RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3
Dakyar likitoci suka samu numfashin Badiyya ya daidaita, cikin dare aka tafi da gawar Firdausi Kankia, amma anbar Ladi da kanwar Firdausi; Jamila a wajen.+ Musaddiq yace shi sam bazai yadda a kashe mishi yar uwa a banza ba, domi daga gani kisan gilla ne, kisan was intentional. Saboda haka yayi alkawarin gano duk wanda ya aikata hakan. Washe gari da safe aka ma Firdausi sutura, bayan an kaita an dawo, su Kausar sai kuka suke, sai yanzu suke realizing abubuwan da take fadi, sai yanzu suka yadda da maganarta. Ashe da gaske take idan tace na bankwana? Basu taba kawo ma ransu cewar da gasken mutuwar zatayi ba. DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Musaddiq yan sanda ya dauka akaje gidan, Malam Tanko suka iske zaune kofar gida yayi jugum. "Sannu Malam," Inspector Sadat yayi magana, yana mika mashi hannu alamar sallama. Malam Tanko mika mashi hannun yayi, "Yauwa yaro," ya fada, domin jikinshi yayi sanyi, yasan dole a nemeshi cikin case dinnan, tunda shine mai gadi. "Tsoho so muke a fada mana wanda ya shigo gidannan last jiya," Inspector ya fada, yana scrutinizing face dinshi, domin yaga idan akwai alamun rashin gaskiya ko babu. "To nidai jiya wajen karfe 9, wani yaro yazo yace ana sallama dani, nace yaje ya kira mutumin amma yaqi, dole na bishi domin inga waye, danaje kuma banga kowa ba, sai na dawo," Malam Tanko ya fada, zufa na keto mashi, domin yasan tabbas laifi ne barin wajen aikinshi dayayi cikin dare. Fatan shi daya Allah yasa suyi sparing dinshi. "To daka dawo baka ga alamun an shiga gidan ba?" Inspector ya kara tambayarshi. "Aa gaskiya ban gani ba, amma duk ranar Friday Baban Badiyya yana zuwa, to bansan ko yazo bani nan ba," Malam Tanko ya fada. "To kai bakaiji wani sound ba haka alamun buga mutun jikin bango? Yarinyar kuma batayi ihu ba?" "Gaskiya Yallabai banji ba," Malam Tanko ya fada yana goge zufar data keto mashi. A haka akaita tambayarshi yana bada amsa, duk yabi ya rude, rayuwarshi bai taba arba da yan sanda suna mashi tambayarsu ta kure gaskiya ba. Ba kamar yan sandan Nigeria, tsoronsu zai saka ka amsa laifin da bakasan kayi ba, ga iya yima mutum rijiya ya fada koda mutum bai aikata hakan ba. Da aka shiga aka ga abun ba alamun zaa gane wanda ya aikata hakan sai suka tambaya ina yarinyar, wata kila ita ta gani. Gaba daya suka tafi asibitin domin suga Badiyya, bayan sunje likitoci suka fada masu akan ta shiga coma, baza'a iya cewa ga ranarda zata farfado ba, saidai a jira ikon ubangiji. Ba yadda ba'a yiba domin a karbi camera hannunta kodan kila a samu wani evidence, amma abun ya gagara, da alama jikinta yayi frenzing tare da camera, kuma yadda ta rike camera kamar rayuwarta gaba daya ta dogara da camera ne. Babu yadda suka iya saidai sukace a basu number Ahmad, domin shine last chance dinsu; kuma first suspect dinsu. Saida tayi 2 missed calls sannan a kira na ukku ya daga. "Hello, wake magana?" Ya fada, alamun an takura shi. "Inspector Sadat ne, mun kira ne domin muna suspecting dinka akan kashe tsohuwar matarka; Firdausi," Inspector ya fada, cikin kakkausar murya, domin daga jin muryar Ahmad yasan baida gaskiya. "Firdausi kuma?" Ya tambaya, tsananin mamaki karara a muryarshi. "Eh ita. Ance kaine kullun kake zuwa gidan duk ranar Friday, but jiya bakaje ba, that means kanada masaniya akan hakan." "Yallabai, ni banma san ta rasu ba, yanzu ya Badiyyar? Lafiyarta kalau kuwa? Ni ina Lagos naje aiki, amma yanzu zanbi next flight Insha Allahu," Ahmad ya fada, fatanshi Allah yasa Badiyya lafiyarta kalau. "Badiyya tana asibiti, kuma daka dawo kayi reporting a police station, inba haka bazaka wanke kanka ba," Inspector ya fada, yana kashe waya. Nan ya sanarda Musaddiq yadda sukayi, shi kanshi ya daure, to wa ya aikata ma Adda Fiddi wannan ta'addancin? Wajen karfe 4 na marece Ahmad ya diro Dutsinma, looking worried, a haka yaje police station din, ya rokesu da su barshi yaje yaga Badiyya, yana zuwa ya ganta kwance lifeless, wasu hawaye masu zafi suka sulalo mashi. Haka ya zauna yanata kallonta, saida mahgrib ta gabato, sannan ya tashi ya tafi, duk zaman da yayi kannen Firdausi ba wanda yace mashi sannu, haka yasha zamanshi ya tashi ya tafi. *** Badiyya bata tashi ba sai bayan kwana uku, a lokacin data tashi bata cewa kowa komai ba, camerata ta kara rungumewa. Kowa tsoron yi mata magana yake, kuma sunga bata nema Momynta ba, tunani suke ko batasan ta rasu ba. Amma lura da sumar datayi ya nuna tabbas may be har wanda yayi kisan ta gani. But nobody dare to utter a single word about her Momy. Musaddiq zuwa yanzu ya hakura, abun yaci tura, babu iota of possibility cewar Ahmad yayi kisan, kuma basu da wani suspect inba shi ba. Haka ya hakura yabar case din, kuma saboda sisters dinshi sun nuna mashi akan ya hakura, ko an gane wanda yayi kisarnan ba dawo masu da Adda Fiddi zaiyi ba. Bayan an sallami Badiyya, kausar tace zata tafi da ita Kano, tunda acan take aure, amma fir Ahmad yaki, a cewarshi bamai raba shi da yarinyarshi. Akai akai yace bai yarda ba, haka Gwaggo tazo taita zuba ruwan bala'i akan sun jama kaninta sharrin kisa, kuma yanzu sunasan rabashi da diyarshi, salan su cunkusa mata tsanar mahaifinta. DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Da sukaga bala'in Gwaggo bana karewa bane, kuma dama sudin ba yan bala'i bane, balle ga abunda yake damunsu. Sai suka hakura akan zasu barta ta tafi wajen Gwaggo, amma akan sharadin duk hutu zata rika zuwa wajensu. Budar bakin Gwaggo sai tace wannan kuma sai taga dama, tunda yanzu diya dai ta uba ce. Ganin Gwaggo na neman saida masu hali cikin asibiti yasanya suka hakura. Har akazo za'a tafi Badiyya batayi kuka ba, wanda hakan ba karamin daga ma yan uwan Firdausi hankali yayi ba, domin yarinya kamarta yaci ace tayi kuka. Sai mutum ya kalle ta deep into her eyes sannan zaiga kukan zucin da take, zaiga plea din da take akan karsu barta wajen Gwaggo, amma ba yanda suka iya, Gwaggo tafi karfinsu. A haka Gwaggo ta rike hannunta suka nufi motar Ahmad, Badiyya ta juya tana kallon yan uwar Mamarta, ko kwalla daya ya kasa zuba daga idonta. Babu abunda ta dauko na daga kaya daga wancan gidan, camera hannunta kawai ta tsira da ita. Ahmad yayi igniting motar, suka dauki hanyar KATSINA TA DIKKO DAKIN KARA. Sai a lokacin wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo daga idonta, memories dinta da mahaifiyarta suna mata ebbing cikin kwakwalwarta.Bayan sun isa Katsina, Ahmad ya aje su a GRA, kafin ya tafi saida yayita ma Badiyya magana amma bata amsa shi ba, kamar ma tsoronshi take, haka ya gaji ya wuce. Badiyya sai binsu da idanu take, wanda sukazo yima Gwaggo jaje da Allah ya kyauta, kowa sai ya mata gaisuwa amma ko nuna alamar ta gane batayi.+ Gwaggo ta kawo mata abincin rana, kallon abincin tayi ta kauda kai "ke kici abinci, badan kinga na kawo maki ba, kinsan halina ai," tayi kwafa, tana kara tura mata plate din gabanta. Badiyya kara turbune fuska tayi "ni Gwaggo banasan dry jollof rice," ta fada, tana kumburo baki. "Kam bala'i! Kinci uwarki, ai ba uwarki ta siyo kayan abincin ba balle kice wani abu, maza kici ki bani kwano na ko kuma wallahi in maki bugun tsiya yanzu," fadar Gwaggo, sai kumfar baki take kanar tana fada da babban mutun. Badiyya sanin halin Gwaggo da tayi, dan lokacin da Firdausi ke kawota weekends ba karamar wahala take shs ba, kullun saita kunsa mata tuwo da abincin da bata saba ci ba, kuma idan taki ci ta kamata tai mata bugun tsiya, wai bazata jamata sharri ba, ace bata bata abinci. A haka wata kawar Gwaggo, wadda ake cewa Larai tazo, Badiyya sai wasa da shinkafar take, Larai kallonta tayi ta watsar, dan tun asali diyarta taso Ahmad ya aura amma yaki. "Wai Binta wannan diyar bata iya gaisuwa bane? Ko dan uwarta ta rasu sai akace kuma bazata gaida mutane ba?" Fadar Larai, tana kallon Gwaggo. "Tayani gani Larai, wannan shegiyar diyar, me hali kamar na uwarta. Wai yanzu ma cewa tayi bazata shinkafa ba," Gwaggo ta fada, tana kara zabga ma Badiyya hararar tsana. "Inyeee! Lallai to ko uwarki ita taci ta girma, shegiya dangin bakin hali," fadar Larai egoistically. Haka sukata kyararta, sai zagin uwarta sukeyi, wanda hakan ya saka Badiyya kuka, tana kuka tana tura shinkafar badan dadi ba, tunano lokacin da suke zuwa gidan Gwaggo da Momynta tayi. Bayan ta gama cin abincin, taje da niyyar wanke kwanon, domin har yanzu bata manta da rules din Gwaggo ba, tsawar da aka doka mata ne yasa ta firgita hade da yarda plate din tangaran ya fadi, aikuwa cikin rashin sa'a ya fashe. "Yau na shiga ukku ni Binta, wannan diya dangin asara da bakar kafa, daga zuwanki har kin fasa mani plate, to wallahi ubanki zanci kafin uban naki ya dawo ya biya ni," Gwaggo na fadin haka tayo kan Badiyya gadan gadan, wanda Badiyya har ta kusa sakin fitsari dan dama tasan Gwaggo bazata taba sparing dinta ba. Aikuwa tana zuwa ta jawota ta cigaba da jibga, Badiyya sai ihu take, sai da Larai taga tayi likif sannan ta taso "Binta ya isa haka, kinsan yanzu mutane na shigowa kar ace wani mugun abu kike mata," Larai ke magana, tana wani kallon Badiyya, kallon kaskanci. "Tashi ki wuce daki," Gwaggo ta fada, tana hankada ta. Da gudu ta ruga dakin da take kwana idan tazo, kan gado ta fada, kuka ta cigaba dayi, sai yanzu ta yarda lallai Momynta ta rasu, kuma babu me iya rescuing dinta daga muguntar Gwaggo. Wani baccin wahala ne ya sace ta, tana bacci taji an daka mata duka a baya "tashi kije ubanki na kira, kuma saura kice mashi na bigeki, ya tafi in kara maki. Minahika me kama da uwarta," Gwaggo ta fada hade da mata kwanya saman kai. Sumu sumu ta tashi, tana fita falon Ahmad an zubo mashi lafiyaryar shinkafa da miya yana ci. Rabewa tayi daga jikin wata kujera,tana wasa da yatsunta. "Badiyya zoki zauna kusa dani," Ahmad ya fada, mouth full. Karkada kai tayi hade da gyara zamanta, ko dagowa ta kalli inda yake batayi ba. "Badiyya tsoron Dady kike yanzu? Taso kinji," cewar Ahmad yana daga hannunta alamar mikar da ita. Aikuwa tanajin hannunshi akan nata ta firgita, a take ta fara ja da baya, tana wani lumfashi kamar zata shide. Ganin haka yasa yayi saurin releasing hannunta, yama mata kallon rashin fahimta. Yanzu kuma tsoronshi takeji?. DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Be kara tanka ta ba, saida ya gama cin abincinshi sannan ya kalleta "Badiyya zomuje a siyo maki kaya," ya fada a raunane, yadda ta firgita ba karamin taba mashi zuciya yayi ba. Kin ko motsi tayi, saida Gwaggo tazo tayi mata magana sannan ta mike jiki babu lakka ta tafi. Koda suka shiga mota ko kallon inda yake batayi ba, sai rawar sanyi take tsabar tsoro, shi abun mamaki yake bashi bashi, ko me tagani? Kome yake bata tsoro haka. A kasuwar haka yaita daukar kayan ko kallon inda yake bata yi, kuma ko hannu bata saka ta dauka ba, ya gama jidar kayanshi yakai mota ta shiga suka tafi. Bayan sun isa ta dauki kayan ta tafi dasu dakinta, tabar Ahmad da Gwaggo na magana akan god knows what. Tana shiga dakin ta kwanta, kaf sai yanzu rasuwar Firdausi ke damunta, ba kamar dazu da taji Gwaggo da Larai suna zaginta, sai taji kamar taje ta shakesu suma su mutu. Tana nan zaune akayi sallar maghrib, fita tayi taje tayo alwalla, wajen dawowa taji an fisgota "Dan uwarki meyasa idan Ahmad yana maki magana baki amsawa? Kuma meyasa idan ya tabaki kike wani kamar zaki shide? Koda yake bazanga laifinki ba, dangin tsiya da bakin hali ne suka haiheki, shegiya uban yan jan sharri, yanzu da wani ya gani sai ace wani abu ai," Gwaggo ta fada, tana mata kwanya saman kai, itadai Badiyya ko kezau, bakuma ta dago ta kalleta ba. Har ta gama ta turata sannan ta wuce dakinta. Bayan tayi sallah, tana zaune Gwaggo ta kwala mata kira taje ta amshi tuwon dare taci tayi sallar Isha'i. Ta kwanta sai kuma ta tuno da camera ta, ai ta saka video ranar, bari ta dauko tagani, kila taga wanda ya buga Momynta. Taje ta lalubo camera ta, wanda ta zamar ma wata treasure, bayan ta zauna kan gadon, hannunta na rawa ta kunna hade da shiga ciki. Ta tsaya tana kallon video, wata zuciyar na ce mata ta kunna wata nacewa Aa, can dai tayi karfin halin kunnawa. Zaune taga Firdausi tana kallo abunta, amma ta lura da yadda take ajiyar zuciya, can sai taga Firdausi tayi hanyar kofa tare da saka hijab, alamun anyi knocking kuma namiji ne..........Kasa ida kallon tayi, nan take ta saki camera ta cigaba da kuka, she can't just believe it wai Momynta ta rasu, yanzu bazata kara ganinta ba kenan? Shikenan yanzu batada me santa. Su Uncle Musaddiq sun daina santa tunda har suka barta wajen Gwaggo. Kashe cameran tayi taje ta maidata inda ta daukota, dawowa tayi kan gadonta ta cigaba da kuka; daganan baccin wahala me cike da mafarkai ya kwashe ta. Cikin bacci taji an daka mata duka, "Tashi dan ubanki kiyi sallah, kin kwanta kina bacci kamar dangin asara," ta tsinkayo muryar Gwaggo na fadin haka, kuma tayi hanyar fita. "Saura ki ki tashi wallahi, in dawo inci uwarki shegiya dangin mayu," ta kara fada, hade da banging kofar. Badiyya kwakwalwarta tayi mata zafi, she's still a kid, bata taba experiencing wadandan abubuwan wahalar ba a rayuwa, batasan cewa akwai cruel mutane haka ba a duniya. Kuka ta fashe dashi, dan ba haka Momynta ta saba tana tadata sallah ba, kuma yanzu tana mafarkin Momynta ta dawo, ta fada mata karya suke mata cewar ta mutu, kafin ta maida mata amsa Gwaggo ta tashe ta. Tana cikin kuka ta tuna cewar Gwaggo idan ta sameta anan ba karamar wahala zata sha ba, sumu sumu ta mike ta wuce tsakar gida domin yin alwalla. Tayo alwallar ta dawo, sai rawar sanyi take; kasan cewar an fara sanyi. Har tazo zata shiga daki Gwaggo ta kwala mata kira, "kiyi maza kiyi sallar, ga wanke wanke can kiyi mani, idan kin gama ki share tsakar gidan," fadar Gwaggo, domin a cewarta yanzu ta hutu, kamar yadda Larai ta bata shawara, ta cigaba da wahalar da ita da aiki, har ta gaji ta gudu wajen dangin uwarta. Ita dama badan tanaso ta dauko ta ba, saidan Ahmad ya bukaci hakan, kuma bazata iya ce mashi A'a ba. Badiyya goge kwallar da tazo mata tayi, da hanzari ta shiga daki domin gabatar da sallar ta, tana gamawa ta fito ta fara wanke wanke, bayan ta idar kuma ta kama share tsakar gidan, bayanta sai rikewa yake. Tanayi tana kuka, dan ita a rayuwarta bata taba kwatankwacin irin wannan aikin ba, komai Momy keyi mata, ko kuma Ladi me aiki, amma yau gata tana sharar tsakar gidan Gwaggo. Ni kam nace yarinya bakiga komai ba. Da kyar ta gama sharar nan, ta koma dakinta wajen takwas na safe, ba karamar gajiya tayi ba, kirjinta sai heaving yake kamar me asthma. "Ina kike? Ko shikenan kin gama aikin," fadar Gwaggo cikeda kumfar baki. Ita kuwa Badiyya tanajin haka tayi maza ta kwanta a tunaninta idan taga tana bacci zatayi kyale ta. Ba'afi minti uku ba taji an watsa mata ruwan sanyi a jiki, firgigi ta tashi, hawaye na fitowa daga cikin idanunta. Wannan wace irin rayuwa ce? "Ki tashi dan uwarki kije ki share wajen awaki a boys quaters, ko ni kike nufin zanyi sharar wajen," Gwaggo ta fada, tana harararta kamar idanunta zasu fado. Badiyya rau rau tayi da idanu, "Gwaggo bafa ki fada mani da can ba," ta fada tana goge hawayenta da tafin hannunta. "Iyyeh! Lallai yarinya ta biyo halin uwarta, yanzu ni kike maida ma magana Badiyya? To dan uwarki ki tashi kije ki share wurin. Kuma daga yanzu ayyukanki kenan, kullun sai na kara maki wasu," Gwaggo ta fada, tana matse mata kunne. Badiyya ta saki kara "Gwaggo dan Allah kiyi hakuri," ta fada tana kuka. "Maza ki tashi ko sai naci uwarki," ta fada tana hankada ta. "Kuma ki cire wadannan kayan, dan idan kikayi mura bazan baki magani ba." Badiyya tana hawaye haka ta cire kayan jikinta ta chanza wasu sannan ta fita domin share wajen awakin. Bayan ta gama tazo ta zauna, domin wata irin yunwar azaba ke cinta, bata taba kaiwa karfe tara na safe batayi breakfast ba, amma ya zatayi? Dole sai Gwaggo ta bata. "Koni zanzo in kawo maki breakfast din?" Gwaggo ta fada daga falo. Tanajin haka tayi murmushin murna, hade da wucewa falon domin yin breakfast din. Tana zuwa Gwaggo ta turo mata cup din koko da bread, tsayawa tayi tana kallon abincin da Gwaggo. "Bazaki ci bane? Kin tsaya kina kallona kamar mayya," Gwaggo ta zabga mata harar hade da mata rankwashi bisa kai. "Gwaggo bana shan koko da bread, ki bani kosai," Badiyya tayi raurau da ido, dan bata saba shan koko da bread ba, saidai kosai. Shima sai sunje Kankia ne suke ci sometimes. "Ohhh Allah sarki ai ban sani ba, to karbi wannan," Gwaggo ta fada hade da mika mata tray din indomie. Takai hannu zata karba ta bige hannun, "shegiya kwadayayya kamar uwarta, yanzu da karba kuma zaki? Dalla matsa bani wuri, shegiyar yarinya mara tarbiyya. Maza ki shanye kokon nan tas ki bani kofi na," Gwaggo ta daka mata tsawa, aikau ba bata lokaci ta fara tura kokon tare da bread din tana kwalla. Wajen karfa daya saiga Ahmad yazo, yana zuwa ta koma daki ta rakube, domin yanzu ta tabbatar ma kanta duk wanda ya buga Momynta a bango namiji ne, dan haka bazata taba zama tare da namiji ba. Koda kuwa Sultan am ne! Kira Gwaggo ta kwala mata, hakan yasa ta fita falon badan taso ba, saidan yanzun wani irin bala'in tsoron Gwaggo takeji. Tana fita ta iske yanacin abincin rana, kallonta yayi, "Badiyya zo muci," ya fada cikin shigar lallashi, da murya tausassa. Kallon Gwaggo tayi taga ta zabga mata harara, maganarta ta jiya ta fado mata a rai, mikewa tayi jiki ba lakka ta karasa inda yake, plate dinshi ya ajiye gabanta tare da zama kasa kusa da ita, alamar suci tare. Saida takusa minti biyar kafin ta saka hannunta cikin abincin, ci suke ba wanda yayi ma kowa magana, amma mistakingly idan hannunsu yayi brushing sai tayi shuddering, nan take numfashinta zai fasa sama sama, kamar zata shide. Domin ita yanzu a rayuwa tsoron maza take, gani take kamar zasu kasheta yadda suka kashe Momynta. Da dai yaga kamar zata kware tsabar tsoro, sai ya zare hannunshi cikin abincin ya bar mata. Bayan ta gama ci ta kwasa taje ta wanke, ta dawo har zata wuce dakinta ya kara kiranta, "Badiyya zo mu zauna mana, ko gudun Dadynki kike yanzu?" Batayi magana ba tazo ta raba nesa dashi ta zauna, shima dan tasan Gwaggo sarai idan ya tafi tana iya jibgarta. Haka ya gaji da zaman ya tashi ya tafi bata ce mashi kala ba, Gwaggo sai janshi da magana take amma yaki kulata. Tashi yayi yabar gidan, zuciyarshi na mashi zafi, rayuwarshi Badiyya ce abu mafi soyuwa a wajenshi, amma meyasa yanzu take gudun shi? Meyasa yanzu take jin tsoronshi? Meyasa ko kusa dashi bata san zama. Badiyya mikewa tayi ta tafi daki ta kwanta, kamar jira take ta yada kafadarta kan gado; ai kuwa bacci yayi awon gaba da ita. "Badiyya kiyi hakuri kinji, Allah yana tare dake, kuma komai yayi zafi yana tare da sauki," fadar Firdausi, tana share mata hawayenta. "Momy ina kikaje kika barni gidan Gwaggo?, Momy meyasa zaki tafi ki barni," Badiyya ta rungume mahaifiyarta, tana matsanancin kuka. "Kiyi hakuri Badiyya, ba'a san raina na tafi na barki ba nima, haka Allah ya kaddara mana," Firdausi ta fada soothingly tana patting bayanta. "To Momy ance man kin rasu, Momy naga an buga kanki da bango, Momy waye ya bugaki?" Badiyya ta tambaya tana dagowa daga jikin mahaifiyarta. "Gaskiya ne Badiyya na rasu, kuma bazaki kara ganina ba. Sannan nan gaba zaki gano wanda ya bugani da bango. Kiyi hakuri ya ta, Allah yana tare da ke," tana fadan haka ta bace bat. Badiyya na farkawa daga bacci, hawaye shabe shabe kan fuskarta, tunowa da tayi Momynta tayi mata confirming tabbas ta rasu, anan take ta saki wata uwar kara, "MOMY!!!".Rayuwar Badiyya a gidan Gwaggo batayi mata dadi ba, gashi yanzu ko Ahmad din da yake zuwa ya daina, koda bata mashi magana ba, takan ji sanyi a ranta. Yau ta tashi da safe, feeling dizzy, domin yanzu bata samun hutu ko kadan, kullun sai tayi aiki, kuma abincin da Gwaggo zata bata ba isarta yake ba. Yanzu ko makaranta ta daina zuwa, dama tunda ta dawo bata koma ba, tanaso tayi ma Dadynta magana amma yabar zuwa. Bayan ta gama aikinta, taje tayi wanka, tana zaune taji Gwaggo ta kwala mata kira, ta tashi domin ta daura dan kwalinta, Gwaggo ta kara wani kiran. Jiki na rawa haka ta tafi, tana zuwa taje ta rakube "Gwaggo gani." Gwaggo harara tabita dashi, "Dan uwarki shine sai nayi maki kira biyu zakizo ko? Sannu Badiyya," mika mata plate din dumamen tuwo tayi "Ungo kici maza kije bakin round about ki siyo mani kayan miya." Badiyya tsayawa tayi tana kallon dumamen tuwon, ta saba duk ran sunday bata iyacin abinci sai tasha coffee. "Gwaggo coffee zansha." "Eh lallai yarinya, coffee ubanki, ko ki dauki tuwonan kici ko in ballaki wallahi," Gwaggo ta daka mata tsawa, amma Badiyya ko gezau. "Badiyya ki dauka kici, tun muna mu biyo wallahi," Gwaggo ta janyo ta tana tura plate din gabanta. Badiyya ko motsi batayi ba, balle ta nuna zata ci. "Wai ni zaki ma kafiya? To ko ubanki be isa ba balle ke, yau saina ci uwarki," ta mike tsaye, ta janyota tana jibga. Badiyya ba abunda yake fita daga daga idonta banda hawaye, taki ko motsi, kuma taki cewa tayi hakuri. Wani wurgi Gwaggo tayi da ita zuwa bakin kofa, zuwa lokacin Badiyya tayi ligib, ko motsi batayi. "Badiyya!!!" Musaddiq ya fada a rude, yana rikota. Domin tunda aka kawo Badiyya basuzo sun ganta ba, shiyasa yayi deciding akan zaizo ya ganta. Yana zuwa kuwa yayi gamo da wannan alamari. Dagota yayi, idonshi ya cicciko, "Wallahi hukuma zata rabani dake," ya fada yana ma Gwaggo wani irin mugun kallo, ranshi yakai kololuwa wajen baci. Gwaggo haka ta cigaba da banbami, amma ko kulata baiyi ba, yaje ya debo ruwa ya yayyafa ma Badiyya ta farfado, tana ganinshi ta fashe da kuka. Duk wani tsoron maza da take ta daina, domin dama yanzu shi kadai takeda assurance din bazai kashe Momynta ba. Amma bayanshi; batayi trusting kowa ba, koda kuwa Sultan am ne. "Uncle ka kaini wajen Momy, Uncle kasheni zatayi kamar yadda aka kashe Momy," Badiyya ta fada tana kuka, rayuwa tayi mata kunci. Ganin Musaddiq ba karamin hope ya bata ba. DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Baice da ita komai ba, haka ya dauketa suka wuce, suna fita yaga motar Ahmad tayi igniting off, da tsananin mamaki Ahmad ya fito yana kallonsu. Ganin Badiyya a hannun Musaddiq lifeless ba karamun mamaki ya bashi ba. Mika mashi hannu yayi sukayi musabaha "Musaddiq lafiya naga haka?" Ahmad ya tambaya, alamun neman karin bayani. Wani kallo Musaddiq ya watsa ma Ahmad "Dama ni nasan ba abun alkhairi yasa kace zaka daukota ba, an kashe mata uwa yanzu ma anaso a kashe ta," Musaddiq ya fada, yana yin hanyar motar da yazo da ita, ta wani abokinshi dake Katsina. Dakatar dashi Ahmad yayi "Ya kayi magana ban gane ba, kuma ka dauki yarinya zaku tafi," Ahmad ya fada, ranshi ya fara baci, ba abunda yake tada mashi hankali kamar matsalar Badiyya. Daya ga Musaddiq ba magana zaiya ba, saima wani kallo da yake binshi dashi "Badiyya zo ki fada man abunda ya faru," ya fada tare da saka hannu alamun zai dauketa. Hannunshi na tabata ta zumbura kamar zata fadi, anan take ta firgita, ta kankame Musaddiq tana nurfarfashi. Ahmad baisan lokacin daya fara hawaye ba "Badiyya dan Allah mena maki? Meyasa kike kina yanzu? Meyasa ko hannuna bakiso kiji jikinki," ya fada yana zubar hawaye. Ba Badiyya kadai ba, har Musaddiq sai daya tausaya mashi, domin sun sanshi da tsananin taurin rai. Tsayawa Badiyya tayi tana kallonshi, hawayen data gani idonshi yasa ta tuno Momynta, nan take tayi tsalle ta rungume shi. Wani irin kuka suka saki a tare, ba wanda yake lallashin wani "Dady, Momyna," shine kawai abunda Badiyya ke furtawa, shi kuwa ya rungume ta tsam, wasu hawaye masu zafi na zuba daga idanunshi. Musaddiq shima hawayen ya share, sannan yaja Ahmad ya mishi bayanin abunda ya gani, kuma ya mishi kashedi akan ya lura da harkarta inba haka ba zai dawo ya dauketa. Ahmad ba karamin bacin rai yaji ba, a tunaninshi Gwaggo tana kula da Badiyya, ashe shiyasa Badiyya ke gudunshi? Ashe shiyasa bata sakin jikinta, nan take ya share hawayen idonshi ya nufi cikin gidan. Gwaggo na ganinshi dauke da Badiyya munta ta duri ruwa, nan ta fara inda inda "Malam Ahmad anzo kenan, to bismillah,ka sh..." wani kallo daya bita dashi ya sanya ta gumtse bakinta. "Yaya a rayuwa ke na tashi nagani a matsayin uwa da uba, kece kika raineni har na girma, ke kike mani komai a rayuwa har nayi hankalin yima kaina. Ashe dama Yaya bazaki iya rainan gudan jini na kamar yadda kikayi mani ba? Ashe dama bazaki so Badiyya kamar yadda kika so ni ba? Ban taba tunanin tsanar da kika ma Firdausi zata koma kan Badiyya ba. Nagode," ya fada, ya ajiye Badiyya kan kujera ya dauko mata ruwa tasha. Gwaggo batace komai ba, tayi tsuru tsuru, kasa bashi hakuri tayi ma. Sunanan zaune sai jan Badiyya da labari yake, itama tayi giving in, anan take fada mashi tanasan taje makaranta, wanda yayi mata alkawarin gobe Monday zai maidata Saldefi. Bayan sun gama maganarsu, ya tashi zai tafi ya juyo ya kalli Gwaggo wadda tun dazu take kallonsu, bakin ciki yai mata tsaye. "Yaya ni zan tafi, kuma wallahi na dawo naga Badiyya ko kwarzane a jikinta, kinsan what I'm capable of doing, kinfi kowa sanin yadda zuciyata take," yana fadar haka ya juya yayi ma Badiyya murmushi sannan ya juya ya tafi. Badiyya na ganin ya tafi ta mike sum sum ta wuce daki, ita kuwa Gwaggo abun duniya ya mata yawa. Ahmad bai taba buda baki yayi mata musu ba balle bakar magana, amma yau gashi saboda diyarsa ya gaya mata magana, harda mata kashedi. Kuma tasan tabbas he meant it, zai iya yin komai tunda har ya furta, dan shi baya magana biyu. Tana cikin wannan tunanin Larai ta shigo, har ta zauna taga mutuniyar bata kula ta ba "wai Binta meke damu ki? Tun dazu na shigo amma baki lura ba." Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke, sannan ta labarta mata komai, zama tayi tai jugum sai daga baya wani mischievious smile yayi plastering a face dinta. "Karki sake ki dauki wannan a matsayin matsala, ni inada shawara, amma sai kin yarda," ta fada tana matsowa kusa da ita. Gwaggo gyara zama tayi, "inajinki Larai, kome nene zanyi wallahi, abun ya tada mani hankali. Yaron nan bai taba koda mani musu ba, amma yanzu hada bakar magana, kuma kinsan shiyake mani komai, in yayi fushi bansan yadda zanyi ba," ta fada hade da goge wata irin zufa data keto mata. "Yauwa.... kinga dama yarinyar nan, Adama, wata biyar da suka wuce mijinta ya saketa, kuma ta gama idda. Mezai hana kawai ya aureta, in yaso ita can ta cigaba dacin uwarta," Larai ta fada tana murmushi. "Hmm Larai kinsan halin Ahmad dai, tun tuni mukaso hadasu aure yaki,kina ganin zai yadda ne yanzu?" Gwaggo ta fada, alamun babu nasara. "Aa nasan bazai yarda ba, wajen wani Malami zamuje ya hadasu, in yaso sai musa a raba shi da diyar, kinga daganan ana iya cin uwarta hankali kwance," Larai ta fada, tana fadada murmushinta. "Tabbas hakane, to yaushe zamuje wajen malamin? Kinsan fa Ahmad ya dau zafi, kuma kinsan yadda zuciyarsa take." "To malamin ba'a ganinshi sai ran Juma'a, sai mu bari sai ranar," Larai ta fada, wani irin farin ciki ya saukar mata, ganin burinta ya kusa cika. "To Allah ya nuna mana, tabbas sai Firdausi tayi dana sanin auren Ahmad, ita kuma wannan diyar sai ta gwammace batazo duniya ba,"Gwaggo ta fada tana wata irin dariyar mugaye.Tunda Larai ta tafi,Gwaggo bata kara kulata ba, da asuba ta shiga ta tada ta tayi sallah, tana gamawa taje tana wanke wanke, bayan ta gama ta fara shara. Jin karar ana shara yasa Gwaggo fitowa, tana fitowa taga Badiyya ta dage sai shara take, ga kayan wanke wanke a gefe, da sauri ta karbe tsintsiyar "Yanzu Badiyya tsabar minahinci kinji abunda ubanki yace jiya amma shine kike wata shara ko? Tsabar kinasan rabani da dan uwana ko? To ta Allah ba taki ba, kafin ki rabani dashi nizan rabaki dashi. Munafukar Allah," Gwaggo ta fada tana harararta, ta dauki tsintsiyar tayi wurgi da ita. Nan ta barta tsaye tayi hanyar Falon "kuma daga yau karki kara wani aikin, har zuwa lokacinda zanyi maganinki keda ubanki," tana fadar haka ta wuce. Badiyya saida ta kusa minti biyar a tsaye tana tunanin wannan sudden change din daga wurin Gwaggo, can kuma ta tuna yau Daddy zai kaita makaranta, nan taje ta dibi ruwa ta kai toilet tayi wankanta. Kayan da Ahmad ya siyo mata ta saka, zama tayi tai jugum, tunanin rayuwarta take, yanzu Dady ne kadai gatanta, kuma shi kadai zata rika sakarma fuska, babu ruwanta da maza, koda kuwa Sultan am ne. Kiran da Gwaggo ta kwala mata ne yayi jolting dinta out of her reverie, tana fitowa ta iske Gwaggo ta ajiye mata plate din kwai da bread, sai tea a gafe. Wani irin murmushi tayi, wanda tun bayan rasuwar Firdausi bata kara irinshi ba. Zama tayi dirshan kasa, ta fara ci, tunda Momynta ta rasu rabanta da taci abinci mai kyau da yawa haka, tana zaune tanaci kamar wadda ta shekara bataci abinci ba, haka Ahmad ya shigo ya isketa, wasu unshed tears ya goge sannan ya karaso ciki. Murmushi yayi hade da zama kusa da ita, tana juyowa ta ganshi, murmushi ta mishi mai kyau, "Dady ina kwana?" Ta tambaya, hade da shanye sauran tea din. "Lafiya kalau Badiyya, yar Dady ta shirya ko?" Ya tambaya yana riko hannunta. Daga mashi kai tayi hade da niyar fita, kwanukan a hannunta. Rikota yayi, "Badiyya ina zaki? Taho mu tafi kawai," raurau tayi da ido, dan tasan idan bata wanke kwanukan nanba Gwaggo dukan tsiya zata mata. Girgiza mashi kai tayi "Dady zan wanke kwanukan ne," ta fada, tanayin hanyar fitan. "Ke zaki wanke kwanunkan kuma? Kankan yabar zuwa ne?" Ya tambaya, bamboozled. Dan yasan Kankan shike ma Gwaggo komai, yayi sharar tsakar gida, wanke wanke, ya share wajen awaki, sannan kuma yayi gadi. "Ni bansan koya daina zuwa ba, amma kullum ni nake share ko ina, kuma nayi wanke wanke. Nidai Dady kabarni inje in wanke, kafin Gwaggo ta fito," ta fada, hade dayin hanyar wajen. Fizgo ta yayi, kwanukan ya karba ya ajiye a kasa, "ki jirani ina zuwa," yadda yayi maganar ya nuna mata tabbas ranshi ya baci, ita kuwa bada wani abun tayi ba, kawai fada mashi tayi. Nan take yayi hanyar dakin Gwaggo, Gwaggo wadda tunda yazo take labe tanajinsu, tana ganin yayo hanyar dakinta jikinta ya fara rawa, dakinta tayi sauri ta koma ta fara dube duben karya. Yana shigowa ta washe baki "Ahhh Malam Ahmad, mun kwana lafiya?" Yadda taga ya hade rai ba karamin bata tsoro yayi ba. Girgiza kai yayi, trying so hard not cry "Yaya, kin kyauta da abunda kikayi, kuma wallahi indai wani abu ya sameta sai na dauki mataki. Nagode sosai da saka Badiyya aiki, inhar wani ciwon ya kamata wallahi sai na saka mata," yana fadar haka ya fita, binshi tayi tana "Ahmad tsaya ka saurare ni, kayi hakuri dan nan," amma bai saurare ta ba, tana fita falo taga Badiyya, sai maganarta ta koma ciki. Baice da ita kala ba, saima kama hannun Badiyya da suka fita waje, ko kara kallon inda take baiyi ba, ita kuwa Badiyya duk ta tsure. Suna fita yaga Kankan yazo yana washe mashi baki, hade rai yayi "Kankan meke hanaka zuwa aiki?" Kankan inda inda ya fara, koda ya kalli Ahmad, bai taba ganin irin expression din a face dinshi ba, he knew not to lie "Alhaji ai Hajia ce tace nabar shiga ciki, na tsaya a gadin kawai," ya fada bawai dan yaso ba, dan Gwaggo tayi warning dinshi akan karya fadama kowa. "Idan ka kara missing day daya, a bakin aikinka," Ahmad yana fadan haka yaja hannun Badiyya suka shiga cikin mota. Haka ya tsaya a ali cook yayi mata takeaway na snack da youghurt, domin tayi break na school, bayan sunje school ya gama filling komai anan ya barta ta shiga class ya wuce. Badiyya na shiga class Momynta ta fado mata a rai, hawaye har sun fara cika mata ido, sai friends dinta sukazo kowa yanata murna, domin Badiyya akwai shiga rai. Bayan sun tashi ya kaita taci abinci sannan ya maidata gida, ko gidan bai shiga ba ya kara gaba. Badiyya na shiga, sum sum ta wuce daki, jakar books dinta da ledar unifoam dinta ajiye akan gado sannan ta kwanta bacci, dan saida Ahmad ya siya nata abinci sannan. *** Gwaggo kiran Larai tayi a waya, akan tazo tana nemanta urgently. Ba'afi five minutes ba saiga Larai, dayake munafurci ake shirin kullawa, kuma hadi da abun ita zaiyi benefitting. Zama tayi gefen Gwaggo, ita kuma Adama ta zauna a wata kujerar, dafa kafadarta tayi "Binta ki daina damun kanki, fada mani meya faru," Larai ta fada placatingly. DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Gwaggo ta numfasa sannan ta shiga basu labarin abunda ya faru, shiru sukai suna kallonta, da taga shirun yayi yawa "Larai ba abunda za'a iyayi har juma'ar ko?" Gwaggo ta tambaya da worried face. Shiru Larai tayi, saican Adama ta fara magana "Ni ina ganin muje wajen Malamin nan na hanyar Jibiya, inyaso shi ya hada auren, shi kuma na ranar Juma'a sai ya raba tsakaninsu," ta fada tana murmushi, dan dama ita tun kafin tayi aure takesan Ahmad, dan yaki yarda ne ta hakura. Dukkansu murmushi sukayi, "Idan Allah ya kaimu gone ai sai mu tafi," Gwaggo ta fada tana fadada murmushinta. A tare suka amsa da "Amin" farin ciki fal cikin ran Adama, domin Allah zai mallaka mata masoyinta.

0 Comments