YAR FARI CHAPTER 16

YAR FARI CHAPTER 16
Kafin ranar suna abubuwa dayawa sunfaru daga ciki harda yunwa data ragu daga garin, sannan kuma ka samuwar ruwan sama domin damina tashiga sosai akullum sai anyi ruwa, tafkuna da kogi sun cikada yawa, Yanzu haka manona harsun fara sasaabe (sharar gona),+ Itakuwa jakadiya wacce tafad'awa sarki zancen haihuwar sarki yasanya anyi mata kyauta taban mamaki, Ranar suna anyi hidima sosai anyi bikn suna kamar wani babban taro masarautu dayawa sun hallara domin tayashi murnar samun karuwa, wajan qannnensa kuwa zaka iya fad'in sunma fi sarkin murna domin kowa ya nuna tasa bajintar akan wannan qaruwada aka samu, Anshari yakai 5days ana bikin suna, Yayinda abubuwa dayawa suka warware wa garin." Mahaifiyarta kuma tana samun kulawa wajan sarki domin ahalin yanxu ya tattara duk wani soyayyarsa yadawo da'ita akan uwargida da yarinyarta, Wannan abu yayi matukar d'aga hankalin mutanen gidan wanda sukeda sanya hannu cikin abubuwanda yake faruwa cikin masarautar, Uwar gida tana kaffa-kaffa dakowa domin kuwa yanzu cikin gidan zata iya fad'in dai-dai ne batasan halinsuba, DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Domin anyi a idonta tagani sai dai tasan wad'anda sukayin basusan cewa tasaniba, dasun sani kuma toda bazasu barta hakaba, itama dasai sun kasheta tunba yanzuba, Shiyasa akullum take taka tsan-tsan da mutanen gidan gabaki d'aya yanzu tasan wannan yarinya ita kad'au za'a nemi ad'auka domin kasancewarta d'iya guda d'aya awajan sarki, tunda tasan sauran nabayan dalilun suna d'aukeda cikine yasanya aka kashesu, Dukda matsananciyar kunyar yarinyar dayake damunta, bai hanata hana kowa d'aukartaba hatta da masu aiki da rainon yarinyar da aka samo, Babarta tad'auko wajanta itace take kulada yarinyar, Kunya kuma kokad'an bata bariba akullum kunyar yarinyar qaruwa yakeyi acikin ranta, Yauma haka Kuka sosai yarinyar takeyi kamar ranta zai fita amma uwar gida taki d'aukanta domin kunya takeji tad'auketa wani yazo ya risketa da yariyar d'auke ahannunta, Sarki wanda dawowarsa kenan daga fada yabiyo domin duba d'iyarsa dasauri yaqarasa domin jin kukanta dayayi ya tsananta, Akwance yasamu yarinyar akan gado yayinda mahaifiyarta takecan gefe zaune tad'an kishin gid'a da tuntun tabawa yarinyar baya, Dukda kasancewar kukan yarinyar yana ta6ata cikin zuciyarta amma kunyarda takeji yasanya bazata iya tashi tad'auketaba, Qarasawa yayi yad'auketa domin yasan halin kunya irinna mahaifiyarta, bazata iya d'aukan taba, kuma dama wannan al'adace wanda hausa fulani suka d'auketa na kunyar y'ay'an fari, Sanda yad'an jijjigeta sannan yazo cinyarta ya ajiyeta yace" kishayarda ita zan dawo zuwa jimawa, Ficewa yayi daga d'akin, Kallon yarinyar tayi sannan tayi saurin kawarda kanta, anutse tafara shayarda yarinyar harta gama sannan tarufe jikinta, Haka sarki yadawo yasamesu yad'auki yarinyar yafice da'ita, Uwar gidace take tafiyada jakadanta abaya, ko'ina zataje ohow, dakatawa tayi daga bakin qofa domin jin irin magan ganunda suke tasowa daga cikin d'akin, hawayene yafara gangarowa cikin fuskarta bata shigaba tajuya tadawo, Ahanya suka had'uda sarki zai dawo matada yarinyar, Kallon yanayinta yayi amma kuma bai furta komaiba saboda mukarrabansu dasuke bayansu, Sanda suka shiga d'aki ya kalleta yana fad'in daga ina kuma kike?" Naga kinfito daga sashin sa'ada, D'agakai tayi tace" eh daga nan nafito, mun kwana biyu bamu had'u bane shiyasa naje dubata banma sametaba, STORY CONTINUES BELOW  Hmm kawai yace" baison tofa komai amma shikam yana kallo matsayinta na babba data daina nemanta idan ita bata nemetaba, tunda yanada labarin cewadata haihu batazo taduba lafiyarta data d'iyarba, waikuwa duk wanda zaka haihuwa yakasa zuwa dibaka ba masoyinka bane, Kallonta yayi yace" kukanda naga alamun kinyi kuma maiy faru?" Bbu abunda yafaru tafad'a bakinta yana rawa, Uhmm kawai yace" domin yasan bahaka bane, ama Amma kuma sanin zurfin ciki irinnata idan yamatsa tafad'a masama saita shiga wani halin, Ajiye yarinyar yayi akan gado sannan yace" kiyi muku addu'a kukwanta domin dare yayi kada kisake fita dai-dai wannan lokacin, Gyadakai tayi yayi mata sallama yafice, data kwanta akan gado yarinyar tana kan gado tagwammaci tayi Shimfid'a takwana aqasa, kamar kullum haka takwana aqasan tabar yarinyar akan gado." Haka rayuwa tacigabada tafiya al'ummar garin Gombe suna cikin kwanciyar hankali, Yayinda sukuma iyalan sarki suke cikin kwanciyar hankali, itakuma uwargida tanada nata farin cikin wanda mijinta yake bata tawani 6arin dakuma taraddadi dakuma fargabar zaman gidan cikin zuciyarta." Gimbiya Asma'u tanata girma gakuma wata iriyar qiba datake zabgawa, Kumatunta ko bread iya kaci, gashi kuma kwata-kwata badata wayo tafi iya 6arna akan komai." Yarinya tana girma sosai yayinda hartakai shekara biyu sai kibanra take narkawa, batada wata matsala, Duk wata hanya da mahaifiyarta zatabi taga takare d'iyarta shi takebi, Alokacinda Gimbiya asma'u tacika 4yrs akan fitada ita cikin gari azazaga da'ita, al'ummar gari suna sonta fiyeda yanda sukeson mahaifinta, Wannan al'amari yayiwa mahaifinta dad'i yayinda yayiwa wasu daga cikin masarautar zafi, domin basu d'auka cewa yarinyar zata samu kar6uwaba, sun d'auka al'ummar gari zasuyi adawa da ita akan cewa anhaifo musu d'iya mace matsayin magajiyar garin, Amma kuma sai sukaga aksanin haka domin irin soyayyarda take samu yafi irin wanda mahaifinta yasamu, Tan y'ar qaramarta amma hattada tsofi dasuke garin girmamata sukeyi, Wannan abu yayiwa al'ummar garin zafi sosai, Wata rana Uwargida ta'aika akirawa sarki yana zaune a fada, baizoba sanda yabari aka tashi sannan yanufi d'akinta donjin dalilin kiranda takeyi masa yana fada dabazata iya jira atashiba, Ga mamakinsa kuka yashiga yasameta tanayi, kamar ranta zai fita tsaida ita yayi akan saita fad'a masa dalilin kukan, Tana kuka tafara fad'in, wata alfarma d'aya nake nema awajanka, Ninasan ba lallai diyata tagirma taredaniba, amma inaso dam Allah kataimaka kakulaminda ita kobayan raina, Inason karaineta da hannunka banso kabada ita awani kokuma wata, Mekike fad'ane tagari?" Sarki ya tambaya hankalinsa yad'an fara tashi, Abunda nake fad'a shine kwannan zan iya rabuwa daku zantafu nabarku, Kada kabari wani abun yasanu yarinyata zanbada rayuwatace akan naceci tata rayuwar, Hajara! Hajara! Kifad'amun wanda yake shiryamun wannan Aika-aika akan iyalina, Saina d'auki mummunan mataki akansa, Sarki yafad'a ransa gana suya, Girgizakai tayi tace" Aa kayi hakuri bazan iya fad'a makaba, domin fad'a maka dai-dai yakeda rasaka sannan kuma murasa d'iyarmu, harda kaina, za'a shafe babinmu munafukai kuma azzalumai sud'auki sarautar qasarnan, wanda al'ummarda aka barmaka hananunka zaku shiga halin ha'ula'i, Kawai kaidai kayi hakuri haka Allah yarubuto maka arayuwarka, STORY CONTINUES BELOW  Ficewa yayi daga d'akin yana huci domin maganarta tata6a masarai sosai, Samun mahaifiyarsa yayi yamata bayanin yanda sukayida uwar gida, aikuwa hankalinta tayatshi sosai, Tana fad'in halliru kasand irin wannan agidan sannan kaki fad'amun?" Wata rana muna za'a wayi gari babumu kenan?" Maza kasanya tsaro yafina baya a girbinta, domin wani abun yasamu jikata bansan wani hali zan shigaba, Yanzu kakiramun uwargida tazonan, aikawa sarki yayi aka kirata, bayan tazo hajiya tasakata agaba akan saita fad'a mata wanda yakeda shirin aikata wannan mugun aikin, tana kuka tace hajiya ki yafeni, amma jin wannan abun bazaiyi muku dad'iba, kawaidai asanya tsaro domin gudun faruwar wani abun nan gaba, Hakan za'ayi domin umarninda nabashima kenan yanzu, Hakan kuwa akayi aka qara matakan tsaro asashin uwargida, yayinda komai yafara tafiya normal itama tafara kwantarda hankalinta, Yanzu tabar yawan koke-koke datakeyi abaya, Alokacinda Gimbiya asma'u takeda 7yrs shekaru biyar, bayan magrib dare yayi sosai, Wata mai yiwa uwargida aiki tsohuwace tukuf tazo yiwa hajiya sallama zata tafi dake ita ba'anan take kwanaba, Miqewa Gimbiya asma'u tayi tana fad'in zanbiki baba kinga kullum nikad'ai nake kwana akan gado itafa aqasa take kwana kuma konayi mata magana bata kulani kawai mutafi taredake, Sunkuidakai wannan tsohowa tayi tace" Allah yataimakeki inani ina tafiya dake?" Bazaki iya kwanan gidanmuba, Zan iya nika kitafi dani, wannan tsoguwa taki firr amma kuma sanda gimbiya tatakura, itakuma uwargida tana jinsu taqi cewa komai, Da gimbiya tamatsa uwar gida tadubi wannan tsohuwa tace kuje kawai, Tsohuwar zatayi magana uwargida tad'aga mata hannu adole tayi shiru, Itakuma tsohuwa tace toh Rankishi dadd'e aito bakya kwanake d'ayaba ga jikata saita tayaki kwana, Naji amma kuam kada kiyarda wani sayan cewa da gimbiya kika tafi domin kare lpyrta idan wani abun yasameta zan d'auki mummunab mataki akai, Allah yahuci zuciyarki in sha Allah babu wanda zai sani kuma babu wani abunda zai faruda ita, Sallama sukayu suka tafi, yarinyar takwanta akan carfet d'in d'akin, itakuma uwar gida kamar yabda tasaba kwana aqasa bazata iya kwanan gadonba yasanya takwanta acan wajan kwanciyarta, Washe garida asubahi sarki yafito domin zuwa yatashi matansa kamar yanda yasaba, tundaga wata qofa yaga dakarunda suke tsaron kofar dukansu azube, yarazana dan haka yaqrasa harzuwa qofar shiga d'akinta dika dakarun azube suke ankakkshesu, Yana shiga d'akin ganin gawar uwargida kawai yayi da d'iyarta acan gefe, Daganan sarki baisake sanin yanda yakeba." Itakuwa Gimbiya asma'u data dawo taga abunda yafaruda mahaifiyarta tayi kuka na tashin hankali domin grman kalmar mahaifiya yawuci wasa, Dukda karancin shekarunda dakuma rashin saboda basuyida mahaifiyartaba bai hanata jin zafin mutuwarba, Mai martaba sanda yayi 2days baisan yanda yakeba kodaya farfad'o 6arin jikinsa d'aya baya amfani, Gashi jininsa yahau yaki saukowa, koda yafarfad'o yatuna yarasa matarsa mafi soyuwa awajansa da d'iyarsa sai jini yasake hawa, Alokacinda wad'anda suka aikata wannan aiki sukasan cewa bada Gimbiya asma'u suka kasheba hankalinsu yatashi domin suna kallon sunyi aikin banza kenan, Itama bata cikin hayyacinta shiyasa bata nemi mahaifintaba sanda akayi bakwaida rasuwa, Ranarda mahaifinta yaganta yasan bata mutuba aikwua ciwonsa yad'anyi sauki, Amma sunzauna sunsha kukan rashin uwargida, Ranarda akayi bakwai d'in mutuwar uwar gidada daddare qanwarsa datazo daga garin aurenta itama aka tashi babu ita tamutu, Itama 6aro-6aro angane kasheta akayi, Aikuwa mahaifiyarsu hajiya qaramar haukane kawai batayiba, Alokaci aka sanya mummunan tsaro cikin fada, Tsaronda aka sanya na gaskene hakan yasa aka d'auko tsawon shekaru batareda anji anske aikta wata 6arnaba, Gimbiya asma'u sai girma takeyi yayinda tun tana shekara 11 ake aikowa neman auranta daga masarautu kala-kala, Amma taqi aminta dahakan, shima kuwa mahaifinta gani dayayi d'iyarsa takanki aminta da auren y'ay'an sara kuna yasanya shima anasa wajan kwata-kwata baya matsanta mata, Domin dama qaramar yarinyace sai-dai idan zaiyi mata auren wuri, Ya tattara duk wani soyayyarsa akanta baida wani burida yawuce yaganta cikin kwanciyar hankali, Yakanyi alfahari idan yaganta yanda take mu'amalada talakawanta takanyu mu'a maladasu kamar itad'in bakowa bace gatada kyauta dakuma sanin yakamata takan yankewa duk wani mai laipy hukunci tuntana yarinyarta kuma hukuncin yayi dai-daida laipynka, Sannan kuma takanyi adalci idan laipyn bakai wanda za'a hukuntashiba." Ahalin yanzu gimbiya asma'u ta gagari way'anda sukeso suga bayanta domun kuwa koda wani abun sukayi 6ata lokacinsu sukeyi bakamata yakeyiva, Idan kuma zancen yimata wani abun kota hanyar had'a bakida wad'anda suke gadon rayuwartane abun baya yiwuwa domin irin sonda suke mata na tsakanida Allah ne." Gimya amsa'u tafita zagaye kamar yanda tasaba, sanda sukazo wani wajan tad'agawa masu mata rakiya hannu tace" kubarni anan, akwai abunda zanyi acan baya nayi mantuwa zan d'auko bazan dad'eba zan dawo, dafarko sunso yimata gardama domin gargad'i dasukasha wajan mahaifinta akan cewa sukasance koda yaushe suna tareda ita, amma kuma ganin yanda ta6ararai yasanyasu cimi umarninta badan sunsoba, Tad'anyi tafiya kad'an tafiyar batayi nisaba tatsaya, hararar bishiyar tayu sannan tace kafito daga 6oyenda kake, Shiru akayi kusan 2minute ba'a kulaba, tsawa tayi tana fad'in nace kafito daga 6oyenda kake kina kirasu yanzu sufitomin dakai, Dasauri yafito jikinsa asanyaye kansa yana qasa, D'an kallonsa tayi sannan tad'auke idanuwa tace dankai nadawonan, inaso kafad'amun menene dalilin dayasa kullum idan zan wuce saika zubamin abu anan hanyar?" Fad'amun nace, angaya maka bana lurada kaine?" Kullum saika zuba abu kafin nawuce kuma ina kallonsa, D'an saurayin wanda kana kallonsa zakaga talauci tattare dashi amma sai dai yanada fuskar salihai kuma kawai nutuwa tattare dashi yanuna kansa cikin tsoro yace nii?" Eh kai qarya zanmaka tafad'a cikin tsawa, Girgizakai yayi Kamar zaiyi kuka yafara magana yana fad'in kinbiya kiyimun raii dan Allah kiyi hakuri, Rufamin baki bbu wani hakurinda zanyi, yanzu akwai wajanda zanje inaso kaje fada kajirani, saika fad'i mai kake barbad'amun akan hanya, Sannan kuma saura kada natardaka awajan, saigaka abunda zanmaka, Juyawa yayi yana waiyayenta itakuma tawuce takoma wajan masu jiranta."Juyawa tayi wajan wad'anda suke jiranta ta iskesu suka tafi, Zagaye suka dungayi suna kallon mutane dakuka yanyinda suke ciki masu neman taimako ayi maua masu bukata abiya musu,+ Ba'ita tadawo fadaba sai wajan yamma liqis, ga mamakinta dai-dai shiga fada taganshi zaune yatakure waje d'aya, Daga cikin rumfarda take ciki take hangoshi, Wani irin tausayinsa ya kamata bata ta6a tunanin cewa zatace yazo kuma yazoba, Tayi tunanin cewa guduwa zaiyi, Umarni tayi musu akan su ajiyeta bbu musu suka ajiyeta tayi umarnida akaira matashi, aikuwa akaje aka kirashi yana zuwa yabube gabanta kansa yana qasa jikinsa sai 6ari yakeyi, Cikin kaisaita iriinna sarauta tafara magana, nayafe maka laipynka amma kuma zanyi maka kashiadi naqarshe banason sake kallonka, banason naqara kallo kazibamin wani abun koma meneneshi jakini?" Gydakai yayi jiki yana rawa, tashi kaje tafad'a, godiya yafaryi muryarsa tana 6ari, itakuma tayi musu umarni akancewa sud'auki runfar sutafi d'auka sukayi suka shige da'ita cikin masarautar." Yana haki ya'isa cikin gidansu, mahaifiyarsa datake bakin murhu tana tuqa tuwa tace" daga ina kake haka?" Sai wani haki kakeyi, Bai iya fad'a mata daga yanda yakeba balle kuma takaiga binciken maiya aikata har kaishi wajan, Idan tasan dalili kuwa lallai zai fuskanci babban hukunci domin aynzu hakanma bai fidda tsammanin tasan mai yayiba sai dai idan hankalinsa baizo wajanba, Babansane yafito yana kallonsa yace d'azu naje wucewa naganka zaune aqofar fada, mai kuma yafaru kake tsaye awajan?" Gabansa yafara luguden duka, cikin tsoro yace" uhmm baba naje wajan wani abokinane, Babansa yasan baida wani aboki acimin fada amma kuma sanin halin yara akowani irin lokaci zasu iya kulla abota yasanya yashashan tarda zancen, Qanwarsa hadiza itace tazo tata6ashi yana juyiwa dama sarai yasan halinta dakomai mutum yayi tasani, Idanuwanta yafi nasu budewa shikam wani lokacin har tsoronta yakeji domin ko'a boye kayi wani abun saita tonoshi, Hakuri yafara bata ganin irin kallonda take masa, Da ihu tajuya wajan mamansu taba tsalle take fad'in yaya yanason,,,,, saurin rufe mata baki yayi acikin kunneta yarad'a mata magana hakan yasa tayi shiru." Tsagaitawa goggo tayida bata labarin sannan tadubi yaya tace jamillu kutashi muyi sallah domin lokacin sallar la'asar yayi, Miqewa sukayi domin gabatarda sallah kowanne ransa cikeda zullumin wannan labari mai kikeda tausayi, Barinma husna wacce hawaye yakeyi mata yawa akan fuskarta, tarsa aciki d'aya mai takeji, tausayin gimbiya asma'u narasa mahaifiya kokuma tausayin sarki wanda yarasa mata biyu da ciki bayan shekaru da rasa haihuwa alokacinda yasamu kuma alokacin Allab yake kar6ansu, Gakuma ciwon rasa salihar mata ga qanwarsa, lallai wannan sarki yaga tashi hankali babba, yaga jarabawa kala-kala, Wannan laabri da akafara bawa husna saita kejin kamar ita tata damuwar bawanu damuwa bane, Dama haka duniya take, duk yanda kake kallon ana jarabtarka dajarabawa wani yafika, duk dukiyarka wani yafika kamar yanda duk talaucinka wani yafika, Idan kan kallon damuwar wasu kana mantawa da kai kanada taka damuwarma, Matsalar wani tasha gaban taka kamar yanda taka tasha gaban nawani, Shiyasa akoda yaushe sannan kuma akowani irin haki katsinci kanka, na kyau kokuma akasin haka saika godewa ubangijinka." STORY CONTINUES BELOW  Sunyi sallah sun idar kowa damuwarsa d'aya yaci gaba dajin labarinda goggo take bayarwa donhaka suka nemi waje suka zauna." Bayan tagakowa ya tattaro hankalinsa gareta tadubi jamilu tace" jamiilu kamar yanda kowa yake tambaya kuma itama husna take taraddai akanmu cewa mu mayune kokuma mu masu kanbun bahakane, abun bahaka yakeba, Muba mayu bane, kuma muba masu kanbun baka bane, haka Allah yayimu da wata irin baiwa wacce shi kad'ai yasan irinta, Amma mutane dayawa basu fahimci hakanba yayinda wasu suke kiranmu da mayu wasu kuma suke kiranmu da masu kambin baka, wasu suce tsabi, Kod'aya bbu acikin wannan lamari, Muhaka Allab yayimu, Kamar yanda kasani ni qanwar kakankace uwa d'aya uba d'aya kuma nice wannan qanwarsa hadizan, Munada dangi dayawa sosai, kuma kusan duka daginmu sunada wannan baiwa d'aid'aikune aciki zaka samesu basuda ita, Mu biyarne acikin iyayenmu, Niceh qarama duka aciki, kuma niceh qarama acikinsu, amma ni lamarina akwai d'aurekai sosai acikinsa, Dominni tawa baiwar daban take, Wani lokacin harsu kansu iyayena sukanji tsorona, saboda wasu abubuw naban mamaki dasuke kallo, Yayana yacigabada bin Gimbiya asma'u bai daddaraba baikumaji kashaidinda tayi masaba, akullum yana binta duk yanda zataje sauda qafa amma sai dai yaqara tsaro bai ta6a barin tagane cewa yana binta, amma sai dai akwai wani dalilin wannan bibiko dayake mata, bayan soyayya dayake mata, Akwai wani sirri, Domin kuwa wannan abuda yake zuba mata ahanyar wucewarta maganine, domin akullum akwai wasu qulle-qulle da'ake binta dashi, aduk lokacinda tazo wucewa kuma har indai tataka wannan abun tofa yakan karye, Ashe yaya bai saniba gimbiya asma'u tasan yana biyeda ita, arana ta biyu da takamashi, sosai tayi masa bara zana akan zata iya sanyawa ad'aureshi nanma yanuna mata kamar yaji amma kuma baijiba domin yaci gaba, Haka tana kallonsa babu yanda ta'iya domin tahakura ta kyaleshi, bazata iya fad'awa mahaifintaba domin tasan saiya d'auki mummunan mataki akai, Itakuma bazatazo ad'auki wani mataki akansaba tunda ba cutarda ita yakeyiba, zata barshi duk lokacinda ya gaji aizai hakura da binta." Daga masarautar kano aka aiko neman auren asma'u amma kuma sarki yahana, mahaifiyarsa data kirashi yanuna mata cewa bayason tayi nisada masarautane domin itan tatafi basusan maikuma zaizo yasake faruda masarautarba, Aikuwa itama tagoyi bayansa lokacinda taji dalilinsa, D'akinsa yakira Gimbiya Asma'u bayan sun d'an ta6a tad'i yace mata, kada taga idan anzo neman auranta yana hanawa dukda yasan itama bawai zata aminta dasu bane, amma yanaso tasani bai bayaso tayi nisada garin, bayaso tayi nisada fada domin bayan ransa baisan mai zai iya faruwba, Sannan kuma shibaice sai miji mai kud'i kokuam sarauta zata auraba idan tasamu wanda takeso duk karamcin arzikinsa zai aura masa ita, tunda sunada dukiya bai kumaga wani abunda zasu baukataba bai kumaga daliin dayasa zaiso dukiya samada farin cikin d'iyarsaba." Hayaniya sukaji daga waje kamar fad'a-fad'a amma don ganin mai yake faruwa sai suka fito suji, Rikicine akeyi awaje sosai domin an ebo damhinmu gabaki daya za'a qonasu wai dama andad'a ana tananin cewa mu mayiune saigashi yanzu kuma Alla ya bayyana, Alokacin nayi fad'a dawata yarinya shine bata kwanaba tamutu, Shinefa danginta suka tada rikici kamar yanda nafad'a muku dama nikam tawa dabanne, bakamar tasauranba, DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Tabbas anyi haka munyi fad'a da ita kuka bata kwanaba, abunda haryanzu naksa ganewa kuma akullum nake tambayar kaina kenan, Nasan mutuwar ta dalilinane amma kuma bansan yaya akayi hakan tafaruba domin banyi wata mumunan Kalma akantaba, bakumayi mata wan abunba, Batareda wani bincikeba tunda ga laipy yafito aka yanke mana tsattsauran hukunci yayinda wasu daga cikinmu za'a d'aureau wasu kisa domin bazasu zaunada mugaye agarinba, Gimbiya asma'uce tanuna rashin amincewata da hukuncin sannan kuma tace kowanne daga cikinmu yakoma gidansa, baza'a yanke hukunci babu daliliba domin mutuwar yarinyar ba kwakkwaran dalili bane, Kowama yana mutuwa sai dai lokacinsa baiyiba, Aikuwa wannan abun yaqarawa gimbiya Asma'u daraja a idanuwanmu dakuma idanun wanda dama basu gamsuda hukuncinda aka yanke manaba, Amma kuma wajan mutanen garifa bbu kwanciyar hankali domin kuwa bamu isa mu fitaba za'afara gaya mana baqaqen maganganu wasu harda Jifa, mundaina shiga mutane mundawo saniyar waye, Intakaice muku munga tijara kala-kala awajan jama'ar gari sanda abun kuma yakwana biyu sannan kuma yalafa sai d'an abunda ba'a rasawa." Wata rana takasance ranar bakin ciki ga gimbiya asma'u domin kuwa nawayi gari babu mahaifinta ankasheshi kamar yanda aka kashe sauran y'an gidan, Bazan iya misalta muku tashin hankakinda jama'ar wannna gari suka shigaba domin rashin shugaba adali irinsa, Gimbiya asma'ukam haukane kawai batayiba tadawo babu uwa babu uba, Sai kakarta wacce take nuna mataso tadakulawa sannan kuma take tsaya mata akan duk wasu matsaltsalunta, Ragamar riqon sarauta yadawo hannunta dukda karancin shekarunta bai hanatayin aiki yanda yakamataba, tana gudanarda mulkinta yanda yakamata, Makiyanta kuwa ta gagaresu domin ahalin yanzu kallonta sukeyi kawai sunrasa dalilin dayasa koda abu sukayi bayayin tasiri ajikinta, Amma kuma ahakanma sunakai domin basu fasaba, Da taimakon Allah da taimakon yayana Gimbiya take samun kariya dako wani irin sharri." Gimbiya asma'u tasaba da ganin yayana akoda yaushe yana binta duk yanda zataje, amma cikin wannan kwanakin kwata-kwata tadaina kallonsa, hakan bakaramin tada mata hankali yayiba, domin tadamu sosai kamar wata mai rashin lpy." Acan gida kuwa shikam ashe angane cewa yanason gimbiya kuma yana bibiyarta shine yashiga tashin hankali domun bayan fad'a har dukansa sanda akayi, Sannan aka sanya masa takunkumi sosai domin aganinsu zai jawo msus bala'ine, suna fad'in abaya ba'a kashesuba amma kuma yanzu shi yana shirin jawo musu abunda zai sanya akashesu, Shikuwa jiyakeyi cikin ransa koda bazai auretaba taimakonta yanzu yafara, duk wani hukunci daya kamata ace iyayensa suyi masa sunyi amma kuma abun babu sauki, Suna cikin wannan lamarin basu gama warwareshiba nikuma naje najawo musu babban abun munyi fad'ada wata tana cemun maiya dukda ta girmeni tadukeni sosai, Amma kuma kafin takaqasa gida tafad'i ta mutu, nan aka nufo gidanmu, Aikuwa suka cillawa gidan wuta sannna kuma akabimu da dika basu tsatayadamu ko'inaba sai fada."Gimbiya asma'u tana zaune cikin d'akinta dayake ita bata cika fita fadaba wannan sakon ya'isa gareta, Fita tayi domin jin abunda yake faruwa, Aikuwa taci karoda qara wacce tarasa yanda zatayi gabaki d'aya da'ita, Idan wancan lokacin tace bbu kwakkwaran shaida wannan lokacin tasan bbu abunda zatayi, dole tad'auki mataki, gashi kuma hankalinta yatashi sosai lokacinda tayi arbada abunda mutanen garin suka aikata, yanda suka d'auki hukunci atafin hannunsu,+ Daidaida qananun yara basu barsu ba cikin dangin sanda sukayi masu duka suma wata qaramar yarinya batada wayo sosai alokacinda aka dukesu harda ita dukan dan haka lokacinda suka iso fada suma kawai takeyi, Aikuwa gimbiya bata kaiga yanke hukunciba yarinyar tarasu, Sosai suka shiga tashin hankali, Itakuma gimbiya ranta ya6aci sosai haryakaiga tafice daga cikin fadar batareda taqara fad'in komaiba, Hakan yad'agawa jama'ar gari hankali sosai domin shirunta yana nufin ranta ya6acu kenan, Natakaice muku gimbiya takai sati bata fito fadaba, alokacin jama'ar gari sukayita dana sanin abunda suka aikata, aikuwa akullum suna cikin masarauta domin bada hakuri, Domin suna tsoron kada fushinta yajawo musu wani abun nadaban, Sanda taga yanda jama'ar gari suka shiga tashin hankali ta dalilin fushinta sannan tasauko, Bata qara tada maganarba yayinda suma mutanen garin basu qara tada magabarba." Dahaka alhalinmu suka samu kwanciyar hankali domin jama'ar gari suna tunanin suta6amu su ta6o fushinta." Ba'a dad'eba jama'ar fada dakuma qannen mahaifinta suka matsa mata akan lallai saita nemi miji tayi aure, domin tadaamu mai tayata riqe muqamin, aikuwa itadai tace musu batada dalilin yin aure yanzu, kuma batada wanda takeso todon haka abata lokaci tukunna, Lokacinda suka bata harya ciki babu wani kwakkwaran amsa, Aikuwa suka nemi d'aya daga cikin y'ay'an sarakunansa akeji dasu anahiyar aurewancin wannan qasa suka aura mata, tayarda auren amma kuma da sharad'i d'aya akan sai dai lallai yabaro garinsa yadawo garin dazama domin dama bashine yarimaba, hakan kuwa akayi domin ya amince kwarai dagaske, anyi shagu lulluka awannan biki kala-kala, d'umbin mutane da sarakuna sun samu halattar wannan aure, yayinda gimbiya tayita kuka domin taso ace mahaifanta suna raye tayi auren, sugani tasan zasu kasance cikin farin ciki, da'ace suna raye ta tabbata ranar zata kasance tafi kowacce rana fari agaresu, Mijinda aka aura mata kwata-kwata baifi kwana ukuba aka kasheshi, bayan yafita zai koma garin mahaifinsa aka bishi hanya aka kasheshi, Kai wannan al'amarifa yadamu jama'ar cikin garin sosai irin kashe-kashe da aka faka dashi kuma cikin masarautar sun tabbata cewa dasanya hannun wani nacikin masarautar akeyin koma menene, domin dama saita d'an gari akanci gari." Bayan faruwar wannan lamari da wata biyar aka sake aura mata d'an gidan sarkin katsina, wanda shima kwanansa biyuda d'aura auren aka kasheshi, Irin lamarinda yayita faruwada mahaifinta shine yake faruwada ita, Aikuwa haka akayitayi domin ahalin yanzu duk masu neman auranta sunja baya, Hartakai yanzu haka ana neman wanda zai auri sarauniya amma anrasa, Yanzu haka anysanya makudan kud'i dukiya duk wanda yayarda ya aureta, Amma shiru kakeji bbu wanda yafito, domin ta auri maza samada biyar babu wanda bai mutuba kuma basa kaiwa 1week ake kashesu wasuma basa had'uwa da'ita, ahanyar garinda zaizo ake kashesshi." Wannan abu yadami jama'ar gari dakuma y'an uwanta, itama kanta dukda kasancewar wad'anda take aura d'in ba sonsu takeyiba amma wannan abu yafi mata ciwo fiyeda kowa domin dazafi ace kullum idan tayi aure miji saiya mutu." STORY CONTINUES BELOW  Wara rana ana zaune cikin fada dogarawa suka shigo dashi, kallonsa takeyi rabonda taganshi harta manta domin ahalin yanzu bama fita takeyiba kwata-kwata, Durkusardashi akayi agabanta akace yafad'i abunda yakawoshi, bai boyeba yashaida cewa yanason aurentane, Wasu daga cikin wajan sunyi murna yayinda wasu sukayita magana akan cewa yana d'an talakawa dangin mayu zaizo neman auran sarauniya, Gimbiya tanemi kyebewa dashi domin taji dalilin dazaisa yazo neman auranta, Yashaida mata sonta yakeyi, amma haka firr taki domin itama tana sonsa kuma tasan qarshen wanda ya aureta mutuwace, amma kuma haka yaqi firrr yaringa roqonta harta amince, Aikuwa ba'a d'auki lokaciba aka d'aura aure, Iyayensa dasukaji kamar zasuyi hauka domin sunsan ta'iya yiwuwa d'ansu bazai kara nanda sati d'aya aduniyaba kenan, Aikuwa duka danginsa aka tattarosu suka dawo cikin fada dazama, aka basu layinsu daban, Tun jama'ar gari suna sanya idanuwa bayan sati d'aya suji mutuwarsa har suka daiba domin kuwa yananan garas bbu wanda yasameshi, Awannan lokaci aka ringa kulla aure tsakanin danginmu dakuma dangin sarauniya, yayinda aka had'a aka zama dangi d'aya, Azaman gimbiya da minibta bbu irin rashib hankali wanda basu ganiba, bbu kuma hanyar daba'a biba don neman rayuwarsu, Ana haka sarauniya tasamu ciki, Murna kuwa hakayita cikin wannan gari, aikuwa tahaifo yaronta mai cikeda lapy, Alokacinda gimbiya tasamu cikin yaronta nabiyu alokacin tanemi barin sarauta, wanda wannan dalili bakowa bane yasanshi sai itada mijinta dakuma zaynab bawa idan kunbiyota cikin labarinta na GIMBIYA ASMA'U, Kowa tunaninsa idan ta'ajiye wannan sarauta zata damkata wa qannen mahaifinta amma saita nemi babban malamin garin tabashi riqon sarautar, Mutanen gari basusiba amma bbau yanda suka 'iya domin sunsa bazatayi haka bbu kwakkwaran daliliba, Bata yarda tafita cikin gidan sarautaba saidai tasa aka gina wata fadar abayan tata wacce batakai tata girmaba, Sannan kuma sukaci gabada zama da mijinta y'an uwanta da y'an uwansa lpy, shine hartayita haifan yaranta, gabaki daya yarnta babu mace duka mazane sannan kuma autansu shine mahaifinka jamilu, Sannan kuma y'an uwana sukayi wani abunda suka rufe bakin kowa ba'a kara nemansuba, Amma kuma anyi yarjejeniya anrubuta an ajiye cikin masarauta, cewa kobayan shakaru d'ari nawa wani daga cikin dangin GIMBIYA ASMA'U ya nemi sarauta tadawo hannunsu abasu batareda tada rikiciba, Nima wata rana cikin dare kawai na tattara kayana nabar garin, domin wasu dalilai masu qarfi wanda sukayita faruwa lokacin komawarmu cikin gidan sarauta, Zanzo ace nabaku labarin wad'annan manyan dalilai dasuka rabani da ahlina nadawo cikinan nake zaune nikad'ai, Amma yin hakan kamar yiwa zaynab bawa shisshigine cikin rubutunta, domun idan kuka bita cikin littafinta na GIMBIYA ASMA'U har labarin bayan barina gida zatayi muku." Ba'abar cikin masarauta hakaba sanda akayita yimus d'auki d'ai-d'ai suma domin jin haushin basu sarauta da akayi, Tabbas anyi maganin wannan wad'anda suke aikin amma kuma bansan wanene yayiba Aqarshe ina cikin wanan gari shekaru saba'inda wasu abubuwa dasuka wuce naji labarin rasuwarsu itada yayana dakuma wasu daga cikin danginmu." Masu karatu zakuji nakatse wanan labari na Gimbiya asma'u yanda yakamata yazo bahaka yazoba, akwai tarin abubuwa dayawa wad'anda yafaru amma ba'a fad'esuba domin wannan sharan fagene kawai cikin labarin, domin sun d'auki kashi 30 cikin d'ari sunga saura 70, Toh 70% cikin wannan labari ba'a fad'eshiba idan kunason cikikekken labarin Gimbiya asma'u, saiku biyoni cikin littafina NA GIMBIYA ASMA'U domin warware tarin tambayoyinda suke cikin zuqatanku." Zan sake jadddaa muku cewa wannan ba komai bane cikin labarin GIMBIYA ASMA'U."1 Tsayawa goggo tayida basu labarin sannan tace" wannan shine abunda zan'iya fad'a muku cikin wannan labari mai cikeda rikid'arwa, Nisawa husna tayi cikin ranta tarin tambayoyine bazata iya 6oyesuba idan ta6oye zata cutu dan haka tace" Amma suwaye suke wannan kisan?" kuma suna rayene wanda suke aikata hakan?" ina nufinn ko akwai jikaninsu ko y'ay'ansu?" Kuma menene dalilin dayasa Gimbiya zata ajiye sarautar iyaye da kakanni, Baki qarasa mana labarin su kakaninmu wad'anda suka haifi yayaba mukaji suma yaya suka qare, Sannan an dad'e ana fad'amun cewa gimbiya asma'u tace" za'a haifi magajiyarta, menene dalilinta na fad'in haka?" Sannan kuma itada kanta tarubuta wasika ta'ajiyemun shekaru samada tamanin dasuka wuce menene dalilinta?" Sannan kuma itada kanta tace wai za'a haifo mata takwara, kuma koda anyi qoqarin sanya sunan suna bzai sanyuba harsai ita mai sunan tafito da sunanta, Menene dalilin dayasa nake kamanni da ita?" Fara bata amsa goggo tayi dacewa husna wanda suke wannan kisan sunada matuqar yawa cikin wannan masarauta, Amma ciki harda sa'ada koh?" Husna ta jefo mata tambaya, Murmushi tayi sannan tace husna kenan, wannan lamari yanada d'aurekai amman kuma zan'iya shaida miki cewa mutane dayawa sunada sanya hannu, amma kuma zancen suna raye banda tabbaci domin kuwa dabazasu barki kikai iwar hakaba, Amma Saboda kauda wannan d'umbim tambayoyi dakuka damuwa datake cinki wata rana kitashi keda kanki keje wajan zaynab bawa na tabbata ita zata zauna ta baki labarin duk wani abunda yake faruwa, Ita zaynab bawan tasanine?" husna tatambaya, hmmm husna kenan marubuciyacefa, kinsan kuwa marubuci duk yanda labari yaje saiya shiga ya nema yarubutashi, Gyadakai husna tayi sannan tace in sha Allah zan jeni, Goggo taci gabada fad'in sannan ajiye sarautama tanada nata babban dalilin, Kakanninku narabu dasu tun ban girma sosaiba, wasu daga ciki banma sansuba, amma labarinsu yana cikin labarin GIMBIYA ASMA'U, zaki samu labarinsu ciki harzuwa lokacin haihuwarki, sannan wannan hasashe gimbiya tayi bawai tasan gaiibu bane, tayi hasashene akan ko bayan ita tasan da yardar Allah, Allah zai kawo mai maye gurbinta, Sannan kuma zancen kamannni haka Allah yayiku kamaninnku d'aya dai-dai da muryarku bata bambamtaba asma'u, komai naku d'aya, Tarubuta wasika ta'ajiye miki bansa dalilintaba, wannanma." Sannan mahaifinku yafad'amun duk y'ay'ansa yarufe muku baiwarda Allah yayi muku acewarsa saikum mallaki hankalin kanku, domin gudun faruwar abunda yafaru abaya yasake faruwa, Amma yanzu yaya kuka gani idan kuna buqatar hakan ku manya guda uku yana iya bud'e muku, Kallonsu husna kawai takeyi bakinta yakasa bud'uwa tafad'i koda kalma dayane, Dakyar ta'iya bud'e bakinta tace."Dakyar husna ta'iya bud'e bakinta cikin sanyin jiki da mutuwar jiki tace" nidai yaya banaso bakuma dan inakin baiwarda Allah yayimunba, Aa sai dai ina kallon lokaci baiyiba, idan lokacin yayi nida kaina zanyi maka magana, Amma bansan ko mamii da buddy ba zaka iyajin ra'ayoyinsu, Murmushi yaya yayi dama yasan hakan zata faru tawajan husna shiyasa baiyima mamakin jin amsartaba, Juyawa yaya yayi wajan mamii yace" kefa mamana?" Shiru tayi tana tunani kawai saitace yaya nikam na amince kabud'emun, Gyadakai yaya yayi sannan yace naji mamanaa amma zanbaki sharad'i domin banason abunda zaizo yatayarmunda tashin hankali anan gaba, Gyadakai mamii tayi sannan tace" na'amince, Juyawa yaya yayi wajan Al'ameen yace" muhammadu kaifa yaya ka am1ince kokuma Aa?" Kan al'ameen yana qasa domin wannan labari yagama rud'ar masada kai jikin yayi mugun sanyi yace" yaya nikam zan jira har lokacinda didi zata amince danata sannan nima na'amince, Toh Allah yakaimu lokacinda raida lpy, Ameen duka suka amsa, Ummii da umma da babysis wani irin mamakine yakamasu dajin wannan labari jikinsu duka yamutu zasufi zatonsa almara aka fad'a musu amma kuma yanayin zancen baiyi kamada qaryaba Abdul shikuwa bai waniyi mamakiba sosai domin dama shikam akullum yana kallon something special and unique tattareda husna, Umma ma taji mamaki amma bacan sosaiba, itadai tasan labarin abaya amma batayi tsammanin haka labarin yakeda rikid'arwa dakuma tashin hankaliba, lallai su husna manyan mutanene sosai, amma kuma ahakan suja boye komai domin neman zaman lpy, Ummii dakyar mamaki ya'iya barinta tabud'e baki tace" husna d'iyata ashe sarauniyace, dama tunba yanzuba husna i see somthing special in you, you're different, Qasa dakai husna tayi batason zancen cewa wai ita sarauniyace, domin itaba sarauniya bace kamannine kad'ai, sannan kuma there's nothing that special attatare da ita, she's normal person just like everyone, ummii taci gabada fad'in, Lallai nayarda ku mutanene masu kykkyawan zuciya, wanda samun irinsu yakanyi wuya, baku d'auki duniya bakin komaiba, Zaman lpy da kwanciyar hankali tafi kuku duk wani kyalkyalinda yake cikin wannan duniyar, kowa burinaa yaga yazama wani mai mulki kokuma sarauta, koda kuwa bai gajetaba amma kunaku burin shine kuka y'an uwanku cikin kwanciyar hankali, kai bama kad'ai y'an uwankuba kowani d'an adam da Allah ya halitta kunason ganinsa cikin farim ciki,+ Kudubafa nida babu abunda yahad'ani daku sai d'umbin zumuncu dakuma zamam natare, sai y'an uwantaka data kasance na addinin musulunci, amma shekaru ashirin kuka d'auka kunason ganina cikin farin ciki, sannan kuma kuka d'auki d'iyarki mafi soyuwa awajanku, mafi soyuwa cikin danginku gabaki d'aya kuka bawa d'ana, nikam mai zance muku cikin wannan duniya?" Allah kad'ai shien zai biyaku abunda kukayi gareni, bazan gushe dayi muki add'ua akan Allah yakara dawo mukuda farin ciki cikin ahlinku gabaki d'aya, Ayau nagani kuma naji nasan cewa Lallai wannan zuri'ace mai cikeda tarihi da d'umbin zumunci, Wanda kowani d'an adam zaiso yakasance d'aya daga cikinta kokuma yahad'a jini da ita, Alhamdulillhi dogiya wajan ubangiji daya kasance nasanku cikin rayuwata." DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Yaya kansa yana qasa yace" wannan va wani abu bane, Allah yashige mana gaba baki d'aya, amma duk wamda yad'auki husna kamar d'iyarsa tacikinsa banajin akwai wani abunda zai neme banyi masaba, kekuma kind'auki husna kamar d'iyarki asma'u dakika haifa cikin cikinki, sannan kuma cikin 12yrs kika ki amincewa dako wace mace tarabi yaronki husna kad'ai kikeso kamar yanda aysha tafad'amun sunyi zancen da Asma'u(babysis), sannan awannan lokacin bakida tabbacin cewa husna tanada aure kokuma akasin haka, tanada rai kokuma akasin haka, cikin ranki kinyi amanna dazaki dawo kisamu d'iyarki, wannan soyayyace ta hakika." STORY CONTINUES BELOW  Sannan yajuya wajan umma wacce kanta yake qasa, ayau tadad'a jin zafin rashin kasancewar husna d'aya daga cikin danginta, Umman faruq yaya yakira sunanta, D'agowa tayi tana dubansa idanuwanta sunyi jaa, yaya yafahimci halinda take ciki take ciki, sannan kuma yasan dolene tashiga wani hali, Juyawa yayi wajan goggo yace" goggo wannan itace mahaifiyar mijin husna na farko faruq, wanda ranar auren Allah yayi masa rasuwa, yaya plz! Husna takatseshi, Owh sorry wanda ya6ata, yaya yayi saurin canja zancen, D'agowa umma tayi tana dubansu tace" Yayan husna kaima ya yarda da abunda husna take fad'a kenan?" Akan cewa bai mutuba 6ata yayi, Nisawa yaya yayi yace" nayarda da abunda husna tafad'a har indai husnace tafad'eshi, sannan kuma tun alokutan baya nake fad'a muku husna bazatayi ta wannna abun batareda daliliba, Girgizakai umma tayi batason yarda da abunda zuciyarta takeson aminta bakuma tason yarda dacewa faruq bai mutuba domin sawa kanta abunda baida tabbas, Amma har indai yaya zasu kasance sunada wannan baiwa da aka fad'eta cikin labarin tabbas zai kasance d'anta yana raye, Amma domin kauda waswasi kawai sai tace abar wannan maganar kawai domin haryau husna bata kawo kwakkwaran daliliba, itadai kawai abunda tashaqu dashine tatashi dashi, zuciyarta takasa aminta cewa tarasashi, Shiru yaya yayi domin baison aja maganar, Husna kuwa hawaye suna kwarara akan idanuwanta tace" shikenan umma idan ayanzu baki gaskataniba wata rana zakice nafad'a miki gaskiya, Tana fad'in haka kuka yaso yaci karfinta, jawota jikinta umma tayi tana kallashi tace" sorry d'iyata ba abunda nake nufiba kenan, Bai kamata muyita tasoda wannan zancenba bayan kinsan nanda 9days kinzama matar wani, Allah yayi miki albarka yabaki zaman lpy agidan mijinki, umma tana wannan maganar zuciyarta tana rawa, bawai dan kuka zatayiba sai dai kawai dan lokacin zuciyarta tayi nauyi da zafi, Cikin wajan babu wanda basu bashi tausayiba, itakuma husna tayi kuff jikin umma, umma tana bubbuga bayanta, tausayin husnane fall cikin ranta, tarasa wani irinso take yiwa umar data kasa manceshi cikin ranta har izuwa yanzu shekaru shidda, Goggo kuwa tazuba musu idanuwa guskarta babu yabi babu fallasa, Kawai sai kallonsu takeyi cikin nasarin wani abun, Yaya shikam cikin mutuwar jiki, yafara maganada fad'in, goggo itace wacce nake fad'a miki husna tun tana qarama awajanta tatashii, Duk,,, d'aga masa hannu umma tayi tana fad'in, kabar wannan zancen kawai abu d'aya nasani shine husna d'iya tace, Murmushi duka sukayi suna mamaki irin wanna soyayya dake tsakanin umma da husna, kowanne babayaba wajan son juna." Shiru yaratsa wajan na y'an mintuna, Goggoce takatse shirunda fad'in jamilu dare yanayi banson kuyi tafiyar dare hakan babu dad'i, kuma ina bukatar kubarsu anan na kwana uku saboda naga yanda yanayin jikinta zai kasance, saiku dawo kud'aukesu, dada hali ita husna da 1week zaku barta amma kuma abun yazo saboda haka itama kwana ukun yayi, Yayane ya amsata da fad'in In sha Allah yanzu zamu tafi kaka, Allah yabata lpy, Ameen duka wajan suka amsa, Sannan suka fara shiri, Shiryawa sukayi dukansu, Kusan 5:30pm suka nufi cikin gari domin d'aukan motocinsu sutafi, Husna da babysis sunso surakasu har cikin garin amma yaya yace" Aa bazasu jeba, bazai yiwu suzosu kuma sudawo sukad'aiba, don haka sukoma kawai, Abdul yaso sud'an ke6e da husna dukda kasancewar bawani magana zasu yiba amma kuma suga juna kawai yake bukata, Domin yasan idan yakoma zaiyi missing d'inta sosai gashi kuma ga dukkan alamu wajan babu service, Balle yakirata, 🙄nikuwa nace abdul koka kiratama mai zaka iya fad'a mata?" STORY CONTINUES BELOW  Sharewa yayi kawai domin kunya bazata barshi yanuna cewa yanason magana da itaba, Haka yana kallonsu sukayi musu rakiya iya bakin ga6ar suka juya." Basu dad'eda komawaba aka kira magrib, sallah sukayi sannan suka zauna suna d'an tad'awa gabaki d'aya babysis tasanya husna jin kunya domin kuwa tahanata cewa komai, Agaban ummii taketa zancen yanda yanayin bikin zai kasance, Itakam husna tana kallon rashin kunyar babysis agaban ummi saita ringa wannan zancen kuma tasan zata sanyata jin kunya, amma takasa fahimtar hakan, Ummi itada kanta tafahimci hakan, dariya kawai tayi musu tanason komaai irinna husna, tanason kunya irin tata, domin mace mai kunya tayine takota ina, Itada abdul d'in dukaba bayaba wajan kunya zataga yanda za'ayi ranar aurenan, itanne kokuma abdul d'inne?" Wani lokuta dayawa idan ummii tazauna tana kallon husna takanga wasu daga cikin halayyarsu iri d'ayace da abdul d'in(female version) dinsa kenan, Sai dai ita tad'an fishi sakewa." Bayan sunyi isha'i basu wani d'auki lokaciba suka kwanta bacci domin yanayin sanyi nawajan." Magani sosai goggo take yiwa ummii domin zan iyace muku ciki kwana d'ayanda sukayi cikin wajan ummii taji gabaki d'aya qafofinta sun sake batajin wani zafi kokuma nauyi, Ga dukkan alamu maganinda akeyi akwai gagarumar nasara aciki." Haka wajan husnama, itama wasu irin ganyayyaki goggo take bata tanaci, kona menene ohow?"🙄 ***** *MADINA* Duk wata damuwar duniya tataru tayiwa abba yawa tako'ina bbu sauki yanzu haka yakira wayan Alhaji yafi abunda yafi amman kuma yaqi d'agawa, Ga wajan hajiyama babu sauki domin kuwa ita tamayi masa gargad'i akan kada yasake yakirata idan baisamo iyalansaba, gashi haryznu yayi iya nemansa baigano yanda suka tafiba, Wayarsu tadaina shiga gabaki d'aya, abunda bai saniba shine sukam sun dad'eda sake layi, wancan sun zubdasu kozaiyi kiran duniya bbu wanda zai samu cikinsu, daga ummii har babysis da da muhammad d'in, kullum hankalinsq baya jikinsa, Yakira y'an uwansa yayyunsa da qannensa akan yana tunanin cewa su zasu fad'a gaskiyar lamarin ko iyalansa sun iso gida amma amsa d'ayace suke bashi shine basu isoba, Abunda bai saniba shine gabaki d'ayansu hajiya tayi musu gargad'i da iyaka akan idan suka yarda suka tofa masa wani abun koda batasan wanda yafad'aba acikinsu to duka ransu saiya 6aci, haka yasa suka guji 6acin ranta sukaki fad'a masa." Yanzuma haka wajan aiki yake zaune idanuwansa sunyi jazirr, Baisan yana yiwa ummii da yaranta wani mahaukacin soyayyaba sanda suka 6ace yanemesu yarasa, Lallai yasan idan yarasa ummi cikin rayuwarsa yayi babban rashi domin ko ayanzu ya fahimci amfaninta gareshi, yakuma fahimci muhimmancinta da girmanta gareshi." Ganin babu wani abunda zai iya ta6ukawa cikin office d'in yasanyashi yamiqe yanufi gida, Abba yarame gabaki d'aya ya fice hayyacinsa cikin sati d'aya har wani d'an tsufa yayi, Shiga gidan yayi kai tsaye yanufi sashinsa, rabonsa daya duba hafiiza kokuma yasanyata cikin idanuwansa tun ranarda yashiga neman ummii tashaida masa bai bata ajiyartaba." Da daddare kuwa bacci 6araowa kawai shine yad'auki abba, Aikuwa farkawanda zaiyi yafarka dawata matsamanciyar qaunaarta zai iya fad'in cewa ko farkon ganinsa da'ita bai sota irin hakaba, Yanda yakeji cikin zuciyarsa zai iya shiga mummunan hali idan bai gantaba nanda kwana d'aya, Kwanciya yayi akan bed domin rashin qarfin jikinda yake fama dashi, Yana kwace duk wani abun duniya yadameshi, baisan lokacinda yafara sumbatuba yana fad'in, Why safiyya?" Menayi miki haka?" What have i done to deserve such funishment?" Kin rabani dake kin rabani da yarana wanda nake kallonsu naji dad'i, Plz safiyya come back, am sorry bazan sake d'aukan hukunci akankiba, safiyyaa i know ke masoyiyiyar asalice bazaki ta6a cutataba bansan menene yarufemun idanuwa naba, harnakiga aikata mummunan hukunci, nafurta miki kalma mai zafi, kalmarda ubangiji kansa bayaso afurtata, Am sorry, Am sorry safiyya, STORY CONTINUES BELOW  Hmm abba kennan kayi wasada damarka kabawa kanka da ummii distance mai tsayo, yayinda itakuma ummii tayi qoqari wajan maintaining distance d'in." Haka abba yayita sumbatu kamar qaramin yaro, Har bacci yad'aukeshi, yana tashi yamiqe yahau had'a kayansa sanda yagama had'a komai yafice, Shikam yama mantada hafiza cikin gidan, Shidai bazai tsaya ako'inaba sai nigeria, zaije wajan mahaifiyarsa yarqoeta tadaina fushinda takeyi dashi kozaiji sanyi cikin wannan lamarin." Idan yaso idanta huce kozata taimaka masa wajen neman iyalansa, domin yasan koda addu'ar alkairi tayi masa ita mahaifiyace kuma in sha Allah za'a dac." Aikuwa dama shikam yanada visa ko'ina zaije cikin fad'in duniya, domin shine DR d'inda babu kamarsa, akoda yaushe yatashi zuwa wata qasa sai an had'ashida security guards, domin tsaron lapiyarsa, Wannan karonma hakanne yafaru, Aikuwa basu dad'eba jirginsu yad'aga zuwa nigeria." Karfe shida na yamma 6:00pm tayiwa abba acikin garin abuja, Abba bai tsaya wani abunba sai sallah kawai dayayi, yana idarwa kai tsaye sukabi jirgin zuwa gombe, Aikuwa yana isa dama ansanarda government d'in qasar isowarsa sun tanada masa motocin hawa, Yana zuwa yashiga suka wuce gida kai tsaye, Lokacinda ya'isa cikin gidan ana fitowa daga sallah, aikuwa abba yana fita amota idanuwansa suka sauka akan abdul, wani irin sanyin yaji cikin ransa yanzu ya tabbatarda cewa iyalansa suna kusa basuyi nisaba, koda daga nesa yaganshi yahangi wata y'ar cika dayayi, wato hakan yana nufin sunjin dad'insu batareda yana kusa dasuba kenan?" Qarasawa yayi abdul zai sanya qafafunsa cikin sashinsu yaji andafashi, tsayawa yayi cakk, domin koda ace bai juyowaba yasan mahaifinsane, kodaga yanayin takunda yaji akusa dashi yasan mahaifin sane, Balle yakaiga kashim turarenda yasan mahaifinsa kad'ai yake amfani dashi, saikumashi, amma shi nasa yad'an bambamta, domin kuwa yanayin had'i dawani, Kasa juywa yayi, gabaki d'aya sai kunyar mahaifinsa tacikashi yabiyewa son zuciya yasa6awa mahaifinsa, Amma kuma babu yanda ya'iyane domin kuwa umarnine daga mahaifiyarsa, Yabi umarninta kuma yaga alkhairai dayawa cikin bin umarninta dayayi, Ahankali abba yake buga hannunsa akafad'ar abdul, Juyowa abdul yayi jiki banu kwari, Yana juyiwa abba yayi hugging d'insa yana fad'in natuba, yarana natuba, kuyafeni, nasan nayi laipy amma kada kusake yimun irin wannan hukuncin, wannan hukuncin yayi tsamari agareni, Abdul baice komaiba har abba yasakeshi, yad'an qara bubbuga kafad'unsa sannan yace" ina umminku?" Shiru abdul yayi yarasa maizai cemasa, abba dayaga baice komaiba kawai saiya sakeshi yashige ciki, Tsayawa abdul yayi yana jiran fitowarsa domin yasan dole zai fito don ummii bata ciki, Aikuwa abba daya shiga yafara duba d'aki bayan d'aki amma kuma baiji alamun kowaba, mai hakan yake nufi kenan?" Inakuma suka shiga?" Fitowa yayi yana tunanin hala suna sashin hajiyane dan haka yana fitowa yawuce abdul kai tsaye yashiga sashin hajiya, Sallama yayi yashiga, apalour yasamu hajiya tana amsa sallamarsa tahad'erai, ya'iso koda gaisuwarsa bata amsaba, haka yayita zama yana neman afuwa wajan hajiiya amma ko kulashi batayiba, aikuwa datagama zai takureta kawai saita tashi tafice masa takoma d'aki, tarufo qofa duk iya zamansa haka yagaji zama bata gitoba, Ganin lokaci yana tafiya hat anyi isha'i gashi kuma baiyi magrib ba yasanya yafice, yashiga masallaci yagabatarda sallolinda yake kansa yadad'e yana addu'a cikin masallaci sannan yafita zuwa sashin mahaifinsa domin yaji dawowarsa, Shikam yayi sa'a ya amsa gaisuwarsa bayan nan kuma bai sake kulashiba, har yagaji da zamansa yafita, Yanemi twins sugaya masa yanda mahaifiyarsu take amma sukace basu saniba dama kuma basu sani d'inba, Abdul kuwa basu sake had'uwaba, Yana zaune cikin d'aki dare yatsala sosai gashi kuma bacci yaqauracewa idanuwansa, Yana cikin tunane-tunane hafiiza tafad'o masa cikin ransa, mtsww yaja tsaki, itace duk tajawo masa wannan fitinar shiyama manta daya barta acan, daya dawoda ita gida nigeria bazai qara kuma komawa da itaba sai dai tazauna anan domin bazai tafida annobaba, Shidai danma sakin aure babu kyaune toda yasketa yahuta domin kwata-kwata baisan dalilin aurenta dayayiba, baiga kuma amfanintaba, auranta babu wani abubda yaqara masa sai dai bakin ciki da takaici." Danna waya yayi tatura mata text dan yana buqatar ganinta tadawo nan, STORY CONTINUES BELOW  Baifi 5minute da tura message d'inba, amsa tashigo, yayi mamakin dabatayi bacci aqannan lokacinba, Kud'i take buqata, tsaki yaja sannan yace" jarababbiya, transfer d'in yayi mata na kud'in sannan yakashe wayarsa." ***** *RUGAN DATTI* Shigowa gidab yayi da sallama innna wacce take madafi(kitchen) tana fitowa, Sannu hamma tafad'a tana kallonsa cikin tausayawa irin halinda yake ciki yanzu, Yawwa yafad'a yana zama akan kujera y'ar tsugunno datake tsakar gidan, waige-waige yafara yana fad'in ina asma'uta?" Tana bacci ai bakaji gidan yayi shiru bane?" Inna tafad'a tana ajiye masa ruwa cikin kwanon d'ansha, Amsar ruwan yayi kafin takarasa ajiyeshi aqasa, yabud'e sanda yasha sosai sannan ya ajiye yayi hamdala yana fad'in ngd, Murmushi tayi takar6i kwanon takaishi ma'ajiyi ta'ajiyeshi sannan tadawo kusa dashi tazauna, Hamma yajikin naka?" Dasauki maryam yanzuma kawai nad'an gajine nadawo gida nahuta, Aikuwadai gara karinga hutawan yawan fitan zai iya jawowa lpyrka wani abun, Barina shiga daga ciki nayi bacci, ida ankira la'asar kitasheni kinji?" Gyadakai kawai tayi dukda ba ganinta yakeyiba, takoma taci gabada aikinta, shikuma yahau dago yafara bacci, Da lokacin la'asar d'inma yayi bata tasheshiba ya farka, Yad'aura alwala yafita, sanda yazo zai fita yace" maryam kitashi asma'u daga baccinnan haka kada tafarka da fitina, Toh innna ta amsa, shikuma bayan yafita bai dad'eba yadawo ga dukkan alamu sallan kawai yayi daganan bai tsayin komaiba." Dubanta yayi yace" kigama abunda zakiyi zuwa jimawa kad'an zamu shiga wajansu baffa nakwana biyu banga abubakarba, Ainama gama, barina shiga wanka yanzu idanna fito saimu tafi, Nadai haneki dayi wankan daff la'asar d'innan amma kinkiji, Kayi hakuri hamma aikine yayimun dare innna tafad'a tana mai ladabi gareshi, Wanka tashiga bata dad'eba tafito tana fitowa tashirya da saurinta, sannan tayiwa asma'u wanka tashiryata, Suka fita domin nufan gidan baffa, Sun dad'e acan gidan sosai, Abubukar yana kalllonsu yazoda murna yamaqalesu, Aikuwa suma sun nuna murnarsu daganin d'annasu, Hajjo kuwa innar innna sai kawarda kanta tayi domin itaka ko'a tarihi bata ta6a kallon rashin kunya irinta innna da mijintaba, Yana d'aukeda yaron Yafice yakoma gidan mlm buba, Yadad'e acan sosai harsaida inna tashigo tasameshi, Suka fita tare suka koma gidansu innna, Mlm bello yashigo yasamessu yazauna suna tad'i, nan yake tambayarsa yaya jikin nasa ya shaida musuda sauki domin yakwana biyuma baiji ciwon kayinba, Toh Alhmdllh Allah yaqara sauki da afuwa, Ameen suka amsa, Said dare yafarayi sannan sukayiwa su baffa sallama suka nufi gidansu, Sunso abubakar yabisu amman duk wannna maqalewarda yakeyi musu yana kallon suntashi tafiya tashige cikin gidan mlm buba, Baisake fitowa har suka tafi." Bayan sunyi sallar asubahi suka zauna domin cin tuwon dare, Bayan sungama ta ebo ruwa tazuba masa hankali yawanke hannunsa sannan yawanke bakinsa yatshi da asma'u ahannunsa yashige d'aki, Sanda tagama shirya duk wani kayanda tayi aiki dasu sannan tawuce zuwa d'akin, Tasamu asma'u tayi bacci saishi kad'ai yana jiran shigowarta, Sannu da hutawa tafad'a tana zama kusa dashi, Murmushi yayi sannan yace kece mai sannu aii kekayi aiki, Kakwanta kaga dare yayi kuma kanada bukatar hutu kaji! Hannunta yakamo yakawota jikinsa yakwanta sannan itama takwanta ajikinsa, maryam! Yakira sunanta na'am hamma ta ama tana jin yanda zuciyarsa take bugawa, Mai yasa kike sona?" taji ya jefo mata tambaya, Sanda tad'an dad'e kafinnan tad'an d'aga kanta tana kallonsa kamar yanda shina itan yake kallo, murmushi tayi sannna tace saboda kanada tsarka kekkiyar zuciya, zuciyarka mai kyauce kokadan babu wani mummunan abu acikinta, Wani irin sarawa kansa yayi maganrda tayi tana masa yawo cikin kansa ya tabbbata ba yanzune yafajin wannan maganarba, ya tabbata bayanzune farkon jin wannan maganarba, amo maganar tafara yimasa cikk kunne dawata irin sauti wanda yasan wannan sautin sani na haqiqa." Ahankali yafara ganin duhu yana gifta masa, idanuwnasa suka fara lunshewa, wani irin abu yashafe kwakwalwarsa, Shikenan ya zama mutum mutumi gangar jikinsa tana jikin amma kwkwalarsa bata taredashi, innna wacce taji saukan numfashinsa tad'auka bacci yayi, saita sanya hannuwanta taqanqameshi anan itama bacci yad'auketa."Da asubahi innna tafarka lokacin gari harya fara haske, tarigada tasan cewa idan asubhi yayi shine yake fara tashi, dake tasake jiki da hakan shiyasa takwanta har lokacin sallan asubahi tawuce, Ahankali tatashi tamiqe tana kallonsa da mamaki ahankali da furta cewa hamma wani irin bacci mukayi haka?" Yau gashi har baccin yakai mun makara sallan asubahi, duk wannan maganrda takeyi bai matsaba, sai numfashi dayake ajiyewa ahankali, Hamma! Hamma! Tad'an jijigashi, Shiru yayi sai saukan numfashinsa dayake tashi, Hamma wannan wane irin baccine haka?" Jijjgashi taqarayi Amman shiru, yanzu abun yafara bata tsoro domin duk baccinda yakeyi sai dai bata kira sunansaba zai tashi amma yanzu har jijjigashi takeyi ko'alamun farkawa bayayi, Jijjigashi tafarayi hawaye yana zirya akan fuskarta tafi 30minute tana tashinsa shiru, hamma dan Allah katashi idan wasa kakeyi hakan yafara d'agamun hankali, tanata sumbatu Ahaka har asma'u tatashi, itama tahau kan babanta tana bubbugashi domin dama asma'u ko bacci yakeyi idan tatashi toshima yatashi, domin zatayita tsalle akansa harsai yatashi, innna tatsaya tana kallon ko idan d'iyarsa tahau kansa zaitashi, amma shiru, hankalinta yayi mumnunan tashi, gyalenta tad'auka tafice daga gidan batayi takan d'iyartaba, tabarta ajikinsa tanata yimasa surutu, Tana gudu haki takeyi amma taci gabada gudun sanda takai gidan baffanta, dawowarsa kenan daga sallan asubahi sukayi kici6us, tana haki take kuka tana fad'in baffa hamma umar, hamma umar yaki tashi abacci, ke tsaya kiyimun bayani wani irin yaki tashi abacci?" baffa yafad'a yana qoqarin fahimtarta, Baffa tun d'azu nake tashinsa daga bacci amma yaki tashi gashi kuma yana numfashi Amman kuma yaki farkawa, subhanallahi wannan wani irin al'amarine?" nima bansaniba baffa, wuce muje gidan toh, baffa yafad'a yana kallon innna wacce take rikice, Sauri-sauri gudu-gudu haka tashige gaba, shima yabita dasauri, Inna wacce tana d'aki take jiwo maganar inna sama-sama tafito amma kafin tagama futowa bata samu kowa awajan, Amma tana hangensu, domin basuyi nisa sosaiba bata bisuba sai kawaita koma tad'auko mayafi tanufi gidan mlm buba domin fad'a masa abunda yafaru kozai bisu abaya." Suna isa baffa yashiga d'aki yayi iya qoqarinsa yatasheshi amma kuma abun ya faskara, karan mashind'in mlm buba awaje, fita yayi, yayi masa bayani, suka shigo suka d'aukoshi, atsakiyan mashin suka sanyashi mlm buba agaba mlm bello abaya, suka nufi cikin garin dukku, Itakuwa innna aka barta cikin tashin hankali, dataga zaman gidan ya isheta kawai saita d'auki asma'u takulle gidan, tanufi gidansu, Bayan ta'isa innarta tatambayeta abunda yafaru, tana kuka take basu lbr, Sosai suka shiga rarrashinta, Har rana babusu baffa babu labarinsu, aikuwa innna banda aikin kuka babu abunda takeyi, Hatta abinci tagagaraci." Kafin yamma kuwa harta d'an rame sai amai kawai takeyi kamar zata amayarda hanjin cikinta, sosai su innarta suka shiga damuwa, domin dama bataci komaiba gakuma amai daya sanyata agaba, Sukuwa su baffa acan asibiti bincike sosai akahauyi yayinda bincike yanuna cewa yana shirin dawowa cikin hayyacinsane, Amma kuma yana bukatar manyan likitoci kusa dashi alokacinda zai farfad'o, Dan haka akayi admitting nasu zuwa asibitin cikin garin gombe, nasu wani d'auki lokaciba suka tsari mota suka wucecan, Bayan sunje likitoci suka dubashi sannan aka kwantar dashi, Ba'asan iya tsawon lokacinda zai d'auka awannan haliba, domin akwai masu d'aukan samada 1month akwai kuma wanda basa kaiwa haka, STORY CONTINUES BELOW  Sannan kuma za'a bukaci kud'i mai yawa domin jinyace mai tsayi sosai, Shine mlm buba yazauna shikuma mlm bello yadawo domin tanada musu duk wani abunda za'a bukata, Aikuwa daya dawo ko ruwa bai shaba suka hau kansa suna tambayar Yaya maijiki?" Cikin nutsuwa yayi musu bayanin duk wani abunda yafaru, jikinsu yayi mugun sanyi, Inna tacewa baffanta akan itace zataje tayi jinyar mijinta, baffa yahanata yace tanada goyo dan haka tazauna agida shida mlm buba zasuna kwana bibbiyu awajan, Kuka innna tasanya tana fad'in itakam kada yahanata yin jinyar mijinta Suma matan gidan sun goyi bayanta domin sunce itace takeda hakkin jinyar mijinta, Baffa yace mata takoma gida tashirya domin zuwa gobeda safe zasu wuce domin ana bukatar kud'inda za'a siya magani, Aikwuwa alokacin takoma gida tahad'a kayanta da kayansa cikin akwatinda yasiyo musu, cikin jakarta ta hannu kuma tahad'a kayan yarinyarta, Duk wani abunda zasu bukata ta tattara, Baffa yazo yad'auketa suka shiga mota atasha har zuwa gombe, suka Isa abitin ake yabiya duk wani abunda ake bukata, itakuma tana zauneda mijinta ad'aki, tazuba masa idanuwa kamar wanda yakeyin bacci, Suna cikin d'akin wata nurse dawani nurse sukazo sukaja gadonsa domin canja musu d'aki baffane ya bukaci hakan, domin bayason wajan hayaniya domin anshaida musu hayaniya zata iya takurawa kwakwalwarsa domin yanzu yana tariyo tunaninsa na bayane, alokacinda yake tariyo tunanin kuma idan aka dameshi wasu daga cikin tunaninsa na lokacin zai iya shafewa gabaki d'aya, Shiyasa baffa da mlm buba suka saki kud'i kawai aka canja musu d'aki su kad'ai a aminity, Su baffa sukayiwa innna sallama suka tafi akan zasu dawo bayan kwana biyu, amma domin yanayin tafiyar bazai yiwu ace kullum suna hanyaba sunbar mata duk wani abunda zata bukata koda anan gaba wani abun zai taso." **** Wani abu mamaki shine ummii kwananta biyu cikin wajan tawarke sumul,💃💃💃💃💃😂😍💞💖❤💋 idanka ganta zaka iya rantsewa bata ta6a jinyaba, garau take tafiyarta, kamar bata ta6ayin jinyaba, Komai nata yadawo normal hattada shaking da body dinta yakeyi yadaina radawo umminta na baya, umminda muka sani kyakkyawa mai cikeda haiba, Cikin kwana biyu ummii harwani qiba tayi gashi fatarta tad'an murmure kumatunda dukya ciko, kafafunma sunyi subul-subul dakyau sunciko famm, bbu yanda bai cikaba cikin jikinta, gashi wani sharr takeyi dukda itaba wata fara face batada haske, abba yafita haske sosai, Cikin y'ay'an kuma abdul yayi kamada abbansa yad'auko kalarta itakuma babysis tayi kamada umminta tad'auko kalar babanta." Zaune babysis sukeda husna awajanda sukaje farkon zuwansu, tunda suka isa wajan husna take tuna abdul da magan ganunsa gareta, Har jikin bishiyanda suka d'auki pic sanda tatsaya tana dubanta, Har wajan wannan ruwan, Tayi shiru sai tunane-tunane takeyi, bazata yaudari zuciyartaba tasan kokad'an batason abdul amma kuma yanayinsa yana burgeta, Komai nasa kalar burgewane, hattada farcen hannunsa, Murmushi tayi data tuno lokacinda takamashi yana kallonta, sau dayawa takan fahimci yana kallonta koda kuwa ace bai d'ago kansa gabaki dayaba, koda suna zaune idan yana pressing phone nasa tasanba phone d'in yake kalloba rabin hankalinsa yana wajanta, Tanutsa cikin wannan tunanin taji muryar babysis tana fad'in, Sarauniyar broda dan Allah kifad'amun waishin dagaske kikeyi babu wani event da zakiyi?" D'agakai husna tayi tana fad'in babyshish sau nawa kikeso nafad'a miki?" DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Nafad'a miki babu wani event da zanyi shi event d'in menene amfaninsa?" STORY CONTINUES BELOW  6atarai babysis tayi tana fad'in haba utuna wannan abu tayaya za'ayi yayuwu?" 6ta friend and broda are getting married, sannan you're telling me not to celebrate?" Tayaya kike tunanin yiwuwar hakan?" Babyshish nifa ban hanaki yin event ba niceh nace bazanyiba, Gyara zama babysis tayi tana fad'in owoh haba aisaiki fahimtar dani mana, kece bazakiyiba amman ni idan nayi babu matsala, Zakiyi attending ina?" May be husna tafad'i, Kokonton zuwanma kikeyi?" Eh aidole nayi kokonto idan zakiyi event dayawaba, Bazanyi wani event dayawaba sai kace wau y'an qauye daga kamu, reception sai bud'ar kai thats all, D'age kafad'a husn tayi tana fad'in not bad, zan iya zuwa, Harara babysis ta wurga mata tana gad'in ke dan kinga ina lallashin kinema shine kike wani feleqe, kadama kije kinji, Wani kallo husna tawatsa mata tana fad'in sai kuma kiyi, kinma samu nace miki zanje d'in, matsowa kusa babysis tayi tana fad'in nikam husna menene sirinne?" Kinga yanda kikayi kyau fatarki tacanja gawani sai cikowa da kikayi, Kallon kanta husna tayi tana fad'in inaga yanayin wajanne, yasanya hakan, The weather?" Shineni bai canjamin nawa fatarba?" Miqewa husna tayi tana fad'in kai babysis kije ki tambayi goggo toh, Dama nasan dahakan aii babyasis tafada, wato irin wariyar nan waike amarye shine tawani tsumaki ana gyara miki jiki sai wani kyau kike qarawa, Kijira lokacinki yazo mana kiga kobaza'a yimikiba, Tafiya babysis tafarayi sannan tawuce husna tana fad'in waima dad'in abun duk wani abunda akeyi don yayana akeyinsa, Kuma yanzu saina rigaki isa nacewa ummii wai abunda ake baki yayi kad'an sukara yawansa, Inna lillahi husna tafad'a domin tasan tsaf babysis zata aikata, innna lillahi idan babysis tafad'i wannan maganar dawani ido zata kalli ummii?" Binta tayi tafara bata hakuri tana fad'in babysis plz kiyi hakuri, Sauri babysis tafara sosai ganin husna tanaso ta cimmata itama babysis d'in saita qara harda gudu, husna tana kallon haka itama tafara binta da gudun, Haka suka isa har izuwa wajan, ummii suka kalla tsaye abakin wajan, babysis ta'isa tana haki hakama ita husnar hakin takeyi, Kallonsu ummii tayi tana fad'in menene hakan?" Badai gudu kukayiba?" Yanzu husna idan babysis zatayi saiki biye mata?" kinsan cewa ked'in auranki zaura 1week, ina kuma amfanin gudun, illa zai jawo miki sosai, Kada kikara kinji?" Gyadakai husna tayi tana fad'in toh ummii, amma kunya duk tawani rufeta tarasa yanda zatayi, Yawwa daman ummii abunda yasa nayi gudun aikafa zan fad'a miki, Rigeta husna tayi tanayi mata idanuwa akan tayi hakuri, Bige hannunta tayi tacikaba da fad'in ummii kiji wai husna tace baza tayi eventa ba kuma ko anhad'a bazata jeba, Ajiyar zuciya husna tasauke tayi tunanin abunda tafad'a d'azu zatace, Bin ummii abaya husna tayi tana fad'in ummii kada kikoma ciki kizo muje ciki kiga yanayin wajan saiki d'an warware qafarki, Mezan gani kuma aciki?" Yanzuku bakwajin tsoro kuke shiga wannan waje daba hasken kirki dashiba, Babu wani abun tsoro Allah ummii kizo mushiga kigani, Ajiyat basket d'in hannunta tayi tana fad'in muje toh, Gaba suka fara yana biye dasu, Ummii tana kallon wajan jitakeyi kamar kadata tabar wajan, Yarannan kuce shiyasa kuke dad'ewa ba'a gankuba, ashedai wajan dad'ine haka dashi, Sun d'an d'auki lokaci sannan suka zaga cikin wajan harda tawajanda basu ta6a yiba hartanan sukayi." Saita suka d'an dad'e kafinnan suka juyo, Harara goggo ta tallaw husna tana fad'in ban hanaki tafiya wanna yawonba?" Shiyasafa amaren yanzu gyaranku bazaiyi kyauba saboda yawo, Azamanin baya idan yarinya zatayi aure, auren saura wata d'aya take daina fita gabaki daya, Shiru husna tayi sannan ta sunkuida kai, ummii tace aikuwa danma bakiga abunda sukayi d'azuba, kinsan cewa gudu suka dingayi, Kamo husna goggo tajeyi tayi saurin kaucewa tana dariya, Inaga idan mukaje gida saina sake yimata wani gyaran saboda ita tad'auki komaida wasane, Ummiine take wannan maganar tana nufan d'aki, Aikuwa dai da alama domin nima nad'auki cewa komai cikin wasa tad'aukeshi, Itadai husna batace komaiba babaysis kuma dariya kawai takeyiwa husna, Wajan goggo husna tadawo tana fad'in nikam gabaki daya wannan wajan babu service neh?" Inason yin waya amma kuma yaqi tafiya, Taho muje nanuna miki wajan service d'in goggo tafad'a tana tafiya dakyar kafafunta duka sun riqe, Wani waje sukaje sannan tace tsaya adai-dai nan saikiyi wayan, tsayawa husna tayi tana kira aikuwa yashiga, yaya takira da umma suka fara gaisawa sannan daga qarshe takira anty, Gamawa tayi tad'ago zata tafi, taga goggo tana kallonta, Muje nagama husna tafad'a, bazaki kira saurayin naki bane?" goggo tatambaya, Aa dama umma da yaya da anty kawai zankira, Kikirashi asma'u, yaronanna yana sonki sosai hakama mahaifansa, ke meysa bazakiyi qoqari ki cusa sonsa cikin rankiba?" Maiyasa baza kiyi yaqida zuciyarkiba?" Kowa cikin wannan rayuwa datasa qaddarar, D'agokai husna tayi tana kallonta, Tace dan Allah inaso na tambayeki amsa nakeao kibani, Shin yaya umar yana raye?" Ninasan yana raye, nasan bai mutuba, Murmushi goggo tayi sannan tace" asma'u kenan, dazaki gane dakin kar6i qaddararki hannu bibbiyu, Wannan auren kiyi addu'a yazamana alkhairi agareki, Umar kuma idan yanada rabon auren jininki kob yanzuba zai aura Asma'u, kikwamtarda hankalinki sannan kisanya komai ubangiji yayi miki mai kyaune kinji?" Gyadakai husna tayi, goggo tace yawwa gimbiya asma'u, maza kirashi kinj?" Gyadakai husna tayi sannan tayi dialing number d'insa, Abdul yana zaune yayi iya neman layin husna amma kuma bai shigaba, sannan kawai yatura mata message kamar yanda yakeyi kullum idan yayita trying yaki shiga, Yana zaune yaji wayarsa tafara ruri, Bai cikin mood d'inda zai iya d'aukan waya domin muryarta kawai yake bukatarji, Haka harta katse bai d'agaba, kallonta goggo tayi sannan tayi murmushi tace" kiyi hakuri kisake kora bakisan awani irin hali yake yanzunba, Kara dialing tayi awannan karon d'an tsaki yayi sannan yad'auki wayat ganin wata number daban wanda baida ita yasanya ya latsa had'eda karawa akunne, DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Husna kuma dama layikanta guda biyune, shine tayi kirada wanda yakeda kud'i aciki, Assamalu alaika! Husna tafad'a, Alokacinda muryarta tadoki dodon kunnensa yayi dai-dai da lumshewar idanuwansa, had'eda sakin murmshi."

0 Comments