ALQAWARI BAYAN RAI CHAPTER 4

ALQAWARI BAYAN RAI CHAPTER 4
A bakin Rafi suke ita da Rahmata da Nafi, dutsuna ne k'ananu irin masu sumul sumul a hannun ta tana jefa su ciki rafin. Yanayin garin yana mata dad'i sosae. Tunani take Ko ya Mummy da Affan suka shiga lokacin da suka neme ta, har gobe bazata manta Alherinsu gareta ba. Yanayin Kallon Da Affan yake mata da irin kalamen da ya fad'a mata in ta tuno yakan sa ta manta halin da take ciki na wasu yan lokuta. Firgigit ta dawo daka duniyar Tunanin da take bayan jin hannuwan Rahma kan kafad'arta. "Me kike Tunanin ne Yar uwa? Naga farin ciki lullub'e akan fuskarki." Murmushin ta ta kara fad'a d'awa, "Ba komai Yar uwa yanayin garin ku kawai ke burgeni." Karaf Nafi dake gafe ta amshe "Kwarankwatsa Tunanin Saurayin ta take, Haba ko Rahmata dubi yadda take murmushi mana." Daria gaba d'aya suka sa. "Gaskia Nafi ke yar sa'ido ce, ni yarinya dani ina na isa saurayi? Umm?. " Aman ta tambaye tana murmushin "Ji mata da wata magana, aradun Allah in a nan garin namu kike da tuni kina da ya'ya kamar biyar Ko Rahmata? Muma da kika ganmu haka karatu ne ya tsayar damu, Baffanmu na birni shi ya hana a mana aure da wuri ai da tuni muna d'akin mu abunmu." "To uwayen Surutu, aikin kenan ko? "Sukaji Muryar Baffa Mainono a kansu, cikin azama suka shiga d'eban ruwa kowacce tana tsoron masifar sa.. Da daddare suka saci jiki sukayi dandali don suna son nuna ma Aman irin kalar Rayuwarsu. Farin ciki sosae tayi don ba k'aramin burgeta abin yayi ba, ashe akwae irin wannan rayuwar me dad'i bata sani ba, gaskia dama zata dauwama A kauyen su Rahmata da bata da sauran damuwa. Tana chan aikin tunani Bata san su Rahmata kowacce tayi wajen Saurayin ta ba. Kamar daka sama taji sallama "Assalamu Alaiki ya kyakkyawa." D'ago idonta tayi don ganin me mata sallama, wani matashin Bafulatani ne, fes dashi cikin yar shararsa Fara k'al da ita, gefen fuskar sa bille ne kwance na fulani. "Wa alaika salam." ta bashi amsa tana gyara zama.. Is'hu kenan d'an gidan Sarki, gaye me k'walisa da gayu kaf kauyen ba wanda ya kaishi, yan mata da yawa sun mato kansa sae dae bashi da time d'insu, a ganinsa shi da ya fita har jihar Sokoto inda yayi secondary d'insa, sannan ya dawo Sa'adatu Rimi yayi NCE d'in sa ai yafi k'arfin yan matan garinsu.. Cikin k'warewa da nasan salon daidai wayewar sa yake karya zancen Soyayya ma Aman, gaba d'aya ma ita dariya ya bata. Zuba kawae yake, yan mata da yawa sunji haushin Aman, Rahmata nachan da nata saurayin Lado aka kai mata rahoto, da azama ta taho don gasgata wa. Zama tayi gefen Aman, aikuwa hira ta koma kanta, farinciki kamar me yau gata ga d'an k'walisa Is'hu. Naira d'ari ya zaro sabuwa kal da ita ya mika ma Rahmata na kamun k'afa. Ba wani bata lokaci ta karbe tana k'ara jaddada masa komae yazo gidan sauk'i. Ko a hanya da suka taho dasu Rahmata sae da suka k'ara jaddada mata kar tayi sake Is'hu babban Yaro ne. Ita gaba d'aya ma yadda yake magana da wani sa turanci shi yafi mata dariya, shi a nasa tunanin ya gama birgeta da turanci be san itama ba iyawa tayi ba.. STORY CONTINUES BELOW  "Rahma kenan, ni da nake akan hanya har ina da lokacin soyayya? Ki tuna ma abinda yake gaba na mana"Ta fad'a tana k'ara d'aga kafarta don har ga Allah tsoron yadda suke ratsa kunya kunya take, shiru garin sae kukan karnuka da shanu. "Wannan ba hujja bace, ki daiyi tunani" "Shikenan zanyi."Ta katse maganar badon ta gamsu ba. Lab'ewa sukayi a jikin wata bishiyar Mangoro saboda hango hasken fitila a k'ofar gidan nasu, ba tantama Kawu ne a zaune. Hantar cikin su ce kawae ke kad'a wa don sunsan kashin su ya bushe. Dal ya dalle su da fitilar yana son gasgata zargin sa. "Kun mak'e ubanku, kunzo nan ko sae nazo na same ku?"Cikin rawar jiki suka karasa gabansa, d'aya bayan d'aya ya sake dalle su. Salati yayi ganin harda bakuwa. "Wato Rahmata don k'wal Ubaku sae da kuka fita ko? Har da jan yarinyar mutane kuna nuna mata ku kun Rik'a ko? Zako kuci ubaku bari Baffan Burni yazo zan sanar dashi komae." Sudae sunyi tsilli tsilli da ido suna jiran saukar kara. Ba wata wata ya shiga rarumo wani kara a gefen sa, ganin yayo kansu yasa suka ranta a na kare sukayi cikin gida suna kyalkyala dariya kasa kasa.. Nafi ta shige kulin su (Bangarensu) su kuma suka k'arasa d'akin gaji, tana jinsu suka shigo suna daria suna kwaikwayon maganar kawu, Aman saboda daria harda rik'e ciki. Murmushi kawai Gaji tayi ta cigaba da jan tasbah. Baiwar Allah😥 (Please include her in Ur prayers). "Gaskia yau naji d'adin fitar nan. Aman tace tana gyara musu wajen kwanciya." "Keko ni?" Rahmata ta bata amsa tana tayata jan zanin gadon. Fad'awa sukayi a tare sannan suka tafa. Hira aka dasa sabuwa murya k'asa k'sa wadda duk akan zancen Is'hu d'an kwalisa ne😝.. Da gari ya waye suna zaune sae ga muryar Kawu ya nufo d'akin gaji, da sauri suka mik'esuka tada sallah, dama wannan shine abun da Rahmata Da Nafi suke in sunsan sunyi laifi.. Ganin suna sallah yasa shi gaida Gaji ya fice yana sababin zae kamasu ne. Kyal kyalewa sukayi da daria bayan ya tafi.. A haka sukai tayin wasan b'uya har ya manta ma.. Sosae Aman take jin d'adin zaman ta a kauyen Mad'achi, Rahmata sam bata barin ta da damuwa, lokaci d'aya ne ma take shiga k'unci in Rahmata ta tafi tallan fura da Nono ko kuma ta tafi makarantar boko, makarantar Allo kuwa dama tare suke tafiya. Bata da matsala da kowa, Halima ce kawae da take mata wani kallo, wannan kuwa be dameta ba sam, ganin cewa dole dama ka samu wanda zae k'ika duk kuwa kirkin ka.. ☆☆ Mutanen Lagos kuwa ana chan, sosae Nana take jin dadin company d'in Farhan sae dae sam tak'i nuna masa, Abun nasu kamar wani fad'a haka suke, in suka had'u sae ya b'ata mata rai amma kuma yana komawa gida zae ta aiko mata da sak'onnin Friendship masu kwantar da zuciya, Sosae take jin d'adin sak'onnin nasa, bata tab'a gwada masa reply ba sae dae duk sanda yayi jinkirin turo mata sae taji ba dadi. Flashing kuwa in ya fara mata sae ya kashe b3 sannan yake kyaleta. Ganin ya gama duk abinda ya kawo shi yasa yayi deciding yaje yayi mata sallama. Shigar English Wear yayi, dogon wando da longsleeve riga kasancewar weather d'in akwae d'an sanyi sanyi. Kin shiga yayi da mota ya dannan mata kira. "Ina waje."Kawae yace ya kashe yana bin wak'ar *Mariah Carey* 'Always_Be_My_Baby.. Cikin shigar Doguwar riga Abaya ta fito,tayi rolling da Red Veil me santsi, Lek'e lek'e take tana neman motar tasa. Chan ta hango shi daka gefe. "Rainin hankali yau kuma achan ya tsaya kenan."Kamar kar ta k'arasa haka taji, amma sam zuciyarta bazata barta ba. Tafiya ta shiga yi har gaban motar tana yatsine fuska ita a lalle an takurata. Ba k'aramin kyau tayi masa ba, gani shigar da tayi wanda be tab'a ganin ta da ita ba.. "Gorgeous." Ya ambata A zuciyarsa. Dan nesa dashi ta ja ta tsaya. "Haba kauyis ki d'an matso mana ko so kike aji miki kalamen soyayar da kike mun kullum." Iyakar k'uluwa ta gama kuluwa, wai itace kauyis. Karasa wa tayi ta bud'e gaban motar ta bar kafafunta ta waje. "Yawwa Yan mata ko kefa, amma da kamar wata ta Gona."Ya fad'a yana dariya kasa kasa irin ta rainin hankali. Dan satar kallonsaa tayi ta gefen ido, Sae da zuciyar ta ta d'an buga ganin irin kyau da yayi. Da sauri ta juya ganin suna kokarin had'a ido. "Hahaha, Woww yau na kama Mighty Nannncy tana satar kallon Handsome Farhan. Woo ni yarinya taga Nose." " Kallon wa? Allah ya kiyaye ni kofar Gate nake kallo naga kamar wani tsaye wajen. Ta bashi amsa tana sake tamke fuska. "Eh Gaskia ne nima naga wani ya wuce ta chan, Umm muga, muga. ya shiga waiwaye alamun neman abu." " Opps kinga ashe ma gashi kusa." ya fad'a yana pointing kansa. "Kaga malam naga abun nakama yaxo da rainin hankali. Ka fad'a abun da ya kawo ka ko na wuce ina da abubuwan yi.." Murmushin ya karayi yasan duk borin kunya ne.. Saita kansa yayi sannan yace "Dama sallaama nazo don ni zan koma in da nafi wayo, don naga kamar ke kinyi parking ma gaba d'aya kin dawo nan, baki damu da kowa ba. Ni kam Ina missing family na sosae." A take taji zaman LAGOS din ya isheta., gashi kuma daka ji magana ya fad'a mata a karshe. "Ok Safe flight Sae anjima."Da sauri ta fice don a lokaci d'aya wani bacin rai yaxo mata. Shima kawae kallon ta yake har ta shiga cikin gida. Tafiyar da yace zae yi ne ko kuma me ya b'ata mata rai haka? He Can't say. Ya dad'e a zaune ganin yana bata ma kansa lokaci yasa shi bawa Gateman sako cikin wata big Nylon leather ya bata sannan ya bar unguwar. Lokaci d'aya transfer Letter na Affan ya fito, abun ka da hanya an dawo dashi kano cikin k'aramar hukumar Kibiya. Shine ya zab'i kudancin kanon don yana sha'awar irin rayuwar da suke.. Babu wani b'ata lokaci ya fara shirye shiryen sa don har ga Allah ya matsu. Daddy kuwa kallon Local yake masa, a ganinsa ga cikin gari mene zaeyi wani da k'auye, cikin ko in kula yasa akae signing komi ya bashi. Lokacin da ya gama shirinsa wani dad'i yake ji kamar ya jawo gobe. Mummy kallon sa kawae take tana mamakin irin simple life d'in Affan, Sam be d'auki duniyar da zafi ba. Da sassafe ya jawo trolly d'insa ya sauko k'asa yana jiran fitowar Mummy. Cikin shigar Alfarma ta sauko, a ransa kawae yake ayyana irin gayu da k'walisar Mummy. "Lalle Affan irin wannan sammako haka?". Ta fad'a tana k'arasowa cikin parlon fuskar ta d'auke da murmushi. Shafa sumar kansa yayi yana daria k'asa k'asa. "Ba haka bane Mummy, Ina kwana?" "Lafia lou Affan ya shirin tafiya?" "Na had'a komi nawa dama jiran fitowar ki nake, nasan be zama lalle mu had'u da Daddy ba cox naji dawowar sa late." "Eh gaskia don barci yake ma ynxu haka, Sae kayi Breakfast kafin ka wuce." Kitchen ta wuce ta barshi zaune tsakiyar Parlo yana k'ok'arin had'a cornflakes. Har waje ta rakashi ya shiga mota in da driver zae kaishi kano line ya hau mota. Yana zuwa mota ta kusa cika saura mutum d'aya, gaba ya shiga gefen wani matashi cinyar sa d'auke da jaka, gaisa wa sukayi sannan kowa yaja bakinsa yayi shiru, hira ake da mai motar wanda yawanci akan siyarsa ne Kwata kwata tafiyar bata fi minti 50 ba wanda a ak'a'ida Affan zae iya zuwa kullum ya dawo amma sam ya'ki ya zab'i zaman chan. "In anxo kwanar ruwa zan sauka". Affan yace yana sake duba address d'in d'an majalisar garin da Daddy ya bashi wanda yayi saving a cikin draft. A tare suka sauka da wannan na gefen nasa, har ya wuce shi yana tsaye,yayi saurin tsaidashi "Emm Abokina Tambaya nake". D'aga mashi kai yayi sannan ya cigaba "Gidan d'an majalisar garin nake nema". "Ok hanya d'aya mukai ma. Muje ko". A tare suka jera k'ofar kudu in da gidan d'an majalisar yake. Unguwa ce babba irin estate d'in nan, gidan d'an majalisar ya fita daban don haka suna fara hango gidajen ya gane. Har cikin gidan matashin saurayin ya raka shi "A'a Habu saukar yaushe?" Matar d'an majalisar ta tambaya Kafin ya bata amsa taga Affan biye dashi. Gaida da sukayi sannan habu yayi mata bayanin Affan. A take ta gane shine wanda honourable ya kira ta d'azu yace zae zo. Tarbar girma akayi masa aka bashi masauki me kyau ya huta, in da gobe zae shiga secretaria yayi reporting.. ☆☆☆ Washegarin tafiyar Affan sae ga Nana ta dawo, kallon ta Mummy kawae take, yarinya kamar me aljanu, haka ta shigo tana wani basarwa, ko cikanki Mummy bata ce mata ba. "Sannu da gida Ma". "Yawwa sannu, sae yau kika ga damar dawowa kenan". "M sorry". Shine kawai abinda tace taja trolly d'inta ta wuce ciki. "M Sorry?"Mummy ta nanata kamar me bitar kalmar, Yau Nana ce da bata hakuri, lalle ne abun da mamaki. Tabe baki tayi tanaa addu'ar Allah ya shirye ta. Kan gado ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya, takalmi ne me shegen tsini k'afarta amma bata damu da cire shi ba, tun da suka rabu da Farhan a lagos taji komae yayi mata zafi, gashi d'an text da flashing da yake mata ma shiru, gaba d'aya sae taji taa takura da rashin jinsa, sae dae girman kanta ya hana ta kira shi. Tsaki taja a karo na biyu tana sake gyaara kwanciyar ta.. Alamun shigowar text taji a wayarta wanda yasa tayi saurin jawo wayar GT-Bank ta gani rubuce akan screen d'in wayar, dogon tsaki taja ta kifa kanta tana jin wani iri. "Wato me makon ki tashi ki cire kayanki shine kika kwanta haka da takalmi ko? Wai ni Nana sae yaushe zakiyi hankali ne"? Muryar Mummy ta karad'e d'akin. Mik'ewa tayi jiki ba lak'a ta fara ko'karin cire takalmin k'afarta. Kwafa Mummy tayi ta ajiye mata abinci akan bed side drawer ta juya ta fice. ( *Umm tsakanin d'a da mahaifa kenan, no matter how angry iyaye suke basu tab'a kin kulawa da yayansu. Ya allah ka bamu ikon yima iyayen mu biyayya da kyautata musu*). Sae data gama yangar ta,ta shirya cikin doguwar riga me duwatso. Hango haske akan wayar ta tayi alamun kira ne ko text, da azama ta k'arasa bakin gadon tana k'arasa wa wayar na katse wa, wani k'ululum takaici ne ya mamaye ta ganin sunan Farhan da tayi saving da *Mr Naci*, zama tayi tana jiran wani kiran nasa, shiru shiru ba alamun zae kara kira, jiki a sab'ule ta zame ta zauna zuciyar nan a cunkushe. Wasa wasa kwanan Farhan Uku be kara kiran Nana ba, gashi bada wani abun yayi ba, abubuwa ne suka sha kansa da yawa, ya shiga busy sosae so bashi da enough time na making pleasure calls sae dae abinda ya shafi bussiness. A tare suka fito da Na'eem daka conference hall, kowannen su a gajiye yake, Parking lot suka wuce in da Farhan ya shiga yaja suka wuce gida.. Sae daya huta ya sake duba wayar sa ko Allah zae sa yaga Nana ta kira shi ko da text ne. Jinjina irin halin ta yake, sam bazaka gane abinda tasa gaba ba. Fasa kiran nata yayi shima ya fice zuwa part d'in Hajja. *Mad'achi Rano* "Niko Rahmata ina sha'awar binki cikin gari wallahi". "Kai anya kuwa zaki iya? Akwae wahala fa, ki bari kawae ranar da kasuwar Rano take ci sae muje muci kasuwa". Cikin gamsuwa Aman ta yarda tana Allah Allah ranar kasuwar ta zagayo.. Ranar Jum'a shine ranar da kasuwar Rano take ci, Tun da sanyin safiya mutane suke fara shigowa daka k'auyuka cikin shiga ta Alfarma don cin kasuwa, Rumfuna birjik kowa yana ko'karin kasa kayan sa, duk wani abu da mutum yake nema zae sami shi ranar, b'angaren yan kayan miya daban, masu kayan abinci irin su shinkafa, maiwa, Accha, gero da sauransu suma bangare daban. In ka koma ban garen su barkono, citta kanumfari, kuka, kubewa gasu nan. Yan fulani da suke shigowa da Fura da Nono daka kauyuka irin su Mad'achi, Lausu, Bacha da sauran su suma suna nasu bangaren. In kuma aka koma bangaren Nama (Tsire, balangu, kilishi) Gasu nan birjik😋😋.. Kai abin dai sae wanda ya gani. Sannan wani abu da zae kara burgeka da garin shine, ranar jumma'ah duk wani gida da kaje zaka samu anyi Tuwon Shinkafa Miyar Taushe da nama😋, Wasu harda Man Shanu. Wannan al'ada ce tun iyaye da kakanni Abubuwa dae kam bazasu lissafu a wannan d'an page d'in nawa ba. Abun da zance kawae shine duk wadda ta samu dama ya kamata taje taci kasuwar Rano😛😜 (Ni miss xo nace hafsatu tana advertising garinsu😏... So annoying) A k'ofar gida Is'hu ya faka Machince d'insa suka fito, Rahmata ce ta hau tsakiya cikin shigar fulani, sae Aman ta hau bayanta ita cikin shigar tasu har da d'ige d'ige a fuskar ta. Sam Is'hu ba haka yaso ba, yaso Aman ce a tsakiya amma ba halin magana. Kasuwa ta cika ta batse mutane kowa yana harkar gabansa, Gefe suka samu suka ajiye k'waryar Su don tun a hanya Is'hu yayi musu juye ya basu kud'in. Cikin kasuwa suka kutsa suna kallon yadda kasuwa take ci gwanin ban sha'awa. Duk in da suka gifta sae an kalle su ganin irin kyau da Allah ya basu. Dukkansu ba baya ba sae dae kowacce da yanayin kyawun da Allah ya bata. Yamma lik'is sannan suka gama yawon su cikin kasuwar. Abubuwa da yawa suka siya suna ta murna.+ Gidan yayar Is'hun ya kaisu suka gaisa da matar, sannan suka d'au hanyar komawa gida. A d'aki suka baje suna kallon abubuwan da suka siyo, sosae abun yake birge Aman, sae murmushi take k'asa k'asa. Cikin dare barci ya k'auracewa idon ta, abubuwa da yawa sun faru a rayuwarta wanda bazasu misaltu ba, farkon rayuwar ta a gidan Abby, gidan Hajiya Batool, Zuwan ta Nigeria da fuskar Farhan wanda bazata manta ba. Juyi tayi tana tuno envelope d'in da Ya Muhassin ya bata ta manta ta a gidan su Affan. Fuskar mahaifin ta dake jikin hoton ne ke mata yawo a k'wak'walwa. Hoton shine kad'ae hope d'inta na neman mahaifinta amma ina, ta hak'ura har zuwa lokacin da zasu gaji da zama da ita suma, duk tunanin ta bata tab'a kawo haka kano take da girma ba, ina ma zata fara neman wanda bae san ma tana existing ba, Ya Allah. Haka tayi ta juyi har aka kira sallar asubah bata samu ta runtsa ba. Mik'ewa tayi ta tashi Rahmata sannan ta fice don yin Alwala. ☆☆☆ Zaman Affan ba k'aramin dad'i yake masa ba, duk wani arrangement ya gama making, monday zaeyi resuming duty a wata Government Secondary School. Suna waya da Mummy tana k'ara k'arfafa masa gwiwa ☆☆ Cikin shigar Kayan NYSC ya fito, kayan sun karb'e shi sosae kamar don shi dama aka yi su, Habu ya tarar yana ko'karin yi masa knocking, musabiha sukayi sannan suka fita suna taba hira har suka k'arasa Makarantar. Daidai lokacin ana Assembly hakan ya bawa principal damar introducing Nasa, ihu da tafi kawae ake musamman ma yanmatan sun ga handsome, wani irin feeling ke shigar sa ganin irin warm welcoming da ya samu from both teachers da students d'in. Stage aka bashi ya hau don introducing kansa, For the first time ya d'anji tsoro kasancewar yana da *stage fright* Amma ganin irin nutsuwar da students d'in sukayi ya sashi dakewa ya fara magana. Cikin kwarewa da harshen turanci yayi introducing kansa. Malam come see yadda yara ke ihu, bayan komi ya natsa aka rufe assembly, Teachers suka wuce StaffRoom, Students suka wuce Classes nasu ana maida zancen sabon malamin. ☆☆ Duk irin dakewar zuciyar Nana Boss sae ta zama wani iri, ba wannan ajin ba jin kai, tunanin ta d'aya me yake damunta? Sam ta kasa sukuni amma sae dae ta kasa yarda da abinda zuciyar ta take fad'a mata akan Farhan. K'asa ta sauko ta sami Mummy a kitchen tana yankan Carrot da Green Beans, Saman Fridge ta samu ta haye ta mika hannu alamun Mummy ta bata Piler d'in hannun ta, mamaki kwance fuskar Mummy da ma duk masu aikin dake cikin kitchen d'in, samun kanta tayi da sakin murmushi tana addu'ar Allah yasa Addu'ar tace Allah ya Amsa, sakin mata tayi ta koma gfe tana kallon yadda take aikin cikin yanga. Sae data d'au wajen 30minute sannan ta gama. A ranar duk aikin kitchen d'in da ita akayi sae dae bata ce ma kowa uffan ba. Zaune take a bakin gado tana drying kanta da Hand dryer, jin an murza handle d'in k'ofar yasa ta mayar da hankalin ta don gani me shigowa. Mummy ce ta shigo fuskar nan tata d'auke da murmushi don gaskia Nana ta faranta mata rai yau sosae. STORY CONTINUES BELOW  "Sannu Mummy". "Yawwa sannu Nana, ana aikin cire kan ne? "A ah Mummy ina d'an gyra sa ne." "Owk tom kawo na k'arasa miki". Ba musu ta mik'a mata Comb ta jiye dryer din. Zama Mummy tayi sosae ta Kwantar da k'afarta, hakan ya bawa Nana damar d'ora kanta akan k'afar Mummy, a hankali ta shiga jan gashin suna tab'a hira sama sama. Sae data gama gyara mata kan sannan ta bar d'akin tana tunanin abubuwa da yawa. Har cikin zuciyarta taji dad'in yadda Mummy ta bata time nata sosae, atleast ta rage mata tunanin dake damun zuciarta. Da daddare ma d'akin Mummyn ta tafi, hira sukayi sosae sae wajen sha d'aya ta baro d'akin tana addu'ar Allah yasa Farhan ya mata text. Missed calls nasa ta gani guda uku, cikin tashin hankali ta shiga dialing number nashi for the first time in her life da zata kirashi. "The User U r Calling Is busy now, please try again later". Shine abunda baturiyar Mtn take fad'a mata. Tsaki tayi ta ajiye wayar a gefe tana jiran kiransa don tasan yayi activating Call waiting so zaega missed call nata. Shiru shiru kamar an shuka dusa, ba kiran Farhan ba dalilinsa. Haka ta k'araci zaman jiranta ta hak'ura tae barci cikin kunchi. Adaidai lokacin kuwa Na'eem ne keta faman waya da budurwarsa a wayar Farhan. "Gaskia Man ka rainan wayo, ta wayar tawa kake Lurv d'in naka? Shiiisshh yayi masa alamun bayason Babe d'in tasa taji, ganin wayar tasa bata k'are bace yasa Farhan jawo computer d'insa ya shiga aiki. "Blow mie A kiss Baby". "Muahhhh". Tae masa daka d'ayan side d'in. "Ummm Yummy, thanks bby, Sweetdreams of mie, Lurv U, Bye". "Bye". Ta fad'a sukayi hanging a tare. "Mtsw, kaifa mugun d'an air ne, a gabana kake wani Muaah da lurv u ko mene". Kyal kyalewa Na'eem yayi da daria. "Lalle ma bruh sae kace wani d'an 10th century, ya kake abu kamar baka waye ba?"1 "Eh naji ban waye ba bani wayata malam". "Allah ya baka hak'uri, Credit d'ina ne ya k'are kuma na kasa saya ta bank shisa, by the way ma an kira ka ina waye, ko wata wace? Emm bari naga". Yana ko'karin danna wayar. Fizgewa Farhan yayi ya fice zuwa Parlor yana tsaki, Daria Na'eem yayi ya wuce toilet don watsa ruwa. Ganin Mighty Nancy, sunan da ya mata saving yasa shi sake kallon wayar. "Is this for real? Nana ta kirani? Lalle za'ai ruwa da soyayyen kifi". Har ya fara dialing number nata back yaga past 1 yayi saurin katsewa don yasan tayi barci. ☆☆ Asuba nayi Nana ta mik'e don dama ba wani dadin barcin take ji ba. Duk irin abun ta bata wasa da sallah, akwae himma wajen sallah. ( _Never Judge mutum by appearance, bamu san meke tsakanin sa da mahalliccin sa ba_. Allah yasa mu dace). Wayarta ta fara jawowa a tunanin tazata ga missed call d'in Farhan, ganin babu yasa ta ajiye wayar a kasalance ta shiga toilet. Wajen 7:30 ta sauko k'asa, gidan shiru ba wanda ya tashi. Zama tayi ta shiga operating wayarta zuciyarta ba dadi, ta riga ta gama admitting ma kanta son Farhan take. Tsoron ta d'aya Allah yasa bada budurwar sa jia yake waya ba. Wani tausayin kanta ne ya kamata. Ganin zaman ya isheta yasa ta fad'a kitchen ta shiga had'a breakfast me rai da lafiya wanda take koya a page d'in Sheema's kitchen.2 K'amshi ne ya fara tarar hancin Mummy, da mamaki tabi hanyar k'amshin har kitchen, Nana ce tsaye tana ko'karin bud'e oven k'amshin grilled chicken da yasha kayan had'i ya sake kaiwa hancin Mummy bakunta. "Me zan gani"? Mummy ta tambaya With a wide Open Mouth. "Ina kwana Mummy"? "Lafia lou Nana, Kece a kitchen da safe haka"? "Nice Mummy, Kije parlo ki zauna yau nice zanyi serving d'inki." Ba musu Mummy ta juya parlor tana maida Salivar don k'amshin kam was beyond. Sae da sukaci sukayi nak sannan suka shiga hirar duniya wanda duk a cikin hikima Mummy take k'ara yi mata nasiha, da koya mata dabarun zaman duniya. Ringing wayar ta ta farayi, ai har wajen tuntub'e ta kusa yi tana tsoron karta katse. "Hi". Tace bayan ta kara wayar kunnenta ta nufi sama. "Hello Yan mata, kin tashi lafia"? "Lafia lou". Ta fad'a sounding so delighted jin muryar sa. Hira suka yi wanda ya mantar da ita b'acin ran da take ciki. So take ta tambaye sa ta kira jia taji busy amma sam bata da wannan bakin. Samun kanta tayi da tambayar sa yaushe zaka shigo bayan ta fad'a masa ta dawo daka lagos. "Huh, Yau ni ake son gani kuma? Lalle na cire tuta, Mighty Nana tana son gani na, ok bari naga zuwa yamma in na fto daka office." Kunya ta d'anji sannan sukayi sallama. Farin ciki sosae take bayan ta dawo wajen Mummy kasa controlling kanta tayi. "Nana meke damunki? Through out da kika dawo U are acting strange". Shiru tayi tana tunani me zata cema Mummy. "Common dont be shy, afterall am Ur mother so baki da kamata. Feel free kinji." A hankali ta bawa Mummy labarin had'uwar su da Farhan har zuwa yanzu da sukayi waya, abu d'aya ta b'oye mata na son da take masa. "Dama ita rayuwa duk abinda kake ganin kafi karfi to Wlhi shine yake zuwa yafi k'arfin ka, shisa kullum nake kara nuna maki illar wulakanta mutane, naji dadi da kika gani kuskurenki". Nasiha Mummy tayi mata sosae. Da yamma Farhan yaxo, hira suka yi sosae sannan ya tafi yana mamakin sudden change na Nana. Safiya ce me cike da ni'ima, iska ce tsaftacacciya irin ta k'auye me dad'in shak'a kasancewar babu wasu cunkoso ko ababen hawa, ranar garin kawae zaka kalla kasan cewa sanyi yana gaf da bak'untarsu.+ Aman ce ta fito tana gyara d'aurin zani wanda Rahmata ta koya mata shima dakyar ta koya. Ji tayi an kwashe da daria, da sauri ta waiwayo. Rahmata ce da Nafi tsaye suna mata dariya. Nafi ce ta fara tsaida dariyarta sannan tace "Wannan irin d'aura zani haka Aman? Kalli fa ki gani duk yayi bakin kaza". Daria suka kara k'washewa gaba d'aya harda Aman d'in wanda sae a sannan ma ta lura da yadda ta d'aura zanin. Gyara mata sukayi sannan suka d'unguma zuwa babban Garken shanunsu inda yake chan gaba da gidajensu Cikin garken suke k'ara shiga sosae suna tsallake kunya- kunya, kana kallon Aman kasan a tsorace take, Rahmata kallon ta take kawae kamar tayi dariya don ganin irin firgicin da idon Aman ya nuna "Masha Allah , yanxu Rahmata duk wannan shanun naku ne?" Aman ta fad'a lokacin da suka isa wajen Shanun "Haha, Aman kenan, wad'annan shanun ko kaso d'aya cikin shanun da muke dasu basu kai ba, lokacin da kika xo Wada ya riga ya tafi kiwo kudu dasu wanda daf yake da dawowa don kam akalla yayi wajen wata biyu da tafiya. Jinjina kai kawae Aman take ba tare da tace komae ba. K'arasa wa sukayi har gaban Shannun ga karnuka nan sae faman zagaye suke, Pure Madara K'aramin k'anin Rahmata Ya tatso masu cikin k'warya, gefe suka samo kasan wata bishiyar mangoro suka shanye kayansu sannan suka shiga hira gwanin sha'awa. Zagaye suke cikin garken, bishiyoyi ne birjik irin su kanya, magarya, mangoro da sauransu. Ba wani b'ata lokaci Nafi ta d'ane bishiyar Kanya kamar wata yar biri ta shiga kad'o musu. Ihu da murna suke in ta jeho sae ayi rigerigen d'auka, ganin Aman tafi kwasa yasa itama Rahmata ta d'ane bishiyar suka bar Aman a k'asa. "Auw don ni ban iya hawa bishiya bako? Shikenan bari nima kuga." Daria sukayi,ita kuma ta mik'e zuwa bishiyar Magarya, ganin Magaryar k'asa k'asa daidai hannun ta ba wani b'ata lokaci ta saka hannun ta don cirowa, wani ihu ta saka tana kiran sunan Allah jin wasu abubuwa sun soke mata hannu, da sauri Nafi da Rahmata suka diro sukayi wajen ta wanda lokacin har jini ya fara fita. Yarfe hannu kawae take hawaye na fita daka idanun ta. Nafi ce ta duba hannun sannan ta maida kallonta zuwa bishiyar Magaryar take girke a gefe. "La'haula, bishiyar Magarya kika sa hannu Aman? Ai sae da dabara ake cirowa duk k'aya ce jikin ta, sannu". "Kinsan ba sani tayi ba, laifin mune dabamu fad'a mata ba ai, sannu kinji Aman."Rahmata ta bata amsa tana rik'e da hannun Aman d'in Share hawayenta tayi ta kirkiro murmushi ganin yadda suka damu. "Yama daena mun zafin ai, ku wuce muje wajen mangoron chan don ni shi nake son shama". Gaba tayi suka rufa mata baya suna jinjina k'arfinn halin ta don sokewar Bishiyar Magarya ba abu ne me sau'ki ba. STORY CONTINUES BELOW  Sae da suka d'ebi Mangoron sannan suka tafi gida suna d'an tab'a hira sama sama don duk a gajiye suke ga k'afarsu kamar an tono ta daka toka. ☆☆☆ Cikin shigar English wear Affan ya fito yana gyara zaman takalmin sa, k'amshin turaren sa me sanyi ne zae fara yi maka sallama. Sae daya lek'a suka gaisa da Matar Honourable sannan ya fito xuwa makaranta. Yana k'arasawa gate d'in makarantar yaga ana dukan latti, ganin sa yasa kunya ta kama yanmatan da suke da crush kansa. "Sannun Malam yahya". Yace da malamin dake rik'e da bulala sharfad'ed'iya yana zuga ma yayan mutane kamar An aiko shi. "Yawwa sannu Malam Copper". Ko'karin shigewa makarantar yake malam yahya ya tsaida shi. "Malam yau dutyn kane, ga kuma yan makara da yawa ko zaka tayani?" Zaro ido Affan yayi yana kallon students d'in. "A ah Malam yahya daka taimaka ka cigaba don Allah". Principal ne ya k'araso bayan yaji meke faruwa. "Malam Affan ai aikin kane don naga kad'an makara ne shisa na nemi Malam Yahya ya tsaya kafin ka k'araso, tunda ka k'araso sae ka karbi aikinka". Murmushi Malam Yahya yayi ya saki bulalar ya wuce yana daria k'asa k'asa don yaga kamar tsoro a idanun Affan. Kallon d'aliban kawae yake shi be masan ta ina zae fara duka ba, dukan ma wai harda mata wanda baya jin zae tab'a iyawa. Idea ce ta fad'o masa, Paper da Biro ya ciro ya mik'a ma prefect dake a duty. "Ka Rubuta sunan Kowa sae su wuce aji, in an tashi kar wanda ya tafi". Karb'a yayi ya fara rubuta sunan su d'aya bayan d'aya. Lokacin da aka tashi gaba d'ayansu suka had'u a harabar makaranta, malamai da yawa sun tsaya donjin me ya tsaida su sai suce sabon malamin nan ne ya tsaida su. Fitowa yayi bayan ya rufe Office d'in ya Umarce su dasu biyo shi. Babban Waec Hall d'in makarantar suka shiga, kowa ya sami waje ya zauna. Cikin cool voice d'insa ya fara magana. "Inason mutum uku zuwa hud'u su tashi su fad'a mun daliliin da yasa suke makara". Mutum uku daka cika suka bada uzurinsu wanda duk dai maganar bata wuce basa tashi da wuri ne ko kuma aiki ne yake musu yawa da safe. A nutse ya shiga koya musu dabarun da mutum zaeyi amfani wajen ganin ya taimaka ma iyayensa, sannan kuma ya samu yazo makaranta da wuri. Duk kansu sun gamsu kuma sunyi alk'awarin zasu gyara. Washegari kuwa an samu raguwar yan makara sosae don kaso 50 cikin d'ari sun xo akan lokaci. Wannan shine farkon samun cigaban Affan a cikin makarantar. ☆☆ Zaune suke suna hira wanda dukka hirar tasu tsokana ce. Bushewa Farhan yayi da dariya yana kallon ta up and down "Ai kin dade da bani mamaki, wai don kawae nace doguwar riga tana miki kyau sae ki koma sakawa bil hakki da gaskia". Turo baki tayi tana k'are ma kanta kallo, duguwar rigace wadda akayi ta da yadin kimono, black and red, ba k'aramin kyau tayi cikin kayan ba sae dae bata jin dadin sasu don ba wani sabawa tayi ba. "One-Zero kaci wasa, bazan ce komi ba amma ka jira nawa move d'in" " Yarinya baki da wani bakin magana don na gama gano komae, anga handsome guy an wani makal'e masa toh bana so akae kasuwa". Sosae maganar ta bata daria, aikuwa ta shiga yi ba tsaywa, kallonta kawai Farhan yake yadda take daria, murmushi kawae yana jin wani sanyi cikin ransa. Mota ce ta shigo bak'a tasha tint sae wasu motocin biyu dake take mata baya. "Daddy ya dawo". Ta fad'a tana mik'ewa. "Welcome Daddy". "Yawwa Nana, bako kika yi ne" ? "Yes Daddy. Wani friend d'ina ne." "Ja'ira Kin ma fad'i gaskia". Dariya sukayi gaba d'aya adaidai lokacin da Farhan ya k'araso. Tsugunawa yayi har k'asa ya gaida Daddy sae dae zuciyar sa tana tuno masa ina yasan fuskar sa? Kasa tunowa yayi sae kawae ya basar. Bayan sun koma wajen zaman su ne ya kalli Nana yace; "Niko kamar nasan Daddy a wani waje amma na kasa tunowa". "Ba mamaki ka sanshi d'in ai, kasan yan siyasa basa b'uya." "Exactly. Ina ganin shi naji na tab'a ganin sa." Hira suka cigaba da yi, sae da aka fara kiraye kirayen sallar magrib sannan yayi mata sallama ya tafi. Wani tsalle tayi akan gado sae da bayan ta ya amsa. "OMG, Am In Lurv". "U r in mene"? Muryar Mummy dake shigowa d'akin ta katse ta. Da gudu ta k'arasa ta rungume Mummyn tana sunne kanta a chest d'inta. Tapping bayanta Mummy tayi "Lalle Yarinya ta ta girma, Thanks Almighty Allah, Atleast had'uwar ki dashi Has change U alot. Kin kusa Fita daka Nana Boss ki Koma Nana Baby." K'ank'ame Mummy ta sake yi tana kyal kyala daria kamar ba Nana Boss ba. "Mummy please ki yafe mun duk abinda nayi miki, Am a changed person now, am willing to do duk abinda kike so." "Karku damu Nana, Allah ya yafe mana baki d'aya. Ameen". "Mummy ina tunanin Yarinyar nan, kullum da ita nake kwana a raina wlhi, sam ban kyauta mata ba, ban kyauta ma kaina ba, ina tsoron hakkin ta." "Karki damu ki cigaba da addu'a, In sha Allah zamu ganta." "Thank U Mum". "U are Welcome". _In life ba komi mutum yake nema yake samu ba, duk wani abu da ya sami bawa Kasa zama tayi sae faman juyi take ita kadae a d'aki tana imagining how life will be ita da Mr Naci d'inta.+ "Emm Amma fa be furta yana sonki ba". Wani bangare na xuciar ta ya tunasar da ita. "Amma ai Action speaks louder than Voice". Wani b'angaren xuciar ya k'ara sanar da ita "Watever ma dai ni ina son sa, i dnt bloody care ko baya sona, nasan with time zae soni. Balle ma nasan yana sona". Tayi assuring kanta tana murmushi. A gurguje ta shiga toilet ta d'auro Alwala, tana idar da sallar ta shiga ta watso ruwa sannan ta sauko downstairs. Daddy zaune ya baza ciki yana kallon News a Aljazeera, gefe kuma kayan marmari ne yana kaiwa baka. Daidai wajen k'afarsa Nana ta samu ta zauna , d'agowa yayi yana kallon ta don yasan tare suke zama amma wai yau Nana ce a k'asa shi yana sama. "Sannu da hutawa Daddy". "Yawwa yar gidan Daddy, taso mana ki dawo kusa dani". "A ah barta anan Alhaji "Mummy tayi interupting nasu lokacin Nana har ta mik'e. Cike da mamaki Daddy yake kallon Nana data koma k'asa ta zauna jin maganar Mummy. Bece komi ba ya maida kansa ga Tv yana mamakin sauyin wasu daka cikin halayen Nana. Jin zaman gaba d'aya a takure take, gashi Mind nata sam baya tare dasu. Mik'ewa tayi bayan tayi musu saida safe ta haura sama. Zama tayi ta jawo wayar ta ta shiga kiran layin Farhan. Daidai lokacin yana shigar da wasu documents cikin computer. "Hello Mighty Nana", Ya fad'a bayan ya kara wayar a kunnensa. Daria tayi irin mara sautin nan, hira suka d'an tab'a wanda duk ita ke bada points d'in gashi ita ba wani sabawa tayi ba. "Kinga I will cal u if am tru ina wani urgent aiki ne." Jiki a sanyaye ta amsa masa sannan ta kashe wayar. Haka kawae sae taji ranta ba dad'i, tunani kala kala take, dama shine dalilin da yasa bata tab'a engaging kanta a relationship da wani ba, tana ganin yadda maza ke wula'anta mata and ita kuma bata jin zata iya. Ita mutum ce me son a sota kuma a nuna an damu da ita sosae. Kwancia tai tana playing game d'in Night riders, tana jiran kiran tsammani. Ganin har past 12 be kira ba yasa ta hak'ura ta kashe wayarta ta kwanta tana tunani har barci ya d'auke ta. ☆☆☆ "Subhanallah"ya furta yana k'ok'arin kunna flash light d'in wayarsa. K'arfe biyu da rabi na dare agogon wayarsa ya nuna. "How comes barci ya d'auke ni haka", ya fad'a yana ko'karin mik'ewa. Tattara takardun sa yayi ya kashe system d'in ya fad'a gado. Da safe bayan ya shirya ne ya tuno da kiran da yace zae ma Nana, text message ya turo mata, sannan ya wuce zuwa office. After kamar 30mint da zuwan sa Office sae ga waya daka police station, urgent kira ne wanda yasa dole ya bar aikin gaban sa ya nufi Police station d'in. STORY CONTINUES BELOW  Mutum uku ne maza zaune a bayan kanta, jikinsu sanye da singlet, fuskar nan ta kumbura alamun sun sha kashi wajen yan sandan. Kallo d'aya yayi musu ya gane su. D'aya bayan d'aya ya mika ma officers d'in dake wajen hannu suka gaisa, daka nan wani sergent yayi leading nasa zuwa Office d'in D.P.O "Welcome Mr Kurfi". D.P.O ya fad'a yana nuna masa wajen zama. Zama yayi sannan D.P.O ya fara masa bayani akan kama gangs d'in da suka ji masa cio last time, an kama su da laifuka da yawa. One thing da suka ce shine; "basu san ina yarinyar tayi ba,"and to his optimum suprice shine mace ce ta sasu suyi kidnapping na yarinyar, a very Young girl kuma. " Bamu san dai mene tsakanin su ba, amma zuwa gobe zamu sa a zo mana da suspect d'in don muji gaskiar abun" Girgiza kai kawae Farhan yayi, haushi da mamakin wai mace zata iya sa a wulak'anta yar uwar ta mace akan wani abun duniya, watak'il ma akan saurayine, mtsww. "Ok Sir duk yadda kukayi u let mie kno, dnt take it easy with the girl, ayi punishing nata sosae." "That's our job Mr Farhan, U dnt have to worry". "Ok,Thanks alot sir, i do appreciate." Shaking hannu sukayi sannan Farhan ya fice yana jinjina lamarin.1 ☆☆☆☆ Sallama yayi ma matar honourable akan sae monday zae dawo, direct tasha ya tafi ya hau mota. A daidai bakin titi suka tsaya suka d'auki Rahmata da Nafi wanda zasu cikin kano saida fura sannan su wuce hotoro gidan Baffan birni. Hira su suke ana tafia har suka gangaro kan maganar Aman. "Ohh yanzu Aman tana chan ta gama cika zata fashe, gidan zae mata rashin dadi". Nafi ta fad'a tana gyara zaman k'waryar ta. Jin an ambaci sunan Aman sae da gaban Affan ya d'an buga, hankalin sa ya bayar kachokam wajen hirar tasu. "Eyii kedai bari duk ba dad'i nima nakeji, amma ya zamuyi dole muje mukai sak'on Gaji Gidan Baffan bunni kinga lokaci yana k'ara matsowa". "Haka ne kam". Nafi ta amsa tana jinginar da kanta don sam bata son warin fetir shisa ma bata fiya zuwa waje me nisa ba. Sam be fuskanci inda maganar tasu da dosa ba, sae kawae ya bar maganar akan hirar suce kawae, sae dae kawae sunan daya tsaya masa a rai, tunani barkatai yake har aka xo kano line aka sauke kowa. Ko dayaje gida yayi mamakin samun Nana, be gama mamaki ba sae da yaga yanda suke abu ita da mummy kamar wasu twins, haka ya k'araci kwana biyun sa yana shirin komawa be sami wata gamsasshiyar amsa daka bakin Nana ba akan b'atan Aman. Ranar da zae koma da safe Mummy ta takura sae ya d'au motar sa, beyi musu ba ya shiga motar suna d'aga mishi hannu. A bakin gate ya tsaya mamaki fal xuciar sa ganin yan sanda tsaye suna magana da maigadi. "Yawwa ga Alhaji k'arami nan ya fito kuyi masa magana". Maigadin ya basu amsa yana kallon Affan "Lafia kuwa officer na ganku anan?" "Eh lafia amma ba k'alau ba, munxo ne akan wani case, muna son ganin Nana boss domin zata bimu station don amsa wasu tambayoyi". "Nana kuma Officer me tayi?". "Yes ofcourse ita, wannan duk ba damuwa bane in munje chan zaku ji komae". "Ok, ku shigo ciki na sanar da Mummy". Binsa sukayi shi kuma ya shiga kwala ma Mummy kira. Wajen gware yayi fitowa, cikin tashin hankali take tambayar "Lafia Affan? irin wannan....." Sauran maganar ce ta mak'ale ganin yan sanda a bayan sa Kamar yadda sukayi ma Affan bayani haka sukayi ma Mommy ma, tuni idon Nana ya raina fata. Suna ji suna gani yan sandan suka tisa k'eyarta har cikin motar su, Affan ne ya shiga motar sa tare da Mummy suka rufa musa baya,yana k'ok'arin dialing Number Daddy. Adaidai lokacin kuma Daddy na chan yana shek'e ayar sa, sam beji kiran ba, daka karshe yarinyar tasa, tasa hannu ta kashe wayar ma baki d'aya. Wa'iyazubillah *INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN**3 _Rayuwar nan abun tsoro ce, ni ko ke, ko kai bamu san ranar mutuwar mu ba, muji tsoron Allah abubuwan da muke aikata wa a social media, muna ganin babu me ganin mu, Allah yana kallon mu kuma rak'ib da attid alk'alamin su baya gajiawa wajen rubuta duk abinda muka aikata, muyi ko'karin gyara rayuwarmu ta boye tsakanin mu da mahaliccin mu sae Allah ya gyara mana tsakanin mu da mutane. Halin da muke ciki zina tayi yawa, bamu sani ba cewa hannu, baki, ido duk suna aikata zina, basae ka kai kanka ko kin kai kanki waje domin yin zina ba, a halin yanzu muna rubuta zina da hannuwanmu, muna aikata zina da idanuwanmu ta hanyar kallon batsa_ *Ya Allah ina rok'anka daka karemu da karewar ka, ka kawar da shaid'an da wasi wasin sa a zukatanmu, ka kara mana karfin imani da tsoronka. Ameen*

0 Comments