GADAR ZARE CHAPTER 10

GADAR ZARE CHAPTER 10
Cikin kakkausar murya tace " what a matuk'ar razane "neme kake a bedroom d'in Zarah, in da in da Nasir ya fara yi yana kame-kame, ido Aunty Zainab ta k'ara zarowa waje kamar zasu fad'o k'asa take idanta suka kad'a sukayi jajir kamar gauta, a zuciye taci kwalar rigarsa cikin rawar murya tace " Naseer me kayiwa 'yata? ta fad'a a tsawace, cikin rawar baki yace " ummmm hmmmm da da da da dama bacci sukayi shine na kai su bedroom d'in su, ganin yadda yake magana cikin rawar murya da tsoro ne yasata k'in gaskata abinda ya fad'a mata, da sauri ta bangaje shi ta wuce d'akin Zarah'n dan gano ta. + Kwance ta iske ta tana ta baccinta hankali kwance babu alamar akwai wani abu ko faruwar wani abu dan kamar Naseer ya sani ya tsaya ya gyara ta sosai sannan ya fita ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske had'i da cewa "Alhamdulillah tana goge gumin dake zubo mata, a parlor ta iske Naseer tsaye inda ta barshi duk a tsoroce Naseer yake kamar kace masa k'et ya zunduma da gudu, kallansa Aunty Zainab tayi ita dai har a lokacin hankalinta yak'i kwanciya dan kwata-kwata bata yarda da Naseer d'in ba, haka kawai taji zuciyar ta na bugawa gabanta naci gaba da fad'uwa, a ranta tace " dole na sakawa Naseer ido sosai akan Zarah, a fili kuma ga mamakin Naseer yaga ta sakar mishi murmushi tace " am so sorry little bros, sai ta kansa Naseer yayi had'i da sauke ajiyar zuciya a hankaki ba tare data ji ba yace " haba Aunty Zainab kina tunanin faruwar wani abu ne a tsakani na da Zarah, ita fa k'anwa tace dan da ita da Ikram duk d'aya na d'auke na rasa meyasa kike tsoro na akanta, cikin dakewa take kallanshi har ya dasa aya batare data ko k'ifta idanta bane tace " ba haka bane Naseer akan yara na zan iyayin komai saboda ina matuk'ar san yarana. " Babu abinda na tsana kamar lalacewar tarbiyyar yara na zan iya yin yak'i akan duk abinda zai lalata min tarbiyyar su, Naseer abinda yasa kaga ina taka tsan-tsan akan ka sabonda bana san lalacewar zumuncin dake tsakanin ahalinku da namu ne wanda tun kafin a haifemu akayinsa k'ara matsowa gaf dashi ta kuma yadda suna iya jiyo numfashin juna idanta cikin nasa tace " kamar yadda kaji nace zan iya yin komai aka su to ina komai zan iya yi ciki kuwa harda kisan kai, da bada rayuwa ta, zan iya tsinke numfashin duk wanda yake neman datse min tarbiyyar yara, gaba d'aya jikin Naseer ya d'auki kerrrrma had'i da rawa dan ya gane hannunka mai sanda tayi masa, bai iya cewa komai ba sai murmushin yak'e dayayi mata kawai ya fita, bayansa tabi da kallo tana ayyana abubuwa da dama a ranta. Ranar kwata-kwata Naseer bai runtsa ba dan yadda yaga rana haka yaga dare sai juye-juye kawai yake ya kasa komai sai tarin tunaninnika iri-iri dasuka addabi zuciyarsa, Allah Allah kawai yake gari ya waye saboda yadda ya matsu yayiwa Dadyn sa maganar auren shi da Zarah, wajen k'arfe 10:30am ya fito cike da damuwa ya samu duk 'yan gidan su a dining area, shima zama a d'aya daga cikin kujerun cikin damuwa, Momyn sa ce ta lura da halin da yake cikin dan haka tace "autan Momy da Dady ya akayi ne? na ganka cikin damuwa, murmushi yayi kawai ya kasa cewa komai, a hankali Dady ya d'ago yana murmushi idansa nakan Naseer yace " kema kin san halinsa rigimamme ne, halin nasa na rigimar zai d'an tab'a. K'ara tab'a fuska yayi cikin shagwab'a yace " Allah Mom & Dad ina cikin matsananciyar damuwa seriously, cikin nutsuwa Mom da Dad suka mik'e had'i komawa kusa dashi kansa Momy ta rafa shafawa yayinda Dady ya rik'o hannayen shi cikin nashi yace " fad'amin damuwarka Auta na, cikin shagwab'a yace "Dady AURE nake so cak daga Dady har Momy suka tsaya daga abinda suke yi murmushi Dady yace " Alhamdulillah Auta ya girma, ka samo matar? k'eyarsa ya shafa cikin alamun jin kunya yace " eh, "dat is my boy cewar Momy tana murmushi, Dady yace " wacece yarinyar hope dai 'yar mutunci ka samo mana, dariya yayi had'i da cusa hannunsa cikin kwantaccen gashin kansa yace " Dady ai 'yar gida za'ayi dan 'yarku ce ma, dariya sukayi had'i da cewa wace ita? "ZARAH yace batare da fargabar komai, cak duk suka tsaya saboda sun san halin da ake ciki akan Zarah dan har yanzu batasan suwaye asalin iyayenta ba, idan ko matuk'ar Naseer zai aure ta sai ta asalinta kuma sun san babu abinda surukar tasu Zainab ta tsana sama da hakan, cikin sanyin jiki Momy tace " ita Auntyn taku ta sani ne? "No Mum ku zaku sanar da ita, "ita Zarah'n ta sani ne? Dady kuma jiho masa wata tambayar "Momy & Dady tambaya haka da yawa? " eh dole muyi maka tambayoyi saboda kasan halin da ake ciki akan Zarah da Zainab, kai kasanin kanka ne babu abinda Zainab d'in ta tsana sama da Zarah tasan ba itace mahaifiyarta ta gaskiya ba, kuka sosai Naseer yasaka harda hawayensa yana duddura k'afa,ni dai Allah kawai a bani auren Zarah in ba haka ba na fara karuwanci, dariya sukayi daga d'aya Dady yasa hannu ya mutsini bakinsa, Momy kuma ta rankwashe shi, Dady yace "karka damu Auta matuk'ar Zarah na sanka babu abinda zai hana ka aure ta in sha Allah, sai dai idan Allah bayyi matar bace. Kiss yayiwa iyayen nasa yana cewa " yawwa Dady thank you & I love you, tea d'in Momy ta d'auka tana saka masa a baki had'i da shafa kansa, zuciya Naseer fes ya fita bayan ya gama karyawa, shawara sosai Dady da Momy suka inda daga k'arshe suka yanke fara yiwa Zainab da Mannir magana kafin su nufi Abban Zarah kai tsaye saboda suma a basu girman su a matsayinsu na wa'yanda suka rik'e ta, washe gari Dady yayiwa Mannir waya yace kome yake yazo nan da kwanaki biyu karya wuce haka, sosai hankalin Mannir ya tashi dan haka ya kira wayar Zainab yake tambayar ta kota san abinda ya faru " mik'ewa tayi daga cikin yaran ta koma bedroom cikin nutsuwa tace " wallahi ban san meya faru ba d'azu dai nima Momy ta kira ni tace idan ka tashi zuwa mu taho tare, cikin sanyi jiki yace " Allah dai yasa lafiya, "Amin kawai Zainab tace itama cikin sanyin jikin, gawar da maganar yayi ta hanyar cewa " ina yara na? dariya tayi tare da kwala musu kira, da gudu suka shigo a tare mik'awa Zarah wayar tayi tana cewa " ga Dady, cikin shagwab'a Ikram ta fara diddira k'ara tana cewa " Allah Momy kin fi san Zarah a kaina komai ita kike fara yiwa ko ki bawa kafin ni, komai ita, ko kiran sunan mu zakiyi Zarah kike fara kira kafin ni, wani lokacin ma idan zaki kira sunana mantawa kike yi ki kirani da sunanta Zarah, murmushi Zainab tayi had'i da rungumo ta jikinta tace " Ikram basazi tab'a gane dalili bane, amma kema ina sanki sosai kamar yadda nake santa, Zarah na waya da Dady amma gaba d'aya hankalinta nakan rungumar da Ikram tayiwa Momy da sauri tayiwa Dady sallama had'i da mik'awa Ikram wayar tana tureta daga jikin Momy ita kuma tana shigewa jikinta dariya Zainab tayi danta fahimci kishi Zarah keyi dan haka ta mik'e tana cewa ni karku karya ni, Naseer kuwa tunda akayi abin nan bai kuma zuwa gidan ba duk da yana cikin tsananin damuwa da cutuwa na rashin ganin Zarah'n kwana biyu, suma su Zarah sun gaji da cikiyarsa dayi masa waya dan a rana sai suyi masa sau 10 suna tambayar shi yaushe zai zo. K'arfe 1:20pm na rana Mannir ya dira a Amin Kano international Airport, yana fitowa ya hangi direba na jiransa batare da b'ata wani lokaci ba ya shiga cikin motar suka nufi gida, kasancewar sun san Dady na kan hanya yasa suka gyara gida tsaf had'i da shirya dinning table, suna jin k'arar tsayawar motar da gudu suka fita suna rige-rigen isa gare shi da sauri shima cike farin cikin ganin yaran nasa ya k'araso gare su da sauri ya d'aga Zarah sama yana juyi da ita jin k'arar buga k'afa yasa shi juyawa Ikram ya gani tsaye ta kwab'e fuska tana k'ok'arin yin kuka da sauri ya sauke Zarah ya nufi inda Ikram tana itama d'agata sama yayi yana dariya yace " haba Ikram meyasa kin fiya rigima da yawa ne, cikin shagwab'a tace "bakune kai da Momy sai kuyi ta nuna man san ka ba, dariya yake yana shiga cikin gidan tsaye ya iske Zainab taci uban kwalliya tana sakar mishi murmushi, da sauri ya k'arasa inda take yana dire Ikram a k'asa, cike da d'okin ganin juna ya rungume a k'irjinsa yana mayar da numfashi ganin yaran su na tsaye yasata janye jikinta daga taja hannunsa zuwa bedroom, sai da yayi wanka yayi sallah sannan suka fito dinning area gaba d'ayan su har yaran suke cin abincin cikin raha. Bayan sallar magrib bayan yayi sallah suka nufi gidan El-Mustapha, a parlor suka iske Momy zaune tana lazimi, sai da ta k'asa sannan ta mik'e cike da fara ta nufo su, har k'asa suka durk'usa suka gaida ita, sannan ya tambayi Dady da Naseer, " suna masallaci Momy ta bashi amsa cike da kulawa jin an kira sallar ishsha ne yasa mik'ewa ya fiya zuwa masallaci, bayan idar da sallah tare suka shigo da Dady da Naseer suna raha abin sha'awa kasancewar Dady shi mutum ne mai sauk'in kai da wasa da dariya, direct dinning suka wuce kasancewar acan suka hango Momy da Zainab zaune. Abincin suke ci hankali kwance, Mannir ya kalli Naseer yace " kai ka fiye ci wallahi haba ka rink'a ci a hankali mana, kafin Naseer yayi magana Dady yayi saurin cewa " ah Mannir kafa daina wasa da Naseer karya rainaka dan ya kusa zama sirikinka yayi maganar yana kallan fuskar Zainab, Mannir da bai gane abinda yake nufi ba yace " sikina kuma Dady? yama nemi sirinsa tun wuri, itako Zainab datasa maganar gabanta ne yayi muguwar fad'uwa a firgice ta d'ago kai tana kallan Dady ganin ita shima yake kallo yasata yin yak'e had'i da sunkuyar da kanta bata k'ara kai komai bakinta ba cukalin kawai take juyawa Dady da gaba d'aya halinsa yana kanta yayi murmushi gami da amsa tambayar Mannir "'yar ka yake so Zarah zaka bashi? Ruwan da Mannir ya k'urb'a bai kai da had'iyiwa bane ya fito dan ba hanyar da zai wuce take ya kware ya shiga tari, daga Momy har Dady kallansa kawai suke babu wanda yake k'ala ba, Zainab da hankalinta yakai k'uloluwar tashi kasa motsi tayi, cikin tashin hankali Mannir yace " what? a razane had'i da cewa wacce Zarah? Murmushi Dady yayi irin nasu na manya yace " *FATIMA MUHAMMAD DAURA* hope yanzu ka gane wacce nake nufi? Kallan Zainab Mannir yayi karaf suka had'a ido ganin yanayinta ne ya ganar dashi manufarta, mayar da kallansa yayi ga Dady yace " haba Dady yama za'ayi Naseer ya auri Zarah, hakan ma bazai tab'a yiyuwa ba, Naseer zayyi magana Dady yayi saurin dakatar dashi da hannunsa ba tare daya kalli inda Naseer yake ba idansa nakan Mannir yace " meyasa hakan bazai yiyuba? "Dady dat is impossible ace Naseer zai auri Zarah, a tsawace Dady yace " nothing is impossible, gaya min abinda zai hana yiyuwar hakan, shin addini ne ya haramta aure a tsakanin su ko al'ada? bani Hadith ko ayar data zo akan ba aure tsakanin Naseer da Zarah, sannan ka fad'amin dalili guda d'aya wansa Naseer bai cika ba acikin sharudd'an aure, ko ka gayamin rashin nagartarsa dazai hana a bashi aure, ni dai a iya sani na ban haifi mazinaci, d'an shaye-shaye ko d'an gay ba, dan Allah ya tsare ni, gaba d'aya maganar da yakeyi da Zainab yake yi dan yaga lokacin da Mannir ya kalle ta, yana dai fakaicewa ne kawai da Mannir,Dady yaci gaba. "Yanzu a ganin ku kunyiwa Zarah da mahaifiyarta adalci kenan? da sauri Zainab ta d'ago kai tana kallan Dady dan babu abinda tafi tsana arayuwarta irin tayi musu laifi, da mamaki take kallan Dady batare da tayi magana ba, shima ita yake kallo ido cikin yace " yes Zainab abinda make nufi kenan, duk kun san Zarah kad'ai mahaifiyarta ta haifa, amma kunk'i sanar da ita gaskiya kodan ta rink'a yiwa mahaifiyarta addu'a, shin tun haihuwar Zarah har kawowa zuwa ta tab'a yiwa mahaifiyarta addu'a ko sau d'aya ne tak arayuwarta, kun san darajar addu'a d'a ga iyayen su musamman mamata, take jikin Zainab yayi mugun sanyi ta fara zubar da hawaye dan bata tab'a tunanin haka a rayuwarta ba, Dady yaci gaba " har zuwa yaushe zaku sanar da ita gaskiya ko mahaifiyarta zata rink'a samun addu'ar tilon 'yarta d'aya jal a duniya, shin yaushe ne Zarah zata san cewar ita marainiya ce danta rungumi maraicinta ta tallafawa mahaifiyarta da addu'a, kun san meye amfanin haihuwa a duniya? "To idan baku sani ba yau ku sani wannan yana daga babban dalilin haihuwa, tunda Fatima ta rasu bata tab'a riskar addu'ar Zarah ba, shin kuna tunanin da zata dawo duniya zata yi farin ciki da hakan? sosai kukan Zainab ya k'ara har ya fara yawa hakan bai hana Dady ci gaba da magana ba " Zarah macece duk tsiya gidan wani zata idan ma bata auri Naseer ba dole wani zata aura, kuma komai daren dad'ewa wallahi Allah Zarah sai ta san bakune asalin iyayen ta ba, duk ranar data san hakan badaga gare ku zaku fahimci abinda nake nufi, dan matuk'ar wani ne ya sanar da Zarah gaskiya zaku shiga mummunan tashin hankali dan sai tayi muku boye akan rashin adalcin da kukayi mata, tana iya jin ma kun fita a ranta. Dan haka ina baku shawara akan tun wuri tun kan dare yayi muku ku gaggauta sanar da Zarah gaskiya da kanku koda bazaku bawa Naseer aurenta ba, kuma bawai ina yin maganar akan Naseer bane ina yin maganar ne saboda ku kan ku da kuma gaskiya na dad'e inasan baku shawara akan haka, cikin tsananin kuka Zainab ta mik'e ta nufi gaban Dady ta durk'usa dakyar ta iya sausauta kukan tace " nagode, nagode sosai Dady da nusar dani abin da ban sani ba, ko na manta, idona ya rufe daga ganin gaskiya, kuma nayi hakan ne saboda bana san Zarah ta shiga damuwa kota san zafin maraici bayan ni mahaifiyarta ta rik'e ni tsaka ni da Allah, murmushi Dady yayi yace " Zarah ba marainiya bace matuk'ar tana da uwa irinki Zainab, da sauri ta d'ago ta kalli Dady, murmushin sa yaci gaba sayi" eh Zainab kowa yasan irin so da gatan da kikewa Zarah fiye da 'yar cikin ki, kuma har gobe Zarah bata da uwar data fiki a duk fad'in duniya saboda ke k'anwar mahaifiyarta ce uwa d'aya uba d'aya, kuma shi kanshi mahaifin Zarah kamar d'a yake ga mahaifinki Alhaji Abdullahi, kuma shiya rik'e ki sannan yadda zakiyiwa Ikram baki ya kamata haka zakiyiwa Zarah ma ya kamata saboda kin shayar da ita, cikin kuka tace " in dai nice mahaifiyar Zarah na bawa NASEER AURANTA. Nasa ranar auren da kai na nan da wata biyu, da saboda tsananin farin ciki Naseer mik'ewa yayi ya d'auki Zainab cak yana zaga parlor da ita , yak'e Mannir yayi yace " kai aje min mata karka karya min ita kasani k'ara aure ban shirya ba, harara ta wurga mai, gaba d'aya akayi dariya, hawayen fuskarta Naseer ya shiga goge mata yana rarrashinta, a hankali ta Zainab ta kamo hannun Naseer cikin nata tana kallansa hawaye na zuba tace " Allah ya sani nafi san Zarah fiye da komai a rayuwa ta bana iya had'a santa da komai, Naseer Allah da mala'iku da Dady, Momy, Mannir suna shaida na baka AMANAR ZARAH har abada har iyakar rayuwarku ta fad'a tana kallan fuskar Naseer da take ta fara zubar da gumi zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi k'irjinsa yayi masa mugun nauyi, k'ara rik'e hannunsa tayi gam cikin nata ta mayar da gaba hankalin ta kansa tace " ka karb'i amanar dana baka? Take jikinsa ya d'auki kerrrrrma kamar mazari ko'ina na jikinsa rawa yake, take mak'ogwaronsa yayi masa mugun d'aci, gashi idan kowa na kan sa dan haka cikin rawar baki yace " a'a b........ a....... n.... b'...... a, b..... a, gaba halin su yayi mugun tashin duk suka mik'e a firgice suna kallansa, da sauri ta saki hannunsa tana yi masa wani irin kallo a fusace tace ".......... A fusace tace " what Naseer me kake nufi? Murmushi yayi wanda ya k'ara bayyanar da kyan fuskarsa hannun nata ya sake rik'owa cikin nashi yana kallanta ido cikin ido yace " Aunty Zainab kin tab'a ganin ambawa mutum amanar kansa da kansa? bata bashi amsa ba idanta dai na kansa, yaci gaba " Aunty ki kwantar da hankalinki domin Zarah itace ni, ni ne ita, Zarah rayuwa ta ce, wallahi Allah babu wani abu da nake so a duniya sama da ita, tun a yarinta nake san ta, a lokacin ban san meye so ba ina dai jinta ne kawai a raina, Aunty da so da k'aunar Zarah na girma dashi na ginu a raina , in ba Zarah ba Naseer, matuk'ar ina raye bazan tab'a bari Zarah ta nemi wani abu ta rasa ba, bazan tab'a bari ta shiga halin damuwa ko k'unci ba, bazan tab'a barinta a wani yanayi marar dad'i ba balle harta kai ga ta koka. "Aunty! Zarah ya kamata kibawa amana ta domin santa nake mata yayi yawa ya wuce tunanin mai tunani, ya wuce hasashe, ya wuce duk inda ake tsammani, Aunty akan Zarah kwata-kwata bana iya controlling kai na, idan na kanta mantawa nakeyi da kowa da komai, na manta ni kai na waye, please ina rok'on ku ku tayani da addu'a Allah ya sausautawa zuciya ta kanta, ya k'arasa maganar hawaye na gangarowa daga idansa, jikin Aunty Zainab yayi mugun yin sanyi, take zuciyarta ta karaya tausayinsa ya kamata, a hankali ta k'ara matsawa kusa dashi tana goge masa hawayen fuskarsa itama hawayen na zubo mata. "Aunty ni garkuwa ni a gare ta, bazan tab'a bari wani abu ya sameta ba, matuk'ar ina raye, idan ko har ina raye wani abu na bak'in ciki ya same ta wallahi bazan tab'a yafewa kai na ba, ya bud'i baki zayyi magana tayi saurin hana shi, cikin farin ciki take murmushi yayinda hawaye ke zuba daga idanta, yau burinta ya cika ko yau ta mutu tasan Zarah tana hannu na gari wanda zayyi zame mata kariya kuma garkuwa, wanda zai kawar mata da maraicinta ya zame mata uwa da uba, ya bata gatan duniya da matabbacin farin ciki a duniyarta, a hankali tace " nagode Naseer, nagode sosai, Allah ya barku cikin matsananci dauwamammen farin ciki mara yankewa, Ubangiji ya sawa auren ku albarka, Allah ya tsare ku da tsarewarsa ya kare ku, Ubangiji duk wanda zai zamewa raywarku matsala Allah ya d'ai-d'aita rayuwarsa ya tozarta shi ya wulak'anta. Murmushin jin dad'i Naseer yayi had'i da cewa " Amin ya Allah Momy, matsowa kusa dasu Mannir yayi yana dariya yace " yanzu fa Naseer da Zainab an d'inke dan tunda ta baka auren Zarah'n ta ba yakai a duniya, dariya yayi yace " to Dady yayi maganar da sigar tsokana, dariya sukayi gaba d'ayan su had'i da cewa " au har mun zama Momy & Dady tun yanzu? " ah ba dole na ba, ai ba jira da zafi-zafi kan bugi k'arfe, dariya Dady yayi dake tsaye a gefe tun d'azu yana kallansu cike da tausayin Naseer yace " ai dole k'auwar nak'i, kuma idan da kara ai dole ace da mijin iya baba, haka dai suka sha hira da barkwanci. Zainab kwance akan bed ta kasa runtsuw tunda suka bar gidan Mannir take cikin damuwa ta kasa skin ranta yaran ma har sun gane sun fahimci tana cikin damuwa, a hankali Mannir ya zauna kusa da ita yayinda idanunshi ke kanta k'uri baya ko k'iftasu, sai da ya rik'o hannunta cikin nashi sannan Zainab tasan ya shigo, firgigit tayi alamun tsorata, suna had'a ido ya sakar mata murmushi, martanin murmushin ta mayar masa, har a lokacin idanuwansu na sark'afe cikin na juna, "Zainab wai meyake damunki ne tunda muka dawo daga gida kika canja, kika shiga damuwa, idan akan auren Naseer da Zarah ne, ki kwantar da hanklinki matuk'ar baki so babu mayyi miki dole, idan baki san auren ko hanlinki bai kwanta, kawai a hak'ura, kar azo a jawo matsalar da muzuncin dake tsakanin iyayen mu shekara da shekaru ya lalace. "Duk yadda zamu so Zarah ko muso mata alkhairi a bayanki muke, dan zan iya cewa duk duniya babu wanda ya kai ki san ta, Aunty Zainab batayi magana sai da ta bari ya kai aya sannan cikin sanyin jiki tace " ko d'aya My dear, ni damuwata ba akan auren Naseer da Zarah bane, ni asalima naji dad'i yayi farin cikin auren nasu, dan ina gani addu'a ta dana dad'e inayi ta k'arb'u dan ina da yak'ini akan Naseer zai rik'e min ita, zai bata duk wani abu da mace ke da buk'atar samu daga wajen mijinta, "to akan me kika damuwa? Mannir ya tambaya. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace " ta yadda zan fuskanci Zarah na sanar da ita banice mahaifiyarta ba, ba nice na haife ta ita ba 'ya ta ce ta ciki na ba, ta k'arasa maganar hawaye na zuba, "akan wannan kike damur min kanki, yayi maganar cikin dakewa, kai ta d'aga masa alamar eh, murmushi yayi sannan yace " na riga da na gama tsara komai, da sauri ta kalle shi tace " kamar ya? "eh yace, Family meeting zamuyi dan harna gama fad'uwa duk wad'anda suka dace, "su waye suka dacen, dawa-dawa ka gayyata? " na sanar da mahaifin Zarah, nace yazo da iyayensa, kakanin Zarah'n sannan na sanar da Babanku nace yazo da su Momy kuma na sanar da su Dady da Momy sai Naseer, Zarah, Ikram, ni da ke, "yaushe za'ayi? Zainab ta tambaya, kai tsaye yace " on 16/jan/2019 kinga jibi kenan, cikin sanyin jiki tace " Allah ya kai mu, "Amin yace yana jan hancinta. MEETING DAY A babban parlor gidan Mannir kowa ya hallara yayinda gaban Zarah keta fad'uwa ta rasa dalili, kowa ya nutsu saboda kowa da manyansa a wajen, El-Mustapha ya kalli Naseer yace " bud'e mana taro da addu'a, kai ya risina cikin girmamawa ya fara addu'a, sai ya kammala sannan El-Mustapha ya kalli Alhaji Abdullahi yace " kai ya kamata kayi bayani, cikin sanyin jiki Alhaji Abdullahi ya kalli Zarah wacce gaba d'aya tausayinta ya gama kamashi yace " Fatima a hankali ta d'ago kai ta kalle shi had'i da cewa " na'am cikin sanyin jiki, yaci gaba " wannan gaba d'aya naki ne danke akayi shi, ita dai kallansa kawai take batare data kuma cewa komai ba, " saboda lokaci yayi daya kamata kesan ke wacece, kisan asalinki da kuma iyayenki da gaskiya domin komai daren da d'ewa wata rana dole sai kin sani, da k'arfi k'irjinta yayi muguwar bugawa cikin rashin fahinta ta kalli Zainab da tunda aka zauna take sharar hawaye, itama ita take kallo, cikin rawar baki Zarah ta bud'e baki zatayi magama amma ta kasa furta koda kalma d'ayace, yaci gaba Zarah, ZAINAB DA MANNIR!!! BA SUNE IYAYENKI NA GASKIYA BA, wata irin saukar aradu Zarah taji a ranta take kunnuwanta suka fara jiyo mata tsawa kamar ana ruwan sama. A hankali Alhaji Abdullahi ya nuna mata Muhammad Daura yace " wannan shine mahaifinki, sannan ya nuna mata iyayensa dake gefe yace " wad'annan sune kakanninki na wajen uba, sunan mahaifiyarta FATIMA shine aka mayar miki dashi bayan rasuwarta, kuma Fatima 'yata ce ta ciki na Yayar Momynki Zainab ce uwa d'aya uba d'aya itace ta rik'i Zainab tun daga yaye harta aurar da ita, ni da Mama ya nuna mahaifiyarsu Zainab yace " mune kakaninki na wajen uwa, daga nan kwashe labarin komai tun daga zuwan Abbanta kano har Aurensa da FATIMA 'yarsa da labarin Zuwairat da komai ya sanar da ita bai b'oye mata komai komai. A hankali ya mik'a mata photo album k'ato yace " gaba d'aya hotuman mahaifiyar ki ne aciki, tun tana yaririya, har zuwa girmanta harda wanda tayi da cikinki, tab tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, fad'ar halin bak'in ciki da damuwar da Zarah ta shiga ma b'ata lokaci ne, dan ta shiga mummunan tashin hankali hannunta na rawa ta k'arb'i photo album d'in, amma ta kasa bud'awa, ci gaba yayi da magana da magana "sannan mun bada AURENKI GA NASEER, mik'ewa Zarah tayi rungume da album d'in a k'irjinta, tana shirin fita dan ita bama tasan inda kanta yake ba, kwata-kwata bata cikin nutsuwarta da hayyacin ta. Idanta babu ko d'igon hawaye saboda tsabar tashin hankali ita rok'on Allah ma take akan ta samu tayi kukan ko ta samu taji dad'in ranta, ganin bata cikin hayyacinta yasa Naseer yunk'urawa zai rik'o ta, da sauri Dadynsa ya rik'e masa hannu batare daya kalle shi ba, hakan yasashi komawa ya zauna dole, a firgice Aunty Zainab ta mik'e cikin matsanancin ta rungume ta a jikinta. A hankali Zarah ta zame jikinta daga Zainab tana k'ok'arin barin parlor, k'ara rik'o ta Zainab ta yi cikin kuka tace " please Zarah karki fishi dani na rashin k'in sanar dake gaskiya da wuri a baya baki kai ahekarun dazaki iya d'aukar bak'in cikin maraici ba shiyasa, a fili Zarah ta maimaita MARAICI!!!! sai lokacin taji wani irin kuka yazo mata aiko da k'arfi ta sake shi, wani irin mahaukaci kuma matsanancin kuka ta durk'ushe a wajen tanayi, duk wajen sai da akan tausaya mata harda masuyin kwalla da hawaye, cikin fitinan kuka tace " yanzu ina 17yrs a duniya mahaifiyata tana da 17yrs da rasuwa amma ko sau d'aya ban tab'a yi mata wani addu'a ko wani abu da zai sanyata cikin farin ciki harya san tana da 'ya ba, mai yasa baku sanar dani da wuri na k'araci rayuwata wajen yi mata addu'a ba, mai yasa zakuyi mana haka ni da ita ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka. Cikin kuka Zainab ta k'arasa inda take " wallahi Zarah banak'i sanar dake dan wani abu bane sai dan san da nake miki, Zarah ina sanki fiye da kowa da komai a rayuwa ta, dan Allah Zarah karki barni, da sauri Zarah ta rungume Zainab tana cewa " Momy bakiyi min komai ba sai alkhairi, kin min gatan da kowacce take bawa 'yarta, kuma kin shayar dani ke kikayi rainona, ke kikayi min komai Momy ya za'ayi na barki ko nayi fishi dake matuk'ar ina san ganin dai-dai a rayuwata, duk duniya bani da uwar data fi har yau har gobe, Momy bazan tab'a yin fishi dake ba duk girman laifin da zakiyi min, nasan kina so na Momy ni shaidace, ta fad'a tana k'ara shigewa Zainab d'in sosai ko zataji sanyi a ranta. Cikin kuka Ikram ta taso itama ta rungume su, duk jama'ar dake wajen babu wanda bai zubar da hawaye ba saboda tsabar jin tausayinsu, cikin kuka Zainab tace " na k'ara miki wani lafin dan nabada aurenki ga Naseer, murmushin k'arfin hali Zarah wanda yafi kuka ciwo tace " bakomai Momy, nasiha mai ratsa jiki, jini, jijiya da duk wata gab'a dake jikin mutum El-Mustapha yayi musu, ya kuma k'ara bawa Zarah hak'uri akan ta rungume jarabawarta, ta godewa Allah ma ita tana da mahaifi da kuma dangi da 'yan uwa masu tsananin k'aunarta, ga kuma uba Zainab da Allah ya bata, akwai wanda ake haihuwarsu ba uwa, ba uba, ba wa, ba k'ani, babu dangin uwa balle na uba, basu da kowa a duniya amma suke rayuwarsu cikin farin ciki da godiyar Allah, haka sukayi ta kawo mata musu da k'issoshi, suka nuna mata shi kanshi wanda akayi duniya da lahirar damunsa haka ya taso ba uwa ba uba cikin maraici, sosai jikinta yayi mugun yin sanyi ta kuma k'ara godewa Allah abisa ni'imomin dayayi mata, ta kuma rungumi K'ADDARAR TAH, had'i da guduwar niyyar yiwa mahaifiyata addu'a ba dare ba rana. Tun daga wannan ranar Zarah ta shiga yiwa mahaifiyata addu'a sosai, kuma tsoran Allah ya k'ara shigarta, a d'ayan b'angaren kuma wata azababbiyar soyayya ce ta shiga tsakanin Zarah da Naseer, 24hrs suna tare a waya ko zahiri kullum yana gidan Aunty Zainab wajen Zarah, kwata-kwata bashi kowa da kansa sai nata, gaba d'aya rayuwa da lokacinsa ya sadaukar mata, sosai soyayya mai tsananin k'arfi ta shiga tsakanin su, ta yadda d'aya baya iya yin 2hra ba tare da yaji ko yaga d'ayan ba, kowannen su ji yake kamar bazai iya yin rayuwa babu d'ayan ba, ji suke numfashi suma yana fita ne da k'ara ruruwar so da k'aunar junansu. Naseer da zaune a bedroom d'in su yayinda Ikram ke gefe bacci ya d'auke ta, suna tsaka da hira Zarah ta hango kenkeso (cockroach) ai bata san sanda ta fad'a jikin Naseer tana ihu ba shi kuma sai dariya yake, da ita ya mik'e a jikinsa ya kashe kenkeson yakai toilet, sannan ya dawo da bedroom, a lokacin hankalin Naseer ya dawo jikinsa, tana k'ok'arin sauka daga jikinsa yasa hannu ya k'ara matse ta gam, ya k'ura mata ido itama shi take kallo yanayin kallan da sukeyiwa junane yayi mugun kashe musu jiki had'i da saukar musu da sakala, a hankali Naseer ya tallafo hab'arta da hannusa yakai bakinsa saitin nata, kasa hana shi ta yi sakamakon muguwar da jikinta yayi, a hankali ya had'e bakin su waje d'aya ya shiga aika mata da hot kisses, yayinda hannunsa ke kai breast d'inta, dai-dai lokacin Aunty Zainab ta shigo, cak ta tsaya numfashinta yana k'ok'arin d'aukewa idanunwa take sukayi jajir suka firfito kamar zasu fad'o k'asa. Da k'arfi tace " NASEER!!! a zabure duk suka mik'e, cikin matsanancin tsoro suke kallanta, cikin kerrrmar jiki da rawar baki Naseer ya bud'e baki zayyi magana ta daka masa wata gigitacciyar tsawa a fusace had'i da cewa " get loose 4rm here, da sauri yana kerrrrma ya fice, a hankali ta maida kallanta ga Zarah dake tsaye jikinta nata kerrrrma, takai wajen 5 minutes tsaye kawai tana kallanta, batare data ce mata komai ba, a hankali ta juya zata fita, har ta kai bakin k'ofa ta juyo tace " karki sake ki bari yayi miki wayo ya karb'e abu mafi girma da daraja a wajen ki da rayuwarki (BUDURCI), ta juya ta k'arasa ficewa, kasancewar Mannir baya nan ya koma Paris tun bayan gama meeting ya koma dan bai gama course d'in da aka tura shi ba, yasa gari na wayewa ta kira Dadyn Naseer tace " please Dady ina so matso da bikin Zarah da Naseer a mayar dashi nan da days, next Friday, jin yadda muryarta ke rawa yasa shi fuskarta akwai wani abu dan haka ba musu ya amince. Sosai aka shiga shirye-shiryen biki haik'an, wanda shi Naseer hakan ma dad'i yayi masa, shidayake namiji ne dakewa yayi ya nuna kamar babu abinda ya faruwa, sab'anin Zarah da tunda Zainab ta kama su ta koma wasan b'uya da ita, kwata-kwata ta daina fituwa falo ta koma zaman d'aki, itako Zainab tayi banza da ita, ana saura kwana biyu d'aurin aure Zarah ta tashi da mugun zazzab'i da cewon kai ga yawan amai, kwata-kwata bata jin dad'in jikinta, sosai ta galabaita a cikin yini d'aya tak, Ikram ce tazo ta sanarwa da Zainab cewar Zarah bata da lafiya sosai, a firgice ta mik'e ta nufi bedroom d'in ganin halin da take ciki ne yayi masifar tada hankalin Zainab, da sauri ta koma parlor ta kira Naseer tace idan yana kusa please yazo gida yanzu yakai Zarah hospital, kasancewar basa baya kasa shima hankalin shi yayi masifar tashi yace" wallahi Aunty bana kusa, meke damunta bata jira bashi amsa ba ta mik'e ta zaki key d'in mota da hijab ta sumgumi Zarah tayi hospital, da sauri doctor suka karb'e ta sukayi ciki da ita gwajin farko likita ya gano Zarah nada shiyar ciki na wata hud'u, umarni yayiwa Zainab data biyo shi office, bayan ta zaune ne, cikin murmushi yace " congratulations your daughter is pregnant, "ban gane ba doctor tace, murmushi yayi had'i da cewa Zarah tana da ciki harna wata hud'u.............. Dariya Aunty Zainab tayi had'i da cewa " kai badai ciki ba, duba dai da kyau ka ganin, murmushi yayi had'i da cewa " ciki ne da ita mana harna wata hud'u, tsaki tayi cikin fishi ta mik'e tana magana " baka san aikinka ba wallahi, ban san mahaukacin daya baka aiki ba, a baya Doctor ya biyo ta yana mata magana amma ko kallansa bata yi ba, direct wajen Zarah ta wuce, da taimakon nursing suka saka ta a mota ta, tana driving tana mita ita kad'ai harta k'arasa k'ofar wani private hospital. Da gudu nursing suka fito, cikin girmamawa suka gaida ita had'i da d'aukar Zarah suka wuce ciki da ita, nan ma gwajin farko Doctor ya shaidawa Aunty Zainab tana da shigar ciki na 4 months, nan ma tijara ta zazzagawa Doctor d'in sannan ta d'auki Zarah tayi ficewarta, wasa-wasa dai sai da Aunty Zainab taje hospital har biyar amma duk maganar d'aya ce shine ZARAH TANA DA CIKI, har government hospital taje amma duk haka ake ci mata, sosai jikin Zainab yayi mugun yin sanyi amma har a lokacin bata yarda Zarah nada ciki ba, zaune tayi a cikin mota ta kasa yin komai jikinta sai kerrrrrma, a hankali ta juya ta kalli Zarah, takai wajen 10 minutes bata d'auke idanta daga kanta, tana san gano wani abu amma ta kasa, rasa abinyi tayi, ta jima tana tunani kafin daga k'arshe ta yanke shawarar kiran Family doctor su, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi sannan ta ciro wayarta daga cikin jaka tayi dialing. Ringing d'aya yayi picking cikin girmamawa, yace " Hajiya ya gidan? bata samu damar amsa masa ba illa cewa da tayi " kana ina yanzu? "ina asibiti ya bata amsa cikin kulawa, "ok ina san ganin ka right now, ok bani nan da 30 minutes zan zo in sha Allah, "no badamuwa bari nazo kawai ina kan hanya, cikin mamaki abinda take so da sauri haka yace " ok sai kin k'araso, batayi magana ba ta kashe wayar had'i da yiwa motarta key, dayake ba tazara sosai in 15 minutes ta k'arasa, waya tayi masa ta sanar dashi ta k'araso, da saurin sa yazo yana murmushi, martanin murmushi ta mayar masa cikin yak'e, ganin yanayin datake ciki bak'aramin bashi mamaki yayi ba, yace " Hajiya baki da lafiya ne? " No Zarah ce bata d'an jin dad'i ta fad'a tana kallan cikin motar inda Zarah ke kwance, bin inda ta kalla yayi da kallo shima, da sauri yace " subhanallah bari nayiwa nursing magana, yana tafiya yana magana a ransa "wanne irin so Zainab takeyiwa yarinyar nan ne haka, daga bata da lafiya duk ta rud'e ta canja gaba d'aya ta fita daga hayyacin ta, yana maganar harya k'arasa inda nursing suke ya shaida musu akwai mara lafiya a waje, tare da Aunty Zainab suka shigo, office d'insa ya kai ta yace ta zauna kafin su gama duba Zarah ba musu ta zauna. Direct d'akin duba marasa lafiya aka wuce da ita, bayan ya gama yi mata duk abinda ya kamata ya bata taimakon gaggawa ta farfad'o, sai da yayi test yakai 5 tyms amma sakamakon dai d'aya ne, sai da yayi test kala-kala a k'alla shida amma duk dai ciki yake gani. Yayi masifar mamaki da shiga mummunan tashin hankali dan shi a iya saninsa yasan Zarah bata da aure, jiya ma Naseer ke sanar dashi cewar jibi auran su, a tunanin ta yadda zai sanar da Zainab wannan maganar ya farayi dan yasan akwai babbar matsala, amma yasan ya zama dole ya sanar da ita gaskiya, dan haka cikin sanyin jikiya nufi office d'in, cikin rashin kuzari ya zauna a kujerar zaman sa yana fuskantar ta, a hankali ya kira real name d'inta abinda bai tab'a yi ba dan ta d'au magarsa mahimmnci " Zainab!, gabanta ne yayi mummunar fad'uwa jin ya kira ainahin sunta, bata iya amsawa ba illa ido data zuba masa a matuk'ar tsorace. Sai da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan yaci gaba " Zainab ko wanne mutum da kika gani a rayuwa yana da k'addararsa da jabarwa dan Allah bazai tab'a barin mutum ba jarabawa abinda nake so dake kiyi k'ok'arin cinye taki jarabawar please, kuma ki fahince k'addara, kar hakan ya zame miki sanadiyyar kamuwa da ciwo, dan duniya tasan irin mugun san da kike wa Za..... hannu ta d'aga masa had'i da cewa " what is going on? just go to straight to the point, cikin sanyin jiki yace " Zainab ina so ne ki fara fahimta kafin na sanar dak....... katse shi tayi ta hanyar cewa " go on Mr Doctor. Cikin rawar murya yace " she is pregnant, a zabure Aunty Zainab ta mik'e tana huci tace " kai ma haka zakace kenan idan su sauran basu san Zarah kai ai kasanta tun kafin tasan kanta, amma kai ma mayar da kanka kamar sauran, murmushi had'i da mik'ewa yace " zo muje abinda yace kenan ya wuce gaba ta bishi a baya, umarni ya bawa nursing dasu kai Zarah scanning room, a baya suka bi su da Zarah, suna shiga yacewa nursing su fita, bayan sun fita ya kwantar da Zarah, ya fara yi mata scanning ya kalli Zainab yace " kalli kiga, baby Zainab ta gani yana ta wutsil-wutsil har an kusa gama masa halitta, Doctor yace " idan test zayyi k'arya scanning bazayyi k'arya yanzu dai kin gani da idanki. Ya k'arasa maganar yana juyawa gefenta gabansa ne yayi muguwar fad'uwa ganin halin da take ciki, tsaye take cak kamar mutum-mutumi, idanuwanta kan na'urar scanning d'in, ta kasa koda matsa hannunsa da sauri ya mik'e ya k'arasa inda take yana kiran sunanta cikin tashin hankali " Zainab!!!!, bata ko matsa ba, hannu yakai ya tab'a ta yaga ta tafi luuuuuuu ta fad'i, cikin tashin hankali ya fara kwalawa nursing kira da k'arfi da gudu suka shiga. Kai tsaye Emergency aka shigar da Aunty Zainab had'i da juna mata Oxygen, Doctors biyar ne akanta suna iya k'ok'arin su amma shiru har wajen 3hrs suna kanta amma babu ko alamar motsi gashi kuma zuciyar ta na bugawa, duk hunhunta yana motsi bare suce kota mutu, sun bata iyakar taimakon su amma babu wani ci gaba, haka suka hak'ura suka fito da ita suka kai ta d'aki had'i da saka mata na'urori kala-kala harda Oxygen d'in. Itama Zarah an kwantar da ita asibitin kasancewar tana masifar jin jiki, sai bayan komai ya lafa Doctor ya kira El-Mustapha da Naseer ya nasar dasu halin da ake ciki, a rikice Naseer da Momy da Dady suka k'araso asibitin bayan sun sanar da familyn Zainab, kusan lokaci d'aya suka k'araso, a rud'e Naseer yake tambayar Doctor abinda ya faru, cikin in ina Doctor yace " Zarah ce bata da lafiya shine Hajiya ta fad'i, kamar daga sama Doctor yaji Naseer yace " meke damun Zarah!? A tsorace Doctor ya d'ago ya kalli Naseer, yanayin yadda ya d'ago ya bawa kowa mamaki, kame-kame Doctor ya fara yi ya rasa abin cewa, a zafafe Naseer ya nufi shi yana cewa " baka ji ana maka magana ne? Kayiwa mutane shiru, da sauri el-mustapha ya k'arasa wajen had'i da dakatar da Naseer ya kalli Doctor yace " meke damun Zarah? yayi maganar yana kallansa ido cikin ido, ajiyar zuciya Doctor ya sauke dan yasan maganar kallan da Dadyn yake yi masa. Cikin rawar baki yace " she is pregnant, "wad'in cewar Naseer da k'arfi, kan Doctor a k'asa yace " Zarah tana da shigar ciki na wata hud'u. A razane Naseer ya shak'i wuyan Doctor yana cewa "ubanka ne yayi mata ciki? Dakyar El-Mustapha ya k'ace Doctor daga hannun Naseer, ya kalli Doctor a firgice yace " wake da cikin Zarah ko Zainab? A tsorace Doctor yace " Zarah ce keda cikin 4 months, ai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi kasa motsawa sukayi jin maganar da Doctor ke fad'a, a razane Naseer yayi baya had'i da kurma mahaukaciyar k'ara da k'arfi wacce tayi sanadiyyar farkawar Aunty Zainab, cikin kuka ta fara magana " Zarah kin cuce ni duk irin tarbiyyar danayi muku, da tsarewar danake yi muku, duk abinda kuke so shi nake yi muku dame har namiji zai rud'e ki, yanzu da wanne idan zan kalli Abbanki da mahaifiyarki da k'arasa cikin mahaukacin kuka. Naseer ma kukan yake yi sosai kamar ransa zai fita, kamar k'aramin yaro, kai Abban Zarah ya dafe had'i da zaman dirshen a k'asa ya kasa cewa komai, El-Mustapha da Momy tsaye sukayi kamar an dasa su, a hankali idan Aunty Zainab ya sauka akan Naseer dake kuka tuburan yana yarfe hannu. A zuciye ta mik'e ta nufe shi tana tangad'i, cakumar kwalar rigarsa taci cikin matsanancin kuka tace " Naseer ka cuce ni, ka lalata min abinda na dad'e ina b'oyansa, cak ya tsaida kukansa jin abinda Aunty Zainab ke cewa, da wani irin kallan mamaki yake binta, dukan k'irjinsa ta farayi tana cewa " Naseer meyasa, meyasa zakayi min haka, akan me, menayi maka, lokacin daka tsaya a gaba na kake min bayanin irin sanda kake yiwa Zarah da irin ingantacciyar kulawar dazaka bata, na yarda da kai sosai da zuciya d'aya, na aminta ko bana raye zaka rik'e min Zarah hannu bibbiyu bisa amana da gaskiya. " Ashe ba haka bane, na yaudari kai na danayi saurin yarda dakai Naseer, ta k'ara fashewa da matsanancin kuka, idansa Naseer ya runtse da k'arfi yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, k'irjinsa nayi masa wanirin zafi, mak'ogwaronsa yayi masa mugun d'aci, gaba d'aya jikinsa rawa yake yana tsuma, shi kansa yasan babu abinda zai fitar dashi daga zargin yiwa Zarah ciki har sai idan ita Zarah ta farka ta fad'i wanda yayi mata cikin sannan zai fita daga zargi daga wajen kowa dan yasan a halin yanzu bashi da mafita ko abincewa, da gudu Zainab tayi hanyar fita cikin zafin nama Abba ya rik'o ta, kallo d'aya zakayi mata kasan kwata-kwata bata cikin hayyacin ta. A firgice tace " Abba ka kyale ni taje wajenta ta fad'a min wani tsinannan ne yayi mata ciki please Abba, tayi magana tana k'ok'arin kwacewa, kanta Abban ya shafa had'i da had'iye abinda yake ji yace " a'a Zainab ki bari sai kin ji sauk'in jikinki tukunna, "Abba babu abinda yake damuwa na lafiya k'alau, kwanciyar hankali na d'aya ku kai ni wajen Zarah, kanta ya shafa ba tare daya ce komai ba, sai ya lallab'a ta Doctor yasa mata drip da yaya mata allurar bacci. Ana ranar Dady ya kira Mannir yace duk abinda yake yi ya dawo gida, dan ba lafiya, washe gari jirginsu yayi landing a airport d'in AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT, hankalinsa a tashe yayi gidan inda ya tarar da Ikram kawai, ya tambaye ta abinda ke faruwa, kasancewar batasan abinda k'e faruwa ba tace masa Zarah ce ba lafiya dan iya abinda ta sani kenan, sai da yaje asibiti yaga Zainab ma ba lafiya. Tunda Naseer ya koma gida ya shige bedroom d'in sa ya rufe yake ta rusa kuka, yak'i bud'ewa yak'i ci yak'i sha babu yadda Dady da Momy basuyi akan ya bud'e k'ofar ba amma yak'i, kuka kawai yake tuburan baji ba gani, babban bak'insa yadda aka lalatawa Zarah rayuwarta. Duk budurin da akeyi Zarah batasa ni ba, dan bata san wainar da ake toyawa ba. Sai da su Aunty Zainab sukayi sati d'aya a sabitin sannan aka sallame su, Zarah ta warke sumul babu abinda yake damunta , haka ma Zainab ta warke sai da batayiwa kowa magana tun da abin ya faru burinta kawai taga Zarah. Suna shiga gidan ita da Mannir suka tarar da Zarah da Ikram a parlor da gudu Zarah ta nufu Aunty Zainab tana" Momy I really misses you so much, Mannir shima dabe san meke faruwa ba yayi tsaye yana murmushi, a zabure Aunty Zainab tayi kan Zarah ta shak'e ta, wani irin mugun duka ta ko'ina ta shiga yi mata tana kuka, da sauri Mannir ya k'arasa inda take ya kwace Zarah. "Lafiyarki kuwa Zainab kike mata irin wannan dukan me tayi miki? Cikin kuka tace " Mannir ka bani ita ta sanar dani uban da yayi mata cikin jikinta, a kid'ime Mannir yace " what! Ciki Zarahn? "Eh mannir Zarah CIKIN SHEGE TAYI ta d'auko mana magana da abin kunya. "Kin san abinda kike cewa kuwa? Jakarta ta bud'e ta ciro d'auko gaba d'aya test d'in asibitin dataje, ta had'a da scanning duka ta mik'a masa hannunsa na rawa ya karb'a ya zauna akan kujera yana dubawa, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yake ta maimaitawa bai san sanda takardun suka zube k'asa ba, Zarah da tunda taji maganar ciki jikinta ke kerrrrrrma ta durk'usa had'i da d'aukar takardun tana dubawa, wani irin mahaukacin ihu ta saki had'i da zubewa k'asa a sume, a matuk'ar zuciye Mannir ya mik'e ya zage iyakar k'arfinsa ya shiga kasar mata mahaukatan naushi da duka tako'ina, take ya had'a mahangurb'a, dukan dayake mata ne ya farfad'o da ita daga suman datayi. Sosai Mannir ke dukan Zarah, amma Zainab na tsaye ko gezau batayi, ita Zarah tama kasa kuka saboda gaba d'aya ba'a cikin hayyacinta take ba, ba zafin dukan tafi ji ba, zafin da zuciyar ta take yi mata shi tafi ji, kanta Mannir ya kama ya gwara da bango wanda sai da yayi sanadiyyar d'aukewa numfashinta. Fad'uwa a k'asa a sume jini na zuba ta bakinta da hanvinta, fuskarta ta kumbura sumtum, gaba d'aya Mannir ya gaba sab'a mata kamanni, duk da suman datayi amma hakan baisa Mannir tausaya mata ya kyaleta ba, dukan nata yaci gaba dayi kamar mahaukacin zaki, dukan daya sumar da Zarah haka dukan ne ya farfad'o da ita. Sai ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, anan ta zube tana mayar da numfashi sama-sama saboda wahala ta kasa tashi, jikinta duk a fashe, cikin kuka Ikram tazo ta ja ta bedroom taKaita kan bed ta kwantar ta sata gaba tana kuka. A hankali Zarah ta d'ago kumburar kanta ta da jajayen idanta ta kalli Ikram dakyar ta iya bud'e bakin tace " Ikram da gaske ciki ne dani? Kai Ikram ta d'aga mata hawaye na zubo mata alamar "eh, ido Zarah ta lumshe tana ambaton " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, had'i da shafo cikin ta, aiko wutsil taji ya motsa, a hankali ta bud'e idanta tana sauraran yadda Babyn ke motsawa sosai a cikinta, hakan ne ya k'ara tabbatar mata akwai d'a acikin cikinta, ita dai tasan ba'a tab'a samun ciki sai an kwanta da d'a namiji (sex) dan ta karanta a addini da kuma biology, ita kuma a iya saninta babu wani namiji daya tab'a saninta 'ya mace ko ya kusance ta, balle harta samu ciki, sai dai idan saka mata akayi dan ta tabbatar bata tab'a samun ciki haka nan ba, haka Zarah ya kwana cur bako gyangyad'i balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, har gari waye, haka ma Aunty Zainab da Mannir babu wanda ya iya runtsa, balle kuma Oga Naseer. Da sassafe Aunty Zainab ta shiga d'akin Zarah ta tarar da kwance cikin bargo tana ta kakkarwar sanyi, Ikram na gefenta, tsaye tayi a kanta tana kallanta cike da muguwar tsana dan yanzu kwata-kwata bata k'aunar ganin Zarah tace " Zarah ki sanar dani uban da yayi miki cikin nan, cikin kusa Zarah tace " wallahi Allah Momy ban san waye ba, nima ganin cikin kawai nayi a jiki na, wasu fitunannun marika ta watsawa Zarah wanda yasata hantsilawa cikin fushi tace " karki k'ara kirana Momy ni ban haifi MAZINACIYA ba, tsayar da kukanta Zarah tayi ta k'ura mata ido kawai, had'i da maimaita sunan da Momy ta kira ta MAZINACIYA!!! , a hankali tace " Momy wallahi nima ba mazinaciya bace, na rantse da girman Allah ban tab'a aikata laifin ZINA ba, K'ADDARA TAH ce haka. Cikin zafin rai Aunty Zainab tace "cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, dakyar Zarah ta yunk'ura ta mik'e, dakyar ta take taka k'afarta, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa na rantse da girman Qur'an dake kai na bansan wanda yayi min ciki nan ba, ban kuma tab'a aikata zina ba. Jikin Aunty Zainab yayi mugu mugun yin sanyi, gaba d'aya jikinta ya saki, zuciyar ta daina yi mata zafi da tafarsa dake ji, tasan Zarah tana da cikekken ilimin addinin islama, tana kuma da nutuwa da hankali tasan bazata tab'a rantse mata da Qur'an akan k'arya ba, a harzuk'u Mannir ya k'arasa shigowa d'akin dan dama yana tsaye yana kallan duk abinda ke faruwa, bai jira wata-wata ba hau dukanta tak'o ina baji ba gani, ya zage yadda zai daki k'aton gardi namiji d'an uwansa yayi ta kai mata naushi da kutufo a ko'ina, cikin rashin imani da tausayawa. 1 Ya rink'a gwara kanta da bango, yana d'aga ta sama yana jefarwa har sai da ta daina numfashi da motsi amma bai dai na dukanta ba, wata irin razananniyar k'ara Ikram ta fasa had'i da fita da gudu tayi wajen wayar Zarah, da sauri dayi dialing number Naseer, da kamar bazai d'aga sai kuma yayi picking ganin number Zarah ce, a gigice tace " Uncle kazo da sauri Momy da Dady zasu kashe Zarah, kayi sauri please karta mutu, a gigice ya fito da gudu yayi habar gidan dai-dai lokacin da Momy da Dadynsa ke yin parking sun dawo daga unguwa, ganin yadda Naseer ya fisgi motar a haukace sun san ba lafiya ba, dan haka suka rufa mishi baya. Yana yin parking bai jira motar ta gama tsayawa ba ya fito yayi cikin gidan a haukace, a gefen motar sa su Dady sukayi parking suma suka fito suka nufi cikin gidan. Naseer na shiga gidan ya jiyo ihun Ikram a bedroom d'in Zarah a hanzarce ya nufi can ya shaga kai tsaye dai-dai lokacin da Mannir ya shak'eta yana cewa " mu zaki rainawa hankali, kin tab'a ganin inda akayi cikin haka nan ko a ruwa ake sha, idanuwanta suka firfitu waje gaba d'ayansu suka kakke numfashinta ya tsaya.......... A haukace Naseer ya k'asa wajen yasa hannu ya fisge Zarah daga hannun Mannir ya kalle shi ido cikin ido yace " wallahi duk abinda ya same ta bazan tab'a yarda ba sai nayi shari'a dakai, tsabar baka da imani ka zage iya k'arfinka da Allah ya baka a matsayinka na namiji kayiwa mutum wannan mummunan dukan sai kace ka samu dabba. Murmushi Mannir had'i da cewa " ai dole kaci haka tunda ka lallab'a ka d'urwa 'yar mutane ciki, shege munafuki mazinaci, masik'i kawai, abinda dama damai bak'ar zuciya, gadan-gadan Naseer yayi kan Mannir dai-dai lokacin da iyayen nasu ke k'arasowa, tsawa Dady ya dakawa Naseer had'i cewa " stop! Karka soma ina ruwanka da shiga tsakanin su ba tare ka gansu ba, yayi mata duk abinda zai iya, idan ma kashe ta zayyi gashi nan gata, tunda bashi da hankali yaga idan hukuma zata kyale shi, yayi maganar yana kallan Mannir dake ta faman huci. Aunty Zainab dake tsaye tunda aka fara abin bata motsa ba sai taga Naseer ya sumgumi Zarah yana niyyar yin waje da ita, da sauri tasha gabansa tana jefansa da kallan tsana tace " ina kuma zaka kaita? bayan ka riga da ka gama lalata, kallanta yayi ido cikin ido yace " kamar yayafa? "Ni zaka kalli ido na kace min kamar yayafa? sau nawa ina kama da ita, a zabure Dady ya juyo yana kallan ta yace " Zainab mekike kice? Hawayen fuskarta ta fara sharewa sannan tace " eh Dady gashi nan ku tambaye shi idan k'arya nake masa, wallahi sau uku ina kamashi yana romancing d'inta, kafin Dady yayi magana Naseer yace " da kika ganni ina romancing d'inta, kin ganni a kanta ne? ko kuma kin tab'a kamani akan ruwan cikinta ina sex da ita ya fad'a idansa cikin nata, dama Naseer akwai bak'ar zuciya, ganin ransa yayi masifar b'aci kuma sun san idan ransa ya b'aci haka idonsa rufewa yake yana iyayin komai yasa kuwa yin shiru, a hankali ya sunkuya ya sab'i Zarah a kafad'a yayi waje, Dady da Momy suka bi bayansa. Amma kafin su iske shi ya figi motar a 360, da sauri suka shiga mota suka bi bayansa, a k'ofar wani had'add'e private hospital yayi parking, da hanzarinsa ya fito ya shiga cikin hospital d'in bai jima suka fito da Doctor da nursing, kai tsaye emergency aka wuce da Zarah, tsaye Naseer yayi a k'ofar emergency room d'in yana safa da marwa, a haka su Dady suka k'araso, da sauri suka nufe shi, Dady yace " ya ake ciki ne? Naseer ya bud'e baki zayyi magana Doctor ya fito a gigice da sauri Naseer ya tare shi, Doctor yace " ina mijinta? batare da fargabar komai ba Naseer yace " nine? " accident d'in data samu gaskiya ya munana dan harda karaya biyu, a razane Naseer yace " what!!! KARAYA!!! a d'an tsorace doctor yace " eh k'afa da hannu, zaman dirshan Naseer yayi a wajen a k'asa ya fasa gigitaccen kuka, Kallan sa Doctor kawai yake yana mamakin namiji kamar Naseer amma da karyayyar. '''Ni ko nace hmmmmm Doctor baka san so bane''' Sosai zuciyar Dady da Momy ta karaya, a hankali Dady ya cewa Doctor " kuyi duk abinda ya kamata kawai, ku d'orata, "ok doctor kawai yace ya juya ya koma cikin Emergency room, a hankali Dady ya durk'usa a gaban Naseer ya rungumo shi jikinsa yana lallashi yayinda Momy ke shafa kansa, a zuciyar Dady yana jinjina tsantsan rashin imani irin na Mannir, cikin kuka Naseer yace " Dady kana jin Doctor ma cewa had'ari ta samu dan shi a tunanin sa accident ne, babu wanda zayyi tsammanin wannan duka ne, Dady Mannir kwata-kwata bashi da imani, baya ganin akwai ciki a jikinta idan wani abu ya same ta fa, wallahi Momy bazan yarda ba sai nayi shari'a dashi kona rama mata, daga Momy har Dady babu wanda yace k'ala. Wayar Dady ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ya sanar dasu halin da ake ciki, basu jima ba suka k'araso tare, cikin mummunan tashin hankali, anan Dadyn Naseer yayi musu bayanin duk abinda ya faru batare daya b'oye musu komai ba, sosai zuciyar Abban Zarah ta sosu, amman ya daure ya b'oye bai bari ko fuskarsa ta nuna ba, balle a gane yaji zafin abin, Alhaji Abdullahi ne ya harzuk'a ya rufe idonsa yayi ta zazzaga ruwan bala'i san ransa. Sai da akayi a k'alla 5 hrs sannan aka fito da Zarah jiki duk nad'e da bandeji, da hanzari su Naseer suka mik'e suka bayan su, wani shegen d'aki aka kaita mai shegen kyau da k'ayatuwa babu abinda babu harda kitchen da bathroom & toilet, a bakin gadon kusa da ita Naseer ya zauna had'i da k'ura mata ido hawaye na zuba, sosai al'amarin ya bawa duk jama'ar dake wajen tausayi, wajen 11:00pm na dare Dady ya kalli Momy da Naseer yace su fito su tafi, amma bud'ar bakin Naseer yace " in tafi ina? Juyowa Dady yayi yana kallansa dan yasan dama za'a rina, fuska d'aure had'i cewa amma kasan dai bazai yiyu ka kwana nan ba ko? "ni fa Dady babu inda zani nabar Zarah, haba sai kace dai marar gata da galihu bayan wannan mahaucin dukan sannan atafi a barta babu wanda ya lura da halin datake ciki ga ciki a jikinta, a hasale Dady yace " to idan ma za'ayi jinyar tata kasan dai baka d'aya daga cikin jerin wad'anda suka dace ko? " please Dady kayi hak'uri amma babu inda zani, babu yadda Dady, Momy, Alhaji Abdullahi da Abban Zarah basuyi akan Naseer ya tashi ya tafi ba amma fafur yak'i ko motsi, dayaga an dame shi ma sai cewa yayi " wai me kuke gudu ne bayan mai afkuwa ta afku duk abinda kuke tsoran karrya faru ya rigada ya faru, dan ni babu inda zani, sanin Naseer na kafiya tun yana yaro yasa Momy cewa " shikenan kuje ni zan kwana dasu, sosai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi sukaji dad'in karar da Momy tayi, dan haka suka shiga yi musu godiya " lah bakomai an riga an zama d'aya, Momy tacewa Dady " ka bawa driver barguna da pillows ya kawo min, Dady yace " to muje mana ki d'auko duk abinda ya kamata inyaso sai na dawo dake, ba musu ta mik'e tabi bayansa. Zarah najin k'arar rufe k'ofa ta bud'e idanta dan ta dad'e da farkawa kunya ce kawai ta hana ta bud'e idanta, duk budurin da akayi da Naseer akan kunanta, hawaye na zubo mata ta k'ura masa ido had'i da kiran sunansa a hankali " Uncle!!, a hanzarce ya juya yana kanta shima hawaye na zubo masa, dakyar ta bud'i baki tace " wallahi Allah Uncle ban san yadda akayi na samu ciki ba, please ka yarda dani, Allah yadda kuka ga cikin nan a jikina haka nima na ganshi, wallahi Allah Uncle ban tab'a sanin wani d'a namiji ba, ban tab'a aikata zina ba, har rantsewa su Momy da Dady da Qur'an nayi amma sunk'i yarda dani ta fashe da matsanancin kuka. Shima kukan yake ya kasa cewa komai, "Uncle jibi irin dukan da Dady yayi min, Momy har kira na da MAZINACIYA (My up coming novel) tayi, kowa yak'i ya yarda dani, babu mai yi min uzuri, laifi na kowa yake dabuwa, nasan kai kowa yake zargi amma ni ban tab'a ji a raina ko sau d'aya zakayi min haka ba, na rasa mai yasa kwata-kwata zuciya ta tak'i zarginka, Uncle karka d'ai kawai a rage min a masu so na, na baya dan Allah Uncle karka guje ni, please ka yarda dani wannan ABU A DUHU (Next novel d'ina in sha Allah) yake, daga ni har kai babu wanda yasan MEKE B'OYE (shi kuma upper novel d'ina) har yanzu babu wanda yasan GASKIYAR AL'AMARI (Next upper novel d'ina) balle kuma duniya tasan SIRRIN B'OYE (My new novel). A hankali yasa hannu yana share mata hawayen dake zubo mata yace " karki damu Zarah, nima na rasa me yasa har yanzu zuciya tak'i ganin laifinki ko sau d'aya ba, wallahi na yarda dake 100% kuma ina tare dake d'ari bisa d'ari, cikin rawar murya tace " thank you Uncle, thank you so much, duk duniya a halin yanzu bani da sama dakai, bani da masoyi na gaskiya mai k'aunata tsakani da Allah sama dakai.1 _Ni ko nace hmmmmm Zarah kenan baki daddara ba kenan har yanzu_ Goshinsa ya d'ora akan nata suna kuka babu mai lallashin wani, Momy dake tsaye tana kallansu tun d'azu batare dasun sani ba, ta share hawayenta sai a lokacin ta samu sausauci a zuciyarta, d'an gyaran murya sannan tayi sallama, da sauri Zarah ta rufe idanta. Cikin tausayawa Momy ta k'arasa inda suke ta zauna a kusa da had'i cewa " ki bud'e idanki Fatima dan duk naji mai kuka ce, banbi Dady ba ganin dare yayi yace zai bawa driver ya kawo min, dan haka naji maganarki tun daga farko har k'arshe, a hankali Zarah ta bud'e idanta ta sauke su akan Momy yayinda hawaye keta faman ambaliya a fuskarta tace " wallahi Allah Momy ban san yadda akayi cikin nan ya shiga jikina ba, ban san mafarin abun ba illa BAK'IN GANI (still my novel) danayi, hawayen Momy ta goge mata karki damu Zarah, na yarda dake kuma nayi miki alk'awarin ina tare dake akoyaushe ko'ina, murmushin yak'e wanda yafi kuka ciwo Zarah tayi, Momy tace " karki sake ki damu karki saka komai a ranki balle ki jawowa kanki ciwo kinji, kiyi hak'uri kowanne d'an Adam da irin k'addararsa, sosai Momy ta kwantarwa da Zarah hankali sannan ta kira doctor ya dubata aka bata magungunanta. Sannan Momy ta bata light food tad'anci d'an mitsitsi shima ba'a san ranta sai da Momy da Naseer suka matsa mata dakyar taci, , a b'angaren Aunty Zainab kuwa kwata-kwata bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare dan bacci k'aurace mata yayi, haka ma Mannir dan shi safa da marwa ma yayi tayi a d'akin har gari ya waye. Washe gari da sassafe Zainab da Mannir, Ikram suka tafi gidan su Momy dan jin yadda Zarah ta kwana, dan ita Zainab tun da Zarah ta rantse mata da Qur'an kwata-kwata ta daina ganin laifinta ta karkata gaba d'aya laifin ta d'orawa Naseer dan tasan idan ba shi babu mai d'urkawa Zarah ciki, shine suke kullum kuma koyaushe, Mannir dai baya nan balle ta zarge shi dan yanzu 4 months 2 weeks kenan baya k'asar. Suna isa harabar gidan Dady na fitowa d'auke da kwandon breakfast, ya gansu sarai amma ya d'auke kansa ya shiga mota had'i da yiwa driver alamar ya taho, da sauri Mannir ya nufe shi yana yi masa magana amma Dady ko kallan inda suke bayyi ba balle ya amsa masa ya bawa driver umarni daja motar. Da hanzari Mannir ya koma cikin motar yana yiwa Zainab alama data shiga, ya figi motar ya rufawa Dady baya, acan Dady ya iske Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ana ta drama da Naseer ya tafi gida yayi wanka ya shirya ya dawo amman yak'i, su Dady suna gaisawa Mannir da Zainab shigo d'akin, a hasale Naseer ya mik'e zai zuba tijara Dady yayi saurin hanashi, Mannir na niyyar nufar gadan Zarah Dady yayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu, Zainab tsaye tayi k'em ganin mummunan halin da Zarah ke ciki duk jikinta nad'e da bandeji har fuskarta ga k'afarta da hannunta d'aya a sak'ale duk da k'arafa alamar d'ori , sosai Zainab ke kuka cike da tsananin tausayin Zarah. Mannir yace " please Dady ka barni na ganta wallahi tun jiya muke neman asubitin da kuke, daga ni har Zainab hankalin mu a matuk'ar tashi yake dukkan mu babu wanda ya runtsa. A hasale Dady yace " kuna san nata ne kai da matarka zaku had'a kai kuyi mata wannan mugun dukan da har Doctors suna tsammanin accident ne, babu wanda yayi tunanin wannan duka ne harda karaya biyu. "Karaya fa Dady Mannir ya fad'a a razane yana zaro ido, " baka da gani ne ko baka da ido ne ko dazaka shiko part d'in bakaga an saka Orthopedic ba, " dan Allah kayi hak'uri wallahi ban.... bai kai ga k'arasa maganar ba suka jiyo ihun Naseer, duk suka kalle shi,, da gudu ya nufi gadan Zarah yana kwala mata kira Zarah!!! gaba d'ayan suka kalli wajen, jini ne fitowa Zarah ta baki ta hanci data kunnenta, idanuwanta gaba d'aya sun kakkafe bak'in ya d'auke sai iya farin kawai, jikinta ya sandare, sai kaf-kaf datake kamar mai farfad'iya. A haukace Naseer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan Doctor da k'arfi duk ya fita daga cikin hayyacinsa, nutsuwarsa ta gushi ihuuuu kawai yake yana kuka, hannunsa Zarah ta rik'o da d'ayan hannunta mai lafiya dakyar tace " Naseer, yau ne rana ta farko data ambaci real name d'insa a razane ya d'ago yana kallanta ido cikin ido yana kuka kamar ransa zai fita, murmushin k'arfin hali tayi masa tace " nagode sosai da soyyayyar daka nuna min, dazan rayu dana yi maka..... bata k'arasa ba ta fara aman jini gunduwa-gunduwa dakyar ta tallafo fuskarsa tana murmushi tace " uncle mutuwa zanyi, please ka daina kuka, na baka amanar Momy na Ikram ka kular min dasu yadda zaka kula da kanka, ka yafewa Dady na please karka rik'e shi a ransa. Hannunsa da rik'e tana zabure-zabure can kusan tayi salati jikinta ya saki........ Da k'arfi Naseer ya kira sunanta yana jijjiga ta ZARAH!!!!!, a haukace yake kwalawa likita kira iya k'arfinsa yana ihuuuun hauka, a wajen Aunty Zainab ta zube a k'asa akan gwiwoyinta tana hawaye amma ta kasa kukan, a razane Mannir ya fita yana kwalawa Doctor kira a matuk'ar firgice, da sauri Doctor da Nursing suka shigo, gam Naseer ya rik'e tana ihuuu, sai da kyar aka b'amb'are daga jikinta aka shigar da ita emergency. Shak'ar wuyan Mannir yayi yana ihuuu, kwata-kwata baya cikin hayyacinsa da nutsuwarsa ya gama fita daga hankalinsa, ya shak'e shi iya k'arfinsa yana cewa " wallahi idan Zarah ta mutu kai ma sai ka bita, matuk'ar ina raye bazan bar makashin Zarah yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai dai nima a kashe ni, kakarin mutuwa Mannir ya shigayi yana kokawar kwace kansa amma ya kasa, Dady da Momy na zaune babu wanda yayi yunk'urin komai balle yayi magana, sai Abban Zarah ne yaje yana k'ok'arin kwace shi, amma ina ya kasa, wani gigitaccen mari Abba ya yarfawa Naseer, a kid'ime Naseer ya saki Mannir yayi kan Abban, ganin Abba ne yasa shi sakinsa da sauri yana yarfa hannu. Ya durk'ushe a wajen yana kukan mutuwa, gaba d'aya wajen kowa tunanin wannan wanne irin ne Naseer yake yiwa Zarah, duk anyi jugum-jugum a k'ofar emergency room d'in, babu mai cewa k'ala, illa Naseer dake ta faman hawaye yana jin zuciyar sa kamar zata buga. Iya wuya kam Zarah tasha kamar zata mutu dan sai da ta gwammaci mutuwarta akan ci gaba da rayuwarta, su kan su Doctors d'in sai da suka sha bak'ar wahala kafin su samu numfashinta ya dawo dai-dai, su kansu sun tausaya mata ganin irin bak'ar wuyar dataci, sai akayi 3hrs sannan aka fito da ita, da sauri Naseer ya mik'e ya nufi gadan da ake turata a ciki, yana binsu a baya har suka mayar da ita d'akinta, da sauri Naseer ya k'arasa bakin gadon ya zauna ya rik'o hannunta cikin nasa, kowa ya tsaya cak yana kallan ikon Allah, Doctor ya sauke ajiyar zuciya yace " jininta ne ya hau sosai, kuma tana cikin matsananciyar damuwa ayi k'ok'ari arink'a kwantar mata da hanklinta da zuciyarta nagaf da tab'uwa. A hankali Zainab taje bakin gadon ta shafa kan Zarah tana hawaye, zuciyarta nayi matuk'ar k'una da tafasa, tana jin k'irjinta kamar zai fashe saboda tsananin zafin dayake yi mata, ita kanta tasan tana tsannin k'aunar Zarah, amma dole tayi nisa da ita, mayar da kallanta tayi wajen Mannir tace " muje, cikin muryar kuka ta kalli Ikram tace " ki tsaya kiyi jinyar 'yar uwarki har ranar za'a sallameta zan sa driver ya kawo miki kayanki da duk abinda kike buk'ata kinji, cikin sanyin jiki Ikram tace " to Momy, dan tana tsananin san Zarah itama a ranta fiye da tunanin. Harta kai bakin k'ofa ta juyo ta kuma kallan Ikram tace " karki anyi haka kice zakiyiwa Zarah wani abu marar kyau, idan har naji kona gani nida kai na zan kashe ki wallahi, dan har yau har gobe Zarah tananan a zuciyata daram kamar da babu abinda ya ragu dan Zarah bata da uwa sama da ni Zainab ta fad'a kallan saitin Naseer, kuma har bada baza'a tab'a canjawa tuwo suna ba, murmushi Ikram tayi tace " haba Momy yanzu har kina tunanin zan iya yiwa wani abu mummuna, duk duniya fa bani da 'yar uwa ko d'an uwa kamar ta, tare muka taso kamar twice muka sha nono d'aya, Momy Duk duniya Zarah bata da kamar mu muna bamu da wanda yafita duk wanda yake tak'amar yana santa ko sanin ciwonta a bayan mu yake Momy dan munfi kowa sanin zafinta. Tun daga ranar Momy, Ikram da Naseer ke jinyar Zarah, sai dai ita Momy bata kwana anan da dare take tafiya tabar Ikram da Naseer su kwana da ita, sai da Dady da Abban Zarah suka matsawa Naseer sannan yake tafiya da safe ya dawo da yamma, amma dole ce ta sashi hakan badan yaso ba, tun daga ranar Zainab bata kuma zuwa ba, sai dai kullum sai ta kira wajen sau 10 ta tambayi jikin Zarah, shiko Mannir dama ya gama course d'in daya kai shi Paris dan haka tunda ya dawo bai koma ba, shi Mannir kullum sai yaje asibitin sau biyu da safe idan ya fito zai tafi office sai biya yaga jikin nata haka ma da daddare, amma ko kallansa Naseer bayayi, har gwara Momy da Dady suna amsa masa gaisuwarsa sama-sama, haka kullum Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sai sun zo. Iya bak'ar wahala kam Zarah na shantashanta dan sau biyu ana fasa kukan mutuwarta, Allah sarki yarinya k'arama amma ta had'u da k'addara mai girman gaske, kullum cikin matsanancin kukan bak'in ciki take da takaicin rayuwarta, duk tayi bak'i ta rame ta lalace kamar ba Zarah ba, kwata-kwata tak'i sausautawa zuciyar ta, Naseer da Ikram na iya bakin k'ok'arin su wajen d'ebe mata kewa da gusar mata da damuwa, yayinda a hankali cikinta keci gaba da girma yana k'ara fituwa kullum yana yawan yi mata motsi wani lokacin ma ko bacci take idan ya motsa sai ta farka. A haka har akayi wata biyu, jikinta kam yanzu sai dai muce Alhamdulillah, kasancewar akwa ingantacciyar kulawa ta warke, dan har an cire mata d'aurin k'afarta dana hannunta, hannun ya warke sumul sosai, duk inda Mannir yaji mata ciwo ta ya warke babu taso ko d'aya illa k'afarta da har yanzu da saura dan kwata-kwata bata iya taka ta, doctor yace next week za'a fara koya mata tafiya da abin koya tafiya, sab'anin hannun daya warke sosai kamar bata tab'a karyewa a hannun ba dan ko tabo babu babu abinda bata iyawa da hannunta kamar dai yadda ta saba a baya. Haka ma a b'angaren damuwa ta d'an rage kad'an dan zamu iya cewa ba laifin tunda yanzu tana samu tayi hira dasu Momy, Ikram, musamman kuma Naseer data sawa ranta duk duniya babu mai santa kamar shi, ta rage kukan da take yawan yi sab'anin da, da'indai bacci ba bacci takeyi ba to tana cikin aikin kuka 24hrs, amma yanzu har murmushi take yi sosai. A hankali jikin Zarah yaci gaba da samun sauk'i sosai, yayinda Naseer ke koya mata tafiya, hankali cikin ikon Allah yanzu tana iya tafiya da sandar ita kad'ai batare da an rik'e ta ba, tana iya yin komai da kanta har zuwa tailed da bathroom tayi wanka ko kashi tayi sallah, yanzu babu abinda akeyi mata da kanta take komai, haka ma abinci tana ci sosai kasancewar cikin jikinta mai sa cin abinci sosai ne, dan yanzu cikin Zarah yana da wata bakwai. Yau ma kamar kullum Naseer na zaune a gefen Zarah, Momy nakan sallaya, Ikram na kallan wani a MBC Bollywood ta tattara hankalinta gaba d'aya wajen kallanta, Naseer ya kalli Zarah yana murmushi yace " yanzu kina da 3 months a asibitin nan, gashi doctor yace " zaki kai har nan da next month, anya bazaki gaji bakuwa, da naso na matsa masa dole sai ya sallame ki, saboda na fuskanci kun k'usa da zaman hospital, martanin murmushin ta mayar masa had'i da cewa " ku baku gani da d'awainiya dani ba sai ni zan gaji da zaman asibitin, zune ya kamata ku gaji da wahala dani ai, da sauri ya d'ora hannunshi akan lips d'inta had'i cewa " shhhhhhhhhh karna kuma jin kince muna zamu gaji dake ko muna wahala dake kinji ko? Kai ta d'aga masa alamar eh, cikin sanyi murya tace " uncle kayi hak'uri idan na b'ata maka ban kumawa, murmushi yayi had'i da jan hancinta yace " ai baki laifin a wajen Uncle d'inki, dariya tayi tace " ina godiya Uncle, haka dai sukayi ta hira cikin jin dad'i da annashu yayinda gaba d'aya hankalin Momy na kansu, tana satar kallan su. BAYAN WATA D'AYA Kwanci tashi asarar mai rai, rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, yau watan Zarah hud'u cif-cif a asibiti tana jinya yayinda cikinta ke da wata takwas, ta warke sumul babu abinda yake damunta, ko ciwon kai bata ji, tana cikin k'oshin tafiya sai dai d'an abinda ba'a rasa ba namai juna biyu musamman kuma mai tsohon cikin wata takwas yama shiga wata na tara, lafiya lau take tafiyarta kamar da bata ko d'ingishi, haka jikinta babu tabo ko kwarzane, ta dawo normal kamar da, yadda kasan ba itace tasha jinya har ta wata hud'u ba, cikin ikon Allah Zarah ta dawo kamar da, sai dai har lokacin tana cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa gami da takaicin duniya musamman idan ta kalli cikin jikinta ta tuna yau ita ke d'auke da cikin shege kuma cikin shegen ma wanda ba'a san uban sa balle asalinsa ba, sai taji gaba d'aya ta tsani kanta da duniyar gaba d'aya. Tun tana jin kunya tana b'oye-b'oyen cikin harta gaji ta daina ma, tunda shi ciki d'an duma ne da kansa yake bayyana kansa, ta d'auki damuwar duniya ta d'orawa kanta tayi mugun bak'i ta rame, har zuciyarta ma ta k'ek'ashe ta bushe rak'ayau ta daina kuka sai na zuci dan su kansu hawayen sun bushe, sun k'afe sun gaji da zubowa. D'aukar da takardar sallama Doctor ya shigo yana fara'a ya mik'awa Naseer yace " yau dai mun sallamar maka MATARKA mun huta da rigimarka sai kuma an dawo mana haihuwa, dan su ma'aikatan asibitin tsammanin su Naseer mijin Zarah ne, satar kallan Zarah Naseer yayi dan yaga reaction d'inta aka ci sa'a kuwa itama shi take kallo had'i da zaro ida waje kamar zasu fad'i k'asa. Murmushi Naseer yayi had'i cewa " ah wallahi kun huta fa, Doctor ya kalli Zara yace " to maman biyu Allah ya raba lafiya, sai kinzo haihuwa murmushin yak'e Zarah batare datace komai ba, Dady, Momy, Mannir, Alhaji Abdullahi, Abban Zarah, Ikram duk suna wajen, gaba d'aya suka fito wajen harabar motoci Zarah tayi tsaye ta rasa wacce zata shiga dan tana tsoran karta yiwa Naseer laifi, dan tasan halinsa. Kuma ma bata isa ta nufi motar Mannir batare da izinin Naseer ko Dady ba, su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suna tsaye suna kallan ikon Allah, suna so suga hukuncin da Dady zai yanke, kallan Zarah Dady yayi yace " ki shiga motar Naseer, ya kalli Naseer yace " ka kawo ta gida na, da hanzari Mannir yace " Dady na d'auka gida zan wuce dasu, wata muguwar harara Dady ya watsawa Mannir data hana shi k'ara cewa komai, da sauri Ikram tace " Dady nima Zarah zanbi, "ok jeki shiga motar Naseer ku taho tare, cewar Dady yana shiga mota had'i da bawa driver umarnin tafiya. Sosai hukuncin Dady yayiwa su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dad'i har ran su, bare kuma oga Naseer da ji yayi kamar Dady ya mallaka masa duniyar gaba d'aya saboda tsananin farin ciki da jin dad'i, Naseer bai wuce dasu Zarah gida kai tsaye ba sai da ya biya dasu yawo sosai dan d'ebewa Zarah kewar zaman datayi a hospital, kuma yasanta da shegen san yawon tsiya, bai mayar dasu gida ba sai dare shima lura da yayi Zarah ta gaji kasancewarta mai tsohon ciki, sun tarar Momy da kanta tayi girki ta shirya dinning batare data saka 'yan aiki sunyi mata ba, acwarta na tarar Zarah ne, bedroom d'aya Momy ta basu ita da Ikram dan tasan idan aka warewa Zarah bedroom ita kad'ai Naseer damunta zayyi ya hanata sakewa, amma idan yana ganin idan Ikram zai rink'a rage wani abun kodan ita badan su ba, tunda ta lura yana d'an jin kunyar Ikram d'in. Sai da sukayi wanda da sallah sannan suka fito falo suka tarar da Momy, Naseer, Dady gaba d'aya su ake jira aci abinci Momy tace bamai ci sai Zarah tazo dan ita tayi girkin,cikin shagwab'a Naseer yace " kai Momy ni da Dady ba duk yunwa muke ji, murmushi tayi had'i da cewa " to sai ka tashi ai gata nan ta fito, dariya yayi yana kallan Zarah yace " yau Momy tayi mana horan yunwa saboda ke, ta hana mu cin abinci wai sai kin zo, murmushi kawai tayi batare datace komai ba, Momy tace " to Bissimillah, gaba d'aya suka nufi dining table, cikin kwanciyar hankali suke cin abincin su yayinda Naseer keta aikin tsokanar Zarah yana janta da hira, tana bashi amsa sama-sama. Mannir na komawa gida Aunty Zainab ta tare shi da sauri dan ta k'agu taji yadda takaya, murmushi had'i da tallabo fuskarta ya zaunar da ita akan sofa shima ya zauna a kusa da ita, idansa cikin nata yake kallan ta, cikin mutuwar jiki ya girgiza mata kai, da sauri tace " ban fahimta ba please ka bud'e baki kayi min bayani yadda zan gane, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace " an sallami Zarah yau daga hospital kuma ta warke sumul kamar bata tab'a yin ciwo ba, da hanzari tace " tana ina ya ban gan ku tare ba? Cikin mutuwar jiki yace " Dady ya hana ta biyo ni, dan ko kallanta bayyi ba balle ya saurari ni, daga nan ya kwashe duk yadda sukayi da Dady ya fad'a mata, a hankali tace " cikin ya zube ko yana jikinta har yanzu? sai da yayi d'an jimmmmm kafin yace " Zainab ina cikin zashi, yanan mana a jikinta sai ma girma dayayi sosai, dan ina tunanin ma ta kusa haihuwa, dak'arfi da runtse idanuwanta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da k'arfi yayinda k'irjinta yayi mata mugun nauyi, Mannir zai sake magana tayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu. Ita kanta tasan yanzu kwata-kwata bata k'aunar ganin Zarah, ta rasa meyasa take jin ta tsane ta a ranta, saboda bazata iya ganinta d'auke da cikin shege ba yasa har Zarah ta gama zamanta a hospital bata tab'a zuwa dan zuciyarta bazata iya jurewa hakan ba. Kullum kuma koyaushe Naseer na tare da Zarah 24hrs yana tare da ita baya matsawa konan dacan musamman ma yanzu da cikinta ya shiga watan haihuwa, dan yanzu jiran haihuwa suke ko yaushe, cikinta ya tsufa sosai ta zama, zama dakyar tashi dakyar, kullum Naseer yana kusa da ita baya matsawa konan da can, dan ko fita zayyi tare dasu yake fita, kuma kullum sai ya raba dare a d'akin su kafin ya tafi, haka da asubar fari yake zuwa duba su, sosai Momy da Dady ke bata kulawa tamkar 'yar cikin su da suka tsugunna suka haifa, a b'angaren Mannir ma kullum sai yazo gidan sau biyu ganin Zarah, sosai Zarah kejin dad'in zuwansa, dan ta saki jiki dashi sosai kamar da, bata tab'a nuna masa wani abu ko fuska na cewar yayi mata laifi ba, asalima itake bala'in jin kunyar sa, idan bai zo ba har waya take masa ta tambaye dalili. Kullum yazo sai ta tambaye shi Momyn ta, dan sosai take kewar Zainab, tana san ganinta dan dai babu yadda zatayi ne, tasan duk ranar data furta haka rai ran Naseer da Dady yayi masifar b'aci, sosai take yiwa Mannir kukan tana san ganin Momynta, duk sanda yazo sai rok'e shi akan ya bawa Zainab hak'uri dan tasan har yanzu fishi take da ita, babu yadda Mannir bayyi akan Zainab taje taga Zarah ko sau d'aya ne ba amma tak'i. Yau ma kamar kullum Mannir ya gama shirinsa tsaf zai je duba Zarah, yazo zai wuce ta parlor Zainab tace " ina zaka haka kake ta sauri? "zani duba 'ya ta ne, ga mamakinsa sai yaji tace " zani da sauri ya kalli inda take, bata saurare shi ba, taje ta sako hijab ta iske shi a parlor tace " muje ko?, batare daya ce komai ba ya wuce tana binshi a waya. A parlor suka iske Momy, Dady, Naseer da Zarah, Ikram zaune, jin sallamar Mannir yasa Zarah mik'ewa dakyar tana cewa " Dady yau ma Momy bata zo ba ko, har yanzu tana fushi dani akan abinda ni kai na ban san asalinsa ba ko? tayi maganar hawaye na zubo mata, har lokacin Zarah na masifar son Mannir da Zainab, kuma ko sau d'aya bata tab'a ganin laifin d'ayan su ba, tana jin su a ranta kamar a baya dan babu abinda ya ragu daga san da take yi musu, kuma tana d'aukar su a matsayin iyayenta, data kallansu a matsayin duk duniya bata da kamar su, hab'arta Mannir ya kama ya d'ago kanta yana murmushi yayinda yake yi mata nuni da bakin k'ofar parlor. Zainab ta hango tsaye tana kallanta idanta yana zubar da hawaye da sauri Zarah ta saki Mannir ta nufi Zainab tana tafiyar dakyar, tana k'arasawa ta rungume Zainab had'i da sakin rikitaccen kuka mai ban tausayi, tana cewa " Momy kiyi hak'uri ki yafe min wallahi nima ban san asalin cikin nan na jikina ba, Momy har rantsuwa nayi miki da Qur'an dan ki yarda dani amma har yanzu kin k'i yafe min balle ki fahimce ni, Momy kin san fushin iyaye ba k'aramin bala'i bane ga rayuwar d'a, Naseer yayi dan har a lokacin babu wanda yake yiwa magana tsakanin Mannir da Zainab, yana k'ok'arin mik'ewa yaji Zainab cikin kuka tace " bazan tab'a yafewa masik'in da yayi miki cikin nan ba wallahi ko waye shi tayi maganar tana kallan Naseer, murmushi had'i da girgiza kansa ya mik'e yayi shigewarsa d'aki a hankali Zainab ta b'anb'are Zarah daga jikinta niyyar yi mata magana tayi arba da turtsetsen cikin Zarah wanda kwata-kwata bata lura dashi ba sai lokacin, take taji zuciyar ta tayi mata bak'i k'irin k'irjinta ya fara yi mata zafi yana tafasa yayinda mak'ogwaronta ya shiga yi mata k'una take taji tsanar Zarah ta sake dirar mata zuciyar ta, da sauri ta hankad'ata baya, Zarah tayi baya taga-taga zata fad'i Naseer yayi saurin tare ta,take idanuwanta sukajyi jajir kamar gauta cikin zafin rai ta nuna Zarah da yatsanta tace " Allah ya isa tsakani dake Zarah, bazan tab'a yafe miki ba, kin cuce ni kin tozarta ni a idan duniya kin wulak'antar da duk tarbiyyar dana baki. A matuk'ar hasale, zuciyar sa nayi masa tururin zafi gami da rad'ad'i cikin k'onar zuciya ya je daf da Zainab ta yadda suna iya jiyo numfashin juna ya d'aga hannu zai yarfa mata mari yaji anyi sauri rik'e masa hannu ta baya yana juyawa yaga Zarah a matuk'ar hasale tana kalan shi ido cikin ido babu alamar tsoro ko fargaba a zuciye cikin matsanancin b'acin ta. d'aga hannunta ta.................

0 Comments