RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 2

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 2
A haka a rungume suna kuka har Badiyya tayi barci, bayan Firdausi ta tabbatar baccin yayi nisa, sai ta dauketa ta ajiye kan gado. Ta dawo ta cigaba da hada kayan Badiyya, tana yi tana kuka. Ita yanzu in tace ta koma Kankia ya zata yi? Aikin ta fa? Wanda tasan shi zai rufa masu asiri, dukda Allah nanan. Lokacin data gama hadan kayan Badiyya tsaf, har daya na dare tayi. Batabar ko tsinke a wajen ba, saboda bata da niyyar dawowa gidan, koda taso hakan; bataga alamun hakan a idon Ahmad ba. A haka ta tashi ta wuce dakinta, ta janyo troleys dinta ta shiga hada nata kayan, bata gama ba har saida ukku na dare tayi. Tana gamawa taje dakin Badiyya. Data shiga dakin, ta hango Badiyya ta makure, daga gani baccin bana kwanciyar hankali bane. Zama tayi gefen gadon ta kurama Badiyya ido, domin tana tausayin yarinyar, ita yanzu ta fara rayuwa. Ita tayi yarintarta cikin aminci da kulawar iyaye, amma Badiyya bata samu hakan ba, tun tana yar kankanuwarta damuwa ta fara samun mazauni a cikin zuciyarta. Da taga zaman bazai amfaneta da komai ba, saita tashi ta dauro alwalla, tazo ta tada sallah, tanayi tana kuka. Ita yanzu ya zata yi? Ba Baba, ba Mama, kannenta duk matane, kuma kowacce na gidan mijinta, kaninta daya; Musaddiq, shima yarone. Tana nan zaune tana karatun Al-Qurani, in abun ya tunkuro mata sai ta tsaya tayi kuka iya yinta, sai ta gaji dan kanta sai ta cigaba. A haka har aka fara kiraye-kirayen Sallah. Ta tashi daga zaunen da take, ta tada Badiyya domin ta gabatar da Sallar Asuba su tafi; bataso gari ya waye masu cikin wannan bakin gidan, wanda ba komai cikinshi sai bakin ciki ta takaici. Badiyya na farkawa, ta tsaya tana kallon mahaifiyarta; wadda a yanzu har idanunta sun fada. "Momy zamu tafi din?" Ta fada, daga yanayin da maganar ta fito za'a gane da abun ta kwana cikin ranta. "Badiyya na fada maki tun jiya ai ko?" Firdausi ta fada tana mai mikewa tsaye, domin batason yarta taga weak side dinta. Not in this kind of situation. "Ki tashi kiyi Alwalla, kizo muyi sallah." Ta fada, tana komawa saman dardumar; hade da cigaba dayin lazuminta. Badiyya batace komai ba, domin yanzu yawan damuwa yasa ta fara gane yanayin mutane, a lokacin da mutane kesan magana da lokacin da basu so. A hankali ta turo kafar bayin, tana fitowa ta hango kayanta hade da hijab dinta; daga gani su Momynta ke nufi zata saka yau. Daukar hijab din tayi hade da fadin. "Momy mu fara." Firdausi bata ce kala ba, ta mike suka tada sallah. Suna gamawa Firdausi ta kalleta cikin kulawa. "Badiyya, kije kiyi wanka, yanzu zamu tafi." Ta fada, tana kallonta cikin sigar damuwa. Badiyya ta turbune fuska, "Momy, mu bari sai gari yayi haske." Ta fada, idanunta na kawo ruwa. "Kuma bazanje makaranta ba?" Ta tambaya, alamun rashin jin dadi a maganarta. "Zakije Badiyya, yanzu so nike inje in nemi transfer." Ta fada mata, domin ta kwantar mata da hankali. "Ki tashi, kinga Dady yace karmu kai karfe tara. Kuma kinga kema karki makara school." Ta fadi tana yin hanyar waje. Badiyya ta mike zata cire kayanta. "Momy ke ina zaki?" Ta tambaya. "Zanje na hada maki breakfast, kafin ya dawo." Ta fadi tana rufo kofar dakin. A haka Badiyya ta shiga shiga wanka, tana fitowa taga ba uniform dinta, data duba inda ta saba ajiyesu sai tagani. Ta tabbatar Firdausi mantawa dasu tayi da tasakasu cikin akwati. Firdausi tana fita ta kira Malama Rukayya ta fada mata, domin mijinta a ministry of education yake aiki, taji ko zata samar mata da transfer. Aikuwa cikin sa'a aka samu, tace dama ana neman teachers a Dutsin-ma sai dai nan gaskiya. Wanda ita Firdausi ba haka taso ba, taso ace ta samu Kankia. A haka dai ta mata godiya, wanda ita Malama Rukayya ta shaida mata zuwa gobe transfer zata fito. STORY CONTINUES BELOW  Tana fitowa daga kitchen, tray din toasted bread da tea na hannunta sukayi kacibus da Ahmad. Wani kallo ya wurga mata "Me zaisa kiyi amfani da kayan abincina? Ai inace kinada kudi ko?" Ya tambayeta cikin sigar wulakanci. Girgiza kanta tayi alamar he get it wrong, ita har wani appetite din cin abinci gareta? "Kayi hakuri, bani zanci ba, Badiyya zata ci." Ta bashi amsa, murya can kasa. Tsaki kawai yayi ya wuce dakinshi, binshi tayi da kallon mamaki, bata taba tunanin zaiyi turning into something vulgar ba. A haka ta iske Badiyya tayi shirinta tsaf, tana saka kwalli ta sameta a dakin. Murmushi tayi hade da ajeyi tray din. "Su Badiyya yau hada kwalliya?" Ta fada, murmushinta na fadada, domin ganin yarinyarta cikin walwala yana sakata nishadi. "Kai Momy, kwalli ne fa." Ta fada, tana zumburo baki, alamun shagwaba. "To yi hakuri, yau yan shagwabar sun taso." Ta fadi tana dariya. Murmushi Badiyya tayi, hade da zama kusa da ita, ta janyo tray din. "Momy, kizo muci." "A'a Badiyya, kedai kici." Ta fada tana mata murmushi. Badiyya ta kyabe fuska. "Momy please." "Allah Badiyya kici, innaje school zan sayi abu naci." Ta bata amsa, daga haka Badiyya bata kara cewa komai ba ta fara cin abincinta. A haka ta gama ci suka fidda kayansu kaf! Firdausi ta juyo ta kalli gidan, kallon karshe. A haka ta fita daga cikin gidan, zuciyarta na mata nauyi. *** Firdausi taje school dinsu tayi informing dinsu akan zata chanza gari, tayi signing out abubuwa da komai da komai. Sunyi sallama da dukkan Malaman, domin Firdausi mutun ce mai Al-umma. A haka da aka tashi taje ta dauko Badiyya, daga Saldefi direct suka nufi hanyar Kankia. Suna shiga garin tayi hanyar Bakin Kasuwa, inda gidansu yake. Bayan sun shiga sunyi exchanging pleasantries, an kira su kausar an fada masu, koya yanata jajanta abun. Suna zaune sunci abinci, kewar Mahaifanta na kara yawaita cikin zuciyarta, inta juya ta kalli dakin Mama da Baba; sai taji dama zataga sun fito suna mata wannan murmushin nasu me cikeda kauna, farin ciki da annashuwa. Wajen karfe tara akace ana sallama da Firdausi, da har bazata je ba sai Musaddiq yace taje may be Ahmad ne. Fadan haka yasa tace Badiyya su tafi tare. Suna fita Badiyya ta hango Sultan, ai da gudu ta ruga ta rungume shi, "Sultan am, Dady ya kore mu." Ta fada hade da fashewa da kuka. Hugging dinta back yayi, yana patting bayanta. Dazu da Abbanshi yazo yace mashi zaije Kankia, shine yake fada mashi wai Ahmad ne ya saki Firdausi; zaije ya bata hakuri. Dakyar ya samu ya taho dashi saboda yasan Badiyya tana cikin wani hali, domin dukda halin Dadynta; ba karamin so take mashi ba. "Sultan am, ka kaini wajen Dady, wallahi nayi missing dinshi." Ta fada, wasu hawayen na fitowa daga idonta. Shi kanshi Sultan dauriya yake, amma ya kusa hawayen. He know how it feels when missing one of your parents. Da kyar ya iya bude baki, "Badiyya kiyi hakuri kinji ko?" Ya fada cikin sigar lallashi. Daga Firdausi har Kamal tsayawa sukayi suna kallansu, kowa da abunda yake ayyanawa a ranshi. Kamal ne ya fara dauke idonshi daga kansu. "Firdausi ya kuma mukaji da abunda ya faru?" Ya fada, fuskarshi na nuna alamun damuwa. "Hmm... bari Kamal, Allah dai ya kyauta." Shi kawai ta iya furtawa, domin bakinta ba abunda zai iya fadi a yanzu. A haka suka cigaba da magana, suma Sultan da Badiyya suna tasu maganar in a hushed tone. "Sultan, kazo mu tafi, dare yayi." Kamal ya fada yana kallon agogon hannunshi. A haka suka tafi har wajen mota tana makale dashi, da kyar ya samu ta rabu da jikinshi ya shiga mota. Zuciyarshi duk ba dadi. Firdausi haka taja Badiyya suka shiga, tanata wani irin kuka. Bakin ciki yai mata yawa, ga rashin ganin Dady, ga yanzu Sultan am ya tafi. Shikenan bata kara ganinshi. Su Kamal kuwa tunda suka kama hanya ba wanda yace kala, shi Sultan tunanin halinda yabar Badiyya yake. Shi kuma Kamal; tunanin kusancin dake tsakanin Badiyya da Sultan yake, Maimuna tasha fada mashi sun shaku amma be taba kawo kusancin ya kai haka ba. Bayasan tai experiencing rayuwa irinta Firdausi, she've had alot. "Sultan, karka yaudari yarinyar nan, ka rike amana, kar kayi mata rikon da Ahmad yayi ma Firdausi ba." Kamal ya fada, hankalinshi yana kan titi. "Abba wa?" Ya fada, alamun rashin fahimta karara kan fuskarshi. "Badiyya mana." Kamal ya bashi amsa. "Abba ai ba wani abu tsakaninmu." Sultan ya fada da niyar kare kanshi. "Hmm.. yaro yaro ne." Kamal ya fada da wani murmushi plastered on his lips.Badiyya cikin dare haka taita maimaita sunan Sultan, ita Firdausi abun har ya fara bata tsoro, kardai yarinyar nan har soyayyar Sultan ta shiga ranta? Abunda yake tsaya mata a rai kenan.+ A bangare Sultan kuwa; kwana yayi abun ya tsaya mashi a rai, domin shi bai taba kawo wani abu cikin ranshi ba, hasalima ya dauki Badiyya a matsayin kanwarshi, saidai dukda matsayin daya bata; yasan ta taba wani bangare a cikin rayuwarsa, wanda saida Kamal yayi magana sannan ya fara realizing. Da sassafe Firdausi ta tada Badiyya, bayan tayi mata wanka ta shirya ta, suna breakfast; wanda Firdausi ce ta bada aka siyo masu koko da kosai, domin Musaddiq kadai ke zama cikin gidan, babu kayan abinci. "Nikam Musaddiq, ya zanyi da Dutsin-ma? Ko zuwa zan rikayi kullum ina dawowa?" Firdausi ta fada, yadda tayi maganar yana nuna ta rasa mafita, batasan me zatayi ba. "Ayi haka kuwa, Adda Fiddi?" Ya amsa tambayarta da wata tambayar. "Kudin mai ai zaiyi yawa, kuma yaushe kika tashi har ki isa Dutsinma." Ya kara fadi, hade da juya kanshi. "Nima ina tunanin haka Musaddiq, amma yanzu ya za'a yi? Kaga yau zanje Katsina in karbo transfer, sai in karbo transfer letter Badiyya." Ta fada, tana satar kallon Badiyya, domin batasan ya zata dauki maganar chanza nata makaranta ba. "Yauwa!! Akwai wani gida da aka bani cikin gado na, sai kije ki zauna." Musaddiq ya fada, yana murmushin gano mafita. "Gidan yana Unguwar Rimi." "Lahh! Ni nama manta da gidannan wallahi." Ta fada, murmushi bayyane kan fuskarta. "Nagode, Allah ya bar zumunci Musaddiq." "Kai Adda Fiddi, miye na godiya kuma dan Allah? Miye a ciki danna baki gida ki zauna? Dan Allah ki daina." Musaddiq ya fada, fuskarshi na nuna alamun baiji dadin godiyar data mashi ba. "To Musaddiq, Allah yabar zumunci." Ta fada tana murmushi, hade da patting cinyarshi alamun jin dadi. Musaddiq mikewa yayi, ya kalli Badiyya; wadda tayi shiru tana kallansu, domin ita yanzu burinta daya; ta ga Sultan. Chanza mata makarantar da za'ayi bai wani daga mata hankali ba. "Badiyya, zo muje ki rakani bakin kasuwa." Musaddiq ya fada, yana mikewa tsaya. Badiyya bata furta komai ba ta tashi tayi entwining hannayensu, daga haka suka fita. "Kuyi sauri fa, yanzu zamu tafi." Firdausi ta fadi da yar kara, domin suji abunda take fadi. Suna fita da Musaddiq yaje ya siya ma Badiyya chocolates, da kayan zaki, domin ya lura she need someone to vulgarize her back into her jovial self. A haka ta nuna mashi farin cikinta, wanda har dariya tai mashi, abun ba karamin dadi ya mishi ba. Suna komawa gida suka iske Firdausi ta fito, harta handbag dinta na hannunta. "Badiyya taho mu tafi to, tunda baza'a mani tayin chocolates dinba." Firdausi ta fada da sigar wasa, tana me jan hannunta. "Kai Momy, kinsan fa ina baki, ko Dady idan ya siyo man ina baki ai." Badiyya ta fada tana zumburo baki. "Kyaleta kinji Badiyyar Uncle, ku tafi kar kuyi rana." Musaddiq ya fada, yana shafa kanta alamun tayi shiru. "Bye Uncle, zance Sultan am ya turo mani pictures dinmu wayar Momy sai ka gani ko?" Ta fadi tana washe baki, domin a ganinta dole Momy ta kaita gidansu Sultan am. "Yauwa My Bady, kice ya kara daukarki wasu ma." Musaddiq ya fada yana murmushi, domin ya lura maganar Sultan kadai ke sakata farin ciki. "To Uncle karka damu." Ta bashi amsa, tana me shiga motar. "A gaidaman da Sultan am." Musaddiq ya fada da karfi. A haka suka tafi tana ta shan chocolates dinta, itadai Firdausi kallonta kawai take. STORY CONTINUES BELOW  Suna isa garin Katsina, Badiyya tayi rau rau da ido. "Momy, muje gida ko?" Ta tambaya. "Badiyya, kinaso in bata maki rai ko?" Firdausi ta fada cikin fushi, domin bataga dalilin da zaisa ta damu da mahaifinta ba, wanda ya watsar da ita kamar ba daga jikinshin ta fito ba. "To gidan su Sultan am fa? Inaso naganshi Momy, kinga fa yace school zai koma." Ta fada, alamun san yin kuka karara a fuskarta. "Wai Badiyya meke tsakaninki da Sultan dinnan ne?" Firdausi ta tambaya, saboda ita tsoro da haushi abun yake bata. Instead of ta tsaya tayi karatu, bata so soyayya ta shiga ranta at this age, though abun is not that serious, amma ai with time. Ita bacin karatunda tayi ai da yanzu batasan yadda zatayi ba. "Momy, Yayana ne fa. Nidai gaskiya ki kaini wallahi." Badiyya ta fada, tanata zumburo baki alamar zatayi kuka. "Ki bari muje school dinku sannan, wai yanzu ma abun school din baya damunki ko? Lallai Badiyya, wallahi na lura yanzu hankalinki yana kan Sultan." Firdausi ta fada, tanayin hanyar da zai sadata da Layout. "Kai Momy, wallahi Aa, banaso na kara saka maki damuwa shiyasa na nuna kamar ban damu ba, amma wallahi na damu." Ta fada, tayi narai narai da ido. "Kuma idan naga Sultan am hankalina zai kwanta, sai nazo kema na kwantar maki da naki." Jin abunda Badiyya tace yasa Firdausi yin shiru, domin tasan tabbas Badiyya yarinyace ta gari, kullun burinta shine ta faranta mata. A haka suka isa bakin gate din gidan su Sultan, Badiyya ta sauki ta tsaya taga Firdausi bata fito ba. "Momy, ke bazaki shiga bane?" Ta tambaya, tana me kare mata kallo. Kafin Firdausi ta bafa amsa saiga Sultan ya zo zai shiga gidan, da leda hannunshi, alamun daga shago yake. Da hanzari ya nufi inda Firdausi take, "Anty ina yini? Anzo lafiya?" Ya fada yana russunawa, domin shi yanzu kunyarta ma yake ji, tunda Abbanshi yayi mashi magana jiya ya fuskanta sosai da abunda yakeji game da Badiyya. Saiyasa ya yanke shawarar daina kula Badiyya a gaban iyayensu, har sai ya tabbatar da abunda yake feeling towards her. "Lafiya lau Sultan dinmu, yanzu mutuniyarka ta hanani sakat, wai ita a kawota taga Sultan am." Firdausi ta fada tana dariya. "To Badiyya ga Sultan am, ni zan tafi kinji."2 Daga mata kai kawai Badiyya tayi, har ta fara tafiya ta dawo, "Sultan bani number ka, idan na dawo sai na kira." Ya karbi wayar ya bata number, tana juyawa ta tafi ya kama hannun Badiyya, "kanko a mauni (kinyi kyau)." Ya fada yana murmushi, kallonshi tayi itama tayi murmushinta. Tsayawa tayi tana kallon yanda dimples dinshi suka lotsa. Daya lura da abunda take kallo, "Badiyya, me kike kallo." Ya tambaya yana kara mata murmushi.2 "Gani nayi kumatun kowa lafiya lau, amma naka yaji ciwo." Ta fada, alamun tausayi karara kan fuskarta. Wata irin dariya yayai yasa suka kara lotsawa, sauri tayi ta rike hannunshi. "Sultan am, ka daina dariyar, wallahi deepening abun yake." Ta fada, tana janyo shi iya yadda zata iya taba wajen, hannu takai wajen kumatun, a hankali ta taba wajen kamar yace mata da zafi. "Da zafi ko Sultan am?" "Aa Badiyya babu zafi, muje ciki akwai abunda zan miki suprise dashi." Ya fada yana jan hannunta, a haka suka karasa parlour. Suna shiga, tana jiyowa domin neman wajen zama idonta ya hadu dana Ahmad, wata irin ta saki. "Dady!!! Wayyo Dady na." Ta karasa da gudu ta rungume shi, wasu hawayen da batasan tanadasu ba suka fara zubo mata.2 Rungumeta yayi tsam, shi kanshi yayi missing Badiyya. "Badiyya ta, ya kike? Nayi missing dinki My Bady." Ya fada a hankali, wanda iyakar kunnenta kadai zaiji. A haka saman cinyarshi sukaci abincin rana, yau Badiyya ko wajen Sultan bataje ba. Kamal sai kallonsu yake, bakin cikin yana taso mashi, saboda yasan Ahmad yayi ma kanshi asara, tunda har ya rasa Firdausi da diya me sonshi. Badiyya na kan cinyar Ahmad, sunata magana wanda ba wanda yakejin me suke cewa. Wayar Sultan tayi ringing, daga da idonshi yayi ya kalli Badiyya; wanda ta sakar mashi da wani fleeting smile. Yana dauka, "To Anty, yanzu zata fito." Haka kawai ya furta, a hankali Badiyya ta sauko daga jikin Ahmad, ta kalleshi; kallo me cike da manufofi, na farko shiya ja masu, shi yace su tafi, gashi kuma yanzu tana san zama da mahaifinta, amma bazata iya barin Momynta ba. Dakyar aka samu Sultan yajata suka nufi gate, tanata kuka, shima Ahmad daga gani juriya yake; ya fara reaping what he sow. Dan koda Kamal yace suje yaga Firdausi kiyawa yayi, baisan da wane ido zai kalleta ba.2 "Badiyya kiyi shiru kinji? Banso kiyi ciwon kai, zan kira Anty anjima." Sultan ya rada mata cikin kunne, nodding kanta tayi alamar tagane. Share mata hawaye yayi sannan ta zauna, Firdausi batace kala ba; dan tayi tunanin kukan rabuwa da Sultan takeyi. A haka suka isa Kankia, ba wanda yace kala. *** Bayan sunci abincin dare; wanda Firdausi ce ta siyo kayan abincin yau. Suna zaune sukaga hawaye nabin kuncin Badiyya. "Badiyya lafiya? Meke faruwa?" Musaddiq ya tambaya a rikice, abun ya bashi tsoro, yarinya karama; amma har tasan tayi zaune tana tunani harda hawaye?. Ita Firdausi duk a tunaninta rabuwa da Sultan yasa take kukan, "Tashi ki wuce daki." Ta fada da yar tsawa, domin ita abun ya isheta. Sum-Sum Badiyya ta mike ta shiga, tana kwance daki Firdausi tazo ta sameta, zama tayi gefenta hade da tada ta zaune. "Badiyya tunda dai kuka zaki rikayi idan kinga Sultan, to Allah bazan kara kaiki ba." Firdausi ta fada, alamun rashin jin dadin abun. "Wallahi Momy badan saboda naga Sultan am nake kuka ba." Badiyya ta amsa a raunane. "To saboda me kike kuka?" "Yau nefa naga Dady, shima yace yayi missing dinmu, nama fada mashi zamu koma Dutsin-ma to shine yace zaizo." Badiyya ta fada mata, wasu hawayen na fita daga idonta. "Badiyya meyasa kika fada mashi?!" Firdausi ta fada, alamun kwata kwata bataso hakan ba. "Momy kiyi hakuri, nayi missing dinshi shiya sa." "Koma ki kwanta." Shi kadai Firdausi ta fada, hade dayin hanyar waje. Da sassafe Firdausi ta tashi, ta tada Badiyya domin suyi wanka, bataso ta makara a ranar zuwanta aiki na farko, gashi zataje tayima Badiyya registration a Demonstration primary school. Firdausi ta hada masu tea da bread hade da kwai, suna zaune suna ci hada Musaddiq, kallon Badiyya tayi taga tayi shiru, alamun damuwa karara akan fuskarta. Allah yasani wannan damuwar ta Badiyya na damunta, kar wani ciwon yaje ya hauta tun tana yarinya. Ta bude baki zatayi magana kenan ringing din wayarta ya katse ta. Kallon Badiyya tayi, wani murmushi na samun mazauni akan labbanta, tasan koba komai, yin wayar zai sakata ta danyi nishadi. "Hello Sultan." Firdausi ta fada, tana kallon Badiyya. Dago ido tayi, jin an ambaci sunan Sultan, amma sai bata ce komai ba, saboda ta lura yin maganar Sultan yana bata ma Firdausi rai. Bayan sun gama gaisawa da Firdausi sai ta mika ma Badiyya. "Badiyya, Sultan na magana." Badiyya na saka hannu ta karba ta tashi tayi hanyar daki, kallonta suka tsaya yi. "Badiyya dan za'ayi waya da Sultan shine baza'ayi gabanmu ba ko? Lallai yarinya." Cewar Musaddiq yana dariya, domin shi mamaki ma take bashi. "Hello Sultan am." Badiyya ta fada, bayan ta zauna kan gado, wasu hawaye da batada masaniyar na menene suka fara zubowa. "Badiyya ya kike? Bakiyi kuka bako?" Ya tambaya cikin kulawa. "Momy haushi taji dan na fadama Dady zamu koma Dutsinma." Ta fada murya a dakune. "Dole taji haushi kinji, yanzu kibar nuna mata kin damu, ki cigaba da wasa normal yadda kika saba." Cewar Sultan, da alamun rarrashi, dama yasan za'a rina; dan Badiyya bata da wayon da zata boye ma Firdausi wani abu. "Toh Sultan am." Ta fada a raunane, tana goge hawayen idanunta. "Wace unguwace a Dutsinma?" Sultan ya tambaya. "Ban sani ba, amma naji Uncle yace ko Unguwar Rimi." Cewar Badiyya, yadda tayi maganar na tabbatar da bata sani ba din. "Ohhh, anjima zan maida Hajiyarsu Abba gida, idan nazo zan shigo, ai wajen marece kun koma ko?" Sultan ya fada, domin shima yanaso ya ganta.2 "Allah Sultan am? Eh yanzu ma zamu tafi ai." Ta fada, muryarta cike da jin dadi. "Toh shikenan Badiyya, sai na zo, kibar kuka kinji." "Toh Sultan am, sai kazo." Daga haka ta karar da call din, ta tashi domin ta mayarwa Firdausi wayarta, ta kuma ida breakfast dinta. Tana fita taga Musaddiq bayanan, sai Firdausi kadai, wadda itama ta gama hade komai nasu waje daya; ita kawai take jira su tafi. "Momy ga wayan." Ta fada, tana mika mata wayar, Firdausi ta karbi wayar ta saka a jaka. "Badiyya kiyi sauri ki ida mu tafi kinji." Cewar Firdausi, alamun bataso suyi late. Badiyya nodding kanta tayi, ta koma ta zauna domin ta ida yin breakfast dinta. Dama Badiyya akwai sluggishness balle ga damuwa ta kakaba ma ranta. A haka ta gama breakfast, Musaddiq har ya fitarda kayansu waje. Sun shiga mota sun zauna, Musaddiq ya zagayo bangaren Badiyya. "Toh Badiyyar Sultan, sai nazo ko?" Ya fada cikin sigar wasa. Zumburo baki tayi, domin ita ko sunan Sultan yanzu bataso a fada gaban Firdausi. "Kai Uncle, ni Badiyyar Uncle ce ba Sultan am ba." Ta fada tana zumburo baki, alamun shagwaba. "Ana cewa Sultan am, kuma wai ba Badiyyarshi bace." Musaddiq ya fada yana dariya. Kafin Badiyya ta kara magana Firdausi taja mota, tana fadan "Musaddiq idan na biyema badinages dinku sai nakai biyu na rana ban tafi ba." Da dan karfi domin yaji. STORY CONTINUES BELOW  Dariya Musaddiq yake "Toh Adda Fiddi, Allah ya tsare." Ya fada da karfi tare da wucewa hanyar kasuwa. *** Sunje Firdausi tayi reporting a school dinda xata fara aiki, taje tayi ma Badiyya registration a nasu school din, bayan sun fito ta kalli Badiyya "Yanzu Bady sai muje kasuwa ko? A sayi uniform." Ta fada tana murmushi, domin daga yanayin Badiyyar ya nuna zataso school din. "To Momy kinada kudin ne? Ko ki kawo waya na kira Dady." Badiyya ta fada a raunane, gani take kamar Firdausi batada kudi. "A'a Badiyya, inada su, daga yanzu nizan rika maki komai kinji." Firdausi ta bata amsa, hade da yimata wani lopsised smile. Badiyya ta daga kai, a haka suka shiga mota suka nufi hanyar kasuwa. Firdausi na magana da mai shago Badiyya ta tabo ta, "Momy, wancan ba Ladi bace?" Badiyya ta fada, hade da nuna matar da hannu. "Badiyya babu kyau nuna mutane da hannu, ki daina." Firdausi ta fada, tana buge hannunta. "Momy wallahi itace." Badiyya ta fada kamar zatayi kuka, domin ita tabbas Ladi tagani. Dole Firdausi tazo ta taba matar, tana juyowa "Ahh, Hajia, keda kanki?" Ladi ta fada, mamaki karara kan fuskarta. Firdausi murmushin ta maida mata, "Ladi, wallahi kuwa." Ta fada, Badiyya na lafe jikinta. "Ai mun dawo nan, munanan Unguwar Rimi." "Lahh! Nima anan nake gidan yarinyar data haihu, zan shigo insha." Saida Firdausi tayi mata kwatancen gidansu sannan ta koma shagon da zata sayi kayan, bayan sun gama siyayyar suka hau mota suka wuce gida. Suna shiga suka iske gidan tsaf dashi, wani murmushi ne ya subuce ma Firdausi, dan tasan tabbas aikin Musaddiq ne, dama jiya yace mata zaije Dutsinma amma be fada mata ne zaiyi ba. Gidane dan babba ba laifi, domin Baba ya taba zama gidan lokacin da aka mashi transfer, parlour ne babba, sai daki ukku, ga kitchen. Gida ne daidai. Yar siyayyar da tayi a kasuwa ta shiga kitchen ta aje, sannan suka wuce daki. Kayan Badiyya ta dauka takai su wani daki sannan itama ta dauki nata takai. Tun Badiyya na shekara biyar ta saba kwana daki ita kadai, domin sun lura tanada wayau sosai; shiyasa suka bata daki daban. Yanzu abun har yabi mata jiki, in kaga ta kwana wani waje, to kuka takeyi. Sunje sunyi wanka duk shirya, Firdausi ta dafa masu indomie, domin ita kadaice abunda zatayi saurin dahuwa suci dan yanzu. Wajen biyar na yamma sukaji ana sallama, Firdausi ta janyo hijab dinta ta saka "Ka shigo." Ta fada da karfi, domin mutumin yaji. Kara sallamar yayi hade da shigowa cikin parlour, Badiyya na ganinshi ta mike tsaye. "Sultan am, ashe zakazo." Badiyya ta fada alamar taji dadin ganinshi. Karasowa inda take yayi ya zauna "Badiyya, gani nazo." Ya fada yana murmushi. "Aunty ina wuni?" Ya fada yana kallon Firdausi. "Lafiya lau Sultan, ya akayi ka gane gidan? Ko Badiyya ta maka kwatancene?" Firdausi ta tambaya, domin ganinshi ya bata mamaki. "Na shigo unguwar sai na hadu da Ladi kan hanya, ita taman kwatance." Ya fada, yana tafa hannayensu shida Badiyya. "Ohhh Allah sarki Ladi." Firdausi ta fada tana mikewa tsaye. "Bari na kawo maka ruwa." Cewar Firdausi, tana yin hanyar kitchen. "Eh wallahi, tamace nafada maki sunanan zuwa." Ya fada, yana maida kallonshi kan Badiyya, wadda tayi shiru tana kallon yadda dimples dinshi ke lotsawa. "Sultan am, Momy ta kaini makaranta yau." Ta fada tana murmushi. "Allah Badiyya? To ki maida hankali kinji? Nima gobe zan koma makaranta." Cewar Sultan, yana pinching nose dinta. "Kai Sultan am, yanzu bazan sake ganinka ba?" Badiyya ta tambaya, rashin jin dadi karara kan fuskarta. "Ai zan dawo Badiyya." Ya fada cikin sigar lallashi. Sunata magana, har ya samu ya lallasheta, harta fara dariya. Sunanan zaune wajen minti talatin saiga Firdausi ta fito da kula a hannunta. "Ga taliya nan na sulala maka, dayake yau muka dawo gidan." Firdausi ta fada tana ajiye kular da plate a gabanshi. "Anty wallahi dakin barshi, saida naci abinci sannan na taho." Kafin Firdausi ta bashi amsa wayarshi tayi ringing, dauka yayi ya kara a kunne. "Hello Abba." "Sultan ka jira Ahmad anan gidan, motarshi ta lalace, shima Katsina zai dawo." "To Abba." Sultan ya fada, hade da yimashi kwatancen gidan. Itadai Firdausi tsayawa tayi tana kallonshi, amma tanasan san tambaya taji wa yakema kwatance, saidai data tuna Abba yace sai tayi tunanin ko kamal ne zaizo. Suna zaune suna hira aka kara sallama, bayan sun amsa sallamar wanda ya shigo ya saka Badiyya da Firdausi frenzing. Ahmad yana shigowa yayi wajenda Badiyya take, tasowa tayi ta rungumeshi, hugging dinta back yayi ya zauna yana kallonta. Firdausi tsayawa tayi tana kallonsu, abun haushinma ko kallon inda take bai yiba. Ahmad suka gaisa da Sultan, sunata kallon kallo da Firdausi, baice mata kala ba, itama. Badiyya sai surutu take mashi, yana nan zaune ya hango kular abinci gaban Sultan. "Sultan zuba man abincin, kasan nayi missing abincin wifey." Ya fada yana mata wink, kauda kai tayi gefe. Bayan ya gama cin abincinshi, ya juya ya kalli Firdausi, wadda ta hade rai kamar bata taba dariya ba "Wifey fushi kike dani, I'm sorry dan Allah." Ya fada yana wani karya murya, shidai Sultan wani kallo sukayi sharing shida Badiyya, kowanne fatanshi Allah yasa Firdausi ta hakura. Wani kallo ta wurga mashi "Sultan dare zaiyi fa, ko ba Kamal yace ka koma da wuri ba?" Ta fadi hakan ne domin su tashi su tafi. Kallo Badiyya Ahmad yayi da pleading eyes "Badiyya ki tayani bawa Momy hakuri." Ahmad ya fada, yana kallonta, alamar neman temako. A tare suka buda baki harda Sultan, "Momy pleaseeeeee." Sukayi wata muryar shagwaba. Yadda fuskokinsu sukayi, da yadda muryarsu ta fito yabawa Firdausi dariya, dariya tacigaba dayi harda kyakyatawa. Ganin tana dariya yasasu dariya. "Na hakura My Bady, Sultan ka tashi karkayi dare." Ta fada, hade da galla ma Ahmad wata harara, wanda hakan ya nuna mashi bata hakura dinba, kawai tace hakane saboda Badiyya. Amma yadda yaga yanayinta akwai hope. A haka suka rakasu bakin gate, Badiyya nada niyar yin kuka Sultan yanata bata hakuri. Bayan sun tafi saiga Ladi da Malam Tanko, inda suke fada mata Ahmad ya sallamesu. Ta fada masu akan zata kara daukar Malam Tanko aiki, ita kuma Ladi saidai ta samu wani wuri saboda kudin zasuyi mata yawa. Jin haka yasa Ladi tace zatayi mata aikin kyauta, tunda dama akwai dakin maigadi a gidan saisu zauna, danko gidan zama basu dashi.Rayuwar Firdausi da Badiyya ta fara daidaidaituwa, sun fara sabawa da zama su kadai, Badiyya tun tana maganar Sultan har ta daina, itama Firdausi ta cire komai a ranta ta rungumi yarinyarta suna zamansu. In ka cire zuwanda Ahmad keyi aduk sadda ya gama lectures, to ba abunda yake bata ma Firdausi rai yanzu. Har ta fara maido kibarta, jikinta ya kara haske, though ita bamai hasken bace, chocolate skin gareta, irin mai glowing dinnan. Dogowa ce, surar jikanta daidai, duk wanda yaga Firdausi a karo na farko sai ya kara kallanta. Badiyya carbon copy din Firdausi ce, shiyasa komai nata harta halinsu daya, inka cire kafiya da take dashi; wanda wannan halin Ahmad ne.2 Firdausi yanzu harta saba da zuwan da Ahmad keyi masu, duk ran Friday dama da daddare sai yazo. Takan boye rashin san hakan domin koba komai, yakan debema Badiyya kewa. Amma badan ranta yanaso ba, tunda yanzu ba aure ne tsakaninsu ba, sharrin shaidan ake gudu. Tunda yake zuwa bai taba mata maganar gadon ta ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dukda rashin yin maganar komawarta yana damunta; dan a tunaninta zuwan dayake zai ce ta koma ne, amma sai taga baiyi magana ba. Yau sun tafi makaranta, dayake Thursday ne, sunje school, ana tashi Firdausi ta biya ta dauki Badiyya, ko lesson bata tsaya ba, domin tanaso suje kasuwa; zatayi siyyayya. Sun shiga kasuwa Badiyya taga Momynta na siyan kayan provision kamar na yan makaranta. "Momy wannan kayan fa?" Ta tambaya, domin gani take sun masu yawa. "Badiyya namune." Ta fada tana shafa fuskar Badiyya, domin wata kewa takeji ta yar tata kamar basu tare. "Momy yayi yawa ai." Badiyya ta fada, tana karema kayan kallo. "Rabi nakine, ko bananan sai kiyata ci, idan sun kare ko Uncle Musaddiq ya kara maki." Firdausi ta fada tana murmushin, murmushi me cike da ma'anoni. "To Momy dayan rabin fa?" Badiyya ta tambaya, tana kallon mahaifiyarta. "Rabin na Sultan ne, dazu Kamal ya kirani akan Sultan yace akai mishi ke ranar visiting, kuma saturday ne, shiyasa na siya. Ko bananan sai ki kai mashi ko?" Firdausi ta bata amsa, tanajin soyayyar yarinyarta. "To ke Momy ina zaki?" Badiyya ta tambaya, domin ita bata gane wannan 'ko bananan' din da Momynta ke fada ba. "Nima ban sani ba Badiyya, amma inaji kamar zanyi tafiya ne." Firdausi ta bata amsa, abunka da yarinya bata kara fadan komai ba.2 A haka aka kwasar musu kayan aka kai mota, suka shiga suka nufi hanyar gida. Bayan sunci abinci suna kallo, Firdausi sai kallon Badiyya take. Badiyya ta turbune fuska "Wai Momy menene? Naga tun dazu sai kallona kike, ko fuskata ta baci ne?" Badiyya ta tambaya, hade da saka hannu tana goge ilahirin fuskarta. Wani irin murmushi Firdausi tayi "Aa Badiyya, fuskarki lafiya lau take." Firdausi ta fada, hade da janyo yarinyarta ta rungume, wasu weird feelings ne ke mata yawo cikin kai tun dazu. "Momy ki kiramani Uncle please, yace zaizo kuma baizo ba." Badiyya wacce ke lafe jikin mahaifiyarta ta fada. "To Badiyya bari na kirashi." Fadan haka, sai ta fiddo wayarta tayi dailing number Musaddiq. "Hello Adda Fiddi." Musaddiq ya fada lokacinda yake amsa wayar. "Musaddiq, Badiyya tace kayi mata alkawarin zuwa amma baka zo ba." Firdausi ta fada hade dayin dariya. "Kice mata yau na shigo Dustinma zanzo insha Allahu, hada wani abu na kawo mata." Musaddiq ya fada shima yana dariyar. "Yauwa, gara dai kazo ko kallon bankwana na maka." Ta fada hade dayin murmushi. "Sai kazo." Ta fada hade da ending call din. STORY CONTINUES BELOW  A haka taita kiran sisters dinta daya bayan daya, kowa sai tace mashi kiran ban kwana, duk sun zama curious. Sunanan zaune, akai akai takan juya ta kalli Badiyya tayi murmushi, itama murmushin take maida mata. Sai sukaji sallamar Musaddiq. Da gudu Badiyya taje ta rungume shi. "Uncle, oyoyo." Ta fada tana dariya. Cillata yayi sama yana dariya shima. "Badiyyar Sultan, ya kike?" Ya tambaya da sigar wasa, yana ajiye ta kan kujera. Kallon Firdausi yayi hade dsyin murmushi "Adda Fiddi ina yini." Kallonshi tayi tana mayar mashi da murmushin. "Lafiya lau Musaddiq, ya gidan, ya makaranta." Bayan sun gaima gaisawa, ta kawo mashi abinci yaci, sai Badiyya ta hango wata yar leda gefenshi. "Uncle miye ciki?" Ta tambaya hade da bude ledar. Buge hannunta Firdausi tayi." Badiyya miye haka? Yanzu halinda zaki rikayi kenan in bananan?" Muryarta na nuna alamun bata ji dadin abunda tayi ba. Musaddiq ne ya mikama Badiyya ledar. "Sorry My Bady, ai tsarabar kice ma." Ya fada yana kara mika mata ledar. "Lah! Momy camera." Badiyya tayi ihu, hade da fito da cameran, rungume shi tayi "Uncle nagode, kaga sai naje muyi pictures da Sultan am jibi ko?" Ta fada tana dariya, alamun taji dadin cameran sosai. "Ko ba komai, nasan ko bananan akwai masu son Badiyya." Firdausi tayi magana cikin ranta, batasan ta fito fili ba. Kallonta Musaddiq ya tsaya yana yi, "Adda Fiddi tafiya zakiyi ne?" Ya tambaya, yana scrutinizing face dinta. "Aa Musaddiq, me ka gani?" "Babu komai." Ya bata amsa, bayaso yayi probing dinta. A haka sukayita fira suna dariya, Badiyya sai daukarsu pictures take. Wasu suna dariya, wasu suna magana ma basu sani ba. *** Suna zaune da daddare, Badiyya sai daukar Firdausi pictures take, tun tana cewa ta bari har ta hakura ta kyaleta. Sallamar da akayine ya dawo dasu cikin hayyacinsu, saida Firdausi ta saka hijab sannan sukayima mutumin iso. Yana shigowa suka tsaya suna kallonshi, dan bai saba zuwa da daddare ba inba ranar Friday ba. Yana shigowa suka zauna shida wani abokinshi mai suna Gaddafi. In har Firdausi zata iya tunawa, to farkon fara tarayyar Ahmad da Gaddafi ne silar gurbacewar halayen Ahmad, tayi kokarin ta rabasu amma ta kasa, abunka da ba ita keda iko dashi ba. Yake ta masu wanda baikai har zuciyarta ba, domin ganin Gaddafi yasa wani abu yayi gnawing at her, kwata-kwata batasan ganinshi tare da Ahmad. Domin tunda Ahmad ya lura batasonshi shiyasa ya daina zuwa dashi gida, amma ko meya kawoshi yau? Oho. Tashi tayi ta wuce kitchen domin kawo masu wani abu, tabar Badiyya nata masu surutu tana daukarsu pictures. Dawowa tayi ta ajiye masu kulolin, kallon da taga Gaddafi nabinta dashine yasa taji duk ta kasa nutsuwa. Bayan sunci abinci sundan gaisa, suna zaune wanda Badiyya nata nuna ma Gaddafi pictures dinda ta dauka. Ahmad tasowa yayi ya dawo kujerar da take kusada ta Firdausi, wani irin mischievious kallo yake mata, yana smirking. "Gimbiyar mata." Ya fada cikin sigar gatse. Kallonshi tayi ta watsar, ta maida kallonta kan TV. Haka yayi ta surutunshi itadai tayi banza dashi, amma tana lura da yadda suke sharing wasu irin kallo tsakaninshi da Gaddafi, but she choose to play dumb. A haka har suka tashi zasu tafi, Badiyya na makale da Gaddafi, it seems they really get along. Har sunzo wajen bakin gate, sai Ahmad ya juya ya kalleta "My lady, na lura kina kewar mijannan naki, in kinasan ki dawo ba matsala, kinsan abunda nake bukata ai." Ya fada, yana wani smirking. Kallonshi tayi hade dajan wani irin mugun tsaki "Only in your dreams man. Once I'm done, I'm done." Tayi groaning in dissapointment, hade da kallon Malam Tanko, "Malam idan sun fita a rufe gidan, Saida safe." Ta fada tanayin hanyar cikin gida, domin hakan ya zaman masu sabo, duk sadda Ahmad yazo takan rakoshi har bakin gate tace a rufe gidan sannan ta koma. Ko takan Badiyya bata biba ta wuce ciki hade da banging kofar. Ahmad kallon wajen data bi yake a gufule, har shi Firdausi zata ma tsaki? Lallai. Sallama sukayi da Badiyya, ta koma cikin gida su kuma suka shiga mota hade dayin gaba. Tana shiga ta iska Firdausi zatayi hanyar daki, kallonta tayi hade da fadin "Momy goodnight." Tanayin hanyar dakinta. "Aa Badiyya, yau tare zamu kwana." A haka tajata suka tafi dakinta, labari sukayi har wajen karfe biyu, saida sukayi Nafila tukun sukaje suka kwanta. The moment was scintillating, Firdausi ji take kamar yau ce rana ta karshe da zatayi spending da yarinyarta.Da sassafe Firdausi ta tashi, kasancewar yau juma'a, haka ta nufi kitchen, a inda ta iske Ladi me aiki, zuwa tayi suna aikin cikin girmamawa, Ladi ta lura da yadda take ta ajiyar zuciya. Kallonta tayi cikin kulawa "Hajia , ko bakida lafiya ne?" Ta tambaya, tana zama kusa da ita. "Aa Ladi, yau jina nake wani iri wallahi, kamar wani abu zai faru dani." Firdausi ta bata amsa, hawaye na taruwa cikin idonta. "Dan Allah ko bayan raina ki kulamin da Badiyya." Ta fada, hawayen da take rikewa suna samun mazauni akan kuncin ta.3 "Subhanallahi, Hajia ki daina fadan haka dan Allah, ba abinda zai sameki." Ladi ta fada, tana dora hannunta saman kafardar Firdausi. A haka taita bata baki, har suka gama abincinsu suka nufi falo. Firdausi ta zauna jiran Badiyya taga ko zata fito amma taji shiru, shiga dakin tayi ta ganta kwance tana bacci. Bata yi mamakin hakan ba, domin jiya basuyi bacci da wuri ba. "Badiyya ki tashi." Firdausi ta fada, tana patting bayanta softly. "Momy please ki bari na kara." Badiyya ta fara cikin muryar bacci, hade da juyawa. "Badiyya ki tashi kinji, ko firar karshe nayi dake, baza muje school ba yau." Ta fada tana murmushi, domin jin hakan yana iya sakata ta tashi. "Dan Allah Momy?" Badiyya ta furta, hade da zama saman gadon. "Eh mana, tashi kije kiyi wanka, muyi kwalliya kiyi mana pictures da camera ki." Firdausi ta fada, murmushinta na fadada. Badiyya mikewa tayi ta shiga toilet, ita kuma Firdausi ta fita parlour. Tana gamawa, ta saka kayanta masu tsada, ta shafa kwalli da dan jambaki. "Momy nayi kyau?" Ta fada, tana jujjuyawa, yayinda ta shiga palourn. "Eh mana My Bady, zo muyi breakfast sai muyi pictures din ko?" Firdausi ta fada, tana janyo hannunta. A haka suka zauna suna cin breakfast dinsu cikin soyyaya, bayan sun gama suka dauki pictures iya yinsu. "Momy kara tsayawa nayi maki." Badiyya ta fada, tana kara saita camera. "Badiyya Allah nagaji, wanda mukayi sun isa fa." Firdausi ta fada, tana turbune fuska alamar wasa. "Nidai Momy Aa, bari Ladi tazo tayi mana tare." Tana fadar haka taje ta kira Ladi. "Kinga idan kika saita, sai ki danna nan wajen." Badiyya ta fada, tana nuna ma Ladi yadda zata dauki picture. A haka suka saita tanata daukarsu pictures, wani waje suyi dariya, wani waje suyi murmushi, hada dai tayita daukarsu. Sai wajen 11 suka gama. Firdausi kallon Badiyya tayi "Badiyya zo muje yawo cikin gari." Ta fada, wani murmushi na bayyana a fuskarta. "Allah Momy?" Badiyya ta fada, hade dayin tsalle. Murmushi tayi mata, haka sukaje suka dauki veils dinsu sannan suka fita. Yawo suketayi cikin gari, su shiga can su shiga nan, Badiyya sai murnar farin ciki take, ta leko kanta ta window, ta rufe idanunta, iska na bugunta. "Badiyya maido kanki cikin mota kinji? Ko so kike a buge ki?" Firdausi ta fada, hankalinta yana kan tukin. "Momy dadi nakeji, gobe zamuje wajen Sultan am ko?" Badiyya ta tambaya, tana maido kanta cikin motar. "Eh Badiyya, amma ni bandi ni ai, Uncle Musaddiq zai kaiki katsina." Firdausi ta fada tana murmushi. A haka Badiyya bata kara cewa komai ba, a haka suka je wajen shan ice cream, har sunzo zasu shiga Badiyya ta hango wata yarinya kamara iya shekarunta tanata kuka, ta hada kai da guiwa. Janye hannunta da yake jikin rikon da Firdausi tayi mata, ta nufi wajen yarinyar. "Meya sameki?" Badiyya ta dafa ta, idanunta sun ciko da kwalla. Allah yayi mata tausayi a rayuwarta. Dagowa yarinyar tayi tana kallonta, hawayenta na kara zubuwa. "Abbana da Ummana sun rasu, Kishiyan Ummana ta koreni daga gidan, yanzu bansan inda zan gano yan uwana ba." Ta fada, hade da kara fashewa da kukan. "Wayyo Allah kiyi hakuri, ya sunanki?" Badiyya ta tambaya, tana goge hawayen fuskarta. "Sunana Ikhlas Muhammad." Yarinyar ta fada. A haka sukayita labari, Badiyya sai bata hakuri take, da Firdausi ta gaji da jira sai tazo ta zauna kusa dasu. "Badiyya wacece wannan?" Ta tambaya, tana dafa yarinyar. "Momy sunanta Ikhlas, Abbanta da Ummanta sun rasu, Kishayan Mamanta ta korota, kuma batasan inda zataga yan uwanta ba." Badiyya ta fada, wasu hawaye na zubowa daga idonta. "Allah sarki Ikhlas, kiyi hakuri kinji, komai yayi zafi maganinshi Allah. Taso muje kici abinci." A haka Firdausi taita lallabata, Allah yasani yarinyar ta bata tausayi. A haka sukaje sukaci abinci sukasha ice cream. Bayan zasu tafi Firdausi ta kalleta, tausayawa karara kan fuskarta "Ikhlas kije gidan ki bata hakuri, kice ta barki ki zauna kinji." Firdausi ta fada da sigar lallashi. "Toh Momy, Nagode." Ikhlas ta fada, murmushi saman fuskarta. "Badiyya sai anjima." Ta fada hade da rungumeta. A haka su Firdausi suka tafi, zuciyarshi tayi masu nauyi. Da badan tanajin wani feeling a ranta ba, da sai ta dauki Ikhlas ta mayar da ita gidansu. *** Bayan sun koma gida, Badiyya sai tunanin kawarta takeyi, a haka sukaci abincin dare, Firdausi sai janta da labari take domin ta saki jikinta. Aikuwa abun yayi, domin bayan sun gama cin abincin, haka suka zauna sunata kallon _Jennifer's diary_. Badiyya sai dariya take hada kyakyatawa, bawai dan tana gane banbancin good English dana Jennifer ba saidan ko yadda maganar ke fitowa abun dariya ne. A haka sukayita kallo har wajen karfa 9, saida Firdausi ta fara gajiya sannan ta kalli Badiyya "Badiyya jeki wanka, muzo mu kwanta kinji." Tashi badiyya tayi, ta saka camera ta in video mood, ta ka ajeta kan dinning table, wanda yake daidai bakin kofar kitchen. Har ta tafi ta juyo ta kalli Firdausi, an unreadable expression plastered on her face. "Momy ga camera ta nan na ajiye, zata kallan mani komai kike yi har na dawo." Ta fada da karfi tana wucewa hanyar dakinta. Firdausi murmushi kawai tayi ta cigaba da kallonta. Badiyya taje tayi wanka, zama tayi ta fara contemplating akan wane kaya zata saka gobe, ta fiddo da duk kayan da takeso, ta kalli wannan ta kalli wannan. Dubawa take wanda zaifi kyau idan ta saka, wanda idan sunyi picture da Sultan am zaiyi kyau. Da dai taga zaman bazai yiwu ba, saita tashi ta nufi hanyar parlour da nufin Firdausi tazo ta zabar mata. Tana zuwa, ta lallaba ta dauki camera ta, domin tunaninta wani abune Momy kesan yi. Lekawar da zata yi falon, taga Firdausi a kasa, jini ya babbaje, ga bango parlour da alamun buga kanta akayi. Nan take jikinta ya kame, jininta yabar gudana, zuciyarta ta daina pumping, kwakwalwarta ta kasa gasgata mata abun take gani. Malam Tanko ganin dare yayi, kuma Firdausi ta saba zuwa tayi musu saida safe, tun lokacin da take zuwa yayi harya wuce, kasa hakura yayi "Ladi, kije ki duba su Hajia ko lafiya, naga shiru bata fito ba." Malam Tanko ya fada, alamun ya damu. "To Malam nari inje in duba, Allah yasa lafiya." Ladi ta fada, tanayin hanyar cikin gidan. Ladi tana shiga tayi gamo da abun tashin hankali, Firdausi kwance cikin jini, ga Badiyya makale da labule da camera a hannunta, da alamu itana she's unciouncious. Domin duk jikinta yayi frenzing, heart dinta kadai ke beating vigourously. Da alamu abun ya bugan mata zuciya. A take Ladi ta kurma wani ihu, wanda hakan ya janyo hankali Malam Tanko zuwa cikin gidan. Yana shigowa ya gani, salati ya fara hade da daukar wayar Firdausi domin kiran yan uwanta, wanda last call dinta Musaddiq ne. Baa fi minti talatin ba Musaddiq yashigo, domin dama tun jiya baibar garin ba, a haka aka kwashesu aka tafi dasu asibiti. Anyi anyi Badiyya ta saki camera hannunta amma taki saki, babu yadda likitocin suka iya saidai a haka suka cigaba da bata taimakon gaggawa. Wanda ita Firdausi suka tabbatar ta rasu, sanadin bugata da bango da aka rinka yi.

0 Comments