.." Sabon kuka ta sake saki tana jan jiki,da kyar ta iya mik'ewa tabi bayan Captain Adama suka fice,d'aki bayan d'aki ta dunga bi da ita tana nuna mata band'ankunan da zata wanke,a k'alla saida ta nuna mata band'akuna sama da ashirin kuma kowanne bayan ta wanke saita tabbatar da sun fita,sannan kullum zata wankesu sau uku a rana,daga nan suka nufi kitchen nan ta nuna mata uban wanke²n da zata yi sannan ta juya da niyyar tafiya ta barta,ai fa nan Aisha bata san lokacin da zube gaban captain Adama tana rok'on ta akan ta tausaya mata,ta bari har ta samu sauk'i idan bayanta ya warke saita fara aikin,wani mugun kallo ta sake jifanta da shi tana durk'usawa kusa da ita ta d'ago fuskarta "Ke yarinya ce...amma makira...Lokacin da kika aikata abunda kika aikata shin kin tuna da yadda k'arshenki zai kasance..? Irinku abunda ya kamata ayi mukuma ya kamata yafi haka dan gaba ko saku akayi bazaku aikata ba.."2 "Dan Allah aunty wollahi nayi miki alk'awari ina samun sauk'i zanyi duk abunda kika ce nayi amma kimin wannan afuwar dan k'aunarki da annabin rahama.." Har captain Adama ta juya zata bar wajen ta juyo ta kalli Aishar,yadda ta rik'o mata k'afa yasa cikin fushi ta fizge k'afarta tayi cikin kitchen en,gishiri ta kamfato kana ta fito inda Aisha take ta kama hannunta ta shiga janta,a tunanin Aisha captain Adama ta hak'ura kamar yadda ta rok'eta,koda suka dawo cikin d'aki nan ta wurgata cikin d'akin sannan ta fizge mayafin data rufe jikinta da shi dan bata ga ta sa Riga ba a yanzun,gishirin data taho da shi daga kitchen ta dunbuzo sannan ta shiga bursunawa Aisha a jikinta,duk inda ya fashe da inda ma bai fasheba sai data mulke mata shi da gishiri,aiko azaba kam Aisha ta shashi a wannan lokacin jinta take kamar ba a duniyar data sani take rayuwa ba. Sanda captain Adama ta juyo kan Ladidi kuwa tuni ta jima da shiga layin ban hak'uri dan yadda taga Aisha na wata irin gantsarewa da ihu sanda ake murza mata gishirin,amma ina ko kad'an captain bata saurara mata ba bare taji hak'urin da take bata nan tasa aka rik'e mata ita ta mammanna mata shi a jikin ciwukanta,kana kuma ta sake tusasu a gaba suka nufi kitchen dan aikatuwa,kamar yadda ta nunawa Aisha aikin ta hakama ta nunawa Ladidi manyan tukwanen da zata kankama a wuta sannan ta kula dasu har zuwa sanda masu girki zasu karb'a... ^^^^^ Bacci ne ya d'auke shi tun daga rufe idon da yayi a haka yadda yake a kan kujeran duk jikinsa a takure,waiwayowa YASEER yayi a hankali ya kalleshi cikin tausayi dan yadda yaga ya takure jikinsa guri guda,ya jima yana kallonsa kafin ya mik'e k'afarsa akan k'aramin table en da yake kusa da shi ya rufe idonsa shima yana y'an tunane²,k'arar shigowar text wayarsa yasa shi saurin bud'e ido yana kallon wayan,kamar kada ya duba sak'on haka zuciyarsa taketa sak'a masa dan bai san abunda zai tsinto a cikin sak'on ba,amma ina tuni wani sashi na zuciyarsa ya bashi shawaran dubawa kawai,a hankali ya d'auka waya ya bud'e sak'on ya fara karantawa *"BRAVO* Lallai ne yaseer ka cika wawa mara tunani da har ka iya sadaukar da abunda ba lallaine ka sake samun dama akansa ba...Sai dai kuma kayi namijin k'ok'ari da har ka iya hak'ura da mulkin nan ka zab'i kub'utar da d'an uwanka,sai dai ka sani abunda ka aikata...ka tafka babban kuskure da zai kaika ga yin dana sani anan gaba,hallau kuma ka sani wannan abun daka aikata dai² yake da jefa kanka a matsalar data fi wacce ka fidda d'an uwanka aciki.....!" Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa,yana tunanin yadda zaiyi da hanyar da ya kamata yabi ya kare kansa wani sak'on ya sake shigowa "Ba kana tunanin kai mai wayo bane..Abunda zamu shaida maka shi ne,idan har kayi k'ok'arin sanar da wani wannan sirrin muna so ka tabbata yin hakan dai² yake daka sake jefa rayuwarka a matsala,wannan karon baza muyi k'ok'arin sake aikata kuskuren da muka yi a baya ba na baka damar da kai kuma kak'i amfani da ita,amma ka saurari hukuncin da zai biyo baya muddin wani yasan da wannan....." Shiru yayi yana goge gumin daya fara tsatstsafo masa zuciyarsa cike da taradaddin wanda yake aiko masa da wad'annan sak'onnin da kuma ta inda sak'on yake zuwa masa,a fili ya furta "Waye mai wannan sak'on...?" Tunani ne iri² ya addabe shi,nan yayi ta tunanin ya zama dole ya sanar da wani matsalar da take damunsa,dan bai kamata yayi shiru ba,dan yin shirun nasama zai iya hadsasa masa wata matsalar,tambayoyin da suke ta taso masa daga cikin zuciyarsa su suka hana masa samun nutsuwa.."Shin su waye suke masa wannan barazanar...? Dole nefa ya binciko su duk inda suke,kuma dole ne ya sanar da wani wannan matsalar dan gudun kada a k'ulla masa sharrin daya fi na YAZEED,shin waya kamata ya sanarwa..??" Farkawar YAZEED dai² lokacin da suka had'a ido yasa shi d'an saita nutsuwar sa,kallonsa yazeed yayi cikin wani irin murya ya furta "Wace ce JEEDDAH..?? Mamaki ne ya kama Yaseer jin tambayar data fito a bakin yazeed har ya kasa bashi amsa ya tsaya kawai yana kallonsa "Malam tambayar ka nayifa ka tsaya kallona haka..Kaga wani abune na kallo a nan..?" "A'a...! Kawai dai ina mamakin maganar taka ne..amma.! Wai ma mene ne dalilin wannan maganar taka ne..?" "Ina ruwanka da dalilin yinta...Tambayar ka nayi nd ina buk'atar ka amsamin..?" Harararsa Yaseer yayi sannan ya furta "To ban santa ba nima,idan ka damu da saninta zaka iya zuwa ka bincika da kanka..." Juyowa yazeed yayi ya kalleshi "Koh....?" "Ehhenn! Naga kana da damar yin haka,so no need ka tambaya ai.." "Okay...! Ka kyauta.." Ficewa yayi ya bar Yaseer nan yana binsa da kallon mamaki,dan ko kad'an baiyi tunanin yazeed en zaiyi masa irin wannan maganar ba a kuma irin wannan lokacin da yake ciki damuwa.. ^^^^^ B'angaren jeeddah kuwa tun bayan da aka fito daga fada bayan yanke hukunci bata zame ko ina ba sai gida dan bazata iya tsayawa kallon wannan dukan ba saboda tausayin Aisha data fara,direct gida ta nufa ta shige d'aki ta kwanta dan yadda take jinta kamar bata da lafiya,haka ko da Inno ta shigo gidan ta isketa a haka data tambayeta cewa tayi kanta ne yake mata ciwo,sannu ta mata sannan ta mik'a mata kud'i akan taje ta samu magani tasha saita kwanta ta huta kafin ta dawo,dan itan zata koma cikin gida. Yamma lik'is y'an aiken maimartaba suka risko k'ofar gidan su jeeddah,sallama sukayi tun daga bakin k'ofar sannan suka samu Yaro suka aika cikin gidan. Tashinta a bacci kenan itama lokacin tun bayan da Inno ta barta a kwance ta samu bacci ya d'auke ta,tana fitowa tsakar gida Yaro ya shigo yana gaya mata sak'on da aka turo shi,hijab ta saka har k'asa sannan ta d'auki nik'ab ta d'aura a fuskarta kana ta fita,da zuwanta k'ofar gida ta iske fadawa na dakon fitowarta,ganin fadawa a k'ofar gidan ita kanta saai da abun yaso bata tsoro,amma haka nan ta danne tsoron ta ta gaishesu,sak'on maimartaba na kiranta da yake suka sanar da ita sannan ta basu uzirin zata kulle gidan yanzun ta dawo,komawa tayi cikin gida ta sake kimtsawa sannan ta fito ta kulle gidan suka d'unguma suka nufi cikin gida tana gaba suna biye da ita,duk inda suka ratsa kuwa sai kallonsu ake saboda ganin yadda fadawa ke binta a baya,a tunanin wasu daga cikin mutane ko laifi tayi aka tuso ta a gaba,a haka har suka isa b'angaren fulani,gaban jeeddah sai fad'uwa yake dan bata san abunda yake faruwa ba dan basu ce mata komai ba kawai dai sunce maimartaba ya aiko su tafi da ita yanzun,wannan yasa take cikin fargabar rashin sanin me zata je ta tarar.........

0 Comments