MAFARKIN ABDULL COMPLETE

MAFARKIN ABDULL COMPLETE
Zaune take gaban fannin kimiyya (Faculté des Sciences) ta jami'ar Abdoul moumouni (Université Abdoul Moumouni Dioffo) da ke Niamey a jamhoriyar Nijar. Sun fito lectures kenan kasancewarsa ɗaliba yar aji uku a fannin tsirrai (plant biology), Yarinya ce 'yar kimanin shekaru ashirin a duniya, tana da matsakaici tsawo, Albarkan mazaunen da ke gareta da kumatunta yasa akan mata kallon mai jiki kasancewar ta ma' aboki yar sa hijab. Kalarta mai tsada ne, baka ce ba wuluk ba ma'abociyar fararen idanu kalar madara. Wasu na mata kallon mai girman kai yayin da dayawa kan so ta saboda hakurin ta da yalwataccen fara'an da ake samu a fuskanta. A zahirance kallon wayarta takeyi fuskarta ba yabo ba fallasa, amma tunaninta ya tafi chan wani duniyar. Ko a aji yau ba zata ce ga abinda akayi musu ba. Kiran da ya shigo wayarta yasa ta sakin ajiyar zuciyar da ya sa kawarta da ke zaune gefenta kallonta. "Sweetyna kana lafiya, duk hankalina ya gaza kwanciya, ina ka shige" Ta faɗi a marairaice kamar zatayi kuka. "barci na tashi ya kike ya makaranta?" "Alhamdulillah, ka ci abinci" Ta sake tambaya cikin yanayin kula "Bana jin cin abincin ne, ga de ni nan Haj na min favorite ɗina" Ya faɗi yana dariya. Itama dariyan tayi. Haka suka cigaba da hira cike shaukin juna. Har wajen mintuna ashirin sannan suka rabu cike da kewan juna. "Halima fisabillillahi bazakiyi ma kanki faɗa ba, wallahi Hammad ba aurenki zeyi ba. Ki natsu ki roki Allah ya baki nagari, kada so ya rufe miki ido" faɗin kawarta da ke zaune a gefenta. "Faɗima wallahi muna son juna da Hammad, kun kasa fahimtarmu ne, kuyi mana fatan alkhairi kawai" "ina guje miki halin mazan zamanin nan ne, basu da alkawari musamman in son da mace ke musu ya zarce misali, duk abin sa kar ki yarda ayi gwajin takalmi da ke" Faɗima ta ce cikin halin ko in kula. "in ma gwajin riga zai yi ba komai bane mu dai muna son junanmu kuma za muyi aure" Ta faɗi a kufule duk ranta ya ɓaci. Fuuuu ta tashi kamar mai shirin tashi sama. *** Da kyar ta iya isa gidan baffanta da take zama wanda ke bayan Homeland Hotel, da ke Off Ave du General de Gaulle, a wahalance ta yi sallama, ta iske matar baffanta haj Mas'uda a zaune tana kallon tashar Sunna TV. "Momma barka da gida" Ta faɗi tana mai samun wajen zama a kusa da kafanta. Kallo ɗaya tayi ma ta ta fahimci bata cikin natsuwa. "Halimatus sa'adiya taje makah da madina ta sha miya mai daɗi har da kadangare soyayye" Ta shiga rera mata tana tafi. Dariya Halima ta farayi yayinda ranta ya fara sanyi. "faɗa min waya taɓa ki" Ta tambayeta tana mai tsareta da idanu. "Faɗima ce na rasa mai na tsare mata, tsakani da Allah nake zaune da ita amma sai ta yi ta min bakin ciki da hassada" Ta faɗa ido cike da kwalla, zuciyar ta na mai jin an ci amanar kauna. "tohhhh fa, me ta yi miki, kwata kwata ba tayi kalan mai wannan halin ba" Ta amsa mata fuska cike da alhini. "Momma a 'yan kwanakin nan sai tayi ta ce min in rabu da Hammad ba aure na zaiyi ba, ki duba fa ko haushin yafi mijinta kyau da kuɗi take yi ko mai yasa ni ban sani ba" Ta karasa tana kukan da yafi jini ciwo don a duniya bata da kawar da take kauna sama da Faɗima duk da kasancewarta kanwa a wajen kishiyar uwarta. "Na rasa me ke damun mutanen zamanin nan. Sam bama son gyara, da ga an nuna mana kuskurenmu maimakon mu gyara sai mu ce ana mana bakin ciki ko hassada. Mai sonka ke gyara maka, nasan son da Faɗima ke miki ba za ta bari ki cutu ba. Hammad dai iyayen ki ba sonsa suke ba, asali ma cewa su ka yi ki rabu da shi, ina mai shawartanki da ki roki zaɓi Allah in Hammad ne alkhairi Allah ya tabbatar in ko ba shi bane Allah ya kawo wanda ya fi shi a komai" "Momma ko ba Alkhairi bane Allah ya sa mu mallaki juna, ina sonsa da yawa Momma" Ta katse ta gudun yan aameen su amsa ma addu'ar ta,. "Halima ko dai Hammad ya sanki a ɗiya mace ne, in ba haka ba wannan irin nacin son da kike masa ya zarce hankali, dama mamanki ta faɗi na karyata gashi kina neman gaskata maganarsu". Ba ta jira amsarta ta ba barta zaune tana gunjin kuka. Kiran sallar la'asar da akayi ne ya tashe ta daga barcin wahalan da ya kwashe ta a wajen. Tashi tayi ta sallace la'asar da azahar ɗin da ake bin ta bashi. Tare da Momma da babbar yar momma Amina da suke kira Amna suka kammala girkin dare. Suka shirya, karfe shida duk suka haɗu gaba ɗaya suka ci abincin, don ka'ida ne a gidan cin abincin dare karfe shida don ya zazzage kafin ayi barci, sannan abincin safe baya wuce karfe takwas ɗin safe duk don samun ingantacciyar lafiya. Bayan kammala sallah isha'i ta koma ɗaki da nufin barci. Shafin Facebook ta shiga don duba abubuwan da ke kai, har zata sauka sai sakon gayyata ya shigo ta buɗe sai taga "ABDOULLAH ABOUBAKAR (ABDOUL ABOU)" Sai da ta duba shafinsa ganin bai bada wasu bayanansa masu mahimmanci ba iyaka dai taga shima ɗan Zindar ne. Har zata goge sai ta tuna da tobashinta Abdoul Abou sai tayi tunanin Shine. Tsaki ta ja kafin ta amince. Haka ta cigaba da shige shigenta tana hira da kawarta da suka haɗu a Facebook ɗin Tiddar Azzoubir. Da ta gama ta kalli agogo ganin goma saura na dare ta sa ma ranta tabbas Hammad ya gama kallon kwallo. Waya ta ɗauka ta kira shi sai da ya kusan tsinkewa sannan ya ɗaga. Yanayin yanda ya amsa mata yasa ta tambayeshi ko ya fara barci ne "ke dai bari hajiyata, wallahi na ɗanyi aron hannu ne kinsan gajiya yake sawa" Ya faɗi cikin halin ko in kula Bakin ciki ya cikata amma haka nan ta ɗaure ba tare da nuna ta damu ba tace "sweetyna yaushe zaka daina zuwa rage ruwan nan ne, lokaci yayi da ya kamata mu san mai muke ciki" "anya in munyi auren nan baza'a samu matsala ba, kishin ki na neman kaiki ga zargi na, gaskiya da sake toh" Ya katse ta a fusace. Nan take ta fara bashi hakuri da kalaman soyayya da tasan yafi so. Haka suka shirya suka cigaba da soyayya har sha ɗaya da rabi sannan sukayi sallama suna masu begen junansu Juyi ta ke yi hannunta rungume da filo Mafarki take amma na ido biyu (day dreaming) ga ta da Hammad ɗin ta sunyi aure. Auno su take irin soyayyar da zasu kwasa, kamar an mintsile ta tashi tayi ta lalubo kananan kayan da ta siya don kaiwa gidan aurenta. Murmushi ta saki gani take an ɗaura aurensu da Hammad an gama. "Toh in ya cigaba da Aron hannu fa?" wannan sashi na zuciyar mutum da ba'a taɓa yaudara ya tunatar da ita, bata ɓata lokaci ba tayi fatali dashi kana ta faɗin "ai na san zai daina da munyi aure". Kwanciya tayi don tayi barci amma ko gezau barcin ya gagare ta, sai ma tunani da ke neman kar da ita, bata bari ya hargitsa ta ba ta dauki wayarta ta hau Facebook "Assalamu Alaikum yan mata" Ta iske na Abdoullah Aboubakar, ita sam ta manta wani Abdoul. Amsa sallamar tayi , ashe yana kusa nan yayi ta janta da hira, tun tana sharewa har ta fara bashi amsa.3 *** TUSHEN SU Alhaji mousa uomarou ɗan asalin garin Zindar ne, duk da tarihi ya nuna fatauci ya kawo kakanninsa Kasar Nijar daga Kano, har auratayya da chakuɗeɗeniya ya sa sun zama yan kasa. Yara biyu Allah ya mallaka masa wato Idrisa da Abbas. Gidansa sannan nan gida ne da a unguwar yadakwandage kasancewar yafi sauran rufin asiri. Yayi kokari wajen ganin yaransa sun samu yalwataccen ilimin zamani, haka ma na addini. A rana ɗaya sukayi aure inda Idrissa ya auri Mas'ouda balarabiyar Kasar Aljeriya amma mazauna Kasar Nijar shi kuma Abbass ya auri yar gwoggonsu khadija. Wata goma sha ɗaya bayan aurensu khadija ta haifi yar ta mace wacce aka sa ma suna Halima. Mas'ouda kuma sai bayan shekaru haɗu Allah ya buɗe mata kofar haihuwa. Lokacin Idrissa ya sami aiki a fannin kuɗi da tattalin arzikin yammaci Afirka wato Union Économique et Monétaire Ouest Africaine (UEMOA). Don har sun koma garin Niamey da zama. Halima ta taso cikin gata da kula, sannan ta sami ingantaccen ilimi tun daga na addini har zuwa na zamani. Rashin haihuwar mahaifiyarta tun bayan haihuwanta yasa Abbass kara aure, inda ya auro Sauda. Tun da ya auri Sauda kuma haihuwa ta sake buɗe wa a gidan. Sai ya zama kamar ana gasar haihuwa ne a gidan tsakanin khadija da Sauda. Bayan Halima ta kammala sakandarenta a LYCÉE AMADU KURAN DAGA (LAKD) ta samu gurbi karatu a université Abdoul Moumouni Dioffo, dalilin haka ta koma gidan baffanta Iddrissa. A shekaran Halima ta haɗu da Hammad wata rana ta dawo daga registration dai dai kwanar da ya raba su da homeland hotel shi kuma ya fito daga otel ɗin. Hammad Touareg(Buzu) ne ɗan asalin Agadez ne. Fari ne kyakkyawa kamar shi ya kera kansa. Ba shi da hayaniya don magana wahala take bashi Yana da son kyale kyalen duniya amma mace da kuɗi sune kan gaba. Bai sha wuya wajen zulmiyar da Halima zuwa ga sonshi ba amma bai taɓa yunkurin taɓa ta ba yanda bai yi yunkurin zuwa neman aurenta wajen iyayenta ba. A dalilin haka iyayenta suka raba ta da shi amma fir ta ki don a tunaninta bata fara sonsa don ta daina ba haka kuma a shirye take da ta jira shi duk lokacin da ya shirya suyi auren. Babu abinda ya fi faranta ran Halima kamar ta zauna tana MAFARKIN ido biyu. Zaune take da Hammad suna ciyar da junansu abinci a baki, suna yi suna jifan juna da kallo mai cike da kauna. Yaransu suka shigo suna kwala mata kira cike da murnan dawowasu.... Ire-iren mafarkan nan Halima keyi sai ta ji duk duniya babu macen da ta kai ta dacewa da samun masoyi. A haka har ta kai aji uku ana saura mata shekara ɗaya ta kammala karatunta hakan ya tada hankalin iyayenta don sun so ta kasance a ɗakinta a wannan shekaran kasancewar ta cika shekaru ashirin a duniya. Nan dai Halima ta kekashe ta ce ita bata da masoyi sai Hammad.... WANNAN KENAN *** Washegari kamar kullum ta Shirya ta isa makaranta, faɗi ma bata ga wani fara'anta ba, ba yabo ba fallasa suka kasance tare har aka tashi. A hanyar ta na komawa gida ta shiga Faba-faba (wata yar bus da ake motar haya dashi a Nijar) nan ta iske wasu yan mata biyu a ciki. "Kin san Allah Faɗima, ko da tonton oumar ya ce an tsaida ranar auren mu da Hammad ban yarda ba, tsoro na kar in ya ce ya fasa" faɗin ɗaya daga cikinsu. Wacce da gani ta fi rawan kai. "ke ma kinsan yana sonki kawai don ya fiye ka'idoji ne amma kawai ki kiyaye shike nan. Allahu ya nuna mana" faɗin wacce aka kira da faɗima. Hankalin Halima ya kasu kashi kashi sai take ji kamar Hammad ɗin ta ne, wani zuciyar na faɗi mata ai Hammad ba ɗaya bane a duniya. Bata san sanda bakinta ya fara furta "kar dai a ce ke ce amaryan grand frère (yaya namiji)". Nan duk suka juyo suna kallonta. Murmushi ta sakar musu sai ta ɗauko littafin da ahlin ɗinsu Hammad sukayi wai barka da sallah ta ce "ko ba wannan bane angon naki grande soeur (yaya mace)" Nan ma fuskarta cike yake da murmushi yayin da ranta ke rokon Allah kar ya kasance Hammad ɗin ta. "kinga irinta ko Sadiya, da rashin mutunci mukayi da kin kwan ciki, yi hakuri kanwarmu . Ya gida ya su mama" "Lafiya lau, gashi har na zo in da zan sauka, zan faɗa masa mun haɗu da pretty damsel ɗinsa" Ta faɗi tana dariyan da yafi kuka ciwo. Tana sauka ta hau kabu-kabu wanda shi ya karasa da ita gida. Jinta take kamar mahaukaciya, haukan ma sabon shiga. Ko da ta isa ɗaki ta shiga Direct, sai da ta tuɓe ya rage daga ita sai breziya da siket sannan ta kira shi a waya. "Akan me zaki je kina min bincike Halima, ko an ce miki sadiya bata san duk yan gidanmu bane" Ya tare ta da shi kafin ya amsa gaisuwanta. "Ai ban san cewa gidanku ɗaya ba sai yanzu. Yanzu Hammad sakayar da zaka min ke nan" Ta faɗi a raunane, idanunta na fitar da kwalla. Zuciyarta kamar ta fitar dashi saboda azaba kunan da yake mata. "ki fahimce ni Halima, ban taɓa miki Alkawarin zan aure ki ba, ina sonki mais (but) kin san hali na, hakan yasa kike zargi na kuma kike bincike na, bafa muyi aure ba kenan. Kuma kinga sadiya shekarunta goma sha shida ne kawai, zan iya zama in tsara ta yanda nake so" Ya karasa yana dariya. Halima da jikinta ke karkarwa burinta ta tashi daga muguwar MAFARKIN da take tayi kokarin faɗin "Amma Hammad.... " bata kai aya ba ya katse ta da ban hakuri. " Don Allah Halima kiyi min rai s'il vous plaît (please) kada wannan ya taɓa soyayyar mu kinji Don Allah " bata karasa jinsa ba tayi hurgi da wayar ta kara rushewa da kuka wanda ya fi jini ciwo. Tsabagen kukan da tayi ya haifar mata da matsanancin ciwon kai. Tun da ta shige ɗaki ba ta fito ba sai faɗi ma mommansu zazzaɓi take yi. Washe gari ma haka ta yini sukuku, mamaki ya cika ta rashin ganin kiran Hammad, zuciyar ta guda na ingiza ta kan cewa ta kira taji ko lafiya yayin da ɓangaren zuciyarta mafi gaskiya na faɗi mata ta kyale shi. Waya ta ɗauka ta kira Abdoul saboda amincin da ke tsakanin su yasa basa kyashin faɗi ma junansu sirrin rayuwarsu. Saurarenta yayi cikin natsuwa da fahimta. Sannan ya ce "ki ɗaure ki fitar da shi a ranki tun a yau, kar ki saurare shi, zafin da zaki ji kaɗan ne akan sai gaba ki sami ɓacin ran da yafi wannan. Ina office yanzu za muyi magana in na koma gida" Ta gode masa kana ta ɗan yunkura don cire damuwa a ranta. Haj. Mas'ouda na ankare da duk wani take takenta amma ta basar. Cikin lokaci kankani ta zabge ta rame, fara'anta ya zama ragagge ga yawan tunani. A lallaɓe ta kammala jarabawan zangonnan ta tafi Zindar. Abdoul kaɗai yasan matsalarta hakan ya sa shakuwa fiye da farkon haɗuwansu. Bakin cikinsa ɗaya sanda suka haɗu tana tare da Hammad da babu abinda zai hana masa aurenta. Ga shi saura wata bakwai a ɗaura aurensu da Agaysha. Kaifin basiranta da hankalinta yasa yake saka ta kan gaba a dukkan lamuransa don duk shawarar da zata bashi matukar zai yi amfani da ita toh akwai nasara.+ *** Tana Zindar aka ɗaura auren Abdoul da Agaysha. Duk wani shiri na biki akan shawaran Halima akayi. Halartan bikin ne kawai batayi ba amma ko a ranar sunyi waya yafi sau goma, yana lallaɓata da ban hakuri akan matsalarta da Hammad. Amarya Agaysha ta tare a gidanta da ke Jeune cadre wanda ya sha gyara kasancewarta yar gidan masu kuɗi.. Agaysha Iggalher fara ce mai jiki, tana da tsawo bata da wani diri amma baza'a kira ta a chushe ba, yar asalin agadez ce buzuwa ce, amma ta taso a Dosso, iyayenta masu kuɗi ne kuma yan boko. Sun haɗu da Abdoul ta hannun yayanta sidi inda da farko ta ki amincewa da shi kasancewarsa talaka, amma tunda ya samu aiki ta makale masa. Aurensa bai sa shakuwarsu ta ragu ba sai ma a ce ta karu don duk wanda yake tare da ita ya san alakarta da Abdoul, wanda bai san danginsu ba takan ce masa yayanta ne, walau uwa ɗaya ko tubashinta. Tayi samari kala kala amma ba wanda ta yi soyayyar wata uku da shi ba gani take duk mayaudara ne. "Na rasa me ke damun matan adarawa (hausawa) da buzaye sam basu san wani abu kula da miji ba, duk soyayyar da za'a maka kafin ayi aure ne sama they are not caring😡" Abdoul Ya turo ma Halima ta bbm ɗin da suka maida hanyar hiran su, hakan yasa suka rage 2go. Ɗan Aljani dariya haɗe da ɗaga hannun ba ruwa na ta tura masa "Allah ba wasa ba, kin san aboki na bayarben nan da wannan inyamurin wallahi har ban son zuwa gidansu, kinga dai ba Kasar su suke ba amma matan basu yi kyashin kula da su ba" Ya sake tura mata, bata so ta shiga harkan iyalinsa, don bata so ayi mata. Amma ta dake ta amsa da "Allah GF (grand frere) matanmu na kokari wajen kula sai dai abinda ba'a rasa ba, aure ɗan hakuri ne" Ta tura haɗe da aljani mai murmushi "Ni wallahi har danasanin aure yanzu nake, kai aure dama haka yake, mace bazata natsu ta kula da kai ba wai kar ka raina ta, na yaushe kuma. Shi yasa mazan Hausawa da buzaye suka gwanance a Aron hannu " Sai da tayi dariya ma'ishi kasancewa ta san ya tsani kalmar nan ta aron hannu da gayu ke amfani dashi mai makon zina. "dariya ta kike wai, kin san dai a nahiyar mu anan ba Kasashen fa suke da Al'ada iri ɗaya kamar Nijar da arewacin Nijeriya. Toh kina isa arewacin Nijeriya zaki ga korafin iri ɗaya ne, matan banda rashin kula har da da rashin biyayya suna tunanin gyaran gado ne kawai aure, mstwww " Nan ma dai dariyar ta sake bin shi da shi, tana mamakin sa. Toh ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Don kuwa yanda ta tsara rayuwar Aurenta bata tsammanin za'a samu matsala da ita a wannan fannin. Burinta kullum rayuwar aurenta ya zama sanadin shigar ta Aljanna mai babban daraja. Ganin ba ta niyyar bashi haɗin kai balle har ya c faɗa mata matsalarta yasa ya juye hiran zuwa tambayar ta ya zancen karatunta da take shirin kammalawa. Karfe goma na dare yai mata sallama ta sa masa tsiya faɗi take "wajen buzuwa fa zaka kake sallama, ashe suna da rana haka" dariya sukai gaba ɗaya sannan sukai sallama. 2012 Zaune take tana kintsa kayanta saboda zata kai ma Haj Mas'ouda ziyara kasancewar ta kammala karatunta na licence na shekaru 3, (kwatankwacin kwalin degree inji yan 9ja) sakamako fito yayi kyau. Wannan zuwan ma baffanta ya sa ta nemi gurbin karatun masters a cewarsa tunda taki aure. Wayarta ce ta fara kuka, kallon number ta yi don ko mutuwa take bazata manta numb nan ba. Kamar bazata ɗaga ba chan dai yana gab da tsinkewa ta ɗaga haɗe da sallama. "meye duniyar ne Halima, ace zaki iya share ni haka. Shekara biyu kenan fa, haba Halima alkawari bai ce haka ba" Ya faɗi yana mai kwantar da murya. " qui est sur la ligne (wanene akan layi) ta faɗi a ɗan fusace duk da ta fahimci muryan. Dariya yayi mai isarsa sannan yace " mon nom est Hammad de agadez (sunana Hammad daga agadez)" Ya faɗi yana dariya. "Au wai kai ne, ni ban gane muryan ba." Nan suka gaisa. "ina takwarata" Ta tambaya "hmmmn hajiyata kinsan mun rabu kuwa" Ya faɗi cikin halin ko in kula. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Me yayi zafi haka Master" Ta faɗi tana mai dafe kirji kamar yana ganinta "Wallahi bazan iya ba, idanunta sun buɗe da yawa, duk wani hanyar rage ruwa ta san shi, wai yarinyar nan ce ke faɗa min don bana laguda ta toh tana shakkar son da nake ikrarin ina mata" "haba Hammad, yarinya ce fa karama, hakuri zakayi, amma dai da aka tsaida rana sannan zaka ce ka fasa, ka yi hakuri" "yarinya ce karama amma ko ke da kika gama jami'a ba za ki yi abubuwan da take ba, har ɗaga wuya fa ance tana yi." " Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ni ko ta ɓata wayonta kuma ta kunyata ku, Allah raba mu da zaɓen tumun dare." Ta faɗi tana mai kashe wayar. Cigaba da shirya kayanta tayi sannan ta ɗauki hanyar Niamey Sai chan cikin dare sannan ta labarta ma Abdoul duk inda hankalinsa ya kai a yawa duk sun tashi. Ya rasa meyasa lamuran Halima ke tsayar masa a rai, ko dan tana mutunta shi ne ko menene shi kan shi ya rasa ganewa. Tun daga ranar Halima da Hammad suka fi tif da taya mannewa kafin a ankara shakuwarsu tafi na da. *** Ziyara suka kai birnin Paris na Kasar Faransa. Sun sauka a ɗaya daga cikin otel da suka fi tsada watau RITZ Paris da ke lamba ta 15 Place Vendôme, 75001 Paris. Sunyi wanka, sun rama sallolinsu sannan suka zauna cin abinci. Daga nan kuma suka Lula duniyar da su kaɗai suka san da shi don kawar da gajiya. Basu kai ga isarwa ba yaji saukan ruwa a fuskarsa. A firgice ya farka yana lalube ko idanunsa zai kai ga Halima amma ina sai ta kai ga Agaysha tana huce kamar mai shirin dambe. "Zina kake min a kan gadonmu na sunna" Ta faɗi hawaye na kwarara daga idanunta. "Zina kuma Agaysha" Ya faɗi a ruɗe, ko dai abinda ya ke tunanin a mafarki ne a gaske abin ya faru, amsar da ta bada ya dawo da shi daga tunani. "Ya zaka kwanta kana numfarfashi a cikin barci, Allah ya isa tsakanina da Aljannar da ke shiga gona ta. Don taga bana ganin ta, kai kuma sai jin daɗi kake" Ta karasa tana gunjin kuka. Rungumo ta yayi yana tura mata sakonni masu wuyan fassarawa, "mafarki nayi kina shayar dani zumanki nefa ma femme (matata)" da haka ya rufe bakinta. Bata sake ɗaga zancen ba yayin da shi kuma ya gagara cire shi a ransa. * ** Zaune take tana kwalliya, murna ne fal a cikinta don grand frère ɗinta Abdoul zai kawo mata ziyara. Sanye take da riga da skirt na material mai kaloli, ɗinkin ya fito da surarta ya bayyana asirtaccen kyawun da Allah ya mata. Feshe jikinta tayi da turaruka fin kala biyar, duk da kasancewarsu masu saukin kuɗi sun fitar da kamshi mai daɗi da kwantar da hankali. Karfe biyu ya iso, kiranta yayi a waya cewan ya iso, yayin da ita kuma ta zura hijabinta purple kasancewar shine kala mafi karanci a kayan. Falon su tayi masa iso, wanda ke fitar da sassanyar kamshin freshener irin na Larabawa. Lumshe ido yayi sanda ya sa ka fara guda a cikin falon. Kamshin da ya daki hancinsa ya sa masa nishaɗi, se da ta kawo masa abin tarba sannan ta samu waje ta zauna. "yan mata" Ya faɗi fuskarsa yalwace da murmushi. "yayan yan mata" Ta faɗi tana maida masa da murmushi. Tsare ta yayi da ido yana neman abinda zai bambamta ta da halimar da ke zuwa masa a mafarki, mafarkinsa na jiya ya dawo masa inda yayi Wai Halima ta haihu an samu Abubakar suna ce masa saadik . Hure masa fuska tayi. Nan da nan yayi farka daga duniyar tunanin da ya shiga. "lafiya grand frère" Ta faɗi cikin yanayin damuwa. "Babu komi je pense à ton avenir (ina tunanin future ɗinki ne) " Ya faɗi yana murmushi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan iyakarsa fatan baki ne. "wani abun ya faru ne?" Ta faɗa a ɗan firgice, kallonsa take cikin kwayar idonsa ko zata fahimci wani abun. Ganin bata fahimci komi ba yasa ta saukar da idonta. "abinda da Hammad ya miki mana, aka ce miki baya damuna ne. Addu'a ta kullum Allah baki miji na gari, shekaru ashirin da biyu ai ba a ce da ke yarinya ba" Ya faɗi ya na basar da damuwar da ta shiga kamar bai san tayi ba. "Au da ma Shine, ai mun shirya kasan na faɗa maka wancan yarinyar bacin biyan maza da take har da ɗaga wuya tana taɓa wa, wai karamar yarinyar da aka rabu da ni yar jami'a saboda ita kenan" Ta faɗi tana dariya kasa kasa. "don ta sha giya Shine me? Ba hakan ya ganta ya ce yana so ba, in ita giya tasha ke anya beyi gwajin takalmi da ke ba, wani irin zuciya gare ki, kina tunanin zai chanza ra'ayinsa ya aureki ne bayan tun farko ya nuna miki shi ba mijin aure bane, haba Halima da hankalinki da komi kina bari so na sarrafa miki rayuwa, oh ku ne masu bin na turawa da suke cewa 'everything is fair in love and war' Ko? Toh ki sa ma ranki cewa rien est juste dans l'amour et la guerre (nothing is fair in love and war)" Ya faɗi a fusace, tabbas ta san gaskiya ya faɗi amma ya zatayi da son Hammad. Kuka take mai hana sukuni ido ya sa mata duk da yana jin kukan har kahon zuciyar sa. Sai da tayi mai isarta sannan ya fara lallashinta. "Kinsan rayuwarki na da mahimmanci a tattare dani, kiyi hakuri kiyi tunani kinfi karfin Hammad in aka dubi halayya da kamala, ki hakura tun yanzu kafin ya kara miki wani takaicin gaba. Ki kuma cigaba da addu'a Shine maganin komi" haka yayi ta bata kalaman karfin gwiwa har ta sake. "Ana fa fama da zazzaɓin cizon sauro, da typhoid ga tattalin arzikin duniya na cikin ha'ula'" Ta faɗi tana mai sauya hiran. "Eh wallahi, ko ina har fa Nijeriya kuma rashin tsaftar muhalli duk ke kawo hakan fa" Ya faɗi cikin halin ko in kula. "Ta ya kenan?" Ta tambayeshi don bata fahimce shi ba. "sakacin mu yayi yawa, ba ma gyara gwata a anguwanni, bola ko ina, ciyayi sun fito jikin gidaje, amma son kai irin na mutanen mu yanzu ba'a gyarawa. Sauraye sun samu mafaka, in ka gyara cikin gidan ka ai zaka fira waje, kinga dole zazzɓin cizon sauro yayi yawa. Typhoid kuwa yanzu kinga damina ne, muna tara ruwan sama muna sha ba tare da an tafasa shi ba. Tsakanin sama da inda ka tara ruwa ai akwai germs da zasu shiga. Ko rijiyoyi da suka cicciko kinga ai ko alam mutum yasa dattin zai kwanta kafin a sha." "wai yaushe ka fara aiki da asibiti ban sani ba. Tunaninka sak abinda ya ke faruwa. Allah dai ya kare mu da lafiya". "Aameen ya rabbi" Haka suka cigaba da hira yaje yai sallan la'asar ya dawo, sai wajajen biyar na yamma yai musu sallama suka rabu. Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon soyayya suka fara da Hammad, duk tayi masa zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai kawancenmu yafi soyayya mahimmanci kar ki bari zugin kewaye ya zama katangar biyan bukatar zukatanmu" a haka yake binta da daɗin baki har ta saduda. Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su ya zama hiran da suke na batsa ne, tun bata sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan bata kula na musamman. Sukan kashe awanni suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa, wata rana suna cikin irin wayar se ya ce mata "Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan min wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya" Ya faɗi cikin sigar rarrashi. "Anya sweetyna kana so na kuwa, kasan dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na ba don faranta ranka" Ta ce a fusace "wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi aron hannu da ke, wallahi iyakarmu romance, ba zan taɓa keta haddinki ba." haka yai ta faɗa mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta amince. Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu Kasar Faransa. "haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a zolayance "Na duba ne naga tabbas in ba wani kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida, shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda tafiyanmu ta nuna zuwa France" "aiko da ka taka zero, yanzu take shirin shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj Mas'ouda da ke shigowa falon. Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda, murmushin yake ta sakar masa wanda ya tabbatar masa da zarginsa. "shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya samu kansa da tambayar kansa hakan. "Sai muje mu dawo kawai momma" Ya faɗi ma Haj Mas'ouda yana murmushi "Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad wanda sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce fuskanta na nuna alamun takaici. "Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki da akayi ne yasa ta yin shiru. Se dai a ranta tai ta surutun an sa mata idanu. Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran ta. Sake-sake kawai takeyi don har sun kai ga gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau kara. Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa wayar kana ya sa wayar a handsfree "baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren. Da ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar da ta shige. "se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata yaran mutane toh Halima tafi karfin ka kuma ka fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa" bai jira amsar Hammad ba ya figi motar zuwa gida. Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan ta fara kuka tana salalami "Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki haba nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace an gama kwakule ki. Tir wallahi da halinki" Ta faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce. Kafafunta ta riko tana rokon ta, rantsuwa take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su asali ma wannan ne na farko nan dai ta kwashe yanda sukayi ta fada musu. "Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya kara tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji ne, duk macen da na lagudata ta yarda ta aure ni wahala zata sha, kuma haka duk wani namiji yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu sauran mutunci tsakani. Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa ga aikata, zina, kuma da yake ce miki turmi da taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da yace kada mu kusanci zina, kinga kenan hatta karatun batsa, zantuttukan batsa, kallon batsa ana iya danganta su da kananun zina, kuma abin nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne kuma azaban Allah gaskiya ne. Momma na wuce sai in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda. Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin ciki da kunya.Da kyar ta iya tashi ta sallaci magriba da isha'i sannan ta sa tuwon shinkafa da fakku (malohia murzazza) don taci. Jinsa take kamar maɗaci haka tai ta tutturawa har ta cinye kaɗan ɗin da ta ci. Har zata kwanta ta yi tunanin ta ba Abdoul hakuri don ta san da wuya ya sake amincewa da ita. Nan ta iske missed calls ɗin Hammad fiye da talatin. Bayan ta tura sakon ban hakuri ga Abdoul ta kwanta tana wasikar jaki nan sai ga kiran Hammad ya sake shigowa, kamar bazata ɗaga ba don yana gab da tsinkewa ta ɗaga da sallamanta "Ni zaki wulakanta Halima? Nasan hana ki zuwa akayi amma ya akayi baki tsara su yanda mukayi planing ba, kin ban mamaki kuma ki rusa mana budget don wallahi zancen aurenmu yasa naso haɗuwar mu ba komi ba wallahi" Yayi shiru yana huci a tunaninsa zata ce wani abu sai tayi shiru wanda hakan ya kara harzuka shi. "kin ma maida ni mahaukaci ne ko, haka Allah ke abunsa, ya bani daman mallakar ki a matsayin mata nai wasa da wannan daman yanzu gashi kuma soyayyar ta dawo min kina min wulakanci" Ya faɗi kamar zeyi kuka. "tsaya! tsaya! Hotel ne zakayi zancen aure dani, ina in har haka ne gidanmu yafi dacewa da muyi, ban taɓa haɗa makwanci da namiji ba kuma bazan fara akanka don kana min barazanar aure na zaka yi ba. Na kara gode ma Allah da ban saɓa masa saboda kai ba, wallahi kunyar da naji yau yafi min sau dubu akan wanda zanji ranar kiyama inda na cikata umurninka." Ta karasa tana mai shessheka. "haba Mon amour (masoyiyata) kin san Allah ɗaya ko to Je t'aime de tout mon Coeur (ina sonki da dukkan zuciyata. Kiyi min rai ki sake bani lokaci mu tattauna wallahi duk abinda zamu tattauna mai mahimmanci ne, akan zancen aurenmu ne. Ki taimaka min ba son ni ba" Ya faɗi cikin sigar lallashi da ban hakuri. "Na ji gobe ina gida kazo kawai" Ta faɗa a takaice. "wani irin kina gida, haba sweetyna kar kiyi min haka, in zaki samu fitowa ki same ni a hotel din. Don Allah ba don ni ba" abinda ya samu kansa da faɗi kenan bayan ya tattara natsuwarsa zuwa yanda bazai bayyana fushinsa. "bafa zan saɓa ma Mahalicci na don faranta ma abinda ya halitta ba. Kayi hakuri kawai kazo gida" itama ta faɗi kai tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba. "lallai duniya juyi juyi yanzu duk son da ake min an dena ne, sai ni kuma da Allah ya jarabta da sonki. Wai ba kiyi mamaki ba Halima, anya zan iya rayuwa babu ke, ki taimaka. Mana don Allah" Ya karasa da sumbatar iska, wanda yasan Halima na so kwarai da gaske koda ranta a ɓace yake da ya mata takan manta inda kanta yake. A mamakinsa sai yaji tace "Ni in bazaka zo ba muyi maganar anan shike nan, banyi mamakin chanzawarka ba don kana son gani na komi zaka iya" "shike nan kin zaɓi rabuwarmu akan ki zo, kin san dai babu abinda zan miki, just tattaunawa zamuyi akan mafitanmu" Ya nace akan son yardar da ita akan ra'ayin shi. "se da safe don na ga baka da niyyar gane annabi ya faku. Bazan saɓa ma Mahalicci na bafa" bata jira cewarsa ba ta kashe wayar. Buɗe kofar da akayi yasa tayi saurin share hawayen da ya gangaro mata. Har ga Allah tana son Hammad amma ya ta iya. Rungumarta Haj Mas'ouda tayi tana share mata hawayen. "kin cika yar hallak Halima, ubangiji ya dubi hakurin ki ya baki mijin marainiya, kar ki sa damuwa a ranki, wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka mata masu cewa zasu bada kansu don a auresu babban kuskure ne da suke tafkawa, in Allah beyi shine mijin ba sai dai bakin ciki ya kashe su don bayan asaran mutuncin su har da asaran masoyi. Kuma duk saurayin da kika ba shi kanki walau karami ko babban zina wallahi ranar da aka ɗaura aure duk son kan koma kiyayya, hantara da wulakanci zaki kwasa maimakon soyayya da tattali. Halima bakya mamakin meyasa auren yanzu babu karko wallahi maimakon mata su gina soyayya a zukatan masoyan su sukan gina sha'awa ne, tura ma samari kalamai da hotonan batsa wai da sunan su rike su har su aure su. Daga ranar da akayi auren kuma ya kashe kishin shaawarsa se ya fara gasa ta. Ki cigaba da addu'ar zaɓin Allah ki aje son rai. Gara ki so mijin da kika aura da ki auri mijin da kika so. Kar kiyi gaggawa a aure, Allah ne mafi sani a dukkan Al'amura, Allah ya miki Albarka " Ta karasa tana lallashi ta, sannu a hankali ranta ya in fara haske ta nemi bakin cikin ta rasa. Hamdala tayi ta nanatawa a zuciyarta akan gatan da Allah ya mata na samun mai ɗaura ta a hanya. *** Sannu a hankali ta fara farfaɗowa daga cutar da ke addabarta, tun tana tuna Hammad sau ba adadi har ya zama takan kidaya su, tafiya tafiya har bai wuce ya faɗo mata sau biyu ko uku a rana ba. Kwatsam wata ɗaya da faruwa wannan Al'amarin suna kallon tashar Dounia TV (Radio Télévision Dounia) su duka har da baffa, bayan Ummitr Bingel sa Gimbiya Zuby sun gama shirin da sukanyi na mu shakata sai aka sako tallan auren Hammad da wata Amina. Shiru ya ratsa su a falon har aka sa wani shirin. Se chan ne baffa ya nisa ya musu nasiha mai ratsa zuciya, ya nuna musu illar yaudara da kuma mata su zubar da mutuncinsu. Tun daga ranar ta tattara lamuran Hammad ta sa a bola sannan ta kona. Ta samu aiki a makarantar da ta gama wato Université Abdou Moumouni bayan ta kammala masters ɗin ta. Ba laifi tayi kiba tayi kyau abinta yayinda maza suka sa ta gaba, ita kuma bata basu uzuri daga sun nemi raina hankalinta zata kora su, tsoranta zuciyarta ta kamu da son wani ta kara wahala. *** 2014 ... Gari na wayewa dare na yi kwanaki na tafiya har su isko watanni. An wayi gari Halima kan manta Hammad in ba taji an kira sunan shi ba ko taganshi kasancewar yakan kawo matarsa makarantar da take aiki. Bata da wani abokin ɗebe kewa da ya wuce Abdoul sun shaku sosai, komi ta samu in na yara ne takan siya ma yaransa ne safiyyah da ta ci sunan mahaifiyarsa hakan yasa suke ce mata Ummu abiha ,sai biyun Halima kuma a hakan suke kiranta. Agaysha ta san da zaman Halima kuma tana kishi da ita amma bata ɗauka da gaske bane don a cewarsa Halima kawarshi ce kawai da ya ɗauka kanwarsa uwa ɗaya. Hakan ya kwantar mata da hankali don duniya in dai kawance kawai Abdoul ɗin ta zeyi da koma wacece ba soyayya ba toh babu abinda ya shafe ta. Kalmar budurwa ne dai ta tsana don ko da wasa kace mata "ga budurwan Abdoul" toh zaka shiga cikin jerin makiyanta da bata da kamar su. *** Wata rana cikin ranaku, Halima na zaune a ofishinta da ke cikin Faculté des Sciences, kira ya shigo wayarta wanda daga amon kiɗan ta san yayanta ne. Da sallama ta amsa wani farin ciki na ratsa ta, lumshe ido duk sukayi a yayin da suka ji muryoyin junansu, shiru sukayi na yan dakikai, su kaɗai suka san mai zukatansu ke raya musu. "yan mata jiya nayi mafarki da ke wanda naga ya chanchanci in isar miki shi ta hanyar labarta miki". Ya katse masu shirun. "wow! Allah sa alkhairi ne MAFARKIN ABDOUL ɗin" Ta faɗi tana dariya. Shima cikin dariyar ya caɓe "Au wai har kin sa mai suna ne, tun kafin kiji" tun kan ya dire tace "kasan da ace ina da fikrar rubutu babu abinda zai hana in mai da shi littafi har in sa mai sunan MAFARKIN ABDOUL" Ta faɗi cike da alamun iyakan gaskiyarta kenan. "wai tsaya, in kuma mafarki nayi ana nakaɗa miki duka, shima alfahari zakiyi dashi" Ya faɗi yana mai cigaba da dariya, wanda ta kasa bambantashi da na keta. Cikin Alamun gundura da dariyarta tace "Ni ba abinda ke cikin mafarkin ya sani murna ba balle ka samu abin tsokanata da shi, wanda yayi mafarkin ne ke da mahimmanci Alaranma" dariyan ya cigaba da yi ba tare da ya damu da fushin da ta fara ba. " Toh hajiya halimatu ai ba yau ne farau ba, ina ga ba'a cike sati. Banyi sau biyu ba, wannan dai kawai ya tafi da hankali na sannan ya magance min matsalar da nayi shekaru biyu ina fama. Shiyasa zan faɗa miki in ba haka ba ai se kin biya. Ya sake kara sawa yana dariya. "yanzu kana da matsala shi ne baka taɓa faɗa min ba, kuɗi ne ko ciwo ko har yanzu mamansu Ummu abiha ba ta dena tozarta ka bane." Ta faɗi kamar zatai kuka. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa take da mahimmanci a gareshi. Takan nuna damuwa ko farin ciki yayinda ɗaya ya same shi. "ba ko ɗaya, wato ke hajiya ko. Kina kwasan. Albashi, toh cepa miliyan ɗari nake so, karkaɗa kunni ki sha labari" Ya faɗi. Yana dariya, itama ta tayashitayashi MAFARKI...+ "Na ganni ne a wani lambu mai ban sha'awa, bayan kayan marmari da ya yalwatu a cikin lambun har da wasu furanni masu fitar da daddaɗar kamshi wanda ya sa na kara kishingiɗa a resting chair ɗin da nake zaune a kai. Lumshe idanu nake farin ciki na yalwatuwa a zuciyata. Sallaman da kikayi ne yasa na buɗe idanu ina mai sakin murmushi. Farantin hannunki kika aje a gefe sannan kika fara shayar dani salad ɗin kayan marmarin da kika zo da shi. Wanda daɗin sa bai sa na ankara da ya kusan karewa ba har se da kika daga Yankar karshe na abarba sai na na riko hannunki haɗe da spoon ɗin da ke baki na. Hakan yasa kikai saurin ɗago idanu kika kalle ni, idanunmu na haduwa kika kasa ɗauke idanu na wasu dakiku. Muna cikin haka sai ga yara biyu sun zo a guje suna kiran "Abbu! Ummu!" kallo ɗaya nayi musu na san yan biyu ne kuma daga tsatsonki suka fito saboda tsabagen kaman da sukayi da ke. Sun faɗo jiki na kenan suna haki kiran sallah ya tada ni daga barci, faɗa min me kika karanto a ido na da kika tsare ni da kallo" Ya karasa yana mai tsokanarta, "ka bari sai mun sake haduwa a dreamland sai ka min tambayar, kasan me?" Ta dakata ko zai amsa "A'a se kin faɗi" Ya bata amsa Se da tayi dariya son ranta sannan tace "za ka yi kyau da rubuta labarin soyayya fa. Wannan iya tsara lbr haka" ba ta dena dariyar ba shi kuma kansa duk ya ɗaure, "yanzu ba za ta ba MAFARKIN mahimmanci ba bare ta kai ga fahimtar abinda ya ke damuna game da ita b" Ya faɗi a ranshi yayin da a bayyane shiru yayi mata kawai. Jin ya kyale ta yasa T faɗin "hello!" dariya kawai ya bi ta dashi kana sukai sallama. Shiru tayi tana tariyo labarin da ta sanya ma MAFARKIN ABDOUL, bata san me ke shiganta ba ta dai tsinci kanta cikin wani yanayi daga tafin kafarta har Kirjinta wanda salon bugun zuciyarta ya chanza nan take. Amon muryar Abdoul take ji a kunninta sa'ilin da yake bata labarin. Nan take wani farin ciki ya mamaye ranta yayinda tsoro kuma ya shige ta sanda ɓari guda na zuciyarta yace da ita "in baya sonki fa". Nan take sai ta shiga damuwa. Sai sa su ka yi sati biyu babu wani kwakkwaran magana da ta shiga tsakanin su, iyaka sukan gaisa da ɗan hira sama sama. "Amarya a gidan Abdoul barka da yini" Ya shigo WhatsApp ɗinta daga lambar aminin Abdoul Yahai. Aljani mai dariya kawai ta tura masa sannan suka gaisa a mutunce. "kina gara ɗan uwa na fa Halima shi tsoransa ki yankuna shi wanda hakan zai taba zumuntarku amma wallahi nasan duk kuna sonjunanku, meye amfanin cutar da kai, in shi ya kasa buɗe hanya ke baza kiyi ba? Ya tura mata haɗe da aljani mai jan kai. Bata ce komi ba sai aljani mai dariya da hawaye ta tura masa, ganin bata da niyyar bashi haɗin kai yasa ya kyale ta. Daren ranar ta tsawaita hirarsu da Abdoul har yake faɗi mata mafarkan da ya keyi kusan kullum inda yake kara hura mata wutan sonshi a ranta. Chan dai ta ɗaure ta tura "inaama! Inaama!" Yana gani ya tashi zaune, sannan ya kira ta. Ringing biyu ta ɗaya da sallama. "me kike cewa ne Halima ɗazu" addu'a yake ta faɗi abinda ranshi ke son ji. " cewa nayi inaama! Inaama MAFARKIN ABDOUL zai tabbata. Da an samu maaurata gwanaye da zasu sadaukar da rayuwar su wajen faranta ma juna" Ta faɗa bil hakki abinda ke ranta kenan. Ya daɗe da sanin Halima irin mutanen da masana psychology kan kirasu da extrovert ne, sam bata ɓoye ra'ayinta akan abu, ya daɗe yana jinjina mata ɓoye soyayyar sa dake zuciyarta, ko da yake matantakanta ya taimaka mata ainun wajen ɓoyewa. "Halima kina da matukar mahimmanci a rayuwata, in na koma zindar karshen sati, zanyi magana da mama da Maman Ummu akan auren mu, fata na kar su kawo matsala, shekara mai kamawa zamu tabbatar da MAFARKIN ABDOUL, sai in kama miki gida a nan Niamey ko ya kika ce" mamaki ya cikata, wannan sai kace jira yake ta furta. "Amma wannan assurance ɗin da kayi min anya beyi wuri ba, bana son abinda zai taɓa alakarmu fa, kasan ban iya son abu ba, ina sonka da yawa Abdoul" Ta furta a sanyaye wanda hakan yasa yaji tausayin ta ya mamaye shi. " kar ki damu ina tare da ke insha Allah ba gudu ba ja da baya" da haka suka dulmiya duniyar soyayya ba ji ba gani. Wasu kalaman in ya furta mata har mamaki takeyi da ma chan yana sonta ne. Da kyar sukayi sallama bayan sun tsara yanda zai nemi aurenta da kuma yanda aurensu zai kasance. Cikin watanni biyu sun shaku sosai fiye da wanda sukayi a baya. Kulan da suke ba junansu abin ba'a magana, ko da yaushe suna nane da juna walau a Chat ko a waya. Cikin tsarinsu ne bazata faɗa ma kowa ba har se yaje yayi magana da iyayensa in sun tashi zuwa neman aurenta. Duk yanda yaso zuwa aiki ya hana shi motsi kasancewar ya fara aiki da Ministère des Affaires Étrangères et de la Coopération ( Nigerien Ministry of Foreign Affairs and Cooperation) hakan yasa ya kan bi tawagar da ke zuwa duba République Niger ambassade na sauran kasashe. Yanayin rashin zama yasa bai tafi da Agaysha ba amma wani sa'in musamman in yara na hutu sukan je a tare.Soyayya suke mai cike da tsafta, har yanda aurensu zai kasance sunyi, wani zuwansu Abuja a tarayyan Nigeria ya siya yadin material ya bada a Hanifa boutique ya ba da a ɗinka bridal gown a Hanifa creations & couture da ke lamba ta 10, Gimbiya Street area 11, garki Abuja. Tun da ya kai yake manta santin ɗinkin. Don sai da ya ba mai wajen haj. Hadiza shawara in da hali ta buɗe musu a Nijar ko suma zasu ci romon ɗinki hadaddu. Dariya tayi tace " me zai hana, Nijar da Nijeriya ai duk ɗaya suke, zamu duba se a buɗe a Niamey in de zaku kawo ɗinki". Yini yayi yana faɗa ma Halima karamcin su tun daga siyan material har ɗinki fatansa su cika masa alkawari. Halima bata tabbatar da haɗuwan dinkin su ba sai da ta leka shafinsu na Instagram, rudewa tayi tana nuna ma momma haj mas'uda, faɗi take "momma anya bazamu aika sauran ɗinku nan ba, ɗinki sunyi kyau" itama dai haj mas'uda ta yaba da kyawun dinkin har tayi shaawar aika ma kawarta haj. Maijidda dake birnin Kano in za'a samu wanda ze kai tunda suna home delivery a Nijeriya. Hakan kuwa sukayi sanda Abdoul ya tabbatar masu da cika alkawarin su. Sai akayi da Abdoul ya karbo tunda za'a kammala kafin su dawo Nijar. Bata tsaya ba sai da tayi booking kwalliyar da za'a mata wajen ramat makeover, sannan ta bada aikin waka wajen mai zazzakar murya da amon muryarta yafi zuma daɗi wato sa'a Vocal. "wai ke iyayensa basu zo ba duk kun gama shiri ko dai ku zaku aurar da kanku ne," faɗin haj mas'uda da ta fada mata ta yi booking wakar sa'a Vocal, da irin karamcin da sa'a tayi mata da ta kira ta a waya. "momma kinsan yace January yake so ayi, da sunzo za'a yi komi gaba ɗaya" Ta faɗi tana rufe ido. "Au! Wai dama kina da kunya, bayan ina ganin kosawa a tare da ke." itama ta faɗi tana dariya. "momma shekaru na fa ashirin da biyar, kinga kenan ai na tsufa, ko" dukan da aka kai ma cinyarta yasa ta yin shiru. "Toh shi ɗin kin tabbatar da ya isa da iyalinsa? Kuma baza'a samu matsala ba, kin san maza in har basu isa da matansu ba aurensu matsala ne. Ki cigaba da addu'a de, in Alkhairi ne Allah ya tabbatar, in babu ya zaɓa miki abinda yafi alkhairi" Jikinta yayi sanyi, yaushe rabon da tayi addu'a, a ganinta ai shi ne alkhairi tunda ya zo bayan rabuwanta da Hammad. Haka dai ta fara istigfari tun daga zaune. Ranar itace har da tsayuwar dare. Dawowannan Abdoul ya sa ta farin ciki da annashuwa, gani kawai aurensu ya zo. Bayan ya aje musu sakon ɗinki ya dauki hutu ya wuce zindar. Nan ma ya samu tarbo mai kyau daga Agaysha. Sai da ya kwana biyu sannan ya fara mata Maganar wata rana suna hira "Madam aure nake son yi, ba don bana sonki ba sai don gazawarki wajen kula dani, ina sonki, banda niyyar kara aure amma yanda kike tafiyar dani yasa har shakuwar mu tayi karfi da Halima tace tana so na, kuma nayi niyyar aurenta" Ya faɗi kai tsaye. Kuka sosai ta fara, ganin yayi shiru yasa ta cakume masa wuyar rigarsa tana ihu tana kuka "kaci amanata, Halima ta munafunce ni, tayi ta ban shawara ashe sonka takeyi toh wallahi baka isa ba, zan kai karanka wajen baba don wallahi bazan yarda ba, ka gama zubar min da mutunci a idonta sannan kace zaka aure ta" rungumar ta yayi yana bata hakuri. Rigima taki ci taki cinyewa, kuka Agaysha takeyi ta ki cin wani abinci, tayi baki ta rame, yaranta ko wanka bata musu, ya bada hakurin taki, har sai da ta tsare shi ya kira Halima. Ringing yake Halima na kallo taki dagawa don takaicin tunda ya koma ko WhatsApp yaki hawa, bai dauki wayarta ba haka bai kira ta ba.. Sai da yayi kira uku sannan ta ɗauka da fara'arta ta gaisheshi, a dakile ya amsa sannan yace "Na kira ki ne in baki hakuri, sannan in faɗa miki bazan iya aurenki ba, tunda na faɗa ma Maman Ummu abiha zancen auren gida na ya koma sansanin rigima, matsalar gida na yasa nayi tunanin kara aure kuma ta min alqawarin canzawa, kiyi hakuri ki jingine zancen soyayya tsakaninmu". Saurin tare shi tayi tana mai kuka "kar ka min haka, ina sonka zan jira ka har zuwa sanda zaka shirya amma don Allah kada ka rabu da ni" kuka take Bil hakki. "kinga Halima matata ta ishe ni bazan iya ba nace, ko ana dole, mtswww" Ya karashe da jan tsaki kana ya kashe wayar. Tun daga ranar bai sake ɗaga wayar Halima ba, Agaysha kuwa hadiye shi ne batayi ba saboda kula. Tarairayan da yasa ya manta wata Halima a doran duniya. A ɓangaren Halima tun tana ganin abin wasa, taga har anyi sati ba kiranshi ba alamun shi yasa ta kira amininsa Yahai Bayan sun gaisa ta faɗa masa duk abinda ya faru ta kara da faɗin "ka bashi hakuri in laifi na masa, duk Dokan da zai sa min na yarda in dai zai aure ni, don Allah ka taimaka min." "shike nan Halima, yanzu haka yana hanya munyi alkawari zamu haɗu, zan kira ki yayinda nake masa maganar don ki ji komi daga gareshi" godiya tayi ta zuba masa kamar yai mata bishara da Aljanna. Ba'a yi awa ɗaya ba kuwa sai ga kiran Yahai, da saurinta ta ɗaga tayi shiru tana ji Yahai yace "wai ni Abdoul ina Halima ne ya zancenku ya kwana" "mtsw! Tana chan, ni bazan kara aure ba ina son zaman lafiyan gida na, tunda na faɗa mata ban sake neman ta ba" " ko dai ka gano wani mugun halinta ne, yanzu kake neman rabuwa da ita? " Yahai ya sake tambaya "kasan in da banyi aure ba babu abinda zai hana aje Halima a matsayin mata, rigima ce dai banso. In kana so kuma Allah sanya Alkhairi". Mamaki da takaici ya cika Halima, ta yi saurin katse wayar kafin taji abinda zai ɓata mata rai. Tsam ta tashi ta je ta faɗa ma momma abinda ke faruwa, mamaki ya cika ta kwarai amma ta bata hakuri haɗe da nasiha akan addu'ar su ya karɓu Abdoul ba Alkhairi bane a gare ta. *** A kwana a tashi Halima ta zama wata mara fara'a, kallon ko wani namiji a matsayin mayaudari take in akai mata magana tace tunda Abdoul yayi kowa ma zeyi. Wata rana kawarta faɗima ta zo gidan momma kamar yanda ta saba kawo mata ziyara. Suna cikin hira tace "wai dama Agaysha Iggalher ce matar Abdoul?" "Eh! Ina kika Santa?" itama ta tambaya. "kin san kanwar miji na ke auren babanta, da kyar uwar ta yarda akayi, jiya muka haɗu a gidan da yake ita ayshatou din ta haihu, Shine fa take nuna hotonki wai kin nace ma mijinta kina son shi har tana muyi kafa kafa da mazajenmu kwacen miji ki keyi " kukan da Halima ta fara yasa yin shiru. Ta fara bata baki tana cewa " bafa na faɗa miki don ki bata ranki bane, ina so dai ki yi aurenki ki huta sa surutunta, don ta ɗauki alwashin sai ta hukunta ki"+ "Ta ya zata hukunta ni, asiri ko tsafi bazai taɓa kama ni ba don na rike addu'ar da manzo SAW yace mu rike ma kariya. Manta da ita kinji yar uwa, jiya na dawo daga zindar fa" haliman ta karasa tana mai chanza hiran. Bayan magriba ta dauki waya ta kira Abdoul, sun gaisa kamar da ya tambaye ta mutan gida, itama haka. Chan ta ce "Na kira ka ne in ce ka ja ma matar ka kunni, babu abinda zanyi da mijinta, tun tana kira na tana zagi na ban tanka mata ba, har ya kai zata dinga yawo da hoto na da guntuwar wasikar da ban san da zamansa ba wai na rubuto maka, ai laifin ba nawa bane naka ne mijinta. Don Allah ku fita harkata nima daga yau na fita naku" "kinga bazaki zo ki ma mata na sharri ba, kuma Allah ya saka mata, aure ne dai nace banyi ko dole ne" Ya katse ta a fusace, "in da ina bin ta da sharri kasan da tuni na barka ka saketa ko, ko ka manta sirrin gidan ka yayi zama hannuna, Allah bamu Alkhairi" Ta kashe wayar gaba daya ta sallaci isha'i wani farin ciki take ji ta rasa na menene, hatta yan gidan sun kula don sai da baffa ya ce mata "Halima Albishir ɗin Aljanna akai miki?" Tayi dariya tace "kusan haka ne fa, kasan an ce budurwa in bata taɓa zina ba ta rasu tayi shahada da ladan jihadul Nafs. Ko dai zancen mutane ne baffa? " Ta tambayeshi tana dariya. " se kinga auren jikokinki Halima, Allah sa jinkirinki alkhairi ne " momma ta katse musu. " Allah dai yasa in tafi a sa'a, momma bata so in tafi, se hakuri in lokaci yayi" Ta faɗi tana dariya Haka sukai hira har goma da rabi sannan tai musu sallama ta je kwanciya Kwanciyar ta ke da wuya ta fara ciwon ciki, da kyar ta daga waya ta kira momma, a ruɗe ta shigo ta iske ta cikin amai cikin na murɗa mata. Cirko Cirko sukai akanta, bayan cikin ya lafa, faɗi take "ku yafe min, kuce su mama su yafe min, na yafe ma kowa" "ciwo ba mutuwa ba ai kinji sauki, sannu halima" kawai suke cewa. Huɗu da minti arba'in cikin ya sake motsawa, wannan karan tana wani irin mika in ya rike ta. Ɗaukan ta sukai zuwa mota don kaita asibiti basu san sun kai ta ga ajalinta bane. Daidai kwanar fita anguwansu tayi wani mika haɗe da salati, shike nan ta amsa kiran ubangiji. "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai baffa ke faɗi. Hajiya mas'uda kuwa mutuwar zaune tayi. Hawaye na gasar tsere a fuskarta. NADAMA....+ Tunda ya sauke wayar jikinsa yai masa sanyi. Anya ya kyauta mata kuwa, yarinyar da ke ɗaukan shi mai babban daraja ya yankuna haka. Shiru yayi kalamanta na dawo masa ɗaya bayan ɗaya. "wai me yasa ake ɗaukan maza masu mata mayaudara ne, duk wanda nace ma kai zan aura sai sun ce Allah sa kar kayi min halin, in dai aje wani spare, tunda soyayya ba mota bace meye amfanin tara samari" Ta faɗa masa wata rana suna waya. "Ni dai ba yaudaranki zanyi ba. In kinga ba mu yi auren nan ba mutuwa ce, kece fa mafarki na kece tunani na a farke" sai da yaji kunyar kansa da ya tuna alwashinsa gare ta. "momma cewa tayi ba komi ya sa maza masu aure iya yaudara ba sai ganin suna da matan su a gida, ba su da halin karin aure amma su je suna kwadayin soyayya da wasu, basa ko la'akari da suna da yaya mata ana iya musu suma. Wasu kuma ba laifinsu bane matan su ke hana su aure, su ma basa tunanin mazajensu na iya mutuwa ko su rabu wani mara matan ne zai aure su, ai aure kanta wa'adi gareta ban ga abin tashin hankali akai ba" "lafiya ka zauna kana tunanu" Agaysha ta katse masa tunaninsa nan de ya zauna sukuku har lokacin barci yayi ya kwanta. *** Sanye take cikin shiga mai kyau, kyallin da tufan jikinta ke fitarwa kaɗai abin kashe ido ne, babu wani al'auranta da ke waje, fuskarta cike yake da murmushi. "Abdoul kaga ɗaukakan da Allah yai min ko, ka gafarce ni in na saɓa maka amma na tafi bazan sake damunka ba" Ta na faɗin haka ta fara tafiya, taurari sun kewaye ta, haske ya bayyana, kamshi ta ko ina. "Halima! Halimaaaa! Halimaaaa!" yake faɗi iya karfinsa wanda ya tada Halima daga barci. Kallon agogo yayi karfe biyar na asuba ya tashi ya ɗauro alwala nan ya fara jero nafilfili kasancewa biyar da rabi ake kiran sallah. Tunani yake dole ya je Niamey su sasanta kansu bazai ma Halima haka ba, bata chanchanci abinda yai mata ba, ai Halima matar alfahari ce, wacce Burinta tayi aure tayi Ibadan da zai zama sanadin shigar ta Aljanna. Yana fita Agaysha ta kira kawarta da ke mata rakiya zuwa gidan malamin da ke mata aiki akan zasu je, Abdoul ya tashi cikin dare yana kiran sunan Halima. Ko da ya dawo sallah yayi mamaki da bata tsare shi da masifa ba, illa hillatarsa da tayi ta yi har ya shagala. In bayan sun samu nutsuwa take faɗa ma sa zai kai ta gidan kawarta zasu je ta'aziyya, ba gardama ya amince. Karfe goma sha biyu suka bar gida ya sauke ta sannan ya karasa share zamna don ya samu sallar Jumma'a a Grande Mosque de Zinder. Bayan an iddar da sallah ne aka bada sanarwan za'ayi sallan jana'iza, na wata baiwar Allah da ta rasu. Haka kawai yaji tsoro ya shige shi. Bai gama jawo natsuwa ba idonsa ya kai ga baffa, da mahaifin Halima suna share kwalla. Kallon zanin da aka rufe ta yayi in bai manta ba yana daya daga cikin ɗinkunan da ya amso masu har yana mata tsiyar tayi zani plane. Se da ya sa ma zuciyar sa mahaifiyarta ce ta rasu sannan ya samu natsuwar tashi ayi sallan da shi. An idar haka yabi tawagar farko, ya kula da yanda mahaifinta ya rushe da kuka sanda suka yi ido hudu dashi. A harabar masallacin aka shigo da hillux aka shimfiɗe gawar. Yana ta kallon mutane ɗai ɗai, ga yan uwanta mata daga sashin mata na masallacin. Da kyar ya shiga motarsa, inda wasu yan anguwan su haliman suka cika motar. A hankali akai ta tuka motar har makabarta inda an riga an gine mata lahda ɗinta. Ko a nan sai da mahaifin Halima ya jawo shi, yayin da ake maida kasan da zai rufe ta. Suna nan tsaye bayan an rufe ba ma kusan minti arba'in suna mata addu'a kamar yanda manzo SAW ya umurce mu kar muyi saurin barin makabarta yayinda muka rufe wani namu. Har suka fito babu wanda yace uffan, ya kula da Muguwar kallon da baffa ke jifan shi da shi, yayin da mahaifin Halima ke masa kallon tausayi. Sun fito gate din makabarta kenan mahaifin Halima yace "Abdoul ya hakurin mu, Halima kuma wa'adi ya cika. Sai mu" be kai aya ba sai ganinsa sukai a zube sumamme. Shafa masa ruwa akai sannan aka sa shi a mota, baffa ne ya ja motar suka dunguma zuwa gida. Banda ajiyar zuciya babu abinda Abdoul ke yi, ina ma zai farka daga barcin nan. Nasiha sosai suka haɗu sukai masa har baffa da ke cike da jin haushin sa. Ya shiga cikin gida yai musu ta'aziyya sannan ya koma wajen maza. Shi dai zai kira kan shi da mutum mutumi don motsin kirki gagaransa yayi. Ya kasa yarda Halima ta rasu. *** Can su Agaysha sun gurfana gaban malaminta, bayan duk surutanshi da shafe shafensa yace "Halima anyi ta ne kawai don ta kawata MAFARKIN ABDOUL, sai de akwai wasu yara a gaba da nake hange, kuma bana tsammanin naki ne amma tabbas na Abdoul ne, yanzu de za'a yanka bakin bunsuru ayi rubutu dashi ki sha, kishiya sai ta abin hawa ba dai mutum ba, " yana gama faɗi ta aje masa cepa dubu talatin sannan suka juya. Ko da ta isa gida bata iske shi ba, nan tsoro ya cika ta kardai ya je wajen Halima ne. Karfe tara da rabi ya shigo gidan da sallama, a cikin ta amsa amma ganin idanunsa jawur gashi yana jan kafafu wanda shi ne abin da yafi tsana a rayuwa. "lafiya abban ummu" Ta faɗi a firgice tana taro shi, a zuciyarta fata take Ace an ɗaura ma Halima aure amma se taji yace "Allah yayi ma Halima rasuwa jiya da dare" "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah ya jikanta yasa ta huta. Wai hankali na yanzu zai kwanta babu mai takurawa miji na" dukan da ya fara mata ta ko ina ya sa tayi shiru haɗe da shekawa ɗaki ta rufo kofa don gani take mutuwar ta taɓa kwakwalwar sa. Nan shima ya zube yana mai sakin kuka, abubuwa da dama yai ta dawo masa dangane da soyayyar su da Halima.Dashi akayi zaman makoki aka gama, Agaysha ko a kwalar riganta don tunanin ta Abdoul nata ne ita kaɗai. Duk da walwalarsa ya zama tarihi ba don son da yake ma Halima ko kuma don ya gagara ɗaukan kaddara, A'a, ya kasa yafe ma kansa rabuwa da Halima da yayi. Shin dama bai shirya aure bane yaje ya fara neman ta. Shi ma yana cikin jerin maza masu yaudara kenan. Me yasa ya gaskata ma Halima zancen da ake cewa maza masu aure sun fi yaudara.+ Mafi yawan lokutta ba laifinsu bane tsoron fitina yake sawa su hakura, amma ai Allah ya basu ikon yi me yasa ya biye ma Agaysha har ya saɓa ma Halima, ya ci amanar yardan da ta mishi, ya sa kafa ya ci mata mutunci duk da girmama shi da take yi. Me yasa tun farko ya amince zai aure ta bayan yasan bai shirya kari ba. Anya Halima ta yafe masa kuwa. Da irin wannan tunanin ya shirya ya je gidan baffa. Cikin sa'a ya same shi a gida. Bayan sun gaisa sunyi ma juna ta'aziyya sai kawai ya sa musu kuka, tun suna takaici har ya dan soma basu tausayi. Basu hana shi ba har sai da yayi mai isarwa sannan ya ce "Halima ba ta yafe min ba ta tafi ta barni. Na ɓata mata da yawa ban san da hakan ba sai da lokaci ya kure min, fitinar Agaysha ya sa na ki zuwa, ni kadai na san abinda na fuskanta." Ya karasa yana sakin wani kukan mai tsuma zuciyar mai saurare. "Da ma chan ba sonta kake ba Abdoul mu barshi a hakan kawai" faɗin momma don ita da tana da hali zata murkushe shi take ji. "mu dai barshi a yana sonta ɗin, babu sauran abinda za'a iyayi se dai hakuri. Halima kafin ta rasu sai da ta furta yafiya ga kowa. Muyi fatan inda take tafi nan da ta bari, in da rabo ai ss ku kasance a Aljanna," kuka dai Abdoul ya cigaba, nan Baffa ya zauna yayi ta bashi baki, nasiha yake masa mai shiga jiki sannan ya rufe da addu'a. *** 2016... A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, shekaran Halima ɗaya da rasuwa. Kullum kwanan duniya sai Abdoul ya bi ta da addu'a wani zubin har da sadaka da azumin nafila da niyyar Allah ya kai ladan zuwa gareta. Agaysha tun da ta buɗe idanu ta tabbatar da gaske Halima ta rasu ta chanza salon rayuwar aurenta duk wani nau'i na kula da take ma Abdoul ta janye. Bata kyashin zaginsa ko ci masa mutunci ko a gaban wanene. Ta kanyi amfani da kuɗin da dangin mahaifiyarta ke dashi tayi ma danginsa gorin arziki. Irin haka ne ya faru yau, ya shigo ya iske tana hira da kanninshi. Duk suka gaisa da shi ita kuma ta yi kamar bata ganshi ba. Har ya shiga ɗaki ganin minti goma bata biyo shi ba yasa ya dawo falon ya same su. "Madam me kika girka, zanyi baki wasu Diplomate yan Nijeriya zasu zo" Ya faɗi zuciyarsa na bugawa ɓat! ɓat! Kar ta kwaye masa baya. Ilai kuwa buɗan bakinta sai cewa tayi " Au nom de Dieu il partir au restaurant le plus près pour nous acheter à manger (kasan Allah ka je Restaurant mafi kusa ka sayo muku abinci) , don ko naka na ba kanninka, ni na gaji ba abinda zanyi tun safe nake aikin girki Haba!" ta karasa tana murguɗa bakin ta. Kallonta yake yanda ta jinɓire waje ɗaya. Rigar sa mai tambarin wajen aikin su ne ta sanya da zaninta. Shike nan don tana da ciki ba zata yi ma kanta faɗa ta dinga kwaliya ba, ko yaya ne ta yi shiga mai kyau. "kin san Allah babu abinda zai hanaki girkin nan in ba so kike rayuka su ɓaci ba" Ya faɗi yana haɗa fuska ko Allah zai sa yayi mata kwarjini amma ina don tsaki tayi tace "banga uban da ya isa ya sa nayi girki ba, dilla kalle ka wai kai har namiji ne anan. Mtsww! An dai rako maza wallahi, banda ba makwanci wahala ba abinda mutum zai buga kirji ya ce ya iya. Ka gayyato Halima daga inda take tayi maka" Ta faɗi tana barin shi zaune a inda yake. Kaninsa dama tun da ta fara masa masifa suka fice daga wajen. Dafe kansa yayi da hannu biyu yana tunanin wani irin hukunci zai mata. Ashe dai haka take. Wasu siraran hawaye ne suka fara zubo masa, yana tausayin kansa. A haka ya fara tunanin rayuwar sa, wanda ya sani da wanda aka bashi labari. ABDOULLAHI ABOUBAKAR Asalin kakanninsa yan jihar Borno ne a gabashin Nijeriya, sana'ar siyar da citta da tafarnuwa ya kawo su Nijar inda suka sauka a zindar. Mahaifinsa Aboubakar ya taso ɗan dangi kasancewarsa auta cikin yaran kakansu talatin da shida. Yayi karatu zuwa sakandire kafin ya faɗa harkan kasuwanci, tun yana karkashin ubangidansa mommadou har ya samu kantin kansa. Amanarsa da gaskiyarsa yasa ubangidansa masa tallar yarsa mafi soyuwa a gareshi Safiyyah . Nan take kuwa don shi ma ya daɗe yana sha'awar mallakarta a matsayin mata sai dai tsoro ya hana masa tunkararta. Anyi biki amarya ta tare a nan cikin gidansu tare da sauran yan uwansa maza. Shekarar su ta farko ta haifi yarsu Aisha, daga nan sai Abdoul wanda tsakanin sa da Aisha shekara uku ne, daga nan kuma Safiyyah tayi haihuwa bakwai wanda ya cika su tara gaba ɗaya. Duk abinda Alh Aboubakar ya tara akan karatun Yaransu yake karewa, makaranta mai kyau yake tura su, duk da kasancewar daga shi har safiyyah ba suyi wani karatun zamani ba hakan bai hana Yaransu samun sakamako mai kyau ba don kullum suna musu addu'ar samun nasara. Abdoul na da rauni ɗaya 'yan uwansa, baya son abinda zai ɓata musu, burinsa farin cikinsu sannan yana hakuri da duk wani mai son su. Wannan raunin da kuma kalaman Halima ya hana shi ɗaukan muguwar mataki akan Agaysha don duk abinta bata wulakanta su sai da in shi ta zage su a gabanshi ko tayi amfani da kissa ta hana masa yi musu wani abin arziki. Karar da wayarsa tayi yasa ya dawo daga duniyar tunanin da yake. Share hawayen da ya gangaro masa yayi sannan ya ɗaga wayar. "kun iso? Toh gani nan" Ya faɗi yana ɗaukan mukullin mota. Fita yayi dasu zuwa Assemblée, Auberge Mourna ya tsaya inda ya kasance gidan abinci mai lamba ɗaya. " wannan rowan abinci har ina, salon kada mu gaisa da Madam ne ko" faɗin Ɗahiru ɗan jihar Kano. Dariya Abdoul yayi yace "kun san tayi nauyi. Muna gama waya ɗazu sai ga kiranta. Wallahi oder nayi ɗazu na kai masu" Ya karasa yana istigfari a zuciyar sa. Ya kashe musu kuɗi sun ci sun yi kat sannan suka koma gidansa gaban sa na faɗi. Ba laifi ta karɓe su da kyau kuma ta chanza kaya zuwa shiga na kamala. Har cikin ransa ya ji daɗi don har lemun abarba da kankana ta basu mai sanyi.Hira sosai sukayi da abokansa, sai da akayi magariba sannan sukayi sallama. Ranar duk sai ta wanke laifukanta saboda lafiyayyar abinci tuwo da fakku (malohia murzazza) ta kawo musu karfe shida na maraice. "Ga fa fakku ku ci ku ba Yan Nijeriya labarin daɗinsa" Ta faɗi tana dariya. Kasancewar ta gwana a fannin girki yasa basu so ya kare ba, tas suka tashi da shi suna ci suna santi. Kudi suka aje mata dubu hamsin na kuɗin Nijeriya, zo Kuga murna wajen Agaysha saboda sanin da tayi in ta juya su zuwa cepa zata samu kusan dubu ɗari don ma darajar cepa ya faɗi. Da naira dubu daya za'a baka cepa dubu uku, Yanzu kuwa dubu da dari shida zaka samu. Ko da ya dawo daga rakiyansu ya iske har ta gyara wajen ta baɗe gidan da kamshi. Har cikin ransa ya ji daɗi. Nan suka baje hira bayan ya ja musu limancin isha'i.+ *** "Yanzu Agaysha haka zamu dinga kallon su Ummu Abieha da sadiya, shekarun Sadiya and kusan talatin fa balle ayi maganar Ummu. Wai bakya jin wani iri ganin su a gida ba aure" faɗin Abdoul ransa ya kai kololuwa a ɓaci. Ace Yaransu mata babu wanda ya fito da niyyar aure. "wallahi kuwa babansu, duk masu zuwa kuma da matan su, da anyi maganar aure matayensu su tada rigima, nima fa abin na damu na." Ta faɗi tana gyara zama. "kin san har Halima ta mutu bata yafe min ba, kar ya zo alhakin ta ne ya ke kama mu. Allah ka yafe mana yaranmu su samu mazajen aure" Ya faɗi yana kwalla. "Aameen ni ko na hudu ne in dai za'a so su ba komi, " faɗin Agaysha "Amma ke bakya son kishiya, kike fatan ayi ma wasu don a auri yaranki. Lallai son kai ya miki yawa" Ya faɗi yana mikewa, don ya fara jin kiran sallah. Kiran sallan ya ki karewa, tun yana Jinsa daga nesa har yaji na bayan gidansu an kira. Leman da ya ji yasa ya taɓa gadon da yake kwance. Jike yake da zufa, da ma ana mafarki mai tsawo ne haka, shi dai har ga Allah bai taɓa ko jin labarin mafarki a bayyane kuma mai tsawo hakaba, tun da ya samu natsuwa da Agaysha, kalaci kawai yayi barci ya kwashe shi kafin ya kai ga wanka. Kallon agogo yayi karfe huɗu da minti biyar, tabbas la'asar aka kira, shi kuwa wani irin barci ne wannan tun karfe tara na safe. Abinda bai sani ba haka kawai Agaysha taji bata aminta da shi ba, ta sa masa maganin barcin da take ɗura ma yaranta in suka ishe shi. Don kar ma ya nemo Halima kafin ta dawo daga wajen bakanta. Abin tambaya anan shin dama ana mafarki a barcin da ba na Allah ba ko kuwa MAFARKIN ABDOUL daban ne. Amsar na wajenku masu karatu😜 Tashi yayi jiki babu kwari, yunwa yake ji amma bayi ya fara isa yayi wanka, gami da alwala. A zaune yayi sallah sannan ya shiga kitchen ya iske tayi tuwo kafin ta fita. A nan ya zauna ci hannu baka hannu akushi. Sannan ya samu karfin gwiwan fita. Gidan Yahai yaje don ya samu rakiyansa, nan ma ba wani zama yayi ba suka ɗauki jiki zuwa gidan iyayen Halima. Bayan an musu iso, sun gaisa da mahaifinta wanda murna ya hana shi ɓoyewa. Baffa ya faɗa masa komi dangane da alakar Halima da Abdoul banda rabuwansu. Nasiha sosai yayi musu musamman akan aje mace fiye da ɗaya a gida, mahimmancin hakuri da adalci. Sunyi murna kwarai da karamcin dattijan arziki. Tsoron Abdoul ɗaya yanda Halima zata amshi Zancensa, hakan ya sa Yahai ya bashi shawara da ya bi ta hannun iyaye kawai. Yasan dai yana da fada a wajen iyayenta maza shi yasa ya fara da mahaifinta. Bayan tafiyar su Abdoul ya ɗaga waya ya kira Baffa. Nan ya ke faɗa musu zuwan Abdoul da kuma yanda suka kwashe. "shi Abdoul ɗin ne yazo wajenka?" Ya tambaya cike da mamaki. Dariya yayi sannan ya bashi amsa da cewa "shi fa, ko minti uku basu yi da fita ba. Ga ma tsarabar da ya kawo ma yara nan. Yace zuwa Asabar kaga jibi kenan zai shigo wajenku". "Allah ya kaimu, yanzu muka dawo asibiti Halima har oxygen aka sa mata da muka isa, mun aza ma rai yayi halinsa sai mommansu ta nace akan Halima bata rasu ba. Amma Alhamdulillah har drip ɗin da akasa an cire kafin in dawo. Ban kira ku ba don bana son hankalin ku ya tashi ne" hawayen da suka zubo masa ya goge don ya san da Ace Halima ta rasu ko iyayenta baza su kai shi rashin ta ba, in bai yi karya ba ai cewa zaiyi ya fisu sanin wacece Halima da darajan da Allah ya bata. Samun irinta sai an tona. "Allah ya bata lafiya, gobe bayan Jummu@ zamu zo mu duba ta, in kuma an sallame ku shike nan" Ya faɗi bayan ya gama tunanin anya a duniya akwai sauran masu riko da zumunci irin yayansa. "Toh shike nan, Allah ya baku iko, ya sanya Alkhairi tsakanin ta Abdoul in babu ya musanya mana" "kai baffa ba bu ko yar kunyar nan. Yar farin ku ce fa kar ka bari a ji kana kwararo addu'a fa" mahaifin Halima ya tare shi da tsokana, nan sukayi dariya. *** Ko da su Abdoul suka isa gida Agaysha ta dawo tayi yan birne birnenta wanda aka tabbatar mata da in har Abdoul ya shigo gidan toh sai yanda tayi dashi. Suna gab da shiga gidan Yahai ya ja shi gefe yace "karanta addu'ar shiga gida haɗe da suratul ahad, ba wani jinsi na shaiɗan da zai kasance tare da kai. Kayi sallama kuma tun daga bakin kofa kar ma Ace sun rako ka zuwa bakin falo. Ire iren sakacin nan ke sa tsafi yai tasiri a gidan mutum. Rashin yin addu'ar fita gida da shigowa " Ba musu ya karanta, suka shiga da sallama. A ciki ta amsa tana yatsine fuskanta kamar taga kashi. Cikin tsawa ta ce " Daga ina kake na dawo baka nan" Ta tambaya kamar wani ɗan ta da take shirin mazga. "Gida na ya zo fa gashi na kawo miki shi har gida, dafatan banyi laifi ba" Yahai yai saurin amsa mata don ya san kaidinta, Allah kaɗai yasan tsafin da tayi. "Auho! Kasan akwai wata karuwa da take neman rusa mana zaman lafiya a gidanmu, wallahi na aza wurinta ya je don yau da asuba sunanta ya tashi da shi a baki, tsoron zuwansa wajenta na bashi maganin barci a tea, kasan abinda ya ban mamaki" Ta karasa tana jefa ma Yahai tambaya, dama ita haka take da son nuna isa, in tayi abu gani take wayonta ne ya kaita ga hakan. "Sai kin faɗa madam" "ko da na fita kuka yake yana kiran Halima ta rasu, tsakanin ka da Allah ko a littafi ka taɓa karanta mutum na barci yana mafarki Alhali barcin magani ne, nayi Alkawari sai na hukunta yarinyar nan, duk tsafinta sai na hukunta ta" Ta karasa tana kara yamutsa fuska kamar Halima ne a wajen. "gaskiya shi yasa na gagara yarda da ita, a sani na ke kaɗai ce aboki na ke so, kwatsam ya zo min da zancen wata Halima. Allah raba nagari da mugu, mtsw! Mata basa kyautawa wai takan namiji su siya wuta da hannunsu, sai ki ji suna malam malam yoh ko da ayar Kur'ani akai lakani dashi ai bazai tashi da ga shirka ba. Annabi ya faɗi su zasu fi yawa a wuta. Kuma ba komi bane zai kai matan zamanin nan wuta sai son mallake ɗa namiji. Allah ya shirye ta da sauran masu yi " Fuuuuu! Ta shige ɗaki ba tare da ta amsa aameen din ba. Nan ya ja Abdoul kofar gida suka tsara yanda komi zai kasance. Ya kara nanata masa kar ya yarda tasan aikinta bai ci ba, tunda hutun sa ma ya kare, ya lallaɓa ta kafin ya wuce.Ranar Asabar tun da safe Abdoul ya shirya ma tafiya. Karfe tara Yahai ya iso suka ɗauki hanyar Niamey. Duk kayan marmarin da suka gitta mawa sai sun tsaya sun siya. Sannu a hankali suka isa, hiran da ya ɗau hankalinsu yasa basu ga wani nisan tafiyar ba. Sun isa sun taradda an sallame Halima har ta dan warware. A falon Baffa aka sauke su inda shi ya fara tarbonsu kafin kowa. Bayan sun gaisa ne ya kalle su yace "ko zan san me ke tafe da ku?" Duk da sunyi mamakin tarbon arziki da suka samu, amma basu yi tunanin zai jefe su da wannan tambayar ba. Sunkuyar da ka Abdoul yayi sai Yahai ne ma da yayi karfin halin tattaro natsuwarsa ya ce "Baffa mun zo neman izinin ka ne, don neman auren Halima" Shiru ya sake ratsa wajen. Zukatansu nai musu ki ɗan lugude don basu san ko zai amince ba. "Ba zan ce komi ba sai Halima ta faɗi ra'ayin ta, in ka samu ta amince ka gaggauta turo min waliyanka, in kuwa bata amince ba ina rokon ka arziki kar ka sake zuwa min gida, na barku lafiya" yana kai aya ya tashi ya shige gida. Sun zauna ma kamar minti goma sai ga Halima ta shigo da kawarta Shamsiyya Ummu A, fuskarta a sake, amma ko kallon ɓarayin Abdoul bata yi ba. Hankalinta gaba ɗaya ta ba Yahai. Sun gaishe shi, sai shamsiyya ta kalli Abdoul ta ce "ɗa na! Fatan dai kana lafiya" da murmushi mai nuna tsantsan farin cikin an san da zamansa ya ce "Mommy ina fa lafiya, nayi zunubi mai girma, don Allah ki sa baki a yafe min kinji" Ya faɗi yana marairaice fuska. Jin duk sunyi shiru ya sa ya fara basu labarin duk abinda ya faru da ya koma gida har zuwa mafarkansa da yayi masu ban al'ajabi. Shamsiyya dai da ka kalle ta kasan ta na cike da tausayin sa yayin da Halima tayi ko oho, ganin sun tsare ta da kallo ne alamun suna son ji daga gareta ne ta muskuta ta ce "Abdoul mafarki ba gaskiya bane, Allah ne yake aikowa bawa wasu lamarika daga cikin buwayarsa, domin ya haskaka masa wata baiwa tashi wadda zai gane rayuwa da abinda yake cikinta.... Idan bawa yayi mafarki mai dadi kona ra'ayinsa sai yayi Sadaka kamar yadda yazo a hadisi Majma'ul Bahraini cewar "Annabi yace kunemi yayewar bakin ciki, da bacin rai wajan yin Sadaka " hardai zuwa karshen hadisin, shiyasa akeso bawa ya kasance mai yawan addu'a aduk lokacin dazai kwanta barci, sbd yanayin mafarkin dazai iyayi, idan mai dadine sai yafadama mafi kusanci dashi kuma abokin sirri agareshi amin domin yatayashi rokon Allah nake alheri akan mafarkin. Idan kuma mafarkin abin tsorone kokuma tashin hankali wanda zai haifar da bacin rai, ana so kana farkawa ka nemi tsari ka tofa ɓarayin hagu sannan ka chanza kwanciya, shima dai mutum sai yayi Sadaka yanemi tsari akan abinda yagani acikinsa, yanemi kuma zabin Allah na alheri akan mafarkin, yazama mai sirri akansa wajan barwa cikinsa sirrin mafarkin, tosai Allah yaji tausayinsa kuma yayi imani tare da tawassali da Annabi wajan zabin alherinsa. Wannan bayani kadan kenan daga cikin abubuwan da Mafarki yakunsa, Allah yasa mudace da rabo mai amfani adukkan rayuwarmu Amin. " tana kaiwa nan ta tashi tsam sai zuwa cikin gida. Dukkansu ba wanda kansa bai ɗaure ba don a zahiri sun ga tsantsan rashin bawa lamarin mahimmanci. Sunyi zugum na wasu yan mintoci chan shamsiyya tayi karfin halin magana inda ta ce "Kun san ba lafiya ta cika ba, jiya aka sallamo ta daga asibiti, mu ɗan ɗaga mata kafa. Ɗa na kasan dai kai me laifi ne sai ka san yanda zakayi ka wanke kanka" Duk sukai dariya sannan suka tambaye ta jikin Halima inda ta amsa musu da taji sauki sosai. Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani sukai sallama suka tafi. Wasa wasa se da akayi wata biyu Abdoul na zaryan neman sulhu amma Halima ta kafe akan ba'a haifi namijin da zai wulakanta ta ba, nan ta maida hankali a aikinta ba ta saurari zancen ba. Yanzu ma zaune take ya zo, momma ta kora ta dole taje gare shi, tsayuwa tayi a kan shi, bata ce masa komi ba. Kiran da taga ya shigo wayarta ne ya hana mata cewa komi don niyyar ta kwance masa rashin mutunci . Ɗaga wayar tayi da sallama. Maimakon a amsa sallama sai saukar ashar taji, neman tsari take da ga sheɗan. Faɗin da tayi "Abdoul yafi karfin ki jaka" nan ta fahimci wacece kuma. Shiru tayi ma wasu dakiku sannan ta ce "kin kira a sa'a ma, tun ɗazu ya ke jira na fitowar kenan se ga kiranki, gashi ku gaisa" Ta karasa tana mai mika masa wayar fuskarta cike da murmushi. "macuci, azzalumi, annamimi, wallahi in baka tuba ba wutan Allah sai ya ci ka" Ta faɗi tana haki bayan muryarsa ya sauka a dodon kunninta. Murmushi kawai ya saki ya katse kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. "bani wayata, meye nufin ka na kashe min wayar gaba ɗaya" Ta faɗi a tsiwace, kallonta yake yana so idanuwar su su haɗu amma fir ta ki. "Ki zauna, magana nake so mu yi" Ya ce yana nuna mata kujera. Zama tayi babu gardama. "Halima, L'erreur est humaine, (ko wani mutum na tare da kuskure) ki yi hakuri s'il vous plaît Il faut me pardonner. (don Allah ki yafe min)" Ya faɗi yana rusunawa. Ganin tayi shiru ya sa ya cigaba "Nasan ba a son rai mafi yawa daga cikin mata ke auren mijin aure ba, burin kowacce mace ta kasance uwar gida, amma ina zamu kai kaddarar rayukanmu. Allah ya faɗi a cikin littafi mai tsarki LIKULLI AJALIN KITAAB, wato ko wani kaddara a rubuce ta ke. Ba wai zan aure ki don in cikata giɓin da nake da shi a gida na ba, kin san dai ina son matata, toh ba wai zan aure ki don son nata ya ragu bane, sonki da kaunarki yasa nai sha'awar aurenki, don in yi bautan Allah in nemi yardansa. Bayan wannan banda wani dalili. Bana so in miki karya shiyasa kika ga nayi shiru akan zancen laifin da nayi Il faut me pardonner." tsare ta yayi da idanu, burinsa su haɗa ido amma fir ta ki yarda. Shiru sukayi na kusan minti biyar, zuciyar ta na rawa kamar pendulum, chan dai ta tuna isa da mulki da Agaysha ke Gwadawa akan Abdoul na ta ne ita kaɗai yasa ta tsaida zuciyarta ta ce kamar bazata magantu ba "ka turo ayi magana" Ta na faɗi ta shige cikin gida. Murna a tare da shi ba'a magana, sai da ya kira baffanunsa suka tsaida masa da ranar da zasu je sannan ya bar falon da aka sauke sa. Itama da ta shiga ciki ta faɗa ma momma abinda ta yanke ta ji daɗi sosai. Nan suka yi addu'ar Alkhairi amma kowannensu zuciyar sa kal da murna. *** Kamar yanda suka yi alkawari haka suka zo da zancen neman aurenta. Iyayensa sun yaba da karamci da halin girma iri na iyayen Halima. An tsaida auren bayan wata uku kamar yanda Halima ta roka sanda momma ta tambaye ta. Tun da lokacin wani sabon shaukin kaunar juna ya shiga tsakaninsu. In baya gari ko Kasar suna manne da juna a waya. Agaysha tayi asirin, tayi tsafin amma kullum lokacin bikin matsuwa yake duk da bokanta ya tabbatar mata baza'a taɓa auren ba. Yau ma ta shirya zuwa maraɗi don ganin wani boka, sarkarta da ammbasadan Nijar a Saudiyya ya ba Abdoul ne ta siyar, tayi karyan zuwa ta'aziyya ta ɗau hanyar maraɗi. Sanda layi ya kai kanta ta shiga don ganin sa. Kallo ɗaya yayi mata ya kwaɗaitu da ita. Nan ya ce mata "Halima ba ko mi bace face abin da zai kawata MAFARKIN ABDOUL, yanzu dai ɗan tsatsuba ya na son ya ji kalan ruwanki, da shi zai halaka Halima" " Ruwa kuma.! ya mai biyan bukatu" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "eh! Kwaye min wannan zanin in ɗiba" ba musu ta Kwaye, ta tsorata da ya cire zanin da ya ɗaura a kugu amma zuciyar ta da ta tuna mata shike nan kafin ta koma an hallaka Halima da auren saura mako ɗaya ya sa ta sakin jiki. A wahale ta fito runbun boka ta sa mu abin hawa, Gidan kawarta Taghayshuwane ta je, nan ta huta washe gari ta koma zindar. Shiru! Shiru tana jiran a ce mata an fasa aure amma sai shirye shirye ake, ta kira boka yace shi dai yasan baza'a yi auren nan ba, ta kwantar da hankalinta ko an taru za'a fasa. Hakan yasa ta ji sakayau fatanta a fasa ranar ɗaurin aure don zai fi musu zafi. BIKI BIDIRI .... Karfe goma na safen 13 ga watan febweru 2016 a Nijar, Nijeriya, Kamaru da Chadi aka ɗaura Auren Abdoullah da Halima bisa ga sadaki mafi karanci. Anyi shagulgula sosai inda mawakiya Sa'a Vocal ta wake ango da amarya. Hanifa creations and couture suka fito da amarya da ango da zafafan ɗinkuna inda mutane sukai ta santi. Ranar Lahadi da safe aka yi walima a gidan ta da ya kama mata a nan Niamey. Agaysha bata yarda da an ɗaura auren ba sai da aka kai amarya gidan iyayen mijinsu da maraice sannan taga sun dau hanyar Niamey. Nan ta ɗau waya ta aika ma Abdoul sako kamar haka "Ango mijin Amarya, ina maka murna, na ba ka wata uku kyauta kasha amarci lafiya" ko da ya karanta sai da yai dariya a ransa cewa yake "wannan bata san abinda ke damunta ba" nuna ma Yahai wayar yayi ya karanta. "mtswww ! Wasu matan fa na kwafsawa, akan wani dalili zaki bar ma wata mijinki wata kawai don ya auro ta da yaudaran kai zata ginshe shi. In kaga an ginshi juna amaryar bata iya takunta bane. Ai ta baku daman fahimtar juna a ne amarya kuma ta kafa gwamnatin ta da kyau. Aminina kasha amarci lafiya" Ya karasa suna masu tafawa.An watse taro Lafiya yan Uwa sun koma gidajensu lafiya lau sai addu'an zaman lafiya da aka bi maauratan dashi. Ɓangaren Agaysha kuwa kawayenta na nuna mata gara da tayi hakan kafin wata ukun ya wuce za'a tura mata warin jaɓa da ɓallewan jini. Haka dai sukayi ta shawara har dare ya tsaga. Washe gari ma haka sukai ta bata shawaran da suke ganin zai fishe su, kafin suka watse aka barta da kunan zuciya. Mafarkin ido biyu ta yini tana yi, idonta na hasko mata Abdoul ɗinta da Halima. Tayi kuka kashi kashi, ta yini tana tsine ma bokayen da sukayi mata aiki, barinma wanda ta ba jikinta. Kamar an muntsile ta, wayarta ta ɗauko ta kira shi don ta ci masa mutunci. Ringing biyu ya ɗaga. "mace mai garɗi Uwargidan Abdoul kina lafiya" Ya faɗa yana kasa da murya, hakan bai hana ta jin kaurin muryar kamar saukar aradu. "kasan kuwa an ɗaura auren" abinda bakinta ya iya furtawa kenan. "Kinsa kokwanto, baki bada gaskiya akan zan iya hana auren ba. Aiki da kokonto ai ba zai taɓa karɓa ba." Ya faɗi daga chan ɓarayin. "Kokwanto kuma?" Ta tambaya tana zare idanu kamar yana ganin ta. "Eh! Ai da kin mika gaskiya, kin amince zan iya yin komi duk da ba haka ba. Amma bai yi latti ba, ki samu ki zo sai a tura mata cuta wanda zai kar da ita har lahira." jin hakan ya saukar mata da wani farin ciki da bata san daga ina ya fito ba. Haka dai yai shawo kanta da zantuka na karfin gwiwa da tabbatar mata da Halima mai karan kwana ce. Tunani da kukan da ta yini tana yi ya saukar mata da zazzaɓi, wasa wasa tana zata ji sauki ta samu ta leqa maraɗi amma ina sai da tayi sati kwance. Kullum Abdoul kan kira su sau biyu ko uku a rana don ya ji lafiyansu, amma tana ɗauka zata mika ma su Ummu Abeyha wayar su yi masa magana. Auren na da sati biyu ya samu zuwa duba su, nan ya iske duk ta rame tayi baki, da ya tambayi dalili ne yaji ta yi ciwo, bai tambayi dalilin ta na kin sanar da shi ba. Dare na yi ta wuce ɗakin Yaransu ta kwanta abin ya ɓata masa rai har ya tunkare ta da zancen, buɗan bakinta kuwa sai cewa tayi "Ni fa sai munje anyi maka gwaji zan kara amincewa da kai, ba zaka auro min raguwan sida sannan in amince maka ba" tana faɗin haka ta juya baya. Bakin cikinsa ya ninku amma sai bai nuna ba. A daddafe ya karaci kwanakin da ya ɗiba zai yi on yazo yayi ya kara gaba. *** A Ɓangaren amarya da ango kuwa soyayya suke gudanarwa mai tsafta. Tun da ya amfana da sadakinsa ya kara jinjina ma Halima, ya san ba karamin jihadi tayi ba na tsare mutuncin ta. Ace mace yar shekara ashirin da shida ai dole tana da sha'awa, zata bukaci abokin ɗebe kewa tunda dai mutum ce ba dutse ba. Amma yana da ga cikin jihadi (jihadul nafs) wanda yafi kowane nau'i na jihadi daraja fin karfin zuciya. Yayinda mutum yai hakuri, ya danne sha'awarsa har zuwa lokacin da ba ma sha'awa hakkinsa zai kai ka ga aljanna ne ba wuta ba shima babban nau'i ne na jihadi mai babban daraja (ni safiyyah Ummu Abdoul nace Allah ya kare mu da zuriarmu daga aikata zina da sauran Alkaba'ir, Aameen ya rabbi ). Tun lokacin yake bata wani daraja na musamman don ta karyata masu bahagon tunanin duk yar da ta je jami'a har ta kammala to lallai ta siyar da yan matancinta. Wasu ma har kauɗin kiransu karuwai suke yi, su kan manta babu tsattsauran sheda a musulunci kamar shedan zina.2 "banga kaddarar da zai kaini ga auren yar jami'a ba, balle a ce ta gama har tana aiki, ai duk ba budurwa cikinsu sai dai budur-budur" faɗin wani abokin aikinsa. Tsakin da ya ja ne ya dawo da hankalin Halima wajen shi. "Sweetyna! Lafiya kake tsaki" Ta tambaya fuskanta cike da damuwa. Kallon cikin idonta yake zuciyarsa na ayyana masa tsarkin da ke tattare da dukkan lamuran ta,chan dai ya ce "Ina mamaki ne, yanda wasu mazajen musamman namu na Hausa Fulani ke jifan matan da suka yi karatun boko da rashin tsarki... " nan dai ya bata labarin yanda sukayi da abokin aikinsa mai wancan tunanin. "ka ji ka dai sweetyna, wai me yasa mazan hausa fulanin kuma suke ganin nasu kalar tsarkin a matsayin ado. Amma fa laifin matan ne, sakarkaru, su bari ko wani gardi ya taso sai ya ba gaɓɓai huɗu wahala, kuma su garadan ganin kansu suke a tsarkaka yayin da matan najasa. Duk namijin da kaji yana kiran matan jami'a ko wa'inda suka Gama a Yan iska toh Allah sweetyna ya san inda yake haɗuwa da su. Sai ka ga namiji ya gama sheke ayarsa wai shi a dole zai ma Allah wayau se ya koma ma auren karamar yarinya. Hukuncin mace da namiji a fagen shari'a dai ɗaya ne, duk namijin da yayi saɓon Allah toh saɓo ne dai dai da na mace, hukuncin su ɗaya sweetyna" Ta karasa tana sakar masa wasu sakonni mai gamsar da mai amsa. "Allah ya bar min ke Amaryar Abdoul" Ya faɗi yana sumbatarta a goshi. *** June 2016 Raywarsu na tafiya gunin ban sha'awa, Abdoul yayi kiba sosai, haskensa ya fito sosai. Da gani hankalinsa a kwance ne. Duk sati biyu yana zuwa zindar yayi kwana biyar, matukar yana kasan. Agaysha dai kiri kiri ta ki amincewa da shi, akan sai an masa gwajin sida, yayinda sai chushe chushe takeyi a jikinta da birne birne duk don Halima ta mutu. Sau biyu yaranta na zuwa hutu wajen Halima, duk suka dawo takan lura da chanjin da take gani tattare da su, nan ta fara rigimar baya adalci Halima daɗi ta ke ci. "Halima aiki takeyi ba ta jira sai na ɓata kafin ta yi" Ya iya ce mata ya barta nan. Kwatsam! Wata rana ta je fitsari sai ta ga kyankyaso a cikin masan, kasancewar ta matsoraciyar kyankyaso yasa ta tsuguna tayi a kasa, ta tsorata ainun ganin kalar Fitsarin kamar jini ga wasu fararen ababenan a ciki wanda da ta kalla da kyau sai ta ga ashe tsutsotsi ne. Ta firgita ainun, kasancewa ya fi sati take jin azaba yayin fitsari, kuma bata taɓa tunanin in tayi ta duba ba, tana tsarki take matsa wajen da zai flushing. "kar dai Halima ce ta turo mata" wani sashi na zuciyarta ya faɗa mata. "ko kuma naki ne dawo miki ba" ɗayan sa shin mai faɗin ya ce hakan. Shiru tayi duk a tsorace. Wa za ta kira, gashi ana azumi balle ta je wajen boka. Wasa wasa ciwo ya cin magani, tsutsotsin har fitowa suke, tunda aka je asibiti likita ya ce sanadiyyar chushe chushe ne ko kuma jima'i da mai ciwon ko duka ya jawo hakan Abdoul ya sa ma ransa chushe chushe ne, ya haɗa kan yaransa sai Niamey, sai de ya turo mata kuɗin magani in ya samu sarari ya leqo ta don cewa yake "kinga ranar zuwa wajen boka" Sai da su Halima suka je Zindar da sallah sannan ta iske laluran Agaysha, kwarai ta tausaya mata nan ta ɗauki alwashin taimaka mata. Bata yi shawara da kowa ba ta shirya komawa har da Agaysha kasancewa Abdoul ya riga su komawa. Da fari taki yarda su tafi tare sai da ta tambayi kawayenta nan suka zuga ta akan taje sai ta haɗa mata tuggun da zai fitar da ita. Ko da Abdoul ya gansu bai ce uffan ba, don yana shirin zuwa wani course a Spain. Ba zai dawo ba sai Satumba. Nan Halima tayi ta haɗa ta da likitocin mata gwanaye masana makamin aiki, sannan ita ce har sako tayi aka haɗa mata magunguna daga Egypt duk ta haɗe ma Agaysha. Basa ko zaman hira, iyakansu gaisuwa sai bayani akan magani in an kawo. Duk bidirin nan daga aljihun Halima ne hakan ya kara mata daraja a idon Abdoul. September 2016.... Fari da kyawun Agaysha ya fito sosai, lafiya ya samu tana son ta nemi gafaran Halima amma sam bata ba ta fuska ba, don ko aikin gida bata yarda ta sa mata hannu ba. Ranar da Abdoul zai dawo ta ga abin mamaki don shirin da tayi don tarbansa ko ita da ya yi shekara a France bata yi masa ba a lokacin. Da ya shigo gidan kuwa taga abin mamaki, ita da yara suka tarbo shi tun daga gate, Agaysha na kallon su ta window, yaran nan fa ba na Halima ba amma bata yi son kan raba su da uban su ba. Nan tayi mamakin kyawun hali irin na Halima. Sai da ya kintsa ya zauna cin abinci sannan ta fito tayi masa sannu da dawowa. Ya amsa a hankali ya dago ya kalle ta, ya girgiza da kyan da tayi. Sai ka ce kafin suyi aure. Fitowan Halima ya kalle ta yace "me kike ba my dear da ta chanza haka" dariya Halima tayi ta ce "kace kawai na fita iya kula, ai se Ka biya kawai" "Ai gidanki na nan a Aljanna mai babban daraja" inji Agaysha. Duk sunyi mamaki don Halima bata taɓa mata abu don ta ce ta gode ba ma. Nan ta dage ta roke su gafara, inda ta ke faɗin ta ga illar boka da bokanci, ta ga illar zalunci da mugunta. Nan duk suka yafe mata tare da kara mata nasiha akan tsoron Allah, wuta gaskiya ce haka Aljanna ma gaskiya ce. 8th October, 2016 Tun a hanyarsu na dawowa asibiti Halima ke tsokanar su "Ya kamata ku je honeymoon fa, wata 9 kenan fa rabonku da juna, tab ni dai na yafe har sai na haihu nayi arba'in" Ta faɗi tana kallon Abdoul da ke harararta. Asibiti suka je aka tabbatar da lafiyan Agaysha. "wai ido kika sa mana ne haka, mu de tsofai tsofai damu ina zamu kai honeymoon" Ya faɗi yana kashe ma Agaysha ido. "meye na kashe mata ido " Halima ta faɗi tana dariya. "Halima ba fa rayuwar Abdoul kawai kika haska ba, har na wa da yaranki. Allah ya sauke ki lfy ya kara mana kaunar juna" "Aaameeeen!" suka faɗi su duka... And they live happily ever after.... Et il vécurent heureux pour l'éternité.... Godiya ta musamman ga Haj. Mas'ouda Moulaye. Thank you all for sticking around, MAFARKIN ABDOUL is neva complete without u. I Luv u all fisabillillahi.

0 Comments