ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6
ya ce, “Ke! Wa ya ce ki taba mani album? Ina ruwanki da kayana?” Ya fauce album din ya danna a jaka ya ja zif. Ya shiga zuba mata bala’i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ummi dariya kamar ta kashe ta san (borin kunya ne yake nannade shi da hauka). Ta ce, “Ka yi hakuri Ya Fa’iz ban san baka so a taba ba”. Ta dauki wasu daga cikin hotunansa ta ce, “In dauki wadannan Ya Fa’iz?” Ya dube su daya bayan daya ya ce, “Me kika ce?” Ta mike da hotunan a hannunta za ta fita, har ta kai bakin kofa ya ce, “Tsohuwa!” A kufule ta juyo don ya kirata da sunan da ta tsana a rayuwarta, amma ga mamakin Ummi sai ta ga ya yi murmushi. “Don mi kike son hotona bayan duk kun tsane ni don kawai ina gaya muku gasiya?” Ummi ta girgiza kai tana dariya, ta ce, “Allah Ya Fa’iz bamu tsaneka ba, daman can kai ne ka tsanemu, kuma mu har mun manta ma wallahi. Mun san kuruciya ne ga shi yanzu tunda ka shiga Poly ai baka cika shiga lamarinmu ba balle ka takura mana. Wani abin ma in aka ce ka yi ai ba za ka yi ba”. Ya ce, “Ko? In ku kun manta ai Hussainar taku ba za ta taba mantawa ba. Domin na zalunceta na wulakanta ta na ci mata mutunci da yawa, wanda nima wallahi ban san dalili ba. Yanzu har nauyinta nake ji saboda halin RAI da muhimmancin ZUMUNCI, kunyarta nake ji wallahi-wallahi Ummi.....” Ummi ta yi sakatoto! Tana duban sa cike da shakkar ba da Fa’izu (Abubakar) take magana ba, wani ne dai mai matukar kama da shi. Ko kuma mafarki take yi. Ta ce, “Yaya Fa’iz wai kana nufin Fa’izah?” Ya girgiza kai ya ce, “It may be itan, it may also be kuma ba itan ba.....” veces *Ban gane ba?” Ummi ta tambaya her voice is trembling (muryarta tana rawa). Ya ce, “Ba za ki gane ba Ummi, kowa ma ba zai taba ganewar ba, amma Allah ya ga zuciyata na yi nadama da dana sanin abin da na yiwa Fa’izah”. Ummi ta dan yi zuruu! Tana dubansa, ta ce, “Na tabbata na kuma hakkake cewar Fa’iza ba ta rike ka ba sam a zuci Ya Fa’iz, kullum addu’arta Allah ya shiryi Ya Fa’iz ya ganar da shi illar ‘KARYA, MUGUNTA, ZALUNCI da muhimmancin zumunci”. Fa’iz ya dafe kai ya dubi Ummi duk idanuwansa sun sauya launi, ya ce, “Yanzu Ummi duk da wadannan sunayen Fa’izah ke kallo na? Kuma haka Ummi?” Tune din muryarshi wannan karon (in subdued) a karye. Ita ma Ummin ta karaya a wannan gabar, ban da girgiza kai alamar, “A’a”. Ba abin da ta ce. Ya yi mata alamar ta tafi kawai ta kyale shi. Washe gari kowa ya shirya za a tafi rakiyar Fa’iz, sai na zari mayafi na yi wuf na shige gidan Baba Barau na buya a kitchen. Neman duniya Ummi ta yi ba ta ganni ba, dole suka hakura suka shiga mota. Daga tagar kitchen din ina hango shigar Ya Fa’iz mota, yana dan waiwaye kowacce kusurwa ta A.B Bamalli Estate kamar mai neman wani abu. Daga bisani ya shiga motar Ya Aliyu ya ja suka fita a get din. Na yi wata irin doguwar ajiyar zuciya kamar an zare min kaya a kafa, kamar kuma an sauke dutsen Dala da Gwauron Dutse daga kaina. Na yi wata irin kakkarfar ajiyar zuciya. KK KK BAYAN SHEKARA DAYA Shekarar ta zo ne da tarin sauyuka masu yawa cikin A.B Bamalli Family. Tafiyar Fa’iz da tafiyar Yaya Aliyu bada jimawa ba jami’ar Lagos yin digiri na biyu. Don haka a hutu na gaba da muka zo mun yi kewar Yaya Ali ba kadan ba. Na yi kiba na yi bul-bul na dan yi haske dai-dai misali, sai sheki da kyalli nake yi, ke kuwa babu fargabar Fa’iz ko kadan wanda shine kadai matsalata a rayuwa. A wannan hutun da muka zo ranar wata asabar ina dakin Hajjah ina sallah na jiyo sassanyar muryar Yaya Aliyu a tsakar gida yana gayas da Hajjah. Bai tambayi kowa ba, bai tambayi komai ba daga gaisuwa sai “Hajjah ina Fa’izah ne? Ban ji motsinta cikin gidan nan ba”. Hajjah ta ce, “Tana ciki, nake jin sallah take. Ka san in aka soma doka nafilfilin nan sai Allah. Ai ma hushi ake da kai tunda ka tafi Lagso ba sako ba aike balle waya”’. Ya kama kai abin ban dariya, ya ce, “Oh! Ni Aliyu Bamalli na shiga uku!! Ya yo cikin dakin da gudu-gudunsa. Hajjah ta yi dariya ta ci gaba da abin da take yi. Zaneerah ta ya da tawul din da take tsane jikakken gashin kanta, ta zaro ido ta wara hannuwa tare da daka tsalle ta dire gabana ta ce, “Yaya Aliyuuu! Muryarshi a tsakar gida Fa’izah!!” Ta yi wuf ta yi bakin kofa zata fita. Na ce, “Ke Zanirah baki da hankali ne? Haka za ki fita daure da tawul?” Zanirah ta dubi kanta ta ce, “Oh! Na gode Fa’izah, kin san Allah duk na rude sabida murna”’. Na bita da kallo a lokacin da take zurma doguwar riga a jikinta, jikinta har rawa yake yi. Ni yadda take rawar jiki a kan Yaya Aliyu da al’amarin sa, ko ni da ya fi nuna kulawarsa a kaina bana yin hakan balle irin wannan zumudin, ni haushinsa ma nake ji wallahi tunda ya tafi bai neme mu ba, ba waya ba sako. Tana kokarin fita yana kokarin shigowa, sai suka yi karo garam! Ya yi hanzarin ja da baya tare da ware ido. “Zanirah kin makance ne?” Da gudu ta nufe shi ya yi hanzarin kaucewa a hankali ya ce, “Zanirah kin girma, shekaru goma sha biyar, kada ki sake ki kara yi min irin wannan oyoyon kin ji ko?” Ko ni kaina ba don na nutsu ba da ba zan ji shi ba, domin cikin kwantaccen sauti ya fada. ‘“Wannan sai su Hanifa sune yara (diyar Baba Sadi)”. A raina na ce, “Ai ko Hanifa ba za ta yi haka ba, ita ma Zanirar ban san yau ina ta samo wannan bakuwar al’adar ba wadda sam bamu tashi da ita ba. Amma da na yi la’akari da dadewar da muka yi bamu ga Yaya Aliyu ba, sai ban ga laifinta ba, at the same time, na yi mata uzuri da ajizanci wanda dan Adam baya rabo da shi. Zanirah na dariya ta ce, “Yaya Aliyu ka rage min fa, da watanni biyar cur!” Ya ce, “Yar gari, ashe kina sane?” Bai koma ta kanta ba ya shigo ya russuna har inda nake, kamshin daddadan turarenshi ya doki masunsunata. “A roka damu Alasabbinak.’’. Na zumbura baki na gyara zaman carbina cikin hannuna na kau da kai. Cikin dariya ya sassauta murya ya ce, “Na yi laifi ne Princess? I’m so sorry. Wallahi ban yi da niyya ba....” Na kara turo baki na kau da kai. Yaya Aliyu ya yi dariya ya sa hannu cikin bakar leda ya bude, kamshin wani irin lafiyayyen balangu ya doki hancina. Na hadiye wani tsinkakken miyau ji kake mukut! Dariya ta kashe Yaya Aliyu. Ya sa hannu ya zare carbin ya tura min kunshin balangun gabana. Ai ban bata lokaci ba tuni na ja kunshin leda cinyata na juya mai baya, na manta da fushin na soma dauka ina dannawa wani na bin wani. Zanirah ta zo ta zauna za ta ci na doke hannun ta, ta ce, “Yaya Aliyu Fa’izah kadai ka sayo wa?” Muryarta abin tausayi. Ya ce, “Eh, domin shine favourite dinta, kowa ma na sayo mai abin da ya fi so a rayuwarshi”. Ya sa hannu a aljihu ya fiddo alawar cakulet mai kwakwa (Bounty) ya mika mata. Zanirah ta yi tsalle ta cafke ta yi waje, na tattara ledar namana na mike zan bita amma Yaya Aliyu ya rike gefen hijabina, gaba daya na juyo. “Wai me na yi ne don Allah Fa’iza? Na taho gari ya gari tun daga Lagos domin ki amma kike zumbura min baki?” Na bude baki cikin mamaki na ce, “DOMIN NI?’ Ya yi saurin girgiza kai, ya ce, “A’a, DOMIN KU”. Na ce, “To sakar min hijabin na gaya maka kada Hajjah ta shigo”. Ya yi saurin saki. Na koma na zauna na ce, “To don me tunda ka tafi makaranta ba sako ba waya Yaya Aliyu? Don me za ka koma makaranta Yaya Aliyu?” Ya yi murmushi ya ce, “Fa’iza ke yanzu ba makaranta kike ba?” Na ce, “To in anyi degree ba shi kenan karatun ya kare ba? Da dadewa na taba jin an ce ka yi digiri”. Ya girgiza kai “Is just the beginning Fa’izah digiri na farko shine tushen duk wani ilimi. Ilimi ba shi da iyaka, ba shi da karshe sai dai ka yi iya wanda za ka iya ka bari. Ina so na yi ilimi mai yawa ba digiri kadai ba, ko baki son wata rana in zamo Farfesa kamar Baban A.B.U? In yi gida nawa na kaina a duk inda nake so a outside ba a A.B Bamalli Estate ba cikin kauyen Giwa? In yi family mai tsari irin na Baban A.B.U? In yi rayuwa mai tsari irin ta Baban A.B.U? Ba irin ta su Baba Barau ba Fa’izah”. Ban san sanda na tuntsire da dariya ba. Na ce, “Ai ni na yi zaton don ka gaji da kai mu makaranta da dauko mu ne da zuwa mana visiting shi ya sa ka koma karatun don ka gaji da saya min nama, Zanirah (Bounty) Ummi (Kit-kat), ka gaji da kai mu shopping da koya mana karatu, shine ka tafi’’. Dariya mai suna dariya kam Yaya Aliyu ya yi ta har ya gaji, ya ce, “Fa’iza yaushe za ki daina wauta ne don Allah? Shin in tambaye ki, da can waye ya sani yi muku hidimar makaranta? Waye ya sani sai muku balangun da alawa? Waye yake sani in kula daku in ba don ina son ku ba? Na rantse da sarkin sarakuna ba zan taba gajiyawa da hidimta miki ba muddin rayuwata! Ko da bani da shi, zan yi aikin karfi da lafiyata in nemo in yi miki in har za ki yi farin ciki. Balle kuma alhamdulillahi Allah ya hore mana arziki na _ duniya_ dai-dai gwargwado, ta yadda har nake raina ‘yar hidimar da nake muku wanda har ke kike kallon ta kike kiranta hidima. Ko da duk abin da na mallaka zai kare wurin sai miki nama ba zan damu ba, saboda dalilin da har yanzu kika kasa ganewa. Kada ki kara saka wannan a ranki (wai ina yi muku hidima), kada ki kara tunanin hakan, sa a ranki wannan Dutyn Aliyu ne”. Ina wani irin murmushi mai fitowa tun daga karkashin zuciyar dan adam na ce, “Ba zan kara ba Yaya Aliyu”. 2K OK 2K 3K Washe gari muna gidan Baba Na’ibi (gidan su Yaya Aliyu) muna kallon wani wasan kwaikwayo na ANTAR-BN-SHADDAD da ABLAH, domin mu zuri’armu kaf daga shekara kasa da sha takwas, ba a kallon inafinan Turawa, na Hausa ko na India, ko na ‘yan kudu (Nigerian Film), sai hikayoyi na Larabci da Risalah, ko tarihin Sahabbai da ake yi a matsayin film kamar na Khulafa’urRashidun. Domin wannan finafinai da na zayyano a sama a ganin Hajjah duk nau’i ne na illata tarbiyyar yara da hana su mai da hankali ga karatu. Daga na_ yake-yaken Larabci (Adventure) sai zaluncin da Isra’el ke yiwa ‘yan’uwa musulmi na _ yankin Gaza, sai Islamic Channel wadanda suke nuna halin da kasashe marasa karfi ke ciki, irin su Somalia da irin tallafin da NGO’s suke yi musu, irin su ‘Human Appeal Organization’ masu daukar nauyin irin wadannan kasashe ta _ hanyar abinci, ilimi, asibiti da tufafi. Wadannan al’umma masu _ ban _tausayi abubuwa ne dake karawa yara imani da wadatar zuci. Sai ko labaran Larabci na Aljazeera, CNN, BBC. Saboda yawan kallon al’amuran Larabawa da nake, da_ sauran labaran Larabci da kallon rayuwarsu a talabijin, dadin-dadawa ana yin Larabci as (Subject) a ajinmu, sai ya kasance na iya Larabci sosai, kuma shine harshe mafi soyuwa a gare ni tun ina (Area One). Tun ina karama Allah ya dora min kaunar Alifun-Ba’un, Alifun-Arnabun, Ba’un-Bagaratun. Maryam ta dube ni muna cikin kallon ta ce, “Wai me Antaru ya ce kenan Fa’izah?’ Na fassara mata, ban ida rufe bakina ba Yaya Aliyu ya shigo. Ya samu gefen mahaifiyarshi ya zauna, ta ce, “Ya ya dai Yayansu? Na ganka rather moody? In ce ko ka dauki abincinka ka ci?” Ya dan yi tsaki ya ce, “Mama na sha kunun alkama fa a wurin Hajjah yanzun nan”. Ta dube shi tsaf, cikin babbar murya ta ce, “Aliyu!” Da hanzari ya dago ya dube ta. “Na gaji kullum magana daya ta ki ci ta ki cinyewa. Yanzu kamar kai Aliyu sai an rarrasheka ka ci abinci za ka ci, sai ka ce wani karamin yaro, da gangan kake wasa da lafiyarka, to na daina, sai dai ka kashe kanka kai kadai, wallahi ka kwanta ciwo ko hanyar asibiti ba za ka ganni ba. Ko da yake in ka kashe kanka ai kai ka jiyo, wa ka yiwa asara?” Na juyo daga kallon T.V na ce, “Mama mu mana? Mu aka yiwa asara”. Zanirah ma ta ce, “Tabbas mu ya yiwa asara, we cannot, never found a caring brother like him, Yaya Aliyo don Allah daure ka dinga cin abinci in ka mutu mun shiga uku’. Na ce, “Mun shiga uku ko mun shiga tara?” Ummi ta ce, “Har mun lalace’’. Zanirah ce ta mike ta yi kitchen da zafin namanta, ta shako plate da dankali soyayye da murtukekn kwai, ta zo ta zauna tsakanin Mama da Yaya Aliyu kasancewar suna zaune kujera daya ne mai cin mutum uku. Cike da kulawa ta mika mishi, kana cikin muryar lallashi da kulawa ga karamin yaro in ya ki cin abinci ta ce, “Yaya Aliyu don Allah ka ci”. Gaba daya aka kwashe da dariya har Maman dake bambamin fada, babu shakka yadda muke kula da Yaya Aliyu da hidimarsa, da yadda shima yake kula damu da al’amuranmu, yana yi mata dadi, don ko Maryam da suke ciki daya ba ta kulawa da al’amarinsa kamar yadda muke masa, haka shima. Ga shi tana masifar son Yaya Aliyu kamar ba dan fari ba. Ita cikakkiyar lauya ce mai zaman kanta, sam ba ta irin kawaicin Momina, mu’amalarta da Yaya Aliyu kamar ta Yaya da kaninta mai binta da suka fito ciki daya. Hakan ba karamin bani sha’awa yake ba, in yi ta dakacen ina-ma a ce nice. Na taso tsam daga inda nake zaune zuwa garesu na ce, “Mama tashi ki bamu fili in bai ci ba dura zamu yi masa”.

0 Comments