RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 1

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 1
Yarinya ce karama ta fito daga cikin makarantarsu, tana ta murmushin murnan ganin mahaifiyarta. Da gudunta ta ruga ta rungume ta tana mai fadin "Momy, ina wuni" mahaifiyarta tai murmushin farinciki hade da amsata. "Lafiya kalau my Bady, ya school?" Da haka ta dauketa ta saka ta cikin mota suka tafi. Suna tafe Badiyya nata mata surutu har suka karasa gidansu dake Barhim Estate, kuka road, a cikin jihar katsina. "Momy, ina Dady yake?" Badiyya ta tambaya tana me cire kayan jikanta. Ladi me aiki tazo ta dauki kayan tai wajen daya kamata dasu. "Bady, Dadynki yana wajen aiki, amma ya kusa dawowa." Mahaifiyarta ta bata ansa tana me shiga cikin kitchen. "Kizo kici abinci Badiyya, kafin lokacin Islamiya yayi." Ta fada da karfi domin yar tata taji. "Momy, bari naje nayi wanka tukun, jikina yanamin ba dadi." Badiyya ta amsa hade da ruguwa zuwa dakinta. Mahaifiyarta me suna Fiddausi, wadda a yanzu taji wani irin mugun bugawar zuciyar ta dakyar ta amsa yarinyar ta. "To Badiyya, kiyi sauri." Da sauri taje parlour ta bude jakarta domin ta dauki wayarta, fatanta daya Allah yasa ba Dadyn Badiyya bane wani abu ya sameshi, domin zuciyarta taki daidaituwa. Cikin hanzari ta dauki wayar ta kara a kunnenta. "Hello Ahmad, da fatan kana lafia ko?" Ta fada a yayinda ya amsa wayar. "Lafiya kalau Fiddausi, wani abu ya faru ne?" Ya tambaya a hargitse, domin yadda yaji muryarta yasan ba lafiya ba. "Babu abunda ya faru wallahi, kawai naji bugun zuciya ta ya karu, shiyasa nai tunanin ko wani abu ne ya sameka." Ta bashi ansa tana me goge hawayen dake fitowa daga idonta. "Babu komai Firdausi, ki kwantar da hankalinki, ganinan dawowa gidan. Amma kina iya kiran gida kiji ko lafia." Ya bata amsa, domin ya kwantar mata da hankali. "To shikenan, Allah ya tsare." Ta amsa a takaice tana me karar da call din. "Badiyya kiyi sauri." Ta fada da karfi, yayinda take dailing number kanwarta Kausar. "Hello Kausar." Ta fada a hankali. "Na'am Maman Badiyya." Kausar ta ansa a raunane. "Kausar lafiya naji muryarki wani iri?" Firdausi ta tambaya a gigice, bugun zuciyarta na tsananta. "Yaya Fiddi." Ta fada sai kuma ta tsaya. "Baba ya rasu." Ta fada hade da fashewa da wani matsanancin kuka. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un." fadar Firdausi hade da fasa wata irin kara, wayar dake hannunta ta sulale ta fadi. Tana nan zaune hawaye na kwaranya daga idonta, ta rasa meke mata dadi, meyasa Baba zai tafi a lokacin da suka fi bukatar shi? Meyasa shima zaibi Mama a lokacin da kowa ya dogara a kanshi?. Tana cikin wannan halin ne Ahmad yaxo ya iske ta a haka, da gudu ya karasa yana mai tambayarta ko lafia. "Firdausi, lafiyarki kuwa?" Ya tambaye a kidime, domin duk abunda zaisa fiddausi kuka to ba karamin abu bane. A hankali ta dago raunannu idanunta ta saukesu a fuskar mijinta, wanda a yanxu shine gatanta, dashi kadai ta dogara bayan Allah, bata da wani gata daya rage shi. "Baba ya rasu." Ta fada tana me kara fashewa da wani kukan. "Innalillahi" kawai yake furtawa, domin ya kasa magana. Kanshi ya daure. Kullu Nafsin za'ikatul Maut! Saidai muce Allah ubangiji ya jikan Alhaji Salisu Zubairu. Badiyya ta fito a guje, tana fadin "Momy wane kaya zan...." Maganar ta tsaya mata a makoshi, domin ganin halin da iyayenta suke ciki. Da kyar ta taka taje inda suke. "Momy, Dady meya faru?" Ta fada a hankali, domin ta rasa meke mata dadi. A matsayinta na yarinya yar shekara goma, wadda take primary 5; ganin iyayenta haka yasa komai na duniyar ya tsaya mata chak!. STORY CONTINUES BELOW  "Babu komai Badiyya, jeki hado kayanku kamar kala biyar keda Momynki, kizo mu tafi." Ahmad ya ansa mata a hankali. "Dady ina kuma zamuje?" Ta tambaya a rude, domin ba kasafai suke tafiya har ta kwana wani waje ba. "Kankia zamuje, kiyi sauri Badiyya." Ya bata ansa. A hankali ta tashi taje ta dauko masu kayansu, ta fito ta mika ma Momynta hijab suka fita. *** Suna shiga garin Kankia sukaga motoci sunata shiga, alamun babban mutun ya rasu, domin yanzu za'ayi jana'izarshi. Firdausi da kyar ta fito daga cikin mota, hawaye na fitowa daga cikin idonta, wai yau itace Mahaifinta ya rasu. Bata taba tunanin hakan ba. Tana shiga cikin gida, itadai Badiyya murna take yau sunzo Kankia, xataga Baba. Tana zuwa taga kannen mamarta suna kuka. "Anty Kausar, meke faruwa? Ina Baba?" Badiyya ta tambaya a kidime, domin ba haka ta saka zuwa ta iske gidan ba. Kasa ansata kowa yayi, domin tausayinta sukeji, Baba yafi kowa shakuwa da Badiyya duk gidan. Firdausi ce ta rungume yarinyarta, tana wani gunjin kuka. A haka suka je sukayima Baba addu'a sannan aka fita dashi domin kaishi gidanshi na gaskiya. Badiyya itadai bata gane komai ba, abun daya tsaya mata a rai shine; taga Baba kwance cikin fararen kaya, sannan yanzu wasu maza sunzo sun fita dashi. Wata mata taji tana cewa "yanzu shikenan Alhaji, har abada!" Sai a lokacin abun ya daki zuciyarta, badai Baba ya rasu ba? Aikau a take ta fashe da wani matsanancin kuka ta fadi sumammiya. Mutane sukayo kanta, Firdausi abun duniya ya isheta, ta rasa dame xata ji. Aka Daukesu aka kaita asibiti, nan likitoci suka fada masu ta shiga coma, farfadowarta ba yanzu ba. Abun ya tada mata hankali sosai. A haka akabar wata tsohuwa wajenta, dakyar aka samu Firdausi ta dawo gidan domin karbar gaisuwa. Ranar sadakar Ukku Badiyya ta farfado, farkon maganarta shine. "Ina Baba?" Dakyar mahaifiyarta ta tsagaita kukanta ta taso ta rungume ta. "Kullu nafsin za'ikatil maut, Badiyya kin tuna wannan ko?" Mahaifiyar ta fada cikin sigar lallashi. Badiyya a hankali ta daga kanta. "To Baba ya rasu, muma lokacin mu zeyi koba yanzu ba. Kiyi hakuri Badiyya, kiyi tawakkali." Tana fadin haka Badiyya ta fashe da kuka, anan fa koke koke ya dawo. A haka har akai kwana bakwai sannan kowacce ta koma gidanta. Dukkansu saida aka raba masu gadonsu sannan suka tafi, domin sunce basu san abar mahaifinsu da nauyi. Allah ya jikan musulmai, idan tamu tazo yasa mu cika da imani. Ameen. *** Firdausi rayuwa take kamar da, saidai har yanzu mutuwar bata saketa ba, kullun da safe sai ta dauko waya xata kira Baba sai ta tuna ashefa babu shi a doron kasa. A haka take ta hakuri tana mashi Addu'ar samun Rahamar ubangiji. A bangaren Badiyya kuwa, hidimarta ta cigaba dayi kamar ba abunda ya faru, abunka da yaro. Yau Firdausi ta tashi da safe, yau ne ranar da zata koma a bakin aikinta, wanda take teaching a makarantar Salama international school. Ta shirya Badiyya tsaf sannan ta biya ta aje ta a Saldefi International school tukun ta wuce wajen aikinta. In a blur, lokacin tashi yayi. Taje ta dauko Badiyya suka dawo gida. Sunje Islamiya sun dawo, har sunci abinci suna rage dare; ta hanyar yin kallo sai ga Ahmad ya dawo. Da gudu Badiyya taje ta rungume shi. "Dady sannu da zuwa." Ya shafa kanta yana me jin soyayyar yarinyarshi cikin ranshi. "Yauwa Badiyya." Ya fada yana zama kan kujera. "Mikoman abinci na." Ya fada tare da kallan Firdausi. A hankali ta tashi taje ta dauko mashi. Bayan ya gama ci ta lura sosai akwai magana a bakinshi. "Badiyya jeki kwanta, kinga dare yayi." Ta fada cikin siyasa tare da kallan mijinta wanda ya sakar mata da murmushin ashe kin gane. Badiyya batai hesitating ba taje ta rungume su daya bayan daya hade da yimasu peck a kumata. "Sai da safe." Ta fadi hade da shigewa. "Dadynmu." Firdausi ta fada tana murmushi. "Naga kamar akwai magana bakinka ko?" Ta fada tana zama kusa dashi. Yayi wani irin murmushin wanda ba wanda zaice ga ma'anarshi inba shiba. "Hakane Momynmu, akwai magana." Ya fada yana kallon kwayar idonta. "To fadota inji Dadynmu." Tai mashi murmushinta me tsada. "Dama so nake ki bani gadonki domin inja jali dashi, kinga kasuwar yanxu sai a hankali." Ya fada yana sosa keya, yana mata wani irin kallo.5 "Dan Allah kayi hakuri, bawai bazan baka bane, amma wallahi nima business zan faru dasu." Ta fada a hankali, domin ta soma tsoron mijinnan nata, saboda wani sa'in yakanyi abu kamar ba shi ba. Nan take yahau ta da bala'i, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, san duniya ya rufe mashi ido. Ya manta da baiwar Allahnnan gadon tane, hakkin ta. Badiyya ta fito daukar ruwa, abunda ya zame mata ibada, sai taji hayaniyar mahaifinta, kamar dai ba magana yake ba. Tana lekawa ta hango mahaifinta tsaye kan mahaifiyarta yana ta zabga mata fada tayi shiru tana ta share hawaye. Badiyya jikinta yai sanyi ta rasa ina zata, bata taba ganin iyayenta cikin wannan halin ba. A hankali ta taka ta wuce dakinta tana hawaye, domin bata san susan ta gansu a wannan yanayin. Ba abunda yake tada mata hankali fiye da hawayen mahaifiyarta. To jama'a shin ko Firdausi xata bada gadonta?7 Ko Ahmad zai hakura in bata bada ba? Ko kuwa zai dauki mataki? A daren jiya Firdausi bata rintsa ba, maganganun Ahmad ne keta mata yawo cikin kai, kuma ita bazata iya bashi gadonta ba. Tasan halinshi sarai, bawai sana'ar zaiyi dasu ba, illa iyaka yaje ya nemi matan banza.1 A haka ta tashi looking pale, gaba dayar duniyar bata mata dadi, gashi ba wanda zata fadama damuwarta. Dama Baba ne ko Mama, kuma Allah ya dauki abunshi. Yau Ahmad ko gaisuwarta bai amsa ba, ya tashi yanata daddaure fuska ya fita, ko breakfast beyi ba. Abunda kuma ba halinshi bane, koda yanajin yan wulakancinshi yakan amsa gaisuwarta har ya karya, amma yau ko daya beba.3 A hankali ta taka taje dakin Badiyya, wanda ta isketa har ta fito wanka. "Momy ina kwana." Badiyya ta gaishe ta a hankali, domin itama abun ya dameta. Ta zauna a bakin gado ta karbi vaseline din hannun Badiyya ta fara shafa mata. "Lafiya lau My Bady, ya naga kin tashi da wuri yau?" Ta tambaya tana me kamo hannayenta. "Ko baki lafiya ne?" "Aa Momy, kawai rai na ne yakemun ba dadi, kuma naga bakizo kin tada ni ba saiyasa kawai na tashi." Ta bata amsa, tana me zama akan gadon domin saka wandon Uniform dinta. "Kiyi sauri ki fito, karmu makara." Firdausi ta fada tana me fita daga dakin domin ta duba Ladi me aiki kota gama. A haka ta fita taje kitchen ta iske Ladi na soya kwai. "Ladi, an tashi lafia." Firdausi ta fada cikin girmamawa, bata da girman kai ko kadan. "Lafiya lau Hajia, ina kwana." Ladi ta fada tana me russunawa. "Hajia baki lafia ne?" Ta tambaya cikin kulawa. Domin Firdausi bata iya boye damuwa ba, hasali ma in tana cikin damuwa kallo daya zakai mata kagane. "Lahh, ba komai Ladi, me kika gani." Firdausi ta bata ansa, feigning a smile on her face, bataso Ladi ta fahimci halinda take ciki. "Ba komai Hajia, kawai na lura da yanayinki ne." Ladi mata yar kimanin shekara Arba'in da biyar ta fada. Ita da mijinta Malam Tanko yan karamar hukumar Dutsinma ne, rashin aikinyi ya kawosu Katsina. Malam Tanko yana gadin gidan, ita kuma Ladi tana masu aikace aikace, dakinsu yana cikin gidan. Firdausi ta kauda maganar Ladi, ta tayata kai kayan bisa dining table, hade da kwala ma Badiyya kira. "Badiyya, wai me kike yi ne?" Ta fada tana zama bisa daya daga cikin kujerun dining din. Badiyya ta fito rike da school bag dinta a hannu, tazo ta zauna a kujerar da ta zama tata, a hankali da kalli inda Dadynta ya saba zama taga wayam. To kodai Dady fushi yake har yanzu ta tambayi kanta. "Momy banga Dady ba." Ta tambaya, hade da tsare mahaifiyar tata da ido, alamar tana bukatar amsa. "Umm-ummm." Firdausi ta fara inda-inda, tambayar tazo mata a bazata. Saboda ba kullun suke breakfast tare dashi ba. Lecturing yake a Isa Kaita college of education dake dutsinma, to in yanada lectures din safe yakan riga su fita, wani sa'in kuma sukan rigashi. Yanada shaguna biyu a sabon layi, dasu ne yake fake ma Firdausi akan kasuwa tayi kasa. "Dady ya tafi school Badiyya, kiyi sauri mu tafi." Ta fadi hade da janyo kula tana zuba masu abincin. Badiyya bata kara cewa komai ba, a hankali suka ci abincinsu suka fita. "Momy, karki buge shi." Badiyya ta fada a razane, hadi dayin wata irin kara. Sai a lokacin Firdausi ta lura ta dade da shiga duniyar tunani, bata lura da yaron dayazo wucewa ba. Batace da Badiyya komai ba, a haka suka karasa Saldefi International School ta ajeta. "Momy dan Allah ki kula, kibar tunani." Ta fada tare da fita cikin motar. "Allah ya tsare." Ta fadi tana mai rufo marfin motar. A haka Firdausi ta karasa makarantar, tana ayyana ma ranta; insha Allah zata rika kokarin boye damuwarta, kodan Yarinyarta. *** STORY CONTINUES BELOW  "Malama Firdausi, meke damunki ne wai? Yara nata surutu kin zabga uban tagumi." Fadar Malama Rukayya, tana mai jijjiga ta. Tana cikin class dinta ta jiyo hayaniyar mutane tayi yawa, shine ta shigo ta iske ta tanata tunani. "Firdausi kin cika sakama kanki tunani wallah." "Ohhh... sorry Malam Rukayya, wallahi hankalina bayan wajen ne." Ta fada tana taba fuskarta, alamun batasan sadda tunanin yai awon gaba da ita ba. A bangaren Badiyya kuwa, suna zaune cikin class, Malamin Mathematics ya shigo anata darasi saiga Malam Obinna ya shigo. "The above named students doesn't pay their school fees, you should tell your parents to pay for your school fees." Ya fada hade da karanta sunayensu. "Badiyya Ahmad, you didn't complete your last term fees, you should complete it and pay for this term also." Ya fada hade da fita hanyar waje. "You won't be allowed to enter the school on monday, if you didn't pay." Kamar jira suke ya fita suka kwashe da dariya, abunka da yara. "Badiyya Ahmad, complete your last term fees." Yaran keta fada, sunma maida abun waka. Saidai Maths teacher yai masu tsawa tukun sukayi shiru. Badiyya ba abinda take banda kuka, bata taba jin bakin ciki irin na yau ba. Tasan Momynta bata sani ba, data biya mata. A haka har lokacin tashi yayi, dayake ranar thursday ne, ba kowa ke tsayawa lesson ba. Haka Firdausi tazo daukar yar tata ta ganta wani iri, yau ko surutun Badiyya batai mata ba. "Badiyya wai meke damunki?" Firdausi ta fada cikin shigar damuwa, yanayin yar tata be mata dadi ba. "Ba komai Momy, yau Dady da wuri zai dawo ne?" Ta boye mata, hade da tambayarta idan yau da wuri Dadynta zai dawo;domin ta fada mashi. "Ban sani ba Badiyya, saidai mu jira mugani." Ta bata ansa, tana me shan round din da zai sada su da unguwarsu. A haka sukai shiru, ba wanda yai magana har suka isa. Kowa da abunda yake sakawa cikin ranshi. "Kiyi sauri ki wanka, ki fito muci abinci." Firdausi ta fada tana me cire hijab dinta, tansan halin Badiyya da wanka. Koda tace taci abincin kafin tayi baci xatai ba. "Toh Momy." Ta fada hade da rugawa zuwa dakinta. Itama yunwar ta isheta, wankan daine ya zama mata ibada. *** Sun gama cin abincin dare, suka zauna suna kallo. Uffan, ba wanda yace da dan uwanshi, kowa yana saka abunda ya dameshi cikin rai. Firdausi tayi maganar har ta gaji, akan Badiyya taje kwanta amma fir taki, ita a dole sai Dadynta ya dawo. Suna nan zaune wajen karfe tara da rabi Ahmad yai sallama, fuskarnan a dakune. "Kawoman abinci." Ya fada yana me kara tumke fuskarshi. Batace dashi komai ba, dan ta lura yau yan rashin imanin ne bisa kanshi. Wani lokacin halinshi tsoro yake bata. Bayan ya gama cin abinci, Badiyya tazo ta zauna kusa dashi. "Dady, ance mu biya kudin makaranta." Ta fada a raunane. "Kuma ashe har na last term ba'a ida biyaman ba, yan ajin mu sukai taman dariya." Ta fada hade da fashewa da kuka. Firdausi kawai tsayawa tai tana kallonsu, dama abinda yake damun Badiyya kenan? Shine dan wukalanci Ahmad ashe ko kudin last term be ida ba, amma ko ya fada mata. Ai gashinan yajama diyarta wulakanci. "Ke karki takuraman dan Allah, jeki kwanta." Ya fada hade da dagata daga jikinshi. "Ranar monday zamuje a biya." Sadaf sadaf ta mike ta wuce daki, itama yau tsoronshi takeji. "Kingani ko? In zaki bani kudi ki bani." Ya fada a tsawace, yana mai ma Firdausi wani irin kallo. "Ahmad dan Allah kayi hakuri, wallahi..." Bata karasa ba taji wani irin wawan mari kan fuskarta, nan take ta kurma wata uwar kara. A razane Badiyya ta fito daga dakinta, da gudu ta shiga falon. Hannun daya daga da niyar sake marinta Badiyya ta rike tana me zubda hawaye. "Dady dan Allah karka daketa, in kan kudin makarantar ne wallahi na yafe. Bazan kara zuwa ba." Ta fada tana wani irin matsanancin kuka. Wurgar da Badiyya yayi yana wani huci. "Kisani, I'm capable of doing anything akan kudi. Ko ki bada cikin mutunci, ko in karba da karfi da yaji." Ya fadi hade da wucewa dakinshi.1 Badiyya ta rarrafa ta rungume mahaifiyarta, a tare suka saki wani kuka me ban tausayi. Ita Firdausi tanajin tausayin yar tata, ita kuma Badiyya kukan mahaifiyarta ne ke tada mata hankali. Dan bata gane me yake faruwa bama. Tohhhh Jama'a.. kome Ahmad zaiyi dan karbar kudin?2 Shin Firdausi xata bashi kudin kodan Badiyya?Dakyar Firdausi taja yarinyarta suka wuce daki, yau a dakin Badiyya zasu kwana. Bayan sun shiga dakin, Badiyya ta dago kai ta kalli mahaifiyarta. "Momy wai me kikayi ma Dady?" Ta fada tana share ma Firdausi hawayenta. "Badiyya ban mashi komai ba, kuma karki saka abun a ranki kinji." Firdausi ta bata amsa, tana goge hawayenta. Dole ta zama me juriya kodan yarinyarta. Kuma Allah na gani bazata bada dukiyarta aje ayi shaye-shaye, neman mata, caca, dasu ba. Dan itama batasan yana wannan halayen ba sai kwanannan.2 "Badiyya jeki alwalla kizo muyi nafila kinji." Firdausi ta fada, tana daga Badiyya daga jikinta. A hankali ta tashi taje tayo alwalla ta dawo. "Momy kema kije kiyi." Ta fada tana me shimfida masu darduma a tsakiyar dakin. Firdausi batace komai ba ta tashi ta shiga toilet tayo alwalla. "Toh Momy wane hijab zaki saka?" Badiyya ta fada, tana murmushi domin tasan hijabanta bazasuyi ma Momyn ba. "Bani doguwar hijab dinki na saka." Fiddausi ta fada, tana mika hannu domin ta ansa. Badiyya taje ta bude wardrobe dinta ta fiddo doguwar hijab dinta ta mika mata, tana sakawa a tare suka fashe da dariya. "Momy kinga yanda hijab din ta miki kowa? Kamar tantabara sunan wata tsuntsuwa." Badiyya ta fada hade da fashewa da wata irin dariya. Itama Firdausi dariyar tai "Badiyya bansan wulakanci, tunda dai takai mani iya gwiwa ai ba dole sai na saka hannun ba. Taho muyi sallar ni." Ta fada hade da janyo ta suka tada salla. Bayan sun idar da sallar suka dauko Al-Qurani suna karantawa, har zasu rufe sai Badiyya tayi caraf. "Momy bamu karanta Suratul Mulk ba, kinga ance tana haskaka kabari. Mu karanta mu sadaukarwa Baba da ita." Ta idasa a raunane, domin tuna sunan Baba yakan sata wani iri. Firdausi jin abinda Badiyya ta fada ya kara mata san yarinyarta, Allah ya jikan Baba. "To Badiyya mu karanta." Ta fadi tana goge hawayenta. Suna gama karantawa, Badiyya ta daga hannu alamar addu'a. "Ya Allah ka jikan Baba, Allah ka gafarta mashi. Ya Allah kasa Dady ya biyaman kudin makaranta, wallahi inasan zuwa makaranta. Ya Allah kasa Dady karya kara dukan Momy, Allah kasan banjin dadin ganin kukanta." Ta fadi hade da shafe fuskarta, ta dago da kanta taga mahaifiyarta na kallanta. "Momy, bakice Amin ba." Firdausi ta share guntun hawayenta ta kalli yarinyarta, tana me alfahari da wannan kyautar da Allah yai mata. A da tana damuwa da rashin haihuwarta, amma yanzu ta gode ma Allah daya hada duk abunda take bukata danta yazamo yana dashi a akan Badiyya. "Ameen Badiyya, taso muje mu kwanta." Ta fadi hade da mikar da diyar tata. Sunje sun aje Al-Qur'anin da hijaban inda ya kamata, suka kwanta. Firdausi tai masu addu'a hade da shafe masu jikinsu. Ta kwanta tana me fuskantar yarinyarta, A hankali Badiyya takai hannunta kan shatin hannun Ahmad tana shafawa. "Momy da zafi ko?" Ta fada a raunane. Cikin karfin hali Firdausi ta ansata. "Badiyya ba zafi, ki kwanta kinji. Karmu makara gobe." Ta fada hade da rufe mata idanuwa da hannunta. Ta hankali Badiyya ta furta. "Ya Allah kasa Dady yabar dukan Momy." Firdausi bata ce komai ba, saidai jawo yar tata datai ta rungumeta. A haka bacci barawo yai awon gaba dasu. *** Sun tashi da safe, Firdausi ta shirya Badiyya tsaf, a tare suka fita parlour domin yin breakfast. Sun saba duk ran Friday, Ahmad be fita da wuri, amma yau basu ganshi ba. "Momy ina Dady yake?" Badiyya ta tambaya, tana me kallan mahaifiyarta da alamun tambaya. "Nima ban sani ba Badiyya, ko motsinshi banji ba yau. Koda asuba dana koma daki ban ganshi ba, kila tunda yaje salla be dawo ba." Firdausi ta amsata, itama ta damu da rashin ganinshi. Fatanta daya Allah yasa ba irin abunda ya saba yimata bane zai kara, dan in ya saka kafa ya fita to bata kara ganinshi sai bayan sati biyu kuma. A lokacin Badiyya bata yi wayau ba, to ta dauka ya daina wannan dabi'ar, ashe me hali be chanzawa. Badiyya daga kanta tayi alamar tagane, kawai ta cigaba dacin abincinta. Bayan sun gama Firdausi ta kalle ta. "Badiyya muje in biya maki kudin makarantar." Ta fadi tana murmushi, ganin zata cika ma yarta wani bangare daga cikin burikanta. "Allah Momy?" Badiyya ta fada tana tsallen murna. "Eh mana, kiyi sauri, kinga yau short day ne kar bank su rufe." Fadar haka, Badiyya da gudu ta tashi ta dauko jakarta suka fita. Sunje ta biyama Badiyya kudinta, tun a bank Badiyya ke kallan mahaifiyarta tana murmushin farin ciki. "Momy nagode sosai, Allah ya kara budi." Ta fada tana rungume Firdausi. "Ameen Badiyya." Firdausi ta fada tana shafa bayanta. "Allah yai maki albarka." "Ameen Momy, dan Allah in dan kudin makaranta yasa Dady fita gida kice ya dawo kin biya mani." Badiyya ta fada kamar xatai kuka. Firdausi tai wani murmushin takaici "Badan kudin makaranta ya tafi ba, amma zan kirashi." A haka suka karasa makaranta, ta ajeta ta wuce wajen aikinsu. Bayan sun dawo gida, sunci abinci. "Momy ki kiraman Dady, kingafa ya saba dawowa da wuri ran Friday, amma yau be dawo ba." Badiyya ta fada a raunane. "To Badiyya." Firdausi ta fada hade da dauko wayarta tai dailing number Ahmad. "Kinga wayar a kashe take Badiyya." Ta fada, itama abun ya soma damunta. "Bari in kira maki Anty Maimuna ku gaisa ko?" Ta fada, da niyar mantar da ita. Aunty Maimuna matar aminin Ahmad ce, sun shaku sosai da Badiyya, hasalima sune makwaftansu na farko da suka farayi. "Yauwa Momy kiraman ita." Badiyya ta fadi cike dajin dadi. Bayan sunsha waya da Badiyya sai a lokacin ta bawa Firdausi suka gaisa sannan suka kashe wayan. Dare nayi suka tafi kwanta, bayan Badiyya ta gama jajen Mahaifinta. Itama Firdausi abun ya bata tsoro. A haka dai suka kwanta badan sunso ba, saidai dare yayi sosai. *** BAYAN SATI DAYA. "Momy nifa gaskiya ki nemo man Dady na." Badiyya ta fada hade da fashewa da wani matsanincin Kuka. Itama Firdausi dauriya kawai take, domin ya dade beyi haka ba, kuma koda baze dawo ba yakan yi mata text akan karta tada hankalinta, amma wannan karan ko duriyarshi bata ji ba. Ta buda baki zatai magana kenan taji ringing din wayarta, dubawar dazatayi taga Kamal ne aminin Ahmad. "Kiyi shiru ga Uncle Kamal nan yana kira, kila yasan inda Dadyn yake." Tana kara wayar a kunne. "Hello Kamal, ya gida? ya yara?" Ta tambaya. "Lafiya Firdausi, dan Allah Ahmad na gida?" Ya tambaya a firgice. "Aa wallahi, muma nan shi muke nema, yakai sati daya baya gida. Wani abu ya faru ne?" Ta tambaya, bugun zuciyarta na tsananta. "Ni dazu muka rabu dashi, bayan munje gidana munci abinci. To yanzu ina dawowa na iske Maimuna cikin jini, shine nakeso in kira ya taimakan da mutane." Ya fadi hankali a tashe, tana jin sasshekar kukan shi. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un." Firdausi ta fada a kidime. "Badai kana nufin Maimuna ta rasu ba?" "Ta rasu Firdausi, saidai muyi hakuri. Ki kirashi dan Allah, na rasa ya zanyi." Ya bata amsa, cikin matsanancin tashin hankali. "An kashe Maimuna, an kasheta. Bansan waya aikata hakan ba." Kukan dayaci karfinshi ne yasa ya kashe wayar. Badiyya na ganin tana hawaye ta taso ta zauna kusa da ita. "Momy Lafiya?" Ta tambaye a rude, domin taji Momy na kira mutuwa. "Anty Maimuna ta rasu, kashe ta akai Badiyya." Firdausi ta bata ansa tana fashewa da kuka. "Aunty!" Badiyya tayi ihu. "Shikenan ni, duk masu sona su suke mutuwa." Ta fada hade da fashewa da matsanancin kuka. Allah ubangiji ya jikan musulmi, ita mutuwa riga ce, inyau kaine gobe bakai bane. Allah yasa mu cika da imani. Tohhh.... Jama'a kun ganni da wani update din kuma ko? Nima na kosa in cigaba dajin labarin RAYUWAR BADIYYA.1 Shin kowa ya kashe Anty Maimuna? Ko ina Ahmad yaje? Meyasa be dawo gida ba?A daren Badiyya fir taki bacci, wai ita sai ta kaita taga Anty Maimuna. Firdausi abun duniya yai mata yawa; batasan ko sunga Ahmad dinba, shin waya kashe Anty Maimuna? Tambayar datafi tsaya mata a rai kenan. Ashe dama Ahmad yana gari har yake zuwa wani waje cin abinci, amma bazezo gida ba? Kodan Badiyya. Dakyar ta samu ta lallaba Badiyya tayi bacci, ita kuma bacci ya kauracewa idonta. Wai meke shirin faruwa da rayuwarsu? Ahmad ya tafi yayi sati bai dawo ba, Amma kuma Kamal yace tare suka ci abincin rana, Sannan kuma an samu gawar Anty Maimuna. Haka ta tashi taje ta dauro Alwalla tazo ta tada sallah, tanayi tana kuka; domin Allah ya karkato da hankalin Ahmad ya dawo gida. Ko badan ita ba, kodan Badiyya. Bayan ta gama sallah, ta karanta Al-Qurani; har zata rufe maganganun Badiyya suka dawo mata a kwakwalwa. Ta bude ta karanta Suratul Mulk, hade dayi ma Baba, Anty Maimuna da Mama addu'ar samun rahamar Ubangiji. Bayan ta gama karatun Al-Qurani, ta zauna tana pouring heart dinta ma Allah, dukda bata furta kalma ko daya ba, Amma taji dadin yin shirun da tayi. Koba komai wani bangare na zuciyarta ya mata sanyi. A hankali ta tashi taje ta kwanta kan gadon ta, ta janyo Badiyya wadda taji tanata shesshekar kuka, ta rungume ta; tana rufe idonta cikin yanayin damuwa. *** Da safe Badiyya, ta farka bata ce kala ba; a sanyaye tayi wanka taje sukai breakfast. Itama Firdausi mutuwar ta tsaya mata a rai, gashi tanaso taje amma wayar Ahmad bata shiga balle ta fada mashi. Bayan sun gama breakfast, a hankali Badiyya ta tashi ta shiga dakinta. "Momy, ki karba ki saka mu tafi." Ta fada a raunane, tana mika ma Firdausi Hijab dinta. Itama ta saka tata tai mata tsaye bisa kai. Firdausi a hankali ta karbi hijab din, tai tsaye tana kallon Badiyya, domin batasan da wane baki zata fada ma Badiyya bata iya fita sai Ahmad ya yarda. Dan tasan kota fada mata ba yadda zatai ba. Dakyar ta bude baki kamar bataso. "Kinga ko, Badiyya matar aure bata fita saita tambayi mijinta." Ta fadi tana janyota ta zauna kusa da ita. "To kinga Dady be dauka ba, ki bari sai wayarshi tayi." Ta fadi tana kallanta, burinta Allah yasa Badiyya ta fahimci me take fadi.1 Badiyya ta dade tana kallon mahaifiyarta, alamun bata gane ba, sai da kyar ta iya bude bakinta. "To Momy, yanzu bazamuje bane?" Ta tambaya, hawaye na fara zuba daga idonta. "Aa Badiyya, bari in kara trying number shi in gani." Firdausi ta fada hade da dauko wayarta. Tana kira taji ta shiga, murmushin farin ciki tai ma Badiyya. Har saida ta kira sau uku tukun Ahmad ya dauka. "Hello." Ya fada a dakile, dagajin muryarshi yana cikin damuwa. "Ina wuni." Ta fada, a dardare. "Meya faru?" Ya tambaya, alamun baida lokacin gaishe gaishe. "Dama jiya ne, Kamal yake fada man wai an kashe Maimuna." Ta fada hade da nuna damuwarta. "Sai kuma aka ce maki ban sani ba." Ya katseta, cikin kosawa. "Kayi hakuri. Dama so nake naje, in masu gaisuwa." Ta fada a dardare. "Na hanaki zuwa ne?" "Aa kayi hakuri." Kamin ta sake cewa wani abu ya kashe wayar.1 Tai smiling lopsidedly. "Badiyya, dauko man car keys dina mu tafi." Firdausi ta fada hade da saka hijab dinta, tana mikewa tsaye. Badiyya ta mike a hankali ta wuce zuwa dakin Momynta, tana mai jin dadin atleast zataje taga Sultan. Bayan ta fito ta mika mata, suka fita. Suna tafiya ba wanda yace ma wani komai, a haka suka karasa Layout. STORY CONTINUES BELOW  *** Suna shiga gidan, Badiyya ta gaida mutanen wajen, hade da yi masu gaisuwa kamar yadda taji Firdausi tayi. Maimakon ta zauna, sai ta dubi Mahaifiyarta. "Momy, bari naje na duba Sultan am." Ta fada, hade da yin gaba, tana me tunanin halin da Yayanta kuma Abokinta yake ciki. Firdausi batace da ita komai ba, a haka ta zauna anata jajanta abun. Hango kannen Sultan tayi; Khadija da Khalil, suna kan jikin Kakarsu. Badiyya tana tafiya, tayi hanyar balcony; domin tasan nanne wajen zamanshi mostly. Aikuwa tana zuwa ta hango shi ya hade kai da gwiwa, shi baiyi kuka ba, kuma bai dago fuskarshi ba. Sultan yarone dan kimanin shekara sha biyar a duniya, Khadija itace tsarar Badiyya, sai Khalil yana da shekera biyar. Kamal ya auri Maimuna yana me karancin shekaru, domin shi bai zurfafa karatunshi ba. A hankali ta taka, ba tare da yaji takun taba. Tana zuwa ta zauna kusa dashi, ta riko hannayensa, kamar yadda yake mata in tana kuka; in sunyi fada da Khadija. Kamar batason magana. "Sultan am." Ta fada, idanunta na cikowa da hawaye. "Kayi hakuri dan Allah." Tana me karfafa rikon da taima hannunshi. Ya dago raunannun idanunshi ya saukesu kanta, shidai Allah yasa sun shaku da Badiyya. "Na'am Badiyya." Ta fada, yana kokarin kirkirun murmushin daba lokacin fitowarshi bane. "Ba komai Badiyya." Batasan ganin Sultan cikin wannan halin, a rayuwarta bayan Momy, Dady, Baba, ba wanda takeso da kuma suka shaku kamar Sultan. Batasan ganinshi cikin damuwa ko kadan. Duk da shekarun daya bata, hakan be hanashi yi mata wasa ba. "Dan Allah Sultan am, karkayi kuka, nima wallahi banso Anty ta mutu ba." Ta fada a raunane, idanunta har sun fara kawo hawaye. Tana kiranshi Sultan am; saboda Maimuna bafillatana ce, takan koya masu wani sa'in. Sultan am, yana nufin Sultan dina. "Badiyya, dole nayi kuka. Bansan waya kashe Ammi ba." Ya fada, idanunshi na kawo hawaye. Tun jiya har yanzu beyi kuka ba, saida yaga Badiyya. Yayi iyakar yinshi domin kukan yazo amma yaki zuwa, sai yanzu Badiyya tasa yazo. Ka yaya ne yaji Rahama a zuciyarshi. "Insha Allah, Sultan am, sai mun gano wanda ya kashe Anty." Ta fada, alamar alkawari a cikin idanunta. Wani murmushi dabai kai zuciyarshi ba, yayi. "Badiyya, ai bazamu iya ba, kinga fa mu yara ne." Ya fada, yana janyo ta jikinshi, domin yanzu haka kuka take. Baisan sadda nashi hawayen shuka fara zuba ba. "Sultan am, ai sai mun girma. Muna tare har mu girma ko? Domin mu gano wanda ya kashe Anty." Ta bashi amsa, tana me lafewa cikin jikinshi. "Sultan am, ka daina kuka dan Allah." Ta fadi, hade da goge mashi hawayenshi. Sunanan zauna, jefi jefi sukan yi maganar dabata wuce 'Eh' ko 'Aa' ba, rabin maganar ma Badiyya keyinta. Sai sukaji kiran sallar Maghrib. "Badiyya, bari naje masallaci." Ya fada, yana mikar dasu tsaye. "To Sultan am, nima bari naje, kar Momy ta fara nemana." Ta bashi amsa hade da wucewa cikin gidan. Bayan anyi sallah, Firdausi ta kara masu gaisuwa, har sun fito zasu tafi; sai Badiyya ta hango Ahmad yana fitowa daga masallaci. Da gudu taje ta rungumeshi. "Dady, ina kaje? Wallahi nayi missing dinka, kazo muje gida please." Badiyya ta fada, hawaye na kwaranya daga idanunta. "Badiyya, nima nayi missing dinki, amma kuje gida ni zanzo anjima kinji?" Ya bata amsa, yaname bambareta daga jikinshi. "Aa Dady, dan Allah kazo mu tafi, wallahi komun tafi bazaka zo ba." Ta fadi a raunane, wasu hawayen na zarya a idonta. "Ki wuce ku tafi Badiyya!" Ya fada adan tsawace. "Zan dawo mana."1 Fir Badiyya taki tafiya sutafi, Firdausi ba daman zuwa tajata saboda wajen duk maza ne. Tai tsaye ta harde hannayenta bisa kirji, tana kuka. Shi kuma Ahmad, beda niyyar binta. A haka mutane suka samu dakyar Ahmad yabisu sukaje gida. Murna wajen Firdausi ba'a magana, domin ko ganinshi kadai yana rage mata wata damuwar.1 A tare suka ci dinner, Badiyya sai janshi da labari take, amma yana amsawa sama-sama. Wani irin hot glares ne yake turama Firdausi. Har saida Badiyya ta tafi ta kwanta, Firdausi nason tambayarshi ina yaje har sati daya, amma tsoro takeji. Ta gaji da zaman; baice mata komai ba, ta mike zata tafi ya kirata a wulakance. "Keh!" Ta juyo, dan ta tabbatar da ita yake. "Kin chanza shawara, ko har yanzu kina kan bakarki?" Ya tambaya hade da kara tumke fuska, alamun rashin imani da san duniya sun rufe mashi ido. Da kyar ta iya buda bakinta. "Ahmad dan Allah kayi hakuri." Ta fada muryarta na rawa, domin cin mutuncin yayi yawa. Kana mijinta, ka fita gida har sati daya baka dawo ba, amma kuma kana mata wani irin kiran wulakanci. *_Maza kuji tsoron Allah, bafa ku kadai keda hakki a aure ba, mata ma suna dashi, wani cin mutuncin yayi yawa. Mu kuma Mata, Allah ya kara mana hakuri da juriya. Allah ya ganar damu baki daya. Ameen._* Takowa yai yazo har inda take, taja da baya. " ki sani, wallahi inhar baki bani kudinnan ba, zan maki abunda baki taba tsanmani ba." Ya fada, cikin wata kalar siga taban tsoro. "Na baki nan zuwa gobe." Ya fadi hade da wucewa hanyar dakinshi. Firdausi takai minti talatin tana nanata maganganun Ahmad, me hakan yake nufi? Saida tagaji dan kanta, da kyar taja nauyayyun kafafunta ta wuce dakinta. Tasan koda taje dakin Badiyya batai barci ba, kuma bata shirya ma tambayoyin Badiyya ba. Jama'a kuyi hakuri da rashin ganin update dina yau da wuri, wallahi Yayata aka kwantar a asibiti. Saidai fatan Allah ya bata Lafiya. AMEEN. Ashe bayan Momy, Dady, Baba; Badiyya ta shaku da Sultan. Shin ko Badiyya da Sultan zasu cika alkawarinsu? To wai me Ahmad zaiyi, dayake ikirarin ya bata nan zuwa gobe?Firdausi dakyar ta bude idonta, tana budewa taga gari ya fara haske. "Innalillahi." Ta fada, hade da daukar wayarta ta duba taga karfe shida da rabi na safe. Da hanzari ta tashi taje tayo alwalla tazo ta kabbara sallar Asuba, tana gamawa ta tashi tayi hanyar kitchen. A kan hanya ta hadu da Ahmad ya dawo daga masallaci, dabi'ar shi ce baya dawowa sai haske ya fara fitowa. Indai kan sallah ne, to sai kace Ahmad yafi kowa imani.1 Da sauri ta dauke idonta daga kan fuskarshi, sai taga ya kara mata kyau. Tunda take bata taba jin soyayyar Ahnad a ranta ba irin ta yau, ya kara mata kyau da kwarjini. "Lafiya ta kuwa? Wannan irin so ne haka tunda asubar fari?" Ta tambayi kanta, a yayinda take shiga kitchen. Tana cikin kitchen taji fitowar Badiyya, domin ta saba dukda weekends ne bata wani barcin kirki. "Momy ina kwana?" Badiyya ta fada tana me rungume Mahaifiyarta. "Lafiya lau, My Bady, bari in hada maku coffee keda Dady ko?" Ta fadi hade da ajiye doyar da take ferawa ta dauko coffee maker. Shan coffee ya zamanma Ahmad da Badiyya jiki, dama shi ya koya mata. Bacin Firdausi tai masu da gaske da sun zama addicted to it, amma yanzu duk weekends sai sunsha. Badiyya nanan tsaye har ta gama ta miko mata. "Kibi a hankali, karki kone." Ta fada mata, hade da mika mata cups din. Badiyya a hankali tai prowling zuwa parlour, inda ta iske Ahmad ya kunna TV yana kallon Morning News. Sai data ajiye cups din a center table tukun ta dago fuskarta cike da murmushi. "Dady ina kwana?" Ta fada hade da miko mashi coffee shi. "Ga coffee musha, kaga jiya dama bamu sha ba." Ta fada hade da yar dariyarta, domin ta tuna yadda sai sunyita rokon Firdausi tukun take hada masu. Yar dariya yayi, shima moments din suna dawo mashi cikin kai, haka suka zauna suna kallo sunashan coffee su.1 Sai wajen bakwai da rabi na safe tukun Firdausi ta gama. Ladi me aiki bata nan taje gida, diyar kanwarta ta haihu. Saida Firdausi ta gama jere kwanukan a saman carpet, yau a kasa zasuci abincin. Kamar yadda suka saba yi lokacinda rayuwarsu tana daidai. "Ku sauko muci." Ta fadi tana murmushi, har cikin ranta yau takejin soyayyar Ahmad, ta rasa miye dalilin hakan. Shima yau ba laifi ya saki fuskarshi, ba kamar jiya ba. Basu ce komai ba suka sauko kasa sukaci abinci, bayan sun gama breakfast Ahmad ya nufi hanyar dakinshi da niyar yin wanka. Badiyya ta mike hade da fadin, "Momy bari naje nayi wanka." Tana me nufar hanyar dakinta. Firdausi daga mata kai kawai tayi, ta nufi hanyar dakin Ahmad. Tana shiga taganshi bakin gado yana waya yana murmushi, wani bakin ciki ne taji yazo mata a wuya, dukda bata da tabbas din dawa yake magana. Bata ce komai ba, tayi hanyar toilet ta hada mashi ruwan wanka ta dawo bakin gadon ta zauna. Baice mata kala ba ya tashi ya shiga ya watsa ruwan, yana fitowa yaga ta fiddo mashi da kayanshi. Ya saka kayanshi yai hanyar fita, Firdausi tabi bayashi har yazo bakin kofa baice mata komai ba. "Dady, dan Allah inaso na kara zuwa gidan gaisuwa." Ta fada a dardare. "Na hanaki zuwa ne?" Ya fada, yana mata wata irin harara. "Aa." Ta fada, kanta na kallan kasa. "Karki dauki maganar dana gaya maki jiya a matsayin wasa, inhar baki bani ba.... hmmm." Ya furta hade da yimata wani kallo, sannan ya fita ya barta tsaya kamar gawa. Ita wallahi ta rasa ya zatayi. Firdausi ta shiga dakin, ta fada ma Badiyya ta fito su tafi; domin tanaso taje gidan Yaya. Yaya itace kadai Yayar Ahmad, wajenta ya taso bayan iyayensu sun rasu. Badiyya cikin hanzari ta shirya, domin tanasan gara ganin Sultan am, tasan koba komai zata debe mashi kewa. *** STORY CONTINUES BELOW  Sun fito daga Barhim, mai makon Firdausi tayi hanyar Layout sai tayi GRA, anan gidan Yaya yake; wadda badiyya ke kira da Gwaggo. Suna isa tayi parkin ta kamo hannun Badiyya domin su shiga ciki, Badiyya ta turje tace ita sam bazata shiga ba. Gwaggo kwata-kwata bata sansu, duk sadda sukazo saita bata masu rai. Da kyar Firdausi ta lallabata ta samu ta shiga, suna shiga suka iske Gwaggo ta fito daga Boys quaters. "Ahh! Maraba da yan Barhim, ba'a ganinku sai kun mula kunsha iska." Ta fada, tana wanke hannun ta. "An shigo birni an waye." Ta fadi tare da shiga falonta. Su Firdausi tsaye sukai, sai daga baya suka ji Gwaggo nacewa. "Ku shigo mana, ko gyamar gidan ake kuma?" A hankali suka karasa falon, suka iske ta zaune kan kujera ta dora kafa daya kan daya. Firdausi ta zauna kasa hade da janyo yarinyarta suka zauna. "Ina yini, Yaya." Firdausi ta fada a hankali, dan tasan Gwaggo komai laifine a wajenta. Gwaggo ta jiyo ta wani galla masu harara. "Ita wannan shegiyar yarinyar bata iya gaisuwa bane?" Jin haka Firdausi ta zunguri Badiyya. "Gwaggo ina yini?" Badiyya ta fada tanata daure fuska, dan batasan yadda Gwaggo ke masu magana, dukda batasan me wasu maganganun ke nufi ba. Bata ansata ba saima tsaki data ja, a haka har sukai kusan minti talatin, amma Gwaggo ko kallon inda suke batayi ba. Firdausi ta mike a hankali tana fadin "Yaya, zamu wuce." Ta fada tana janyo hannun yarta. "A gaida gida." Gwaggo ta fada, ko kallonsu batayi ba. Zuciyar Firdausi duk ba dadi, tana zuwa wayan Yaya ne bawai dan itama abun bai bata mata rai ba, saidan Badiyya ta saba da dangin mahaifinta. Amman ba komai, komi na duniya me wucewa ne. Har suka isa Layout ba wanda yace wani abu, Badiyya sai bata fuska take kamar zatayi kuka. Suna isa, Firdausi da kyar ta samu Badiyya ta shigo gidan. Koda suka shigo kin shiga cikin parlour tayi, ta zauna bakin kofa tanata zane a kasa, daka gani kasan tana cikin damuwa dukda yarinya ce. Sultan ya shigo zai dauki ruwa yaga yarinya durkushe bakin kofa, sosai yake kallonta ya kasa ganewa, yana duba yatsun kafarta ya gane wacece. "Badiyya meya faru?" Ya tambaya yana janyota jikinshi. "Sultan am, na tsani Gwaggo wallahi, kullun saita saka Momy damuwa in mukaje." Ta fada, hawayen data dade tana rikewa suka zuba. "Gidanta kuka je ne?" Ya tambaya, damuwa shimfide kan fuskarshi. "Eh mana." Ta fada, tana goge hawayenta. "Kuma saida na fada ma Momy kar muje amma taki yarda." "Kar ki tsane ta Badiyya, babu kyau tsanar mutun kinji. Kuma kinga Yayar Dadynki ce." Ya fada, yana tayata goge hawayenta. "Bari na daukeki picture, kinyi kyau." Ya fada yana ciro wayarshi. Ta bude baki zatai magana ya dauketa. "Wow! Badiyya kinga kyaun da kikai kuwa?" Ya fada yana kamo hannunta domin ta gani. "Lah! Sultan am, muyi tare to." Ta fada, tana murmushin farin ciki. "Eh muyi, kinga dama next week zan koma school, sai inta kallo ko?" Ya fada hade da daga wayar yana snapping dinsu. A haka sukaita pictures, dariya suke harda kyakyatawa. Firdausi a haka ta fito ta samesu domin su tafi gida, bataso Maghriba tayi masu anan. "Aa, Malam Sultan, ya hakuri?" Firdausi ta fada. "An gode Allah Anty." Ya fada yana sosa keya. "To Allah ya jikanta. Badiyyar Sultan am, sai ki taso mu tafi ko." Firdausi ta fada tana dariya. "Bye, Sultan am, sai to min garti( sai na zo)." Ta fada, hade da kama hannun Firdausi. A haka ya raka su har bakin mota sannan ya koma cikin gida. *** Suna dawowa gida ana kiran sallar maghrib, Firdausi ta shiga daki tayi sallah har tazo fita taga paper kan mirror. Dum! Gabanta ya fadi, a hankali ta karasa ta bude takardar. _In har kinasan cigaba da zama lafia, to ki tabbatar kin yanke shawara kafin na dawo gida._ "Ahmad bazaka hakura ba ashe?" Ta fada hade dayin hanyar waje, bata kara yadda ya saka mata damuwa. Ta fita ta samu a Badiyya parlour tana zaune, sai dariya take ita kadai. Har Firdausi ta zauna batasan ta zauna ba, saida ta dafa ta tukun. "Badiyya, dariyar me kike?" Ta tambaya tana murmushi, domin itama dariyar yar tata ta saka ta farin ciki. "Momy, wallahi Sultan am nake tunowa." Ta fada tana murmushi. Firdausi tsayawa tayi tana kallonta, yanzu har Badiyya tasan ta zauna tana tunanin namiji? Bataso yarta tasha wahalar maza, domin basu da tabbas. "Badiyya kibar zama kima tunaninshi kinji, jekiyi assignment dinki." Firdausi ta fada tana kokarin tada ta zaune. Badiyya tayi nodding kanta alamar ta gane sannan ta wuce dakinta domin yin assignment. Firdaus nanan zaune Ahmad ya dawo. Bayan ya gama cin abincinshi; itadai batace dashi kala ba. Saida ya mula yasha iska sannan ya kalle ta. "Kin gama shawarar ko kuwa?" Ya tambaya. "Ahmad kayi hakuri, wallahi business nakesan farawa dasu, ya kakeso inyi?" Ta bashi amsa, hawaye har sun fara zuba daga idonta. "Kina nufin bazaki bani ba ko? To ni banga amfanin zama dake ba, tunda har bazaki iya taimakamun ba." Ya fada yana mata wani irin kallo. Kallo daya zakai mashi ka kauda fuskarka, saboda yadda ya hade rai abin tsoro ne. "Ahmad me kake nufi? Ya kake so nayi? Duk taimaka makan da nake bai isa ba?" Ta tambayeshi kukanta na tsananta. "Ohhhhhh..... gori zakiyi mani? Dama saida Yaya ta fada, kina zuwa kina cewa kina taimakamun. To banga amfanin zamana dake ba. Kije na sake ki saki biyu." Ya fada hade da bin hanyar fita. "Kuma ki dauki diyarki ku tafi, banson kukai man karfe tara na safe cikin gida." Yana gama fadar haka ya wuce dakinshi.5 Firdausi tsaye tayi, ta kasa koda kukan, wanda yake zuba ma ya daina zubowa. Sai a hankali kwakwalwarta take tuna mata da kalmar 'Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.' Tana fara karantata hankalinta ya dawo, sai lokacin wasu hawaye masu zafi suka fara kwaranya daga idanunta. Meyasa Ahmad zai mata haka? Me yasa sai lokacin da bata da kowa zai rabu da ita? Me yasa zai watsa mata kasa a ido lokacin da tafi bukatarshi akan komai?. Wannan duk kan dukiya ne? Dukiyar da hakkin ta ne? Dukiyar da gumin mahaifinta ne?. A take ta saki wata kara tare da fashewa da matsanancin kuka. Takai awa daya tana kuka, kafin ta tashi taje dakin Badiyya domin ta fara hada mata kayanta. Tana zuwa ta iske Badiyya na karatun Al-Qurani, nan take wani sanyi ya ratsa zuciyarta. Batace da ita komai ba, ta janyo akwati ta fara debo kayan Badiyya tana sakawa a ciki. Saida Badiyya ta gama karanta Surar tukun ta taso tasu wajen mahaifiyarta. "Momy kuka kuma? Meya faru? Dady ya kara dukanki ne? Me za'ayi da kaya kuma?" Duk wadannan tambayoyin tayi sune cikin sigar damuwa. "Badiyya, kiyi hakuri kinji, Dady ya sake ni. Yace na tafi na bar mashi gida, tare zamu tafi." Firdausi ta fada, wasu hawayen na zubo mata. Badiyya batasan me kalmar saki ke nufi ba, saidai tasan lokacin da kawarta Hindu ke basu labarin Babansu ya saki Mamarsu, kuma daga lokacin basu kara ganinshi ba. A nan take ta fashe da kuka, ita kanta batasan kukan na menene ba. Kukan zasu rabu da Dady ne ko kukan Momynta na kuka? Koko kukan halin da zasu shiga ciki take yi?. Toh Jama'a... Hakika Rayuwar Badiyya na cikin rudani, saidai muyi fatan Allah ya shige masu gaba. Shi kuma Ahmad, Allah ya ganar dashi gaskiya. Koya Rayuwar Firdausi da yar tata zata kasance?

0 Comments