BABBAN GORO CHAPTER 12 KARSHE

BABBAN GORO CHAPTER 12 KARSHE
Part ɗin Momy ya nufo, zuciyarsa cike da sake-sake saman kujera ya zauna yana shafa kansa, wani tunanin yazo masa, wayarsa ya duba ya shiga nema number Safiyyah, ya daɗe yana nazari kamin ya danna calling, Dauke wayar yayi daga kunnensa bayan sun sanar masa da number tana kashe, Number Lubna ya kira ita kan ta shiga sai dai tayi ta ringing har ta kashe ba'a ɗauka ba, sai a kira na biyu ta ɗauka ta muryar bachi “Hello Yaya” “Sauko gani nan parlour” Yana faɗar hakan ya kashe wayar, yana mai cigaba da nazari, ta ɗaukar kamar minti biyar zuwa takwas sannan ta fito sanye da kayan bachi ta ɗora top sama, kusa dashi ta zauna tana hamma “Yaya gani” Kallonta yayi a natse “Ya za'ayi naga Safiyyah yanzu? Kin san inda Gwaggo ta kai ta gurin magani?” “A'a amman yanzu ai tana gidan Gwaggo kaje can zaka ganta” “Sun dawo ne?” “Eh sun dawo tun jiya ko shekaran jiya oh jiya, oh na dai mata amman taji sauki fa” Gyara zamansa yayi cike da mamaki yace “Taji sauki” “Eh baka sani ba, maybe dan hankalin ka ba kwance ba yasa Momy bata faɗa maka ba amman taji sauki gaskiya” Shiru yayi yana tunani, “impossible” Da karfi ya furta har Lubna ta kalleshi “Lafiya yaya?” Kallonta yayi DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI “Da gaske taji sauki kin ganta da idonki?” Tashi yayi yana faɗin “Lafiya kalau i need to see her” A gaggauta ya fice daga parlour, da kallon mamaki Lubna ta bishi har ya fice sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, part ɗin sa ya koma ya ɗauki keys ɗin motarsa ya nufi parking space, yana shiga motarsa ya ɗauki hanyar da zata sada shi da gidan Gwaggon sa, a bakin gate ɗin gidan ya fara tsayawa yqna tunanin idan ya shiga me zai ce mata! Ka fara shiga ka fara gasgata zancen Luban tukuna, a nan ya danna horn, mai gadin ya buɗe masa, har kusa da kofar yayi parking, ya fito ya nufi kofar parlour, bell ɗin gidan ya tsaya bakin kofar yana kallon Windows ɗin parlour, Sai da ya danna yafi a kirga sannan aka buɗe masa kofar, wata matashiyar yarinya ce sanye da uniform, “Ina kwana Yaya” Bai tsaya amsa gaisuwar nata ba ya kunno kai cikin parlour yana faɗin “Ina Gwaggo?” “Tana ɗakinta bari na kira ta” Ta faɗa bayan ta maida kofar ta rufe ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan tana karanta, kamin ta karasa Saif ya kirata “No Farida zo ba sai kin kira ta ba” Da wowa tayi tazo daidai shi ta tsaya, “Gani Yaya” Dukowa yayi tq yadda ita kaɗai zata iya jin mi yake faɗa yace “Ina Safiyyah?” “Tana ɗakin su Husna” “Taji Sauki?” “Eh taji sauki haukan ya cire” Shiru yayi kamar mai nazari, sannan ya sake kallonta yace “Samo min biro da Paper” Da sauri ta juya nufi wani gurin da ina jin an tana deshi ne don aje bags dan bags ɗin suna da yawa, wata ja naga ta ɗauko ta nufo inda yake ta zauna ta bude ta fiddo littafi ta ɓalli paper ta ciro biro ya mika masa, “Thanks” Ya faɗa yana kokarin karɓa, a nan ya shiga rubutu a paper ya dunkule ya mika mata tare da bironta, “Ga wannan ki ba Safiyyah idan ta tashi bachi kinji?” “Toh tafiya zakayi?” “Eh kice ma. Gwaggo ina gaida ta” Yana kaiwa nan ya juya ya nufi kofar fita. Ya daɗe zaune cikin mota bayan ya isa gida, sai da lil Minal ta faɗo masa a rai sannan ya fita daga motar ya nufi Part ɗin sa, yadda ko yake tsammani haka ta tashi daga bachin sai kuka take tana kiran “Mah mah mah” Tana bursar da yawu, murmushin karfin hali yayi ya mika hannu ya ɗauke ta “Yeee kin tashi yar mama” Kara fashewa tayi da kuka, ya shiga jijjiga ta ya fito ya nufo part ɗin Momy, dinning ya nufa gurin da ya hango su Momy suna breakfast, Momy ta mika mata hannu “Zo ki sha tea” Juyar da fuskarta tayi ta kara fashewa da kuka, Saif ya ɗanyi Murmushi yaja kujera ya zauna yana faɗin “Momy ina kwana” Momy ta amsa cike da jindaɗin ganin yau ran nasa a sake ba kamar baya ba duk da idan ka kalleshi zaka gane yana cikin damuwa, “Momy ai bata manta ɗorin da kika sa akayi mata ba” Murmushi tayi, ta shiga haɗa ma Saif tea, “Momy anjima Safiyyah zata zo ko da bana nan dan Allah a kira ni” “Miya faru?” Momy ta tambaya daidai lokacin da ta aje masa tea gabansa, “Wai Safiyyah tana da hannu cikin rashin lafiyar Kairat shine nake son na tabbatar” “Inji wa kuma wannnan wace irin magana ce haka” “Nima haka tazo min sai dai ban tabbatar ba yanzu ne ake son na tabbatar” Momy ta dafe kai “Wannan abun har yaushe zai kare tsakanin ka da Safiyyah ne? Yarinyar nan daga samun lafiyar ta sai kuma ka ɓullon da wannan abun” Bai ce komai ba ya kurɓa tea ya tashi yana faɗin “Zanje Asibiti sai na dawo” Momy bata ce masa komai ba har ya fice. Ba shi ya dawo gidan ba sai azahar duk da bai samu ganin Kairat ba dan basu barsu ya shiga ba ya window ya tsaya yana kallonta sannan ya dawo gida har lokacin lil minal na lake dake wanka ma daker ya samu ta sauka yayi, yana fitowa ta rarrafa ya ɗauke ta, ɗauke da ita ya saka tufafinsa mai ma bata barshi ya shafa ba turare kawai ya fesa ya fito ya nufo Part ɗin Momy, Mai aikin Momy ce ta karɓe ta da karfi wai za'ayi mata wanka, Saif ko yabi ya ɓata fuska dan baya son jin kukan lil minal ɗinsa, yana kokarin zama Lubna ya fito ɗaga ɗayan parlour tana leken ɗakin Momy har ta karaso kusa dashi ta zauna tana haki, shi dai kallonta yake har ta fara magana “Yaya Safiyyah ta kira tace ba zata samu damar zuwa ba wai Gwaggo ta hana ta sai ta kara samun karfin jiki, amman Momy tace kar a faɗa maka” Fuskar tunani yayi da mamaki, sai kuma ya shi da sauri Lubna ta rika hannunta “Yaya karka ce nina faɗa maka Momy tace bata son tashin hankali, zata iya yi min faɗa” “Ba zan bari taji ba” “Toh ina zaka?” “Gurin ta sai na tabbatar da abunda nake zargi ki kula min da Lil Minal please” Bai tsaya jiran mi zata sake cewa ba ya fice.Kai tsaye ya shigo cikin gidan, kana kallon fuskarsa kasan wani abun ne ke tafe dashi, Sama sama ya gaisa da Gwaggonsa yana tambayar ina Safiyyah “Lafiya?” Gwaggo ta tambaya ganin yanayinsa “Lafiya kalau nazo gaishe ta ne naji ance taji sauki” “Eh taji Sauki bari a kira maka ita” Tashi tayi ta nufi ɗakinta ba ɗan ta bamsu ba komai ɗin ba, dan tasan Safiyyah bata da matsayin da Saif zaizo gaishe ta ɗan taji sauki duk da tana ganin yana tausayin halin da take ciki, amman kuma miyasa tun lokacin bai zo ba sai yau! Da wannan sake-saken ta tura kofar ɗakin Safiyyah ta shiga. Kofar ɗakin ya tsura ma ido har sai da yaga fitowar Gwaggo, “Gata nan zuwa” Kai kawai ya ɗaga mata ta shige ɗakinta, ya sake maida idonsa kan kofar ɗakin da yake saton Safiyyah na cikin dan ɗakin Gwaggo ta shiga, ta ɗan jima kamin ta fito har ya fara tunanin koya tashi ya shiga ɗakin ne, sai gata ta fito sanye da Abaya fara da farin gyale ta lulluɓe kanta, a hankali take tafiya har ta k'arasa kusa dashi, ko wannen su yana kallon ɗan'uwansa, ita tana masa kallon data saba masa sai dai yau ya ɗan babbanta dana kullum, shi kuma yana mata kallon ta iya zai fara! Shi fa har yanzu bai gama yarda ita ce da hannu a ciwon Kairat ba, tunawa da abunda tayi ma Minal yasa shi kawar da wacan tunanin nasa, ya ɗauke kai daga kallonta yana muna mata kujera “Zauna mana kinyi min tsaye a ka” Sai a lokacin ta samu damar yi masa magana, sai dai jikinta yana bata kamar wani abu zai faru, yadda gabanta yake faɗuwa ita kanta tasan ba lafiya ba duk da wata zuciyar nace mata na ganin Saif ne sai dai bata gama gasgata hakan ba, “Ya jikin naki?” Muryasa ta daki dodon kunnenta, kamar ta ɗago kai ta kalleshi sai kuma taji ba zata iya ba, kanta a kasa ta amsa mishi “Naji sauki sosai” Shiru ne y biyo baya, kamin ya cuta maganar data razana ta “Kin warke Kairat ta kwanta, wani yace min warke warki ya haddasa ciwon Kairat” A razane take kallonsa, ta kasa buɗe baki tace masa komai sai tunanin take wanda ya faɗa masa wannan maganar take. Shafa, no Shafa ba zata sona asirinta ba to wanene? Ita kaɗai fa tasan sirrinta, ina Saif yaji wannan maganar? “Ba ki ce komai ba” Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, zufa ce ta karyo mata ta gangaro tare da hawaye. Daga ita har shi kallon Kofa sukayi ganin shigowar Momy, Saif bai jidaɗin ganinta ba sam dan yasan ba zata barsa yayi abunda ya kawo shi ba, aiko ya canka a daidai dan tana karasowa kusa shi ta katsa masa tsawa “Tashi ka wuce gida” “Momy..” “Rufe min baki ba zai yiyu ba Saif ba kai kaɗai muka haifa ba amman kullum kai ne da matsala cikin gida, karka manta mahaifinka yana da wasu yayan maza idan har ganin kake ni kaɗai na haifa namiji” Yanayin ta ya nuna ranta a ɓace yake kuma yasan ya baza ta saurara masa ba, mafita ɗaya ce yabi abunda tace, tashi yayi ba ɗan yaso ba sai dan bashi da mafita sai wannan ya nufi kofa, har zai fice ya tsinkayo muryarta tana magana dashi “Gaskiya ne Saif, lafiyar dana samu ya haddasa ciwon Kairat” “Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un” Momy ta faɗa tana zauna, wannan furucin na Momy ya haddasa Gwaggo fitowa ɗaga ɗakinta daman can a tsawale take tana son tasan wainar da suke toyawa a falon, “Lafiya, miya faru?” Momy bata bata amsa ba sai ta kalli Safiyyah tana faɗin “Me kike nufi asiri kika mata?” Kallon Momy tayi ta kalli Saif ta sake kallon Momy sai ta soke kai, hawaye na mata zuba “Ba sabon asiri ba ne” Sai kuma tayi shiru, dawowa Saif yayi ya zauna Gwaggo ma ta zauna sai duk suka kafa mata ido, ta daɗe sosai kamin ta fara magana Wannan ya faru da gaske “Lokacin da nake haukan son ka ne Saif, bayan rasuwar Minal a maimakon ka kalle kace kana so na sai ka tsallake ka kace yar'uwarta kake so, A lokacin ne ya shiga damuwa da neman mafita, sai kawata Shafa ta kaini inda wani malami ya fara yi min aiki akan zaka so ni, ya bani wani kwalli yace ya na shafa, ranar da na shafa kwallin ranar ce kayi min marin da baka taɓa yi min ba ba kuma tare da nayi maka wani abun ba, daga ranar sai na watsar da lamarinsa na sake zuwa gurin wani shima akayi a banza shiru ba, kuma sake zuwa gurin wani shima haka, a haka muka ziyarce malamin ukun huɗu sai a na biyar muka dace shima kuma cewa yayi dai idan baka tare da Kairat sannan ne zaka iya aure na, kai nasa aka fara yima sai dai duk inda na buga sai ace kai asirin ba zai kama ka ba, ita nayi mata aka ce ba zai kamata ba idan har ina son na samu nasara toh sai na ɗauki aljana” DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI A nan tayi shiru tana hawaye, kowannen jikinsa yayi sanyi da jin tomin taɓun labarinta, sai da ta share hawayenta sannan ta cigaba “Gani bana da mafita sai wannan yasa na zuba kuɗi akayi yanka aka bada duk wani abun da aljanar ke bukata na ɗauketa, sai aka samin ita cikin kwalba, da ita nake magana a duk lokacin dana tashi, farkon abunda ta farayi shine haddasa tsoron Minal a don Kairat, ita ce tace min naje na samu kayan da Minal tafi sawa cikin tufafin ta na kaima Malamin sai nace ba zan iya samun rigar ta sai tace na kawo hoton ta, nan ma nan ma nace bana dashi sai Shafa tace min na shiga media zan samu tunda ta taɓayin instagram tana kuma Facebook sannan jarida da dama sun buga hoton ta lokacin da ta rasu da lokacin auren ta da kuma lokacin da taso kashe kanta, hakan nayi na samu hotonta na kai malamin ya haɗa wasu siddabaru ya bani yace naje cikin gidan da zata zauna nayi gina na saka kwalbar a kasa sai wannan layar a sama na rufe, a lokacin ne na samu sa'a dan za'a je gyara ɗakin Lil Minal ne, a hakan mukaje tare da Lubna da shafa, Shafa ce ta ɗauke mata hankali har nayi abunda zanyi na gama bata gano ba, Tun daga lokacin ne duk abunda aljanar tayi ma Kairat sai na sani, takan faɗa min tana son haddasa fitina tsakanin ku amman ta kasa saboda tana son shiga cikin jikin Kairat ne gashi ita kuma tana addu'a duk lokacin data raɓe ta sai taji kamar zata kama da wuta, Kuma kullum cikin rufe jiki take, tayi-tayi har ta gaji bata samu sa'ah ba sai wata rana da Kairat ta cire ɗankwalinta ta wuni bata saka ɗankwalinta a kai ba, A ranar ne ta samu sa'ah ta shiga jikinta, ta rika. Haddasa mata tsoron Minal tana ganin kmar ita dan kawai ta gagara zama a gidan ta fita. Wata rana ina zaune parlour sai naga aljanar cikin bakin kaya jikinta naci da wuta tace min bata daina Addu'a ba duk ta qona ta, kuma yanzu an tono layar dana binnen, kamin na yi wata maganar sai kawai yaji tayi ciki na, sai wani irin zafi ya rufe ni bansan lokacin da nayi ihu ba, daga lokacin ban sake sanin inda nake. Ba sai lokacin da na farka na gannin gaban malamin, Ban san hauka nayi ba sai da Gwaggo ta faɗa min, a gaban gwaggo nace zan rabu da aljanar sai malamin ya tuna min da alkawarin dana ɗauka ba rabuwa da ita har a bada idan har ina son rabuwa da ita toh sai na fasa kwalbar idan kuma har na fasa kwalbar na karya alkawari zata iya cutar dani, A nan ya faɗa min a halin yanzu ma data fita jikina tana jikin Kairat kuma ta samu sa'ar shiga jikinta ta ta dalilin kiran sunanta da tayi ta amsa kuma data ganta sai ta ihu bata ambaci Allah ba, Ya faɗa min cikin biyu ɗaya ko dai ni ko Kairat” Tana Kai aya ta fashe da wani irin kuka, Gwaggo ta sun kuyarda kai, Momy da Saif suka kalli Juna. Kuka ta rika rusawa, jikinta har rawa yake, dukan su sai da idanunsu suka cika da kwallah, banda Saif da ya tafi wata duniyar ta tunani. Momy ta share hawayen idanunta ta kalli Safiyyah+ "Ni na rai ne ki tun kina karama har kika girma ni nayi miki tarbiya na baki duk wata kulawa da kike bukata, amman ban nuna miki wannan hanyar ba baki tashi kika ga ina binta ba, miya kaiki aikata wannan mummunan aiki Safiyyah?" Dagowa tayi ta kalleta "Momy kin yi gaskiya baki nuna min irin wannan hanyar ba ban kuma ga kina binta ba, amman kece kika sani shiga wannan halin kika rufe ido kika kyale ɗanki yayi yadda yake so bayan kinsan ina sonsa kuma shi ne ya fara nuna min son tun farko, . Nasan da ace nice bana sonsa da sai kin bi duk hanyar da kike ganin zata ɓulle ki aura masa ni amman da yake nice nake so sai kika rufe ido kika manta da halin da zan shiga"2 Saukowa Momy tayi daga saman kujera zuwa kasa carpet, ta kama hannayen Safiyyah tana hawaye "Ban taɓa jin banbanta ki da ɗan dana haifa ba, naso cillas ta Saif ya soki sai ya juya min baya Mahaifinsa kuma ta goya masa baya, kullum cikin ganin laifin sa nake, tun da kika kamu da wannan ciwon ban sake ganin farin Saif ba daga ni har mahaifinsa, kuma saboda ke ne Safiyyah da ace ina da halin da zaki aure dana sa ya aure ki, ki daina zargina Safiyyah" Lumshe ido tayi, tana wasu irin zafafan hawaye, "Babu laifin Momy a ciki, ba kuma laifi na ko na wani wannan laifin kaddara ne, shin zaki iyaja da ita?" Ba tare daya motsaa inda yake ba yayi mata wannan furucin, buɗe ido tayi ta kalleshi kamin tayi wata magana ya sauko saman kujera ya duka kasata yadda zata iya fuskantar shi, "Ashe ke jahila ce Safiyyah, tunda kike ganin Momy zata iya yi miki abunda Allah baiyi miki ba, bayan nan kika tsallake kika je gurin wani boka yayi miki abunda Allah baiyi miki ba jin jahilci kaddara, kin kuma jahilci Allah, dan shine yadda ya so ga wanda ya so ga kuma wanda ya so tun lokacin da kika yi kulle kulle wa Minal bai isa ya nuna miki duk abunda ya samu mutun daga Allah bane, yanzu kuma sai kisa na aure ki dole jahila kawai"3 A fusace yake mata maganar, har sai da taja baya tana sauke dogon numfashi, sannan ya kalli Momy yace "Tashi muje Momy karki sake zubar da hawayen ki akan wannan" Bai jira cewarta ba ko kuma tashin ta ba ya nufi kofar fita, Momy ta rik'a fuskar Safiyyah "Miyasa kika faɗi wannan maganar Safiyyah? Miyasa baki rufa ma kanki asiri ba?" "Saboda a yanzu na banbance tsakanin tsakuwa da hatsi, na kuma gane shayi ruwa ne, na gaji Momy lokacin kuka ya kare kunci da bakin cikin soyayya ya kare na shafe shafin Saif a zuciyata, Na yarda da babu mai maka sai Allah Momy babu yadda banyi ba amman Saif yaki ya kula ni ma balle ya so ni, Momy na aikata abubuwa da yawa sanadin soyayyar Saif kuma gashi ban kai ga cin nasara ba, nayi sanadin shigar Minal cikin halin bak'in ciki, Soyayyar, kiyayyah, da kuma kishi abubuwa ne da suke rufa idon bawa, baya ji baya gani har sai ya aikata abunda zai aikata sannan ya gane kuskuren da yayi, Na ɓata tsakanin ta da Saif, na ɓata tsakanin ta da Deen, kuma ta mutu ba tare da na nemi gafarar ta ba, na yaudari kai na da abubuwa da dama da zuciyata ta rika raya min kamar wani zai iya bani ba Allah ba, na cuci kaina na yi hasarar lokaci na ɓata tsakanin na da ubangiji na na kuma ɓata tsakani na da ku"2 Kuka take sosai, Momy ma rungume ta tayi tana kukan, Gwaggo ma kukan take har da sarkewa. *** *** *** Kansa saman sitari yana sauke ajiyar zuciya, jin yake ya tsani Safiyyah sosai fiye da da, duk da wani ɓangare na zuciyarsa yana tuna masa da irin son da take masa, sai dai kuma abubuwan da ta bayyana masa yasa ya kara tsanarta tunawa da Minal ga kuma halin da Kairat take ciki yanzu. Ya dade cikin motar sannan ya fito jikinsa kamar a mace ya nufi cikin gidan, saman kujera ya zauna ya dafa kansa yana murzawa, Sai da yayi awa uku da dawowa gidan sannan Momy da dawo fuskarta a kumbure alamar kuka tayi sosai, Lubna ce hankalinta ya tashi ganin Mahaifiyarta haka, gashi Saif ɗin ma tun da ya dawo baiyi ma kowa magana ba, kuma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa ta damu sosai, saɓanin Saif da tasan me ke faruwa, da kallo ya bi Momy har ta zauna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai yana cika ma bakinsa iska DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI "Ni Momy ban ga anfanin wannan damuwar da kike sa kanki ba, wannan yarinyar bata da tunani kuma wallahi duk abunda ya samu mata ta sai na raina mata hankali" "Kai ma ka yarda tana iya yi mata abunda Allah bai yi mata ba kenan" Kan Momy a kasa take masa maganar, Lubna na zaune kusa da ita cikin da rashin fahimta idan ta kalli Momy ta kalli Saif. Kai ya girgiza "Aa Momy ni ban yarda da wannan ba, kawai dai ita ce sanadi tun har ta faɗa da kanta" "Kamar yadda ka zamo mata sanadin shiga halin da ta shiga ko?" "Oh Momy ki daina shigar mata, kina son shafi laifinta ba, bata gurbi abunda ta shuka ba sai nan gaba" Tashi yayi yasa hannayensa aljihu, ya nufi kofa "Karka fasa kwalɓar nan Saif karka sake jefata cikin wani hali"1 Tsayawa yayi cak, ba tare da ya juyo ba yace "Ban jefa ta ba Momy ba kuma zan jefa ta ba, ita dai ta jefa kanta" "Tun lokacin dana fara haɗuwa da Minal Kairat ce ka fara labarta min, sai kuma gashi kazo min da maganar Minal har ka aure hankalin ka bai kwanta ba har sai da ka auri Kairat, yanzu kuma ta kamu da rashin lafiya duk kabi ka fita hayyacinka har kana kokarin ɓatawa da yar'uwarka, Nasan Kairat tayi maka hallacin tun da ta shayar da lil Minal kuma yanzu tana ɗauke da wani cikin naka, amman ina son kasan wani abu guda ɗaya, Ana chanja mata ba'a chanja yar'uwa ba shin yanzu idan ka rasa Kairat yaya zaka ji?" Juyowa yayi da sauri ya kalleta, kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya haɗiye maganar, tare da numfashin sa, sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi "Haka zaka misalata yadda Safiyyah take ji a ranta baka da tausayi Saif ka canja kwatakwata kamar ba kai ba kana son kanka da yawa babu ruwanka da damuwar kowa sai taka zuciyarka ta mace! Tirr da irin son da kake yima Kairat tirr da son da xai rufe maka ido ka kasa ganin kowa sai ita kaji tsoron ranar da sonta zai wahalar da kai hakkin Safiyyah ya dawo kanka!"8 Tunda ta soma maganar ya dinga jinta gan gan gan kamar ana sara masa gatari aka, sam bai zaci wannan maganar daga Mahaifiyarsa ba, tun tashin ta Momy bata taɓa faɗa masa wata magana makamanciyar wannan ba, amman a yau ta faɗa masa saboda Safiyyah, tsabbas ranta a ɓace yake yake dan har cikin makoshinta furucin ke fitowa, Wani dogon Numfashi Lubna ta sauke zuciyarta na bugawa da karfi ta kalli Momy ta kalli Saif, Shima kallonta yayi ya kalli Momy sai ya ɗauke kai ya fice. Wata tafiya ce yake mai kamar sauri-sauri kuma ba sauri ba, kallo ɗaya zaka yi ma fuskarsa ka fahimci tafiyar ɓacin rai ce yake, yadda ya bar gida sai da hankalin securities ɗin ya tashi, haka ya hau tt yana wani irin gudu kamar dansa kawai aka shinfiɗa titin, kamar wani ifiritu haka ya isa gidansa cikin kankanen lokaci. Har ya zauna maganar Momy ce take masa yawo a kai, tashi yayi ya nufi firjin ya bude ya ɗauki robar ruwa ya ɗaga kansa ya kafa kai, da wani irin karfi yake shan su, sai da ya kusa shaye wa sannan ya sauke kansa yana maida numfashi da karfi, ya jefar da kwalbar, saman kujera ya dawo ya ya zauna ya lumshe ido,har na kusan na mintuna talatin, can kuma ya buɗe ido da sauri kamar wanda ya tuna da wani abu ya tashi ya fito harabar gidan, ma'aikatan gidan ya fara kwalama kira, jiki na rawa suka iso cikin girmamawa, ɗaya daga cikin su ya kalla ya nuna masa gefen da itacen gidan suke2 "Can nake son kuje kuyi ta binciko min wata kwalba, tana nan cikin kasa ku duba da kyau karku ce min baku ganta ba" Da "Toh" suka amsa suka nufi gurin shi kuma ya juya ya dawo falon ya zauna, yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana matsa gashin. Bayan kamar minti arba'in, aka kwankwaso kofar parlour, ya ɗan daɗe kamin ya bada izinin shiga "Yes" Turo kofar akayi aka shigo, hannunsa rike da kwalbar mai cike da hayaki, ya mika masa "Ga abunda muka gani" A hankali ya buɗe ido ya sauke su kan kwalbar, da ido yayi masa nuni daya aje ta saman tebur ɗin dake kusa dashi, yana ajewa ya juya ya fice. Kwalbar ya tsura ma ido, yana taɓa hancinsa kamar mai tunani, zuwa can ya tashi daga gimciren da yake still yana kallon kwalbar, sai da yayi bismillah sannan ya kai hannu ya rik'a kwalbar ya ɗaga sama yana kare mata kallo, wani abu ne a ciki mai kamar hayaki kamar toka da wani abu kasanta ja kamar ruwa jini, Bismillah ya sake yi ya cira kwalbar iya karfinsa ya buga kasa, a nan take kwalbar ta watse.2 Farin hayak'i ne ya turnike gurin daga bi sani hayakin yayi sama ya fita ta windo, Saif kan kallon hayakin yake ba ko kyata ido har sai da ya daina ganinsa, sannan ya kauda kai yana jan numfashi, ya daɗe yana nazarin maganar Safiyyah da kuma ta Momy sai dai maganar Momy ce take ɓata masa rai duk lokacin daya tuna, abunda ya aikata a yanzu gani yake ya aikata daidai ko ba komai ita ta jama kanta kuma itace silar rashin samun kwanciyar hankalin aurensa ga kuma laifinsa da Momy take gani duk a dalilinta, koma miye ta aikata can taje ta karata tun ba shi ya aike ta ba. tsiya ke tada tsohon bashi inji Hausawa, a nan ne ya soma tunanin taya akayi Deen ya san da wannan shirin na Safiyyah? Ita tambayar da ta rika zo masa a rai kenan tana masa yawo a kwakwalwah, wayarsa ce kawai mafita, haka wani ɓangare na zuciyarsa ya amsa masa, a hannunsa ya rik'a juya wayar bayan ya fiddo ta daga aljihu sa, kamin ya soma shafa screen ɗin yana kallon hoton lil Minal, sai da wayar da fara ringing sannan ya maida hankali akan wayar, sai dai bai kaita kunnensa ba sai har sai da mai kiran yayi daf da katsewa, "Ta ya akayi kasan da wannan labarin?" "Ta amsa laifinta kenan? Ka tabbatar da gake nake ko?" Aka amsa masa daga ɗayan ɓangaren, bai damu da ba da amsar tambayar da aka masa ba sai ya a kara jaddada tasa tambayar "Taya akayi kasan da wannan plan ɗin?" Shima ya ɗan daɗe kamin ya amsa "Wata rana ne na fito daga kauyen mu, sai na haɗu da motar Safiyyah ita kuma tana kunna kai cikin kauyen, ganin kamar motar dana sani yasa na juya ya rika bin motar a baya har muka raba hanya, Ta nan ne na hango fuskar Safiyyah kasancewar glass ɗin motor a sauke yake, a haka nayi ta binsu har naga gurin da sukayi Parking, a bakin kofar gidan wani babban boka dake garin namu, Nayi mamakin yadda akayi Safiyyah tasan da wannan bokon, tunawa da abunda tayi min ta kuma yi ma Minal sai ya kawar da wacan tunanin nawa, Bayan naga gidan da suka sauka sai nayi tafiya sai washe gari na dawo gurin bokan na zuba masa kuɗi mai yawa, a nan dake sai ya bayyana min abunda ke tafe da ita da kuma abunda ya aikata mata, ban gasgata hakan ba har sai da naji labarin Kairat ba lafiya, Dana je gurin Mummy dan sanar mata sai na tarar hankalinta a tashe yake bata ma saurare na balle ta fahimci me nake nufi, nasan kai kaɗai ne mafita wanda zan faɗa ko da ba zaka yarda da ni ba, Sai dai nasan wata rana zaka gasgata ni ka kuma yarda ada abunda na faɗa" Lumshe ido Saif yayi, lokacin da Deen ya kai aya a bayanin sa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tasa leɓensa ya ce "Thank you" Deen bai kara ce masa komai ba ya kashe wayar,bayan kamar minti biyar wani kiran ya kara shigowa, ba tare daya duba mai kiran ba ya dannan picking yasa hands free, "Kana ina Saif?" Muryar Nasir ce hakan ya tabbatar masa da shine ya kira ko da ba number sa bace, ya ɗn bata lokaci kamin ya amsa "Ina gida" Wayar ya tsurawa ido bayan katse kiran, har lokacin zuciyarsa cike take da ɓacin rai. Sai da Nasir ya kare masa kallo sannan ya zauna kusa dashi yana faɗin "Lubna tace min kayi faɗa da Momy miya faru?" Ba tare daya kalleshi ba ya amsa "Bata faɗa maka dalilin faɗan ba bata ce maka mi nayi ba?" "Bata ce min ba, ta dai kira ta faɗa min" Sai a lokacin Saif ya kalleshi ya soma labarta masa abunda ya faru, dan abokin dariya ba'a ɓoye masa kuka, shiru Nasir yayi yana nazarin lamarin, bai ga. Laifin Saif ba ko kaɗan itama Momy ya san zafin rai ne ya haddasa tayi haka, kallon Saif yayi ya sake kallonsa damuwa ce kwanace a fuskarsa wanda ke nuna ta zuciya tafi wannan yawa, koba komai yasan yadda Saif ke gudun zuciyar Momy baya son ganin ɓacin ranta sam, kuma hakan kan iya haifar da ɓacin ran Abbah, Hannunsa kan kafaɗar Saif ya ce "Ka kwantar da hankali i will talk to her" "Ba zata saurare ka ba, idonta a rufe yake a yanzu ta kasa fahimta ta saboda Safiyyah, bata dubi halin da nake ciki da kuma wanda zan shiga" "That's Why nace zan yi magana da ita Just have a faith zamu samu mafita" Kai ya girgiza masa, shi kuma ya tashi sai shima ya tashi suka fito tare, shi ya ɗauki hanyar gidan Momy shi kuma ya nufi asibiti, Yana yin parking Lubna ta fito ta tarbershi, sai da suka kawo kofar shiga parlour ta fara masa magana kamar mai raɗa, "Momy ba zara saurare ka ba Ya Nasir, ko ta saurare ka ba zata fahimci abunda kake so ta fahimta ba, nima ɗazu akan hakan sai da ta tashi mari na" Ya ɗan zaro ido yana kallonta da yar dariya "Kece kema dakin samu rabon ki, amman ni nasan zata saurare ni" "Wallahi wahalar da kanka kawai zakayi kila ma kai ma ta kwaɗa maka marin" Wannan karon dariyar gaske yayi "Tana ina ne?"1 "Tana nan parlour ta haɗe rai sosai" Har lokacin magana take masa a raɗa wai kar Momy taji, kumatunta kawai yaja ya kunna kai cikin parlour, bayan kamar mintuna bakwai ita ta rufa masa baya. Har kasa ya risina ya gaisheta kamar yadda ya saba, sannan ya zauna a kujerar dake facing ɗin na ta, cike da fargaba ya soma magana dan shi ma kansa ya tsorata ta ganin yanayinta "Momy, bai kamata a ce kina fushi da Saif ba, bashi da laifi cikin wannan lamarin kuma ki daina ganin laifin Kairat ita ma bata da laifi Momy Saif shine kaɗan ɗa namiji da kika haifa, baya da farinciki sai naki ya kamata a ce ke ce kika fi kowa fahimtar sa" DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Yawun bakinta ta haɗe ba tare da ta kalleshi ta ce "Kasan wani abu Nasir?, Safiyyah tana sa gaskiya naso kai ma da yawa, da ace Saif ne yake son ta da duk yadda zanyi sai naga nayi wajen ganin ya aure ta, ko ka nasan ba karamin shiga da fita zakayi ba wajen ganin abokinka ya samu abunda yake so, Safiyyah Marainiya ce Nasir a hannu na ta tashi ya kamata ace na sama mata duk wani farinciki da take bukata, ban taɓa saka ta abu tayi min musu ba, duk abunda tasan yana faranta min itace kan gaba wajen aikata shi, sam sam sam ban kyautawa Safiyyah ba" "Amman Momy yanzu.... -" Hannu ta ɗaga masa, "Ka aje kalaman ka Nasir, nasan kana kokarin kare abokin ka ne" Bata tsaya jiran komai ba ta tashi ta nufi ɗakin ta, a sannan ya maido kallonsa ga Lubna ta ɗaga masa kafaɗu "Ai na faɗa maka ba zata saurare ka ba" Sumkuyar da kansa yayi kasa yana jinjina al'amarin. Abu kamar wasa sai gashi Momy ta kusan kwashe kwana biyu babu ruwanta da Saif da duk abunda ya shafe shi, babu yadda bai yi amman taki ta kula shi, saboda har yanzu bata daina ganin laifinta ta, a duk lokacin da ta tuna Saif take ɗorawa laifin, gashi tana son zuwa sake duba Safiyyah amman ta kasa, saboda tunanin abunda zata ce mata. A ɓangaren Saif kan jin yake kamar ace masa rai ya huta, dan abun yayi masa yawa, ga matarsa a kwance, har yanzu ba wani sabon labari ga matsalan Momy shi, Mummy ma ta shirya komai da zata ayi aka kaita waje don duba lafiyar ta amicewar Saif kawai ake jira shi kuma ya kasa aiwatar da komai saboda Momy taki tasa baki cikin lamarin, cikin yan kwana biyu nan duk yabi ya rame abinci kirki baya ci iya kacinsa yan ruwan tea ko juice, ita kanta Momy tana tausayin halin da ɗan nata yake ciki ta dai ki nuna masa ne saboda har yanzu bata daina ganin laifinsa ba, dan iya kuskure tasan yayi, amman kuma ya za'ayi abun duk da ya girma ya riga ya gama girma, kuma tun ran gini tun ran zane. Babu ani gwari a tare dashi haka ya shiga ɗakinta, sai da ya zauna kusa da ita kasan carpet sannan ya kalleta "Momy an wuni lafiya" "Lafiya kalau ya jikin matar taka?" "Da sauki, Luban tace kina nema na" "Eh akan maganar matar ka ne, shawarar da zan baka ka bar matarka a nan, da nan da can duka ɗaya ne tunda Allah dai shine yake bada lafiya kawai kasa Allah a gaba kayi ta mata addu'a" Dagowa yayi ya kalleta akaro na biyu, dan bayi zaton jin wannan maganar daga bakinta ba, "Ina nan ina yi Momy kuma Insha Allah haka zanyi" "Allah ya bata lafiya" "Amin" Ganin ta kishingiɗa yasa shi tashi ya fito daga ɗakin zuciyarsa cike da tambayoyi, kao tsaye ɗakin Lubna ya shiga, bayan ya baro ɗakin Momy, tana zaune tasa plate ɗin abinci gabanta sai aikawa take tana dannar waya, "Ke" Ta juyo da sauri ta kalleshi, "Yaya shigo mana ka tsaya can ko wani abu kake so ne?" Shigowa yayi, yayi mata tsaye a ka, "Mi akace da Momy yau" Dariya tayi, "Daman nasan sai ka tambaye ni shiyasa ya shigo ɗaki ai, kaga ta canja yau ko?" Kai ya ɗaga mata, "Wallahi Daddy ne ya rufe ta da ruwan masifa, yace shi sam na zai ɗauki wannan a gidan nan ba, akan me zata rika maka haka, yace idan har bata tausayin halin da kake ciki ai ta tausaya ma lil Minal, Yace kuma Safiyyah ita ta jefa kanta cikin mugun hali, ba kuma ba a cilasla maka yin abunda baka tashi ba, yace kuma Safiyyah itace shi take yar'uwarsa ba Momy dan haka babu ruwanta da abunda ya shafe ta, Daga karshe yace duk abunda ya same ka ita ce kuma ba zai kyale ba, yace duk kabi ka rame ka fita hayyacin ka da wani zaka ji!" Shiru ya ɗanyi kamin ya ce "Ke taya akayi kika ji?" "Nice ma kai ma Daddy gulmar ai" "Wai daman Daddy bai sani ba?" "Eah mana, wacan karon ma ai ɗan yaga Safiyyah ta haukace ne shiyasa kaga yayi maka wannan faɗan kuma Momy ce take faɗa masa wai ai duk kaine da laifi" "Thank you" Haka kawai ya faɗa ya juya, yana murmushi ya fice. *** *** *** Kamar ko yaushe, yau ma ya daɗe yana addu'a bayan ya kare sallah Nafila ta karfe uku da yake yi kullum, ya faɗawa Allah bukatar sa ya kai kukan sa a inda za a share masa, sannan ya tashi jiki ba gwari ya nufi kujerar dake gefen gadon ya zauna, tsare ta yayi da ido, yana tunano yar karamar rayuwar da sukayi a tare, sannan ya kai hannu ya shafa fuskarta da ta bushe, daga bisani ya tura hannubsa cikin nata ya rike yana murza yatsunta a hankali, ajiyar zuciya ya sauke ya jinginar da kansa jikin gadon, jin ta motsa hannunta bai sashi ya ɗago ba dan ba sabon abu bane a yan kwana ki nan takan motsa hannun, amman ba magana ko kuma wani motsin, "Sa... I.. F" Cikin wahalalliyar murya ta kira sunan nasa, aiko ba shi ya ɗago da sauri ganin idonta a buɗe yasa shi gwalo nashi idon ya saki baki yana kallon ikon Allah, ita kan sai kallonsa take da dishi dishin da take ganin, da ba dan kashin turarenta ba da kuma. Sanyi hannunsa ba da ba zata iya gane shi ba, daga kwance ta dake ya rungume ta, kamin ya ɗauke cak ya rik'a waliliya da itar tsakar ɗakin, zuwa can kuma ya ajeta ya faɗi yayi ma Allah Sujadar godiya, sannan ya ɗago ya sake rungume, Ita kan sai kallonsa take tun tana gani dishi dishi har ta fara gani daidai, tayi kokarin ta tunano abunda ya faru amman ta kasa, iya abunda ta sani shine ta daɗe tana bachi, zaunawa yayi saman gadon rumgume da ita kamar wata karamar baby ya rik'a fuskarta "Kairat kina iya gani yanzu kina iya jina? Akwai inda yake miki ciwo? Meke damun ki yanzu?" Hawaye ne ya gangaro daga idonsa, hawayen da ba zan iya tantance na minene farinciki ko akasin haka!. Hannu tasa ta shafe masa hawayen tana kallon idonsa, wanda da ita dashi ban san na waye yafi zurfi ba, "Saif kuka kake yi? Mi ya faru da ni?" "Zan faɗa miki komai daga baya kawai ki faɗa min mike miki ciwo a yanzu?" "Babu" "Kin tabbata?" Kai ta gyaɗa masa, ya tashi, ita dai kallonsa kawai take har ya fice, be daɗe ba ya shigo tare da wasu likitoci guda biyu, Mummy ce ta uku, tayi mamakin ganin yadda ake mamakin tashinta sai abun ya koma mata kamar mafarki, _Miya faru da ni?_ shi ne abunda take ta tunano wa take kuma tambayar kanta amman ba amsa, bayan fitar likitocin Mummy ta rumgume tana kuka, tana yima Allah hamdala, "Mummy miya faru dani" "Komai ma ya faru dear na gode Allah da ya dawo min dake daidai" Tana kallon Saif ya sakar mata murmushi, sannan ya zauna saman gadon yama mai lumshe ido da buɗewa, Mummy ta tashi cikin zumuɗi "Bari na haɗo miki tea ki sha ko kina son wani abun" "Tea ma is okey" Cikin sauri ta fita, sai ita kuma ta kalli Saif da fuskar damuwa "Miyasa aka kawo ni asibiti? Mi ya faru dani ne wai?" Murmushi yayi, "Ni kai na bansan abinda ya faru dake ba, ni dai na dawo ne sai na tararda ke kwace a kasa kin dafe ciki baki iya magana, a nan ne sai na kawo ki asibiti daga lokacin sai hankakinki ya bar jikin ki" Shigowar Mummy ce tasa duk suka kalli kofa, Kairat sai nazarin maganar take dan har yanzu bata gano musabbabin abun ba, Mummy da kanta ta rika bata tea cikin wani irin jindaɗi, Kairat ta lura da hakan, sai tasa hannunta ta rika hannun Mummy, Mummy kuma ta jimke hannun jinjinjin, "Da ace na rasa ki Kairat da bansan yadda rayuwata zata kare ba" "Mummy ba zaki rasa ni ba, ki daina tunanin hakan" Ta shafi kanta zuwa gefen fuskarta, idonta cike da hawaye ta ce "Ina fatar haka" Ta ɗauki lokaci a ɗakin, sannan ta ɗauki cup ɗin tea ta fita, Saif kamar ita yake jira ya dawo kusa da matarsa, ya rungume ta. A jikinsa ta karasa bachin, duk da ba wani bachi sukayi ba. Hasken asuba na fara fitowa su Hajiya Suwaiba suka iso tare da Abbah, daman tun cikin dare Mummy tayi musu waya ta sanar musu, ganin su ne yasa Saif mika ma Mummy cup ɗin tea dake hanmunsa, ya ɗan matsa ba bada space tsakani su, sai Mummy ta cigaba da bata tea shi kuma yana gaisawa da su, Abbah ya kalli Mummy yana murmushi "Hankali ya kwanta ko Ummu Kairat?" Murmushin itama tayi, ta shafi kan Kairat, Hajiya Suwaiba sam bata jindaɗin maganar ba sai dai bata nuna masa ba, dan a yadda ta fahimta a yanzu yana son Mummy fiye da tunanin ta, ganin yadda duk damuwar ta ta zame masa tasa, a halin da Kairat take cikin ta fahimci Mummy yafi tausaya ma sama da ƴarsa Kairat. Hajiya ta murmusa irin murmushin da bai kai zuci ba tace "Yanzu kuma ai kuka da tunani ya kare ko?" Mummy dai murmushi kawai tayi ta tashi ta nuna ma Abbah kujera, ita kuma ta tsaya daidai Hajiya Suwaiba still tana murmushin, "Ga kujera a zauna" Murmushin yayi mata ya zauna yana yi ma Kairat ya jiki, "Jiki da sauki Abbah" Ta amsa tana kallon Hajiya Suwaiba dake kallon Mummy ita kuma tana kallonta. Basu jata da fira sosai ba, suna gurin aka kawo mata breakfast daga gurin Momy kamar yadda aka saba, tara saura Saif ya bar ɗakin ganin basa da niyar fita ya nufo gida da zimmar ya sanar da Momy ya kuma yi wanka ya canja tufafi, a part ɗinsa yayi parking ya fito daga motar da zimmar ya shiga yayi wanka amman sai ya kasa zimuɗin sanar Momy yake, haka ya nufo part ɗinta zuciyarsa cikeda farinciki a fuskarsa ma zaka iya gane hakan, dan tun daga nisa Momy ta gane yau ɗan nata yana cikin farinciki, "Momy ya na ganki da shiri haka? Kar dai ace kinji?" Ya faɗa lokacin daya karaso kusa da ita hakoransa a buɗe, Momy ta ɗanyi fuskar mamaki "Naji me? Da wani labarin ne?" "Yes Momy ba Kairat ta tashi ba" Ya faɗa yana wani abu kamar yanzu ya soma jin tashin nata a zuciyarsa, jin yayi ba zai iya ɓoye murnar sa ba har sai da ya rumgume Momy, Momy tayi dariya tare da godiya ga Allah "Alhamdulillahi amman naji daɗin wannan abun, cuta ba mutuwa ba" "Wallahi Momy tun jiyada dare fa, kar ki so ganin yadda nake jindaɗi" "Ai na gani kan, gashi nan ya kasa ɓoyuwa a fuskarka, aiko yanzu shirin nan da nayi ina son naje duba ta ne idan na fito gurin Safiyyah" "Da banyi sauri ba da kin tararda ni a can ashe" "Lallai kan, bari naje so nake na dawo da gurin akwai bakin da za'ayi daga Europe" "Okey Momy nima wanka kawai zanyi na koma" Murmushi Momy tayi, aka buɗe mata motar ta shiga Saif ya maida ya rufe yana mata Allah ya tsare. Kamar yadda ta faɗa, a harabar gidan su Gwaggo driver yayi parking wani ya fito daga ɗayar motar da sauri ya buɗe mata cikin girmamawa, sauran suka shiga fito da kayanyakin da dace musu a nan zasu kawo, kayan kwalama ne waɗanda tasan Safiyyah tana so, kamar ko yaushe yau ma da sallama ta shiga parlour fuskarta ɗaukeda murmushi duk da Faɗuwar gaba ne a zuciya wanda ita kanta bata sam dalilin sa ba, Sallamarta da kuma sautin takun tafiyarta kana da kanshim turaren ta shine ya tabbatar mata Safiyyah Momy ce ta shigo, "Momy..." Ta kira sunan nata dan ta tabbatar, kasancewar ita kaɗai ce ke parlour, sai da Momy bata amsa ba har sai da ta zauna kusa da ita, "Na'am Y'ata" Hannu ta kai tana shafa jikin Momy har ta kai ga fuskarta, "Momy kece?" Shiru Momy tayi tana kallonta jikinta a sanyaye, dan ta kasa gasgata abunda idanunta suke gane mata, "Momy ke ce amsa min magana" Ta faɗa muryar tana gaf da kuka, Momy ta rika hannunta "Ba ki gan ni bane safiya" "Bana iya ganin ki Momy idanuwana a yanzu rufe suke bana iya bambance baki da fari ko kuma haske da duhu, na kan kane kowa neta hanyar murya ko kuma kanshim turare ne kawai amman ba da ido ba" Hawaye na mata zuba take magana, Momy bata san lokacin da hawayen idanunta suka fara fita ba, ta sauko daga saman kujerar bakinta na rawa ta ce "Safiyyah baki gani kike nufi? Yaushe makanta ta same ki?" "Momy bana gani, a yanzu haka ban gani komai sai duhu" "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un, yaushe wannan abun ya same ki?" "An kwana biyu yanzu, Momy rayuwa ta kenan haka Allah ya kaddara min nawa al'amarin" Duk kan su cikin kuka suke maganar, musamman Safiyyah, "Momy ni da kaina na jefa kai cikin ramen daba zan iya fita ba, ni ka kona kaina da raina ni na salwantar da rayuwarta dan kawai biyan bukatar duniya kuma gashi ban samun biyan bukata ba, Momy abunda nayi neya dawo min, nayi nadamar abun da nayi, sanadin hakan nayi hauka yanzu kuma makanta na rasa masoya na guda biyu akan biyan bukatar da har gobe ba zata biya ba, Momy da ace na karɓi shawarar ki tun farko da ban faɗa wannan halin ba" Lumshe ido Momy tayi hawaye na mata zuba, "Kaddara ta riga fata Safiyyah haka Allah ya kaddaro miki rayuwar ki, haka aka so ya kasance a gareki" Gwaggo ce take maganar tana tsaye kofar kicin tana hawaye, Momy ta ɗago ta kalleta sannan ta share hawayen idonta, "Miyasa ba a faɗa min tun lokacin da abun ya same ta?" "Saboda babu abunda zaki iya yi mata, da kin damu da ita har haka ai da bata shiga halin da take ciki ba yanzu" Cikin kuka Safiyyah ta ce "Gwaggo, Momy bata laifin a nan nice da kai na siyar da kai na inda kuɗin fansar kaina ba zai taɓa samu ba, ba zata iya goge abunda yake rubuce tun kamin a haife ni ba, bata iya tayi min abunda Allah baiyi min ba, Hakika ko wane mumini yaba zama mumini har sai da jarrabawa, ni kuma an jarrabe ni sai dai ban ci tawa jarrabawar ba, Ina ma gaba na zai koma baya baya kuma ta dawo gaba da na gyara komai na rayuwata" "Miyasa kika aikata Safiyyah?" "Sheɗan ne Momy, ya rika doka min gangan ina rawa, ta kuma rufe min ido na rik'a hangen kamar nasara ce, ashe bakin ciki da dana sani ne suke kwankwaso min kofa, ni kuma na amsa musu ba tare da sani ba" Kuka sosai Momy tayi ita da Safiyyah babu mai iya ba wani hak'uri, jinjina al'amari take tana tausayin yadda mai ido farat ɗaya zai zama makaho, hannayen Momy ta kama ta rike gam DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI "Idan har kaddara ta tsaya a nan toh na gode Allah saboda nice na ɗebo ruwan dafa kai na da kai na, a yanzu na zama wata irin kalar mace hakika na cuci kai na da kuma cutar da wasu, bai haifar min da komai ba sai nadama da hasara, ki yafe min Momy" "Baki yi min komai ba Safiyyah koma kin yi min na yafe miki Allah ya warkar miki da wannan lalurar, zanyi duk yadda zanyi wajen ganin kin samu lafiya insha Allah" Cikin kuka Momy tayi maganar, sai da ta samu kujan nata ya ɗan tsagaita sannan ta share hawayen ta tashi jiki ba karfi ta fice. Bata je asibitin ba kamar yadda tayi niya, snanin bakin ciki da ɓacin rai har ta iso gida kuka take, daker ta iya labarta ma Lubna halin da Safiyyah take ciki, itakan bata yi mamaki ba, dan tun lokacin da abun ya same ta ta samu labari, ita tama yi tsammanin sama da haka ne zai faru da ita tunda ita ta jawa kanta, "Momy akan me zaki rika damuwa da halin da takr ciki ita fa ta jawa kanta, sannan ke ba wannan tarbiyar kika mata ba, ba ke kika nuna mata wannan hanyar ba, ita ce ta sauya rayuwar ta ɗauki wanda take ganin kamar itace mafita" "Akwai tausayi Lubna matukar zuciyar musulunci ce jikin ki kika ga Safiyyah sai kin tausaya mata, budurwa da makanta, yarinyar da babu abunda ta nema ta rasa, sanadin so ta kai kanta ta baro kuma ba tare da bukatar ta ta biya ba" Ajiyar zuciya Lubna ta sauke, ta ɗanyi kamar mai nazari, Momy ta share hawayem idonta ta nisa tana faɗin "Allah ka tsare mu daga muguwar kaddara, da mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani" Kanta ta kwantar jikin Momy ta amsa ta "Amin" *** *** *** Kwananta biyu suka sallameta bayan sun tabbatar babu abunda yake damun ta, daker Mummy ta yarda aka maida da gidan mijin dan son tayi ta koma gida har sai yadda hali yayi tukuna, sai gashi Saif yakin yarda a dole ita ta hak'ura, Tunda suka dawo ba wani aiki take yi sosai ba, ga kula da take samu ta ko ina, duk bayan kwana biyu sai tazo duba ta, a ɓangaren Abbah ma haka yake dan a koda yaushe cikin waya suke, Bata da matsala ko ɗaya a yanzu, babu kuma abunda take zumuɗi kamar auren Abbah da Mummy, duk da a ɓoye za ayi shi, amman hakan bai hana Kairat yin wasu abubuwan ba, haka ta rika kai kawo har aka ɗaura auren, aiko ranar farinciki gurin Kairat ba'a magana, gurin Hajiya Suwaiba kan bakinciki ne ya cika ta a nan ne Kairat ta kara tabbatar da Lallai kishi kumallon mata ne tana mamaki yadda Hajiya da ta girmi Mummy amman take kishinta, haka tayi ta tausar ta da kalama da kuma nuna mata Mummy ba mace bace mai matsala, Abbah yaso Mummy ta tare a ɗayan gidansa ko kuma gidan da Hajiya Suwaiba take ciki amman taki ita dai tafi son gidan da take, tunda aka ɗaura aure sau ɗaya Saif ya yarda Kairat taje gidan Mummy, wai a yanzu shi ba zai yarda tana masa yawo da ciki ba ga kuma lil Minal take fama da quiya tunda aka yayeta a yanzu bata yarda da kowa daga Mah sai Pah, Wasa wasa lamarin Safiyyah sai karuwa yake tun ana ganin kamar za a warke haran fara fidda rai, dan babu asibitin da kai ta ba ta ido tun daga nan Nijeriya har waje amman abun sai karuwa yake dan a yanzu har kaikayi suke mata, Tana tafe yar jarorar da Momy ta samo mata tana janta har suka kawo gurin da akace bakon dake sallama da ita yana tsaye, "Gashi nan" Yar jarorar ta faɗa sannan ta sake ta ta juya ta basu guri, shirun da taji yayi yawa ne yasa ta mika hannu zata taɓa mutumen "Ba mutun a gurin ne?" "Hmmm gani ba ganki amman baki iya gani ba, duniya kenan budurwa wawa, ai ni naso kin fi haka shiga matsala, Kyakkyawan dake amman ba ido, kin cancanci shiga ko wace irin matsala ta rayuwa, zaki iya tuno lokacin da kika ɓata tsakani na da Minal kika kira ni wawa saboda na biye miki mun aikata abunda kika yaudare ni a kai kuma kika yaudari kan ki, shin wace irin riba kika ci a yanzu?" Tunda ya soma maganar ta fahimci wanene, wani kalar bakinciki ne ya mamaye mata zuciya lokaci ɗaya hawaye suka rika bin fuskarta wasu na korar wasu, "Deen... -" "Yes anything for me again?" Bata ce komai ba har na tsawon wani lokacin, zuwa can ya kalleta up and down yace "Nazo ne kawai na ganki kuma na fi kowa farinciki shiga halin da kike ciki ina miki fatan alheri" Bai jira abunda zata ce ba ya buɗe motarsa ya shiga, ita ma ɗin bata ce komai ba har yaja motarsa ya bar gurin, sannan tasa hannu ta share hawayen idonta ta juyo da yar sandarta ta dafe dafehar ta shiga parlour, yar jarora na ganin ta, ta tashi ta rika ta, ta zaunar, Ajiyar zuciya ta sauke ta tsura ma carpet ɗin ido kamar wance ke ganin carpet ɗin, wasu siraran hawaye suka zubo mata, ta fi karfi minti talatin a haka sai hawayen take, yarinyar na ganin hakan ta tashi ta faɗa ma Gwaggo, sai gata ta sauko cikin sauri ta zauna kusa da ita "Me kuma ya faru?" Sai da share hawayen sannan tace "Mako mata nake tunani Gwaggo, na cuci mutane da suka yarda dani na zama mai fuska biyu har wanda bai san da zama na ba na cutar da shi" "Har yaushe zaki daina wannan tunanin Safiyyah yaushe zaki bar zuciyar ki ta huta?" "Sai ranar da na koma ga Mahalicci na, makoma ta nake tunani Gwaggo, idan amanar wasu ta tashi kama ni ya zata zo min, wata rana zata zo Gwaggo ke kanki zaki gaji dani ki gujeni, ba zan auru ba Gwaggo dan babu wanda zai auri makauniya, duka kawayena sun bar ni saboda suna ganin yanzu bana iya komai, hakika hausawa sunyi gaskiya da sukace duniya ta ishi kowa ri da wando wanda bai zo ba ta shirya masa balle mu da muke cikin ta" Gwaggo ta share hawayen idonta tana faɗin "Babu wannan ranar Safiyyah, bazan taɓa gudun ki ba Allah dai ya baki lafiya" "Amin amman wannan idon ka ba zan taɓa warke ba" "Kada ki yanke kauna daga Rahama Allah" "Kai ni ɗaki na zan kwanta" Gwaggo da kanta ta rika ta suka nufi ɗaki ko wane zuciyarsa babu daɗi. **** **** **** As usual da ledoji ya shigo parlor, ganin bata parlour kuma bai ji motsinta kicin ba ya tabbatar masa da tana ɗaki, a parlour ya aje ledojin ya nufi ɗakinta, ya tura kofar ɗakin yana faɗin "I'm back" A wahale ta ɗago ta kalleshi tace "Sannu da zuwa" "Yauwa Baby na, ina ɗayar Babyn?" "Ta raka Lubna da kawayenta rabon anko" "Kin san ban cika son yawan fitar nan da take ba ko, bana son ta saba da yawon nan" Ita dai bata ce komai ba nata ya ishata, sai a lokacin ya lura da halin da take ciki, "Meke damun ki?" "Marata ke ciwo" Ta faɗa tana dantsar baki, karasowa yayi ya rik'a ta daker tayi zaune, a nan yaga jini, zaro ido yayi "Subhanallahi" Hannayensa yasa ya ɗauke ya nufi bedroom da ita, ya cire mata kayan jikinta ya gyara mata jikin sannan ya ɗauko doguwar riga yasa mata da hijab, ya ɗauke ta ta nufi mota da ita. Safa da marwa ya rik'a yi a bakin kofar, yana haka Mummy ta iso "Tana ciki?" Shine abunda ta fara tambaya daga isowa, a natse ya gaishe ta bayan ta amsa yace "Eh tana ciki" "Haihuwar ne?" "Ina jin shine ban dai tabbatar ba" Kujera ta samu ta zauna, hankalin ta ba a kwance ba, sai Addu'a take, Saif ma ita yake a inda yakr tsaye, Bayan kamar awa biyu da wani abu wata nurse ta fito daga ɗakin da sauri, "Kuje ku kawo kayan jariri matar ka ta kusa sauka" Tana faɗar hakan ta nufi wata hanyar da sauri, shi kan tsaye yayi kamar wanda bai ji abunda tace ba, Mummy ta kalleshi "Kun sayi kayan jariran?" Ya ɗaga mata kai "Eh suna can gida" "Okey ba ni keys ɗin zan ɗauko" Mika mata yayi dan shi kan baya jin zai iya barin gurin har sai yaji ance matarsa ta haihu. Mummy na karɓar keys ɗin ta ɗauki jakarta ta fice da sauri, ba tayi minti biyar da fita ba sai ga Momy ta iso tare da Nasir, ganin Momy ne yasa shi zama a kujerar dake gurin yana karfafa ma kansa guiwa, a gurin suma suka zauna ko wanne zuciyarsa cike da zullumi, suna haka har Mummy ta dawo, kusan set set biyar tazo dasu na kayan jarirai da duk wani abun da tasan za'a bukata, isowarta yayi dai dai ta fitowar nurse ɗin tace a bata kayan jarirai, Mummy na cikin gaisawa da Momy ta juyo, ta mika mata kayan, gurin karɓa ne ta kalli Saif tana murmushi tace "Matarka ta sauka ta haifa maka kyakkyawan kuma lafiyayyen jariri" "Alhamdulillah" Shine abunda ya furta ta rungume Nasir yana dariya, Mummy da Momy ma ko wanne fuskarsa ɗauki take da farinciki, suna yi ma Allah godiya, Bayan sun gama gyara jaririn suka fito dashi daga ɗakin, Momy da Nasir suka rika rigangan gurin karɓa, "Masha Allah" Nasir ya faɗa yana rumgumar jaririn a hannunsa, Momy ce ta biyu gurin karɓa bayan Nasir, sannan Mummy, Saif ne na karshe, ya rungume ɗansa kamar wanda za'a kwace ma wani irin daɗi yake ji a ransa kamar yanzu ne aka fara masa haihuwa, Kula ta musamman Kairat ta rika samu daga gurin Momy da Mummy, da kuma Hajiya Suwaiba, kwanan ta biyu a asibitin suka salameta bayan sun tabbatar da lafiyar ta da kuma ta jaririnta, Gidan Mummy aka dawo da ita, duk da Hajiya Suwaiba taso a barta ta koma gidan su amman Mummy ta ki yarda, babu irin kukan da lil Minal bata yi ba ganin Momie ta ta wani ɗan, hakan yasa kullum Saif yake zuwa ya ɗauke ta sai dare zai dawo da ita wani lokacin kuma a can take kwana tare da shi. Bayan kwana uku da da dawowar ta aka kawo kayan barka, da kayan kauri, babu abunda ba a saka ba tun daga kayan jarirai har na mai jegon, tun ana kirga kayan har aka gaji, dan kowa akwatunansa daban na mai jego daban na Jariri daban abun gwanin ban sha'awa, sai labarin ake. Ranar suna yaro ya ci sunan kakansa, MUHAMMAD BASHIR aka masa lakani da Aniq. An ci an sha, babu abunda ba a raba ba, Bayan sunan da sati biyar aka bikin Nasir da Lubna, daker Saif ya yarda Kairat taje bikin duk da tayi arba'in sai dai Mummy bata barta ta koma ba tasa ana mata shiri n musamman. anyi biki abunda ake kira biki, an zubar da kuɗi kamar ba gobe, Saif ya nuna ba jinta a gurin biki ta ko ina, yadda yake ɓarin kuɗi sai ka ɗauka bai san zafin neman su ba, ranar Asabar aka ɗaura, bayan anyi dina amarya ta tare dare da aka ɗaura auren. Sai da Mummy ta gama shirya Kairat sannan ta barta ta koma gidan mijinta, bayan an samo mai taya ta reno. Fasalin rayuwar Saif ta canja daga marar mata zuwa mai mata har da yaya biyu, an yanzu kan shi kansa yasan ya girma, ita kan ta Kairat ta canja a yanzu dan kallo ɗaya zaka mata ka gane matar aure ce, saboda yadda ta buɗe ta zama babbar mace, daman hausawa sunce haihuwa na buɗe mace. Rayuwar suke yi ta jindaɗi da kwanciyar hankali, rayuwar da ita ko shi ba su taɓa mafarkin shiga ba. A ɓangaren Mummy ma haka abun yake bata da wata matsala ko damuwa a yanzu, hankalin ta a kwance, Abbah yana kula da ita sosai musamman cikin nan da take ɗauke da shi ita kanta tana farinciki, sai dai wani gefen tana jin kunya wai zata yi haihuwar tsufa, hakan yasa ba kowa ne yasan tana da cikin ba Kairat ma ita kanta bata san tana da cikin ba, Allah ya taimake ta mace ce mai babban jiki hakan yasa ba a gane cikin dake jikinta, idan ba wanda ke kusa da ita kullum ba. Komai ka shuka shi zaka gurba, in ji hausawa, kuma ramen mugunta gina shi ɗan kaɗan ba kato ba, dan wata rana kai ne zaka faɗa, rayuwa ta zamo mata ta tsanani da wahala, saboda rashin ido komai sai dai ayi mata, tun tana mafarkin buɗewar idonta har ta daina tun tana dafe dafe har ta saba, abun da yafi damunta shine na rashin auren da bata yi ba, ta tsaya bata lokacin ta akan wanda ya zama silar makantarta kuma bukatar ta bata biya ba, ganin zaman baya mata a gidan Gwaggo yasa ta tattara ta dawo gurin Momy, dan tasan duk kular da Gwaggo zata bata ba zata kai ta Momy ba, daman tayi tayi ta dawo ita ce taki ganin yanzu babu sarki sai Allah yasa ta dawo gidan, hankalinta yakan tashi duk lokacin da Saif yazo gidan ko ya kawo iyalinsa, babu irin kuɗin da Momy bata kasa ba wajen ganin ta samo lafiyarta amman ya ci tura. Da gudu ta sauko downstairs kamar wata karamar yarinya, rike da waya a hannunta, ta zauna kusa da shi, "Yanzu Humaira ta kira ni... -" (Humaira matar da Deen ya aura kenan) Kamin ta karasa ya walkato ta ta dawo saman jikinsa ta kama karamin bakinta "Tace me?" "Ta haihu ta samu Ya mace" "Masha Allah Allah ya raya, yaushe?" "Wai yau kwana uku ranar Litinin za'ayi suna" "Toh Allah ya raya sai ki samu abunda zaki bata" "Ai dole zanje gobe nayi mata barka" "Yeah, cox jibi zanje wani business trip kuma kila dake zanje" "What?" Ta tashi zaune, "Wasa dai kake ko?" "Aa nima ɗazu Daddy yake sanar min, kuma yace yana da muhimmanci dole naje indai har an tabbatar da abun" "Gaskiya ni ba zani ba" Ta faɗa tana kukan shagwaɓa, "Saboda me?" "Yaushe muka dawo, ni gaskiya ba zan kara fita waje ba sai na yaye Aniq" Dariya yayi dariyar da sai da ta fitar da Beauty point ɗinsa "Amman yarinyar nan kin raina mutane, oh ke abarki kije kina yawo a gari kina matsu ko baki son shayarwa kar ace kin haihu" "Eh mana ai yana takura min kuma ni gaskiya, ina son naga bikin Anty Fareeda yau fa sauran sati biyu" "Whatever, ni dai ba zan je ni kaɗai ba tun da kinsan ba wata matar ni dani ba" Kuka tasa masa ya rungume ta yana murmushi, kamin ya ɗaga ta daga jikinta yana mata kiss "Bari ma naje gurin Daddy na kara tabbatar wa" "Allah yasa an fasa" "Ba Amin ba" Ya faɗa yana smirking. Da Sallama ya shigo parlour, Momy da Nasir suka amsa masa, "Ango ango ango kasha mai" Ya faɗa yana zaunawa saman kujera "Kai wane irin ango watan mu nawa da yin aure bana son shashancin fa" Dariya yayi "Au gaban uwata zaka kira ni shasha?" "Uwata dai kai kana da uwa ne" "Aa sama na faɗo" Dariya sukayi har Momy, "Auto naga uwata ce sai ka nemo wata uwar kuma" "Sarakuwar ka dai" "Aa ni ba wani sarakuta uwata ce kawai kaga tafiyata" Bai bari Saif ya kara cewa wani abun ba yayi ma Momy sallama ya wuce, suka bishi da kallo suna murmushi. "Ya gidan ya kowa da kowa?" "Lafiya kalau, tana gaishe ki" "Ina amsawa Abbah ka yayi maka maganar tafiyar ko?" "Eh daga gurin shi na fito yanzu yace min Saturday zan wuce ya za a shirya min komai" Kamin Momy tayi magana Lil Minal ta fito da gudu ta rumgume masa wuya, "Oyoyo Bah Babyn Mah" Hararar ta yayi yana satar kallon Momy, Momy kan ɗauke kai tayi ta mai da hankalinta gurin Tv, "Bah ina Momie Aniq" "Ke ba Momie ki ce ba" "A a tunda ta haifi Aniq ni ba Momie na bace" Momy ta juyo ta kalleta tana dariya "Ai na manta tace na zama Momy ta wai tunda taga bana da yara, wai Aniq ta bar masa wacan yayi ta kaya" "Har da Ni kin bar masa?" Saif ya tambaya, she's nodded her head "A a wallahi ai kai ba kai ka haife shi ba" Duk dariya sukayi, banda ita data yatsine fuska "Ina kika shafo wannan?" Yana taɓa ink ɗin take Hannunta "Ɗakin Anty Safiyyah" "Toh je kice ina gaishe ta" "Toh" Da gudu ta sauka ta nufi ɗakin, Momy ta kalleshi "Amman kan ba zaka faɗa mata tafiya zaka yi ba, dan zatayi kuka kuma kaga ba hutu suka. Samu ba balle kaje da ita" "Aa ba zata sani ba ma, ai kinga tafi son zama nan" "Eh tace fa ku ba iyayenta bane" Dariya yayi yana amsa kiran da aka masa a waya. **** **** **** Kamar yadda Daddy yace masa Ranar Saturday ya bar kasar zuwa Paris, duk yadda Kairat taso ya barta bai yarda ba a dole ta hakure suka tafi tare, tafiyarsu da wata daya Mummy ta haifi kyakkyawar yarta, aka rada mata suna AMINA sai dai Meena suka kiranta, babu yadda Kairat bata yi ba dan tazo bikin amman Saif ya tsaya kai da fata yaki yarda wai shi ba zata barshi can shi kaɗai ba, sa'arta ɗaya ya kusa kammala abunda yazo yi, bayan suna da sati biyu suka dawo, a gidan Mummy Kairat ta sauka, ta kama jaririyar ta rungume sai zumudi take kamar zata haɗe ta, kamar su ɗaya da Kairat sai dai fari na Mummy ne, Mummy kunya take ji sosai wai tayi haihuwar tsufa ita tana haihuwa Kairat. Na haihuwa, a boye take bata nono ko kuma ta saka hijab,sai dai a can kasan zuciyarta farinciki fal aciki dan gani take kamar Minal ce ta yi dawo. BAYAN WADANSU SHEKARU DANNA WANNAN TALLAR👇DON SAMUN CIGABA AKAN LOKACI Tsiren gudu suke, kowa so yake ya wuce ɗan'uwansa, daga karshe dai Aniq yayi nasara, aiko da gudu yayi gurin Safiyyah yana faɗin "Anty. Ni nayi na ɗaya" "Sai wa kuma yayi na biyu?" Safiyyah ta tambaya tana tataba kansa, "Ni nayi ta biyu" Lil Minal ta faɗa tana smirking, Dariya tayi, "Good ina Amir ta nawa yayi?" "Amir yayi na karshe" Sweets ɗin dake hannunta ta ɗauko ta tana mika musu, duk suka rungume ta suna dariya da yi mata godiya, kansu ta rika shafawa tana hawaye. Kairat dake tsaye a windo tayi murmushi tana rungume hannayenta, bata sarar ba taji an jama kumatu, tana juyowa ya ɗaga mata gira ya kashe mata ido, mur tasha "Zaka fara ko bafa gida muke ba" "Gida muke kan Da nan da can ai duk ɗaya ne" Ya faɗa yana kara motsowa kusa da ita, "Dan Allah ka daina kar fa Momy ta fito ta gan mu" "Toh idan ta gani fa Haramun nayi? Bari ma ki gani" Dukawa yayi ya ɗauke ta Cak, ita kuma ta shiga cuku cukun ganin ta bar jikinsa har suka faɗa saman kujera still bai sake ta ba, Yana kokarin kai hannu ya cire mata ɗankwali yaji alamar motsin fitowar Momy, ba shiri ya sake ta ta nufi kofar fita da sauri, ita kuma ta tashi zaune tana gyara jikinta da murmushi a fuskarta. ALHAMDULILLAH!!! Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki sarki mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kammala wannan littafin, oh Allah i hope for your mercy don't leave me for myself correct all my affairs for me,

0 Comments