ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3
yaro baya jin shi sai ya girma”’. “To ai Zanirah ta girma in ji Hajjah, tun ranar da jini ya ziraro ta kafarta Hajja ta ce ta girma, to ita ka gaya mata mana?” Ya yi dan dummm! Zanirah ta soma kumbura hanci da hurashi ta ce, “Yaya Aliyu wallahi karya take Ummi ce?” Ummi ta ce, “Wallahi ita ce”. A dai-dai lokacin da Yaya Aliyu ya shigar da hancin motar A.B Bamalli Estate, ya yi kyakkyawan horn yaran dake kusa a kofar flat din Baba Barau suka rugo suka fidda kayan a boot suka shigar mana dasu gida. Yaya Aliyu Boys Qtrs dinsu ya wuce bai kara kula mu ba. Su Abba na jidon kaya suna ihu wai za su ci cornflakes din ‘yan bording school. Na ce, “Wallahi duk wanda ya bude mana kaya sai na kabari ya fishi jin dadi”. Ina kwance gadon Hajja na ji shigowar su Ummi, suka shigo da kaya niki-niki, Ummi cike da tsegumi take ce da Hajjah, “Wai Hajja ki duba ki ga duk yawan kayan nan da muka shigo sai da Yaya Aliyu ya sake sayen kwatankwacinsu wa Fa’iza ita kadai ranta”. Zanirah ma ta ce, “Kuma Hajja baki gani ba, wai don dan fadan nan da Ya Fa’iz ya yi mata dazu kafin mu fita ya yi ta lallaminta tana masa wulakanci da kada ido, ita ba ta yarda ba babba”’. Hajjah ta yi kamar ba ta ji su ba ta shiga duba kaya, ta ce, “Ya ban ga kwaki ba bayan kun ce bakwa son wanda na sayo fari kuke so?” Ummi ta ce, “Tab! Waye zai sha miki kwakin? Ki jimu da tsohuwa da neman ta da zaune tsaye”’. Hajjah ta dauki mafici ta yi kanta ta runtuma da gudu. Hajjah ta ce, “Ja’ira, gobe dai kun bari da ‘yan jikokina mu _ huta bakinmu alaykum. Haba! Yara uku duk kun bi kun isheni kamar ina zaune da zaratan “‘yammata”’. Ummi ta zo ta kwanta a gefena ina kwance rigingine na yi nisa cikin tunanin irin kulawar da Yaya Aliyu ke yi mani. Hakika shi dan’uwa ne mai matukar kirki da dabi’un kyakkyawar mu’amalar zumunci. A lokuta da dama ina kwatanta kirkin Aliyu da wani cikin yayyenmu, amma ban ga kwatankwacin shi ba. Halinsa daban, simplicity dinsa daban da dukkan mazan zuri’armu. To amma kulawarsa gareni ta zarta wadda yake yiwa kowa, babban misali su Zanirah da tare muke rayuwa yana fifitani a kansu. Sai a hankali nake jin Yaya Aliyu na kwanta min a zuciya saboda kyawawan halayensa da kulawar da yake yi mun. Tunani na ya gangara ga abin da ya fadi dazu na cewa, wai ba zai iya barci idan ina fushi da shi ba, saboda abin da yaro baya ganewa sai ya girma. Shin mene ne wannan abun? I’m quite curious... Kamar Ummi ta san abin da nake tunani, ta yi murmushi sai cewa ta yi, “Princess har an soma tunanin Yaya Aliyu? Ayi hakuri dai muje kwalejin mu gama, in kuma auren za ayi sai a fada mana mu fara shiri’”’. Na mike a fusace na soma dukanta ina yakushinta ta sa ihu, nan da nan Hajja ta shigo za ni na zamewa kamar ta fadi. Ta ce, ““Wai ke wacce irin masifaffiyar yarinya ce ne Fa’iza? Ke daya duk kin buwayi gidan nan, daga ki yi da wannan sai ki koma ki yi da wancan?” Na sa kuka na ce, “Hajjah cewa fa ta yi wai ina tunanin aure, ‘yar iska ta dauke ni ko me? Bayan ni tunanin su Walida nake yi’. Hajjah ta ce, “To yi hakuri wasa take miki, ke kuma Ummi kada na_ kara _ jin makamanciyar wannan maganar ta fito daga bakinki zan saba miki fiye da zaton ki’. Ta juya ta fita. Zanirah ta bimu da kallo kurum, sai dai na lura tun shigowar ta dakin akwai abin da ke damun ta. 2K OK OK ok Ranar da zamu tafi FGGC Gusau ta kama litinin ashirin ga watan Nuwamba, don haka sanyl ya yi tsanani ainun. Tun asuba muke ta shiri, murna kamar kanmu aka fara zuwa makarantar kwana. Mun yi tsaf cikin uniform abin sha’awa. Na hade gashina cikin (hair-bound) kalar tsanwa cikin sayayyar Yaya Aliyu ne. Hajja dake azkar din safiya a gefe bisa shimfidar sallarta ta shafa addu’a ta juyo ta dube mu. “Yanzu duk wannan azarbabin da kuke wa kuke zaton cikin yayyunku zai mike cikin wannan azababben sanyin ya kai ku makarantar?”’ Na ce, “Wallahi babu kam Hajjah, ai Isa direba ba zai ki ba. Ko ya kika ce Ummie?” Ummi ta ce, “Kwarai’”’. Zanirah ma ta shirya cikin uniform na GGSS Giwa, kasancewar ita makarantar ta daban ta gwamnatin jiha mune a gwamnatin tarayyah. Riga da zani da hijabi shudi da fari, ta yi kyau abinta. Na tuna da banki na da nake tara kudi a ciki da na baiwa Yaya Aliyu amanarsa tun wancan satin. Na ce, “Hajjah ko Yaya Aliyu ya tashi yanzu? Bankina”. Hajjah ta ce, “Tabdi! Aliyu makiyin sanyi ko na ruwan sha shine zai mike miki yanzun? Karfe shidda?” Na janyo farin cambas na daurawa kafata na yo tsakar gida da niyyar daukar suwaita ta a kan igiya da na shanya tun jiya. Cikin mukumukun sanyin nan ma’abocin hazo da ya lullube sararin samaniya, sanye da bakar shirt da shudin wando jeans ya daura ‘thick-coat’ doguwa har gwiwarsa, hannayensa duka zube cikin aljihun coat din domin kare sanyi, yana jingine jikin tagar dakin Hajjah. A hankali na ambaci sunansa cikin mamaki.... “Yaya Aliyu?” Ya lumshe idanunsa da suka kumbura suntum saboda rashin isasshen barci. “In kun kammala Fa’iza ku fito in kai ku, ku nake jira tun bayan fitowata masallaci sallar asubahi”’. Ban ce komi ba na karasa na dauki suwaita ta na koma ciki. Da na gayawa su Ummi Yaya Aliyu ne zai kaimu duk sun yi mamaki suma, Hajjah ba ta ce komi ba. Zanirah muka fara rakawa kasancewar nan wajen gari ne, bayan an kammala mata (registration) an ba ta hostel an hadata da wata prefect muka juyo zamu tafi, idon Zanirah ya cicciko da hawaye. Ta ce, “Yanzu Yaya Aliyu don Allah kwana nawa zan yi a nan?” Muka yi dariya duka ganin yadda hawayen ya soma malalowa a kundukinta. Yaya Aliyu don ya kwantar mata da hankali ya ce, “Haba Zanirah? Ga ki ga gida meye abin damuwa ne? Bayan haka ma na yi miki alkawarin duk sati biyu zan rinka zuwa in ganki, zamu ke zuwa miki visiting duk wata har da Hajjah”’. Ta soma sharar kwalla muka rungume juna, sannan prefect din da aka hadata da ita ta ja hannunta suka shige ciki. Bamu tafi ba sai da muka ga kulewarsu. A kan hanyar Gusau Yaya Aliyu ke ta tsokanarmu ni da Ummi, sai dai jiki da bakin kowaccenmu ya yi sanyi, kai baka ce ‘yan karadin nan na Hajjah bane masu kama da jiniya don kwakwazo a falon Hajjah ba. Wala’allah hakan na da _ nasaba_ da rabuwarmu da Zanirah da tunanin sabuwar rayuwar da zamu je mu taras, ta doka da oda ba irin ta gida gaban kakarmu abin son mu Hajjah ba. Ya tsaida motar a wani masallaci muka yi sallah, ya ce, “Ku dan jirani ko?” Ya tsallaka daya titin ya dawo mana da gasasshen nama da gorar ruwa da ta pepsi, muka ci muka ci gaba da tafiya. Ummi na ta yi min hira na ki kula ta saboda kewar Zanirah. Ta yi tsaki ta ce, “Aikin banza ana ta yi miki magana kin yiwa mutane shiru ke wace ce?” Na ce, “Nice Pirincess Fa’iza Bamalli”. A hankali yadda Yaya Aliyu bai jimu ba. Ummi ta ce, “Umh! Ya Aliyu ka ji yau Fa’izah ta fadi sunan da ka rada mata?” Idonshi a titi ya ce, “Ki bari don Allah?” Ta ce, “Wallahv’. Ya ce, “Kara fadi in ji Fa’iza”’. Na sanya fuskata cikin tafukana ina dariya. Ni yadda Yaya Aliyu ke nuna mana kauna da kulawa irin haka sai nake jin zuciyata na kara kaunarsa a kowacce dakika. Ina ma a ce Yaya Aliyu ya ce yana sona? Ina ma ya zamo miji a gare ni? Da wace irin sa’a zan yi a rayuwata? Kamar ya san kallon shi da tunaninshi nake, sai kawai ya juyo muka hada ido, na yi saurin juyar da kaina ga titi. Ya yi murmushin da ya motsa kyakkyawan sajen da ke gefe da gefen fuskarsa, ya ce, ‘“Kallon na mene ne?” “A kan me zan kalle ka Yaya Aliyu?” “Nima abin da nake son sani kenan Fa’iza, dalilin kallon?’ Na zumbura baki na hura hanci. Ya yi dariya ya kara speed din motar, bamu kara tsayawa ba sai a FGGC Gusau. Bayan ya gama mana duk shige da fice da ake yi daga ofishin vice zuwa na principal, aka bamu hostel daki daya ni da Ummi, amma ba aji daya ba. Ina A tana B. Sai da Yaya Aliyu zai tafi Ummi ta ce, “Yaya Aliyu mai yasa aka raba mana aji?” Ya yi murmushi ya ce, “Saboda ku yi karatu sosai in bakwa ganin juna akai-akai, amma idan an hada ku za ku shagalta da hirar gida ku ki yin karatu”’. Ummi ta ce, “Wa ya ce dasu gidanmu daya? Ga sunanmu ba iri daya ba, ni Khadija Sabi’u Giwa, ita Fa’izah Ahmad A.B Giwa?” Ya nuna mata tsagin mallancinta, ya kuma ja dogon karan hancinmu da hannayenshi hagu da dama, ya ce, “Kowa ya ganku ya ga wadannan to ya san tushenku daya, kuma in har bazazzage ne to ya san zuri’ar A.B ne”. Jinjina kai na yi cikin gasmuwa da kalamansa. Bayan Yaya Aliyu ya mana sallama, har ya juya zai tafi sai kuma ya juyo, idanuwanshi sun sauya launi daga farare sol zuwa na damuwa, “FA’IZAH!” Da wata murya tamkar ba tashi ba. A hankali na juyo na ce, “Na’am Yaya Aliyu!” Ya ce, “Zo”. Tare da yafito ni da hannun daman shi. Na saki hannun Ummi na je gare shi muka tsaya muna kallon juna kamin in sadda kaina kasa a dalilin nauyin da kwayar idanunshi yai min. “Yan dakika kamin ya ce, “Ki daina kazanta, ki aje wasan da ke kanki ki tsaya ki yi karatu, ki zama mai kokari irin Zanirah kin ji ko?” Idona taf da hawaye na ce, “Yaya Aliyu kazantar me nake yi? Mene ne KAZANTA?” Bai bata lokaci ba ya dora da cewa, “Kula da tsaftar jikinki, kamar yadda zuciyarki take da tsabta. Ubangiji yana son tsabta ta yadda har ya mai da ita cikon addini. Tsafta ta hada da tsaftar jiki, da ta suttura, da zuciya baki daya. Tsaftar jiki ita ce, kula da baki (yin brush a kalla sau biyu a rana, wato safe da dare). Tsaftar fatar jiki (yin wanka da sabulu mai kamshi shima a kalla sau biyu a rana, da yawan amfani da sinadaran dake kashe warin jiki na halitta) (body odour), wadannan sinadarai duk na sanya su cikin sayayyar da na yi miki (mouth wash, deodorant spray da rollon) da turaren fesawa a tufafi. Tsefe kai da wankeshi da yin kitso duk sati, kina jina Fa’iza ta?” Na daga mishi kai ba tare da na iya duban shi ba sakamakon wata matsananciyar kunya da ta taso ta Yaya Aliyu ta lullube ni a dalilin kalaman shi. Ba tare da ya saurari cewa ta ba ya ci gaba da cewa, “Don Allah Fa’za ki tsaya ki yi karatu sosai kin ji? Wallahi bana son na ashirin din nan da na talatin da kike dauka a jarrabawar firamare ko na goma sha kaza..... Na dago na dube shi idanuna fal da hawaye, na ce, “Insha Allah Yaya Aliyu zan dage ko don ka ji dadi ka daina jin haushi in Ya Fa’iz ya kirani Jaka! Insha Allahu ba zan kara kaiwa na ashirin ba ma har in _ kare makaranta..... insha Allahu ba zan baka kunya ba.... insha Allah sai ka yi alfahari dani fiye da yadda Ya Fa’iz ke alfahari da Zanirah!” Ya yi murmushi ya ce, “Alkawari....?” Na ce, “Eh, alwakari, kawo ma mu kulla”’. Na bashi dariya sosai kafin ya miko min yatsarshi ta karshe ta hannun dama, na mika masa nawa muka_ sarke. Sannan muka kyalkyale da dariya ba tare da Ummi ta san abin da ya bamu dartya ba, ta janyo ni ta baya. Yana daga mana hannu muna daga masa har sai da muka kule cikin hostel. Rayuwarmu a_ makarantar Gwamnatin tarayyah ta “‘yammata dake Gusau ta ci gaba da tafiya yadda ake so, mun dukufa, ba ma tamkar ni da bani wasa da alkawari ko ya ya yake, fatana Allah ya fidda ni kunyar idanun Yaya Aliyu in kai mishi sakamako mai kyau. Duk da ba class daya muke da Ummi ba amma a hostel ko da yaushe muna tare, tare muke tafiya school arena, class, prep da hostel, dining da sauran_ extra-carricular activities da makaranta kan shirya bayan working time. Bamu yarda mun yi kawa ko guda daya ba, tsakaninmu da kowa sallamar musulunci da abin da ya hadamu. Mun samu exposure na zama da mutane kala-kala ‘yan garuruwa da yare daban-daban, masu halaye da dabi’u daban-daban. 2K 6K Gabatowar karshen zangon karatu na farko muka fara gwaji wato (test), inda na kara zage damtse iyakar iyawata na yi dan abin a zo a gani. Wannan ne dalilin da yasa kafin zuwan jarabawa na dan rike wasu abubuwa da yawa, don haka da muka fara sai ta zo min da sauki, na cinye darasin Arabic da English tsaf, sauran subject din dai gasu nan dai la ba’asa ya fi la shai’in in ji Larabawa. Su Hajjah sun zo mana visiting (ziyarar dalibai) har da su Inna Kubra. Ranar hutu da murnar mu muka nufi bakin gate a zaton mu Yayanmu Aliyu ya zo daukar mu, don baki ganni ba fuska kamar gonar auduga don murmushi. Ina rike da (report card) dina wanda nake kyautata zaton na yi abin kirkin da zai faranta ran Yaya Aliyu, na sauke nauyin alkawari na yi abin a zo a gani. Amma murnata ta daka tsalle ta burma ciki sakamakon ganin mutumin da na tsana da gani a rayuwata, mutumin da na tsani jin muryarshi da ganin fuskarshi mara alheri a gare ni, dan uwan da da za a bani wuka a ce in caka mishi ba komai da na yi gaggawar aikatawa. FA7EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA. Sanye da makubar shadda ‘getzner’ dinkin samarin garin Kaduna masu ji da tashen samartaka, bakar dara mai gezar bakin gashi ya kara haske sosai ya yi fresh ta yadda ko ni da bani son shi a duniya na san Fa’ezz namiji ne abin so ga kowa, ba ga mata kadai ba har maza jinsinsa ba za su bar yiwa kansu fatan zama ko dakacen komawa kamar shi ba. Jingine jikin motar Yaya Aliyu_ kirar ‘Picanto’ (Kia), fuskar nan dinke babu alamun rahama kamar kullum, na damko hannun Ummi kam, kirjina na dukan tara-tara ba ma uku-uku ba. Fuskar Ummi kamar an aiko mata da Manzon rahama ta saki hannuna ta sheka da gudu aguje wai za ta rungume shi. Ya kuwa doka mata tsawar da ta sa ta tsugunnewa a kasa cikin gigicewa. Ganin yadda ya tsoratata ya gigitata ya yankwanata a gaban sauran daliban da ke gefe, ko me ya tuna? Ya yi dan murmushi gajere wanda ya fidda lotsawar gefen kuncinsa na dama. Ya ce, “To ai ke ce abin naki babu kan gado tsohuwa (sunan da suke tsokanarta don ita ce mai sunan Hajjah, shi kuma su Yaya Aliyu su ce mishi tsoho kasantuwar shi mai sunan marigayi Abubakar Giwa (A.B Bamalli Giwa). Yace, “Kai! Ummi ba a girma”. Sannan ne ta iya mikewa a darare. Ni dai ina daga gefe hannuwana sarke a kirji ina kallonsu, a zuciyata in ban da Allah ya kara ba abin da nake yiwa Ummi. Ya budewa Ummi kofa ta zauna a gidan gaba ya rufe, yana sanya kayanmu a boot din mota ya juyo inda nake tsaye ya dube ni, ina tsaye jikin bishiya kawai ina kallon su. Ya rufe boot din motar ya shiga mazaunin shi zai ja motar. Ummi ta ce, “Ya Fa’iz, Fa’iza fa ba ka ganta bane?’ Wata muguwar harara ya yi mata, ya ce, “In na ganta sai me? Sai me zan yi? Ita ba ta ganin mutane? Ba ta san ta gaishe su ba ko don UWARTA! Ta koya mata rashin tarbiyya irin tasu ta kabilu”’. Sai kawai ya ja motar ya badeni da kura. Ummi kira take “Fa’iza! Fa’iza!! Fa’iza!!!” Amma ko sauraron ta bai yi ba. Na durkushe a nan na soma kuka, na yi kuka har muryata ta dashe. Na daga kai na dubi daidaikun daliban da suka rage kwata-kwata babu ‘yan Kaduna, Zaria balle garinmu. Daga ‘yan Kano sai ‘yan Jigawa, sai ko dai-daiku daga jihar Gombe da Adamawa. Na dora hannuna aka na rafsa kuka. Duk dokina na son ganin Hajjah, Zanirah da Yaya Aliyu ya gushe, sai wani irin tukuki da zuciyata ke yi. Wannan wace irin kiyayya ce Ya Fa’iz ke min? Wace irin kiyayya yake yiwa mahaifiyata da ta shafe ni? Wannan ma ai rashin imani ne ba kiyayya ba. Duk irin kin da nake wa Fa’iz babu yadda za ayi in baro shi a jejin da na san ba shi da kowa, a gari mai nisa da babu kowa nashi. Na rasa inda zan sa kaina don bakin ciki, kawai sai na samu gefen bishiyar darbejiya na share na kwanta a wurin ina kuka. Ina addu’ar Allah ya kashe Fa’iz in huta. “Ke me kike a nan a kwance a kasa? Ko ba a zo daukar ki bane?” Muryar wata malama ta doki dodon kunnena. Na dube ta idona jage-jage da hawaye na ce, “Eh”. “Yar wane State ce ke?” “Na zo ne daga Giwa”. “Giwa? Giwa ta jihar Kaduna? Oh! Ke Bamalliya ce ko?” “Eh”. Na amsa a gajarce. “Amma kin yi nisa sosai, yanzu ya za ayi kenan?” Na ce, “Zan kara jira a nan zuwa yamma na san za azo min”. Ta ce, “Ba zai yiwu ki yi ta zama ke kadai a nan ba, ki tashi ki shiga daga Library tare da yaran can ‘yan Niger State, kinga za ki fi hango duk mai shigowa ki fidda naki”’. A sanyaye na ce, “To”. Na mike na kade jikina na dauki jakar littattafaina na rataya, da yake duk sauran kayan sawarmu suna cikin kayan da Ummi ta tafi dasu. Ban dade da zama ba barci ya dauke ni a kan daya daga cikin kujerun labiraren, na farka ne karfe biyar na yamma sakamakon tashin da wata yarinya ta yi min wai in tashi in yi sallar Ja’ asar. Sai kawai na fashe da kuka ganin yadda duhun yamma ya lullube sararin samaniyar subhana. Na bita toilet din dake jikin labiraren muka dauro alwala muka yi sallah, ni azahar ma sai a lokacin na yi ta. Har na idar da sallah kuka nake. Ta ce, “Ki daina kuka, ai tabbas za a zo daukar mu ne, kema da baki da _ nisa kamarmu? Ai iyayenki babu yadda za ayi su manta dake’”’. Cikin kuka na ce, “An zo an dauki Ummi, ni tafiya ya yi ya barni, in Allah ya yarda ba zan dawo makarantar nan ba....” Shigowar daya daga cikin masu_ gadin makaranta yasa muka yi shiru muka zuba mishi mayunwatan idanuwanmu da yunwa da damuwa suka hadu suka jeme su, ya kira yarinyar nan wadda da alama ta girmeni cewar ta zo an zo daukar ta daga Adamawa. Ta fita tana daga min hannu har ta kule. Na kifa kaina cikin cinyoyina na ci gaba da kuka a hankali, ban san sanda sarkin barayin ya Zo ya Sake sace ni ba. Karfe bakwai na magariba na_farka sakamakon azababbiyar yunwar da ta sake murda min ‘ya’yan hanjina, don saboda dokin zuwa gida ko karyawa(break fast) bamu tsaya mun yi ba saboda tunanin tuni Hajjah ta gama shirin karbarmu da hadadden girkinta. Na dafa cikina da hannuna daya na runtse idona da karfi, ganin yadda duhun dare ya mamaye sararin sama, hawaye suka ci gaba da yi min lugude a fuska. Hannun mutum na ji ya cira ni tsaye, na bude ido firgigit na mike a razane cikin fadin ‘“Wayyo Allah..... wayyo Hajjah....” Abinki da cikin da ba komai, sai hajijiya ta kwashe ni yuuuu! Gaba daya na fada ga mutumin da ke tsugune a gabana, na daddage na kara sakin ihu.... “Wayyo Hajjah na shiga uku na lalace.... na mutu!” Ya rungumeni sosai a jikinsa yana fadi cikin tattausar murya irin ta marasa koshin lafiya, “Relax, relax Fa’iza, relax”. Na dauki lokaci ina tunanin mai muryar, kwakwalwata ta shiga tariyo min inda na san mai murya mai taushi da rashin amo. In ban yi kuskure ba zan iya cewa ta YAYA ALIYU CE.... YA YA ALTYU HAIDAR NA’IBI A.B GIWA. Na lumshe idona na dan lokaci, bugun zuciyata na saisaita da zazzafan jikin Aliyu, zuciyata da ta yi zafi na yi min sanyi kadankadan. Tsayin minti biyar Yaya Aliyu na rike dani, ya ce cikin kankanuwar murya, “Fa’izah are you ok?” Na gyada kai, ya sake ni muka mike a tare yana rike da hannuna. Ya dauki jakar litattafaina da daya hannun nasa na hagu muka fita daga dakin karatun, ya bude gidan baya na shiga, ya fiddo cooler din abinci ya bude, kamshin girkin Hajjah ne ya doki hancina, ba girkin cikin gida ba, wannan girki ne da take yi lokaci zuwa lokaci da hannunta, da na dade da sani ya baibaye ni, ya tado min tsohuwar yunwar da na wuni da ita. Yawun bakina ya wani irin tsinke tun kamin in kai lomar farko sanda Yaya Aliyu ke zuba min a farantin cin abinci (plate), dafadukar shinkafa ce da aka yi rabinta da zallar tsokar kaza da ganyen alayyahu da kabeji. Ya bude wata foil paper din ya _ fiddo gasasshen naman nan na kan hanyar Gusau da ya saya mana a hanya a zuwanmu, duk ya ajiye min ya rufe kofar ya shiga mazauninshi ya ta da motar muka soma tafiya. Bayan ya miko min robar ruwan swan mai sanyi ya ce, “Kina iya kwanciya idan kina jin barci in kin gama”. Da gudu ya fizgi motar bayan ya daga ma masu gadi hannu ya kuma yi signing shaidar cewa an dauke ni. Amma fa ya sha fada daga malamin da ke kula da shige da ficen dalibai, har ya bawa uku lada. Magana daya yake fadi masu su yi hakuri ba laifinsa bane. A yayin da wata danja ta tsai damu kusa da wata fitila mai hasken gaske, garin kallekallena mai nuna ciki ya dauka na fara dawowa hayyacina, na dubi hannun Yaya Aliyu wanda ke bisa giyar motar, allurar karin ruwa na gani soke jikin jijiyar hannunsa jini na diga amma bai kula ba, tukin shi kawai yake. Da na kura ido sai na ga hanyar karin jini da wata siririyar allurar ita ma soke duka a hannunsa ya bi fatar jikinsa ya kwanta. Na dube shi a razane domin tun zuwan shi ban ga fuskarshi ba, ya rame sosai ya yi duhu ainun. Na daga murya da karfi cikin tashin hankali na ce, “Yaya Aliyu ka tsaya”. Ba tare da ya juyo ba, haka nan ban ga annuri a kyakkyawar fuskarshi ba ya ce, “A kan me zan tsaya? Bakya ganin tafiyar dare zamu yi?” Na ce, “Ni dai na ce ka tsaya ko? Baka ganin hannunka yana jini ne?” Ya ce, “Babu komi wannan, kina so mu yi kwanan hanya ne?” Na ce, “Eh, mu yi ba komai”. Maimakon ya tsaya sai ma ya kara ware speed zuwa (200), kada ki ga yadda ‘yan idanuwana suka yo waje, suka yi kwalakwala. Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu baka da lafiya.... you are bleeding....” Ya ce, “Don Allah don Annabi Fa’iza ki saurara min, da me zan ji ne? Insha Allahu lafiya zamu je gida babu abin da zai faru sai wanda Ubangiji ya riga ya kaddara”. “To ka tsaya in cire maka allurar...” “Na ce ki barshi ko dole ne?” Yadda ya yi min maganar cikin tsawar da bai taba yi min ba ya sanya hantar cikina kadawa,

0 Comments