ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 2

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 2
Nima dama na fi son gidan Hajja, ko don su Zanirah. Sai muka dunkule mu ukun nan muka bude rayuwar da ta caza kwakwalen iyayenmu a gaba da kakarmu Hajjah. Ta yadda babu ranar Allah da za ta fito ta fadi bamu bar abin fadi ba, domin dukkaninmun nan kowacce da halinta, muka kuma hadu da maganinmu Ya Fa’iz ta yadda babu ranar Allah da ba zamu barta ba tare da Hajjah ta yi shari’a ko rabon fada a cikin ta ba. Ba zan manta ba, a ranar da zan koma Giwa ban iya na yi barci ba saboda doki da murna, da asubar fari kuwa na shiga bubbugawa Babanmu kofa ya fito mu tafi Giwa kafin su Zanirah su tafi makaranta. Don haushi Momi fitowa ta yi ta mammake ni ta kuma ce ba za a tafin ba sai sha biyun rana. Haka na wuni ina duba agogo ina zumburar baki, domin dai har sai da Baban ABU ya shiga cikin makaranta ya fito sannan muka taho Giwa (makyankyasarmu). Muna zuwa kuwa na gayawa Hajja abin da Momi ta yi min, ta ce (ya yin da ta rungume ni) “Ki barta daga yau ganinki ma sai ta cike form, tunda ba ta sonki ni ina sonki. Da kafarta za ta zo neman ki, ki zuba ido”. Ni kam na san abin da ba zai taba yiwuwa bane Momin ABU ta wanko kafa ta zo Giwa domin ni, Sai in tata ce ta kawo ta. Na ce, “Hajja ina su Zanirah ne? Tunda na zo ban ji duriyarsu ba’. Ta ce, “Suna Islamiyya yanzu za ki gansu, kema in Allah ya kaimu gobe Babanku na Giwa (Baba Barau) zai amso miki form daga boko har Islamiyyar ku dinga tafiyar ku tare”. Na shiga tsalle ina murna. Daga nan na shiga kitchen din Hajja na soma bude kuloli da kwanuka ina tsame namomin dake kan abincin ina cinyewa, Hajjah na falo ba ta sani ba. Ni Allah ya halicce ni da shegen son nama kamar mage, Momin ABU kan ce kamar mayya. Don haka ko da nake Zaria Hajja kan sa ayi mani dambun nama mai yawa ta aike mani cikin samira duk sadda Babanmu ya Zo gaishe ta. Dai-dai sanda na bude wani madaidaicin (food flask) ruwan kasa Hajja ta shigo. Na kai hannu zan dauke cinyar kazar dake kai Hajjah ta rike hannuna tana murmushi, ta ce, “A’a, an cinye na kowa to ban da na Hafizina, haba Fa’iza? Don ya ga naman nan tun kafin a dafa shi ba zai zama haramiyarsa ba, dole ne ya ci cinyar kazar nan”’. Na dube ta rike da murfin flask a hannu daya, daya rike da cinyar kaza cikin mamaki na ce, “Hajja waye kuma Hafizi da ya fi kowa da za a sawa kowa abinci a kwanon samira shi a zuba mishi food flask?” Hajja ta ce, “Fa’izu mana, dole ne a girmama Hafizin Qur’ani.Balle Fa’iz da duk ya fiku sona, ku baku yi min sai dai in muku, Fa’iz fa? Naman nan ko idan kika sake kika ci in dai Fa’iz ne sai kin amayo shi’. Na soma yagar cinya ina ci abuna, na ce, “Hajjah ai dama ke kike daure masa yake cin zalin mutane, don bakya ganin laifinsa, kina fifita shi a kan kowa”’. Hajja ta ce, “Ba na gani din, na fifita din”. Na cinye nama na bi lafiyar gado, ba jimawa barci ya kwashe ni, Hajja ta shiga harkokinta. Hayaniyar su Ummi da Zanirah ce ta tada ni.... “Ehu! Fa’iza? Don Allah Hajja da gaske? Da gaske kike Hajjah ta dawo nan da zama?” Ban ji amsar da Hajja ta basu ba, Zanirah ta fyallo a guje ta daka min duka a baya, na tashi wurgigi a firgice, sai kuma muka dafe juna muna kyalkyatar dariya. Bayan sallar isha kowacce ta bude kwanonta za ta ci abinci, Ummi ta ce, “Shegiya Fa’izah dama tunda na ga kwanukan nan lami na san kin zo garin”. Zanirah ta ce, “To meye don ta ci namanmu bayan kin samu ma ta zo? Da kafin ta zo ba cewa kike dama Fa’iza ta zo hutun nan muje muyi shi gidan Baban Kaduna ba? Wai inda ita tafiyar tafi daxi? Amma yanzu daga zuwan ta kin fara yi mata korafin cin nama?” Ummi ta harare ta, ta ce, “Ka ji ta kamar gaske sai wani kakkare ta kike, dama ban san halin bane, gobe ne zuwa jibi za a fara rabon dambe tsakaninku”’. Dai-dai lokacin Fa’iz ya shigo yana sanye da ruwan madarar jallabiya da carbi a hannunsa, farin yaro tas kamar haifaffen Da’ifah, matashi mai garin jiki irin na zuri’ar A.B Giwa. Hancin nan mikakke har baka, kanshi akwai tarin suma. Gefe da gefen fuskarshi tsagin mallancinshi ya fito radau, dogo mai tsayi da kafadu tun a wancan kananan shekarun. Da gani daga masallaci yake rike da tasbaha a hannunshi na dama. Shigowar shi ta katse Ummi da Zanira daga musun su, ya wuce ko kallon mu bai yi ba kai tsaye zuwa kitchen ya dauki filas dinshi ya fita. Jim kadan sai ga shi ya dawo a fusace, ya dangwara min ma’adanar abincin a cinya yana zazzare fararen idanusan wadanda tun a wancan lokacin suke da wata irin baiwa ta kwantaccen ruwa kamar hawayen da bai kai ga zubowa ba a cikinsu, da babbar murya ya ce, “Ke kwalamammiya amayo naman da kika ci ko billahillazee in yi kuli-kulin kubra dake yanzu a gidan nan, in lallasa ki dukan da uwarki ba ta taba yi miki ba”. Na ma rasa me zan ce don mamaki da takaicin ambaton uwata da ya yi, haka Ummi da Zanira sunyi wuri-wuri. Ya ci gaba da magana cikin bala’i. “Kazamar banza mai kashi a wando, wa ya ce ki sa min kazamin hannunki cikin abincina? Tunda ma kika saka wannan kazamin hannun naki wanda ya saba yin dama-dama da kashi cikin fo ba zan ci abincin ba....” Ya daga kwanon shinkafa da taliya da miya ya zazzage min a tsakar kaina, ya ja dogon tsaki ya wuce yana cewa, “Dama dai kwalamammiyar nan ba ta zo gidan nan bane za a tadda kwayar nama cikin abinci. Ni kam shekarar bakin ciki ta zo min in dai da wannan mai kashi a wandon zan zauna cikin gidan nan. Mtsw!” Ya yi ficewarsa yana ci gaba da bambamin fada da muryarshi mai karyayyen harshen larabawan Hijaz, Hausar shi ba ta fiye fita sosai ba. Na fashe da kuka nan take, don ni babu abin da na tsana a rayuwata irin a ce min mai kashin wando (da gaske mai kashin wandon ce a baya, har na kai shekara biyar ban san idan na ji poo-poo in dauko fo in hau ba, sai dai in saki abuna a wando. Hajja da Momi sunyi fadan har sun gaji, kuma a wancan lokacin babu pampers sai napkin, haka su Inna Kubra dake gidan za suyi ta aikin kashi da yi min wanka a famfon wajen wanke-wanke). Tun a wancan lokacin ne bama ga maciji da Fa’iz, kasancewarshi mai masifaffiyar tsaftar gaske da kyankyami. Ya dauki tsana da hantarar duniya ya dora a kaina, duk inda ya ganni sai tsawa da raraka yana toshe hanci. Ban samu sa’ida a zaman gidan Hajja ba sai da Fa’iz ya wuce babbar sakandire a Saudiyaya. Su kam su Zanira dariya ce ta kama su suna makewa bayan wucewar Fa’iz, don sun san halina in ina cikin fushi kayi min dariya a kanka zan huce. Da na kai karar abin da Fa’iz ya yi min wurin Hajja a uwar dakinta tana lazimi cewa ta yi Allah ya kara, ai na gaya miki amma da yake kunnen kashi ne dake sai da kika ci. In gaya miki wannan dabi’ar banza ce, ki daina ta. Kada ki kuma cin rabon wani bayan rabonki haramun ne. Ni bai burgeni ba ma da bai shake ki kin amayo shi ba. Washegari Baban Giwa ya amso min transfer daga makarantarmu (ABU Staff School Primary School) zuwa ta su Ummi wato GIWA SOUTH PRIMARY SCHOOL. A rana ta farko da na fara zuwa Giwa South Primary na dawo da damuwa mai yawa, basu yin Arabiyya ko kadan, babu Arabic a darassanmu sabanin Staff School da muke zuwa ni da Abdallah a Zaria. Shigowarmu gida ke da wuya na watsar da littafan a falon Hajja na zauna shirim ina ta zumbura baki. Hajja dake rike da littafin Bulugul-Maram da Medicated glass a idanunta tana karantawa ta dago ta dube ni ta ce, “Lafiya?” Na yi tsaki na ce, “Bari ke dai Haijja....” Kafin in karasa sai ga Yaya Aliyu, Yaya Bashir da Yaya Fa’iz sun yaye labulen falon sun shigo, kowannensu dauke da sallama a bakinsa. Sun sha anko na farar shaddah (Hilton) sai salki take. Hajjah ce ta amsa musu, kana ta ce, “Har an daura auren?” Suka zazzauna cikin duma-duman kujerun falon, Basheer ya ce, “Eh, alhamdulillah an daura Hajja. Sadaki naira dubu dari Baban ABU ya biyawa Usman (Dan Baba Barau da ‘yar Baba Ibrahim Maryam aka daurawa aure). Sai fatan Allah ya basu zuri’a dayyaba da zaman lafiya da yalwar arziki mai albarka’’.Duka suka ce, ““Ameen”’. Yaya Aliyu da yake duk mun fi shiri da shi ya dube ni a nutse ya ce, “Hajja lafiya Fa’iza ke fushi?” Hajja ta ce, “Gaka gata nan tambaye ta mana, nima haka ta shigo min”. Ya dawo da idonshi kaina alamar sauraro ya ce, “Wa ya tabo min Fa’iza ta?” Na tura baki sosai na ce, “Bayan makarantar su Ummi ba a yin Larabci sai Turancv’. Duka suka sa min dariya ban da Fa’iz da ya ce, “Ji ta don Allah baka kirin da ita, duk gidan nan ita ce mummuna, ko meye gamin ta da Larabawa oho?” Bashir dariya yake shi da su Ummi, Yaya Aliyu ya ce, “Rabu dasu Fa’iza, ai black is beauty. Na rantse dukkan su babu wanda zai samu mata mai kyan ki. Na yi alkawarin canza muku Islamiyya wadda ake koyar da Larabci sosai kin ji Fa’iza na?” Kuka nasa sosai, ba abin da Fa’iz ya fadi bane ya sani kuka, a’a, na tsani ayi min gwasale cikin mutane. Shi kuma Ya Fa’iz na lura baya shakkar a gaban kowa ya ci mutuncina. Halinshi sam ba irin na Yayan shi Bashir da Yaya Aliyu Haydar bane, in ya raina ka kawai ya raina ka, in ya tsane ka sai ka gwammace ko hanya ba ta gama ku ba balle jini. Zama na a gidan Hajjah tare da Fa’iz daga farkon sa har zuwa inda yau ke motsi ba mai dadi bane, kai ka ce babu digon jinin juna a jikinmu. Fa’iz ya tsaneni on the ground of kazanta, ni kuma na tsane shi on the ground of mugunta. Shi Yaya ne ba mai dadi ba ga kannensa, akasin Yaya Aliyu mai son mu, mai janmu a jikinsa da nuna mana kauna ta ‘yan’ uwantaka. A sannu nake fahimtar kazantar da Fa’iz yake yawan ambatawa a gareni da na soma tasawa. Na farko ban damu da_ sanya wankakkiyar suttura ba balle gogaggiya, ban san wani abu wai shi kintsi ko gyaran jiki ba. Uwata ba ta ja ni a jiki ta koya min wadannan abubuwan ba, ban san in gari ya waye in tatsa maclean jikin burushi in goge baki ba, sai dai in afa ruwan shayi da burodina in ci. Ga Hajja tsohuwa ce ba ta mai da hankali kan irin wadannan abubuwan ba, wanka su Ummi kullum sai sun yi amma ni sai in kwana hudu fatar jikina ba ta ga ruwa ba. Balle sabulu da soso, gani kuma daman bani da hasken fata irin na Bamalli, kalar jikina irin na mahaifiyata ne. Idan na cire kaya ban san wanne ne mai datti ba wanne ne mai tsabta ba, haka zan hada duka in danna su a wardrove dina babu ninki balle kintsi sabanin Zanirah da Ummi su da suke ma goyon Kaka. wulakanci da kaskanci bani da bakin kare kaina sai dai in yi ta kuka da tunanin na yi gudun gara na tadda zago, ko in komawa zagon ne (Momin ABU), amma in na daga ido na dubi Ummi da Zanirah na tuna irin kewarsu da zan yi idan na bar Giwa, sai in manta da al’amarin Fa’iz in shigar harkokina, in kuma yi kokarin kaucewa duk wata hanya da za ta sada ni da shi a gidan don in zauna lafiya. Lokacin da muka gama makarantar firamare muna da shekaru goma sha biyu, muka samu gurbi a FGGC Gusau aji daya. Da yammacin ranar Yaya Aliyu ya shigo falon Hajja muna kallon shirin Risalah (The message) daga tauraron dan Adam ba tare da mun juyo ba duka suka amsa sallamar shi amma ban da ni, domin a lokacin ina gefen Ummi ina kuka sosai ni ba zan je makarantar kwana ba, Hajja da su Zanirah sun yi rarrashin duniya na ki yin shiru. Hajja ta ce da Yaya Aliyu a sanda ya zauna, “Yanzu nake cewa Ummi ta kira ka ku je kanti su hado duk abin da za su bukata nima nan na yi musu duk nawa tana din na su yaji da soyayyar miya, dambun nama na Fa’iza da su garin rogo ko za su _ bukace shi, to mutuniyar taka gata nan ta ja ta kafe ba ta zuwa makarantar kwana, ba ta kuma fada ba sai yanzu da aka gama musu komai gobe tafiya’”’. Yaya Aliyu ya matso gefena ya zauna a hankali yana dubana ina ta share hawaye da majina da habar zanina, jikina na_ tashin tsamin tashen balaga da rashin wanka. Ya ce, “Princess Fa’iza Bamalli, gaya mani matsalarki ta kin son makarantar kwana a yau, bayan a da baki ce hakan ba....” Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu Ummi ta ce ana saka yara yin kitso duk sati, yanke farce duk sati, wanka kullum, kuma dole kullum sai ka yi brush safe da dare, ni gaskiya za a takura min, wallahi ba zan iya ba..... Su Ummi suka bushe da dariya har shi Yaya Aliyun. Daga bayanmu muka ji an saki wani dogon tsaki, dukkanmu muka juya, Yaya Fa’iz ne. A hasale ya ce, “Yaya Aliyu don girman Allah ka _ fita hanyar = yarinyar nan mahaukaciya ce. Raina yana matukar baci idan na ga kana shiga sha’aninta. Ni wallahi ba don kamanninta da Baban ABU ba sai in ce canza ma uwarta ita aka yi a asibiti can inda take aiki suka hada baki aka bamu”. Fuskar Yaya Aliyu ta rine da bacin rai, ya dubi Fa’iz a hankali amma ya kasa cewa komai. Hajja ce ta ce, “Hafizi! Wacce irin magana ce wannan? Kada in kara jin makamanciyarta”’. Ya sadda kai ya ce, “Allah ya huci zuciyarku Hajja, amma _ yarinyar nan na_ bukatar makarantar kwanan da ba ta so, don kwatakwata ba ta san ciwon kanta ba, uwarta ta jawo mana baragurbi cikin zuri’a. Kaico! Auren bare bai yi ba wallahi.....” Ya juya ya yi ficewar sa. A fusace Yaya Aliyu ya mara masa baya, ya suka karke ya suka kare oho! Ya dawo fuskarshi babu annuri, ya ce (ba tare da ya dubi kowaccen mu ba) “Ku tashi maza mu tafi sayayyar’’. Yanayin yadda na bude motar_ cikin matsanancin fushi ya sanya Yaya Aliyu juyowa sannu a hankali ya dube ni na ‘yan dakikai, sannan ya sanya ma motar giya muka harba kan titi. Babban Super Market din wanda ke kan hanyar fita garin Giwa kusan duk garin babu kantin da ya yi girma da habakar ta. Babu abin da babu na bukatun yau da kullum. A nan Ali ya yi parkin duk suka fita, ban ko yi motsin dake nuna inada niyyar fitan ba, zuciyata da tunanina duk da karancin shekaruna sun sanya min ayar tambaya a yau a kan Yaya Fa’iz da kiyayyar da yake yi mun da_kuma dangantakar kiyayyar da raini ga mahaifiyata wadda baya jin kunya ko haufin jan sunanta a gaban kowa ya aibata ko ya zage ta. Mintuna biyu Yaya Ali ya yi yana nazarina kamin ya rankwafo tagar da nake a tausashe ya ce, “Fa’izah ba a fitowa?” Sal na ji ya yi min wani kwarjini mai yawa yadda ya yi maganar. A hankali na bude murfin motar na fito. Ya yi dariya ya ce, “Yau dai da alama mulki kike ji Fa’iza, ko duk fushin Fa’iz ne har yanzun?” Ummi ta kulu da bata lokacin da nake yi musu da tarairayar da Yaya Aliyu ke min na yi banza da su, ta ce, “Don Allah Yaya Ali ka rabu da ita sai wani lallashinta kake tana basarwa sai ka ce mu muka kar zomon, ita wace ce?” Ya yi murmushi ya ce, “Ita Princess Fa’izah Bamalli ya ya ranki?” Zanirah ta ce, “Me kenan Pincess?”’ Ya ce, “Princess yana nufin Gimbiya”. Ta tabe baki ta ce, “Sunan da Ya Fa’iz ya ba ta ya fi dacewa da ita ba naka ba”. A kaikaice da baki ya ce, “Wanne suna ne Fa’iz ya ba ta?” Zanirah ta ce, “Impertinence Fa’izah watau Fa’izah mai tsiwa”’. Ya dubi Zanirah sannan Ummi, ya ce, “Wadda ta sake kiran Fa’izah da wannan sunan ban yafe ba, kun ji ko?” Suka daga mishi kai muka shiga cikin kantin. Ko da muka shiga cikin kantin kujera na ja na zauna ina kallon su, dauki banza dauki wofi, wani zubin su juyo su kalle ni suyi kus kus su ci gaba da dauke-dauken su. Shi ko Yaya Aliyu sayayyarsa daban ce da tasu, kwando uku suka cika da kayan zaki masu tsada, hatta biron da zamu yi rubutu basu bari ba. Muna shiga mota kafin Yaya Ali ya tada motar Zanirah ta ce, “Ummi baki daukarwa impertinence rice pudding ba”. Na yi kan Zanirah da duka, yakushi da cizo, dama kiris nake jira. Yaya Aliyu ya dakan tsawa ya ce, “Meye haka ne Fa’iza? Don kinga ina lallaminki shine kika koma hauka?” Idona cike da kuka na ce, “Amma ita ba ka yi mata fadan sake kirana da sunan Yaya Fa’iz ba don kaima ka tsane ni kamar shi, shi kenan....!” Sai a lokacin ne na samu hawaye suka zubo. A tausashe Yaya Aliyu yana ta da motar ya ce, “Lallai Fa’iza har yanzu shagwabar tana nan? Haka za a kwalejin ana musu?” Ummi ta ce, “Ta yi mana in siniyoyi basu lallasata ba?” Muguwar harara na rafka mata ta toshe bakinta da hannun damanta tana “Allah ya huci ran princess”. Mun kusa shigowa unguwarmu ya Cé, “Fa’izah don Allah don Annabi ki dinga hakuri da ‘yan’uwanki kin ji ko? Ko harshe da hakori dole a saba wata rana, ki rage zafin zuciya, kina da zuciya mai zafi’’. Na ce, “Amma shi Ya Fa’iz ba mai yi masa fada kan tsana da tsangwamar da yake yi min a duk lokacin da abu ya shafe ni? Laifina ma kake gani Yaya Aliyu?” Yana girgiza kai ya ce, “Ba maganar Yayanki Fa’iz nake ba, bana so in ga kina halin yara, you are no more a child now, dambe da kokawa na su Walida da su Badar > ne”. Na zumbura baki ban ce komi ba. Ya ce, “Kin hakura Princess ko kina so na kasa barci saboda fushink1?” Sai na bude dukkan idanuwana na dube shi. “Yanzu Yaya Aliyu in ina fushi sai ka kasa barci?”’ Ya yi murmushi ya lumshe ido tare da daga kai sama. Cikin mamaki na ce, “To saboda mene?” Ya ce, “Saboda me? Saboda abin da kwakwalwarki ba za ta fahimta ba a yawan shekarun ki’. “Mene shi wannan abun?” “Wannan abun muhimmi ne mai girma da

0 Comments