ALQAWARI BAYAN RAI CHAPTER 5

ALQAWARI BAYAN RAI CHAPTER 5
Lokacin da suka k'arasa station Affan har ya gaji da dialing number Daddy ya hak'ura, text messege ya tura masa.+ Abinda ake tuhumar Nana akae aka karanto masu, duk jikinsu yayi sanyi don sunsan anyi haka, itama gwanar bata wani musa ba, zancen da ya d'an girgiza su shine su kansu yaran data sa aikin basu san ina Aman tayi ba, ita Nana umarnin suyi nisa da kano da ita kawae ta basu amma banda cutarwa. Zufa ce kawae ke faman keto ma Affan, a farkon jin case d'in har ya fara hamdala yana da yak'inin anga Aman an gama. Farhan ne ya shigo station d'in bayan ya karb'i wayar D.P.O akan sune nemansa. Direct Office d'in ya wuce yana takunsa cikin nutsuwa yana fatan tozali da yarinyar da zata iya aikata irin wannan abun. Murd'a k'ofar yayi tare da sallama, turus yayi ganin Mummy da Affan zaune kan kujera sae Nana wadda ta juya bayanta tana tunani. "K'araso Mana Mr Kurfi". D.P.O ya fad'a yana masa nuni da kujerar dake gefen ta Affan. Zama yayi ya mik'a ma Affan Hannu da D.P.O sannan ya gaida Mummy. Sae a sannan Nana ta d'ago da sauri jin muryar sa, daidai lokacin shima ya kai kallon sa b'angaren da take yana bin bayanin da D.P.O yake masa. "Wannan ita ce yarinyar da tasa gangs d'in aiki har aka samu akasi suka yi maka illah." Ras ras ras gaban sa ya fad'i, "Nanaaaa", Ya furta chan k'asan mak'oshin shi, abubuwa da yawa suka shiga yi masa yawo akae. Tunanin farkon had'uwar su yake da lokacin da yaje gidansu, maganar da Baba Maigadi yayi masa. Duk a tunanin sa Nana irin mutanen nan ne wanda sam basu damu da rayuwar kowa ba, be tab'a tunanin zata aikata irin wannan stupid act d'in ba. Ganin yayi shiru ne yasa D.P.O ya sake maimaita maganar sa, sae a sannan Farhan ya maida idonsa kan D.P.O yace; "I ll leave everything to u, duk abinda kukayi akae shikenan, one thing dana sani shine su fad'i ina yrinyar mutane take, dalilin ta na k'ok'arin salwantar ko kuma ma ta salwantar da rayuwar yarinya. As for my own part na hak'ura na janye" "Sorry Mr Kurfi, ko ka hak'ura hukuma bazata hakura ba". Mik'ewa kawae yayi kansa yana masa wani juyi ya sake gaisawa da Affan sannan ya fice. Kicib'is sukayi da Daddy yana k'ok'arin shiga kamar zae hantsila, hanya ya bashi ya wuce masu biye masa baya suka tsaya a k'ofa. Ganin Daddy yasa D.P.O mik'ewa da sauri ya bashi hannu, da kyr yayi convincing Daddy ya zauna in da Affan da Mummy suka fice waje suka zauna suna maida maganar. "Affan kaga abinda nake jima Nana ko?Wannan wacce irin rayuwa ce." "Karkii damu Mummy komae jarrabawa ce daka Allah, na tabbata Alhakin y'ay'an wasu ne ya fara kama Daddy. Gashi gayen chan ya bada points masu kyau, ya kamata a san in da suka kai Aman "Haka ne Affan, Amma kasan me? Yaron nan shine wanda Nana ta fara shiryuwa saboda shi, son sa take sosae Affan, kana ganin yanzu zae dawo mata ne? Kana ganin ance fa sanadiyar shashancin ta har ya nemi rasa idanun sa, fisabilillah Affan Kana ganin zae cigaba da Son mace Irin Nana"? Cikin muryar Kuka da tsantsar takaici Mummy take magana. STORY CONTINUES BELOW  Handkie mai kyau Affan ya ciro ya shiga share mata hawaye. Daddy ne ya fito hannun sa rik'e dana Nana, D.P.O sae washe baki yake yana ban hak'uri kamar wani laifin Aka ce yayi, assuring nasa kawae yake akan kar yaji komae bazaa k'ara d'aga maganar ba. Girgiza kai kawae Mummy tayi suka rufa musu baya ita da Affan. (K'asar mu kenan, sam ba'a adalci).1 A mota ba abinda Nana take sae kuka, bata baki Daddy yake yana kwantar mata da hankali. Duk a tunaninsa kukan wulak'ancin da aka mata ne, be san ita kukan yadda zata kwashe musu da Farhan kawae take hangowa ba, wani irin abu ta hango a cikin k'wayar idonsa me kama da tsantsar k'iyayya. Ko da suka k'arasa gida ba wanda ya kuma cewa komae kowa ya wuce d'akin sa,sake shiryawa Affan yayi, yayi ma Mummy sallama yaja motar sa. ☆☆ "Malam lafia ne wai ka dawo ka sani a gaba sae faman tsaki kake". Na'eem ya tambaya yana kallon Farhan da ya kusa shanye robar swaan babba. "Mtsww". Ya kara jan wani tsakin a karo na ba adadi yana zame botr d'in wuyan rigar sa. "Tohh Allah kyauta". "Ameen". Ya amsa da sauri. Kira ne ya shigo wayar sa, ta side view ya d'an kalli wayar, wani wawan tsakin ya k'aa ja ganin sunan Nana yana yawo akan screen d'in. "Ko uban me zata fad'a mun"? Ya sami kansa da furta wa. Kallon sa kawae Na'eem yake, sae kuma ya kwashe da daria, "Ni dama nasan za'a rina, akan mace ka zauna kana neman zauta kanka. Haba bruh kamar ba namiji ba, aini wlhi yadda matan nan sukayi yawa ba wadda ta isa ta d'agan hankali, red card kawae zan d'aga mata." "Kai kasan wannan kuma, ni ka barni da abinda ya damen dallah karka wani k'aran stress da surutun ka". "Shikenan dama dae shawara ce". "Baa son shawarar". "Ok Fine, mutum sae rigima da masifar tsiya, i wonder ya matar ka zatayi dakae?" "Me kace"? Farhan ya tambaya yana kallon Na'eem. "No bada kai nake ba, ina karanta wani abu ne". Mik'ewa yayi gaba d'aya ya fice daka Office d'in. Sae faman kira ke sake shigowa wayar Farhan d'in. Jin kiran yana neman damun Na'eem yasa shi d'aukar wayar, sunan da ya gani yasa shi k'ara gasgata zargin sa. "Hello, Farhan, please ka saurare ni, i ll explain everything Don Allah." "Hello Auntyn mu". Ya furta yana komawa mazaunin sa. Jin muryar wani bana Farhan ba yasa Nana ta kasa k'arasa abunda tayi niyyar f'ada. "Hey". Ta amsa masa. "Kiyi hak'uri fa ya d'an fita ne, ni broda nasa ne sunana Na'eem, it seemx kamar u guys are having tough time ko? Karki damu in kika yimin bayani zan taimaka sosae." "Ikon Allah, zubairu kanya" ta fad'a a ranta. "Emm nothing much kawae in ya dawo kace ya kirani please, Thank u". Kafin yayi magana har ta kashe wayar. Bin wayar yayi da kallo, sannan ya tab'e bakinsa "Wannan ai taci uwar Farhan a miskilanci, jifa yadda ta amsa mani. Chan ta matse muku."Ajiye wayar yayi a gefen sa ya cigaba da sabgar gabansa. ☆☆☆ "Amani kenan". Ishu ya furta yana b'antarar rake. "Wato akwae wata bishiyar rake a gonar Mai martaba sarkin musulmi, raken nan saboda zak'i da gard'in sa, har wani d'and'anon zuma yake". STORY CONTINUES BELOW  Gaba d'aya suka kwashe da daria Nafi har da rik'e ciki. "Allah wlhi, ai yara don baku san sirrin cikin rake bane". "Raken ma na gonar Sarkin musulmi ko? "Nafi ta amsa tana daria. "Yo dama ya zaai su sani, girma dai ya fad'i wlhi." juyowa sukayi gaba d'aya suna kallon me maganar, Ma'u ce yar gidan Dagaci tsohuwar budurwa Is'hu da ya daena kulawa zuwan aman. Watsar da totuwar raken yayi, ya sauko daka kan keken nasa. "Ke wai ban hanaki bina duk inda naje ba? Ance ba'ayi ba'ayi akae kasuwa Amma kink'i, aradun Allah zaki ji ba d'adi." "Sae mai don naji ba dad'i, ma yaudari kawae, akan wata banza k'afa kamar langa langa zaka nemi gayan magana, wama yasan daka in da take, aikin banza." Saukar mari taji a fuskar ta, Nafi ce tsaye tana huci. "In zaki zagi Is'hu ke kika sani, ki tabbatar amma baki zagi Aman ba don wlhi zaki mamakin abinda zan mikii. " "Ni kika mara? Ni kika mara?"Ta k'ara maimaitawa tana shafar wajen. "Eh an mare ki, me zakiyi? Ganin ana neman kaurewa da rigima yasa Aman tayi saurin jan Hannun Nafi suka bar Ma'u da Is'hu tsaye suna maida maganganu "Haba Nafi, bansan ki da zafin zuciya ba, abinda take so nefa take rigima akae, kinsan a matsayin dana d'au is'hu ai, be kamata ki biye mata ku zama d'aya ba". "Yarinyar ce dama wlhi a ciki nake da ita, kinga yau na huce haushi na koba komae". "A dinga kai zucia nesa dai kinji, Allah yana tare da masu hakuri". Da haka suka karasa gida suna maida Maganar Ma'u... Abakin turmi suka tarar da matan gidan suna dakan fura. Cikin d'akin Gaji suka wuce Rahmata na kwance ba lafia, zazzabi take me zafi, gefen ta suka zamu suka zauna suna mata sannu, d'aga kai kawae take don ita tasan me take ji. "Anjima in rana tayi sanyi zaa samo babur sae ku raka ta cikin Rano chemist d'in Hafeezu". "Allah ya kaimu". Suka had'a baki gaba d'aya. Da yamma suka shirya cikin tsafta, machine aka samo guda d'aya, tunanin yadda zasu hau machine d'aya su uku Aman take amma taga su ko a jikin sa, sun fito k'ofar gida kenan sae ga Is'hu a nasa machine d'in. "Ina zuwa haka ne?"Ya tambayi Nafi yana gyara tsaiwar machine d'in nasa. "Cikin gari zamu raka Rahmata kemis bata jin dadi". "Allah ya sauwak'e kuxo muje". Nafi ce ta d'ane na Is'hu inda Rahmata da Aman suka hau d'aya. ♡♡♡☆☆☆ A daidai k'ofar gari tayar sa d'aya ta sache ba iska, gangarawa yayi a hankali gefen titi ya sami wani me k'ara iska. Sae da aka kara masa Iska sannan ya shiga motr sa ya d'au hanyar kibiya. Daidai wani gidan mai yana ko'karin shiga idanun sa suka sauka akan Fuskar Aman zaune a bayan machine, bae yi wata wata ba ya fasa shiga gidan Man ya take motar sa, sam hankalin sa na kan su besan akwae tanker d'in mai agaban ba, wani wawan burki yaja lokacin da ya kusa dakar ta, salati kawae mutanen wajen suke don kowa ya gama sadakar wa sae anyi mugun accident. A gigice yake ,ganin irin tsallake rijiya da bayan da yayi, Numfashi kawae yake sama sama, yana maimaita "Alhamdulillah, Alhamdulillah." Sae daya d'au wajen mintuna uku sannan ya sami nutsuwa, fitowa yayi ya nufi in da me tankar man yake ya bashi hak'uri. Ba komae Allah ya tsare gaba kawae yace masa. Komawa yayi cikin mota yana tunanin ko da gaske ne abinda idanun sa suka ganin masa, ko koma irin mafarke mafarken daya saba yini. Shiru yayi yana k'ara kallon hanyar da suka bi. Ganin ba shida wata k'wak'waran amsa yasa shi data motar ya cigaba da tafia. ♡♡ Bayan sun koma gda da daddare suka fito suna sand'a, wata yar k'aramar k'ofa da akayi da langa langa Nafi ta jawo sae ga hanya sosae ta fita, mamaki ya kama Aman ta sauke ajiyar zuciya, durk'usawa sukayi kamar masu rarrafe suka bi wannan k'ofar suka fice daka gidan. Gudu suke cikin duhun dawa, sae da sukayi nisa sosae sannan suka tsayaa suna maida Numfashi suna daria. "Kawae ace zaa hana mutum zuwa dandali wannan ai k'wara ce. Gashi sahibina yana chan yana tsumayi na". "Ke wlhi Nafi kamar ba Yar fillo ba, nafa ji ance yan fulani akwae su da kunya amma banda ke". "Yo Aman ni ai Babata A'i kad'o ce, in kikaji ance kad'o to hausa wa kenan". "Lalle amma ai ita bata haka". Aman ta bata amsa. "Ke fa azamanin dah ko, sam baa aure tsakanin kad'o da fulani, babu shiri ko kad'an tsakanin su, sae zuwan musulunci sosae sannan ne fa abubuwa duka sauya, duk da haka akwae masu irin wannan ra'ayin rik'au d'in har yanzu". Gaba d'aya sae Aman taji kamar Nafi ta kama mata wani tabo ne, dalilin irin wannan banzar ak'idar ne yasa ta sami kanta cikin irin wannan halin. Shiru ne ya ratsa su har suka k'arasa dandali kowacce da abinda take ayyanawa. Aman na gefe tana kallon yadda ake gudanar da abubuwa, maza da yawa suna son kulata sae dae ana tsoron Is'hu. Ganin Nafi bata da niyyar komawa gida ga dare yayi yasa Aman k'arasa wa in da take da k'awayen ta suna ta gabzar gyad'a. "Ya kamata mu tafi gida Nafi". "Haba Aman bari muyi sallama da Garbati ko, kinga yace min yana zuwa yaje sake kaya ne shisa". Bata ce komae ba ta koma in da take ta cigaba da zama. Wasa wasa waje yana ta watsewa Amma Nafi sam hankalin ta yana kan sharholiyar da suke. Akaro na biyu Aman ta sake Mata magana. "Muje". Kawae tace mata don har lokacin Garbati be dawo ba. Sunyi tafia kamar rabi sae suka fara hango wasu abubuwa kamar mutum mutumi tsaye cikin duhu, tsoro da fargaba ne ya kamasu. "Innalillahi mun shiga Uku Aman, yau an tare mana hanya". Cikin rashin fahimta Aman ke tambayar ta "Kamar ya an tare mana hanya"? "Cire takalman ki ki rik'e a hannun, gudu ya kamamu". Shine kawae abinda Nafi tace mata. Ba wata wata suka kwasa a guje, sae dae ko taku biyar basuyi ba Mazan Nan suka cin musu. A tsakiya suka sasu suna dariar rainin hankali. "Kuyi hakuri don Allah". Nafi ta fara magiya. Wani kyayyawan Mari aka sauke ma Nafi A fuska. Janta d'aya daka ciki ya shiga yi yana cewa "yau zamu ci uban yarinya mara kunya. Kuka Aman take ganin itama d'aya yayo kanta. "Tsuntsu daka sama gasasshe". Shine abinda ya furta Muryar Garbati saurayin Nafi ne sak daya fara magana sae dae fuskar nan tasu rufe take ruf. "Su waye Anan"? Sukaji an fad'a daka bayansu. Hasken torch light ne ya gauraye wajen, ba shiru suka kwasa a guje.. Wanda yaja Nafi ne yaji takun gudun yan uwan tafiar nasa, ba shiri shima yabi bayan su. "Keko baiwar Allah me ya fito dake cikin daren nan"?Mik'ewa tayi tana kakkab'e rigarta, ko ina na jikin ta rawa yake. Nafi ce ta k'araso tana shrv'ar hawaye, kalle kalle kawae take kana gani kasan a tsorace take. Sake maimaita tambayar yayi yana ko'karin haske Nafi, saurin kare fuskarta tayi, cikin muryar kuka tace; "Dandali mukazo shine suka tare mana hanya". "Kun sansu ne"? Ya tambaya yana sauke fitilar tasa. "A'a bamu san su waye ba", Nafi ta bada amsa. Kamar Aman ta furta su Garbati ne sae dae bata da sauran courage, shiru tayi tana tausayin Nafi don ba k'aramin son Garbati take ba. "Illar fitar mace cikin dare kenan, na tabbata ba'a san kun fito ba don gidan Baffan kudu akwae sa'ido musamman akan harkar ya'ya mata." Jin yama gane su yasa Nafi ta shiga rok'an da ya rufa musu asiri, shiru kawae yayi ya wuce gaba suna bin sa a baya har k'ofar gida. Sae dayaga sun janye yar langa langar nan sun shige sannan ya juya yana jinjina al'amarin. "Wane anan? "Kawu ya fad'a yana k'araso wa jin motsi. A guje suka kwasa suka shige b'angare su Nafi. "Ja'irai da kun bari nazo nan na same ku ai". Kaf cikin su ba wadda ta samu wani barcin kirki, kowa da abinda yake sak'awa,. Mamakin Garbati kawae Aman take, dama haka ne wani ba da zucia d'aya yake son ka ba. Da gari ya waye suka shiga d'akin Gaji, anan suka tarar da Rahmata zaune tana shafa mai. "Ya jikin Rahma"? Aman ta tambaya fuskarta d'auke da murmushi tana ko'karin zama a gefen ta. "Da sauki sosae, jia nayi ta jiranki har na gaji nae barci". Kallon juna sukayi ita da Nafi suka tuntsure da daria., Sae Da asubah da suka tashi abun ya basu daria, Aman harda gwada yadda Nafi ta rud'e. Waje suka jawo Rahmata suka shiga bata labarin abunda ya faru, "Wallahi Nafi kinfi ban daria, muryar ki har wani rawa take, Anya kuwa baki saki fitsari a wando ba?? Hahaha Ji kake Fas a fuskar Nafi. Wayyo cikina". Aman ta fad'a tana rik'e cikin ta kamar zata kai k'asa. Daria suke dukansu har da Rahmata, "Maganin mara sa jin magana kenan ai, amma ina jin fa Ma'u ce tasa aka rama mata marin da kika mata". A cewar Rahmata Shiru sukayi suna nazari, tabbas zae yiwu ita d'in ce, kafin su gama ftowa daka tunanin sae gata ta tawo hannun ta rik'e da kara tana yan wak'ok'inta cikin jin dadi. Sae data xo daidai su sannan ta k'ara k'arfin muryar tata, Ci kanki basu ce mata ba har ta wuce tana dogara kara a k'asa. STORY CONTINUES BELOW  Kicib'is sukayi da Is'hu sanye da wani kodad'd'en Jeans Da wata Maroon Riga, Ya zura rigar cikin wando yayi zanxaro, fuskar nan tasha tabarau bak'i irin no respecting d'in nan. Washe baki Ma'u tayi ta nufe sa tana daria, "Karki k'araso nan malama, baki ga irin wankan da nayi bane? Ko ni sa'an ki ne?Wannan wankan na Aman ne" "Kayi kyau Is'hu na", ta furta kamar wata wawiya. Tsaki yayi kawae ya rab'a ta gefen ta ya nufi su Aman yana bouncing kamar wanda ya samu dislocation a k'afa.2 Wata irin daria ce kecin Su Aman, aikuwa kafin ya k'araso tuni sun fara ba tsayawa. "Babban yaro A k'auyen Mad'achi, kansulan Yan mata". Shine kirarin da Nafi ta fara yi masa tun kafin ya k'araso tana guntse dariar ta. "Naji wannan kirarin Nafi, Wato da ace Nafi kema kin shiga birni kinyi karatu irin wanda nayi, woo da zamu iya karawa a iya tsara lafazi", "Allah babban yaro". Ta tambaya tana sake k'unshe dariar ta. Hira suka cigaba yana basu abin daria, sam Aman ta manta da kanta da wani damuwa da take ciki, zaman ta dasu Rahmata ba k'aramin dad'i yake mata ba, ji take ina ma zasu dawwama a haka? Soyayya ce me tsafta suke ma junansu. Sae da sukayi maganar zuwa cin Kasuwa sannan suka wuce gida shi kuma Is'hu ya wuce zuwa majlisar su ta rake. ☆☆ Zaro Envelope d'in yayi ya fito da hotunan da suke ciki, tunanin sa kawae ta ina zae fara nemar wa Aman iyayen ta, mai da hotunan yayi ya kishingid'a yana jin ransa ba dadi. Takaicin sa d'aya rashin bin machine d'in da yayi wanda yana da yak'inin Aman ya gani a bayan machine d'in. Toh amma me zae kawo Aman nan? Habu ne ya shigo ya sameshi a haka, "A ah ashe ka dawo ban sani ba." "Na dawo ban jima ba,kaina ne ba dad'i shisa kawae na d'an kwanta." "Ayya sannu Allah ya sawwak'e. " "Ameen". "Ya maganar mu ta zuwa Cin kasuwar Rano kuwa Ko ka fasa.?" Mik'ewa yayi daka kishingid'ar da yayi ya maida hankalin sa akan Habu; "Gaskia ina tunanin na fasa wannan satin, amma mu bari zuwa next week in Allah ya kaimu." "Owk Allah ya kaimu". Da haka suka d'an taba hira sama sama har lokacin sallah yayi suka tafi masallaci. ☆☆☆ Tun Nana na kiran Farhan tana saran zae d'auka har tazo ta saddak'ar da bazae kara d'aga wayar ta ba. Kuka kawae take tana dana sanin abubuwan data aikata. "Aikin kuka ya ganki kuwa". Muryar Mummy ta daki kunnenta. Da sauri ta fad'a jikin Mummyn tana sake sakin wani kukan me ban tausayi. "Na daena Mummy, Na daena wlhi na gyara halina." "Nasani Nana, amma ki sani komae mutum yayi dole ya girba, duk abinda nake gaya miki yau kinga ranar ko? " "Amma Mummy mesa sae dana tuba sannan wannan abun zae faru dani? Eh Mummy?? Mesa?" "Saboda kema lokacin da kike jin aikata duk abinda kika ga dama babu me hana ki, shisa Allah yake so ya nuna miki ikon Shi. Nana ana daena duk wani abun da bashi da kyau ne saboda Allah, amma ke tuban ki saboda soyayya ne, kinga kuwa dole kiga ba daidai ba" K'arfin kukanta ta k'ara ba tare data ce komae ba, sae datayi me isar ta, duk tana jikin Mummyn. Ba wani b'ata lokaci zazza'bi me karfi ya kamata. Tausayi sosae ta bama Mummy, sae dae tana son nuna mata kuskuren ta. Gefen gado ta kwantar da ita ta fita zuwa d'akin ta,. Hannun ta d'auke da paracetamol ta dawo, zaunar da ita tayi ta bata tasha sannan ta fita don kiran Nurse Fati a waya. ☆☆ Part d'in Hajja ya wuce yana rangaji kamar wanda kwai ya fashe ma a ciki, so yake yayi maganar da wani ko ya sami sassauci a ransa. A parlo ya sameta da yan jikokin ta suna kallon tashar Am Hausa, ganin yanayin da yake ciki yasa ta wuce bedroom d'inta,take mata baya yayi ya sameta a zaune gefen gado tana jiran shigowar sa. "Lafia dae Maigida?"Ta tambaya tana kallon sa. "Ba lafia ba Hajja, akan abunda ya faru dani kwanakin baya ne", Nan ya shiga bata labarin abunda ya faru, tun had'uwar su da Nana da kuma zuwa yanzu abunda ya faru a station. Salati kawae take tana mamakin wai yarinya mace karama zata iya aikata wannan shed'ancin. "Hak'ik'a wannna yarinya shed'aniya ce, sam bata dace da shigowa ahalina ba, me za'ai da mace me zuciar rashin imani". Fad'a sosae Hajja take kamar Nana na gabanta, shi kanshi gogan sae da yayi danasanin fad'a mata don chan k'asann zuciar shi yana son Nana sae dae yana son hukunta ta, yana son ta gane rayuwar ma gaba d'aya, duk da dae a yan kwanakin nan yaga chanje chanje a tare da ita, amma hakan bazai hana shi nuna mata kuskuren ta ba. Fitowa yayi bayan Hajja ta sake jaddada masa da ya cire Nana daka tsarin sa, sam basu dace ba, ya amsa mata ne kawae amma baya jin zae iya abun da take nema. Lalubar wayar sa yayi ya shiga black list ya watsa number ta, ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya shiga dialing Number D.P.O. "What!? Kamar ya komae ya wuce? Wato mahaifin ta yaxo ya rufe maka baki da kud'i kar abun ya shafi siyasar sa ko"? Farhan ya fad'a yana huci bayan ya gama sauraran fake bayanin D.P.O. Cikin inda inda D.P.O ya fara magana "Ba haka bane Kawae dae kaga yarinya ce, kuma mace, su wad'annan samarin ai suna tsare har sae mun gano in da yarinyar take". Wani wawan Tsaki yaja, ba wani b'ata lokaci ya katse kiran yana jin wani tsantsar b'acin rai. Gaba d'aya k'asar ta lalace kowa ba gaskia, Allah ya sawwak'e. ☆☆☆ Ranar Friday su Aman suka shirya suka tafi cin kasuwa, ba irin nacin da Habu bema Affan ba akan yazo suje, fafur yak'i, shi sae next week, haka ya hak'ura ya tafi shi kad'ai.. A cikin kasuwar habu ya had'u da Is'hu dasu Aman, kasancewar shima Habun yayi karatu a sokoto amma ya fi Is'hu aji da shekaru, sun san juna saboda I'shu mutum ne me son mutane, ga abun daria, nan fa aka kaure da hira. Duk yawon cikin kasuwar tare sukayi daka k'arshe suka tafi gida ganin yamma tayi, Habu yana ta satar kallon Rahmata, sosae yar Fillon ta burge sa, kudurewa yayi a ransa zaexo ya kawo wa Is'hu ziyara in an kwana biyu ya yad'a manufarsa. Ko daya koma gida hirar su kawae yake yiwa Affan, jinsa kawae yake ba wani fuskanta yake ba, sae da yaji ya ambaci Aman sannan ya mik'e sa sauri; "Naji kamar kace Aman ko"? Ya tambaya da zumud'i "Eh a cikin su akwae Aman, sae dae ita kamar ba bafulatana ba, haka dae kalar ta daban, kuma bata da magana kamar su". "Dan Allah tashi ka rakani muje k'auyen nasu". Affan ya fad'a yana mik'ewa, har ya kai bakin k'ofa ya juyo yaga Habu zaune yana kallon sa da mamaki. "Kaga Habu ka taso mana ko sae dare yayi?" "Ai ban gne me kake nufi bane, daka jin labari sae kace sae munje, yarinyar mafa na lura kamar shi gayen ke sonta." Wani abu ne yaji ya soke shi a zucia, duk da bashi da tabbas akan tunanin da yake, amma sae yaji ransa ya b'aci jin ance akwae me sonta. Jiki a sabule ya zauna yana maida numfashi bece komae ba. K'arin bayani Habu ya sake nema don ganin irin sauyin yanayin daya shiga. Kamar bazae ce komae ba, sae kuma ya shiga bashi labarin abubuwan da suka faru har zuwa ranar daya dawo yaga wata kamar Aman d'in. "Lalle biri yayi kama da mutum, zata iya yiwuwa ita ce Aman d'in taka, don gaskia wannan batayi kama da yan kauyen bama, sae dae yanzu dare yayi ka bari da safe sae muje." Da haka sukayi arrangemnt na zuwa gobe in Allah ya kaimu. *Nima nace Allah ya nuna mana da rai da Lafia*Tun da yayi sallar asubah ya gama shiryawa, eagerness ya hana shi ma ya zauna waje d'aya, sae zagaye yake yana farin ciki, a ganin sa komae yazo k'arshe, yama ga Aman ya gama. Ganin har 8:30 ba Habu ba labarin sa yasashi fita waje yana zazzagaye unguwar, sam be taba tunanin karb'ar number wayar sa ba, ganin lokaci yana k'urewa sosae ya sashi deciding ya tafi da kansa kawae duk wani k'auye nearby ya shiga ko Allah zae sa ya ganta, ba wani b'ata lokaci yaja motar sa. Tun yana shiga k'auyukan a marmarce har ya fara k'osawa, azhar sosae tayi masa, gefen titi ya samu yayi parking motar sa ya isa wajen wasu masu gyaran babura suna alwala, mik'a musu hannu yayi ya nemi su bashi ruwan Alwala. Bayan yayi Alwalar ne suka umarce sa daya jasu sallar ma kawae, Murmushi yayi yace; "Kune kuka fi chanchanta da kuja sallah, d'an gari yafi bak'o chanchanta yaja sallah, haka nan mai gida shine yafi kamata yaja sallah akan bak'on da yaxo gidan sa, sannan maigidan haya da wanda yake hayar gidan, a tsakaninsu waya kamata yaja sallah a ganinku??" Daya daka ciki yace; "Ai mai gidan ne ya kamata nidai a ganina". Wani k'aayataccen Murmushi ya sake yi. "Babu shakka wanda yake hayar gidan shine mafi chanchanta da yaja sallah akan wanda yake gidan sa ne, sae dae duk idan wad'anda na lissafo bazasu iya jan sallar ba, ma'ana basu da isasshen ilimin da zasu ja sallah, wannan sae abi sabanin haka". Jinjina kai kawae suke Alamar gamsuwa, tunda suke basu tab'a sanin wannan ilimin ba sae yau, cikin k'arfin guiwa d'aya daka ciki ya shiga gaba ya jasu sallah. Bayan an idar ne ya mik'a musu hannu sukayi musabiha d'aya bayan d'aya. Kud'i ya ciro a Aljihunsa ya mik'a musu. Murna sosae sukayi daka karshe yayi musu sallama. Har ya kai bakin motar sa ya tuno ya kamata ya tambaya, komawa yayi ya kira d'aya gefe ya tambayesa, "Dan Allah ko akwae wani k'auyen fulani bayan wannan nan gaba kad'an"? "Eh akwae kauyen Yad'o, gaba damu ne nan kad'an". "Ok nagode". Bismillah yayi ya tada motar sa ya shiga, duk da a galabaice yake, ga wani cion kai me zafi da yaji yana ko'karin kamasa, hakan be hana shi nufar k'auyen gaba ba. Mintuna kad'an da barin sa wajen Is'hu ya k'araso yana tura babur d'in sa, so yake asa masa iska, zama yayi akan benchin wajen yana son fuskantar hirar da ake. "Gaskia Bawan Allah'n nan yayi a rayuwa, jifa duk had'uwar sa da wayewar sa amma ba girman kai, kai amma wlhi yaji dadi.." Jin an ambaci wani ya had'u yasa ran Is'hu ya d'an sosu, a rayuwar sa kullum yafi son ace shine yafi kowa a k'auyen, matsawa ya k'arayi yana son jin ainayin labarin. Anan ya fuskanci in da maganar ta dosa, tsaki yayi yana wani buga k'afa shi a lalle bega abun burgewa a hirar tasu ba, ba suyi wata wata ba kuwa suka taso masa kamar zasu cinye shi d'anye, maganganu suka shiga fad'a masa son ransu, dama akwaemasu jiran kiris ganin yabi ya babbake komae a garin, kamar wani kububuwa ya tashi fuu yabar wajen. "Kinsan akwae biki gidan Nan kuwa.? "Rahmata take tambayar Aman tana nink'e zanin data cire. Girgiza mata kai tayi alamun bata sani ba. "Akwae d'aurin auren Xahra yar gidan Baffan burni da Khadija ita ma yar gidan d'ayan Baffan burnin, anan k'ofar gidan ake d'aura auren, su kuma sae suyi bikin su a chan, amma fa muma anan ana bikin. Bayan d'aurin auren za mubi Wata motar muje ayi kamu damu achan, kinsan xahra da khadijan sa'anninmu ne nida Nafi." "Allah sarki, Allah ya sanya Alkhairi". "Ameen, kema ai zaki burnin ko"? "Anya? Gaskia bazan je ba, ni tunani na ma idan ranar yan uwanku suka zo suka ganni me zasu ce a kaina?? "A take yanayin ta ya chanja. Dafa ta Rahmata tayi ckin kwantar da muryar tace; "Karki Damu danginmu basu da wannan matsalar, ki kwantar da hankalinki kinji?" Girgiza kanta tayi alamun ta gamsu,sae dae ba wani gamsuwa tayi ba kawae dai tabar abun a ranta ne. Fita sukayi zuwa gidan Abu me d'inki don karbo d'inkin su wanda sam Aman bata san ma ankai ba sae gani tayi wai harda ita aka d'in ka. Godia ta shiga yi sosae har sae da Rahmata ta nuna alamun fushin ta sannan tayi shiru. Ko da suka koma gida ma haka ta shiga yima Gaji godia, anan take gaya mata ba ita tayi musu ba, Baffan burni ne, Addu'a tayi musu a zuciyar ta wanda bazata tab'a daena wa ba don kam bata da abinda zata biyasu. ☆☆☆☆☆ Wata razananniyar k'ara ta saki ganin Mummy a yashe a k'asan carpet babu alamun rai, iyakar rud'ewa ta gamayi, jijigata ta shiga yi tana kiran sunan ta, talatu mai aiki ce ta fad'o da gudu jin karar Nana. "Talatu Mummy, bansan me sameta ba,ki taimaka mun". Ruwa ta fara d'aukowa ta mik'a mata ta shafa mata a fuska, ajiyar zucia ta sauke sae dai idon nan a rufe ruf yake. "Talatu jeki ce da driver ya fito da mota". Da gudu ta fita ta sa driver ya fto da mota, ko mayafi babu jikin Nana haka suka tallafo ta suka sa ta a mota. Direct Al'ihsan Clinic suka wuce inda suke da File, ba wani b'ata lokaci aka karb'e ta. "Ga wayar ki Hajia ko zaki kira, na d'auko miki." Sae a sannan tunanin kiran Daddy da Ya Affan yaxo mata. Lokacin yana k'ok'arin shiga garin yaji ringing d'in wayar sa. Ganin sunan Nana yasa shi parking gefen titi don a ka'idar sa baya amsa waya yana driving. A rikice ya shiga kiran "Subhanallah, gani nan In sha Allah." Without second thought ya juya motar sa zuwa Kano. ☆☆☆ Hajja ce zaune, Abba, Daddy da sauran matan gidan duk suna zaune, tattauna wa suke akan bikin yar gidan Alhaji Isma'eel Mad'achi da za'ayi sati me zuwa. Alhaji Isma'eel shine Babban abokin Abban, zumunci suke tsakanin su sosae. "Ya kamata wannan karan tunda achan Mad'achin za'a d'aura auren ya kamata muje musu gaba d'aya har chan, ko ba komae naga Gaji musha hira. "A cewar Hajja tana washe baki. "Eh hakan kam yayi daidai, sae muje a d'aura auren, ku kuma ku shiga gidan in an gama sae mu dawo gaba d'aya." "A'a Gaskia". Hajja ta katse shi. "Ni da nake son wuni achan, tafiyar ku daban tawa saban, nida Maman yaran da Majazen nan nawa biyu Farhan da Na'eem sae mun kai yamma gaskia". Murmushi Abba yayi don yasan Hajja dasan k'auye, dama da yaya ma ta yarda ta baro Kurfi, sae da aka kai ruwa rana sannan ta yarda. Addu'ah akayi da manzon Allah(S.A.W) ya Umarce mu yayin da muka gama wani zama, bayan an gama tattaunawa an tsaida yadda tafiyar zata kasance. Ko kad'an da aka fad'a ma Farhan beso ba sae dae ba yadda zaeyi yaja da hukuncin Hajja. Am sorry, Affan da Aman basu had'u A wannan chappy d'in ba, laifin Mss xoxo ba nawa baAn samu Mummy ta dawo daidai, Allurai akae mata aka d'aura mata drip. Dama chan she's hypertensive, aka xo kuma aka k'ara mata wani b'acin rai. Sosae Dr ya k'ara jan kunne akan kula da lafiar ta. Suna zaune a reception Affan ya shigo a birkice, sae da yaji bayani daka bakin Dr. Sannan ya samu peace of mind. Duk iya zaman da sukayi babu Daddy ba dalilinsa, duk abin na ransu sae dae ba wanda ya furta, Affan ransa har wani zafi yake, gaba d'aya abun Daddy ya k'ara zama worst, gashi Election na matsowa, bashi da wani time na familyn sa kwata kwata. Washegari da safe akayi discharging nasu bayan likita ya k'ara jaddada musu bayanan sa na jia. A gida sae nan nan suke da ita kowa na k'ok'arin ganin ya faranta mata Nana bata tab'a sanin irin Son datake ma Mummyn ma sae data ga k'uru k'uru zata rasa ta, nan fa ta k'ara d'aura d'amarar kyautata mata har k'arshen rayuwar ta. Batun Farhan kuwa ya d'ebe ta ya watsa a kwandon shara, duk da abun na damunta amma babu yadda ta iya, dama shi Alhaki kyuikyuiyo ne. Addu'a kawae take tana rok'on Allah ya cire mata son sa A ranta, duk yadda taso abun yafi k'arfin ta, gaba d'aya ta koma wata silent kamar ba Nana Boss me isa da tak'ama ba. Zaune suke a parlo sun gama cin abinci kenan, gaban Affan computer ce yana shigar da wasu muhimman documents, Mummy na zaune itama tana kallon Tv sae Nana dake kwance akan three seater tana danna wayar ta. Kamar daka sama suka ji sallama, janye take da trolly madaidaiciya, sae handbag k'rama me kamar pouse data sak'alo a kafad'ar ta, k'afar nan cikin wani ubansun hill shoe, baba mai gadi na biye da ita da wata k'atotuwar trolly. A guje Nana ta tashi tayi kanta tana kurma uban ihu, itama ihun take suka rungume juna kamar zasu maida kansu ciki. Farin ciki fal fuskar Mummy ta mik'e tsaye tana mata sannu da zuwa. A tsakiyar Parlon suka saki juna,da sauri ta k'arasa ta rungume Mummy, kan Affan tayo zata rungume shi yayi saurin gocewa; "Kefa Hany matsalata dake kenan bakya girma". Turo baki tayi ta koma wajen Mummy ta zauna. Hira aka shiga yi na yaushe gamo, daka karshe suka tashi suka haura sama zuwa d'akin Nana. "Sam yaran nan basu hankali sosae Mummy". Affan ya fad'a bayan sun bar parlon. "Dama ai sae a hankali". (Hany yar gidan Sister Mummy ce da suke zaune a kaduna, rayuwar ta da tsarinta daban yake, Age mate d'in Nana ce sae uban rawar kai, tana final year A ABU Zaria,hutun session akae shine ta kwaso uban kayan nan tayo kano. Sosae suka son junansu ita da Nana) STORY CONTINUES BELOW  "Emm daxu naga alamar akwae maganar da kake so kayi mun ko"? Mummy ta tambayi Affan "Eh akwae Mummy". Gyara zama yayi ya shiga bata labarin abunda ya faru. Farin ciki kawae take, kamar ance Nana ta b'ata an ganta haka Mummy takeji. "Alhamdulillah kaga shikenan na zama me y'ay'a biyu, ga hanan ma uku kenan, naji dadi, amma gaskia ina so ka d'an jinkirta komawar ka saboda akwae abun da nakeso musa ido akae, abune da ya jima yana damuna, kuma da yake zargi nake, shisa ban tab'a sawa a kaina ba, sae jia ne na tabbatar da gaskiar Al'amarin, hakan kuwa shi yayi sanadiyyar halin dana shiga". "Mene ne haka kuwa Mummy"? Ya tambaya yana k'ok'arin kashe system d'in gabansa. "Muje d'akina zakaji komae". Koda suka shiga d'aki, nan ta karanto masa abun da yake faruwa, cikin tashin hankali Affan yake kallon Mummy, "Yanzu Mummy all this years kina zaune cikin wannan musibar Amma baki taba complain ba?" "Kai yaro ne Affan, Baka san ya rayuwar duniyar take ba, kana tunanin danayi wani yunk'urin da zan kawo haka?Inaa". Shiru sukayi kowa yana sak'a abu a ransa, Affan kansa ya shiga duhu sosae sosae, tunanin sa yadda zae yi ya handling case d'in kawae yake. Sallama yayi mata ya tafi zuwa d'akin sa yana jin kamar zuciyar sa zata tsage gida biyu. Da sassafe ya fita lokacin hasken rana be fito na, da sauri Mummy ta lek'a ta window, aikuwa sae ganin bayan motar sa tayi tana kkarin fita gaba d'aya. Addu'a tayi masa sannan ta koma ta cigaba da karatun Alk'ur ani me girma. Nana da Hany ranar ko runtsawa basuyi na saboda hira, nan Nana ta bawa Hany labarin Had'uwar su da Farhan har zuwa halin da ake ciki yanzu. Daria kawae Hany keyi don bata manta irin kalar cika bakin da Nana keyi akan Soyayya, sae gata dumu dumu a ciki, nata ma yafi worst dan da karfin gaske ya damke ta. "Is this for real?"Ta tambaya bayan ta tsayar da dariar ta. "Nana Boss ce wai me maganar Lurv, kuma irin madly inlurv d'in nan, lalle ma tab. Me kikeso ayi yanzu Juliet?" Tsaki Nana tayi ba tare da ta amsa mata ba, mik'ewa tayi ta jawo drawer jikin mirrow ta fara lalube kamar me neman allura. "Common Babe ki daena wani acting, kin kamu and kuma kin riga kinyi admitting, kixo muyi finding solution". "No kawae share". Ta fad'a sounding a bit angry don har ga Allah taji haushin dariar. Mik'ewa Hany tayi ta tako har gabanta, rufe drawer tayi da hannun ta,taja Nana suka koma gefen gado. Zama sukayi ta shiga bata shawarwari akan yadda zatayi, a k'arshen bata barta ba sae datayi convincing nata akan kawae su nemo gidansu suje su bashi hakuri. Idonta ya rufe solution kawae take nema, a take ta yarda suka shirya akan zasu nemi gidan suje tunda ba wahala zae ba. Ko Mummy basu gaya ma ba, suka shirya suka mata k'aryar zasu gidan kawar Hany d'in, basu sha wata wahala ba suka isa k'aton mansion d'in, sae a sannan Nana ta d'anji tsoro ya shige ta, a darare suka danna horn, Gateman ne ya lek'o yana tambayar su wanda suke nema, Cikin in da in da Hany tace Maman su ce ta aikosu wajen hajia sukawo sako, ba wani b'ata lokaci ya wangale musu gate suka samu gefe sukayi parking. Da suka fito rasa ina zasuyi sukae, parts ne birjik duk irin d'aya kuma, shahada sukayi suka nufi wanda yake kallonsu. Farida da Hajja na zaune sukaji ana knocking, "Ana knocking Farida". Hajja ta fad'a mata don yadda ta bada hankalin ta akan waya ba tashi zatayi ba. Mik'ewa tayi ta bud'e k'ofar, yan mata biyu ta gani tsaye, "Bismillah ku shigo mana". Ciki suka shiga kamar munafukai suka rakub'e ak'asan kujera, Hajja ce ta umarce su da su koma kan kujera, da sauri Nana ta mik'e zata hau, Hanny tayi saurin jawota ta dawo kasan. "A ah ba komae nan ma yayi". Hany ta fad'a tana b'alla ma Nana harara. "Allah sarki sae dae ban gane su waye ba". Zasuyi magana kenan aka bud'o kofar aka shigo, Farhan ne cikin Suit Ash yayi kyau sosae, fuskar nan sanye da space wanda ya k'ara fto da zallar kyaunsa, a rikice Nana ta d'ago kai jin k'amshin turaren sa, kamar an buga mata guduma haka taji da suka had'a ido, wani irin mugun fitsari ta ji ya kamata a take, k'arasowa yayi parlon yana musu kallon mamaki, Sake maimaita tambayar Hajja tayi, da sauri ya amsa da; "Ohh bak'i nane ai Hajja, k'annen abokina ne suka zo nan neighbours d'in mu shine yace su shigo su gaishe ki". "Ayya Amma kun kyauta yara, ya manyan naku?" "Suna nan kalou". Hany ta amsa tana satar kallon Farhan. "Ku muje ko". Farhan ya fad'a yana kafe su da ido. "Ah da wuri haka, to ku tsaya ina zuwa". Da sauri Hajja ta fad'a bedroom nata ta d'auko turare masu k'amshi, kafin tazo har sun fita waje, farida ta bawa tace ta kai musu da sauri. Tana fitowa ta hangosu tsaye da Farhan jikin motr su,magana suke hakan yasa ta k'arasa wajen. "Please Nana stay out of my life, mene na biyo ni har gidan iyayena? Ko kinzo kisa garadan naki su sace miki nine?? Ehe"? Ya fad'a yana kallon ta eye ball to eye ball, kwalla ce kawae ke fita a idon ta. Turus Farida tayi jin abinda Yayan nata yake fad'a. Jiki a sab'ule ta k'arasa ta mik'a musu sak'on Hajja ta juya da sauri don kaiwa Hajja tsaigumi. Haka suka ja k'afafuwan su kowacce rai ba dadi don iya kar wulak'ance Farhan yayi masu, sae da yaga ftar motar su sannan yaji be kyauta ba sam, wani sashin na zuciyar sa kuma yace ita ta jawo ma kanta. Tun a hanya ba abinda Nana take sae kuka, Hany ce ta karb'i driving d'in don tsaf Nana zata iya watsa su gefe. Ita kanta ranta babu dad'i, bata zata haka Farhan d'in ya had'u ba, tana ganin shawo kansa abu ne me sauk'i, sae gashi sun zubar da kansu sunje har gida ya watsa musu k'asa a ido.. Da suka isa gida ma babu wadda ta tsaya a parlo suka wuce bedroom nasu kowacce ran nan ba dad'i. ☆☆☆ Da sauri Farida ta k'arasa part d'in Hajja har tana had'awa da tuntub'e, "Umm Hajja, Abun duniya baya k'arewa". Ta fad'a tana tabe baki, "Me faru"? Hajja ta tambaya. "Ashe yanmatan Yaya ne, yace wai k'annen abokin sa, kuma da alama ba biko suka xo don naji Yayan na cewa ta ky'ale sa, ko shima tazo sawa a sace mata shine", "Toh munafuka, Ina ruwanki"? Ya fad'a yana k'arasowa cikin parlon. Da gudu tayi bayan Hajja don ganin b'acin rai kwance a fuskar sa, Hajja ce ta shiga tsakani amma duk da haka sae daya rank'washe ta aka, k'ara ta saki jin zafin rank'washin. "Toh mene abun munafurci anan maigida?? Dama nima nayi tunanin haka, yarinyar a haka kamar ta gari sae shed'an ci fal ciki". Ficewa yayi kawae ba tare da yace komae fa, tab'e baki ita ma Hajjan tayi ta ja Farida d'aki don samun k'arin bayani.. ☆☆☆ A tsaye yake yana k'are ma wasu gidaje kallo, ko shakka babu akwae wani abu da yake faruwa sae de besan mene ba, duk tunanin sa ya kunce musamman da yaji komae daka baki me tushe, sae da ya gama sak'e sak'en sa yaja motar yabar layin. Barin layin sa kenan suka fto suna daria, kana kallonsu kasan suna cikin farin ciki, duk cikin su babu k'aramin mutum, kowanne ya nufi abin hawan sa ya shiga suna d'aga ma juna hannu. Tafiya yayi sosae kafin ya fara tunanin in da ya dosa, duk da mugun son ganin Aman da yakeyi Amma dole ya fara tabbatar da wanzuwar farin ciki a zuciyar mahaifiyar sa kafin kuma ya dawo kanta. Juya akalar motar yayi zuwa gidan wani abokin sa, duk da shi ba ma'abocin tara abokai bane amma yana da yan tsirari wanda tsarin su ya dace da juna. A k'ofar gida ya tsaya ya shiga nemn layin sa a waya, cikin sakonni da bazasu gaja uku ba aka d'aga daka d'ayan bangaren. "Oga kana duniyar nan dama?" Abokin ya tambaya cikin son tabbatar wa. "Ina nan wlhi, gani ma a k'ofar gidan ka". "Ah lallai yau na ciri tuta, bari na sanar da madam sae naxo nayi ma iso". katse kiran yayi ya kwantar da kansa kan steering motar yana sake zurfafa kansa a cikin tunani. STORY CONTINUES BELOW  Mubarak ne ya fto yana d'an waige waige, ganin mota daka chan gefe yasa ya k'arasa wajen ta, kama murfin yayi yana ko'karin bud'ewa, sae a sannan Affan ya d'ago, a hankali ya zare key din motar ya fto, damk'e hannun juna sukayi sa'annan suka yi cikin gidan. ☆☆ "Ah gaskia Nafi kina da nauyi haba". Rahmata ta furta tana gyara zaman mayafin ta. kasuwa suke son xuwa yin siyayyar d'an kunne da yan awarwaro da zasu sa a biki, Aman ma ta shirya abunta tana zaune tana kallon kwalliya wajen Nafi, kasa jurewa tayi ita ma tace; "Haba Nafin Garbati, wannan kwalliya sae kace ranar bikin ne". Jin ta ambaci Garbati yasa jikin Nafi yayi sanyi don dama tun lokacin da abun nan ya faru ya daena kulata sam, zatayi magana kenan taji yaro na magana daka tsakar gida. "Wai ana sallama da Rahmata". Shine abinda kunnuwan su suka jiyo musu. Kallon juna sukayi gaba d'aya don ita rahma bata wani kula samari, in banda haka ma da yamman nan ai a bari ma dare yayi. "Ina Rahman take ne"? Muryar Baffa Mainono ta iso musu ta katse tunanin da kowacce ta shiga yi. "Na'am gani Baffa". Ta amsa tana k'ok'arin fita. "Kije kiga bak'o a waje". Shine abinda kawae yace ya wuce zuwa b'angaren sa. Zura takalmin ta tayi samfurin su kwal, nuni tayi ma Aman da hannu akan taxo ta rakata, aikuwa ta mak'e kafad'a alamar bazata ba. Haka ta hak'ura ta nufi kofar gida zuciyar ta na bugu kamar wadda tayi tsare, haka kawae taji wani fad'uwar gaba mara misaltuwa. Lek'a kanta ta farayi, tsaye ta hango su tare da Is'hu, cikin shadda fara kMal, kunya ta kamata da tunanin me kuma abokin Is'hu yake anan,kasa k'arasawa tayi don duk a tunanin ta ba shine bak'on nata ba, ganin bazata fito ba yasa Is'hu kiran ta, a d'arare ta k'arasa shi kuma ya zagaya bayan d'angar karar dake k'ofar gidan. Introducing kansa yayi yana kallon yadda ta kama k'asan mayafin tana ko'karin yagawa, kasa d'ago kai tayi har sae da ya gaji yace mata; "Ina Aman"? da sauri ta kalle shi sae kuma ta tuno ai yama santa tunda sun had'u a kasuwa. "Ina son tambayar ki Rahma, ya kuke da Aman"? Shiru tayi hakan ya bashi damar ci gaba, "Akwae abokina da ya nuna mun kamar ya santa gaskia, da tare zamu zo ma, amma sae aka sami matsala na fita, kafin na dawo shi kuma har ya tafi, dama dae a kano yake, shisa nakeson ki sanar dani yadda kuke, don a yadda yake fad'an neman ta yake ido rufe". Tsoro sosae ya kamata jin abinda yace, shikenan masu neman Aman ne suka gano in da take, cikin sauri sauri batare da ta kara second d'aya ba ta nufi hanyar gida, kallon ta yake har ta kusa shige wa, d'aga murya yayi yadda zata jishi; "In kin shiga kice mata Affan yana gaishe ta" K'arasa shigewa tayi shi kuma ya nufi in da Is'hu ke jiransa. zama yayi yana kallon Is'hun, reaction d'in Rahma ya nuna akwae wani abu a k'asa, tambayar Is'hu yayi shi kuma ya sanar dashi iya abinda yakeji a gari. Godiya yayi masa ya raka shi har bakin titi bayan ya bashi sak'o ya bawa Rahmata A birkice ta shigo tana kwala ma Aman kira, suma dake zaune zaman jiranta suka fto da sauri, kama hannun Aman tayi suka shige chan k'uryar d'aki, kaf ta fad'a mata abinda Habu yace, sosae ita ma ta tsorota don har k'walla ta taru idonta, cikin k'arfin hali ta mik'e, "Ya kamata na k'ara gaba saboda bana son na saku a cikin matsala". "Matsalar me"? Rahma ta tambaya tana kallon fuskar ta. Hawayn da take mak'ale wa ne ya shiga sakkowa, kuka ta soma kamar dama ta riga tayi tanadiin sa, sae da tayi me isar ta Rahmata tana bata baki sannan tayi shiru. "Muje nayi ma su Gaji sallama ko"? Ta fad'a cikin dakewa. "Sallama kuma, ban gane ba". "Eh sallama dai ta tafia, zanyi godia ne abisa irin karamcin da kuka nuna min, har abada bani da kamar ku". Tsaki Rahmata taja, sannan ta wuce gaba suka nufi d'akin Gaji. Koda Gajin ma taji haka sae ta nuna babu wata matsala, yadda Rahmata ta fasalta mata Habun, babu alamun cutar wa a tattare dashi. Shiru sukayi suna sauraron Gaji har ta kai k'arshen bayanin ta. "Laa na manta yace na fad'a miki affan ko me? Wani suna dae haka wai yana gaishe ki" "Affan"!? Ta fad'a da sauri tana zaro ido. "Eh kamar haka ne sunan, ni ban tsaya ji ba, amma daka jin yadda ya fad'a ya nuna Affan d'in ne yake nemanki. Wata ajiyar zuciya ta sauk'e me nauyi sannan ya lumshe idon ta tana jin wani abu yana mata yawo a kanta. "In dai Affan ne ke nema na, ba macuci bane, Affan masoyine nabhak'ika, sae dae bazan bari mu had'u ba saboda k'anwar sa". Shine kad'ai abinda ta fad'a ta suri takalmanta tayi waje, chan bakin wata bishiyar mangori taje ta zauna ta shiga kundun tunani, wani abu me kamar dutse taji ya danne mata k'irji, Soyayya ce mai k'arfi take ji tana shiga kowanne b'angare na jikinta, sae da aka kira magrib sannan ta karkad'e zaninta ta wuce gida.. Shirye shirye ake kowanne b''angare, duk wasu events anyi su thursday and friday, ranar saturday ta kama d'aurin aure, cikin shigar Alfarma Abba ya fito, kana ganin sa kasan d'aurin auren nasu ne, kichibus sukayi da Farhan yana ko'karin shiga part d'in Hajja, har k'asa ya dur'kusa ya gaida Abban, anan yake masa tunin lalle su taho da wuri don yana son su sami d'aurin auren, Amsawa yayi sannan ya shige part d'in Hajjan. Tafiyar minti arba'een da biyar ta kaisu garin Rano, daga nan suka d'auki hanyar K'auyen Mad'achi, tun daga kan hanyar shiga garin suka fara ganin motoci, haka suka k'arasa, Abba suka fara hangowa dashi da Alhaji Isma'eel suna ta kar'bar gaisuwa, tun kan mota ta tsaya Hajja ke ko'karin bud'e ta, "Tsohuwa da rigima ki bari a gama tsaya wa mana". Na'eem ya fad'a yana daria, Mama ce ta kai hannu dama tana saitin sa ta taske masa k'eya, ihu yayi ya shiga sosa wa. "Kinmun daidai kuwa, ja'irin yaro". A cewar Hajja tana ko'karin kai hannun ta gaba. Farida me zatayi in ba daria ba, shiko Farhan ran nan a b'ace sam ba walwala. Gefe ya samu yayi parking sannan suka fito, Hajja, Maama, da Farida suka shige cikin gidan, su kuma Na'eem da Farhan suka k'arasa wajen su Abba. Gaisuwa aka shiga yi tsaknin su Hajja da Gaji, karb'a ta mutunci akayi musu, Fura da Nono kuwa kamar banza, Hajja bakin nan yak'i rufawa an sami abin da ake so. "Tashi muje d'akin Gaji mu gaida baki". Rahmata ta tab'o Aman da ta fad'a duniyar tunani. "A ah kuje kawae, ni ina nan". Ta bawa Rahmata Amsa bayan ta k'ara maimaita abinda tace. Had'e rai Rahmata tayi ta nuna b'acin ranta sosae, ganin b'acin ranta yasa Aman mik'ewa badon taso ba tabi bayanta. Tunda suka shiga Hajja ta kafe Aman da ido, a take taji zuciyar ta ta kwanta mata da yarinyar, wani irin abu take ji game da ita wanda bata san mene ne ba, har suka gaishe ta bata san suna yi ba, gaba d'aya hankalin ta yana wajen tunani. Sae da Mama tayi magana sannan ta dawo tana kallon su. Amsawa tayi da fara'a tana kafe Aman da ido hr suka fice daka d'akin. Gefen Gaji ta koma yadda ba wanda zae jiyo su ta fara magana....... Shiru Gaji tayi tana sauraron Hajja wadda ta dage tana zubo mata bayani, sae data kai aya sannan Gajin ta samu damar tofa nata.+ "Zancen Gaskia yarinyar Nan Allah ne ya had'a mu da ita, labarin ta yana cike da abun tausayi, kuma bansan ita ya zata fuskanci buk'atar da kika zo da ita ba." "Zata fahimta nasan" Hajja ta katse ta da sauri. Shiru Gaji tayi tana me jin nauyin buk'atar da Hajjan taxo da ita, ganin Gaji tayi shiru yasa Hajja ta cigaba da zuba bayanin ta. "Bari nasa a kira Kawun yaran, sae kuje chan d'akin sa in da ba mutane sosae, sae kuyi magana ko?" "Yawwa hakan yayi Gaji, Allah yasa a daidaita." "Ameen". Gefen kujerar d'akin Hajja ta samu ta zauna, Kawu tsaye ya hard'e hannayen sa yana sauraron ta, gefe kuma Alhaji Is'maeel ne, sae Abban su Farhan shima da yake tsaye, gaba d'aya ya rasa rigima irin ta Hajja. "Wlhi haka nan kawae naji yarinyar ta kwanta mun, ina jinta kamar jini na, kamar yadda nakejin su Farida. Ku taimaka mun na tafi da ita, nayi *Alk'awarin* xan kula da ita, kuma nayi *Alk'awarin* ko *Bayan Rainah* bazata kuma wulak'anta ba. Alhaji Is'maeel ne yyi saurin amsa mata da babu wani abu ai duk d'aya ne. "A'ah Alhaji, baza ayi haka ba, itama 'ya ce, a bata damar ta zab'i abun da take so". Abba ya katse musu hanzari. Hajja kamar ta kai masa duka, shiru tayi tana zazzaro ido tana addu'ar Allah yasa kar Aman tak'i. Da sallama ta shigo d'akin zuciyar ta na bugawa, ganin su Kawu da Baffan burni yasa jikin ta ya kara tsuma, "Shikenan zamana ya kare nasan korata zasuyi"Zuciyar ta ta sanar da ita. "K'araso ciki kinji". Abba ya fad'a yana k'are mata kallo, atake yaji shima ta kwanta masa, lalle ko ba Hajja ba shima zaeso a basu ita, amma bazae tauye mata hakk'i ba dole suji ta bakinta. STORY CONTINUES BELOW  Tunda Kawu ya fara bayani ta sunkuyar da kanta tana jin wani iri, hawaye ne ya shiga sauka daka idon ta, bata son barin su musamman ma Rahmata da suka shak'u sosae, kukan ta ne ya kuma tsananta jin Hajja ta karb'e zancen tana had'a ta da Allah. Ita wace da zaa zauna ana mata wannan magiyar sai kace wadda take zaune gidan ubanta? Ko ba komae mutanen sun mata karamci be kamata suzo da buk'ata tak'i biya musu ba, ko da kuwa tafiyar ta tana nufin yankewar numfashin ta kenan. "Hajja gaskia a kyale yarinyar nan kar mu shiga hakk'in ta". A cewar Abba yana kallon Hajja. Hajja kamar ta kurma ihu haka take ji, dabara ce ta fado mata, a take ta rik'e kirjinta ta shiga jan numfashi, dama chan tana da Asthma, a rud'e suka yi kanta, ganin haka yasa Aman mik'ewa da sauri ta isa gareta, tallefe mata kai tayi, ta shiga shafa mata wajen a hankali tana karanto addu'oi, kakam Hajjan ta damk'e hannun ta, a hankali ta furta; "Zan bisu kawu, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi". A tak'e Hajja ta bud'e ido sae gata zaune dirshan tama manta da wata Asthma, dama chan Abba yayi tunanin pretending tayi, girgiza kai kawae yayi ya fice daka d'aki. ☆☆ A hankali yake driving d'in har ya isa Garin na Kibiya, sae da ya fara biyawa in da yake tunanin xae ga Habu, baya wajen sae wasu abokanan sa zaune suna musu, hannu ya mik'a musu; "Habu fa?"Ya tambaya yana ko'karin zama shima. "Habu yana filin Ball, suna da match da yan Rano united gobe, yana chan suna sake rehearsal" "Owk zuwa yaushe ne kake ganin zae gama?"Ya sake tambaya. "Eh kila sae magrib haka nasan, amma ka tab'o shi a waya mana." "Ai bani da ma number tasa wlhi, ko zaka bani?" "Owk tam".Karanto masa digits en Yayi yasa a wayar sa, sae daya kira sau uka ba'a d'aga ba, mik'ewa yayi bayan sun masa kwatancen Filin ball d'in ya nufi chan don baya son b'ata lokaci, yau yake son zuwa ya d'auki Aman ya wuce gida da ita. Daka nesa ya hango Habu yana motsa k'afarsa, k'arasa wa yayi ya dake sa a gadon baya, da sauri Habu ya d'ago sukayi ido hud'u da Affan, "Man! Ina ka shiga kwana biyu?"Habu ya tambaya suna nufar motar Affan d'in, "Kaji mun d'an rainin hankali, after All jiranka danaayi ranar baka xo ba, har nayi giving up na zazzagaya da kaina, ban samu k'auyen ba, on may way kuma aka kira ni Mummy ba lafia, dole na hak'ura na koma, And u hav the gut to blame mie huh?" "Ya salam Allah ya sauwak'e, Bansan haka bane ai wlhi,nima ranar Maigida ne ya sani a gaba muka tafi gona, i couldnt get the chance na fad'a maka kuma. Anyway i think I hav found her" Cikin murna Affan ya rik'e masa hannu "Da gaske kake dan Allah, wow Am very happy wlhi" "Allah Am serious, sae dae kawae muje tare ka k'ara confirming da kanka" "Right Away, shiga mota kawae pls" Kallon kansa Habu yayi sannan ya maida kallon sa kan Affan, "A hakan zamu tafi, look at mie fa, ka manta ina da babe a gidan ko?" "Mtsw kaji matsalar ka wlhi, to mene? Ni dan Allah bnsan kuma delay, We are talking about my Life fa, and kana son batan time" "Gaskia wlhi sae na chanza zan bika, muje gida nayi wanka nima na fito a mutun, sae muje ai ba guduwa zatayi ba" Badon yaso ba haka ya hak'ura suka tfi gidan su Habun, first time na zuwan sa kenan, cikin d'akin sa ya zauna yana duba time yana tsak'i. Cikin shigar dark Blue shadda ya fito yana saita zaman hular kansa, jawo wani tsumma yayi ya shiga goge takalmin sa, sae da ya gama sannan ya d'auko polish cream ya sami waje ya zauna zae fara polishing takalmin, ai Affan beyi wata wata ba ya fuzge robar yana hararar sa. "Ai wlhi baka isa ba, don iskanci ina jiran ka sae ka batan time?" Daria kawae Habu yake, be taba ganin reaction d'in Affan irin haka ba, infact shi magana ma ba damunsa tayi ba amma ji yanzu sae faman bala'i yake masa kamar wani d'ansa. Zura takalmin yayi suka fita yana b'oye dariyar sa ganin yadda Affan d'in yayi kichin kichin da fuska. ☆☆☆ Rahmata da Nafi kuka kawae suka, ita kanta Aman din idanun ta sun kumburu, ji take kamar tace ta fasa, fitowa waje sukayi chan baya wajen inda bishiyar Mangoron nan da suka saba zama take, kowacce ran nan babu dad'i, suna nan zaune sae ga Is'hu, yasha dogon wandon sa baggy, k'afar nan cikin safa fara wadda akayi mata faci waje da yawa, rigar jikin sa kanta over size ce amma haka yake jin sa kamar wani gomna, wannan wankan dama irin sa yake yi idan ana wani abu a garin, yasan zaa yi bak'i yan birni shisa shima yake fita da fitarsa. "Yan mata adon gari, in ba ku ba gari, in kunyi yawa gari ya baci". Ya shiga yi musu kirari yana sak'ala glass d'in sa akan karan hanci sa, duk da b'acin ran da suke ciki sae da suka yi murmushi, gaba d'aya shigar tasa sae a hankali, ganin basu ce masa komae ba musamman Nafi data saba tunzuro shi, yasa ya d'an sake duban kansa, komae tsaf tsaf yayi assuring kansa. Haka ya k'araci surutun sa ya tafi ya barsu, wani k'aramin yaro ne yaxo yace suxo ana kiransu, jin haka sun san tafiya ce, aikuwa sae suka rungume juna suka sak'e sabon kuka. "Dama suma su Rahmatan zasu je chan gidan Baffan nasu, akwae wani bikin da zaayi yau na k'awayen Amaren, gashi da har da ita Aman d'in zasu". Gaji ta sanar da Hajja da take gyara mayafi ana shirin tafia. "Ba laifi, sae mu tafi gaba d'aya ai, Ni da Maman yaran sae mubi su Alhaji, su kuma yaran sae Farhan su kaisu chan d'in". "Kai Hajja kika ce sae yamma lik'is zamu tafi". Farida da katse ta tana guntse daria. "Yar nema toh na fasa ai, yanzu nake son tafia sae a hanani". Bata k'ara magana ba taja bakin ta tayi shiru tana jinjina rigima irin ta Hajja. Wani bakin ciki ne ya kama Farhan jin abinda Hajja tace; "Mu kaisu biki mu jira har ta gama sae mu tawo gida fa kika ce? Haba sae kace wasu yara?" "Yo kace bazaka ba mana, shine zan san ka iya wulakanci". Abba ne ya shiga tsakani yayi ma Farhan fad'a, Na'eem kamar yayi dariya yana ta satar kallon su Nafi, Da suka takure waje d'aya, Baya suka shiga dukka su hud'un harda Farida, Hajja kuma da Mama suka shiga motar Abba, taf aka cika musu boot da kayan arzik'i, ribas Farhan yayi don shine zae yi gaba, yana k'ok'arin fita daka k'auyen Affan yana sak'o motar sa, wani irin clashin sukayi wanda saura kiris su bugi juna, tsaki Farhan yayi ya k'ara ma motar sa wuta tare da tada kura. "Wanchan kuma waye haka?"Habu ya tambaya yana kallon titin yadda ya bud'e da k'ura. "Waya sani ne, irin dai mara sa hankalin nan ne inaga". Affan ya bashi amsa. K'arasawa sukayi suka sami waje sukayi parking, Kawu dake tsaye suka nufa, gaida shi sukayi sannan ya umarce su da su shigo d'akin zaure. "Innalillahi,an sami sab'ani wlhi". shine abinda Kawu yace bayan ya gama jin ta bakin Affan. " Yanzun nan suka wuce zuwa birni" labarin abun da ya faru Kawu ya basu, Affan kamar ya fashe da kuka don bak'in ciki. " Toh ko zamu iya sanin in da suka tafi?"Habu ya tambaya. Shiru kawu yayi don gaskia be san su waye su ba, bazae fad'a musu kai tsaye ba. girgiza kai kawae yayi alamun be sani ba. "Ni da ba zuwa birni nake ba, ya zaai na sani?, sae dae ku dawo nan da sati uku haka, in d'an uwana yazo daka birni sae yayi muku kwatance." Jiki ba k'wari suka fito, a bakin hanya ya ajiye Habu yaja motar sa sae kano.

0 Comments