ANYI WALKIYA CHAPTER 8

ANYI WALKIYA CHAPTER 8
Ta dauki kimanin minti goma cikin bayi Tana wanka sanan ta dauro alwala ta bude bayin ta fito Tana goge fuskarta Bata lura da ummu dake zaune gefen gado ba Saida ta juyo da nufin zuwa bakin gado ta dauki kayanta Sukai Ido hudu da ummu hannunta rike da turaren Tana jujjuyawa....ja da baya Fatima tayi hade da dafa kirji "ummu yaushe kika shigo?wallahi banji shigowarki ba"+ "In Banda abinki Fatima keda kike wanka ya zaayi kiji shigowata?bayan tahowarki sadik yasamun rigima shi indomie zaici to bansamu me kawoshiba shine nazo kawoshi nadade Ina sallama waje naji Shiru shine Dana turo kofar naji a bude,sai Kuma naji karar ruwa a bayi nasan wanka kikeyi".... Wucewa Fatima tayi wajen dressing mirrow ta dauki Mai Tana Shirin sharawa ummu ta watso Mata tambaya"Fatima me kikeyi da turaren Yan bori?turare Dan d'uri?" Da sauri Fatima ta juyo Tana kallon turaren hannun ummu,sai ta danyi murmushi tace "wayyoo ummu turarena ne na ajiyene idan na fito wanka Nasa Kaya in shafa" Takaicine ya lullube ummu tafara masifa Tana fadin "baki da hankali Amma,da ranki da lafiyarki Zaki shafa wanan turaren?Wanda idan kika shiga cikin jamaa na tabbatar da tushe hanci zaa rinkayi so kike ki janyowa kanki raini ma kenan cikin manyan mutane da ya'yan attajirai,to ki rufamin asiri ki rufawa kanki kar in kuskura inji kina kamshin wanan turaren Domin ni Zaki zubarwa da mutunci,ai kin wuce wanan lokacin Kuma Fatima,yanzun ke Yar gatace Yar ummu da abbah ko"...ta karashe maganar da sanyin murya yadda taga jikin Fatima na rawa, Gyada Mata Kai Fatima tayi baki na rawa tace "insha Allah bazan shafaba ummu dama banida turarene" Murmushi ummu ta sauke "nasani ai naji dazun kamshin turarena kikeyi koh?meyasa yanzun baki daukoshi kin Kara shafawa ba ai na mamanki ne koh" Ta sunkuyar da kanta kasa "toh ummu" "Kokefa yanzun gobe da wuri zansa akaiki kiyi siyayya hardasu turarruka da gyaluluwa da takalma da jakunkuna ko Yar ummu " Dadi ne ya Kama Fatima Wanda har saida murmushi ya subuce Mata sanan ta rufe fuskarta Tana dariya,itama ummun dariya ta shigayi Tana fadin "ja'irar yarinya Zaki sa magauta suyi Mana kallon banza" Itadai Fatima murmushi kawai take ta cigaba da shafa manta sannan ta dauki kayanta ta sanya, ta shimfida daddumarta ta tada sallahrta,bayan ta idar ne ta nade daddumar ta nufi kitchen sadik ya rufa Mata baya yayinda ummu ta Dan kishingida bacci ya dauketa.... ******** Sashen hajiya karama ya sake shiga Yana dube dube ko zai ganta Amma be ganta ba ya dade ciki a zaune har kanwar hajiya ta gaji ta tambayeshi wa yake nema?ko Yana bukatar wani abune Shafa keyarsa yayi sanan yace "dama ummu nake nema kuma bangantaba"....Nan ne ake sanar Masa da ta tafi gida, Yana fitowa sauri sauri ya nufi sashen ummu yayinda rahane ta ruga aguje ta sanarwa da deejahmah taga yarima yayi sashen hajiya zainab da alama wajen Fatima zaije....hankalinta ba karamin tashi yayi ba tunanin yadda zaayi taje taga me sukeyi takeyi..... Shikuwa yarima ya Dade tsaye Yana bugun kofa sanan sadik yazo ya bude Masa ya dauki sadik ya dagasa sama Yana fadin "oga sadik Kaine da bude kofa?rigima babu ko?"...ya karasa shigowa dakin Yana kalle kalle sanan ya dubi sadik yace "Ina ummu ne?" "Tana dakin anty Fatima Tana bacci"... "Owk Ina antyn naka?" "Kitchen ta shiga Tana dafamin abinci".... STORY CONTINUES BELOW Jimm kadan yarima yayi sanan ya radawa sadik daidai kunnensa "jeka ce Ina kiranta"... Da gudu sadik ya shiga kitchen din Yana fadin "anty kizo inji uncle yarima"....gabanta ne ya yanke ya fadi,Jin abinda sadik yace,da kyar ta daure ta dubi yaron tace"tsaya ka tafi da abincinka idan kaje kace Ina zuwa"...ta karasa barewa sadik kwai tasa Masa a gefenn indomie dinsa ya fice parlorn, Saida ta Gama dauraye tukunyar da tayi amfani sanan ta fito fuskarta daure ta karaso gefen kujerar da yake zaune tadan zaune jikin kujerar,....shi kuwa yarima tunda ta zauna gefensa ya nemi natsuwarsa ya rasa,kasa jurewa yayi ganin batace masa komiba tsawon minti uku yadanyi gyaran murya yace "ranki ya dade dik fushin ne?menayi Miki kikeson yimun horo?" Dage kafadarta tayi tai Farr da idanuwanta sanan ta Dan dubesa ta kauda Kai ta turo baki gaba tace "oho Nima bansaniba" Murmushi yayi "sarautar Taki ta motsa kenan?shiyasa kike wani ciccin magani kina shamun kamshi" "Wayasani"shine amsar data bashi, Hannunta ya janyo ta fuzge hade da cewa "kaje wajen wadda kace kanada ita Mana?ai tanada hannu sai ka taba"ta murguda Masa baki Mikewa tsaye yayi ya damki hannunta da kyau ta saki Yar Kara Tana kici kicin kwacewa cikin Jin zafin rukon da yayi Mata tace 'ni ka sakeni?da zafi Allah hannuna zai karye'...kwalla ta ciko a idanuwanta yasa hannunsa daya ya dago habar ta Yana karewa fuskarta kallo sai ga hawaye sharrr sharrr Yana gangarowa a idanuwanta....sassauta rukon yayi ya matso da fuskarsa daff da Tata "kishi bintu?kishi be kamaceki ba Domin ke ya kamata ayi kishinki ba wata ba haba fatyna"...hawaye kawai ke zuba a idanuwanta Wanda batasan dalilinsuba, Hannu yasa Yana sharewa wasu na zubowa a idanuwanta ya matseta a jikin bango hade da shafa kanta Yana fadin "is ok banason kukan kinji?nayi laifi bazan sake cewa zanje wajen wata ba insha allahu" Dago idanuwanta tayi ta sauke Akan fuskarsa da sauri ya shiga girgiza Kai "ya Isa banason kukan kinji?" Kara shagwabe Masa tayi ta Dora kanta a kirjinsa cikin sigar shagwaba take fadin "Nima bansan dalilin da yasa naji wanan yanayin ba,kawai dai nasa tun daga ranan da kacemun kanada wata zuciyata tafara waswasin watarana zaka iya juyamin baya,Dan kawai nayi maka wasa sai kacemun kanada wata ni banaso kabari"...hannunsa yasa Yana shafa gefen fuskarta cikin sigar lallashi "ya Isa nadaina ai Nima wasa nayi Miki koh?"..... Turo kofar yasashi saurin juyawa kawai yayi Ido hudu da tawagar kawayenta deejahmah ciki kuwa hadda ita ko wacce da Jakar kayanta a hannunta, Shigowa parlorn sukayi da sallamarsu a bakunansu da sauri Fatima tasa hannu ta goggoge kwallar dake makale a idonta ta shiga faraar Dole "barkanku da zuwa,kune da laasar din Nan" Kallo kawai suke binsu dashi Dan ko wacce fuskarta dauke da mamaki,...dakyar Sunita taja numfashi cikin inda inda tace"ehh mune wallahi baki sunyi yawa can shine mukace Bari muzo Nan dik muyi wanka mu shirya a Nan idan lokacin dinner yayi ko?" Murmushi Fatima ta sauke tadan bugi yarima dake tsaye kamar statue "yaayah kaje zan kawo maka abincin,me kakeson ci ne?"ta kifta Masa Ido, "Nima naji shaawaer indomie din sadik Amma ni ki soyamun kwai" "Angama ranka ya dade,ango kasha kamshi"...hannunsa yasa yaja hancinta "sai kinsha duka" Ta Dan turo baki gaba ta juya yabi bayanta da kallo,sanan ya fakaici kallon side din deejahmah yaga ta kauda kanta tamkar batasan Yana Nan ba.... Juyawa tayi daki ta tashi ummu ganin lokacin laasar yayi Dan tayi sallah,bayan ummu ta tashi ne Fatima ke sanar Mata da tanada baki.... A parlor tagansu zazzaune Tasha mamaki Dan Bata taba tunanin deejahmah zata tako kafarta gidanta ba kila dai akwai wani dalili,.. STORY CONTINUES BELOW Dan fad'ada faraarta ummu tayi tace "ah ah lallai gidana yayi albarka Yan matan amarya ne da amaryar kanta?to sannunku da hutawa" Suka hade baki suka gaidata ummu ta amsa cike da kulawa ta shige dakinta.... Tunda suka shigo Fatima ke kaiwa da komowa a kitchen Tana hidimar abinci, Fitowarta daga kitchen yayi daidai da Jan tsaki da deejahmah tayi tana fadin "ayi dai mugani idan tusa zata Hura wuta,ai mun rigada munsan komi munsan cewa karuwa ce".... Cakkk Fatima ta tsaya zuciyarta nayi Mata zafi Amma saita danne ta danyi yake hade da juyowa Tana fadin "ai karuwanci ma sai a gidan yaayah wayyoo masoyi"....tace Tana murmushi ta shige, Babu Wanda ya fahimci abinda Fatima ke nufi sai khausar da deejahmah wadanda sunsan komi su Yan matan amarya da ka kawai suke zaune, Shigowa faizah tayi baki dauke da sallama itada Yar uwarta hannunsu rike da jaka cikin faraa faizah tace"munje can akace Kuna Nan Ashe Nan kukayo Ina ummun?" Khausar ce tayiwa faizah nuni da Tana daki ta dire Jakarta ta shige dakin da sallamarta suka gaisa da ummu,bayan ta fito ne sukai Ido hudu da Fatima ta fito kitchen take suka sakarwa juna murmushi, Kallon mamakin ganin Fatima cikin wanan yanayin faizah takeyi Dan rabonta da ita tun ranan da suka gaisa da yarima, Karasawa tayi ta mikawa Fatima hannu suka gaisa suka shige kitchen din tare,kasa boye farin cikinta faizah tayi tace"kaiii k'awata haka kika koma?nayi matukar farin cikin samun yancinki Allah ubangiji ya Kara Haske a lamarinki" Farr da Ido Fatima tayi tace "bayan tun bayan rabuwarmu ranan biki bansake jinki ba" Murmushi faizah tayi Dan tasan ba itabace fauziyya ce kila fatimar Bata ganesuba ta bude baki da niyyar cewa ai ba ita bace aka kwalawa Fatima Kira ummu ce daga daki, Da sauri Fatima taje"yarima yace ki Kai mishi abinda yasaki"... Bata fuska tayi tace"ummu wlhy Yaya takuramun zaiyi nagama nasa a bascket Wai da bakin Nan nake nemawa abinda zasuci" "Kin iya wahala bintu keda zaakawo musu daga cikin gida kin Kama kin dora girki?,yanzun ba wanan ba waye zai kaiwa yarima abincin kike nufi" Jimm kadan tayi sanan tace"akwai Rahane" "Owk" Ta juya ta fita ta shiga kitchen da sauri Jim kadan ta shigo parlorn tsaye tayi Tana karewa kowa kallo sanan ta nuna Rahane da Mami tace cikin Isa "cikinku waye zai kaiwa ranka ya dade abinci?Domin ni naso in ciyar shi saidai hakan be samuba Dan inaso in karrama baki"... Dibbb parlorn yayi tamkar Babu kowa, Ta Kara nunasu da yatsa "ba saina maimaita kalamaina ba kunji abinda nace" Dan durkusawa Mami tayi tana jinjina Kai "munji ranki ya dade" "Shawara ya rage gareku nida bukatata a cika umarnina"...ta dire basket din a wajen, Ta juya abinta suka bita da kallon mamaki da al'ajabi,juyowa Fatima tayi tana jifansu da mugun kallo "inhar bakuje Kun cika umarnina ba to aikinku ya Kare" Da sauri Mami ta sunkuci basket har tana tuntube Rahane tabi bayanta a sukwane, "Dakata,ke haka zakije hannu Babu komi?tsaya inbaki ruwan zafinsa dan nasan Yana bukatarsa"....ta juya cike da yanga duka Ido yayi kanta har kitchen din haka ta dawo ta mikawa Rahane flask Tana binta da kallon raini da wulakanci, Babu wani musu ta amsa ta juya Tana kallon uwargijiyata,Tana Jin tsoron abinda zai biyo baya.... Jinjina Kai kawai fauziyya takeyi a ranta Tana fadin "zakici ubanki lallai kinsamu waje,a zahiri kuwa ajiyar zuciya ta sauke kawai.... STORY CONTINUES BELOW Wayar khausar ce tayi Kara da sauri ta dauka ta Kara a kunnenta "ki tabbatar deejahmah ta shafa abinda na Bata a jikinta da tafin hannunta ki fada Mata sakona"hajiya rahina ke magana ta can bangaren, Kada Kai khausar keyi kamar Tana ganinta hade da cewa "toh in Sha Allah"ta kashe wayar Kasa tai da murya daidai kunnen deejahmah ta kitsa Mata sakon da aka Bata,tsabar takaici ya hanata amsawa da baki Kai kawai ta dagawa khausar din.... ******* Saida akayi magriba sanan ake haramar tafiya wajen dinner inda Mai kwalliya yauma tazo ta tsantsarawa amarya kwalliya a fuskarta tayi balain kyau tamkar ba itaba kamar wata sarauniyar kyau,haka Yan matan amarya ma ko wacce aka bita da kwalliya tayi musu casual ciki kuwa harda Fatima wadda tunda akafara daga girarta fuskarta tafara canja kala ko kafin agama Mata kyawun da tayi baya misaltuwa su kansu Yan matan amaryan Babu wadda Bata Yaba da kyawu irin na Fatima ba musamman da aka canja Mata halitta da kwalliya.... Ankonta dama afnan ta hada ta amso musu tare,tasa doguwar rigar fited gown na less seagreen Wanda shine ankon wajen dinner din tayi masifar kyau ya amshi fatar jikinta, Ita kanta deejahmah Saida ta daga Ido ta kalli Fatima data gifta ta gabanta hassada da bakin ciki hade da kishi suka tarun Mata a zuciya Wanda Taji tamkar ta shake Fatima ta huta, Deejahmah Bata manta da sakon mahaifiyarta ba tayi yadda akace,sai wani kamshi takeyi na musamman Domin Babu karya Tasha gyara..... Faizah kuwa dik inda Fatima tayi suna tare sai hotuna sukeyi a wayar faizar saboda yadda Fatima tayi Mata kyau, Yan matan amarya aka fara kwashewa zuwa wajen dinner inda abokanan ango gigaggun Yan boko kowa yazo da motarsa ta wanan Tana wane wanan,....tunda Fatima ta fito hannunta cikin na faizah su deejahmah na biye a bayansu da kawarta kwaya daya wadda ta rukota suka fito tare,kallo ya koma Kan Fatima dik wani Wanda yayi tozali da Fatima sai yace Masha Allah, Sai kuss kuss abokanan ango keyi yayinda yarima ya kafeta da idanuwa yaji kishi na taso Masa ganin idon kowa a wajen na kanta,...dakyar ya hadiyi mugun miyau ya radawa Ahmad a kunne "ga bintu can ta fito ka tabbatar Kai ka dauketa sanan karka Bari kowa ya rabeta....dik Wanda ka gani kusa da ita kafada Masa matar aurece"....dariya Ahmad ya hauyi Yana fadin "Kai abokina ga amaryarka Amma ta Fatima kakeyi?kasan Allah banganetaba gara da ka fadamun Dan Nima ita nake kallo" Wani mugun takaicine ya Kara lullube yarima ya bugi kafadar Ahmad.... Koda suka karaso Ahmad ya tarbesu ya nuna musu motarsa yace su shiga Nan ba musu Fatima ta shige fuskarta dauke da faraa... Motar wani abokinsu Nan aka tanadarwa amarya da ango suka shiga suka zauna....take kamshin turaren deejahmah ya daki hancin yarima.....yaji wani Abu nayi Masa yawo a cikin jikinsa,Wanda ya haifar Masa da tsantsar shaawarta cikin seconds wadanda basu wuce talatin ba.....hakan ne yasashi juyowa yadan kalleta,ya kauda kansa,din Tana lura dashi...Kara gyara hancinsa yayi ya Kara shakar kamshin turaren Wanda take network din jikinsa ya fara canjawa idanuwansa suka kankance....ya shiga Dan mutsu mutsu da jikinsa a haka suke tafe a motar Amma samm hankalinsa baya jikinsa wata matsananciyar shaaawace take fuzgarsa.... Ko kafin su karasa hall din idanuwansa sun Gama kankancewa haka suka Isa wajen,Wanda suka fito tare ya riko hannunta Dan shiga hall din,dakyar yake taka kafarsa savida yanayin da take ciki,ganin ya ruko hannunta yasa deejahmah yin Dan murmushi a haka suka shiga jamaa sukai caaa suna kashe musu hoto ta ko Ina,abokanan ango suka shiga barin naira na liki har wajen zamansu.... Fatima na zaune gefen faizah Taki an dafa kafadarta ta baya da sauri ta juya wacce ta gani ce yasata saurin mikewa ta rungumeta Tana fadin "ablahhhhh wayyoo Dadi kece" Bakin barrister hauwa yaki rufuwa Tasha leshinta me shegen tsada cikin tsananin farin ciki tace "Fatima kece haka?lallai nayi farin gani alhamdulillah"... Dakyar Fatima ta saketa ta juya ga Ashmah dake tsaye tana murmushi "Aysha Ashe zamu sake haduwa?"..suka rungume juna cike da farin ciki suka zauna table daya da Ablah wadda mamakin ganin Fatima a wanan yanayin ya cikata.... Yarima Yana high table Amma hankalinsa na wajen fatimarsa dikda mawuyacin halin daya tsinci kansa be hanasa kafeta da wani irin kallo ba Yana kallon yadda take faraa da jamaa zuciyarsa nayi Masa tsananin lugude.... Dinner sosai ake gudanarwa inda aka umarci amarya da ango da su sauko Dan nuna farin cikinsu deejahmah na gaba Yana biye da ita idanuwansa suka sauka akanta abinda yakeji ya sake karuwa a jikinsa fiye da dazun,Koda yazo daidai ita besan lokacinda ya rike kugunta ba suna rawa a haka a hankali Mai ban shaawa nanfa jamaa sukai caaa wajenyi musu liki,idanuwan Fatima kyarrr akan hannun yarima dake sagale da deejahmah....dakyar ta sauke numfashi ta Mike cike da yanga ta karasa daf dasu ta bude Yar pos dinta da ummu ta Bata da canjin Yan hamsin hamsin ciki, ta shiga yi musu liki, hajiya babba na gefe tanayi musu, batare da ta lura da Fatima dake gefenta ba,....kallonsa takeyi Ido cikin ido shima idonsa Yana kanta ya sakar Mata da lallausan murmushi,kasa mayar Masa tayi saboda abinda takeji cikin kirjinta.....daga inda yake Yana iya hango Yar kwallar data taru cikin idanuwanta...a haka takeyi musu liki Tana kallonsa Yana kallonta,ganin haka yasa deejahmah babu kunya ta kwantar da kanta gefen kafadarsa.... Saida kudinta ya Kare ,ta juya Tana taku daidai cike da yanga da izzah Wanda Saida ta dauke hankalin daukakin jamaar dake fuskantar wajen,....maimakon ta koma table dinta sai tayi hanyar fita hall din,a idon yarima,Wanda tunda ta juya yabita da kallo zuciyarsa tayi Masa nauyin gaske, gabansa ya shiga tsananin faduwa hade da firgici lokaci daya ya furta a zuciyarsa....."Ina Fatima zataje?"abinda ya tambayi kansa kenan..ya kasayin wani yunkuri sai dai gabaki daya ya rasa yanayin da ya tsinci kansa...Dan ba karamin furgici ya shigaba, Hankalinsa baya jikinsa deejahmah na lura da yanayinsa Amma sai ta share,... Ganin Fatima tayi wajen hall din yasa Ahmad dake gefensu Yana kallon dik abinda ya faru,yayi saurin juyawa ga abokinsa ya Mika Masa drink din dake hannunsa yabi bayanta.... Murmushin mugunta deejahmah tayi a fakaice hade da lumshe idanuwa ta budesu....wani farin ciki ke ratsata Domin tunawa da tayi da plan dinsu na gaba..... Hanyar fita gate Ahmad yaga tayi da azama ya daga muryarsa yace "Fatima"....cakkkk ta tsaya hawaye na gudu a fuskarta wadanda ita kanta batasan dalilinsu ba a haka Ahmad ya taddata tsaye ko motsin kirki batayi sai hawaye dake gudu a fuskarta,+ "Meya faru kika fito Nan Ina zakije?Kuma?sokikeyi wani Abu ya sameki?"....dakyar ya karasa zancensa da yayi tozali da fuskarta wadda ta jike da hawayen bakin ciki, Shiru yayi hade da zura hannunsa cikin aljihun wandonsa batare da yace kokiba, Hajiya zainab ce ta fito daga hall din kunnenta manne da wayarta da alama waya takeyi Tana fadin "idan Kun shigo kuyo hannun damanku zakuga hall din akwai motoci wajen Ina kofar gate"...kamar a mafarki take ganin fatyma tsaye da wani tun daga Dan nesa dasu ta Gane itan ce harta karaso wajen Tana Taku daidai takalminta Yana Kara kwass kwass Wanda shine ya dauki hankalin Fatima ta juya da sauri Dan ganin waye,Aiko idanta ya hadu Dana ummu a guje ta fada jikinta ta fashe da kuka Tana fadin "muje ummu ni banason zaman wajen Nan tafiya zanyi"cikin kuka take maganar harda shassheka,...ba karamin tashin hankali ummu ta shiga saboda irin kukan da taga fatyma Tana rusawa ta Kara rungumeta Tana fadin "me akayi Miki wanene?fadamun ko waye shi sai na tabbatar ya zubar da hawaye kamar yadda kika zubar"....kuka kawai takeyi Tana Kara kankame hajiya zainab,.. Juyowa ummu tayi tanayiwa Ahmad kallon tambaya,da kyar ya sauke numfashi yace "ummu wallahi bansan meya faru ba kawai dai Naga Fatima ta fito hall a yanayin yadda ta fito nasan akwai wani Abu shine kika biyomu Kuma ni Bata ma yimun magana ba" Ajiyar zuciya ummu ta sauke daidai Nan babbar kawarta ta shigo da motarta,wajen da sauri ummu taja Fatima a hankali har sunfara tafiya ta juyo ta kalli Ahmad "jeka kawai Bari muje gida"... Wajen motar kawar Tata suka karasa daidai Nan ta sauke glass din motar Tasha kwalliya itada yaranta Yan Mata guda biyu cikin faraa tace "ranki ya dade muje ciki koh".. "Ah ah muje gida kawai ku saukeni yata Babu lafiya".... Dan leko da kanta tayi Tana kallon Fatima wadda ke faman shasshekar kuka kafin daga bisani ta budewa ummu kofar mota suka shige taja motar zuwa gida..... ********* Akan idon yarima Ahmad ya shigo cikin hall din shi kadai ba tare da Fatima ba wani irin kugi cikin yarima yayi lokaci daya fargaba da tsoro ya darsu cikin zuciyarsa.... Wasu irin yayan zufa ne Suka shiga karyo Masa ta ko Ina dikda sanyin ac dake cikin hall din saboda tsabar haduwarsa ta cikin dummm light din inda suke zaune kallo daya zakayiwa yarima kasan Yana cikin rudani,minti minti yake share zufar dake tsattsafowa a fuskarsa, Dan kallonsa deejahmah tayi hade da Dan darkewa a jikinsa Tana kallonsa cike da kissa tace"lafiya dai ranka ya dade?meke faruwa?Naga yanayinka tamkar kana cikin damuwa menene fadamin"...yadda tayi maganar kadai yasa jikinsa mutuwa take ya Kara nutsa cikin tsantsar shaawarta har baisan lokacinda yasa hannu yadan shafi gefen fuskarta ba take waje yadau sowa hasken camera kawai ke giftawa a wajen, Bakin hajiya rahina yaki rufuwa saboda Dadi Dan waigawa tayi gefen hajiya babba ta rada mata a kunne"turaren baba Sudan yayi aiki dan banza Kinga yadda yake lumshe Ido?" STORY CONTINUES BELOW Girgiza Kai kawai hajiya babba tayi ta sauke murmushi cike da kasa tace"fada da aljani Babu Dadi rahina munyi da manyanshi balleshi karamin alhaki?hmmm hmm kadan kenan sai ya kusanceta yaji yadda take sanan idan har Tasha ruwan dadin Nan na baba Sudan angama sanan sauran hade haden a can zaiyi a binsa to daganan labari zai canja Domin shida wata mace harabada Kuma balle tsintacciyar mage shigiya Yar gaba da Fatima" Wani irin dariya hajiya rahina takeyi Tana jinjina Kai cike da nishadi "Kinga idan ta mallakeshi shikenan sai muga ta tsiya,sanan burina be wuce ta haifawa sarki magaji ba kafin ta sheka Dan banza lahira" Jinjina Kai hajiya babba tayi ta Kara kasa da kanta kadan "yadda Dana ya bakunci lahira wallahi sai kabiru ya bakunci lahira,....kisa Mai sauki deejahmah zatayi mishi Wanda harabada Babu Wanda zaisan cewa itace ta kasheshi" Dan murmushi kawai hajiya rahina tayi tana jinjina Kai Tana ayyana abubuwa da dama cikin ranta".... Dik wata natsuwa yarima baya cikinta ya rasa abinda keyi mishi Dadi Allah Allah kawai yakeyi a tashi a wajen party din .... ******** Kuka sosai Fatima keyi Tana mayarwa hajiya zainab abinda ke faruwa ta karashe maganar da fadin"na hakura da aurensa inhar hKan shi zai samamin farin ciki Domin a bisa alamu sun nuna Yana aurenta zai manta da alkawarina ,zai manta da wata Fatima marainiya wadda yayiwa alkawarin kasancewa da ita har karshen rayuwarta,gara in hakura ummu tunda ni banida sauran gata"ta karashe maganar hawaye na gudu a fuskarta "Babu ranan da zan huta kenan?tunda nataso nake cikin wahala har yanzun Ina cikin azaba daga wanan sai wanan shi kuma Wanda nakeso ya fara canjamun"ta rushe da kuka Mai ban tausayi... Ita kanta hajiya zainab Saida kwalla ta tarun Mata a idanuwa,Fatima na tsananin Bata tausayi,kalamanta suna caja Mata kwakwalwa Saidai dik ba wani Abu ya kawo hakan ba harda kishi data fahimci Yar tanadashi... Janyo Fatima tayi jikinta ta rungumeta ta shiga share Mata hawaye "kiyi Shiru ki kwantar da hankalinki kinji?Allah gatanki nice gatanki ko kabiru zai juya Miki baya ni bazan juya Miki ba kinji yarinyana?" Dago Kai tayi idanuwanta na zubda hawaye hajiya zainab tasa hannu ta share Mata hawaye zuciyarta tayi rauni gabaki daya dakyar ta bude baki tace "kiyi Shiru kidaina kuka Babu Wanda ya Isa ya rabaki da Kabir yadda Allah ya hadaku,idan sunsan wata basusan wata ba kinji ni zanyi musu abinda zan shayar dasu mamaki zan tabbatar musu da din sammakonsu wani a hanya ya kwana ki kwantar da hankalinki zan kwatar Miki yancinki sanan kema zanbaki damar da Zaki kwaci yancinki da hannunki dik abinda sukai Miki zan wargaza shirinsu a Daren yau zuwa gobe..... Kallon mamaki kawai Fatima take bin ummu dashi Tana tunanin yadda zaayi ta wargaza musu shirinsu bayan alamu sun nuna wasu abubuwan da yarima yakeyi yau kadai tamkar Mara hankali Wanda yasha wani Abu ya nuna an rigada an asirceshi....tayaya ummu zata warware asiri cikin awanni bayan washe gari da safe karfe Tara na safe sunan yarima ango?...wasu zafafan hawayene suka shiga gudu a idanuwanta tausayin kanta ya lullubeta,....ga wani irin soyayyarsa dake dawainiya da ita dik bugun da zuciyarta zatayi hade da numfashinta sonsa karuwa yakeyi cikin zuciyara.....ajiyar zuciya ta sauke yayinda hajiya zainab ta kafeta da idanuwa,tausayin yarinyar na Kara ratsa sassan jikinta jinta dafa ta tayi taji jikinta yayi zafi rau alamar zazzabi nason kamata "Fatima tashi kicire kayan jikinki ki wanke fuskarki kizo kiyi sallah kinji tunda baayi ishai ba muka tafi nasan bakiyiba,koh?" Jinjina mata Kai Fatima tayi sanan ta zare jikinta daga rukon da hajiya zainab tayi Mata ta Mike jiki Babu kwari ta nufi toilet ummu girgiza Kai kawai takeyi hade da tausayin karamar yarinya kamar Fatima wadda take fuskantar kaddarori kala kala.... Mikewa hajiya zainab tayi ganin Fatima ta shiga bayi yasa ta tuna da bakinta dake parlor da sauri ta Mike Tana fadin "asha assha hajiya nabarku a parlor nazo lallashin diyata ne".. STORY CONTINUES BELOW Dariya kawar ummu kawai tayi tace "Babu damuwa hajiya aini ba bakuwa bace" Kallon abincin da aka ajiye musu hajiya zainab tayi "bakuci abincinba hajiya" "Wallahi munkoshi sallah zamuyi ma mutafi...." "To ku shiga wancan dakin akwai toilet sai kuyi alwalar,wallahi hankalina dik ba kwance yakeba an kunnowa Yar autata wuta ga autar tawa da shegen rigima" ********* Wajen karfe Tara su hajiya babba suka shigo gida hayaniya ta kacame cikin harabar gidan inda Yan matan amarya keta fitowa daga cikin mota suna yo hanyar gidan hajiya zainab inda suka ajiye kayansu, Ganin haka yasa Fatima saurin gyara fuskarta dikda kumburin da idanuwanta sukayi, Bubbuga kofa Suka shigayi,da sauri ta sakko daga Kan gadon lokacin ummu tabi kawarta tayi Mata rakiya ta fito ta bude musu kofa, Suka shigayi shisshigowa ciki,faizah ta dubi Fatima tace"malama saiki tafi Babu ko sallama?ganin fitarki kawai mukayi" Karbe zancen teemah dollar tayi da fadin "ai maki gani ya kauda idanuwansa Domin irin soyayyar da deejah suka nunawa duniya yau Dole dik wani makiyinsu yabar wajen Wanda bazai iya ganiba" "Ahayyeeeee yau munga soyaya har wani narkewa deejah take a jikin yarima gaskiya sun Dace sosai'cewar Sunita Tana wurgawa Fatima harara, Sororo Fatima tayi tsaye tana kallo da sauraren ikon Allah yadda suke zubo zance tamkar suna jiranta,zuciyarta babu Dadi Amma haka ta daure ta cije tace "ai soyayyar gaskiya itace soyayyar da ake kebewa anayinta ba don ganin idon mutaneba Dan su tafi da abin a baki suna Fadi yazama son asani kenan Domin ko ibadar Allah ce kayita don ganin idon mutane inda kayita anan zaka barta,saboda haka tafiyata tanada nasaba da kishina da mijina yakeyi gudun kada wani ya kulani kafin ya mallakeni in mallakesa a matsayin maaurata" "A mafarki Zaki mallakeshi Fatima Domin Dan asali sai Yar asali ba tsintacciya Yar kwararo Yar rukon gwamnati ba tsohuwar Yar taada wacce tayi kwana da kwanaki a kurkuku"cewar deejahmah Tana murmushi, Takaicine ya rufe Fatima Wanda take taji jiri na Shirin dibarta saboda cin mutuncin da deejahmah tayi Mata cikin mutane,Koda yake ba laifinta bane dama yarima munafuntarta yakeyi Yana xagayawa suna soyayyarsu tunda ya kasa controlling kansa cikin mutane....hawayene ya taru a Ramin idanuwanta Amma saita daure ta juya batare da tace komiba har ta shiga daki abun ya ciyoya ta fito fuskarta Babu walwala lokacin suna zazzaune suna kallo,har gefen deejahmah Fatima ta karasa ta zauna gefen kujera ta watsa Mata manya manyan jajayen idonta Wanda Saida gaban deejahmah ya fadi ta dago Kai Tana binta da kallo,daf da fuskarta Fatima tasa fuskarta ta Soma magana, "Ki tabbatar da dik ranan da aka dauramin aure da Kabir kashinki ya bushe da dik wani Wanda ya goya Miki baya kikeyi dik ku shirya ku daura dammarar fada Dani Domin kubar ganina haka abinda na kudura a Raina sai ya Dade Yana baku mamaki nidake sai min Zama tamkar damusa da ya'yan kura, ki kiyayi gamona dake Domin Yar karuwa saitayi Miki abinda baki taba tunani ba saina tabbatar Miki da tabbas ni Yar kwararoce a Nan ne zaa banbace mowa da Bora a wajen miji" Kallo kawai sukebin Fatima dashi kowa fuskarsa shaye da mamaki,...dagowa deejahmah tayi tadanyi murmushin karfin Hali "idan nabaki damar shiga gidana kenan dik kike wanan furucin" Mikewa Fatima tayi tana Taku daidai dik suka bita da Ido kamar wata tv gashin ganta na Lilo a bayanta yadda tayi parking dinsa da ribom... Tayi hanyar dakinta aka turo kofa bilkisu ce tayi satar hanya ganinsu deejahmah yasata tayi turus zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ta zube a gaban Fatima Tana fadin "afuwan ranki ya dade kiranki ya iso gareni bansamu damar zuwa bane Saida na karasa aikin da nakewa hajiya a cikin gida" STORY CONTINUES BELOW Kauda Kai Fatima tayi tamkar bazatace wani Abu ba dakyar ta bude baki tace"keta shafa Amma kisani bazaki bar gidan Nam ba sai kin karasa mun dik aikin da nake Shirin saki Dan Banga dalilin da zaisa nakiraki tun Rana kimun aiki kiki zuwa ba ,ki shiga kitchen akwai wanke wanke kiyi kafin inzo" Da sauri bilkisu ta Kara rusunawa "angama ranki ya dade na tuba".... Kallon takaici khausar kebin bilkisu dashi sanan ta taba deejahmah tace"Wai saboda tsabar raini irin na wanan shegiyar Wai har baiwar hajiyarmu take Kira tasata aiki tasamu wajene" Yunkurawa deejahmah tayi "kutashi muje bazan iya cigaba da ganin kayan takaici ba" Dukkansu suka Mike suka shiga fita daga gidan Fatima dake daki wajen goma saura tanajin sahun fitarsu ta fito da sauri ta kalli kofar dakin da suka Bari a bude ta rufe ta dawo tayi kitchen, A tsaye ta samu bilkisu kawai saita fashe da kuka ta rungumeta "Yar uwata Ina cikin matsala Domin kabir ya juyamin baya bakiga abubuwan da yakeyiba jiya har cemin yakeyi Wai dadin abun yanada wata"kuka sosai Fatima keyi a jikin bilkisu wadda itama hawayen ne ya wanke Mata fuska da kyar ta lallashi Fatima suka dawo parlor kasan carpet suka zube... Ruke da hannun juna suke bilkisu ta Kare matse hannun Fatima tace "ki kwantar da hankalinki na Dan lokaci ne Amma maganar gaskiya kece a zuciyarsa shi kawai sunyi hatsabibancine sun janyo raayinsa ki Mike da addua kinji?" Share hawaye Fatima tayi ta Kara duban bilkisu da kyau "karyane wallahi dama can Yana sonta munafurcine irin na da namiji Kuma zan bashi mamaki Domin zansamu miji inyi aure in shareshi Dan bazan yarda a nakasani ba shida yaji zai iya yaje can su daddatsa namansa" "Idan kikace haka kinyiwa Allah butulci kinyiwa yarima butulci Domin Babu Wanda zaiyi jihadi irin yadda yayi akanki,karki manta irin wahalar da yayi akanki yakici yaki Sha ya rabu da kowa ciki kuwa harda iyayensa,haba Fatima kiyi Masa uzuri baya cikin hayyacinsa" Take jikin Fatima yayi sanyi Amma can kasan zuciyarta tanajin haushi da takaicinsa ga wutar sonsa dake ruruwa a zuciyarta,.. "Ni Bari ummu ta dawo ma infada Mata ta nemi makaranta tasani kawai Kuma ni bazan sake bin ta kansa ba Dan nasan ba lallai ma ya Kara nemana ba' Murmushi kawai bilkisu takeyi Tana kallon yadda Fatima ke jaraba saboda tsabar kishi.... Dakyar bilkisu ta lallasheta da kalamai masu dadi A haka suka shiga Hira can ta daban... ***** "Wai hajiya Kinga yadda yarinyar Nan ke zuba mulki daga samun yancinta har ruwan iskanci takeyi Wai harda Kiran bilki baiwarki tasata aiki ?bakiga yadda bilki jikinta ke rawaba saboda tsabar tsoronta da takeji" "Dik wanan kafafar da takeyi da Jin Kai da sabon iskancin da takeyi Basu kamaceta ba saboda aransu tayi da Rana tsaka uwarta ba Mai sarautaba ubanta ba Mai sarautaba karewarta ma baasan danginta ko kiristoci bane dik take wanan iskancin to kashinta ya bushe tunda Kabir ya fara shigowa hannu,sanan tunda ta fara muamala da bilkisu to da ita zanyi amfani wajen hada Mata tuggu Dan watarana sai munyi abinda Mai martaba zaisa a ratayeta batare da Taji kamshin auren kabiru ba" Dukansu sukasa dariya kasa kasa,....mikewa hajiya babba tayi da takun takama ta bude drawer ta Ciro gorar ruwan da suka ajiye ta mikawa deejamah"karbi wanan ruwan baba Sudan ne ki shanye shi tas ki shafe fuskarki saidai wani ba kabiru ba Dan gobe iwar haka kin Zama sarauniya" Hannunta har rawa yake wajen karbar gorar ta bude ta zuciyarta fara Tass ta kwankwade ruwan ta shafe fuskarta dashi.... "Karfe Tara na safe zaa daura aurenki Wanda dagashi sai kuma auren khausar da afnan insha Allahu badai shegiya ba a gidan sarauta" STORY CONTINUES BELOW Dadi ya Kara Kama hajiya rahina wadda tun dawowarsu wajen dinner bakinta yaki rufuwa... ******* Yarima Yana bangarensa dik minti biyar sai ya watsawa jikinsa ruwa saboda abinda yakeji take mararsa ta daure ko rufe idonsa yayi deejahmah ke tunanowa da kamshin turarenta,yayinda dayan bangaren zuciyarsa da ya tuna da baiga Fatima ba sai zuciyarsa tayi Masa nauyi,tunanin yadda zaayi ya fadawa ummu Fatima ta bace yakeyi Dan yasan akwai drama Amma tunanin da yakeyi yagansu da Ablah ko Tana gidanta,ya yi tunanin zuwa gidan ummu Amma yaganta lokacin data shiga fada wajen Mai martaba Allah yasa ba maganar batan Fatima taje yi Masa ba,yasa hannu ya sharce zufar goshinsa sanan ya janyo jallabiya yasa ya daga Kai ya kalli agogo karfe Sha daya da minti biyar na dare haka ya zura takalminsa ta nufo gidan ummu... ****** "Bilkisu dare yayi ki kwana a Nan kawai idan kika tafi tsoro nakeji ummu har yanzun Bata dawoba" "Baki gudun ummu tasan tsakaninmu?" "Zan sanar da ita idan lokaci yayi ki kwantar da hankalinki"buga kofar akayi da sauri fatima ta Mike Tana fadin "ga ma tanan"tayi hanyar kofar t bude da sauri taja da baya ganin yarima a hargitse yasata mannewa da bango,ta hade ranata tamkar Bata taba dariya ba kallon mamaki yakeyi Mata kawai ya karasa shigowa ciki Yana binta da kallo da kyar ya bude muryarsa a dishe yace "shine kika tafi ko?"... Cike da tsiwa tace "mezan tsaya inyi Kuna soyewarku kaida amaryarka Wai nabaka wurine kaji Dadi ka nunawa duniya yadda kakeson abarka" "Ke ni kikewa tsiwa da rashin kunya Ina Wasa dakene?" Ya daure fuskarsa Yana watsa Mata mugun kallo, Juyawa tayi tai wucewarta "Dan Kinga Ina sonki Zaki Raina ni ko?ya kamata kisan matsayinki a zuciyata be Dace ke nemi rainani ki wulakantani gaban kawarki ba" Takaicine ya rufeta kawai ta fashe da kuka wato ma yayi Mata laifi Amma yazo yanayi Mata masifa lallai ya nuna Mata tabbas shi Dan halak ne, Shigowa ummu tayi dauke da sadik a kafadarta da sauri bilkisu ta je ta amsheshi ta karbi jakar hannun ummu tayi daki yayinda ummu ta bi yarima da mugun kallo ta juya taga Fatima na shasshekar kuka, Hanyar fita ta nuna Masa "zoka fita mun a gida tunda abinda kayi Mata be ishekiba kazo ka Kara Akan nada koh?fitamun a gida kabiru kafin in sassaba maka" Shiru yayi Yana mamakin ummu yadda ta sauya lokaci daya take kaunar Fatima fiye da kowa takaicine ya lullubesa tayi masa rashin kunya Amma an bige da korarsa to tabbas idan ya tafi sai ya hora Fatima bazai sake dawowa garetaba Dan yafi karfin korar Kare...juyawa yayi cikin takaici yace "Saida safe"ya fita abinsa Fatima tabisa da kallo Tana hawaye... "Kiyi Shiru kidaina kuka dik sainayi maganin ko wani Dan iska a gidan Nan Dani suke zance ki kyaleshi idan ya gadama Kar yasake zuwa sai an kaiki dakinshi saime idan ankaiki ya koro min ke,sauran Yan iskan nagama dasu tunda nasamu Mai martaba zasuji result" Ta wucewarta daki bilkisu na Shirin fita ummu tace ta zauna suyi aiki da safe dare yayi hakanan ta zauna dakin Fatima ,har biyun dare Fatima batayi bacciba Tana kuka Abu goma da ashirin gobe Kabir zai agwance gashi yanzun bayasonta.... Sai wajen asuba bacci barawo ya saceta,haka ta tashi da safe jiki Babu kwari ga masifar ciwon Kai..... ******* Da sassafe aka shirya deejahmah akasa mata alkyabba tayi kyau da ita wajen karfe takwas gida ya rude da busar algaita ta ko Ina manyan mutane da sarakuna kawai ke shigowa yayinda aka bude babbar kofar fada inda anan ne zaayi daurin aure... Babbar Riga da Yar ciki Kabir yasa yayi kyau kamar wani babban mutum maroka dik inda yabi suna bnsa da kida da kirari..... Kuncin da yake ciki yasashi yake kawai yakeyi haka ya shiga gaisawa da mutane haka ya Raba ya shiga fadar yayi kicibis da mahaifin deejahmah yasha Nadi ya dawo daga Egypt har kasa ya tsugunna ya gaidashi ya amsa cike da faraa ....jamaa ne cike da wajen wadanda ya kallon mutum ne aminin sarki Wanda yazo tundaga wani gari sarki ya sashi ya zauna gefensa maimakon galadima dake Shirin Zama Dan ya Mika auren yarsa,damin kudi sarki ya mikawa aminin nasa Yana murmushi Yana fadin Allah yasa alheri Nan akafara gudanar da daurin aure inda aka sanar a loud speaker akwai wani daurin aure Wanda shi zaafara gabatarwa ,.. Take me sanarwa ya fadawa jamaa aka shiga gudanar da daurin aure yadda musulunci ya tanada Saida aka daura auren sanan Mai martaba yayi murmushi yace "alhamdulillah aminina babba na Mika Masa sadakin diyata Fatima marainiyar Allah Akan naira dubu dari biyar Wanda aka daura da Dana kabiru shine auren da muka fara daurawa jamaa ku shaida"take Mai shela ya shaidawa jamaa an daura auren kabiru da Fatima,kallon kallo mutane keyi dama Mata biyu zai aura?" Cikin minti biyar aka Kara yin shela ta daura auren deejahmah akaro na biyu da Dan sarki yarima"....Nan maroka da makida suka fara kidi tamkar jira suke a har gitse galadima ya mike yana fadin "ban yardaba ban amince da wanan auren ba,matukar kabiru zai auri shegiya bazai zauna da diyata ba Dole ya saketa"...Nan jamaa wuri ya dau hayaniya sarki bece komiba sai gaisawa da jamaa da ya cigaba da yi ya shiga bayarda kyauta ga wadanda Allah ya ciyar sukazo daurin aure.....yarima kuwa daskarewa yeyi a zaune dik jamaar dake Mika Masa hannu kasa dago hannunsa yayi ya Mika,yayinda waje ya kacame da hayaniyar galadima da tawagarsa.... Cire malum malum dinsa yayi yai cikin gida mutane Yan kallo suka rufa Masa baya..... Bankado labulen parlorn yayi a fusace "Ina khadijar take "...da sauri deejahma ta dago fuskarta a furgice Jin yadda aka Kira sunanta,+ "Tashi muje sai dai ya zaba ko ke ko Yar shegu Dan bazai yuwu da mutuncina da komi a wulakantani a tozartani cikin dubban jamaa ba wadanda sukazomin daurin aure" Kallon mahaifinta takeyi fuskarta dauke da furgici cikin rashin fahimta bakinta Yana rawa dakyar ta lalubo kalmomin ta hadasu tace "meya faru abbah?" "Au ku bakusan meke faruwa ba Kuna cikin gida ne?" Hajiya rahina wadda ta fito daga daki ta karbe zancen da "Wai meke faruwa ne naganka haka a furgice" Ya bude baki zaiyi magana yarima yayi sallama a parlorn take jakadiyya ta rangada gu'd'a... "Ga munafukin Nan ya shigo,wato dik kananan maganganun da akeyi da dik wata gutsuri tsoma na maganar aurenka da Yar gidan marayu Ashe dagaske ne ,tunda yau ta tabbata cewa Kai din Dan halas ne tunda ka hada baki da Mai martaba andaura aurenka da Mata biyu" Dafe kirji hajiya babba tayi "Mata biyu" 'kwarai da gaske Mata biyu sanan wani wulakanci ma Saida aka daura aurensa da waccan sanan aka daura da yata saboda tsabar cin fuska ban taba tunanin Mai martaba zaimun haka ba" Jikin deejahmah ne ya Kama rawa take kafafuwanta suka dauki rawa tamkar wadda akasawa shocking ta shiga ja da baya a hankali har ta jingina da jikin bango saboda yadda jiri ke dibarta, Takaicine ya rufe mahaifin deejahmah ganin yadda yarima ke faman raba idanuwa,cikin kumfar baki ya Soma zazzaga balai "cikin biyu zaayi daya, matukar kanason Zama da yata saidai a warware wannan auren munafurcin da aka kulla ko Kuma wallahi ka sakar min yata yanzun Nan Dan ba neman Kai nakeyi da ita ba" Zabura hajiya babba tayi tai Kan yarima ta cakumo malum malum dinta bakinta har rawa yakeyi "wallahi saika saki Fatima baka isaba kabiru nagaji da wanan cin Kashi da cin fuska da akemun uban waye yace kasa a daura ma aure da tsintacciyar mage?wanan auren be dauruba wallahi Dole a kwanceshi"....ta shiga jijjiga yarima tamkar wadda ta zare a guje tayi cikin dakinta ta dauko mayafinta ta yafa ta fito kafa babu takalmi ta nufi hanyar fita Tana fadin "wajen Mai martaba zani wanan munafurcin da aka kulla Dole a kwance shi Dan aga bayana anyi haka ne a nunawa duniya cewa kabiru shine Dan gata Dan so,an mance da shegiyar yarinyar itace tayi silar mutuwar dana daya tilo,....nayi hakuri dikda abubuwan da yaron Nan yakemun Dan ya bakantamin Rai Amma yau Dan a nuna Mana iyakarmu shine aka Mana wanan tozarci" Hajiya karama wadda ta fito sanye da lafaya Mai shegen kyau kqlar ja,itace ta rike hajiya babba Tana fadin "karkice zakije fada Akan wanan abinda Allah ya Riga ya kaddara kekinsan bamu Isa mujada hukuncin Mai martaba ba" Hankade hajiya karama tayi "karki kuskura kice Zaki gayamun maganar banaza Samira dan na Dade da sanin ke muna fuka ce kece kika kulla komi saboda anga banida da banida sauran gata banida da namiji shiyasa ake wulakantani a idon duniya"kawai sai hajiya babba ta rushe da kuka Tana fadin "wallahi koni ko ku a cikin gidan Nan" "Dakata safiya ba inda zakije karma kice Zaki bangaren Mai martaba Akan wanan maganar sakarmun yata kawai zaiyi" Yarima Wanda ke tsaye kamar an dasashi sai a sanan ya samu damar magana"mahaifina be bani damar sakin ko wace mace ba ya mun umarni da dik macen Dana aureta to na aureta ne sai mutuwa" STORY CONTINUES BELOW Hajiya rahina dakyar take Tako kafafuwanta wadanda sukai Mata nauyi ta kasaro gaban yarima tana binsa da kallo Tana zagayesa "lallai ka cika Kai babban munafukine shiyasa kukai munafurcin da Saida aka yantata daga baiwa kaida hajiya zainab ko?to mu zuba wallahi summa tallahi saika gwammaci kida da karatu daga Kai har matsoraciyar yarinyar Kuma kasani ya'ta Yar halak ce ba shegiyaba alhamdulillah kowa yasan Yar asalice Dan haka Allah ya bada zaman lafiya kabiru Amma zakayi danasani" Juyawa hajiya rahina tayi taja hannun galadima kafarta ko takalmi Babu suka fice daga parlorn sukai waje, Fitarsu yayi daidai da faduwar deejahmah kasa sumammiya,a guje jamaaar gidan sukai kanta harda yarima Wanda ya cire malum malum dinsa yayi jifa da ita ya ciccibeta yayi waje da ita,bangarensa ya nufa da ita.... ********* Tunda ta daga Kai ta duba agogo taga karfe goma na safe ta tabbatar da an daura auren yarima da deejahma kifa Kai tayi a Kan pillow ta shiga kuka Mai cin Rai Wanda batasan dalilinsa ba,hajiya zainab ta Dade da shigowa dakin tai tsaye ta rike kugunta Tana kallon Fatima wadda ke kuka kamar wadda akayiwa mutuwa,murmushi tayi a hankali ta taka har wajen gadon ta dafa kafadar Fatima ta furta a hankali "kuka ya Kare diyata kin samu yanci a yau din Nan,tashi ki share hawayenki alkawarin Allah ya cika kedin dai da baaso kece uwar gida a wajen kabiru Domin aurenki aka fara daurawa kafin na Khadija" Cakkk Fatima ta tsaya da kuka gabanta ya tsananta faduwa,dakyar ta yunkura ta Mike a hankali ta zauna fuskarta sharkaf da hawaye ta kafe hajiya zainab da idanuwa ko kiftawa batayi, Dariya sosai ummu tayi "kiyi Shiru ki share hawayenki zakaran da Allah ya nufa da cara ko Ana muzuru Ana shaho sai yayi Fatima Allah ya daukaka daarajarki burina ya cika don nayi abinda nasan harabada safiya bazata mance da wanan bakin ciki ba kedin dai kece uwar gida Kuma matar so" Rungume hajiya zainab Fatima tayi Tana kuka Tana dariya lokaci daya,....ita kanta hajiya zainab din dariya takeyi Tana bubbuga bayan Fatima... Dago Fatima tayi tana dubanta Tana murmushi,take kunya ta lullube Fatima ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta.... "Bude idanuwanki bakida wadda tafini nice uwarki nice ubanki Fatima sanan inaji a jikina kedin wata ce inaji a jikina iyayenki zasu bayyana kinji" Bude idanuwa tayi sababbin hawaye na sauka a idonta "ummu nacire Rai da ganin iyayena,zuciyata tafara mantawa da zancen iyayena tunda nasameki a matsayin uwa....nayi babban dace" Share Mata hawaye tayi ta mike tsaye ta fice dakinta,Jim kadan ta shigo da alkyabba baka Mai aikin golden colour Mai shegen kyau da tsada...ta karaso "taso kisa in kaiki fadar sarki sanan daganan mu shiga cikin gida koh" Gabanta ne ya fadi ta shiga girgiza Kai data tunada babban bala'i dake tunkarosu baki na rawa tace "ummu muje wajen Mai martaba kawai mudawo" "Tsoro ba naki bane Fatima dakewa zakiyi muje Mai martaba yasa Miki albarka mu shiga cikin gidan Kai tsaye gidan mijinki ne yanzun Babu shegiyar data Isa ta takaki Dan haka karki kuskura kibari suyi galaba akanki lokaci yayi da zanbaki dama ki Rama abinda dik akai Miki na karbar Miki yancinki na huce Miki takaici sauran yakin zan koma Baya ingani Yar tawa jaruma ce?".... Dago idanuwa tayi ta saukesu Akan ummu sai ta sunkuyar da kanta kasa Tana murmushi.... Canja Kaya tayi daga kayan dake jikinta xuwa hadaddiyar Riiga baka Mai shegen khyau ummu ta Bata ita kyauta daga saudiyya ta siyota,Saida tasa Mata ita sannan ta Dora Mata alkyabba wayyoo zokuga yadda alkyabba ta fito da Fatima tamkar Yar larabawa ta ummu da kanta ta gyara Mata fuska sanan suka fito gidan direct fadar sarki suka nufa.... Saida jakadiyya tayi musu iso sanan suka shiga,....har gaban sarki ummu ta zube ta kwashi gaisuwa dubban jamaa dake cikin fadar kowa sai Allah ya sanya alheri yakeyi fuskar hajiya zainab sai faraa takeyi.... STORY CONTINUES BELOW A gaban Mai martaba ta ajiye Fatima wadda ta gaidashi cike da girmamawa ya amsa fuskarsa dauke da faraa Nan ya shiga yi Mata nasiha wadda batasan lokacinda hawaye ke gudu a idanuwanta ba....yasa Mata albarka sanan cikin jamaa ya shaidawa dik wani Wanda yake fadar yabawa Fatima kujerar makka da dawakai dari da rakuma dari da shanu dari sanan da kujera uku extra ta wadanda zasu rakata aikin hajji...da kyautar motoci uku Wanda natane mallakinta Dasu zata rinka fita Kuma ya Bata bayi goma masu kulawa da ita a matsayinta na uwargidan dansa daya tilo....kabbara ce kawai jamaa keyi a wajen Shesshekar kuka kawai Fatima takeyi Tana sauke ajiyar zuciya ganin komi takeyi tamkar a mafarki...yau itace keda wadanan niimomin gabaki daya?...godiya sosai ummu tayiwa Mai martaba harda Fatima wadda kalmomin godiya da tayi amfani dasu gani takeyi tamkar sunyi kadan....haka kawai Mai martaba ya kasa dauke idanuwansa daga gareta ya rasa dalilin dayasa yarinyar ta shiga ransa ga fuskarta da takeyi Masa gizo lokuta da dama... Sallama Sukai da fada suka nufo hanyar cikin gida....dakyar Fatima ke taka kafafuwanta a haka har suka Isa... ********* Da sallamarsu suka shigo cikin gidan inda kallo ya koma sama,jamaa sai tururuwar fitowa sukeyi Dan suyi kallo dik Wanda ya Dora idonsa Akan Fatima sai yace Masha Allahu saboda wani irin annuri na kyau da kwarjini dake fita a fuskarta, Dakin hajiya karama suka nufa inda maroka Mata Suka shiga wasa Fatima suna yi Mata kirari....faraa sosai Yan uwan hajiya karama suka shigayi suna fadin "Masha Allahu tubarkalla Allah ubangiji ya bada zaman lafiya Allah yasa ace gara da akayi,lallai yarinya kin shigo gidan sarauta da kafar dama hakika kin Zama tauraruwa wadda ke haska masarautar barayar Zaki da kewaye Allah ubangiji ya sa albarka" A gaban hajiya karama Fatima ta tsugunna ta sunkuyar da kanta kasa,...kallonta hajiya karama takeyi Tana murmushi ta dago hannunta ta Dora akanta Tana shafawa "Allah yayi Miki albarka Fatima Allah ubangiji yasa alkhairi a zamanki da danmu kinji?ikon Allah sai kallo dik abinda Allah ya kaddara mu bamu Isa mujada ikonsa ba saboda haka Ina farin ciki da kika kasance daya daga cikin surukaina" Murmushi kawai Fatima takeyi kanta a kasa batare da ta dago ba.... Sautin muryar hajiya babba yasa dakin yin tsit tun daga parlor kafin ta karaso take zazzaga balai "ayyiriri shegiya Mara uba itace surukar Mai martaba itace matar sabon sarki Mai jiran gado,...lallai wanan Abu yayi Amma is a tarihi ban tabajin wanan kwado ba ace Dan sarki ya auri shegiya Yar kwararo...wadda akai cikinta a titi iyayenta suka wofintar da ita...to meye sunan jikokin da Zata haifawa sarki? Shegu?"ta kece da wata iriyar dariyar rashin mutunci, Mikewa hajiya zainab tayi 'ke safiya ki Kama girmanki Domin Ina ganin mutuncinki a matsayinki na matar yayana yau da bakida wanan matsayi Dana kaskantar dake a idon duniya" "Zainabu kenan lallai kin cika kin aiwatar da mugun nufinki sanan kin shammacemu a wanan wasan saidai ki gyarawa shegiyar yarki waje Domin sati daya kacal na baki zai sakota Dan bata Isa tazo gidan sarauta a matsayinta na shegiya tayi kishi da yar asaliba sanan Kuma shekara ta zagayo tace zata haihu baa gidan Nan ba" Murmushin mugunta ummu tayi "burina ya cika na tabbatar da na shammaceku Dan na kulla muku abinda har ku mutu bazaku manta ba,kamar yadda Fatima ta auri kabiru cikin sauki Aka kawo muku albishir na aure haka zaa kawo muku albishir na ta Haifa muku jikoki" "Fatima bazata taba Haifa Mana jikoki cikin gidaba Dan bazamu hada jini da shegiya ba,..Kuma min rigada munsan kece kika hada komi batare da son kabiru ba saboda haka nabaki dama wanan karon Amma Ina gargadinki da karki Bari mu hadu a wasa na gaba Dan zakisha Kashi....yaro Yana can daki tare da matarsa Yana jinyar ta" STORY CONTINUES BELOW Saida gaban Fatima ya fadi Amma saita danne kawai ta gyara zamanta a gaban mahaifiyar yarima.... Kanwar kakar yarima ce dattijuwa tayiwa ummu tsawa Akan Subar wanan fadan da sukeyi tonawa kansu asiri sukeyi cikin mutane....ummu batace komiba tai shiru yayinda hajiya babba ta shiga zazzaga balai...tagaji ta fuce a dakin... ********* Koda deejahmah ta farfado ta ganta a dakin yarima Yana gefen gado ya zabga tagumi Ahmad na gefe shima fuskarsa dauke da alhini sai kawai ta fashe da kuka Tana fadin "ka cuceni Allah ya Isa tsakanina da Kai Kuma wallahi bazan zauna a gidanka ba matukar da wanan karuwar zaka zauna" Dago jajayen idanuwansa yayi cike da balai ya fara magana "karki kuskura ki Kira fatima da karuwa a gabana kingane ko?yadda kike matata haka itama matata ce"...ya Mike a haukace ya fara masifa "waini ya kukeso inyi ne ke baa aure aka aureki?Koko kukadaine mutane?koba Fatima kina tunanin ke kadaice Zaki zauna a gidana?dama banida raayin Zama da mace daya wallahi saboda haka kisani ki bude kunnuwanki daga ke har Fatima Babu Wadda zata shigarmun gida Tana min iko baku isaba wallahi"...Yana nunata da yatsa,...mikewa Ahmad yayi ya kamosa ya zaunar da shi Akan kujera Yana fadin "cool down my friend ka kwantar da hankalinka please kayi hakuri zafin kishi ne irin na mata kawai,Kuma kaga batada lafiya kai meta a hankali" Hura hanci kawai yarima yakeyi zuciyarsa na tafarfasa,....ko Ina xafi Babu inda zaisa rayuwarsa ya huta ,yanzun ya Gama jiyo hayaniyar su cikin gida yasan dik Akan maganar ne ga babban bala'i dake damunsa Wanda ya rasa dalilinsa na fadawa wanan jarabar ta bukata...... Kuka sosai deejahmah takeyi harda shassheka ta dafe kanta kawai hawaye ke gudu a fuskarta,dago kansa yayi ya kalli yadda take kuka tamkar marainiya,wani irin tausayinta ne ya lullubesa,Dan tabbas yasan wanan abun da akayi Mata akwai ciwo Amma shi kansa yasan hikimace babba Mai martaba yayi Dan inba hakanba Babu yadda zaayi ya mallaki bintu,. Tasowa yayi ya dawo kusa da ita ya janyota jikinsa kawai saita fada kirjinsa Tana kuka da shassheka tausayinta ne ya lullubesa ya shiga babbuga bayanta a hankali... Mikewa Ahmad yayi ya fice zuwa parlor ya barsu ciki,.. Kasa cewa daita komi yayi sai lallashinta da yakeyi yayinda tsigar jikinsa ke tashi ta ko Ina,...ganin haka yasata yin shiru hade da lafewa kirjinsa Tana sauke ajiyar zuciya gabaki daya deejahmah kanta ya Gama daurewa babu abinda zatayi ta samu sassaci a cikin zuciyarta Sai kukan,tabbas tasamu Dan relief na zubda hawayenta da tayi ganin bece Da ita komiba yasata mikewa jiki babu kwari Tana takawa a hankali har parlornsa inda ta tadda Ahmad zaune ya rafka uban tagumi ya bita da kallo har ta fice.... Fitarta yasa shi fitowa parlor ya zauna gefen Ahmad...."ya kamata ka canja kayan Nan na jikinka Dan Kai ango ne tunda wadanan sun yamutse kasa wasu kasan dai karfe biyu akwai walima koh?..." Juyowa yayi ya dubi Ahmad fuskarsa dauke da damuwa yace "wallahi ganin komi nakeyi tamkar a mafarki,Amma kasan wani Abu kasan zuciyata farin ciki nakeyi da samun wanna baiwa da Allah yayi mun na amsar adduata cikin sauki na mallaki Fatima a matsayin matar aure Kuma bazan mutu ba sai na cika Mata burinta na mallaka Mata dik wani farin ciki....saidai wasu canje canje da nake gani a wajenta na kishi da ta dorawa kanta' "Nasani friend karka damu yau zaku angwance zaka Kuma lallashi abinka".... "Hmmmm"ajiyar zuciya kawai yarima ya sauke ya nufi Mike yace "Bari insake wanka" "Owk"..... ********** Koda deejahmah ta shiga gida direct dakin hajiya babba ta shiga ta taddasu zugum zugum a kuryar daki tamkar anyi mutuwa, Gefen gado ta nema ta kwanta wasu sababbin hawaye na gangarowa a gefen fuskarta, "Kidaina kukan Nan da kikeyi yanzun min rigada munyi sabon shiri....Kuma yau din Nan zamu aiwatar dashi ai wajen walima zamuje ko?to nasan abunyi wanan gida kece Zaki Soma shigarsa Kuma kece zai fara Tarawa da ita....nasan abunyi na tabayin wanan muguntar da dadewa wadda shine silar samuwar farin cikinmu kema Kuma abinda zanyi Miki kenan....zuciyata ta Gama bushewa nagama Shirina tsafff daga safe zuwa yanzun....ai hajiya zainab tabar shiri tun Rani ta mamayeni ne ta Kuma Sami saa Amma wanan karon bazatayi nasaraba Dan batasan Shirina ba..... ******** Tsaf Fatima ta kwashe labarin rayuwarsu na gidan marayu taba ummu a inda suke zaune a kuryar daki Tana kuka ta fayyace Mata komi dake tsakaninta da bilkisu... Sosai ummu ta jinjina lamarin ta ja dogon numfashi ta sauke..."bilkisu itace zata zame Mana babban makami Domin da nayi niyyar kwatarta ta karfin Hali tunda banida wata baiwa yanzun Amma zamanta a can din alheri ne...saboda Babu Wanda zai rinka samun information Akan abinda suke ciki Dan haka zanbarta a can sanan xan Bata damar Zama babbar aminiyar ta don ta hanyarce zamusan halin da suke ciki Domin yanzun dik yadda zaayi su dauki fansa shi sukeso Dan inada yakinin hajiya babba zata iya kisa tunda itace silar babban al'amari daya faru a masarautar Nan a baya Dan nadade Ina zarginta shiyasa nake tsoron mugun nufinta yasa na bullo Mata ta bayan gida...." Jinjina Kai Fatima tayi cike da gamsuwa sanan ta rusuna tace "nagode ummu Allah ya saka Miki da alheri" "Yauwa Fatima kece fa uwar gida Dan haka dakinki ya kamata yarima ya fara tarewa Dan haka nakeso in Miki wata tambaya " Sosai Fatima ta maida hankalinta Akan ummu "tambayar itace da dai nasan kinada tsarki Amma yanzun bansaniba ko kinyi bako" Kunyace ta lullube Fatima ta dukar da kanta kasa ta girgiza Kai alamar aa "Good jeki wanka ki fito inbaki wani sirri wadda na tabbata inhar hakan ta kasance to babu wadda zata wuce gabanki a wajen miji" Murmushi Fatima tayi ta Mike tayi Shirin wanka ta shige bayi,ta Dade Tana kuka a bayi Tana fargabar abinda ummu ke Shirin Bata umarnin yi Wanda batada agendarsa a yanzun....dikda itama akwai tarkon da tayi da tayi niyyar danawa yarima... Haka Nan tayi wanka jiki Babu kwari ta fito ko kafin tasa Kaya Saida ummu ta turare kayanta da turarruka kala kala sanan ta bita da wasu ta shafeta dasu Tass sai kamshi ke tashi Mai sihirtaccen Dadi... "Nasan yarima yayi Miki laifi Amma tabbas Dole ki bashi kanki yadda Zaki samu damar ramawa....ki kwantar da hankalinki kinji diyata yanzun lokacinki ne Dan haka kiyi abinda nace kawai" A furgice bilkisu ta shigo dakin Tana waige waige tayi zuru zuru daga ummu har Fatima kallonta sukeyi cike da fargaba..... Cakk bilkisu ta tsaya Tana zazzare idanuwa Tana kallon ummu Dan batasan cewa Fatima ta bayyanawa ummu ko ita wacece ba,+ Dukkansu suka zura Mata idanuwa suna jiran suji meke tafe da ita Amma sai ta sauke murmushin karfin Hali ta juya da niyyar fita, Ummu ce tai maza tace "dakata bilkisu nasan komi dake tsakaninki da Fatima Bata boyemin komiba ta fada mun Dan haka ki kwantar da hankalinki kizo ki fadamun meya faru" Juyowa tayi jiki Babu kwari ta tsugunna a kasa,...ummu da kanta ta dago da ita ta zaunar da ita a kujerar dake jikin madubi tace"umhmm Ina sauraronki" Kasa tai da muryarta "hajiya ce naji tace Zata samu daya daga cikin bayin Fatima ta Basu magani da zasu sa Fatima bazata taba haihuwa ba harabada.....sanan cikinsu zatasamu wadanda zasu rinkayi Mata aiki Akan Fatima yadda zasu cutar da ita cikin ruwan sanyi....zasu nakasa rayuwarta batare da kowa ya fahimci sune ba,a yadda naji ma Ashe deejahmah ta auri Kabir ne don ta samu ciki ta haihu yadda zasu kashe shi"...... Daskarewa ummu tayi Bata Bari bilkisu ta Gama bayanintaba ta Soma salati Tana fadin "lallai dik abinda hajiya safiya tace zatayi zata aikatashi Koda kisan Kai ne kuwa karamin aikinta ne,...zamanki da hajiya ba karamin taimako bane ga wanan yarinyar Domin da badanke ba da bamuji wanan babban tuggun da suke Shirin yi ba.....Kai safiya anyi shedaniyar mace,Babu Allah a ranta kwata kwata,batada burin da ya wuce taga tafi kowa ,Babu abinda ke tattare da wanan baiwar Allah sai son zuciya".... Bilkisu ta sunkuya kadan sanan tace"a yadda naji sunce a al'adar ba haushe wadanda akai aurensu Rana daya dik wacce aka fara kaiwa gidan itace uwar gida saboda haka zasu dauki deejahmah su kaita gidan saboda maganin da suka Bata ya zamana itace uwar gida idan har yarima ya kwana a dakinta to Babu shi Babu Fatima" "Innalillahi wa Inna ilahi rajiun.....tabbas maganar haka take daura auren Fatima a farko bashi zai Bata damar Zama uwar gida ba a al'adar bahaushe sai wadda aka fara kaiwa dakin miji,wanan haka yake nagode sosai bilki tashi kije" Jiki Babu kwari bilkisu ta Mike tai hanyar kofa Tana waigen Fatima wadda ke jingine a jikin bango hawaye na gudu a idanuwanta, "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun narasa dalilin da yasa mutanen Nan suka tsaneni bansan me hakan yake nufiba,Allah kana gani dik abinda na aikata banyi hakan da gangan ba nayi ne Domin Kare mutuncina,jarabawa da kaddara tasa na aikata kisan Kai Wanda dik wanan dalilin shi ya janyomin Tsana da kin jini,kodan nakasance Mara iyaye shegiya yasa ake kyamata ake tsanata"...toshe Mata baki ummu tayi 'kar insakejin wanan furucin daga gareki idan ba hakaba zan sassaba Miki" Bude drawer ummu tayi ta Ciro Mata sababbin Kaya wadanda zatasa zuwa wajen walima.... Lafaya ce Mai shegen kyau irin ta shuwa Arab Mai shegen tsada da kyau shi Fatima tasa sanan ta canja Mata wata akyabbar...ta shiryata tsaf ta Kara turare Mata jiki da turarruka masu shegen kamshi ta zaunar da ita a gefen gado, "Fatima kiyi hakuri da dik abinda ya sameki a rayuwa kinji? Babu Wanda yafi karfin kaddara irin wadda ta fada Miki ta fada mishi kinji?Kuma inhar iyayenki nada sauran rayuwa nasan zasu nemeki Kuma Zaki hadu dasu kinji?ki rike mijinki da kyau ki bashi kulawa wadda dik wata macen aure ya Dace ta bawa mijinta kinji?abinda nakeso dake shine yanzun gaskiya bazan baki damar zuwa wajen walima ba Domin mamayarsu zanyi a karo na biyu tunda har ga abinda suka bullo dashi zan bullo musu ta bayan gida" STORY CONTINUES BELOW Wasu siraran hawaye ne Suka zubowa Fatima a kumatu tasa gefen hannunta ta share, "Toh ummu"....tausayi Fatima kawai take bawa ummu.... ******* Shiri sosai sukai na zuwa wajen walima ko wa yasha kayansa masu shegen kyau da tsada,na wanan Yana wane wanan haka waje ya cika da milliyoyin jamaa daga fanni daban daban....wajen da aka tanada Domin zaman amare da ango Nan deejamah da yarima suka zauna, Sai baza idanuwa yarima yakeyi yaga Fatima Amma shiru be gantaba,haushinta ne ya lullubesa ya Gama fahintar inda yarinyar Nan ta dosa Amma zai koya Mata hankali,. Be Gama Shan mamaki ba Saida yaga ummu a wajen walima da kowa na wajen Amma babu Fatima Babu dalilinta,...dikda irin fushin da yakeyi da ita hakan besa ya daina tunaninta ba,Rabon da ya ganta tun ranan dinner dinsu shima basuyi magana ba ko a wani Hali take ciki oho.... A daidai kunnensa ummu tazo ta rada Masa "zan sanarwa da iyayen deejahmah daga Nan akai amarya dakinta kawai tunda yamma tayi sanan jamaa sun fara tafiya gidajensu"....kallo ya bita dashi Yana so ya tambayeta ita Fatima fa?Amma sai ya kasa kawai ya maida kansa kasa batare da yace komiba, Deejahmah dake gefensa sai kallonsa takeyi ta gefen idonta,ta kasa dauke kanta daga gareshi haka kawai takasa daina kallonsa yayi Mata matukar kyau da kwarjini... Har inda su hajiya babba suke zaune suna tsaigumin baazo da Fatima wajen walima ba gudun kunya ace Dan sarki ya auri shegiya yasa aka kulleta a gida,to sun rigada sun Dana tarko Akan daga wajen idan andau deejahmah a mota ayi can cikin gida inda akai musu gini.... Sallama hajiya zainab tayi Amma babu Wanda ya ansa Mata sai rahina....wadda itama tsoron kada Mai martaba yaji labarin halin da suke ciki takeyi yasa ta amsa, "Nazo ne in shaida muku maganar Kai amare gidajensu inaga zai kyautu idan an tashi Nan sai muje a kaisu ko?"....yatsina fuska rahina tayi sanan tace"umm"...ummu ta juya abinta cikin jamaa suka bita da harara, Zare jikinta ummu tayi ta koma gidanta inda dama ta Gama shirya komi tunda dama ta rigada ta kaiwa Mai martaba ita yayi Mata fada, Can ta dibi tawagar Yan rakiya ciki harda jakadiyyar sarki da babbar kawar ummu wadda tazo Mata biki,..ummu tasa motoci sukai layi a kofar gidanta sanan bayi Suka fara fitowa sanan ummu da aminiyarta sai Fatima wadda ke tsakiyarsu suna rike da hannunta,wadda gaba daya komi ganinsa takeyi tamkar a mafarki haka ummu tasata a mota saura suka hahhau tasu akaja su zuwa gidan amarya, Farin ciki ne ya lullube ummu ganin burinta ya cika na sharewa marainiyar Allah hawaye,....gida ne tsararre ginin zamani Mai sashi hudu a ko wanne sama da kasa ne,...gate guda daya ne na shiga gidan Wanda shine ainihin main entrance na shiga ,....rike hannunta ummu tayi suka nufi sashen gate din gidan,... maaikata da dogarawa gidan suna ganin zuwansu suka bude musu gate din gidan hade da zubewa kasa suna kawo gaisuwa, Addua ummu tabawa Fatima umarnin yi kamar yarda al'adar malam bahaushe take anaso ko wace amarya idan ankaita gidanta tayi addua hade da Bismillah ta shiga da kafar dama..haka Fatima tayi sanan suka shiga cikin gidan Wanda harabar gidan kansa abin kallo ne tamkar baa kasar hausa ba haka ummu tayi musu jagora har sashen da ta zabawa Fatima Dan dama tazo gidan taga komi..... Sama suka hau da ita inda Nan ne dakunan kwanan bangarenta suke, Wani daki ummu ta bude suka shiga da ita Basu direta ko inaba sai Kan makeke hadadden gado Dan kasar waje suka direta... "Masha Allahu" shine kawai abinda kawar ummu ke Fadi "tubar kallah Fatima lallai kinzo duniya a saa Domin samin irin wanan daular sai Wanda Allah ya zaba,saboda haka ki Zama Mai biyayya Kuma ki rike Miji Allah ya bada zaman lafiya"... STORY CONTINUES BELOW Nan sukaita Mata nasiha Mai ratsa zuciya sanan ummu sukai sallama ta bi bayan kawartata suka fice..... Bayi biyu ne ke cikin dakin Fatima ko wacce na tsaye gefe da gefe yayinda wasu ke kasa a parlornta mutum hudu Wanda dik nata ne...su zasu rinka kulawa da ita, ********** Sai magriba aka tashi walima inda tawagar jamaa sukayi caaaa a hanyar gidan amarya wadanda sukayo wa deejahmah rakiya da kawayenta da baki wadanda suka zo biki.... Jamaa kowa sai sambarka yakeyi da wanan makeken gida Wanda yasha kayan more rayuwar duniya, Dayan part din aka nufa da deejahmah inda sukai meta rakiya har cikin bedroom itama aka ajiyeta,..too fa Nan kawayen amarya su Sunita Suka shiga kashe selfie a bedroom din deejahmah saboda tsabar haduwarsa .... Dai dai kunnenta hajiya babba ta rada Mata "ki kwantar da hankalinki karki nuna Masa komi Domin dakinki zai Soma zuwa tunda ke aka fara kawowa Kinga kece uwar gida sai yayi Miki kwana bakwai sanan zai koma sashenta lokacin kin mantar dashi wata halitta".... Deejahmah ta jinjina Kai batare da tace komiba,haka suka Gama surutansu sukai Mata sallama harda Yan matan amarya wadanda dama Ahmad ya sallamensu da makudan kudi tun a wajen walima,,,,, Sakkowa kasa hajiya babba keyi cike da Isa da mulki kawai tai Karo da bayi wadanda suna ganinta suka zube ...tabisu da kallon tuhuma Tana kallonsu daya bayan daya "ku Kuma daga Ina" A tare suka hada baki wajen Bata amsa "mune maaikatan sarauniya Fatima wadda aka kawo Nan dazun kafin maraice".....dibbbb network din Kan hajiya babba ya dauke saita juya da sauri zuwa dayar matakalar ta shiga takawa sauri da sauri har ta shige ciki ta nufi kofar da take hangen hasken lantarki tasa hannu ta tura kofar daki, Fatima wadda ke zaune Kan dadduma ta idar da sallah ta dago Kai da sauri,ganin ko wacece yasata sauke lallausan murmushi hade da mikewa ta nade daddumar Tana fadin "Bismillah ranki ya dade,ai ya kamata kishigo kiga yadda Allah yayi da Yar shegiya Yar kwararo"...tai maganar fuskarta dauke da murmushi, "Bismillah ga waje Kun kawo amaryata ne?"ta jefa Mata tambaya dikda zuciyarta na tsananin bugawa.... Kallon takaici hajiya babba keyi Mata "yarinya kinyi kuskuren shigowa hurumin da ba naki ba a guje zakibar gidan Nan da kafafuwanki,idan baki fita da hankali ba Zaki fita da tsananin hauka" "Kinyi babban kuskure hajiya wajen bani damar shigowa gidan Nan Domin kafin infita sai shegiya ta tabbatar da ta Haifa muku jikokin shegu Domin tabar muku tarihi Wanda bazaku taba mantawa ba" Idanuwa kawai hajiya babba kebin Fatima dashi wadda take jifanta da mugayen kalamai a cikin hikima...."lallai kin dakko ruwan dafa kanki tunda daga kawoki ko cikakkun awanni goma bakiyiba kinfara Zama tantiriyar Mara kunya" Yar dariya Fatima tayi ta dago Kai Ido cikin idon take kallon hajiya babba "hajiya dama bakisan dik Dan kwararo bashida kunya ba sai yau?....dik azabar da kikaimun dik a tunaninki biyayyr da nayi Miki tsoro ne yasa nayi Miki su?nayi Miki ne kawai don kedin uwargijiyata ce a wanan lokacin,sanan jira nakeyi insamu damar da Nima zanci nawa duniyar Domin kaf dinku saina baku mamaki,nayi matukar farin ciki da ya kasance ke da kanki kika Tako inda nake har nasamu damar amayar da abinda ke cikina a cikin sauki.... alhamdulillah Allah ya cika mun burina na Zama matar kabiru sanan wani abin farin ciki ma uwargida a wajensa wanan ne ya bani damar Zama sarauniyar sarki Mai jiran gado.....hajiya Dan Allah ga hanya Nan mijina na gab da shigowa"....Fatima ta nuna Mata hanyar Kofa Tana murmushi....1 Kalaman Fatima kawai keyi mata yawo akai tamkar a mafarki.....kallon Dan bakin Fatima kawai takeyi yadda take zaro maganganu tamkar Tana jiranta.....batasan lokacin da gumi ya jikata ba sharkaf.....a tarihin rayuwarta Babu Wanda ya taba tararta ga da ga ya mayar Mata da martanin maganganu marasa dadiba Koda kishiyarta ce balle Fatima dake matsayin surukarta..... Jinjina Kai kawai tayi ta nuna Fatima "lallai kin Kira ruwa bakida laima kinzama kiyashi Mai jawo abinda yafi karfinsa.....lallai kin nunamin ke din cikakkiyar Yar bariki ce Amma da sannu zanyi maganinki Zaki hada kayanki da kanki ki koma gidan marayu...idan nayi Miki me sauki kenan idan baki fita gidan Nan da hauka ba" "Yan rakiyarku suna jiranki hajiya".... A fusace ta fice a dakin Fatima ta bita da malalacin murmushi hade da dafa kirjinta ta furta a Fili "banso na Miki hakan ba tun yanzun Amma gara in shayar dake mamaki ki kwana kina tunanina"... Runtse idanuwanta tayi tana sauke numfashi a hankalinki a hankali harta samu natsuwa a zuciyarta..... Jikinsa a sanyaye ya shigo gidan,direct side din dake facing dinsa ya nufa....Wanda shine na Fatima... Babu kowa a parlorn kafa ta dauke haka ya nufi hanyar matakala Yana takawa a hankali a hankali har ya Haye sama.... A hankali ya tura kofar dakin bakinsa dauke da sallama...ya maida dakin ya rufe, Tsaye yayi gabansa na faduwa Yana tunanin wacece a side din da akace Nan zai shiga ya kwana?....kallo yake binta dashi tun daga kasa har sama inda ya sauke idonsa Akan fuskarta dake sunkuye.....ya kafeta da idanuwansa wadanda yake Kara budesu Yana kallonta saboda gani yakeyi tamkar gizo take yi mishi ita dince kuwa?....ya Kare Mata kallo sanan ya tako a sanyaye ya karaso har inda take ya zauna a gefen gado....zuciyarsa ce ta tsananta bugawa Amma hakan be hanasa Kiran sunanta ba a sanyaye "bintu"...shine abinda ya furta a hankali.... "Allah ya cikamun burina na mallakeki a matsayin matar aurena"...besan lokacin da hawayen farin ciki suka Soma gudu a idanuwansa ba.... Ya matso daf da ita ya dago kanta ya kura Mata ido,....ita kuwa Fatima idonta a rufe suke sai zuciyarta dakeyi Mata lugude.... "Ki bude idanuwanki ki kalleni bintu yau na Zama mallakinki kema kin Zama mallakina....dare da Rana banida burin da ya wuce hakan,kullum adduata shine Allah ya cikamun burina na karshe shine aurenki,sai Allah ya dubi kyakkyawar niyyata ya mallakamin ke cikin sauki....hawayen Dadi ke diga a idonsa suna sauka a fuskarta...itama su ta shigayi suna gudu a fuskarta kawai yasa hannu ya shiga share Mata su Amma tamkar karuwa suke.....tausayinta da soyayyarta suka shiga yawo a jinin jikinsa,...ntake jikinsa ya hau rawa ta rungumeta tsammm a jikinsa da karfin gaske..... ******** Kaiwa da komowa kawai hajiya babba keyi a cikin bedroom dinta Tana tunani kala kala....kalaman Fatima kawai ke yawo a kunnuwanta sunayi Mata amsa kuwwa....."tabbas kinyi kuskure Fatima Wanda bazaki tabayin irinsa ba a rayuwa.....lallai kin dakkowa kanki dala Babu gammo Amma nidake zamuga Wanda zaici riba.....sainayi sanadiyyar zamanki a gidan yari na harabada.... Sundade rungume da juna suna sharar kwalla,dayar yasamu ya saketa kadan ya juyo da fuskarta daidai saitin tasa ya rada Mata "tashi kiyo alwala kafin indawo kinji?"...+ Shafff Fatima ta saki jiki ta share zancen wata deejahmah sai da yadan kashe Mata ido "minti goma zuwa Sha biyar da kikajiki a jikina har kin manta kinada kishiya"...kauda kanta tayi gefe Tana murmushi kasa kasa cike da kunya batare da tace komiba,...ganin hakan yasashi janye jikinsa daga nata ya fice a dakin, Da sallama dauke a bakinsa ya shiga dakin deejah dake zaune ta kafe kofa da Ido Tana sauraron shigowarsa ta bisa da kallo tun daga sama har kasa sanan ta sauke idonta Akan bugaggiyar shaddar dake jikinsa wadda ta dan yamutse kadan botir din rigarsa daya a balle take jifansa da kallo, Zuciyarta ce ta shiga saka Mata cewar lallai yarima daga dakin Fatima yake,...Bata Gama tunani ba ta tsunkayi sautin muryarsa Yana Mata magana,hade da gyara tsayuwarsa a gefen gadonta hade da watsa Mata manyan idanuwansa "na shigo dare ya rigada yayi naso ace nasamu cikakken lokacinda zan hadaku da Fatima in yi muku nasiha,insha Allahu zuwa gobe zan hadaku gabaki daya in tattauna Daku"....shiru tayi tana Mai sauraronsa batare da tace komiba kusan minti biyar har ya gaji Dan kansa ya huro iska a bakinsa "bakice Dani komi ba kindaisan banason sarauta ko" Jinjina Kai kawai deejahmah tayi zuciyarta na cigaba da tafarfasa.... "Saida safe"...shine abinda ya ce Mata ya nufi hanyar fita ta bishi da kallon takaici ,lallai yarima wato ko arzikin Zama a dakinta ma batasamu ba yaje sun Gama iskancinsu sanan zaizo ya tsaya Mata akai yace yazo sallama ko?kwafa tayi tace a ranta "zaka shigo hannu"karar rufe kofarsa yasata dawowa daga duniyar tunanin data fada....ta Mike ta cire alkyabbar jikinta ta nufi wardrobe din jikin bango ta bude inda kayanta suke jere ta shiga zakudo rigar bacci wadda zatasam.. ******** Yana shigowa dakin ya nufi toilet yayi wanka sanan ya fito ya fice jimm kadan ya dawo sanye da jallabiya ya shimfida dadduma da kansa ya ja kusu sallah rakaa biyu sanan suka sallame, ya juyo gareta ya kakama kanta yanayi Mata addua kusan minti goma sanan ya shafa yayi Mata tambayoyi game da addini alhamdulillah wadanda tasani ta amsa, Da kansa ya mikar da ita ya nade daddumar ya ajiye ta gefe wajen switch din globe yasa hannu ya kashe ya ruko hannunta zuwa gado.... Turesa kadan tayi ya rada Mata a kunne "ke meye haka Wai Hira fa zamuyi"...a shagwabe tamkar zatayi kuka tace"nifa banajin yin hirar bacci nakeji".... Murmushi yayi cikin duhu ya Kara janyota jikinsa ra rungumeta sosai yanajin sautin bugun zuciyarta wadda ke cike da fargaba,...yasani Sarai tsorone cike falll zuciyarta kawai sai ya Dora bakinsa daidai kunnenta ya rada Mata "to Bari insaki bacci ai babyna ce ko?rainonki yabar hannun ummu ya dawo wajena"yadan hura Mata iska a kunne yadda yake maganar kadai yasa jikinta yin sanyi tai lamo a jikinsa ya shiga shafo wuyanta Yana hura Mata iska a kunne....dik da yadda jikinta ya mutu bai hanata tsoro da fargabar Jin hannuwansa na yawo a kirjinta da sassan jikinta.... Saida ya tabbatar ya Gama kashe Mata jiki sanan.....😬labari ya canja Dan gabaki dayansa a furgice yake jikinsa rawa yakeyi tamkar ansa Masa shocking Babu abinda yake bukata sama da ita Babu inda baya lasa a jikinta hawaye ke gudu a idanuwanta ganin dik yadda ya koma tamkar mayuwacin Zaki....kasa hanasa tayi dikda fargabar da takeci data tuna da alkawarinta da ummu kawai saita sakar Masa linzami.... Ko kafin asuba yarima yayi round yakai hudu...bai taba tsintar kansa a cikin wanan yanayi ba irin na yau,da yasamu gamsuwa zaiji sabuwar shaawa na taso Masa,ita kuwa shame shame kawai tayi tamkar gawa Tana Jin yadda yake aiki a jikinta,sai wajen asuba ya dagata ya rungumeta jikinsa kawai ya saki kukan farin ciki ya shiga Kai Mata kiss ta ko Ina.... STORY CONTINUES BELOW Hannu yasa ya kunna dumm light yaga yadda hawaye ke gudu a idanuwanta yasa bakinsa Yana lashewa hannunwansa na yawo a jikinta..... Kacokan ya dauketa yayi toilet da ita Nan da Nan ya hada musu ruwa Mai zafi yayi Mata wanka ya gasa Mata jiki sosai sanan ya fito da ita ya kwantar yaja bargo ya rufeta...shima ya shiga yayi NASA wankan Da kanshi ya Ciro Mata doguwar jallabiya a drawer ya sa Mata sanan ya fita Yana Jin Kiran sallah a masallaci ya rufo Mata kofar.... Sakkowa tayi a hankali ta koma bayi tayo alwala tazo ta tada sallah,tanayi jiri na dibarta saboda rashin karfi a haka ta idar da sallar taja jiki ta Haye gado.... Misalin karfe shida ya shigo gidan direct dakin deejahmah ya nufa Yana tura kofar yaganta Tana bacci,..tsaki yayi sanan ya shiga tashinta da tayi sallah dakyar yasamu ta amsa Masa ya fita ya rufo Mata kofar.... Ganin hijabi jikinta Kuma gata a kwance ya bashi amsada tayi sallah sai kawai ya Haye gado ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam Yana laluben bakinta Nan ya shiga tsotsar bakinta a haka bacci ya daukesa Mai dadin gaske... ******** Sai goma na safe deejahmah ta farka da sauri ta tunada batayi asuba ba Nan da Nan ta shiga bayi tayo alwala ta tada sallah sharp sharp gudun kada ya shigo.... Tana idarwa ta fada toilet ta tsala wanka ta fito ta Dade zaune Tana kwalliya sanan ta shirya tsaf da tsaddun material Dan India maroon Wanda yayi masifar amsar fatar jikinta.... Lekowa tayi taji shiru ko Ina a haka ta sakko daga sama kwass kwassss da takalminta har babban parlonnsu Nan taga Yar kararrawa ta Danna saiga bayin gidan dukkansu suna rige rigen shigowa dukkansu ko wacce ta zube... Kallonsu takeyi daya bayan daya tamkar bazata ce komiba cann ta nisa tace "Ina bukatar abun karyawa"... "Toh ranki ya dade"...suka hada baki suka fice a tare... Cikin minti biyar suka shiga shigowa da kayan breakfast kala kala wadanda aka turo wasu daga gidan sarki wasu a Nan sukayi shi....sukai serving dinta da kunun gyada da soyayyar doya da kwai tanaci tamkar Tana taunar magani... Karar fitowa yasata tsayawa da taunar da takeyi ta maida dubanta daga inda take jiyo sawun takalmin, Yarima ne yasha shadda baka da hularsa ja Mai shegen kyau gefensa Fatima ce da red less dinkin sket da Riga fuskarta Babu make up Amma hakan be hana kyawunta na usuli bayyana ba.... A tare suka shigo parlon inda Fatima ta zauna Nan shima ya zauna gefenta hannunsa rike da kwankwasonta... harararsa ta danyi "dik ka Hana mutum sukuni dik inda nabi kana manne Dani Nika cikani" Dan tsungulunta yayi ta zabura Tana fadin "mugunta ko mugunta ko Allah saina fadaka da ummu"yadda tayi maganar a shagwabe yasashi kafeta da idanuwansa Yana murmushi.. Kararrawa Fatima ta Danna saiga bayi sun Kara shigowa "Ina bukatar abinci Amma ba kalar wanan ba Dan ni banajin Shan kunun gyada,a dafomin ruwan zafi a soya min cheefs"...tace cike da Isa... Mikewa deejahmah tayi tana Shirin barin wajen yarima yayi saurin cewa "na cancanci gaisuwa Amma bansamuba deejahmah ko Mulkin ne ya motsa irin na yaran masarautar barayar Zaki?"yace cike da zolaya, Kayataccen murmushi tayi tai farr da idanuwanta "gaisuwarka ta musammance ranka ya dade a daki ya Dace asameka a gaisheka ba cikin mutane ba".... Tabe baki yarima yayi ya dage kafadarsa "yadda kikaga ya Dace"....ta juya abinta Tana juya kwankwasonta... ******** Cikin kwana biyu soyayya Mai karfi hade da shakuwa ce ta Kara shiga tsakaninta da yarima wadda takejinta a sabuwar duniyar da Bata taba tunanin zata tsinci kanta ciki ba.... STORY CONTINUES BELOW Tunda safe sarki ya Aiko neman yarima ya fita Dan Kiran nasa Dan haka Koda Fatima ta shirya sai Bata nemeshi ba tayi fitowarta Dan ta Sha iska... Sallama tayi a parlorn ganin deejahmah zaune Rahane baiwarta da aka kawota Tana famar matsa Mata kafa hannunta dauke da waya Tana chat... Harara ta watsawa Fatima hade da sakin tsaki tace "nibansan dalilin dayasa kike son ki rinka shiga gonata ba bayan kinsan danida ke din ba saanin juna bane babu Hadi hanyar jirgi daban ta mota da ban sai shegen naci da maita yarinya sai kace kaska".. Mikewa Fatima tayi daga inda take ta Tako har gaban deejahmah ta tsaya fuskarta dauke da murmushi "nidake tabbas ba saanin juna bane Domin akwai banbanci tsakanin uwar gida da amarya,sanan akwai banbanci a tsakanin sarauniyar asali da wadda take amsa sunan sarauniya Amma Bata cancaci a kirata sarauniyar sarki ba saidai a kirata da matar sarki Kinga kuwa akwai banbanci,naji Dadi da kika sanar Dani cewa indaina zubar da girmana wajen gaisheda kanwata,saidai hakan bazai yuwu bane saboda kasancewar ni din Mai ilimin addini ce nasan muhimmancin sallama ko a musulunce"...ta juya Tana takawa dai dai deejahmah na Kare Mata kallo, "Samun ilimin addini a gidan marayu bai amfana Miki komiba tunda garin karuwanci kikayi sanadiyyar Rai Wanda ya rataya a wuyanki,sanan ke har kinada wani tunkaho da kikedashi bayan kinsan asalinki?kin manta cewar tsintarki akayi aka Mika ki gidan marayu?kin manta cewa itayayenki wofintar dake sukayi gwamnati ta tsunceki tayi Miki suturar daurawa?....gaskiya bakida Hadi Dani da akayi cikina a sunnah aka haifeni akaimun hakika"...ta kece da dariya Tana karkada kafa Tana bin Fatima da kallon wulakanci .... Ba karamin zafi kalaman deejahmah sukaiwa Fatima ba wadanda sukasa fararen idanuwanta suka canja kala Nan da Nan zuwa naauin ja wata Yar kwalla ta taru a Ramin idanuwanta, "Dikda kasancewata tsintacciyar mage shegiya wadda aka tsinta a gidan marayu hakan be hanani Zama cikakkiyar yarinya Mai tarbiyya da sanin ya kamata ba....hakan yasa mijina yake alfahari Dani a ko Ina sanan kisani nidin ba shegiya bace Sunnah ce ta haifeni" "Idan Sunnah ce ta haifeni Fatima inada bukatar ganin uwa da ubanki sai in tabbatar" A fusace yarima ya shigo parlorm Yana Mai daka tsawa "ya Isa haka Khadija,...dik naji abubuwan da kike fada kedin da kikeda iyayen wace tarbiyyace suka baki ita wadda Zaki fito da ita kiyi alfahari da ita a idon duniya?inace ibadah ma wanan Bata Gama cika a wajenki ba ballantana sanin darajar Dan Adam?karki kuskura insake Jin kin zagarmin Mata wallahi saina sassaba Miki" Hawayene suke gudu a idanuwan Fatima kirjinta na tafarfasa tamkar ta fasa ihu haka takeji cakkk take tsaye ko motsin kirki batayi....yau kwananta shida a gidan miji tun kafin aje ko Ina anfara goranta Mata maganar iyaye?yanzun inda yara gareta fa akeyi Mata wanan gorin?harda yaranta zaa hada kenan....rungumota yayi jikinsa Yana shafa bayanta a hankali..... deejah wadda ke zaune tamkar mutum mutumi ta Mike tayi sama a guje Tana fadin "wallahi bazan yarda ba bazan taba yarda ku hada Kai da matarka ku wulakantani ba".....ta shige dakinta ta bugo kofa... Daukar Fatima yayi tamkar baby ya nufi bangarensa da ita can ya shige daki da ita ya rage rigar jikinsa ya ajiye sanan ya hauro saman gadon ya rungumeta Yana kallon fuskarta wadda har yanzun akwai sauran hawaye a makale... Hannu yasa ya share hawayenta yace "banason kina Kuka a gabanta don anyi Miki gorin iyaye kinji?kidaina kuka ki cire zuciyarki Akan hakan dan kisamu farin ciki dawamamme"... Sababbin hawayene suka gangaro a fuskarta tasa gefen hannunta ta share sanan ta langabar da kanta a kirjinsa Tana sauke a jiyar zuciya....hannunsa ya tura cikin kirjinta ta dago Kai Tana harararsa ya kashe Mata ido "abuna ne fa abarni inyi yadda nakeso ".. Ta Dan turo baki "ni gaskiya zafi sukemun fa kabari "..tace a shagwabe.... Dariya ya kamayi yasa kansa a gefen wuyanta Yana lasar wuyanta da harshensa ya shigayi Mata wasanni masu zafi wadanda yasa Nan da Nan tafara sauke numfashi...ganin haka ya dago kansa ya Dora bakinsa a nata ya shiga aika Mata da hot kiss hannunsa yasa a bayan rigarta ya zuge zip din rigarta Nan da Nan ta bashi hadin Kai suka shiga farantawa juna.. STORY CONTINUES BELOW Sanye take da alkyabba tayo hanyar sashensa a fusace ta nufi kofar Taji saukar numfashinsu....cakkkk ta tsaya Tana Mai Kara sauraren abinda takeji....Nan da Nan idanuwanta suka kawo ruwa ta juya hawaye nabin kuncinta ta nufi sama jiki a sanyaye ta shige dakinta ta kwabe alkyabbar ta fada gado ta saki kuka Mai karfin gaske Tana juyi....lallai ma yarima..tsabar jaraba har da Rana ya hayeta yanayi Mata soyayya ita kuwa ko dakinta ya shigo saidai ya nemi gefen gado ya tsaya ko arzikin Hawa gadonta ya zauna beta samu ballantana abinda ya shafi soyayya...kuka sosai takeyi Mai ban tausayi Wanda takai awa biyu Tana yinsa sanan ta nemi tsakiyar gado ta zauna..... ******** Saida yasamu natsuwa sosai sanan ya shiga bayi ya watsa ruwa ya fito ya rufo kofar yabar Fatima ciki Tana wanka... Karfe hudu da kwata ya shigo dakin deejahmah Tana zaune ta rafka tagumi fuskarta ta kumbura saboda kuka,...kallo daya yayi Mata ya kauda kansa ganin yanayinta dikda ta bashi tausayi Amma be hanasa daure fuska Akan abinda tayiwa Fatima ba, "Ke kinci abinci?"...ji wata tambayar rainin wayau da yayi Mata tun karfe suke daki be fitoba sai yanzun Yana tambayarta kotaci wani Abu, Haushi ne ya lullubeta yasa kwalla cikowa idanuwanta ta girgiza Masa Kai kawai...kwallar da take boyewa ta sulalo a idanuwanta masu zafi ta dago Kai da niyyar Gaya Masa magana yadda taga fuskarsa yasata saurin sunkuyar dakai Tana sharar hawaye... Tausayinta ne ya kamasa jikinsa yayi sanyi,jiki Babu kwari ya karaso har inda take ya hayo saman gadon ya dago fuskarta sai kawai ta fashe da kuka.....da sauri ya rukota "ya Isa haka yi shiru ki fadamin abinda kedamunki kinji deejah"..yadda yayi maganar cike da lallashi yasata kwantar da kanta jikinsa Tana shasshekar kuka "haba Yaya yarima bansan menayi maka ba ni ka tsaneni ko shigowa dakin Nan kayi baka Zama kake ficewarka baka damu da lamarinaba yanzun Kuma a gaban kuyangata Rahane ka dizgani ka wulakantani Akan Fatima"... Jikinsa ne ya karayin sanyi ya shiga shafa kanta"ya Isa nabari Amma kema kidaina wulakantamin Mata deejah matukar bazaki Bari ba to tabbas bazan daina saba Miki ba Dan itama bazan Bari ta wulakantamin Yar uwaba kinji" Haushi maganarsa ta Bata Amma ba yadda ta iya batace masa komiba ta janye jikinta daga nashi ta share hawayenta ta shige toilet...kallo ya bita dashi Yana kada Kai kawai.... Koda ta fito Bata sameshi ba hakan be Bata mamaki ba Dan tasan dama yagadama ne ma ya zauna yanayi Mata lallashin karya bayan ya Gama sauke numfashi wajen wata, Murmushin takaici tayi hade da mugunta ta sauke numfashi "daga gobe kinyi bankwana dashi Yar matsiyata saina tabbatar da na juya masa hankali zuwa gareni...ya Gama shaawarki daga gobe kedashi saidai kallo badai kwanciya ba"...zuciyarta na cigaba da yi Mata tukuki ********** Rass ya ya tadda Fatima tayi shirinta tsaf har tayi wanka,shiga yayi da sallama Yana fadin "baby har kin tashi?".. Juya Masa Kai kawai tayi hade da zumburo baki gaba "Ina kaje?wato tafiya ma kayi wajen matarka kabarni wankan daka savamin ma yau bansamuba kanacan kana lallashi?" Wani kishi ne ya taso Mata Nan da Nan idonta ya kawo ruwa,...jikinsa na rawa ya zauna gefenta ya ruko kuguntd "yi hakuri nayi laifi yanzun tashi muje a sake wanka"...makale kafada tayi ta Kara juya Masa baya Da karfinsa ya rungumota ta fada jikinsa ya matseta tsammm Yana kallon kwayar idanuwanta da yake hango kishi karara..."baby kiyi hakuri kinsan dai hakkina ne insan taci ko bataci ba shine naje na tambayeta ko taci wani Abu" Ta kwantar da kanta jikinsa kawai taji wani irin kamshi da sauri ta turesa ta Mike tsaye tana dire dire "ni bazan yarda ba zuwa kayi ka rungumeta kayi Mata irin abinda kakemun"ta fashe da kukan shagwaba, Dariya ya shigayi ya Mike ya dauketa cakk yayi waje da ita Koda suka fito kicibis sukayi da deejahmah tayi wankan yamma tsoron Allah ne ya kamata ganin da tayi musu hannunsa daya yanayi Mata cakulkuli Tana shura kafafuwa Tana dariya shima dariyar yakeyi suka gifta ta gefenta sukai sama....tabisu da kallo... ********* "Fauziyya gobe nakeso ayi aikin Nan fa?zakije kuwa ?" "Zanje Mana innah karki damu komi zai tafi yadda kikeso" Murmushi innah tayi "dakyau" ********* Daddare suna kwance shida Fatima Tana rungume jikinsa kanta a kafadarsa ta yatsina fuska tace cike da shagwabarta data Saba "habeeby inaso kayimun wani Abu guda daya Wanda dagashi idan kayimun har abada ka gamamin komi" Maida hankalinsa yayi sosai gareta ya gyara Mata kwanciya jikinsa yace "kome kikeso ki fadeshi kanki tsaye bakida wani hijabi tsakaninki da mijinki kinji?wa kikedashi Wanda ya fini?umm? fadamin?ya Kara matseta a jikinsa, A sanyaye tace"so nakeyi ka bani hadin Kai wajen neman iyayena,inaso insan kosu din suwaye,inaso in tabbatar da niba shegiya bace,idan ma ni shegiyace inaso insamu labarin yadda akayi nazo gidan marayu"...tai kwalkwal tamkar zatayi kuka, Ajiyar zuciya ya sauke "nayi Miki alkawarin baki gudun mawa wajen binciken iyayenki a din lokacinda kika shirya" A shagwabe tace "ni ko yanzun ma na shirya"....ya lakuce hancinta "to rigimatu kibari gobe zan bincika inji?".. "Ni ah ah muje tare gidan marayu muyi bincike inaso inje dama".... Ya dade Yana nazarin fuskarta wadda ke dauke da tsananin damuwa yasan cewa gorin da akai Mata ne yasa dik ta shiga damuwar Nan....ita kuwa kafesa tayi da Ido Tana jiran amsarsa,...iska ya hura Mata a idanuwanta ta lumshesu Tana murmushin karfin Hali... "Dik yadda kikace haka zaayi yanzun dai nidai nidai" Dariya ta kyalkyale dashi Tana turesa "Kai baka gajiya ne?umm?' Ya kashe Mata ido yasa fuskarsa daidai Tata Yana kallonta,hannunsa daya yasa ya kawar da gashin daya rufe Mata Rabin fuska Yana Kare ma fuskarta kallo sai kawai taji saukar bakinsa Akan nata ya shiga sarrafashi tamkar sweet... ******** Da wurauri Fatima ta tashi ta kimtsa sanan ta tashesa,bacci be ishesaba haka ya juya yana murza Ido Yana kallon yadda ta dauki kwalliya tamkar wata zinariya ya mance da maganar fitarsu yana Shirin gyara kwanciya tace "Haba habeeb katashi Kar muyi latti " Dago Kai yayi cikin rashin fahimta yace "Ina" "Gidan marayu Mana"ta shagwabe fuska ....

0 Comments