SABON SALON DA NAMIJI COMPLETE

SABON SALON DA NAMIJI COMPLETE
A yanayin garin, hadari ne bak'ik'irin, in banda cida, da walk'iya, baka jin k'aran komai, sai fa labulayen taga da na k'ofa da suke kad'awa da k'arfi, tamkar zasu tsinke daga abin da ya taimaka wurin rik'e su. K'arfe d'aya saura kwata na talatainin dare, agogon dake manne jikin bangon dakin ta nuna. Ajiyar zuciya ta sauke, tare da kai dubanta kan kyakkyawar yarinyar dake kwance a gefenta, wacce ta gama kukan yunwa har bacci ya d'auke ta. A hankali ta fara shafa kan 'yar budurwar, wacce duka-duka baza ta wuce shekaru biyu zuwa ukku da haihuwa ba, idanuwanta ta rintse, hawaye masu zafi suka yayyafo, a bangare guda, tana addu'ar kada Allah ya had'a 'yar tata da miji irin mahaifinta.4 Jin ana k'ok'arin bud'e k'ofar dakin yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tsunduma, ta d'ago manyan idanunta, ta sauke akan mutumen da yake shigowa. Kallon da ta ke mishi, bai sa ya ji a jikinsa ba, haka zalika bai sanya shi tunanin yi mata sallama ba, domin a zahiri, da ita da babu ba zai iya tantancewa wanda ya fi wani muhimmanci ba. Santalar doguwar fuskarsa tamkar wanda ya dawo daga bizne mahaifansa a mak'abarta saboda rashin annurinta, a haka ya sanya kai zuwa dakin baccinsa, bai ko kalli sashen da suke zaunen ba.12 Ba ta yi gigin tanka mishi ba, domin hakan bai zama bakon abu a gare ta ba, illa mik'ewa da tayi, tare da sa6a yarinyar a kafad'a, ta shiga d'aki ta shimfid'ar da ita, ta fito. Kai tsaye d'akin mai gidannata ta dosa, daidai lokacin suka yi kici6is dashi ya fito, da alama wani abun ya manta a waje, dan ko takalman k'afarsa bai kai ga cirewa ba. "Matsa mun a hanya" Yace da ita, fuskarsa tamkar zata fashe saboda tsabar cika. "Magana nake so muyi." Ta bashi ansa fuskarta ba yabo ba fallasa, sai dai tana cikin tsananin damuwa da bak'in cikin da ba zai misaltu ba. "Do I have to repeat myself?" Ya tambaya da kakkausar murya. Bata bashi ansa ba, hakan ya bashi damar cigaba "Sau nawa zan fad'a miki cewar ba ni da lokacin shirmenki? Sau nawa zance dake ki daina shiga harkata matsawar ba ni na tanka miki ba a cikin gidan nan? Ke wace irin marar zuciya ce? Matsa mun a wuri dallah tun ban lahanta ki ba wallahi." Ya k'arasa maganar yana nuna ta da yatsa, a lokaci guda zuciyarsa na tafarfasa saboda tsabar bala'i. Gefe ta matsa, hakan ya bashi damar sanya kai zai fice, sai dai maganar da ta jefa masa, tasa ya ji tamkar ta watsa masa tafasasshen ruwa, tsaye yayi chak, tamkar ba zai motsa ba, ta cigaba da cewa "Anya akwai zuciya a k'irjinka SADAM? Ka tuna cewar yau fa kwana biyar rabonka da agida nan, kuma ko k'wayar gero baka bari ba, amma dan tsabar rashin imani da rashin sanin hak'k'in iyali, shine har kana da bakin cewa baka da lokacina?" Ta ja majina, sannan ta dora da4 "Da wuya idan kana tsoron wanda ya hallicce ka, wanda kuma shine ya shimfid'a adalci a tsakanin ma'aurata." Da matsanancin tashin hankali da bala'i ya nufo kanta, a lokaci guda ya zare belt d'in dake d'aure a k'ugun wandonsa ya nannad'e a hannu, sannan ya isa gabanta. Manya-manyan idanunsa da suka k'ank'ance, suka canja launi daga kalar fari zuwa jaja-jaja ya zara yana fad'in "Idan kin cika yar halak, ki maimaita abinda kika fad'a." Jay dake tsaye, tana shafe hawayen bak'in cikin da suke zubo mata, ta d'aga siririyar muryarta "Na tabbata ba ni bace mutum ta farko da ta taba fadar haka gare ka, zan kuma maimaita, kai d'in baka da imani Kazaure, da wuya idan kasan irin tarin darajar da d'an Adam yake da ita. Ina tantama idan ka san mutuncin kanka ma." "Har in mutu Sadam." Tayi nuni da setin fuskarta, ta kara da "Bazan daina da-na-sanin kasancewa k'ark'ashin inuwa d'aya tare da kai ba..."8 Bata kai ga rufe bakinta ba, ya d'aga belt d'in ya fara tsula mata, kukan da take ba na zafin ciwon bugun bane, kuka ne mai cike da da-na-sani da takaicin rayuwar da ta tsunduma kanta da kanta.5 Mutumen da ta kira da Sadam kuwa bashi da niyyar daina jibgar ta, har sai da ya tabbatar da ta yi galabaitar da baza ta iya tsinana ma kanta komai ba. Daga k'arshe ya hankad'a ta, gefen kanta ya bugu da bangon d'akin, a lokaci guda yasa k'afa ya murje dogayen yatsun hannunta da kwafcecen takalmin Timberland d'in da ke sanye a k'afarsa.6 9 Wurgar da belt din yayi, sannan ya juya a fusace ya wuce, yana wani irin huci tamkar wanda ya ceci kansa dak'yar, daga filin yak'in badar! A wurin ta duk'e tana wani irin kuka mai ta6a zuciya, sai dai da yake k'irjin Sadam babu zuciyar kamar yadda ta fad'a, haka ya wuce ta bayan ya dawo daga d'auko abinda yayi niyya ya shige d'aki, yana mai buga k'ofar da duk iya k'arfinsa. Hakan yayi dai-dai da haskowar walk'iya mai ban tsoro, tare da tashin wata gagarumar tsawa, daga nan aka tsuge da ruwan sama tamkar da bakin k'warya. Idan da sabo ya ci ace ta saba da azabar da take sha kullu yaumun daga wurin mijinta, abin alfaharinta, mutumen da take so fiye da numfashinta, sai dai kuma bata da idon da zata kalli wani da matsalarta, domin idan akwai wani mai laifi, to ba Sadam bane, illa ita, wacce tayi sanadiyyar jefa kanta a kurkutun azabarsa.13 Ta kwashi kusan minti ashirin duk'e a wurin tana kuka, sa'ili da 'yan yatsunta ke mata tsatstsauran zinga, har tana jin tamkar zasu bar gangar jikinta ne. A daddafe ta mik'e zuwa d'aki, jin kukan Rukayya wacce da alamu ta motsa ne ba tare da ta ji mamantata ba. Yarinyar ta dauka ta rungume tsam a k'irjinta, wani kukan ta kuma fashewa da shi, itama Rukayyar kukan take tana fadin "Maami abinci" Cikin muryarta ta 'yan yaran da basu ida k'warewa da maganar ba. Ruwa ta bata ta sha, ta kuma maida ta jikinta ta rungume tana shafa kanta har sai da wani baccin yayi awon gaba da ita. 'Baza ta iya jure zaman cin kashin nan ba.' Tayi furucin a kasar zuciyarta, inda ta fara sak'a hanyar da ya dace ta bi domin k'watar ma kanta 'yanci, duk da ta san bata da shi a gidan SADAM. Amma ya zama dole ta jajirce, ko dan gudun rayuwar da yarinyarta zata taso a ciki. Duk da kasancewar bata da wani wanda zai tsaya mata tsayin daka, wurin samuwar 'yancin nata a matsayinta na mace, halittar da Allah ya fifita fiye da dukkan halittunsa.3 **** Washe gari da sassafe ya fito cikin shirinsa na bak'in wandon chinos, da rigarshi kalar sararin samaniya, necktie d'inshi ma kalar ruwan bula ne mai turuwa, yayi zanzaro irin na matasan da suke ji da tashen kuruciyarsu, belt dinsa kirar Versace, ya taimaka sosai wurin kara fito da kwalliyar tasa. Cikin isa da jin kai ya fito, da alama shirin aiki ne yayi, gefen kafad'arsa ta dama sagale da jakar kwamfutarsa, sai tashin wani dadd'an k'anshi mai tsada yake yi. Nera d'ari biyar ya fitar a aljihunsa, ya d'ora samar teburin tsakiyar palon, bai jira komai ba, ya doshi hanyar da zata sada shi da waje. Da sauri ta fito har tana karo da bango, bata damu da gaishe da shi ba, domin ya sha yi mata kashedi a kan hakan, kai tsaye ta sha gabansa ta fara magana cikin kwarin gwiwar da bata san ina ta samo shi. "Ni kam Allah Ya na gani na gaji da zaman uk'ubar da kake mun Kazaure. Dan Allah ka taimaka ka bani takardata ko dan ka hutar da ni da kai duk gaba daya." Duk wanda ya ga yadda tayi maganar, zai tabbatar ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi kafin ta iya hada kalmomin da ta furta ba. "Matsa mun a nan malama." Ya fad'a a tak'aice, tare da d'aurewar fuska. "Babu inda zanje sai ka bani takarda ta." Ta fad'a yayin da take kallon gefe. Daf da ita ya matsa, har ta kan iya jin saukar numfashinsa mai zafi saman fuskarta, yana jifarta da wani wulak'antaccen kallo, daga bisani ya kama doguwar habarta, ya saita idanunsa cikin nata, kafin ya fara magana. "Sanin kanki ne tsakani na dake babu saki, kin fi kowa sanin idan ma na sake ki baki da inda zaki je, watak'ila ki karaci rayuwarki cikin tasha." Yayi murmushin raini mai kona zuciyar wanda duk ya ci karo da shi, sannan ya kara da fadar "Ni kuma abinda ba zan iya jure gani ba kenan." Tsai yayi da idanunsa a kanta, tamkar mai karantar yanayinta, a karshe ya sake mata fuska, har kuma yanzu murmushin na nan makale da labbansa. "Ba ni hanya in wuce Jameela Kasad."3 Hawayen da take mak'alewa ne suka gangaro, haka kuma bakinta ya kasa furta komai, 'wannan wace irin kaddara ce?' Ta jefi zuciyarta da tambayar, sai dai bata sani ba. Abu daya da zata iya tantancewa shine, ita ce silar komai, ita kuma ta jefa kanta a koma wane irin hali ta tsinci kanta, ta kuma tabbatar da wannan ne dalilin da yasa tayi bankwana farin ciki a gaba d'aya rayuwar gidan aurenta. Sama da shekaru hud'u kenan, tunda ta auri Sadam masoyinta, take fuskantar tasku da bala'i kala-kala a 'yar gajeruwar rayuwar da tayi a duniyarta. Bata ankara ba ya hankad'ar da ita, a karo guda ya gyara zaman jakar dake kafad'arsa, ya wuce yana mai kakka6e jiki tamkar wanda ya taba wani abun kyama. Motarsa, ya shige, ya bar harabar gidan. Kuka ne ya kuma k'wace mata, tunawar da tayi ita d'in yadda take a baya. Rukayya dake la6e a k'ofar d'akin maman tata ta k'arasa fitowa ganin dodon da take tsoro ya fita, dan kuwa a haka take ganin mahaifin nata, hakan yasa Jameela tayi saurin shafe hawayenta, ta mik'e ta kama hannunta tare da k'ak'alo murmushin dole suka koma ciki, domin yi mata wanka. 2 Yes.. yes.. yes! There we go again👌😃 Any guesses yet? Me ya jefa Jameela Kasad a irin wannan tasku na da namiji?13 What do you think of Sadam Kazaure?11 Looking forward to hear yo tantalizing comments hayatiess😃🖤🖤🖤 One more thing, Kar a manta a danna tauraron nan dake gefe kadan da hannun mutum na hagu, a kuma shiga ta akwatin kwament domin ajje ra'ayoyi.😍😍😍4 Abinda kuke ji dangane da labarin shi zai sa ni zage damtse in tabbatar da na gamsargamsar Karfe sha d'aya da yan mintina na dare ta ji kokarin bude kofarsa, da alama ruwan da ake tsugawa ne ya sanya shi shigowa da wuri. Sai da ya rage kayan jikinsa, ya watsa ruwa, kafin ya doshi dakin da ke kallonnasa.1 Kwance take, idanunta a lullube ta zurfafa a kogin tunanin da ya hane ta jin sautin takunshi, Rukayya na kwance saman ruwan cikinta, a haka ya daga labulen da ya suturta dakin, yana mai tura kanshi ciki. Sai da ya k'are musu kallo, kafin ya ja siririn tsaki. A duniya idan akwai abinda ya tsana baya da mahaifinshi, to ba zai taba wuce wadannan halittun guda biyu da suke ikirarin zama a karkashin ikonsa ba. Hannu yasa ya taba ta a hankali, hakan ya haifar da firgici a kasan zuciyarta, ta dago a tsanake ta na mai sauke idanunta a kanshi. "Ki same ni dakina" Furucin da yayi kenan, ya juya da zumar barin dakin, sai dai ganin bata da niyyar motsawa yya sanya shi dakatawa, ya juyo a masifance yana mai kare mata kallo. Mikewa tayi bayan ta gyara ma Rukayya kwanciya, tana mai kauda kanta a dubansa, ta kuma san sarai manufar maganar tashi, sai dai alkawari ta dauka na lokaci yayi da ya kamata ace ya san muhimmancinta. Ganin bata da niyyar ansa shi ya sanya shi dukawa a gabanta, "Kinsan abinda nike bukata Jameela. Ki sassauta ma kanki kiyi abinda na umarce ki, otherwise, zan iya kwata ta karfi matsawar bukatata zata biya. Ki tadda ni dakina." Kululun bakin cikin da ya tokare makoshinta ne ya hana ta furta ko da kalma daya, shin yaushe Sadam zai sauko daka dokin nak'in da ya hau? Yaushe rayuwarsu zata ci gaba kamar yadda suka fara shimfida ta? Tabbas bata tunanin irin wannan ranar mai zuwa ce, idan tayi duba da irin cin kashin da ya kan sauke kanta a safiyar ko wacce rana. Tunaninta ya katse lokacin da taji hannunta cikin nashi, da iya karfinsa na da namiji yake janta, bai dakata ba sai da ya tabbatar da ya shigo tsakiyar dakinsa. Idanunta ta kankame, haka zalika kafafunta a hade wuri guda, hawayen dake makale a kwarmin idonta suka gangaro cikin firgici take magana "Dan Allah kayi hakuri, wallahi ban karasa warkewa daga raunin da kai mun wancen karon ba. Ka yi hakuri dan Allah." A yadda yake jin kanshi a halin yanzu, babu wani hakurin da zai iya yi, asali ma, kalmominta harde masa suke, ya kan ji tamkar muryarta na amsa kuwwa ne a cikin dodon kunnensa, da wannan bai saurara mata ba, kamar yadda itama bata daina yakin kwatar kanta ba.1 Tun bayan da ta haifi Rukayya, Sadam bai taba zo mata ba, irin zuwan da addinin musulunci ya tanadarwa ma'aurata, ya kan yi mata son ranshi ne ba kuma tare da damuwar abinda hakan zai haifar gareta ba. Tun shudewar shekarar farko ta aurensu, baza ta iya kayyade adadin fyaden da mijinnata yayi mata ba, sai dai duk da haka, bata daina zargin kanta ba, domin kuwa itace silar komai.11 Tana ji tana gani ya gama bidirinsa, ya kuma tsallake ta ya shige bandaki abinsa. 'Wannan wace irin kiyayya ce? Wace irin rayuwa ta shigo da kanta?'3 **** Kukan da take a yanzu, ba za ta taba dangantashi da afkuwar abinda ya faru ba, domin ta dad'e da sabawa da kalar azabobi irin na mutumen da tayi gangancin d'aukakawa fiye da iyayen da suka kawo ta duniya! Kukan da take na bak'in cikin yadda rayuwa ta juya mata baya ne cikin dan karamin lokaci, ta mayar da ita marar gata, wacce bata da iko akan irin duk wata cuzgunawa da Sadam zai mata.6 Abu daya da zata iya yi a yanzu bai wuce karyata kalmarshi ta cewar ba za ta iya rayuwa ba tare da shi ba. Dole ta gwada mishi rayuwa da mutuwarta sun ta'allaka ne a hannun wanda ya halicce ta, dan watakila shi din ya manta da haka. Dole ta kawo karshen zamanta a gidan nan ko ta halin ka'ka! Bata damu ba, koda kuwa zata ci gaba da rayuwa ne a tasha kamar yadda ya fada.1 Ta tabbata zai fiye mata kan ta zauna tana fuskantar tasku da tsantsar wulakanci daga mutumen da ta so fiye da kowa, fiye da komai da ta mallaka a doron kasa. Wanda yayi silar barinta gida, yayi silar ta6ar6arewar rayuwa, da 'yancinta na 'ya mace baki d'aya. A hankali ta rarrafa ta wuce d'aki, ta gyara jikinta, har kuma a lokacin hawaye basu daina kwarara a idanunta ba. Daga bisani ta mik'e ta fara had'a duk wani abun da ta san zata buk'ata, duk da dai bakomai ke gareta ba, ta zuba a 'yar madaidaiciyar jaka, jira take gari ya waye kawai ta san inda ta nufa, sai dai duk wacce za'ayi ayi. **** A shirye tsab ya fito cikin wandon khaki kalar royal blue, rigarsa fara tarr, mai dauke da dogon hannu, necktie dinsa kalar sararin samaniya, kafarshi lullube cikin takalman Cole Han, masu launin ruwan kasa mai haske. Yadda yayi zanzaron cikin gwanancewa, sosai ya zauna a kugunsa, jacket dinsa rataye a hannunsa na hagu yana mai daura a agogo, kafadar hannunshi na dama sagale da jakar kwamfutarsa. Ya fito tarrr, tamkar ace wata ne d'an daren goma sha bakwai saboda cikar zati da kwarjininsa.8 "Ke!" Ta ji dakakkiyar muryarsa mai zurfi ta daka mata wata irin razanannar tsawar da ta sanya 'yan hanjinta murd'awa na d'an lokaci. Sai dai bata jin zata iya juyawa, balle tayi yunkurin hada ido da shi. "Where the hell 're you going?" Ya tambaya lokacin da ya karaso gabanta yana k'are masu kallo. Rukayya ce ta fashe da kuka tare da k'ank'ame Mamanta, fuskarta cike da alamar tsoro, tamkar wacce tayi gamo da mugun hatsari. "Shut Up" Yace da 'yar yarinyar, yana zara mata manyan idanunsa tamkar bai ta6a sanin daga inda ta fito ba. D'if, kukan nata ya d'auke, sai dai na zuci da ta cigaba da yi, take fitsari ya su6uce mata, ta k'ara rik'e Maman gam, tana mai tura kanta tsakanin k'afafuwanta. "Dake nike magana kin zura mun idon ki masu kama da na mujiya." Ya fada bayan ya dawo da dubansa gare ta. Bata bashi ansa ba, illa duniyar tunani da ta afka. "Babe idan akwai abinda na fi kauna a tare da ke, bai wuce kyawawan cute lips dinkin nan ba, and of course, your sparkling eyes. I love you way much babe girl." Hawaye masu dumi suka kawo mata ziyara, labbanta kunshe da murmushin takaici. 'Yau kuma sune suka koma na mujiya?' Tayi tambayar a kasar zuciyarta. Warce jakar da yayi a hannunta yayi wurgi da ita, shi ya dawo da ita daga duniyar tunaninta. Ta dago tana kallonsa ido cikin ido. "Na gaji da kai, da mugayen halayenka. Na gaji da bak'in ciki, da takaicin da kake kunsa ma yarinyar zuciyata. Na tsane ka, na tsani duk wani mai k'aunarka, hakan yasa na yanke ma kaina hukuncin barin gidanka, na gwammaci ci gaba da rayuwa a k'ark'ashin gada, kan in zauna a wannan k'untattacen gidan naka da babu komai a cikinsa sai annoba da bala'i. Ka sawwake mun ko kar ka sawwake mun, wannan ruwanka. Na riga na yanke hukunci ma kaina Sadam. I so much hate you." Ta ja majina, tana share hawayen fuskarta, ta duk'a ta d'auki jakarta, tana mai rike hannun Rukayya karkadam, suka raba gefenshi da niyyar wucewa. Langabar da kai yayi yana duban mamaki gare ta, malalacin murmushin da ya kara kawata fuskarsa ya makale a labban bakinsa, bai kalle ta ba, ya sa k'afa ya dauke ta sama, ta fado kasa da wani irin karfi, a take bakinta ya fashe, ya fara zubar da jini.5 "U're very stupid Jameela." Ya fad'a lokacin da ya duk'a ya tallabo ha6arta dake zubar jini. "Wato har kin manta abinda na fad'a miki jiya jiyan nan? Ke wace irin mace ce wacce bata da kokari?" Ya sake ta, yana mai gyara hannun jakar da ke kafadarsa.1 "To bari kiji in tuna miki. Duk in kika ga kin bar gidan nan, ki tabbatar mutuwa kika yi, aka fitar da gawarki."1 Ya juya da sauri ya kama gabansa. Cikin kuka da takaici, ta warci jakar kayanta dake yashe a gefe, ta wurga masa tana fad'in. "Mugu, azzalumi, bazan ta6a yafe maka ba Sadam, ko da hakan ne zaiyi maka katanga da gidan aljanna. Macuci wanda bai san darajar d'an Adam ba." Tsaye yayi tamkar ba zai juyo ba, cikin sakanni goma sha biyar tsumin bala'in da ke kanshi ya gama tashi, ya juyo a hankali ya wanke kyakkyawar fuskarta da mari har sau biyu. Ko ta ina yake dukanta, bai damu da yarinyarsu dake gefe tana kuka tamkar ranta zai fita ba. Dan kanshi ya kyaleta, ya duka ya dau jakarsa ya fice, tare da jawo k'ofar palon ya datse da k'aton padlock... 11 Unmm..unmm..unmm!"Me ke damun ka haka? Naga tunda ka shigo baka da aiki ban da tsaki da yawan tunani. What's the matter?"+ A hankali ya d'ago yana kallon shi, kamar zai ce wani abu sai kuma ya share, yana mai juyar da kansa zuwa kallon gefe. Tsai yayi da idanunsa akan Sadam, "Definitely, there is something terrible that's tormenting your mind."1 Ya fada lokacin da ya karasa gabanshi hannuwansa duk biyun cikin aljihu. Kallonshi Sadam yayi, kamar ya fad'a masa sirrin da ya dad'e yana 6oyewa, a matsayinshi na babban abokinsa k'waya d'aya tal, a duk fad'in garin na Maiduguri. Sai dai ina, ba zai iya yin wannan gangancin ba, bai kuma san ta yadda zai fara masa bayani ba, kamar yadda bai san da wace irin fuska zai kalli abun ba. Yanayin murmushin da ya dora a labbansa na dole ne, ya kalle shi da kyau,1 "Nothing serious, just a little fever. Zan koma ta gida ne in samu in huta." "Kar ka manta da ni dai, matsawar kana bukatar wani abun." "In sha Allah." Ya fad'a da d'an murmushin da ya fi kama da na kafin hali. Hannu SS din ya mika masa, ya ansa suka yi musabaha, sannan ya koma cikin bankin, yayin da shi kuma ya tada motar ya bar harabar wurin. Cikin GRAND PINNACLE HOTEL dake Jimna Road, Pompomari, Maidiguri, ya dakata da motarshi. Mutane ne cike jingim a babban dakin da za'a iya kira da club, maza ne, da matayen da basu san darajar kansu ba. Karfe hudu ne da yan mintina na yamma, amma hakan bai hana madaddalar tara mutane ba. Da yawa shaye-shayensu suke yi, k'alilan a cikinsu ke buga wasan karta, wasu na buga whot, wasunsu kuma sunyi dabdala sun zagaye wani babban teburi, suna ihun da ya karade babban dakin mai yawaitar mutane. Ko da ya shigo kai tsaye gaban teburin ya dosa, hakan yasa hankalin jama'ar ya dawo gare sa, da yawa suna fadin "Sai Kazaure, sai Kazaure." Murmushin nan nasa mai tsada ya saki, ta gefen kumatunsa yana mai nannade hannun rigarsa, ya ja kujera domin sama ma kanshi mazauni. Cikin mintunan da basu haura ashirin da biyar ba, ya gabatar da sana'ar da ya fi kwarewa a kanta, ya kuma samu nasarar kwashe duk wasu kudade da mutanen suka dora.4 Da yawan lokuta ba'a cika tashi daga caca cikin dad'in rai ba, yau din ma haka ta kasance, dan kuwa sai da suka kai ruwa rana da mutumen da bai bar ma koda nera biyar ba. Fad'a sosai ya kaure tsakaninsu, sai da duk suka galabaita, sannan suka saki junan su, yayin da jama'ar wurin suka cigaba da ihu, har sai da Sadam din ya buga musu muguwar tsawar da ta sanya kowannensu shiga taitayinsa. Cikin jin kai da kwarewa a bariki ya isa ga k'atuwar kwalbar barasar dake kan wani teburi ya d'aga, ya tuttula ma yan hanjinshi, a karshe ya wurgar da kwalbar yana mai fitar da numfashinsa cikin sauri.20 **** Shekararshi ta biyu kenan da dawowa aiki garin na Maiduguri, a iya wannan shekarun kuma ya san Sadam, har ya zamo mishi amini, amincin da ya rikida zuwa yan uwantaka. Abinda ya kasa ganewa shine, yadda abokinnasa ke boye duk wani lamari da ya shafe shi, daga ciki kuwa hadda ma adireshinshi, duk da dai ba cika haduwa suka yi ba bayan tashi aiki, idan ma har hakan ta kama, sun fi gane su hadu a wani wurin shakatawa, domin tattauna batutuwan gabansu.6 Profile dinsa na ofis ya bincika domin samun adireshin nasa, dan kuwa a shekaru biyun da ya san Kazaure, bai taba ganinshi cikin irin yanayin da ya ganshi a yau ba, uwa uba, ya kira wayarsa ya fi a kirga ba tare da ya daga ba. Tsoronshi daya kada jikinnashi ne ya tsananta. Titin New GRA ya dauka bayan ya fito, a kofar gida mai lamba 56 ya dakata kamar yadda ya gani a profile din nasa. Ga mamakinshi katon padlock ne a k'ofar palon, yayin da yake jiyo tashin kukan yarinya k'arama, wacce bai san ko wacece ba, dan kuwa a sanin da ya yi ma abokinnasa, saurayi ne gangariya, wanda bai taba aure ba, balle ayi maganar haihuwa. A hankali ya ke ci gaba da tura kai cikin gidan, a lokaci gida, kukan na ci gaba da tunkararsa, kasancewar gidan ba wani girma ne da shi ba. Ta tagar palon ya tura kansa da sallama, da gaggawa Jay dake durk'ushe ta mik'e, ta isa jikin tagar tana mai daga labulen, a sa'a guda idanunta suka fada cikin nashi. Kallon nata yake shima, sai dai bai san abinda zai ce ba, yayi gyara murya a hankali, da zumar fara magana, sai kuma ya tsinkayi tata muryar cikin sheshshekar kuka "Dan Allah malam ka taimaka ka fitar da ni a gidan nan, kaga yarinya ta zata mutu da yunwa, tun safe bata sa komai a bakinta ba." Ido ya fara zarawa yana tunanin anya ya bi adireshin na Sadam dai-dai kuwa? "Ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Ta katse mishi tunanin da muryarta mai rauni, tana mai tsiyayar da hawaye tamkar ace an bud'e famfo ne. Take zuciyarsa ta tsinke, yake kuma jin ko da ba gidan Sadam d'in ba ne ba, dole ya taimaki baiwar Allahn nan, domin a duniya babu abinda ya fi d'auka da daraja da kuma muhimmanci irin mace. Cikin k'arfin hali ya dubeta, "It's okay, I'll help you. Amma ki daina kuka please, kinji?" Da baya ta koma tana sauke ajiyar zuciya, tana mai share hawayenta, daga waje kam tana jin yadda yake kokarin bige padlock din da yayi musu katanga da daddadar iskar duniya.11 *** *** ***Katsina, 2011 Sanye take da faffad'ar farar riga mai dogon hannun da ta tattare shi zuwa gwiwar hannunta. Dogon bak'in skinny skirt ta d'ora wanda ya bi jikinta ya lafe, ya kuma hau har saman cikinta (high waist) ta dai-daita jikinta, sannan ta d'auko tattausan farin mayafi karr, ta yane kanta da shi. A lokaci guda ta duk'a ta sanya bak'ak'en sneakers d'in dake ajje tsakiyar d'akin, ta taka zuwa jikin bags hanger ta ciri jakarta kalar ruwan dorowa mai ratsin bak'i, ta dawo gaban dogon madubin da zata iya hango tun daga kanta har zuwa k'afafunta. Sai da ta k'are ma kanta kallo tsab, daga bisani ta d'auki ipad d'inta, ta fito.4 A tsaye ta samu Goggo da Baffanta, kasancewar haka bafulatanar mahaifiyarta ta horar da ita da kiransu tun tana k'arama. Da alama yayi shirin fita, jikinshi sanye da d'anyar shadda dinkin babbar riga, har ma da hula a kansa. Tura baki ta fara yi, bata damu da gaishe da iyayen nata ba, tana mai bubbuga k'afa, hakan yada Baffan bud'e hannayensa, ta isa gareshi fuskarta a tur6une .1 "Baffa shine zaka fita ba tare da ka ganni ba ko? Kuma kasan fa yau zan fara zuwa school amma shine zaka yi tafiyanka." Ta k'arasa tana shirin matse hawaye. Dariya duk suka sanya, har Goggo dake gefe, a hankali ya fara bubbuga bayanta. "Haba Ummina, ya zanyi in fita ba tare da na ganki ba. Yanzu haka shirin nan da kika ga nayi fitowarki kawai nake jira." Dariya ta saki itama, "Ina kwananku?" "Lafiya lau." Suka ansa a tare, kafin suka zarce samar dogon teburin da aka wadata shi da abubuwan motsa baki. A tare suka fito da Baffa bayan sun gama cin abincin, hannunnta cikin nashi, fuskar kowannensu na tattare da annashuwa da annuri mai bayyanar da tsantsar alfaharin da suke da juna. Wata bak'ar Corolla S taga Baffan da kanshi ya bud'e ya shiga, kafin yayi mata umarnin shiga itama. Juyawa tayi tana kallonsa bayan ta rufe kofar motar, fuskarta d'auke da murmushi "Lallai Baffa kana ji da wannan ranan. Rabon da naga kayi driving da kanka idan zan iya tunawa tun 5th birthday na a Kaduna." Murmushi ya saki mai sauti, hankalinsa na kan titi yace "Ai dole ne in ji da wannan ranan Ummina, kasancewar ta rana ta farko da burin da na ci alwashi a kanki ya fara cika." Juyowa yayi ya kalleta, sannan ya cigaba "Tun ranar da kika zo duniya nake rok'on Allah ya gwada mun ranar da zan ganki kin fito cikin black & white uniform d'in nan, dan na tabbata, za ayi barrister mai adalci, wacce zata taimaki k'asarta, tare da al'ummar da aka zalinta."1 Dariya tayi da ta taimaka wurin lobawar gefen kumatunta.5 "In sha Allah Baffa na." Sauran tafiyar tasu ta kasance cikin labarai na nishadi, har suka iso gaban tsangayar horarwa ta lauyoyi dake jami'ar Umaru Musa Yaradua Katsina. Ya juyo da fara'a yana kallon tilon 'yartasa cike da so da kauna "Yadda na kawo ki makaranta a ranar ki ta farko, ina rok'on Allah ya nuna mun ranar da kika kammala karatun nan lafiya."1 Murmushi mai karko Jay tayi, "Amin Ya Allah Baffana." "Ga mukullinki nan, ki kula da hanya Mamana. Ina kuma kara tunatar da ke alkawarinmu. Ki rike daraja da mutuncin gidanku." Cikin tsananin farin ciki da jin dad'i ta ansa, tana mai sunkuyawa ta d'an kama kafad'unsa, "Allah ya k'ara arzik'i da wadata Baffana. Na gode." "Allah yi miki albarka Baby, ki maida hankali banda wasa kina ji na?" "In sha Allah" Haka rayuwartasu take cike da ababen so da kauna, tamkar ba 'ya da uba ba. Yana tsananin sonta daidai da yadda yake son kanshi. A kullu yaumun, yana son yayi abinda zai faranta zuciyar tilon 'yar tasa, har ya kai ga ta bayyana farin cikin ta a fili ya gani. Daga haka suka yi sallama ya fito, tare da shigewa bayan motarsa da direba ke biye da su dan karasawa wurin aikinsa. **** Kwanakinshi biyu kenan a garin na Katsina, sai dai ya kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali kasancewar ya rasa gano wurin baje kolin sana'arsa. Aiki yake tukuru, amma hankalinsa gaba d'aya ya raja'a a tunanin inda zai ci karo da babbar madaddalarsu ta 'yan caca. Tunawa yayi da Kano ne, har sai ya za6i inda zai je, amma anan neman wurin zuwan ma yake bai samu ba. A gurguje ya fito bayan an tashi aiki, dak'yar da taimakon wani mai irin 'yan k'ananan shagunan nan na siyar da sigari ya kwatanta masa wani wuri. Abinda ya 6ata ran Kazaure bayan isarshi wurin shine ganin yadda suka karya daraja da mutuncin sana'ar da ya daukaka fiye da aikinsa. Tsaki ya ja mai sauti, wanda yayi sanadin jan hankulan mutane da dama, dan shi a ganinshi da yayi irin wannan cacar, ya gwammace yayi yawon bara, ko da kuwa zai kwana babu abinci Ya saba da babbar harka, caca da manyan 'yan caca masu kud'i wanda basa jin k'yashin su d'ora nera miliyan daya a take a lokaci guda. Takaici ya ishe shi yadda mutanen ke ihu, tunawar da yayi hatta motar da yake hawa a caca ya ciwo ta wurin wani bayerabe mutumen Lagos, amma su nan sunzo sun cika mishi kunnuwan kan 'yan kud'ad'en da gaba d'aya basu haura nera dubu goma ba.2 Mik'ewa yayi zai fita, cikin sa'a ya ci karo da wani matashi wanda ya sha yayi tatil, cikin dabara ya tambayeshi inda zai gano wani babban hotel a garin, a haka cikin mayensa ya kwatanta mishi, ba dan ya gane ba ya fito, sai dai sunan wurin kawai da ya rik'e, yasan ba zai sha wuya wurin ganowa ba. Da taimakon wani mai acaba ya iso kofar katafaren otel din da ya amsa sunanshi. Ko da shigar shi wurin take wata natsuwa ta saukan masa, dad'i yake ji har a cikin ranshi, domin kuwa a duniya idan akwai abinda ya fi k'auna, bai wuce yaga ana loda kud'i akan teburin kada caca ba, a kuma samu wani zakaran da ke lashe su cikin d'an k'aramin lokaci. Wannan ne karo na farko da yayi murmushi mai sauti, tun bayan zuwan shi garin, ganin yadda ake facaka da kud'i da muhimman abubuwa akan k'ayataccen teburin kad'a cacar. **** *** ATM card d'inta yayi expired kwana biyu da suka wuce, tun jiya taso ta shiga ta canja sabo, yanayin lectures dinta bai bata dama ba. Dole ta san abin yi, domin tana da buk'atar cire kud'i.9 Tsaye take a traffic jam na k'ofar k'waya, cunkoson ababen hawa a daidai wannan lokacin ya kan bakanta zuciyar mai jiran tsammani. Idanunta ta sauke kan agogon da ke daure a hannunta, ganin lokaci na shirin rugawa ya sanya ta dukan sitiyari, tana mai danna oda da duk karfinta. A duk sa'ar da ta iso gaban Zenith Bank, abu na farko da kan fado zuciyarta shine sunan Jameel sarkin naci. Jameel masoyin Jay ne na a mutu, ma'aikaci kuma a bankin da take ajiyar kud'i. Wulak'anci na gidan duniya babu kalar wanda bata yi ma Jameel, amma ya kasa gane cewar ita d'in ba tsarar irin shi bace. Da wannan tunanin ta gyara parking, ta ciro bak'in tabarau kirar Versace ta mak'ala a idanunta, ta fito cikin zubinta mai tsantsan kwarjini da haiba, ta taka cikin tsanaki zuwa k'ofar shiga.1 Wurin da aka rubuta customer care ta karasa ta zauna a kujerar da ke fuskantar ma'aikacin da ko kallon inda take bai yi ba. "Errnmmm" Ta fara gyaran murya a hankali. A zahiri bashi da niyyar motsawa, sai dai a wannan karon ya d'ago manya-manyan idanunsa masu haske, yana satar kallonta.1 "Ran gimbiya Jay ya dade." Muryar Jameel ta ratsa shirun da ya shiga tsakaninsu. 'Ya Allah!' Tayi furucin a kasarzuciyarta. A zahirance, ta dago tana mai sauke wulak'ance duba gare shi. Kamar baza tayi magana ba, cikin murya marar karfin amo ta furta "Sannu fa." Baki bud'e ya zauna a kujerar gefenta, yana kallonta da mamaki, domin kuwa tun ranar da ya santa, bai ta6a jin kalma mai dad'i irin wannan ta fito a bakinta ba. "Akwai matsala ne?" Ya tambaya yana k'are mata kallo, a zuciyarsa yana jin akwai ranar da zata zo, wacce Jay zata sassauta wulak'ancin da ta kan mishi, har ma su samu damar dai-daita kansu. Hankalinta na kan waya ta ansa da, "Zanyi renewing ATM card d'ina ne, sai dai naga alamar wanda ke kan aikin kaman bai san darajar customers ba."1 Dariya Jameel ya saki mai dan sauti, ya kai hannu ya shafo gashin da ya taru a gefen fuskarshi, "In dan wannan ai da kin kira ni nasa anyi miki, in je har gida in kai miki. Ina da wani amfani ne da ya wuce wannan?"1 Kallon da take mishi yanzu irin kallon tausayi ne, irin kallon da ke nuni da cewar tabbas yana tare da ta6in hankali. Sai da ta ja ajiyar zuciya, fuskarta da alamun kosawa, ta kafe shi da idanu "Kana tunanin akwai irin ka a jerin mutanen da nake adana numbers d'in su cikin wayata? Dan Allah ka koma bakin aikinka, wallahi bani da lokacin batawa." Cikin zafin rai ta maida dubanta ga Kazaure, "Malam zaka ajje abin nan kayi attending customer d'inka ko kuwa?"7 A tsanake ya d'ago ya k'are mata kallo, bai ce uffan ba, ya mayar da kallonshi ga kwamfutar dake gabansa. A daidai lokacin Jameel ya mik'e yana fadin "Please attends my wife to be Kazaure."1 "God forbid." Ta fad'a cikin k'unar zuciya. Bai ce komai ba sai murmushi tare da shafar sumar kansa, ya wuce da hannayensa duk biyun zube cikin aljihu. Abinda ya ke ya bari, ya juyo da kallonsa gare ta, ta dago cikin rashin sa'a ta sauke idanunta cikin nasa. Cikin dakushewar murya, mai hade da sanyin jiki ta furta "Ina son form zanyi renewing ATM card d'ina." Bai ce k'ala ba, ya d'auko form ya mik'a mata, ya kuma maida kansa a aikin da yake, amma lokaci zuwa lokaci ya kan saci kallonta, inda a zuciyarsa yake yaba tsarin halittarta, wacce ya tabbatar ba ta dace da mazaje irin su Jameel ba. Bayan ta cika ta mik'a masa ya ansa ba tare da ya kalleta ba. Yadda yake abubuwan shi cikin jan ajin da bata san ko yanayinsa bane, ko kuwa yayi hakan dan ya birgeta ne, yasa taji zuciyarta ta cure a wuri guda, haushinsa na ba gaira ba dalili ya darsu a kirjinta, har tana jin kamar ta wanke shi da marin da zai dawo da shi hayyacinsa. Wani abu da bata fahimta ba shine yadda ta kasa dauke idanunta a kansa, tana mai lura da dukkan motsinshi, tana kuma kallon yadda yake shigar da abinda ta bashi cikin na'ura mai kwakwalwa, cike da sanin makamar aikinsa. Ya gama tsab, ya d'auko ATM d'in ya saka yace tayi activating pin d'in ta. Sai da ta gama tsab, ya dago da murmushin da ta kasa fahimtar manufarshi ta gefen kumatunsa, ya damka ATM din da ya nannade da farin hankacif dinshi gare ta. "Thank you." Ta tsinkayi muryarta da fadi, labbanta kunshe da murmushin birgewa. Murmushin san nan har yanzu kunshe da bakinsa, a wannan karon yana mai bayyana jerin fararen hak'oransa na sama. Muryarsa mai zurfi ya kaikaita, k'asa-k'asa ya furta "Gaisuwa ya kamata ki fara koyowa, kafin ki dawo kiyi godiya."2 Tsaye tayi tamkar kasa ta bude ta shige tsakaninta, cikin karfin hali irin nata ta juya tana kallonsa. Kamar ba shi yayi maganar ba, idanunsa na kan allon kwamfutar gabansa ya ci gaba "There is my number, ina jiran godiyarki idan kin dawo daga makarantar koyon sallama tare da gaishe da mutane."2 Bai kara komai ba daga haka, yaja earpiece d'in dake jone da kwamfutarsa, ya mak'ala a kunnuwansa, bakinsa na kara fadada zurfin murmushinsa. Watchaaa say bout this?😂😂😂😂 Da sauri-sauri zuciyarta ke bugawa, saboda tsabar masifar da ta juyo da shi. Ji tayi tamkar ya watsa mata garwashi lokacin da maganganunsa suka yi dirar mikiya cikin dodon kunnenta. Ga mamakinta kunnenshi dad'e yake da earpiece, ta san duk maganar da zata yi a banza, dan kuwa ba ji zai yi ba. Lallai yayi sa'a amma da sai ta yarfa mishi bak'ak'en da zasu hana shi bacci a daren yau. Abinda ta rink'a nanatawa a k'asar zuciyarta kenan. Kamar yadda ta kasa motsa kafafunta, haka ta gagara kyafta idanuwanta a kan shi, ji take duniyar na juyawa mata, dan kuwa tunda take, bata taba cin karo da wulakanci irin wannan ba. Har a yanzu hankalinsa na kan aikin dake gabansa, ba wai dan bai damu da tsayuwar tata ba, sai dan kawai ya gwada mata bata da wani muhimmancin da zai maida kansa gareta. Bata iya furta ko kalma daya ba, haka ja kafarta da niyyar barin wurin, kai duban da zata yi gare shi, idanunta suka kulle a tsakiyar nashi. Murmushin mugunta ya jefe mata, yana mai kanne idonsa, hakan ya jaza mata sabuwar kasala, da saurin saukar da nata idon, ta fara tafiya da sauri, da sauri. Ya za ayi ta jure irin kallon da yake mata? A karo guda ya kawar da kanshi, sai dai zuciyarsa dake ta faman sak'a tana warwarewa. *** Ita kanta ta san bata da hakuri, babu kuma wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya. Babban tashin hankalinta a yanzu, shine yadda ta gagara nuna ko da yatsa ne ga mutumin da ya jefe ta da kalaman da tunda ta mallaki hankalinta, bata ci karo da irinsu ba. Mutumen da ko sunanshi bata sani ba, mutumen da ke kokarin canja mata halayya cikin dan kankanin lokaci. Har a yanzu da ta shigo gida, bata daina mamakin yadda bakinta ya kulle kanshi ba, bata daina tunanin dalilin da ya dakatar da kwakwalwarta daga nazarin abinda zata gayawa customer care ba, domin kuwa sunan da take ganin ya fi dacewa da shi kenan. A samar gado ta watsar da kayan hannunta, ta cire mayafin sannan ta zarce kichin, saboda irin yunwar da ke nuk'urk'usarta. Sai da ta ci ta k'oshi, sannan ta dawo d'aki, bata damu da zuwa ga mahaifiyarta ba, domin ta san dole ta zo nemanta. Kayan jikinta ta cire tare da d'aura tawul, kamar zata shiga wanka, sai kuma ta koma ta kwanta, ta fara bincika kayan tana neman wayarta. Kamshin turaren da bata san daga inda yake bugowa bane yake ci gaba da dukan hancinta, hannunta ta kai ga farin hankacif din dake nade da ATM card dinta, ga mamakinta rubutu ta hanga jiki, wanda hakan ya sanya ta warwarewa tana fara dubawa. Lambobin waya ne a jere guda ukku, daga kasa ya kara da1 You must call me Jameela, Jay, whatever. I'm just waiting for your call. Sadam Kazaure4 Maimakon ta ji haushi, sai murmushin takaici da ta saki, wanda a zahiri tana mamakin karfin hali irin nashi. Anya ya san wacece ita kuwa? Ya san maza nawa suke bibiyarta a cikin garin Katsina, ba wai cikin Zenith bank ba kad'ai, tana kuma gara musu kawuna da bango?4 Da alama bak'on fuska ne, dan tunda take bata ta6a ganin mai kama da shi ba. Murmushi ta yi, sai a yanzu take jin, tabbas ita ce zata kawo k'arshen iskanci irin nashi. A zahiri ta furta "Sure, I'll call you, sai dai kiran ba zai zama abin alfahari a gare ka ba Kazaure." Da takaicin shi ta mik'e ta shige wanka, bayan ta loda dukkan lambobin nasa a kan wayarta. 《》《》《》《》 Tun daga lokacin da ta fita yake sakin murmushi wanda ya rasa gane ko na meye, ya tabbatar ma kansa ba soyayya bace, sai dai ya yardar ma kanshi cewar akwai wasu abubuwa da ya gani a tattare da ita, wad'anda zasu taimaka wurin kawar da k'ishin da ke mak'oshin shi. Alal hak'ik'a kuma zai saukar da girma da rawar kan da ya ga tana fama da shi. "She must call me" Ya fad'a a bayyane, yana mai kai duba ga wayarsa, sai dai babu alamar kiran da yake shigowa. Har aka tashi aiki, zuciyarsa fal da tunaninta, haka kuma lokaci zuwa lokaci ya kan kai duba ga wayarsa ko za ayi arashi yaga kiran bak'uwar lamba. A yau, sa'a yake ji a tattare da shi, dan haka bayan da yayi wanka ya shirya, ya fito zuwa Hotel din da zai taimaka ma yawaitar nishadinshi. A restaurant d'in dake cikin hotel d'in ya fara tsayawa ya cika tumbinsa tass, sannan ya mik'e. Yana k'ok'arin fita kira ya shigo masa, la66ansa d'auke da wani makirin murmushi, ya d'aga wayar tare da fad'in "This is Sadam Kazaure, how may I help you?" Jay dake kwance tana kallon fankar dake manne da rufin d'akinta, ta lumshe ido tare da k'ank'ame d'an k'aramin filon dake hannunta. Bata san dalili ba, haka kawai muryarsa tai mata dad'in da baza ta iya misaltawa ba. Daga bisani ta yi gyaran murya tace2 "I know, so you don't have to introduce yourself. Ok?" "But who are you?" Ya tambaya ta d'ayan 6angaren lokacin da yake fitowa cikin restaurant d'in. "That's none of ur business, ina son sanar da kai cewar ka dinga sanin maganar da ya kamata ka fad'a ma customers d'inka, if not wata zata iya yin sanadiyyar aikinka. Nd by the way, ka gode ma Allah da har na iya d'aga baki na ce maka thank you, domin ba kowa ke samun hakan daga gare ni ba." Wannan karon murmushin mai sauti ya saki, ita kanta sai da ta jishi, sannan yace That means I'm special, tunda kin yi mun abinda ba kowa ke samu daga gare ki ba." Ya bud'a murfin motarsa ya zauna, k'afarsa d'aya a ciki, d'aya kuma a waje sannan ya cigaba. "Jay right?" Bata ansa shi ba, shima bai jira hakan ba yace "just admit it, kinga d'an handsome kina so, kin zo kina wani sneaking. Well, ki gode Allah, Kazaure na jin zai iya taimaka miki 'yan mata." Mik'ewa tayi, tana mai wurgar da filon da ke hannunta, zuciyarta na tafasa tace "U're mistaken malam, cuz banga abinda zan so wurin ka ba, idan ma tallan kanka kake, gara ka matsa gaba, anan dai baka yi kasuwa ba."7 "C'mon babe girl" Ya fad'a tare da sakin wata 'yar dariya mai sauti. "Ke kinsan Kazaure ya fi k'arfin a kalle shi a k'ara gaba, kar ki damu, I'll take a very good care of you. Nd I'll be the best boyfriend ever."1 Dariya ma abin ya bata, dan haka ta murmusa, "Ga dukkan alamu abokin fira kake nema, sai dai kuma ni bani da lokacin batawa. A matsa zuwa gaba Malam Kazaure." Da gama fad'ar haka ta kashe wayar, da baya ta komawa ta kwanta, domin ta kasa tantance irin yanayin da take ji a cikin jikinta.1 *** Dariya sosai yayi, bayan ta kashe wayar, bai bata lokaci ba, ya tura mata text din da ya tabbatar ko dutsin dala ta d'ora ma kanta, dole ta sauke, matsawar ta shigo hannun irinsu. A cike sosai ya samu wurin kamar kullun, kida da ihun mutane kawai ke tashi. Bai bata lokaci ba wurin zuba makuden kudaden da ya shigo da su a teburin da ya samu kusan mutum goma zagaye da shi. Mamakin kwarewa da jajircewa irin ta Sadam Kazaure jama'ar wurin ke yi, ya kware a sana'ar fiye da tunanin duk wani mai tunani. Hankalinsa, da duk wata natsuwarsa, ya sadaukar da su ne a kan abinda ya fi kaunar yi fiye da komai. A wasu lokutan yana mamakin dalilin da ya zaunar da shi a aikin gwamnati, ba tare da yayi watsi da shi ba, ya gina Casino nashi na kanshi, ko dan ya daga daraja da mutuncin caca.5 Kwalbar barasa da yasa aka kawo masa, ya d'aga, ya fara kwankwad'a, tamkar zai tafiyar da 'yan hanjinshi. Bai aje ba sai da shanye ta tass, sannan ya wurgar da kwalbar, tare da kwasar wasu daga cikin kud'in da ya tara ya watsa sama, sauran kuma ya cusa a aljihun wandonsa, ya fito ya shige mota, yana jaddadada wa kanshi cewar tabbas zuwan shi garin Katsina ba k'aramin alkairi bane a gareshi ba.5 *** Jameela kuwa ta kasa motsawa daga kan gadon da take kwance, duk kuwa da k'aran shigowar Baffanta da taji, wanda a kullu yaumun ita ce mutum ta farko da take taryarsa idan ya dawo. Shigowar sakon da taji ne yasa tayi saurin duba wayar, tare da bud'a text d'in cikin hanzari. Ba sai kin fad'a ba, 'll surely take good care of myself for you. So you do the same. Okay? Zan kira idan na koma gida. -Kazaure. Bata san me take ji ba a inda take zaune, mamakinshi bai gama barinta ba har yanzu. Tambayar kanta take shi din wane irin mutum ne? Fuskarta dauke da kyakkyawan murmushin birgewa.3 A haka Baffa ya shigo ya sameta, da sauri ta tura wayar karkashin filo, da murmushi ta isa gare shi tana fadin "sannu da dawowa Baffana." "Yawwa Mamana" Ya fad'a da fara'a saman fuskarsa. "Yau ban ganki rije sa kofan motana ba, ko kin fara girma?" Dariya suka saka, har Goggo wacce ta k'arasa shigowa hannunta rik'e da jakarsa. "Na dai gaji da yawa ne yau Baffa, in gaya maka yau 4 credit unit lecture nayi, ga yunwa, ga shi har sai da naje bank nayi renewing ATM card d'ina." Ta k'arasa maganar tana tura dan bakinta. "Eyyyah, sorry Ummina, a haka zaki saba kinji, tashi muje, mamanki tace baki ci abinci ba." Tana gaba iyayen na binta a baya, k'auna da soyayyar da suke mata, ya kasa 6oyuwa a saman fuskokinsu. A al'adarsu dama a part d'in Baffa ake cin abincin dare, bayan sun gama suna kai k'arfe goma, wani sa'in har sha d'aya suna fira, daga nan zata sanya wayoyinta tare da laptop d'inta chaji a nan, ta wuce d'akinta ta kwanta. Sai dai yau abin ya banbanta, tunawar da tayi cewar Sadam yace zai kira idan ya koma gida, haka kawai taji tana son ansa kiran nasa, ko ba komai zai yi abinda zai bata dariya.6 Suna gamawa ta kwashi kayayyakinta ta wuce d'aki, tare da watsa ruwa a jikinta, ta canja zuwa kayan bacci, har kuma a lokacin wayar Sadam bata shigo mata. Ta gama duk wani abu na al'adarta, ta hau gadon ta kwanta, sai dai hankalinta ya kasa kwanciya, har tana tunanin ko dai wani abun ya faru da shi. Ganin har sha biyu da rabi, amma bai kira ba. Ta kasa daurewa, dole ta latsa kira a layinsa, sai dai har ta gama ringing ba'a d'aga ba. Hakan sosai, ya kara tunzura zuciyarta Inda a zuciyarta cewar, tabbas ba lafiya ba.7 'Menene damuwarki da shi?' Wata zuciyar ke tambayarta. Juyi tayi tare da fadin "haka fa, menene abin damuwa da d'an rainin hankali." A haka bacci mai ta samu ya yi awon gaba da ita.K'arfe bakwai da rabi agogon dake gefen gadonsa ta nuna, cikin firgici da magagin bacci ya shafe idon tare da mik'ewa da sauri ya fad'a toilet. Wanka yayi, ya shirya a gurguje. Cikin sauri ya tarkato wayarshi da sauran kayan aikinsa ya fito yana mai watsa su a kujerar dake gefenshi, ya zagaya ya shiga motar, ba tare da 6ata lokaci ba ya zarce wurin aiki.7 Borin kunya ne duk ya ishe shi, lokacin da ya isa, dan duk wani ma'aikacin da ke bankin, babu wanda bai hallara ba. Hakan yasa ya dinga cin magani yana basarwa, har ya isa kujerarsa, bai cewa kowa komai ba.1 Customers da yawa ya samu a wurin, dan haka ya maida hankali wurin sauraren k'orafe-k'orafen da suka zo dashi, bai kuma samu kansa ba, har sai wurin k'arfe sha biyu na rana. Mik'ewa yayi, ya shige office d'in manaja, ya hada coffee ya fito. Ya samu gefe ya zauna, yana kur6awa a hankali, yayin da yake jin wata natsuwa na saukan mishi a lokaci guda. Wayarsa ya fitar a aljihu, wacce chajin gaba d'aya bai fi 20% ba, dan kuwa bai samu halin sakawa a daren jiya ba. Missed call d'in Jay ya ci karo da shi, hakan yasa ya murmusa kad'an, yana gadin "I knew it Sako ya fara rubuta mata, "Hey, how was your night? Terrible, right? Without hearing my sweet voice. Do text me where U're right now, I will come and see you idan na fito lunch. Okay? Do take care.7 -Kazaure. *** A hankali take sauka matakalar benen theatre hall d'in da suka gama lecture, shigowar sakon da ya riski wayarta, yasa ta ja gefe, tare da fitar da wayar a cikin jakarta. Murmushi mai sauti ta yi, ganin lambar Kazaure. "Lallai mutumin nan yaga wurin kwana na, wai me yake d'aukar kansa ne?" "Yan mata text din wa ake ma irin wannan murmushin k'aunar?" K'awarta Miemie ce ke tambaya, lokacin da ta k'araso gabanta tasa hannu ta warce wayan tana dubawa. Dariya Jay tayi, "Dan Allah ki bani wayata, wani d'an duniya ne yake k'ok'arin raina ni, bani kiga yadda zan koya masa hankali." Miemie na karanta text d'in ta kwashe da dariya, "Allah ya kama ki, yau kam sai naga wannan bobon da kike ta faman 6oyewa." Gaba sosai da inda suke ta matsa, ta fara maida masa da ansa ba tare da tunanin komai ba. "Ina cikin school, call me idan ka shigo." "Ya salam! Me kike yi haka Miemie? Idan ya zo zaki san yadda zakiyi da shi wallahi, dan ni kam ba zan iya daukar rainin wayon mutumen nan ba." "Just shut up please…" Miemie ta fad'a tana dariya, "kina so kina wani kaiwa kasuwa, sai ki zo nan ki ishe ni ke bakya soyayya, ke waye, ke waye. To asiri dai ya tonu." "Mtseww, kina da matsala wallahi," Jay ta fad'a lokacin da ta gyara zaman jakarta a kafadarta, ta rungumi dogon littafin da ke hannunta ta fara tafiya, ba tare da ta kara bi ta kanta ba. Bayanta ta biyo itama, a hankali suka fara takawa cike da natsuwa a tattare da su. Kadan ta juya tana kallonta. "Ki yarda da ni Miemie, guy d'in nan ba komai na ne ba wallahi, we just met a bank, day before yesterday, shine fa yake neman raina ni, yana wani abu like he owns the whole of me, sai kace wata matar da yake aure." Murmushi Miemie tayi, a hankali ta furta "Irin na shi salon kenan, nd believe me, maza irinsu, suna saurin sayen zuciyar yan mata, ni bana son wawan namiji, wanda bashi da say, sai abinda mace ta fad'a." "Hmmmm, baza ki gane raini irin na Kazaure ba." Cewar Jay, tare da juyar da kanta. "Zan gane idan ya zo ai" Ta bata ansa, tana dariya. Inda tayi parking suka karasa, a tare suka sama ma kansu mazauni cikin motar, kafin ta tada zuwa inda zasu ci abinci. ** Waayar Jay ce ta fara kururuwar neman agaji bayan sun fito daga masallaci. Ko da ta fitar ta ga lambar Kazaure, bata bata lokavi ba ta mika ga Miemie, ta kara da fadin "kinga d'an rainin hankalin sai yanzu yake kira ko? Sai ki ansa ki san yadda zaki yi da shi." Ansa tayi da sauri, ta d'aga wayan, "Daukan wayar kike ma jan aji? After all na san kin matsu ki sa ni a idonki." Dariya ta so k'wace ma Miemie, sai dai ta daure tana mai kaikaita murya, "Wa ya baka wannan labarin kuma? Wait, what do you even think of yourself?" Ta gefen kumatunsa ya saki murmushi, seta idanunsa yayi a jikin madubin motar, tamkar mai son karantar wani abu. "Da zaki ba mai wayar wayanta, duk da ya fi muku wasa da hankalin da kuke mun." Da sauri ta kashe wayan saboda dariyar da ta ci karfinta. Idamunta a kan Jay, sai dai ta gagara furta ko da kalma guda. "I told you." Jay ta fad'a tana mai anshe wayarta, ta d'ora da "Iskancin Kazaure yawa ne da shi Miemie. Ban san me yake d'aukar kansa ba wallahi." Sakon da ya shigo ne ya dakatar da gaba dayansu, hannu tasa ta bude. Kazaure ne kamar yadda tayi tsammani. Ki gode Allah ina son in taimaka miki, dan bana son ki ba kanki wahalan zuwa bank just to see this handsome man. Will be there in 5 minutes. Muahh.11 -Kazaure. Dariya Miemie ta d'auka, a sa'ar da Jay ta gyara tsayuwa tana yi mata duban tsanaki. "Wannan ba abun dariya ba ne Miemie, kinga kina neman ja mun raini wurin mutumen nan ko?" "I'm Sorry habibty," ta fad'a tana dafa kafad'arta, "wallahi soyayyar taku ne tana bani dariya. Trust me, you'll make a very cute couple ever, this I believe. Ke zafin kai, shima yana ji da nashi." "Mtseww.. you're crazy Miemie." "Point of correction, we're." A tare suka saki dariya, suna ci gaba da jifar junansu da sunayen tsokana. ** "Gashi yana kira, ki ansa kuyi magana." "Zai kara ganewa wallahi." "Sai kuma me? Ke fa kika kira shi Miemie." Bata kara cewa komai ba ta ansa wayar, wuein da suke ta kwatanta mishi,ba'a fi minti biyu ba ya iso, ya adana motarshi gefe kadan da tasu. Yadda ko wane sawu nashi ke sauka a cikin kasa, cike yake da alfahari, da takama. Budawa yake, cikin yanayin da ya kan tafiyar da zuciyar matayen da suka yi arba da kallonsa. Kai tsaye inda suke zaune ya dosa, hakan ya ba Miemie damar gane shi, ta kuma saki baki tana mai yi masa kallon kurilla, murya k'asa-k'asa ta isa setin kunnen Jay tana fadin "He's too cute. Dole kike boye abinki." D'an gajeren tsaki Jay ta yi, dai-dai lokacin da ya k'araso, gefen Miemie ya tsaya, idanunsa na dubanta. "Hi" "Hi" Ta ansa mishi itama, bai damu da yadda ta shagaltu a kallonsa ba, ya sauke idanunsa kan Jay, yana mai kafe ta da mayun idonsa masu neman yin barazana da duk wata natsuwarta. "Kinyi missing d'ina ko?" Ya tambaya la66ansa mak'ale da killer smiling d'insa, hakan yasa tayi k'asa da nata idon, kamar yadda bakinta ya gagara furta ko da kalma daya, illa bugun zuciyarta da ya tsananta. Mik'ewa Miemie tayi, a lokacin ya maida hankalinsa gareta, "Ina zaki je ki banni da ita? Bayan kina ganin sarauta take ji ko magana ta gagara yi mun. Please ki zauna ki taya ni siyen bakin Gimbiya." Yawu ta had'e mak'ot, saboda muryarsa, sosai ta tafi da ita ba.1 Very eloquent nd husky. Ta furta a kasan zuciyarta. A hankali ta juya tana kallonsa. "Ka koyi kula da ita ba tare da taimakon wani ba. Baka san me gaba zai haifar ba. So, you two have a good time." Ta maida kallonta ga Jay, "ki kira ni idan kin gama." Daga haka ta wuce, zuciyarta ya shagaltu wurin yaba haduwa da tsarin halitta na Sadam Kazaure. A wani fannin har tana tunanin ina ma itace tayi dacen cikakken namiji irin shi. ** Gabanta ya duk'a, yana kokarin seta idanunsa cikin nata,4 "Wai meye sai wani shan kanshi kike mun? Ko Nayi laifi ne? Of it's about yesterday, kiyi hakuri, I can explain" Ya k'arasa cikin muryar tausasawa. Ta dago a tsanake, cikin rashin sa'a ta sauke idanunta a nashi. "Ban san me kake nema da ni ba.." Shine furucin da ta hada da kyar, tana kawar da fuskarta a dubansa. Ganin yadda ta tsinci zuciyarta da son k'awata mata tsaruwar halittarshi, a wani bangaren tana mai tabbatar mata da cewar x gayen yayi, dai-dai yadda ake so namiji yazo. Muryarshi ce ta katse ta, cikin tausashshen amo ya fara magana da idanunsa har yanzu a kanta. "Zan iya cewa na riga da na samu abinda nike nema, i mean lokacinki, now abu d'aya yayi saura kawai." "Me kenan?" Muryarta a tausashe ta furta tana kallon kwayar idonsa. "Soyayyarki Jameela. Ban sani ba ko zaki taimaka bawan Allah irina?" Duk wata ga6a da ke jikinta sai da ta dakata na wucin gadi, a hankali ta d'ago ta kalle shi, sai dai ta kasa gaskata abinda take gani a cikin k'wayar idanunsa. "Please" ya fad'a cikin wata irin murya mai rauni. Dak'yar ta iya tattaro natsuwarta, tana mai kawar da kai daga dubanaa ta fara magana. "Abinda nike gani cikin idanunka ba soyayya bane Kazaure. Baka tunanin zai fi kyau mu hak'ura mu mutunta junanm?" "Zata iya kasancewa ke kike jin hakan a tare da ke. Ban san lokacin da hakan ya fara ba, amma ina jin bazan iya rayuwa ba tare da soyayuarki ba. I'm madly in love with you Jameela, nd this is all I can say." A hankali fuskarsa ta fada wani yanayi mai rauni. Cikin tausasawa ya ci gaba "..ki sani ko da wasa, bazan taba takura ki a kan ki so ni ba. Amma idan kina bukata, zan iya baki lokaci daga nan har zuwa sadda kike jin zaki iya bani ansata." Da gama fadar haka ya mik'e, bai jira mai zata ce ba, ya kama hanyar inda ya ajje motarsa. *** A zahiri, sosai maganganunsa sun samu wuri cikin kanta. Sunyi tasiri a cikin zuciyarta mai matukar girma, sun kuma tabbatar mata abinda ke cikin tashi zuciyar kenan. Bata motsa a inda take ba, har lokacin da ta ji wani abu ya tsirga zuciyarta, ya zarce yana bin dukkan wani jini da ke gudana a cikin jikinta. A daidai wannan gabar, so da k'aunar mutumen da bata taba zato ba, suka mamaye dukkan wani lungu da sak'o na sassan jikinta. "I'll take care of you Kazaure."3 A hankali tayi furucin, ta d'ago da zumar k'ara kallon cikakkar halittarsa, sai dai ta neme shi sama ko k'asa, babu shi babu dalilinshi. W aige-waige ta fara yi, can ta hange shi yana k'ok'arin bud'e mota, hakan yasa ta saki ajiyar zuciya, tana mai tsaida idanunta k'yam akansa, sai kuma a yanzu take ganin cikakken zubi da surar da Allah yayi mishi. *** Tun daga ranar da idanuwanta sukai tozali da shi, wani bak'on lamari ya ziyarci zuciya, da gangan jikinta wanda ta kasa banbance ko wane iri ne, a yanzu kam ta gama sakankancewa, har kuma zata iya yi ma lamarin lak'abi da zazzafar k'auna, mai azabtar da zuciya, wacce ga dukkan alamu zata yi wuyar magani. Wani gwauron numfashi ta saki, daga bisani ta murmusa, sannan ta mik'e ta fara kiran Miemie, kasancewar suna da lecture k'arfe biyu. ** A gajiye sosai ta shigo gidan, ga mamakinta ta samu Goggo da Baffa zaune samar teburin cin abinci. Abinda ya tabbatar mata da bai jima da dawowa ba, shine jakarsa da ta gani ajjiye, kan d'aya daga cikin kujerun dining d'in. Fara'a sosai ke shimfid'e a kan kyakkyawar fuskarta, ba tare da ta gaishe da su ba ta isa da sauri ta rungume Goggo ta bayanta, yayin da ta kai duba ga Baffa tana fadin "Baffa yau ka dawo da wuri. Ko dai ko dai?" Ta k'arasa maganar tana dariya, tare da nuna plate din da ke gabanshi, sannan ta koma kujerar gefensa ta zauna. Cokalin hannunsa ya ajje, yana mai tattaro natsuwarsa, ya d'auki hannunta ya rik'e saman teburin, sannan ya dubeta cike da kulawa. "Lallai Ummina kin san waye babanki, wallahi da yunwa na shigo, sanin kanki ne kuma ban saba da abincin waje ba. Jira, ba ma wannan ba, yau naga farin cikinki ya fi na kullun, sa6anin da idan kika dawo school bakya fara'a haka, menene sirrin Mamana?" Ya k'arasa maganar lokacin da ya kuma kai lomar abinci a bakinsa, har kuma a yanzu hankalinsa na kanta. Fara'ar dake kan fuskarta ce ta kuma fad'ad'awa, tana mai kai duba gare shi, tace "ni kaina ban san menene dalilin ba Baffa, haka kawai nake ji na cikin farin ciki, tunda na baro skool." "Da dalili dai Baby." Cewar Goggo dake saurarensu. Daga bisani suka sa dariya, yayin da tace "Allah ba komai Goggo." "Masha Allah" cewar Baffa, inda ya cigaba "ya kamata ki ci abinci kema, da ganin idanunkin nan ba karamar yunwa kika kwaso ba." "A'a fa, ni kam na ci na k'oshi a makaranta, wanka kawai zanyi in huta, tun maghriba bai ida ba." Daga haka ta wuce d'akinta, tana mai watsar da tarkacen hannunta a tsakiyar d'akin, in banda wayarta wacce take k'ok'arin kiran lambar Sadam bayan ta dai-daita zamanta a bakin gado. Har wayar ta gama rurinta amma bai d'aga ba, hakan ba k'aramin jefa damuwa yayi a k'asan zuciyarta ba, tana mai addu'ar Allah yasa ba fushi yayi da ita ba. Kira ta kuma yi a karo na biyu, cikin sa'a ya d'aga, sai dai bai ce komai ba. "Errrnmn" Ta dan yi gyaran murya. Hakan yasa ya sassauta muryarsa mai cike da tsananin damuwa ya ce "Ban san me kike ki fada mun ba Jameela. Bayan k'iyayyata karara da na gani a cikin idanunki, menene yayi saura a yanzu? For God's sake, ki bar ni inji da zuciyata da ke harbawa da so da kaunar wacce bazan taba samu ba."8 Baya ta koma ta kwanta rigingine tana kallon yadda fanka ke juyawa jikin ceiling d'in d'akin. Wani irin shauk'in soyayya ne ke d'ibarta, a rayuwa bata ta6a zaton akwai wani d'an adam wanda zai zo farad'd'aya, har ya samu irin wannan soyayyar daga gare ta ba. Sai da ta tattara natsuwarta, sannan ta fara magana. "Me zaka ce idan zuciyata ta k'aryata idanuwan da suka hangi k'iyayyarka a gare ni?" Bai ce komai ba, sai wani murmushi da ya saki na musamman, ya gyara zama tare da cewa "Zan kasance cikin tsananin farin cikin da ba zai gushe ba har izuwa k'arshen rayuwata." Murmushi ta saki wanda ya nuna ta ji dad'in kalamansa, yayin da ta d'ora da cewar "ka gargad'i idanunka, kada su kasance masu yi mun wannan kallon daga rana irin ta yau."1 Ta numfasa sannan ta cigaba "Su rink'a kallo na a matsayin wata mace ta daban, wacce take da kyakkyawan gurbi a cikin zuciyar Kazaure." Gefen titi ya samu ya yi parking motarshi. A hankali ya furta "Jay?" "Yes!" Ta ansa shi. Cigaba yayi da cewa "Are you really the one?" "I'm Sadam, kana mamaki ne?" "No, I just don't know what to say, I just can't believe it. OMG!" Dariya tayi mai d'an sauti, tare da cewa "ka yarda da ni, I'll never let you down." "No, I can't Jameela, you've to prove it." Juyi tayi, tare da rungume pilo, sannan tace "me zanyi wanda zaiyi proving maka gaskiyata?" Kanshi ya sosa, yana mai lank'washe k'afarsa d'aya, yayin da ya d'ora d'ayan kan steering, sannan yace "Zan so idanuna sun ganki su tabbatar da mun da hakan." "How?" Ta tambaya, tana wasa da yatsun hannunta. "Ina son ganinki yanzu, sai na tabbatar ma idanuna, cuz har yanzu kunnuwana sun gagara gaskata abinda kika fad'a." "Yanzu?" Ta tambaya tare da d'an fito da ido waje. "Yes, if you really mean it." "Of course I mean it, sai dai Baffana baya bari na fita in dai maghriba ya riga yayi." Damn it Ya fad'a a k'asar zuciyarsa. Yayin da a fili yace "Ni kuma ya zakiyi da ni? I want see you seriously, ban san halin da zan shiga ba in ban ganki a daren nan ba." Jin yadda yake magana cike da damuwa yasa itama ta tsinci kanta cikin tsananin damuwar da take da tabbacin ta ninka tashi, muryarta a sanyaye tace6 "I don't know Sadam, I wish I've a way, but wallahi bani da wani alternative, kuma yau Baffa ya dawo da wuri, ban san ya zanyi ba." "Promise me one thing." Ya fad'a kaman zai fashe da kuka. "What?" Ta tambaya tare da tattara natsuwarta gare shi. "Zaki biyo ki ganni a bank gobe kafin ki wuce skool, shine kad'ai hak'urin da zan iya yi, if not wallahi zan zo k'ofar gidanku yanzun nan." Yadda take ji a halin yanzu, zata iya yin koma menene matsawar zai haifar da farin ciki a zuciyar Sadam d'inta, hakan yasa ba tare da wata fargaba ba tace "I promise." Alal hak'ik'a duk wanda yayi duba ga fuskar Kazaure, zai iya cin karo da tsadaddan murmushin da yake saki, wanda yake nuni da cewar yana cikin farin cikin da ba zai ta6a misaltuwa ba, bai ta6a tunanin zata yi sauk'in kai har haka ba, a yadda yaga kanta na rawa rana ta farko da ya fara ganinta. Zan koyar dake soyayyata." Ya fad'a a k'asan zuciyarsa, yayin da a bayyane yace "I feel loved babe girl." Murmushi ta saki, wanda yake bayyana yadda take jin tsantsan soyayyarsa mai cike da wani SABON SALO, wanda ba kowanne namiji bane ya iya ta. I love you Kazaure Ta nanata a k'asar zuciyarta, tare da k'ara k'ank'ame pilon dake k'irjinta. Yadda suke firarsu, mai saurare zai d'auka wasu tsofaffin masoya ne, wanda suka shafe shekaru suna taka rawa a filin yak'in soyayya. Yadda yake jinsa a yau, baya tunanin akwai abinda zai iya raba sa da Jay, ko da kuwa sana'ar da ya gi kauna giye da komai ce. Kusan kwana suka yi suna waya, sai da ya tabbatar da babu wani gurbi da yayi saura wanda bai cike da soyayyarsa ba a zuciyarta, sai da ya cusa mata k'aunar ra'ayoyinsa, ya kuma d'ora ta akan yadda yake son soyayyar tasu ta cigaba da gudana.Bakin skinny skirt, da farar riga mai tambarin H&M ne sanye a jikinta. Jacket dinta baka, jaka da takalminta k'irar Channel ta d'ora, sannan ta matsa gaban madubi ta k'are ma kanta kallo tsab. Gyalen da ta yane kanta fari ne mai tambarin LV da kalar baki, sai da ta tabbatar babu wani wuri da ya bada matsala, kasancewar bata son tayi abinda ba zai gamsar da kallon masoyinta ba, kafin ta Murmusa, tana mai daukar ipad d'inta ta rungume, ta fito zuwa bangaren mahaifinta.+ Zaune ta same su, hannunsa rik'e da remote yana kokarin canja tasha, Goggo da ke gefenshi tana mai hada masa ruwan Lipton din da ya wadatu da kayan kanshi. Tsakiyarsu ta zauna da murmushi saman fuskarta, cikin siririyar muryarta tace "Barka da Asuba Baffana." Murmushi ne d'auke a fuskokinsu gaba daya, yana mai dawo da dubansa gare ta ya ansa, "kin tashi lafiya Mamana?" "Lafiya lau Baffa" ta bashi ansa, sai kuma a lokacin ta kai duba ga Goggo tare da gaishe ta cikin harshen fullanci. Da yaren ta ansa ta itama, hakan yasa duk suka sanya dariya. Baffa ya kalle su da fadin "abin 'yar haka ne ko Ummina?" "Kai ma ai na gaishe ka da yarenku Baffa." "Son kai dai, k'ila ma wani abun kuka fad'a saboda kun san ba ji nake ba." "A'a fa Baffa na." "To shikenan na yadda da ke Mamana." Goggo dai da ke gefe dariya ce tata, sai daga bisani ta kai duba gareta tana tambayar "Kin yi breakfast kuwa?" "Na sha tea dai, na dan makara kadan ma." ta bata ansa lokacin da ta mike, tana gyara mayafinta. "Zo nan Ummina" Baffa ya fada tare da ansar shayin da Goggo ta mik'a masa. Babu gardama ta dawo inda ta tashi ta zauna. "Muje ki ci abinci kafin ki wuce, kina ji na?" Agogon hannunta ta kalla, sannan ta dago da fuskarta a shagwa6e. "Baffa na makara wallahi." Bayanta ya shafa a hankali, "Ya isa haka, tunda hakan kike so ai magana ta kare. Babu dai wata matsala ko?" Dariya mai sauti ta saki, "Bakomai Baffa na." Addu'ar neman sa'a duk suka raka ta da shi, kafin ta fito zuwa harabar gidan. A wanke fes ta samu motarta, bata 6ata lokaci ba ta shige, ta kama hanyarta. Earpiece ta mak'ala a kunnenta, tana tuk'i suna waya da Kazaure, wanda ya shaida mata cewar shigowarsa bankin kenan, ya kuma k'ara da cewar bazai fara aiki ba har sai yaga kyakkyawar fuskarta. Da wannan farin cikin ta k'ara gudun da take, tafiyar mintina goma sha biyar ta kaita gaban Zenith Bank dake kan titin k'ofar K'aura. A gefe tayi parking ta fito, har kuma a lokacin basu daina wayar da shi ba, daga bisani ta shaida masa zuwanta. Ba'a fi minti biyu ba ya fito, hannuwansa duk biyun a aljihun wandonsa, farar riga da bakin wandon da ke sanye jikinsa, sosai sun kawata cikar halitta da zatinsa. Sun matuk'ar ansar kwantacciyyar fatar jikinsa, mussamman yadda zanzaron yayi k'asa-k'asa sai abin ya zama wani salo na daban, cikin natsuwa da jan hankali yake takowa, hannuwansa suna masu budawa, yayin da faffad'an k'irjinsa ke barazanar yin ado a gare shi.3 18 Jikin mota ta jingine tana mai rungume hannayenta zuwa kirjinta, idanuwanta sosai ta buda, dan sun shagaltu a kallonsa, tana jin sautin dirinsa tamkar tashin bom a cikin kirjinta. Kauna da soyayyarsa take jin suna mata yawo a gaba daya gabar sada jini ta jikinta, suna zarcewa kasan ruhinta suna masu sama ma kansu mazauni a tsokar da ke tsakanin kirjinta. "Jay.." Budaddiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Cikin rashin kuzari da dabara ta dai-daita tunaninta, ta d'ago ta jefe shi da k'ayataccen murmushin da ta tabbatar yana kara fito da tsaruwar tata halittar. "Mr. Kazaure, how was your night?" "Not bad" ya fad'a yana mai sosa girarsa, tare da juyawa yana kallon gefe, "you?" "Alhamdulilla, Ta bashi ansa, sa'adda ta cigaba "na cika alk'awari ko?" Tayi maganar da sassanyar muryar da ta sa shi rintse ido, kafin ya bud'e ya sauke su akanta. "Sure, sai dai wannan bai ishe ni ba, so definitely ki saurari zuwana da zaran na fito lunch. Cuz I hate duk wani abinda zai nisanta ni da ke." Kallon shi take, lokacin da zuciyarta ta lula tunanin irin sa'ar da take da shi a rayuwa, godiya take ma Allah da ya had'a ta da irin namijin da take so, mai matuk'ar nuna tarairaya da kulawarsa gare ta. Baya son yin nesa da ni.4 Ta furta a cikin zuciyarta, abin ba k'aramin dad'i yayi mata ba, hakan yasa ta murmusa tana fadin "I'll love that." Ba dan sun gaji da ganin juna ba suka hakura, sai dan dukansu akwai ababen da ke gabansu, wanda kuma sune suka katse jin dadinsu a dai dai lokacin. Hannu yasa a bud'e mata gaban motar ta shiga, a lokaci guda ya mayar da murfin ya rufe, sannan ya tura kanshi cikin glass d'in yana fadin "Do take care of yourself for me." "In sha Allah, nd you do the same. Okay?" "Kar ki damu." Ya fad'a lokacin da ya ja gefe, yana kallon yadda ta murza injin, ta lula saman titi, har ta bace ma ganinsa. *** A haka rayuwar ta su ta cigaba da tafiya, kullun da safe kafin ta wuce makaranta zata ta biya banki ganinsa, inda shi kuma da zaran ya fito lunch, ko sallah baya tsayawa yake kama hanyar makarantarsu. Da haka suke samun damar ganin juna, domin kuwa yanayin aiki baya barin Sadam fita sai yamma, a 6angarenta kuwa bata da damar fita ko ina idan maghriba ta riga ta yi. Idan kuwa tana makaranta, ko da lecture take, da lokacin zuwansa yayi, dole ta fito, baza ta iya jure rashin ganin fuskarsa mai tafiyar da duk wata damuwarta ba, ta gwammace tayi missing lecture, kan ace tayi missing ganin fuskar da ke haifar da farin ciki a birnin zuciyarta. A cewarta wannan ce kad'ai damar da suke da.5 Tsaye ta hange shi gefen motarta, kyakkyawan murmushi ta dora a kumatunta, ta karasa da takunta da ya kan daburta dukkan tunaninsa. A motarshi ya dauke ta zuwa kasan wata bishiya mai yawaitar rassa da sanyin inuwa, yanayin da take gani a tattare da shi a yanzu, bakon yanayi ne, da bata taba cin karo da shi a fuskarsa ba. Idanunsa ya kafe ta da su, muryarsa cike da tausasawa ya ke fadar "How's my baby doll doing?" "Ban san me zan ce ba. Yanayinka na yau yasa na manta yadda nike ji ni kam." Ba ta karasa rufe bakinta ba, ta ji faffadan hannunsa cikin nata. Wannan ne karo na farko da hakan ya ta6a shiga tsakaninsu. Amma ta tsinci zuciyarta da tsinkewa, jinin jikinta yana gudu da dukkan saurinsa, yana haifar mata da kasala, da yanayin da ya fi gaban misali. Hakan bai dame shi ba, dayan hannun ya dora a kan nata, yana mai ci gaba da kallon k'wayar idanunta.4 Dak'yar ta iya tattara natsuwarta, tana mai sauke idonta k'asa, muryarta a dakushe, ta samu kwarin gwiwar hada kalmomin "Sadam what are you doing?" "A ina?" Ya tambaya tare da kafe ta da idanunsa. Cikin sanyin jiki ta fara kokarin zare hannunta da ke cikin nashi, murya na rawa tace "Ka san dai ina sonka, right?" Bata jira ansarshi ba ta cigaba, "please kada mu fara haka da kai, matsawar ba shine abinda ya kawo wurina ba." Fuskarsa na kanta, idanunsa sosai sun k'ank'ance, cikin wata irin muryar da bata sanshi da ita ba ya fara magana, "But this is the 1st time Jay, kuma nayi ne ba dan komai ba sai dan nuna soyayyata a gare ki, what's there dan na rik'e hannunki?" Ya k'arasa sa'adda ya gyara zamansa, sannan ya cigaba "you've no idea how i feel about you Jameela, sanin kanki ne ina k'ok'arin danne zuciyana akan yadda sonki ke azalzala ta, ki tuna ba fa ko da yaushe nake tare da ke ba, d'an lokacin da nake samu in gana dake duka guda nawa ne? Dan na rik'e hannunki shine kuma har ya zama wani abu? Babe kece fa kike ce ba'a barinki fita a gida, kina tunanin hakan baya takura mun ne? Ko kina tunanin bana cutuwa da rashin ganinki a duk sadda na buk'ata? Ki tausaya mun mana, ya kike so nayi da so da k'aunarki da kullun suke k'ara yad'uwa a cikin zuciyata? Ya zanyi da abinda nake ji game dake?"12 Juyar da kansa yayi tare da girgiza sa, sannan ya k'arashe da fadin "I can't take this anymore, tun wuri gara kisan yadda zakiyi da ni, tun ban je na fara neman wasu matan ba." Yana gama fad'ar haka ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa, tare da kama k'ofar motar yana k'ok'arin ficewa. Rigarshi ta rik'e gam, hakan yasa ya dawo ya zauna, narkakkun idanunsa ya zuba mata. "what Jameela? Menene kuma, bayan k'yamar da kike nuna mun? Please ki bar ni na tafi, cuz bazan iya zama wurin da ake k'yamata ta ba."11 "Ba zan iya ba" Ta fad'a tare da kafe shi da idanunta, yayin da zuciyarta ke halbawa fat fat, tana buk'atar agajin gaggawa. Dak'yar ta iya cigaba da magana "Ban ta6a k'yamatarka ba ko sau d'aya, sai dai ina guje ma abinda hakan zai haifar, saboda irin soyayyar da muke ma junanmu, ka yarda da ni, kai ne farin cikina, kaine mutumen da zuciyata ke son gani cikin kowanne irin hali. Ka fahimce ni mana" "Fahimta kamar ya? Sanin kanki ne babu namijin da zai yadda da abinda kike man, nine kullun ina barin aikina ina biyo ki school? No, this can't be babe, gara mu canja shawara gaskiya, ni kam na gaji da ra6e-ra6en nan." Yadda yake maganar yasa hankalinta ya kai k'ololuwa wurin tashi, ajiyar zuciya mai k'arfi take saukewa, tun da take a rayuwa bata taba sanin meye tashin hankali ba sai yanzu da take jin tamkar zata rasa mutumen da numfashinta ke fita da soyayyarsa. "Ban san me kake so ba. Just tell me, I promise I'll do whatever it is."1 "Babe ya kamata kii gane ke ba yarinya bace, ya kamata ki sanar da iyayenki cewar U're big enough to have a boyfriend, tunda dai ke mace ce, kuma dole wata rana aure zaki yi ki barsu. This is the only way out, idan kuma baki yadda ba fine, nasan dama ni kawai nake hauka na, ba so na kike yi ba." Kanta a k'asa yake, maganar da yayi yasa ta d'ago a firgice, ta sauke idanunta a kansa. Sai dai a zahiri ta fad'a duniyar tunanin yadda zata fuskanci Baffanta da maganar wani, ta tabbatar ko giyar wake ta sha, ba za ma ta iya tunkararsa da makamanciyar wannan maganar ba. A wani fannin tana jin baza ta iya sa6a umarnin Sadam da abinda yake so ba, dan haka dole ta sama masu mafita, dole ta san hanyar da zata bi domin tsare mutuncin soyayyarta. A hankali ta d'ago, tana kallon yadda cikin dan karamin lokaci ya fita a hayyacinsa, ta tabbatar kaunar da yake mata ta fi gaban dukkan tunaninta. "It's okay Sadam" ta fad'a cikin sanyin muryar da ta sanya shi juyowa yana kallonta. "Shikenan, zamu yi maganar idan na koma gida. Okay?" "Fine." Ya fada yana yada motar, zuwa gaban facultynsu. "Wull hope to see you in something unique, not this black and white outfit. Na gaji da su wallahi." Murmushi ta saki, wanda masoyin da ake bala'in k'auna kawai ake yi ma irin shi, sannan ta tsaida idanunta akansa "Never mind, zan yi maka gayu, sai dai I'm not good in make up at all." "Ni dai ko ya ne ina so, just assure me zaki bar ni nazo har gida na gani." "I assure you, ko da ban samu yarda da amincewar Baffa na ba." Ta k'arasa maganar yayin da ta rungume hannayenta, sannan ta cigaba, "kai dai ka yadda da ni kawai, ka kuma yadda cewar I can do anything for you." Murmushi ya saki mai sauti, ya k'ura ma steering motar ido, da alama akwai abinda yake tunani, daga bisani ya juyo da kallonsa gare ta sannan yace "tell me you love me, in ba haka ba ko na tafi bazan samu natsuwa a tattare da ni ba." Kanta ta girgiza, inda a zuciyarta take cewa "Sadam rigima" yayin da a fili ta furta "I love you Mr. Kazaure." Lumshe ido yayi, ya kwantar da kansa jikin kujera, "you saved a life. Thanks babe." "Anything for Mr. Romantic." Da sauri ta wuce, ta barshi yana jinjina kalmarta, kafun ya tada motar ya wuce. **** Karfe biyar na yamma suka fito makaranta, tuk'i take, amma kunnenta mak'ale da earpiece suna waya da Sadam wanda yake jaddadada mata zuwansa k'arfe takwas na daren yau. 5 Jin wayar ta su bata da niyyar k'arewa yasa Miemie fara k'orafi, haka ba dan ran Jay ya so ba ta kashe wayar ta tsaida kallonta a titin gabanta. Hannu Miemie tasa ta ta6a ta, "hey what's your problem?" Ajiyar zuciya Jay ta yi, hankalinta na kan titi ta furta "soyayya Miemie." Dariya Miemie tayi tana cewa "eyyeh!" Ba tare da tayi duba gareta ba ta cigab "ban san lokacin da na kamu da soyayyar Kazaure mai tsanani har haka ba, gashi kin dai san agenda ta da Baffa, babu saurayi tunda na za6i karatu, amma fara tarayyata da Sadam na neman rugurguza duk wani buri da na ci ma karatu na. In tak'aice miki Miemie ko abinci bana jin dad'insa irin yadda nake jin dad'in sauraren murya ko kuma kallon fuskar Kazaure. Ina yi mashi wani irin so, wanda Allah ne kad'ai zai iya sanin iyakarsa." Tana kaiwa nan ta juya steering, tare da shiga kwanar da zata sada su da unguwarsu Miemie. Alal hak'ik'a ko ita ta samu kamar Sadam baza tayi wasa da damarta ba, zata so shi, ta kula da shi, ta kuma ririta shi tamkar tsokar nama d'aya a cikin miya. Abinda Miemie ke innatawa kenan a k'asar zuciyarta, daga bisani ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Jay, tace "kin gane ko, soyayya wani abu ce wadda mutumen da ya fad'a tarkonta shi kad'ai yake sanin halin da ya ke ciki, a tunanina idan kika karanta ma Baffa komai, zai fahimce ki, akan ki dinga tarayya da Sadam a 6oye, gara kowa ya sani, ko da akan samu wata matsala zuwa gaba, duk da ba fatan hakan muke ba, amma zaki ga abin ya zo da sauk'i." Tsayuwar motar ta gyara, inda ta juya ta kalleta tace "abinda nake shirin yi kenan, dan shi kanshi Sadam ya gaji da wannan ra6e-ra6en da muke yi. So in sha Allah zan kawo k'arshen abin cikin 'yan kwanakin nan." "Better" Miemie ta fad'a lokacin da ta bud'e k'ofar sannan ta k'ara da cewar "see ya tomorrow lover girl." Dariya ta saka, tare da kai mata duka amma ta kauce, ta fice da sauri tana dariyar itama.1 ** K'arfe takwas saura minti ashirin agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ta nuna, hakan ya tabbatar mata da cewar ko me Sadam yake, yana kan hanyar gidansu. Gaban madubi ta matsa tana k'ara kallon yadda ta cancare cikin fitted gown d'in atamfar holland mai kalar ash nd coffe brown, d'inkin ya zauna d'as-d'as a jikinta, tare da fitar da kyakkyawar surar da Allah ya mata. Kyakkyawar fuskarta babu komai, illa powder da red lipstick d'in da ta shafa a saman la66anta, tayi kyau sosai, domin baza ta iya tuna ranar da ta sanya atamfa a jikinta haka ba, ta fi gane ma k'ananan kaya kasancewar ba wani wuri ta cika zuwa ba. Wakar 'Best I Ever Had' ta Drake da ta fara tashi a speaker wayarta ce ta tabbatar mata da Sadam ya iso, ko kuma yana gab da isowa, domin wannan ne taken shigowar wayarsa, haka zalika abinda ta rubuta a jikin number tasa kenan 'Best I ever had.' A hankali ta taka bakin gado inda wayar take, zaunawa tayi sannan ta d'aga ta kara a kunnenta tana fad'in "This is Mrs. Kazaure, how may I help you?" Dariya ya saki mai d'an sauti ta d'ayan 6angaren, "ina k'ofar gida, will love to see you soon." Fari ta saki, kamar yana gabanta wanda yasa idanunta juyawa suka bada wani haske mai shek'i, sannan tace "will be there in a bit." "Alright Hun" ya fad'a, sannan suka kashe wayar ta mik'e, ta d'aura d'ankwalinta, ta ida fitowa tarrr, bata damu da d'aukar mayafi ba ta fice zuwa palon kai tsaye, ba tare da fargabar abinda zata tarar ba. Cikin sa'a bata samu kowa ba, hakan ya bata damar sanya kai ta fice tare da tunanin abinda zata fad'a ma Baffa, dan ta tabbatar sai yaje neman ta matsawar lokacin cin abincinsu yayi ba tare da ya ganta ba. Da haka ta fito k'ofar gidan ta same shi tsaye jikin mota ya nannad'e hannayensa tare da rungume su a k'irjinsa. Wankan da ya d'auko yau, ya fi na kullun tafiya da ruhi da gangar jikinta, hakan yasa ta kasa d'auke idanunta akansa, inda shima tunda ta fito ya gagara daina kallonta, har sai da ta k'araso, suka bud'e gaban motar a tare, suka zauna, sannan ya had'iye wani yawu da ya tokare wuyansa, murya a raunane yace "you look very beautiful." Wani tsadaddan murmushi ta saki tana kallonsa, domin kuwa tunda mutane ke fad'a mata tana da kyau, bata ta6a jin dad'i ba sai yau da Mr. Kazaure ya fad'a da bakinsa. "Yakake?" Ta tambaya tana gyara zamanta, yayin da ya ansa da "bani da lafiya, but I'm fine now, tunda naga maganin da zan sha in warke." Ba tare da ta fahimci inda maganarsa ta dosa ba ta murmusa, inda shi kuma ya cigaba, da cewar "mu je ne?" "Ina fa?" "Yawo mana" ya fad'a yana k'ok'arin tada motar. "Ba wanda ya san na fito fa, kaga kada Baffa ya duba bai ganni ba." Kallonta yayi, inda yace "to me zaki ce idan ya fito ya ganki a motar wani da bai sani ba?" Shiru tayi tana tunani, daga k'arshe tace "kuma haka ne, amma baza mu dad'e ba kada hankalinsu ya tashi." "Yes, kawai zamu sha ice cream ne mu dawo." Ya tada motar, suka fice, bata ankara ba, ta gansu a titin da zai sada shi da Liyafa Palace. A tsorace ta kalle shi tana cewa "Sadam where are you heading to?" "Liyafa" ya bata ansa kai tsaye, bashi kuma da niyyar kallonta. "Me kuma zamuyi a Liyafa? Ka dai san ba muyi haka da kai ba ko? Wallahi idan Baffa ya gane bana gida akwai matsala." "Oh my God! Babe wai me sa kike haka ne? Anya kina so na kuwa?" "Of course I do Sadam, amma ka gane wallahi akwai matsala idan Baffa ya gane bana gida." Wani wawan birki ya ja dab da kwanar da zata sada su da Liyafa Palace, inda ya saki layi ya sauka a gefen titi, ya gangara k'asar wasu bishiyoyi yayi parking, ya juya ya zuba mata ido yana kallonta. "Ya ishe ni haka please." Ya fad'a cikin wata irin murya mai sauti, a lokaci guda ya kife kansa jikin steering motar yana mai mayar da numfashi. Ganin yadda yayi magana ba k'aramin tsorata ta yayi ba, take hankalinta ya tashi tana tunanin ta inda zata fara shawo kan Sadam wanda ta tabbata ta gama 6ata mashi rai, duk kuwa da soyayyarta da take hange a cikin idanunsa. Hannu ta d'aga zata dafa bayansa, sai kuma ta sauke, amma zuciyarta ta gagara natsuwa, yayin da wani fannin ke ta ingiza ta akan ta dafa bayan ta lallashe shi, wani kuma na gargad'inta, tare da tunatar da ita cewar ba muharraminta bane. Bayan nasa ta dafa, domin zuciyar dake ingiza ta ga hakan, tafi mai gargad'in nata k'arfi. A hankali ta fara shafa bayansa, yayin da ya d'ago da idanunsa wanda suka dad'e da rinewa tare da canja kala yana kallonta. "Why? Why are you treating me like this? Dan kinga ina k'aunarki ko? Dan kinga bazan iya juya bayana a gare ki ba ko? Jameela me sa baki son ki ganni cikin farin ciki for God's sake?" Yadda yayi maganar ba k'aramin razana ta yayi ba, domin wata irin murya yayi amfani da ita, wacce a lokaci guda zata tafiyar da zuciyar duk masoyin da yayi gamo da katar da saurarenta. "Ka daina fad'ar haka please, I don't mean to hurt you wallahi, I'm sorry ka ji. Bazan k'ara ba i promise." Jin haka ya sa ya juyo gaba d'aya, tare da rik'e duk biyun hannayenta, kallonta yayi ido cikin ido yace, "I want to be with you for the rest of my life, I promise to love you, and you alone, but bazan iya jure yadda k'iri-k'iri kike nuna k'yamar ki gare ni ba, bazan jure yadda kike nuna bani da iko da ke ba, bazan lamunci yadda kike tafiyar da ni ba Jameela. Dan haka idan kin gaji da ni ki fad'a man in san stands d'ina. I'm tired of all this babe." Hawayen da bata san ko na menene ba suka sauko a kumatunta, soyayyar da take mishi ta tabbatar sai anyi k'wak'k'waran bincike kafin a samu wacce take son wani kwatankwacin haka. A hankali ta fara magana "bana jin akwai ranar da zata zo wacce zan gaji da kai Sadam, idan kuwa har akwaita, zan rok'i Allah ya d'auki rayuwata akan ace naga wannan rana. I love you, nd you know that, ya kamata ka gane halin da nake ciki mana." Hannunta ya kuma k'ank'amewa tare da narkar da idanunsa ya saita su akanta, sannan yace "you love me right?" "Of course, i do" Ta bashi ansa. La66ansa na k'asa ya lashe, a karo guda ya shafi gefen fuskarta yace "Will you marry me?" 19 Sooooo..A firgice ta d'ago tana dubansa, kallon nata yake shima, a karo guda ya d'aga girarsa, alamar 'you heard me right.' Idanuwansa take kallo, cikin sanyin murya tace "Baka tunanin yayi sauri ace mun fara maganar aure? Ka ga yanzu na fara karatu, and Baffa, kasan munyi da Baffa cewar babu boyfriend ma har sai na gama makaranta. Ta ya kake tunanin zan tunkare shi da wannan batun?" "Oh really? Ni d'in da kike cewa kina k'auna, nine baza ki iya kai maganata wurin Baffa ba ko? Nagode Allah da ya sa na gane stand d'ina tun ba'a je ko ina ba." "Please Kazaure, me sa kake magana haka, dan Allah ka daina maganar nan mana." "Ba wani magana da zan daina Jay, you just don't love me, That's it." Daga haka ya sake hannunta dake cikin nasa tare da juyawa ya gyara zamansa sosai, a karo guda ya maida kallonsa gare ta ya cigaba "ya kike so nayi da rayuwata Jameela? Kin gwada mun bakya so in ra6e ki, nace naji na amince da hakan, yanzu kuma nace muyi aure, kin zo kina bada wasu unnecessarily reasons d'inki, ya kike so nayi?" Ajiyar zuciya ya sauke, "Shi yasa tun farko nace ki sanar da iyayenki, but you refused to. To be honest I can't take this any longer, tunda dai baki da lokaci na, bakya kuma k'aunata, I'll find my way, and I believe I'll find someone who will love, and care for me." Daga haka ya fara k'ok'arin tada motar, bata damu ba, ta sa hannu ta rik'e shi, kuka mai zafi ya k'wace mata, a zahiri baza ta iya fad'ar ko na meye ba, ta dai san a yadda yayi maganar babu alamar wasa ko sassauci a abinda ya fad'a, ita kuma baza fa iya jure ma rashin masoyi kamar shi ba. Shine mutumen da take jin zuciyarta na bugawa tare da soyayyarsa, mutumen da ya koya mata yadda ake so, ya kuma koyar da ita yadda zata so shi shi d'aya a duk fad'in rayuwarta. She can't lose such a person, haka ta cigaba da ayyanawa a k'asan zuciyarta.5 Hannu yasa ya cire hannunta dake jikinsa, fuskarsa ba annuri yace "muje na mayar dake gida." ya cigaba da k'ok'arin tada motar a karo na biyu. "I'm going nowhere, I choose to stay with you for the rest of my life, I love you Sadam." Murmushin takaici yayi, iein wanda ya fi kuka ciwo, "you don't mean it Jay, so stop deceiving yourself, lemme just take you home." "I mean it Sadam, I don't wanna lose you, I love you so much. I just don't know what to tell Baffa, and idan ka rabu da ni ya kake so inyi da rayuwata? Wa kake tunanin zan kalla in samu natsuwar zuciyata? Ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba, you've to know this." Ta k'arasa maganar hawaye na cigaba da kwarara saman fuskarta. Kallonta yake, a karo na farko kenan tun ranar da ya santa, ya ji tausayinta ya tsirga zuciyarsa, kasancewar kukan da take bil hak'k'i da gaskiya, ta kuma kama gefen rigarshi ta rik'e k'ark'adam, kamar wanda yace zai gudu ya barta. "It's okay please" ya fad'a lokacin da ya dafa kafad'arta, a lokaci guda ya ciro handkerchief yana share mata hawayen dake ta faman sintiri akan fuskarta. Wani bak'on al'amari ne ya ke ji a tare da shi, wani irin abu ke yawo cikin jikinsa, a karo guda ya tsirga zuciyarsa, wanda tunda ya santa bai ta6a jin makamancin irinsa ba. Hakan ya k'ara mishi k'warin gwiwa da son ganin ya mallaketa ko ta halin k'ak'a. Sai da ya tabbatar ta daina kukan, sannan ya fara magana cikin wani salo, wanda ya tabbatar duk lokacin da yayi amfani da shi tana fad'awa tarkon da ya hak'a mata ba tare da yasha wahala ba. "Abinda nake so da ke shine, ki kwantar da hankalinki ki fahimci abinda nake nufi Babyna, in dai karatunki kike ji, a wurina ba wata matsala bace ba, dan kin aure ni babu abinda za'a fasa ta 6angaren karatunki, zan tsaya miki in tabbatar kinyi karatunki kamar yadda Baffa yake so. A yanzu za6i ya rage naki, wuk'a da nama duk suna hannunki, matsawar zaki sanar da su abinda kike so, na tabbata zasu amince koda sun nuna rashin yardarsu daga farko, dan haka ki trying luck d'inki, nd believe me, zamu samu cikar burinmu, sai dai idan kece kawai bakya son kasancewa tare da ni." Hawayenta ta share, sosai ta gamsu da maganarsa d'ari bisa d'ari, har ta fara tunanin auren ne kawai mafita ga masoya irinsu, wanda suke jin zasu iya sadaukar da rayukansu wa junansu, ko dan gujewa fad'awa tarkon shaid'an. "Na fahimta, zan kuma fahimtar da Baffa shima, na tabbata zai yarda, zai kuma fahimci dalilinmu, nasan baza mu samu matsala ba tunda dai kace zan cigaba da karatu na." "That's my Angel" ya fad'a tare da murmushi. "Now, smile for me." Hawaye na zuba a idonta ta saki murmushin, a lokaci guda tace "please kada ka k'ara tsoratar da ni irin haka, idan ka kuma yi min haka watak'ila zaka neme ni ka rasa a duniyar nan." "Its okay babyna, ke ma kada ki k'ara denying commands d'ina, in ba haka ba zan d'auka kamar bakya so na ne kinji?" "I won't. I promise." Ta fad'a tana d'aga hannunta sama, tare da murmushi. "I promise you too, babe girl." Dariya ta saki, daga haka ya tada motar suka d'auki hanyar gida, yayin da zuciyarta ta aminta k'warai akan tubalin da Sadam ya gama ginawa a cikinta. Bayan ya kaita gida, bai barta ta shiga ba sai da ya k'ara jaddadada mata irin soyayyar da yake mata, tare da rok'on ta taimaka ta anshi tayin da ya zo mata da shi. Inda tayi mishi alk'awarin zata yi duk abinda ya dace dan ganin sun cimma burinsu. Da haka suka yi bankwana ta shige gida ba dan sun so rabuwa ba, zuciyoyinsu cike da so da k'aunar junan su. Tana shiga mai gadi ya fara sheda mata tashin hankalin da iyayen nata suka shiga, kasancewar yau ce rana ta farko a rayuwarta da ta ta6a fita daddare ba tare da ta sanar da su ba, duk kuma a dalilin Sadam. Da sallama ta shigo palon, fuskarta ba yabo ba fallasa, da sauri Goggo ta mik'e daga zaman tagumin da tayi, ta isa gabanta ta rungume tana dudduba jikinta, a tunanin ko wani abu ya samu 'yar tata ne. Baffa na ganinta shima ya isa inda suke ya ja hannunta zuwa kujera suka zauna, yana k'are mata kallo, sai dai babu alamun wani abu ya ta6a lafiyar jikinta. Hakanyasa ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara magana. "Ina kika shiga, haka Ummi? Kinsa hankulanmu gaba d'aya sun tashi, haba Mamana, idan zaki fita ai sai ki sanar da koda Goggonki ce, amma ki fita daddare ke d'aya, ba tare kuma da kin sanar da kowa inda kika nufa ba, wane dalili ne ya saki fita cikin daren nan? Idan wani abu kike so kinsan ina da wanda zan aika ya samo miki ko ma menene." Kuka ta fashe da shi, tare da fad'awa jikin Baffan. Bai hana ta kukan ba, illa bayanta da ya fara bubbugawa, a haka Goggo ta dawo gefensu ta zauna tasa hannu ta kama hannunta tana cewa "kiyi magana Baby, wani abu ne ya faru?" Baffan ma d'ago ta yayi, suka zuba mata ido domin sauraren abinda zata fad'a.7 "Baffa aure nike so."4 Abinda ta fad'a kenan kanta tsaye, tare da rushewa da wani sabon kukan. "Aure?" Iyayen suka maimaita a tare, yayin da ta d'aga masu kai, alamar abinda take nufi kenan. Sakinta Baffa yayi, a lokaci guda ya mik'e yana girgiza kansa, daga bisani ya fara magana. "Ba muyi haka da ke ba Mamana." Ya tako zuwa gabanta, ya kama hannayenta ya cigaba "Sanin kanki ne ba zan ta6a aurar dake ba har sai kin kammala karatunki, domin da wannan alk'awarin na bar ki kika fara karatun, sannan kuma ki tuna ke kad'ai ce d'iya d'aya tal, dana haifa a rayuwata, da ke na dogara, gare ki kuma na d'ora duk wani buri da nake da shi a rayuwa. Haka kawai, baza ki zo mun da wata sabuwar maganar ba Ummina, domin bazan ta6a aminta da ita ba." Yana gama fad'ar haka ya mik'e ya fara k'ok'arin barin palon, inda a zuciyarsa yake jin wannan ne karo na farko da ta ta6a neman abu a wurinsa ta rasa, wannan ne kuma karo na farko da ta zo da batun da ya ta6a zuciyarsa fiye da tunanin mai tunani, tun ranar da ya haife ta. Rigarshi ta rik'e, ta kuma rushewa da wani kukan tace "wallahi ina son shi Baffa, idan ban aure sa ba zan iya mutuwa kowa ma ya huta." Ido Baffa ya zaro, Goggo ta taso ta d'aga ta, ta rungume, cikin tsasa Baffa ya nuna ta yana cewa "wane banza ne wannan wanda ya 6ata mun tarbiyyar da na shekara ashirin ina ginawa a rayuwata? Wanene shi wanda yake neman ya jaza miki fushi na Ummi? To ina so ki sani koma wanene, bazan ta6a aminta da aurenku ba. Buri na akanki karatu ne Jameela, shi kanshi da ace ban inganta iliminki ba, da babu dalilin da zaisa yayi sha'awar aurenki, haka kuma a halin yanzu babu wani namiji da zai ta6a ganin k'ima da darajarki, matsawar baki da wannan ilimin, dan haka ki rufa wa kanki asiri tun wuri, ki janye maganar banzan da kika kawo mun." Da haka ya cika rigarsa da iska, ya wuce ya 6ace ma ganinsu baki d'aya. Wani matsanancin kuka Jay ta kuma fashewa da shi, domin bata tsammaci haka daga Baffanta ba, duk da ta san da wuya ya amince kai tsaye, amma tayi tunanin zai kwantar da hankalinshi, ya bata dama har ta fahimtar da shi yadda take son Sadam, da kuma alk'awarin da ya yi na cigaba da karatunta a gidansa.3 Duk da kasancewar zuciyar Goggo na cikin hali na tararrabin jin batun da 'yar tasu ta zo da shi, ba shi ya hana ta isa gabanta ta mik'ar da ita ba, tare da k'arasawa saman kujera suka zauna, sannan ta fara tambayar abinda ya kawo sauyin ra'ayi a rayuwarta. Ba tare da ta 6oye mata komai ba ta fayyace mata labarin Sadam, inda ta k'ara da cewar "wallahi Goggo zan iya rasa raina matsawar baku bar ni na aure shi ba, ina son shi sosai, fiye da duk yadda wani mahaluk'i zai kwatanta." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Goggo ce ta fad'a, sannan ta k'ara da "Me yi zafi haka? Sai kace ba musulma ba kike wannan maganar? In dan wannan, ki kwantar da hankalinki, zanyi magana da Baffanki, in sha Allahu zan san yadda nayi na kwatanta masa muhimmancin maganar da kika zo da ita, tunda dai har ke da kanki kika fito kika ce auren kike so, to gara a miki, shine kawai abinda ya fi dacewa." Mik'ewa tayi ba tare da ta ce ma Goggon komai ba ta shige d'akinta, itama ta mik'e ta bi bayan mijinta. Ko da ta shiga da maganar, hannu ya d'aga mata, dan dama zaune ta same shi ya duk'ar da kansa, inda yasa hannuwansa duk biyun ya tallabe shi, da gani yana cikin yanayi na tashin hankali. Ganin haka yasa Goggo tayi gum da bakinta, sai dai a zuciyarta ta ci alwashin nusar da shi, kan abinda ya dace. **** Farin ciki ne fal a zuciyarsa, bayan ganin makuden kudaden da ya tara a gabansa. Kwalbar barasar da ya sa aka kawo masa ya d'aga ya kwankwada, a karo guda ya ajje a teburin da ke gabansa. Cikin ihun murna ya kwashi tarin kud'in dake gabansa, ya sumbace su, yana fadin "Hakika sana'ar nan tana kaunata, fiye da yadda nike kaunarta."9 Ya washe da dariya mai sauti, ya kuma kafa kwalbar barasar a bakinsa, ya sha sosai yadda ya kamata. Wani matashi da ke gefe ne ya taso ya dawo gabansa, kallonshi yake yana son tuna inda ya sanshi, bai furta komai ba, ya d'auki kwalbar barasar, ya zazzage wacce tayi saura a tsakiyar kan Kazaure. "Ina tausayin ranar da cacar da kake k'auna zata juya maka baya. Kai dai taka a sannu 'yan samari. " Duk da yana cikin maye, hakan bai hana zuciyarsa tunzura ba, a masifance ya d'ago yana kallon mutumen "Get the f*ck out of my sight, idiot" Dariya wancen ya saki, hakan ba k'aramin k'ular da Sadam yayi ba, a karon farko ya mik'e yana cakumar rigarsa, daga haka suka fara dambe, da duk wani k'arfinsu Sosai ya faffasawa wancen fuska, haka shima ya samu sa'ar yi mashi wani kyakkaywan naushin da ya sa bakinsa fashewa cikin d'an k'aramin lokaci. Har suka yi suka gama ba'a samu wanda yace dasu su bari ba, illa ihu da wasu daga cikin mutanen suka fara yi, a haka suka saki junansu, kowa yana mayar da numfashi. Yana mik'ewa ya wuce teburin da kud'insa suke da zumar ya d'auka ya kama gabansa, sai dai yaga wayam, babu su babu labarinsu. Hauka ya fara yi yana faffasa bottles d'in giyar da ke gabansa, tare da zage-zage da wasu surutai irin na mashaya, a haka ya fice, yana ta faman zagin mutanen wurin. ** Ta kira wayarshi har ba adadi, amma bai samu halin daga kiran ba. Wani irin kuka mai azabar zafin hawaye take yi, a zuciyarta babu abinda take gani illa fuskarsa, soyayyar da ta ke mishi yasa ta kasa jin haushin rashin d'aga wayar tasa, sai ma ta dinga d'ora laifin akanta, tana tunanin ko dai bai huce a kan abinda ya faru ba? Wannan tunanin yasa ta k'ara zage damtse wajen ganin ta cika musu burinsu ko ta halin k'ak'a.13 Haka dai daren ya kasance mata, kwance kawai take ko kayan jikinta bata canja ba, sai a yanzu ta gane ashe Sadam ba k'aramin taimaka masu yayi ba da ya zo da wannan shawarar, domin kuwa son da take mishi, idan har suka cigaba da zama a haka, zata iya sallama mishi kanta kamar yadda yake buk'ata, domin kuwa baza ta iya jure rayuwa ba tare da shi ba, baza ta iya ganinsa cikin damuwa ta kawar da kanta ba. Number tasa ta cigaba da kira amma shiru, har sai da bacci 6arawo yayi awon gaba da ita. Yanayin da iyayen nata suka ganta a yau da safe, ba k'aramin tayar musu da hankali yayi ba, ita ce 'yarsu k'waya d'aya tal, wacce suka sadaukar da rayuwarsa tare da farin cikinsu gare ta baki d'aya. Da sauri Goggo ta isa gefenta ta zauna, tana shafa kanta, tana tambayar "haba Baby, kar dai ki ce mun bakiyi bacci a daren jiya ba?" Ido ta murza, ta sauke su a kan Baffa wanda ya had'e cikin lallausar shadda dinkin babbar riga ya d'ora hula, hannunsa rik'e da jaka yana kallonta tare da murmushi. Zum6ure baki tayi tana kauda kai a dubansa, mugun haushinsa take ji, da ba mahaifinta ba ne, da zata iya yi masa abinda ya fita shari'ah, sai dai ya gode Allah kasancewar shi mahaifinta, kuma mutum na farko da ta fara kauna a duniyarta. Bata ce da su k'ala ba ta mik'e zata wuce toilet. Baffa ya gyara tsayuwarsa, yana kallonta. "Zo nan Mamana" Ba tare da ta kalle shi ba ta dawo ta zauna bakin gadon tana faman kumbura dan karamin bakinta. Gefen nata ya zauna, ya cire hannu kamo nata "menene abun fushin kuma? Ince ai mun gama magana tun jiya ko? Saki fuskarki kinji, ki maida hankali a karatunki, mazan nan na yanzu duk sai a hankali, idan kika yi karatunki kika tsaya da k'afarki, ke da kanki zaki gane irin gatan da na miki, dan haka ki manta batun mutumin nan da ke k'ok'arin ruguza futuren ki, kiyi facing reality, kinji Ummina." Tamkar Baffa ya watsa mata wuta, haka ta bude da wani sabon babin kuka, cikin ido ta kalle shi, "wallahi bazan iya ba Baffa na, ina son shi sosai Baffa, so mai tsanani, bana jin zan iya rayuwa idan baku bari na aure shi ba." Shiru Baffa yayi, yana kare mata kallo, zuciyarsa yake jin tana tafarfasa, har yana ayyana irin cin fuskar da zaiyi ma mutumen da yayi sanadiyyar wargaza farin cikinsu shida iyalinshi. Shirun da ya ratsa ne yasa Goggo tsoma baki, tana cewa "Alhaji ka duba batun yarinyar nan, tunda ta nuna tana so gara kawai a yi mata auren a huta, tunda dai yace ba zai hana ta k'arasa karatunta ba, kuma in dai aure bai hana karatu ba, ni ke ga ai ba yadda za ayi shi karatun ya hana aure, kuma idan ka tuna...." Muguwar hararar da ya watsa mata, wacce tunda su kai aure bata ta6a sanin ya iyata ba ma ta sanya ta hadiye sauran maganar nan. "Rufe mun baki da Allah!" Ya fad'a cikin wata murya mai k'arfin amo, tare da d'aga hannu. "Bana son k'ara jin wannan maganar a cikin gidan nan, aure dai ne bazan aurar da 'ya ta ba, duk kuma wanda ya kuma tayar da maganar nan, wallahi sai ya gamu da 6acin raina, ba wai k'arami ba." Daga haka ya bar gidan gaba d'aya ko abinci bai tsaya ci ba, dan dama meeting gare shi k'arfe goman safe a Kano. Tun bai ida fita ba ta rushe da wani matsanancin kuka, Goggo ta isa tana lallashinta, amma ta yi kunnen uwar shegu da ita, ta cigaba da risga kukanta, daga k'arshe ta tashi ta shige toilet, hakan yasa itama Goggon ta mik'e ta fita, ga mamakinta babu ko k'yallin motar Baffa, cikin jimami ta dawo ciki, ta wuce d'aki tana tunanin mafitar wannan lamari. Tana fitowa wankan ta shirya tsab cikin bak'ar abayar da aka yi ma ado da bakaken duwatsu masu shek'i, bak'in sneakers ta saka a k'afarta, fuskarta fayau, powder kawai ta iya shafawa, ta zari jaka da makullin motarta, ta kama hanyar waj Haushin da take ji na Baffa shi ne ya shafi Goggo, dan ta tabbatar tunda yace kada a kuma tada maganar, to babu abinda zata iya yi, dan tunda ta taso bata ta6a ganin ta bijire ma umarninsa ba. Rashin ganinta a palon ma dad'i yayi mata, bata kuma damu da k'arasawa d'akin nata ba domin tayi mata bayanin inda ta nufa, kai tsaye ta doshi harabar gidan tana kiran wayar Sadam, har iyanzu bai samu damar d'agawa ba, a haka ta shige mota ta fice, gabanta na fad'uwa ta d'auki hanyar Daura, duk da ba ta6a zuwa ita d'aya tayi bama, balle ayi maganar ta tuk'a mota taje. Cikin yarda da hukuncin Allah ta shigo garin na Daura, bata 6ata lokaci ba ta zarce gidan kakan nata, cikin sa'a ta same shi zaune a islamiyyar dake dangane da gidansa. Da murna ya tari jikar tasa, farin cikin ganinta ya kasa 6oyuwa a saman dattijuwar fuskarsa, duk da mamakin ganinta ita d'aya da yayi, da kuma damuwar da ya gani shimfid'e k'arara a kan fuskarta. Cikin gidan suka k'arasa, a madaidaicin palonshi dai-dai na dattijai suka zauna, a haka Iya ta shigo ta same su, da fara'arta ta k'arasa shigowa ta samu wuri daf da ita ta zauna. Fuskarta babu walwala ta gaishe da kakannin nata, yayin da suka ansa cikin zak'uwa da jin dad'i. "Ya mutan gidan?" Mal. Baba ya tambaya, Iya ta k'ara da cewar "Ya akayi na ganki ke d'aya?" Bata iya basu ansa ba sai kukan da ya k'wace mata, sosai take kukan kamar zata cire idanunta. Cikin tsananin jimami tare da tunani barkatai a zukatansu suka fara lallashinta, suna masu neman ba'asin dalilin kukan nata. Sai da tayi mai isarta, kafun ta lankwashe kafa, ba tare da ta 6oye musu komai ba, ta zayyana masu labarin da ke tafe da ita. A tare tsofaffin suka kwashi salati suka dire har k'arshe, Iya ta d'ora da fadin "Ka ji fa Malam, yahudanci ya gama ratsa zuciyar mutumen nan, har yana neman tauye hak'k'in da Allah ya d'ora a kansa. In banda son kai na d'an Adam, shi duka-duka matarsa tana shekara nawa ya aureta?" Girgiza kai kawai Mal. Baba yayi, "Ni nama rasa abinda zance wallahi, wannan wane irin bak'on al'amari ne? A gidana? Cikin zuri'a ta? Da sake wallahi, sam bazan lamunce ma wannan munnunar dabi'a ba, yanzu shi Kabiru bai ji kunya ba ace 'yar cikinsa ce zata nuna mishi hanyar gaskiya, amma da yake yahudanci ya gama ratsa sa, shine har da sa k'afa ya shure maganar ko, to ni d'in zanyi maganinshi, sai ya san ya bijire ma sunnar ma'aiki (SAW)." Ya k'arasa maganar lokacin da ya sanya hannu a aljihu ya fitar da wayarsa, ya fara k'ok'arin kiran number Baffa. Fitowarshi kenan daga taron da sukan yi a duk k'arshen wata da manajojinsa na sauran rassan kamfanoninsa da ke garuruwa daban-daban a arewacin Nigeria wayar Mal. Baba ta shigo masa. Gefe ya matsa, ya ansa wayar da sallama, ya gaishe da mahaifin nasa cikin dattako da girmamawa. Sama-sama Malam ya ansa shi, ya d'ora da cewa "Ba wannan ne dalilin kiran ba, ina so ka baro duk abinda kake kazo Daura ka same ni yau d'in nan, ba wai sai gobe ba." "Lafiya Malam? Ko akwai wata matsala ne?" Baffa ya tambaya lokacin da ya k'arasa fitowa daga d'akin da suka gabatar da taron. "Babba ma kuwa Kabiru, domin kayi abinda ban ta6a tsammani daga gare ka ba, duk da dai ba abin mamaki bane, idan nayi duba da yadda son zuciya yasa kayi watsi da iliminka na addini, kayi aron wasu al'adu da ak'idu na nasara ka yafa ma kanka tuntuni. Idan ka iso zaka ji sauran bayani." Daga haka ya kashe wayar, ya cigaba da jijjiga kai, yana mamakin rayuwa irin ta mutanen yanzu. Daga bisani ya kai duba ga Iya, yace "ku shiga ciki ko fura ki sama mata tasha kafin shi kuma yazo ya bani dalilinsa na son hana yarinya raya sunnar ma'aiki." "Sallallahu alaihi wa sallam" Iya ta k'arasa masa, suka mik'e gaba d'aya, shi yayi k'ofar gida, su kuma suka kama hanyar shiga ciki. Duk iya tunanin duniya, babu kalar wanda Baffa bai yi ba, sai dai ya kasa gano dalilin kiran gaggawar da Malam ya masa. A haka ya fito ya samu direbansa "shiga mu tafi, Daura zamu je yanzun nan." A tare suka shige motar, zuciyar Baffa fal da tambayoyin da ya gagara ansawa. Cikin ikon Allah tafiyar awa d'aya da minti goma cif-cif, ta kawo su k'ofar gidan Mal. Baba. Babban abinda ya d'aure kanshi kuwa, shine motar Jaay da ya gani, ajje a k'ofar gidan, duk da bashi da tabbacin ita d'in ce, ko a a, domin kuwa wata zuciyar na gaya masa babu abinda zai kawo ta Daura. Bai ida gaskata zarginsa ba, har sai da ya sa kai cikin gidan, ya ko ci karo da ita zaune a palo ta takure wuri guda, sai faman danna waya take yi. Gyaran murya yayi, ya had'a da sallama ya shige ciki, idanunsa akanta, ta dago tana dubanshi, bata ce da shi komai ba, sai dai ta 6angarensa sosai yake mamakin canjawar halayenta cikin d'an k'ank'anin lokaci. "Ba dai k'arata ta kawo ba?" Tambayar da ya yi ma kansa kenan, da haka Malam ya fito yana ansa sallamar, Iya na biye da shi, duk suka nema ma kansu mazauni a cikin palon. Bayan sun gaisa, Malam yayi gyaran murya, ya kalli Baffa wanda har yanzu bai daina mamakin ganin Jay ba, yace "Kabiru." "Na'am Malam." Baffa ya ansa shi, lokacin da ya maida kallonsa gare shi. Har ya bud'a baki zai fara magana, sai kuma ya dubi Jameela tare da cewa "shiga ciki ki jira mu." Ba dan ta so ba ta mik'e ta shige, duk da haka ta la6e bakin k'ofa tana saurarensu, tana mai ayyanawa ranta matsawar Baffa bai amince ba, to baza ta koma gida ba, har sai Mal. Baba ya d'aura masu aure da Sadam d'inta. A palo kuwa Malam gyara zama yayi, "Ummi ta zo da batun da ya girgiza tunanina, nasan kasan komai ba sai na maimaita maka ba." "Haka ne Malam." Baffa ya fad'a tare da girgiza kansa. "Ina so in san menene dalilinka na cewa baza ka aurar da ita ba har sai ta gama karatu? Shin rayuwarta a hannunka take, ko kai ke da lokacin da zata gama karatun? Bayan kuma ta fad'a maka cewar yaron ya amince zata cigaba da karatun agidansa." Sai da ya d'an tsagaita, sannan ya cigaba "Haba Kabiru, da saninka da komai, ya kake neman ka haramta abinda Allah (SWA) ya halatta da kanshi? Me zaka ce ma Allah a ranar gobe k'iyama idan taje ta d'auko maka magana? Bayan kuma yarinya ta fito ta kwatanta abinda take so, kai kuma son zuciya, da al'adun nasara da suka ratsa ka sun sa ka toshe kunnuwanka, ba tare da ka fahimci girman abinda ta zo da shi ba. To ina so ka saurare ni da kyau ka kuma ji abinda zan fad'a maka, tun wuri ka janye wannan mummunan k'udirin da ka cusa a ranka, ka bar yarinya ta auri wanda take so, tun baka gamu da fushi na ba." Duk da tashin hankalin da Baffa yake ciki, amma haka ya daure ya cije, ya ansa umarnin mahaifin nasa, ya kuma k'ara da cewar "Za ayi yadda kace in sha Allah, yau d'in nan zan nemi ganawa da yaron, daga baya sai muyi magana da magabatanshi. Zan aurar masa da ita, matsawar ya cika sharud'd'an da musulunci ya gindaya akan miji nagari." "Masha Allah, Allah yayi albarka, ya kuma sa a dace." "Amin" Cewar Baffa, da haka suka mik'e domin fita sallar azuhr da ake ta kira a masallacin dake k'ofar gidan.5 *** A gigice ya farka yana mik'a, toilet ya wuce yayi wanka had'e da alwala, ya fito ya zira jallabiya, ya gabatar da sallar asuba tare da zuhr, yayin da cikinsa ke ta faman k'ugi, saboda azabar yunwar dake nuk'urk'usarsa. Key d'in motarsa ya fara nema bai gani ba, hakan yasa ya d'auko wayarsa da niyyar ficewa, anan ya ga missed calls d'in Jau da suka tasan ma guda talatin. Hankali kwance ya fito, ba tare da wata damuwa ba, a karo guda ya danna number ya fara kiranta.7 Tsaye suke a k'ofar gidan Malam sun fito da niyyar tafiya har Baffa, wayarshi ta shigo mata, bata damu da mutanen da ke gabanta ba tayi saurin komawa gefe, ta ansa wayar cikin zak'uwa, ta kara a kunnenta tana cewa "Haba Sadam, me nayi da kake punishing d'ina haka? Ka san irin tashin hankalin da na shiga kuwa?" "Hey I'm sorry." Ya fad'a cikin wata irin murya mai rauni. "Wallahi babe dak'yar na koma gida bayan na sauke ki, hankalina ya tashi gaba d'aya, zuciyana ya kasa kwanciya, tunanina zan iya loosing d'inki any moment from now, matsawar bamu samu cikar burinmu ba, wad'annan abubuwan ne suka sanya ni rasa natsuwata, sune kuma suka sa na kamu da rashin lafiya mai tsanani wacce tayi sanadiyyar kwantar da ni tun daren jiya." Fuskarta tamkar mai shirin yin kuka, tace "Oh my God! I'm so sorry dear, shi yasa na nemi natsuwata gaba d'aya na rasa, jikina ya bani kana cikin wani yanayi, amma ka kwantar da hankalinka, yanzu haka ina Daura na kawo k'arar Baffa, kuma munyi nasara Mal. Baba ya tursasa masa dole ya amince." "Babe? No, no, you must be kidding, right?" "I'm not sweedy. Yanzu dai ka gane ko, I'll be on my way right back to Katsina, so zan kira immediately da na shigo." Da haka ta datse wayar, kasancewar Malam da ya fara k'wala mata kira. Gabansu ta isa, daga nan suka yi masu sallama suka shige motar Baffa, yayin da driver ya shiga tata suka d'au hanyar ta Dikko d'akin kara. Tunda suka tafi babu wanda yace ma kowa komai, sa6anin da, da har so suke suyi tafiya tare domin su samu lokacin fayyace ma juna labaran da ke zukatansu. A haka wayar Goggo ta shigo ma Baffa, hankalinta a tashe take shaida mashi cewar Ummi bata gida. "Ga ta nan zaune." Ya bata ansa hankalinsa na kan titi, ya k'ara da cewar "ki kwantar da hankalinki, gamu nan a hanyar gida." Ya kashe wayar, ya ajje, inda ya saita hankalinsa sosai a titi, sai dai zuciyarsa ta gagara natsuwa, ba tare da ya kalleta ba yace "meye sunan sa?" Da mamaki ta d'ago tana kallon Baffan, murmushi ta saki tare da cewa "Sadam." A tak'aice. "Ki ce da shi ya zo ya same ni a gida k'arfe bakwai na daren yau." Wannan karon ta kasa 6oye farin cikinta, hannun Baffan da yake tuk'i da shi ta dafa tana cewa "nagode, nagode Baffana. Zan sanar da shi in sha Allah." Bai ce komai ba, haka kuma bai kalleta ba, murmushin takaici kawai ya saki, inda ya cigaba da tuk'insa, ita kuma dan rashin kunya ta fara k'ok'arin jan shi da surutu, sai dai bai ce k'ala ba, har ta gaji taja bakinta tayi shiru itama.7 Koda suka je gida da sauri ta shige ciki, ta bar Baffa yana gyara parking, inda ta samu Goggo zaune a palon ta rafka uban tagumi, fuskarta babu alamar walwala. Da sauri ta taso ta tare ta, "Ina kika je haka Baby? Wai me yake shirin faruwa da ke? Yanzu ace zaki fita, kuma ina cikin gidan nan, amma baza ki iya sanar da ni ba, sai dai in fito kawai in neme ki in rasa? Wace irin rayuwa kike shirin jefa kanki?" A haka Baffa ya shigo da sallama, da sauri ta sake ta tayi kansa ta anshi babbar riga da hularsa, tare da jakarsa a hannun drivern dake binshi a baya, ta dawo cikin palon inda Baffa ya samu wuri ya zauna, ya had'a hannuwansa duk biyun ya dunk'ule ya tallabe ha6arsa, sai faman cika bakinsa yake da iska yana furzarwa. "Sannunku" ta ce da shi lokacin da ta ajje kayan dake hannunta a gefensa. "Yawwa dai, bani ruwa da Allah." Bata 6ata lokaci ba ta wuce kitchen domin kawo masa ruwan, yayin da Jay ta dawo gefensa ta zauna hankalinta na kan waya da alama text take rubutawa. Bayan Goggo ta aje tray d'in da ke hannunta mai d'auke da gorar ruwa, cup, tare da jug mai cike da pineapple & coconut squash. Tsiyaya lemun ta yi ta mik'a masa tana tambayar "lafiya dai ko? Naga ka dawo da wuri. Ya akai na ganku tare da Ummi kuma?" Ansar lemun yayi ya kafa a baki ya kwankwad'e tass, take yaji zuciyarsa ta d'an sassauta masa, sannan ya aje cup d'in yace "A Daura muka had'u." "Daura?" Goggo ta tambaya idanunta a waje. Girgiza kai Baffa yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya tashi ya wuce d'aki dan muddin ya cigaba da zama kusa da Ummi, ba zai samu natsuwar zuciyarsa ba, dan a yanzu haka ma azalzalarsa kawai take, abinda bai ta6a ji ba dangane da ita tun bayan zuwanta duniya. Kallonta Goggo take tana tambayar "me ya kai ki Daura Ummi? Ba dai kan maganar da Baffanki yace kar ki kuma tadawa ba?" "Kanta mana." Ta fad'a kai tsaye. "Haba Ummi, wai me yake yawo a kanki? Duka-duka kwananki nawa da sanin mutumin nan da har zai sa ki manta da k'auna da soyayyar da muke nuna miki tunda kika taso a cikin gidan nan? Kinsan yadda Baffanki baya son 6acin ranki, na tabbata da kika bari aka bi komai a hankali, da zai hak'ura har ma ya sauko daga dokin nak'in da ya hau. Amma da yake ke d'an Adam ce butulu, shine kika tafi kika kai k'ararsa wurin Malam ko? Dan kinsan shi ba zai iya bijirewa maganar mahaifinsa ba ko? Kinyi dai-dai. Sai dai ina so dake ki bi sannu, kada son zuciya ya kai ki ya baro ki." "To meye laifi na anan?" Ta fad'a tana kallon Goggon. "Haka kawai sai in bari a danne mun 'yancina, bayan kuma bashi da wasu reasons masu k'wari. Ni banga wani rashin kyautawa ta ba, kuma ko Mal. Baba da na fad'a mai, haka yace nayi dai-dai da nayi wayon sanar da shi." Daga haka ta wuce d'aki ta bar Goggo cikin jimami, da tashin hankalin irin tarbiyyar da sukai mata, da kuma rashin nusar da ita muhimmancinsu a rayuwar ta. Gashi nan yanzu reshe yana neman juyewa da mujiya. Girgiza kanta tayi, daga haka ta wuce d'akin Baffa, dan ta san yana buk'atar wanda zai yi magana da shi. Tunda ta taso a rayuwarta yau ce rana ta farko da ta ta6a yin abun da Goggo tace bata kyauta ba, duk kuwa da ta6argazar da take tafkawa, wanda ita kanta wani lokacin idan tayi wani abun tana jin bata kyauta ba, amma son kai da son zuciya irin na iyayenta bai ta6a bari sun tsawatar mata ba, hakan yasa ta mik'e a haka, gaba d'aya rayuwarta bata san akwai wata kalmar baki kyauta ba.6 Kan gadonta ta fad'a hankalinta kwance, ta fara kiran number Sadam, bugu biyu zuwa na ukku ya d'aga tare da cewa "how's my baby doing?" "Great" ta bashi ansa, inda damuwa da fushin da ta shigo da shi, ta neme su sama-ko-k'asa ta rasa, sai wani farin ciki da jin dad'i da suka maye gurbinsu. Muryarsa ce ta katse mata tunani inda yake cewa "me kika samo mana a Daura? I'm eager to hear the result." Murmushi ta saki, sannan ta tura hannunta a baki tana tsotsa a hankali tace "zan fad'a maka, but what wud I get in return?" Jim ya d'anyi, daga bisani yace "I'll love you, & stay by your side for the rest of my life." Wani murmushin ta kuma saki, wannan karon mai d'an sauti tace "promise?" "You know I mean my words, just trust me." "I trust my bae." Ta k'arasa tana dariya. "Now, I'm all ears." Ya fad'a ta d'ayan 6angaren. A haka ta labarta masa duk abinda ya faru, daga k'arshe ta sanar da shi kiran da Baffa yake masa. Wani mugun farin ciki ne ya lullu6e Sadam, yayin da a zuciyarsa yake jin hak'onsa ya kusan cimma ruwa. Daga nan suka yi bankwana ta kashe wayar ta juya tayi kwanciyarta, tana jin wata sabuwar soyayyar Sadam na yawo a gaba d'aya jinin da ke gudanyawa a cikin jikinta.3 **7:00 (PM) Jikinshi sanye da lallausan bak'in yadin filtex wanda ya ji lafiyayyen aikin hannu da zare kalar ruwan gwal mai sheki. An kuma k'awata shi da d'inki irin na samarin zamani wad'anda suka ci suka k'oshi, suke kuma ji da gayu da k'uruciyarsu. A k'afarshi rufaffen bakin takalmi ne na Rockport, ya dora hular zanna bukar da tayi matching da kwalliyyarsa. Yadda yayi karin hular ya fito da asalin zati da haibar da Allah (SWA) ya masa, fuskarshi ta fito tas-tas, manya-manyan idanunsa suka kuma fesowa, in banda jajayen la66ansa da suka fara canja kala zuwa bak'i-bak'i. Hannu yasa ya shafe fuskarsa, sannan ya d'aura bak'ar agogon fata a tsintsiyar hannunsa, ya mak'ala cuplinks a hannuwan rigarsa, ya k'ara gyara zaman hularsa sannan ya fito, hannunsa rik'e da makullin mota, yana cigaba da basarwa yana bada feelings ma duk wanda yayi katarin kallonsa, har zuwa lokacin da ya iso gaban motarshi. Titin GRA ya d'auka, a gefe guda wak'ar Good Enough ta Jussie Smolett tana tashi a hankali, yayin da yake jin kanshi a wata duniya ta daban, tamkar yana yawo a sararin samaniya. Tafiyar minti sha biyar ta kawo shi k'ofar gidan, wannan karon oda ya rink'a yi, mai gadi ya fito ya bud'e masa gate, ba tare da 6ata lokaci ba ya tura motar ciki, ya sama ma kansa wuri yayi parking, sannan ya fito ya jingine da jikin motar, ya ciro wayarsa ya fara kiran number Jay.8 🤗🤗🤗🤗👏Ta tagar d'akinta ta lek'a tana k'are mashi kallo, a hankali take sauke numfashi, domin baza ta iya fasalta yadda ya tafi da imani da ruhinta ba. "I'll be right there," ta fad'a tare da kashe wayar, sai dai ta kasa sake labulen tagar, haka kuma ta kasa motsawa daga inda take, ji tayi k'afafuwanta sun mata wani irin nauyi, ta rasa gane wane irin so take ma Sadam Kazaure wanda ko da muryarsa ta ji, sai bugun zuciyarta ya tsananta, idan kuwa yana gabanta ta kan rasa natsuwarta, wani lokacin har tunaninta ya kan fara yi mata barazanar d'aukewa. A hankali ta matsa gaban wardrobe d'inta ta fitar da wata free gown ta maroon d'in atamfar super java da aka yi ma ado da manyan flowers kalar Orange. Orange d'in gyale tayi d'aurin turban da shi, ta saka Orange d'in slippers na Versace, ta feshe jikinta da turaruka masu dad'in k'anshi, sannan ta d'aura agogonta, ta k'ara kallon kanta, ta tabbatar komai yayi sannan ta fito, inda ta samu Goggo a palo ta shaida mata zuwan shi.+ Ta k'ofar baya ta fito ta same shi a waje. Hanyar palon Baffa suka d'auka, tana gaba yana binta a baya, hakan ya bashi damar k'arewa cikakkar surarta kallo, ya tabbata idan ya sameta ba k'aramin morewa yayi ba. Juyowa tayi da zumar nuna mishi wurin zama, kallon da ta ci karo yana mata shi ya saukar da wata irin kasala a ga6o6in jikinta, hakan yasa ta sauke idonta, ta kuma kasa cewa komai. Hannuwansa na cikin aljihun wandonsa ya taka, ya isa gabanta, killer smiling d'insa mak'ale a bakinsa, yayin da ya d'an had'e girarshi tare da cewa "Gorgeous as always darling." Yaa Allah! She loves everything about this man! A k'asar zuciyarta tayi furucin, ta dago da manyan idanunta tana narkar da fuska,tana mai tsaida dubanta a kansa kamar tana karantar wani abu dangane da shi, daga bisani ta murmusa. Ta bud'e baki zata yi magana, suka jiyo gyaran muryar Baffa, hakan yasa tayi saurin juyawa ta fice, inda shi kuma ya samu d'aya a cikin kujerun falon ya hakimce a kai. K'arasa shigowa Baffan yayi, da sallama ya samu wuri ya zauna, hakan yasa Sadam yin k'asa da kanshi, ba tare da yayi yunk'urin saukowa dan gaishe da sirikin nasa ba, duk da kasancewar yau rana ta farko da suka fara had'uwa, haka kuma ranar da ya zo neman auren d'iyarsa. Kallo d'aya Baffa yayi masa, a zuciyarsa yake innata "abincin wani, gubar wani." "An wuni lafiya Baffa." Maganar Sadam ta katse mashi tunani. Ya kauda kai, tare da cewa "Lafiya, Alhamdulillah." "Ya aiki? Ya k'ok'ari?" Sadam ya k'ara tambaya. "An gode Allah." Baffa yace da shi, tare da gyara zamansa. Sannu a hankali Baffan ya gabatar da dalilin kiran nasa, yayin da ya k'ara da tambayar "ko zan iya sanin wanene kai?" "Babu damuwa Baffa." Sadam ya fad'a, inda a hankali kwance ya gyara zama yana fadin. "Mahaifina dan asalin Kazaure ne ta jihar Jigawa, mahaifiyata yar kasar Niger ce, Allah Ya mata rasuwa tun ina shekara biyar. A yanzu haka, iyayena suna zaune a cikin garin Dutse da ke jigawa, aiki ne ya kawo ni nan nima."6 "Masha Allah," Baffa ya fad'a, a karo na biyu ya juyo sosai ya fuskanci Sadam, sannan ya cigaba. "A zahirin gaskiya, bani da burin aurar da 'yata cikin 'yan shekarun nan. Burina a kanta karatu ne, sai dai kuma ta fito ta gwada mun cewar aure take so, na kuma amince zan aurar da ita, amma da sharad'in zaka barta ta k'arasa makarantarta a gidanka. Ya kake gani?" "Wannan ba matsala bane Baffa, domin ni da kai na ma na mata wannan alk'awarin." "Babu laifi." Cewar Baffa sa'adda ya kora lemun exotic d'in dake gabansa, yace "zaka iya tafiya, idan na gama bincike akanka, zan neme ka, domin in samu ganawa da magabatanka." "Nagode, Allah ya k'ara girma." Sadam ya fad'a lokacin da ya mik'e, yayin da Baffa ya ansa da "amin" yana mai bin bayansa da kallo. Alal hak'ika da shi Ummi zata ba damar za6a mata miji, da babu dalilin da zai sa ya za6a mata irin Sadam, domin bai kwanta mishi a rai ba, tun daga yanayinsa, kaiwa da irin tafiyar da yake yi, dan kuwa shi baya son yaga namiji yana wani bubbud'awa, sai dai bai sani ba wannan yana d'aya daga cikin abubuwan da suka tafi da zuciya tare da gangan jikin 'yarsa. Yana fita Baffa ya d'aga waya ya kira d'aya daga cikin mutanensa da ke Dutse, (Jigawa) ya basu cigiyar bincike akan halayen Sadam da ainahin labarin iyayensa. Bayan ya kashe ya kuma kiran wani anan cikin Katsina, shima yace ya taya shi bincike akan halaye da d'abi'un Sadam Baffa Kazaure. *** Tun daga wannan rana hankalin Jay da Sadam d'inta ya kwanta, basu da wata sauran fargaba, soyayya kawai suka cigaba da nuna ma junansu, dan sun san daga yanzu zuwa kowanne lokaci, zasu iya kasancewa k'ark'ashin inuwar ma'aurata. Duk da Baffa ba wai ya bama Sadam damar zuwa gidan ba, haka kuma kwata-kwata ya daina zama a gida, idan ya fita tun safe baya dawowa sai kwanciyar bacci, ya kuma daina shiga duk wata harka ta Jay, ba wai dan ya daina kaunarta ba, sai dai a zatonshi zata damu har ma ta Janye ra'ayin da ta cusa ma zuciyarta, sai dai kuma ita bata ma san yana yi ba, domin kuwa rashin zaman shi na bata damar ganawa da masoyinta cikin kwanciyar hankali da jin dad'i. Kasancewar zuciyar Baffa har yanzu bata aminta da auren da yake shirin yi ma 'yar tasa ba, yasa ya nuna halin ko-in-kula a yadda Jay ke tafiyar da al'amurranta, sai dai ya ci alwashin ba zai aurar da ita ba har sai yayi duk wani binciken da ya kamata ace mahaifi yayi kafin ya aurar da d'iyarsa. Ta 6angaren Sadam kam hak'urinsa ya kusa k'arewa ganin yadda har yanzu Baffa ya k'i yace komai, yana kuma tsoron kada Baffan ya ci karo da munanan halayensa a wurin binciken da ya ce zai gabatar. Bai yi k'asa a gwiwa ba, ya kuma ci alwashin mallakar Jay ko ta wane irin hali, domin a yadda yake jinta yanzu ba zai iya rayuwa ba tare da mace irinta ba.1 Wasa-wasa har Jay ta kammala exams d'in first semester suka yi hutu suka kuma koma 2nd semester, amma Baffa bai ce komai ba dangane da labarin aurensu, hakan yasa ta yanke shawarar tunkarar shi da maganar, domin yadda Sadam ke nuna damuwarsa, yayin da ita kuma baza ta juri ganinshi cikin tashin hankali ba. *** A hankali yake takawa, fitowa yake daga cikin bankin zuwa wurin da su kan adana motoci a matsayinsu na ma'aikatan wurin. Hannunsa d'aya a aljihu, d'ayan kuma yana kan kunnensa da alama kiran waya ya ke yi. "Babe." Yayi maganar a kasalance, haka kuma duk wanda ya kallesa zai iya ganin damuwar da ke kwance akan fuskarsa. "No, yanzu muka fito lunch, I'll be on my way, so prepare for me. Okay?" Daga haka ya kashe wayar, ya shige mota, ya dauki hanyar Yar'adua University. Fitowarsu lecture kenan ita da Miemie, suna takawa zuwa inda tayi parking, ganinshi da tayi yana doso su yasa tayi saurin mik'a mata key d'in motar dake hannunta tare da cewa "kiyi gaba, zan kira ki idan na gama." A haka ya k'araso wurin yayin da Miemie ta kasa sauke idanunta a kanshi, ba tare da saninta ba books d'in da ke hannunta suka fad'i k'asa, a karo guda ta sake baki tana faman kallonshi. Murmushi ya saki, inda shima idanunsa a kanta yace "Hi." Hakan da yayi ba k'aramin tafiyar da imaninta yayi ba, inda cikin borin kunya tace "Hi" tana mai duk'awa ta kwashi books d'inta ta juya da sauri. Ta rasa menene dalilin da yasa take rasa natsuwarta a duk lokacin da ta ci karo da saurayin aminiyar tata. Da wannan tunanin tayi gaggawar barin wurin, yayin da ya bi bayanta da kallo, har sai da Jay tace "hey, why are you starring at her?" "Was I?" Ya tambaya yana d'aga girarsa, hannuwansa duk biyun cikin aljihu. Shiru tayi ba tare da ta tanka mishi ba, inda shi kuma ya matso gabanta yace "I need to see you, yau na zo da issues, cuz ina cikin matsalan da ban san ya zan shawo kansa ba." Take hankalinta ya tashi, suka jera a tare zuwa inda yayi parking, a tare suka bud'e motar suka zauna, sannan ta zuba mishi ido tana tambayar abinda ke damunsa. Sai da ya shafi sumar kansa, a karo guda ya cika bakinsa da iska ya furzar, sannan ya sassauta muryarsa, ya juyo ya kalleta ido cikin ido ya fara magana. "Jameela" A hankali ta d'ago tana k'are mashi kallo, yadda ya kirata ta, da kuma yanayin da fuskarsa take ciki yasa ta san akwai muhimmiyar maganar da yake son yi. "What?" Gyara zamansa yayi, a karo guda yace "You know I love you right? And I can do anything to be with you." "Sure, and I love you too." "I know that babe, but this time na fara samun negative feelings akan irin son da kike mun." "Why" ta tambaya idanunta a kanshi. "Jay almost 5 months da muka yi magana da Baffanki fa, amma har yanzu bai ce komai ba, and you sit there doing nothing. Babe hak'uri na ya gama karewa wallahi. Na yanke ma kaina shawarar zan hak'ura kawai in samu wacce take so na, someone who will fight for our love, our right. I'm tired of all this go & come, na gaji, kuma ke kan ki kin san nayi hak'uri, ki gane ko, I'm desperately in need of a woman in my life, I'm a healthy man, and big enough for heaven's sake. I can't bear this anymore."7 Duk da Air condition d'in dake kunne a motar, sai da ta ji tsigar jikinta ta mik'e, a karo guda kirjinta yayi wata mummunar bugawa. Kai ta fara girgizawa tana cewa "no, no, you can't do this to me Kazaure, U're the only one I love, and the one I'll spend the rest of my life with. You can't leave me." Ta k'arasa maganar idonta cike da hawaye, dan har ta fara hango irin halin k'uncin rayuwar da zata shiga matsawar Sadam ya juya bayansa gare ta. Hannunta ya rik'e, a hankali yace "what do you want me to do Jameela? Sanin kanki ne nayi iya k'ok'arina wurin ganin na kasance tare da ke but it seems like Baffanki doesn't like me. Shi yasa kawai na yanke shawarar fita harkarki, tunda abinda mahaifinki ya fi so kenan." "That's not an excuse Kazaure, cuz I love you, so I don't care whether Baffa likes you or not, I just choose to be with you, now and forever. I love you so very much Sadam." Girgiza kansa kawai yayi, inda ya saki murmushin takaicin da ya fi hawaye zafi, kallonta yayi tare da cewa "baza ki gane halin da nake ciki ba, yanzu haka maganar nan da nake maki gab ake da yi mun transfer zuwa Maid, dan yanzu ma sai da muka yi maganar da bank manager d'inmu kafin na fito, a yadda nake so bazan iya barin garin nan ba tare da an d'aura mana aure ba, but look at us now, Dad d'inki yayi watsi da maganar mu, how do you think i can wait that long? Ya kike so nayi?" Ya k'arasa maganar tare da dafe kanshi, ya juya yana kallon gefe. Inda ita kuma bakinta ya gagara motsawa, hawaye ne kawai ke ambaliya akan kumatunta, ji take baza ta iya jure ma rashin mutumen da ta fara so a rayuwarta ba, baza kuma ta lamunce ma yadda Baffa ke shirin rusa plans d'in da suka dad'e suna shirya ma junansu ba. She have to do something, abinda take fad'a a ranta kenan, yayin da Sadam ya gagara had'a ido da ita, duk kuwa da idanunta da ta zuba masa kamar mai karantar yanayin da yake ciki. Hawayenta ta shafe, ba wai dan sun daina zuba ba, sai dan kawai tana son tayi maganar da zata kwantar masa da hankali har kuma ta samu ya sauko daga fushin da yake yi. "To kayi hak'uri kaji? In sha Allah zan kawo k'arshen abin nan gaba d'aya, a yau d'in nan zan yi ma Baffa magana, duk da bana sanin lokacin dawowarsa, da lokacin fitarsa, amma zan jira har zuwa lokacin da zai dawo ko k'arfe nawa ne." Juyowa yayi ya kalleta. Ya sa hannu ya fara shafe mata hawayen fuskarta. "Ni ba abinda nake son ji daga gare ki kenan ba, so nake ki mun alk'awarin ko kowa ya juya mun baya ke baza ki ta6a bari na ba, I mean ko da Baffa yace ba zai yarda na aure ki ba, domin muddin na rasa ki, rayuwata tana cikin garari, zan iya fad'awa wani hali wanda ban san ranar fita ta ba. Please, promise me zaki kasance tare da ni cikin ko wanne irin hali." Kanta ta girgiza, hawayenta suka cigaba da yayyafowa kamar ya tunzura ta, a haka ta saki murmushi sannan tace1 "a yadda nake jin sonka na yawo a jiki na, zan iya sadaukar da rayuwata domin in fanshi taka, ya kamata ka gane irin son da nake maka halitta ne, ba wai soyayya bace irin ta cikin movie ko wacce ake karantawa a litattafan Hausa. Soyayya ce wacce Allah wanda ya halicce ni, shi kad'ai zai iya tantance yawan adadinta. Soyayya ce mai had'e da shak'uwa wacce nake jin idan aka yi gigin raba ni da kai tamkar ana k'ok'arin raba ni da rayuwata ne. Na yi maka alk'awarin kasancewa tare da kai, ko da gaba d'aya duniya zasu juya maka baya Kazaure."13 Kansa ya tsinta cikin wani irin yanayi na farinciki, ji yake tunda ya zo duniya bai ta6a jin kalaman da suka mishi dad'i irin wannan ba. "That's all I want to hear from you darling. Please, make everything possible kinji?" "I'll." Ta fad'a bakinta k'unshe da kyakkyawan murmushi. Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya maida kallonsa gareta. "Kinga har na cinye lokaci na ko, barin yi saurin komawa, zan kira ki after mun tashi office." "Alright," Ta fad'a lokacin da ta bud'e motar ta fito, zuciyarta cike da fargaba da tunanin maganganun da Sadam ya zo mata da su. Today is all about #SSDN😃😃2 Let's rock hunnies💃👏 Wayarta ta fitar zata kira Miemie, kiran Goggo ya shigo, ta d'aga ta d'ora wayar a kunnenta tana cewa "Hello." "Ina cikin school." "A'a ban gama ba, ina da lecture 2-4." "Lafiya kuwa?" "Ok, gani nan zuwa yanzu." Da haka ta kashe wayar, ta kira Miemie ta tambayi inda take, bayan ta fad'a mata ne ta cigaba da takawa, zuciyarta duk babu dad'i, ta wani 6angaren maganganun Sadam na kadar mata da gaba, ta wani fannin kuma tana fargabar kiran gaggawar da Goggo tace Baffanta na mata. Da haka ta iso wurin, ba tare da ta mata dogon bayani ba ta anshi key d'inta, ta shiga ta tayar da motar ta d'auki hanyar gida. Da sallama ta shigo, ta samu Baffa ya tafka uban tagumi zaune akan kujera mai cin mutum biyu, gabansa plate ne da spoon, a gefe guda kuma babban foodflask d'in abinci ne. Goggo ce ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray, a tare suka k'araso cikin palon, bayan ta ajje tray d'in ta bud'e foodflask d'in zata fara sa ma Baffa abincin, amma ya d'aga mata hannu tare da cewa "dakata tukun." Kujerar da ke kallonsu Jay ta zauna, "Sannu da hutawa Baffa." Bai ansa ta ba, illa ajiyar zuciya da ya saki, a karo guda ya sauke hannunsa daga tagumin da yake yace "Ta so ki dawo nan Mamana." Mamakin dake kan fuskarta ya kasa 6oyuwa, rabon da ta ji muryar Baffanta haka tun kafin ta tunkare shi da maganar aurensu da Sadam, da haka ta taso ta dawo kusa da shi ta zauna, ya dai-daita zamansa ya fuskance ta sosai, kafin ya kira suna ta. "JAMEELA." A hargitse ta d'ago tana dubansa, kasancewar yau ce rana ta farko da ya ta6a kiran sunanta kai tsaye, ba tare da ya sakaya ba. "Na'am Baffa." Ta fad'a idonta cikin nasa. "A watannin da suka gabata, kin zo mun da maganar da ban ta6a tsammaninta daga gare ki ba." Ya muskuta, sannan ya cigaba. "A farko, na nuna miki k'in yarda, da rashin amincewata akan abun. Amma daga baya na sauke makaman yak'ina, na kuma sauko daga dokin nak'in da na hau. Bakomai ya jaza hakan ba, illa mahaifina da ya sanya baki a maganar, ya kuma ce inyi yadda yake so. Nayi biyayya a gare shi, nayi abinda ya ce Ba tare da na nemi jin dalilin da zai sa ya tursasani akan abinda banyi niyya ba, ba dan komai ba, sai dan kasancewarsa mahaifina, wanda ya kawo ni duniya, wanda Allah (SWA) yace inyi biyayya a umarninsa matsawar basu sa6a shari'ar musulunci ba. Abinda yasa na kawo wannan maganar shine, ina so a matsayinki na 'yata, wacce na haifa a cikina, na kuma baki duk wani farinciki da jin dad'in rayuwa da ki cire soyayyar Sadam a zuciyarki, ki hak'ura da shi, ki manta da duk wata alak'a da ta ta6a shiga tsakaninku ba dan komai ba sai dan sakamakon binciken da nayi a kansa, bai dace da kamilar mace irin ki ba Ummi." A daburce ta d'ago tana kallonsa, wani dodo-dodo take ganin ya koma mata saboda kalmar 'ki rabu da Sadam' da ya kira mata. Nan da nan idanunta suka ciko da hawaye, bakinta na kyarma ta fara magana. "Ba zan iya ba Baffa, ba zan ta6a iya rayuwa ba tare da soyayyar Sadam ba, na gwammaci ka ce ka yafe ni, akan kace in rabu da mutumen da nake so fiye da numfashi na. Ina son sa a duk yadda yake, dan haka ba ruwa na da ko me bincikenka ya tabbatar maka, ni nake sonshi, ni kuma zan zauna da shi, to babu ruwan wani da halayyarsa, so far Sadam bashi da wani mugun halin da za'a k'yamata. Ka taimaki rayuwata Baffa, wallahi zan iya mutuwa idan ka hana na aure sa."14 Wani matsanancin kuka ta ida fashewa da shi. Goggo dake gefensu itama kukan ta saka, saboda tsananin tausayin halin da 'yar tata ke ciki. Ta 6angaren Baffa kam, da za'a bud'a zuciyarsa, za'a iya ganin yadda bak'in ciki yayi masa katutu, tare da tokare masa gefen zuciyarsa. Dak'yar ya saita tunaninsa, ya dafa kafad'ar Jay yace "Ummi, ni mahaifinki ne, kin tabbatar bazan ta6a so miki abinda na san zai cutar da rayuwarki ba. Abinda nake so da ke kiyi hak'uri, ki fawwalawa Allah lamurranki, a sannu zai maki maganin halin da kike ciki. Haka kuma a shirye nake, na aurar da ke ga duk wanda kike so, wanda na aminta da d'abi'u da halayensa, amma ba mashayin giya ba, ba kuma d'an caca ba."2 Yana gama fad'ar haka ya mik'e, hannunsa dafe da gefen k'irjinsa na hagu, inda ba dan k'arfin zuciya irin ta namiji ba, shima da kukan zai saki ko dan ya samu sassauci daga rad'ad'i da zafin da yake ji a cikin k'irjinsa. Cikin zafin nama ta kama bayan rigarsa, kuka take bil hak'k'i, lokaci guda idanunta sun rine, sun k'ara fitowa waje k'ulu-k'ulu. "Kada muyi haka da kai Baffa, kai fa kace ka amince zaka aurar da ni gareshi, ka taimaki rayuwata dan Allah, haba Baffana, ina kulawa da soyayyar da kake nuna mun a da? Ina tarairaiya da son farincikina da kake yi?"5 Ta k'arasa maganar cikin wata azabtacciyar muryar da ta sa zuciyar Baffa tsinkewa, take idanunsa suka yi jajur, a karo guda wata k'walla mai zafi ta sauko masa. Hannun rigarsa yasa ya d'auke ta, sannan ya duk'a gabanta tare da tallabo ha6arta yace "ina so ki tuna k'auna da soyayyar da na nuna miki tun tasowarki, ki d'auke ta ta zame maki wani jigo da zaisa kiyi biyayya a gare ni. Domin kuwa ko da zaki rasa ranki, bazan yarda ki auri mashayin giya ba. Wannan itace magana ta k'arshe da zamu yi dake akan shi, daga yau ki warware duk wata alak'a da take tsakaninku."4 Yasa hannu ya k'wace rigarsa, ya shige part d'insa, inda ya zube a kujera hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarsa, tamkar wani d'an k'aramin yaro. Mik'ewar da zata yi da zumar ta bi bayan baffan, amma cikin rashin sa'a ta sulale ta fad'i k'asa a sume. Kuka mai had'e da salati Goggo ta kwasa tayi kanta, ganin bata numfashi yasa ta warci gorar ruwan da ta kawo ma Baffa ta bud'e ta tuttula a saman fuskarta, cikin d'an k'aramin lokaci ta dawo hayyacinta, tari ta fara yi, daga bisani ta bud'e da wani sabon babin kukan. Kamar wata mahaukaciya ta mik'e tare da warto jakarta ta zazzage, Goggo banda ido babu abinda take binta da shi, a haka ta d'auki wayarta, ta wuce d'aki da sauri, ta fara kiran number Sadam. "Babe." Ya ansa wayar da shi, kukan da ya ji ta fashe masa ne yasa yayi saurin mik'ewa ya fita yana tambayar "what's wrong with you darling?" Bata 6oye masa komai ba, cikin kuka ta fayyace mashi yadda sukayi da Baffanta Duk da ba k'aramin caji kanshi ya d'auka ba, hakan bai hana dabara fad'o masa ba, a karon farko ya saita muryarsa tare da cewa. "I know you love me, and you're ready to fight for our love, right?" "Of course, I'll do whatever it takes to prove that." "Kinyi alk'awarin zaki kasance tare da ni ko da duka duniya sun juya bayansu gare ni. Haka ne?"2 "Zan iya rayuwa da kai, ko da kai kad'ai ne mutumen da yayi saura a duniyar da na san mutane da dama." "Thank you. Now, share hawayenki, ki bani daga nan zuwa gobe, I'll find the solution for all of this. Plans d'in da muka dad'e muna shirya ma kanmu will never go just like that. Trust me babe." Hawayenta ta shiga sharewa, ko bakomai ta samu k'warin gwiwa daga wurin da take tunanin baza ta samu ba. Tayi zaton ba zai nuna damuwarsa ba, ashe ba haka abin yake ba, ashe soyayyar da Sadam ke mata tafi gaban tunanin dukkan tunaninta!4 * *** Ofishin manaja ya zarce bayan sun gama wayar. "Sir, zan gama duk abinda nake daga nan zuwa next week, In sha Allah." "Babu laifi, dama lokacin da aka baka daga nan zuwa end of the month d'in ne." "Ok, thank you Sir." "U're most welcome." Ya bashi hannu suka yi musabaha, sannan ya fito ya zauna a kujerarsa, sai dai zuciya da ruhinsa gaba d'aya sun ta'allak'a ne akan abinda yake shirin aikatawa. Wani fanni na zuciyarsa na tunatar da shi akan had'arin abun, inda har zuciyarsa kan raya mishi, wane irin hali zai tsinci kanshi, idan aka yi ma 'yarsa abinda yake shirin yi ma 'yar wani? Wani 6angaren kuma na tunatar da shi akan rashin yiwuwar hakan. A bayyane ya furta "That won't happen. I'll never have a child. Jay ta ishe ni rayuwa, babu dalilin da zaisa in k'ara ma kaina nauyi." Maganganun da ya dinga yi a k'asar zuciyarsa kenan, har aka tashi aiki bai samu wata natsuwar kirki ba, ko da ya fito bai zame ko ina ba sai k'ofar gidansu Jameela. Bayan ya gyara parking ya cire wayarsa ya kira ta, ba'a d'auki dogon lokaci ba ta fito, idanuwanta sun kumbura suntum, ta ci kuka har ta gode Allah. Ganin yadda ta koma cikin d'an kankanin lokaci yasa hankalinsa ya tashi, handkerchief ya ciro fari sol, sai k'anshin daddad'an turarensa yake ya mik'a mata, ta sa hannu ta ansa ba tare da gardama ba, ta fara shafe kumburarrun idanunta. Shiru ne ya ratsa motar na wasu 'yan dakiku, tunanin yadda zai bijiro mata da k'udirinsa yake, sai dai ya rasa hanyar da zai bi domin fallasa mata sirrin da ya matso a k'asar zuciyarsa. Wannan ne karo na farko, da ya ta6a jin fargabar tunkararta da wani abu tun daga ranar da ya santa. Dakewa yayi, ya juya ya kama hannayenta duk biyun, cikin wata rarraunar murya ya kira sunanta. "Jay." A tsanake ta d'ago kumburarrun idanunta ta sauke a kansa. "Ba zan iya jure ganinki cikin tashin hankali da bak'in cikin nan ba. Ba zan jure ma kallon yadda kike asarar hawayenki a ko da yaushe ba. Babe me zai hana mu k'aurace ma wannan mummunan tashin hankalin da yake barazana da soyayyarmu? Me zai hana mu canja mazauni, mu koma wata duniya ta daban, duniyarmu mu biyu, mu shimfid'a irin rayuwar da muke mafarkin samu just me and you, no tension, nothing, nothing but love and care."3 "How do you think that wud be possible Kazaure? Ka manta k'alubalen da yake gabanmu ne? Ta ya zamu iya samun wannan freedom d'in? Ka gaya mani ta yaya?" Ta fashe da wani zazzafan kuka, wanda yasa ya dafe kansa, yana jin kukan nata har a cikin zuciyarsa. "It's possible, matuk'ar zaki amince da shawarar da nazo da ita." "Sanin kanka ne, ban ta6a k'etare maganarka ba, Dan haka kada ma ka fara tunanin zan bijire ma shawarar da nasan zata zama mabud'in matsalarmu."1 "Nayi magana da bank manager d'inmu kafin in fito cewar zan gama duk abinda nake in wuce Maiduguri zuwa next week, dan haka kizo mu tafi tare, mu shimfid'a kyakkyawar sabuwar rayuwa ta soyayya, just the two of us." Cikin kidimewa ta d'ago manya-manyan idanunta tana kallonsa, fuska ya marairaice, ya d'aga mata kanshi.1 "I'll give you everything you need, I'll love you nd you alone Jameela, zamu samu mai d'aura mana aure ba tare da wata matsala ba, zamu k'aurace ma duk wannan tashe-tashen hankulan da muke ciki, zan baki duk wace irin kulawa kike buk'ata, zamu manta da wannan hayaniyar da muka riski kanmu a ciki, zamu yi rayuwarmu yadda muke so, in yaso bayan wasu shekaru sai mu dawo gida, by then, na san dole Baffanki ya hak'ura, tunda dai babu irin biyayyar da baki mishi ba, shine ya kasa gane abinda kike so, ya kuma kasa baki abinda kike so, so ko ina aka je baza a d'ora miki laifi ba."2 Kanta ta fara girgizawa, hawaye na bin kumatunta. "No please, stop it Kazaure, I can't do this to my own parents, ka dai canja wata shawarar, but wannan will never work, kai kanka ka sani." Baiyi k'asa a gwiwa ba, ya k'ara rik'e hannunta cikin nashi, "This is the only way out Jay, wannan ce kawai hanyar da zamu iya mallakar junanmu ba tare da mun k'ara cin karo da wani k'alubale a gabanmu ba. Kiyi tunani sosai akan shawarar nan, zan baki daga nan har zuwa kwana ukku, duk hukunci da kika yanke, zanyi amfani da shi, sai dai ina so ki sani, matsawar kika karya alk'awarin da kika d'aukar mun na cewar zaki kasance tare da ni no matter what, to bazan ta6a yafe maki ba, kuma har abada bazan daina yi miki kallon maci amana ba." Kafin ta bud'a baki, suka tsinkayi muryar Baffa wanda ya fito domin zuwa sallar maghriba a masallacin da ke gaba kadan da gidansu. "Ummi." Hakan yasa ta fito daga motar, ta k'arasa inda yake tsaye kanta a k'asa. "Wuce ki shiga ciki." Shi kuma ya juya ya kama hanyar inda motar Sadam take. Bata shiga gidan ba ta biyo bayanshi dan gudun kada ya fad'i abinda zai 6ata ran Sadam d'inta. "Barka da yamma" Cewar Sadam yana shafe kansa. Bai damu da ya ansa ba, ya fara maganarsa. "Dan Allah ina so yau ta zama rana ta k'arshe da zaka k'ara zuwa k'ofar gidan nan, kuma rana ta k'arshe da zan k'ara ganin ka da 'yata. Idan ka yi yadda na ce, zamu zauna lafiya, matsawar ka bijire wa umarnina kuwa, tabbas zaka sha mamakin abinda zai biyo." "Baffa" Ya tsinkayi muryar Jay tana yi mashi kallon da yake nuni da bai kyauta ba. Bai bi ta kanta ba, ya nuna Sadam "this is last warning." Kuka ta fashe tana diddira kafa "Ni wallahi bazan iya rabuwa da shi ba, idan ma ka hana shi zuwa, ni zan taka inje har inda yake in same shi." Da haka ta shige gida tana wani irin kuka, wanda ya sosa zuciyar Sadam, ya kuma sa ya k'ara zage damtse wajen ganin sun gudu sun je sunyi aurensu, ko dan ya bak'antawa Baffa, shima ya d'and'ani kad'an daga bak'in cikin da ya ke cusawa zuciyoyinsu.3 Kallon bak'in ciki Baffa ya bita da shi, abin takaici wai wannan Umminshi ce, 'yar da ya shagwa6a ya sangarta fiye da yadda ko wane uba yake sangarta 'ya'yansa. Juyawa yayi ya koma cikin gidan shima, nan ya sameta yashe saman carpet sai rusa kuka take yi. Goggo da abin duniya ya ishe ta, ta saka ta gaba, tana matsar nata hawayen, gashi bata da halin da zata k'etara hukuncin da mijinta ya gindaya, amma ba dan haka ba, da tace ya barta ta auri wanda take son kawai. Cikin d'aga murya ya nuna ta. "Ni zaki wulak'anta a gaban wani ko Ummi? Kin manta da cewar nine wanda ya kawo ki duniya wanda yake da alhakin za6a miki mijin ma gaba d'aya. Banga laifinki ba, laifinmu ne da tun wuri bamu yi ma tufk'ar hanci ba, muka barki kara zuba, muka sa miki ido bamu kwa6e ki ba. Sai dai banyi zaton abin zai zo mana a haka ba, banyi tunanin irin wannan ranar zata riske mu ba."2 "Haba Baffa, wace irin biyayya ce banyi a gare ka ba? Amma ka kasa cika mini burina, Me sa baza ka gane yadda soyayyar Sadam ke azabtar da ni ba? Ko dan kai baka san zafi da d'acin soyayya ba?"13 Ta girgiza kai hawaye na cigaba da kwararowa a fuskarta. "Kayi hak'uri Baffa, amma bana jin zan iya biyayya a abinda kake so, ba zan cutar da kaina in faranta maka ba, bayan Allah ma ya halatta mun abinda kake shirin haramta mun." Wani tuk'uk'in bak'in ciki zuciyarsa ta fara fesarwa, nan da nan idanunsa suka kad'a suka yi jajur, gadan-gadan yayi kanta, Goggo tayi azamar shiga tsakaninsu tuni yasa mata hannu, ya isa gaban Jameela, sai da ya daddage, sannan ya d'aga hannu ya wanke ta da wani kyakkyawan mari. Kafin tayi wani yunk'uri ya kuma kwad'a mata wani, ya sa kafa ya harba ta. "Ke d'in banza, sai kace ke kika haifi kanki? To tunda abin naki iskanci ne, ba kya jin lallashi, zan bi da ke ta hanyar da zata ladabtar dake, jikinki zai gaya miki, tunda kince baza ki bi abinda nake fad'a miki ba." Kuka take amma bakinta ya kasa rufuwa, "Wallahi ko da zaka kashe ni Baffa, ruhina da gangar jikina baza su daina k'aunar Kazaure ba, shine farincikina, abin alfaharina."5 Wannan karon a hargitse ya isa gabanta, ya cakumi wuyan rigarta ya shak'e, ya fara k'ok'arin had'a mata kai da bango. "Na gwammaci in kashe ki, kan ace ina ganin wannan bak'ar ranar da nake fada kina fad'a Ummi. Nayi da-na-sanin irin tarbiyyar da na baki. Ni mahaifinki, ni kika fifita wani D'A NAMIJI a kaina ko? Duniya ce Ummi, zata bi dake yadda kike so a yanzu, amma ina guje miki ranar da zata juya miki ba." Ganin yana niyyar yin kisan kai yasa Goggo ta taso, dak'yar ta 6an6are hannunsa a wuyan Jay, ta fad'i k'asa sharaf, idanunta sun firfito, sai wani irin tarin wahala da take yi. "Kije kiyi duk abinda yayi miki, amma ki sani ba zan lamunci irin iskancin da kika zo mun da shi ba, dan haka ki za6a tsakanin NI da d'an iskan NAMIJIN da na tabbata ba k'aunarki yake tsakani da Allah ba." Daga haka ya wuce part d'inshi masallacin da bai je ba kenan, sai a gida yayi sallar, yana gamawa toilet ya shige ya sakan ma kanshi ruwa saboda yadda zuciyarsa ke k'una, a wani 6angaren har yana nadamar haihuwar Jay a rayuwarsa.10 I told you, today is all about SadJay😂😂 Allah Sarki Baffanmu😢😢 A k'alla sai da Sadam ya kwashi kusan mintina sha biyar a wurin ba tare da ya ya motsa ba. Ganin babu sarki sai Allah yasa ya tada motar ya wuce ya bar unguwar. Yana gab da shiga Federal Medical Center domin duba wani colleague d'inshi marar lafiya, ya fara jin k'aran waya na tashi a cikin motar wanda ya tabbatar ba ringing d'in wayarsa ne ba. A hankali ya maida kallonsa inda yake jiyo k'aran, nan ya ci karo da wayar Jay, ajje a seat d'in da ta tashi. Hannu yasa ya d'auki wayar, sunan Miemie ya gani, hakan yasa ya maida wayar ya ajje, tare da mayar da kai a tuk'inshi. Ba'a d'auki dogon lokaci ba kiran ya kuma shigowa, kamar ba zai d'auka ba, sai kuma wata dabara ta fad'o mishi, take ya saki wani lallausan murmushi, a karo guda ya latsa wayar ya d'ora a kunnensa. "Hello." Yayi maganar da k'ak'k'arfar muryarsa, mai wani irin amo da sauti mai dad'i. "Are you there?" "Errrnmm" Tayi gyaran murya. Duk da ba gabansa take ba, amma zai iya tantance yanayin da take ciki, wanda ya lura tana shiga a duk lokacin da ta ci karo da shi, ko kuma ta ji muryarsa. "Ina wuni" "Lafiya, naje gidansu yanzu, so ta manta wayan a motana." "Ok, ina son magana da ita please, yaushe zaka mayar mata da wayan." "I don't know. Cuz an cire ni daga cikin mutanen da zasu cigaba da zuwa gidansu." "Kaman ya kenan?" "Never mind. Idan kun had'u sai ku tattauna abinda kike son gaya mata. Bye." Ganin yana k'ok'arin datse wayar tayi saurin tare shi. "Sadam." "So you know my name?" Bakinsa k'unshe da wani makirin murmushi. Bata bi ta kan maganar shi ba, ta cigaba "Ka kawo man phone d'in, sai inje gida in kai mata, cuz gobe bamu da lectures, nd kaima zaka buk'aci yin magana da ita, right?" "An zo wurin" Ya fad'a a cikin zuciyarsa, a fili kuma murmushi ya saki. "Very good idea. Text me your address now." A haka yayi parking gaban Male Medical Ward, ya kashe wayar, ya fito ya shige ciki. Maimakon ta yo text d'in a wayar Jay, sai ta yo a wayar Sadam, baki bud'e yake kallon text d'in tare da mamakin ashe dama tana da number shi? Bayan ya fito, sai da ya tsaya a masallacin cikin asibitin yayi sallah, dan har an riga anyi isha'i, sannan ya d'auki titin Layout zuwa gidansu Miemie. A k'ofar gidan yayi parking, sannan ya kira ta da wayar Jay, minti biyu ba'a yi ba ta fito, ta gama fente fuskarta da foundation, ta ci gira, ga kyakkyawan pink janbakin da ta shafa, wanda ya k'ara ma doguwar fuskarta annuri. Ganin bashi da niyyar fitowa a motar, yasa ta k'arasa gefen k'ofarshi ta tsaya, k'irjinta sai dukan tara-tara ya ke, sai dai tayi alwashin sanar da shi sirrin da ke zuciyarta, watak'ila wannan ita kad'ai ce damar da zata iya samu. "Mu shiga ciki mana." "No, ina sauri gaskiya." Yayi maganar lokacin da ya mik'a mata wayar. "Ina son magana da kai if possible." Jim yayi yana dubanta, kamar ya bata dama, sai kuma dabarar da ya shirya ta fad'o masa. "Kina da number ta ai?" "Sure, but tunda gani-gaka kaman abun will be more easier." "As I told you, ina sauri ne, so kiyi texting mun ko me kike son muyi magana akai." "Alright, amma kada ka ga laifi na, and kada ka d'auke ni maha'inciya. Ka d'auka cewar hakan k'addarata ce, ka kuma d'auka cewar idan a kanka abun ya faru, me ya kamata kayi." "Never mind. Ina saurarenki ke dai." Daga nan ya tayar da motar, ya wuce, zuciyarsa fes-fes, domin ko matsawar Miemie za tai mishi texting abinda ke k'asar zuciyarta, to zaiyi amfani wajen kafa wata hujja, da zai sa Jay ta amince akan shawarar da yaje mata da. Bai k'arasa fita layin gidansu ba, text d'inta ya shigo masa, wayar ya janyo ya bud'e, wata dariya ya saki, har yana dukan steering. "Finally." Ya fad'a yana k'ara duban text d'in, a haka ya kashe wayar ya ajje, sannan ya murza giyar motar, ya bata wuta sosai, ya wuce Maikudi Hotel.1 《》《》《》《》 Kwanaki biyu kenan rabon da ta ji muryar Sadam, ko ta d'ora shi a idanunta, gaba d'aya wayoyinta Baffa ya k'wace su, gashi ya kafa mata dokar rashin fita ko da k'ofar gida ne, saboda ita ma ko fita baya yi, kullun yana gida, da ta nemi tai mishi hauka kuma jikinta zai bata labari, kwata-kwata ya daina sassauta mata, ta zamo tamkar ba Ummin nan da yake riritawa ba. Ta rame, ta lalace ta fita daga duk wani hayyacinta a d'an kwana biyun da tayi tana fama da azabar son gani da kuma jin muryar Kazaure. Agogon dake manne da bangon d'akinta ta kalla, k'arfe goma sha d'aya na safe, wata mummunar faduwar gaba tayi, tunawar da tayi gobe ne cikon kwanakin da Sadam ya d'iba mata. Duk da bata yanke shawarar binsa Maiduguri ba, amma tana son ganinsa, watak'ila su canja wata shawarar da ta fi waccen. A hargitse ta fito, gashin kanta duk ya mik'e, idanunta sun fad'a, sun firfito waje, d'akin Goggo ta shige, jin k'aran ruwa a toilet, ya tabbatar mata wanka take, hakan ya bata damar bincika d'akin ta d'auki wayarta, ta ruga da gudu ta koma d'akinta, ta maida k'ofar ta rufe, tare da danna jamlock. Da sauri da sauri ta sanya number Sadam ta danna kira, sai dai har ta gama ringing bata yi sa'a ya d'aga wayar ba. A gaggauce ta shirya, tare da sanya uniform d'inta ta d'auko jakarta, sannan ta sanya wayar a silent ta fito palo. Bata samu kowa ba, hakan yasa ta sanya kai zuwa waje. Zaune ta samu Baffa a k'asan wata canopy dake harabar gidan, k'afarshi d'aya kan d'aya, hannunsa rik'e da jaridar SundayTrust. Gaban shi ta k'arasa, ba tare da ta gaishe shi ba ta juyar da kai, "Zan je school." Bai ko kalleta ba, saboda irin mugun haushin da take bashi, illa ajje jaridar da ya yi, ya mik'e yana k'wala ma driver kira. Da sauri ya iso, yana cewa "Ga ni Alhaji." "Fito da mota ka kai mun ita makaranta, kuma ko nan da can kada ka matsa daga k'ofar ajinsu, tana fitowa ka sako ta gaba ka dawo mun da ita." "In sha Allah Alhaji" Ya mik'e ya fito da motar, ta bud'e gidan baya ta zauna, Allah-Allah take su bar gidan, domin ji take tamkar a cikin prison take. Wayar ta fitar ta tura mashi text, "it's Jay, mu had'u a school yanzu-yanzu." Ba'a fi minti biyu ba, ya dawo mata da ansa "I'll be on my way." Bayan sun shiga makarantar tace da drivern ya kaita students Center a can za suyi lecture, yana ajje ta ta fito ta wuce ciki, inda shima ya fito ya fara bin bayanta, amma saboda yawan d'alibai tuni ta 6ace ma ganinshi. Ta d'ayar k'ofar ta fito, ta wuce inda Sadam yayi parking ta same shi. "Ja muje." "Ina zamu je?" "Mu samu wurin da zamu yi magana, cuz akwai wanda Baffa ya had'o mu tare. Muje tun bai fito ya ganmu ba." Da sauri ya tada motar, da gudu suka bar wurin, ba su tsaya ko ina ba sai da suka je wani daji-daji dake can k'arshen makarantar. Hall d'aya ne duk fad'in wurin, hakan yasa students ke yi ma wurin lak'abi da Sambisa Forest. Bayan ya samu wurin parking, ya juyo yana kallon yadda lokaci guda ta fita hayyacinta, damuwa k'arara kwance saman fuskarta. Hakan yasa ya ji tausayinta ya tsirga zuciyarsa, inda ya fara ayyana cewar dole ya fitar da ita daga rayuwar k'uncin da mahaifinta ya jefa ta. Kallonta yayi, ya marairaice fuskarsa. "Babe, this is the right time for us to runaway. Ba lalle mu kuma samun wani chance d'in da zamu ga juna ba." "No Sadam, bana tunanin wannan shawarar zata yi aiki. Abinda yasa na fito yanzu haka, ba komai bane illa ina so mu canja wata shawarar, muyi abinda hankali zai d'auka." Ido ya bud'e sosai yana kallonta. "Ko? Maganata hankali ba zai d'auka ba kenan? Kin ma d'auke ni wawa, wanda bai san abinda yake yi ba ko Jameela? Saboda na sadaukar da farinciki da jin dad'i na gare ki ko?" "No please, ba abinda nake nufi kenan ba." "What then? What? Jay baki san irin matan da suke bina ina bonsa su ba, ba don komai ba, sai dan irin son da nake miki. Me sa kike son faranta ma wanda bai damu da farinciki, da jin dad'inki ba? Me sa baza ki tausaya ma halin da nake ciki ba?" Kuka kawaj ta fara yi masa, duk da bata son 6acin ran sa, amma bata tunanin zata iya barin mahaifarta, ta koma wata duniya ta daban ba. Wayarsa ya d'auko ya bud'e text d'in da Miemie tai masa ya mik'a mata. "Me zaki ce game da wannan? Please kada ki mun kallon wanda ya yaudareki, cuz I made my mind, zanyi switching mata, tunda ke kam kin gwammaci kullun ki ganni cikin bak'in ciki, da tashin hankali." Hawayen da suke zuba a idanunta suka cigaba da gangarowa, cikin dasassan murya ta fara karanta text d'in This might sound weird, but this is the true feelings of my heart. Na kamu da soyayyarka mai zafi, wacce take wahalar da ruhi da gangan jikina. Na yi k'ok'arin danne abinda nake ji game da kai duk dan saboda dangantakar da ke tsakaninmu da Jay. But kasan zuciya da k'wanji, na kasa Sadam, ba zan iya ba, soyayyarka na wahalar da ni, fiye da duk yadda zan kwatanta maka. Please, ka taimaki zuciyata, wacce take bugawa tare da k'aunarka. A k'arshe, ina so ka duba lamarin aminiyar da ta fad'a soyayyar mutumen da aminiyarta tafi k'auna fiye da kowa, fiye da komai. Girgiza kai ta fara yi, a karo guda ta kama murfin motan tana k'ok'arin ficewa. Hannunta Sadam ya kama, sannan ya danna central lock a motar. "Babu inda zaki je, sai kin sanar da ni matsayina, idan ba haka ba, zan hak'ura da soyayyarki, zan koma wurin da zan samu dukkan kulawa ba tare da nayi facing challenges daga mahaifin yarinyar da take so na ba." "Let go off my hand Sadam" "I won't Jay, babu inda zaki je." Kuka ta fasa mishi, tana kiciniyar k'wace hannunta, amma ya mata rik'on da baza ta ta6a iya su6uce masa ba. Idanuwanta da suka canja, suka koma tamkar famfo ta d'ago, dan kusan kullun cikin kuka take. "Na gwammaci in sadaukar maka da rayuwata, kan ace na wayi gari na ganka kana soyayya da wata, watan ma kuma Miemie, yarinyar da nake yi ma kallon 'yaruwata, wacce na sallamawa duk sirrina." Ta shafe hawayenta, ta juya tana kallonsa. "Miemie zata yi da-na-sanin sanina a rayuwarta, wallahi ka ji na rantse, a kaina zata daina eyeing samarin mutane." Wani sanyin farinciki ne ya dira zuciyar Sadam, hannunt ya sake, amma har yanzu k'ok'arin 6alla k'ofar take, gaba d'aya ta fita a hayyacinta. Fuskarta ya kama da hannayensa duk biyun, ya saita ta akan shi, kallon da ya fara aika mata, shi ya dawo da hankalinta jikinta ba tare da saninta ba. Girgiza mata kai ya fara yi, yana shafan gefen fuskarta "Everything will be alright. Okay?" "Okay, but I need to see Miemie now. Please Ka mayar da ni inda ka d'auko ni." "It's okay." Daga haka ya tada motar ya maida ita gaban Students Center, ko k'ala bata ce mashi ba, ta fito ta banka k'ofar ta wuce, zuciyarta sai azalzalarta take, tana jin zata iya shak'e wuyan Miemie ta mutu, in har da zata ci karo da ita a halin yanzu. A tsaye ta samu drivern jikin motar, sai raba ido yake yana tunanin ta ina zata 6ullo, tana isa ta bud'e baya ta shige, "Shiga muje, but ka fara biyawa ta layout akwai note book d'ina da zan ansa." Bayan ya shigo ya tada motar, yace "ranki shi dad'e amma kinsan Alhaji yace makaranta kawai zan kawo ki ko?" "Amma ai kaji abinda nace, littafi zan ansa, kuma ko shi yake tuk'a motar nace zan anshi littafina dole ya tsaya balle kuma kai, dan haka ka d'auki hanyar da na ce maka, tun banyi sanadiyyar aikinka ba."1 Bai ce komai ba, ya d'auki hanyar da take so, a k'ofar gidan suka yi parking, ta samu yaro ta tura ya yi mata kiranta. Da mamakinta ta fito, ganin Jay ce ta aika kiranta. Da fara'arta ta k'araso "Ke yau wane irin iskanci kike ji da baza ki shiga ba?" A fusace ta fito, gadan-gadan tayi kanta, ba tare da tace komai ba ta d'aga hannu ta falle ta da wani matsanancin marin da yayi baraza da ganinta na wucin gadi. "Munafuka, ma ci amana, to asirinki ya tonu, ashe dama haka kike? Ina nadamar saninki a rayuwata Miemie, kin bani kunya, banyi zaton kina cikin matan da basu san ciwon kansu ba. Bara kiji in gaya miki, Sadam ba ma ci amana ba ne, kuma sanin kanki ne, tsarinshi bai dace da kucaka iri irinki ba, and daga yau sai yau, kada ki k'ara gigin kallon numbersa ma, ballantana har ki tura mashi text, if not wallahi sai na miki rashin mutuncin da kare ma ba zai d'auka ba. Wawiya kawai." Ta juya zata koma cikin motar, amma Miemie ta finciko rigarta ta baya, take fad'a ya kacame tsakaninsu. Dak'yar da taimakon driver, da wasu 'yan tsiraran mutane aka samu aka raba su, kowannensu sai mayar da numfashi yake yi. Wata mata ce ta tura Jay cikin mota, wasu suka tura Miemie gida, a haka driver ya tada motar hankalinshi ya gama tashi, domin bai ta6a zaton Jay zata iya yin abinda ta yi ba. Tana shiga ta samu Baffa da Goggo tsaye, sunyi jungum-jungum. Bata bi ta kansu ba tasa kai zata wuce d'aki, Baffa ya tashi ya taka zuwa inda take "Ina wayar mutane da kika d'auka?" "Wace waya kuma? Ni ban d'auki wayar kowa ba." Ta kuma sa kai a karo na biyu, tana k'ok'arin shigewa. "Zaki bani ko sai jikinki ya fad'a miki?" Ganin bata da wata sauran dubara yasa tana tura baki, ta fitar da wayar ta wurga masa, ta juya zata koma ciki. K'afa yasa ya tokare ta, da zata fad'i da babu abinda zai hana hak'oranta zubewa. "Wato duk abinda nake fad'a miki a banza ko sai da kika je kika had'u da d'an iskan yaron nan ko Ummi?" Bai jira ansarta ba ya cafki kunnenta, suka fita harabar gidan yana k'wala kiran driver. Da sauri ya fito ya duk'a gabanshi. Cikin d'aga murya ya fara magana. "Ya muka yi da kai? Shine na baka amana kaje can ka saki baki ka barta tayi abinda ta ga dama ko?" "Wallahi ba haka bane Alhaji." "To ya ne? Ko kayi magana ko kuma ka tashi ka fita kar kuma ka k'ara dawo mun gida." Jin aikinsa na shirin salwanta yasa ya zayyana mishi abinda ya wakana, har fad'an da suka yi da Miemie, da maganganun da suka fad'a ma juna. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Tashi je ka abinka, ke kuma yau zaki san kin zubar mun da mutunci a idon duniya." Ya juya ya kama hannunta, tana tirjewa tana komai, amma haka ya shige ciki da ita. A d'aki ya jefa ta, sannan ya ciro charger wayarta ya fara dukanta inda ta fara ihu tana neman taimakon gaggawa. Da gudu Goggo ta fad'o d'akin, dak'yar da ji6in goshi ta k'wace ta, har ma tana da-na-sanin gaya masa 6atan wayar tata. "Daga yau babu ke babu fita makaranta, na soke ta har abada, zan kira Malam, in roki alfarmar ya bar ni in tura ki wata k'asa can kije kiyi karatun. Dan na lura idan ba kinyi nesa da gida ba, baza ki daina sa6a umarnina akan d'an banzan yaron nan ba." Cikin tsananin tashin hankali ta d'ago tana dubansa. "Wallahi ba zan je ba, babu inda zan je Baffa, sai dai idan gawata zaka d'auka ka kai wata k'asar." Da gudu ta mike ta shige toilet ta banko k'ofar, dan ta san idan ta shiga hannunsa, ba k'aramin jigatuwa zata yi ba. A wurin ta zauna ta cigaba da shan kukanta, har sai da ta tabbatar sun fita, sannan ta fito.10 This Jay😣😣😣 K'ofar d'akin ta rufe, sannan ta koma kan gado ta d'auko biro da takarda, ta fara rubutu. Ta gama, ta ninke ta ajje a saman dirowar gefen gadon, kafin ta tashi ta d'auki karamar jakarta ta matafiya, ta kwashe cosmetics d'inta, ta d'auki ATM da cash withdrawal slip ta saka a jakar. Duk wani abun da ta san zata bukata a kusa-kusa, sai da ta gama hada shi, sannan ta koma ta kwanta tana tunanin abinda take shirin yi shi ne kawai mafita daga rayuwar k'uncin da take ciki.16 ** K'arfe biyar na asuba agogon d'akin ta nuna lokacin da ta fito daga wanka, tana shirin tayar da sallah. Tun k'arfi Baffa ke knocking k'ofarta, duk da ba bacci take ba, amma ta kasa motsa koda d'an yatsan kafarta, kasancewar yau ce rana ta farko da ya ta6a knocking mata k'ofa a irin wannan lokacin. Dak'yar ta isa bakin k'ofar ta bud'e, tana kallon sa. "Ki tashi asuba tayi." Bata ansa shi ba, haka kawai ta gyara tsayuwarta ta tsinci kanta da son kallonsa, tausayinshi take jin yana ratsa ta duk a lokaci guda. "Baki ji me nace ba ne Ummi?" "Na tashi ai." Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya juya zai tafi, sai kuma ya dawo ya tsaya yana kallonta, daga bisani ya sanya kai zuwa d'akin Goggo. Tana jin lokacin da ya bud'a gate ya fita zuwa masallaci, ta tada sallar, a gurguje ta gama, ta zira bak'ar abayanta, ta yafa gyalen, ta d'auki jakarta ta gama k'are ma d'akin kallo, sannan janyo k'ofar ta fito. Cikin sand'a ta wuce d'akin Goggo ta lek'a a hankali ta sameta a sujada tana sallah, hawaye masu dumi, suka kwacw ma kwarmun idonta, tasa hannu ta toshe bakinta, sannan ta juya da sauri ta wuce harabar gidan. Ta hasken lantarkin da ya mamaye wurin ta hangi mai gadi ya kabbara sallah a cikin d'akinsa hakan ya bata damar sa kai ta fice cikin sauri-sauri, gudu-gudu, har sai da ta tabbatar ta bar unguwar gaba d'aya sannan ta fara tafiya a hankali, yayin da idanuwanta ke cigaba da zubar da hawaye, sai dai zuciyarta ta gama k'ek'ashewa, a tunaninta wannan ce kawai hanyar da zata sama ma kanta farincikin da take ganin kamar tayi bankwana da shi har abada.6 K'arfe bakwai na safe a k'ofar Zenith Bank ya mata, gefe kad'an ta tsaya, tana kallon yadda ma'aikatan wurin ke shigewa suna adana motocinsu, bata motsa ba har sai da taga motar Sadam ta iso, sannan tayi saurin k'arasawa ta shige gabansa. Parking yayi ya bud'e ya fito, ganinta ba k'aramin kadar masa da gaba yayi ba. "Jay?" Ya fad'a idanuwansa waje yana k'are mata kallo. Kai ta girgiza, "Ni ce Sadam. Sai dai bamu da wani isasshen lokacin da za muyi magana, we need to leave now." "Are you serious?" Ya tambaya lokacin da ya taka zuwa gabanta. "I'm Sadam." "I can't believe this." Ya fad'a yana wawwaigawa, tare da shafa tarin sumar da ke kansa. "Alright, yanzu ki shiga ki zauna a mota, cuz dama papers d'in nan kawai zanyi submitting in d'auki hanya." Ya bud'e mata k'ofar ta shiga, inda ya maida murfin ya rufe, ya juya da sauri ya wuce cikin bank d'in. Tana zama ta had'e kanta da gwiwa ta cigaba da rera kukan da ta kasa gane shin na bak'in ciki ne, ko ko na farin cikin zata kasance da masoyinta na har abada..? A haka ya fito ya sameta, bai ce komai ba ya zagaya ya shige motar ya tada. Suna gab da fita garin Katsina ya juya yana kallonta, har a lokacin bata daina kukan ba. Wani irin tausayinta ne ya tsirga zuciyarsa, har yana jin kamar bai yi mata adalci ba, amma idan ya tuna cewar wannan ce hanya d'aya da zai iya mallakarta, sai ya ga wannan d'in shine kawai adalcin da zasu iya yi ma junansu. "Jay" Ya kira sunanta da wata raunanniyar muryar da ta sa ta d'agowa a hankali ta sauke idanunta a kansa. "It's ok please, kinji, ki daina kukan nan mana." "Ba ni ke zuwar da shi ba Sadam. Haka kawai nake jin yana zuba a idanuna." "Ok, now ki share hawayenki, I'm here with you, bai kamata ace kina asaran hawayenki har yanzu ba. Ya kamata kiyi bankwana da bak'in ciki, ki sanya ma ranki cewar duk ko me zaki ci karo da shi zuwa gaba to abu ne na jin dad'i wanda zai faranta miki zuciya, saboda zamu samu cikar burinmu. I promise zan kula da ke, zan baki duk wani jin dad'i da kike buk'ata, zan so ki ke d'aya, ba tare da na had'a soyayyarki da ta kowa ba. Just trust me." Murmushi ta saki, tare da share hawayenta tace "Kawai ina tunanin halin da su Baffa zasu shiga idan suka ci karo da letter da na bar masu ne." Juyawa yayi ya cigaba da tuk'inshi, shiru na wasu 'yan mintina ya ratsa motar, in banda k'aran mugun gudun da yake rafsawa, ba'a jin komai, sai k'aran air condition d'in da ke ta faman busa masu iska a lokaci guda. Ajiyar zuciya ya sauke yana d'ora hannunsa a nata, amma idanunsa na kan titi ya fara magana. "Babe, kada kiyi blaming kanki akan abinda ba fault d'inki ba. Kinyi duk abinda ya dace, kin kuma yi biyayya ma Baffa, but son zuciya yasa ya kasa fahimtar abinda kike so. Ki manta da komai, ki fara tunanin sabuwar rayuwar da zamu fara, just me and you. Kinji?" Kai ta gyad'a mishi, murmushi kwance akan fuskarta, a lokaci guda wani farin ciki ya lullu6e ta, finally, zata kasance da mutumen da ta fi k'auna a duniyarta.5 **Katsina Ganin har sha d'ayan safe ta yi ba tare da Goggo ta ji d'uriyar 'yar tata ba yasa ta fito daga part d'in Baffa ta wuce d'akinta. Ganin k'ofar a rufe yasa ta murd'a handle d'in, ga mamakinta ta bud'e, a hankali ta tura kai tana kiran sunanta. "Ummi. Ba dai bacci kike har yanzu ba?" Tasa hannu ta yaye blanket d'in dake saman gadon, babu ita babu dalilinta, hakan yasa ta isa gaban toilet d'in dake cikin d'akin tana mai cigaba da kiranta, amma shiru, haka kuma babu k'aran ruwa balle tayi tunanin ko wanka take yi. K'ofar toilet d'in ta murd'a ta tura kanta kai tsaye, nan ta ci karo da komai ajje a wurinsa, kuma babu kowa a ciki. "Ina yarinyar nan ta shiga?" Ta tambayi kanta lokacin da ta fito da sauri ta koma part d'in Baffa. A kishingid'e yake yana kora ruwan Lipton d'in da ta gama had'a masa, yadda ta fad'o palon a gaggauce yasa ya tashi zaune "Lafiya?" "Alhaji yarinyar nan bata d'akinta fa." Tari ne ya sark'e Baffa, inda ya mik'e yana tambayar "ban fahimce ki ba?" "Wallahi bata nan, har toilet na duba amma ban ganta ba." "Kin jiki da wani zance, tana yiwuwa ko tana kitchen ai. Muje dai in gani da ido na." Tayi gaba yana binta a baya har d'akin, nan suka k'ara duddubawa, sai lokacin suka lura da ta kwashe gaba d'aya cosmetics d'in da suke saman miron ta. Kuka Goggo ta fasa tana tunanin ina Ummi ta shiga, hankalinsu bai ida tashi ba sai da Baffa ya tsinkayi doguwar takarda kan bedside drower ta, an rubuta BAFFA da manyan haruffa. Da sauri ya isa ya warci takardar ya fara karantawa cikin k'araji. BAFFA. Ina mai matukar baku hak'uri akan rashin bin umarninku Baffana, na za6i in cigaba da rayuwa da masoyina kan na zauna cikin halin bak'in cikin da kake jefa ni a ko da yaushe. Kamar yadda ka bani za6i, na za6i in k'aurace ma gidana, jahata, in koma wata duniya ta daban domin in samu cikar burina. A k'arshe Ina k'ara baku hak'uri, bana kuma son ku bama kanku wahala wurin nema na, domin watak'ila lokacin da zaku ci karo da letter ta, na dad'e da kaiwa inda na dosa. Ina sonku iyayena.9 Wata muguwar karkarwa hannun Baffa ya fara yi, juyawar da zaiyi ya ji zuciyarsa ta buga da k'arfi, a karo guda ya fad'i k'asa babu numfashi.12 (30th Jan, 2012) ***Maiduguri. Misalin k'arfe biyar na yamma suka shigo garin, tafiyar da ta d'auke su awa tara da minti Hamsin da takwas (9hrs:58mins) wacce tayi dai-dai da kilomita d'ari bakwai da sittin da d'aya (761-KM). Kallonta yayi la66ansa d'auke da murmushi, "here we're darling. Me ya kamata mu fara yi?" Murmushin ta saki itama, duk da weather garin bai yi mata yadda take so ba, amma hakan bai hana ta jin dad'i ba. Hannunta ta k'ank'ame a k'irjinta, ta lumshe idanunta ta bud'e tana mai sauke su a kan Sadam masoyinta. "Abinci ya kamata mu fara nema sai muyi sallah, then sai mu san abinda ya dace." "Idan haka ne, gara kawai mu samu hotel d'in da yafi kusa muyi lodging, kafin zuwa gobe muga abinda za'ayi. Ya kike gani?" Girarta ta d'aga sama tare da girgiza kanta, daga bisani ta jinjina babban yatsanta tana cewa "That's very good." Murmushi yayi, a karo guda ya cire wayarsa yayi googling hotel mafi kusa da inda suke, haka aka jero mashi su da yawa, daga k'arshe suka yanke shawarar zuwa Barwee Hotel dake kan titin Kazeem Ibrahim, yana kallon Maiduguri International Airport. Bayan sun isa ya barta a motan, ya fita yayi komai, ya ansar masu key d'in d'akin, sannan ya dawo suka shiga a tare. Wannan itace ranarta ta farko da ta ta6a shiga hotel a duniya, hakan yasa ta dinga sinne kai, tana duk'ar da fuskarta, har suka kai d'akin da zasu sauka. Suna isa ya bud'e mata ta shiga, shi kuma ya koma domin ya samo musu abinci. Tana shiga d'akin ta kwanta rigingine tana kallon ceiling d'in d'akin, a gefe guda kuma sanyin A.C na busa ta, babu abinda ya zo zuciyarta sai gidansu, ta tuna d'akinta, take hawaye suka yayyafo mata, amma ta dake zuciyarta ta mik'e ta fad'a toilet ta d'oro alwala. Tana cikin sallah ya shigo ya ajje abincin shima yayi alwala ya kabbara tashi sallar, bayan sun gama ta juya tana kallonshi, a tunaninta zai d'auki abincin ya koma wani d'akin ne, sai dai taga ya gyara zama tare da janyo abincin, yana cewa "Come and join me." "Ehnn.. Ban gane ba?" "Yh, kizo kici abinci." "Ka je d'akinka, idan na tashi zan ci." "Babe..?" Ya zaro ido yana kallonta. "Wane d'aki zan je in bar matata a nan?" Narkar da fuska tayi, "Amma ya za ayi mu zauna d'aki d'aya? Ba'a riga an d'aura auren ba fa." "To me ke da saura? Gobe ne fa ko jibi. Please come down, bana son yunwa ya illata min ke." "But Sadam.." Bata k'arasa ba ya katseta. "Nothing gonna happen, I promise you ba zan yi abinda zai hurting d'inki ba, so feel free." Kuka ta saka mishi, dole ba dan ya so ba ya sauka ya k'ara booking wani d'akin, ya dawo ya d'auki jakarshi ya fita ko k'ala bai ce mata ba. Binshi tayi har bakin k'ofa tana mishi magana amma ya bonsa ta, ya wuce ya barta a nan. Yunwar da ke azalzalarta ne yasa ta zauna ta fara cin abincin, duk da wani abu da take ji a k'asar zuciyarta, amma haka ta dake, ta daure tana k'ok'arin yakice abinda ke neman daburta jin dad'inta.6 Tana gamawa ta fita zuwa d'akin da yake ta fara knocking k'ofar, amma fur Sadam bai kula ta ba, ya juya ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai san Allah yayi ajiyarta ba. "I'm sorry Kazaure" Ta fad'a da muryar kuka, lokacin da ta tura kanta daf da k'ofar d'akin ta cigaba da knocking a hankali. Ajiyar zuciya ya saki tare da ajje spoon d'in hannunsa ya iso bakin k'ofar ya bud'e, yasa hannu ya warci hannunta suka shige ciki, sannan ya maida k'ofar ya rufe ya zaunar da ita a bakin gado. Gabanta ya duk'a, gwiwoyinsa a k'asa ya d'ora hannuwansa akan k'afarsa. "Jay kina wahalar da zuciya da gangar jikina. Kina gwada mun bani da iko da ke da abinda kika mallaka ko? What's there dan munyi squatting a d'aki guda? Me kike tunanin zanyi miki wanda ban miki tun farko ba? And idan ma wani abu ne ai ni dai zan aure ki ko? To meye a ciki? Bayan kuma ma na fad'a miki ba abinda zan miki, amma kin tsaya kina wani 6ata rai kaman ba kina tare da Kazaurenki ba." "Ba haka ne ba fa, I'm sorry ni dai, kaga shaid'an ake gudu, kuma fa ba nace bazan zauna da kai ba, zan zauna a nan har lokacin da zanyi bacci sai na koma d'aki ka ji?" "Zaki zauna ke d'aya, ni kam da na gama zan tafiyata yawo na." "Mu je tare dai, cuz akwai abubuwan da nake da buk'ata." "Zaki sani." Ya fad'a lokacin da ya koma ya cigaba da cin abincinsa.2 *Katsina Salati Goggo ta d'auka yayin da kukanta ya tsananta, da sauri ta isa inda Baffa ya fad'i ta fara jijjiga shi, amma bai dawo hayyacinsa ba, gorar ruwa ta ciro daga d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ta yayyafa masa, har yanzu bai farfad'o ba, hakan yasa ta fita da sauri ta kira driver, ya kama suka sanya shi a mota suka wuce asibiti. Bayan an shiga dashi, tana tsaye a wurin sai kaiwa-da-kawowa ta ke yi, zuciyarta na azabtar da ita, tana tunanin wannan wace irin k'addara ce ta fad'a ma iyalinta. Kuka ta cigaba da yi, tare da addu'ar neman mafita a wurin Allah, har zuwa lokacin da aka fito da Baffa. Alhamdulillah an samu numfashinsa ya dawo, sai dai yana buk'atar hutu, hakan yasa suka tura shi zuwa amenity domin ya samu daidaituwar zuciyarsa. Da sunan Ummi ya farka a bakinsa, da sauri Goggo ta isa ta kama hannunsa. "Kayi hak'uri Alhaji, amma Ummi ta mana nisan da bamu san inda ta nufa ba." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Wato da gaske ne, ba mafarki nije ba? Anya kuwa Ummi jinina ce? Wannan wata irin k'addara ce?" Baffa ya fad'a, a karo guda ya nemi ta taimaka mashi ya mik'e, ya kalle ta hawaye na bin fuskarsa tamkar d'an k'aramin yaro, hakan ya tabbatar ma Goggo ba k'aramin so Baffa ke yi ma 'yar tashi ba, a hankali ta fara shafe masa hawayen tana lallashinsa, sai ya zamana kamar tana tunzura zuciyarsa ne. "Yanzu menene abin yi Alhaji?" Shiru yayi bai ansa ta ba, daga bisani ya shafe fuskarsa. "Babu wani abin yi, illa mu fawwalawa Allah lamarinmu, shine kawai zai iya yi mana magani. Ni kuwa matsawar nine mahaifin Ummi, to na yafe ta har abada, duniya da lahira. Na k'udurce ma zuciyata cewar ban ta6a haihuwa a doron k'asa ba. Dan haka ko bayan raina, bani da wata d'iya mai suna Ummi. Ita kuma ba dai duniya ta za6a ba, taje ta ishe ta riga da zani har da mayafi." Kuka Goggo ta saka tana bashi hak'uri, amma ina zuciyar Baffa ta riga tayi nisa, inda ya sanya gingimemen dutse ya danne soyayyar 'yar tashi da take barazana da numfashin da yake shak'a.6 Baffa Noo please 😣😢***Maiduguri. Misalin k'arfe bakwai na safe ya fito jikinshi sanye da 3quater da armless d'in riga na kayan sport da aka rubuta 53 a gaba da bayan rigar ya wuce gym d'in dake cikin hotel d'in domin ya motsa jinin jikinsa. Wasan basketball ya samu wasu suna bugawa, nan ya shiga cikinsu aka cigaba da yi tare da shi, wanda a k'alla ya d'auke su kusan mintina arba'in, sannan suka samu damar tsagaitawa tare da zaunawa a bencinan da aka jera a wurin. Gorar ruwan da ke gefenshi ya d'auka ya sha, sauran ya juye a jikinsa, sannu a hankali yake k'are ma mutanen wurin kallo, daga bisani ya juya tare da mik'a ma mutumen da ke gefenshi hannu. "Yau kam naga wanda ya fini k'aunar basketball." Dariya mutumen yayi tare da mik'a masa hannunsa yana cewa "It's my fav sport, in fact ban iya ko wanne irin wasa idan ba shi ba." "I see." Cewar Sadam yana girgiza kansa. "By the way, I'm Sadam Kazaure."3 "Faisal Goni." Ya fada bayan sun mike tsaye. A tare suka fito suna takawa da niyyar wucewa d'akunansu, Faisal ke tambayar Sadam abinda ya zo da shi garin na Maiduguri. "Aiki ya kawo ni. And you?" "Ni kam gari na ne, nan aka haife ni." "But mai ya kawo ka nan? Though nasan ba hurumina ba ne." Yayi maganar tare da 'yar dariya. "Eh to, amma dai ka share. Abin sirrine." "Na so?" "Eh mana. Ko aikin jarida kake ne?" A tare suka sa dariya, "No fa." Ya d'an juya yana kallonsa, "Ernmmm.. Idan baza ka damu ba zan so inyi maka wata 'yar tambaya please." "No problem, ina sauraren ka." Suka koma gefe suka d'an tsagaita da tafiyar, inda Faisal ya mik'a hankalinsa ga abinda Sadam zai fad'a. "Dan Allah ko zaka iya kwatanta mun wani babban masallaci inda ka san zan samu wani babban Malami haka, ina da issues ne da nake son warwarewa." Jinjina kai yayi, yana nazarin maganar tasa, daga bisani ya sauke idonsa akan shi. "Sure, akwai malamai da na sani da dama, sai dai idan babu matsala ina son sanin kad'an daga cikin abinda ke tafe da kai." "Ka gane ko." Sai kuma yayi shiru. "Ehenn, ina saurarenka." "Ka gane, a yanzu haka maganar da nake yi maka, ina tare da yarinyar da nake son in aura, iyayenta sun rasu, sai k'anin mahaifinta, wanda yake takura mata sosai, at first naje gidansu ina son aurenta, but yayi denying, yace dole sai ta auri wani wanda bata son shi, so shine muka yanke shawarar muzo nan muyi aurenmu, daga baya sai mu koma gida." Shiru Faisal yayi, yana tunanin dalilin da yasa ake samun yawaitar irin wad'annan matsalolin. Daga k'arshe ya dafa Kafad'ar Sadam, "Kada ka samu damuwa, I'll help you, I'll take you to my grandfather, babban Malami ne, idan munje sai ka yi mishi bayanin matsalarka, shi kuma zai baka shawarar abinda ya dace." "Kai, nagode gaskiya, naji dad'i sosai. Yaushe kake ganin ya dace mu je?" "Barin baka number na, idan ka shirya sai ka yi mun magana, I'm always free." "Thank You, thank you Mr. Goni. It's very nice meeting you." "My pleasure." Ya sanya mishi number, ya mik'a masa wayar, suka k'ara yin musabaha, sannan kowa ya zarce masaukinsa. D'akin ya wuce, ya yi wanka sannan ya sauka ya samo masu abinci, ya dawo.2 A hankali ya fara kiran sunanta yana tsaye bakin k'ofar d'akinta, bata ansa ba sai dai ta taso ta bud'e k'ofar, ta juya da sauri ta koma ciki. Shigowa yayi shima, ya ajje kayan hannunsa yayi kanta yana tambayar "How was your night?" Shirun da ya ji bata ansa shi ba, ta kifa kai sai kuka take, yasa a hankali ya zauna bakin gadon "Ya kike so inyi ne? Da me kike so inji? Da kukanki ko da abinda ke gabanmu? Babe dan Allah ki daina kukan nan, ya kamata ki gane yanzu wata sabuwar rayuwa zamu shiga, I'm sorry dear, tashi ki ci abinci kinji." "Ina jin kamar ban yi ma Baffa adalci bane Sadam, guiltness ya hana zuciyata sakewa, duk kuwa yadda naso in yakice abinda nake ji. Ina tsoron kada son zuciyata ya kai Baffana ga kamuwa da wata larurar."11 "Oh God! Babe wannan duk wani imaginations ne, ki basar, ki manta komai, ni zan shayar dake jindad'i da farincikin da baki ta6a experiencing irinsa ba. Please tashi kiji, akwai surprise d'in da nazo miki da."6 Mik'ewa tayi, a haka yasa mata abincin, ya hau har saman gadon ya mik'a mata, kalamanshi masu matuk'ar tasiri a zuciyarta yake fad'i mata, cikin d'an k'aramin lokaci ya tafiyar da bak'incikin da take ciki. Bayan sun gama, ya sanar da ita yadda suka yi da Faisal.2 "Kinga ko munje wurin kakansa abinda zamu fad'a masa kenan, dan kada muyi baki biyu." "Amma me sa zamu ce k'anin Babana ne? Me zai hana mu fad'i gaskiya kawai." "No babe, just listen to me, ki bi abinda nace miki kawai. Kina ji ko 'yan matana." Murmushi tayi, wanda iyakarshi la66anta, "Your wish is my command." "That's my boo. Now ki zama ready, 4:30pm zamu je."2 Haka suka cigaba da firar yadda abubuwan zasu kasance, daga k'arshe suka mik'e suka fita wurin swimming pool d'in dake bayan d'akunansu. *04:50 (PM) "Babe, fito mana, muna 6ata lokaci fa." "I'm here, mu tafi kuma, ka wani tsaya kana kallona." "To ba dole ba, wannan irin kyau da kika yi." Jujjuyawa tayi, "ina wani kyau a nan, kana gani ina fama da bak'ar riga kaman 'yar coci." Dariya ya saki, tare da takawa gabanta, idanuwansa dake rikirkitata ya zuba mata, cikin wata sassanyar murya ya fara magana. "To me, U're not like those people. U're someone very special, very dear to my heart. U're one of a kind. And everything about you is way too different from others. U're unique, and difficult to find. Cuz people like you, are very rare darling. You look marvelous. Okay?" K'asa tayi da idanunta, har cikin zuciyarta, tana son yadda Kazaure ke kambata, hakan ke k'ara mata so da k'aunarshi a kowanne lokaci. Girgiza kai tayi, muryanta ciki-ciki tace "Okay." "That's my Angel, and kada ki k'ara had'a kanki da 'yan church daga yau, kinji." Suka fito, suka shige mota, Faisal na gaba suna binshi a baya, suka doshi Bumsa Road da ke cikin unguwar Bolori, Borno, Maiduguri. Gaban wani babban gida Faisal yayi parking, haka suma suka gyara nasu parking d'in duk suka fito, ya shige gaba suna binsa a baya har zuwa cikin gidan. Daga gefen gidan, k'aton masallacin juma'a ne, wanda ya mamaye kusan rabin layin gaba d'aya. Kana shiga gidan, zaka tar da wani part a farkon gidan, inda Faisal ya shigar da su. Yawan tarin littattafan addini da suka gani, shi ya basu tabbacin part d'in Mal. Goni kakan Faisal ne. Da sallama dogo, bak'in dattijon ya fito, jikinsa sanye da alkyabba wacce malaman da suka sha karatu suka k'oshi suka fiya amfani da ita, kansa kuma rawani ne na farin zabuni, shima dai rik'ak'k'un malamai ne kawai suka san sirrin yadda suke nad'a shi. Bayan sun gaisa da shi cikin mutuntawa da karamci, Faisal ya yi mishi bayanin abinda ke tafe da su, inda ya ja gefe, yayin da Sadam ya cigaba da d'ora k'arya da gaskiya wa Mal. Goni. Girgiza kai yayi, a karo guda ya sauke idanunsa kan Jay, yayin da zuciya da fuskarsa, suka bayyanar da tausayinta cikin d'an k'ank'anin lokaci. "Faisal." "Na'am Malam." "Ku d'an bani wuri, zanyi magana da wannan baiwar Allahn." "To shikenan." Da haka suka mik'e suka fita, shi kuma ya maida hankalinsa gare ta. "Menene sunanki yarinya?" "Jameela." "Shin labarin nan da suka zo dashi kin tabbatar gaskiyarshi kenan?" "Eh haka ne Malam." "Masha Allah, amma Jameela, me sa baki hak'ura kinyi biyayya ma kawunki ba? Ko mutumen da ya so had'a ki dashi yana da wasu munanan dabi'u da addinin musulunci yayi turr da su?" Shiru tayi, da kanta a k'asa, kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta d'ago "Bana son shi ne Malam, kuma na kai wanda nake so amma sun k'i su aura mun shi, ni kuma gudun fad'awa tarkon shaid'an, yasa muka yanke shawarar mu gudu muyi aurenmu, daga baya sai mu koma gida, lokacin komai ya zama tarihi." "Shikenan tunda haka kika fad'a, na fahimci uzurinki, sai dai abinda nake son ki gane shine, komai na duniya da albarkar iyaye ya fi riba, amma tunda kinje musu da batunki, basu kalle shi ba, ni zan d'aura muku aure gudun fad'awa wata hanyar, kamar yadda kika fad'a, sai dai ina rok'onki alfarma, da shekara ta zagayo, ku tattara ku koma gida domin ku samu albarkar mahaifanku." "To shikenan Malam. In Sha Allah." Jay ta fad'a, duk da maganar iyakarta fatar bakinta, domin a yanzu babu burin da ya rage mata, irin taga an d'aura aurensu da Kazaurenta Bayan Malam yasa Jay tayi kiransu kowa ya dawo ya zauna, yayi gyaran murya, tare da kai dubansa ga Sadam "Nayi magana da Jameela, ta kuma bani k'arin haske akan lamarinku. Abinda nake so shine, ka barta a nan ta kwana, kai ka koma masaukinku, gobe idan Allah Ya kaimu ka taho da sadakinka, ni zan d'aura aurenku bayan mun gama sallar juma'ah." Wani irin farinciki ne ya bayyana a fuskar Sadam, godiya yai ta zuba ma Malam, lokacin da ya juya yana kallon Jay, itama murmushin ne kwance akan kyakkyawar fuskarta. Sai dai duk da jin dad'in da take na zata samu cikar burinta, hakan bai hana wani fanni na zuciyarta azabtar da ita ba, haka nan dai take daurewa, tana tursasa zuciyarta, tare da danne abin a duk lokacin da ya bijiro mata. Mik'ewa Malam yayi, ya gyara zaman alkyabbarsa, "Idan kun gama, ki shiga daga ciki, zan yi ma mutanen gidan bayaninki." Daga haka ya wuce, Faisal ya rufa mishi baya aka barsu daga ita sai shi a cikin palon. Cikin zak'uwa ya fara magana, "Kinga abinda nake fad'a miki ko? Gashi komai ma yazo mana da sauk'i" Murmushi kawai tayi, shi kuma ya cigaba. "Da na fita daga nan, first abinda zanyi shine neman gidan da zamu zauna, zan sama mana wuri mai kyau, irin wanda kike so babe girl." Har yanzu dai bata ce dashi k'ala ba, shi kawai yake ta surutunshi, hakan yasa ya taso daga inda yake ya dawo daf da ita, yasa hannu ya d'ago kanta dake duk'e. "What...? Haba babe, wato baza ki daina kukan nan ba ko? Wai jira ma, ko dai har kin gaji da ni tun ba'a je ko ina ba?" Kai ta girgiza, hawaye na kwarara a idonta. "Then what? I thought this is what we both want, babe menene abin kukan?" Share hawayen tayi, ta d'ago tana kallonsa. "Sure, this is what we want, but na kasa yafe ma kaina gagarumin laifin da na yi, ina jina tamkar wacce tayi kisan kai wallahi, na kasa samun natsuwar zuciyata." Hannunta ya rik'e, a hankali ya fara magana. "Babe stop blaming yourself please. Ki tuna this is the only right we've, ya kamata muyi amfani da opportunity d'in da muka samu, one day zamu koma gida, nd trust me, Baffa zai fahimci kuskuren da yayi. Haba amaryan Kazaure, gobe kaman haka fa mun zama married couple. Kina so a kai mun ke da kumburarran fuska ne?"3 Girgiza mashi kai tayi, "A'a mana." "Then stop this crying, ki sama ranki kamar bamu ta6a barin gida ba, kisa a ranki kamar dama can nan ne duniyar da muka fara shimfid'a rayuwarmu. Okay?" "Okay." "That's my bae, now smile for me." Ya fad'a cikin wata irin muryar da ta sa ta k'yalk'yalewa da dariya ba tare da ta shirya ba. "Haba ko ke fa, amma kin sa heart d'ina yana boiling, kinsan idan kina kuka har wani extra motsi zuciyana yake yi." "Sweet mouth nko" "No be sweet mouth babe, kinsan ina bala'in sonki." Dariya tayi sosai, "Ai nima ina mutuwar sonka." "I know that babe girl, ba sai kin 6ata bakinki ba." Kiran sallar maghriba da aka kwad'a a babban masallacin da ke gefen gidan shi ya katse su, a gurguje Sadam yayi mata sallama, ya fito, suka had'u da Malam da Faisal suka yi alwala suka wuce masallaci.2 Faisal ne ya taimaka masa zuwa wurin wani agent na gidaje, cikin ikon Allah kuma aka dace. Gida ne irin compound, mai part-part a ciki sun kai guda goma, sai dai kowa da gate d'inshi, ta yiwu ma har ku gama rayuwarku wani bai san wani ba. Gidan ba laifi self-contained ne, mai d'auke da d'akunan kwana guda biyu, kowanne da toilet a ciki, sai kitchen, da madaidaicin palo, dai-dai ango da amarya. Ba'a samu matsala ba Sadam ya biya kud'i, aka bashi makullan gida, daga nan ya zarce hotel, zuciyarsa cike da tunanin yadda za'a yi ya samu kud'ad'en da zai sayi kayan da za su saka a cikin gida.2 'Dole ya nemi inda zai buga caca da sauran kud'in da suka rage mishi, idan akayi sa'a, zai iya samun abinda ya ninka su, har ya samu biyan buk'atarsa.'4 Shawarar da ya yanke kenan, hakan yasa bayan ya isa hotel yayi sallar isha'i, ya fito, a restaurent d'in wurin ya ci abinci, sannan ya wuce bar (mashaya) dake cikin hotel d'in, watak'ila yayi dace da abinda yake nema. Cikin sa'a ya ci karo da dandazon mutane akan wani faffad'an teburi. Abinda idanunsa suka hango masa ne yasa annurin fuskarsa k'ara bayyana, ya zarce gaban manajan wurin yasa aka kawo masa kwalbar barasa, ya d'aga ta sama, ya sha kamar rabi, sannan ya cire kud'i ya d'ora, ya zarce teburin da ake buga cacar. Mutanen da ya samu a wurin, wasu irin hatsabibai ne da suka fishi sanin daraja da mutuncin caca, dan haka ba'a d'auki dogon lokaci ba suka tatike gaba d'aya abinda ke aljihunsa. Kuka ne kawai Sadam bai yi ba saboda bak'in ciki, wannan wace irin rana ce? Mamakin kansa yake anya shi d'in ne kuwa? Ta wani 6angaren kuma yana mamakin k'wazo irin na mutanen da suka yi wuju-wuju da hazik'in d'an caca irin Kazaure. Cikin zafin zuciya ya ida kwakwad'e sauran barasarsa ya fito yana wasu irin surutai, ya koma d'akinsa.2 (Friday, 01 Feb, 2012.) Masallacin ya cika sosai yayin da Sheikh Mal. Goni yake gabatar da hud'uba mai ratsa zuciya, wacce gaba d'aya ta ta'allak'a ne akan hak'k'in da 'ya'ya suke da shi akan iyayensu. Yayi hud'uba mai zafi, wacce da yawa mutanen da suke wurin sai da suka zubar da k'walla, daga bisani aka tada sallah aka gama, kafin ya bukaci awwalin Sadam wato Faisal ya matso, shi kuma ya zama na Jameela, jama'ar wurin suka shaida aurensu, akan sadaki nera dubu talatin cif-cif, wanda sai da Sadam ya siyar da agogunanshi guda biyu, sannan ya samu kud'in.2 Bayan sun koma cikin gidan Mal. Goni yayi musu kyakkyawar nasihar data ratsa zukatansu, ya kuma k'ara rok'on alfarmar da zaran sun cika shekara, su tattara su koma mahaifarsu, domin kuwa albarkar iyaye ce kawai, zata sa su samu biyan buk'atar komai a cikin rayuwar auren nasu. Sallama suka yi musu, tare da godiya, sannan suka fito suka shige mota, fuskokinsu d'auke da jin dad'in cikar burinsu da suka samu. Bayan sun hau titi sosai, Jay ta kalle shi, amma sam hankalinsa baya wurin da alama ya shiga tunani mai zurfi. "Me ke damunka?" Ta tambaya tana ta6a kafad'arsa. Firgit ya juyo yana kallon ta, kamar zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru ya cigaba da tuk'inshi.2 "Sadam! What's your problem? You seems not happy at all. Menene?" Hannunshi ya d'ora akan nata, hankalinshi na kan titi ya fara magana. "Ina tunanin abubuwan da zamu zuba a gida ne, cuz gaba d'aya kud'in hannuna sun k'are, and hotel ma dak'yar na samu na k'arasa biyan kud'insu, ina jin haushin kaina that I can't provide all your needs, I'm sorry Angel, in sha Allah everything will be just fine. Kinji."1 Dariya ma ya bata, a gefe guda kuma ta ji ta d'an tausaya mishi, hakan yasa ta bud'a jakarta, ta ciro ATM card d'inta, ta d'aga mishi. "We'll buy all we want with this. I've enough money, so have no worries, yau ranan farin cikinmu ce." A kaikaice ya juya yana kallonta, "are you serious?" "Very, so ka d'auki hanyar da zamu samu bank, idan muka cire kud'in sai mu wuce kasuwa." ***Katsina. Sannu a hankali yake takawa tare da taimakon Goggo da ta kama hannunsa zuwa cikin gidan. "Sannu Alhaji." "Yawwa. Taimaka mun da wayar can dake k'ara da Allah." Ba tare da tace komai ba, ta juya domin d'auko wayarsa da ke neman agaji wacce ya bari a cikin mota. Shi kuma ya k'arasa shiga ciki ya zauna a d'aya daga kujerun da ke girke a palon. "Ga shi na d'aga, Malam ne yana kan layi." Ansa yayi ya kara wayar a kunnensa. "Assalamu alaikum. Barka da Juma'ah Malam." "Wa alaikumus Salam. Barka dai Kabiru, ya k'arfin jikin?" "Alhamdulillah, gamu nan ma yanzu muka dawo daga asibitin." "Ahh, to madalla, ai na kira wayar Ummi d'azu da na kira ka baka d'aga ba sai na ji ta a rufe, ina ta tunanin ko jikin naka ne yayi tsanani." "A'a da sauk'i ma kam. Alhamdulillah." "Haka ake so ai. Ina ita Ummin take ne?" Shiru Baffa yayi, yana tunanin abinda zai fad'a mashi, can ya tsinkayi muryarsa. "Kana ji na kuwa? Ba ni ita inyi magana da ita." "Malam Ummi bata nan."+ "Ina ta je ne? Taimaka ka had'a ni da ita, akwai maganar da zanyi da ita." Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma zuciyarsa ta fara bugawa da sauri-sauri, yasa hannu ya dafe wurin, tare da cije la66ansa na k'asa, da alama yana jin jiki ba kad'an ba. Ganin haka yasa Goggo tayi saurin anshe wayar ta d'ora a kunnenta, ta gaishe da Mal. Baban. "Maryama ba dai jikin nashi ne ya motsa ba?" "Shi ne fa wallahi Malam." "Subhanallah. Kinga, kula da shi, bani Ummi inyi magana da ita, nima ina nan na shirya driver kawai nake jira mu taho."2 Kuka Goggo ta fashe da shi, hawaye na tsiyaya a idanunta, ta labartawa Mal. Baba abinda ke faruwa. Salati kawai ya d'auka, tare da kashe wayar, ita kuma ta duk'e a wurin ta cigaba da gunjin kuka. Kallonta Baffa yayi kamar ba zai ce komai ba, ya daure yace "haba Maryama. Menene zaki tsaya kina asarar hawayenki ga 'yar da bata damu da farinciki ko bak'incikinki ba? Tun wuri gara ki mance da kin ta6a haihuwar wata mai suna Ummi, in ba haka ba kina gab da kamuwa da ciwon zuciya kamar yadda na kamu da shi." Bai jira ansarta ba ya mik'e ya wuce part d'insa, yana shiga ya maida k'ofar ya rufe 0 da makulli, ya duk'e a wurin yana wani irin kuka marar sauti sai wasu zafafan hawayen da suke kwarara a saman dattijuwar fuskarsa. K'auna da son ganin fuskar 'yar tasa suka bijiro masa, duk kuwa da fushin da yake da ita, amma hakan bai hana zuciyarsa shiga tararrabin halin k'uncin da 'yarsa zata kasance ba tare da mataimaki ba, domin kuwa yana da yak'inin cewar Sadam ba soyayyar gaskiya yake yi mata ba. Wayoyinta da ya k'wace ya tashi ya d'auko ya kunna, kyakkyawar fuskarta ce ta bayyana lokaci guda akan tangamemen screen d'in da ke shimfid'e jikin wayar. Fuskarta ya fara shafawa, tare da tunanin yadda rayuwa zata kasance ma 'yar yarinya kamar ta, ba tare da iyaye ba. Text message d'in da ya shigo wayar ne ya katse mashi tunani, a karo guda ya sa hannu ya bud'e ya fara dubawa. Withdrawal alert ne daga ZenithBank suka dinga shigowa sun kai guda biyar, a na k'arshen ya tsaida idanunsa inda yaga an cire kud'in ne a First Bank dake kan titin Sir K. Ibrahim, Borno, Maiduguri Branch.3 "Maiduguri Ummi?" Yayi maganar cikin d'aga murya, zuciyarsa dake bugawa fat-fat, itace ta hana shi k'arasa fad'ar abinda ya so fad'a, ya saki wayar ya mik'e da sauri domin d'aukar maganinsa. **Maiduguri. Komai da zasu buk'ata, babu abinda basu siyo ba. Haka suka dawo suka fara shirya gidan, da taimakon masu babbar motar da suka d'auko masu kaya. Basu samu kansu ba sai wurin k'arfe taran dare, duk da haka ma ba komai suka gama ba. Girki ne abu na k'arshe da suka yi, sannan suka wuce wanka. Jay ce ta fara fitowa, ta bincika kayan da suka siyo ta fito masu da wasu kyawawan couple's pjs nata pink masu vest da bumshort, nashi kuma blue masu 3quatern wando da armless d'in riga. Lokacin da ya fito ta gama had'ewa, kallonta yake kamar yau ne rana ta farko da ya fara ganinta, kasancewar yau d'in ce rana ta farko da ya ta6a ganinta a irin wannan shigar. Zuciyarsa ce ta buga da k'arfi, alal hak'ika yarinyar tana da abubuwan da ba kowacce mace ce ke da su ba. Ashe da ya rasa ta ba k'aramar asara zaiyi ba a rayuwa. Abinda ya dinga sak'awa a k'asar zuciyarsa kenan. A hankali ya fara takawa zuwa gabanta, k'ugunshi d'aure da towel, hannuwansa sun k'ara bud'awa, haka faffad'an k'irjinsa ya k'ara masa kwarjini, ba kamar yadda d'igo-d'igon ruwa yayi ma kyakkyawar fatar jikinshi ado. Ganin yadda ya tsaya ya k'ura ma halittarta ido yasa tayi saurin wartan abayan dake gefenta tana k'ok'arin d'orawa a saman kayan jikinta. Murmushi ya saki ta gefen kumatunsa, ya k'arasa inda take, yasa hannu ya fincike abayan. "Me kike 6oyewa?" "Dan Allah ka bani Sadam, kaga dai ba kyau ai."1 Dariya yayi sosai, hadda buga k'afa. "Ba kyau? Indeed." "Eh mana ai ka sani. Ka bani please." Gefen fuskarta ya shafa, ya saita idanunsa cikin nata, yana yi mata wani kallo na goggun 'yan duniya. "That was then Babe. Its now officially, Mr.&Mrs. Sadam Baffa Kazaure. So feel free, and have no worries. Okay?" Ya k'arasa maganar da wani makirin murmushi a saman la66ansa, ya d'age girarsa, yana cigaba da aika mata wani mayunwacin kallon da yasa dole tayi k'asa da kanta, kafin ya wuce gaban mirror ya fara taje sumarsa. Tsaye tayi ta kasa motsa ko d'an yatsan kafarta, a zuciyarta tana ayyana cewar a kullu yaumun al'amurran Kazaure na kasheta, tare da sanyata ta mance duniyar da take ciki. Yana lura da yanayinta, hakan ya bashi damar matsawa kusa da ita, yana k'ok'arin cire towel d'in jikinsa domin sanya kayan da ta ciro masa. Da sauri ta juya ta fita, shi kuma ya saki dariya mai sauti, ya cigaba da abinda yake yi. Kitchen ta wuce ta fito da warmers d'in abincin da suka yi, ta jera a tsakiyar palon, ta koma ta d'auko plates da spoons ta fito da su a hannunta, a dai-dai lokacin ya fito, yayi saurin isa wurin yasa hannu ya anshe daga hannunta. "Kai. Wane ni in bar amarya da wannan aikin. Me sa kika ba kanki wahala haka? Wannan ai duk aikin ango ne."1 "Hmmmm, ashe ma aikinka. Kai da ko ruwan zafi baka iya had'awa ba kana nan kana wani cika baki, wai aikinka." "Yes durl, it's my duty. Now, bani plates d'in nan kiga yadda zanyi serving d'inki." Bata ce komai ba ta mik'a masa, ya juya ta biyo bayanshi suka dawo tsakiyar palon. Shi yayi serving dinsu a wahalce, dan bai iya komai ba. Suna cin abincin yana yi mata labaru masu dad'i, cikin farin ciki da jin dad'i suka yi suka gama, babu wata sauran damuwa a zuciyarta, ta san ta 6angaren Sadam bata da wata matsala, haka kuma bata tunanin akwai wani lokaci da zai zo wanda zasu samu matsala da junansu. Bayan sun gama cin abincin ma shi ya gyara wurin ya kwashe kwanukan, ya kuma taimaka mata suka wanke su, sannan suka wuce d'aki. Toilet ta shiga tayi brush, ta fito amma bata ganshi ba, hakan ya bata damar k'ara gyara gadon, tare da kashe fitila ta koma ta kwanta. Shigowa yayi da ruwa a cikin cup, ya kunna fitilar ya d'ora cup din saman mirror, sannan ya bud'a jakarsa ya fito da wasu pills ya 6alla guda d'aya, ya d'auki ruwan ya hau samar gadon ya mik'a mata. "Open your mouth Baby." "What's that?" "Ki bud'e bakinki ki sha mana. Zan cutar da ke ne?" "A'a fa, but ka fad'a mun 1st." Ruwan ya ajje a gefe, ya juya tare da kashe lumsassun idanunsa, yasa hannu ya kama hannuwanta, sannan ya fara magana. "Babe kin san ina k'aunarki, kin san kuma bazan ta6a yin abinda zai cutar da ke ba.?" "I know Kazaure, but ina ganin ba komai ba ne dan na tambaye ka ko?" "Yeah, its nothing, but from now on, bana so kina questioning actions d'ina, be a good wife, and do whatever I ask you to do please." "But Sadam.." "Shhhh.. just do as I said. Please."7 Yayi maganar lokacin da ya d'ora yatsansa akan bakinta, ya karkata kai tamkar mai shirin yin kuka. Hannu tasa ta cire yatsan nasa, ta sakan mishi lallausan murmushi, a zuciyarta, ta rasa me yasa bata ta6a jin haushin duk abinda zaiyi ba, haka kuma bata tsammanin akwai ranar da zata zo wacce zata ji haushinsa. Hannunta ta dora a kan fuskarsa, a hankali tana kallonsa, tasa babban yatsanta ta shafi cikakkar girarsa, "It's Okay Hunnay, I'll try my best, and I'll be the perfect wife ever." Hannunshi dake cikin nata ta k'ara k'ank'amewa sannan ta cigaba "Trust me, you won't regret having me as a wife, cuz I love you so so very much." "I won't for sure, cuz U're a blessing to me. I love you so very much too Angel." Ya d'auko ruwan tare da mik'a mata maganin, tasa hannu ta ansa, ta saka a bakinta, ta bi da ruwan ta had'iye, sannan ta mik'a masa cup d'in. "That's my boo. Kinga every night zaki na shan maganin nan, so ko da na manta please ki tuna mun kinji, dan ba'a so ayi skipping d'inshi ko sau d'aya. May be zan baki shi ki ajje a hannunki, amma ba yanzu ba." "Na ji, but promise me, akwai lokacin da zaka fad'a mun ko na menene."1 Dariya ya saki, lokacin da ya mik'e da cup a hannunsa, sai da ya je bakin k'ofa sannan ya juyo, "zanyi deciding, amma ba yanzu ba." "Please.." Tuni ya wuce yana girgiza kansa, ya mayar da cup d'in kitchen ya dawo, ya kashe fitilar sannan ya koma kusa da ita ya kwanta. A hankali ya raba ta da jikinshi, duniya yake jin tana juya masa, taushin fatarta mai kamar audiga, ya jefa shi a wani na daban, har bai san yadda zai fassara soyayyarta ba. Wani bakon lamari take ji a tare da ita, sosai ta lafe a cikin rikonsa, a hankali kwakwalwarta ta gagara ansa sakon da yake aika mata a yanzu. "Sadaam please.." "Shhh.. let us be please.." Ya ja duvet din da ke gefe ya lullube su, suka ansa bakuncin wata duniya, mai wahalar fitowa. "I love you" Shine kawai abinda zaka iya ji daga bakin Kazaure. *** Washe gari ma tare suka gabatar da duk wani abu da yayi musu saura, zallan soyayya mai asalin aji da tsabta Sadam d'inta ke nuna mata, ko nan da can baya barinta ta matsa, yana mak'ale da ita, yana tunatar da ita muhimmancin da take da shi a rayuwarsa, da yadda zai kula da ita har izuwa numfashinsa na k'arshe. **Katsina. Maganinsa ya d'auko ya dawo palo ya d'auki ruwa ya sha, ya koma kan kujera yana mai cigaba da al'ajabin yadda Ummi ta wulak'anta mutuncinta, da gatan da ya yi mata a rayuwa. Shigowar Goggo ce ta katse tunaninshi, "Alhaji su Malam ne suka iso." D'agowa yayi yana kallonta, bai ce komai ba ya mik'e ya fara tafiya, ta rufa masa baya zuwa inda ta baro su. "Sannunku Malam. Ya hanya?" "Yawwa, Alhamdulillah. Ya jikin naka?" "Jiki Masha Allah, ana samun cigaba." "To madallah. Allah ya k'ara sauk'i." "Amin." Baffa ya ansa da shi, shiru na wani d'an lokaci ya ratsa wurin, a haka Goggo ta shigo d'auke da tray a hannunta, ta ajje kan centre table ta samu gefe ta zauna. Kan Mal. Baba a k'asa, ya had'a hannayensa wuri guda yana jinjina kai, daga bisani ya d'ago yana kallon Baffa. "Kabiru menene gaskiyar abinda Maryama ta sanar da ni a waya? Ina Ummi ta nufa kuma wane mataki kuka d'auka? Kuma me ya hana ku sanar da ni tun farko?" "Malam abin ne ba dad'in ji. Ban san ta ya zan fara fad'ar irin wannan mugun abu ba." "Tunda ka sa k'afa ka shure maganata, ai dole fad'ar irin wannan yayi ma bakinka nauyi Kabiru." "Ba haka bane Malam. Al'amarin ne Allah kad'ai ya san dalilin faruwarsa." "Rufe mun bakinka kawai." Yayi maganar yana d'aga masa hannu, sannan ya cigaba. "Nan na kira ka, na ce ka aurar da yarinyar nan, amma kayi biriss da zancen, ba komai yasa nace ka aurar da ita ba, sai dan saboda gudun irin abin nan da ya faru. Shi na gujewa tun farko Kabiru, shi yasa nace ka aurar da ita ga wanda take so, amma da yake kai kunnen k'ashi ne da kai, baka d'auke ni da daraja ba, shine kayi watsi da maganar. Ai yanzu kaga sakamakon taurin kai. Yanzu ka fad'a mun wa gari ya waya a irin wannan aika-aika da aka tafka?" "A'a, wallahi Malam ba laifi na bane, ga Maryama nan ita shaida ce, na yi bincike a halayyar yaron na gano yana da d'abi'un da bai dace ace na d'auki 'ya na bashi ba. Bincike na ya tabbatar mun Sadam mashayin giya ne, kuma d'an caca. A yadda na samu labari daga garinsu ma hatta mahaifinshi bai d'auke shi da wata daraja ba, yanzu Malam ta ya zan d'auki 'ya in ba mai irin wannan halayyar? Kuma sai da na kira Ummi, na zaunar da ita na zayyane mata abinda ke faruwa, nace ni ta kawo wani ma, amma da yake Ummi bata d'auke ni a bakin komai ba, ta sa k'afa ta shure maganata. Dan k'arfin hali har da bar mun wasikar cewar kada in sha wahalar nemanta, wane mataki kuma ya rage in d'auka fisabilillah?" "Wannan yasa a kullun nike takaicin irin tarbiyyar da kuka bata. Kuma sanin kanka ne, babu ranar banza da bana tunatar da kai cewar 'ya'ya amana ce ta Allah ya damk'a a hannun iyayensu, amma da yake al'adun nasara sun gama ratsa k'wanyarka, baka ta6a d'aukar maganata da muhimmanci ba, kun bar yarinya sakaka, baku san ku nuna mata dai-dai ba tun asali, ta ya yanzu da girmanta, ta kai wani munzali na sanin abinda take so kake tunanin zata yi maka biyayya? Kaima ka san abinda ba zai ta6a yiwuwa ba ne Kabiru."4 "Amma duk da haka Malam ai ya kamata Ummi ta san mutuncimu a matsayinmu na iyayenta." "Rufe mun baki da Allah, tunda kuke kun ta6a nusar da ita muhimmancin naku ne? Yanzu wannan abu da me yayi kama? Allah ya gani baku kyauta mun ba wallahi, wannan abun kunya har ina? A cikin zuri'a ta?" "Malam abinda abinda ya faru ya riga ya faru, mun kuma tabbatar da hannunmu a tafiyar Ummi, ban k'i ace duka laifin na mu ne ba, amma ayi hak'uri. A fara tunanin hanyar da za'a bi a ganota." Cewar Goggo da ke zaune gefe, kanta a k'asa da alama hawaye take zubarwa. A fusace Baffa ya d'ago, "Ba da yawu na ba. Kuma ban bada izinin a nemi Ummi ba har abada." "Kabiru? Kana cikin hankalinka kuwa?" "A hankali na nake Malam, amma na dad'e da mantawa da na ta6a haihuwar wata mai suna Ummi a rayuwata." "To baka isa ba, dole ka tashi muje gidan talabijin da na rediyo mu bada cigiyarta. Kuma dole ka sanya kud'i ga duk wanda ya samo ta. Tashi wuce ka shirya ka fito mu tafi." Kukan da Goggo ta fara yi ne ya ta6a zuciyar Baffa, tausayinta sosai ya tsirga raunatacciyar zuciyarsa, kamar ya tafi Maiduguri neman Ummi, sai dai kuma ya riga ya sanya ma zuciyarsa dangana, ya kuma shafe babin Ummi a matsayin d'iyar da ya ta6a haifa a doron k'asa. K'asa yayi da kanshi, hawaye na kwarara a idon babban mutum kamarsa, murya na karkarwa yace, "Kayi hak'uri da abinda zan fad'a Malam. Wallahi ba zan ta6a asarar lafiyata wurin neman Ummi ba, ba kuma zan ta6a fita neman 'yar da ta fifita wani k'ato akan mahaifanta ba. Ka gafarce ni dan Allah." Yadda Baffa yayi maganar, ya tabbatar ma Mal. Baba iya gaskiyarsa kenan, sai dai kuma yana tausaya ma d'an nashi, saboda ya san irin k'auna da shak'uwar da ke tsakaninshi da tilon 'yar tasa. Shiru na wasu dak'ik'u ya cigaba da wanzuwa a tangamemen palon, in banda sheshshekar kukan Goggo, ba'a jin komai, yayin da kan Baffa har yanzu yana k'asa, ya kasa had'a ido da mahaifin nasa, kasancewar yau rana ta farko da ya ta6a yi masa umarni ba tare da ya cika ba. **Maiduguri. Rik'e take da jakar Laptop d'inshi, yayin da shi kuma yake tsaye gaban madubi, yana taje sumar kansa, sosai take kare mishi kallo daga cikin madubin, "Please, gayun nan ya isa haka, sai kace wanda zai je wani gagarumin taro." Comb d'in da ke hannunsa ya tura a aljihu ya taka zuwa gabanta, a lokaci guda yana gyara collar rigarsa. "First day in office, I've to look extraordinary, dan su san Kazaure ba sa'an yin su bane. Kin gane ai." Ya k'arasa maganar yana d'aga girarsa tare da shafar gefen fuskarta. "Duk wanda ya ganka ai ya san kai d'in na daban ne, I'm just scared kada 'yan matan Borno su fara eyeing mun kai."1 "Ke d'aya ce Baby na, baki da number two. Now gimme a peck." Ya tura mata gefen fuskarsa, tayi pecking, sannan ya ansa jakarsa suka fito hannunsa cikin nata har zuwa bakin k'ofa. "Sai na dawo ko?" "You take care of yourself for me please." "I'll Hunnay. You do the same." Ya raba ta da jikinsa, shiru na dogon lokaci ya ratsa tsakaninsu,suna jin yadda zukatansu ke bugawa da soyayyar junansu. "I love you Mrs. Kazaure." Ya yi kargin halin fada lokacin da ya dago ta, ya sumbaci saman goshinta, ya juya ya fara tafiya. "I love you too Mr. Kazaure." Ta fada tana daga mishi hannu. Da haka ya tada motar ya wuce, ita kuma ta koma ciki. Haka rayuwar tasu take tafiya, cike da soyayya, shak'uwa da jin dad'i.1 《》BAYAN WATA BIYU《》 Sanye take da bak'in skinny jeans tare baby pink d'in T-shirt da ta kama ta sosai, mai gajeran hannu an rubuta Be My Baby, tare da zanen k'atuwar rose flower a gaban rigar. Ta takure kanta wuri guda a cikin kujera mai cin mutum daya, k'afafuwanta da hannayenta, ta had'a su wuri guda tana tunanin ina Sadam ya shiga, kasancewar har yanzu bai dawo daga aiki ba, bai kuma ta6a kai irin wannan lokacin basa tare ba. A hankali ta d'aga kanta, ta sauke idonta jikin agogon dake mak'ale a bangon palon, k'arfe bakwai da mintina hamsin da biyu cif-cif, ta san duk wani magidancin arzik'i indai baya masallaci, to yana gidansa a irin wannan lokacin tare da iyalinsa. Tsoronta d'aya kada taje ko wani abun ya same shi, ga shi ita ba waya ba, balle ta nemi sanin halin da yake ciki, domin kuwa tun da yake bai ta6a kai irin wannan lokacin a waje ba, duk da yawan traffic jam na garin, bai ta6a kai k'arfe bakwai bai dawo gida ba.1 Hawaye ne suka fara sintiri akan fuskarta, addu'a ta fara yi Allah ya ku6utar da mijin nata a kowanne irin hali yake ciki. K'arfe tara da rabi na dare ya shigo gidan, ta ci kukanta ta gaji, har bacci ya d'auke ta a wurin. K'aran bud'e k'ofar palon ne yasa ta mik'e a firgice, ta sauke idanunta a kansa. Da sauri ta tashi ta isa inda yake, jikinsa ta fara duddubawa ko wani abun ya same shi, amma bata ga alamar hakan ba, yayin da ta 6angarensa biyu-biyu ya ke ganinta, a karo guda zuciyarsa ce ke k'awata mashi kyakkyawar surarta fiye da yadda yake ganinta a baya. Bai damu da yadda take kallonsa ba, gadan-gadan ya nufe ta yana k'ok'arin d'aga ta sama. "Are you ok?" Sai a lokacin ya fara tunanin dai-daita natsuwarsa. "I'm fine dear. Me ya faru ne?" "No U're not fine Sadam. Kalla fa idanunka. Me ke damunka dan Allah?" Ta matsa gabanshi, ta yadda har zasu iya jin numfashin juna. Wani mugun wari da taji yana fita a jikinshi, wanda bata san d'an gayun kazaurenta da shi ba. Ido ta k'walo waje "Sadam warin me haka? Ina ka tsaya? Me yake damunka?"1 "Hey nothing fa. Muje ciki, I wanna take a shower" "Ba inda zamu je sai ka fad'a mun inda ka samo warin nan." "Babe ba komai fa, muje inyi wanka I'll explain." Ya matsa gabanta yana k'ok'arin had'a ta da jikinshi a karo na biyu, amma tayi saurin ja da baya, ta fashe da wani irin kuka tana toshe bakinta, tana yin da baya, da baya yayin da shi kuma ya cigaba da takawa yana binta, domin tunda yake bai ta6a ganin tayi mashi kyau irin haka ba, barasar da ke kanshi ta cigaba da k'awata mishi ita, a haka har ta had'e da jikin kujera, shi kuma ya isa daf da ita, ya sa hannu ya fisgeta suka wuce ciki. Allah ne ya taimaketa da yamma tayi wankan tsarki, amma da a haka Sadam zai fad'a mata ba tare da hankalinshi na jikinshi ba. Haka kuma bai damu da bata magani kamar yadda ya saba a ko wacce rana ba. Anya wannan Sadam d'inta ne? Mutumen da ke riritata yana lalla6a tamkar jaririya yau shine ya zo mata a haka? Addu'a ta fara yi a k'asar zuciyarta, 'Ya Allah kada kasa maganar Baffa ta kasance gaskiya.' Kuka take mai tsananin zafi, hannayenta duk biyun tasa ta kama shi ta k'ank'ame, sai dai bai ma san tana yi ba, baccinshi ya ke cike da kwanciyar hankali. Ganin babu abinda kukan zai k'are ta da shi yasa ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, tare da alwala ta fito ta kabbara sallar isha'i ta gama, tayi zaune a wurin tana k'are ma Sadam kallo, da alama bashi da sauran damuwa. Bata tashi a wurin ba sai kusan k'arfe d'aya na dare, shima baccin da ke idonta ne ya ci k'arfinta, a hankali ta ra6a gefenshi ta kwanta, inda ta sa hannu ta rufe masa bakinsa da ya hangame.5 * ** Sannu a hankali ya fara bud'e idanunsa, hasken ranar da ya fara lek'owa ta windon d'akin ne ya haske santaleliyar fuskarsa wanda ya sanya shi d'ora hannu a saman fuskarsa, yana mai juyi zuwa gefenshi. Zaune ya mik'e yana kallon jikinsa, yanayin da ya samu kansa ne yasa ya fara tunano abinda ya faru a daren jiya, take ya dafe kai, hotonan abinda ya wakana na cigaba da dawo masa, a wani 6angaren na zuciyarsa yana jin haushin irin aika aikar da yayi. "Its just a cup. Ya Allah!"3 Yayi maganar a bayyane. "Ko dan na dad'e ban sha ba?" Ya kuma tambayar kansa shima a bayyane. Bai samu ansar ba, alarm d'insa ya fara ruri, dan haka ya mik'e ya wuce toilet yayi wanka tare da alwala ya fito. Sallah ya kabbara a haka ta shigo ta same shi, har ya gama tana zaune a gefen gado yayi addu'a ya shafa, sannan ya isa gabanta. "How's my Angel doing?" Bata ce komai ba ta juyar da kanta, hakan yasa ya tsargu da kansa, a hankali ya matsa ya koma gefenta ya zauna tare da kama hannayenta duk biyun. "What's wrong with you darling?" "Me ya faru da kai jiya?" Ta jefa mishi tambayar tana kallon k'wayar idanunsa. Tarin sumarsa ya shafa, yayi duban tsanaki zuwa gare ta, bai ce komai ba, ya sake hannunta ya mik'e ya isa gaban mirror ya fara shafa mai. "Magana nake kayi mun banza." "Na ji ki, but kada kisa abin a ranki. Pretend like its never happened."6 "How can I? Image d'in abun ba zai ta6a gogewa a zuciyata ba. You better tell me the truth, dama kana shaye-shaye?" A hargitse ya juyo ya watsa mata mayun idanunsa. "Wane irin magana kike yi haka?" "Saboda mashayi ne kawai zai iya yin abinda kayi jiya, kuma ka dad'e baka dawo gida ba, and kayi abubuwan da ban ta6a sanin zaka iya su ba." "Will you just shut up please?" Ya fada vikin dakakkiyar muryarsa. Calm down Kazaure Ya shafa tarin sumarsa, yana mai kankan da murya ya ci gaba "Me sa baza ki gane ba? Well, an samu matsala ne jiyan nan, so ki basar da maganan kawai." Hawaye ne suka fara bin kumatunta, ta mik'e ta isa, gabanshi tana kallon yadda ya maida hankali ga abinda yake ba tare da ya juyo ya kalle ta ba. "Ta ya zan iya mantawa Sadam? Wato hasashena ya zama gaskiya kenan ko?" Juyowa ya yi cike da jin haushin yadda take magana, a zucoyarsa yana jin kamar ya share ta, sai dai ya daure, ya bud'e hannayensa yana fad'in, "Come here darling." Babu gardama ta fad'a jikinsa, domin abinda ta fi buk'ata a dai-dai lokacin kenan. Kanta ya fara shafawa, har sai da ta daina kukan, sannan ya zaunar da ita a stool d'in dake gaban mirror, ya duk'a gabanta ya kama hannayenta yana wasa da su a hankali, daga bisani ya fara magana. "Babe tsautsayi ne kawai, kin san ba hali na ne ba. Mun je dinner bikin wani christian colleague d'inmu ne suka yi serving d'inmu giya ba tare da mun sani ba, ba ni kad'ai bama almost duk mutanen dake wurin sun sha, but i promise you next time, bazan k'ara shan komai a waje ba. Kinji?" "Amma ni ai baka sanar da ni zaka je wani dinner ba." "Yeah, banyi niyyar zuwa ba nima, mutane ne suka yi forcing d'ina. Dan haka kinga maganan nan ya wuce kawai tunda dai na fad'a miki yadda aka yi." "Na ji, amma dan Allah next time ka tabbatar ka duba komai aka baka kafin ka sha. Kaga kada inje wataran a baka abinda zai kashe mun kai." "Stop saying that please, Zan kiyaye kinji 'yan matana." Dariya ta saki tare da shafa gefen fuskarsa. "That's why I so much love you. Akwai ka akwai jin magana." "Ba dole na ba. Kinsan bana son abinda zai ta6a kyakkyawan wurin nan." Yayi maganar tare da dafa setin da zuciyarta take. "To tashi ka k"arasa shirinka, ka riga ka makara ma." "Oyaa help me, tun ban k'arasa makara ba." "Right away." Ta mik'e tare da ciro masa kayan da zaisa, ta fito masa da takalma, sannan ta wuce kitchen ta had'a masa abinci a lunchbox, ta hado mashi tea a cup, ta dawo d'akin. Tsaye ta same shi yana gyara necktie d'inshi, cup d'in hannunta ta bashi, sa'adda ta kama necktie d'in ta k'arasa d'aura masa, shi kuma yana kur6ar tea d'in hankalinshi kwance. Hannuwansu sagale da na juna suka fito zuwa bakin motarsa, ta duk'a tayi pecking d'insa, sannan yayi mata sallama ya tada motar ya tafi.7 《》 Kayan da ke hannunta ta zube a saman kujera, sa'adda ta zauna, tare da cire mayafin da ke kanta. "Woah! Na gaji wallahi, ga wani irin ciwon kai da nake ji, na manta mu siyo magani ma." K'ofar palon ya rufe, ya k'araso gabanta. Ya ciro roban ice cream ya mik'a mata. "An shi nan da kinsha ciwon zai bari." "I don't think so, nafi three days ina yin shi fa, and kusan kullun da fever nake kwana wallahi." Ta anshi ice cream d'in ta bud'e, tasa spoon ta d'auka ta kai bakinta. "Amma me sa baki fad'a mun ba, though wani lokacin ina jin jikinki da zafi, but banyi tunanin fever ba ne ba…" Yunk'urin aman da ta fara yi ne ya katse maganar tasa, da sauri ya isa gabanta "Hey, what's wrong?" Kafin yayi wani motsi ta wurgar da roban ta mik'e da gudu ta shige toilet. Amai ta dinga yi sosai, har sai da ya tausaya mata, shi ya taimaka mata da ruwa ta gyara jikinta, sannan ya kamata suka fito.1 Palo suka dawo, ya zaunar da ita a kujera, ya ɗauki gyalenta ya sanya mata, ya juya ya ɗauki makullin mota, sannan ya kamata. "Tashi muje asibiti Babe." "Dare ya riga yayi fa, mu bari zuwa safiya kawai. Na ji ma na daina ciwon kan." "Are you sure?" "Da gaske fa." "Alright then. Amma me kike tunanin ya saka ki amai har haka?" "I can't say gaskiya. Kaman ice cream ɗin nan ne." "Ke fa kike ta cewa zaki sha, kuma ni tunda nake ban taɓa ganin ya saka ki amai ba. Bakya tunanin wani abun?" "Bakomai, kai dai kada ka wani damu fa." "No, seriously hankalina a tashe yake. Gaskiya ki tashi muje asibiti." "Ba fa inda zamuje cikin daren nan, kayi hak'uri zuwa safe."2 Ba wai dan Sadam ya so ba haka kawai ya hak'ura duk kuwa da dukan tara-tara da zuciyarsa ke yi, tare da addu'ar kada Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya. A daren ranar haka ta kwana da wani irin zazzaɓi mai zafi, hakan yasa Sadam ya k'ara sarewa. Duk da ba sanin alamomin masu ciki yayi ba, amma zuciyarsa ta kasa natsuwa, haka kuma a lokuta da dama ya kan ji ance mata suna amai da zazzabi mai mugun zafi a farko-farkon samuwar cikinsu. Sai dai ta wani ɓangaren ya kan ɗan samu kwanciyar hankali idan ya tuna da ta na shan contraceptive pills din da yake bata (maganin hana ɗaukar ciki). Amma kuma bugun zuciyarsa ya kan tsananta idan ya tuna ranar da ya je mata yana cikin maye. Da wannan tunanin ya kwana, hakan yasa yana tashi da safe bai yi maganar kaita asibiti ba, ya fito ya wuce wani chemist mafi kusa da su ya anso PT strips (pregnancy test strips) ya fito. Ko da ya koma a duk'unk'une ya same ta kyarma kawai take yi, saboda azababben sanyin da take ji, duk kuwa da zafi irin na garin Maiduguri. Gaban gadon ya isa ya ɗan ɗaga bargon da ta lulluɓa da shi, yasa hannu ya taɓa wuyanta, zafin da ya kai mashi bak'unci ne yasa shi sauke hannun cikin gaggawa. "Sorry Babe. Daure ki tashi kiga" "Ya kamata muje asibiti Sadam, ina jin jikin nan sosai wallahi." "Zamu je ai, now tashi kiyi amfani da abin nan, daga nan sai kiyi wanka muje asibitin." Da haka ya taimaka mata ta mik'e, ya ɗauko towel ya mik'a mata, ta ansa ta ɗaura, ya kama hannunta suka wuce toilet ɗin. Abun ya fitar ya bata, yace ta karanta taga yadda ake amfani da shi, ta ansa ta duba anan ta gane amfaninsa. Murmushi tayi, tare da girgiza kai. Process din ta bi tayi amfani da shi, kafin tayi wankan ta dawo. Zaune ta same shi ya buga uban tagumi da alama ya faɗa kogin tunani, domin ko fitowarta bai ma ji ba. Gabanshi ta isa, ta sa hannu ta dafa kafaɗarsa "are you ok?" Firgit ya ɗago, "Ina abun yake?" "Yana ciki." Bai ce komai ba ya tashi ya shige toilet ɗin, strips ɗin ya ɗauka wanda dama a k'alla ana son a barshi yayi kamar minti biyar, ta yadda za'a gane ainahin gaskiyar gwajin da aka yi. Abinda idon Sadam ya gani ne yasa shi dafe kai, hannunsa dafe da kirji yayi baya tare da jinginewa jikin bango. "Positive?" Yayi maganar da k'arfi, wanda hakan yasa ta faɗo toilet ɗinn cikin sauri, tana tambayar abinda ke faruwa. Bai bata ansa ba ya cigaba da girgiza kai. "No, no.. This can't be." "What?" Ta tambaya lokacin da ta sa hannu ta anshe strips ɗin ta na dubawa. Abinda ta gani, wanda ya tabbatar mata positive kenan, yasa ta washe baki, ta isa da sauri tana kokarin rungume shi, amma ya sa mata hannu. "Wait please. Don't tell me you're happy with this?" "Of course I am, wannan ai abun farinciki ne. Nan ba da jimawa ba zamu zama parents, ya kamata muyi farinciki mana." "Dallah dakata mana" Yayi kanta da sauri, ko me ya tuna kuma, sai kawai ya juya, yasa hannu ya shafi tarin sumarsa, ɗayan hannun rik'e da kugunsa, ya ma rasa menene abinda ya kamata yayi. "What? Ban gane me kake nufi ba." "Well, fito muje asibiti. Ban yarda da abin nan ba. Jira ma tukun, wai kina shan maganin nan da nake baki ko kuma kina fakar idona ne ki watsar?" "Ka ji ka da wani magana, abinda a gabanka nake sha, kai fa kake bani da hannunka. And me ma ya kawo maganar maganj?" "Ya Allah! Kinga shiga kisa kayanki ki fito muje asibiti kawai." Daga haka ya wuce ya fita, gaban mota ya buɗe ya shiga, kasa yayi sosai da seat ɗin ya shingiɗa, tunanin yadda abin nan ya kasance kawai yake yi, inda ya gama yanke shawara abinda zai yi, matsawar suka je asibiti aka kuma tabbatar da gaskiyar lamarin. A haka ta fito ta same shi, ya haɗa zufa idanunsa a rufe, bai ma san da isowarta ba. "Sadam." Ta kira shi a hankali, dan ta rasa dalilin da ya sa shi rasa natsuwarsa cikin ɗan kankanin lokaci. Bai tanka ta ba ya tashi zaune, ya gyara zaman kujerarsa, sannan ya tada motar, hakan ya bata damar shiga ta zauna, zuciyarta duk a cunkushe duk kuwa da farincikin k'aruwar da suka samu da take yi. Shiru ne ya ratsa motar, babu wanda ke ce ma ɗan uwansa komai, har suka iso asibitin, kasancewar private ne, sai basu sha wahala wurin ganin likita ba. Bayani likitan ya bukaci Jay ta masa na abubuwan da take ji, a take ta zayyana mishi komai, hakan yasa yace su biyo shi zuwa ɗakin scanning. Idon Sadam kyar akan allon na'urar, sai dai ya kasa fahimtar komai, cikin ɗimuwa ya kai duba ga likitan ganin yace Jay ta mik'e ta gyara jikinta. "She's four weeks, four days pregnant. Congratulations Mr. Kazaure." Ya mika masa hannu, amma Sadam ya bige hannun ya mik'e.1 "What the f*ck! Pregnant?" "Sure. Are you alright?"1 Likitan ya tambaya yana kallonsa, fuskarshi cike da alamar tambaya. "I'm not!" Sadam yayi maganar a tsawace, kan shi tsaye ba tare da ya damu da kallon da likitan ke masa ba. "Whats your problem?" Jay da ta k'araso gabansa ta tambaya, tana kokarin kama hannunsa. Ganin hakan yasa likitan ficewa yana faɗin "ku same ni a office." Hannunta Sadam ya kama, fuskarsa ta gama bayyana halin da zuciyarsa ke ciki, juyo da ita yayi, ya zaunar ta a kujerar da ya tashi, sannan ya duk'a gabanta, yasa hannu yana shafar kumatunta. "Babe me kike ganin ya dace ayi da cikin nan, dan gaskiya is too early ace mun fara haihuwa. Duka-duka wata nawa ne da aurenmu, amma ace har zamu fara tara yara? Bazan lamunta ba gaskiya." "Me kake nufi kenan? Kana tunanin a zubar da cikin ko me?" "Kwarai ma kuwa, in ba haka ba kema zaki tsufa da wuri, kizo ki tara ya'ya, kinga daga nan zaki gundire ni, har kiga na fara neman wata a waje, ni kuma abinda bana son ya faru kenan, saboda ina son ki sosai, and bana son na haɗa soyayyarki da ta kowa."9 "Wannan ba hujja ba ne Kazaure. Cikin nan fa ba shege ba ne, ka tuna da aure muka same shi, gaskiya ni ba zan iya zubar da shi ba." "Dole a zubar da shi Jay, cuz I'm not f*cking ready to be a father yet! Tashi muje."1 "No Sadam, I can't do such evil, ba zan kashe kyautar da Allah yayi mun ba. Ina son baby na tun daga lokacin da na gane ina ɗauke da shi." Hannunta ya k'ank'ame, "Zamu samu wasu babe, but this one, dole a zubar da shi, ki tuna ta yadda akai muka yi auren mana, yanzu haka kawai sai ki ɗauki yaro ki koma ma su Baffa da shi idan mun tashi komawa? Haba Baby na, think over it mana, ki tuna yanzu muka fara rayuwarmu, muna jin daɗinmu, muna more kuruciyarmu, haka kawai sai mu wani fara haihuwa ko amarcinmu bamu gama ci ba?. Babe kinsan ina son ki, kuma ba zan so abinda zai cutar da ke ba, so ki tashi kawai muje in yi ma Dr bayani, cuz dama an faɗa mun asibitin nan suna irin aikin nan a ɓoye, kinga baza mu sha wani wahala ba. Please baby na." Ya kama fuskarta da duk hannayensa guda biyun, yana aika mata da wani sakon kallo wanda a duk lokacin da ya yi mata shi take daburcewa, ta manta tunaninta, ta kuma bi duk abinda yace mata tayi. Take huɗubarshi ta ratsa ta, zuciya da gangar jikinta suka aminta da gadar zaran da Sadam ya kulla mata.2 "Na ji, amma ka yi mun alk'awarin this is the first and also the last." "I promise you babe, wannan ma dan kawai mu samu lokacinmu mu ci amarcinmu, mu kuma morewa kuruciyarmu. Kin gane ai?" Ya wani ja girarsa sama, ya sakan mata makirin murmushinsa ta gefen kumatu. Murmushin ta saki itama, ta mik'e suka wuce office ɗin likitan, Sadam yayi mishi bayanin shawarar da suka yanke. Shiru likitan yayi, daga bisani ya ɗago ya kalle shi, "Tabbas muna yin wannan aikin, amma ba kowa ya sani ba, saboda aiki ne mai haɗari, haka kuma akwai buk'atar kuɗaɗe masu ɗan nauyi." "Kada ka damu Dr, wannan duk ba matsala bane, in dai za'a samu biyan buk'ata." A take a wurin Sadam ya saka hannu, likita tare da masu taimaka mashi suka wuce da Jay ɗakin da za'a murje cikin da ke jikinta.Wani madaidaicin gado likitan yayi mata nuni da, alamar ta kwanta a kai. haka kawai ta tsinci zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri, dakewa tayi ta cire takalman k'afarta ta hau saman gadon ta kwanta. Tana kallon yadda ma'aikatan ke kokarin fara gudanar da aikinsu gadan-gadan, cikin gwanacewa, suke yin komai, hakan ya tabbatar mata da lallai zubar da cikin za'a yi.+ "Noooooo!!!!" Ta fad'a tun k'arfinta, a karo guda ta mik'e ta warci takalmanta, ta juya tare da bangaje likitan ta fito a sikwane. Sadam da ke zaune ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana danna waya a kofar ɗakin da aka shiga da ita, ya ganta ta fito sai wurga ido take, bata bi ta kanshi ba ta wuce da sauri, ta fito harabar asibitin. Inda suka yi parking ta isa ta buɗe motar ta zauna, zuciyarta na wani irin bugawa dam-dam, take wasu zafafan hawaye suka k'wace mata, ta fara rera kuka tamkar zata cire idanunta. A wani ɓangare na zuciyarta ta fara kokonton soyayyar da Sadam ke yi mata, yayin da ta wani fannin ta fara zargin ko tana ɗauke da wani mugun abun ne a tattare da ita wanda yasa Sadam baya son haɗa zuri'a da ita. A haka ya iso wurin, ya zagaya ta inda take ya buɗe motar, a lokaci guda ya duk'a gabanta, ya ma rasa ta ina zai fara magana, saboda yadda yake ji a zuciyarsa tamkar ya kwalfa mata mari akan irin wannan shirmen da ta yi mishi. Dak'yar yake iya ɗaga ido ya kalleta, domin tunda ya gane tana da ciki yake ganin gaba ɗaya ta canja mishi, har wani muni yake ganin tayi, haka kuma yakan ji tashin zuciya idan har ya k'unacewa kallonta.6 "Me kike nufi da kika zo nan kike yi ma mutane kuka?" A galabaice ta ɗago rinannun idanunta da suka k'ara fitowa waje, hawaye na kwarara take kallonsa, "Bazan iya aikata wannan mummunan alkaba'in ba Sadam, wanda nayi na gujewa iyayena ma ya isa haka, ba sai na saɓawa mahaliccina ba kuma. Kayi hak'uri ka tashi mu tafi." A take idanunsa suka canja launi, wani hayak'in balai ya fara tashi a cikin kansa, barasar da ke cikin kwalwarsa ta motsa lokaci guda, a bala'ince ya mik'e tare da buga samar motar, idanunsa a waje yace "This is nonsense. Me kike nufi kenan? Ni Kazaure zaki haife ma ɗa? Hmmmm.. this is bullsh*t! Tun muna mu biyu ki fito mu je kawai, tun baki gane irin tashin hankalin da taurin kanki zai haifar ba. Tashi muje."3 Kallonshi take a tsorace, anya wannan kazaurenta ne? That lovie lovie ɗin nan? Me cewa zai kula da ita da duk wani farincikinta? wannan handsome man ɗin da bata taɓa ganin mai kamarsa ba, wanda kalamanshi suka sanya ta faɗawa dumu-dumu a soyayyarsa. Shine yanzu yake neman juye mata? Ya ke neman komawa wata halitta ta daban mai ban tsoro? No, wannan ba Sadam ɗina bane ba. A bayyane tayi maganar tana takure jikinta, tare da k'ank'ame hannuwanta zuwa kirji. "Oh mamaki ma kike yi ko? To zan iya yin abinda ya fi haka matsawar kika bijirewa abinda nake son kiyi. Fito a motar nan tun ban ɗaga ki sama na shigar da ke ciki ba." Wannan karon tsoron dake zuciyarta ya gama bayyana a saman fuskarta, kafafuwanta ta naɗe, ta haɗe su da kanta da hannuwanta ta takure a kujerar, hawaye na kwarara wani na bin wani ta fara girgiza kai. "Please Sadam, ba haka muka yi da kai ba, ni ce fa, babynka, Jay ɗinka mai k'aunarka. Please ka taimaka ma babyn da ke cikina, wanda bai san komai ba, ka dubi soyayyar da nake ma kayi hak'uri ka bar ni na haifeshi, ina son shi wallahi, ina son shi Sadam."2 Ta kuma ɓarkewa da wani kukan, wanda yasa wasu daga cikin mutanen da ke wurin fara taruwa suna kallonsu. Hannu Sadam yasa ya sosa cikkaken gashin girarsa, sa'adda ya juya ya wurga ma mutanen da suka fara taruwa mayun idanunsa. "Uban me kuke kallo ne?"2 Sum-sum suka fara darewa, wasu na gulmarsu, wasu kuma suka ɗan matsa gefe suna cigaba da kallonsu, yayin da shi kuma ya juya yana kallonta, daga k'arshe ya duk'a ya ɗago ta gabaaya a yadda take a dukunkunen zai shigar da ita ciki. Ihu ta saka tana zillewa, dak'yar ta kwaci kanta a hannunsa, ta koma da gudu ta shige motar tana wani irin kukan zuci, wanda babu hawaye sai dai ajiyar zuciya. Bai k'ara gigin ɗaga ta ba, hannuwansa ya yarfa, sannan zagaya ya shiga motar ya ja da saurin bala'i, ya fita a wurin. Wani irin mahaukacin gudu ya dinga yi tamkar wanda aka sallamo daga gidan mahaukata.1 A k'ofar gida yayi parking, ya fito ya zagaya gefenta ya buɗe, zaune take ta haɗa kai da gwiwa kuka kawai take yi, yasa hannu ya damki nata hannun suka wuce cikin gidan. A palo ya zaunar da ita, sannan ya koma gefenta ya zauna, idanunsa sun koma tamkar garwashin wuta saboda bala'i, zuciyarsa kam ba zai iya tantance abinda yake ji ba, illa wani abu da yake bijiro masa dangane da Jay. "JAMEELA" Bata daina kukan ba, haka kuma bata kalle shi ba. Bai damu ba shima ya cigaba. "Kinsan Allah, idan kika ce Ba za'a zubar da cikin nan ba, sai dai ki nema ma abinda kika haifa wani uban, ba dai Kazaure ba." Sororo ta ɗago, ta sauke idanunta kansa. "Me kake nufi Sadam? Wa nake da shi bayan kai? Ina kuma zan je neman wanda zai zama uban abinda ke cikina?" "That's none of my business, matsalarki ce ke da abinda ke cikinki, cuz ni ban shirya zama uban kowa ba, ke idan baki sani bama ki sani, bani da burin haihuwa kwata-kwata a rayuwata. Dan haka zaman lafiyarki tare da ni shine ki tashi mu koma a zubar miki da abin nan, idan ba haka ba sai kin gwammaci zaman kurkuku akan zaman gidan nan, dan ni ba zan iya zama da mai ciki ba." "You must be kidding Kazaure. Wai ka ko san da wa kake maganar nan?" "Wa kuwa wacce ta wuce ke Jameela? Ki bi abinda nace kawai, shine zaman lafiyarmu."5 "Are you really the Sadam I knew? Anya kana kaunata kamar yadda kake faɗa a baya kuwa?" Wani mugun haushin yadda take maganar ma yake yi, daga k'arshe mikewa kawai yayi, ya saita yatsanshi a kanta "Ke ni fa ba mahaukaci ba ne, duk abinda nayi kuma ina cikin hankali na, kin gane ko, ba wani maganar shirme na tambaye ki ba, dan haka kada ki kawo mun nonsense a wurin nan. Kiyi abinda nake buk'ata shine rufin asirinki, rashin yin hakan kuwa ba komai zai jaza miki ba illa azaba, dan ni bana ɗaukar reni ko kalilan." Yana gama faɗar haka ya juya ya fita ya bar gidan gaba ɗaya, cikin wata irin azaba da yake ji a zuciyar dake kwance tsakanin k'irjinsa. Ido ta bishi da, mamaki sosai ke shimfiɗe saman fuskarta, har kuma yanzu ta kasa gaskata abinda kunnuwanta suka jiye mata. Bata ɗauke idonta ba, har sai da ya ɓace ma ganinta, sannan ta ɓarke da wani irin kuka tun k'arfi, amma Sadam ko waiwayenta baiyi ba, haka yasa kai ya fice a gidan baki ɗaya. Sai da tayi kuka mai isarta, daga bisani amai ne ya taso mata, da gudu ta mik'e ta wuce toilet ta dinga kwara shi, tamkar zata amayar da 'yan hajin cikinta. A galabaice ta fito, ta kwanta kan gado, har yanzu ta kasa daina mamakin Kazaure, a zuciyarta ta gama yanke hukunci kan baza ta taɓa zubar da cikinta ba, ta tabbata a hankali Sadam zai fahimce ta har ma su samu damar dai-daita tsakaninsu. Yunwar da ta addabeta ne ta fito da ita ta wuce kitchen ta ɗora abinci, har tayi ta gama Sadam bai dawo ba, kuma yau ba ranar aiki ba, shi da baya fita ko ina in har weekend ya kama. Tun tana zaune a palon har ya kai ta shingiɗa, k'arshe bacci ne ya ɗauke ta, har kuma a lokacin bashi da niyyar dawowa gidan.5 Misalin sha ɗaya na dare yayi parking motarshi, wanda ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida, saboda irin mayen da yake ciki. Gyara tsayuwar motar yayi, sannan ya kwaso kuɗi da ke zube gefen kujerar da yake, ya tattaro doguwar rigar shaddar da ke jikinsa ya zubo kuɗaɗen wanda da alama a caca ya samo su, ya saka wayarsa, da makullin motar ya fito, ko motar bai tsaya rufewa ba, ya tunkari k'ofar shiga cikin gidan. Motsinshi ne ya farkar da ita, ta mik'e zaune, sai dai bata ganin komai, tafiya yake shima ba tare da ya san ina ya dosa ba, saboda tsabar duhu dake palon, bai ankara ba ya ci karo da hannun kujera, take yayi baya zai zube, a dai-dai lokacin aka dawo da wutar nepa, hakan yasa ta mik'e cikin sauri ta isa wurin, kafin tayi yunk'urin taimaka masa tuni ya kai k'asa, kuɗin da ke cikin rigarsa suka watse, sai dai ya kasa tsinana ma kanshi komai saboda yanayin mayen da yake ciki. Ganin yawan kuɗaɗen da suka tarwatsa tsakiyar palon yasa ta k'walo ido waje, ta fara tambayar kanta inda ya samu mak'uden kuɗaɗe har haka. Da sauri ta matsa gabanshi ta kama hannuwanshi ta mik'ar da shi, haka yake binta da kallo tamkar yau ya fara ganinta, ta wani ɓangaren kuma yana k'ok'arin tuna wani abu, amma ya kasa tuna ko menene. Warin da ta ji a jikinshi irin na ranan nan ne yasa tayi saurin ture shi, ta ruga ciki saboda amai da ya ci k'arfinta. Faɗuwa yayi sharaf, take ya fara wasu surutai, idonsa a rufe bai ma san abinda yake faɗa ba, har bacci yayi gaba da shi. "Sadam." "Meye ne? Dallah kada ki ta..kura..ni mala..ma." Yayi maganar cikin maye mai haɗe da gigin bacci. "Ka tashi ka ji, magana za muyi." Shiru bai ko motsa ba, haka kuma bashi da niyyar motsawar. Hannunsa take ta jijjigawa, amma Sadam bai san duniyar da yake ba, banda surutai marassa kan gado, babu wani abu da yake iya yi.1 Kukan da Jay ta saka ne ya sanya shi buɗe ido a firgice, sai dai ya kasa fahimtar me ya ke faruwa, a haka ya koma ya cigaba da baccinshi, ita kuma ta cigaba da wani azababben kuka, mai wani irin zafi da takaici, wai wannan mijinta ne, masoyinta abin alfaharinta. Ya za tayi da irin wannan munanan ɗabi'u da kazaurenta ya ɓullo mata da su? Ya zata yi da son zubar da cikin da yake wanda hakan ne kawai zai dawo masu da farincikinsu. Shin zata amince ne ko dan su cigaba da jin daɗinsu? Ko kuwa zata reni cikin ne? 'Watak'ila wannan ita ce kaɗai damar da zata samu a doron k'asa.' Da wannan shawarar ta fi gamsuwa, ta shafe hawayenta. "Ba zan zubar da cikina ba." Tayi maganar da hannunta a kan mararta tana shafawa, yayin da wasu sabbin hawayen suka cigaba da kwarara tamkar an buɗe famfo a fuskarta. Mik'ewa tayi ta fara janshi, a haka har ta shigar da shi ɗaki bai ma sani ba, hannunsa ta fara bubbugawa. "Sadam. Sadam. Ka tashi ka hau saman gado." Kakarin amai ya fara yi, ɗagowar da zaiyi ya wanke mata gaba ɗaya jikinta da aman giya mai bala'in wari. Ihu ta saki, tare da ture shi a jikinta, ta wuce toilet ta cigaba da kuka, ta gama gyara jikinta ta fito shima ta cire mashi kayan, dan ya gama birgima a cikin aman da yayi, ta barshi daga singlet sai boxers, sannan ta mikar da shi dak'yar, ta fa ɗora jikinsa a gadon, sannan ta tallabo k'afafuwan, ta dai-daita mashi kwanciyar, kafin ta zauna ta tsura mishi ido, hannuwanta na tallabe da fuskarta, tana tunanin yadda rayuwa ke shirin juya mata cikin ɗan k'aramin lokaci.3 《》 Bai tashi ba sai goma da wasu mintina na safe. Dak'yar yake buɗa idon, sa'adda ya sauke su akan Jay dake zaune ta rafka tagumi ta tsura ma allon gadon da yake kwance ido, sai dai a zahiri ta faɗa wata duniyar ce ta daban. Mik'ewa yayi zai isa gabanta, nan ya tuna cewar tana ɗauke da ciki, take zuciyarsa ta fara tashi, ya haɗe rai ya canja akalar tafiyarsa zuwa toilet. Tana nan zaune har yayi wankansa ya fito, ta tashi ta ɗauko ɗan k'aramin towel zata fara goge mai jiki, amma ya ɗaga mata hannu "Stop it please." "Me yasa? Aiki na ne fa, why now?" "Na ce bana so. Ko za ki mun dole ne?" Baya tayi ta koma inda ta tashi ta zauna, tana kallo ya gama shirinsa, ya fara neman makullin motarshi, amma bai gani ba, bashi kuma da niyyar tambayarta. K'ofar fita ya dosa, cikin k'arfin hali ta mik'e ta tare k'ofar. "Ba inda zaka je Sadam." K'ugunsa ya kama, fuskarsa babu annuri yake kallonta a wulak'ance. "Saboda?" "Sai ka faɗa mun gaskiyar abinda kake ɓoyewa." "Me kenan?" "Ka fi ni sani ai, ashe dama da kace an baka giya a wurin dinner ba gaskiya ka faɗa mun ba? Me sa kake son ka fara azabtar da ni ta wannan hanyar? Ka tuna cikin nan fa ba ni na yi ma kaina ba. Kai ka yi mun shi Sadam, menene laifi na ko laifin abinda yake cikin ciki na?" "Ai dan saboda na san ni nayi cikin shi yasa nace da ke mu je a zubar, amma ke kin gwada mun ni ban isa ba ko? To ina mai yi miki albishir da rayuwar k'uncin da zaki cigaba da fuskanta daga nan har zuwa lokacin da zaki canja shawara kizo muje a cire abun nan." "Wasa kake yi Sadam. Wai har rayuwar tamu ta kai ga haka? Duka-duka me muka fara a cikin rayuwar auren da har zaka bijiro da waɗannan halayen? Haba Sadam, ka tuna cikin nan kyauta ce daga Allah fa, kuma akwai dubunmu da suke nema ba su samu ba. Ka je kayi tunani, nasan lokaci zai zo da zaka gane gaskiyar abinda nake faɗa maka. Amma ba zan taɓa zubar da cikin nan ba wallahi."3 "Fine! Zaki cigaba da rayuwa a uk'ubance kenan. And da kike maganar rayuwar aure, an gaya miki abinda ke gaba na kenan? Aure da tara iyali? Ni Kazaure? Kema kin san banyi kama da irin mutanen nan ba. Da farko I thought tunda kika biyo ni, to zaki bi duk wani umarni na, amma tunda haka kika zaɓa a sannu zan fayyace miki ko wanene Kazaure. And tun asali da kin bi shawarar mahaifinki, da baki faɗa a tarkon irina ba. A da nayi tunanin zan iya hak'ura da wasu ɗabi'u nawa saboda ke, amma a yanzu na gane ke ɗin ko wacce iri ce. Na gane taurin kai, shine abinda ya kawo ki inda kike a yanzu. Ina so ki sani ko da idanuwanki zasu faɗo k'asa saboda kuka, ba zai rage ni da komai ba, shan giya kuma da kike magana, dama kece baki sani ba. Ke bama shi kaɗai ba, abubuwa da yawa, dan babu hali na k'wara ɗaya da mahaifinki ya yi miki k'arya. Ni ɗin dai nine, wannan Sadam ɗin da Baffanki ya zayyana miki ɗabi'u da halaye na. Bani hanya in wuce."11 Kuka ta fasa, ta cakumi gaban rigarshi, "Ka ci amana ta Sadam, ashe dama ba so na kake yi ba? Kasa na wulak'anta iyayena saboda kai? Ba zan taɓa yafe maka ba. Ka cuce ni ka ci amana ta."3 "Are you crazy? Sake mun riga Dallah, ke wawiyar wane gari ce? Ni nace miki bana son ki? Idan har zaki bi shawarar da na baki, zamu cigaba da rayuwarmu yadda muka fara ta. Amma idan taurin kanki ya hana, wallahi kinji na rantse, ke da kanki zaki fahimci irin gingimemen giɓin da kika yi ma rayuwarki." Ya k'wace rigarsa, ya koma ciki ya canja ta, dan ta riga ta cukwikuye, sannan ya fito tana duk'e a wurin tana kuka, ya wuce ya kwashe kuɗinsa da makullin motarshi ya ɗauki wayarsa ya fita ya bar gidan.Yadda yake buga k'ofar tamkar zai ɓalla ta ne yasa da yawa mutanen da ke cikin compound ɗin suka farka, har ma wasu suka firfito domin gane ma idanuwansu abinda ke wakana. Jay dake zaune ta ci kuka ta gode Allah, har idanunta sun fita daga ainahin kamanninsu, tana jin shi amma tayi biris da shi, har sai da ta ji surutun mutane ya fara tashi, sannan ta mik'e ta isa bakin k'ofar ta zare jamlock ɗin da ke jiki, ta buɗe k'ofar, ta dawo ta zauna a kujerar da ta tashi. Yanayin da ya banko k'ofar ya shigo ya kuma maida k'yauren ya buga, shi ya tabbatar mata da yau ma a cikin mayensa ya dawo.+ Kanta yayi gadan-gadan ya ɗaga hannu zai wanka mata mari, tayi saurin mik'ewa ta ja da baya, inda ya faɗa kujerar da ta tashi yana nuna mata yatsa. "Wane irin iskanci ne haka? Kina ji ina buga k'ofa baza ki buɗe ba." Shiru kawai tayi bata da niyyar ansa shi, hakan yasa ya tashi ya isa gabanta tare da sa kafa ya kwashe ta, ta zube kasa.2 "Menene dalilinki na rufe mun k'ofa? Ina magana kin tsare ni da ido kamar na mayu."8 Hannunta take murzawa saboda azaba, domin akan hannun ta faɗi, ta mik'e tana yarfa hannun tace "An rufe ɗin, idan akwai abinda zaka yi sai dai kayi, domin banga dalilin da zaisa ka tafi wayon shaye-shayenka ba ni kuma in bar k'ofa a buɗe, ta yadda wani zai shigo ya kashe ni, tunda na san kai ba damuwarka bace." "To dama ni me zai dame ni? Kada kiyi gigin kawo mun raini anan fa, dan Wallahi yanzu zanyi fata-fata da bakinkin nan na marassa kunya."6 "Naje nayi Sadam, sai dai idan kashe ni zaka yi ka kashe ni. Wannan wane irin bala'i ne?" Ta fashe da wani kuka, ga hannunta sai azaban raɗadi yake yi mata. Har ya buɗe baki zai yi magana, sai kuma ya fasa, ya juya ya shige ɗaki ya k'yaleta. Juyawa tayi ta bi bayanshi itama. Ganin ta shigo ɗakin yasa shi neman wuri ya zauna, yana kallonta, bata damu da shi ba, ta fara rage kayan jikinta zata canja wasu, inda shi kuma ya mik'e a fusace, zuciyarsa har wani tafasa take, ya runtse idanunsa, dan baya son kallon halittarta yanzu. "Me kike yi haka? Dallah malama kwashi kayanki ki fita a ɗakin nan tun ban tattaka ki a wurin nan ba." Bata tanka shi ba, haka kuma bata daina abinda take yi ba. A zuciye ya isa gabanta ya finciki hannunta ya wurgar da ita a kofar ɗakin, sannan ya dawo ya buɗe wardrobe ɗinsu ya dinga kwaso kayanta ya na watsar da su a tsakiyar d'akin, daga k'arshe ya sa k'afa yayi kwallo da su, wasu kuma ya kwasa ya watsa a saman fuskarta. "Daga rana mai kamar ta yau, idan kika k'ara gigin zuwa kusa da ɗakin nan, wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi. Wawiya kawai, an gaya miki zan iya k'ara haɗa gado da mai ciki ne?" Mikewa tayi tana gyara zanin jikinta, cikin takaici ta fara takawa zuwa inda yake, tana nuna shi da hannu, yayin da hawayenta suka cigaba da gangarowa wani na bin wani. "Amma ka cika butulu Sadam, maci amana wanda bai san mutunci ba. Ni zaka watso ma kaya waje dan saboda baka da mutunci ko?" Hannunsa ya dunk'ule ya kaiwa bakinta naushi, idanuwansa har wani rufewa suke saboda tsabar bala'i. "Ni kike ce ma marar mutunci? Ke kin san da wa kike magana kuwa? To zan gwada miki cikkaken rashin mutunci yanzun nan, ba wai sai anjima ba." "An faɗa maka ɗin, wanda bai san darajar mutane ba." Ta juya da sauri zata shige ɗayan ɗakin, amma yayi saurin kama gashin kanta da k'arfi, ya juyo da ita tana fuskantarshi, sannan yasa k'afa ya kwasheta ta faɗi, bai barta haka ba, sai da ya k'ara yin k'wallo da ita, sannan ya nuna ta,6 "Idan ke tak'amarki rashin kunya, to ki sani ni ba'a yi mun in k'yale, idan kuma kin cika cikakkar marar kunya gobe ma ki k'ara, nima ba zan taɓa gajiya da azabtar dake ba." Ya k'ara hankaɗar da ita, sannan ya juya ya shige ɗakin, ya mayar da k'ofar ya rufe. Kuka ta dinga yi mai cike da da-na-sani da nadama, ta kasa motsa ko da yatsanta ne, tunanin rayuwar da ta jefa kanta ta kawai take yi. Wani abu da ta ji yana bin k'afafunta ne ya sanya ta kurma wani ihu, domin a zatonta cikin jikinta ne ya zube, da sauri ta shiga ɗaki ta kunna fitila, ashe fitsari ne ta saki a wurin saboda azabar dukan da Sadam yayi mata. Hamdala tayi, tare da shafa mararta, a haka ta shiga toilet ta gyara jikinta, har kuma yanzu bata daina zubar da hawaye ba.7 《》 Haka zaman na su ya cigaba da tafiya Jay tana cikin uk'uba da azaba kala-kala daga wurin Kazaure. Har cikinta ya girma, ya fito sosai, amma Sadam bai daina k'untata mata ba, asalima bai taɓa jin zai iya tausaya mata ko a zuwa gaba ba. K'arshe ma daina zama gidan yayi, ya ga damar yayi tafiyarsa ya kwana biyar ba tare da ya san halin da take ciki ba. Yau ma kwananshi ukku kenan baya gidan, ba tare da ta san inda ya nufa ba, ga ciki yayi girma haihuwa na iya zuwa cikin ko wanne lokaci, inda ko riga k'waya daya, Sadam bashi da niyyar siya ma babyn. A kullu yaumun tai mishi maganar, bai damu da larurar da ke gabanta ba zai bubbige mata baki, yace ta nemi uban babyn ya siya mashi kaya. Tunda ta tashi yau take jin wani irin yanayi a tattare da ita, take wata dabara ta falo mata, hakan yasa ta mik'e ta hada kayanta cikin wani ɗan madaidacin akwati, ta rufe ko ina na gidan, ta fito ta tare taxi ta shiga. Gidan Sheik Mal. Goni ta dosa, duk da ba wai zata iya ganewa ba, domin rabonta da gidan tun ranar da aka daura masu aure. Cikin ikon Allah ta samu mai taxi ɗin da ya san unguwar, amma duk da haka sai da suka sha tambaya, sannan suka gano gidan. Bayan ya sauke ta ta ɗauki jakarta ta wuce ciki, kai tsaye part ɗin Mal. Goni ta dosa, inda ta same shi zaune yana karatun al-Qur'ani mai girma. Da sallama ta isa, ta samu gefe ta zauna, sai da ya kai aya, sannan ya rufe al-Qur'anin yayi addu'a ya shafa, ya juyo yana kallonta. "Ina wuni Malam." "Lafiya lau yarinya. Daga ina haka?" Hawaye ne suka k'wace mata, domin ita kanta ta san ta fita hayyacinta ta yadda ba lalle bane wanda ya santa a baya ya gane ta a lokaci guda ba. "Lafiya dai?" Maganar Sheikh Goni ta katse ta. "Jameela ce." Tayi maganar cikin sheshshekar kuka. "Jameela?" "Eh wacce muka taɓa zuwa nan tare da Faisal." Shiru Malam yayi yana nazari, daga bisani ya tsaida idanunsa akanta. "Tabbas anyi haka. Jameela ina mai gidan naki?" Har ta buɗe baki zata zayyana mishi komai, sai kuma wata zuciyar ta gargale ta, hakan yasa ta shafe hawayen ta gyara zama sannan ta fara magana. "A wurin aiki ne aka tura shi Lagos domin yin wani aiki na wasu 'yan kwanaki, to kasan bamu san kowa ba a garin nan, shine yace inzo nan in zauna saboda halin da nake ciki dan kada na zauna a gida ni laya babu mataimaki." "To Masha Allahu, wannan ai ba abun kuka bane Jameela, nan ma ai duk gida ne, babu wata damuwa, hakan yayi dai-dai da kuka yi wannan dabarar. Tashi mu je ciki." Ta mik'e ta ɗauki jakarta, Malam yayi gaba tana biye da shi zuwa cikin gidan. 5 Bangaren Hajiya Malaa uwar gidan Mal. Goni suka dosa, kasancewar nan ne inda ta taɓa kwana a farkon zuwanta gidan. Bayan sun gaisa Malam yayi mata bayanin Jay, sai a lokacin ta gane ta, ba'a samu matsala ba dattijuwar ta anshe ta hannu bibbiyu, tare da tausayawa halin da take ciki. Anan Malam ya fita ya barsu, yayin da Hajiya ta shigar da ita ɗaki, ta sa aka kawo mata abinci mai rai da lafiya. **Bayan Kwana Biyu. Tunda ya shigo harabar gidan ya hangi gate ɗinsu a kulle, bai ida gaskatawa ba sai da ya isa wurin, ya ganshi gark'ame da k'aton padlock. Parking yayi ya fito ya dumfari wurin, tabbas abinda ke faruwa kenan, gashi baya da extra key balle ya buɗe ya shiga. "Ina yarinyar nan ta nufa?" Yayi maganar a tsawace, sai dai bashi da ansar tambayar, haka ya koma cikin motar ya kwantar da seat, ya shingiɗa yana jiran yaga ta ina zata ɓullo. Wasa-wasa har la'asar, babu Jay babu bayaninta. Cikin k'unar zuciya ya tada motar ya fito yana tunanin wurin zuwa, k'arshe dai ya juya motar ya ɗauki hanyar Shehu Laminu way, zuwa Kyarimi Park, ko ba komai ya kalli tsirrai da namun daji ya samu kwanciyar hankalinsa. A wani ɓangaren na zuciyarsa yana k'iyasta kalar azabar da zai yi ma Jay idan ya dawo. Gudu ya cigaba da yi sosai, zuciyarsa na wani irin tafasa, har ya isa wurin yayi parking, ya fito da k'aton sunglasses ɗinshi ya ɗora, a hankali ya fara bada takun faɗi, yana takawa a gadarance, ya isa ya siya ticket, sannan ya shige ciki. Yanayin wurin kaɗai ya tafiyar da bak'incikinshi cikin ɗan lokaci, yana jin wani farinciki na mamaye dukkan wani lungu da sak'o na zuciyarsa. Ya ɗauki kusan awa daya a nan yana kalle-kalle, sannan ya fito ya bi wata hanya da yaga mutane da yawa suna bi, wanda mafi akasarinsu fararen fata ne mazauna k'asarmu. Wani tsauni mai tsawo ya ke hangowa, ya cigaba da tunkarar wurin, nan ya tadda wani sign board din da aka rubuta 'Mandara Mountains.' Zubi da tsarin wurin sosai ya k'ayatar da Sadam Kazaure ba kaɗan ba, har ya rink'a jin tamkar ba a Nigeria yake ba, kasancewar yadda rana tayi k'asa tana so ta fadi, tayi ja-ja da kuma yadda halittar dutsen ta k'awata wurin, sai abin ya bada wata irin siffa ta daban, mai daɗin kallo, tare da wani irin kyau, wanda ya fi gaban misali. 2 "Nature is beautiful." Cewar Sadam a bayyane, yayin da ya matsa daf da wani mutum ya mik'a masa BlackBerry Bold5 ɗinshi "Dan Allah malam ka ɗan yi mun pic mana." "No problem." Mutumen ya anshi wayar, shi kuma ya gyara tsayuwarsa, mutumen ya saita ya kashe mai hoton da ya daɗe bai yi irinsa ba. Godiya yayi mishi ya anshi wayar, ya cigaba da zagayawa zuciyarsa fes-fes, sai da maghriba ta kawo kai, sannan ya fito. Wurin da yayi parking ya dawo, yana k'ok'arin buɗe mota, ya ji an dafa kafadarsa. A firgice ya juya, ganin Faisal Goni yasa shi washe hak'ora, ya mik'a masa hannu suka tafa.1 "Faisal Goni. Longtime? Ya abubuwa? Sadam ya faɗa hannunsa cikin na Faisal, fuskokinsu taf da murmushi, tare da jin daɗin ganin juna. "Kazaure sarkin kirki. Ina nan fa, kai dai ba ka yada zumunci ba." "Wallahi abubuwa sai Alhamdulillah. Ya wajensu Malam?" "Duk kowa lafiya. Ina Jameela fa?" "Fine itama. Tana gida." "Masha Allah. Sai a haka ake ganinka kai dama. Sai kuma yaushe kenan?" "Haba, kada kace haka mana. Za ka jini in sha Allah. Zan shigo da na samu lokaci." "To shikenan. Allah yasa, a gaishe da amarya." "Zata ji in sha Allah." Da haka suka k'ara shan hannu, sannan suka yi sallama kowa ya kama gabansa. Koda ya koma har yanzu gidan a kulle ya me, lokaci guda zuciyarsa ta k'ara dagulewa. "Wannan wace irin wawiya ce? Wa ma ta sani a garin nan da zata je wurinsa? Kar dai gida ta koma?" Duk shi ɗaya ya ke wannan maganar, haka zalika bashi da wanda zai taimaka masa da amsoshin tambayoyinsa face Jameela. Ganin wankin hula na neman kai shi dare, yasa ya kira wani colleague ɗinshi (abokin aikinshi) mai suna SS Tafseer, yana tambayar ko yana gida. Suna gama wayar ya tada motar a sikwane, ya fita harabar gidan baki ɗaya. **11:30 (PM) Ciwon da take ji a yanzu ya ninninka wanda ta rink'a ji ranar da ta zo gidan Mal. Goni. Zaune tayi dirsham a tsakiyar ɗakin Hajiya Malaa, inda ita kuma Hajiyar ke kwance saman gado tana ta sharar bacci abinta. Wata irin azaba Jay ta rink'a ji, tamkar ranta zai fita, hakan yasa ta fara wani nishi mai sauti, wanda ya farkar da Hajiya Malaa daga nannauyan baccin da take yi. A gaggauce ta diro daga gadon ta kama ta, "Lafiya? Ba dai nak'uda ba?" Bata iya bata ansa ba, sai hawaye da suke kwarara a idanuwanta, waɗanda ba na azabar ciwon da take ji bane, na tunanin ashe haka Goggo tayi nak'udarta, amma har ta iya bijere ma umarninsu? Lallai hak'k'insu kadai, ba zai barta ta ji dadin rayuwa ba. Ga shi yanzu ta biyo k'aton da ta ke tunanin yana sonta fiye da su, ashe bai ma san daraja ko mutuncinta ba.4 Mik'ar da ita Hajiya tayi, anan taga wani ruwa na zuba a jikinta, alamar tana gab da haihuwa, da sauri ta zaunar da ita ta warci hijabi ta fita. "Barin kira Malam." Ta wuce cikin gaggawa zuwa part ɗin Mal. Goni. A tare suka fito bayan ta sanar dashi halin da Jay ke ciki, suka mik'a zuwa wani part da ke gaba kaɗan da nashi. Sunan Faisal Malam ya fara kira, cikin sa'a idonshi biyu, ya fito da sauri ya iso gabansu. "Malam lafiya? Ya akayi ne?" "Kaga, ta shi fito da mota ku kai yarinyar can asibiti." "Wace yarinya kenan?" "Yarinyar nan Jameela mana, da ka taɓa kawo su nan, ita da mijinta, tashi maza da Allah." "Jameela?" Ya nanata a k'asar zuciyarsa, mamakin abinda ya kawo ta gidansu yake yi, haka nan dai ya mik'e ya fito da motar, amma kan shi ya riga ya gama kullewa, yana buk'atar k'arin bayani. Hajiya na ganin ya juya, itama ta koma ciki da sauri domin ta fito da ita, sai dai tana saka k'afarta dakin, jariri na faɗowa, tare da tsallara wani irin kukan da ya sata k'arasawa ciki a sikwane. Taimaka masu ta fara yi, sannan ta fara k'ok'arin gyara wurin, tana cikin aikin Malam ya shigo domin jin dalilin da ya hana su fitowa. "Ina zuwa na tarar ta sauka. An samu 'yar budurwa kaga." Tayi mishi nuni da yarinyar da ke k'udundune a cikin zani. "Masha Allah." Malam ya fada lokacin da ya kai hannu ya ɗauki kyakkyawar yarinyar mai asalin kama da Kazaure tamkar yayi kaki ya tofar. Kiran sallah yayi mata a kunnuwanta, yayin da Hajiya ta cigaba da gyara wurin ta gama, sannan ta shiga toilet ta taimaka ma Jay ta gaggasa jikinta, ta kamo ta suka fito. Ruwa mai zafi ta ɗauko ta yima yarinyar wanka itama, sannan ta dubi Jay "Bani riga a saka mata saboda sanyi." Bata kula da abinda take faɗa ba, domin ta daɗe da faɗawa duniyar tunanin kirki irin na jama'ar gidan Mal. Goni wanda suka mutunta ta suka karrama ta, ba tare da sun san ko ita ɗin wacece ba. "Jameela" Hajiya ta kira ta, firgit, ta ɗago da idanuwanta da suka ciko da kwallah. "Na'am Hajiya." "Ba ni riga in sanya ma yarinyar nan." Kame-kame ta fara yi, tana dudduba ɗan akwatin da ta zo da shi "Wallahi ban riga na siya kayan ba, da yake Sadam ya yi tafiya, kuma a zato na har zai dawo kafin na haihu." "Da gangan kika yi wannan saken Jameela. Haihuwa ai shirya mata ake yi. Ko dan wannan ne na farko a wurinku shi yasa. Gashi kuma dare ya riga yayi balle a fita a siyo. Dole dai ayi hak'urin zuwa safiya." Bata ce komai ba, tayi k'asa da kanta, hawaye ne ke kwarara a idanunta, ta kasa yin k'wak'k'waran motsi, yau itace ta haihu ake neman rigar da za'a sanya ma ɗiyar duk irin isa da iko da kuɗin da ta tashi a ciki. Lallai wannan ba komai bane illa jarrabawa ta Allah, wanda ya kan jarrabi bayinsa da kalolin k'addara, mai kyau ko kuma kishiyarta. A haka suka kwana Hajiya Malaa na ɗawainiya da su, washe gari Mal. Goni ne ya ɗauki alhakin siyen duk wani abu da Jay da jaririyarta zasu buk'ata. Ko da Faisal ya shigo da safe ya tabbatar ma idanuwansa Jameela ce, fita yayi ya kira wayar Sadam yana tambayar ina Jameela. "Tana gida, ni na fito office." "Kaje dai ka duba. Amma bana tunanin tana gida kamar yadda ka faɗa." "Me kake nufi?" "Ka fi ni sani Kazaure." Ya kashe wayar, yana tunanin abinda ke faruwa. Kiran Sadam ne ya shigo masa, ya ɗaga ya kara wayar a kunne "Ka yi confirming ko?" "No, wait please, ka ganta ne?" "Wato baka ma san ina ta shiga ba ko? Wane irin zama kuke yi ne haka?" "Lafiya lau fa, nayi tafiya na dawo ban sameta ba. Idan ka ganta ne ka sanar da ni da Allah." "Tana nan gidan Malam yanzu haka, tare da babyn da ta haifa jiya cikin dare." "What? Haihuwa?" "Sosai kuwa." Innalillahi yake nanatawa a ranshi, a k'arshe yace "ga ni nan zuwa da zaran na fito lunch in sha Allah." "Sai ka iso." A tare suka kashe wayar, Sadam ya koma cikin bankin, amma ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunanin irin muzgunawar da zai yi ma Jay da abinda ta haifa yake yi, domin kuwa ba zai taɓa yarda a lak'aba mishi 'ya ace ta shi ce ba.9 I didn't get a chance to edit well well👏👏👏 Let's rock this shaa😍👏 Gudu ya dinga rafsawa, hakan yasa ya isa gidan cikin ɗan k'aramin lokaci, zuciyarsa a hargitse yayi parking ya fito, kai tsaye part ɗin Mal. Goni ya dosa da sallama, sannan ya tura kansa ciki. "Wa alaikumus Salam. A'aha, wannan kamar Sadam ai. Shigo mana." "Nine Malam." Ya faɗa lokacin da ya cire takalmansa, sannan ya shiga ya zauna tare da tank'washe k'afafunsa ya k'ura ma zanen carpet ɗin dake shimfiɗe k'asar palon ido. "Malam Barka da aiki, da fatan mun same ku lafiya.?" "Lafiya lau. Alhamdulillah. Har ka dawo kenan?" Ya buɗe baki zai tambaya daga ina? Sai kuma Malam ya cigaba. "Ai a ranar da ta zo take ce mun an tura ka aiki Lagos da kwana biyu ita kuma ta haihu. Nace lallai kunyi dabara da kuka yi tunanin kawo ta nan, da a gida zata haihu baka nan." Dariyar yak'e Sadam yayi, yana sosa kai, zuciyarsa na harbawa, ya daure yace "Eh wlh, yanzu ma ita nazo ɗauka ai." "Kai haba dai? Ba za ka barta ta ɗan k'ara kwana biyu ba? Kasan jikin mai haihuwa yana buk'atar taimako."+ "Haka ne, ai akwai wata da zata cigaba da taimaka mata a can ɗin."5 "To Masha Allah. Barin sanar da ita ta fito." Ya mik'e ya shiga ciki, lokaci zuwa lokaci ya kan kalli agogonsa, a zuciyarsa ya dinga addu'ar kada Allah ya kawo Faisal har sai sun bar gidan. A cikin gida kam artabu aka sha da Jay kan baza ta koma ba, hakan yasa Malam ya gyara zama yana tambayar "ko kuna da matsala ne?" Kamar ta faɗi masa ainahin yadda zaman nasu ya kaya, sai kuma ta tuna k'aryar da ta masa ranar da ta zo gidan, hakan yasa ta fashe da kuka ta k'ank'ame hannun Hajiya Malaa. "Bana son in rabu da Hajiya ne wallahi. Kuma idan na koma gida ban san wa zai cigaba da kula da ni kamar yadda take man ba." "Allah sarki." Cewar Hajiya Malaa. "Wannan ba wani abu bane Jameela. Kar ki damu, akwai abubuwa da zan baki da zaki cigaba da amfani da su, sannan kuma ki cigaba da kula da kanki, kamar yadda nake miki da ikon Allah zaki dawo jikinki na ainahi. Tsabta, abinci mai kyau, duk za su taimaka miki. Dan haka kada ki damu, idan kin samu lokaci kuma ai zaki dinga lek'o mu. Tashi maza ki shirya kayanki." "Nagode maku Hajiya, nagode, Allah ya k'ara rufa mana asiri baki ɗaya." "Amin Amin." Suka ansa gaba ɗaya har Malam da ya mik'e ya sa hannu ya ɗauki jaririyar dake cikin lallausan farin shawul ɗin da ya siya mata, sai kanshi take, ya juya ya fita, ita kuma Hajiya ta cigaba da taimaka mata tana haɗa kayanta. Har yanzu Sadam na zaune sai mazurai yake, da alama akwai rashin gaskiya a tattare da shi, a haka Malam ya shigo, gadan-gadan yayi kanshi ya mik'a masa jaririyar. "Kai mata addu'o'i, sai ka yi mata huɗuba dan bamu san sunan da kake son kiranta ba." What? Ni in ɗauki wannan abar? No it can't be.3 A zuciyarsa yake sak'e-sak'en nan, a fili kuma ya saki wata dariya dak'yar, yana duban Malam. "Wallahi ban iya ɗaukan yara ba Malam. Akwai wata rana da na ɗauki wani yaron k'anwata sai da na yi masa targaɗe saboda irin rik'on da na yi mishi. Sai sunyi k'wari tukun."6 "Subhanallah, a'a ni kam ba zaka karya mun mata ba, barin rik'e abata, idan Jameela ta fito ta anshe ta." Ya juya ya zauna da yarinyar yana k'are mata kallo, tare da tofe ta da addu'a, daga bisani ya ɗago yana kallon Sadam wanda ya tsura ma k'ofar shigowa ido, kamar mai jiran wani. "Ya kamata ayi mata huɗuba fa. Matso nan kayi mata a hannuna." Wata makirar dariya yayi wacce iyakacinta laɓɓansa. "Malam ai duk ɗaya ne, ka yi mata da duk sunan da ya kwanta maka." "Kai haba da Allah?" Malam ya tambaya fuskarsa cike da annuri, a zuciyarsa yana yaba alkunya irin ta Sadam Kazaure.2 "Sosai ma kuwa, ai ba wani abu bane." Cikin jin daɗi Malam yayi ma yarinyar huɗuba, ya ɗago da murmushinsa, "Gata nan an samu Rukayya. Sunan mahaifiyata ne. Allah yasa ta biyo ɗabi'u da halayenta." Sadam bai ce komai ba sai murmushin takaicin da ya fi kuka ciwo. A haka Jameela da Hajiya Malaa suka shigo, a gaggauce ya gaishe da Hajiyar, ya rink'a watsa ma Jay wani kallo mai nuni da 'zaki sani idan na kama ki.' Ya tashi yayi ma Malam sallama da wata godiyar munafunci ya fita ya shige mota. Jay kam kuka ta dinga yi, dak'yar ta anshi Rukayya suka fita, Hajiya ta fito da kudi ta damk'a mata, Malam ɗauke da kayansu, ya saka masu a motar itama ta buɗe gidan gaba ta shiga, Sadam ya figi motar a sikwane suka bar unguwar. Suna fita layin ya ja gefe yayi parking, hannu yasa ya toshe hancinshi, yana yi mata wani wulak'antaccen kallo. "Warin me haka nake ji kamar turaren 'yan bori?"1 Kallonshi take fuskarta cike da mamaki, me yake nufi? Ba dai haɗaɗɗiyar khumra da Hajiya Malaa ke mata wanka bace yake nufin tana warin 'yan borin? "Ke Dallah kwashi kayanki ki koma baya, ina magana kin tsare ni da idanunki masu kamar an shak'e mujiya." "Ba inda zan je. In kuwa na fita, sai dai ka maida wata gidanka ba dai Jameela ba." Steering ya saki, yasa hannu ɗaya ya tallabi k'irjinsa, ɗayan kuma ya tallabe haɓarsa kamar wata mace, yana jinjina kai yana kallonta. "Lallai kin ci abinci. Ni kike gaya ma magana haka? Bari kiga abinda zan miki." Ya fita ya zagaya ya buɗe k'ofar, sannan ya fincike ta, yana k'ok'arin fitar da ita. Ganin bai ko damu da Rukayya da ke kan cinyarta ba, asali ma k'ok'arin fitar da ita ya cigaba da yi, yasa ta fashe da kuka tana daka masa wata gigitacciyar tsawa. "Da Allah Malam ka saurara ma rayuwata. Kai wane irin mutum ne marar tausayi? Haba Sadam. Ka dubi yarinyar da ke jikina ka mutunta ni ta dalilinta mana." Dariyar 'yan bariki ya saki, ya ɗago da kanta yana kare ma yadda take kukan kallo, daga bisani ya sake mata fuska ya fara magana. "Ni me ruwa na da yarinyar dake jikinki wanda har zai sa in tausaya mata? Kinga da Allah malama fito mun a gaban mota ki koma baya in taimaka in kaiku gida in ba haka ba kuma idan kina da kudi fita ki samu acaɓa ya k'arasa da ke, cuz I've a lot to do na saki na taho wurinki." Hawayen idonta basu tsaya ba, ta ɗago su ta saita idanunta a kanshi tana girgiza kai. "Ko da ruwanka ko babu, baza dai a taɓa canja ma tuwo suna ba, 'ya dai 'yarka ce, komai zaka faɗa ba zai taba canja hakan ba. Sake mun hannu in fitar maka a motar da kai kanka kasan na fi k'arfin ka wulak'anta ni saboda ita." Sakinta yayi ya ja gefe yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ta gefen kumatunsa, ya matsa yasa k'afa ya murje yatsun k'afarta da ta ziro waje tana shirin fitowa. "Wannan motar da kike gani, a yanzu ko duka danginki zasu taru baza ki taɓa maganin kamar ta ba. Dan haka ki iya bakinki, tun ban faffasa shi a bakin titin nan ba." K'ara ta saka, tana kiciniyar k'wace k'afarta, sai da ya murje ta da takalmanshi, sannan ya ɗaga ya matsa gefe yana jiran ta fito. Bayan ta fito tana ɗan ɗingisa kafar, kamar zata shiga motar, sai kuma tayi gaba tana cewa "Mugu kawai, Allah ya isa." Tuni ya cafko ta ya buɗe bayan motar ya tura ta. "Ina kike tunanin zaki je? Ni da ke ai mutuwa kawai zata raba mu, dan haka babu inda zaki tafi. Ke ko kin tafi ma sai na nemo ki na cigaba da gana miki azaba. Kin manta zaɓata kika yi a kan iyayenki, ta ya ni kuma zan bari ki suɓuce mun? Shiga muje akwai horo mai tsanani wanda ya dace da masu taurin kai irinki, sannan kuma ki gaya mun wanda ya baki izini kika tafi gidan Mal. Goni."4 Rukayya ta matse gam a k'irjinta, tana kuka, har sai da irin rik'on da ta yi mata yasa ta tsallare da wani irin kukan da yasa Sadam yayi saurin shigewa motar ya ja suka ɗauki hanyar gida. A k'ofar gidan yayi parking ya fito ya buɗe boot ya ciro kayansu ya watsar, sannan ya juya yana kallonta. "Me kike jira da baza ki buɗe gidan ba?" Kallon nashi take itama, lokacin da take k'arasa fitowa a motar. "Amma ai kana gani yarinya ke hannuna ko? Sai ka rik'e ta in buɗe, ko kuma ka ansa ka buɗe k'ofar kai." "Lallai kina da aiki yarinya. Babu daya da zanyi a ciki, dan haka ki saɓa 'yarki ki goya, ki buɗe mun gida in shiga Dallah." Hakan kuwa aka yi, ta goya ta a baya, sannan ta buɗe gidan ta juya tana kallon yadda ya harɗe jikin motar sai cika yake yana batsewa. Yau da tana da wani gata, da babu dalilin da zai sa ta cigaba da zama da wannan mugun mutumen wanda bai san darajar ɗan Adam ba. Tunaninta ya katse sa'adda ya iso ya bangaje ta, ya shige ciki kafaɗarsa sagale da jakar da ya ciro ta kayanshi daga boot ɗin motar. Kayanta ta kwasa itama, ta shiga da su ciki, kai tsaye ɗakin da ya koma nata ta wuce, tana k'ok'arin kwantar da Rukayya a saman gado ya shigo a gadarance ya tsaya bakin k'ofar rik'e da k'ugunshi. Babu riga a jikinshi, daga shi sai singlet da dogon wando, sai slippers ɗin dake sanye a k'afarsa. "Je ki share mun ɗakin can, bacci nake son yi naga yayi k'ura da yawa bazan iya kwanciya a ciki ba." "Shara? Haba Sadam ka tausaya mun mana, yau fa duka-duka kwana na ukku da haihuwa. Ka bari jikina ya dawo gare ni mana." Ta koma ta kwanta a gefen Rukayya, ta juya mashi baya. "Ke ba magana nake miki ba?" Shiru tayi bata tanka shi ba, kuma bata da niyyar juyowa ta ansa shi. Hakan ya bashi damar k'arasawa cikin ɗakin ya farɗo k'afafunta da suke rabi saman gado, rabi ta mik'ar da su, ta faɗo tsakiyar ɗakin, bai jira komai ba ya warci hannunta ya shigar da ita ɗakinsa ya wurgar, yana wani irin huci ya fara nuna mata hannu. "Wallahi, wallahi, kinji na rantse, ko mutuwa kika yi kika dawo sai kin gyara d'akin nan kin wanke mun toilet, I don't bloody care."1 Dakewa tayi itama, ta mik'e tana murza hannunta ta isa gabansa fuskarta a murtuke. "Ba zan share ba Sadam, ai ba jaka bace ni da zaka na treating dina kamar wacce ka samu a arha a garaɓasar yak'i. Nima mutum ce kamar ka, wacce ta san ciwon kanta."1 "Oh really? Ashe kinsan ciwon kanki kika wulak'anta iyayenki kika biyo wani wanda baki da guarantee na zai kula da ke ko ba zai kula da ke ba? To bari kiji in gaya miki a wuri na baki da banbanci da wacce na ciyo a garaɓasar yak'i, dan haka dole kiyi abinda nake so, saɓanin haka kuwa ba komai zai jaza miki ba sai bala'i da tashin hankali. Wuce ki fara aikin da na saka ki."4 "Ka fad'i duk abinda yayi maka, Amma kada ka manta yaudara da mayaudaran kalamanka ne suka yi tasiri a kaina, har suka sa na bijire ma iyayena na biyo ka, wannan ne ma yasa bazan taɓa yafe maka ba har izuwa k'arshen rayuwata. Kuma bazan yi sharar ba, sai dai kayi duk abinda zaka yi." Mari ya wanka mata, sannan ya shak'i wuyan rigar ta. "Ke kin san da wa kike magana kuwa? Zan iya illata ki a banza a wofi, kuma na illata banza wallahi, idan har baki yi abinda nace da ke ba."1 Hannuwanta duk biyun tasa ta tokare k'irjinsa, ta fashe da wani irin kuka mai zafi, tana bubbuga gaban rigarsa da hannayen nata, sai dai bai ma san tana yi ba, kasancewarshi mutum mai cikakkar halitta, har sai da tayi iya k'arfinta ta gaji, sa'adda ya cafke hannun, ya wurgar da ita a tsakiyar ɗakin ya fita ya ɗauko mop, da tsintsiya ya wurga mata, ya jawo k'ofar ya datse, ya tsaya bakin k'ofar. "Idan kin tabbatar kin share kin gama komai, kiyi mun magana in buɗe ki. Marar kunya kawai." Ya koma Palo ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana girgiza k'afa, zuciyarsa na wani irin tururi na hayak'in bacin rai. Kuka ta saki tun k'arfinta, ta fara bubbuga k'ofar, Amma Sadam yana ji yayi kunnen uwar shegu da ita, haka tayi zaune a wurin saboda k'arfinta ya kusa k'arewa, ta cigaba da shafe hawayen da ke saukan mata wani na bin wani, har ta fara jiyo kukan Rukayya sama-sama, da sauri ta ɗauki tsintsiyar ta fara share ɗakin, yayin da kukan yarinyar ya cigaba da tsananta, amma ko motsi Sadam bai yi ba balle ayi tunanin zai iya taimaka mata. A gurguje tayi komai ta gama, ta wanke toilet ɗin ta goge, sannan ta dawo bakin k'ofar tana bubbugawa a hankali. "Sadam ka buɗe ni dan Allah." Sai a lokacin ya tashi ya koma bakin k'ofar, ya kara kunnensa, yana jin yadda take magana k'asa-k'asa cikin sheshshekar kuka. Cikin wata irin kakkausar murya yace, "kin gama abinda na saka ki ne?" Shiru tayi bata ansa shi ba, haka yasa ya kuma maimaita maganar a karo na biyu. "Nace kin gama aikin da na saka ki?" "Please, ka taimaka ka buɗe ni, baka jin yarinyar can na kuka ne? Have mercy mana, please Kazaure." Ai kamar ta tunzura zuciyarsa, ya buga k'ofar da k'arfi. "Ki bani ansa mana, if not sai dai ki kwana a ɗakin nan wallahi. I don't give a damn!" "Na gama." Tayi maganar a sanyaye cikin wata irin murya mai ban tausayi. Key ya ciro a aljihunshi, ya bude k'ofar, tana rakuɓe a gefe tana share hawayen da suke sintiri akan fuskarta. Da sauri ta mik'e zata fita, yasa hannu ya cafko ta "Babu inda zaki je sai na tabbatar da aikin da kika yi idan ya gamsar da ni tukun." A tsiwace ta juyo itama. "Dallah sake ni inje ga 'ya ta, tunda kai baka san darajarta ba." Hannunsa ya dunk'ule, ya nuna ta da shi "ko dai ki rufe mun bakinkin nan, ko kuma in farfasa shi muga na tsiwa. Wuce muje." Tsaye tayi ta k'i motsawa, ba tare da tace komai ba, sai kunkuni da take ta faman yi, har kuma yanzu hawayenta basu tsagaita ba. K'eyarta ya tura suka shiga toilet ɗin, sannan ya fito ya dudduba cikin ɗakin, komai dai gashi nan tsab, hakan yasa ya kalleta "Allah ya taimake ki yarinya, amma yau da sai kin yaba ma aya zak'inta. Fita anan ki bani wuri." Yayi wurgi da hannunta, ta juya tana share hawaye, ta fita tana yi mishi Allah ya isa a cikin zuciyarta. ** Zaune take a palo wurin k'arfe biyar na yamma ya fito yayi wankansa ya haɗe cikin bak'in wando da farar t-shirt mai gajeran hannu k'irar polo, k'afarsa sanye da bak'ak'en slippers din maza na Zanotti. Sumarsa da ya taje, ta mik'e tsaye irin ta 'yan duniyar matasan nan, sai hakan ya k'ara fito da kyakkyawar fuskarsa, ba kamar yadda wani saje ya fara kwanta masa luf-luf yayi wa kyawawan jajayen labbansa da suka fara komawa bak'ak'e ado. Baki ta sake tana kallonshi, tana jin lokacin da wani abu yayi mata karan tsaye a k'ahon zuci. Soyayyarsa da take dannewa ce ta bijiro mata, har ta rink'a jin tamkar ta mik'e ta rungume shi, ko dan ta shak'i daddaɗan k'anshin turaren da ke fita a jikinshi.2 "Bani abinci da Allah kin k'ura ma mutum ido kamar wacce baki taɓa ganin mutane ba. Please kada ki ja in faɗi mana."1 Borin kunya ne yasa tayi k'asa da idonta, tana kallon Rukayya, ba tare da tace da shi komai ba. "Baki ji me nace bane?" "Amma ai kasan babu wani abu da yayi saura na abinci a gidan nan. Nima fitowarka nake jira." "Ni zaki faɗa ma haka? Duka-duka yau three months fa da na kawo kayan abinci. Kina nufin kin dafe su kin cinye?"1 "Menene kayan abincin da kake magana? "Oh k'arya zan miki kenan? Kin dai kwashe abinci kin siyar kin zo nan kin zauna kina ce mun ba abinci, wato ni ga mai kudin banza ko? To wallahi sai dai yunwa ta kashe ki." "Allah ya kiyaye mun wannan halin tsiyar, kai ma ai kasan ban gaji tsiya ba, cikin arzik'i na tashi gaba da baya." "Ke dallah rufewa mutane baki, ina arzik'in da kike magana yanzu? You better shut that your mouth up kafin in zubar miki da hak'oran kin nan." Banza tayi mishi, ya juya ya zuba hannayensa a aljihu, ya cigaba da buɗawa, ya fita ya barta a wurin, hakan ya bata damar k'are ma cikakkar halittarsa kallo.Rayuwa a gidan Sadam Baffa Kazaure rayuwa ce mai cike da tsantsan tashin hankali, rashin wadata, rashin gata, da rashin daraja a matsayin Jameela Kasad na mace mai isa da iko, wacce ta tashi cikin gata, soyayya, da tattali na iyayenta. A haka zaman na su ya cigaba da wanzuwa cikin tsananin matsi da takura tamkar ba masoyan da suka yi k'aura domin cimma burin soyayyarsu ba. Sun kasance tamkar wasu gagaruman mak'iyan da aka yi ma auren dole, aka tura su wata duniya ta daban.3 Duk wasu kalaman yaudara da Sadam yayi amfani da su wurin saye zuciyar Jay, yanzu sun tashi a tutar babu, sai ya zamana tamkar babu wata kalmar so da ta taba gittawa tsakanin masoyan guda biyu. Zama dai kawai suke yi da juna na dole, na babu yadda wani zaiyi da dan uwansa, yayin da ta bangare Jay, tana zaune da Sadam saboda rashin inda zata dosa, dan ta san ko tasha giyar wake, bata isa ta tunkari iyayenta a halin da take ciki ba. Har zuwa lokacin da aka yaye Rukayya Sadam bai daina k'untata ma rayuwar Jay da 'yartasa ba, har ya kai ga yarinyar ta fara gane irin karan tsanar da ya dauka ya dora musu, ta yadda bai taba damuwa da ita ko abinda ya shafe ta ba, haka zalika idan ta tunkari inda yake ba zai duba k'ank'antarta ba, zai daka mata tsawar da zata razana ta, ya zara mata manyan idanunsa dake daburta hankalinta, wani lokacin yasa k'afa ya dungure ta tamkar bai taba sanin inda yarinyar ta fito ba. Wannan ne yasa take masifar tsoronsa, matsawar yana wuri to bata iya motsi mai k'arfi har sai ta tabbatar da ya bar wurin. **Jan 30th, 2016 K'arfe goma sha biyu dai-dai na dare ya fito harabar Grand Pinnacle Hotel, hannuwan rigarsa a nannade zuwa gwiwar hannun, k'afarsa babu ko takalmi, tafiya kawai yake tamkar mahaukacin da ya fara hauka a ranar. Kai tsaye wurin da yayi parking motarsa ya dumfara, zuciyarsa a hargitse kasancewar yadda wani hazik'in dan caca yayi mishi warwas, ya tatike duk wani abu da ya shiga wurin da shi tun daga kan kudadensa, agogon da ke hannunsa, har zuwa takalman da ke sanye a k'afarsa bai bar masa.4 Motar ya shiga, a sikwane ya fita a hotel din cikin kunar zuciya ya dinga rafsa gudu tamkar wanda zai tashi sama. Cikin sa'a babu yawaitar abun hawa a titi nan, kasancewar dare ya riga yi, duk wani mutumen arzik'i yana gaban iyalinsa a dai-dai wannan lokaci. Zuciyarsa a dagule ya kawo kofar gidan, ya fita ya bude gate ya shige da motarsa yayi parking, ya fito ya tunkari k'ofar shiga palon fuskarsa a murtuke kamar kowacce rana, sai dai bakin cikin da yake ji a yau ya fi na sauran kwanakin. Ga mamakinsa k'ofar a bude ya sameta, sabanin kullun da sai yayi ta faman bugawa kafin yake samu Jay ta bude mishi. Hannun k'ofar ya murd'a ya shiga, ya maida k'ofar ya rufe, ya juyo da zumar k'arasawa ciki, sai dai ya kasa d'auke idanunsa da suka yi kicibis da kyakkyawar surarta dake kwance tana bacci saman doguwar kujera, Rukayya na a k'asar carpet din dake shimfid'e tsakiyar palon. Zafin da ake yi a garin ne ya sanya ta cire rigarta, ta tsaya daga ita sai half vest, da wani dogon budadden purple skirt, wanda shima rabinshi ya tattare, hakan ya kara bayyanar da kyawawan surorinta muraran, a waje ana kallo. Idanuwansa da ya shigo dasu kunshe da masifa ne suka fara washewa, ya gagara sauke dubansa a kanta, yana yi mata wani mayen kallon da ba zai iya tuna lokacin da yayi mata irin shi ba domin kuwa tunda ya gane tana d'auke da cikin Rukayya bai k'ara jin yana sha'awar kusantarta ba sai fa a wannan lokacin da yake ganin tamkar an k'ara k'awata surar jikin nata ne. Kanshi ya girgiza ya shafe idonsa, a zuciyarsa yana ayyana barasar da ke kansa ce take dibarsa, har ma take k'awata masa surorinnata, dan kuwa a ganinshi Jay bata da sauran wani abu da zai gani har ma yayi sha'awa a wannan lokacin. Da wannan tunanin ya juya a hankali ya fara tafiya zuwa d'akinsa, sai dai kuma mayun idanunsa sun gagara kauda kansu akan k'irjinta da ya cika sosai tamkar bata taba shayarwa ba. Dawowa yayi cikin sand'a kamar wani barawo ya isa gaban kujerar yana cigaba da kallonta, baccinta take sosai hakan ya bashi damar duk'awa gabanta passionately ya fara shafa gefen fuskarta. A hankali ta fara bud'e ido, a k'arshe ta sauke su a kan mutumen da ke tsugunne gabanta, wanda yayi nisa sosai a abinda yasa gaba. Da sauri ta mike a firgice tana tambayar "Me he haka kuma?" Bai bata ansa ba ya mik'e cikin borin kunya ya tura hannuwansa cikin aljihu ya fara tafiya, daga bisani ya juyo yana kallonta "Ki same ni a dakina." Bata ce komai ba, ta mik'e tana k'ok'arin d'auke Rukayya, sai a lokacin ta lura da yanayin da jikinta ke ciki. Da sauri ta zira rigar ta, ta dauketa ta kaita d'aki, sannan ta fito ta doshi d'akin Sadam. "Shigo mana." "Yau kuma? Ka manta ka bige mun warning akan shigowa d'akinka ne?" "Kinga, ba dogon zance nake so ba. Nace ki shigo." Bata k'ara cewa komai ba ta tura kanta ciki, ta samu gefe ta tsaya tana kallon ikon Allah. Gabanta ya iso da (contraceptive pilss) da ya ballo a hannunsa ya mik'a mata, ya d'auko wata gorar ruwa dake ajje a gefe, ya mik'a mata. "Sha kizo nan ki same ni."1 Ya koma bakin gado ya harde k'afafunsa. "Maganin me haka?" "Ki sha nace. Bana son dogon bayani." "Ba zan sha ba sai ka fad'i ko na meye." "Na planning ne, dan bazan kuma yin sakacin da nayi a baya ba." Tsayuwarta ta gyara, mamakin dake zuciyarta bayyane sosai akan fuskarta, 'wato dama maganin da ya rink'a bata kenan?' Kawar da tunanin tayi duk kuwa da kasancewarta cikin alhini, ta had'e fuska tana dubansa. "To kai me ruwanka da bani maganin planning kuma? Ko har ka manta da ka daina hada gado da me ciki ne?" "Hak'k'i na nake buk'ata, so ki sha maganin nan tun muna cikin laluma, ki zo nan ki same ni." 'Lallai wannan shi ake kira da SABON SALON D'A NAMIJI.'5 Abinda ta fada a kasar zuciyarta kenan, a fili kuma ta kalle shi tace "Amma baka tsoron Allahn ka Sadam. Kai yanzu banda rashin kunya har kana da bakin da zaka daga kace kana neman hak'k"inka a wuri na? Kai yaushe rabon da ka sauke nawa hak'k'in da ya rataya a wuyanka?" Labbansa na k'asa ya cije, ya rasa abinda zai fada, kawai ya mik'e a fusace ya isa gabanta ya warce maganin ya fara k'ok'arin tura shi a bakinta. A karo guda itama ta fara kiciniyar k'watar kanta, sai dai k'arfinsu ba daya ba, tuni ya kai ta k'asa, sannan ya fara kiciniyar matse mata baki. Ganin yana shirin illatata yasa ta bude bakin, ya tura maganin, tare da warto gorar ruwan da ta fadi gefe ya bude ya tsiyaya mata, bai jira komai ba ya fara cire kayan jikinsa. Hannayenta ta hade, ta mak'alkale zuwa k'irjinta, zuwa yanzu, idanuwanta sun fara fara kawo ruwa. Bai bi ta kanta ba ya fara k'ok'arin cire mata kaya itama, sai dai tasa hannu ta rik'e skirt dinta gam-gam, hawaye na kwarara a idanunta. "Ki rufa ma kanki asiri ki bar ni nayi abinda nayi niyya. Idan ba haka ba ke zaki wahala a banza a wofi, wallahi, domin kukan ki ba zai hana ni aiwatar da abinda nayi niyya ba." "Me zai hana ka kashe ni kawai in huta da wannan azabar da kake mun Sadam. Na gaji. Na gaji da halin k'asak'anci, da bak'incikin da kake cusa ma zuciyata." Tayi maganar tana dukan gaban k'irjinsa da ya matso daf da ita yana k'ok'arin had'a jikinsu. Bai bi ta kan maganar ta ba, haka kuma bai damu da yadda take bugunshi ba, yasa k'arfi ya farka rigar dake jikinta, kasancewar hankalinsa gaba d'aya baya tare da shi ko alama. Kuka ta saka mai k'arfi, tare da toshe idanunta da duk hannuwanta biyu, hakan ya ba shi damar aiwatar da abinda yayi niyya cike da mugunta da rashin tausayi, sannan ya mik'e ya shige toilet ya barta tana cigaba da zubar da wasu zafafan hawaye.2 Har ya gama abinda yake ya fito, amma tana wurin a kwance, sai da ya ji tausayinta kadan ya tsirga zuciyarsa a daidai lokacin, hakan yasa ya taka zuwa gabanta yasa hannu da niyyar ya tayar da ita, amma ta buge hannun ta mik'e a bala'ince ta tofa masa yawun da ya cika mata baki. "Mugu azzalimi. Bazan taba yafe maka ba Sadam. Ka ci amana ta. Allah sai ya saka mun wallahi. Da izinin Allah zaka ga sakamakon cutar da ni da kake yi." Towel din jikinsa yasa ya share yawun da ta tofa masa ya mik'e zuciyarsa na wani irin tafasa. Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya dawo da baya ya d'auke ta da wani wawan marin da ya sa ta hango taurarin da suke yawo a sararin samaniya. "Be careful, you bloody fool." Yasa hannu ya warce ta ya fitar waje, sannan ya dawo ya mayar da k'ofar ya rufe, ya zauna bakin gado yana mayar da numfashi.1 Mik'ewa tayi dafe da kuncinta ta wuce d'aki tana zubar da hawaye ta gyara jikinta, ta fito ta canja riga ta kwanta a gefen Rukayya ta k'ank'ame ta tana wani irin kuka a hankali wanda ke taba zuciyar dukkan wani mai saurarenta.2 Da tunanin abinda ya wakana Sadam ya kwanta, hakan yasa washe gari tun kafin su tashi ya fita ya bar garin ma kwata-kwata, duk kuwa da ya san basu da isasshen abincin da zai wadacesu su ci a iya kwanaki biyar din da zai yi na tafiyarsa. Haka suka cigaba da zama a wahalce, cikin tsananin matsi har zuwa ranar da ya dawo.1 CIGABAN LABARI **Sadam A waje yayi parking ya fita ya shige cikin gidan da niyyar ya kai masu abincin da ya siyo, ya fito ya kama gabansa. Mamaki ne sosai shimfiɗe a kan fuskarsa, ta yadda ya hango k'ofar palon a wangame. Bai yi k'asa a gwiwa ba ya cigaba da tunkarar wurin, har ya isa bakin k'ofar yasa hannu yana shafa wurin da aka bige yana tunanin wanda yayi wannan gagarumin aikin. Cikin ɗan lokaci zuciyarsa ta motsa, wani irin tururin tashin hankali ya fara tashi, ya mike, ya wuce ciki ya fara duba kaf ɗakuna da kitchen, har ma da toilets ɗin gidan, amma wayam, babu kowa sai k'aran fans ɗin dake wulwulawa a ɗakuna da palon gidan. A hargitse ya fito, k'irjinsa sai dukan tara-tara ya ke yi, hankalinsa gaba ɗaya baya jikinsa, ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana tunanin inda Jay ta dosa a cikin halin da ya barta. Ta wani ɓangaren kuma yana tunanin wanda ya fitar da ita, kasancewar ya san ko mak'wabtansu babu wanda suke mutunci da shi, babu wanda ya taɓa shiga gidansu, kamar yadda suma basu taɓa shiga gidan kowa ba. "Faisal Goni." Abinda ya faɗa a bayyane kenan, domin kuwa kaf mutanen da yake hulɗa da su cikin garin Maiduguri babu wanda ya san gidansa bayan Faisal Goni. "Zai gane ba shi da wayo. Sai na yi mishi rashin mutuncin da sai ya ji dama bai taɓa sani na ba a rayuwa." A haukace ya fito gidan, bai tsaya kullewa ba ya shiga ya figi motar ya ɗauki hanyar gidan Mal. Goni. Tun a hanya ya fara kiran wayar Faisal, da sallama ya ɗaga yana faɗin "Kazaure sarkin kirki. Ashe har yanzu kana ajiyar number ta." "Sosai kuwa, saboda irin wannan ranar. Ina matar mutane?" "Matar wa kenan?" "Kada ka raina mun hankali Malam. Ina matata?" Dariya Faisal yayi, "I don't know what you're talking about. I'm sorry." "Zaka sani idan na zo na same ka. Wallahi sai kayi da-na-sanin sani na a rayuwarka. In banda rainin hankali, ya zaka zo har gidana ka ɓalla mun k'ofa ka fitar mun da mata, kuma in kira ka kana cewa baka ma san zancen ba. Zaka sani idan na faffasa maka baki."12 "Hey. Take it easy mana. Ni tunda na sanka ma ban taɓa taka hanyar gidanka ba. And ka faɗa mun idan na ɗauki matarka ina zan kaita? Ni me ma yayi haɗi na da wata matarka? Kawai dai kana k'untata ma yarinya ta gudu ta kama gabanta, kai kuma ka zo nan kana tada jijiyoyin wuya. Shawarata gare ka tun dare bai yi maka ba ka san inda zaka nemi matarka, cuz ni rabona da Maiduguri ma yau wata guda kenan. Ina Lagos wurin aikina."2 Ya kashe wayar, ya bar Sadam yana banbami, bakinsa har kumfa yake saboda masifa, haka kuma bai daina tunkarar gidan Mal. Gonin ba. A k'ofar gidan yayi parking ya fito, ya jingine jikin mota, kasancewar sallah da ya ga ana yi a masallacin da ke jikin gidan, wanda ya tabbatar Malam ne limamin da ke jan al'ummar wurin. Sai da suka gama, a kan idonsa kowa ya gama fitowa amma babu mai kama da Faisal a ciki, a haka Malam ya fito shima, yayi saurin shan gabansa, ya bashi hannu suka gaisa, sannan suka shige ciki.1 A palo suka zauna, shiru na ɗan lokaci ya ratsa tsakaninsu har sai da Malam yayi gyaran murya, ya na mai duban Sadam, fuskarsa ɗauke da murmushi. "Sadam lafiya kuwa? Yau kaine a gidan namu." Kamar yana jira, ya ɗago da manya-manyan idanunsa da suka yi jajir yana kallon Malam. "Babu lafiya Malam, Faisal ya je har gida ya ɓalle mun k'ofa ya fitar da Jameela." "Faisal? Wane Faisal ɗin ma wai tukunna?" "Faisal nawa ka sani ne?" Yayi maganar yana wani juya kai, irin na marassa ɗa'a.3 "In dai Faisal nawa ne yaushe ma ya zo garin? Kuma me ye alak'arshi da matarka?" "Ina zan sani ni? Ka dai mishi magana kawai ya fito mun da mata tun muna mu biyu." "Dakata da Allah, abin duk bai kai na haka ba. Barin kira shi muji." Ya fitar da wayarsa ya lalubo number Faisal ya danna kira, bugu biyu zuwa ukku ya ɗaga tare da sallama. Hands free Malam ya saka, ya ajje wayar a k'asa ta yadda kowa zai iya jin maganar da za su yi. "Me yayi haɗinka da matar Sadam Faisal? Yaushe ma ka zo garin ban sani ba?" "Ya Salam. Ba dai wurin ka mutumin nan ya zo ba? Ya kira ni fa, na faɗa mishi ni rabona ma da Maiduguri yau wata ɗaya cif-cif, amma dan ya raina hankalin mutane shine zai zo maka. To wai ni me ye haɗina da wata matarshi can?"2 "Ka saurare ni da kyau. Kana jina?" "Ina ji." "Idan kana da masaniyar inda matarshi take ka sanar da ni tun muna mu biyu." "Malam wai baka yarda da ni bane? Wallahi ban sani ba. Mutumen nan bashi da kirki wallahi, watak'ila takurar da yake yi ma yarinyar ne yayi mata yawa ta gudu, dan naji ance bashi da hankali kuma mashayin giya ne." A take idanun Sadam suka k'ara juyewa, dan masifa har wani yellow-yellow yake yi, a hargitse ya sa hannu ya warci wayar kamar Faisal na kallonsa ya fara nuna wayar. "Zaka gane hauka na idan muka haɗu da kai, wallahi sai na illata ka, sai na zubar maka da hak'ora idan baka fito mun da matata ba. Babu wanda ya san gidana a duk faɗin garin nan bayan kai."2 Ya wurgar da wayar, ya mik'e a fusace ya fita.1 "Sadam. Sadam. Sadam.." Mal. Goni ya dinga kiransa, amma yayi kunnen uwar shegu da shi, ya fita ya buga mishi k'ofa, yayin da shi kuma ya bi bayansa da kallo yana girgiza kai, a zuciyarsa yana addu'ar 'Allah ya kyauta.'1 **Jay. Har suka bar unguwar bata daina zubar da hawaye ba, sai da taga mutumen yayi parking gaban wani restaurant, bai ce mata komai ba ya fita ya anso masu abinci, sannan ya dawo ya shiga ya tada motar suka cigaba da tafiya. "Ka sauke ni a nan ma ya isa, nagode da taimakonka." Bai ko kalle ta ba, balle ta sa ran samun ansarshi, domin kuwa zuciyarsa ta gama karyewa a irin yanayin da ya same ta a ciki, haka kawai ya ji yana buk'atar taimaka mata, idan da hali ma yana son sanin ainahin labarin rayuwarta. Gidanshi da ke Old GRA suka dosa, gida ne tsararre ginin zamani, ya shiga ya samu wuri yayi parking, a dai-dai lokacin wani matashin da bai wuce shekaru ashirin da biyar ba ya fito hannunsa rik'e da na wani yaro wanda a k'alla zaiyi shekara ukku zuwa hudu. Ganin sunyi parking yasa yaron ya k'wace hannunsa, ya ruga da gudu ya isa inda suke, a lokacin SS ya buɗe motar ya fito, tare da ɗaga yaron sama yana dariya. Dariya yake yi sosai shima, a haka ya zagaya ya buɗe ma Jay k'ofa, ya ɗauko ledar abincin da ya siyo yayi gaba zuwa cikin gidan. Duk da bai ce mata komai ba, buɗe k'ofar da yayi ya tabbatar mata yana nufin ta fito ta shigo, hakan yasa ta ziro k'afafunta a hankali ta fito Rukayya saɓe a kafadarta, ta tunkari k'ofar da ta ga sun shiga. Babu kowa a palon, sai tv da ke ta faman aiki, sai wani sanyin AC mai haɗe da k'anshi mai daɗi, da ya daki hancinta a lokaci guda. Gefe ta zauna, sannan ta kwantar da Rukayya wacce har yanzu baccinta take yi, a haka ya fito yana kiran Farouq. Wannan matashin ne ya fito daga wani ɗaki ya iso gabansa yana faɗin "Sannu da zuwa Yaya." "Yawwa, taimaka mun da plates da cups da abin sha da Allah." "Okay." Ya juya zuwa kitchen, shi kuma ya isa wurin da ya ajje ledar abincin da ya shigo da ita, ya ɗauko ya kawo gaban Jay, a lokacin yaron ya fito daga ɗakin da SS ya fito ya rugo ya haye bayansa. "Haba Jafar. Yanzu fa ka girma ya kamata ka daina hawa na haka nan. Kalla nan, kaga ga sister nan na kawo maka ku dinga wasa, amma banda cin zali kana ji na?" Dariya Jafar yayi, lokacin da ya sake shi ya ruga wurin Rukayya yana taɓa fuskarta, ya kalle shi yace "Daddy da gaske zata zauna a wuri na? Wannan kuma ai dai Mammy ce ko?" "Sosai kuwa. A nan zata zauna ku rink'a zuwa school din su Uncle Farouq, kuna yin wasa tare." Hannunta ya fara jijjigawa yana dariya, hakan yasa ta tashi a baccin, yadda yake mata wasa ita ma sai ta washe ta dinga k'yalk'yala dariya, duk kuwa da cewar a rayuwarta bata san kowa ba bayan mahaifiyarta. A haka Farouq ya iso da tray ɗauke da plates, spoons, da cups ya ajje a k'asa ya koma ya kawo masu abin sha, sannan SS ya kalle ta, "Sauko ki sa mata abinci." Bata yi gardama ba ta sauka ta sa masu abincin, a tare suka rink'a ci ita da Rukayya da Jafar wanda suke ta wasansu tamkar sun daɗe da sanin juna. Abincin ya ɗauka shima ya ɗauki plate da spoon ya juye ya koma kan table yana ci, sai dai hankalinsa gaba ɗaya yana kan su, tausayin matar da bai san ko wacece ba ya dabaibaiye dukkan jijiyoyin jikinsa. Bayan sun gama cin abincin ne ta tashi ta tattara wurin, ta haɗa plates ɗin wuri ɗaya, tana shirin ɗaukewa ta tsinkayi maganarsa. "Ki bar shi Farouq zai ɗauke. Jafar kaje ka nuna ma Mammy ɗakinta tayi wanka ta huta ka ji." Ya k'arasa maganar yana kallon ɗan kyakkyawan yaron da ke gabansa. Da sauri ya mik'e ya kama hannunta ya fara ja, hakan yasa ta saki murmushi mai haɗe da wasu zafafan hawaye, ta kama hannun Rukayya suka doshi hanyar da Jafar yayi. Ga mamakinta ɗaki ne lafiya lau na mace, ta yadda taga takalma da jakunkunan mata a jere, tsab-tsab. A bakin gado ta zauna tana k'are ma ɗakin kallo, a zuciyarta kam ta rasa tantance yanayin da take ciki, shin farincikin rabuwa da Sadam take ko ko bak'inciki? Ta wani ɓangaren kuma tana tunanin inda zata dosa daga nan. A k'arshe dai mik'ewa tayi ta shiga toilet tayi wanka, ta yi ma Rukayya, amma yadda Jafar yasa rigima shima sai anyi mishi, dole ta fara yi musu, sannan tayi ta fito Cikin ɗan k'ank'anin lokaci ta ji yaron ya shiga ranta, ganin yadda tunda suka zo gidan ya kasa matsawa ko ina yana mak'ale da ita yana kiranta Mammy, yana wasa da Rukayya. Hakan yasa ta fara tunanin ko ina ta shi Mammyn ta nufa? Sai da ta shirya yaran, sannan tayi sallolin da ke kanta, gamawarta kenan, ta mik'e tana ninke sallayar SS yayi sallama a bakin k'ofar ɗakin. Bayan ta ansa shi, ta k'arasa ninke sallayar, ta fita ta same shi tsaye gefen k'ofar hannunwansa cikin aljihun farar jallabiyar dake jikinshi. "Idan babu damuwa ina son muyi magana da ke." "Babu komai." Ta faɗa lokacin da ta fito a ɗakin, yayi gaba ta rufa masa baya suka koma palon. Shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara, a k'arshe ya kai duba gareta, a nan ya fahimci ba k'aramin kyau Allah yayi mata ba, sai dai da alama wahala ce ta dafar da ita. "Astagfirillah." Ya faɗa a k'asar zuciyarsa, kasancewar yau ce rana ta farko da ya taba yi ma wata mace irin wannan kallon tun bayan rasuwar matarsa, abar kaunarsa. "Baiwar Allah, menene sunanki?" "Jameela." Tayi maganar muryarta a sanyaye. Shiru yayi sannan ya tsaida idonsa akan tv, ya cigaba da magana. "Naje neman gidan wani colleague ɗina ne a unguwarku, kwatsam sai na ci karo da case ɗinki. Idan bazan takura ki ba, zan so inji ainahin labarinki, da dalilin da yasa kika samu kanki kulle a cikin gida babu mataimaki." Tun bai kai k'arshe ba hawaye suka fara ambaliya akan kumatunta, kuka sosai ta fara rerawa hadda sheshsheka, yayin da ta ke girgiza kanta, hakan ya k'ara haifar da tausayinta da son taimaka mata a zuciyarsa. "Babu komai a labarina face tur ga masu ɗabi'a da halaye irin nawa. Babu komai a labarina face da-na-sani, da takaici a wurin iyayen da suka haifi 'ya mai irin halayena. Malam kayi hakuri, amma labarina baya tattare da komai illa tashin hankali, nadama da kuma da-na-sani wanda watak'ila har k'arshen rayuwata bazan daina yinsu ba." Ta k'ara fashewa da wani irin kukan da ya rink'a taɓa zuciyar SS Tafseer, ya kuma k'ara masa kwaɗayin son sanin labarin nata domin yana ji a jikinshi shi ne zai zama silar warwarewar matsalolinta. "Kada ki damu Jameela. Kada kuma kisa wannan a ranki, ki daure ki sanar da ni, ta yadda zan taimaka miki, in fitar dake daga halin k'uncin da zuciyarki ke ciki." "Kayi hak'uri bawan Allah, amma bana tunanin akwai wani taimako da zaka mun bayan wanda ka riga ka mun. Nagode da wannan, amma ba zan iya sanar da kai babban kuskuren da na tafka a rayuwata ba." "No please. Kada muyi haka da ke mana. Naga neman taimako bayyane a cikin idanunki Jameela, please, I beg of you to lemme help you. Kiyi hak'uri ki sanar da ni mana." Girgiza kai ta cigaba da yi, a k'arshe ta mik'e da sauri ta kama hanyar ɗakin data fito, a haka shima yayi saurin mik'ewa ya sha gabanta. "Kada ki biye ma son zuciya, ki hana kanki amfani da damar da kika samu. A yadda na fahimta, labarinki na cike da wasu al'amurra wanda tunanina kaɗai ba zai iya fassara su ba har sai kin taimaka wurin sanar da ni. Idan kika yi haka Jameela, zan zame maki wata katanga da zaki jingina jikinta domin samuwar maganin matsalolin da kike ciki. Ki daure ki sanar da ni. Dan Allah."+ "Kayi hak'uri, amma mutane irina basu dace da wata katangar da zata jiyar da su daɗi ba, face in cigaba da yawo a cikin duniya har izuwa lokacin da Allah zai anshi rayuwata." Cikin wani matsanancin kuka take maganar, hakan kuma ya k'ara dagula lissafi da tunaninshi, sai dai bai yi k'asa a gwiwa ba, ya cigaba da rok'onta yana haɗa ta da Allah da ma'aikinsa, har sai da ta ji ita kanta tana son sanar da shi labarin da bata taɓa sanar da kowa ba, labarin da take kwana da shi ta tashi da shi, wanda yake sanya bugun zuciyarta k'aruwa a duk lokacin da ta tuna gingimemen giɓin da ta yi ma k'uruciya, da rayuwarta baki ɗaya. Bata ce komai ba, ta juya ta koma cikin palon ta zauna, hakan ya bashi damar dawowa ya zauna shima ya zuba mata idanu yana kallonta. "Nayi kuskuren wulak'anta iyayena akan namijin da bai san daraja ko mutuncina ba. Mutumen da ya raba ni da farincikina, ya raba ni da iyayena, ya kuma sa na wulak'anta babbar aminiyata. Mutumen da bai san k'ima ko daɗin kyautar da Allah mahalicci yake yi ma bayinsa ta 'ya'ya ba. Mutumen da ya ɗaukaka sana'arsa ta caca da shan giya fiye da 'yarsa da matar da yake aure. Malam ina mai tabbatar maka cewar a duk faɗin duniyar nan ban taɓa cin karo da mugun mutum, azzalimi, maha'inci, marar tausayi, wanda bashi da imani, marar tsoron Allah kamar mijina Sadam Kazaure ba." Wayar SS da ke rik'e a tsakanin hannuwansa biyu da ya haɗa wuri ɗaya ce ta sunɓule ta faɗi k'asa, idonsa a waje ya ɗago yana kallonta. "Sadam Kazaure?" "Sunanshi kenan. Shine mutumen da ya wulak'anta mun rayuwa ya mayar da ni ba kowan kowa ba, duk kuwa da irin gata da soyayyar da iyayena suka nuna mun." "Dakata tukun. Kina nufin gidan da na same ki shine gidan da naje nema na aminina, abokin aiki na Sadam Kazaure?" "Shakka babu. Nan ne gidanshi." K'asan carpet ya sauko ya zauna, zuciyarsa na wani irin k'una, a karo guda ya tank'washe k'afafunsa yana kallon Jay, dak'yar yayi k'arfin halin ɗaga bakinsa "Ki cigaba ina sauraren ki." Zamanta ta gyara itama, tare da share hawayen da suka ɓata mata fuska, ta fara bashi tarihin soyayyarsu da Kazaure, tun daga ranar da suka fara haɗuwa har izuwa ranar da ya taimaka ya fitar da ita daga uk'ubar da take ciki, ba tare da ta rage komai ba, daga rayuwar rashin 'yancin da tayi a gidan Sadam Baffa Kazaure. Shiru na dogon lokaci ne ya cigaba da wanzuwa a cikin palon, yayin da Jay ke share hawayenta, tana wata irin sheshshekar kuka mai cike da nadama da da-na-sanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. "Alal hak'ik'a labarinki ya fi gaban tunanina Jameela. Sai dai ba wannan ba ne zai sa ki yanke k'auna daga rahamar Allah ba, wanda na tabbata wannan yana cikin k'addarar rayuwarki. Na tabbata wannan itace ishara da Allah ya ke son nunawa iyayen da basu damu da tarbiyyar yaransu ba, kuma ki ɗauka cewar wannan wata jarabawa ce da Allah yayi miki, wacce mutum mai k'arfin imani ne kawai zai iya cinye ta. Ki yi hak'uri ki share hawayenki, da izinin Allah zan taimaka miki, zan sada ki da iyayenki domin ki samu damar neman yafiya a gare su."5 Kuka take tana girgiza kanta. Idanunta sun rine, sun fita daga ainahin kamaninsu, hancinta yayi ja sosai abinka ga farar fata. "Bana tunanin Baffa na zai iya yafe mun. Haka dangina baki ɗaya. Na kasance mutum ta farko data fara ɓata sunan zuri'armu, haka kuma nice mutum ta farko wacce ta bijirewa umarnin mahaifinta a kaf faɗin zuri'armu. Ka gaya mun da wane ido zan kalli iyaye na? Kana tunanin ina da bakin da zan nemi gafararsu? Ta yaya zasu gafarta ma 'yar da ta ɗaukaka farincikin wani k'ato akan farincikinsu? Ba zan taɓa komawa gida ba, na gwammaci na k'are rayuwata a haka har izuwa lokacin mutuwa ta."1 "Wannan wata magana ce wacce bata da tushe kike yi. Ki cire wannan a zuciyarki, ki rungumi k'addarar da Allah ya ɗora miki, domin na tabbatar a yanzu kinsan minene rayuwa, kin kuma san wanene namiji. Dan haka ki manta da komai, ki fara tunanin dai-daita rayuwarki, da yadda zaki kula da tarbiyya da rayuwar yarinyarki. Ni kuma na miki alk'awarin in sha Allahu jibi idan Allah ya kaimu Juma'ah, zan kai ki har cikin gidanku domin sada ki da Goggo da Baffanki. Ki shiga ki kwanta, zamu k'arasa magana idan Allah ya kaimu."1 Bai jira ansarta ba ya mik'e ya fita harabar gidan, zuciyarsa har wani bugawa take da k'arfi saboda yadda yake jin da zai ga Kazaure a yanzu, da babu dalilin da zai hana shi shak'e masa wuya ya aika shi barzahu. Agogon hannunsa ya kalla k'arfe goma har da wasu mintina na dare, hakan yasa ya hak'ura ya koma cikin gida, ya tabbatar zasu haɗu a banki da safe.2 **Sadam. Babu kalar tunanin da Sadam bai yi ba, amma ya kasa gano inda Jay zata nufa a duk faɗin garin maiduguri. Takaicinsa ba wai na rashin ganinta ba ne, na tunanin yadda zai zauna ba tare da ya cigaba da takura ma rayuwarta ba, har ta fahimci kuskuren da tayi na haihuwa da shi, domin ya lura duk abinda yake mata bai sa tayi nadamar haihuwar da tayi ba. Sai dai ya ci alwashin zai nemo ta a duk inda ta shiga, domin kuwa tunda ta zaɓi zama da shi, to kuwa bata isa ta suɓuce masa ba a kowanne irin yanayi zata tsinci kanta. Mik'ewa yayi da sauri, ya zari makullin motarsa ya fita, kai tsaye titin da zai sada shi da Grand Pinnacle Hotel ya ɗauka, domin kuwa yadda yake jin kansa na gab da bugawa, barasa ce kawai zata taimaka masa wurin samun natsuwar k'wak'walwarsa. Mintina goma sha biyar suka kawo shi bakin hotel ɗin, bayan ya shiga yayi parking yana k'ok'arin fitowa wayarsa dake ajje gefe ta fara ruri, hakan ya dakatar da shi, ya buɗe k'ofar motar tare da fitar da k'afarsa ɗaya waje, ya ɗaga wayar ya sanya a hands free, sannan ya k'arasa fitowa, yana k'ok'arin rufe motar.1 "Ya aka yi kake kira na yanzu? Saboda kasan anyi albashi ko? To dakata ka ji in gaya maka, idan kana tashi ka nemi na kanka gara tun wuri ka mik'e ka nemi naka, dan ni ba a wurinku zan lalace ba, nima babu wanda ya taimaka mun lokacin da nake nawa karatun."1 "Ba wannan bane yasa na kira ka ba ma wallahi, Baba ne bashi da lafiya sosai muna nan Kano asibiti, kuka kawai yake yana kiran sunanka, bai ma san ina da number ka ba, nine nayi tunanin in sanar da kai, dan Allah Yaya kayi gaggawar tahowa idan ba haka ba komai na iya faruwa wallahi."2 Tsayuwarsa ya gyara, a lokaci guda idanunsa suka juya, duk da fuskarsa dama babu annurin, amma maganar wanda ya kira shi ta k'ara tsananta bak'incikin da yake ciki. "Ya kira sunana yace mun me? Ko ya manta abinda yace da ni? Ka gaya mun wanda aka yi ma abinda akai mun ta yaya zai kuma kallon inda mutumen nan yake? To ka buɗe kunnuwanka da kyau ka saurari abinda zan faɗa maka, ko mutuwa mutumen nan yayi, kada ka sake ka kira ni. Ka dai ji abinda na faɗa maka."10 Ya ja wani mugun tsaki, yana k'ok'arin kashe wayar, ta ɗayan ɓangaren aka cigaba "Haba Yaya Sadam, duk fa abinda zaka faɗa baza ka taɓa canja shi a matsayin mahaifinka ba, kuma koma me ya maka ya kamata kayi hak'uri ko dan darajar kawo ka duniya da yayi, ka daure ka zo ka saurari abinda zai faɗa dan Allah, watak'ila abu ne da zai amfani rayuwarka gaba ɗaya, dan Allah Yaya ba dan abinda yayi maka ba." "Kai Dallah rufa mun baki, an gaya maka ni sokon mutum ne? Ko an gaya maka ina da lokacin ɓatawa? Ko kuma kana tunanin kare ya cinye mun zuciya ne? Ina so ka sani matsawar mutumen nan yana numfashi, to har abada bazan kuma taka k'afata garin nan ba, tunda dama ba kowa na ajje a garin ba."1 Yana gama faɗar haka ya kashe wayar ma gaba ɗaya, ya juya ya fara tafiya, yana tunanin da mai zai ji, da bak'incikin Jay, ko ko da bak'incikin kiran da k'aninsa ya mishi? Zuciyarsa a daburce ya shige ciki, tashin farko kwalbar barasa guda ya ɗaga ya zazzage a cikinsa, sannan ya k'ara buɗe ta biyu, har sai da ya kai ga ya kasa gane komai saboda irin giyar da ya tuttula ma cikinsa k'arshe ya rink'a jin kamar numfashinsa na ɗaukewa saboda azabar tashin hankalin da ke damunsa. Bai iya motsa ko da yatsar hannunsa ba, asali ma bai san abinda yake faruwa ba har sai da misalin k'arfe goma sha ɗaya na washe garin ranar. **Jay. K'arfe bakwai dai-dai na safiyar ranar alhamis SS ya fito da shirinshi tsab-tsab cikin bak'ak'en suit da farar riga daga ciki, k'afarsa dake ɓoye ciki rufaffen bak'in takalmin Alfani, ita ce ta fara yi ma Jay dake duk'e tana gyaran pillows ɗin kujera sallama, hakan yasa ta ɗago tare da gyara hijab ɗin jikinta tana k'are mashi kallo. K'anshin da ta shak'a na turaren Mediterranean (Elizabeth Arden) ɗinsa shi ya bata damar tuno da ɗan gayun Kazaurenta, wanda a kullu yaumun yake cikin daddaɗan k'anshin da ke kashe zuciyar mai shak'ar shi. "Ina kwana." Muryarsa ta doki dodon kunnenta, hakan ne kuma ya katse ta a tunanin da take. "Ina kwana. An tashi lafiya?" "Alhamdulillah, ba dai shara kike tunda safe haka ba? Da kin bari Farouq ya dawo school duk shi yake aikin gidan ma." "Ba komai ai." Tayi maganar muryarta a sanyaye. A haka Farouq da Jafar suka fito da shirinsu, da sauri Jafar ya isa ya kama hannunta yana washe hak'ora. "Ina kwana Mammy." "Ka tashi lafiya?" "Lafiya lau. Ina Rukayya?" "Bacci take yi. Ina zaka je haka?" "Daddy zai kaimu school ɗin su Uncle Farouq, shi kuma ya tafi wurin aiki ko Daddy? Kuma kullun haka muke yi." Yayi maganar yana kallon Babanshi. "Ni bazan ansa ka ba, tunda ka fito ko gaishe ni baka yi ba." Dariya yayi, ya koma gabansa yana cewa. "Na manta ne Daddy, barin gaishe ka yanzu. Ina kwana?" Dariya duk suka sanya, in banda Jay, a haka ya juya yana kallonta. "Zan je wurin aiki, akwai komai da zaku buk'ata a store. Jafar ka zauna kuyi wasa da Rukayya mana, kaga yau ba sai ka bi Uncle Farouq school ba ko?" "Daddy da gaske?" "Sosai mana. Ga Mammy zata dafa muku abinci mai daɗi." Da murnarshi ya juya da gudu ya shige ɗakin da Rukayya take, yayin da Farouq ya matso yana dariya. "Aunty ina kwana." Kunya ce ta lulluɓe ta yadda k'aton saurayi ke kiranta aunty, haka dai ta maze ta ansa shi da "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Har sun sa kai zasu fita, sai kuma ya dawo da baya "Yawwa, aunty da Allah idan za ki girkin nan ki ɗan sa da ni." "Wuce muje ni kada ka makarar da ni." Cewar SS suna dariya gaba ɗaya, a haka suka fita suka barsu a gidan. Wani irin yanayi take ji a tattare da ita, rabon da ta samu sakewa irin haka har ta manta, amma duk da haka tana tunanin halin da Sadam zai shiga, ba tare da ya san inda ta dosa ba, ta wani fannin kuma tana tunanin ba zai wani damu ba tunda dama ba k'aunarta yake yi ba. Sai dai ita ta kasa yakice tunaninsa a k'asan zuciyarta.13 **Sadam. Idanunsa ya fara buɗewa a hankali, sai dai ya kasa gane shin rana ce ko dare, kasancewar mashaya 'yan uwansa da ke zube a wurin suna ta kwasar baccinsu bil hak'k'i da gaskiya. Hannunsa ya duba da zumar gane lokaci a agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun, sai dai ga mamakinsa babu agogon kamar yadda ya tabbatar ya shigo wurin da ita. Bakinsa ya cika da iska ya furzar, kansa na wani irin sarawar da ya sanya shi saka hannu ya dafe kan, ya mik'e zaune. Wayarsa dake cikin aljihu ya fitar ya kunna, k'arfe goma sha ɗaya da mintina ashirin da biyu, hakan yasa shi mik'ewa tsaye da sauri, sai dai sauran barasar da ke jikinsa ta k'ara mayar da shi ya faɗi k'asa sharaf. Mik'ewa ya kuma yi a karo na biyu, ya fara bin bango ya fito wurin motarsa. Shigarsa ke da wuya wayarsa ta fara ruri, amma bai ɗaga ba, har sai da ya juya motar ya fita a hotel ɗin, sannan aka kuma kiran wayar a karo na biyu. A kasalance ya ɗaga yana tsaki, ya sanya ta tsakankanin kafaɗarsa da wuyansa, yayin da ya cigaba da tuk'i da hannuwansa duk biyun. "Saheeb ba nace kada ka k'ara kira na akan maganar nan ba? Ka bar ni inji da abinda ke damuna da Allah." "Yaya wallahi Baba na gab da mutuwa matsawar baka zo kun sadu da shi ba yanzu, watak'ila sai dai ku haɗu a lahira, tsakanin jiya da yau ya suma ya kai sau biyar, kuma duk farkawar da zaiyi sunanka ne kawai a bakinsa. Dan Allah Yaya ka sassauta zuciyarka, yanzu wannan ko ba mahaifinka bane ai ya kamata ace ka tausaya mishi, duk wani fushi da kake da shi a banza in har ya mutu da bak'incikinka. Dan Allah ka zo ka ji abinda yake son sanar da kai." "Maganar banza kenan. Me ya hana lokacin da ya wulak'anta ni baka yi masa wannan wa'azin ba? Ko sai ni da ka raina ma wayo? Idan ka kuma kira na akan maganar nan sai na sassaɓa maka kamanni wallahi."2 Ya kashe wayar ya wurgar, ya cigaba da rafsa gudu har ya isa gida, lokacin k'arfe sha biyu na rana, bai san ta ina zai fara bayani idan yaje banki ba. Wanka ya fara yi ya shirya, a haka wayar Saheeb ta kuma shigowa, a masifance ya ɗaga ya kara a kunnensa. "Zan ci u…" Maganar shi ce ta mak'ale jin muryar mahaifinshi cikin tsananin tashin hankalin da ya tabbatar masa ciwo na galabaitar da shi. Shiru yayi yana saurarensa, ya kasa cewa komai, har ya gama, a k'arshe ya kashe wayar ya zube a kujera, fuskarsa na bayyanar da alhini da tashin hankalin da yake ciki, bai ankara ba hawaye suka fara bin kumatunsa, shekara shidda cif-cif rabon da ya ji murya ko ya sa mahaifin nasa a idanuwansa. Haka kawai ya ji yana son ganin shi, duk kuwa da haushinsa da yake ji, ta wani ɓangaren kuma yana tunanin barin Maiduguri ba tare da ya san ina Jay take ba. "Zan dawo gare ta." Ya faɗa a bayyane, a karo guda ya mik'e ya fara haɗa jakarsa, ya fito ya wurga ta a bayan boot, ya rufe gidan sannan ya yi tunanin zuwa banki ya sanar da su, kafin ya wuce. Ganin har sun fito lunch, amma Kazaure bai zo aiki ba yasa SS fitowa, ya wuce inda yayi parking ya shige mota da niyyar zuwa gidanshi ko Allah zai sa ya ci karo da shi, ta yadda zai samu damar faffasa bakin mugu marar tausayi irinshi.1 Cikin rashin sa'a yana fitowa ya mik'a titi domin ya juya ya ɗauki hanyar gidan Sadam, a dai-dai lokacin shi kuma motarsa ta iso bakin bankin, a waje yayi parking ya fita da sauri ya shige ciki. Ba'a fi minti goma ba ya fito, ya kama hanyar ta dabo tumbin giwa, cikin tsananin fargaba da tunanin abinda zai tarar, duk kuwa da wani irin k'una da zuciyarsa ke yi. ** Ko da ya isa a kulle ya samu gate ɗin gidan, ya duba ko ina amma bai samu wanda zai tambaya labarin Kazaure ba, haka ya shiga mota ya koma, zuciyarsa a dagule tare da tsinewa maza masu halaye irin na Kazaure. Har aka tashi aiki bai samu daidaituwar tunaninsa ba, al'amarin Sadam ya gama ɗaure duk wasu jijiyoyin jikinsa, k'arfe shidda da rabi na yamma ya isa gida a gajiye, rigarsa ta sama tare da jakar laptop ɗinshi sagale a hannunsa na dama, ya shigo gidan da sallama. A palo ya same su zaune, Jafar da Rukayya na wasa, Jay na zaune a gefensu. Jafar na ganinshi ya tashi da gudu ya isa ya k'ank'ame shi yana dariya. "Sannu da zuwa Daddy." "Yawwa yaro na. Ina Rukayya?" Yayi maganar yana murmushi yayin da ya mik'a mata hannu yana mata nuni da ta taho, amma ta mak'ale kafaɗa alamar ta ki, k'arshe ma tashi tayi ta koma jikin mamanta ta kwanta, tana kallonsa a tsorace. Girgiza kai yayi, sa'adda ya k'ara jin wata k'iyayyar Kazaure, wanda ya wulak'antar da kyautar da Allah ya mishi, ga shi nan ta sanadiyyarsa har ya sa yarinyar tana tsoron mutane. A tausashe ya d'ago yana kallon yadda Jay tayi k'asa da kanta, tausayinta sosai yake ji, har yana ganin ta kamar k'anwarsa ta jini. "Jameela." "Na'am" Ta ɗago dara-daran idanunta, cikin rashin sa'a ta sauke su cikin nashi. "A'uzubillah." Ya faɗa a cikin zuciyarsa, kasancewar wata kibiya da tayi mishi suka a k'ahon zuciya. Dak'yar ya dai-daita kansa, duk kuwa da bai san menene dalilin da yasa yake rasa natsuwarsa a duk lokacin da ya kalleta ba, a matsayinta na matar aure, matar amininsa. "Tunda na fita nake neman Kazaure, sai dai har yanzu bamu haɗu ba, naje har gida amma ban same shi ba, cuz yau ko wurin aiki bai je ba. So wannan ba matsala ba ce, gobe zamu tafi in sha Allah, daga baya idan na dawo zan san duk yadda nayi na gana da shi" A firgice ta k'ara dagowa tana kallonshi, sai dai idanunsa na kan tv, bata iya furta komai ba, illa wasu ZAFAFAN HAWAYE da suka wanke mata fuska. Bai lura da halin da take ciki ba, ya mik'a mata ledan abincin da ya shigo da shi, ya kai dubansa ga Jafar "Ina Farouq ya kawo maku plates. Na san k'ila baku ci abinci ba ko?" "Mun ci abinci Daddy. Kaima ga naka can kan table Mammy ta dafa mana mai daɗi."1 "Chap, Yaya yau waye zai ci abincin waje? In gaya maka Aunty Jay ta mana wani girki mai daɗi da na ci kunnena har motsi ya dinga yi." Farouq ya yi maganar lokacin da ya k'araso cikin palon ya zauna, yana yi ma yayan nashi sannu da zuwa. "Kai ga ka ba gwanin cin abincin waje ba dama, dole kunnenka yake motsi." "Ai wallahi dan dole nake zaune garin nan, na matsu muyi hutu ko na tattara in koma gaban Hajiya in cigaba da cin abincinta mai daɗi." Dariya suka sanya a tare, SS ya kalle shi, "Ka ko ga gobe in sha Allahu zamu tafi, idan kana da sak'o ka bayar in kai mata." "Da gaske Yaya? Me zaka je yi Katsina gobe?" "Jameela zan kai gida." "Ai ko k'afarku k'afata, tunda dai ka ga weekend ne nasan kuma duk inda Sunday tayi kaima dole ka dawo." "Ka zauna kayi karatu. Ba ka ce mun exams zaka fara ba?" "Haba ai da saura Yaya. Allah nayi missing Hajiya ne." Jay dai saurarensu kawai take yi, bata tsoma bakinta ba har suka gama, sai da SS ya shiga ciki sannan ta kalli Farouq "Dama ba nan ne asalin garinku ba?" Dariya yayi ya ɗauki remote ya fara latsawa. "Haba aunty, ki ganni fari tas kice da ni yaron Maiduguri? Bari mana ai bana ma kama da bak'ak'en mutanen nan." Dariya ya bata sosai, hakan yasa ta murmusa tace "Ya suke ne su 'yan Maidugurin? Kuma ma na sani ko shuwa ne kai." "Bari mana aunty. Wannan Kt bobo ne." "Da gaske Katsina kuke?" "Eh wallahi." "To ya kuke da mai gidan nan?" "Yaya na ne same Mother same Father." Har ta buɗe baki zata kuma yin wata tambayar, sai gashi ya fito, hakan yasa tayi gum da bakinta, ta maida hankalinta a tv, k'arshe da taga bata ganewa ta mik'e ta koma ɗaki. "Amma ka san baka cikin jerin mutane masu imani ko?" SS yayi maganar idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, ya juya yana kallon yadda iska ke kaɗa bishiyoyin wurin cikin kwanciyar hankali, tare da busa musu sassanyar iska mai daɗi. "Ban fahimce ka ba. Wace irin magana kake yi haka?" "Baza ka fahimce ni ba dama, tunda ka kasance mutum marar tausayi, marar imani wanda bai san darajar mace ba. Ina tantama idan akwai zuciya a k'irjinka Kazaure. Ashe baka da mutunci ban sani ba? Ashe dama kana da MATA?" Wani irin bugawa zuciyarsa tayi har yana sa hannu yana dafe wurin, idanunsa a waje ya juya yana kallon shi, sannan ya cigaba. "Na daɗe ina jin labarin mazaje wanda su kan wulak'anta matayensu ta hanyoyi da dama. Da yawa cikinsu idan aka bibiya, laifin na matayen ne. Amma kai da yake ka kasance butulu, ma ci amana, da ka tashi sai ka wulak'antar da matar da ta baro iyayenta, ta biyo ka a matsayin mutumen da ta fi k'auna a gaba ɗaya duniyarta. Mutumen da ta mutunta, ta bama amanar ruhi da gangar jikinta. Mutumen da ta fawwala ma duk wata soyayya da ke cikin zuciyarta. Amma ka rasa ta wace hanya zaka saka mata, sai ta hanyar nuna k'yama ga abinda ta haifa, wanda ya zama gudan jininta, tsatsonta, abinda ya tsaga jikinta ya fito. Abun bai tsaya a nan ba, sai da ka haɗa mata da duk wani kalar wulak'anci na duniya da ka iya. Baka da imani Kazaure, haka zalika ina tantamar addininka, anya ma kana tsoron Allah kuwa? Ban san haka kake ba, da tun asali ban buk'aci saninka ba, da ban ɓata lokacina wurin aminta da kai ba. Ina mai shawartar ka da tun muna mu biyu ka bani takardar sakinta, tun mahaifinta bai yi maka mummunan ɗaurin, da igiya zata yi rara ba." Duk da bugawar da zuciyarsa ke yi, hakan bai hane shi sakin wani makirin murmushi ta gefen bakinsa ba. "Me kake so ka gaya mun? Wai kana nufin duk neman da nike ma Jay dama tana wurinka? Lallai yau zan ga wanda ya tsaya maka a duk faɗin garin nan, dan sai ka fito mun da mata ko in faffasa maka baki wallahi, domin kuwa zan yakice amincin da ke tsakanina da kai, in yi maka rashin mutuncin da hankali ba zai taɓa ɗauka ba. Ina ka kai mun mata?"1 Ya k'arasa maganar cikin wata kakkausar murya, da jajayen idanunsa a waje. A karo guda yasa hannu ya cakumi kwalar rigar SS. "Get your hands off me, you bloody fool. Sanin kanka ne, bani da lokacin da zan ɓata wurin faɗa da ɗan giya. Ka bani takardarta nace, tun ban canja maka kamanni ba." Hannuwansa da ya ke k'ok'arin dunk'ulewa SS ya rik'e gam. Kallonsa yake da idanuwansa a waje. "Don't you dare!" Ya wurgar da hannun ya faɗi k'asa, sannan ya cigaba. "Da kake maganar aminci, ai ni na daɗe da yakice ka a cikin jerin mutanen da na sani ma, balle kuma amini. In baka sani ba, ina da-na-sanin, sanin ka a rayuwata Kazaure. Rashin mutunci kuma da kake magana, dama ina za'a samu mutunci wurin ɗan caca, mashayin giya? Ka ɓata wayonka wallahi, ina tausaya ma Rukayya, dan na tabbata wata rana zata yi da-na-sanin kasancewarka mahaifi a gare ta. Sai dai duk ba wannan ba, ka bani takardar sakin Jay, shine kawai buk'atata, akwai wanda zai kula da ita da 'yarka, tunda kai baka san daraja da mutuncinsu ba." Duk da kasancewarshi ɗan cacan, haka zalika mashayin giya, amma a duk lokacin da wani yayi mishi wannan gorin, to fa sai yayi rashin mutunci ma ko wanene kuwa. Manya-manyan idanunsa da suka daɗe da canja kala zuwa ja, ya k'ank'ance. Kyawawan jajayen laɓɓansa, ya cije, a karo guda wata 'yar kwalla, ta yayyafo a gefen idonsa na dama, baiyi wata-wata ba, ya dunk'ule hannunsa ya kai ma bakin SS naushi. "Be careful!" Ya faɗa yana wani irin huci tamkar mayunwacin zakin da ya ci karo da nama, haka kuma gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa sun tashi, sun fito ruɗu-ruɗu ana ganinsu. "Ka san abinda bakinka zai faɗa a kaina, dan wallahi da ace ba kai ba ne, da babu abinda zai hana ni shak'e wuyan koma waye in aika shi lahira, in ya so nima sai dai a kashe ni. Kuma kayi gaggawar fito mun da mata, tun ban kai ga yin k'aranka ba." Hannu SS yasa ya na shafe jinin da ya fara ɗisa daga bakinsa, kallon Sadam yake irin duban da aka fiya yi ma marassa hankali, a lokaci guda yana sakin murmushi. Handkerchief ya cire ya dafe wurin, bai ce komai ba ya fara k'ok'arin buɗe k'ofar yana shirin fita. Farɗo shi Sadam yayi ya dawo da shi ciki, a karo guda ya danna central lock a motar. "Kana tunanin zan bar ka ka fita a wurin nan ba tare da ka sanar mun inda matata take ba? To wallahi baka isa ba." Bai ce komai ba, ya cire wayarsa ya fara k'ok'arin kiran wata number. Da sallama aka ɗaga ta wancen ɓangaren, bayan yar gajeruwar gaisawa, ya bukaci mai wayar ya haɗa shi da Jameela. Sai da ya tabbatar da an bata wayar, sannan ya danna hands free suka fara magana da ita. Wani wawan ihu Sadam ya saki tare da wartan wayar. "You can't leave me Jameela. Kinyi gangancin barin gidana. But trust me, I'll find you. Wallahi I'll. Definitely, I'll find you." Ya wurga ma SS wayar, ya kuma cakumar wuyan rigarsa. "INA KA KAI MUN MATA?" Yayi maganar da wata irin lion voice, sai dai ko gezau SS bai yi ba, haka ya sa hannu ya cire hannayensa da ke jikin wuyan rigarsa. Ganin ba shi da niyyar magana, yasa Sadam ya tada motar a sikwane, ya ɗauki hanyar gidan SS. Murmushin takaicin da ya fi kuka ciwo SS ke yi, ta wani fannin kuma yana jin kamar ya shak'e wuyan Kazaure ya mutu, kowa ma ya huta. A haukace ya iso k'ofar gidan ya fara danna horn tamkar zai banka gate ɗin ya shiga. Da gudu mai gadin ya zo ya buɗe k'ofar, kafin ya tura motar ciki, yayi wani wawan parking, ya fita ko rufe k'ofar motar bai yi ba ya shige ciki, sai dai ga mamakinshi, k'ofar palon a rufe take gam da makulli. Dawowa yayi ya same shi zaune a motar yana danna wayarsa, tamkar bai san abinda Sadam ɗin ke nufi ba. "Shiga ka fito mun da matata." "Kai ka ke ɓata ma kanka lokaci Kazaure. Sanin kanka ne a yadda ka ji muryar Jameela, kasan tana cikin kwanciyar hankalin da tasa ta manta da kai da irin bala'in da ka saka ta. Wallahi, ka ji rantsuwar musulmi kenan, ko ka yi shawarar rubuta mun takardar sakinta, ko kuma yanzun nan in saka ka cikin gidan nan in rufe, har sai na shaida ma mahaifinta ya zo da bataliyar police ɗin da zasu kama ka. Haka kuma idan kana tunanin akwai wata soyayyarka da tayi saura a zuciyar matar da ka muzgunawa, to kana yaudarar kanka. Ta daɗe da shafe babinka a littafin rayuwarta. Marar zuciya kawai." "Naka wasa ne SS. Jay tawa ce. Kai ɗin nan baka isa ka raba soyayyar da muka gina sama da shekaru shidda ba. Baka isa ka raba ni da ita ba, idan ka fasa kiran mahaifinta baka haifu a cikin naka iyayen ba. Idan baka sani ba ka sani, Jay baza ta iya rabuwa da ni ba, in fact, rayuwarta is incomplete without me! Kasa ido kayi kallo, zan nemo ta, zan dawo da ita gare ni, sannan kuma zan gwada maku gaba ɗaya kuskuren da kuka yi na neman raba ni da ita. Fitar mun a mota Dallah Malam." Kallonshi kawai SS ya ke, a zuciyarsa yana ayyana, anya Sadam bai samu taɓuwar hankali ba? "Baka isa ba Kazaure, domin kuwa ba ni nace ka kawo ni nan ba, kai kayi niyya ka zo, dan haka baka isa ka ajje ni nan ba, kasan ina da ayyukan yi a wurin aikina ai." K'ala bai ce ba, ya shiga motar ya ja a hargitse, ya fita gidan. A k'ofar bankin yayi parking, hakan ya ba SS damar fita, sai dai shi bai fito ba, sai ma reverse da yayi yana k'ok'arin barin wurin. Waya SS ya ciro a aljihunsa da niyyar kiran Baffa, ko me ya tuna kuma, sai ya maida wayar ya juya ya shige ciki. ** Gida Sadam ya wuce, ya rufe ko ina ya shige k'uryar ɗaki ya zauna yana wani irin numfashi, bai ankara ba ya ji hawaye na silalowa saman fuskarsa, wanda ya rasa gane ko na menene. Na tafiyar Jay ne, ko ko na halin da yake ciki ne? Bai sani ba. Hakan yasa ya fasa wani gagarumin ihun da hatta ɗakin da yake ciki sai da ya ansa. Kuka ya dinga yi wi-wi, irin kukan da ko da mahaifinsa ya rasu bai yi irinsa ba. Ya ɗauki a k'alla mintina talatin yana abu ɗaya, k'arshe wata dabara ta faɗo mishi, inda ya yanke shawarar kiran yayanshi Sa'id, ya faɗa mishi bashin da banki ke binshi, in ya so ko a kuɗin gadonshi ne a cire a bashi ya biya. Har ya fara kiran number sa, sai kuma wata zuciyar ta gargaɗe shi kan yin hakan tamkar ya tona asirin halin da yake ciki ne. Take ya kashe wayar, ya wurgar da ita, zuciyarsa na bashi shawarar cewar caca ce kawai zata kawo masa kuɗaɗen da ya ke da buk'ata. Da wannan shawarar ya aminta, a haka kuma bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi. **A week later. Tun daga waccen ranar, Sadam bai k'ara komawa banki ba, baya zuwa ko ina, kullun yana gida k'unk'ume a k'uryar ɗakinsa, illa idan ya ji bak'in ciki ya ishe shi, maimakon ya dinga kai kukansa ga Allah, kamar yadda Sa'id ya shawarce shi, a'a, sai dai ya fita ya siyo giyarshi, ya sha yayi tatul, har sai ya manta abinda ke yawo a cikin k'walwarsa, sai dai matsala ɗaya, da ke addabarsa ita ce, ko wace irin giya zai sha, dai-dai da rana ɗaya bai taɓa manta fuskar Jay, da yanayinta ba, wanda a yanzu yake ganin tamkar babu wata mace a duniya, da ke da zubi da tsarin surarta. Fitowa yayi, ya shige motarsa zuwa Hotel. Ba dan komai ba, sai dan saboda irin sa'ar da yake ji a tattare da shi, haka kuma ya gaji da zaman cikin gidan, dole yana buk'atar fresh air. A harabar Hotel ɗin yayi parking ya fito, ya rufe motar, kafin ya zarce zuwa ciki. Gefe daya ya samu ya zauna, bayan an kawo masa kwalbar barasa, yana korawa hankalinshi tashe, domin kuwa ya daɗe da yin bankwana da kwanciyar hankali. A sannu yake duban mutanen da ke zaune saman faffaɗan teburin da ake buga caca. Cak idonsa ya tsaya kan wani farin inyamurin mutum, mai cikakkar halitta da k'aton tumbi, jikinsa sanye da wani kakkauran leshi ɗinkin fadee, kansa sanye da hula, irin wacce suke lankwasawa ɗin nan. Ganin yadda kuɗi suka zauna ma mutumen yasa zuciyar Kazaure ta gama raya masa cewar ya samu wurin da zai tatsi kuɗin da zai biya banki bashinsu. Mik'ewa yayi da kwalbarsa a hannu ya isa wurin manajan da ke kula da wurin, bai yi wata-wata ba, ya ɗora makullin motarshi, kasancewar ita ce kaɗai abu mafi tsada da yayi mishi saura, ya juya ya koma kan teburin ya zauna, yayin da aka biyo shi da cards ɗin buga cacar. Sai da suka gama wacce ya samu suna yi, sannan ya ɗora na shi suka fara gwabzawa da inyamurin nan. Cikakkiyar awa ɗaya ba su yi da farawa ba, Sadam ya samu nasarar ciyo zunzurutun kuɗi nera dubu ɗari bakwai a wurin inyamurin, tare da dawowar motarsa da ya ɗora a kai. Ihu jama'ar wurin ke yi, abun mamaki har da inyamurin da aka cinye, a karo guda ya sa hannu ya daki kafaɗar Sadam. "What a boy!" Inyamurin ya faɗa, faffaɗar fuskarsa ɗauke da murmushi mai sauti, a karo guda ya kama hannun Sadam, tare da taimaka masa ya kwashi kuɗinsa suka fito a tare hannuwansu cikin na juna, abinda ya rink'a ba al'ummar wurin mamaki har ma da Kazaure. Gaban motar Sadam suka isa, ya buɗe ɗayan gefen ya zuba kuɗinsa, sannan ya dawo inda mutumen yake, ya bashi hannu suka gaisa. "Na daɗe ina neman hazik'in mutum ɗan caca irinka, sai dai ban samu ba." Murmushi kawai Sadam yayi, hakan ya ba mutumen damar cigaba. "Zan ɗaga maka darajarka, in ɗaukaka fasaharka zuwa wani mataki da baza kayi tsammani ba." "Ban fahimce ka ba." "Zan yi signing ɗinka da wata k'ungiyarmu da mu kan tura matasa irinka zuwa Las Vegas domin gwanancewa a kan wannan sana'ar. Cuz a gaskiya jarumtakarka, ta fi k'arfin ka zubar da basirarka a wannan ɗan k'aramin Hotel ɗin wanda na tabbata duk in ka samu kuɗi da yawa a nan basu wuce miliyan guda." Mamaki ne sosai shimfiɗe saman fuskar Kazaure, abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa shine, tunanin yadda zai tafi wata k'asa, ba tare da Jay ta dawo gare shi ba, sai dai wata shawara da ta faɗo mishi tasa ya saki murmushi, ya ɗago yana kallon mutumen. "Ya za'ai in yarda da maganarka?" Dariya yayi, ya ciro katinsa mai ɗauke da address ɗinsa na New Mexico ya mik'a ma Sadam, ya ansa yana dubawa, sosai ya gamsu da bayaninsa, ɗari bisa ɗari. "Yi mun cikakken bayani ta yadda zan fahimta mana." "Kada ka samu damuwa, idan ba ka da wani uzuri yanzu, mu shiga daga ciki, sai muyi magana cikin sirri, kasan komai yana buk'atar sirri." Kamar bai yarda da mutumen ba, sai dai kuma da ya tuna da cewar yana da buk'atar kuɗi, sai ya juya suka mik'a zuwa ciki. Bayanai mutumen ya fara yi mishi ɗaya bayan ɗaya, wasu yana ganewa, wasu kam sai a hankali. A k'arshe inyamurin ya mik'e ya shiga toilet kamar mai shirin yin wani abu, sannan ya fito. Kasancewar barasar da ke jikin Sadam ta fara ɗibar shi, sai bai kula da yanayin da mutumen ya fito ba, gadan-gadan yayi kansa, ya fesa masa wata farar hodar da ke hannunsa, bai yi cikakkun mintina biyu ba ya faɗi a wurin tamkar marar numfashi. Da sauri ya tura shi cikin restroom din, ya nemi aljihunshi ya lalubo key ɗin motarsa. Cikin wani irin sauri ya juya ya fita. Wurin motar ta Sadam ya isa, ya buɗe, kuɗaɗen da ya zuba suna nan ajje a gefe, haka zalika gate pass ɗin da akan ba mutum kafin ya shiga ciki, shima yana nan a tsakanin kujerar driver da ta mai zaman banza, haka ya shiga ya tada motar ya isa ya basu abinsu, ya mik'a titin, ya bar wurin baki ɗaya. Sadam Kazaure...this is just the beginning😂😂😂 A galabaice ya fara buɗe idanunsa a hankali, ya sauke a kan mutane biyun da ke tsaye gabansa. Mik'ewa yayi yana mai cigaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya ba tare da ya fahimci halin da yake ciki ba. "Are you okay?" Kallon mai maganar Sadam yake yana son tuna abinda ya faru, amma ya kasa, bai ce komai ba, ya mike, ya zira takalmansa da ke yashe a gefe, ya fito harabar hotel ɗin. A gaban reception ya tsaya yana kalle-kalle, sai dai cajin da ke cikin kansa bai barshi ya tuna komai ba dangane da abinda ya wakana, idan ko har zai tuna wani abu, to ba komai bane illa lokacin da ya shigo wurin, ya zarce zuwa mashayar da ke cikin hotel ɗin. Bai takura kansa ba wurin son sanin abubuwan da suka faru daga wancen lokacin, illa mik'ewa da yayi da zumar zuwa inda ya ajiye motarshi, sai dai kaf wurin, babu motar dake da k'arancin kuɗin tashi. Manya-manyan jifajifai ne, da k'ayatattun motoci danginsu BMW, Mercedes, da makamantan irinsu, hakan yasa idanun Sadam suka fara rena fata, a karo guda ya tura hannunsa a aljihu da niyyar fito da makullin motar, ya latsa security, ko Allah zai sa a dace, sai dai makullin yace neme ni inda ka ajje ni. Da gudu ya koma cikin reception ɗin, yayi sa'ar ganin mutumen da ya taimaka masa, ya isa gabanshi da sauri. "Na manta key ɗin motata a ciki please." "Bamu ga key ba gaskiya. Dan ba fito wurin ba sai da na tabbatar da cleaners sun gyara shi." "No please. Kada kace haka mana." "I'm serious Malam. Sai dai ko wani wurin ka jefar da shi." Faɗuwar gabansa ce ta tsananta lokacin da ya tuno da inyamurin da suka haɗu, sannu a hankali abubuwan da suka faru a daren jiya suka dawo cikin k'wanyarsa, hakan yasa shi zubewa a wurin tare da tallabar kanshi da hannuwansa duk biyu. "Ya kashe ni."3 Yayi maganar a bayyane. Ganin abin nashi ba na wasan yaro ba ne, yasa manager wurin ya kira securities suka fitar da shi har wajen hotel ɗin sannan suka koma ciki. Zuciyarsa gaba ɗaya babu daɗi, ya rasa menene abinda ke shirin afkuwa a rayuwarsa, tashin hankali da rashin natsuwar da yake ciki gaba ɗaya sun wanzu a saman fuskarshi. Dak'yar ya iya ɗaga k'afarsa ya fara takawa, sai da yayi tafiya mai 'yar tazara sannan ya samu taxi ya k'arasa da shi gida. Hankalinsa bai gama tashi ba, sai da yazo gidan ya same shi rufe, kasancewar makullan gidan da ya haɗa tare da na motarshi. *** "Sagiru ya batun maganarmu? Sanin kanka ne bazan taɓa barin Ummi ta koma ma yaron nan ba. Tunda naga alamar abinda kake so kenan." "Wallahi ba haka bane Alhaji. Yanzu haka fitowa ta gida kenan, daga nan kuma wurinshi nayi, domin nima yau satina ukku kenan ban sa Kazaure a idanuwa na ba. Baya zuwa office, haka kuma baya ansa duk wani kira da nike mishi, dalilin da yasa nike son a bi komai a hankali ba komai bane, illa idan muka kai maganar court kamar mun daɓa ma kanmu wuk'a ne." "Ban aminta da wannan shawarar ba. Tunda har yaron nan ya fara guje maka, tabbas yana da abinda yake shirin yi. A nufin shi ya gudu ya bar mun 'ya da aurenshi a kanta ko? To wallahi bai isa ba. Ba kuma zan taɓa lamunta ba. Ya bar ganin yayi na farko ya ci riba, wannan karon sai na yi mishi wulakancin da kare ma ba zai ɗauka ba wallahi. Ka dai ji na rantse." "A yi hak'uri dai alhaji. In sha Allah yau ɗin nan za'a yi ta ta k'are." "Kada ka ba kanka wahala Sagiru, dan na tabbata yaron nan ba zai bata takardarta ba har sai na bayyana gabanshi, dan haka ka jira ni ina nan tafe." "Haba Alhaji. Kayi hak'uri ka bar komai a hannuna mana, zan kula da duk abinda ya dace." "Hak'urina ya k'are Sagiru, haka zalika kana buk'atar mataimaki. Ina nan zuwa gobe in sha Allah." Bai jira ansarshi ba ya kashe wayar, hakan yasa SS ya bi fuskar wayar da kallo, yana tunanin abin yi. Wayar Shamsu abokin aikinsu da ta shigo ne ta katse mishi tunani, haka ya ɗaga wayar da sallama ya kara a kunne. "Weekend Alhamdulillah" "Ina gida, yanzu dai nike shirin fita." "A'a bani da labari wallahi." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Kazauren?" "Shi yasa ya daina zuwa aiki kenan? Amma yayi ganganci. Bai taɓa sanar da ni ba wllahi." "Zamu yi magana in sha Allah." Ya kashe wayar ya fara kaiwa da kawowa, haka zalika ba zai iya jurewa abinda ake shirin yi ma aminin nashi ba. Duk kuwa da cewar babu wanda ya kaishi tsanar halayenshi a dai-dai wannan lokacin. Motar ya shiga da sauri, a guje ya bar gidan zuwa gidan Sadam. A kofar gidan yayi parking, ya fita ya kutsa kanshi ciki, tare da sallama, sai dai ba'a ansa ba. Bakin k'ofar ya isa ya fara bubbugawa, cikin wata irin kakkausar murya aka ce "Waye ne Dallah?" "Ka buɗe ka gani mana." A dai-dai lokacin ya buɗe k'ofar, idanunsa sunyi jazur, da gani a cikin maye yake, k'afarshi babu takalmi, cikakkar sumar da ke kanshi ta cukwikwuye alamar bata samu ajin sharta ba, wandon da ke jikinsa tamkar zai faɗi k'asa saboda mugun ass down ɗin da yayi, hatta da boxers ɗinshi gashi nan muraran ana kallo. "Kana so ka kashe kanka ko? Wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka Sadam? Wai kai wane irin mutum ne a duniyar nan?" "Kayi abinda ya kawo ka ka k'ara gaba Dallah. Me ruwanka da rayuwata?" "Wannan bak'in halin naka shi ke hana ka cigaba a rayuwa, idan zaka rufa ma kanka asiri ka koma mutumen arzik'i, ka rufa, idan kuma ba haka ba, wallahi rayuwarka tana cikin haɗari, hatta aikin da kake tak'ama da shi yana gab da barin hannunka, tunda ka ci kuɗin mutane, ba tare da saninsu ba, kuma manager ya rufa maka asiri, amma da yake kai butulu ne sai ka watsa masa k'asa a ido. Dalilin zuwa na nan bakomai bane illa in taimaka maka, ka kawo abinda yake hannunka, mu haɗa mu biya su kuɗinsu, kana sane da cewar gobe ne dateoline ɗin da manager ya baka, duk da ma maganar ta gama fitowa, sai kasan ya zaka yi da sauran k'alubalen da suke gabanka." "Idan wannan ne ya kawo ka, gara ka ɓace ma ganina tun wuri, dan bana buk'atar taimakon kowa a wannan lokacin. A shirye nike in anshi duk wani hukunci da banki zata yi a kaina, sannan zan baka shawara da ka daina ba kanka wahala a wurin mutumen da bai san ciwon kansa ba iri na." Ya juya da sauri zai koma ciki, amma SS yasa hannu ya cafko nashi hannun, ya tura k'ofar da k'afarsa, ya bi bayanshi suka shiga. "Me sa baka tausayin kanka? Me sa baka tausayawa zuciya da gangar jikinka? Wai kai wane irin mutum ne dan Allah?" Juyowa yayi yana kallon SS, kuka ne ya ciyo shi, take yasa hannu ya toshe bakinsa, a lokaci guda ya faɗa kafaɗar SS yana wani irin kukan da ya rink'a taɓa zuciyoyinsu.3 "Kana ganin na cancanci a tausaya mun? Kana tunanin ina jerin mutanen da ya kamata a tausayawa ne? Ni kaina nasan bana ciki SS, na riga na wulak'anta rayuwata, na wulak'anta kaina, na kuma wulak'anta duk wani da zai iya yin taimako a gare ni. Me sa baza ka bari a hukunta ni ta hanyar da zata ladabtar da ni ba? Me sa baza ka barni in ɗanɗani bak'in cikin da wasu suka ɗanɗana ta dalilina ba? Ina tababar kaina da kaina, domin kuwa bani da wani mak'iyi, wanda ya wuce mun kaina." Hawaye ne suka yayyafo a idon SS, duk da mugun haushinshi da ya ke ji, hakan bai hana mishi jin tausayin kalaman da yayi ba. Gefe Sadam ɗin ya koma ya zauna ya haɗa kanshi da gwiwa yana ci gaba da wani irin kuka, shima SS zama yayi a ɗaya daga kujerun palon, yayin da shiru na dogon lokaci ya cigaba da wanzuwa a wurin. "Yanzu menene abin yi?" "Ban sani ba SS. Ban sani ba wallahi, illa iyaka, ina maraba da duk hukuncin da banki ya yanke a kaina." "Idan na fahimce ka, kana nufin baka da kuɗin da zaka biya su?" "Bani da su." "Ina motarka? Kuma wannan ma ai gidanka ne ko?" "An sace ta. Wannan kuma ba gidana ba ne ba." "Kana nufin shekaru kusan bakwai din da kayi kana aiki baka tsinana ma kanka tsiyar komai ba Kazaure?" Bai bashi ansa ba, shima kuma baiyi tsammanin hakan ba. "Ko da yake, tunda ka jefa kanka a bala'in caca, da shan giya, ai baza su barka ka tara komai ba. Allah ya kyauta maka halayenka Sadam." Banza ya mishi, sai gunjin kukansa kawai da yake yi, haka SS ya k'araci zamansa ya mik'e. "Ka tabbatar ka halarci meeting ɗin da za'a yi a bank gobe, ni kuma zan ga abun da zan iya yi." Ya juya ya fita, zuciyarshi a dagule, yana tunanin mutum mai irin halayen Kazaure. Mik'ewa Sadam yayi zuciyarsa na wani irin tafasa ya rasa menene abinda ke mishi daɗi, ta wani ɓangaren yana jin tsanar kanshi da halayenshi. Wani wawan ihu ya saki, a lokacin da ya matsa gaban television ɗin dake girke saman tv stand yasa hannunsa tun k'arfi, yayi wurgi da ita, take tayi gefe ta bada tartsatsatsa! Ya duk'e a wurin shi kuma yana cigaba da rizgar wani irin kuka mai azabar zafi da raɗaɗi.1 *** B abban ɗakin taron cike yake mak'il da duk wani ma'aikacin bankin. Manager ne ya mik'e tare da karanto sharuɗɗan da mutum kan ɗauka kafin fara aiki a kowanne irin banki na duniya. Ya gama ya karanto hukunce-hukunce da su kan hau kan duk wanda ya saɓa ɗaya daga cikin dokokin da suka gabata, sannan ya bayyana laifin Sadam a matsayin wanda ya saci kuɗin banki ba tare da saninta ba. "Wannan sata ce." A cewar MD wanda shima yana zaune a wurin. Ya gyara zamansa, sannan ya cigaba. "Domin kuwa ba wai a banki ba, ko a ina ne mutum ya ɗauki abu ba tare da sanin mai shi ba, sata kawai za'a kira shi." Da yawa a cikin jama'ar wurin kai suke girgizawa, alamar sun aminta da batun na MD, daga bisani ya buk'aci Sadam da yayi bayanin dalilin da ya sa ya ɗauki kuɗin, ya kuma kawo hujjojin kare kai idan yana da su. A yadda yake a zaune, kanshi a k'asa yana wasa da yatsun hannayensa, ta gefe guda hawaye na silalowa a saman kumatunsa, ya fara magana. Jawabin da ya yima manager shi ya maimaita a wurin, sai dai manager ya mik'e a fusace yana faɗin "Wannan maganar banza ce. K'arya yake yi. Domin kuwa binciken dana gudanar a kanshi ya tabbatar mun maganar k'arya ce. Haka kuma nayi duk wani binciken da ya kamata, amma ban samu wata kadara k'wak'k'wara a tare da shi ba." Bai k'ara cewa uffan ba tun daga nan, shiru kawai yayi yana sauraren abinda zai biyo baya. Hakan yasa MD ya cigaba da jawabi kamar haka: "A matsayinka na ma'aikacin wannan banki, wanda ya ha'ince shi, ya kuma ci amanarshi, ya saɓa ma banki dokoki da hukunce-hukunce, daga rana mai kamar ta yau, bankin ya dakatar da kai daga aiki da shi. Haka zalika bankin ya gurɓata duk wasu takardunka, ya kuma kore ka daga aiki a k'ark'ashinshi, sannan kuma babu inda zaka je su anshe ka, a matsayinka na ha'ini, ma ci amana. Abinda ya yi saura tsakaninka da banki shine ka biya kuɗaɗen da ka ɗauka, sanin kanka ne banki baya ɗaukar asara ko ta kobo ɗaya."3 Ya san k'arshen maganar kenan, ya kuma san wannan ne hukuncin da ya dace da mutumen da bai san daraja ko ciwon kansa ba. Handkerchief ya fitar tare da toshe bakinsa, yayi kukanshi son ranshi, wasu na tausaya mishi, waɗanda kuma suka san halinshi, suna cewa maganin irinshi kenan. SS ne ya fito da kuɗi nera dubu ɗari biyar ya mik'a su ga Manager, tare da neman lamunin cewar zai cika sauran zuwa gaba. "Kada ka manta ba loan muka bashi ba, balle mu k'ara mishi interest muyi mishi lamuni. Satar kuɗin mutane yayi, idan baya da su gaba ɗaya akwai police da na kira zasu wuce da shi su kai mana ajiyarsa prison har zuwa lokacin da zai biya sauran kuɗin" MD yayi maganar gabanshi gaɗi, ba tare da ya tausaya ma halin da Kazauren ke ciki ba. "Alfarma na rok'a a matsayina na ma'aikacinku nima. A yi mun wannan taimakon."2 "Wannan abu fa doka ce SS, haka zalika ko ɗan dana haifa ne ya taka ta, iyakar abinda zan mishi kenan." Ya juya yayi kiran wani security, yace ya kira police ɗin da suke waje. Haka polisawa kusan bakwai, suka shigo cikin bak'i da blue ɗin uniform ɗinsu, MD yayi musu nuni da Kazaure, suka isa gabanshi, suka ɗora masa handcuffs suka mik'ar da shi. Kukan da yake a wannan lokacin, sosai ya taɓa zuciyar SS, da duk wani mai imani a wurin, hakan yasa ya isa gabanshi, ya rungume shi.1 "Zan fitar da kai Kazaure. Just trust me." Ya sake shi suka tusa k'eyarsa gaba suka wuce, inda su kuma suka cigaba da gudanar da abubuwan da suka yi saura, suka fito zuciyoyin mutane da dama a wurin babu jin daɗin abinda ya faru. **** Washe gari da misalin karfe ɗaya na rana, wayar Baffa ta shigo ma SS. Dagawa yayi da sallama ya ɗora a kunnenshi. "Ina office." "Zan zo yanzu in sha Allah idan na fito lunch." Ya kashe wayar tare da mik'ewa, yana karasawa inda motarshi ke ajje. Hotel ɗin da Baffa ya sauka ya isa, bai shiga ciki ba, ya mishi waya ya sanar mishi da zuwansa, hakan yasa ba'a ɗauki dogon lokaci ba suka fito tare da direbanshi. Fitowa yayi a motar suka gaisa cikin karamci da girmamawa, daga bisani ya sanar mishi da tsautsayin da ya faru da Kazaure. "Wannan ba damuwata ba ce Sagir. Yaron nan ai kaɗan ma ya gani daga abubuwan da zasu faru da shi, kuma ko da banki bata ɗaure shi ba, zuwan nan da ka ga nayi, da niyyar ɗaure shi na zo. Dan haka ka shiga muje inda ya ke, ni dai takardar sakin 'ya ta kawai nike buk'ata." Bai yi gardama ba, ya juya ya shiga motarshi, su Baffa suka rufa mishi baya har zuwa Maiduguri Central prison. Ba su sha wahalar ganinshi ba, haka kuma babu komai da aka taɓa a lafiyar jikinshi, illa kayan jikinsa da aka canja zuwa irin na sauran prisoners ɗin da suke gidan. Wata irin mummunar faɗuwar gaba yayi lokacin da ya hango Baffa zaune, a silale ya iso wurin, kanshi a k'asa ya zauna yana jiran abinda zai biyo baya. "Wannan kaɗan kenan ka gani Sadam. Irin bak'in cikin da ka cusa ma zuciyata lokacin da ka gudan mun da 'ya, bi'izinillah, sai ka ɗanɗani wanda ya fishi. Ba zan taɓa yafe ma azzalimi irinka ba. Kuma a niyyar da nazo da ita garin nan, in sa a ɗaure ka, irin ɗaurin da ko labarin irin laifin da kayi, wani ba zai so ya ji ba, amma Alhamdulillah, banki ta gama mun komai, yanzu abu ɗaya yayi saura tsakanin mu, ga takarda da biro ka rubuta mun sakin 'yata."2 Kuka yake marar sauti tare da girgiza kanshi, a yadda yake jin jay a zuciyarsa yanzu, ba zai taɓa gangancin furta saki a gare ta ba, balle kuma har ya rubuta. Jin son ta yake wanda bai taɓa jin kwatankwacin irinshi ba yana yawo a duk wani jini da yake gudanyawa a cikin jikinsa. Ya san shi mai laifi ne a gareta, amma yana da yak'inin cewar har gobe akwai sauran soyayyarsa a cikin zuciyarta, kamar yadda ya wayi gari A DARE D'AYA, ya ji ya kamu da matsanancin son ta wanda ya fi gaban misali, ya kuma ninninka duk wani tarihin soyayya da ya taɓa wanzuwa a duniyar masoya. A yanzu ji yake tamkar ya cire zuciyarsa ya nuna mata yadda soyayyarta tayi fata-fata da kowanne lungu-da sak'o na birnin zuciyarsa.5 "Kayi hakuri. Amma bazan iya ba Baffa." "What? Da sauran ka yaro. Nace da sauran ka. Ko dai ka rubuta mun sakinta, ko kuma in sa kurtayen nan suyi ta jibgarka, har sai ka kasa tashi wallahi." "Da zaka mun haka, da zan kasance cikin farin ciki, kuma ko bakomai, zan samu natsuwa a zuciyata ta wani fannin, kasancewar an hukunta mutumen da ya fifita farin cikinshi akan na wasu. Mutumen da yayi gagarumin laifin da ya cancanci hukunci. Mutumen da ya banzatar da macen da ta bashi amanar ruhi da gangar jikinta, ya wulak'antar da 'yar da ya haifa a cikin jikinsa, saboda wani dalilinshi can marar tushe. Kayi hak'uri Baffa, amma ko da zaka ɗora mini bakin bindiga, bazan taɓa furta kalmar saki a kan Jay ba, ina k'aunarta, itama, tana k'auna ta."8 "A da kenan, a yanzu kuwa ban da tsana da k'iyayyarka, babu komai a cikin zuciyarta." Ya tsinkayi muryar SS cikin zafin nama yayi maganar, tamkar ba mutumen da ya gama tarairayarsa jiya jiyan nan ba. "Me hakan ke nufi?" Yayi maganar a cikin zuciyarsa. Amma ya kasa gano dalili. "That will never happen Sagir. Jay is belong to me. Tawa ce ita. Numfashina ce ita. Matsawar ba ita bace tace in sauwak'e mata, to babu wanda zai sa in furta kalmar saki gare ta."2 "Fine. Zan fitar da kai. In kai ka har gabanta, anan zaka fahimci rashin amfanin da kake da shi a wurinta. A lokacin zaka gane babban kuskuren daka tafka na tunanin cewar har yanzu tana k'aunarka. Baffa ka daure ka tashi muje, nayi alk'awarin jibi in sha Allah zan zo da Sadam har gida, kuma ba zai fito ba har sai ya bama Ummi shedar sakinta kamar yadda kuke bukata." "Wannan maganar banza ce, ba kuma zan lamunta da ita ba. Haka kuma ba zan bar wurin nan ba har sai ya furta da bakinshi cewar ya sake ta." "Wannan ba zai taɓa faruwa ba Baffa. Ba zan taɓa furta wannan mummunar kalmar da bakina ba, ko da zaka maida gabana gabas, ka kashe ni." Hak'uri SS ya cigaba da bama Baffa, dak'yar ya lallaɓa shi suka tafi, akan cewar zai ida biyan bashin da ake bin Kazaure, zai kuma zo da shi har Katsina zuwa jibi in sha Allahu.2 Wani irin asirtaccen kuka ta rink'a yi, mai tsananin zafi da raɗaɗi a cikin zuciya, irin kukan da duk wanda ya san darajar so, dole ya tausaya mata ya kuma gane ɗacin da take ji a cikin zuciyarta ba na komai bane illa na RABUWA DA MASOYI. Cikin ɗan k'aramin lokacin da ta ganshi, suka yi musayar kalamai na dole, tabbas na dole zata kira kalaman da ta jefe shi da su, domin kuwa Allah ne kaɗai zai iya sanin menene ainahin gaskiyar abinda ke ranta, shine kuma kaɗai ya san irin k'arfin halin da tayi wurin jifar Kazaure da kalaman da ta yi wa lak'abi da munana. Da sauri Baffa ya kawar da idonsa daga kallon Sadam wanda ya fita yana wasu irin hawaye waɗanda ya tabbatar da sun taka na 'yarshi azabtarwa a cikin zuciya. Sune kuma suka sa a take ya ji tausayin mutumen da bai taɓa tsammani ba ya ɗarsu a cikin zuciyarsa, sai dai kuma a karo guda gagarumin laifin da Sadam ɗin ya tafka ya faɗo mishi, hakan yasa ya ji k'iyayyarshi ta dawo sabuwa fil, har ma ya rink'a jin wani sanyin farin ciki na saukar mishi, ganin yadda zuciyar Kazaure ta fara ɗanɗana ɗacin bak'in cikin da suka kwaahe shekaru suna ɗanɗanawa. K'ofar palon ya turo ya shigo, sai dai ga mamakinshi tuni Sagir ya riga shi isa inda take a duk'e, idanunsa k'yam a kanta. Muryarshi da ya tsinkaya yana magana ce ta sanya shi yin tsaye a bakin k'ofar yana kallonsu. "Yanzu a kan Sadam ne kike asarar hawayenki haka,? Why please? Ba dai kina nufin har kin manta wanene shi ba? Ta yadda na lura kina bak'in cikin rabuwa da shi ko? No please. Shine fa mutumen da ya cusa ciwo a zuciyarki da ta mahaifanki. Ya k'yamace ki, ya k'yamaci 'yarki, gudan jininki a lokacin da kuke buk'atar shi fiye da komai. Jay me kike hange a tattare da shi wanda har rabuwa da shi zata sa ki zubar da hawaye? Kazaure ne fa mutumen da bai san daraja da mutuncinki ba. Kina nufin ni na fiki jin zafin abinda yayi miki ne? Please kada ki tada hankalinki ta dalilin shi, you don't deserve him at all, you deserve to be love and well taking care of, Kazaure ba zai taba baki farin cikin da ya gagara baki tun asali ba. Please ki cire shi a zuciyarki, ko ba komai zaki samu natsuwar ruhinki." A galabaice ta lago da rinannun idanunta ta watsa mishi wani irin mayen kallon da bata taba tsammanin zata iya yi mishi irin sa ba. Hakan yasa zuciyarsa ta fara k'issima masa abubuwa da dama, haka kuma ba tare da ya shirya ba, ya ja bakinshi yayi shiru, domin a yadda ta ɗago ɗin duk mai hankalin da ya kai duba gare ta zai iya gane yadda DAFIN SO ke ɗawainiya da ita. A hankali Baffa ya k'arasa takowa tsakiyar palon, gabansu ya isa, ya juya yana kallon SS "Barin yi magana da ita." Bashi da yadda zaiyi, haka kuma ba dan ranshi ya so ba, ya juya ya k'are mata kallo, har yanzu kukan ta ke yi, kukan da yake jin zuciyarsa na motsawa da sautinshi, sai dai bashi da wata hanyar dakatar da ita, illa ya bata lokaci har zuwa sadda zata fahimci yadda bacin ranta ke azabtar da zuciya da gangar jikinsa. Juyawa yayi ya fita, hakan ya ba Baffa damar isa kujerar dake gabanta ya zauna, wata irin k'auna, da kuma tausayin 'yar tashi suka saukar masa a karo guda, kasancewar abinda ya ke hange a cikin idanuwanta, ba komai bane illa soyayyar mutumen da tayi k'aryar tsanarshi fiye da komai, fiye da kowa. "Me sa kika cuci kanki bayan na baki zaɓi Ummi?" A ɗiririce ta ɗago, dan bata taɓa tsammanin hakan daga gare shi ba, sai dai kuma wannan abun da tayi, shine kawai hanyar da zata iya bi ta dawo da farin cikin iyayenta da ta ɗauke shekara da shekaru. "Ba zan iya cigaba da zama da shi ba Baffa. Iyakar gaskiyata kenan, ban kuma cutar da kaina ba." "Yaushe kika yi hankalin ɓoye damuwarki Ummi? Bayan kuma gata nan ta bayyana k'arara a saman fuskarki. Kina sonshi Ummi, kina matuk'ar k'aunarshi." Kukanta ne ya tsananta, ta tabbatar da canjin da aka samu daga gare ta na ɓoye damuwarta kamar yadda Baffan ya faɗa, saɓanin da can, da bata san wani abu alkunya, ko kuma zurfin ciki ba. Ta kuma tabbatar da k'aryar da tayi ta cewa bata k'aunar mutumen da numfashinta ke fita da soyayyarshi, duk kuwa da rayuwar k'uncin da tayi tare da shi. "A da dai na so shi Baffa, son da ya jaza mun fushinku na tsawon shekaru, son da ya hana mun kwanciyar hankali, ya kuma dakatar mun da farin cikina, ya hana ni samun cikar burin karatuna. Sai dai kuma ba komai ba ne idan na yi duba da Rukayya, sai in yardar ma kaina cewar hakan k'addara ta ce, haka kuma Allah ya tsara mun K'ADDARAR AURENA. Nayi bankwana da Sadam, nayi bankwana da soyayyarshi, bana kuma tunanin akwai abinda zai sa in koma mishi ko da kuwa shi kaɗai ne D'A NAMIJI da yayi saura a wannan duniyar ta mu. Zanyi biyayya gare ku, zan bi umarnin duk yadda kuke son ku juya ni, zaku same ni 'ya mai bin duk wasu dokoki da zaku shimfiɗa a gare ni." "Alal hak'ik'a ina mai matuk'ar alfahari da ke Mamana. Sai dai hakan ba shi zai sa in koma yar gidan jiya ba, ba shi zai sa in danne hak'k'in da kike da shi a yanzu ba. Na riga nayi sake da damata a lokacin da ya kamata inyi amfani da ita, a zahirance musulunci yace mu zaɓa ma 'ya'yanmu mazaje a lokacin aurensu na farko, amma idan aka samu akasin hakan, har ya kai ga saki ya shiga tsakanin ma'auratan, to fa a wannan gaɓar ba mu bane za muyi ruwa muyi tsaki ba, alhakin na kan yarinya, ita zata zaɓa ma kanta wanda duk ya kwanta mata, illa iyaka idan mun hango ba dai dai ba a cikin lamarin, sai mu bada shawarar da muke ganin zata yi amfani. To a wannan gaɓar zaɓi na ki ne Ummi, ni kam na riga nayi sake da damata tun farko." "A matsayina na 'yar da ta bijire ma umarninku na farko, na baka wannan damar Baffa, na mik'a wuk'a da nama gare ka, zan kuma yi biyayya ga duk yadda ka so ka juya ni." "Allah ya shige mana gaba, Allah kuma yasa mu fi k'arfin zukatanmu. Ki share hawayen nan da Allah, sannan ki k'ara tunani akan abinda ya kamata a yi." Ya mik'e ya fita, hakan yasa SS da ke zaune saman kujerun da ke gaban palon yayi saurin mik'ewa shima, ganin Baffan ya sa kai zuwa cikin gida, a take ya juya ya shige palon. Har yanzu a inda ya barta ta ke, illa kawai kukan da ta ɗan tsagaita, kanta a tsakankanin k'afafunta da ta haɗa wuri guda. "Jay." Ya kira sunanta da wata sassanyar muryar da ta sa ta ɗago gaba ɗaya, ta sauke mishi jajayen idanuwanta. "Ki daina kukan nan please. I'm here for you. For Rukayya. I'll take good care of both of you." Duk da ba wai ta fahimci inda maganarshi ta sa gaba ba, hakan bai hana bugun zuciyarta tsananta ba saboda yadda taga yana jifarta da wani kallo, wanda ta hangi irinshi a idanun Kazaurenta a haɗuwarsu ta yau ɗin nan. Bata ce uffan ba, ta mik'e zata fita, yayi saurin shiga gabanta, ko me ya tuna kuma, ya kauce ya bata hanya, tasa kai ta fita, ba'a ɗauki dogon lokaci ba Jafar ya turo k'ofar palon ya shigo. Sosai ya ji daɗin yanayin da ya ga yaron nasa, hakan kuma yasa ya k'ara k'aimi ma abinda ya ke ji dangane da ita a cikin zuciyarsa, duk kuwa da cewar ya tabbatar da sai ya sha bak'ar wahala kafin idan da rabo ya samu ta amince mishi, domin yadda ya hangi soyayyar Kazaure ɓaro-ɓaro a idanunta, ya tabbatar abu ne mai wahalar gaske ta yakice shi a lokaci guda. "Zan koya mata yadda zata so ni, irin son da baza ta taɓa tsammani ba."1 Wani ɓangare na zuciyarsa ke innata hakan, da wannan kuma ya gamsu, a karo guda ya saki murmushi ya ɗaga Jafar sama yana juyawa, a tare suka saki dariya mai sauti, mai cike da so da jin daɗin ganin junansu. "How's my boy? Ina Rukayya?" Ya sauke shi suka zauna a kujera. "Tana can wurin Goggo. Ita tsoron mutane ne da ita." "Eyya. Baka faɗa mata cewar Daddy ne ba ai, na san da baza ta ji tsoro na ba." "Na faɗa mata fa, har ta taho sai Mammy tace ta koma inzo ni kaɗai. Daddy ina Uncle Farouq?" Bai damu da maganar ta Jafar ba, kasancewar yadda ya faɗa tunanin dalilin da ya sa Jay ta hana Rukayya zuwa wurinshi. "Ka ji Daddy?" Sai lokacin ya firgita, da murmushi a fuskarshi ya ɗago yana kallonshi. "Yana school. Exams ya ke yi, amma yace in gaishe ka." A haka suka cigaba da firarsu, sai dai gaba ɗaya hankalin Sagir baya jikinshi, ganin sun shafe kusan mintina arba'in shi da Jafar ba tare da Jay ta dawo ba balle ya k'ara ganin fuskarta. Cikin gidan suka shiga, ya gaishe da Goggo, amma ko k'yallinta bai gani ba, hakan yasa suka fito shi da Jafar ɗin suka isa inda yayi parking. Sai da ya shiga motar ya zauna, sannan ya ciro wayarshi ya tura mata text, kafin ya tada motar suka bar harabar gidan. **Sadam. Tafiya kawai ya ke, amma bai san ina ya dosa ba. Tunanin da ya addabi k'walwarshi kam bai wuce na yadda ya kasa tantance damuwar da tafi tasiri a zuciyarsa ba, ya kuma kasa banbance shin sakin da ya yi mata adalci ne ko rashin shi? Idan kuma yayi duba ga tashi damuwar sai ya rink'a ganin tamkar bai hukunta kanshi ta hanyar da ta dace ba. A nashi tunanin mutum irinshi bai cancanci ace ya cigaba da shakar numfashi a doron k'asa ba. Amma ya zai yi da soyayyarta da yake jin tana yawo a cikin jinin da ke kewayawa a jijiyoyinshi yana kaiwa zuciya, da sauran sassa na jikinshi? 'Bai sani ba' amsar da ya ba kanshi kenan, sannan kuma bai san ina zai dosa daga inda yake a tsaye ba. Bai damu da irin kallon da mutane ke bin shi da ba, domin kuwa ya riga yayi nisa a sahun masoyan da soyayya kan sa su zauce, a wani lokacin har a bisu da kallon masu taɓin hankali. Kanshi tsaye ya mik'a da zumar tsallaka titi, bai damu da duba titin ba, haka cikin rashin sa'a wata bak'ar motar EOD da ta kawo kai a dai-dai lokacin tayi sama da shi ta watsar a tsakiyar titin, kasancewar mahaukacin gudun da matuk'in motar ke yi, sakamakon rashin yawaitar ababen hawa a lafiyayyen titin na GRA. Wani mai k'aramin shago na siyar da kati shi ya fara ganin abinda ya wakana, salati ya saki, da sauri ya rugo wajen tare da taimakon mai motar da wasu yan tsiraran mutane suka ɗaga shi suka saka a motar suka wuce asibiti. Sai da suka kwashi kusan awa ɗaya yana cikin A&E na Federal Medical Center, kafin wata nurse ta lek'o tayi kiran mai motar da ya kawo shi. Gaban gadon da yake kwance mutumen ya isa, kallonshi yake da mamakin dalilin da yasa mutum mai hankali irinshi ratsawa tsakiyar titi ba tare da ya duba ba. Nurse ɗin ce tayi mishi bayanin yanayin jikin na Sadam, inda tace bai samu wasu raunuka ba, illa buguwar da yayi kawai, sun kuma yi mishi allurar bacci zai iya farkawa a ko da yaushe. A nan yayi zaune ya rasa abin yi, a k'arshe ya fitar da wayar Sadam dake aljihunshi, ya duba ko Allah zai sa ya samu wanda zai kira. Cikin rashin sa'a wayar babu charge, haka ya matsa gadon da ke gaba kaɗan da nasu suka ara mai charger ya jona ya kunna wayar. Dialled calls ɗinshi ya shiga, nan ya ci karo da number Sa'id a farko hakan yasa ya danna kira, bugu biyu zuwa na ukku aka ɗaga wayar da sallama. "Sai yau ka ga damar buɗe wayar Sadam? Yanzu kai tsakani da Allah haka muka yi da kai?" "Ernnmmn ba mai wayan ba ne gaskiya." "Wanene to?" Nan ya yi mishi bayanin abinda ya faru, inda shi kuma tashin hankali yasa shi sakin salati yana tambayar abinda ya je da shi Katsina. "Gani nan zuwa yanzun nan." Abinda ya karkare wayar da shi kenan, hakan yasa wancen ya ɗan samu sassauci, ya koma bakin gadon ya zauna. **** Jay I love you. I can't do without you. I love you so very much. Wallahi zan kula da ke zan canja halayena. Please kada ki guje ni, idan kika bar ni ban san ina zan sa kaina... Sa'id da ke gefe yayi saurin toshe bakinshi, duk da bai san tak'amaiman inda maganar tashi ta dosa ba, amma hakan yasa ya gane yadda ciwon so ke azabtar da zuciyar ɗan uwan nashi. A hankali ya fara buɗe idon yana kallon jama'ar wurin one after the other, a k'arshe ya sauke idonshi kan Sa'id da ke rik'e da hannayenshi. "She hates me Yaya. Tace bata so na, dole ta sa na sake ta. Ina son ta wallahi, ina matuk'ar k'aunarta." "Sadam me ke damunka? Wacece haka?" "Yaya ka taimaka mun ta dawo gare ni, ina son ta wallahi." "Ya isa haka please. Ka duba yanayin da kake ciki mana, ka koma ka kwanta yanzu, zamu yi magana idan ka tashi." "Ni bana jin komai wallahi, bana jin ciwon komai Yaya. Me nake yi a nan? Ina ne nan kuma?" A dai-dai lokacin nurse ta iso, ta buk'aci da su bashi fili ya samu natsuwar jikinshi, kafin suyi mishi wasu maganganun da zasu iya taɓa lafiyarshi. Juyawa duk suka yi suka fita, sai dai ya k'i yarda ko hannunsa ta kama, a cewar shi shi babu abinda ya same shi. K'arshe mik'ewa yayi ya saka takalmanshi, ya kuma ɓalle drip ɗin ruwan da aka saka mishi, yana k'ok'arin wucewa, nurses maza suka kama shi suka mayar da shi saman gadon suka zaunar, amma ganin yadda ya dage shi baya jin komai, dole suka yi discharging ɗinshi, suka fito tare da Sa'id da Saheeb, suka yi ma mai motar da ya kaɗe shi godiya suka shige ta su motar. Duk yadda Sadam ya so ya k'ara ganin fuskarta bai samu damar hakan ba, saboda hanyar Dutse direct Sa'id ya ɗauka hankalinshi a tashe ganin yadda Sadam ɗin ya koma, ya fita daga hayyacinshi, in banda kiran sunan Jay ba shi da wani aiki. **** Palon cike yake dam da manyan yayyenshi da masu hankali daga cikin k'annenshi. Kuka yake yi sosai, irin kukan da duk wanda ya gani ya san mai yin shi yana cikin tashin hankalin da ya fi gaban misali. "Ka ɓata rayuwarka Sadam. Ka cuci kanka, most especially ka cuci yarinyar da ta ɗauki trust ɗinta ta baka. Wannan abu kamar a duniyar kafirai? Haba Sadam wannan wace irin masifa ce ta faɗa maka? Yanzu ai ga irinta nan, kai idan ma ba rashin kunya irin taka ba har kana da idon da zaka ce ta koma maka? Ai wallahi ko ni na haife ta ba zan bata shawarar ta koma ma mutumen da bai san ciwonta ba, wanda ya k'yamace ta ya k'yamaci yar da kuka haɗu kuka haifa. Baka da imani Sadam. alhakinta ne yake bibiyarka." "Wallahi Yaya ban san me ya shiga kaina ba a wancen lokacin, ban san menene dalilin da ya sa na tsani Rukayya ba, na gane kuskurena, ku taimaka ku shige mun gaba ta dawo ɗakinta, zan kula da ita, da Rukayya, zan basu duk wani farin cikin da na hana su a shekarun baya." "Maganar banza maganar wofi. Yanzu da kaga ka rasa komai ko? Shine zaka k'ara janyo ta ka bata wata sabuwar wahalar. To ba da wani a cikinmu ba za'ayi wannan ɗanyen aikin. Abu ɗaya da zamu yi maka shine mu shige maka gaba ka nemi yafiyarta, ko Allah yasa ka koma mutum kamar kowa, domin kuwa ba wanda ya san ranar mutuwar wani." Da haka suka watse suna alhinin halaye irin na Kazaure, suka bar shi zaune dirsham a tsakiyar palon yana kukan da-na-sani da nadamar rayuwar da yayi. ****Bayan Sati Biyu**** **Sadam.+ Yana shiga Kano ana fara kiran sallar isha'i. Dam-dam gabansa ke faɗuwa, a haka ya wuce AKTH (Aminu Kano Teaching Hospital) inda mahaifin nasa ke kwance. Saheeb ya kira yana tambayar inda suke, bayan ya kwatanta masa, ya juya kan motarshi zuwa wurin, k'irjinsa na cigaba da bugawa da sauri-sauri. Jiki ba k'wari ya fito a hankali ya rufe motar, sannan ya doshi ɗakin da ya hangi yayyensa da k'annensa zagaye da gadon da mahaifinsu ke kwance. A k'ofar ɗakin ya rakuɓe jikin bango yana kallonsu ɗaya-bayan-ɗaya, yayin da yake ganin tamkar abinda ya faru shekaru shidda da suka gabata ne zai maimaita kansa a wurin. Saheeb k'anensa da yayi saurin isa gare shi ya kama hannunsa fuskarsa ɗauke da murmushi, a karo guda kuma hawaye na gangarowa, shine yasa hankalin mutanen da ke wurin ya kai wurin da suke a tsaye. Sa'id babban yayansu ya taso, ya kamo hannunsa da niyyar ya shigo da shi, amma Sadam ya fara tirjewa, yana bige hannun, shi a dole ba zai shiga ba, duk kuwa da hawayen da ke zuba a saman fuskarsa. "Sadam." Mahaifin nasu ya kira shi, hakan yasa shi tsayawa cak, ba tare da ya juyo ya kalle shi ba. "Ka juyo ka kalle ni Sadam. Na san ni mai laifi ne, sai dai kuma ba laifina bane nima, ka bani dama in rok'i gafararka dan Allah." Hawayen da suke mak'ale a idonsa ne suka cigaba da gangarowa, hannunsa sai kyarma ya ke, haka ma jikinsa baki ɗaya, amma baya jin zai iya juyawa ya kalli fuskar mahaifin nasa, dan da ya kalle shi sai ya tuna abinda ya faru shekaru shidda da suka gabata. "Ka yi hakuri ka saurare shi Sadam. Watak'ila wannan ce kawai damar da zaku samu ku fahimci junanku. Domin kuwa tun bayan tafiyarka, duk wanda ya kalli Baba ya san yana cikin wani tashin hankalin da bai furta ba ne kawai. Kayi hak'uri, ka dubi darajar haihuwar da ya maka." Cewar Sa'id da ke tsaye a gefenshi. Sai a lokacin Sadam ya juyo, idanunsa sun gama canjawa, sun rine sun yo waje, ya ɗaga su ya watsa mishi wani mayen kallon da ya faɗar mishi da gaba. "You're right. Saboda ni ba mutum ba ne ko? Saboda ni haihuwa ta aka yi ba ni da wani 'yanci ko iko ko? Saboda yana mahaifina, shi yasa zai yi yadda yake so da ni ko? Ya wulak'anta ni a duk sadda ya ga dama, sannan ya dawo yace in yafe mishi a sadda ya ga dama. Tabbas babu mai tsoron Allah a cikinku."4 Hannunsa da ke cikin na Sa'id ya fincike, ya juya yana kallon ragowar 'yan uwan nasa ɗaya-bayan-ɗaya. "Gaba ɗayanku nan babu mai tsoron Allah, na faɗa ba kwa tsoron Allah. Gaba ɗayanku son zuciya, da munafurci ya sa kun danne gaskiya kun k'i ku bayyanar da ita. Sai a yanzu ne zaku gwada kuna k'aunata? Bayan duk gaba ɗayanku babu wanda bai nuna k'iyayyarsa a fili gare ni ba. Idan ba ku sani ba ku sani, duk duniya ba ni da kowa sai mahaifiyata kaɗai, kuma itama ta rasu, dan haka na riga na shafe babin mahaifina, na kuma manta da cewar ina da sauran wasu 'yan uwa a wannan duniyar baki ɗaya." Yana gama faɗar haka ya juya a hargitse, ya doshi hanyar fita, sai dai manya-manyan mazan da ke wurin suka tarye shi suka dawo da shi ciki har zuwa gadon da mahaifin na su ke kwance. Dak'yar ya iya ɗaga hannunshi, ya kama hannun Sadam da shi, idanunsa na zubar da hawaye hakan ne ya karyar da zuciyar Kazaure, ya juyar da fuskarshi, dan baya son ya cigaba da kallon shi, saboda yana jin k'auna da soyayyar mahaifin nasa, yayin da ta wani ɓangaren yake jin ba zai iya yafe ma abinda ya mishi ba. Wani irin kuka ya ɓarke da shi shima kamar ɗan k'aramin yaro, hakan yasa duk yawancin jama'ar da ke wurin sai da suka zubar da hawaye. **(Six Years Earlier.) Alh. Baffa Kazaure, d'an asalin garin Kazaure ne ta jihar Jigawa yana zaune a garin Dutse, tare da matarsa Haj. Daso, wacce tayi saura a cikin matattakin da ya dinga aure. Yana da 'ya'ya sama da goma sha biyar. Sananne ne a nahiyar ta su, yana da wadatar arzik'i, sai dai babbar matsalar bashi da wadatar zuciya. Sadam ne d'anshi na biyar da ya haifa tare da wata matarsa mai suna Ramatu, mutuniyar Zinder, ta k'asar Niger. Mahaifiyar Sadam ta rasu tun yana d'an shekara biyar, yana d'aya daga cikin yaran da suka tashi a hannun matan uba. Mahaifin nasu mutum ne ma so abun da ya mallaka, bai yarda da yaranshi ba, kamar yadda bai yarda su taba wani abu na dukiyarshi ba, haka zalika zai iya yin komai, a kan kudin da ya samu a duniyar nan. Rayuwa a gudanshi, rayuwa ce mai cike da wahala, musamman ga yaran da iyayensu mata basa nan, domin kuwa a wasu lokutan kud'in makaranta ma sai an kai ruwa rana da shi sannan yake bayarwa. Irin rayuwar taskun da Sadam ya tashi a ciki tare da matan uba shi ya taimaka ya taso da k'ek'asassar zuciya, bashi da kunya, ga shi da taurin kai, baya mutunta mace, bai ta6a d'aukar ta halitta mai daraja ko muhimmanci a rayuwarsa ba. Gaba d'aya karatunsa yayi shi ne cikin matsi, da rashin wadata, duk da kasancewar mahaifin nasa mai abin hannunshi, hakan yasa hatta uban nashi bai rangwantawa ba. Lokacin da yake Jami'a a BUK yana shiga matsananci hali kafin ya samu abinda zai taimaki kanshi, a wasu lokutan yakan ji tamkar yayi sata, sai dai rashin son wulakancinsa ke sawa ya hak'ura, har daga baya wani inyamurin abokinsa ya rinjaye shi da fad'awa sana'ar caca, tare da k'awata mashi irin ribar da ake samu, da yadda idan ka zama zakaran gwajin dafi jama'a zasu dinga baka wani respect na daban a cikin sana'ar. Sadam d'an gayu ne, irin matasan nan ne masu jiji da kai, da son a fantama, sai dai yana da wata irin zuciya mai mugun zafi, baya shiga harkar mutane, haka kuma baya son a cika shige masa. Yana son rayuwar hutu, haka kuma yana son a rink'a kanbama shi, a kullu yaumun yana son yayi bajintar da jama'a zasu ce sai Kazaure. Yana son kanshi fiye da kowa fiye da komai. Kyakkyawa ne, dai-dai yadda ake so namiji yazo, domin kuwa dogo ne mai cikakken zati da haiba, yana da haske mai d'aukar hankali, amma ba fari bane tass ba. Faffad'a ne, kasancewarsa masoyin motsa jiki, idanuwansa dara-dara wanda suka fara canja kala zuwa jaja-jaja saboda 'yan zuk'e-zuk'e da yake yi a duk lokacin da ya samu wata gara6asa mai tsoka, ko kuma aka samu akasin tatike shi a teburin caca. Yana da shekaru talatin da biyu cif, yayin da ya fara aiki da Zenith Bank reshen jihar Kano, daga bisani akai masa transfer zuwa garin Katsina. *** Madaidaiciyar drawer ce da ke manne da bango, kusan rabin ta shak'e yake da mak'uden kuɗaɗe dalar Amurka. A gaban drawer Hajiya Daso ce take kwasar kuɗi tana zubawa a jakar da ke rataye a kafaɗarta, ta gama ta zuge, sannan ta maida drawer ta rufe kamar yadda ta same ta. Juyowar da zata yi suka yi ido huɗu da Sadam, wanda zuwanshi gidan kenan daga Kano inda yake aiki a wancen lokacin. Tana ganinshi gabanta yayi mummunar bugawa dan kaf cikin yaran gidan babu wanda ta tsana kamar sa, haka kuma babu wanda yayi mata karan tsaye irin shi. "Wato dama duk satar da ake a gidan nan ke ce ko? Sai kizo kina ja mana bala'i, ya rink'a ganin mune muke satar masa kuɗi. To wallahi ko ki mayar da su ko kuma kinsan abinda zai biyo baya." Duk da bugun zuciyar Hajiya Daso da ya tsananta, amma haka ta dake, ta saki wani murmushin yan duniya, ta k'ara matse jakarta, ta juya ba tare da tace da shi komai ba. Bayan rigarta ya janyo tun k'arfi, ya wurgar da ita a tsakiyar ɗakin. "Kinji abinda nace ai ko? Wallahi ko ki mayar da kuɗin nan ko kuma da ya fara cigiya zan faɗa mishi kece ɓarauniyar gidan nan." Shewa Hajiya tayi, tare da buga k'afarta. "Wallahi, wallahi sai kayi da-na-sanin wannan rashin kunyar da ka mun. Kai har ka isa kasa k'azamin hannunka ka farɗo ni haka? Zaka gane kayi da Hajiya Daso." Da sauri ta juya, ta koma ɗakinta, ta fara kaiwa-da-kawowa tana tunanin abin yi tun Alh. Baffa bai dawo ba, dan ta san matsawar ya dawo ya fara cigiyar kuɗinsa, to babu abinda zai hana Sadam faɗin halin da ya same ta a ɗakinshi. Ita kam da ta mayar da kuɗin nan, ta gwammaci barin gidan, domin ba tun yau take neman wannan damar ba. Asali ma wannan ne yasa ta shanye bak'incikin da take fuskanta a gidan, ta k'i tafiya kamar yadda sauran matattakin da ya aura suka tafi. Wata shawara ce ta faɗo mata, hakan yasa ta tashi ta yafa gyalenta tare da faɗin "Ban ga ta zama ba." Gidan aminiyarta Haj. Indo ta dosa, daga nan ta zayyana mata labarin abinda ya faru, a haka suka mik'e suka tafi wani k'auye gurin wani gingimemen boka. Bayan ta yi ma boka bayanin abinda ke tafe da su ne ya fara tsubbace-tsubbacenshi, a k'arshe ya basu wasu layoyi, ɗaya ta rufin baki ce zasu saka a bakin mataccen damo, ɗaya kuma idan suka jefa ta a tsohuwar rijiya to Alhaji zai yi ma Sadam mummunan wulak'anci, k'arshe ma ya kore shi baki ɗaya, shi kuma Sadam ɗin idan ya bar gidan, ko dai ya haukace ko kuma ya koma mai wata irin bak'ar zuciya, wacce zata kawar da shi daga addininshi, domin muddin ya cigaba da yin sallah da sauran al'amurran addini yadda ya kamata, to asirin zai iya karyewa, haka kuma duk ranar da ya dawo gida, to fa Hajiya Daso sai dai ta shiga duniya ko kuma ta haukace. Da wannan sharaɗin boka ya ba su layun, tare da k'ara jaddada masu yadda za su gudanar da aikin. Haka suka ansa, hajiya ta buɗe bakin jaka ta zube mashi kudi, suka ɗauka suka tafi, a ranar ba su koma gida ba sai da suka tabbatar sun aiwatar da duk abinda boka ya faɗa musu. *** 1 Ranar wata juma'a da misalin k'arfe takwas na dare, wanda yayi dai-dai da sati ukku kenan da faruwar abin, palon Alh. Baffa cike yake dam da yaran gidan gaba ɗayansu babba da yaro. Bala'i kawai yake yi, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya tsare su cewar su fito masa da kuɗin da suka ɗaukar masa ko kuma ran kowa sai ya ɓaci a gidan baki ɗaya. Suna haka Sadam yayi sallama da jakarshi, zuwan shi garin kenan, yayin da ya samu gefe ya zauna, anan ya fahimci abinda ke faruwa, hakan yasa ya juya yana kallon yadda Hajiya Daso tayi kicin-kicin da fuska, saboda rashin imani, da rashin tsoron Allah irin nata. Ya buɗe baki kenan zai yi magana, Hajiya tayi karaf, "Yawwa ga ɓarawon kuɗinka nan Alhaji. Ga shi nan ya iso." "Ban fahimce ki ba Hajiya. Kina nufin kinsan wanda ya ɗaukan mun kuɗi kika bar ni ina kumfan baki haka?" "Sosai kuwa, Sadam ne shi na gani a ɗakinka ranar da kace an ɗauki kuɗin." Kafin Sadam yayi wani yunk'uri Alh. Baffa ya isa gabanshi ya wanke shi da mari, bai ankara ba ya kara ɗora mishi wani. "Ni zaka ɗaukan ma kuɗi? Wato kaje kayi caca da su ko? To baka isa ba tsinanne, wallahi sai ka fitar mun da kuɗina, ɗan iskan banza, ɗan iskan wofi, kasan wahalar da na sha na tara kuɗina? Wato ka gansu a ajje sai ka ɗauka na baitil mali ne, shine ka kwashe mun rabin kuɗi ka zo nan ka zauna, wallahi baka isa ba, sai ka fito mun da kuɗina."6 Mik'ewa yayi da sauri, yana shafe kumatun da ya sha mari. "Na ji ni ɗan caca ne, amma ban taɓa ɗaukar abin wani ba. Kowa da ke nan ya san ni ba ɓarawo bane, dan haka ga ɓarauniyar kuɗinka nan a gefenka." "K'arya kake ɗan iska. Shekara ta nawa da Hajiya Daso, bata taɓa yi mun sata ba sai yau? Ku ɗin dai kune ɓarayin gidan. Dan haka ka fito mun da kuɗina ko kuma ka fita ka bar mun gida bani k'aunar ganin ka har abada, na tsane ka na tsani mai k'aunarka Sadam. Dan iskan yaro wanda bai san daraja da mutuncin kansa ba, ɗan caca kawai. A haka zaka k'are, ka mutu kana caca. Fitan mun a gida kafin in fasa shegen kanka." Hawaye ne suka fara bin kumatun Sadam ganin yadda taimako ke neman zame mashi bala'i, hakan yasa ya juya yana kallon 'yan uwanshi hawayensa na cigaba da yayyafowa. "Ku faɗa mishi ni ba ɓarawo bane, wallahi na ganta, na ganta da idanuna, wallahi, wallahi na ganta." Ya ɗaga hannu yana rok'onsu, amma haka kowannensu ya kawar da kanshi duk kuwa da bak'incikin abinda mahaifinsu yayi mishi da suke ji. Hannunsa Alh. Baffa ya kama ya wurgar da shi a waje, ya dawo ya ɗauki jakar da ya shigo da ita ya wurga mishi. "Ka fitar mun a gida tsinanne, wanda bai san mutuncin kanshi ba. Kuma har abada bana son in k'ara haɗa fuskata da taka. Sannan kuma kuɗina da ka ɗauka, ka ɗauki bala'i da masifa, ka ɗauki wutar jahannama."8 Kuka ya dinga yi yana rok'onshi, amma yayi banza da shi, haka kuma kaf 'yan uwanshi babu wanda yayi yunk'urin kare shi, hakan yasa ya mik'e, ya kakkaɓe jikinsa, ya share hawayensa, ya kalli mahaifin nasa, ya girgiza kai kawai ya juya ya fita, ya shiga matorshi ya koma Kano wurin aikinsa, daga nan ya fara neman transfer zuwa Maiduguri, amma bai samu ba sai dai aka maida shi katsina, duk da haka ya cigaba da neman ta Maidugurin, wacce ya samu daga baya, tun daga wannan lokacin yake kwana da wannan bak'incikin yana tashi da shi, hakan kuma yasa tun daga wannan ranar bai k'ara haɗa fuskarshi da ta mahaifin nashi ba, har sai yau da Allah mai kowa mai komai yayi nashi ikon a kansu. Sai da ya shekara biyar cif-cif da tafiya, sannan Haj. Indo aminiyar Haj. Daso tayi silar tona asirin, ta sanadiyyar wani gagarumin faɗa da suka yi kasancewar labari da Haj. Daso ta samu na cewar Alh. Baffa na shirin auren aminiyar tata, yayin da ita kuma ta sanar da Alhaji irin tuggun da Hajiyar ta rink'a haɗawa a gidansa, daga ciki kuwa hadda tafiyar Sadam. Wannan ne yayi sanadiyyar fara ciwonshi, yayin da ya sa malamai suka cigaba da addu'a, har asirin ya karye, wanda hakan ne ya ba Sadam damar takowa yaga mahaifin nasa. *** Hannunshi Alh. Baffa ya k'ara k'ank'amewa, idanunsu na zubar da hawaye. "Na san laifina Sadam, ba sai ka tuna mun ba. Na kasance mai son zuciya a dukkan al'amurrana, na kasance mutum wanda ya fifita son abin duniya akan 'ya'yan da ya haifa, na kasance mutum mai tarin dukiya amma son abin duniyar da nake da shi ya mayar da ni marar wadatar zuciya. Ina da-na-sanin lokuttan da suka gabata ba tare da na kyautata maku ba, nayi sanadiyyar taɓarɓarewar tarbiyyar iyalina. Sadam ka yafe mun, ka gafarta mun dan Allah mahaliccinmu. Ina ji a jikina, ina numfashi a wannan duniyar ne kawai dan in samu damar neman afywarka, ka gafarta mun dan haihuwar da na yi maka..." Bai ida kai k'arshe ba, ya ja wani irin numfashi. Hannunsa da ke sagale a cikin na Sadam, ya zame ya faɗi k'asa sharaf. ***Jay.. K'arfe sha biyu na ranar juma'a SS ya dawo gidan, ga mamakinshi babu kowa a palon sai Farouq da Jafar da suke zaune cikin shiri suna jiran dawowarsa. "Wai har kun gama shiryawa?" "Mun gama Yaya, kai kawai muke jira." "Ina su Rukayya fa?" Ya tambaya yana kallon Jafar. "Rukayya bacci take, ita kuma Mammy tun ɗazu kuka kawai takd yi, na ce tayi hak'uri amma bata daina ba." Shima ya fashe da kuka, ya tashi ya koma jikin Babanshi tare da k'ank'ame hannuwansa. "Kuka? Na menene?" Yayi maganar a cikin zuciyarsa. A fili kam bai iya cewa komai ba, illa Jafar da ya ɗaga sama, suka wuce ɗakinshi, ya gama shirya jakarsa, sannan ya kamo hannunsa tare da jawo jakar a ɗayan hannun, suka fito palon. "Farouq kwashi kayan nan duk ka saka a mota ka jira gamu nan fitowa." "Ok." Ya ansa da shi, yayin da ya iso ya anshi jakar, ya wuce waje shi kuma da Jafar suka isa bakin k'ofar ɗakin da take ciki. Sallama ya fara yi, sai dai ba ta da niyyar ansawa, domin kuwa ta inda yake ma yana jiyo yadda sheshshekar kukanta ke tashi. "Jameela." Ya kira ta a karon farko, sai dai bata ansa ba, haka kuma bata tsagaita da kukan da take yi ba. Zuciyarsa ce ta fara sak'e-sak'en dalilin kukan nata, amma ya rasa gano komai, a k'arshe ya yanke shawarar watak'ila tana tunanin yadda zata yi ido huɗu da mahaifanta ne. Labulen k'ofar ya buɗe tare da tura kansa a hankali, a duk'unk'une take can k'arshen gado jikinta sanye da doguwar riga, ta yane kanta da mayafin rigar, ta haɗa kai da gwiwa, kuka kawai take tsakaninta da Allah, yayin da Rukayya ke kwance a gefe tana shan baccinta. "Jay." Ya kira ta da wata kasalalliyar muryar da ta sa ta ɗago rinannun idanunta cikin sauri, domin kuwa muryar Kazaurenta ta ji ba wai ta SS Tafseer ba. "Kukan me kike yi?" Maganar da ya k'ara yi ce yasa ta fahimci ainahin wanda ke gabanta, cikin takaici, ta mayar da kanta ta kifa kamar yadda take a da. "Kina tunanin yadda zaki haɗu da su Baffa ko?" Shiru tayi bata tanka shi ba, hakan ya bashi damar cigaba. "Kada wannan ya sa ki damu kanki. I promise you zan san duk yadda zanyi ki samu gafarar mahaifanki. In sha Allahu zan dawo miki da farincikin da kika rasa a rayuwarki. Tashi ki k'arasa shirinki mu tafi." A hankali ta fara share hawayenta, ta ɗago tare da zuba mishi idanunta da suka yi jajur saboda tsabagen kuka. Kanta take girgizawa, a lokaci guda ta fara magana. "Ina ji a jikina iyayena ba za su taɓa yafe gagarumin laifin da na musu ba, Ina ji a jikina nayi bankwana da duk wani farinciki na rayuwa. Hakan yasa nake so kayi hak'uri da abinda zan faɗa, ba wai kuma hakan na nufin ban gode ma karamcin da kai mun ba." Takowa ya fara yi zuwa cikin ɗakin, hannuwansa cikin aljihu ya jingine da bango yana kallon ta. "Ban fahimce ki ba?" "Bazan iya barin garin nan ba, ban san da wane ido zan kalli iyayena ba. Kayi hak'uri." "Why now? Bayan duk shirin da muka gama yi? After all na ce miki zan nema miki gafararsu, I'll put all the blame on me, dan haka ki share hawayenki, ki tashi muje please. Kada muyi dare." Bakinta ne ya fara motsi alamar tana son yin magana, sai dai bata san ta ina zata fara ba. Tsayuwarsa ya gyara, a karo guda ya sa hannu ya shafi sumar da ke kansa, ya juya kamar zai fita, kasancewar yadda ransa ke shirin ɓaci lokaci guda. Har ya kai k'ofar fita, sai kuma ya juyo, kallon shi take itama, hakan yasa ya kawar da kansa tare da ce ma Jafar ya je palo ya jira shi, sannan ya dawo inda ya bari ya tsaya. A yadda ya fara maganar zaka fahimci ya gane manufarta, ya kuma fahimci abinda ta kasa furtawa, duk kuwa da motsin da laɓɓanta ke yi, hakan kuma ba zai rasa nasaba da nauyin sanar da shi abin take yi ba. "Haba Jameela. Ke fa mace ce mai daraja. Halittar da Allah ya ɗaukaka fiye da sauran halittunsa. Yanzu har kin manta duk wani bak'inciki da kika shak'a ta sanadiyyar Kazaure? Har kin manta irin rayuwar taskun da kika shiga a gidansa? Mutumen da ya mayar da ke abar tausayi ne har yake birge ki? Kina jin baza ki iya barin garin nan saboda shi ba ko? Fine. Ki tashi in mayar da ke gidan nasa, ki tashi in mayar da ke wurin Kazauren da kike so."2 Ya juya jikinsa babu k'wari, zuciyarsa na harbawa, yana jin yau Jay da k'anwarsa ce babu abinda zai hana ya zubar mata da hak'oran gaba. In banda so bala'i ne, amma me kuma zata yi da azzalimin mutum irin Kazaure? Me zata yi da mashayi, mai yawo lungu-lungu yana neman inda zai buga caca. Mutumen da ya wulak'anta ta, ya wulak'anta kyautar da Allah ya mishi, mutumen da bai san mutuncin kansa ba, balle ya san na wani.5 "Ba haka ba ne fa." Ta katse mishi tunanin ta hanyar maganarta. A fusace ya juyo, "To ya ne? Bayan Kazaure wa kika sani a garin nan da kike son zama da shi? Shi ɗin dai ne. Sai dai ina so ki fahimci cewar matsawar kika koma ma mutumen nan, hak'k'in yarinyar nan da ke kwance ma kawai ba zai barki ba. Me Kazaure yake da shi wanda baza ki iya yakice shi a birnin zuciyarki ba? Me ya tanada miki da kike kwaɗayin komawa gare shi banda tarin masifa? Ko kuma kina tunanin baza ki taɓa samun miji kamar sa ba? Haba Jay, kiyi tunanin da basirar da Allah ya miki mana. Ke mace ce da babu namijin da zai kalle ki ya barki matsawar zai samu dama, ke mace ce da ke da wasu qualities da ba kowacce mace ke da irinsu ba, trust me, zaki samu wanda ya dama Kazaure a komai, wanda zai so ki, ya ɗaga darajarki, ya baki duk wani farinciki da ya dace da mace irin ki."1 Ya k'arasa maganar da wata tattausar murya, tamkar mai shirin yin kuka. Kukanta ta cigaba da yi, kukan nata ba k'aramin taɓa zuciyarsa yake ba, haka dai ya daure ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya sa hannu ya ɗauki Rukayya da jakar kayansu ya fita ya saka a mota, sannan ya dawo. A yadda ya barta, haka ya dawo ya tadda ta, da alama ko motsi bata yi ba. "Tashi muje in mayar da ke inda na ɗauko ki. Dan na riga nayi waya ma Hajiyarmu cewar zamu zo gida yau, dole in ɗauki hanyar Katsina komin dare."4 Bata ce uffan ba, haka kuma bata da niyyar motsawa. "Ba ki ji me nace ba ne?" "Ni nace maka ina son komawa ne?" Tayi maganar cikin kukan da ya sa ya rasa natsuwarsa, kansa ya ɗaga sama, tare da tura leɓansa na k'asa cikin bakinshi, ya rasa gane manufarta, ya rasa fahimtar ainahin abinda ke zuciyarta. "Ya kike so nayi Jay? Please tashi muje kawai." Bata yi magana ba ta mik'e tare da gyara mayafin jikinta, yayi gaba, sannan ta rufa masa baya. Sai da ta fita, sannan ya kashe duk wasu electronics na gidan, ya fito ya rufe ko ina, ya same su a motar sunyi shiru, Jafar ma duk son wasansa, da ka kalle shi kasan yana cikin damuwa. Kujerar mai zaman banza ya koma ya mik'a ma Farouq key ɗin motar, dan yadda yake jin zuciyarsa, idan shi zai yi tuk'in to watak'ila ajalinsu ne ya zo. Bayan sun fito yana shirin ɗaukar hanyar fita gari, SS dake danna waya ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Ka fara shiga ta Nuj, zamu ajje su Jameela kafin mu wuce." "Me sa Yaya? Ta fasa tafiya ne?" "Ya isa da Allah. Kayi abinda nace maka." "Daddy nima a ajje ni da su, ba zan bika ba." Jafar da ke zaune a gefenta yayi maganar, idanunsa cike da hawaye, tare da sa hannu ya mak'ale hannun Jay da fuskarta ke lulluɓe cikin mayafi. Sai a lokacin ta ɗago, taga dai gadan-gadan gidan nata suka dosa, haka kuma yadda Jafar ya rik'e ta ba k'aramin tausayi yaron ya bata ba. Rungume shi tayi ta cigaba da zubar da hawaye, tana ganin sun zo titin da daga shi sai kwanar gidansu, ta ɗago da idanunta. "Farouq ina zaka je?" "Yaya yace zamu ajje ku gida." "Juya mu tafi inda zamu, ni bamu yi haka da shi ba." Baki Farouq ya washe dan dama ba da son ransa aka ce ya sauke su ba, haka kawai yake jin ta tamkar 'yar uwarsa, kasancewar a 'yan kwanakin da tayi a gidan, sun shak'u sosai, ta yadda zasu zauna su sha firarsu, tamkar sun daɗe da sanin juna. Wayar da ke hannun SS faɗuwa tayi, a karo guda ya juyo da kansa, cikin rashin sa'a ya sauke idanunsa a kanta, ita da Jafar sun mak'alk'ale juna kamar wani na shirin raba su. Murmushi ta sakan mishi, wanda ya sanya shi faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" a bayyane. Da sauri ya juya, fuskarsa ɗauke da murmushin shima, sai dai yana ta bonewa dan baya so su gane yanayin da yake ciki. "Yaya ba ka ce komai ba. Ko ba ka ji me Aunty Jay ta faɗa ba?" "Me tace?" Ya ɗago yana satar kallonta ta wutsiyar ido. "Zata bi mu mana." "Ok. Allah ya sauke mu lafiya." "Abinda kawai zaka ce kenan Yaya?" "Akwai abinda ya fi addu'a ne?" "Babu fa, amma ya kamata ka yi farincikin ladar da zaka samu idan ka kaita wurin su Baffa." "Takura ta nayi ai. To meye abin farinciki tunda ba da son ranta zamu je ba?" "Ni fa ba wanda ya takura ni. Ina son in je mana. Kai ne dai baka fahimce ni ba." Jay da ke gyara ma Jafar da yayi bacci a jikinta kwanciya tayi maganar, kanta a k'asa. Juyowa yayi ya k'are mata kallo, tausayinta ya cigaba da wanzuwa a cikin zuciyarsa, bai iya cewa komai ba sai girgiza kai da yayi ya maida kallonsa a wayar da ke hannunsa. ** Kallon garin take tamkar bak'uwar da bata taɓa zuwa ba, wani iskan rahama ta rink'a jin yana ratsa ta, a karo guda wata natsuwa ta rink'a sauka a cikin zuciyarta. Shekaru biyar ɗin da tayi rabonta da garin yasa ta ga canje-canje da dama, taga irin cigaban da aka samu sosai. "Kowa ya bar gida, gida ya bar shi." Abinda ta faɗa a cikin zuciyarta kenan, har sai da SS da ya kasa ɗauke idanunsa a kanta, ganin bayyanannen farinciki a kan fuskarta yace "Ya kike ji a cikin zuciyarki?" Murmushi tayi, kanta a k'asa tana kallon yadda Jafar da Rukayya suke wasansu. "Ba zan iya misaltawa ba. Wani fannin farinciki, wani fannin kuma fargaba da tashin hankali." Kamar ya ce wani abu, sai kuma yayi duba ga Farouq wanda tuk'insa kawai yake, amma da alama kunnuwanshi na gare su, hakan yasa yayi shiru ya gyara zamansa. Titin GRA Farouq ya ɗauka, yayin da zuciyar Jay tamkar zata fasa k'irjinta ta fito. Wannan karon fargaba da tsoron da take ji, gaba ɗaya sun bayyana ne a fuskarta, hannun yaran da ke gefenta kawai ta matse k'amk'am a nata hannun har suka kawo k'ofar gidan Alh. Kabir Sani. **Sadam+ "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Sa'id da ke tsaye gefensu ya faɗa, tare da matsawa yana duba idanun mahaifin nasu, kasancewar shi likita, anan kuma ya tabbatar da Baban nasu ya ansa kiran mahaliccinsa. "Lafiya?" Sadam da ke zaune ba tare da ya fahimci abinda ke faruwa ba ya tambaya yana kallon Sa'id. Bai iya cewa komai ba, illa kafaɗarshi da ya dafa, ya juya ya fita idanuwansa taf da hawaye, hakan ya ba sauran 'yan uwan damar k'arasawa bakin gadon domin gane ma idanuwansu abinda ke wakana. "Ya rasu." Cewar ɗaya a cikinsu, hakan yasa Sadam ya mik'e ya koma jikin bango ya dafe kanshi, kuka yake bil hak'k'i da gaskiya, har sai da 'yan uwan suka tausaya ma yanayin da yake ciki. Basu ɓata lokaci ba suka fito da gawar, bayan anyi duk abinda ya kamata, suka shige motocinsu, suka ɗauki hanyar Dutse. Shigarsu gidan kenan, tun ba'a shigo da gawar ba suka samu mutane na faman rirrik'e Haj. Daso da kanta ya mimmik'e tsaye, tana faman k'wacewa ita a dole sai ta fice. Hauka take tuburan, domin kuwa duk wani abu da ke ɗakinta sai da ta fasa shi, kafin aka samu taimakon k'attin maza majiya k'arfin da suka rik'e ta. Sa'id da ya fara shigowa ne ya ci karo da diramar da ake yi, gefe ya jingine yana kallon yadda k'aik'ayi ya koma kan mashek'iya, ta wani fannin kuma mutuwar mahaifinshi na damun zuciyarsa. Kallon mutanen da suka rik'e ta yayi "Ku sake ta, dama zaman jiran lokaci kawai take yi." Suna sakinta kuwa ta runtuma da gudu, ta fita a gidan, yayin da jama'ar k'ofar gida ma babu wanda yayi gigin tarye ta. Gawar suka shigo da, 'ya'yan nashi ne suka taimaka wurin gyara ta, in banda Sadam da har yanzu bai daina zubar da hawaye ba. A haka suka ɗauke shi zuwa makwancinshi na gaskiya, suka saka shi cikin k'asa, duk kuwa da irin dukiyar da ya tara, wacce shi bai ci ba, bai kuma bar 'ya'yansa sun anfana da ita ba lokacin da yake rayuwa. Bayan sun gama duk abinda ya kamata, suka dawo gida suka cigaba da zaman makoki, sai dai kuma ruhi da gangar jikin Sadam Baffa Kazaure, ko alama basa tare da shi. Domin kuwa sunyi nisa sosai ga al'amurran da suka addabi rayuwarsa, wanda suka haɗa da ɓatan Jay, da kuma mutuwar mahaifinshi. ***Jay. Idanuwanta da ke kulle ta buɗe lokacin da ta ji motar ta tsaya, hakan ya tabbatar mata da sun shigo cikin gidan. Ido ta ware tana kallon yadda gaba ɗaya gidan ya canja mata, yayin da maganar SS ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta dulmiya. "Muje ko?" Yayi maganar lokacin da ya fito, yasa hannu yana k'ok'arin buɗe masu k'ofa. Kai ta fara girgizawa, zuciyarta a raunane, haka hawaye suka gagara zubowa a busassun idanuwanta. "Its okay, na fahimci abinda kike son faɗa, ku fito mu je please." SS yayi maganar ta hanyar katse mata ta ta maganar da ta so yi. Bata iya cewa komai ba, illa hannun Rukayya da ta kama ta fitar da ita, ta zuro k'afafuwanta waje, ta biyo bayanta, sannan ta juya ta fito da Jafar shima. Wata doguwar baranda suka mik'a, wacce da alama ita zata sada su da k'ofar shiga, duk kuwa da kasancewar ba su da tabbas, ganin yadda aka canja tsari da yanayin gidan baki ɗaya. A k'ofar palon suka tsagaita, SS ya danna doorbell ɗin da ke mak'ale jikin rufaffen k'yauren, wata yar budurwar da bata fi shekaru ashirin zuwa da ɗaya ba, ta iso, ta buɗe k'ofar. Cikin rashin sani ta gaishe da su, SS ya tambaya "ko masu gidan suna ciki?" "Suna nan." Ta bashi ansa lokacin da ta koma gefe, hakan ya bashi damar sanya kai ciki, ya juyo yana yi ma su nuni da su shigo suma. Kanta a k'asa ta ɗaga k'afarta dak'yar, ta shigar a tsararran palon da ya wadatu da sanyin AC, mai haɗe da k'anshin turaren wuta. A karo guda bugun k'irjinta ya cigaba da tsananta lokacin da suka k'arasa cikin palon, kowannensu ya nema ma kanshi mazauni. Wucewa 'yar budurwar tayi zuwa ciki domin ta sanar da masu gidan, hakan yasa SS ya kai duba gareta, yanayinta kaɗai, ya fassara tashin hankalin da ke shimfiɗe cikin zuciyarta. Gaban Goggo da ke biye da yar budurwar da taje kiranta ne yayi mummunar faɗuwa lokacin da ta tunkaro palon tun bata k'arasa fitowa ba. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Shine kawai abinda ta iya furtawa a dai-dai sa'adda ta ziro k'afarta cikin palon da suke. Kamar wacce aka mintsina, ta ɗago idanunta da suka zama tamkar garwashin wuta, sai dai babu ɗigon hawaye ko k'alilan, ta sauke su a kan kyakkyawar dattijuwar mahaifiyarta, wacce rabon da ta ga wannan fuskar ta ta mai cike da haske da annuri, shekaru biyar kenan cif-cif. Hawayen da take ta son su zubo mata ne suka fara kwarara tamkar an buɗe famfo, a haka Goggo da ta kasa ɗauke idanunta a kan Jay ta idasa shigowa, ta zauna daɓas, a kujerar da ke gefen Farouq. Duk da bak'i da lalacewa da jikinta yayi, hakan bai hana mahaifiyar ta ta gane ta ba, haka kuma duk da shekarun da ta kwasa ba tare da su ba, haka zalika bai canja k'auna da soyayyar da take mata ta ɗa da mahaifi ba. "Ummi!" Goggon ta fada cikin wata irin murya mai k'arfin amo, ba tare da ta maida kai ga gaisuwar da mutanen wurin ke yi mata ba. Kai take jinjinawa, alamar ita ɗin ce, yayin da zafafan hawayen da suke zuba, ba su tsagaita mata ba, har zuwa lokacin da Goggon ta iso gabanta ta mik'ar da ita, ta haɗa ta da jikinta suka k'ara fashewa da wani gagarumin kukan da ya tsuma zuciyar SS da ta Farouq, har ma da ta 'yar budurwar da ta shigo ɗauke da tray domin kawo masu abubuwan motsa baki. Babu wanda yayi gigin tsayar da su, sai da suka yi mai isarsu suka gama, sannan Goggo ta zaunar da ita, ta juya tana kallon sauran jama'ar wurin. SS ne ya fara gaishe ta, ta ansa tana mai mai son tuna inda ta san fuskarsa, sai dai ta kasa a haka ya gabatar da Jafar a matsayin ɗanshi, Farouq kuma k'aninshi. Gaishe ta suma duk suka yi, ta juya tana kallon Rukayya. "Wannan kuma fa?" Shiru kawai suka yi babu wanda ya iya ansa ta, sai Jay da ta zube a k'asa tare da dafa gwiwoyin k'afarta tana kuka, tana neman yafiyar mahaifiyar ta ta. "Ki yafe ni Goggo. Ki gafarta mini, ki ji k'aina ki yafe mun laifin da na yi. Na san na bak'anta zuciyarku, na san nayi laifin da ban cancanci yafiya ba, amma kuyi hak'uri, ku gafarce ni domin Allah." "Kinyi kuskure Baby, kinyi babban laifi na fifita namiji akan iyayenki, sai dai kuma mu muka taimaka miki wurin hakan, mu ne bamu tsaya mun kula da ke mun tarbiyyantar da ke ta hanyoyin da musulunci ya tanada ba, mune muka bi son zuciyarmu, muka bi da ke ta yadda muke so, dan haka ba ke kaɗai zaki nemi yafiya ba Ummi, nima ki gafarta mun, ki yafe mun a bisa irin tarbiyyar da na baki, wacce duk itace ta kai mana rayuwa izuwa haka." Ta mik'ar da ita ta zaunar a gefenta, a lokaci guda ta daga hannunta sama "Allah nagode maka da ka dawo mun da farincikina. Allah nagode maka da ka bani wata dama domin gyara ɓannar da nayi, Allah nagode maka da ka dawo mun da Ummi lafiya."4 Juyawa tayi tana kallon SS, ta rasa ma abinda zata ce da shi, gashi tana jin a zuciyarta kamar ta san fuskarshi, sai dai ta kasa tuna ko a ina ne, a k'arshe ta mik'e tana cewa "Barin sanar da mai gidan. Ta so muje Ummi." Ta faɗa tana kallon Jay da har yanzu kuka kawai take yi, sai dai ta samu wani ɗan sassauci ganin yadda Goggo ta anshe ta hannu bibbiyu. Girgiza kai tayi, alamar baza ta je ba, bata takura ta ba, ta juya cikin hawaye da murna ta doshi part ɗin Baffa da ke hagu da palon da suke ciki. Dawowarshi kenan daga sallar isha'i ya zauna da niyyar fara kallon labarun duniya a tashar Aljazeera, Goggo ta shigo da sassarfa, tamkar wacce aka biyo da gudu. "Lafiya?" Baffa ya tambaya yana gyara zaman medical glasses ɗin dake idonsa. Bata iya cewa komai ba, illa "Akwai babban al'amari a palon bak'i, taso ka gani Alhaji." "Me ke faruwa?" "Ta so ka gani da idonka." Ta juya zata fita, yayin da ya ajje remote ɗin hannunsa, ya mik'e ya rufa mata baya. Duk da yawan shekarun da ya kwasa bai ganta ba, da canjawar da halittarta tayi, da kuma baya da ta juya mashi, ba shi yasa ya mance yanayin wacce ke zaune gabansa ba, ba shi kuma ya hana shi danne k'auna da soyayyarta da suke barazana da lafiyar da Allah ya bashi ba. Cikin tsananin fushin da ya kasa ɓoyuwa a saman fuskarsa ya juya da zumar komawa inda ya fito, SS yayi saurin mik'ewa, ya isa gabanshi tare da rissinawa ya gaishe da shi. "Sagir?"3 "Nine Alhaji." "Dama kana duniyar nan?" "Tabbas ina raye. Sai dai ba matsala ta ba ce ta zo da ni a yanzu." "Ta wacece kenan?" "Ta Jameela ce." "Wacece haka kuma?" "Jameela dai 'yarka." "Ni nike da 'ya Jameela? A ina ka samu wannan labarin?" Yayi maganar yana nuni da k'irjinsa. "Ka ganta fa Alhaji. Ummi ce ta dawo kallo nan ka ganta." Goggo tayi maganar tana nuni da inda Jay ke zaune tana wani irin kukan da Baffa ke jin shi har cikin zuciyarsa. Juyowa yayi a fusace, ya fara magana cikin wata dakakkiyar murya mai k'arfin amo da karsashi. "Ban san maganar da kuke yi ba, domin ni Alhaji Kabiru bani da wata 'ya mai suna Ummi, ko kuma Jameela kamar yadda kai ka faɗa. Dan haka minti ɗaya na ba mutanen da suke cikin palon nan su tattara su fita su bar mun gidana." Kuka Goggo ta saka mai wani irin sauti, wanda yasa Rukayya fashewa da kuka ta matsa ta k'ank'ame mamanta, a dai-dai lokacin Baffa ya kai idanunsa kan 'yar yarinyar da ke asalin kama da mutumen da ya fi tsana a gaba ɗaya duniyar nan, wanda yayi silar rugurgujewar jin daɗi da farincikinsa. Kawar da kansa yayi, sannan ya juya ya fara tafiya, yana kwaɗa kiran mai gadi. Ganin haka yasa duk suka mik'e, suka doshi hanyar fita, amma Goggo ta kama hannun Jay da Rukayya ta rik'e k'ark'adam. "Me sa ka bar irin mutanen nan suka shigo mun gida? Me sa baza ka fara neman izinina kafin wani ya shigo ba?" "Ayi hak'uri yallaɓai, ban san za'a samu matsala ba wallahi." "Tashi ka fitar mun da wannan." Yayi nuni da Jay, sannan ya cigaba. "Kuma daga yau, ko katangar gidana bance ka barta ta kara taɓawa ba." Cikin tashin hankali mai gadin ya mik'e yana raba ido, hakan yasa Goggo ta k'ara matse hannun Jay "Babu inda zata je Alhaji, idan kuma ka matsa akan a fitar da ita, to k'afarta k'afata, sai dai duk mu bar maka gidan ni da ita." "Ya isa haka." Cewar SS da ya matso gabansu. Sai kuma a yanzu Goggo ta tuno inda ta sanshi. "Sake ta muje." Yayi maganar yana kallon Goggo, yayin da Baffa ya juyar da kai. "Matsawar kika k'ara ɗaga k'afarki daga inda kike, to ki tabbatar zamanmu ni da ke ya zo k'arshe Maryama."5 Daga haka ya juya da sauri, kasancewar wasu zafafan hawaye da suka taho suka wanke dattijuwar fuskarsa. Suna kuka suna komai, haka SS ya raba hannun Jay da ke cikin na Goggo da kalaman rarrashi, suka fita daga palon, suka doshi inda suka yi parking motarsu.1 *** B abu wanda ya iya cewa wani abu a cikinsu, hatta da yaran. Kowa ka kalla a cikin motar, akwai abinda yake sak'awa a k'asar zuciyarsa, in banda Jay da har yanzu sheshshekar kukanta ke tashi, ta wani ɓangaren kuma tana da buk'atar k'arin bayani jin yadda Baffanta ya kira sunan SS kai tsaye, wanda ita bata ma san cikakken sunan nashi ba. Farouq ne yayi gyaran murya, idanunsa a kan titi. "Ya kamata ace Baffa yayi hak'uri ya saurari abinda ke tafe da mu, duk da dai naga alamar kun san juna kai da shi." Shiru SS yayi mashi, hakan yasa ya ɗan juyo yana satar kallon shi. "Yaya fa. Baka ji me nace ba ne?" "Ina jinka Farouq, amma sanin kanka ne yanzu ba lokacin magana ba ne, dan haka ka kula da tuk'inka muje gida tukun." Babu wanda ya k'ara cewa uffan, har suka shigo cikin Barhim, unguwar da ta kasance inda mahaifiyar tasu ke zaune. Gida ne madaidaici, mai yalwar wurin ajiyar motoci, (parking shade) inda suka samu mota guda biyu a ajje, ɗaya lullube da riga, yayin da ɗayar ke ajjiye a gefe, da alama ita aka fiya hawa. Sai da Farouq ya gama gyara parking, sannan kowa ya fito, SS ya buɗe bayan motar ya ɗauko Jafar wanda yayi bacci a saman kafaɗarsa, Jay ta kamo hannun Rukayya suka mik'a zuwa cikin gidan. Fuskar dattijuwar matar da suka samu zaune k'unshe da kyakkyawan murmushi, hakan ya fito da asalin kamarsu da SS. Farouq ya isa ya zauna gefenta yana gaishe da ita, labbanshi k'unshe da murmushin farinciki shima. "Sannunku, sannunku." Fara kyakkyawar dattijuwar mai shekaru kusan hamsin da bakwai ta rink'a maimaitawa, ta yi saurin kama hannun Rukayya tana kiran "yar budurwa" duk da ba taɓa ganin su ta yi ba, daga ita har Jameela. Karamcin matar ne ya sa Jay shafe hawayenta cikin gaggawa, fuskarta da murmushin da iyakarsa laɓɓanta, ta rissina har k'asa tana gaishe da ita. Cikin jin daɗi ta ansa, a karo guda ta kai duba ga fuskar SS wanda babu walwala a tattare da shi, lokacin da yake shimfiɗar da Jafar saman doguwar kujera, ya koma gefe ya zauna. "Sannunku Hajiya, ina wuninku." "Lafiya lau Sadic. Ya hanya?"1 Jin sunan da Hajiya ta kira SS da shi wanda ya sha ban-ban da wanda Jay ta ji Baffanta ya kira shi yasa tayi saurin ɗaga kai tana kallon yanayin da ya ke ciki. Ba tare da wata damuwa a fuskarsa ba ya ansa da "Alhamdulillah. Mun same ku lafiya?" "Lafiya lau muke. Ya ka ji da rigimar Farouq?" "Ga shi nan fa, exams zai fara amma saboda rigima sai da ya biyo mu, na faɗa mishi final year tana buk'atar karatu, amma rigima irin ta Farouq ta hana shi maida hankali wallahi." "Ya zaka ce haka Yaya? Bayan kai da kanka kana yaba ma k'wazona a karatu, kawai dai ina missing Hajiya ne, bazan iya ganin mai zuwa garin nan in k'yale ba." Yayi maganar yana kallonta, da 'yar dariya k'unshe a bakinshi. "A dai maida hankali Farouq. Allah kuma ya taimaka." "Amin." Gaba ɗaya suka ansa da shi, sannan 'yan mazan suka mik'e domin sauke faralin sallolin da ke kansu, ba tare kuma da Hajiya ta tsayar da su don sanin wacece matar da suka zo da ita ba, illa ma mik'ewa da suka yi tare da Rukayya a hannunta, ta juyo da murmushinta tana kallon Jay. "Tashi kema kije kiyi sallah, kafin su gama ku ci abinci, na san ba komai kuka ci a hanya ba." Tashi tayi ta bi bayanta, suka isa ɗaki ta nuna mata toilet sannan ta fito. Sai da suka gama duk abinda za suyi, suka ci abincinsu, bayan sun dawo palon sun zauna, sannan SS ya yi ma Hajiya bayanin wacece Jay, da dalilin da ya sa suka kawo ta nan. Fuskar Hajiyar kawai zaka kalla ka gane yadda tsantsan tausayin Jay ya mamaye ta, a hankali tasa hannu ta gyara ma Rukayya da tayi bacci a gefenta kwanciya, sannan ta maida kallonta ga SS. "Yanzu menene abin yi? Wanene mahaifin nata?" "Jikar Mal. Baba ce." SS ya faɗa a tak'aice. Hakan ya sa Hajiya fito da ido waje, a karo guda ta furta "Allah sarki. Lallai ka cika ɗan halak Sadic. Allah ne yasa zaka rama karamcin da mutumen nan yayi maka ta wannan hanyar." Tsagaitawa tayi, tana kallon Jay cikin wani irin yanayi, sannan ta cigaba. "In sha Allahu komai zai warware kinji. Ki saki jikinki, ki ɗauka tamkar a gida kike, da izinin Allah za'a samu mafita." Bata iya cewa komai ba, saboda yadda maganganunsu suka ɗaure ta, inda ta fara tambayar kanta wai shin wanene wannan SS Tafseer?1 "Tafseer?" Ta maimaita sunan na k'arshe a cikin zuciyarta. Duk yadda aka yi yana da alak'a da family ɗinta, kasancewar inkiyar kakanta Mal. Baba kenan, haka zalika shine cikon suna na ukku, da mahaifinta yake amfani da shi. "Wanene wannan?" Ta k'ara tambayar kanta, duk kuwa da cewar ta tabbatar bata da ansar, matsawar ba wani a cikin mutanen da ke zaune gabanta bane ya ansa ta. Da wannan sak'e-sak'en a zuciyarta, suka mik'e zuwa ɗakunansu, domin kuwa dare ya riga yayi, sai dai daga ita har Sagir S. babu wanda ya samu damar runtsawa a cikin daren kai tsaye. ***Washe Gari. Da shirinshi ya fito cikin ɗanyar farar shadda ɗinkin kaftani, riga da wandonta. Bak'ar hular da ya ɗora a kanshi, ta k'ara haskaka santaleliyar fuskarsa, mai cike da kwarjini da annuri, yayin da ya fara takowa cikin palon Hajiya, k'afafunsa lulluɓe cikin bak'in takalmi na H&M. Ita kaɗai ce a palon, sai 'yar budurwar da ke taimaka mata da aikace-aikacen gida, wacce tana ganin shigowarsa ta gaishe da shi, ta mik'e ta wuce kitchen. "Ina kwana." Ya gaishe da ita, cikin jin daɗi ta ansa, tana k'are ma yadda yayi wani ɗan wuya kallo, ma'ana ya rame, duk da kasancewar kusan wata guda kenan, bata ganshi ba. "Lafiyar ka kuwa Sadic? Ni sai naga duk ka rarrame." "Lafiya lau Hajiya. Ina Jameela?" Ya tambaya ta hanyar kawar da maganar da ta kawo, domin kuwa shi kanshi ya lura da hakan cikin 'yan kwanakin nan. "Tun da suka ci abinci ta shiga yi ma yara wanka, kaga har yanzu basu fito ba." "Zan koma gidan Alhaji ne, zan je muyi magana da shi, idan nayi sa'a ya saurare ni to, idan kuma banyi sa'a ba, daga can zan wuce Daura kawai, duk da alk'awarin da na ɗauka na ba zan k'ara zuwa gidan Mal. Baba ba, amma dole in hak'ura inje ko dan samuwar farincikin ita Jameela."2 "Hak'uri dai zaka yi Sadic, shi mutum a kullun alkairin da aka mishi ya kamata ya rink'a tunawa, ba wai sharri ba. Kuma ma banda abinka, Malam ai ba laifinshi bane. Allah dai ya taimaka ya kuma bada sa'a kai dai." "Amin." Ya faɗa, kafin ya mik'e, hannuwansa cikin aljihu, idanunsa a kan k'ofar ɗakin da Jay ke ciki. Bai jira fitowarsu ba, yayi ma Hajiya sallama, ya fito harabar gidan. Gidan Baffa ya dosa, zuciyarsa taf da fargaba, domin kuwa shi ya san wanene Baffan, matsawar ya hau dokin nak'i, to fa sauko da shi sai wanda ya shirya. A farfajiyar gidan ya same shi zaune k'asar wata canopy da ke gefe kadan da inda suke parking motoci. Jaridar WeeklyTrust ce rik'e a hannunsa yana dubawa, idanunsa ɓoye cikin medical glasses ɗin da ya k'ara ma dattijuwar fuskarsa annuri. Wannan ba shi zai hana ka gane yanayin bak'incikin da zuciyarsa ke ciki ba, ta yadda yake sakin tsaki lokaci-zuwa-lokaci, a karo guda kuma yana kai duba ga k'ofar shigowa ta gidan, tamkar mai jiran wasu gagaruman bak'i. Ganin motar Sagir da ta shigo, ba k'aramin farinciki ya ji a cikin zuciyarsa ba, hakan yasa shi sauke wata ajiyar zuciya ba tare da saninshi ba, duk da ba wai ya nuna jin daɗin a saman fuskarsa ne ba. Jaridar da ke hannunsa ya ajje, ya tattara hankalinsa zuwa ga SS da ya tunkaro inda yake zaune.4 A kujerar gefenshi ya zauna, tare da rissinawa ya gaishe da shi, shima cikin halin ko in kula ya ansa duk da yanayin guiltiness da ya samu zuciyarsa a ciki. "Na zo ne a kan maganar Jameela." Yayi maganar kanshi a k'asa. "Idan wannan ne maganar da ta kawo ka, gara tun baka ɓata ma kanka lokaci ba, ka tashi ka koma inda ka fito." "Ka daure, ka yi hak'uri ka saurari batun da nazo da shi." "Batun menene Sagiru? Batun 'yar da na haifa na mutunta na gwada mata soyayya ta watsa mun k'asa a ido shine batun da zan tsaya in saurara? Ko ko batun 'yar da ta fifita soyayyar wani k'ato a kaina? Haba mana, kuyi mun adalci mana, ku tuna irin k'ask'anci da tozarcin da Ummi ta yi ma rayuwata, ku tuna bak'inciki da tashin hankalin da ta cusa ma zuciyata mana." "Alal hak'ik'a Ummi tayi kuskure babba, kuskuren da ya koyar da ita darussan rayuwa, kuskuren da yasa ta fuskanci hukuncinta tun ba'a je ko ina ba, kuskuren da ya hana mata jin dad'i da walwala. Sai dai ina son ka tuna dukkan wani dan Adam ajizi ne, kuma mai laifi ne, a haka kuma Allah yake gafarta mana, ka tabbata kuma da ace ba'a yafiya a duniya da babu abinda zai kawo ni gabanka har in nema ma 'yar da ka haifa yafiyarka, ka tabbata da idan naga 'yarka cikin wani mugun hali babu dalilin da zai sa inyi k'ok'ok'arin fitar da ita. Kayi hak'uri, ka gafarce ta, ka dauki tafiyarta a matsayin k'addara wacce ta rigayi fata, kuma isahara ce akan iyaye masu hali irin naku, haka kuma rabo ne na yarinyar da ta dawo da ita, domin kuwa idan Allah yayi rantsuwa akan aure, ko wata irin matsala za'a samu sai fa an daura, haka kuma idan rabo ya ratsa tsakani to ko akan titi ne sai an haifi yaron. Ka gode Allah da bata dauko maka wannan abun kunyar ba, ka kuma gode Allah da ya bata ikon gane kuskurenta, har ya karkato maka da hankalinta gida. Ka tuna cewar ba ita kadai ke da kamasho a tafiyarta ba, akwai taimakon ku, ku iyayenta da kuka hane ta tarbiyya mai kyau, wacce kai ba haka aka yi maka ba, domin kuwa ni shaida ne akan haka. Ka dubi darajar Allah, ka rungumi 'yarka domin kaima ka samu damar gyara laifin da kayi. Wannan ne kawai abinda zan iya yi, zuciya dai taka ce, kai ne kuma wanda zaka yi controlling duk abinda ta ayyana maka." Da gama faɗar haka da wasu 'yan mintuna ya fara k'ok'arin mikewa, jin shirun da Baffa yayi kanshi a k'asa, da alama ba shi da niyyar cewa wani abu. "Na bar ka lafiya."10 SS ya kuma faɗa, sa'adda ya sanya kai zuwa inda yayi parking motarsa. "Sagiru." Baffa yayi kiran shi cikin wata dasashshiyar murya, marar k'arfin amo, wacce ta sanya SS tausaya mishi, saboda juyowar da yayi, ya ga hawaye na zuba a fuskar babban mutum kamar shi.. A hankali ya fara takowa, ya koma inda ya tashi ya zauna yayin da zuciyoyin su duk biyun a dagule, babu wanda ya iya cewa komai. SS ne yayi k'arfin halin daga kai ya kalle shi. "Mun kasance 'yan Adam mafi rinjayen ajizanci, a haka kuma Allah mahaliccinmu yake gafarta laifukan mu. Me yasa mu baza mu gafartawa wasunmu ba ko dan mu samu dace da kyakkyawan rabo? Me yasa baza muyi yak'i da zuciyoyinmu ba, ko dan mu samu nasarar yakice shedan din da ke addabar mu? Kayi hak'uri ka gafarta mata ko kaima ka samu dawowar farincikin da ka rasa shekaru biyar da suka gabata, na tabbata Ummi ta gama gane duk wani kuskurenta, idan kayi duba da yadda kamanni da yanayinta suka canja baki daya. Ka taimaki zuciyoyinku kai da mahaifiyarta da suke kwana su tashi da takaicin rashinta." "Na san Ummi tayi gagarumin laifi Sagiru. Sai dai ba wannan ba ne ya hane ni gafarta mata ba. Ina jin kunyar yadda zan hada ido da ita a matsayina na uban da ya sanya hannu wurin tabarbarewar tarbiyyarta, a matsayina na uban da son zuciya, da soyayyar da nake mata suka hane ni dora ta akan hanya madaidaiciya. Ka taimaka mun ka rok'a mun yafiyar Ummi domin ban san da wane ido zan daga in kalle ta ba, duk da kaima ina maganar da kai ne cikin jin nauyin abinda na yi maka, ka tambaya mun afuwarta Sagiru, ban ce kuma ka matsa mata akan dawowa gidana ba, ka tambaye ta idan har tana da ra'ayin hakan. Idan kai mun wannan, zan kasance cikin farinciki da jin dadin da baki kadai ba zai iya misalta shi."5 Wani irin hamshak'in murmushi SS ya dinga zubarwa, domin kuwa ya manta da duk wani tabo da yake kallon Alhajin da shi, kwata-kwata ya manta da duk wani abu da ya taba wanzuwa na rashin dad'i a tsakaninsu, kalaman da Alhajin yayi kadai sun wadatar da farincikin zuciyarsa, sun dawo ma Alhajin da daraja, da mutuncinsa da yake gani a shekarun baya. "Babu batun takura ko matsi da zan yi mata. Idan baka sani ba, wannan ita ce damar da Ummi ta rink'a nema tun daga lokacin da ta bar gida, har izuwa yanzu. Da izinin Allah zan dawo maka da ita yanzun nan ba wai sai anjima ba." Da gama fad'ar haka ya mik'e zuwa inda yayi parking. "Sagiru." Baffa ya kira sa, hakan yasa ya k'ara dawowa, sai dai wannan karon bai kai ga zama, yayin da murmushin da ke kunshe a labbansa har yanzu bai gushe ba. "Yau kasa na ji kunyar da ban taba jin irinta ba. A yau na tabbatar kai din dan halak ne wanda yake rama alkairi ma sharri. Hakan ya k'ara maka wata daraja da k'ima a idanuna. Ashe wannan halaye naka su suka sa Malam ya aminta da kai, ya fifita soyayyarka a kanmu. Ka sani a yau din nan ina da-na-sanin abinda ya gabata duk da kasancewar na yi shi ne cikin k'uruciya." Tsayuwarsa kawai ya gyara ya cigaba da sauraren yadda Baffa ke magana cikin lallami, tamkar ba wanda ya sani shekarun da suka gabata ba. "Wannan ba komai ba ne. Domin kuwa abinda kayi a yanzu ya shafe duk wani abu da ya faru a cikin zuciyata. Gafarar Allah ita ya kamata mu cigaba da nema. Barin je in dawo." "Allah ya dawo da kai lafiya." "Amin." Yana fita Baffa ya zaro kyakkyawan handkerchief a gaban aljihunshi, ya cigaba da share hawayen da suke sintiri akan fuskarsa, yana tuna yadda son zuciya yasa ya wulak'anta mutumen da yayi silar dawowar farincikinshi a wannan lokacin. "Lallai na kasance mutum mai son kaina fiye da kowa. Ya Allah ina rok'on ka da ka dai-daita mun halaye na. Bana son in kuma maimaita kurakuran da na yi a baya."2 A fili Baffa ya rink'a wannan bayanan, a k'arshe ya mik'e ya shige ciki zuwa dakin Goggo, inda ya same ta kwance a k'arshen gadonta, da alama jikin nata sai a hankali, domin kuwa tun ranar da ta dora Ummi a idonta, da suka tafi take fama da matsanancin zazzabin da ya k'i jin magani. Da sallama Baffan ya shiga d'akin, sai dai bata ansa shi ba, domin kuwa wannan karon ba k'aramin haushin abinda yayi take ji ba. Murmushi yayi ya zauna gefenta, saboda ya san da kwanan zancen. "Taimaka ki tashi a hada mun abinci ina da bak'in da zasu zo yanzu ba da dadewa ba. Sannan kisa a gyara wancen d'akin na Ummi, domin a nan zasu sauka." "Wasu irin muhimman bak'i ne haka da suka fiye maka lafiyata?" "Bak'i ne da za su kawo maganin ciwon da ke damunki. Daure ki tashi." "Ban fahimce ka ba fa." "Idan sun zo zaki fahimci komai." Ya juya ya fita da sauri, hakan yasa ta mik'e itama, dak'yar ta wuce kitchen tasa masu aiki suka fara hada-hadar girke-girke, sannan ta fito zuwa d'akin Jay ta bude, tare da yaye manya-manyan fararen k'yallayen da aka sa aka lullube abubuwan cikin d'akin saboda gudun k'ura. Zuciyarta a raunane suka fara aikin gyara ɗakin, k'aunar ganin tilon 'yar tata na cigaba da azabtar da idanuwa da kuma birnin zuciyarta, yayin da ta wani ɓangaren take mamakin halaye irin na mijinta, wanda duk idan aka kalli fuskarsa, za'a iya ganin yadda zuciyarsa ke kwana ta tashi da bak'incikin rashin 'yar tasa, amma kafar kai ta hana shi bayyanar da hakan. A haka suka yi suka gama amma zuciyarta dank'are da tunanin hanyar da zata bi domin dawo masu da farin cikin da suka rasa, wanda ta tabbatar mijin nata ya fi ta azabtuwa nesa ba kusa ba. Kitchen ta koma, suka cigaba da haɗa k'ayatattun girke-girke na ban mamaki, sai dai duk da cunkushewar da zuciyarta tayi, haka kawai sai ta ke samun wata natsuwa a hankali tana saukar mata, har sai da ya kai ga ta daina jin irin raɗaɗin da take ji a zuciyar tata a lokutan baya. *** Ba'a yi cikakkiyar awa guda da tafiyar SS ba, suka dawo gidan tare da Jay, Rukayya, Jafar da Farouq, har ma da Hajiya. Wannan karon da k'warin gwiwarsu suka fito gaba ɗaya suka doshi babban palon gidan, saɓanin wancen zuwan da aka sauke su a palon bak'i. A zaune Baffan yake, yadda ya tattara hankalinsa ya mik'a ma k'ofar shigowa, shi kawai zai tabbatar maka da akwai abinda yake jira. Yana ganin an buɗe k'ofar, ya mik'e tsaye, zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, har iyanzu bai daina tarabbabin ganin 'yar tasa ba. Tunda ta shigo ta gagara sauke idanunta a kanshi, murmushin da taga yana jifarta da shi, shi ya k'ara tabbatar mata da gaskiyar labarin da SS ya je mata da. Annurin fuskar da take ta son gani, wanda rabon da ta ganshi shekaru biyar kenan da suka gabata, shine take hange shimfiɗe akan dattijuwar fuskar mahaifin nata, masoyinta na farko, domin kuwa da soyayyarsa ta buɗe idanuwanta a duniya. Da sallama suka k'arasa shigowa ciki, a lokacin da wasu hawaye suka yayyafo a kumatun Baffa, cikin dabara yasa hannu ya ɗauke su, yayin da duk suka zauna su kuma, sannan ya ɗago da hannayensa ya mik'a ma Rukayya alamar ta iso gare shi. Da Hajiya suka fara gaisawa, duk da kasancewarta ba bak'uwa ba a fuskarsa, amma hakan bai hane shi jin nauyin ɗaga ido ya kalle ta ba. A haka Farouq ya gaishe da shi shima, Jafar kam tuni ya isa ya zauna a ɗayar k'afarsa, inda ya ga Rukayya ta zauna ɗayar. Duban Jay ya ke, duba mai tattare da so da k'auna irin na ɗa da mahaifin da suka kwashi shekaru basu gana da juna ba. "Ka yi hak'uri Baffa na.." Ta fara maganar hawaye sharaf-sharaf a idonta, amma ya dakatar da ita, ta hanyar ɗaga mata hannu. Mik'ewa yayi, tare da zaunar da yaran a kujerar da ya tashi, sannan ya fara takawa zuwa gabanta, kasancewar palon mai girma, sai ya zamana akwai tazara sosai tsakaninsu. Ganin haka yasa Hajiya ta mik'e, a karo guda ta yi ma yaranta nuni da su tashi suma, hannun Jafar ta kama, suka koma palon bak'i, domin su basu damar ganawa da juna. Zaune take a k'asar carpet ɗin da ya mamaye palon, ta duk'unk'une fuskarta a tsakanin k'afafunta, banda kukan nadama, babu abinda Jay ke yi, hakan yasa zuciyar Baffa ta k'ara karyewa, sa'adda ya isa gefenta ya zauna, tare da sa hannu ya kama nata hannayen. "Ya isa haka Mamana." A tsorace ta ɗago da rinannun idanunta ta sauke a kanshi, tabbas ba mafarki take ba, Baffanta ne a gefenta, shine kuma yake kiranta cikin siga mafi soyuwa a zuciyarta. Da da ne, da babu abinda zai yi mata katanga da faɗawa jikinsa, sai dai a yanzu, ta kai wani munzali, wanda ta tabbata hakan ne ya hani Baffan nata sanya ta a jikinshi shima. "Ka yi hak'uri ka yafe mun Baffa. Na san ni mai laifi ce, laifin da ya fi gaban a yafe mun kai tsaye, laifin da ya jefa zuciyoyi da lafiyarku cikin hali na ha'ula'i. Laifin da ya koyar da ni darussa iri daban-daban na rayuwar biladama, ya koyar da ni zama a hali na akwai, da kuma hali na babu, laifin da ya wa'azantar da ni, ya nuna mun irin gagarumin muhimmancin da iyaye suke da shi a rayuwar 'ya'yansu. Na rantse maka da Allah Baffa, bakina kaɗai ba zai iya bayyana halin da laifin da nayi ya jefa ni ba, har sai kace ka gafarta mun, ka kuma bani dama, domin ganin canji a tattare da ni." Cikin wani irin azababben kuka take wannan jawabin, hakan yasa k'wallar da Baffa ke ta faman taryewa, suka suɓuce, suka silalo saman kumatunsa, hannunta da ke cikin nashi ya k'ara k'ank'amewa, a karo guda ya fara magana. "Ya isa haka Ummina, ya isa haka kinji. In dai ta nine na riga na yafe miki, na gafarta duk laifin da kika yi, na kuma shafe shi a cikin zuciyata. Nima ki gafarce ni, ki bani damar gyara bayana." "Ba kai mun komai ba Baffa na, illa k'auna da soyayya da ka nuna mun, wanda ni a nawa rashin wayon na ɗauke su a matsayin wani makami da zan yi yak'i da ku. Duka laifin dai nawa ne, nice na kasa fahimtar muhimmancin abinda ka rink'a nuna mun, a yanzu kam na yi alk'awarin ba zan k'ara bijirewa duk wani umarni da za kai mun ba." "Alhamdulillah. Allah na gode maka da ka bar ni da raina don ganin wannan ranar." Suka tsinkayi maganar a bayansu, hakan yasa suka waiga a tare, Goggo suka gani tsaye bakin k'ofar palon, bakinta k'unshe da murmushi, a karo guda kuma hawaye na zuba a idanuwanta. K'arasawa tayi ta zauna, inda suka sanya Jay a tsakiyarsu, fuskokinsu bayyane da tsantsan farincikin da ke kwance k'asar zukatansu. A haka duk suka nemi yafiyar junansu, a lokaci guda rayuwarsu ta baya ta dawo musu, har ya zamana tamkar wani abu na bak'inciki bai taɓa wanzuwa a tsakaninsu ba, idan aka yi duba da yadda suke raha, da nuna jin daɗin kasancewa da junansu. Sun ɗauki kusan awa guda a haka, tamkar sun manta da bak'in da suka ajje a palon bak'i, daga bisani Goggo ta mik'e ta fita, suka gaisa sosai da Hajiya, tare da k'ara yi masu godiya, da kuma k'ara ba ma SS hak'urin abinda ya gabata, domin kuwa yanzu da ta gane shi ɗin ko wanene, sai take jin nauyinsa sosai, a haka suka dawo cikin palon, Goggo ta wuce domin kawo masu abinci. Kowa ka kalla a cikinsu fuskarsa k'unshe take da murmushi, illa matsala ɗaya da ke damun zuciyar Jay, tunanin halin da Kazaure ke ciki a yanzu, wacce ta tabbatar bata da damar saninta. Goggo da masu aikinta ne suka dinga shigowa da manya-manyan warmers na abincin da suka girka, a tsakiyar palon suka baje komai, anan suka ci suka sha cikin farin ciki, ta wani fannin cikin jin kunyar SS da mahaifiyarsa.1 Bayan sun gama cin abincin ne SS ya basu labarin da Jay ta bashi, babu abinda ya yi saura wanda bai faɗa masu ba, hakan yasa suka k'ara tausaya mata, yayin da zuciyar Baffa ta k'ara tunzura, k'iyayyar da yake yi ma Sadam ta dawo sabuwa fil. "Kasan Allah, sai na sa an ɗaure yaron nan, sai nasa an nemo shi a duk inda ya shiga a faɗin garin Maiduguri. Sai yayi da-na-sanin wulak'antar mun 'ya da yayi. Yanzu in banda rashin imani, da rashin tsoron Allah irin na yaron nan, bayan tunzura ta da yayi ta bar gaban iyayenta, shine yayi mata sakayya da irin wannan azabar? Zai gane kuskuren da yayi na taɓa gudan jinina, tilon 'yar da na haifa a gaba ɗaya rayuwata."3 Kallon shi kawai SS yake yi, dan ya san zai iya yin abinda ya fi wanda ya ambata, sai dai idan son samu ne, su bi komai a hankali, duk kuwa da cewar shima yana da tabon Kazauren a k'asan tashu zuciyar. "Ka ce bai bata takarda ba?" Baffa ya tambaya idanunsa k'unshe da tashin hankali. "Bai ma san inda ta ke ba a halin da ake ciki yanzu." "Zai sani idan na gurfanar da shi gaban kuliya." "Kafin nan da ka daure kayi hak'uri na samu ganawa da shi, tunda na faɗi maka abokin aikina ne, ni da kaina zan kawo shi har gabanka, in yaso sai ayi duk abinda ya kamata, amma idan aka je da maganar court, kamar wani tonan asiri ne zamu yi ma kanmu."3 Jinjina kai ya fara yi kamar ya gamsu da maganarsa, ko me ya tuna kuma, take ya mik'e, ya ce "Ba zan iya ba Sagiru. Wallahi sai na ɗaure yaron nan, sannan inga wanda zai tsaya masa, sai na gwada mishi irin gatan da Ummi ke da, wanda ta watsar ta bishi, ta yadda a gaba zai ji tsoron k'ara ɗaukar 'yar wani ya gudu yayi aure da ita." "Na ji fa, ba wai kuma na hana ka ɗaukar mataki ba, a'a. Ka yi hakuri ka bani wannan damar, domin ni kaina, ina so a gwada mishi irin kuskuren da yayi a rayuwa ko dan zuwa gaba." Dak'yar SS da sauran jama'ar wurin suka samu Baffa ya tausasa zuciyarsa, a k'arshe ya amince da buk'atarsa. Sai dai kuma Jay ta kasa cewa komai, kuka kawai take yi, ta wani fannin kuma tana tsoron matakin da Baffan ke shirin ɗauka. Sai wurin k'arfe huɗu na yamma sannan suka fara shirin komawa gida. Bayan duk sun fito, gefe SS ya koma yana kallon yadda ake artabu da Jafar kan sai an barshi a gidan, ganin abun nashi ba mai k'arewa ba ne, yasa yace da su Farouq su shiga motar, bari ya lallaɓa shi su tafi. Sallama suka yi ma su Baffa suka shige motarsu, su kuma suka koma ciki, shi kuma ya fara takawa a hankali, ya isa inda Jay ke tsaye, hannunta rik'e da na Jafar da Rukayya. Kasa haɗa ido yayi da ita, kasancewar wani yanayi da yake shiga a duk lokacin da ya k'unace ma kallonta. Hannun Jafar ya kama, da wayo, da wayo, ya ɗaga shi sama, a kunnenshi yayi mashi maganar da ta sanya shi k'yalk'yalewa da dariya, ya fara ɗaga ma Jay hannu. "Mammy sai gobe." Hannun yaron ta rik'e, hakan ya ba SS damar dakatawa sai dai ya kasa juyowa, takowa tayi tana kallon Jafar, amma a zahiri ba shi din take kallo ba. "Kana ganin ya kamata ace har ka tafi ba tare da nasan ainahin wanene mutumen da ya taimaka mun ba?" Yadda tayi maganar, ya san da shi take, sai dai ya kasa ansa ta, saboda yadda muryarta ke ansa kuwwa, a cikin k'walwarsa. "Zan so inji labarinka, idan da hali zan so in san menene mahaɗarka da Baffana. Zan so ka yi mun wannan taimakon shima, idan har ban takura ka ba." Har yanzu ya kasa cewa komai da ita, hakan da ta ji ita kuma yasa ta shafi gefen fuskar Jafar "Be a good boy yarona, ina jiran ka gobe tunda safe ka ji?" Ta juya ba tare da ta jira mai zasu faɗa ba duk biyun, a haka jiki ba k'wari, ya isa wurin motar, zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, ya shiga ya tada suka tafi. *** K'arfe goma na safiyar washe gari a gidan Baffa ta yi musu, kasancewar a ranar zasu wuce Maid, sai dai kuma baya jin zai iya tafiya ba tare da ya sanar da ita abinda ta buk'ata daga gare shi ba. Bayan sun gama gaisawa, ya ɗago a daburce, ya sauke idanunsa a kanta. "Kin shirya?" "A shirye nike dama, but da naga har goma tayi, sai na fitar da raina daga son sanin labarin, dan a zato na kun daɗe da hawa hanyar Maiduguri." "Hmmmm, kinsan ai bazan ma fara ba. But ba wani interesting abu a labarin fa, amma tunda kinyi insisting, zan sanar da ke." "Ko ma yaya ne, haka nan ma ina son in sani." Jin haka yasa Farouq cire earpiece ɗin dake kunnensa, ya mik'a hankalinshi gare su, yayin da SS shima ya kai duba ga agogon dake ɗaure a hannunsa, sannan ya ɗago ya fara magana kamar haka.... Hello lovers..3 I wrote this book since august, 2016. Ina da shi a ajje, editing kawai nike, ina updating muku. While, Hawayen Zuciya, yanzu nike kan rubuta shi, sau kun yi hakuri da yadda kuke samun tsaikonshi.7 Thanks y'all for the love.1 Bari mu ji me SS ya zo mana da shi🙌🙌 "Na tashi ana kira na Abbakar Sadic Surajo Galadima, duk da a wancen lokacin duka-duka ban wuce shekaru goma zuwa sha ɗaya a duniya ba, domin kuwa ina shirin tafiya aji ɗaya na makarantar secondary. Ko da ina da k'uruciya a wancen lokacin, amma bazan manta yadda muka tashi muna rayuwa da iyayena cikin jin daɗi da kwanciyar hankali ba. Mahaifina Suraj Galadima haifaffen garin Katsina ne, cikin unguwar Sha'iskawa. Su biyu iyayensu suka haifa daga shi sai k'anenshi Jafar Galadima. Kakansu na ukku wanda ya haifi Baban Babansu shine Galadiman Katsina na farko, bayan rasuwarshi sarautar ta koma hannun ɗanshi, ma'ana wanda ya haifi babansu. Sun kasance mutane masu rufin asiri da wadatar zuciya tare da neman na kasansu, cikin ikon Allah ba wasu kuɗi ne da su na azo a gani ba, hakan yasa bayan rasuwar Galadima na biyu, sai sarautar ta fita kwata-kwata daga cikin zuri'arsu, abin nufi aka siyar da ita ga masu hannu da shuni, amma hakan bai hana musu cigaba da bearing da sunan Galadiman ba. Sana'ar Abbana a wancen lokacin, itace siyar da motoci, domin ba zan manta ba suna da wani company na siyar da motoci mai taken KASAD MOTORS, wanda a kullu yaumun naje wurin sai na tambayi ma'anar abun, sai dai yace idan na girma zai sanar da ni. Haka kuma idan har naga sabuwar mota a wurin nace irinta nake so idan na girma, ina tuna yadda yake kallona da murmushi a fuskarsa yana girgiza kai, wanda sai daga baya na fahimci manufar wannan murmushi nasa, haka zai sa hannu ya shafi sumar da ke kaina, sannan yace "Wannan motocin da kake gani Sadic, daga su nike ci nike sha, daga gare su ne nike yi muku duk wata hidima da kai da Mahaifiyarka. Ina nufin ba dukiyata bace ba, dukiyar wani attajiri ce, uban gidana wanda ya yarda da ni, ya bani amanar kayansa. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka, ka sa a ranka cewar zaka girma ka zama mai DOGARO DA KAI." A kullu yaumun wannan sune kalamanshi gare ni, sai dai a wancen lokacin ban san ainahin inda maganganun nasa suka dosa ba, ban kuma san wanene mamallakin dukiyar da yake juyawa ba. Sunan Sagir S. Tafseer kuwa ya samo asali ne ranar wata bak'ar laraba." Jinkirtawa yayi, idanuwansa suka ciko taf da hawaye. Kallon da Farouq ke masa na mamakin yadda ya ji ya kira mahaifinsu Jafar a matsayin k'anen mahaifinshi. "Me hakan ke nufi?" Farouq ɗin ya tambayi kanshi, sai dai ya san baya da ansar tambayarsa, dole ya gyara zama tare da zura ma SS idanunsa domin warware masa tambayoyin da suke addabar zuciyarsa. Handkerchief ya ciro a gaban aljihunshi ya share idonsa, da murmushi ya ɗago yana kallonsu, sannan ya cigaba. "Dole nike kiran ta da bak'ar laraba, kasancewar rana ce da na rasa mahaifina, abin tunk'aho na. Rana ce da NA MANTA KOMAI na k'uruciyata, na manta wanene ni, na manta garina, gidana, da ma sunana gabaki ɗaya. Rana ce da bazan taɓa mantawa da ita ba, rana ce ta bak'in ciki, ranar da ta zama silar komai a LABARIN RAYUWATA. Tafiya muke da Abbana mun dawo daga Kano kan maganar makarantata. A ranar bai yi niyyar zuwa Kanon ba, sai dai sak'on da ya samu daga uban gidanshi da ya tafi k'asar Japan a wancen lokacin, kan yaje ya anso kuɗaɗen da aka tara na company ɗinsu da ke Kano, ya haɗa da na hannunshi ya tura mishi domin zai yo safarar motoci daga can k'asar zuwa nan gida Nigeria. Hakan yasa yace to in shirya muje daga can sai mu biya ayi maganar admission ɗina. Kuɗi ne muka taho da su, makuden kuɗaɗe, masu yawan gaske, domin ni kam bazan iya tantance yawansu ba, sai dai na ji Abbana yana cewa a k'alla zasu tasan ma nera miliyan ashirin da biyar, domin kuwa a k'asar boot ɗin motarshi a ka rink'a shirya su, a haka ma sai da wasu suka yi saura. La'asar sakaliya, muka kamo hanyar Katsina, gudu sosai Abba ke yi, kasancewar maghriba ta kawo kai, ga shi kuma ana jita-jitar hanya bata da kyau. A wani K'auyen da babu yawaitar mutane, haka zalika abubuwan hawa, wani bawan Allah ya tsaya tsakiyar titi yana ɗaga hannu ma Abbana, alamar yana buk'atar taimako. Cikin gaggawa Abba ya ja birki tare da yin parking a gefen titi hakan yasa mutumen ya taho da hamzari yana nuna ma Abba wata mota da ke girke a gefe, cewar motarsa ce battery ya bashi matsala. Kafin Abba ya buɗe baki yayi magana tuni wasu gardawa majiya k'arfi sun bayyana a kanmu. Abba na ganin haka, ya tura ni bayan motar, ya duk'ar da ni a k'asa, yayin da mutanen suka saita shi da bindiga suna tambayar kuɗi ko kuma ranshi. "Kuyi mun rai." Furucin Abbana kenan, yana rok'on mutanen, da hannayenshi a sama, idanuwansa sun fara zubar da k'walla. "Kada ka ɓata mana lokaci Dallah. Ka bayar da kuɗi ka fanshi ranka." "Nera ba ni da ita." Fadar Abba, har yanzu ina kallon yadda hawaye ke sintiri akan fuskarsa, wani na bin wani, tamkar an buɗe famfo marar kan gado. "Ku bincike mun motarshi." Abinda babban su yayi musu umarni kenan, cikin ɗan k'aramin lokaci suka fara bincika motar, inda suka gano kuɗaɗen da aka shirya a k'asar boot ɗin motar Abbana. "Wato mu zaka raina ma hankali ko?" "Wallahi ba kuɗi na bane ba, kuɗin mutane ne, ku taimaki rayuwata, ku bar ni in isar da amanar da na ɗauko." Bai ida rufe bakinsa ba suka saki harsashin bindiga a cikin k'walwarsa, hakan yasa na fasa ihu ni a tunanina suna jina, sai dai ban sani ba ashe basu ma san ina yi ba, a wata duniya ta daban nike ihuna. Tun daga nan na silale na kwanta a k'asar motar, ina jin yadda suke maganganu, sai dai na kasa fahimtar komai a maganar tasu, na manta menene ya faru a lokacin, na manta menene ya kawo ni halin da nike ciki a lokacin. Biyu a cikinsu, suka shigo motar Abba, sauran suka shiga ɗayar motar da ke gefe, suka dinga tafiya, ban san ina za su je ba, haka kuma ban san ya aka k'are da gawar Abba ba. Abinda zan iya tunawa guda ɗaya ne, yadda wani a cikin mutum biyun da ke motar Abbana ya juyo ya ganni duk'unk'une a k'asar motar, yasa dan uwansa ya tsaya, suka fitar da ni suka saita bindiga a kaina zasu harbe, sai dai ɗayan yace ya kyale ni, suka bar ni a nan suka shiga motar suka yi tafiyarsu. A bakin titin na kwanta ina kukan da ban san ko na menene ba, domin kuwa NA MANTA KOMAI, ban kuma san ko a ina nike ba. Haka na dinga ganin wucewar motoci iri daban-daban, amma ban ko iya motsawa ba, ina kwance a wurin ban san abinda nake buk'ata ba, kuka kawai nike yi, har sai da ya kai idanuwana babu sauran hawaye. Wata mota da ta wuce naga ta dawo da baya, inda nike kwance suka tsaya, sannan wani dattijo da ke bayan motar ya buɗe ya fito ya tunkari inda nike kwance. Tambaya ta ya fara yi dalilin da ya kwantar da ni a wurin, amma ban sani ba, ya sunana, shima ban sani ba, ina iyayena, duka duk ban sani ba, sai naga yana tofa mun addu'a, a karo guda ya kama hannunna ya mik'ar da ni muka shige motar, ya zaunar da ni a gefensa, ya umarci drivern da ya ja motar muje." Wannan karon Jay ce ke zubar da wasu irin zafafan hawaye. Kuka take irin mai tsuma zuciyar nan, Farouq kam idanunsa sun kaɗa sunyi jazir, domin tunda ya zo duniya bai taɓa jin labari mafi muni irin wannan ba, yayin da ta ɓangarenta take tausaya ma rayuwar da SS ya shiga lokacin da yake tsananin buk'atar mataimaki a gefensa. Kallon su kawai yake yana girgiza kai, domin kuwa duk lokacin da ya tuna ranar, yana jin ina ma tare da shi ɓarayin suka harbe, ya tabbata da bai gamu da wasu bak'in cikin da suka wanzu a rayuwarsa ba. Sai da suka tsagaita da kukan, sannan ya cigaba. "Kakanki Mal. Baba shine dattijon da ya tsince ni, dattijon arzik'i mai kamala da nasibi na rayuwa, shi ya suturta ni ya 'yanta ni, ya mayar da ni mutum mai gata, ya raɗa mun suna Sagiru, a cewar shi tunda yayi Kabiru, wato Baffanki, kasancewar har a lokacin ban san wanene ni ba. Haka na cigaba da zama cikin sabuwar rayuwata mai daɗi, domin kuwa babu abinda nake iya tunawa, sai ya zamana tamkar nan ɗin ne inda na fara rayuwata tun asali. Tun daga ranar da na fara zama a gidan, Malam yake faɗin ya sama ma Kabiru ɗa, domin a wancen lokacin na kan ji Iya matarsa na cewa "Tabbas ba k'aramin daɗi Kabiru zai ji ba, na samun wannan gagarumar kyauta daga Allah, mutum kusan shekaru bakwai da aure amma bai taɓa haihuwa ba, na tabbata zai ji daɗin wannan abu fiye da kai Malam." Sai dai kuma lokacin da Kabirun da suke magana ya zo, Malam ya je mishi da batun, sai ya zamana bana cikin jerin yaran da yake so, k'arshe ma yace ma Malam babu dalilin da zai sa ya ɗauki annoba da hannunsa ya kai gidanshi, dan haka Malam yayi hak'uri, shima ya fitar da ni a gidansa, tun ban girma na ɓata mishi tarbiyyar gida da sunan zuri'a ba. Duk da ina k'arami a sannan, amma ban mance furucin Malam ga Baffanki ba. "Lallai da sauran ka Kabiru. Wannan ɗan k'aramin yaron ne kake yi ma mugun hasashe? To kai idan baza ka zauna da shi ba, ni baka isa ka hana ni zama da shi ba. Zan kula da shi saboda Allah, in ilmantar da shi domin Allah, har izuwa lokacin da zai samu dawowar tunaninsa, ko kuma lokacin da zai samu damar ganawa da danginsa." Tun daga wannan rana sai ya zamana hatta da sauran yaran gidan suna nuna tsangwamarsu gare ni wacce ban san ko ta micece ba, a wurin Mal. Baba da Iya kawai nake samun dama-dama, sai fa 'yar karamar k'anwarsu Nafisa, wacce muke kusan kai ɗaya da ita. Malam ne da kanshi ya maida ni makarantar primary nayi aji na karshe, sannan ya kaini FGC Daura na fara karatuna na secondary, ta ɓangaren islamiyya kuwa shi da kanshi yake koyar da ni, haka muka cigaba da zama cikin kwanciyar hankali da sabbin iyayena masu matuk'ar nuna soyayyarsu gare ni fiye da 'ya'yan da suka haifa. A haka na cigaba da wata irin makauniyar rayuwa, domin kuwa ban san ko wanene ni ba, haka kuma fuskokin mutanen da nake gani ba irin wanda na saba gani bane a baya, hakan ya k'ara taimakawa wurin rashin dawowar tunanina. Har lokacin da na fara girma Baffanki bai janye karan tsanar da ya ɗora a kaina ba, haka zalika bai janye k'udurinsa na san fitar da ni daga zuri'ar gidan Mal. Baba ba. Babban abinda yayi wanda ya tashi hankalina, shine yadda ya ja k'ima da mutuncina suka zube a idon Malam, har kuma yace ba zai iya cigaba da zama da mai irin halaye na ba. Duk da a wancen lokacin ban san kowa ba, bani da wasu dangi da suka wuce mun su a gaba ɗaya rayuwata, haka Baffan yasa aka kore ni a gidan kan wani dalili marar tushe, marar asali, wanda ko a mafarki aka ce zan aikata haka, ni kaina zan yi gardama da abun." Sai a yanzu hawaye suka yayyafo mishi, handkerchief ɗin da ke hannunshi yasa ya toshe bakinsa, kuka yake irin kukan da baya da sauti, sai dai duk wanda ya kalli mai yin irin shi zai tabbatar da ba k'aramar azabtuwa zuciyarsa ke yi ba. "A lokacin ban wuce shekaru goma sha takwas ba, domin kuwa gama secondary school ɗina kenan, Malam na fafutukar nema mun admission zuwa jami'a. Dakina shine na farko idan ka shigo gidan, ina kwance ina bacci babu riga a jikina, gaba ɗaya gidan babu kowa sai Nafisa, Malam yana k'ofar gida, yayin da Iya ta fita unguwa, sauran 'yan uwanta kuma gaba ɗaya suna gidajensu. Ban san me ya shigo da ita ɗakin ba, na farka dai na ganta tsaye a kaina, hakan yasa na mik'e ina tambayar abinda ke faruwa, kafin tayi magana Mal. Baba da Baffanki sun shigo gidan. Kamar Malam ya manta wani abu a waje, sai ya koma, yayin da Alhajin ya k'arasa shigowa shi kaɗai, gadan-gadan kuma yayo ɗakin nawa, ba tare da munsan wainar da ake toyawa ba, ta duk'a gefen katifa ta tana shirin ɗaukar wani English novel, wanda ɗaukar shi ɗin ne ya shigo da ita ɗakin, a lokacin Alhaji wato Baffanki ya buɗe labulen, ni kuma na mik'e zaune domin in bata damar ɗaukar abin ta fita in cigaba da baccina. A ranar nayi bak'in cikin da mutuwar mahaifina kawai ta fi shi bak'antuwa a zuciyata, a ranar nayi kukan da har sai da hawayena suka k'are. Ta inda Alhaji yake shiga ba ta nan yake fita ba, har Malam Baba ya dawo ya zayyana mishi a yanayin da ya ganmu, sai dai Malam bai gaskata abun ba, amma Baffanki ya dinga faɗa, har yayi wani furucin da, da wuya in manta da shi. "Na faɗi maka yaron nan annoba ne Malam. Ka ganshi a 'yan shekarunsa har ya san ya ɓata maka tarbiyyar 'ya, amma baza ka iya yin komai ba ko? To wallahi yau sai ya bar gidan nan."3 Daga wannan rana na bar gidan, duk da bayanin da yarinyar tayi na k'aryata hasashensa, haka kuma ba da son ran Mal. Baba ba, haka na fito zuciyata k'unshe da bak'in cikin da ya sa nayi alk'awarin bazan kuma komawa gidan ba har abada, na gwammaci cigaba da rayuwa a tasha, kan in koma gidan da ake jifa ta da k'azafin zina. Sai dai kuma abinda baki sani ba shine, wannan fitowa ta taimaka mun k'warai wurin dawowar tunanina, kasancewar wata motar masu zuwa Lagos da na bi, domin k'aurace ma garin baki ɗaya, kwatsam a hanya muka k'ara cin karo da ɓarayi masu manyan bindigogi. Yadda suka tare mu yasa na fara tunani kamar na taɓa cin karo da irin yanayin, lokacin da na ga sun ɗora bindiga akan drivern motar, sai na fara duk'ewa k'asar wurin da nike, sannu a hankali na fara tunano abinda ya faru shekarun baya, k'arshe na kurma wani gagarumin ihun da ya sa na silale na faɗi k'asa sumamme. Lokacin da na farka sai na ganni kwance a asibitin da ban san ko ina ne ba, wata nurse ce take faɗa mun wasu ne suka kawo ni, ganin na daɗe ban farka ba suka ajje mun jaka ta suka k'ara gaba. Ita ce ta sanar da ni sunan garin da nike, ita ta bani kuɗin mota, kan in koma gida in nemi iyayena. Haka na fito na wuce motor park, na shiga motar Katsina duk kuwa da cewar idan naje can ɗin ma ban san ina zan dosa ba, amma na tabbata ba zan rasa wanda zai taimaka mun ba. Cikin dare na isa garin, hakan yasa na kwana anan tasha tare da masu motar da muka zo da su, washe gari na bazama neman dangina. K'ofar K'aura na dosa, gidanmu na da kenan, da tambaya na samu wanda suka gane ni, k'arshe aka kaini gidan wata makwafciyarmu k'awar Mahaifiyata, itace ta ɗauke ni zuwa wata unguwa can k'arshe-k'arshen gari, a cewar ta can ne inda Hajiyarmu ke zama. Gida ne ɗan karami ginin kasa ɗaki ɗaya ne sai makewayi, sai wani kitchen a gefe da aka zagaye da k'arfen langa-langa. Matar da ta fito daga ɗakin, hannunta rik'e da d'an yaron da bai wuce shekaru hudu ba, tabbas fuskar Mahaifiyata gare ta, sai dai na kasa yardar ma kaina ita ɗin ce, domin kuwa ni sanin da na yi ma mahaifiyata mace ce 'yar gayu, mai kyaun surar da duk duniya ita kawai ke birge ni. Kuka muka dinga yi tamkar zamu cire idanuwanmu, ta ɓangare na, na sauyin da na gani a tattare da ita ne, yayin da ta ɓangarenta na famin da na yi ma zuciya da gangan jikinta ne. Kasa daurewa nayi na fara tambayar ya labarin Abbana, amma sai naga kukan da mahaifiyata ke yi a wancen lokacin ya k'ara tsananta, ta juya ta ce ma yaron da ke gefenta ya koma ciki ya jirata, ba gardama ya wuce ciki, a karo guda ta matse hannuna cikin nata, haka kuma hawayenta basu tsagaita ba, tana kallo na ido cikin ido. "Ka bani labarin abinda ya faru da kai da mahaifinka, domin kuwa na daɗe da fitar da raina da ganinku, amma cikin iko na ubangiji sai ga ka ka dawo gare ni, ina Abbanka?" Kukan nike nima, a haka na labarta mata gaba ɗaya abinda ya faru, a k'arshe na tambayi yadda akai rayuwa ta sauya mata lokaci guda, da kuma labarin yaron da take tare da shi. "Uban gidan Abbanka Alhaji Kabir, mamallakin company KASAD MOTORS shine ya wulak'antar da rayuwarmu, ya fitar da mu daga gatan da muke da shi a da." "Ban fahimce ki ba Umma?" "Sadic shi ya anshe duk wata kadara da mahaifinka ya tara, a cewar shi Abbanka ya gudan mishi da kuɗaɗen da ya aike shi ansa ne, domin kuwa har yau maganar da nake maka bamu san ya labarin gawar Abbanka ta kasance ba, shi yasa ya k'i yarda kan cewar mutuwa ko kuma wani tsautsayin ne ya faɗa mishi, shi yasa ya k'i yarda da k'addarar da Allah ya jarabce shi da, shi yasa ya bijire ma hukuncin ubangiji. Yanzu haka maganar da nake maka akwai sauran kuɗaɗenshi da bamu k'arasa biya ba."1 Kuka na kuma fasawa, saboda a nawa tunanin abinda Alhajin ya yima Mahaifiyata ba k'aramin cin zali bane. A sama guduwa Abbana yayi, sai na rink'a ganin ai bai dace ace ya huce haushishi akan matar da aka gudu aka bari ba. Mik'ewa nayi zuciyata na wani irin k'una, duk da ban san ina zan dosa ba a wancen lokacin. "Ina zaka je?" Ta tambaye ni, hawaye na zuba a idonta, rashin abin cewa yasa na koma na zauna, a haka muka cigaba da kukanmu sai da muka yi mai isarmu muka gama. "Ina Uncle Jafar?" "Kayi hakuri da abinda zai fito bakina, amma shima Allahn da ya fimu k'aunarsa, ya yi mishi rasuwa." Innalillahi wa inna ilaihir raji'un na rink'a nanatawa, a lokacin ji nike tamkar nayi ma Allah wani gagarumin laifi ne, wanda ya rink'a jarabtata ta wadancen ɓangarorin. Kasa kukan nayi, saboda hawayena sun gama k'arewa, a galabaice na ɗago ina kallonta "Shi kuma wancen yaron fa? Ina kika samo shi?" "Amanar Jafar ce Sadic, shi ne kaɗai ɗa guda ɗaya tilo da ya haifa, kuma wurin haihuwarsa mahaifiyarshi ta rasu, hakan yasa ya ɗauke shi ya damk'a mun, ko ranar da zai rasu sai da yace kada in sake in ce ma Farouq ba nice na haife shi ba, dan haka ina rok'on alfarmarka, ko da wasa bana son inji wata magana ta biyo baya a tsakaninka da shi, daga rana irin ta yau, ya zamana kun zama 'yan uwan juna, wanda suke uwa ɗaya, haka ma uba ɗaya." K'asar carpet Farouq ya sauko ya zauna dirsham, jajayen idanunsa, sun k'ara fitowa waje, sai dai babu ko ɗigon hawaye, kallon SS yake yi, irin duba na tausayawa, idan ya tuna yadda yayan nashi yayi ɗawainiya da shi, domin kuwa shine cin shi da shan shi, haka kuma shi ya kula da karatunshi baki ɗaya, har izuwa yanzu, ashe ba shak'ik'inshi ne ba, ashe ba uwa ɗaya ta haife su ba kamar yadda ya zata. Hakan ya kara masa wata daraja da k'ima a idanunsa, bai san lokacin da ya fashe da kuka ba, ya isa gabanshi, ya sa hannu ya k'ank'ame shi. Shima kukan ya saka, itama Jay shi take yi, jin irin tozarcin da Baffanta yayi ma mutumen da ya kuɓutar da ita daga tata rayuwar ha'ula'in. Sai da suka kwashi dogon lokaci suna abu ɗaya, sannan suka sassauta, hakan ya ba SS damar cigaba da bayaninsa. "Tun daga ranar na ɗauki soyayyar duniya na ɗora a kan k'anina abin alfaharina Omar Farouq, kasancewar shi kaɗai ne ɗan uwan da ya rage mun, shine gata na, nine gatanshi, sai kuma mahaifiyarmu. A washe garin ranar da na dawo na yi shirina na fita, ban tsaya ko ina ba sai company da Abbana ya ke aiki, cikin ikon Allah na samu Alhaji yana nan, haka na zauna ina jira, har lokacin da mutane suka tsagaita sannan na shiga. Zaune yake a tangamemen office ɗin, kan shi a k'asa yana ta 'yan rubuce-rubuce na shigo da sallama k'unshe a bakina. K'asar office ɗin na zube ganin mutumen da ban taɓa zato ko tsammani ba, mutumen da ya wulak'anta ni, ya tozarta ni, ya ci mun zarafi, duk da kasancewata ta k'aramin yaro, mai k'arancin shekaru. Duk da mamakin ganinshi da nayi, hakan bai hane ni fayyace mishi guzurin da naje da shi ba, na gaya mishi abinda ya faru da Abbana, a k'arshe nace Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu da shi, ban bari yayi magana ba na juya na fita, duk kuwa da irin mamakin da na gani shimfiɗe a kan fuskarsa. Tun daga nan muka bar garin Katsina, muka koma Kano da zama wurin wata yayar mahaifiyarmu, a haka nake bin yaran gidan zuwa kasuwa, kuɗin da nake samu da su aka sanya Farouq a makaranta, nima da su ne na samu nayi joining Bayero University, ina zuwa kasuwa, ina kuma karatuna, sai ya zamana Allah ya tallafa mana, tafiya tayi tafiya, sai gashi na buɗe ɗan k'aramin shago na siyar da atamfofi a cikin kantin kwari. Haka rayuwarmu ta cigaba, cikin rufin asirin Allah, kuɗin da na tara, na dawo Katsina na siya fili na fara gini, a lokacin kuma ina neman aiki, cikin sa'a na samu a nan Zenith Bank, reshen jahar Katsina, sai muka tattaro muka dawo gida, a haka na haɗu da Aysha marigayiyar matata, wato mahaifiyar Jafar. Soyayya mai tsabta muka yi da ita, domin kuwa so na take tsakaninta da Allah ba dan abin hannuna ba. Bayan munyi aure muka cigaba da zama da ita, da mahaifiyarmu sai k'anina abin alfaharina, wanda bana iya rayuwata ba tare da ina jin numfashinsa a kusa da ni ba. Muna da shekara ɗaya da aure aka yi mun transfer zuwa Maiduguri, a lokacin kuma Farouq zai shiga jami'a, hakan yasa na yanke shawarar nema mishi admission a UniMaid, domin mun riga mun saba da juna, bama iya yin nesa da junanmu ko alama. Haka muka baro Hajiya a Katsina, bayan na samo mata yarinya da zata na ɗebe mata kewa, muka koma Maid da zama, sai dai kusan duk k'arshen wata zamu zo mu duba ta, mu koma. Abu na k'arshe da ya taɓa zuciyata sosai shine mutuwar Aysha. A ranar da ta haifi Jafar, bata ko saka shi a idanunta ba, Allah wanda ya fimu k'aunarta, ya anshe abinshi, haka shima ya tashi maraya, a hannun Hajiyarmu, har sai da yayi shekaru biyu sannan na dawo da shi hannuna, yana samun kulawarmu ni da Farouq. A ranar da na haɗu da ke ban san ko wacece ke ba, haka kawai na tsinci zuciyata da son taimaka miki, domin a duniya babu abinda nafi ɗauka da daraja da muhimmanci irin mace, na tsani duk wani wanda zai wulak'anta mace, hakan yasa ni ke jin tsanar aminina Sadam Kazaure. Ko da kika bani labarinki, har na fahimci ke ɗiyar Alhaji Kabir ce, banyi mamaki ba, duk da ba wai na ji daɗin abinda ya faru dake bane ba, amma nayi believing da maganar hausawa da suke cewa ALLAH BAYA BARIN HAK'K'IN WANI A KAN WANI."2 Murmushi yake yi, a karo guda yana shafe hawayen da ke kwarara a idonsa, haka ma Jay, haka ma Farouq wanda a yanzu yake jin kiyayyar Baffa, ba kamar juyawar da yayi, ya ganshi tsaye tare da Goggo, da wani dattijo, wanda ya tabbatar shine Mal. Baba, saboda tsabar kamar da ya ga suna yi. Mik'ewa SS yayi ya isa gaban Malam ɗin da niyyar gaishe da shi, sai dai ya buɗe mishi hannuwansa, ya faɗa jikinshi, gaba ɗaya wurin ya k'ara kacamewa da kuka. Gafara Baffa ya k'ara nema a wurin shi, tare da mik'a mishi wasu fararen takardu, a cewar shi dukiyar mahaifinshi kenan da ya ansa, wacce ya gagara taɓawa tun daga ranar da ya gane cewar shi ne ɗan mutumen da yayi mishi aiki da gaskiya da amana, mutumen da ya haɓaka mishi tattalin arzikinshi a lokacin da yake da rayuwa, wanda da taimakonshi ne ya zama abinda yake a yanzu. Dak'yar suka samu SS ya ansa, shima sai da Mal. Baba ya haɗa da wa'azi da nasihohi masu ratsa zuciya, wanda ya cire ma kowa da yake gurin tabbunan da ke k'asar zuciyoyinsu, shekara da shekaru. A k'arshe suka mik'e suka musu bankwana, domin kama hanyar Maid, amma dole tasa suka bar Jafar a nan saboda irin borin da ya rink'a yi shi a dole sai an barshi a wurin Mammynshi. Jay da ta fito raka su, ta kasa haɗa ido da shi, haka kuma ta rasa da wane baki zata bashi hakuri, sannan kuma tai mishi godiyar abinda yayi mata. "Allah Ya tsare hanya. Ya kai ku lafiya." Abun da ta iya furtawa kenan, ta juya, ta koma ciki. ***Sadam. Fuskarshi babu walwala ya fito, jakar da ke hannunsa ya saka a bayan motar, sannan ya juya yana kallon yadda 'yan uwansa suka zagaye wurin tamkar wanda zai yi wata tafiyar da babu dawowa. Sa'id ne ya kalle shi, fuskarshi da murmushi. "Ka tabbatar ka dawo next weekend ɗin fa, kaga dai yadda rayuwa ta koma mana, bamu da wani mataimaki, mune zamu taimaki kanmu, mu kuma taimaka ma k'ananan k'annenmu. Dan Allah Sadam ka natsu, ka shiga tunanin ka, idan son samu ne ka nemi transfer ka dawo kusa da gida, ka kuma samu mata kayi aure, kai dai kaga ai ba yaro ba ne ba." Kallon shi kawai yake, domin kuwa bai son komai game da halayyarshi ba, bai san wanene ainahin mutumen da ke tsaye gabanshi a yanzu ba, bai san yana da aure ba, har ma da albarkar 'ya. Ta ɓangarenshi kam, bai san ta ina zai fara faɗi ma danginshi yadda rayuwarsa ke tangal-tangal ba, asali ma shi kanshi bai taɓa gane hakan ba sai a wannan lokacin. "In sha Allahu zanyi bakin k'ok'arina." "Masha Allah, ka kiyaye sallolinka a kan lokaci, ka kula da addininka sosai fiye da komai da zaka sa gaba, kana dai ganin yadda rayuwarka ta kasance, ka kuma ji tsoron Allah a duk inda kake, ka kiyaye hak'k'in wani a kanka, domin kuwa Allah yana yafe ma bayinsa kowanne irin laifuka da za su yi, amma baya yafe zaluncin da wani ya yi ma wani. Allah ya bada sa'a, ya tsare ka daga kowanne irin sharri." Gabansa ne yayi mummunar faɗuwa. Kalaman yayan nashi sosai, sun taɓa raunatacciyar zuciyarsa, wacce mutuwar mahaifinshi ta gama rugurguza duk wani shiri da yake cikinta. Sai ya rink'a ganin tamkar ya san halin da yake ciki, shi yasa yake yi mishi irin wannan nasihohi. Murmushi yayi, wanda iyakacinsa fatar laɓɓansa, yayi musabaha da kowa sannan ya juya da zumar shigewa mota.1 Kiran da ya shigo wayarsa ne ya dakatar da shi, ya fitar da wayar daga aljihunsa ya duba, (Bank Manager) ɗinsu ne, hakan yasa ya ɗaga da sauri, ya ɗora a kunnensa. "Alhamdulillah. Mun gode Allah." "Yau zan taho in sha Allah, dan har na fito ma." "Akwai matsala ne?" "Ok to sai na k'araso din." Maganganun da yayi kenan, ya kashe wayar ya mayar a aljihu, ya shiga motar tare da ɗaga masu hannu ya fita daga harabar gidan. Ya rasa dalilin da ke hana shi samun sukuni a zuciyarsa, duk da ya san mutuwar mahaifinshi ta taɓa shi, amma yana ji a jikinsa akwai wani gagarumin abun da ke addabar zuciya da gangar jikinsa wanda ya gagara gane ko menene shi, haka dai ya rink'a rafsa gudu a titin, sallah kawai ke tsayar da shi, bai isa Maid ba, sai misalin takwas saura na dare. Sai da ya tsaya yayi takeaway a wani restaurent, sannan ya kama hanyar zuwa gida. Ga mamakinshi yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi, wannan karon gaba ɗaya dabararsa ta gama kwancewa, ya rasa wa zai tunkara da batun ɓatan Jay da tilon 'yarsa? Ya rasa ina ta dosa da take neman jefa mishi kokonta a kasan zuciya, menene dalilinta na guje mishi? Ko ta daina k'aunar shi kamar yadda ta rink'a faɗa a ranar da suka yi karonsu na k'arshe? Wanene ya kuɓutar da ita? Ita ce tambayar da ya fiya nanatawa a k'asar zuciyarsa, amma bai samu ansa ba. Buɗe gate ɗin ya fara yi ya shiga da motar, sannan ya fita ya rufe, ya kwashi kayansa daga cikin motar, ya mik'a zuwa ciki.3 Hankalinshi a tashe ya zube kayan da ke hannunsa a kan kujera, ya koma ya zauna shima yana k'are ma yadda gidan yayi wata irin k'ura kallo. Bai san ta ina zai fara ba, dan haka ya kwantar da kansa a kujera, zuciyarsa na bugawa fat-fat, idan da wani zai k'unace mishi, to babu dalilin da zai hane shi jin yadda bugun zuciyar tasa ke tsanantawa. A daren ranar bai iya tsinana ma kanshi komai ba, haka kuma bai samu wadataccen bacci ba, duk da wannan dama ba sabon abu bane a wurinshi ba, dan rabon da yayi bacci mai kyau, tun ranar da ya kwana a mashayar Grand Pinnacle Hotel. Hakan yasa ya ci alwashin matsawar ya kai washe garin gobe, to babu abinda zai yi mishi katanga da zuwa neman ɓatacciyar matarsa. *** Bakwai da rabi dai-dai na safe ya gama shiryawa. Fita yayi ya shiga motar ya fitar da ita, ya rufe gidan, ya koma ya tada motar, ya wuce ya bar harabar wurin baki ɗaya. Tsaikon da aka samu na cinkoson ababen hawa, shi yasa ya iso wurin k'arfe takwas saura minti biyar, a hamzarce ya fita ya ɗauki jakar laptop d'insa, a dai-dai lokacin motar SS ta danno kai wurin da suke adana motoci a harabar bank ɗin. Sai da ya tsaya ya k'are mishi kallo ya tabbatar da lafiyar shi k'alau babu wani abu da ya same shi, amma ya k'i ya kira yayi mishi ta'aziyyar mahaifinsa, a matsayinsa na mutum mafi kusanci da shi a cikin gaba ɗaya ma'aikatan da suke aiki a wurin, domin kuwa kaf ma'aikatan bankin babu wanda bai kira shi ba, in bayan shi SS ɗin. Yana ganin ya gyara parking, yana k'ok'arin fitowa, ya juya da sauri ya wuce zuwa ciki. Office ɗin manager ya isa, ya bashi hannu suka gaisa, ya k'ara yi mishi ta'aziyya, sannan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ke girke gaban k'aton teburin da ke ɗauke da computer, printer, da sauran muhimman takardu na ma'aikata. Mik'ewa manager yayi ya dubo wasu fafaren takardu guda biyu, da suke cike da rubutu a cikin tarin takardu da ke gabansa, sannan ya koma kujerarsa ya zauna. "Kazaure ya aka yi haka? Ko ince mai zaka ce game da waɗannan takardun?" Ya mik'a ma Sadam, wanda yayi saurin sanya hannu ya ansa yana dubawa. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." A zuciyarsa ya so yayi maganar, amma Allah da ikonsa sai ta bayyana a fili, har manager na taya shi k'arasawa. "Sanin kanka ne banki baya ɗaukar asara, sanin kanka ne kuma banki baya zama da masu yi masa ha'inci da zagon k'asa. Ya aka yi kayi wannan gagarumin aikin? Ya aka yi haka? Haba Kazaure." Zufa ce ta yayyafo a goshinshi, duk kuwa da standard A.C ɗin da ta fuskanto shi tana hura mishi sassanya iska mai fitar da k'anshin airfreshner mai daɗi. "Amma kasan wannan cin amana ne ko? Saboda duk wani ma'aikacin banki kafin ya fara dole sai yayi rantsuwa da kula da hak'k'ok'in banki, da kuma kula da dukiyoyin mutane. Haka kuma idan loan kake nema a matsayinka na ma'aikacinmu, kasan baza a taɓa hana ka ba, amma me yasa ka munafurci banki ka ɗaukan mata kuɗi ba tare da sani ba?"1 Manager ne me wannan maganar yana kallonsa, amma Sadam ba shi da bakin magana, dan bai taɓa zaton har asirinsa zai tonu kafin ya mayar da kuɗin ba, bai taɓa tunanin caca zata juya mishi baya haka ba, domin kuwa ba zai iya cewa ga abu ɗaya da yayi ba da zunzurutun kuɗi har nera miliyan daya da ya ranta wanda ya wuce masa caca, wanda a lokacin, tunaninsa zai samu abinda ya fisu, sai dai cikin rashin sa'a, a ranar da ya je teburin caca da sauran kuɗin, k'arshe ko takalmi bai dawo da shi ba saboda irin warwas ɗin da akai mishi.2 "Me kayi da kuɗin mutane har haka Kazaure?"2 Maganar manager ta dawo da shi daga kogin tunanin da ya tsunduma. Cikakkar sumar da ke kansa ya shafa, yana tunanin irin k'aryar da zai shirya, sannan ya ɗago yana kallonsa. "I'm sorry sir. Wallahi bani da wani alternative lokacin da na ari kuɗin nan, kasan Dad ɗina ya sha jinya, to a gaskiya a lokacin ne na ari kuɗin na bada aka fitar da shi waje, to cikin rashin sa'a ma sai gashi bai tashi ba. In sha Allah zanyi k'ok'arin dawo da su tun kafin abin ya fito fili." "Amma kai kanka kasan baka kyauta ba ko? Saboda wannan kamar cin amana ne. Amma tunda ka ce haka, zamu yi rubutu a baka daga nan har zuwa k'arshen wata ka fito da kuɗin mutane, idan ba haka ba, banki zai dakatar da albashinka, haka zalika zamu yi gwanjon duk wata kadara da ta kasance mallakinka." Bai iya furta komai ba, kanshi a k'asa, haka manager ya gama 'yan rubuce-rubuce, ya sa hannu, sannan ya mik'a mishi shima ya sa hannu, ya tashi ya fita zuwa bakin aikinsa. Aikin da ya haye masu shi ya hana shi ganin SS, kasancewar shi yana sama inda yake ansa k'orafe-k'orafen customers, yayin da SS yake kasa, fannin Accountants. Lokacin da suka fito lunch yana cikin mota ya kifa kansa jikin steering, yana tunanin inda zai samo makuden kudɗaɗen da ya ranta, ta wani ɓangaren yana tunanin inda Jay ta nufa, a faɗin garin Maiduguri. Tsaye SS yayi, yana jifarsa da wani irin wulak'antaccen kallo, zuciyarsa da ta k'untata, take wani irin tafarfasa, a karo guda take bugawa da sauri-sauri. Bai ce da shi k'ala ba, ya buɗe gaban motar ya zauna, idanunsa na kallon gabansa yace "Ja mu je." Dagowa yayi yana dubansa, a lokaci guda yana mamakin canje-canjen da ya ke gani daga aminin nashi. Bai yi gardama ba, ya tayar da motar suka fita daga wurin, duk da ba wai ya san ina zasu je ba. "Titin bypass zaka ɗauka." Yayi maganar fuskarsa babu annuri ko alama, dan kuwa ji yake zai iya illata shi matsawar ya nemi kawo mishi raini a dai-dai lokacin. Bai tanka mishi ba, ya canja akalar motar zuwa inda ya buk'ata, sai da suka yi tafiya mai 'yar tazara, sannan suka dakata a k'asar wasu bishoyoyi da ke gefen titi... Brown envelope ɗin da ke gabanshi ya tsura ma idanu, a karo guda ya mik'a hannu zai ɗauka, sai kuma ya komar da kanshi jikin kujera ya kwanta, yana cika bakinshi da iska yana furzarwa, a hankali, yake lumshe dara-daran idanuwansa, wanda dogayen eyelashes suka yi ma ado, suka k'awata santalar fuskarsa, mai ɗauke da kwantaccen saje. K'aran da wayarsa tayi ne ya sanya shi buɗe ido yasa hannu ya zaro wayar a aljihu, ya ɗora a kunnensa. "Ayya yarona. I miss you so much. Ka samu Mammy ka manta da ni ko?" Hands free ya saka wayar yana gyara zamanshi ya janyo envelope ɗin ya fara dubawa. "Ban manta da kai ba Daddy. Ina Uncle Farouq?" "Ya koma school saboda exams, yace kuma in faɗa maka yayi fushi shima." Dariya Jafar ke yi sosai, tamkar yana gaban mahaifin nashi yace "To kuyi hak'uri Daddy. Yaushe zaka zo?" "Owh kai baza ka dawo ba kenan sai dai ni in zo ko?" "Idan ka zo zamu dawo tare hadda Mammy da Rukkayya ma." Shiru yayi yana nazarin maganar ta Jafar, a zuciyarsa yana addu'ar ina ma hakan zata kasance. Murmushi yayi a zahiri "Baka bani Rukayya mun gaisa ba ka tsaya nan kana surutu." "Barin bata to." Ta wayar yana jiyo yadda suke drama da ita kan ta ansa wayar, amma fur yarinyar ta k'iya, hakan yasa SS yace da shi ya k'yale ta, kafin ya k'ara cewa komai tuni ya mik'a ma Jay wayar1 "Mammy kema ku gaisa da Daddy to." "Hello." Ya ji muryarta ta daki speaker wayar, hakan yayi dai-dai da faɗuwar farar takardar da ke hannunsa wacce ya zaro daga cikin brown envelope ɗin gabanshi. Cikin rashin k'warin jiki ya ɗauki wayar tare da cire hands-free ɗin ya ɗora a kunnenshi. "Ya kuke?" Yayi maganar cikin wata irin kasallaliyar muryar da bai san sa'adda ta juye ta koma haka ba. "Alhamdulillah. Ya aiki?" "Babu daɗi, and idan na dawo gidan ma ba daɗi, babu kowa sai ni kaɗai. I'm tired da irin zaman nan haka." "Eyyah. Sai hak'uri ai. Gashi kuma mun yi maka fashin Jafar." "No fa, bakomai ai." "Madalla. Sai da safe to." "Ernmm." Sai kuma yayi shiru. "Ya dai?" "Uhnmm, nothing. Good night and take care of yourself and the kids." Yayi saurin kashe wayar bai jira ansarta ba, a karo guda ya dafe kanshi, yana tunanin abinda ke shirin faruwa da zuciyarsa.2 Tunda yake a duniya, marigayiyar matarshi Aysha ce mace ta farko da ya taɓa jin kwatankwacin abinda yake ji a yanzu. "Me ke shirin faruwa da ni?" Yayi maganar a k'asar zuciyarsa, yayin da a fili yayi gaggawar furta "Astagfirullah wa'a tubu ilaih." Takardar da ta faɗi k'asa yasa hannu ya ɗauko, a sannu ya fara dubawa. A zahirin gaskiya bashi da niyyar taɓa kuɗin nan, duk da kasancewarsu halaliyarsa, abin kuma da mahaifinsa ya bari, amma bashi da wani zaɓi a yanzu, dole ya taimaki amininsa da ke tsananin bukatar taimako. Tattara takardun yayi ya mik'e ya shiga kitchen, ya fito hannunshi ɗauke da lemun five alive tare da glass cup, ya zauna ya tsiyaya ya fara sha, sai dai a zahirance zuciyarsa tayi nisa sosai a wani tunanin na daban.2 *** Sky blue ɗin shadda ce sanye a jikinshi, ɗinki da aka mata ya yi matuk'ar ansar shi, haka zalika ya fito da ainahin kamala da cikar zatinshi. Ash color ɗin takalman da ke k'afarshi rufaffu ne k'irar HEM&OMAKIE. Cikin gaggawa ya fito hannunsa rik'e da hularshi sky blue mai ratsin ash kaɗan, a lokaci guda yana mak'ala cuplinks a hannuwan rigarsa, yayin da ya zaro bugaggar agogon Rolex a aljihunshi mai silver chain ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa, ya dai-daita zaman hularshi, kafin ya isa ya ɗauko takardun nan da Baffa ya bashi ya fito ya rufe ko ina na gidan, ya shiga mota, ya fita ya bar harabar wurin. Diamond bank ya nufa, cikin sa'a, bai sha wahala wurin ganin manajan bankin ba, a nan ya gabatar mishi da papers ɗin dake hannunshi, ya basu suka je suka yi duk abinda ya kamata, suka tabbatar da shi ɗin ne mamallakin dukiyar da aka zuba a account ɗin da ya nuna musu. Lokacin da aka gwada mishi tarin makuden kuɗaɗen da Baffa yayi saving da sunanshi, ba k'aramin mamaki yayi ba, duk da kasancewar mahaifinshi na da rufin asiri, amma bai yi tsammanin ya tara dukiya har haka ba. Sai dai kuma idan yayi duba da yadda aka ajje kuɗin na tsawon shekaru, ta yiwu ta haka ne aka samu yawaitarsu, kasancewar juya su da aka cigaba da yi ta hanyar da ya dace. Bai ɓata lokaci ba yayi signing cheque, ya fitar da miliyan guda a ciki, yayi sallama da manajan ya fito, ya dauki hanyar Zenith bank.4 Kai tsaye ofishin nasu manajan ya zarce, ya k'arasa biyan bashin da suke bin Sadam. ** K1 wanaki hudun da yayi a prison gaba ɗaya ya fita hayyacinshi, ya k'ara bak'i, da wata irin rama, hakan yasa ko da SS ya kalle shi sau ɗaya bai kara kallonshu ba. Sai da suka yi duk cike-ciken da zasu yi, kafin suka fito mishi da waya, da takalmanshi suka mik'a mai, bayan ya saka ya iso gaban SS da ya juyar da fuskarshi, ya daki kafaɗarsa tare da faɗin "Thanks Bro." "Come with me." Ya ja hannunshi ba tare da ya kalli bak'ar fuskar tashi ba suka fito waje. "Where to?" "Just follow me." A dai-dai lokacin suka iso gaban motar, ya buɗe seat ɗin mai zaman banza ya mishi nuni da ya shiga, haka ya shiga, shi kuma ya zagaya ya shiga seat ɗin driver sannan ya tada motar suka bar wurin. Hanyar fita gari suka lauka, a karo guda ya cire wayarsa ya fara kiran Farouq. "Ina hanya zan je Katsina yanzu in sha Allah. So ka kula da karatunka please. Will call idan na dawo." "Ok, zata ji in sha Allah." Ya kashe wayar, ya murza gear, sannan ya taka motar ya fara wani irin mahaukacin gudun da rabon da yayi irin shi ba zai iya tunawa ba. "Stop the damn car Tafseer."3 Murmushin da SS ya saki ta gefen kumatunsa, a karo guda ya juyo yana kallon Kazaure shi zai tabbatar da kallon da ya ke masa irin kallon da aka fiya yi ma masu matsalar k'wak'walwa ne. "You must be crazy, and why the hell should I?" "I am going nowhere. I'm not even ready to meet her yet." "You're insane Kazaure, baka kuma isa kasa in fasa abinda nayi niyya ba." Shiru Sadam yayi, kanshi a k'asa yana haɗa 'yatsun hannunshi wuri guda yana wasa da su kamar k'aramin yaro, a lokaci guda hawaye suka fara sintiri a kan fuskarshi.2 "Me sa baza ka fahimci halin da nike ciki ba a matsayinka na mutum mafi kusanci da ni? Me sa baza gane yadda k'auna da soyayyarta suke azabtar da zuciya da idanuwana ba? Sagir da wane ido kake son in kalli Jay? Da wane baki zan nemi gafararta da ta 'yar da na wulak'anta tamkar wacce na tsinto a bola. Na tsani kaina SS, ina tababar imanina, ban san me gaba zata haifar dangane da alhakin mutanen da ke kaina ba." Kallon shi kawai yayi ya juyar da kanshi ba tare da yace k'ala ba, duk kuwa da yadda yake hango tsantsar nadama a idanuwanshi. "A matsayinka na aminina, abokina, nayi zaton zaka taimaka wurin ganin na dai-daita rayuwa ta da ta iyalina. Amma me sa ka tsaya tsayin daka kan dole sai na saki matata? Me hakan ke nufi? Me haɗinka da ita?" Idanunshi a titi yana mai cigaba da rafsa gudunshi, sai dai tambayoyin da ya jera mishi sun sa ya kusa kasa controlling abinda yake ji a k'asan tashi zuciyar. "Saboda baka kamace ta ba Kazaure. And rabuwarku ce kawai zata taimaka maka wurin gane katafaren giɓin da ka yi ma rayuwarka, kaima zaka ɗanɗani bak'in cikin da ka ɗanɗana ma zuciyoyin mutane da dama." "You're mistaken. Jay baza taɓa bari na ba. She loves me, and trust me sai na dawo da farincikin da nike tunanin na rasa. Zan rok'i gafararta, and zata yafe mun har ma ta dawo mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai cike da aminci da tsantsar soyayya. A yadda nike jin ta a halin yanzu, bana tunanin zanyi sakacin da zata kuɓuce mun a karo na biyu."4 Murmushi SS yayi na takaici, bai bi ta kan maganarshi ba ya k'ure volume ɗin wak'ar da ke tashi a motar, ya kara wuta. *** Su biyu ne zaune a cikin palon, sai dai duk wanda ya kalli fuskar Kazaure, zai iya tabbatar da alhini da tsananin tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki. Rabon shi da gidan shekaru biyar kenan, tun zuwan shi na k'arshe da Baffa yayi mishi korar kare, hakan yasa ya ga canje-canje da kuma banbance-banbance na da yawa daga cikin zubi da tsarin gidan. Tsaye tayi bakin k'ofar tana k'are mishi kallo, duk kuwa da baya da ya juya mata, hakan ne kuma ya ba SS damar karantar yanayinta itama ba tare da saninta ba, donib kuwa tayi nisa a tunanin yadda zata haɗa idanuwanta da na mutanen da ta fi k'auna fiye da komai, a karo guda kuma take jin k'iyayyarshi fiye da duk wani abun k'i da ke doron k'asa.2 Mikewa SS yayi ya iso bakin k'ofar da zumar fita ya basu wuri, sai dai ba tare da ta kalle shi ba tace "You don't have to. I don't need any privacy with him." Jin muryar Jay yasa Sadam yayi saurin mik'ewa bakinsa na kyarma, a karo guda idanunsa na k'yaftawa. "Jaaaaay!" Bata damu da halin da yake ciki ba, ta tako ta shigo cikin palon, SS ya rufa mata baya ya koma inda ya tashi ya zauna. "Alhaji fa?" Ya tambaya yana kallon ta. "Ya fita, amma Goggo ta kira shi yana kan hanyar dawowa." A lokacin Sadam ya isa gaban kujerar da ta ke zaune ya duk'a gabanta, hannuwansa duk biyun ya mik'a da shirin ɗora su kan gwiwoyin k'afafunta. "Don't you dare touch me!" Tayi maganar da wata irin kakkausar muryar da ta sa Sadam yayi saurin sauke hannunsa, ya koma k'asar carpet ɗin ya zauna yana kallonta. "Me sa kika bar ni Jay? Me sa baza kiyi tunanin halin da zan shiga ba idan na dawo na samu baki nan? Babe ni mai laifi ne, of course, sai dai bai kamata ace kin hukunta ni ta hanya irin wannan ba. I'm so sorry, ki yafe mun, Ki zo mu koma mu ci gaba da rayuwarmu. Na miki alk'awarin canja duk wasu munanan ɗabi'una, zan kula da ke da 'yar da muka haifa, zan baki duk wani farin ciki da ya dace da ke." Kallon shi take irin kallon da ke cike da so da k'auna, mamaki da tausayi, ta wani ɓangaren k'iyayya da kuma jinjina ma rashin kunya irin ta D'A NAMIJI. Sallamar Baffa ce ta sa gaba ɗayansu suka kai duba ga k'ofar, a karo guda faɗuwar gaban Kazaure ta tsananta ganin yadda annurin fuskar mutumen ya ɗauke, lokacin da ya dora idanunsa a kanshi. Cikin rashin k'warin jiki ya tashi ya koma gefe ya zauna, sannan suka fara gaisawa da SS, Sadam kam da ya gaishe da shi bai ko kula ba balle ya bi ta kan gaisuwar ta shi.1 "Ernnnm Ummi." A hankali ta ɗago tana dubanshi. "Na sanar da ke duk yadda muka yi da yaron nan lokacin da na je Maiduguri. Haka kuma kamar yadda Sagiru yayi alk'awari gashi ya kawo shi, yanzu saura ya rage tsakaninku." Juyawa tayi tana kallon Sadam wanda shima ɗin ita yake kallo. Idanunsa da suka ciko taf da hawaye yasa taji nata idon ya kawo ruwa a lokaci guda. "Ke nike saurare Ummi, idan kuma kina ganin zan matsanta miki, to kiyi duk abinda ya dace. Ke dai ba yarinya ba ce, haka kuma kin fini sanin bak'in cikin da kika shak'a ta dalilinshi" Ya mik'e ya fita, SS kam juyawa yayi yana kallon yadda suke aika ma junansu wani kallo wanda ya sa shi jin wani abu ya tokare k'ahon zuciyarsa.3 "Babe ki taimaka ki ceci rayuwata kada ki bar ni, idan kika bar ni wallahi zan iya rasa raina, idan kuma har na cigaba da rayuwa a doron k'asa, to ina mai tabbatar miki da cewar zan cigaba da zama a cikin yanayi na bak'in ciki da tashin hankalin da ba zan iya misalta miki ba."1 Jajayen idanunta ta ɗago tana mishi duban da ta kasa tantance na so ne ko na k'iyayya? "A duniya idan har da wani zai tambayeni labarin mutum mafi munin halaye, ina mai tabbatar maka da labarinka zan bayar Kazaure. Inda wani zai tambaye ni labarin mutum mafi son kanshi fiye da kowa haka zalika labarinka zan bayar. A da na so ka, so na hak'ik'a, irin son da ban taɓa yi ma wani mahaluk'i kwatankwacin irin shi ba. Irin son da da wani zai ce mun yana existing a wannan duniyar da sai in gardamata, amma a kaina ya faru, a zuciyata na rink'a jin shi, amma wannan bai hana mun tsana da k'iyayyarka ba a yanzu. Ina jin sonka kwatankwacin yadda nike jin k'iyayyarka, sai dai ga dukkan alamu k'iyayyar da nike maka ta rinjayi soyayyar, hakan yasa bazan taɓa iya cigaba da zama da mutum mai bak'ak'en halaye irin naka ba. Na tsane ka Sadam, na tsani duk wani mai k'aunarka, dan haka ka sauwak'e mun, ka bani takardarta a nan wurin ba wai sai mun je ko ina ba."3 Ta duk'e ta fashe da wani irin azababben kuka mai tsananin zafi da ciwo a cikin zuciya. Da sauri ya isa gabanta yana k'ok'arin sa hannu ya ɗaga ta SS yayi azamar shiga tsakaninsu. "You heard her. She hates you, dan haka idan har ba kare ya cinye maka zuciya ba ya kamata ka sauwak'e mata Kazaure." "Just move aside Malam. She's still my wife. I love her, and ba zan iya rabuwa da ita ba. Ina Son ki Jay, soyayya mai tsanani wacce ban taɓa jin labarin irinta ba a tarihin rayuwar masoya. Na canja halayena Jay, ki dawo gare ni please, nayi alk'awarin barin shan giya, zan bar caca a matsayinsu na ababe guda biyu da na fi k'auna fiye da komai, zan koma mutum na gari, I'll be a good husband to you, also a very good father to our daughter. I love you."3 "But I hate you Kazaure. I don't wanna be with you anymore. Ka sauwak'e mun matuk'ar kai ɗin ɗan halak ne wanda aka haifa ta hanyar aure. Na tsane ka, ba kuma zan iya cigaba da zama da fasik'i mashayin giya ba. Ina jin kunyar ranar da Rukayya zata girma a nuna mata kai a matsayin mahaifinta. Ina da-na-sanin saninka a gaba ɗaya rayuwata." Kuka Sadam ke yi mai taɓa zuciyar duk wani mai saurare, ita kanta mamakin mutumen da ke gabanta ta ke yi, ta wani ɓangaren ta kasa gaskata ainahin mutumen da ta ke kallo a yanzu, wanda halayyarsa gaba ɗaya ta sha banban da ta tsohon kazaurenta mai zafin zuciya, da saurin fushi. "Duk da kasancewar nayi alk'awarin sauwak'e miki matukar kin bayyanar da son hakan da bakinki, sai dai ban za ci hakan daga gare ki ba, haka kuma ba zan daina rok'on yafiyarki ba, bazan yi k'asa a gwiwa wurin son kasancewa tare da ke ba. I love you Jay, this is all that matters, I can't do without you. You're my life."2 "Me sa baza ka gane bata da buk'atarka a yanzu ba? Me sa baza ka gane yadda take son ta kwatanta maka k'iyayyar da take maka ba?" "What are you up to? Menene damuwarka da matata?"2 "That's none of your business. Kayi abinda ta ce maka that's all that matters." Juyawa yayi yana kallonta, kuka kawai take, a hankali ya taka ya isa gabanta ya duk'a. "Babe kin daina so na wai?" "I hate you Sadam." "But I love you. I want to spend the rest of my life with you." "Bana son k'ara ganin fuskarka ko a mafarki, ina rok'onka da ka sauwak'e mun ka tashi ka ɓace ma ganina." "Idan haka zai kawo miki sassaucin abinda kike ji game da ni, I'll do as you pleased. Fine. Shikenan."1 Ya sa hannu ya goge zafaffun hawayen da suke zubo mishi, ya kalle ta da wani yanayi ya na cigaba "Na sake ki, SAKI D'AYA. Ki sani, hakan ba zai sa in k'aurace daga gare ki ba, ba zai sa in daina son ki ba, haka kuma ba zai sa in hak'ura da ke ba, nayi hakan ne ba dan komai ba, sai dan in hukunta kaina a matsayina na marar adalci, marar tausayi, wanda ya cusa bak'in ciki a cikin zuciyarki. Nayi haka ne dan in baki dama ki fahimci irin son da nike miki, ki kuma gane canjin da aka samu a rayuwata. Jay na rasa mahaifina, amma banji zafi ba kwatankwacin bak'in cikin da nike ji yanzu da zan rasa ki ba. I love you, and will always do. Zan dawo gare ki, na san a lokacin kin samu natsuwar zuciyarki, na kuma san a lokacin zaki gane irin nadamar da nayi."5 Idanunsa sun kaɗa jajur, hawaye na kwarara, ya mik'e ya fito, anan yayi kiciɓis da Baffa da ke tsaye bakin k'ofar yana sauraren duk abinda ya wakana. Kallonshi yayi, ya girgiza kai. "Nayi abinda kake so Baffa. Na sake ta. Ina fatan hakan zai goge tsanar da kake mun a cikin zuciyarka. Ko ba komai, mun haɗa jini da ita, idan babu aure tsakanina da ita, akwai Rukayya, wacce ta zama rabin jinina da na 'yarka. Na barka lafiya."6 Ya juya da sauri yasa hannu ya toshe bakinshi yana kuka yana komai haka ya fito a gidan tamkar mahaukacin da ya fara hauka a ranar.7 😢😢😢😢😢 3 Jay's Outfit.. *** A cikin sati biyun da suka gabata, ta mayar da kanta tamkar mai zaman takaba, kullun tana gida, a gidan ma a ɗaki take rufe kanta, cikin sa'a ta samu Rukayya ta fara sabawa da mutanen gidan, hakan yasa take barin ta tana sakewa. Jafar kuwa tun ranar da Babanshi ya zo, yayi mata text cewar ya tafi da shi, ko kayansa bai tsaya ya ansa ba. In banda k'unci da rashin walwala babu abin da yayi katutu a zuciyarta, sai ɗan lokaci zuwa lokaci da ta kan taɓa karatun jamb ɗin da zasu zana sati mai zuwa. Babban abinda ke addabar zuciyarta bai wuce yadda take son ta manta Sadam ba, amma ko sau ɗaya hoton fuskarshi, bai taɓa bacewa a cikin zuciyarta ba, ta kasa daina mafarkinshi kamar yadda duk lokacin da idonta ya kai kan Rukayya take ganin tamkar mahaifin nata ne, ba don komai ba sai dan asalin kamar da suke da shi. Komai nashi ta ɗauko, hatta da manya-manyan idanunsa da sukan tafiyar da bak'in ciki da damuwar da ke zuciyar Jameela. "Haba Ummi, ina kike shirin jefa kanki haka? Yanzu a yi mutum a duniya ba zai fito yayi fira da iyayenshi ya ma ji daɗi a ranshi ba? Sai dai tunda kika dawo gidan nan baki da wani aikin da ya wuce ki shige ɗaki ki kulle? Haba Ummin Baffa." Da murmushin k'arfin halin da ta k'ak'alo ta ɗago tana duban Goggo wacce a zahiri bata san lokacin da ta shigo ɗakin ba. "Wallahi babu komai Goggo, karatun jamb ɗin nan ne ya sako ni gaba, kinga Baffa bai tashi sanar da ni ba sai satin da ya wuce, kuma ni na ma rasa ta inda zan fara karatun wallahi, ga shi next week za ayi exam ɗin ban ma san ya zanyi ba."2 K'arasawa tayi ta zauna a bakin gadon, kallonta take cike da so da kuma tausayawa kalamanta, Ummi da a da take mutum mai tsananin son karatu, yau itace take maganar ta mance yadda ake yi. Girgiza kai tayi, sannan ta kama hannunta, hakan yasa Jay ta mik'e daga kwancen da take tana murmushin k'arfin hali tana dubanta. "Banda abinki Ummi ai daurewa zaki yi, idan kika yi la'akari da yanayin da muke ciki zaki gane cewar baya son ki rasa wannan damar a karo na biyu. Kiyi hak'uri ki daure kiyi karatu, kada ki tsaya wurin duba k'urewar lokaci. Kina jina?" "Haka ne Goggo. In sha Allah zanyi iyakar k'ok'arina." "Allah ya taimaka, ya miki albarka, ya kuma shige mana gaba baki ɗaya." "Amin amin." "Yanzu ki tashi ki je ga abinci can an kammala, ki daure ki saka ma cikinki wani abu." "Zan tashi in sha Allah." Da haka ta mik'e ta fita, ita kuma tayi baya da kanta, ta koma ta kwanta tana mai cigaba da aikin tunaninta. *** Tsaye take gaban madubin tana k'are ma kanta kallo, ta kuma kasa gaskata irin canjin da take gani a tattare da ita cikin 'yan kwanaki. Bak'ar abaya ce a jikinta k'irar India wacce aka yi ma ado da zanen filawa kalar ruwan gwal mai sheki, bak'in gyalen abayar ta lullube kanta da shi, bayan ta tattara cikakken gashin kanta ta ɗaure a tsakiyar kan, inda kuma tayi naɗin cikin wani salo da ya k'ara fito da doguwar fuskarta wacce haskenta ya k'ara dawowa a ɗan hutun da ta fara samu a gidansu. Bak'ar agogon fata ta ɗaura wacce aka rubuta MK (Michael Kors) a fuskar agogon, ta sanya bak'ak'en sneakers a k'afarta, sannan ta rataya reddish brown ɗin jakarta kirar channel, ta ɗauki wayarta, ta matsa gaban madubin tana kallon yadda ta canja completely, duk da cewar ba wani make-up ta tsaya yi ma fuskar tata ba. Murmushi ta saki, tana jin wani yanayi a tattare da ita, ta juya ta fita zuwa ɗakin Goggo. Tsaye ta same ta tana k'ok'arin buɗe wardrobe, da alama shirin wanka ta ke yi, a haka ta isa suka gaisa, ta dube ta da fara'a da jin daɗin yanayin da ta ganta. "Wai ba dai har kin shirya ba?" "Na gama komai Goggo, Baffa kawai zan gani in tafi." "Allah yasa ayi a sa'a, Allah ya bada rabo mai amfani." "Amin. Amin" Ta juya tana kallon Rukayya da ke kwance tana bacci kan gadon Goggo, sannan ta mata bankwana ta fita zuwa part ɗin Baffanta. "Sannu da hutawa Baffa. Ina kwana?" "Alhamdulillah Mamana. Har kin fito kenan." Baffa ya faɗa lokacin da ya mik'e daga shingiɗar da yayi, jikinshi sanye da jallabiya mai gajeran hannu, hannunshi na dama rik'e da casbaha, hakan na nuni da lazumi ya ke yi. "Na fito Baffa." "Masha Allah. An shi nan, mota na nan waje na sa Ado driver ya fito da ita an wanke anyi duk abinda ya dace, ki kula da titi, Allah ya bada sa'a." Yayi maganar sa'adda ya mik'a hannu saman stool ɗin da ke tsakanin kujerar da ya ke da wacce ke gefe ya ɗauko makullin mota yana mik'a mata. Kasa ansa tayi, haka kuma kanta a k'asa tana girgiza shi. "Nagode Baffana, amma ba ni da hannun da zansa in anshi kyautar ka a halin yanzu. Kayi hak'uri ka bar ni in saka maku da alherin da kuka yima rayuwata tun daga ranar da kuka haife ni har izuwa yau da baku gajiya ba."2 Murmushin dattako Baffan yayi, a zuciyarsa yana alfahari da canjin da ya ke gani a tattare da 'yar tasa, sai dai ba wannan ba ne zai sa ya hana ta morewa da kuma jin daɗi daga dukiyar da ya tara domin ita da mahaifiyarta. "Kada ki damu Mamana. A kullu yaumun ina alfahari da ke, ina kuma mai yaba ma k'wazonki wurin son ganin kin daɗaɗa mana. Anshi nan kiga, wannan kyauta ce ta musamman daga gare ni. Allah yi miki albarka." Hannu biyu ta sa ta ansa, a karo guda idonta suka ciko da k'walla, tana cigaba da rattaba ma Baffa addu'o'i, ta mik'e ta fita. Bin bayanta yayi da kallo, alal hak'ik'a yana jin daɗin yadda take rayuwa a natse yanzu, yana matuk'ar son yadda take girmama su tana basu wani matsayi na daban, take kuma sanya buk'atarsu a farko kafin tata. Ba dan ba dan ba da sai ya ce gara da aka yi haka, tunda ko ba komai, yanzu Umminshi ta zama mutum sak kamar kowa, yarinya mai ladabi da biyayya ga iyayenta, anan kuma dabarar samo mata malamin addini da zai cigaba da koyar da ita addininta ta faɗo masa. Yayi murmushi tare da cigaba da jan casbahar da ke hannunsa. Bak'ar BMW M4 ta gani an parka a gab da k'ofar palon sai k'yalli ta ke, a hankali ta kai duba ga number motar ta gane number tsohuwar motarta ce a jiki, a karo guda ta latsa makullin da ke hannunta, a take ta ji motar ta ansa kuwwa, tare da nuna haske daga fitilun da suka k'awata gabanta. Cikin jin daɗi ta shiga ta tada motar, Allah ya taimaketa automatic ce, amma ta san da manual ce da baza ta iya tuk'a ta kai tsaye ba. Yadda ta juya steeringwheel ɗin, a take kuma tayi reverse, sai ya zamana tamkar bata kwashi wasu shekaru ba tare da ta yi tuk'i ba. Da reverse ta fita daga gate ɗin gidan, sannan ta juya ta hau titi sosai, ta murza motar ta fara tafiya hankalinta kwance. Titin F.C.E ta dosa kasancewar can ne centre ɗinta, cikin walwalar da ta rasa ko ta mecece ta isa har gaban hall ɗin tayi parking, sannan ta fito ta wuce ciki. Sun kwashi kusan awa ukku kafin suka kammala komai, saboda tsaikon network da suka rink'a samu. Fitowa tayi ta fara takawa zuwa inda tayi parking, sai dai jikinta ya bata tamkar wani yana kallon ta. Sai da ta isa gaban motar, sannan ta juyo, cikin rashin sa'a ta sauke idanunta a kansa. Murmushi ya jefe ta da shi, hakan ya k'ara tabbatar mata da cewar shi ɗin ne dai ba wai mai kama da shi ba ne ba. Murmushin itama ta saki lokacin da ya iso gabanta, idanunshi a waje yana binta da kallon mamaki. "So it's you?" "Sure. Nima ina ganin kamar kai, kamar ba kai ba. Me ya kawo ka garin nan?"2 "Wallahi nine fa. k'anwata na kawo jamb, saboda d'aukar alhaki irin na mutanenmu duk garuruwan da ke kusa da Maid su rasa inda zasu cillota sai Katsina. Tun jiya muke garin nan." "Sai hak'uri ai. Ina kwana bamu ma gaisa ba." "Wallahi fa, Alhamdulillah. Ya ke kam me ya zo da ke nan? Ina Kazaure and baby na san tayi wayau ko?" "Its a long story. Baby ta girma har tana shirin shiga school ma. Ya wurinsu Malam da Hajiya?"1 "Kowa lafiya lau. But please ya aka yi na ganki nan?" "Ka share kawai Faisal. Ba abinda zan ce wanda ya wuce Alhamdulillah. Please Ka bani number Malam da na Hajiya zan kira su in sha Allah. Dama ina ta tunanin ina zan samu numbers ɗinsu." Bai k'ara cewa komai ba, ya karanta mata numbers ɗin, inda shima ya buk'aci tata, ta bashi suka yi bankwana ta shiga ta tafi, sai dai ta bar zuciyar Faisal Goni taf da tunani kala da kala, a ciki kuwa hadda wani bak'on lamari da ya ziyarci zuciyarsa, a take ya fara addu'ar Allah yasa hasashenshi ya zama gaskiya5 ***Bayan Shekara daya*** A hankali ta ɗago tana k'are mishi kallo. Ba fari ba ne, haka kuma ba za a saka shi a jerin bak'ak'e ba, irin chocolate color ɗin nan ne masu wahalan samu, sumar kanshi a cike take dam, wacce ta kwanto ta gefen fuskarshi, ta saukar da wani saje mai asalin kyau, da bala'in tsada, kasancewar ba a fuskar kowanne namiji zaka iya ganin irinshi ba. Yana da madaidaitan idanu masu haske da shek'i, 'very attractive', haka kuma eyelashes ɗin da suka mik'e tsaye saman idon sai suka k'ara mishi kwarjini, suka kuma k'awata shi. Idan ta koma ta kan siffar jikinshi, tsayayyen namiji ne dogon gaske sai dai bai cika faɗi ba. Zubin jikinshi ya fi yanayi da zubin fulani, irin dogayen nan masu kalar jikin 'yan hutu. Cak ta tsaida idanunta kan laɓɓansa, wanda suka kasance jajaye daga ciki, yayin da bak'i ya zagaye su, hakan ya k'ara ma santalar doguwar fuskarsa ado. 'Tabbas namiji ne, ya zo da zuwanshi, ta yadda ake son namiji ya zo, domin a wannan ɗan lokacin da ta karance shi bata hango makusa ko kaɗan a tattare da shi ba, most importantly, idan tayi duba ga kyawawan ɗabi'u da halayenshi, sai dai bata tunanin zata iya ansa tayin da ya zo mata da shi, kasancewar zuciya da ruhinta gaba ɗaya sun ta'allak'a wurin son mutumen da ta haramta ma kanta soyayyarshi, hakan yasa take jin tayi bankwana da soyayyar kowa a gaba ɗaya rayuwarta.2 "Shekara guda din da ta gabata, na yi ta ne cike da rashin natsuwa da matukar tashin hankali, na takura zuciyata, na wahalar da ita, na sanya ta cikin wani hali na tunani, na bari har sai da lokaci yayi sannan na dawo gare ki. Ba zan ɓoye miki ba, na kamu da wani zazzafan ciwo a taakanin kirjina, wanda matsawar baki taimaka wurin bani magani ba, Jay bana tunanin zan samu sauk'i ko kuma sassauci a tare da ni."2 Kai ta fara girgizawa, wasu zafafan hawayen da bata fahimci ko na menene ba suka yayyafo a idonta na hagu, ta kawar da kai ta goge su, sannan ta juya tana kallon shi. Bata san me take ji game da shi ba, ta dai san ba so ba ne, sannan kuma baza ta kira shi k'i ba, dan ko ba komai, bai cancanci ta jefe shi da kalmar k'iyayya ba. Duk da cewar ta so ta fahimci hakan tun rana ta k'arshe da suka rabu, amma bata yi zaton zai iya tunkararta da wannan gagarumin batun da ya sosa mata zuciya ba, yanzu gashi nan ya dauke ta, ya mayar da ita ruwa tsundum a soyayyar Kazaurenta, wacce ta samu ta ɗan lafa a k'asan zuciyarta. Hawayen da ta ke mak'alewa ne suka kasa tsayawa, hakan yasa suka gangaro a kumatunta. Ganin hakan ba k'aramin tsirga zuciyar SS yayi ba, da sauri ya mik'e ya isa inda ta ke, hannu yasa ya dafa kujerar da ta ke zaune, kawar da kanta tayi saboda kallon da ya ke mata ba zata iya jurar irin shi ba. "Watak'ila zaki kira ni mutum mai son kai, ma ci amana, ko kuma wanda bai san darajar abota ba. Idan kika yi mun kallon ɗaya daga cikin waɗannan, hak'ik'a kin zalunce ni. Jay ban zo wurinki da wata manufa ba face alkairi, haka kuma ko ta wane irin hali ba zan taɓa bak'anta zuciyar da zaki ara mun ba. Zan rik'e ki da amana da gaskiya, zan kula da ke in baki kowanne irin farin ciki a rayuwa. We ain't kids, balle mu tsaya muna ɓata lokacin juna, we're big enough to know what we feel about each other. If you don't like me, say it, and I promise I'll understand." Mik'ewa tayi da sauri, tana ciigaba da girgiza kai, har tana bige hannunshi dake kan kujerar da ta tashi, bata iya furta komai ba, ta juya ta bi ta k'ofar baya ta wuce ciki, cikin sa'a babu kowa a palon, direct ɗakinta ta faɗa, ta maida k'ofar ta rufe, sannan ta zube kan gado a take ta rink'a kuka marar sauti, mai tsananin zafi. Alal hak'ik'a ko a duniyar film ta ga namiji ya furta ma mace kalmar I love you, ba kowa take tunawa ba illa Kazaure, haka zalika yanzu da Sagir ya furta mata kalmomin, babu abinda ke yawo a cikin kanta bayan ranar da Sadam ya furta I love you a gare ta. Ya zata yi da soyayyar mutumen da ya wulak'anta ta ya wulak'anta gudan jininta? Ya kuma zata yi da SS da ya bijiro mata da tashi soyayyar? A matsayinshi na mutumen da ya taimaka wurin samun freedom a rayuwarta. Mutumen da yayi mata halaccin da ba kowa ba ne zai iya yin irin shi a wannan duniyar tamu da taimako ya zama abu mai matuk'ar wahala.2 "Ya Allah kai ne gata na, bani kuma da zaɓi face wanda ka yi mun. Ya Allah Ka warware mun matsalolin da suka addabi rayuwata."1 Ta k'arashe da kuka mai sauti, a dai-dai lokacin wayarta da ke jone jikin chaji ta ɗauki ruri alamar text yana shigowa. 'Da zaki san yadda kukan ki ke wahalar da zuciyata, na tabbatar da kin daina zubar da hawayenki har abada. I won't force you to like me, I just wanna let you know that I'm madly in love with you. See ya tomorrow. ....SS'2 Wani abu ta ji ya tsirga tsakiyar kanta, a karo guda ya cigaba da yawo a cikin jinin jikinta. Bata ankara ba call ɗin wata sabuwar number ya shigo mata, sai dai har wayar ta gama ringing bata da mu da ta ɗaga ba. Kiran ne ya k'ara shigowa a karo na biyu, hakan yasa ta shafe hawayenta, sannan ta ɗaga wayar ta ɗora a kunne. Muryar Faisal da ta ji yasa ta ɗan ɓata rai, a karo guda tana mamakin mutum irin shi, wato dan ya ga ta daina ɗaukar waccen number tasa, shine ya bijiro da kiranta da wata sabuwar number. "Ina jinka." Ta bashi ansar tambayar da yayi cewar "kina ji na kuwa?" "Ina ta kira baki ɗaga ba, and Malam told me kunyi waya, hakan na nufin tawa wayar ce bakya ɗauka ko?" "Haba Faisal, me sa baza ka fahimci abinda nike kwatanta maka ba? Kai kanka kasan wutsiyar rak'umi ta yi nisa da k'asa. And by the way, wallahi ba abinda ke gabana kenan ba, kuma sanin kanka ne ko aure zanyi babu dalilin da zai sa in faɗa ma saurayi wanda bai taɓa aure ba. Kayi hak'uri mu bar maganar nan please." "But ba haramun ba ne ai, idan kika lura ma sunnah ce mai k'wari, dan haka ki k'ara nazarin maganata, in sha Allah ina nan zuwa gobe da safe."3 "What? Please I'm begging you kada ka ba kanka wahala, wallahi abinda kake nema a wuri na ba zai taɓa samuwa ba Faisal, kayi hak'uri mu cigaba da zumunci kawai." "Ba zan iya ba Jay. Domin kuwa tun ranar da na ganki na kasa samun sukuni a zuciyata. A lokacin da kuka yi waya da Malam kika sanar mishi labarin rabuwarku da Kazaure ina zaune a wurin, kuma tun daga nan na ci alwashin sai na mallakeki ko ta wane irin hali."3 Bakinta ta cika da iska ta furzar, wannan wane irin abu ne ke shirin faruwa da ita? Upon all people, why SS? Why Faisal Goni? Mutanen da suka fi kusanci da Kazaure. Hakan na nufin dama munafuntar shi suke yi kenan...7 "You heard me ba. Ina nan tafe in sha Allah. Take care of yourself for me." Ya kashe wayar, sai kawai ta tsinci kanta da bin wayar da kallo, abin ma mamaki ya rink'a bata, ta wani ɓangaren kuma yana bata dariya. Me mutane suke son mayar da ita? Tambayar da ta yima kanta kenan, amma bata san ina zata samo ansar ba. *** Da shirinta ta fito hannunta sagale da jaka da makullin motarta. Inda Goggo da Rukayya ke zaune ta isa. A gefe ta zauna itama da murmushi a fuskokinsu, yayin da Rukayya ta isa da sauri ta faɗa jikinta. "Mammy ina zaki je?" "Tare da ke zamu je ai. So bana son surutu. Idan munje zaki gani." Murna ta fara yi, sannan Jay ta juya tana kallon Goggo. "Zan je gidansu Miemie. In sha Allah baza mu daɗe ba zamu dawo."3 "Kai amma kin kyauta Ummi. Haka ake son mutum ya zama mai gyara kuskurenshi a duk lokacin da ya fahimci hakan. Allah ya tsare, a gaishe mun da Hajiya." "Amin. Zasu ji in sha Allah." Ta mik'e suka fito hannunta rik'e da na Rukayya, ta buɗe mota ta saka ta, ta ɗaura mata seatbelt, sannan ta zagaya ta shiga, ta tada motar suka tafi. Cikin mintuna sha biyar ta isa gidan, ta fito ta zagaya ta fito da Rukayya tare da kama hannunta, ta rufe motar sannan suka sanya kai zuwa ciki. Hajiya suka tarar zaune a palon, ta k'arasa suka gaisa, sai dai yanayin kallon da matar ke mata na alamar sani ne, amma ga dukkan alamu ta manta inda ta san fuskar tata. "Jameela ce Hajiya. Miemie na nan kuwa?" "Haba ko da na ji. Nifa ina ta yi miki kallon sani amma na kasa tunawa. Ina kika samo yar budurwa? Zo taho nan mu gaisa." Ta k'arasa maganar tana mik'a hannu ma Rukayya, amma ta mak'e kafaɗa, ta matsa, ta kara mak'ale hannun Mammynta. Murmushi kawai Jay tayi, bata iya cewa komai ba, illa Rukayya da ta kalla tana cewa "Kije Hajiya na kiran ki." Dagowar da zata yi, kwatsam ta sauke idanunta a kan Miemie wacce bata san lokacin da ta fito ba, har ta tsaya tana kallonta. "Jay?" Ta faɗa idanuwanta a waje. Sai a lokacin Hajiya ta juya, "Kinga ashe tana kusa ma. Ku shiga ciki mana." Mik'ewa suka yi, suna bin bayan Miemie, anan suka fara kallon-kallo. A k'arshe Miemie ta isa ta rungume Jay, take suka fara hawaye, suka yi mai isarsu suka gama, sannan suka zauna suka fara firar yaushe gamo. Labarin duniya da na rayuwa suka tsunduma sosai, Miemie ta bayyana mata halin da ta shiga bayan ta samu labarin tafiyarsu da Sadam, yayin da itama Jay ta labarta mata yadda rayuwa ta kasance mata bayan ta bar gida. Wani sabon babin kukan suka buɗe, dak'yar suka tsagaita, Miemie ta kamo Rukayya tana cewa "Rabon wannan fine girl ɗin tamu ne. Gata nan kamarta sak da Kazaure, hatta idanun bata bari ba." "Owh, wato har yanzu baki manta shi ba ko? Kodai har yau baki daina crushing ɗin shi ba."1 "C'mon." Miemie ta faɗa a tak'aice, a karo guda suka sa dariya, a dai-dai lokacin wayar Jay da ke ajje gefe ta fara ruri. 'Faisal Goni' Shine sunan da ya bayyana kan screen ɗin wayar tata, idonta a waje "Ba dai da gaske yaron nan yana Katsina ba?" Kamar baza ta ɗaga ba, sai kuma ta ɗauka, ta ɗora wayar a kunne tare da faɗin "Hello." "Yes dear. Ga ni cikin Katsina, ban san ina zan dosa ba." "Lallai kai ɗin nan. Amma ya muka yi da kai dan Allah?" "Batun ya muka yi duk bai taso ba, I'm already here. Just text me your address." "Ni bana gida wallahi, and ba yanzu zan koma ba, so ka jira idan na koma I'll let you know." "C'mon Jay, annabi yace mu daraja bak'onmu fa. Why not ki texting mun address ɗin inda kiken inzo, tunda dama dai ganinki ya zo da ni garin."1 "Okay. I'll." Ta kashe wayar, ta juya tana kallon Miemie da ta zura mata ido, saukar da wayar tayi, tare da juya idonta, ta langaɓar da kai alamar 'kinga wani ɗan wahalar ko'. Dariya Miemie ta yi, "Kina nan dai da halinki Jay. Well lemme guess..." Ido ta fito da waje, "Guess what? Abeg stop it girl." "Girl you said?" "Yes now. Ain't you?" "No! Not at all Jay. Ko dan kinga kin ajje Rukayya kike kira na girl." Murmushi kawai tayi, a lokaci guda ta tura ma Faisal address ɗin gidan su Miemie, sannan ta dawo da hankalinta gare ta. "Tashi ki shirya please, akwai wanda zai zo ganinki." "Gani na? Waye shi?" "Dallah ki tashi, naga baki da buri a rayuwa wanda ya wuce miki boko, to ni zan haɗa ki da Mr. Right. Oyaa get ready sweetheart." "Hey, wai yaushe kika koyi manyance haka? Kina wani abu kamar babbar mata. Idan ma baki sani ba ki sani, soyayya baya gaba na wallahi." "Saboda kin rasa wanda kike so ko? Na gudan miki da crush nko." "Abeg, stop it mana. Ko lokacin yarinta ne kawai wallahi, sai daga baya na dinga dariyan abun, and yanzu da kika faɗa mun yadda zamanku ya kaya da kuma halayenshi, sai naji na k'ara tsanarshi wallahi. Ba dan ya haɗa jini da baby na ba ma da sai na mishi RM mai license."2 Kallonta Jay tayi, ta kuma gaskata abinda take faɗa. Bata ce komai tayi ɗan murmushi, a karo guda tace3 "Well, ki tashi ki shirya dai, cuz I believe zaki so guy ɗin da na kawo miki."1 "Really? But ki faɗa mun yanayinshi. Is he cute? Attractive? Good looking? Handsome? Or what?"2 "Da zuwan shi ya zo babe girl, he's just your type." "I hope so." Tayi maganar da murmushi a bakinta, sannan ta mike ta zaunar da rukayya a inda ta tashi, ta faɗa toilet. Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba wayar Faisal ta shigo ma Jay, bayan ta ɗauka ya shaida mata zuwan shi unguwar, daga nan tayi directing ɗinshi har k'ofar gidan su Miemie. Suna kashe wayar Miemie ta fito cikin baby pink ɗin abaya, tayi kyau ba kadan ba, yanayinta sosai ya bayyanar da kalar gayunta, haka zalika duk wanda ya dube ta, zai gane ta sha boko yadda ya kamata. Dakinta ta shigar da Rukayya ta haɗa ta da chocolates da teddies ɗin da ke ajje saman gadonta, sannan suka fita zuwa wurin Faisal. A wajen gidan suka same shi tsaye jikin mota, ya haɗa hannayenshi ya rungume yayin da ya baza idanunsa ma k'ofar fitowa gidan. Miemie ce a gaba, Jay na rufa mata baya, hakan yasa ko da ya ɗago sai ya sauke idonsa kan 'yar kyakkyawar budurwar da ke ta tsaye gabanshi. Bata damu da kallon da ya bita da shi ba, a haka suka iso inda ya ke, suka ɗan gaisa sama-sama, sannan suka yi mishi iso zuwa cikin gidan. A palon Abban su Miemie aka sauke shi, ta wuce ta kawo mishi ruwa, da abubuwan motsa baki. Sannan ta koma kujerar da ke gefen ta Jay ta zauna tana latsa wayar da ke hannunta. Sai da ya ɗauki ruwan da ta tsiyaya mishi a cup ya kai bakinsa, Jay ta kalle shi da murmushi, "Meet my friend, Barr. Miemie Hussain." Cup ɗin hannunsa ya ajje ya juya yana kallonta. Jay ma kallonta tayi, tana nuna inda ya ke zaune "Faisal Goni." "Pleasure to meet you Barr." Yayi saurin faɗa. Hakan yasa ta ɗago da murmushin ta, "Same here." "Ina son magana da ke please." Faisal ya faɗa yana kallon Jay, lokacin da ta mik'e tana shirin barin wurin. "Please. This is all I can do for you Faisal. She's my best friend, so treat her well. I mean well, well."4 Bai iya cewa komai ba, illa ido da ya bita da shi. Ta juya inda Miemie ke zaune. "Barin shiga wurin Hajiya." "Alright, will join you in a bit." Kallonta tayi, irin kallon da ke nuni da 'haba munafikfik.. ta saki dariya mai ɗan sauti ta juya ta shige ciki. D'akin Miemie ta koma ta kwanta rigingine, tana kallon yadda fan ɗin dake mak'ale jikin ceiling ɗin ɗakin take juyawa, sai dai a zahiri ba wannan ba ne abinda ya addabi zuciyarta, tunanin ta inda zata ɓullo ma SS yanzu, shine damuwarta. Ba tare da ta samo mafita ba, wayarta da ke cikin hannunta ta fara ruri, hakan ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninta, ta ɗago da wayar tana kallon screen ɗin. Da ɗan sauri ta ɗaga ta ɗora a kunnenta tare da sallama. "Muna gidan har yanzu." "Ok gani nan zuwa yanzu in sha Allah." Ta kashe wayar, ta juya tana kallon Rukayya da hankalinta gaba ɗaya ya tafi a wasan da take yi. "Babe tashi muje gida kinji, Goggo na nema na now now." Babu gardama ta ajje teddy da ke hannunta ta mik'e ta iso wurinta, tana tsaye tana gyara gyalen abayanta, ta ɗauki jaka da key ɗinta suka fita suka yi ma Hajiya sallama suka wuce, ba tare da ta shiga wurinsu Miemie ba. *** Ko da suka shigo harabar gidan bata kawo komai a ranta ba, duk kuwa da bak'in motoci biyun da ta gani girke a cikin gidan, haka ta gyara parking, ta fito hannunta cikin na Rukayya suka sanya kai zuwa ciki. Palon bak'in shine a farko, kafin ka mik'a wani dogon corridor da zai sada ka da sauran sassa na gidan, ga mamakinta, sai ta tarar da takalman maza a k'ofar shiga kusan guda biyar, a take kuma ta ji gabanta yayi wata mummunar faɗuwa, bata yi k'asa a gwiwa ba ta tura kanta ciki a hankali. Zaune yake a kujerar da ke kallon k'ofar shigowa, ganin mutumen da bata yi zato ba yasa wayar da ke hannunta ta sunɓule ta faɗi k'asa, hakan kuma ne ya jawo hankalin sauran jama'ar da ke wurin. Bata damu da yanayin da zuciyarta ta shiga ba, na tsananta wurin bugawa, ta duk'a a hankali, ta ɗauki wayarta, ta ɗago da fuskarta a ɗaure tam, tamkar bata taɓa dariya a duniya ba.3 Hannun Rukayya ta k'ara matsewa a nata, ta juya da sauri tana shirin komawa da baya. "Jay..." Ya kira ta da sark'ak'k'iyar muryarsa. Chak ta tsaya, ba tare da ta juyo ba, hakan yasa Rukayya juyawa ta kai kallonta inda ta ji maganar ta fito. Kuka ta saka mai k'arfi, tare da tura kanta tsakanin kafafuwan Mammynta, ga dukkan alamu, hakan ba zai rasa nasaba da fuskar Sadam da ta kalla ba.3 A lokacin sai da ya ji tamkar k'asa ta tsage ya shige tsakaninta saboda kunyar da ya ji. Dak'yar ya ɗaga k'afarshi ya tunkari inda suke tsaye, sai dai sallamar Goggo da ta 'yar budurwar da ta biyo bayanta ɗauke da tray ya sa shi dakatawa, ba tare da ya kai inda suken ba. "Dawo nan ki zauna Ummi." Dak'yar Rukayya ta yarda suka juya cikin palon, har kuma yanzu bata daina kukan ba, tana kallon Sadam zata k'ara fashewa da wani sabon kukan tamkar wacce taga dodo. A gefen Goggo suka zauna, hakan yasa shima sadam ya dawo inda ya tashi ya zauna, sai dai ya gagara sauke idonshi akan Jay da Rukayya ganin irin canjin da aka samu a gaba ɗaya yanayinsu. Brothers ɗinshi maza guda huɗu da suka zo tare, su suka fara gaishe da Goggo, ta ansa fuskarta ba yabo ba fallasa, sai a sannan Jay ta gaishe da su, suka ansa cikin sakin fuska, haka kuma ko da basu sani ba sun tabbatar da ita ɗin ce tsohuwar matar Sadam, saboda Rukayya da suka gani mai asalin kama da shi. Shiru na wani ɗan lokaci ya cigaba da wanzuwa a wurin, daga bisani Sa'id yayi gyaran murya ya fara magana. "Mun so ace mun tadda Alhajin, sai dai cikin rashin sa'a bamu samu ganinshi ba. Amma tunda mun samu damar ganawa da ku zamu yi amfani da wannan damar mu bada hak'urin abinda ya faru. Wallahi babu ɗaya a cikinmu da ya san halin da Sadam ke ciki, sai fa bayan afkuwar abin nan sannan ya sanar da mu." Salis da ke gefenshi ya ɗora da bayanin yadda rayuwar Sadam ɗin ta kasance, rabonshi da gida, da kuma dalilin barinshi gidan baki ɗaya. Yana gamawa Sa'id ya cigaba. "Duk da akwai makircin asiri a tattare da shi, amma yayi gangancin wulak'anta matar da ta sadaukar mishi da farin cikinta, ya kuma guji 'yarsa, wacce ya tabbatar jininshi ce. Yanzu ku duba ku ga yadda yarinyar ke kuka saboda ganin fuskarshi. A yanzu bamu da abinda zamu faɗa, saboda abinda ya faru, ya riga ya faru, illa muna masu baku hak'uri akan abun, ayi a hak'uri a gafarta ma juna dan Allah."1 Shiru Goggo tayi tana saurarensu, ta wani ɓangaren tausayin Sadam ɗin ya tsirga zuciyarta.1 "Tabbas abinda ya faru ya riga ya faru, fatanmu ɗaya Allah ya yafe mana baki ɗayanmu." "Madallah, mun gode k'warai, Allah ya sa mu fi k'arfin zuciyarmu. Kema kiyi hak'uri dan Allah, ki yafe duk wani abu da ya shiga tsakaninku." Ya k'arasa yana duban Jay da kanta ke k'asa, a karo guda kuma Sadam ya rink'a yi mishi alama da hannu cewar yayi maganar maida aurensu. Wata muguwar harara ya daka mishi, a haka suka ɗan sha lemun da aka kawo masu, sannan suka mik'e, Goggo ma mik'ewar tayi, suka yi sallama ta wuce ciki, su kuma suka fita zuwa harabar gidan. Yana ganin kowa ya fita, ya rage palon daga shi sai ita, sai kuma Rukayya da tayi bacci a jikinta, ya mik'e ya tako zuwa inda take, a gabanta ya duk'a, tare da k'ura mata mayun idanunsa.2 "How have you been?" Banza tayi kamar baza ta ansa ba, haka ta rink'a jin muryarsa na ansa kuwwa a cikin zuciyarta. "Good, I can see. Kin canja gaba ɗayanki, kin k'ara kyau abinki." Wato mai hali baya fasa halinshi kenan, ta innata a cikin zuciyarta, sai dai ta kasa furta komai, kamar yadda ta gagara ɗora idanuwanta a kanshi. "Kinga yadda Rukayya take gudu na ko? Me sa baki bata hak'uri on my behalf ba? Na ji kunya sosai yadda naga tana kuka lokacin da ta ganni. Please I'm so sorry for everything babe, please." Sai a lokacin ta juyo ta kalle shi, a take ta dake zuciyarta, ji tayi ta samu wani confidence da yasa ta watsa mishi kallon raini. "Ashe kana da kunya Sadam? Ashe akwai ranar da zata zo wacce har zaka ji kunyar abinda kai ma yarinyar da bata ji ko ta gani ba? Please idan wannan labarin ne ya zo da kai, ka tashi ka tafi dan bani da lokacin da zan ɓata wurin saurarenshi." "Babe kiyi hak'uri mana, na zo dan in nemi gafararku, ki yafe mun ki dawo ɗakinki mu cigaba da zaman mu." Kafin ta buɗe baki tayi magana, wayarta da ke rik'e a hannunta tayi beeping alamar text ya shigo, bata damu ba ta kai dubanta gare shi. "In dan wannan ne, da baka ba kanka wahalar zuwa ba, dan na riga na yafe maka na kuma manta da kai da duk rayuwar bak'in cikin da nayi tare da kai. Dan haka ka sani, har abada ba zan k'ara zama k'ark'ashin inuwa d'aya tare da kai ba Sadam, babu wata soyayyarka da tayi saura a cikin zuciyata."3 Text ɗin da ya k'ara shigo mata ne yasa tayi saurin buɗewa, ta fara karantawa. 'Ga ni a cikin gidan ku, 'll like to see to soon. SS'1 'Ka same ni a guest room.'1 Bata san lokacin da tayi rubutun ba har kuma ta tura, abu ɗaya da ta sani shine tana son bak'anta zuciyar Kazaure, watak'ila hakan zai sa ya fita a harkarta. "You're lying." Muryarshi ta dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa. "I can see the love you've for me in your eyes. You love me and nothing can change that. Kiyi hak'uri ki yafe mun, ki zo mu zauna mu fara sabuwar rayuwa mai inganci. I promise to shower you with love and care. I love you Jay, so very much. I cant live without you." Murmushin takaici ta saki, a karo guda tana jin kalamanshi na bugun zuciyarta, sai dai bata da wani option, and this is the best for both of them, zata tursasa zuciyarta ta hak'ura da son mutumen da ba za su taɓa k'ara kasancewa tare ba har abada. Kallon shi tayi ido cikin ido, a karo guda ta girgiza kanta.2 "That was then Sadam, A da na so ka, son da nike tunanin bazan taɓa iya fitar da shi daga zuciyata ba. As for now, my heart is already giving to someone. Someone who will take care of me and the baby you live your life hating. Idan da zaka ji shawara da ka daina nuna fuskarka a gaba na da sunan kana neman soyayyata, saboda na riga na shafe babinka a zuciyata, na manta da kai, da rayuwar da nayi tare da kai, na kuma riga da na damk'a zuciyata ma wanda ya cancanta." "This is insane." Ya fada yana kauda kai daga dubanta. "You belong to me Babe, and me alone. Wallahi ba wanda ya isa ya raba ni da ke I love you, look into my eyes babe, zaki gane son da nike miki babu k'arya ko yaudara a ciki, i love you with all my body and soul." Ya sassauta muryarshi, a karo guda hawaye suka sauka a kuncinshi, bai damu da yadda suka wanke mishi fuska ba, burinshi ɗaya Jay ta fahimci zazzafar k'aunar da ke harbin mishi zuciya.1 "Babe please, you deserve no one, but me. Nine fa. Your Sadam. The man you love, you care for. Please dont do this to me i beg you." "I did already Sadam. There come the man I'll spend the rest of my life with."1 A dai-dai lokacin SS ya tura k'ofar palon ya shiga. Juyawa yayi da sauri yana kallon k'ofar. Ganin mutumen da ya shigo ya sanya shi sakin wata dariyar da bai san ko ta mecece ba. "But this is SS. My very good friend."1 "Of course. And he's the man I choose to be with. Will you excuse me now please?" Ta mik'e da shirin takawa zuwa inda SS ke tsaye, wanda ke son ya fahimci abinda ke faruwa. Dariya sosai Sadam ya yi, daga bisani ya tak'aita, ya d'ago da idanunsa da suka canja color tuntuni. Cikakken sumar kanshi ya shafa, a karo guda ya juyar da kai yana kallon yadda suka tsaya. Ganin perfect match din da suka bayar ya sanya shi sakin wani razanannen k'ara tun k'arfi, da alama bai san lokacin da ya sake shi ba. "Bull sh*t! This totally bullbsh*t! You hear me?" Ya tafi da sauri da shirin jacking din SS, idanunshi a waje domin yadda ya ke jin zuciyarsa, zai iya yin ajalinshi. Cikin zafin nama Jay tayi gaggawar shiga tsakaninsu tana fad'in "What's your damn problem with my decision? Ka kama gabanka Malam, we're done here." "What's going on?" SS ya tambaya yana kallon Jay, ya juya ya kalli Kazaure, kanshi ya gama kullewa, ya kasa fahimtar abinda ke faruwa. Juyar da kai Sadam yayi, labbansa na k'asa ya tura cikin baki, ya kama waist dinshi da hannu daya, dayan yasa ya shafi tarin sumarshi, juyowar da zaiyi hawaye suka wanke kyakkyawar fuskarshi da ta fara fita daga hayyacinta.1 "Tell me you're kidding please." Yayi maganar da hawaye taf a idonshi. "I'm not Kazaure, I love him, and I'll soon marry him." Sosai kan SS ya kusa ya buga jin abinda Jay ta fada. Ta wani bangaren ya kasa gaskata kunnenshi, yayin da ta wani bangaren yake tunanin abinda ta ke shirin yi, a matsayinta na wacce yake neman soyayyarta, amma ta k'i amincewa. "Enough of this bull sh*t!" Sadam ya fada tun k'arfi cikin wata irin lion voice din da ta ansa kuwwa a gaba daya wurin. Palon ya fara zagayawa, zuciyarsa na cikin tashin hankalin da bai san ta ina zai fara maganinsa ba. Kallonshi Jay ta ke zuciyarta a k'ek'ashe, domin ta gama yanke ma kanta hukuncin rabuwa da shi ko ta wane irin hali. "So this is what you're up to?" Ya juya yana kallon SS, sannan ya cigaba. "But we're friends Tafseer. Ain't we?" Yayi maganar da lallausar murya, irin ta mai neman sulhu. Duk da fahimtar manufar Jay da SS yayi, hakan bai hana shi jifar Sadam da kalaman da suka fito bakinshi ba. "Of course we're. But banga abin tashin hankali a ciki ba. Ka saki mata zan aura, there's nothing wrong with it."1 "Owwh really? There's nothing wrong with it? Alright then, but wallahi. Ka ji na rantse? Baka isa ba Tafseer. Jay is mine. She's a mother of my kid, so to me she belongs, and no one else. Kuma zan gwada maka kai baka isa ba, mayaudari kawai." "Please out of this room Kazaure." Jay tayi maganar idanuwanta a kasa, muryarta na wani irin rawa. "Amma..." "Now. Please!" Ta katse shi cikin kakkausar muryar da ta razanar da Rukayya har ta farka a baccinta. Idanuwansa ne suka k'ank'ance, a take zuciyarsa ta karye, ya rasa me ke masa dad'i a gaba daya rayuwarsa. Murya k'asa-k'asa ya fara magana. "Babe idan zaki hukunta ni, ki hukunta ni ta kowanne hanya, but please don't do it this way. He's my friend. I can't bear to see you guys falling in love with each other. Please I'm begging you." "Kana bata ma kanka lokaci Sadam. Idan baka sani ba then lemme tell you, wallahi ko kai daya ne namiji da yayi saura a wannan duniyar na hak'ura da kai, ba kuma zan iya cigaba da zama da kai ba. Ka nemi gafara na, na yafe maka. Then what else do you want from me? The remaining pieces of my broken heart?"2 Murmushi tayi irin na takaici mai zafi a cikin zuciya, ta girgiza kanta, a karo guda hawaye suka silalo mata sannan ta cigaba. "That's impossible Kazaure, bazan taba k'ara yin wannan gangancin ba. Never!"1 Ta juya da sauri ta wuce ciki saboda kukan da Rukayya ta fara yi. "Jay. Jay please..." Sadam ya rink'a kiranta, amma ko kallon inda yake bata yi ba, ta shige ciki da saurinta. Juyawa yayi gadan-gadan ya doshi inda SS ke tsaye, collar rigarsa ya damk'a, yana kokarin hade shi da bangon, sai dai a lokaci guda yasa hannu ya cire hannunsa da ke jikin collar tasa, ya daddage, ya wurgar da shi.1 "Be careful Mr. Kazaure. Kayi sa'a I'm not as stupid as U're, amma yau da sai ka gane baka da wayo wallahi."1 "Baka isa ba Tafseer. Me sa zaka yaudare ni? Me sa zaka ci amanata? I trusted you with all my life amma ka rasa ta ina zaka saka mun sai ta wannan hanyar ko? Zaka yi da-na-sani SS, ni Sadam Kazaure sai na baka mamaki wallahi." A dai-dai nan Sa'id ya leko yana kiran Sadam tare da fad'in "Kai muke jira Malam. Ka zo mu tafi." Juyawa yayi yana nuna SS da hannu, daga bisani yayi k'wafa, ya girgiza kai ya juya ya fita. Shi kam k'arasawa yayi cikin palon yana gyara wuyan rigarsa da ya fara squeezing, ya zauna a daya daga kujerun da ke wurin, ya dora kafarshi daya kan d'aya, yayi balancing hannuwanshi, a karo guda ya fara tunanin abinda ya wakana. "So she used me."2 Yayi concluding, yayin da ya gamsu da abinda zuciyarsa ta ayyana 100%. Wayarsa ya cire ya typing mata text 'Let's talk, he's gone.' 'Okay.' Tayi replying mishi. Ba'a dade ba, ta fito kanta a k'asa, domin ta kasa gaskata abinda ta yi. Bayan ta zauna ya d'ago yana dubanta, har yanzu kanta na kasa, ta gagara hada ido da shi. "What's all this about?" Ya tambaya cikin natsuwa, ya kuma gagara sauke idanuwansa a kanta, duk kuwa da yadda yake jin zafin abinda tayi. "I'm sorry please. I just wanted to.. to get rid of him. Kayi hakuri dan Allah." "Is that why you used me? Saboda I'm nothing to you, cuz he's the one only one da kike gani a matsayin namiji ko? You did good Jay, and thank you very much for that." Ya mike da sauri, yana shirin barin palon. Duk da kasancewarshi ba gwanin zafin zuciya ba, abin nan ya taba shi sosai, har yana ganin he's less important a wajenta. "Ba haka ba ne fa." Ya tsinkayi muryarta lokacin da ya kai k'ofar fita, wacce ya tabbatar da kuka take kasancewar yadda maganar ta rink'a rawa, dakyar ta iya furtata. Chak ya tsaya, kamar zai juyo, domin a duniya idan akwai abinda ya tsana bai wuce kukan ta ba, amma ina irin kishin da ke nukurkusarshi ba zai taba barin shi ba, haka ya sa kai ya fita ya barta zaune a wurin. Hawayen da ke zuba a fuskanta ta shafa, ta dago da hannun tana kallonsu, ta tabbatar da kuka ne take yi, amma ta rasa dalilin da ya sanya ta zubar hawaye har haka. Murmushi ta saki, ta fara shafe fuskarta, ta mik'e da sauri ta bi bayanshi, sai dai a lokacin da ta fito, ta hangi motarshi na barin gate din gidan. Da sauri ta koma ciki ta d'auki waya ta fara kiran shi, amma har yayi ringing ya gama bai daga ba. Ta rasa dalilin da yasa ta kasa natsuwa saboda fushinshi, sai dai idan ta tuna cewar tayi provoking dinshi, sai ta ji hankalinta sosai ya tashi, hakan kuma ya sa ta k'ara kiran wayar a karo na biyu, amma shiru, ba shi da niyyar dauka. 5 Missed calls ta bar mishi ba tare da ya biyo bayan kiran nata ba. Ta rasa duk wata natsuwarta, ta kasa zaune ta kasa tsaye. A ganinta laifin duka nata ne, ta bata ma mutumen da ya taimake ta, wanda yake sonta da gaskiya, tsakaninshi da Allah ba wai dan wani abu da take da shi ba. Mutumen da ya mutunta, ya dawo mata da darajarta ta 'ya mace, ya kuma dawo mata da farin ciki da jin dadin da ta dunga ganin kamar tayi bankwana da su.+ Da sauri ta fita, inda tayi parking ta tasan ma, ta shiga ta tada motar ta dauki hanyar gidan Hajiya, domin ta gama yanke shawarar ansa tayin soyayyarshi wadda a da take jin kamar baza ta iya ba, amma idan tayi duba da abubuwa da dama, sai taga a duniya babu wanda ya cancanta da ita bayan shi, shine zai so ta as who she is, ya kulan mata da 'yarta, rabin ranta. Haka kuma tayi alk'awarin zata koyar da kanta soyayyarshi, tunda dama bata jin kiyayyarshi, sai dai son da take ma Kazaure ya hana ta tantance abinda take ji game da shi. Da wannan tunanin ta iso k'ofar gidan, zuciyarta na ta faman sake-sake, ta yi parking a waje ta fito, ta shiga ciki da sallama kunshe a bakinta. "Wa alaikumus Salam." Hajiya da ke zaune a palo ta ansa ta da fara'a sosai a kan fuskarta. "Ai ni nayi fushi Ummi. Sai yau ake ganinki?" Kanta a k'asa ta karasa ta zauna tana dan murmushin da ya fi kama da na dole. "Hajiya ina wuni" "Lafiya lau. Alhamdulillah. Ya mutan gidan?" "Lafiya lau wallahi." "Masha Allah. Ina ta zuba ido ko Rukayya in gani amma naji shiru." "Ina ta son zuwa nima, abubuwa ne sai a hankali." Ta k'arashe tana kallon Hajiyar. "Haka ne kam. Allah yayi taimako." "Amin ya Allah. Ina Yaya Sadic kuwa?" "Dazun nan muka yi bankwana yace zai biya ta can kafin ya wuce, ashe bai je ba?" "Ina zai wuce?" Ta tambaya da dan sauri, cikin razana, idanuwanta a waje. "Borno mana. Ko me ya hana shi zuwa?"1 Murmushi ta kakalo, a karo guda idonta ya cike da kwalla tace "May be yana sauri ne." Ta mik'e tana gyara gyalen abayanta. "Dama na zo ta unguwan ne na shigo in gaishe ku." "Har kin tashi kenan?" Hajiya ta fada lokacin da ta mik'e ta shiga d'aki ta fito da turare a leda, ta mik'a mata tana fad'in "Ki gaishe da mutan gidan." Ansa tayi tana godiya, sannan ta juya ta fita, hankalinta a tashe, tana tunanin halin da SS ke ciki, kasancewar tunda ta san shi bata taba ganin abinda ya bata mishi rai kamar wannan ba. ***Sadam. Tunda suka fita ya dukar da kanshi a tsakanin kafafunsa, kuka yake wanda bashi da sauti, hawaye kawai ke kwarara daga idanunsa, a lokaci guda yake da-na-sanin kofsawar da yayi a iya zaman da suka yi da Jay. Da ya san akwai irin wannan rana a duniya, da babu abinda zai hana shi mutunta ta, ya rik'e ta da daraja, ya bata dukkan soyayyar da tayi deserving, sai dai shi kanshi ya san is too late for him to cry, ya riga yayi loosing opportunity din da ya samu a baya, ya kuma san wutsiyar rakumi tayi ma k'asa fintinkau! Ya san ba shi da sauran amfani a wurinta kamar yadda ta fada, most especially idan yayi duba ga yanayin da yake ciki na rashin aikin yi a yanzu.1 "She's yours. And you alone." Wata zuciyar ta tunatar da shi. Hakan yasa a bayyane ya furta "And I'll fight for her. To me she belongs."2 Da sauri Salis da ke zaune a gefenshi ya d'ago da kanshi yana tambayar "Me ke damunka?" Kamar dan k'aramin yaro, sai ya fashe da kuka, ya fada kafadarshi yana fad'in "I love her Yaya. So very much." Bayanshi ya fara bugawa a hankali, sannan ya tadar da shi daga kafadar tashi. "You've to face the reality Sadam, yarinyar nan da wuya ta hak'ura ta koma maka, ka daure ka cire ta a zuciyarka." "But she loves me. I saw it wallahi, she still do loves me. Bazan iya daina sonta ba har izuwa k'arshen rayuwata. And I promise sai na dawo da ita gare ni ko da hakan na nufin zan rasa rayuwata ne."2 "Kai kana da matsala wallahi. Yanzu ka kwantar da hankalinka ka magance matsalolin gabanka kafin ka fara wani tunani." Banza ya mishi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba, ya juya ya cigaba da kukanshi, a haka har suka iso gida, ya fita da gaggawa bai ce ma kowa komai ba, ya wuce dakinshi ya shiga ya maida k'ofar ya rufe tare da sanya mata jamlock. Dan k'aramin room fridge din da ke gefen tv stand ya dosa ya bude, yasa hannu ya fito da kwalbar giyarshi, kallonta yake a hankali, rabon da ya sha yau kusan watanni hudu kenan, wanda a lokacin yayi alkawarin ba zai kara ba, amma a yanzu baya ganin wani abu da zai taimaka mishi ya mance abubuwan da suka faru kamar barasar. Daga kwalban yayi ya fara tuttula ma cikinshi, sai da ya shanye tass, sannan yayi wurgi da ita, ya fada saman gado yana cigaba da rera kukanshi, wanda duk wanda ya gani ya san soyayya ce ke azabtar da zuciyarsa.8 ***SS. Tuki ya ke a babban titin Kano zuwa Maiduguri, amma zuciyarsa gaba d'aya bata tare da shi, haka ma tunaninshi. Tunda ya ke a duniya bai taba ganin macen da yake mutuwar so kamar Jay ba. Jin soyayyar ta yake tamkar da ita aka halicc zuciyar shi, amma ba zai iya jure ganin yadda take daukaka soyayyar Kazaure a kan tashi ba, wadda ya tabbatar da duk duniya babu wanda ya kaishi kaunarta. "Why wud she take me for granted?" Ya tambayi kanshi tare da buga steering hannunsa. "I love her so much, but i can't take this anymore. I can't bear seeing her loving someone else...." Bai k'arasa rufe bakinshi ba babbar trailer da ta taho ta daga motarshi sama, ta watsar a gefen titi, hakan ya sanya shi fad'in "La'ila ha illallahu, wahdahu la shari kala, lahul mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kulli shai'n kadir." Tun daga nan bai kara sanin inda kanshi ya ke ba. Dakyar trailer drivern ya samu daidaituwar tunaninshi, da sauri ya taka birki, hakan ya ba motocin da ke bayansa damar tsagaitawa suma, kafin wani dan lokaci wurin ya gama cikewa da mutane.5 Dakyar suka fito da shi, saboda yadda motar ta lankwasa, tamkar babu halittar dan Adam a ciki. Wayarsa suka lalubo, a karo guda suka danna number Better half, wacce take a farkon call log dinshi, ta inda suka fara tunanin may be matarshi ce. Kwance take a ruf da ciki, bugun zuciyarta ya tsananta sosai, haka zalika faduwar gaban da take ji bata taba experiencing irinshi ba. Wayarta da tayi k'ara ne yasa ta mik'a hannu dakyar ta dauka, ganin number SS, yasa tayi saurin dagawa ta dora a kunnenta. Muryar da taji tabbas ba tashi bace, hakan yasa ta tambaya "Wa ke magana?" "Yawwa. Hajiya mai wayar ne ya samu accident, wanda a halin yanzu bamu da tabbacin yana mace ko yana raye." Da sauri ta mike tsaye zumbur, zuciyarta ta buga daaaaam! Hankalinta ya tsananta tashi, yayin da a lokaci guda taji wasu zafafan hawaye sun sauka akan kumatunta! "Kuna ina yanzu?" Ta tambaya dakyar lokacin da ta fito palo ta samu Goggo da Baffa a zaune. Bata iya cewa komai ba ta mik'a ma Baffa wayar. Ido ya bita da, ya ansa ya dora a kunnensa anan mutumen yayi mishi kwatancen inda abun ya faru, shima cikin tashin hankali ya mik'e yana fad'in "Ku taimaka ku kaishi asibiti mafi kusa, gani nan tafe yanzu-yanzun nan." Ya kashe wayar ya juya yana salati yana kallon yadda Jay ke kuka tsakaninta da Allah, tana yi ma Goggo bayanin abinda ya faru, lokaci guda fuskarta tayi jajur, ta fita a kamanninta. "Barin je. Kada wanda ya sanar da mahaifiyarshi a cikinku." Da sauri ta mike ta bi bayan Baffa, hakan yasa ya juyo yana kallonta, "Ki koma ki zauna Mamana, yanzu zamu dawo tare da shi in sha Allah." "Ka taimaka muje tare Baffa, ba zan iya zama a nan ba." Kukan da take shi ya fi bashi tausayi, hakan yasa yace ta zo suje kawai. "Nima ba kwa barni anan ba ai." Cewar Goggo da tayi gaggawar shiga ta fito da hijabinta, suka dunguma zuwa harabar gidan. Da sauri driver ya iso da katuwar Jeep, suka shige suka d'auki hanyar gidan Dr. Mukarram wanda ya ke kwararren likita, kuma shi ke duba Baffa a duk lokacin da bashi da lafiya, ko wani daga cikin iyalinshi. Cikin sa'a suka same shi, basu bata lokaci ba suka kama hanyar Kauyen da SS yayi accident din. Tafiyar ta d'auke su kusan awa d'aya, kafin suka isa clinic din da SS ya ke da taimakon mutumen da ya d'auki wayarsa, wanda shine ya rink'a directing dinsu. Kai tsaye dan k'aramin d'akin da aka kwantar da SS Dr ya zarce, anan ya fara aikinshi cikin kwarewa, sai dai ba zai iya yi mishi komai ba saboda karancin kayan aiki, hakan yasa ya bashi taimakon gaggawa, sannan suka saka shi a mota suka d'auki hanyar gida. Kuka Jay take mai azabar zafi, bata damu da su Baffa da ke cikin motar ba, ta kama hannun SS wanda bai san abinda ke faruwa ba ta rik'e karkadam, ta rasa dalilin da yasa ta shiga wannan mummunan tashin hankalin ganin shi a cikin irin wannan yanayin. Federal Medical Center suka zarce lokacin da suka shigo Katsina, direct A&E suka wuce da shi domin ceto rayuwarshi ciki2 Da sauri Dr Mukarram ya juya zai shige ciki, Jay ta matsa tayi gaggawar rik'e rigarsa, ya juyo a hankali yana kallon yadda gaba d'aya ta fita a kamanninta. "It's okay Ummi. I'll in sha Allah try my possible best." "It's all my fault Dr. Please I'm begging you to save his life no matter what. Just promise me." Tayi maganar idonta taf da hawaye, yayi jajur, ya dade da canja color tuntuntuni. Hannu yasa ya cire rigarsa da ke hannunta, a karo guda ya gyara zaman face mask din da ya riga ya daura a fuskarsa. "I promise you, zanyi bakin kokari na, I mean zanyi duk iya abinda Allah ya bani iko. So kici gaba da addu'a kawai." Bai jira me zata ce ba ya juya da sauri ya wuce ciki, Goggo ta isa gare ta, tana juyowa ta zube a jikinta tana wani irin azabtaccen kukan da ke azabtar da idanuwa da kuma zuciyarta, Allah ya sani tana da-na-sanin abinda ta yi ma mutumen da ya mik'a mata soyayyarshi kacokam, ya kuma 'yanta ta, ya daukaka mata darajarta ta 'ya mace. "Laifina ne Goggo. Idan ya mutu ya zanyi da rayuwata? Me zan fada ma Jafar? Goggo me zan ce ma Hajiya? Ya zanyi da rayuwata ni JAMEELA!"2 Ta kuma sakin kuka mai zafi, wanda sai da yasa Goggo ta matse nata hawayen, ta ja ta zuwa kujerun da ke girke a gefe suka zauna, kuka take mai tsuma zuciya, dak'yar Goggo ta fara lallashinta, sannan ta tsagaita kukan a nan ta fara nusar da ita illar abinda take fada. "Ba laifinki ba ne Ummi, wannan iko ne na Allah, wanda rayuwar dan Adam kacokam take hannunsa. Kiyi hakuri ki daina kukan nan, a halin yanzu babu abinda Sagir ke buk'ata wanda ya wuce addu'armu. Kiyi hakuri dan Allah." Shiru tayi, sai ya zamana ta koma tana yin kukan na zuci, tare da addu'ar Allah ya tashi kafadun SS ko dan ta rama mishi alkairan da ya yi ma rayuwarta. ***Sadam. Duk da kwalbar giyar da ya tuttula ma cikinshi, hakan bai hani hotunan abubuwan da suka wakana dawowa a cikin k'wanyarsa ba. Kuka yake yana jijjiga gadon da ya ke kwance, a k'arshe ya mik'e ya k'ara bude fridge ya fito da wata kwalbar giyar, ya daga yana zazzaga ma cikinshi, tamkar wanda bai san illar da hakan zata haifar masa ba. Cikakkun mintina goma ba'a yi ba ya fara wani irin tangadi, jiri ya fara dibansa, a lokaci guda ya ga d'akin na birkicewa, yana komawa up-side-down, hankalinsa gaba d'aya yana neman barin jikinshi, sai dai har iyanzu ya gagara daina ganin picturen Jay da SS lokacin da suka jera a gabanshi, ya gagara daina tuno kallon da SS ke jifarta da shi mai cike da salon so, da kuma kauna mai dukan zuciya.1 Wani irin kururuwa ya fara, a take ya cigaba da faffasa abubuwan da ke cikin d'akin, hakan ne kuma ya jawo hankalin sauran jama'ar da ke cikin gidan. "Sadam. Sadam. Lafiyarka kuwa?" Yan uwanshi da ke bakin k'ofar d'akin suke tambaya tare da k'ok'arin bude k'ofar, sai dai ya datse ta gam, daga ciki, haka kuma bai daina bige-bigen da ya ke ba, bai kuma damu da ya bude k'ofar da suke ta faman bugawa ba. Wani wawan bugu Salis ya kai ma k'ofar, amma ko motsi bata yi ba, a karo na biyu ya ja da baya yayi mata kyakkyawan bugun da yasa jamlock din ya fita daban daga jikin k'ofar kasancewarta ta katako, hakan kuma yayi dai-dai da zubewar Sadam a tsakiyar d'akin yana wani irin gurnani, tamkar zakin da ya ci karo da nama. Da sauri-sauri numfashinsa ya fara fita, daga bisani yayi wani razanannen kara, sannan numfashin ya d'auke gaba daya.2 "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Suka fara nanatawa a lokacin da kusan mutum bakwai suka fad'o d'akin abinka ga gidan yawa. Sa'id wanda ya ke likita shi ya fara dudduba shi, amma kasancewar ba shi da komai na aiki, yasa yace su d'auke shi su wuce asibiti kawai, haka zalika yanayin na Sadam ya tashi hankalinshi sosai, bama ya kwalaben giyar da ya gani suna yawo a tsakiyar d'akin. Salis, Saheeb da Shu'aib suka ciccibo shi dak'yar, suka saka a mota, Saheeb ne ya zagaya ya tada motar suka d'auki hanyar Dan Masara Specialist Hospital, kasancewar a can Sa'id din ke aiki. ***SS. Wasa-wasa sai da suka shafe kusan awa biyu zaune a wurin amma shiru babu wani labari, har kuma a lokacin Jay bata daina zubar da hawaye ba, lokacin da ta ke zaune saman sallaya dan nesa kadan, da inda Goggo da Baffa ke zaune saman kujeru. Gaba d'aya fuskokinsu sun shiga alhini, babu wanda ya ke cema dan uwansa wani abu, har zuwa lokacin da Dr Mukarram ya fito, a lokaci guda yana cire gloves din hannunsa, hakan yasa Baffa yayi gaggawar mik'ewa ya isa gabanshi, kafin yace wani abu wata nurse ta turo SS saman dan k'aramin gado fuskarshi lullube da farin mayafi. Hakan da Jay ta gani yasa tayi saurin tasowa itama, a tare suka iso gaban Dr suna tambayar abinda ke faruwa. "I'm sorry." Ya fada yana kallon Jay. A take ta wara idanunta tana fad'in "Sorry for what Doc?" Bai ansa ta ba yace da Baffa "Muyi magana a office." Ya juya ya fara tafiya, har kuma a lokacin bai bata ansar tambayar da ta yi mishi ba. Ganin hakan yasa suka yi gaggawar bin bayan nurse din da ke tura gadon da SS ke kwance, zuwa wani dan karamin daki wanda babu kowa a ciki, haka kuma bai yi kama da inda ake kwantar da marassa lafiya ba. "Ina ne nan?" Ta tambayi nurse din. Instead of ta bata ansa, sai ma juyowa da tayi da sauri "Please ku dakata a waje Hajiya, idan an gama komai za'a muku magana. "Komai? Kamar ya kenan?" "Kuyi hakuri ku jira a waje, babu wanda ake bari ya shigo nan." "I'm going nowhere Ms. Nurse." Ta tafi da sauri ta yace mayafin da aka lullube fuskarshi, gani tayi ya k'ara wani mugun kyau wanda tunda take bata taba ganinshi a tattare da shi ba. An wanke bruises din da ya samu, an kuma zagaye goshinshi da farin bandage, sai dai babu wani wuri da ke motsawa a gaba daya sassan jikinshi. "Nooooooo!!!!! This can't be."1 Ta fad'a tana zara idanunta da suka cike taf da hawaye, tana girgiza kai, a lokaci guda ta kama hannunsa tana jijjigawa. "Dont do this to me please. I love you SS. Kada ka tafi ka barni please, wallahi zan kula da kai, ina sonka, ka taimake ni kada ka mutu ka bar rayuwata a cikin tashin hankali. Wake up please. Please ba dan ni ba Ya Sadic, dan Allah, saboda k'aunar da nike maka, idan ka mutu ba zan taba yafe ma kaina ba, nice sila, ni nayi sanadiyyar mutuwarka. Ka tashi dan Allah. Wallahi ina sonka da gaske, ba wasa nike yi ba..."1 Cak bakinta ya datse, jin da tayi hannunshi da take rik'e da shi ya k'ank'ame nata hannun, a tsorace ta fara dawo da kallonta gare shi, sannu a hankali ta sauke idanunta a kan nashi idanun da suka bude tangaram tamkar ba wadanda ta gani dazu ba. Ganin haka yasa nurse din da ke tsaye gefe ta fita da gudu, har tana bige Goggo da ke tsaye a wajen k'ofar. "Do you really love me?"7 Taji shakakkiyar muryarsa ta fada, labbansa kunshe da wani kyakkyawan murmushin da ya k'ara mishi haske da kwarjini. "Of course Ya Sadic, and will always do, please don't leave me." Kafin ta kara cewa wani abu taji hannunsa da ya rike ta ya fadi kasa, idanunsa sun koma sun rufe ruf tamkar ba shi yayi maganar ba.5 😭😭😭😭😭😭😭😭😭 A duniya bai taba tsammanin akwai ranar da zata furta mishi wannan kalmomin da bakinta ba. Sai ma ya rink'a jin tamkar a aljanna ne suka had'u, domin yanayin wurin ya canja mishi gaba d'aya, ya koma tamkar wani ni'imtaccen garden mai yawan shuke-shuken flowers masu dad'in kallo da dad'in kanshi. Mikewa yayi zaune sosai, yana jin tamkar bai taba jin wani ciwo a jikinshi ba, hakan yasa ta fashe da wani kuka, a lokaci guda labbanta kunshe da kyakkyawan murmushi, hannunsa ta rik'e karkadam tana nanata kalmar "Alhamdulillah ya Allah." "Owchh.." Ya fad'a tare da langabar da kai yana kallonta "kin matse mun hannu akwai zafi fa." Da sauri ta sake shi, ta share hawayen da suka bata fuskanta, ta matso daf da shi tana cewa "I'm sorry Ya Sadic. Yanzu me kake ji? Ina ke maka ciwo? Me zan baka? Me kake so?" Kallonta yake kamar ya samu television, kauna da soyayyarta suna ratsa duk wani lungu da sako na cikin jikinshi, ashe a duniya akwai irin wannan farar ranar? Wai soyayyarshi ce yake hange a idanuwanta ko kuma tausayin halin da yake ciki ne?3 "Ya Sadic ina ke maka ciwo? Ai dai baza ka mutu ba ko?" "Wanne zan ansa a ciki? Jay tambayoyin sunyi ma patient yawa ai." "Just tell me baza ka taba bari na ba, nd you'll forever stay by side."1 A hankali yasa hannu ya d'ago da doguwar habarta, ya saita idanunshi cikin nata, yana aika mata da wani lallausan murmushin da ya sanya ta fara mayar mishi da martani ba tare da sani ba. Gefen da zuciyarsa take ya dora hannunta, har kuma yanzu bai sauke idanunsa a kanta ba1 "Kinga nan?" Ta girgiza kai alamar ta gani. Ya cigaba "This is where you belong. Da soyayyar ki aka halicci wurin, duk ranar da kika ga zuciyana ya daina bugawa da kaunarki, then there will be no me in this world. Ina son ki, so mai tsanani. Irin wanda ban taba yi ma wata halitta irinshi ba. I love you with everything I've. I love you so so very much. Allah kadai ya san iyakarshi."1 "I love you so much too." Bakinta ya furta ba tare da ta sani ba. "Say it again. Ban ji abinda kika ce ba, ears nawa suna bani problem." "Kai Ya Sadic. Ko wanda ke waje ya kamata ace ya ji me nace fa." "But ni banji ba. I told you I've problem with my hearing. Just say it again."2 Daf da kunnenshi ta matsar da bakinta, cikin natsuwa take magana, hakan yasa ya shagaltu sosai a kallonta, yadda take sarrafa tongue dinta, da yadda lips din ke motsawa yasa ya ji wani abu tun daga kanshi ya sauka har zuwa babban yatsanshi. "Ban taba tunanin ina sonka haka ba sai lokacin da naga da gaske baza ka dauki wayana ba, naga da gaske kayi fushi da ni, naga kuma ina shirin loosing my true love, my hero, my saviour, my, my, my.. My everything. The love I feel for you is far, far away from all the love stories in this world. I love you with every fibre of my being. I love you beyond words, beyond measures. I love you so very much, from the very bottom of my heart. I'll take care of you, and I'll give you all the love you deserve. Ina sonka Ya Sadic."6 She's lovable.3 Ya fad'a a k'asar zuciyarsa. A fili kam ya gagara sauke idonshi a kanta, ya shagaltu sosai wurin kallon labbanta da suke fitar da kalamai one after the other, a dai-dai lokacin aka tura k'ofar d'akin aka shigo, hakan ya sanya shi gyara zama tare da yin wani dan tari yana dafe kirjinshi.1 "Sannu Ya Sadic. Sannu ka ji." Ya daga mata kai yana yamutse fuska, Dr. Mukarram da Baffa da Goggo suka k'araso ciki suna ta faman yi mishi sannu. Kallonshi Dr yayi, tare da winking idonshi na dama, hakan yasa ya dan saki murmushi, yayi saurin kawar da idonshi yana dafe kirjinshi.3 "Tunda ka tashi abinda ya kamata ayi yanzu inaga muyi discharging dinka kawai, naga jikin da sauki." Da sauri ya kalle shi, yayi mishi magana da idanunshi, hakan yasa Dr yayi murmushi mai sauti, sannan ya juya yana kallon Baffa.2 "Na manta akwai 'yan gwaje-gwaje da ya kamata muyi, zamu canja mishi d'aki, mu bar shi a nan har zuwa lokacin da zai k'arasa warwarewa." "Haka ya kamata gaskiya." Daga nan ya koma ya kwanta tamkar bai taba magana ba, aka tura shi zuwa amenity, Jay sai tattalinshi ta ke, ta kasa zaune ta kasa tsaye, a times har mamakin kanta take, sai dai yadda take jin shi a cikin jikinta, bata tunanin zata kara bari yayi nesa da ita. Sai a lokacin ta kira Hajiya ta shaida mata abinda ke faruwa, ta kuma sanar da ita cewar jikin nashi da sauki, sosai da sosai. Ba'a fi minti arba'in ba ta iso asibitin, d'auke da manyan warmers na abinci, sai a lokacin suka tuna da batun abinci, domin a yadda hankalinsu ya tashi, kwata-kwata babu wana ya yi tunanin wani abinci. Yadda yaga mutane sun zagaye shi yasa ya k'ara narkewa a gado, duk da ba wani ciwon kirki ya ji ba, amman ya san idan yana haka dole Jay ta bashi attention dinta, domin a zahiri, babu karya a maganganun da tayi, a inda yake a kwance yanzu haka, zai iya hango yadda soyayyarshi ke yawo a cikin idanunta. Gabanshi ta karaso da plate mai d'auke da jallof spaghetti da ta ji wadatattun veggies, ta ajje a table din da ke gefen gadon, sannan ta tada mishi pillow, ya mike dakyar yana cije labbansa, ita kam sai faman sannu take mishi, sannan ta zauna a kujerar da ke girke gaban gadon, ta mika mishi plate din. "Ka daure ka ci Ya Sadic, kaga ga magani zaka sha yanzu." Juyar da kansa yayi, yana mata nuni da ido alamar ba zai iya ba. "Ka daure mana Sadic. Anyi rashin lafiya babu cin abinci." Hajiya tayi maganar tana dubanshi da tausayawa. "Daurewa zaka yi Sagir, ba dan dadi ba zaka ci dama." Goggo ta anshe itama, hakan yasa ya dan bata fuska, "Hannuna ne bana iya dagawa, ciwo yake sosai."6 A lokacin wayar Baffa tayi k'ara, ya dauka ya fita, haka Hajiya ta mike ta iso gabanshi, ta d'auki abincin zata fara bashi, amma Jay tayi saurin ansa, ta fara bashi, a hankali yake bude bakin yana ansa, a dabarance yana aika mata wani kallo da ke saukar mata da kasala a lokaci guda. Sosai ya ci abincin, kafin tasa tissue ta goge bakinshi, ta dauko ruwa da magani ta mika mishi. Bud'e bakin yayi, da nufin ta saka mishi, ta marairaice fuska, tana mishi alamar su Hajiya na gani fa. Noke kafada yayi, tare da dan turo baki, a hankali yace "Bakya tausayi na ko?"1 Bata ce komai ba, ta bashi maganin yasha, sannan ta gyara mishi pillow ya koma ya kwanta. Wayarshi da ke hannunta ta fara ringing, ta duba taga Farouq ne, sai da ta daga, sannan ta kara mishi a kunne. Da alama Jafar ne mai kiran, kasancewar yadda yake ansa wayar, a haka Baffa ya shigo tare da cewa "Dare yayi, ya kamata mu k'arasa gida." Sai da ya katse wayar suka yi bankwana da Baffa, tare da yi musu godiya, sannan ya yi gaba, Hajiya ma suka fita tare da Goggo, ya kasance d'akin daga shi sai ita. "Barin je Ya Sadic. Sai da safe." Ta mik'e daga kujerar da take zaune, ta gyara mayafinta sannan ta juya zata fita. "Tafiya zaki yi ki barni ko?" A hankali ta dakata, ta juyo tana kallon yadda ya kafe ta da idonshi, ta dawo da baya, ta tsaya gabanshi. "It's not my wish too. Ban ki ace na kwana ina kula da kai ba, but I've to go. Zan dawo early tomorrow morning in sha Allah." "Early. You promise?" "I promise." Murmushi yayi, yace "Kije su Baffa suna jiran ki. But please call me da kunje gida kinji?" "I'll in sha Allah. Allah ya baka lafiya." "I love you." Sai da taji wani sanyi ya sauka a zuciyarta, fuskarta d'auke da murmushi ta juya ta fara tafiya. "Jay.." "I love you too." Shine kawai ta fada, ta juya da sauri ta fita tana wani irin smiling, a lokaci guda tana jin wani irin sauyin yanayi a tattare da ita. Sallama suka yi ma Hajiya suka tafi, sannan ta koma ciki. ***Sadam.1 Da gaggawa nurses suka turo gadon dora mara lafiya zuwa kofar Emergency room din, kafin suyi komai, oxygen suka fara daura mishi domin samun daidaituwar numfashinsa, sannan suka dora shi, suka tura zuwa ciki. Duk da kasancewar Sa'id likita, amma a wannan gabar ya kasa yin komai, banda kaiwa-da-kawowa, babu abinda suke daga shi har sauran 'yan uwanshi saboda al'amarin na Sadam yayi matukar girgiza su, tare da haifar musu da tunani kala da kala a cikin kwakwalensu. Bayan kamar minti arba'in wani dogon Dr ya fito, kai tsaye ya tunkari inda suke tsaye, ganin hakan yasa Sa'id yayi saurin k'arasawa ya mik'a mishi hannu. "Barka da aiki Dr. Fa'iz. How's he?" "Alhamdulillah Dr. Sa'id." Ya juya suka fara takawa a tare zuwa office d'inshi. "Dr issue din Sadam babba ne gaskiya, wanda har bansan ta ya zan fara yi maka bayani." "Kamar ya kenan Dr? Please meye matsalar ne?" "Ka san komai Dr Sa'id. Amma me yasa kuka yi irin wannan saken har kuka barshi ya yi reaching this kind of situation?" "I don't understand what you're talking about Dr. What's going on?" Zama yayi, a karo guda ya cire labcoat din da ke saman kayanshi, sannan ya juya yana kallon Sa'id wanda shima ya sama ma kanshi mazauni a daya daga cikin kujerun da ke girke gaban teburinshi. "Kana nufin baka san Sadam yana shan giya ba?" A zahirance ba zai ce bai sani ba, haka kuma ba zai ce ya sani ba, sai dai idan ya tuna da kwalaben da ya gani dazu a dakinshi, to ba zaiyi tantamar yana sha din ba. "I can't say actually, but naga kwalaben giya a dakinshi yau din nan, which I think he had too much to drink, that's why ya samu kanshi a halin da yake ciki." "Sure, but this not the first time da ya fara, and you already know how excessive drinking of alcohol yake causing matsaloli kala daban-daban a lafiyar dan Adam, dama rayuwarsa baki d'aya."7 Gyara zamansa ya yi, kafin ya ci gaba "Bayan kasancewar giya cikin manyan kaba'irai da Allah Ya yi hani da su, mashaya giya suna tare da babban kalubale masu tarin yawa a tarihin rayuwarsu. A duk lokacin da mutum zai sha giya, abu na farko da zata fara yi, shine zata tafi direct zuwa bloodstream nashi, daga nan zata yi distributing ma gaba d'aya sauran sassa na jikinshi. Tana farawa da excretory system na mutum, inda take haifar da alcoholic hepatitis which can lead to the development of jaundice. Shine wanda zaka ga fatar mutum ya lalace yana wani yellow-yellow, haka ma idanunsa. Wannan zaiyi causing serious liver problem, wanda muke kira cirrhosis a likitance. Daga nan zata yi transferring to central nervous system na mutum shine zaka fara ganin canji a dabi'u da kuma halayyar mutum, idan tafiya tayi tafiya, giyar zata fara shiga cikin brain din mutum, ta haifar mishi da blackouts or memory loss, in sometimes, abun yana komawa mental problem. Excessive alcohol drinking, yana damaging salivary glands na mutum, ya hana shi jin dad'in komai, yayi causing mishi appetite loose. Daga nan zai fara haifar mishi da cututtuka irinsu: Gum diseases, Tooth decay, Stomach ulcer, Heartburn, & Dangerous internal bleeding. Giya tana taka muhimmiyar rawa wurin dakusar da digestion na dan Adam, ta wannan bangaren tana haifar da cututtuka irinsu Mouth cancer Throat cancer & Esophagus cancer (hanyar da abinci ke bi zuwa cikin dan Adam.) In the case of person's circulatory system, giya tana lalata zuciyar mutum, and it will lead to Heart attack High blood pressure Heart failure, & Stroke. Giya tana lalata immune system na mutum, ta inda zata hana su yak'ar cututtukan da ake kamuwa da su ta wannan hanyar irinsu Tuberculosis (TB) & Pneumonia." Ya saita dubansa a kan Sa'id "Dr. Wannan kad'an kenan daga cikin abubuwan da giya ke haifarwa a lafiyar dan Adam, kafin kuma mutum yaje ga Allah ya had'u da azabar da aka tanada ma mashaya giyar a nan duniya. Nasan kuma ka riga ka san wadan nan abubuwan, sai dai ina mamakin yadda baka dakatar da Sadam daga fadawa wannan mummunan hali ba." Shiru Sa'id yayi, tare da jinjina bayanan na Dr. Fa'iz, sai dai hankalinshi gaba daya ya fi karkata akan son sanin halin da dan uwan nasa ke ciki. Bakinshi ya cika da iska, ya furzar, ya dago a raunane yana duban Dr. "Now what's wrong with my brother?" A hankali a ajje pen din dake hannunshi, ya d'ago ya kalli Sa'id. "I'm so sorry to say, but he's suffering from one of the most life threatening diseases." "What's that?" Sa'id ya tambaya hankalinshi a tashe. "Cirrhosis, I mean liver inflammation (liver disease)"4 "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Wannan wane irin tashin hankali ne?" "Hak'uri za'a yi Dr. Ga wannan zaku je ku karasa sauran test a lab ku dawo da results din, then sai mu san wane magani ya kamata mu dora shi a kai." Bai iya cewa komai, yasa hannu ya ansa, ya mike dakyar ya fita inda 'yan uwanshi ke tsaye suna jiran fitowarshi. *** A hankali take juya steeringwheel din motar cikin gwanancewa da kwarewa, hankalinta a kwance da alama bata da sauran damuwa, illa lokaci zuwa lokaci da take tunanin mutumen da bata taba tsammanin zata so ba ko a mafarki. Mutumen da ya canja duk wani tsari nata, ya mantar da ita rayuwar bak'in cikin da ta riski kanta a baya. Alal hak'ika soyayyar SS tayi mata k'ulli mai dabaibaiyi, wanda bata san ta kamu da ita ba sai a daren jiya, kasancewar kalaman da ya rink'a shirya mata a cikin waya sun sa ta tsinci kanta cikin wata duniyar k'auna mai wuyar fassaruwa. Jin soyayyar tashi take har a cikin jinin jikinta, wanda a yanzu har mamakin kanta take, sai dai bai kamata ya zama abin mamaki ba, idan tayi duba ga yanayinta na mace mai son tsananin kulawa da tattali, haka kuma ya zo mata da wani SABON SALO na daban, domin a zahiri na shi salon ya sha banban da irin salon soyayyar Kazaure. Nashi salon soyayyar, wani irin salo ne mai tsayawa masoyi a k'ahon zuciya, ya mantar da shi komai, face soyayyar masoyin da zuciyar ke so da gani. Murmushin da ke fuskarta ta fadada, a lokacin da ta kawo 2nd gate na shiga FMC. Bayan securities sun gama bincika boot dinta, ta murza motar ta wuce ciki, direct amenity din da yake ta isa, tayi parking a waje, sannan ta fito da basket din lafiyayyen breakfast din data shirya mai, ta dauka tare da rufe motar ta juya domin k'arasawa ciki. Kwance yake ya zuba ma k'ofar shigowa ido, da alama akwai abinda yake jira, hannunsa na dama rik'e da wayar da ke saman kunnensa yana ansawa, Hajiya na zaune k'asan dan k'aramin carpet din da ke shimfid'e tsakiyar d'akin, Jay ta turo k'ofar bakinta k'unshe da sallama ta shigo. Tsab, ya sauke idanunsa a kanta, a lokaci guda ya ja wata sassanyar ajiyar zuciya, tare da narkar da idanunsa, tamkar mai shirin yin kuka, yana kallonta. "I'm sorry." Tayi mishi alama da idanunta, sai dai bai ce komai ba, ya kashe wayar, ya juya musu baya, duk kuwa da yadda ya kwadaitu da son k'ara kallon fuskarta wadda yake ta zaman jiran gani tun bayan tafiyarta. Murmushi tayi, ta k'araso inda Hajiya ke zaune ta duka suka gaisa, sannan tayi mata ya mai jiki. "Alhamdulillah Ummi. Ya su Hajiya?" "Suna gaishe ku. Sai anjima zata zo, Baffa ne zai tafi Lagos yanzu, shi yasa ma bamu taho tare ba." "Babu komai ai, da ta zauna ta dan huta ma. Allah ya kaishi lafiya." Juyowa yayi yana kallon yadda ta zauna a gefen Hajiya bata da niyyar isa inda yake, ya manta da fushin da ya ke yi ma, domin kuwa ya shagaltu sosai wurin kallonta, yana ganin yadda ta sake suna maganarsu da Hajiya cikin natsuwa da wata irin kamalar da ta k'ara mata kyau da kwarjini.1 "Patient." Muryarta ta dawo da shi daga tunanin da ya fad'a, ashe har ta taso ta iso gabanshi ba tare da ya ankara ba. "Yawwa, to sai na dawo Ummi." "Sai kin dawo Hajiya." Ta juya ta fita, shi kuma ya k'ara juya mata baya ba tare da yace k'ala ba. "Ya Sadic ya jiki?" "Ba ki so ki sani ba ai tunda kike zuwa yanzu." "I'm sorry Ya Sadic. Wallahi breakfast dinka ne ya tsayar da ni, kuma ma ai na zo da wuri ko." "Ki duba agogonki zaki gane." "10:30 fa Ya Sadic. Kaga ko ai na zo da wuri." "Amma ya muka yi da ke jiya?" Ya juyo da shiny idanunsa yana kallonta. Kwantar da murya tayi, a karo guda ta dan langabar da kai. "I'm sorry I said. Nasan nayi laifi ai. Now daure ka ansa ni ya jikinka?" Murmushi ya saki, wanda ya k'ara ma doguwar fuskarshi annuri, sannan ya fara k'ok'arin mik'ewa, amma ya kasa, hakan yasa ya saki dan k'ara kadan "Arrrgh!" Ya koma ya kwanta yana kallonta. "This is your answer." Yayi maganar yana nuni mata jikinshi da ido. "I'm sorry ka ji. Sannu, lemme help you ka mik'e zaune, na san ko abinci baka ci ba." Bai ce komai ba, ya tsaya yana k'ura mata ido, yayin da ita kam ba tare da damuwa ba ta zame pillow daya dake k'asan wanda kanshi yake, ta jingine da gadon, sannan ta d'ago wanda yake kai, ta k'ara jinginewa. Hannu ta mik'a zata kama kafadarshi, taji wani irin yarrr, ya shiga ta hannun, ya bi duk wani jini da ke aiki a jikinta, a k'arshe ya isa har zuwa k'wak'walwarta. Da sauri ta sake kafadar, ta matsa tana dan matsa hannun, ta kasa cewa komai, haka kuma ta gagara sauke idonta a kanshi. Hakan ne ya faru da SS, shima kuma kasa maganar yayi, a lokaci guda ya saki ido yana kallonta. Dak'yar ya iya dai-daita tunaninsa, yayi gyaran murya kadan yana tambayar "Any problem?" "Errrnmm.. ka tashi ka zauna." Ta fara gyara murya tana in'ina. "Alright." Ya fada yana gyara zamansa. "Sannu Ya Sadic. Are you okay?" "I'm fine." "Sannu to, barin sa maka abinci. Nasan ko magani baka sha ba ko?." Murmushi yayi, sannan ya girgiza kanshi a karo guda yana lank'wasa yan yatsunshi yace "Wa yace miki ban sha ba?" "Zuciyata." Bakinta ya furta kai tsaye, domin bata san lokacin da maganar ta fito ba. "But why? I mean why zuciyanki?" Shiru tayi, ta cigaba da hada tea a mug din da ke hannunta, ta gama tass, ta dago da plate din da ta sa mishi abincin, ta iso gabanshi ta dora saman table sannan ta juya tana nuni mishi da gefen da zuciyarta take. "Tambaye ta, zata baka ansa." Shiru yayi yana kallonta, nisan da ke tsakanin su ba wani mai yawa ba ne, daga inda ya ke yana jin saukar numfashinta da ke fita da wani irin k'anshin da ya dauke shi, ya kaishi wata duniya ta daban, hakan ya sanya shi lumshe ido, ya bude a hankali. Har yanzu tana tsaye yadda take, tana kallonshi. "Ehhnn now."1 Tayi mishi alama da idanunta. Murmushi kawai ya iya yi, domin baza ta gane yadda yake jin ta a cikin tashi zuciyar ba. "I'm hungry." "Oops. I'm sorry." Da sauri ta juya ta dauko mug din ta mik'a mishi, amma ya k'i ansa, ya tsaya kawai yana dan tura baki kadan. "Amma kinsan bana da lafiyan hannu ai. Ina zan iya rik'e k'aton mug din nan."5 "Ka warke fa ya Sadic. Kuma ba wani nauyi ne da shi ba ma. Try it please." Ta fad'a idanunta a kanshi, itama tana dan tura bakinta gaba. "I can't. And idan kinsan zaki bani wahala me sa kika bar Hajiya ta fita?" "But Ya Sadic..." "But what Angela? I can't, bazan iya rikewa ba. Can't you see that imma patient here?"4 Yayi saurin katse ta da maganarshi, wacce yasa ta sake baki tana yi mishi kyakkyawan duban yadda yake abu kamar wani Jafar. "Naji. Ka sha tea din ni sai in baka abincin." "If that's the case, then na hak'ura da both. I told you hannuna ba zai iya dauka ba." "Amma Ya Sadic sai ka daure fa, a haka zai warke ai. Issokay zan baka yanzu, but na gobe da kanka zaka sha. Promise me?" Wani lallausan murmushi yayi, ya mik'a mata dan autan yatsanshi yana fad'in "I promise you Angela." Noke nata yatsan tayi cikin mug din da ke hannunta, tai mishi nuni da ido, tace "I trust you." "Ki kawo mana inyi proving miki." "Never mind patient. Now have your breakfast. Aaahh." Ta k'arasa tana bude bakinta kadan, lokacin da ta matsar da tea din zuwa bakinshi. Bud'e bakin yayi tana bashi a sannu-sannu, ya dan ci ba laifi suna fira kadan-kadan, cikin dan lokaci sun saba da rayuwar soyayyarsu, mai cike da shauki, kauna, kulawa, tattali, da kuma aminta da juna. **Sadam. A hankalinshi, ya fara bud'e idanunsa yana kallon mutanen da ke wurin one after the other, a sannu ya sauke idonshi kan Saheeb dake zaune a gefe yana latsa wayar da ke hannunsa. Hannu ya mik'a yana shirin taba shi, hakan yasa ya taso da sauri ya iso gabanshi. "Sannu Yaya. Ya jikin naka?" Kai ya daga, a hankali ya furta "Da sauki Saheeb. Ina Yaya Sa'id?" "Barin sa a kira shi, yace idan ka farka ayi mishi magana dama." "Ok, bani ruwa in sha. K'ishi nike ji." Ya bude locker dake gefen gadon ya fito da gorar ruwa ya bashi, ya dan sha kadan, cikin 'yan mintina ya fara wani irin tari, hakan yasa Saheeb yace da wata nurse ta taimaka ta kira musu Dr. Fa'iz ko Dr. Sa'id. Ya dawo inda Sadam ke kwance yana mishi sannu, har a yanzu bai daina tarin ba, cikin galabaituwa ya fara k'ok'arin amayar da ruwan da ya sha, tsab ya amayar da shi, yayin da wani ruwan mai kalar jaja-jaja ya biyo baya. Tissue ya ciro ya mik'a mishi, ya ansa ya fara shafe bakinshi, wani tarin ya k'ara taso mishi, yasa tissue ya toshe bakin, dagowar da zaiyi, jini ya ganj kwance jikin tissue din da ya toshe bakin da ita. Da sauri Sa'id tare da Dr. Fa'iz suka iso, wani nurse namiji na biye da su, hannunshi rik'e da file din Sadam. "Sannu Sadam. Ina ke maka ciwo yanzu?" Bai ce komai ba ya mik'a ma Sa'id tissue din da jinin ke jiki, hakan ya k'ara karyar da gwiwarshi, ya ansa ya juya yana kallon Dr. Fa'iz.1 "Menene abin yi Dr? Kaga aman jini yake yi. Please save my brother, please Dr. Fa'iz. Do something dan Allah." "It's okay Dr. Sa'id. Wannan yana daya daga cikin matsalolin da cuta irin tashi ta kan haifar, but in sha Allah zai samu sauki. Wannan ba wani abu bane ba." Ya gama duba file din da nurse ya bashi, ya cire paper ya rubuta magani ya mik'a ma Sa'id. "A tabbatar da an samo shi yanzu-yanzu, a bashi abinci kafin ya sha maganin. I'm sorry Dr." Ya k'arasa yana dafa kafadarshi, sannan ya juya domin komawa bakin aikinshi. Jiki babu k'wari Sa'id ya juya ya isa bakin gadon ya zauna tare da mik'a ma Saheeb papern maganin da kudi, ya tsura ido yana kallon yadda Sadam ya fita hayyacinshi a yini daya da kwana d'ayan da yayi yana cikin ciwo, hakan ya k'ara tabbatar mishi ba k'aramin azabtuwa dan uwan nashi ke yi ba, ya kuma k'ara gaskata maganar Dr. Fa'iz da yace cirrhosis is the most life threatening disease. Hannunshi ya rik'e, yana shafawa a hankali, haka ya d'ago manyan idonsa da suka gama kodewa yana dubanshi, labbanshi da suka bubbushe yake motsawa alamar yana son yin magana, hakan yasa Sa'id ya tayar da shi ya jingine da bango, ya koma ya zauna yana dubanshi cike da tausayawa, ba don k'arfin zuciya irin ta namiji ba, da babu abinda zai hana shi kuka har ma da hawaye.1 "Kaga halin da ka jefa kanka ko Sadam?" Murmushi yayi mai tsananin zafi, wanda iyakacinsa fatar baki. "Na gani Yaya, but ba laifina bane ba. Ina sonta ne, so kuwa mai tsanani, wanda shi ne ya kaini ga komawa tsohuwar dabi'ata, wacce a da na riga da nayi bankwana da ita."2 "Dan Allah zan rok'e ka Sadam, ba dan ni ba, ka cire yarinyar nan a zuciyarka. Sadam ka gama illata rayuwarka, ka bata lafiyarka, ka wulak'anta gatanka na dan Adam da Allah ya yi maka. Ka kasance cikin mutanen da basu san ciwo ko mutuncin kansu ba, yanzu ka duba kaga halin da munanan dabi'unka suka jefa ka, nasan kuma ka sani dama irin wannan ranar tana nan zuwa gare ka. Ni dan uwanka ne, dole nike fada maka gaskiya, domin a duniya babu wani wanda zai fada maka baya na. Sadam ka kasance cikin mutanen da suka mayar da caca sana'arsu, suka mayar da giya tamkar abincin cinsu, wanda sanin kanka duk wanda ya samu kanshi a wannan halin yana tare manya-manyan alkaba'irai wanda idan har bai tuba ba to zasu iya yin sanadiyyar kai shi wuta. To gashi yanzu tun ba'a je ko ina ba, ka fara girbe abinda ka shuka, a lokaci guda kuma ka fada tarkon k'aunar matar da ka gama wulak'antawa, ka dauki takalmin da kake takawa ya fita daraja nesa ba kusa ba. Ka daukaka sabon Allah fiye da sunnar ma'aiki. Ta ya zaka ga dai dai a rayuwarka Sadam? Ta ya Jameela zata tsaya ta kuma saurararka? Wanda dama kasan mutuwar aure na daya daga manya-manyan abubuwan da caca ta kan haifar. Ban san me zan iya yi maka a wannan gabar ba, illa iyaka zan roka maka Allah ya yaye maka cutar da ke damunka." Hawaye ne suke fita ta gefen idonshi, ya san shi mai laifi ne, irin laifin da bai cancanci yafiya ba, haka kuma a ciwon da yake tattare da shi, ya san rayuwarshi a doron k'asa k'alilan ce, dan haka matuk'ar yana k'aunar Jay kamar yadda yake fada, yake kuma jinta a cikin zuciyarshi, to ba zai so ya k'ara hurting feelings dinta zuwa gaba ba, ba zai dawo da ita gare shi ba, a k'arshe ya mutu ya barta da tabo a cikin zuciya, domin ya san baza ta taba gafarta mishi ba, matuk'ar yayi wannan zalincin gare ta a karo na biyu. A hankali ya juyo yana kallon Sa'id. "Babu abu guda daya da kayi karya a halayyata, amma ka sani ba laifina bane ba. Hakan kuma k'addarata kenan, ba kuma zan taba gushe mata ba. Bazan iya daina son Jay ba Yaya, domin kuwa da shi aka halicci zukatanmu nida ita, kamar yadda nasan itama baza ta taba daina sona ba, sai dai bacin rai yasa ta mik'a soyayyar da take mun ga wani. Ina so ka sani Yaya, ko bayan bana rayuwa a doron k'asa, Jay ita ce mace ta farko da na taba so a gaba daya rayuwata, ita ce kuma mace ta k'arshe da zan so a wannan yar k'alilan din duniyar tawa da tayi saura. A yanzu idan nace ina son ta dawo gare ni, alal hak'ik'a na zama cikin masu son zuciya, domin bani da komai, bani da kowa sai Allah sai ku, babban tashin hankalin bani da lafiyar da zan bata farin cikin da na hane ta a lokacin baya. Amma ina so kayi mun wata alfarma guda, ka dauke ni ka kaini gare ta, domin ina so ko da mutuwa zata riske ni, to ta same ni a lokacin da nike tare da ita. Ina son inga smiling face din 'yar da na haifa, wanda tunda ta zo duniya ban taba gani ba, I want to hold her tight in my arms, to whisper I love you in her ears. Ina so ta daina jin tsorona, ta yadda ko bayan rayuwata zata iya tunawa da ni ta yi mun addu'a. Ka taimaka ka cika mun wannan burin nawa Yaya Sa'id, idan kai mun wannan ka gama mun komai a matsayinka na dan uwana, abin alfaharina."5 Kukan da Sa'id ke mak'alewa dole sai da suka sauko a wannan lokacin, k'auna da wani irin tausayin Sadam suka yi mishi kyakkyawan bugu a gefen k'irjinshi na hagu, yana jin inama wani zai iya d'auke ciwon da wani ke ji, da ko babu dalilin da zai hane shi fansar Sadam daga halin da yake ciki. Hannunshi da ke cikin nashi ya k'ara k'ank'amewa, hawaye na zuba a both idanuwansu yace, "Kayi hak'uri ka daina irin wannan maganar Sadam, shi ciwo ai ba mutuwa bane ba, mutum million nawa ne suka rayu daga cutar cirrhosis, Allah kadai ya san adadin su, shine mai warkarwa, shi kuma zai warkar da kai da izininshi. Zaka tashi a kan k'afafunka, har ma ka cika ma kanka burin da kayi alwashi a cikin zuciyarka." "Na yarda Allah ne kadai mai iko a kan komai, rayuwa da mutuwa duk a hannunshi suke, baka da masaniyyar ranar da zaka mutu, haka nima, dan haka na rok'e ka da girman Allah ka sada ni da Jay da Rukayya, ina so in musu kallon k'arshe, ina son in rabu da su muna farin ciki muna jin dad'in ganin juna. Ina so idan mutuwa zata zo ta same ni tare da iyalina, nasan jama'a da yawa zasuyi mun addu'a, za kuma su yarda cewa Kazauren da, da na yanzu suna da banbanci a halaye da dabi'u." Hawayenshi ya shafe, ya kalle shi da murmushi a fuskarshi, wanda da gani iyakacinsu labbanshi. "In sha Allah zan cika maka burinka Sadam, sai dai kafin nan da k'afafuwanka zaka taka muje har gabanta. Da yardar Allah." Murmushi yayi a karo guda ya girgiza kanshi, Allah kadai ya san irin azabar da yake ji a cikin jikinshi, haka kuma akwai changes da dama da yake ji dangane da shi, irin wanda tunda ya zo duniya, bai taba experiencing irinsu ba.1 ***Bayan Kwana biyu*** "A'ah, kaga lover patient ya warware kamar ba shi ba. Kai ba dan ba dan ba ai da sai kayi ta zama a nan, na tabbata da zaka fi jin dad'i fiye da ko ina." Dr. Mukarram da ya gama auna B.P din SS ya fad'a, yana dariya sosai. Shima dariyar yayi, ya gyara hannun rigarsa da Dr yayi folding, ya kalle shi. "Ba haka bane fa Dr, kawai dai kawai dai." "Kawai ni na gane ai. Ba sai kayi bayani ba ai." Dariya suka kuma sakawa, a lokacin Jay ta turo k'ofar ta shigo da sallama, da sauri ta isa gefen SS ta tsaya, yana ganin haka ya langabar da kanshi, ta juya tana kallon Dr. "Is he okay?" "Very. Soyayya kawai ce matsalarshi yanzu." Murmushi tayi ta dan sinne kai cikin gyalenta, sai yanzu take jin kunyar yanayin da ta shigo. "Komai yayi dai-dai, magani ne zaka daure ka cigaba da sha, a hankali zaka samu dawowar k'arfin jikinka. Allah ya k'ara sauk'i, sai mun zo daurin aure." Ya mik'a mishi hannu, suka gaisa, a lokaci guda yana shafa sumarshi da d'ayan hannun "Ai kune kan gaba Dr. Thank you." "Ai fa, to ni dai sake mun hannu in wuce patients na can suna jira na." Suna dariya yayi musu sallama ya fita, ya juya yana kallon Jay, a hankali ya koma da baya ya kwanta tare da rungume hannayenshi. "Lover patient wake up. Kwanciyar me zaka yi kuma bayan Dr yayi discharging dinka. Get up now." "Lover patient? Ina kika samo sunan nan?" "Bakin Dr. Mukarram. And you deserve it. Now, tashi muje tun bamu ba Hajiya wahalan dawowa ba." Shiru yayi yana kallonta, amma a zahiri ba ita din yake kallo ba, yana jin yadda soyayyarta ke bombing gabobin jikinshi ne, tana haifar mishi da kasala, da tsananta bugun zuciya.2 "Zauna ki ji. Let's talk please." "But SS, we need to go. Idan munje gida sai muyi maganar ko Mr lover patient." "Angela."1 Ya kira ta da wata irin silent voice, mai tsananin taushi da dad'in saurare, ta juyo a natse ta zuba mishi idanunta, nan ta gane da gaske akwai maganar da yake son yi da ita. "Come and sit here with me." Muryarshi ta katse mata tunanin, a lokaci guda ta dakata daga hada drugs dinshi da ke zube saman table, ta juya ta koma kusa da shi ta zauna tana kallonshi. "How much do you love me?" Ya tambaya yana kafe ta da idanunsan da ke sanya ta rasa natsuwarta, a lokaci guda ya mik'e zaune yana jiran ansarta. "I love you a lot." "I'm just afraid of something Angela." "What? You don't have to Ya Sadic. I love you so so very much, and nothing can change that." "Na ji fa, ba wai ban yadda ba, but ki describing mun yadda zan fahimta, in kuma yardar ma kaina ke tawa ce har abada." Idanunta ta juyar, tana wasa da yatsun hannunta, a Sannu ta dago tana kallonshi. To be honest tana tsananin tausayin halin da taga zai shiga a baya, wanda hakan ne yasa ta fara jin wani abu dangane da shi, wanda bata san tana tare da shi ba, a yanzu tana jin shi tamkar dan uwanta na jini, ta wani bangaren kuma tana jinshi sosai a kusa da zuciyarta domin a 'yan kwanakin da suka yi spending tare ya saye zuciyarta da natsatstsiyar soyayyarshi mai hana ta bacci a kowanne dare saboda tana son gari ya waye, ta dawo gare shi ta kalli fuskarshi ko dan ta samu kwanciyar hankalinta. "Idan nace zan bayyana yadda nake sonka, to zamu kwana a nan, har mu kara kwana. Cuz ban sani ba Ya Sadic, all I know is ina jin zuciyata na bugawa da sonka, a times bana iya bacci cuz I'm thinking of you, a times abinci na gagarata cuz I wanna spend the time I'll waste eating food with you. Ina jin kamar I'm the most luckiest woman on earth, saboda yadda kake so na. Haka kuma ina samun kaina cikin yanayi na nishadi a duk lokacin da nike tare da kai, ko nike tunaninka. I just love you."4 Idanunshi a lumshe yana jin duk ko wace maganarta tana shiga kunnensa, sannan ta wuce ta samu mazauni a cikin zuciyarsa. Yana yi mata wani irin sark'ak'k'en so, wanda duk wanda ya kalle shi zai fahimci hakan, yana jin ta sosai a cikin jikinshi. Baya son abinda zai zo ya shiga tsakanin soyayyar da suka fara shimfidawa, sai dai a matsayinshi na masoyinta yana jin tamkar baiyi mata adalcin raba ta da mutumen da ta wayi gari da soyayyarshi ba, yana jin kamar da rashin uwa ne yasa akanyi uwar daki. Ta wannan bangaren ya kasa samun natsuwar zuciyarsa, dan yana ganin soyayyarshi kamar iyakacinta bakinta, kuma kamar tana yin hakan ne dan kawai ta kwantar mishi da hankali. Bud'e idonunsa yayi, ya ci karo da nata idanun a kanshi, kallonshi take fuskarta ta gama bayyana sirrin zuciyarta. Mamakin yadda take kokarin yakice soyayyar Kazaure take yi, wanda wannan wani sirri ne nata na daban, Sai dai ta tabbata har ga Allah baza ta taba son SS kwatankwacin yadda ta so Sadam Kazaure ba. Amma tayi alkawarin baza ta taba bari har ya fahimci hakan ba. "Tell me, who do you love most tsakanin ni da Kazaure????"7 Muryar SS ta dawo da ita daga kogin tunanin da ta fada, ta dago a razane ta sauke idanunta cikin nashi. Ta dade tana kallonshi, ta kuma rasa abun cewa. A zahiri, ansar guda daya ce tal, sai dai idan ta bayyana ta gare shi, tamkar ta rama sharri ma alkairi ne. A matsayinshi na wanda ya taimaki rayuwarta a lokuta da dama.+ Murmushi ya saki, a lokaci guda yasa hannu ya d'ago habarta ya saita fuskarshi cikin nata,2 "It's hard to answer this ko?" Bai jira mai zata ce ba, ya dan lashe labbansa, "Never mind Angela. Tashi mu wuce gida." Kafin ta bude baki tayi magana wayarta dake cikin jaka ya fara ruri, ta mike ta fito da shi, ta daga a hankali ta dora a kunnenta. "Sai yau kike kira na Miemie?" "I'm sorry dear. Kina gida ko? Cuz ina hanya zanzo, abubuwa sun sha kaina, ga labarai kala da kala tun ranan can ban k'ara ganin ki ba."1 "Yayi kyau parrotee. Ina FMC ni kam, but yanzu zan fito. Idan kin riga kin fito ne ki iso ta nan sai mu wuce." "Ok, barin zo ta nan din please." "Sai kin zo." Ta kashe wayar ta juya tana kallon SS da kanshi ke k'asa. Bata ce komai ba ta cigaba da parking kayansu da ke wurin, ta fitar ta saka a mota sannan ta dawo d'akin. Har yanzu yana zaune yadda ta barshi. Ta k'araso gefenshi ta zauna tana matsa hannayenta, ba ta iya cewa komai ba, idanunta a k'asa. A hankali ya juya yana karantar yanayinta. Murmushin karfin hali yayi, tare da muskutawa kadan yana fuskantarta. "Me muke jira?" "Nothing fa. Kai nike jira." "Nima ke nike jira ai." Murmushi tayi ta mik'e, ta fara tafiya zuwa bakin k'ofa, a dai dai nan wayar Miemie ta shigo mata. Dagawa tayi ta fara yi mata kwatancen inda suke, hakan yasa SS ya ziro kafafunsa ya sauko a gadon ya fara takawa, bai ce mata komai ba, ya wuce ya fita. Tana gama wayar itama ta bi bayanshi da sauri, tana kallon yadda yake tafiya da karfinshi, ta risko shi tana cewa "Ka warware Ya Sadic. Kaga yadda kake wani bouncing." "Ina wani bouncing a wurin patient? Ki ba'ance ni son ranki Hajiya." "Ba wani ba'a fa. Wallahi ka kara kyau, ka kara fresh, kaman ba patient ba." "Tunda ina ganinki me zai hane ni inyi fresh? Na love." Dariya tayi, a lokacin suka iso bakin motar, a nan suka samu Miemie na k'ok'arin parking itama. Da sauri Jay ta isa inda take, SS ya bude motar ya zauna a gefe, kafarshi daya a ciki, daya a waje yana kallonsu. "Long time babe." "Ki share kawai. Things sun hana ni sakat. Ya wancen bobon fa, ina kika samo shi?"1 "Ya salamu. Da wace irin kawa ne Allah ya hada ni? Miemie kin shiga ukku wallahi. Ina mutunminki?"2 Dariya sosai Miemie ke yi, sannan ta fito tana dan satar kallon SS. "Naga fine bobo ta ya ba zan tambaye ki ba. Ke maganar da nazo da ita kenan. Gayen nan wawa ne wallahi, wai ina kika san shi ma?"10 "Faisal ne wawan Miemie? Amma sai naga kamar kin falling mishi. Me yayi ne?" "First class wawa ma kuwa. Ai ni kin bar ni da mamakin inda kika san shi ma. Well, mu karasa gida dai kisha labari. But kafin nan, da Allah who's that guy?" "Mtsewww. Allah dai ya shirya ki. He's my cousin to. Shige muje ki bi mu a baya." Dariya tayi, ta koma ta shiga motar, itama ta juya ta isa inda tasu motar take, ganin haka ya sanya shi shigo da dayar k'afarsa ciki, ya rufe, ya juya yana kallon yadda take kiciniyar daura seatbelt. Hannunsa yasa ya zaro belt din, sannan ya zagayo da shi ta setin waist dinta, bai ce da ita komai ba, ya fara kokarin daura mata. Shiru tayi, tana jin saukar numfashinsa har a saman fuskarta, a karo guda kanshin turaren Mediterranean dinssa ya cika mata hanci, hakan yasa ta lumshe ido tana shakar daddadan kanshin da ya fara saukar mata da wata irin kasala. Idanunsa ya dago yana kallon yadda ta lumshe nata idanun, ta kara wani irin kyau, yadda ta dage fuskarta, sai abun ya k'awata dogon hancinta, eye lashes dinta sun mike tsaye san6al, yayin da wet glossy lips dinta ke wani irin shining mai matukar birgewa. Bugun zuciyarsa ya rink'a jin yana karuwa, a hankali ta bude idonta, tsaf idanunta suka sauke cikin nashi. Babu wanda ya iya iya cewa komai tsakaninsu, murmushi ta jefa masa na karfin hali, kafin ta ta tada motar, suka fara tafiya Miemie na biye da su, har suka iso Barhim. Hajiya na shirin fitowa, suka yi sallama a cikin falon, suka shigo. "Wai ba dai har anyi sallama ba? Ina ta sauri nace k'ila kuna ta jin yunwa na barku ku kadai." Murmushin karfin hali Jay ta yi "Wallahi har mun taho Hajiya. Tun dazu ma aka yi discharging dinmu, mun dan bata lokaci wurin hada kayan nan ne." Ta ajje kayan a gefe, ta zauna a gefen Miemie wacce tuni ta sama ma kanta mazauni. "Sannunku." "Yawwa. Ina wuni." Miemie ta gaishe da ita, ta juya tana satar kallon SS.5 "Lafiya lau yan mata. Barin sa a kawo maku abincin to." "A'a wallahi, wucewa ma zamu yi. Ina da bakuwa ne."4 "Ba za dai ku ci abincin ba ne Ummi. Amma ba komai. A gaishe da mutan gidan." "Zasu ji in sha Allah." Hajiya ta k'arasa shigewa kitchen, suka mik'e a tare ta juya tana kallonshi. "Ya Sadic ga k'awata Miemie da nike ta baka labari." Juyawa yayi da murmushi yana kallonta. "Barrister ya kike?" "I'm fine. Ya jiki?" Ta fad'a jiki ba k'wari, a karo guda ta ji kunyar kallon da ta tsare shi da. "Jiki Alhamdulillah."10 "Allah ya k'ara sauki." Ta juya ta fara tafiya. Mikewa yayi, ya matso inda Jay ke tsaye, har yanzu ya gagara daina kallonta. "Ka zauna Ya Sadic. Kaga har yanzu baka k'arasa warkewa ba. Zan kira ka anjima, and zan dawo gobe idan Allah ya kaimu." "Who told you ban warke ba? As long as ina kallonki, to ji nike tamkar babu abinda ya faru da ni. But tunda ke kike son na zauna fine. I just wanna say thank you for everything. And idan baki zo early morning ba, to wallahi zaki ganni a gidan ku." Dariya tayi, a karo guda ta dan zara ido. "No please, zan ma zo in sha Allah. And thanks for what? Ka bari mana. Me wani abun godiya" "Since you insists. Do take care of yourself for me." Murmushi tayi tana kallon shi. "I'll. Ka tabbatar ka sha drugs dinka fa. Allah ya k'ara sauki." Ta juya da shirin wucewa. "Jay" A hankali ta juyo, tana cin karo da idanunsa cikin nata, 'why is he acting strange?' Ta tambayi kanta. A fili kam dan murmushin da iyakarsa labbanta tayi, tana nuni mishi yadda ya tsaya daf da ita. "Oops." Ya fada lokacin da yake matsawa. "I'm sorry." "Never mind." Ta fad'a a fili. "Tell me you love me." Ya kafe ta da ido yana saurarenta. "Of course I do. And you know that." Murmushin karfin hali yayi, ya koma ya zauna. "Alright then. Sai na ji ki." "Okay." Ta juya ta fara tafiya, har sai da ta bace ma ganinsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Ya rasa wane irin so ya ke mata, wanda ke hana shi controlling yanayin da yake samun kansa a duk lokacin da yake tare da ita.8 *** "Jay bazan iya da halin namiji irin Faisal ba. Ya cika son mata wallahi. A ranar da kika bar gida mun dan fara sabawa da shi haka, k'arshe ma a garin nan ya kwana, the next day ya zo muka fita zan gwada mishi gari, could you imagine gayen nan daga mun je Jifatu store na matsa ina neman wani perf ta other wing din da yake, ina zagayowa na ganshi da wata chikala suna exchanging number. Wai dan raini irin na shi he was telling me ai she's a friend he knew. Daga nan na basar da wannan, after ya bar garin nan, sai da ya kwana ukku bai kira ni ba, and next kiran da na mishi naji wata wawiya ta dauka, tun daga nan na fita da shi, na tsane shi. Sai bayan nan yake isata da kira, wai ni zai raina ma hankali, bai san ni uwar dakinshi ce ba."9 Wata muguwar dariya Jay ke yi hadda fad'i k'asa. Miemie kam kallonta kawai take ta gama kulewa, a lokaci guda ta kai mata duka a baya. "Ke wallahi nonsense ce. What's funny? Kin hada ni da gaja kina wani dariya. Wawan ga shi dai namiji har namiji, amma ba hali."1 "Haba mana. Jikan Malam ne fa, da Allah ki bar zaginshi, wallahi familynshi suna da kirki." "To albasa bata yi halin ruwa ba a nan." "I'm sorry sweetheart. Wallahi ni ban san haka yake ba, na dai san shi kawai, amma bansan halayenshi ba. Haka Allah ya so, kila dama ba mijinki ba ne ba." "Ai ni gara ma da ban fara son shegen ba. Dama ina ni ina auren bak'in mutumen nan? Ke sai yanzu nike jin ba zan ma iya zuwa Maid zaman aure ba."3 "But maid is a nice town fa. Ga mutanen garin da kirki." "Kya ji da shi Jameela. Now tell me about that your cousin. That fine boo bae."9 Wata sabuwar dariyar Jay ta saki, "Nan kuma kika dawo? To kwalelenki. That one na my property." "Ban gane ba?" "Zaki gane zuwa gaba." Ta mik'e tana dariya, ta wuce kitchen ta kawo mata abubuwan motsa baki.3 ***A week later***1 "I hope everything is ready?"+ "Good job. I'll be there in a bit. Thank you." Ya saki lallausan murmushi, tare da ajje wayar, ya matsa gaban mirror yana k'ara gyara sajensa, ya wanke jikinshi da turare, sannan ya d'auki key din sabuwar BMW f30 dinshi, ya fice, a zuciyarsa yana jin wani sabon nishadi na yawo a duk illahirin jikinsa. Titi ya mik'a, yana tafiya cikin natsuwa, hankalinsa, da zuciyarsa, gaba d'aya sun tafi ga son kallon fuskarta, wacce yau kwana ukku kenan rabon da ya dora ta a idanunshi. Cikin 'yan mintina ya iso gidan, bai shiga ba illa waya da ya cire ya fara kiranta, ta daga da muryarta mai laushi tana fad'in "Hello." "Hi." Ya fad'a a sanyaye, dan yadda tayi maganar ta gama saukar da wata kasala a gabobin jikinshi. "Ka iso ne?" "Ina waje. I'm waiting for the Queen." Murmushi mai sauti tayi, tare da juya manyan idanunta tamkar yana ganinta. "Will be right there." Ta kashe wayar, tana k'ara kallon yadda ta hade cikin black and gold din English gown dinta mai tuttle neck tare da dogon hannu wanda ya matse a k'arshe. Dankunne, agogonta da bracelet dinta duka gold in color, yayin da ta sha turban head wrap da black scalp, tayi light make-up a fuskarta. A tsaye ta hange shi in black shima, illa silver agogon da ya daura a hannunsa, yana tsaye bakin motar ya zuba mata idanu yana kallon yadda take taku cikin natsuwa, ta k'araso a hankali ta tsaya a gefenshi. "Barka da zuwa Ya Sadic. Ya karfin jiki?" Ajiyar zuciya ya sauke, cikin karfin hali ya furta "Kinyi kyau Angela." Murmushi kawai tayi, tana juyar da kanta. Dukawa yayi gaban motar ya bud'e dashboard ya fito da white necktie, ya d'ago yana kallonta. "Juya ki ga wani abu." "Me ne?" "Ki juya mana. Trust me." Bata kara cewa komai ba, tayi yadda ya buk'ata, ya warware necktie din ya zagayo da shi ta fuskarta, ya daure idanunta.3 "Please Ya Sadic. What's this?" "Let's go." Ya fada, yana zagayawa ta other side din motar, ya bud'e mata ta shiga. "Please don't open your eyes Angela." "Ok. But where are we heading to?" "Just keep quite please. Yanzu zamu je ba wani nisa ne da wurin ba." A lokacin ya tada motar suka doshi titin da zai sada su da Chinese restaurant. Duk yadda taso ta bude idonta, SS ya hana, har suka iso wurin ya gama parking, ya fito ya zagaya ya bude mata kofar ta fito, kafin suka mik'a zuwa ciki. Babu kowa a restaurent din, illa ma'aikata, a gaba d'aya wunin ranar SS yayi booking wurin, wannan ya sa babu wani mahaluki da ya ci abinci a wurin ranar, k'arshe ma Close kawai suka sa a k'ofar shigowa. D'aya daga cikin ma'aikatan ne yayi musu jagora zuwa wani k'aton hall, wanda a k'alla zai iya d'aukar mutum hamsin. Duk wasu extra tables sai da aka fitar da su, illa table guda daya, da chairs biyu, a tsakiyar hall din, an yi hadadden decoration komai red, ga roses an baza a kasa ko ta ina, sai wani lafiyayyen kanshi da ke tashi, wanda shi kadai zai iya sanya nishadi a zuciyar masoyi. Dim light aka kunna na red bulbs, tare da candles da aka saka a red containers, wurin ya k'ayatar sosai, dai dai yadda SS ya ke son ganinshi. A bakin kofar ya tsaidar da ita, ya k'arasa ya dauko bouquet of red roses din da aka yi tying da green ribbon, mak'ale da dan k'aramin card a jiki, ya iso ta bayanta ya warware necktie din fuskarta, ya ziro da hannunshi da flowers din ke rik'e ta gabanta, ya mik'a mata. Baki ta sake tana kallon tsaruwar wajen, sosai ya tafi da duk wani imaninta, ta yi saurin sa hannu ta anshi flowers din da murmuahin mai birgewa a fuskarta. Gaban table din suka isa, ya ja mata kujera ta zauna, har yanzu bata daina mamakin abun da ta ke gani ba. Juya flowers din take a hankali, tana scenting daddadan kanshinsu, a jiki ta ci karo da kyakkyawan karamin katin dake mak'ale jiki, da sauri ta bude, fuskarta taf da jin dad'i ta fara dubawa. I will always protect you from the thorns. Abinda ta gani a rubuce kenan, ta dago tana kallon shi, shima ita din yake kallo fuskarshi na aika mata da sakon murmushi mai cike da salon k'auna. "Let's eat." Ya fad'a yana nuni mata da rufaffen plate din da aka shigo da shi, aka ajje gabanta, bakinta ya kasa furta komai, wani shauki take ji mai wahala fassaruwa. A haka ta sa hannu ta bude plate din. Abinda ta ga ni ne ya sanya ta dawowa da sauri, ta sauke idanunta cikin nasa da ko kadan, basu kauce a kallonta ba. Yar karamar paper da aka yi ma shape din zuciya, red color jikinta d'auke da fararen rubutu ta dago tana sauke idanunta a hankali. Wanna share every meal with me???1 She's totally speechless, ta tsaya kawai tana kallonshi, a lokaci guda tana ganin yadda kibiyar sonta ke yawo a cikin idanunshi. Murmushi ya yi, ya mik'e ya ciro wayarshi ya danna kira, within seconds, wani waiter ya shigo, a lokaci guda duhu ya gauraye hall din, sai dan hasken candles din da ke haskawa kad'an-kad'an. Cikin yan mintina, hasken projector ya bayyana a bangon da ke facing Jay, yayin da k'aton hotonya ta ya bayyana baro-baro, wanda a zahiri bata san lokacin da aka d'auke shi ba. She's My life1 Aka rubuta a k'asar pic din. Hoton zuciya ne ya bayyana, mai dauke da rubutun da ya taimaka wurin bayyanar fararen hakoranta, tana nutsar da kallonta ga abun da ke fuskantarsu. SADJAY Bayan ya d'auke, rubutu ya fara bayyana, wanda gaba d'aya kalamai ne na soyayya masu tsuma zuciyar masoyi tun daga rana ta farko da ya fara ganinta har izuwa randa ya fara sonta, happy memories dinsu a asibiti, da yadda soyayyarsu ta cigaba da kasancewa, a k'arshe aka yi wani rubutun da ya sanya Jay mikewa tsaye da manyan bakake. WILL YOU MARRY ME? These memories are great, but I'd like to creat more... A dai-dai nan SS ya iso gabanta, murmushi ya ke yana dubanta, ya gagara furta komai, a zahiri ba zai iya tantance yanayinta ba a day dai lokacin. Shiru tayi tana k'ura masa idanu, daga bisani ta fara girgiza kai, wasu zafafan hawaye suka k'wace mata, wanda ba komai ya jaza hakan ba, illa tunanin ranar da Sadam yayi proposing dinta. A zahiri da zata iya, da babu abinda zai hana tace ma SS a'a, sai dai baza ta iya ba, ta kuma ci alwashin koya ma kanta soyayyarshi ko ta wane irin hali. Shiru yayi yana kallonta, a zuciyarsa yana ayyana abubuwa da dama, wanda kuma a take ya gaskata su, ya aminta da su. Murmushin dole ta kakalo, tasa tissue ta d'auke hawayenta, amma wasu sabbi na sake gangarowa, ta mik'a mishi yatsanta na biyun karshe, tana hawaye, tana murmushin dole, ya saki nashi tattausan murmushin, ya zaro siririn gold ring din daga gidanshi, ya saka a hannunta. "I Love you Angela." Ya fada yana kokarin kama hannayenta. Da sauri ta ja da baya, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ci gaba da binta, bakinshi kunshe da wani irin kyakkyawan murmushi. Ido waje take kallon yadda shiny idanunsa suka fara canja kalarsu, cikin razana ta furta "Are you okay?" Bai iya furta komai ba, ya mika hannuwansa yana rike da nata, bai san me ke yawo cikin kansa ba, amma yana jin yadda soyayyarta ke dukan din wata gaba da ke jikinsa, yana jin tamkar zai iya rasa ta daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Yana kaunarta tsakaninsu da mahaliccinshi, ba zai kuma iya jure rashin ta a gefenshi ba. "I Love you Angela, so very much. I love you with every fibre of my being." Flower bunch din da ke hannunta ta wurgar a kasa, cikin idanunsa take kallo, kafin ta fizge hannunta a na shi, ta kalli tsakiyar idanunsa lokacin da hawaye ke zuba a nata idanun. "Na gode Ya Sadic." Ta fada da wata raunatacciyar muryarta, ta juya da sauri tana neman hanyar fita. Bai fahimci mahaifarta ba, amma ya ga bacin rai a tsakanin idanunta,ya ga wani abu wanda ba ya son ya yarda da fassararshi a fuskantar. Bai taba zaton rike hannayenta zai zama wani abu irin wannan ba. Bai bari ta karasa fita ba, ya isa da sauri ya shiga gabanta, bai san me zai fada mata ba.12 "I'm sorry please. I doesn't mean to hurt you. I'm sorry Angela." Mamakinshi take sosai, ta rasa me zata ce da shi, cikin zafin nama ta daga hannu ta saita a kan fuskarshi da zumar wanke shi da mari, sai dai kwarjinin da yayi mata, yasa tayi k'asa da hannunta ta fashe da wani irin kuka. Cikin tashin hankali ya k'araso yana shirin kama hannunta, tayi gaggawar d'ago manyan idanunta.5 "Don't you dare touch me again." Chak ya tsaya a wurin yana kallonta, hankalinshi a tashe domin a zahiri bai san sa'adda zuciya ta debe shi ba har ya kai hannuwansa saman nata. "I'm so sorry Angela please. Wallahi ba laifi na ba ne ba."1 Mikewa tayi a fusace ta fita, shima ya biyo bayanta da sauri, tana shirin fita main gate na restaurent din ya dake zuciyarsa ya finciki hannunta, bai damu da yadda take tirje-tirje ba, da kuma yadda ma'aikatan wurin ke kallonsu, ya bud'e gaban motar ya saka ta, ya rufe, kafin ya zagaya da sauri ya shige ya tada motar suka bar harabar wurin. Wani irin azababben kuka take wanda ya ki ya ji lallashi da ban bakin da SS ke mata, sai ya zamana tamkar yana k'ara ingiza hawayen da suke ambaliya a fuskar tata ne. Har suka iso gida ya shigo da shirin gyara parking, bata bari motar ta k'arasa tsayawa ba ta bude da k'arfi ta fice ta fara takawa zuwa ciki, ba tare da ta damu da bakuwar motar da ke girke a gefen da suka yi oarking ba. "Jay.." Ta ji muryar da ko a wane irin tsanani zata riski kanta, baza ta taba manta mamallakinta ba, bata juyo ba, amma ta tsaya tsab, haka ma hawayenta suka kafe a lokaci guda. Jingine yake jikin motar, haka SS shima ya jingine jikin tashi motar ya zuba masu idanu yana kallonsu. A hankali ya taka ya isa inda take tsaye, ta juyo tana kallonshi, yayi baki sosai ya rame, dan har wani extra space ke akwai a rigar jikinshi, ta kalle shi tun daga sama har kasa, wani kuka ne ya k'ara kubuce mata, ta juya da sauri zata shige ciki. SS ta gani a gabanta, ya zuba mata idanu yana girgiza mata kai alamar kada tayi haka. Gabansu Sadam ya isa ya mik'a mishi hannu suka gaisa. "Magana kawai nike son yi. Nothing more." "Magana?" Ta fad'a tana kallonshi, "I thought babu wata magana da tayi saura a tsakaninmu." Duk wanda yaga yadda tayi maganar ya san cikin k'arfin hali ta yi ta, domin kuwa fuskarta, ta bayyanar da sirrin zuciyarta, ta yadda hawayenta suka dinga sintiri ba kakkautawa, tana yi ma Sadam wani irin kallo mai cike da tausayin halin da yake ciki duk da bata san me ke damunshi ba, amma tana da tabbacin abun ba zai rasa nasaba da ita ba.1 "Ki saurare shi please." SS yayi maganar dan ya riga ya gama karantar zuciyarta, a lokaci guda ya juya zai koma bakin motarsa. "Gaba dayanku nike son magana da, please kada ka tafi." Kamar ba zai dawo ba, sai kuma ya ja ya tsaya a inda yake, yana kallon yadda wasu kibiyoyi ke fita daga idanuwansu suna kai suka ma zuciyoyinsu.1 Wani bakin kishi ne ya turnike shi, sai dai bashi da bakin magana, idan yayi duba ga gagarumin laifin da ya aikata mata.. Motar Baffa da ta sako kai cikin gidan ne ta sanya kowa cikinsu shiga taitayinsa, ganin yadda annurin fuskarsa ya d'auke cikin dan lokacin da ya fito yana dubansu daya bayan daya. Jay da ke tsaye tsakiyarsu ya zuba ma ido, a zuciyarsa yana tambayar me suke son mayar mishi da gida? Maza har guda biyu sun saka mishi 'ya a tsakiya suna kare ma halittarta kallo.1 "Barka da zuwa Alhaji." SS yayi saurin fada, ya juyo ba yabo ba fallasa yana kallonshi. "Barka dai Sagir. Lafiya kuwa?" "Sannu da zuwa Baffa." Sadam ya anshe yana sussunne kai, Baffa ya juya ya k'ura masa ido yana son tuna inda ya san fuskarshi. "Lafiya lau. Ehnmm dama.." "Ya dai? Ina jinka." "Dama ina son yin magana da su ne." Sadam ya k'arasa mishi, yana kallon Baffan. "Uhhnmm Sagiru?" "Na'am Alhaji." "Ka jira ni a ciki, dama ina son ganinka." Ya juya yana kallon Jay da kanta ke k'asa ta kasa motsi, tana hada yatsunta wuri guda. "Me kike jira da baza ki wuce ba ke kuma?" Sum-sum ta juya ta shige ciki tana shafe hawayen da suka yi saura a idonta, duk da ta so ta san abinda ke tafe da Kazaure, amma bata da wani zabin da ya wuce mata na Baffanta. Ya juya yana kallon Sadam, zuciyarsa taf da mamakin canje-canjen da yake gani a tare da shi. "Ya aka yi ne Sadam? Akwai matsala ne?" Shiru yayi kanshi a k'asa, dan a zahiri ba Baffa ya zo gani ba, amma tunda ya yi mishi katanga da wacce ya so ganin, zaiyi amfani da wannan damar ya isar mata da sakon da ya zo da shi, watak'ila Baffan ya fahimci halin da yake ciki. "Ina sauraren ka." "Dama zan ce ne ayi hak'uri da abubuwan da suka faru, komai muk'addari ne daga Allah." Juyawa Baffa yayi ya kira drivernsa da hannu, ya iso da sauri ya mik'a mishi jakar hannunshi. "Shigar mun da wannan ciki." Ya ansa ya wuce, sannan Baffan ya gyara tsayuwarsa, yana k'ara karantar yanayin na Kazaure. "Komai muk'addari ne kamar yadda ka fada. Hakan ma yasa kaga ban mayar da kai prison ba, ba don komai ba sai dan albarkacin jini da ka hada da jikata. Dan haka in dai bada hak'uri ne ya dawo da kai gidan nan, to ka kama gabanka, mun riga da mun hak'ura da duk abinda ya gabata." Kanshi a k'asa bai iya dagowa ya kalle shi ba, ya fara magana. "Baffa nayi nadamar duk wani abu da na aikata, na fahimci dukkan kuskuren da na yi, amma ina neman afuwar a bani dama in gyara laifukana saboda Allah, ba dan halaye ko dabi'una ba."2 "Dama? Kamar ya kenan Sadam? Idan na fahimce ka kana nufin Ummi ta koma ta cigaba da zama da kai?" Murmushin dattako Baffa ya zubar yana girgiza kai. "Yaro man kaza, bai gasu ba ya kashe wutar." Dagowa yayi ya gama k'are mishi kallo, tabbas ba zai rasa matsala a k'walwarsa ba, Baffan yake innatawa a cikin zuciyarsa.1 "To jira kaji Sadam, ko da kai kadai ne namiji k'wallin k'wal da yayi saura a doron k'asa, bazan taba yarda Ummi ta koma maka ba. Haba Sadam, ka yi ma zuciyata adalci mana, ka barni da ciwon da ka dasa a cikinta shekara da shekaru mana, ka kuma so ma dan uwanka musulmi abinda ka so ma kanka. Ka barni inji da haushinkan da nike ji a cikin zuciyata, wanda darajar 'yarka yasa ban iya yin komai a kanshi ba. Dan Allah na rok'e ka, wannan ya zama zuwanka na k'arshe gidan nan da sunan ka zo neman yardar Ummi ta koma gidanka." Hawaye ne suka silalo a fuskar Kazaure, wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa. Fuskarsa da ke k'asa ta gama bayyana tsantsar nadamar da ya tsinci kanshi a ciki, hakan yasa shi shafe hawayen, ya d'ago yana duban Baffa. "Ba wai nufina kenan ba Baffa, na sani, a yanzu bani da cikakkar lafiyar da zan ba ma Jay farincikin da na hane ta a baya, ba ni da komai, ba ni da kowa sai Allah. Ina nufin a bani dama in dinke 6arakar da ke tsakanina da ita da kuma diyata wacce har a yanzu bata daina gudu idan ta ganni ba." Ko bai fad'a ba duk wanda ya kalle shi ya san ba shi da lafiya, sai dai ba hakan ba ne zai sa Baffa yayi sakacin amince mishi, har ma ya ansa buk'atarshi. "'Yar taka dai Sadam, amma Ummi babu wata baraka a tsakaninku da tayi saura wacce zaka dinke, dan haka ka bani 'yan mintina, yanzu zan shiga in fito maka da Rukayya, in ya so sai kayi duk yadda kaga dama da ita. Idan ma suma zata yi idan ta ganka, babu abinda zanyi, a sannu dole ta hak'ura, tunda dai kaine mahaifinta." Bai iya cewa komai ba, domin kuwa ba shi da ta cewar, ya kuma san a hali irin na Baffa, ya taki muguwar sa'a har ma da ya tsaya yana maida magana da shi. Jin haka yasa Baffa ya wuce ciki, inda ya samu Jay zaune a palonshi ta had'e kai da gwiwa, bai san tunanin me take yi ba. "Ummi." Ta d'ago a razane, domin kuwa bata san sa'adda ya shigo gidan ba. "Na'am Baffa." "Ina Rukayya?" "Tana ciki wurin Goggo." "Shiga ki hado mata kayanta, ku zo nan ku same ni." Kallon rashin fahimta take yi mishi, sai dai bai bata fuskar tambayar dalili ba, ta mik'e jiki babu k'wari ta fita zuwa cikin gidan. Bayan kamar minti sha biyar suka shigo hannun Rukayya cikin nata, Goggo tana bin su a baya. Barka da dawowa Goggo ta yi mishi ya ansa, kafin suka samu wuri suka zauna suna jiran abinda zai fad'a. Gyaran murya yayi, ya d'ago yana dubansu. "Ummi na yanke wannan hukuncin ba don komai ba, sai dan watak'ila wannan itace kawai hanyar da zan iya dakatar da Sadam daga zuwa gidan nan. Bazan boye miki ba, a duk lokacin da na ga yaron nan zuciyata na bak'antuwa, domin kuwa tabon abinda yayi har yanzu ya kasa goguwa a idanuwana. Sai dai ban sani ba ko kina da ra'ayin k'ara zama da shi, domin kuwa ba zan tauye miki hakkin abinda kike so ba." Faduwar gabanta ne ya tsananta jin kalaman na Baffanta. Allah ya sani Sadam shine mutum na farko da ta fara so, sai dai yanzu a shirye take da ta bayar da ko da rayuwarta ne domin ta fanshi farin cikin iyayenta. Abinda bata fahimta a nan ba shine ina yake shirin kai mata Rukayyarta? Kanta a k'asa tace "Bani da sauran wata hujja da zata sa in k'ara kwadayin zama da shi Baffa, a shirye nike in siya maku duk wani farin cikin da zai faranta zuciyoyinku." "Masha Allah. Naji dad'in kalaminki Ummi. Ina so ki sani, yanzu Sadam zai tafi da Rukayya, suje can su samu daidaituwar tsakaninsu, domin bana so yana fakewa da 'yarsa, ni kuma yana dagula lissafin tawa diyar." "Ya kaita ina Alhaji? Mutumen da bashi da aure, ba uwa ba uba. Gaskiya wannan ba shawara ba ce ba." Goggo ta fad'a fuskarta a raunane tana kai duba ga Rukayyar da bata san abinda ke wakana ba. "Ina sane Maryama, amma duk yadda za'a yi baza a canja shi a matsayin mahaifinta ba, ku bar shi ya tafi da ita, ta nan ne zasu samu jituwa a tsakaninsu, ala bashshi idan komai ya dai-daita, na tabbatar da ta san shine mahaifinta, na tabbatar zai dawo da ita, amma bana son kara ganin fuskar yaron can a harabar gidana." Kukan zuciya Jay ta fara rerawa, bata da yadda zata yi, bata isa kuma tace bata yarda da hukuncin da Baffan ya yanke ba. Haka tana ji tana gani Baffa ya kama hannun Rukayya suka fita, suka samu Sadam tsaye a jikin motar da babu wanda ya san inda ya samo ta. Da farko bata gane shi ba, har suka iso gabanshi, ya duka a hankali yana shafar gashin kanta da ya sha gyara, ta girma ta k'ara wayo sosai, hakan ya k'ara fitar da ainahin kamanninsu a zahiri. Kuka ta saka tana kama hannun Baffa tana k'ank'amewa, haka ya fara lallashinta, shima Sadam din yana yi, har sai da ya kai ga kukan nata ya sa Baffan tausaya mata, amma bashi da yadda zaiyi, hakan ne kawai zai sa su samu sauk'i daga zaryar da Sadam din ke yi musu. A bayan motar ya saka ta da jakar kayanta, ya juya da sauri ya koma ciki, ya bar Sadam da aikin lallashi tare da mugun da-na-sani da nadamar halayenshi da suka gabata. A haka ya ja motar ya fita, kuka yake kamar ran shi zai fita, haka itama Rukayya ke nata kukan har suka dau hanya. Cikin gidan Baffa ya koma ya same su tamkar masu zaman makoki, yayin da tausayin halin da ya san Umminshi zata shiga ya dabaibaye zuciyarsa. "Kiyi hakuri Mamana. This is the best for all of us." "Babu komai Baffa. Na san baza ka taba yin abun da zai cutar da waninmu ba." Sosai ya ji dad'in yadda ta nuna bata damu da abinda yayi ba, duk kuwa da cewar ya san ta ciki na ciki, hakan yasa yake alfahari da ita, yanzu ne kuma ya san ya haifi 'yar da za'a kira da 'yar albarka. "Ummi a zahiri na gaji da wannan tarin matsalolin na yaron nan, yau wannan gobe wancen, idan har kin san ba zaki koma mishi ba gara kiyi aure, ya san kin mishi nisa har abada, amma wannan rayuwar bata da wani amfani, matsalar yau daban ta gobe daban, yau na ganki da Sadam gobe in ganki da Sagir, bazan lamunci haka ba gaskiya. A yau baki ji yadda zuciyata ta rink'a tafasa ba lokacin da na shigo na hange ki a tsakiyarsu, abin takaicin ma da nayi duba ga yanayin shigarki ko mayafin kirki babu a tattare da ke, a matsayinki na uwa, wacce ta san daraja da mutuncin kanta. Kinyi wannan shigar kin tsaya a tsakiyar mazaje, ta ya shaidan ba zaiyi tasiri a zukatansu ba, daga nan sai kiga an aikata abinda ba shikenan ba, duk da nasan ba haka kike ba, amma duk inda mace da namiji suka kai ga kebanta to na ukkunsu shedan ne, idan ba'a yi sa'a ba sai kiga ya samu galaba a kanku. Dan Allah ki natsu ki sanar da ni ainahin gaskiyar zuciyarki, idan baza ki koma ma yaron nan ba, ga Sagiru nan, yaro mai natsuwa da sanin ya kamata, kuyi aurenku ku huta da wannan gallafirin a kan titi, can a gidanki sai ki cigaba da karatunki dan na san ba zai taba hana ki ba." Shiru tayi tana sauraren maganganun na Baffa wanda suka sa hawaye fara tsiyaya a idanunta. Gaskiya guda daya ce, haka so guda daya ne kuma ba kowa take yi ma shi ba illa Kazaure, amma furucin Baffanta na cewar duk sa'adda ya ga Sadam zuciyarsa na bakantuwa, hakan yasa ta san har abada baza su taba komawa tare ba, kuma dole ta hak'ura da shi da soyayyarsa, ko dan ta dadadawa mahaifin da ya nuna mata kauna fiye da kowa a doron k'asa. Idan tayi duba ta bangaren SS kuwa, ta san yana matukar kaunarta, haka itama ta kan ji wani abu dangane da shi wanda ya sha banban da irin wanda take ji dangane da Kazaure. Watak'ila kaunarshi take yi wacce ita ba so ba ne da zai iya tashi daga nan, ya koma wani gun tana jin zata iya zama da shi har k'arshen rayuwarta, sai dai abinda yayi mata yasa ta fara shakku a kanshi, duk da cewar ta gaskata maganar Baffa da yace shaidan zai iya shiga tsakanin mace da namiji a lokacin da suka kebanta, hakan yasa ta dora ma kanta laifi dangane da wasu abubuwa da suka wakana.7 Shine mutumen da ya fi cancanta da ita, amma dole ta gwada mishi kuskurenshi ko dan zuwa gaba. Hawayenta ta shafe, ta juya tana kallonsu.1 "Ina maraba da duk hukuncin da ka yanke a kaina Baffa, idan har kana ganin Ya Sadic shi ya fi cancanta da zama miji a gare ni, to zan yi biyayya gare ka, zan kuma aure shi, dan haka ka daina kawo maganar Sadam a wannan lokacin, bazan taba iya koma ma mutumen da ganinshi kawai zai bakanta zuciyar mahaifina ba." Hawaye ne suka wanke idon Goggo, sosai tayi farin cikin jin maganganun nata, tayi magana masu ma'ana da muhimmanci, tayi magana mai kwantar da zuciya da sanya iyaye su zama masu alfahari da 'ya'yansu. "Allah ya yi miki albarka Ummi." A tare suka fad'a ita da Baffa, bakunansu kunshe da kyakkyawan murmushi. "Tashi ki je, zanyi magana da Sagirun." Ta mik'e a hankali ta wuce d'aki, yayin da Baffa ya fita zuwa inda SS ke zaune. Barka da Sallah Beautiful people ❤❤ Da sallama Baffa ya shigo palon, hakan yasa SS ya mik'e yana ansawa, kanshi a k'asa a karo guda bugun zuciyarsa na tsananta, domin kuwa ya gama yi ma kanshi hisabi tun Baffan bai sanar mishi abinda ke tafe da shi ba. Sai da ya zauna, sannan shima ya koma ya zauna yana k'ara gaishe sa, Baffa ya ansa fuskarshi sake, sai dai SS bai fahimci hakan ba kasancewar har yanzu kanshi na k'asa yana jiran abinda zai biyo baya. Gyaran murya yayi yana dubansa. Sai ya ji wata sabuwar k'aunarshi ta shige mishi, yadda ya ga ya mik'a duk wani hankalinshi wajen sauraren abinda zai fad'a. Murmushi yayi a zahiri na jin dad'i. "Ehnmm Sagiru." "Na'am Alhaji." "Shin akwai wata alak'a ne tsakaninka da Ummi?" A hankali ya d'ago yana kallon Baffan, shima idanunsa a kanshi, hakan yasa yayi saurin yin k'asa da nashi idanun. "Hakan da ka yi ya bani ansar tambaya ta. Amma me sa baka sanar da ni ba tun wuri?" "Ita din ce bata bani dama ba wallahi." "To ni na baka dama. Zan kira Hajiya zamuyi magana, daga nan zamu gana da yan uwan mahaifinka, sai in sanar da su ranar da za'a daura aure." A sikwane ya d'ago yana duban Baffa, fuskarshi ta gagara boye farin cikin da zuciyarsa ke ciki. "Nagode. Nagode Alhaji. Allah ya tabbatar mana da alkairi." "Amin Sagiru, sai dai ina da wata 'yar buk'ata idan baza ka damu ba." Shiru yayi yana sauraren shi. Hakan yasa Baffa ya cigaba. "Ina fatan zaka bani goyon baya wajen tsaya mata a harkar makarantarta, duk da ina da tabbacin ba za'a samu wata matsala daga gare ka ba." "In sha Allah zan yi duk wani kokari dan ganin na cika maka wannan burin, zan kula da ita, zan bata duk wata gudanmawa da ya kamata ace na bayar da yardar Allah. Nagode da wannan karamci, Allah ya k'ara girma." "Amin ya Allah. Ina ga iyakar maganar kenan, duk yadda muka yi da Hajiya kuma nasan zata sanar da kai. Allah ya shige mana gaba." Daga haka Baffa ya fita, ya barshi baki bude, wani irin farin ciki yake ji har bai san ta ina zai fara bayyana shi ba. Wayarsa ya fitar ya fara kiran Jay amma har ta gama ringing bata dauka ba. *** Kuka take mai azabar zafi da ciwo a cikin zuciya, ta rasa wace damuwa ce ta fi k'arfi a cikin matsalolinta. Shin soyayyar mutumen da baza ta taba komawa ba, ko rabuwa da 'yarta gudan jininta? Ya za tayi da auren huce haushin da take son lak'aba ma kanta? A zahirance bata da ansar tambayoyin nan, illa addu'a kawai da zata cigaba da yi har lokacin da Allah zai warware mata matsalolinta. Haka ya gaji da zamanshi ya tashi ya fita, har a lokacin bai daina kiranta ba, haka kuma bata da niyyar ko da kallon sashen da wayar ke ajje.4 ***Sadam. Har suka iso gida Rukayya bata daina kuka ba, shima idanunsa sun kunbure sun canja launi, haka ya iso yayi parking, ya bude bayan motar da niyyar daukarta da jakar kayanta. A hankali ya zauna a gefenta, tana ganin haka ta fara shanye kukan ta, idanunta a waje, ta had'e jikinta wuri guda tana ja da baya har sai da ta matse da k'ofar motar, tana jifarshi da wani irin kallo wanda ke nuni da tsabagen tsoron da ke cikin zuciyarta.1 Haushin kansa yake ji ba kadan ba, murmushin dole ya k'wak'wulo ya mik'a hannu zai taba ta, ta fashe da kuka tana girgiza kanta. "I'm sorry Baby. Bazan miki komai ba kinji. Ina son ki. Zo muje ciki in baki abinci da sweet." Kuka kawai take tana girgiza kai, ya k'ara kwantar da murya ya kama hannunta. "C'mon sweetheart. Daddy ne fa. Kina son in baki ice cream ko? Da chocolates in siya miki sabon kaya, muje park kiyi wasa. Zo muje bazan dake ki ba fa." Ai kamar ma yana tunzura ta, kuka take kamar ranta zai fita, haka ya cigaba da lallashinta, dak'yar ya iya daukarta a kafada ya d'auki jakarta a d'ayan hannun suka mik'a zuwa ciki. Dakinshi suka wuce ya zaunar da ita, sannan ya fara bud'e jakarta ya cire kayanta ya fara jerawa cikin wardrobe d'insa, teddies dinta da wasu tarkacen kayan wasa da aka zubo a kasan jakar ya fitar, ya gama jera kayan sannan ya iso gabanta ta ci kuka har ta hak'ura tayi shiru.4 "Zo nan Sweetheart." Ya bud'e hannayenshi, amma ko motsi bata da niyyar yi. Shiru yayi yana kallonta, ya rasa me ke masa dad'i, ga wata irin k'aunar yarinyar da yake ji, sai dai bai san ta ina zai fara shawo kanta ta daina tsoronsa ba. Murmushi yayi ya isa ya d'auki daya daga cikin teddies dinta ya fara mik'a mata, amma tana ansa tayi wurgi da shi ta tsallare da kuka.8 "Oh God! I'm sorry Baby. Zo muje in kaiki wurin aunties dinki. Zo nan in goya ki."1 Ya duk'a gabanta yana nuni mata bayanshi, babu gardama ta haye bayan, domin duk a tunaninta wurin Mammynta zai kaita. Cikin gidan ya shiga nan fa ya fara cin karo da k'annenshi yan mata, duk ba wanda a yanzu bai san tarihin Sadam ba a gidan, haka ganin kamarsu da Rukayya yasa suka gane itace 'yar tashi.1 "Feena." Ya shigo yana k'walla kiran daya a cikinsu, da sauri ta fito tana ganinshi ta fara dariya. "Ya Sadam ina ka samo fine girl?" "She's your niece. Kina wani tambaya ta. Baki ga kama ba ne?" "Ba dai Katsina ka je ba? Tun dazu Ya Sa'id ke nemanka lokacin shan maganin ka yayi babu wanda ya san inda ka tafi." "Zan sha yanzu, but please ki kawo mun abinci in bata kinji." "Ka kawo ta mana Ya Sadam. Kai da ba lafiya gare ka ba." "Na sani Feena, but this is the only thing i can do for her. Kin san komai fa."2 Murmushi tayi ta mik'a hannu ma Rukayya, ga mamakinta sai ta saki dariya ta taho wurinta, hakan yasa Sadam ya sauke ta, Feena ta kama hannunta suka shiga babban palon gidan, yara da manya duk a nan ake zama a sha firar duniya a watse kowa ya wuce dakinshi, dan yanzu gidan dai babu mata, dama Haj. Daso ce tayi saura a matan babansu, ita kuma ta haukace ta shiga duniya, sai wata k'anwar mahaifinsu da mijinta ya rasu ta dawo gidan da zama ita da 'yarta. Cikin ikon Allah duk jama'ar gidan sai suka d'auki k'auna suka dora ma Rukayya, kowa sonta yake yana son ta zauna a wurinshi, amma Kazaure yayi katan-katan ya hana a cewar shi shima yana son ya bama 'yarshi soyayya kamar yadda kowanne uban arzik'i ke yi. A nan suka ci abincin, inda ya rink'a bata da kanshi, abin ka ga yarinta gashi kuma fuskarshi kawai ta sani a cikin fuskokin wurin, sai ta rink'a ansa tana ci, sai da ya tabbatar da ta k'oshi tass, sannan ya k'ara daukarta suka koma dakinshi ya mata wanka ya canja mata kaya, ya kaita wurin Feena, dan duk ya fi sonta a cikin k'annen nashi, sannan ya koma yayi wanka ya shirya yayi sallar maghriba, yana nan zaune yana lazimi har aka yi ishsha'i ya fita masallaci yayi sallah, sannan ya dawo ya wuce cikin gidan. D'akin Feena ya zarce ya gansu suna ta firarsu da Rukayya, ya tsaya a bakin k'ofa yana kallonsu, a lokaci guda soyayyar 'yar tasa na yawo a gaba daya jijiyoyin jikinsa . "Feena ta shi muje a siya ma Rukayya chocolates ko?"14 Ya k'arasa shigowa yana kallonta, itama kallon nashi take yi, sai dai wannan karon bata rushe da kuka ba. Gabanta ya duk'a ta haye bayansa, ya mik'e dak'yar, dan ba wata cikakkar lafiya ce da shi ba, haka kuma yarinyar irin chubby kids din nan ce, dan girman jikinta ya fi na shekarunta. A motar Sa'id suka zauna shi yana baya da ita, Saheeb na zaune a driver seat suna jiran fitowar Feena. D'auke ta yayi ya dora ta kan k'afafunsa, yana kallon yadda take abu a tsorace, ya san har yanzu bata daina tsoronsa ba, ya kama cheeks dinta ya fara jijjiga fuskarta, yana mata chakulkuli. "Smile now.." Hakan yasa ta fara k'yalk'yale dariya tana kwantawa jikinshi, wani dad'i na daban ya dinga ratsa zuciyarsa, ya tsaya yana kallonta a zuciyarsa yana yaba kyawun smiling face dinta, dan tunda yake a duniya bai taba ganin dariyarta ba sai yau, ashe irin baiwar da Allah ya mishi kenan amma ya guje ta? Hannuwansa yasa ya mak'alk'ale ta, yana jin k'aunarta sosai tana fasa k'irjinsa tana zarcewa cikin zuciyarsa. "I love you Cutie pie." Ya fada lokacin da ya d'ago fuskarta, ya kuma kama cheeks dinta yana girgizawa. "Kina so na?" Kai ta girgiza alamar "A'a." Shiru yayi, jikinshi yayi sanyi, amma ya daure yace "Me sa?" Hannunta ta tura a hancinsa tana wasa da shi, kamar bata ji me yace ba. "Me sunana?" Ya k'ara tambaya yana rik'e hannun da take wasan da shi. Shiru tayi tana kallonshi, a lokacin Feena ta iso, Saheeb ya tada motar suka fara tafiya sannan ta d'ago tana kallonshi, cikin daga murya tace "KAZAURE..."1 Dariya suka kwashe da har su Feena da ke gaba, Sadam ya kalle ta yana dariya sosai wacce rabon da yayi irinta ba zai iya tunawa ba. Dak'yar suka tsagaita, ya sauke ta ya zaunar a kan seat, ya juya yana fuskantarta, tare da kama hannayenta ya rik'e cikin nashi. "Sunana ba Kazaure ba ne ba, daga yanzu Daddy zaki na cewa. Kinji?" "Ni ina da Daddy ai, kai ba Daddy na ba ne ba." "Noo, nine Daddynki mana. Baki da wani Daddy baya na." "A'a fa ni Daddyn Jafar ne Daddy na, yana siyo mun shokolates da iyish kiyiim." Shiru kawai Sadam yayi, a zuciyarsa yana innata 'wato bayan fashin mata da SS yayi mishi har ma da na 'ya?' Murmushi yayi ya k'ara matse hannunta.2 "Wancen Daddyn Jafar ne, ni kuma Daddynki. Zan na siyo miki duk abinda kike so nima, in goya ki, in baki abinci in miki wanka, in kaiki yawo ko ina da ina. Because I love you so very much." Shiru tayi tana kallonshi kawai, ba wai dan ta fahimci duk abinda ya fad'a ba, a haka suka kawo gaban wani k'aton Store. Shopping suka yi dai-dai da dai-dai dan ba wasu kudi ne da shi ba, wannan ma a credit card din Sa'id da ya basu aka cire, suka fito suka shiga motar suna cigaba da dan zagayawa a gari, har sai da ta dan sake da shi, a k'arshe bacci ya d'auke ta sannan suka d'auki hanyar gida. Haka ta cigaba da zama tare da shi, so da tattali babu kalar wanda baya bata, duk abinda ya kamata ace mace ce zata yi mata to shi da kanshi yake mata, a bangare guda kuma k'auna da soyayyar Jay na cigaba da azabtar da zuciya, da gangan jikinsa.1 ***Three Weeks Later.*** ***SS. Gab da la'asar suka shigo garin Katsina, bayan motar ya juya yana kallon Jafar sai baccinshi yake, sannan ya dawo da kallonshi ga Farouq da hankalinshi ke kan titi. "Ku ajje ni ta GRA ku k'arasa gida Farouq. Ina son magana da Jay cuz har yau ta k'i ta d'auki phone calls d'ina, gara ayi wacce za ayi a gama yau, na kasa samun natsuwar zuciyata, kar muje mu muna ta shiri ita kuma ya kasance abin baya gabanta."1 "Haka ne Yaya, amma ka daure muje gida ka dan huta mana, zuwa anjima ba sai in kai ka ba?" Shiru yayi yana kallon gefenshi, Allah kadai ya san halin da yake ciki, sai kuma shi da zuciyar ke jikinshi, a hankali ya cika bakinsa da iska ya furzar, fuska a raunane yace "Baza ka gane ba Farouq. Wallahi sati ukkun nan da nayi ba tare da na ji muryarta ba ji nike kamar nayi shekara biyu ne. A duniya ban taba zaton akwai wata mace da zata canja tunani haka ba. Ina son ta sosai Farouq, irin son da har bansan adadinshi." Murmushi Farouq yayi, ya juya da fuskar tsokana yana kallon shi. "Ai ko baka fad'a ba zan iya gane haka Yaya. Cuz ban taba jin kayi firar mace da ni ba, ko Aunty Aysha da kuka yi auren saurayi da budurwa banga kana rawar jiki ba irin wannan." Kunya ce ta cika SS, ya juya yana basarwa, Farouq ya sanya dariya, a lokaci guda ya canja akalar steering dake hannunshi. Sosai SS ya shagaltu wurin tunanin matsayin da yake da shi a wurin jay, duk wani abu da ya kamata na maganar aure an gama gabatar da shi tsakanin iyayensu, kwana biyar kacal ya rage a daura auren, sai dai babbar matsalar a yanzu shine yadda ta ke nuna halin ko in kula a lamarinshi, rabon da ya saka ta a ido sati ukku kenan cif-cif haka zai zo gidan ya gama zamanshi amma baza ta fito ba, ya kira waya tayi ringing har ta gama, amma baza ta dauka ba, har ya gaji ya koma bakin aikinsa. A da yana tunanin abinda yayi mata ne ya haifar da haka, a yanzu kam wasu tunane-tunane sun cika k'wanyarshi, sun hane shi sakat, addu'a kadai yake ga Allah yasa ta zama mallakinshi. A harabar gidan suka yi parking, ya fito tare da kwashe phones dinshi dake zube a gaban motar, ya daga ma Farouq hannu, ya juya zuwa ciki. Zaune ya hange su k'asan canopy tare da malamin da ke koyar da ita littattafan addini, tana sanye da maroon din hijab hannunta rik'e da alqur'ani hankalinta gaba d'aya ya ta'allak'a ga abinda ke gabanta. Kallonta ya sake baki yana yi, hakan da ya gani yasa ya k'ara kamuwa da matsananciyar soyayyarta, wacce yake jin ko da sama zata had'e da k'asa ba zai iya daina sonta ba, ji yake ko da tace ta tsane shi ba zata aure shi ba, ba zai taba iya hak'ura da ita ba, he'll fight till end, har sai ya samu cikar burinshi. Wayarshi da tayi k'ara ne ya dawo da shi daga tunaninshi, ya maida hankali ga wayar, wani abokin aikinsu ne, ya daga sannan ya k'arasa shigewa palon ya samu wuri ya zauna. Sun d'auki kusan mintina sha biyar suna wayar, wadda yawanci duk a kan shirye-shiryen bikin na SS ne, sannan suka yi sallama, ya cigaba da latse-latsenshi har zuwa k'arfe biyar da rabi, ya san lokacin tashinta yayi, kuma dole sai ta bi ta inda yake kafin ta wuce cikin gida. Bai kai ga k'arasa tunaninshi ba ta turo k'ofar ta shigo, chak numfashinta ya dakata na wucin gadi, lokacin da tayi arba da doguwar fuskarshi, ya sakan mata shiny idanunsa da suke wani shining yana kallonta. Murmushi mai taushi ya jefe ta da shi, amma ta daure fuska tamkar wacce bata taba dariya a duniya ba. Qur'aninta ta k'ara matsewa ta fara takawa zata wuce zuwa ciki. "Haba Angela. Dan Allah kiyi hakuri ki sassauta punishment din nan da kike bani, wallahi ina azabtuwa ba wai kadan ba." Juyowa tayi a hankali ta fara takowa cikin palon, hakan baya rasa nasaba da tunanin da tayi, ta zauna a daya daga kujerun da ke fuskantarshi tana rungume da Qur'aninta a kirji, hakan yasa shima ya koma ya zauna, hankalinshi a tashe yana kallonta. "Please Angela. It wasn't my fault wallahi, duk sharrin shaidan ne, and you didn't gimme a chance to explain myself. I love you, and you know that, bazan taba yin abinda zaiyi hurting feelings dinki ba. Kin sani ai." Murmushin k'arfin hali tayi, ta dago da manyan idanunta ta sauke a cikin nashi. "At first, I thought you were the one Ya Sadic, I mean the one I'll spend the rest of my life with. But now, ka gama tona kanka, ka bayyana true color dinka. And ka bar ganin su Baffa sun ajje maganar aure tsakanin mu kayi tunanin zasu yi mun dole, NO, that can't be, nasan sunyi hakan ne dan basu san kai din ko wanene ba, amma zan fallasa musu labarinka, zan sanar da su ainahin wanene mutumen da suke shirin hada ni aure da. Cuz ko da ni da kai kawai muka yi saura a duniya bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, bazan taba iya zama da mai hali irin naka ba, in takaice maka Ya Sadic dole a kai mun a maganar aurena da kai, amma ni zuciyata tana da wanda take so, wanda da shi kadai ne zan iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar. So, ka daina ba kanka wahala, kaje ka nemi matar aure, dan ko da a ranar daurin aurenmu ne, sai na fallasa sirrin da kake tunanin tsakanin ni da kai ne. Kuma ina mai tabbatar maka hakan zaiyi sanadiyyar rugurgujewar auren na mu."26 Ta mik'e a tsanake ta bi ta gabanshi ta wuce ciki, sai dai ko dan yatsanshi ya gagara motsawa, tunani da mamaki sun gama cika zuciyarsa har sun sa ya rasa gane abinda ya kamata yayi. Wani gagarumin tashin hankali ne ya ziyarci zuciyarsa, take numfashinsa ya fara kaiwa da kawowa, zuciyarsa kam tamkar an dora dutse tayi, ya mik'e dakyar dan baya gani sosai, a duniya idan akwai mafi munin magana da ya taba ji to baza ta taba kai wannan da ya ji daga bakinta ba. A kafa ya fita gidan, tafiya kawai ya ke, bai san ina zai dosa ba ma. **Two Days Later** Kuka take tsakaninta da Allah wanda ta gagara gane ko na menene, a hankali ta fara shafe hawayenta, ta mik'e da zumar zuwa ta sanar da Baffa gaskiyar zuciyarta, a dai-dai lokacin Baffan ya turo k'ofar dakin nata ya shigo hannunshi rik'e da katuwar Brown envelope guda biyu. Da sauri ta koma ta zauna ta kirkiro murmushin dole tana fad'in "Sannu da zuwa Baffa." "Yawwa Mamana. Ashe dai kina ciki?" "Ina nan Baffa." "An shi nan kiga" Ya mik'a mata daya a cikin envelopes din, ta ansa ta zaro paper da ke ciki, admission later dinta ne ya fito, cikin sa'a ta kuma samu law din kamar yadda ta cika, take wani farin ciki ya kai ma zuciyarta ziyara ta d'ago da jin dad'i tana kallon Baffa. "Nagode sosai Baffana, Allah ya saka da alkairi." "Amin Ummina, anshi wannan shima ki duba to." Ya mik'a mata d'ayan envelope din wanda ya fi wancan nauyi ta sa hannu biyu ta ansa tana kokarin fito da abinda ke ciki. Wedding invitations ne sun kai guda d'ari biyar masu masifar kyau ta d'auki d'aya daga ciki ta duba, taga dai tabbas shirin bikin suke yi, ta dago idanuwanta taf da hawaye tana kallon Baffa. "Lafiya?" Ya tambaya yana kallonta, bata iya cewa komai ba ta fashe da wani irin zazzafan kukan da ya tayar da hankalin Baffa. "Haba Ummi, babba da ke kike wannan kuka haka? Ko dai baki son yaron nan ne?" Da sauri ta girgiza kai, tana shafe hawayen "Ba haka bane Baffa, kawai dai ina ta missing Rukayya ne, ya kamata a dawo mun da ita."3 Murmushi mai sauti yayi, "Haba Ummi, in dan wannan ai ba matsala ba ce ba, zan aika da kaina a anso ta, ki kwantar da hankalinki da Allah."4 Haka ya cigaba da yi mata nasihohi, a k'arshe ya kwashi wasu daga cikin iv's din ya fita, inda ta kife kai ta rink'a rera wani irin kuka, wata sabuwar k'auna da soyayyar Kazaure ta taso mata, tana jin kamar tana kokarin jefa kanta a mugun hali ne.15 Tun daga wannan rana Baffa, ya fara inviting duk wasu abokananhi na nesa da na kusa, na kudu da na arewa babu wanda bai gayyato ba domin ji yake tamkar wannan ce rana ta farko da zai fara aurar da ita, shirye-shirye kawai suke daga shi har Goggo, 'yan uwa na nesa da na kusa duk sun fara hallara, amarya ce kawai ke rufe kanta a d'aki ta ci kuka har ma ta gode Allah, babu wanda ta gayyato, ko Miemie bata fad'i ma labarin bikin ba. Haka ya kasance ta bangaren SS, shiri Hajiya da sauran danginshi ke yi, sun hada gagarumin lefe tamkar wanda za'a kai ma budurwa, latest kaya suka zuba suka dauka suka kai gidan Baffa, haka suma suka cika su da abubuwan arziki, sai dai zuciyar angon ta gagara natsuwa, hankalinshi gaba d'aya baya tare da shi, rabon invitations ma da yawa Farouq ne yayi shi, kasancewar duk babu wasu mutanen SS din wanda bai sani ba. Haka abubuwan suka cigaba da wakana, shirye-shiryen biki ake ko ta ina, gidan Baffa ya kacame, hayaniyar dangi kawai ke tashi. Kwana biyu ya rage a daura aure Goggo ta dauka wata Sudanese tazo ta fara aikin gyaran jikin amarya, cikin d'an lokaci kuwa ta fito sharrr da ita abin ba'a cewa komai. ***D'aurin Aure*** And ango da amarya aren't ready😁😁 Ranar ta kasance juma'a, yayin da daurin auren ya kama k'arfe biyu dai-dai na rana a babban masallacin juma'a dake garin Daura inda kakanta Mal. Baba ke limanci. Da misalin k'arfe goma sha d'aya na safe k'ofar gidan na Baffa ba masaka tsinke, sai ka dauka anan za'a daura auren, al'umma ce bila-adadin, baza su k'idayu ba, a haka ma da yawa daga cikin mahalarta daurin auren sun dade da isa Daura. Tunda gari ya waye Jay bata fito a d'aki ba, kuka take bil hak'k'i da gaskiya, tayi har ta gaji, ba tare da jama'ar gidan sun ankara da yanayin da take ciki ba. Sudanese din da ke mata gyaran jiki ce ta shigo da hadaddiyar khumra ta mik'a mata, tare da cewa ta shiga tayi wanka da ita. Ba musu ta ansa ta wuce toilet tayi wanka fitowar da zata yi taga Miemie zaune a bakin gado tana aika mata harara.+ "Baki da mutunci wallahi. Yanzu ke da Goggo bata sanar da Hajiya ba da sai dai inji labarin kinyi aure ko? Wai me kika d'auki friendship dan Allah? Abun wasa ko? To jira kiji Allah zai iya kama ki da laifi ta wannan hanyar." Murmushin karfin hali tayi, ta k'araso bakin gadon ta zauna jikinta daure da towel. "Baza ki fahimta ba Miemie." Da sauri ta katse ta "Ai bance zan fahimta ba dama, dallah tashi ki saka kaya ni ba excuse dinki nike son ji ba, tafe nike da Khady's Maquillage zata tsantsara miki make up, dan nasan ke kam ba gwanar shi ba ce ba." "And who ask you to bring her? To ku tattara ku kama gabanku dan ni ba wani make up da zanyi babe." "Wannan ne fa baki isa ba, dole ta gyare ki yanzu na daurin aure, kafin kuma na anjima idan zamu fasa dinner." Bata jira ansarta ba ta juya da sauri tana kiran make up artist d'in. Lokacin da suka shigo ta saka skirt and blouse na purple and cream din super Sheraton, dinkin ya zauna yadda ya kamata a jikinta, tun ba'a kai ga fara fentin fuskar ba, ta fara wani irin sheki da annurin haske. "Make yourself comfortable Cute, wannan crazy amaryar ba kirki ta cika ba." Miemie tayi maganar tana kallon Khady. Ita dai bata ce komai ba, murmushi tayi tana ta kallon Jay, tare da yaba kyau da haduwa irin nata. "Ya kike?" Jay ta juya da murmushi tana kallonta. "Lafiya lau, ya aiki?" "Alhamdulillah. Idan kin gama gara mu fara dan zamu iya kai two hours bamu gama ba." "Ina zuwa please, sai dai bana son heavy make up naturally, ki mun light one kawai, shima dan stubborn girl din can ta matsa." "Oho dai, ana so ana kaiwa kasuwa, abeggi ki sauri ki zo dan nima nan so nike a cancare ni." Dariya suka yi gaba dayansu, a lokacin ta gama tattara gashinta ta kama da ribbon, sannan ta iso gabansu ta zauna aka fara shafe-shafen. Karfe d'aya dai-dai ango da bataliyar abokanshi suka iso harabar gidan, ya fito cikin takun isa da kasaita, ya hade cikin danyar farar shaddar Gezna, babbar riga da yar ciki da wando, an zuba wani sassanyan ash din aiki a gaban rigar, kafarshi lullube cikin rufaffen ash din takalmin Kenneth Cole masu masifar tsada, hular PMB da aka sak'a da ash din zare zaune saman kanshi, yayin da wani irin haske da kwarjini ke zuba a jikinshi, duk kuwa da fadawar da idanunsa suka yi. Baban palon gidan suka tasar ma, sun kai su ashirin, a waje suka dakata, shi kuma ya tura kanshi ciki babu wata fargaba ko faduwar gaba a tare da shi. Zaune take fuskarta lullube da mayafi, ya iso a kasaitance ya zauna a kujerar da ke fuskantarta. Ganin bata da niyyar magana, yasa shima ya ja bakinshi ya kulle, domin kuwa ya zo da shirinshi na komai ta fanjama fanjam. A hankali ta sauke mayafin, ta d'ago da manya-manyan idanunta da Khady's Maquillage ta k'awata da mascara da eyeshadow ta sauke a kanshi. "Barakallahu fih ahsanil khaliqiiin." Kalmar da SS ya iya furtawa kenan, a lokaci guda zuciyarsa ta buga dam, tamkar zata fasa k'irjinsa ta fito. Dak'yar ya dai-daita kanshi, ya juyar da kai, sannan ya maida kallonsa ga silver agogon dake daure a hannunsa. "Ban san me kike son sanar mun ba. Kin fi kowa sanin a kan hanya nike kuma tare da mutane." Abinda ya faru da shi, shine ya faru da ita, sai dai har zuwa yanzu zuciyarta bata daina harbawa da sauri ba, domin kuwa a yadda take kallonshi yanzu ji take tamkar bata taba ganin halittar namijin da ya kaishi kyau da cikar kamala ba, duk kuwa da fadawar da ta lura idanuwansa sunyi, wanda ta tabbatar hakan ba zai rasa nasaba da uk'ubar da ta jefa shi a ciki ba, take ta manta dalilin da yasa tace tana son ganin nashi ma. Ganin bata da niyyar magana yasa ya mik'e, fuskarsa ba yabo ba fallasa, a karo guda ya tura hannuwansa a aljihun rigarsa ta ciki, ya tsaya tare da buda k'afafunsa, hakan ya k'ara k'ayatar da cikakken zubinshi a idanun Jay, sai dai bata da bakin da zata yabe shi. A tausashe ya fara magana ba tare da ya dubi inda take ba. "Nasan kina da wanda kike so, ina kuma sane da cewar aure na da ke had'i ne na su Baffa. Ban manta da cewar baza ki taba iya rayuwa da ni ba ko da ni kadai nayi saura a doron k'asa. Ban kuma manta da cewar baza a miki dole ba. Sai dai ina so ki sani ba wannan bane zai sa in watsa k'asa a idon mahaifinki ba. Ba wannan ba ne zai hane ni tafiya d'aurin auren da akai miki dole ba, dan nasan abinda kika kira ki tuna mun kenan. But da zaki birge ni, da sai ki daga waya ki sanar da mahaifinki cewar baza ki iya aure na ba kafin in isa, na san wannan ce kawai hanyar da zata sa su fasa abinda suke shirin yi, tunda ba za suyi miki dole ba, nima da kin yi mun gagarumin taimakon da zanyi ta zuba miki godiya har karshen rayuwarmu, cuz zaki saving dina daga fadawa auren matar da babu ko da digon soyayyata a ruhinta."1 Bai jira ansarta ba, ya juya zuwa inda bataliyar abokanshi ke tsaye, suna ganinshi suka fara tsokanarshi, ya maze ya fara bouncing, yana wata makirar dariya ya iso suka shige motocinsu, suka d'auki hanyar ta Abdu tushen Hausa. Suman zaune Jay tayi, bata ankara ba ta ji wani ruwa-ruwa kwance saman kuncinta, tasa hannu ta shafa da sauri, hawaye ne suke kwarara a idanunta. Me hakan ke nufi? Ta tambayi kanta. Ba tare da ta samu ansar ba ta mik'e da sauri da niyyar bin bayanshi, amma ina bata tarda kowa ba illa k'urar da motocinsu suka tayar. Jiki ba k'wari ta koma cikin palon ta zauna, tunani kala da kala sun cika zuciyarta, ta san muddin ta rasa namiji irin SS baza ta taba samun kamar shi ba, kamar yadda ta san ko ta sha giyar wake baza ta taba iya sheda ma Baffa ta fasa aurenshi ba, haka kuma ko da ita Sadam ne mutane biyun da suka yi saura a duniya baza su kuma zama a k'ark'ashin inuwa d'aya ba.1 ***Daura. K'arfe biyu da mintuna goma sha biyar dai-dai aka daura auren. Tsabar farin cikin da SS ke ciki, Allah kadai ya sani, haka ya fito suka fara gaisawa da mutane suna yi mishi fatan alkairi da samun zuri'a ta gari, daga nan suka wuce Daura Motel inda Baffa ya shirya musu reception, aka ci aka sha, tare da addu'o'i da neman zaman lafiya. Suna gama sallar la'asar suka d'auki hanyar Ta Dikko d'akin kara. *** Ko da suka dawo bai bi ta kanta ba, gida kawai suka zarce suka je suka cigaba da shirye-shiryen dinner su, ya dai san koma menene bata da yadda zata yi da shi yanzu, tunda ta riga ta zama mallakinshi. Shigowarsu kenan Farouq ya tare shi da sauri, hannunsa d'auke da manyan ledoji guda biyu ya mik'a mishi. "Wai Yaya ka manta da kayanku na dinner ne? Tun safe ina can ina jiran isowarsu." "Ya Allah. I'm so Glad to have a bro like you. Wallahi na manta. Yanzu komai ya iso ne?" "Eh komai yayi ready, ga naka nan, wannan na amarya ne ka dauka ka je ka kai mata dan kar ma tayi tunanin sanya wasu kayan." "Haka ne Farouq, ka shige da nawa, barin samu wani ya kaini." Ya d'auki ledar kayan yana waige-waigen neman daya a cikin abokanshi da zai mik'a shi gidansu Jay, amma bai samu dole ya kira wayar Farouq yace ya kawo mishi key din mota kawai ya je da kanshi. Motarshi na shiga motar su kazaure na tura kai a harabar gidan, ya fito hannunshi rik'e da ledar kayanta, yayin da Saheeb k'anin Kazaure ya gyara parking, suka fito hannunshi cikin na Rukayya. Gabansu SS ya k'arasa ya mik'a ma Sadam hannu suka gaisa. "How you Daddy's girl?" Ya duk'a yana shafa kan Rukayya. "Daddy ina Jafar? Nima ya zo ya ga sabon Daddy na." "Oh no please. Ni kuma fa?" "Kai ai Daddyn Jafar ne inji Daddy na ko?" Ta daga kai tana kallon Kazaure wanda kwata-kwata hankalinshi baya tare da su, jin wasu matasa guda ukku da suke doso inda suke tsaye suna cewa "Muje ga angon can ma." Gabansu suka iso suka mik'a ma SS hannu, tare da fad'in "Allah ya bada zaman lafiya." "Amin nagode." Ya fad'a da murmushi sai a lokacin ya ci karo da fuskar Kazaure da ya k'ura mishi ido yana jifarsa da wani mahaukacin kallo. K'asa yayi da idonsa, a sa'ar da ya kafe shi da nashi idanuwan yana jiran k'arin bayani. "I'm sorry Kazaure, aurena da Jay Allah ne kawai ya hada shi, wannan ne kawai abinda zan iya cewa." Daram dam, zuciyar Sadam ta buga tun k'arfi, wato da gaske auren suka yi. Bud'e baki yayi zaiyi magana, ya ji k'irjinshi ya rik'e, da sauri ya dafe ya duk'e a wurin yana wani irin numfashi. Jajayen idanunsa ya d'ago, take hawaye suka fara shatata, murmushin k'arfin hali yake da bakinshi da ya bubbushe tsabar wahala yace. "Thumbs up Tafseer. You did a great job." Yayi nuni mishi da babban dan yatsarshi yana jinjina mishi. "No please, kada kace haka mana, abinda Allah ya riga ya tsara kenan Kazaure, none of us can deny this fact. Haka Allah ya tsaro mana rayuwa." "Indeed." Ya fad'a yana girgiza kai, wasu zafafan hawaye na kwararo mishi, ya mik'e da sauri ya tunkari inda suka yi parking, SS ya bi bayanshi yana kiranshi amma ina bai tsaya saurarar shi ba, ya bud'e gaban motar ya zauna, kanshi ya kifa a tsakankanin kafafunsa yana wani irin azabtaccen kuka, nan da nan idanunsa suka yi jajur, ya d'ago yana duban SS da hankalinshi gaba d'aya ya gama tashi a halin da ya ga Sadam. "I'll never forgive you Tafseer. We've been friends for so many years, amma kayi betraying dina ko? Ba zan taba yafe maka ba."1 Kafin SS yace wani abu tuni ya juya da wata tsawatacciyar murya yana ce ma Saheeb "Start the damn car!" Rukayya na kuka tana musu magana, amma basu saurare ta ba, a razane ya tada motar suka bar harabar gidan, SS ya bi bayansu da kallo, zuciyarsa taf da tausayin abokin nashi, sai dai ya san tabbas ba shi da qualities din da zai sake zama mijin Jay for the 2nd time. Bai ma shiga gidan ba, ya samu wata ya hada hannunta da na Rukayya tare da akwatinta da suka ajje, ya bata kayan Jay yace ta kai mata, ya cire wayarsa ya typing mata text, kafin ya juya ya shiga motarshi ya bar gidan shima. *** K'arfe bakwai na dare aka d'auki amarya zuwa gidanta da ke Barhim Housing Estate, babu nisa sosai da gidan Hajiya. Gida ne k'aton gaske, part biyu ne kowanne part d'auke da manyan bedrooms guda ukku da parlour biyu, da kitchen, da toilets a kowanne d'aki, sai wangamemen guest parlour a tsakiyar parts din guda biyu, an k'awata ko ina da kayan alatu na jin dad'in rayuwar dan Adam. Kuka take tamkar karamar yarinya, majina ko ta ina tana tirjewa, amma haka aka tura ta k'uryar dakinta, 'yan uwa da Hajiya Miemie babbar k'awa zagaye da ita suna ta mata iskanci. Tara na dare kowa ya gama shirin tafiya dinner, in banda amarya da ko motsawa ta k'i tayi daga inda take zaune. Sai da wata k'anwar Goggo tayi mata tatass, sannan ta mik'e tana zunbure baki tayi wanka ta fito, Khady's Maquillage na zaune a gefe ta k'ara tsantsara mata kwalliya, Miemie ma ba'a zauna a baya ba, ta matso aka gwangwaje ta, nan da nan d'akin ya dau sheki da wani lafiyayyan kanshi na wata kalar khumrar da Jay tayi amfani da ita. Kayan da SS ya aiko mata Miemie ta d'auko ta iso gabanta da su, ta zazzage saman gado. Tail gown ce ta light Brown din bridal material mai masifar tsada, ta sha kyau har ta gaji, sai light Brown din high hills da clutch dinsu k'irar Jimmy Choo, sai golden necklace, earrings, bracelet da wristwatch suma a cikin wani dan k'aramin akwati. Bayan ta saka, Cute ta tying mata head, ta gama gyare ta tsab-tsab, cikin d'an lokaci ta fara haskawa tamkar fitilar lantarki, illa rashin murmushi a fuskar tata. Goma da 'yan mintina anguna suka iso aka fara jidar 'yan mata da iyaye da duk wanda zasu halarci dinner. Liyafa palace suka dosa, a gefe guda, Miemie ce tare da wani fine bobo abokin ango sun jero, su suka take ma Jay da SS baya suka haura cikin hadadden decorated hall d'in. Bayan Hajiya Sauda kanwar Goggo ta gama kwarara addu'o'i ga ma'auratan na neman zaman lafiya da zuri'a dayyiba, aka shiga cikin programs gadan-gadan yayin da MC ya umarci masu d'aukar selfie da suka yi tsaye cirko-cirko da su matso kusa. Bayan nan MC ya buk'aci ganin ango da amarya a tsakiyar fili. Kallonta SS yayi fuskarsa d'auke da lafiyayyen murmushi ya mik'a mata hannunsa alamar ta taso su fita. Kallonshi tayi ta juyar da kanta, da alama bata da niyyar bashi hannun kamar yadda bata da niyyar mik'ewa. Tashi yayi daga seat dinshi ya zagaya ta gefenta, bai damu da yanayinta ba, ko kallon da jama'a suka tsare shi da ba, abu daya ya ke tunawa, yin hakan bai saba ma shari'ah ba. Hannunta ya kama, ya mik'ar da ita, a lokaci guda ya sanya dayan hannun yana tattare tail din rigarta da ya shimfidu a tsakiyar wurin. Wani irin birgewa yayi, hakan yasa wurin ya kaure da ihu, cikin jin kunya ta dora hannunta a kan nashi, tana kallonshi cikin wani salo mai wuyar fassaruwa, suka k'arasa cikin filin. Flasher ce ke tashi ko ta ina, a tsanake suke taka rawarsu ta masoya har suka gama, suka koma seat dinsu kafin aka fara ciye-ciye ta tande-tande. *** Har suka iso gida babu wanda ke ma dan uwanshi magana, illa wani irin shock da suke fuskanta daga hannayensu da ke cikin na juna, suna jin yadda zuciyoyinsu ke harbawa da soyayyar junansu, sai dai babu wanda ya iya daga bakinshi, balle ya fayyace ma dan uwanshi sirrin da ke kasan ranshi. Bayan Farouq ya gyara parking, ta juya idanunta a narke tana kallonshi, hakan yasa ya sake mata hannunta da ke cikin nashi, da sauri ta bud'e motar ta fice, ajiyar zuciya ya sauke, shima ya bud'e nashi 6angaren ya fito suka yi bankwana da Farouq, sannan ya juya zuwa ciki. Tun daga parlour ya fara rage babbar riga da hular da ke kansa, ya rik'e a hannu yana tasan ma part d'inta. A rufe gam ya tar da k'ofar da makulli, ya tsaya da mamakinshi yana kallon k'ofar, bai iya yin komai ba ya juya ya shige nashi b'angaren yayi wanka ya kwanta yana tunanin wane irin zama ne za su fara haka. Dak'yar bacci yayi awon gaba da shi bayan ya yi wanka ya canja kayan jikinshi, ba shi ya farka ba sai da ladan ya k'walla kiran sallar asuba a masallacin da ke gefen gidansu. Mik'ewa yayi da salati, ya shiga yayi alwala ya fita ya wuce part dinta, ya manta da k'ofar na rufe, sai da ya murda sannan ya tuna, ya koma ya ciro keys din jikin tashi k'ofar ya duba extra nata da ke had'e da nashi, ya bude, ya shiga ya zarce dakinta. K'aran AC kawai ke tashi, sai k'anshin turarenta da ya had'e da na air freshner mai masifar dadi. Fitila ya kunna, a lokaci guda haske ya gauraye dakin, baccinta take tamkar bata da sauran damuwa, ya zauna a gefe ya tsura ma kyakkyawar fuskarta ido yana kallonta. Juyin da tayi ne yasa shi saurin mik'ewa ya fara tashinta "Jay." Yana yi yana dan bubbuga blanket dinta, ta bud'e idonta a hankali ta sauke kanshi. "Ki tashi kiyi sallah." Daga haka ya juya ya fita, ya barta da mamakin yadda akayi ya shigo mata, dan ta tabbatar da sai da ta rufe k'ofar lokacin da ta shigo. Toilet ta wuce ta d'oro alwala ta fito ta fara gabatar da raka'atanil fajr, tana gamawa aka tada sallah, ta tashi ta bi jam'i, suka gama, yayin da tayi zaune a wurin tana azkar, har zuwa k'arfe shidda, sannan ta mik'e tana k'ok'arin nade abun sallar. A dai dai lokacin ya dawo daga masallaci, ya shigo ta part dinta domin ya tabbatar da ta yi sallar. D'akin nata ya shiga, ganinta a tsaye ya sanya shi tsayawa a bakin k'ofa yana k'ura mata idanu. Jin kamar alamun mutum, ya sanya ta juyawa, idanunsu suka hade cikin na juna. Da sauri ta sauke nata, bata ce komai ba, ta maida kai ga abinda take yi. A hankali ya k'araso ciki, ya tsaya bayanta tare da ansar abin sallar hannunta, bai damu da yadda take bata fuska ba, ya zare hijabin jikinta, yasa hannu yana shafa dogayen hannayenta, cikin murya marar k'arfin amo, yace "Good morning Angela." Tsigar jikinta gaba d'aya suka mik'e, wani abu ya taso tun daga cikin kanta, ya sauka a babban yatsar k'afarta, da sauri ta k'wace jikinta, tayi gaggawar isa bakin gado ta kwanta ba tare da tace da shi uffan ba. Tsaye kawai yayi, baki bude, zuciyarsa na harbawa da gaggawa, yana tunanin dalilin da yasa take k'yamatarshi har irin haka mana. Gaban nata ya isa ya duk'a yana kallon yadda tayi kicin-kicin da fuska, ya sauke ajiyar zuciya tare da kama hannunta yana duban k'wayar idonta da suke shirin zubar da hawaye. Ganin hakan yasa ya sake hannun nata ya mik'e kawai ya fita a sashen nata baki daya. Tana jin yadda ya buga k'ofar palon, ta fashe da kuka, ita kanta k'arfin hali kawai take yi, ta rasa menene abinda ke damunta, domin kuwa ji take zuciyarta na harbawa da sauri, a hankali ta saki dan murmushi, ta koma ta kwanta tana sinsinar k'anshin turarensa da ya gauraye dakin har ma ya dusashe nata, ta lumshe ido, tana tunano yadda take son namiji dan gayu mai k'anshi, wannan na daya daga cikin abubuwan da suka sa Kazaure ya tafi da ruhi da imaninta Throw pillow din 1pda ke gefe ta janyo ta rungume, har yanzu k'anshin bai bar hancinta ba, tunanin yadda rayuwarsu zata fara ta tsunduma, a haka har bacci yayi awon gaba da ita. Bata farka ba sai wurin sha d'aya, ta sha wankanta tare da tsantsara kwalliya, kwata-kwata ta manta da batun SS, wanda ya kamata ace ta bashi breakfast tuntuni. Da sauri ta wuce kitchen ta fara kalle-kalle dan bata ma san mai zata fara ba. Wata dabara ce ta fad'o mata, ta koma daki da sauri ta dauki wayarta, ta kunna data ta shige whatsapp. Group dinsu na Ladies Domain ta leka, dan ta san can ne kawai zata samu recipe cikin gaggawa, cikin sa'a kuwa taga Yasmeen ta turo recipe na Omalet Sandwich. A gurguje ta karanta, ta tashi ta koma kitchen ta bud'e k'atuwar deep freezer dake girke, ga mamakinta ta samu fresh kayan miya, bata b'ata lokaci ba ta ciro albasa, attarugu da tumatir, dai-dai buk'atarta, ta yayyanka, sannan tasa oil kadan a pan, ta zuba kayan miyar ta saka spices ta soya sama-sama, ta ajje gefe. Egg and milk ta had'a wuri guda, ta kada, suka had'u sosai sannan ta fito da toaster, ta fara zuba soyayyun kayan miyar a kowanne column, daga bisani ta zuba k'wan, ta rufe, sannan ta jona ruwan zafi a kettle. Cikin 'yan mintina ya gama yi, ta kwashe a warmers, ta had'a kayan tea a tray ta hada ma SS nashi, ta dauka zuwa sashen da ta tabbatar nan ne nashi. Da sallama ta tura k'ofar ta shiga, palon shiru babu alamar mutum, sai k'aran television kawai, ta isa ta ajje tray a dinning table, ta juya ta fito. Ta dawo ta zauna ta na cin1 nata abincin. ***** Har kusan k'arfe biyu bata ji motsinshi ba, har ta gama hada lunch, ta dauka ta kuma shiga part d'in ta zarce dinning, amma yadda ta ajje na safe haka ta same shi, sai ta ji wani iri, amma ta maze ta d'ora wanda ta shigo da shi, ta kwashe wancen ta koma ta kwanta, dan abincin ma kasa ci tayi tana tunanin abinda ya hana shi cin nashi abincin. Wayarta ta d'auko ta fara dialling number sa, dan ya fara bata tausayi, haka kuma ya kamata ace ta sassauta horon da take bashi. Ta kira har ta gama ringing bai daga ba, ta tashi ta koma palonshi, ta zarce bedroom, duk ta duba har toilets, amma baya nan. Dakin ta kakkabe ta gyara komai a wurinshi, sannan ta fito jiki ba k'wari ta koma dakinta ta kwanta ta rasa me ya kamata ta yi a lokacin. Har aka yi maghriba aka yi isha'i amma bata ji alamar dawowarsa ba, ta kira shi ya fi a k'irga nan ma bashi da niyyar dagawa. Har goma tayi, ta gaji da yi ma bakin da ke zuwa ganinsu karya, ta kuma ga ji zama a palon, mikewa ta yi ta wuce d'aki tayi wanka ta shirya kanta, amma zuciyarta sam babu dadi, babban abinda ke damunta shine yadda ko gaishe da shi bata yi ba da safe. Haka ta kwanta sukuku, sai can wurin sha biyu, sannan ta ji shigowar motarshi, ta tashi ta lek'a ta window tana kallonshi. A idonta ya shigo cikin gidan ta koma ta kwanta tana tunanin may be zai shigo ya duba ta. Shiru-shiru bata ji motsinsa ba, ta fara latse-latsen wayarta, har sai da ta ji cikinta ya fara kuka sannan ta tuno da rabonta da abinci tun breakfast, a kasalance ta mik'e, ta zari rigarta da ke gefe ta dora a kan 'yar k'aramar nighty din jikinta ta fita zuwa kitchen. *** Yana shiga ya hangi jerin warmers saman teburi, ya isa da sauri ya bude, kamshin abincin ya daki hancinsa, duk da ba yunwa yake ji ba amma sai da ya ji marmarinshi, haka dai ya daure ya rufe, ya wuce ciki. D'akin ma a gyare tsab-tsab ya gani, take murmushi ya kwace mishi, ya fad'a gadon, zuciyarsa cike da son ganinta, amma ba zai iya jurar wulak'anci da k'yamar da take nuna mishi ba. mikewa yayi zuwa wanka, ya fito ya shirya cikin farin dogon wando Nike marar nauyi, da armless shirt dinsa, ya baza turarenshi, ya koma kan gadon ya kwanta, zuciyarsa na wani irin bugawa, shauk'in so da son ganin fuskarta na neman ya dagula lissafin k'wak'walwarsa. Juyi kawai ya ke yana tunanin yadda zai iya bacci ba tare da ya ganta ba, ko ba komai hak'k'inshi ne ya tabbatar da tana cikin k'oshin lafiya kafin ya kwanta, hakan yasa ya mik'e tsam, ya d'auki key ko da zai ci karo da k'ofar a rufe, cikin sand'a ya isa ya murd'a k'ofar a hankali, ga mamakinshi ya ji ta bud'e, sad'af-sad'af ya shige ciki, ya mik'e zuwa d'akinta. K'ofar a bud'e ya same ta, cikin mamaki ya tura kanshi, sai dai babu kowa, illa wayarta da ke ajje kan bedside locker, da duvet din da aka tattare wuri guda alamar mutum ya tashi a wurin. Bakin gadon ya isa ya zauna, duk a zatonshi tana toilet, ya mik'a hannu ya d'auki wayarta, ya latsa gefe, yayin da haske ya bayyana jikin screen din, inda ya ci karo da pic dinsu na dinner kwance saman screenlock dinta. Da mamaki yake kallon pic din, a zahiri bai san sa'adda aka d'auke shi ba. Ta wani bangaren yana jin dama-dama, hakan na nuni da akwai yiwuwar soyayyarshi a k'asan zuciyarta. Murmushin da ke fuskarsa ne ya k'ara fadada, a hankali yake shafa setin fuskarta yana kara yi ma Allah godiya da yasa ta zama mallakinshi. K'aran fashewar abu da ya ji, shi ya dawo da shi daga dogon tunaninsa, ya juya da sauri, suna hada ido ta fashe da wani irin kuka tana yarfe hannu. Cikin razana ya isa gabanta, ruwan zafin da ke cikin mug din ya fallatsu a jikinta, da sauri ya kai hannunsa setin wurin, kamar tana jira ta fad'a jikinshi ta cigaba da rera kukanta. "I'm sorry Angela, garin ya kika 6arar da ruwan zafi haka a jikinki?" Dagowa tayi tana tura baki, a lokaci guda ta dora hannunta a kirjinshi; idanuwanta cike da hawaye tace "Ba kai ne ba."1 Dariya ma yadda tayi din ya bashi, amma ya gintse, ya kwantar da ita sosai a jikinshi, yana shafa bayanta a hankali, cikin rada yana fad'in "Maganin mai tsiwa kenan." Kuka ta sake fasawa, ta fara mutsu-mutsun kwace jikinta, amma yayi mata rikon da duk wacce aka yi ma irinshi dole ta shiga taitayinta. Rigarta ta sama ya zare, a hankali ya dago da kanta, shiru tayi tana ajiyar zuciya, ya kama hannunta ya zaunar a bakin gado, sannan ya fara tattara wurin da mug din ya fashe, ya fita ya d'auko mop ya goge, duk tana kallonshi, sai da ya gama tsab ya dawo ya zauna a gefenta ya mik'a hannunsa ya dora a kan nata. "Me sa baki bacci ba?"1 Shiru tayi, hawaye suka ciko idanunta, ta matsa daf da shi, ta kankame shi tana fad'in "I'm so sorry please Ya Sadic. Ka yafe mun dan Allah, kuma kada ka k'ara bari na ni daya ka ji?"1 Wani irin yanayi ne ya ke ji a tare da shi, farin ciki, da jin dad'i ne suka kai mishi ziyara a zuciya, a hankali ya ke matsawa setinta, yana jin yadda take kwantar da duk jikinta a kafadarshi, hannu ya sa ya k'ara had'e ta sosai da gaba daya jikinsa, kafin ya tura hannayensa a tsakanin gashinta. Idanunsa a lullube, yana jin saukar duk wani numfashi da zata ajje, yana jin yadda kauna da shauki soyayyarta ke razanar masa da zuciya, muryarsa a kaikaice ya seta bakinsa a daidai kunnenta ya ke fadin "Me sa ba zan ba ki space ba? Bayan na san kina da wanda kike so Angela." Da sauri ta sa hannu ta na toshe bakinshi, idanunta taf da hawaye ta ce "Kana so Allah yayi fushi da ni ko? Ni bani da kowa duk duniya in ba kai ba. I love you with all my heart." "But me sa kika rink'a punishing dina da yawa? Me sa kika ce baza ki iya zama da ni ba?" "Ka manta laifinka ko? And kaima kasan babu wanda ya cancanta da rayuwata bayan kai, is just that I wanted to punish you. I'm so sorry sweetheart." Ajiyar zuciya ya sauke, dago ta ya yi yana kallon cikin idanunta, itama shi din take kallo, yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, kafin ya maida ta cikin jikinsa, a cikin kunnenta ya ke fadin "I'll always love you Angela. You're my better half. Zan kula da ke in baki farin cikin da baki taba samun irinshi ba, I'll in sha Allah be the best husband to you. I'll make you the happiest woman on earth, nd will make sure that every woman is jealous of you. I love you so so very much Jameela. I love you." Hawaye take jin suna zubo mata a dai dai lokacin, wanda ta rasa gane ko na meye, domin a zahiri yau ita ce rana ta farko da take jin ta comfortable in someone's arm, take jin duniyarta na tafi mata dai-dai da yadda take so, take kuma gaskata ko wacce kalma ta fito a bakin Sadic. Idan har zata iya fassara abinda take ji, to baya wuce tace soyayyarta da Kazaure soyayya ce da suka gina bisa son zuciyarsu, domin tunda take da shi bata taba jin yanayin da take ji ba, kamar yanzu da take tare da SS. Fuskarta ya d'ago, ya saita hancinsa a kan nata, yana kallonta labbansa kunshe da murmushin birgewa, sannu a hankali idanunsu suka fara kullewa, a lokaci guda ya dora labbansa saman nata ya fara kissing dinta cikin wani irin salo wanda shi kadai ya san sirrinshi. Wani irin SABON SALON soyayya SS ya shiga nuna mata, k'auna ce zalla, wacce babu mix hakan ya k'ara masa wata daraja da k'ima a idanuwanta, ta kuma tabbatar da k'aunarshi halitta ce a cikin ruhinta, wacce ta fi k'arfin a kira ta da SO wanda zai iya tashi daga wannan bishiyar ya koma wata, ta kuma tabbatar da son da take yi ma Kazaure ba komai ba ne, illa kasancewarshi namiji na farko da ta fara so a duniyarta, amma a zahiri, k'auna mai cike da shak'uwa ba kowa take yi ma ita ba bayan Abbakar Sadic Galadima. **Three Months Later** Cikin natsuwa ta mik'e daga seat din da take zaune lokacin da lecturer'n ya fita, hannu ta saka cikin jakarta, ta fito da pale purple din abayanta, wanda ya wadatu da kyawawan duwatsu, ta d'ora saman black and white uniform dinta, kafin ta fara takawa a hankali, tana fita daga theatre hall din da suka gama lecture. Kasancewar ranar juma'ah yasa ta fara takawa da dan sauri, dan ta san mijinta na hanyar zuwa Katsina a day dai irin lokacin. Tana fitowa gaban faculty ta ciro car key dinta, tayi unlocking motar daga inda take, ta cigaba da takawa cikin sassarfa har ta iso wurin da tayi parking. Ba tare da wata damuwa ba ta bude motar ta shiga, ta juya da zumar ajje handbag dinta a seat din da ke gefenta, tayi arba da doguwar fuskarsa ya zuba mata wadatattun idanunsa, yana tallabe habarsa da duk hannuwansa yana kallon ta, labbansa d'auke da hamshakin murmushi. Hannu tasa ta murje idonta, hakan da tayi ya sanya shi sakin dariya, ya maida hannunsa a kan idanunta ya kulle, a hankali ya fara waige-waige, ya tabbatar da babu mai kallonsu, ya matsar da fuskarshi daf da nata, yayi pecking kumatunta kafun ya bude idon nata yana fad'in "Kin yarda ba mafarki kike yi ba yanzu?" "Oh Allah! You scare the hell outta me Ya Sadic. Yaushe ka iso nan? Saurin da nike in isa gida in isa in shirya maka abinci, ashe har ka riga ka iso." "To ya kike so inyi? Kin ko san a takuren da nike rayuwa cikin five working days din da bana ganinku? Daurewa kawai nike yi Angela." Hannunta ta dora a kan nashi da ke ajje tsakanin seat dinsu, a hankali take murza dogayen yatsunsa, daga bisani ta d'ago su ta had'a da labbanta, ta sumbace su a hankali, sannan ta maida kallonta gare shi.2 "You've no idea how much I missed you. Sai dai babu yadda zamu yi, and I believe sooner or later, we'll be together forever. I mean no more long distance." Idanunsa a lumshe yana sauraren ta, yana murmushi, a hankali ya bude su, ya kalle ta yace "So I believe Angela, sai sa nike ta neman transfer, idan ma ban samu ba aikin kawai zan ajje in dawo gida in cigaba da business, ina kallon matata." "No mana, let's just pray for the best." Ta k'ara matse hannunta cikin nashi tana kallon idonsa bakinta d'auke da murmushi. "As you said Hun. Now, start the car." "And what about you?" "i mean be my driver for the second time." "And.. motarka?" "Yana wurin Farouq, dama shi yayi dropping dina a nan, tunda naga motar matata nace yaje kawai na samu sabon driver kuma." Dariya tayi mai d'an sauti tace "Wato ka samu driver?" "Ehhhn now. Let's go." Kallon yadda ya kwantar da seat dinshi take, yayi baya ya kwanta tare da tallabe kanshi da hannayenshi, idanunsa a lumshe, dogayen eye lashes d'insa sun kwanto, hakan ya k'ara k'awata santalar fuskarsa mai cike da yalwar gashi. He look damn cute and adorable. Ta sa hannu ta shafi gefen fuskarsa, da murmushi mai kayatarwa a a bakinta, ta juya tana k'ok'arin tada motar taji ya rik'e hannun nata, yana kallonta. "Just kidding Queenie. Wane ni in sanya Queen driving?" "It's nothing ai, as you're the King here." Da murmushi ya fito ya zagaya ya bud'e ta, hakan yasa bata yi gardama ba, ta zira kafafunta waje ta fita, ya d'auke handbag dinta dake ajje, ya rataya a kafadarsa, ya bita a baya ya bud'e mata other side din. Sai da ta shiga, sannan ya rufe, ya bud'e baya ya saka jakar, ya zagaya ya shiga, ya tada motar suka fara tafiya, hannunsa daya rik'e da nata, d'ayan kuma yana juya steering, har suka fito cikin gari. School d'in su Jafar suka tasan ma, dan lokacin tashinsu ya riga yayi, suna isa suka hange su zaune kasan canopy din da yara ke zama dan jiran masu daukarsu, da gudu suka rugo ganin Daddy da Mammynsu a tare. Rukayya ya fara dagawa sama dak'yar, dan ta k'ara zama 'yar lukuta, ya juya ta sosai, tare da pecking gashinta yana fad'in "Daddy's girl ta zama big girl, ehhn." Tana dariya, ya ajje ta, ya isa ga Jafar da ya matsu turn d'insa ya zo, instead of ya daga shi, sai ya mik'a mishi hannu yana fad'in "Salamu Alaikum Bigbro." Dariya ya saki, ya miko da nashi hannun "Wa alaikumus Salam Daddynmu. Yaushe ka dawo?" "Ban dade da zuwa ba. And i thank God, ka yarda ka zama big bro. Ya skool nd your lil sis? Kuna karatu dai ko?" "Sosai ma Daddy, ka tambayi Mammy ka ji ma, har koya ma Rukayya nike yi." "Ba wani nan Daddy, nima ina koya mishi ai. Ko Mammy?" Rukayya ta yi saurin fad'a tana kallon Jay da tayi folding hannayenta ta zuba musu idanu. Dariya SS yayi, ya kama su a both hannayensa, yana tsakiya suka fara fita school gate din, sai da suka shiga mota yace "Yau zan ga wanda ya fi wani idan mun koma gida ai." Ta bayanshi Rukayya ta ziro hannayenta ta kankame wuyansa, tana murna tace "Yawwa, zaka ga yadda nike koya ma Ya Jafar Maths Daddy, kullun sai Aunty ta k'wala mishi ruler saboda bai iya ba." "Rukayya!" Jay ta fada tana kallonta. "Ya kike holding wuyan Daddy kuma? Ba ki ga driving ya ke ba ne? Maza sake shi ki samu wuri ki zauna. kina ji na ba?" Ta karashe tana kama hannunta, ta zaunar da ita gefen Jafar da ya cika fam, kamar zai fashe saboda Rukayya ta tona asirin bai iya maths ba. Dariya SS ya saki lokacin da ya hangi fuskarshi ta madubin da ke gaba, hakan yasa ya kuma had'e rai yana shirin fara kuka. "Oh no handsome, don't please. Kai da zaka zama lawyer me ya yi hadinka da Maths?" Jay ta fad'a tana shafa kyakkyawar fuskarsa, a take, bai san lokacin da ya saki dariya ba, "Haka ne Mammy, ita kuma ta zama Banker irin Daddy, a kaita aiki Maiduguri, ni kuma ina tare da ke a gida." "Yes now, mr handsome. High five.." Ta bashi hannu suka tafa, suna yi ma Rukayya gwalo. Kallonsu tayi, ta juyar da kanta, idan da sabo ta saba da halin Jafar da Mammy, bata ce komai ba har lokacin da suka iso gida. Suna shiga bata tsaya yin komai ba, ta cire uniform dinta, ta canja zuwa wata turquoise blue din armless gown, ta had'a gashinta wuri guda ta daure, ta fito kitchen inda ta samu Ummilo yar matashiyar dake taimaka mata da ayyukan gida, suka fara k'ok'arin had'a girke-girken da ta san sune fav din mijinta. Chicken ta fitar daga fridge zata wanke, Jafar ya shigo da gudu, yana maida numfashi ya labe a bayanta, Rukayya da ke biye da shi ta k'arasa shigowa tana fad'in "Wallahi sai na rama ni ma." Towel ta janyo ta goge hannayenta, ta kama shi ta k'ara boyewa a bayanta, sannan ta juya tana kallonta. "Ke kam kin cika fitina, ina kika taba ganin lil sis na dukan big bro dinta?" "Mammy shine ya ja ni fa." "Wai haka handsome?" Ta juya tana kallon Jafar da ke baza idanu. "Ba wani nan fa Mammy, in haka ne ta nuna igiyan da na ja ta da shi mana."1 Dariya Jay ta saka, dan ta san kwana yayi. Ta duk'a ta dafa kafadarta "Kiyi hak'uri Daddy's girl, in sha Allah ba zai k'ara jan ki ba." Da kuka ta juya tayi part d'in SS, yayin da Jay ta juya ta kamo shi suka fito "Handsome ka cika jan fad'a, ga shi kai kuma ba k'arfi ba." Dariya ya saki yace "Mammy kina ganin Rukayya yar lukuta ina zan tsaya ta kama ni."1 Tare suka saka dariyar, suka wuce ta shirya shi domin zuwa masallaci da Daddynsu. Sai da suka fita kafin ta samu natsuwar yin aikinta a tsanake, cikin dan lokaci suka gama shirya komai, sannan ta yi ma Rukayya wanka ta shirya ta cikin powder blue din gown, ta gyara mata dogon gashinta, ta kalle ta tana murmushi, hakan ya k'ara fito da kamarta sosai da babanta. "Wuce ki jira dawowar su Daddy, nasan gidan Hajiya suka tsaya gashi har la'asar ta kusa." Tayi saurin kawar da tunaninta, ta mik'e ta wuce toilet. Sai da ta d'auki kusan mintuna talatin tana wanka, ta fito tayi sallah, sannan tayi zaman dirsham a gaban mirror ta fara tsantsara gayu, dan yanzu ta zama expert wurin kwalliya, ta lura kwalliya na daya daga cikin abinda SS ke sha'awa, hakan yasa ta zage, ta koya. Ta gama shafe-shafenta ta mik'e ta bude wardrobe dinta, wani lallausa lace ta fitar, kalar aqua blue da ratsin gold, dinkin skirt and peplum blouse, sosai yayi asalin dacewa da kyakkyawar k'irar jikinta. Ta murza saurin da ya kawatar da surar fuskarta, kafun ta fara wanke jikinta da kalaluwan perfs dinta da ke zube saman mirror, sannan ta saka gold din givenchy slippers a k'afarta, ta fito zuwa palo. Ummilo ta hango a kitchen tana ta faman goge-goge, ta isa ta same ta, tana fad'in "Sannu Ummilo, ina kika ga Rukayya ta shiga? Ban ganta a parlour ba." "Yawwa Hajiya. Ina ga tayi waje, dan na ji kamar k'aran bude gate, kila Babansu ne ya dawo." Ummilo ta fad'a tana sosa kai, irin na ladabin 'yan aiki. "Ok, yi ki k'arasa ki zo ki wuce gida kema." "Na gode Hajiya." Ummilo ta dan rissina, yayin da Jay ta fara kwasar warmers tana fita zuwa part d'in Boss. Ta gama jera komai a dining table din, ta juya tana ciro cups daga cupboard ya shigo, a hankali ya isa ta bayanta, ya k'ura mata ido yana kallon irin kyawun da tayi. Tana juyowa idanunsu suka had'e cikin na juna, kafin ya yi karfin halin sakan mata murmushi tare da anshe cups din ya mik'a hannu ya dora kan table, yana tallabe da bayanta da d'ayan hannunsa. Juyowa yayi, yayi holding dinta very tied, hannunsa zagaye da waist dinta, ya lumshe ido yana shakar hadadden kanshinta, wanda a jikinta kawai yake jin irinshi. A hankali ya bud'e idonsa, ya isar da fuskarshi jikin nata, ya had'e kan su wuri guda, cikin wata lallausar murya ya fara yi mata wata salon magana wacce tafi kama da rada. "Ina sonki Angela. And everything about you is driving me crazy. A kullun ina gode ma Allah da ya mallaka mun ke. I so much love you hunnay." Ya had'a bakinsu a lokaci guda, hakan yasa ta tsinci kanta da zagaye wuyansa da hannayenta, idanunsu a rufe, tana jin wata sabuwar k'aunar mijin nata na ratsa ko wanne lungu na jikinta, she's very excited to have such a caring and romantic husband, who's willing to sacrifice everything for the sake of her love. "I love you so much Darling." Tayi whispering a setin kunnenshi idanunta a kulle tana feeling warm body temperature dinshi. Alamar tahowar 'yan biyun sararinsu ne ta katse musu best moment dinsu, ya sake ta da sauri ya ja kujera ya zauna yana kallonta, bakinshi d'auke da 'yar dariya. Dariyar ta sake itama, ta juya ta k'arasa fito musu da cups, da gudu yaran suka bud'e k'ofar suka shigo, suka yo kan SS da ke zaune yana dariya. "Haba mana handsome, kai fa big boy ne, ka daina biye ma 'yar lukutar nan kuna gudu kada wani ya fad'i ka ji?" Jay da hannunta ke rik'e da plates tana jerawa a gabansu, tayi maganar, tare da shafa kan Jafar lokacin da ta iso kujerarshi. "Ni fa ba ruwa na Mammy, shine ke gudunshi amma sai kice nice." "Manta da su Daddy's girl, ke da ma zan siya ma ice cream banda su." "Can maku dai, muma muna da kudin siyen more than ice cream. Yarinya sai guje-guje kamar 'yar wrestling." Suka kwashe da dariya ita da Jafar, lokacin da ta zauna ta gama serving dinsu, sannan suka natsu, suka fara cin abincin. Suna gamawa, Jay ta fara tattara plates din zuwa kitchen, ta tarar Ummilo har ta tafi, dole ta tsaya domin wanke su da kanta. Jin shiru bata dawo ba yasa SS ya baro yaran ya biyo ta, inda ya same ta tsaye gaban dishwasher zata fara wanke plates din. Ta bayanta ya iso ya had'a ta da jikinshi, ya dora fuskarsa a kafadarta, tare da zira hannunsa, ya ansa sponge da ke hannunta, ya fara wankewa tana d'aurayewa, a gefe guda yana sinsinar k'anshin wuyanta, tare da jaddada mata irin muhimmancin da take da shi a duniyarshi. Shiru tayi, tana saurarensa, a wani bangaren tana mamakin wane irin so SS ke yi mata? Alal hakika sai dai ta nemi wani abun, Amma ta bangaren rayuwar aurenta, babu wani abu da tayi lacking, duk wata soyyaya ta duniya babu kalar wacce bata samu daga mijinta, haka ma kula da tattali, irin wanda ko wacce mace ke mafarkin samu a rayuwar aurenta.1 "Alhamdulillah." Ta furta cikin siririyar muryarta, a dai-dai nan suka gama wanke plates din, ta juyo gaba dayanta, tana kallonshi. Kafin ta buda bakinta ta ji wani abu ya taso daga cikinta, yana shirin fitowa daga bakin. Da sauri ta sake shi, tana sa hannunta a baki, tana toshewa, kafin wani cikinsu yayi motsi, gaba d'aya abincin da ta ci ya dawo ya wanke farar shaddar da ke jikin SS.2 Jaaaaaay🤣🤣🤣🤣🤣 Da sauri ya rik'e ta, har ta gama, kafin ya fara tambayar+ "Are you okay?" "I'm fine." Ta fad'a dak'yar, ya kama hannunta suka wuce toilet, bai damu da yadda jikinshi ya baci ba, ya taimaka mata ta gyara nata jikin, sannan suka fito ya kwantar da ita a kujera, ya shiga rage kayan jikinsa. Kitchen ya koma ya gyara wurin da ya baci, kafun ya fito ya same ta hannunta dafe da kanta, idanuwanta a lullube. "I'm sorry Angela. Me ke damunki please?" Ya k'arasa yana taba wuyanta, sai dai babu alamar zazzabi. "Headache?" Ya k'ara tambaya hankalinshi duk a tashe. Ganin haka yasa tayi k'arfin halin tashi zaune, ta samo murmushi ta dora a fuskarta. "Never mind. May be abincin da na ci ne bai kwanta mun ba. But I'm fine." "Are you sure?" Ya tambaya fuskarsa cike da damuwa, kamar mai shirin yin kuka. "I'm Sweedy." Ta mik'a hannuwanta ta dora a kafadunsa, tare da tallabo kanshi, ta dora fuskarta saman forehead d'insa, tana kallonshi da murmushi. "Alhamdulillah." Ya fad'a a bayyane, tare da zagaye hannunshi a kanta, yana lumshe idanu. Dakyar ta mik'e tana jin jiri na dibarta, ta shiga ta had'a mishi ruwan wanka, sannan ta dawo ta kwashi kayan da ya cire, ta kama hannunshi suka wuce bedroom, ta cire towel ta mik'a mishi, ya ansa ya daura, kafun ya shige wankan. Kayan hannunta ta saka a laundry basket, ta bude jakarta ta fito da PTstrip din da ta siya jiya tana dawowa school, kasancewar sati biyu kenan da ya kamata ace taga period dinta, amma bata gani ba. D'akin da ke opposite inda ya ke ta shiga tayi amfani da strip din ta fito, ta barshi a can, kafin ta dawo ta cire mishi kayan da zai saka idan ya fito. Tsab ya gama shirinshi, suka fito hannunsu cikin na juna zuwa part d'in shi. Kamar kullun suka samu Rukayya da Jafar sai tsalle-tsalle suke, sai da suka ga shigowarsu, sannan suka natsu suka yo kansu da gudu. "Daddy tafiya zamu yi?" Rukayya ta tambaya tana kama hannunsa. Sai da ya zauna kasar carpet, ya tank'washe k'afafunsa, ita kuma ta haye kansa yana shafa gashin kanta a hankali yace "Ba yanzu ba Rukayya, sai zuwa anjima dai." "Daddy ice cream din fa?" Bakinta a kunbure tayi maganar idonta cike da k'walla. "Oh no, c'mon Daddy's girl, don't be mad. Ok? Zan kai ki but sai anjima. Kinga yau Juma'a ne, ya kamata muyi wani abu da Allah zai yi farin ciki da mu daddare kuma sai in kaiki ki sha ice cream ko?" "To me zamu yi ne yanzu?" "Karatun Qur'ani mana. Ke dama baki iya ba." Jafar ya fada yana kallonta. "Inji waye to? Ai dai na iya ko Daddy na?" "Ba wani kin iya, in kina so mu yadda sai ki karanta muji." Jay da ta k'araso da tray din juice da cupcake ta fad'a, kafun ta ajje a tsakiyarsu, ta koma gefen Jafar ta zauna, tare da lankwashe kafafunta itama, irin zaman da suka yi. Da sauri suka yi bismillah suka fara karatun, tun suna yi ana musu gyara, har ya kai suma iyayen sun saka bakinsu sun cigaba da yi a tare. Sai da suka kai suratul mutaffifin sannan suka yi shiru, domin a nan suka tsaya a islamiya, su Jay ne suka cigaba har An-Naba' sannan suka yi addu'a suka shafa. Rayuwar tasu gwanin ban sha'awa, cikin natsuwa da tsabta, tare da kare hakk'okin addini, a cewarta baza tayi sakacin da iyayenta suka yi ba wurin tarbiyyantar da nata yaran. Cake d'in da ta ajje suka fara ci, amma banda ita, ta mik'e ta wuce d'aki domin duba result dinta. Cikin matsananciyar murnar da bata san adadinta ba, ta rungume strip din ta ruga da gudu da shirin fad'i ma SS, sai dai wata zuciyar taji tana shawartar ta da ta fad'a mishi in a romantic way.2 Murmushi tayi, ta koma tayi disposing abun, lokacin an fara kiran sallar maghriba tana fitowa ta ci karo da Rukayya da ta falfalo a guje ta shigo. "Ya Allah. Rukayya wai yaushe zaki hankali? Ina yarona?" "Sun je masallaci da Daddy." "Muje muyi sallan muma ko. Amma dan Allah ki rink'a natsuwa, kullun cikin gudu kike fa" Ta rik'e hannunta suka wuce ciki, zuciyarta cike da wani irin farin ciki, marar misaltuwa. A duniya ta na son yara. Tana son ta gansu suna yawo a tsakiyar palon ta, ta kalle su da murmushi, ta tabbatar duka nata ne. *** Suna gama sallar isha'i suka fita gaba dayansu, Kalam-wahid shopping mall suka nufa, SS na tuk'i amma hankalinsa gaba d'aya, yana kan Jay da ke zaune gefenshi, ya kama hannunta ya rik'e cikin nashi, fuskokinsu na bayyanar da sirrikan da ke cikin zukatansu.1 "What's the event?" Ya tambaya yana matso da bakinsa dai-dai kunnenta, yayi maganar yadda yaransu da ke baya baza su taba jin me ya fad'a ba. "Me ka gani?" "You look exciting. Shine nike son kiyi sharing moment din da ni." "I must be, tunda ina tare da kai. This is the event." Ta dago hannunshi da ke rik'e da nata, tana signing mishi da idonta. Murmushi yayi, a fakaice ya kai kallo ga yaran da suke ta wasansu, ya d'ago hannun nata yayi pecking, yana mata wani irin kallo, wanda a duk lokacin da ta ci karo da shi take tsintar kanta cikin mutuwar jiki. A dai-dai nan suka iso wurin, ya gyara parking duk suka fito, kafun ya shiga tsakiyar yaranshi, ya kama su da hannayensa suka wuce ciki. Sun kwashi kusan mintuna talatin a wurin, suka fito da kayan da suka siya, suka saka a boot, kafun suka karasa gidan Baffa. Zaune suka same shi shi da Goggo a palonshi, da gudu su Jafar suka isa suka fada kanshi, Jay da SS da ke biye da su, suka karasa shigowa da sallama a bakunansu. "Haba mana so kuke ku k'arasa dan tsohon nan ne? Ku daga ni ku je ga wata kujera can mai laushi. Ta fini k'wari." Yayi maganar yana nuni musu da Goggo da ke fuskantarsu. Dariya duk suka saka har ita, suka k'araso ciki suka zauna tare da gaishe da su. Kallonsu Baffa yake cike da birgewa da sha'awa, haka ma Goggo zuciyarta ta samu natsuwa ganin yadda rayuwar tilon 'yarta ta samu canji cikin dan lokaci. Sun jima a nan, kafun suka musu bankwana suka tafi. Ko da suka kai gida su Jafar har sunyi bacci, SS ne ya d'auke su d'aya bayan daya ya shigar da su ciki, Jay ta canja masu kaya zuwa na bacci, ta kai kowannensu dakinshi, ta tofe su da addu'a sannan ta fito. Bata ganshi a palon ba, sai kawai ta wuce dakinta domin yi wanka. Jakar da ke hannunta ta zubar saman gado, ta d'auki wani abu ta isa gaban wardrobe d'in SS, inda kayan baccinsa ke ciki, ta ajje a hankali tana murmushi, kafun ta rufe, ta cire kayanta ta wuce toilet din da ke cikin dakin. Tana gamawa ta fito ta shirya cikin olive green din silky nighty, ta tattara gashinta wuri guda ta daure da dan k'aramin ribbon, sannan tayi wanka da perfs, masu sanyin kanshi, ta tsaya tana kare ma kanta kallo, a lokaci guda tana shafa cikinta, she just can't believe it. Jin tafiyar SS yana kusanto d'akin yasa tayi saurin tattare kayanta da ta zubar saman gado, ta boye jikin labule tana kallon shigowarshi. A tsanake ya tura k'ofar ya shigo, kanshin turarenta ya sanya shi lumshe ido, ya bud'e amma bai ganta ba. Gaban wardrobr dinsa ya isa, yana budewa ya ga d'an k'aramin abu, an wrapping da sheet, take ya sake kyakkyawan murmushi, ya dauka ya zauna a kujerar da ke gaban gadon, ya fara budewa. Baby's shoes ya gani masu kyau, had'e da paper da ta fad'o daga ciki, ya duk'a ya dauka ya fara karantawa. "I love you so much Ya Sadic. And I know you'll be the best father a child could ever have." Murmushin da ke fuskarsa ya k'ara fadadawa, yana tambayar kansa me hakan ke nufi? Bai ida rufe bakinsa ba ta bud'e labulen da ta boye ta fito, a cikinta ta saka katon balloon da ta busa, hannunta rik'e da plain sheet da aka yi rubutu jiki, ta seta hannun a dai-dai cikinta. Cikin matsanancin farin ciki ya iso gabanta, da sauri ya duk'ar da kanshi setin cikinta, yana shafa katon balloon din da ta dora tare da karanta rubutun da ke jikin takardar. To Mr. & Mrs Galadima, I'm sorry it took me kinda late to get here...8 "Yaa Allah! Is this for real Angela?" "Ehhhhn now!" Ta girgiza kanta bakinta kunshe da murmushi mai kayatarwa. Hannunta ya rik'e yana jin dad'i, ya rasa me zai yi ya nuna farin cikinsa. Kallonta kawai yake, idanunsa sun fara wani shining da alamar kamar ruwa a ciki, ya bud'e baki zai yi magana, ta had'a lips dinsu, tana mai zagaye hannunta a bayanshi. Hakan ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya had'a ta sosai da jikinshi, a zuciyarsa yana yi mata addu'a da neman kariya daga ko wanne irin sharri. Sun dade a haka, sannan ta sake shi, ta fito mishi da pjs kalar sea green, ta wuce had'a mishi lipton, wanda ya kan sha a kowanne dare. Lokacin da ta dawo kwance ta same shi ya rungume baby's shoes din da ta saka a kayanshi, idanunsa a lullube, da alama yana jin soyayyar babyn tun bai iso duniya ba. Sai da ta kare mishi kallo, sannan ta dora mug din da ta shigo da shi kan bedside locker, ta isa ta zauna gefenshi. "Tashi ga tea dinka Ya Sadic." A sannu sannu ya bud'e ido, ya sauke a kanta, bai ce komai ba ya janyo ta jikinshi, ta kwanta shiru, ba wanda ke magana cikinsu, bayan wasu 'yan mintuna ya mik'a hannu ya kashe fitilar da ta haskaka d'akin. ***Sadam. Sautin karatun al-Qur'ani mai girma ne ke tashi cikin k'ira'ar Sheikh Ahmad Sulaiman, yayin da Sadam ke zaune hannunshi rik'e da goran ruwa yana shirin saka magani a bakinshi, Saheeb ya tura k'ofar dakin ya shigo. Maganin da ke hannunsa ya k'arasa sakawa a bakin, ya kora da ruwa, sannan ya d'ago a hankali yana dubanshi.1 "Ya aka yi?" "Dama Ya Sa'id ne yace in zo in tabbatar idan ka sha maganinka." Murmushi yayi, wanda iyakacinshi fatar baki, hakan ya k'ara bayyanar da tsantsar ramar da fuskarsa tayi, ya ajje ruwan hannunsa a gefe, ba tare da yace komai ba. "Yace idan ka gama ka zo akwai maganar da zaku yi." "Ta me fa?" "Wallahi ban sani ba. Haka dai yace in fad'a ma." "Alright, ka je gani nan fitowa." Ya komar da kanshi jikin kujera ya jingine, tare da lumshe idanunsa, yana jin dad'in yadda karatun ke ratsa ko ina na jikinshi, yana zarcewa mishi har kasan zuciya. Mikewa ya yi, kafun ya ja remote ya latsa, ya mik'e ya fita kiran da Sa'id ke mishi. Yayyenshi guda hudu ya samu zaune a palon, ya isa ya mik'a ma kowannensu hannu suka gaisa, sannan ya tattare jallabiyar jikinsa, ya zauna a d'aya daga kujerun wurin. Shiru na 'yan dakiku ne ya wanzu a palon, daga bisani Sa'id yayi gyaran murya ya juya yana fuskantar shi. "Sadam." Ya kira sunanshi cikin natsuwa, da muryar da ke nuni da dattako, da kuma tausasawa. "Na'am Yaya." "Wato a gaskiya na gaji da ganinka cikin halin nan da kake ciki, saboda nayi believing depression yana k'ara tension ma mutum, yana hana zuciya da gangar jikin mutum su samu natsuwa. Haka ne?" Ya tambaya yana kallonshi. "Haka ne." Salis ya bashi ansa da sauri, inda shi kuma ya cigaba. "You need to move on Sadam, tun baka k'arasa kashe rayuwarka ba. Ka rungumi k'addararka, ka canja tsarin da kake shirin jefa kanka a ciki." A hankali ya d'ago yana kallonshi, take zuciyarsa ta tsinke, amma ya daure yace "Yaya ai na dade da yadda da irin k'addarar da Allah ya dora mun. Me sa kake magana haka?" A takaice Sa'id yace "Ka samu wata matar ka fara sabuwar rayuwa, wannan ne kawai zai tabbatar mun da cewar ka yarda da k'addararka." Murmushi yayi mai zafi. Domin bai san abinda zai ce a wannan gabar ba. "Wato dariya ma abin ya baka ko?" "No, ban san me zan ce bane Yaya, kuma ni a yanzu babu wata mace da zan iya kallo ince tana birge ni." "To ni na samo maka, kuma bana son wani dogon bayani, ka ansa mun da ka amince kawai." "Amma Yaya.." "Amma me? A haka zaka karaci rayuwarka ne Sadam?" A hankali ya sassauta murya yace "Shike nan, na amince." Ba tare da ya san wacece matar da suka zaba mishin ba. "Masha Allah." Suka had'a bakinsu suna fad'a, daga bisani suka fitar da kudin da bai san adadin su ba, Salis ya mik'a mishi. "Wannan shine rabon gadonka wanda aka kasafta lokacin da kake asibiti, ina shawartarka da ka samu business din da zaka fara wanda zai taimaka maka ka tsaya da kafafuwanka, ita dai duniya ba matabbata ba ce ba. Allah yasa mu dace." "Amin amin." Suka ansa, kafun Sa'id ya cigaba. "Na riga nayi magana da mahaifin yarinyar, dama amincewarka kawai nike jira, dan haka next week idan Allah ya kaimu za'a daura aure." "Allah ya kaimu lafiya." Duk suka mik'e suka fita, suka barshi zaune yana da-na-sanin halaye irin nashi, inda ya rink'a jin inama baya zata dawo, da kuwa ya shimfida rayuwarsa bisa tsari na addinin islama.4 Hawaye ne suka wanke fuskarshi, ya shafe su a hankali, ya mik'e ya koma dakinshi, amma sai ya zamana tamkar an k'ara turo wasu sababbin hawayen ne. Kukanshi yayi mai isarshi, ya gama, sannan ya tashi ya fita jin kiran sallar maghriba da aka fara. *** Kamar yadda Sa'id ya fad'a, ranar juma'a ana gama sallah aka daura auren Sadam da amaryarshi Farida, wacce har a lokacin bai san ta ba, illa sunanta kawai da ya sani. A part d'in mahaifinsu amarya ta tare, bayan sunyi walimarsu ya su, ya su, dare na yi 'yan uwanshi suka rako shi d'akin amarya. A hankali ya tura kanshi cikin palon, gabanshi na tsananta bugu, ya yaye labulen tare da tura kanshi ciki. Zaune ya hange ta ta bashi baya, illa daurin kallabinta na ture ka ga tsiya da ya ansa mishi sallama. Jiki babu k'wari ya zagaya gabanta, chewing gum take taunawa k'as-k'as, tana ganinshi ta mik'e da sauri ta iso gabanshi.4 Cikin tashin hankali Sadam ya k'walo ido waje "Fareeda?!"4 Murmushin 'yan duniya ta saki, ta cigaba da nufo inda yake tana shirin unbutton rigarshi. "Ni din dai ce. Ka ga yadda Allah yayi nashi ikon ko." "No please, you must be kidding." "I'm not Kazaure. Allah ne ya kashe ya bani."2 "Ke dallah dakata mun malama. Ina kike tunanin zan kai mace irinki wacce tayi aurarraki har ban san adadinsu ba." Shewa ta saki, ta k'ara hankado kallabinta gaba tace "Da na taimaka maka din? To jira ka ji, ni din nan dai nice babu sauyi, kuma zama daram dam a cikin gidan nan, dan dama na dade ina mararinka tun muna 'yan yara."3 "Oh Allah!" Shi kadai Sadam ya iya fad'i, ya zube a kujera yana dafe kanshi. Ya san wacece Fareeda, tare suka tashi tun suna yan yara take crushing dinshi, a ganinshi ba ta da qualities din matan da zai iya so kaf a duniyarshi. Cikin karairaya ta juya tana cewa "Kayi ka gama ka zo nan ka same ni, mazaunai nike, dole a zauna da ni. Ba saki ba kuma yaji. Ehee."4 Zuciyarsa cike da damuwa, ya kira wayar Sa'id, yana dauka ya fashe da kuka "Haba Yaya, ka rasa wacce zaka had'a ni da ita Sai Faree Social, macen da duk unguwan nan babu wanda bai santa ba da shegen aure-aure. Ni wallahi ban san ya zanyi da ita ba." "Daurewa zaka yi ku rufa ma kanku asiri ku zauna lafiya."1 Daga nan ya kashe wayar, ya bar Sadam da cizon yatsa. Bashi da yadda zai yi din, dole ya tashi ya bi ta a baya suka shige the other room.9 KADUNA ***Four years later*** Excuse the mess, the children are making memories... Wadataccen palo ne mai girman gaske, wanda ya kawatu da kayan jin dad'i na more rayuwar dan Adama. A k'asar lallausan kapet d'in da ke shimfide text books ne kusan guda goma a barbaje ko wanne ya kama gabanshi. Tarkacen su pencils, sharpeners, cleaners da kuma school bags guda ukku yashe a tsakiyar palon Ta 6angaren haggu kuwa d'an k'aramin cup ne da spoon an had'a cereal an sha rabi, an zubar da rabi a k'asa, ga kuma saura an bari a cikin cup d'in da wasu kananan teddies, da whistle na wasan yara duk a wurin. Ta gefen dama yaro ne da zai kai shekaru tara duk'e yana faman rubutu, da alama homework din mai matuk'ar muhimmanci ne, ganin yadda yara ke guje-guje a tsakiyar palon amma shi ya natsu ga aikin gabanshi. Da gudu yarinyar da zata yi shekaru takwas ta biyo 'yar k'arama mai shekarun da baza su wuce hudu ba, hannun k'aramar rik'e da mug mai tea a ciki, ta ruga da nufin kauce ma wacce ta biyo tan, cikin rashin sa'a ta fad'a ma Jafar da ke zaune yana rubutu, take mug din ya fadi kasa, ya fashe, tea din ya watse a tsakiyar palon. Dagowa ya yi yana kafe ta idanunshi, ya mike da azama yayi kanta, da saurinta ta mik'e ta zura da gudu, itama Rukayya da ta biyo ta ganin ya tunakaro su, ya sa ta juya da gudu, a sa'a guda suka yi kicibis da Jay da ta fito hannunta d'auke da fine boy din da bai wuce watanni takwas ba, idanunsa da kalar lips dinshi, tamkar ace SS ne lokacin da yake k'arami.4 "Da gani wannan laifinki ne Rukayya. Me kuka mishi?" Ta kalli Rukayya da tayi girman ban mamaki tana tambayarta. "Wallahi Mammy ba ni bace, Fatima ce ta d'auke mun pencil zanyi homework, na bita in ansa shine ta fad'a ma Ya Jafar ta fasa mug ta zubar mishi da tea a kan text book." Kunnen 'yar k'aramar ta kama, "Ke na rasa wace irin 'ya ce wallahi, me sa kika je kika zuba ma handsome tea jikin littattafai?" Kuka mai karfi Fatima ta saka, Jay ta turar da ita, ta isa ga Jafar da har yanzu yake cika yana batsewa. "Haba mana handsome nawa, kayi hak'uri mana, kai fa big bro ne. Baza su k'ara ba." "To Mammy duk laifin Rukayya ne fa, ita ta tura ta ta fad'a mun fa, ni gaskiya bazan yadda ba." "Ku zo nan." Jay tayi kiran Rukayya da Fatima, suka iso ita tana kuka, ita kuma tana tura baki tana ma Jafar kunkuni. "Ko wacce ta ba shi hak'uri, if not ke zaki share palon nan gaba dayanshi." Ta k'arasa tana nuna Rukayya. Da sauri suka had'a baki suna bashi hakuri, ya kwashe da dariya ganin yadda 'yar lukutar fuskar Rukayya ta mairairaice tana begging dinshi. "Kun sila yara, ku tashi ku je wasanku." Ta mik'e tana harararshi ta k'asar ido, tana juyawa ta ci karo da SS da yayi tsaye bakin k'ofa yana kallon duk me suke yi. Da gudu suka yi kanshi, ya daga Fatima yana dariya, yaron da ke hannun Jay ma yana ganinshi ya fara daga hannu yana wangale baki. Tana ajje shi ya rarrafa ya isa gabansu, ya ajje Fatima ya daga shi sama yana juyawa, yana kallon yaron da ke ta wangale baki ba tare da ya san komai ba. Hannun Jafar ta kama suka isa gare su, ta gefen damarshi ta koma ta tsaya, ya sanya hannunshi ta baya ya tallabi kafadunta, yana kallonta dauke da murmushi a fuskarsu, yaran suna tsaye, zagaye da su. Wani tsantsan dad'i marar misali Jay take ji a ruhinta, yau ga ta tana rayuwa dai-dai da mafarkin Baffanta, ta gina iyalinta nata, na kanta wanda suke cike da kwanciyar hankali da soyayyar junansu, ga shi tana gab da kammala karatunta, a zahiri bata da abun da zata ce illa Alhamdulillah a ko wanne lokaci. Muryar Jafar ce ta katse mata tunaninta, ta jiyo shi yana cewa "Daddy kawo shi mana, kaga so yake in d'auke shi nima." Ya mik'a hannu ma yaron, babu gardama ya mik'a masa shi, ya juya zai yi ma Jay magana suka ji yo knocking a bakin k'ofar palon. Rukayya ta ruga da gudu ta bud'e ga mamakinta, ta ga Daddy Kazaure da Aunty Faree, har ma da 'yar cute baby mai kama da babanta. Kallon-kallo aka fara yi tsakaninsu, domin wannan ce haduwarsu ta farko, bayan shekaru biyar da suka gabata. Daga bisani SS ya isa ya dan daki kafadar Sadam, ya bud'e hannayensa, shima ya bud'e nasa, suka shige cikin jikin juna, sannan suka rufe yana fad'in4 "Long time bro?..." Wani sabon knocking din ne ya katse su, Rukayya ta k'ara komawa ta bud'e. Miemie ce ta fara shigowa, da mamaki take kallon mutanen da ke tsaye tsakiyar palon, a lokaci guda ta saki dariya tace "Surprise.." That fine bobo na dinner su Jay abokin SS mai suna Salim ya bud'e k'ofar ya shigo. "Here come my fiancee."4 Duk suka sanya dariya, suka fara gaisawa da SS, sannan suka gaisa da Kazaure, suka koma kan kujeru suka zauna, nan da nan gidan ya k'ara hargitsewa da hayaniyar yara da ta manya. Hannu Kazaure ya mika da shirin daukar dan yaron da ke hannun jafar, ba musu ya iso gare shi, ya daga shi sama yana kallon SS, "Sadam.." SS ya fada yana shafa kan yaron. "I can't believe this. Kana nufin is yi mun takwara kenan?"3 "What are friends for?" SS ya yi maganar yana daidaita zamanshi. Jay, Miemie da Faree Social ta wajen Kazaure suka wuce kitchen domin kawo masu abin sha. **Verily, with every HARDSHIP, there is ease. (Q94:V06)**2 Thank you so very much guys for giving SSDN a chance. I truly appreciates y'all maximum support.1 Allah Ya gafarta kurakuren da muka yi, Ya sa jama'a su amfana da darussan da muka rubuta. Amin. KARSHE

0 Comments