BABBAN GORO CHAPTER 10

BABBAN GORO CHAPTER 10
Hawaye ne suka gangaro daga idon dattijon, ya kalli Mummy da fuskar tausayi ya ce+ “Kiyi min ko wane irin hukunci Salamatu na cancanci ko wane irin hulakanci daga gare ki amman ina son ki saurare ni ki kuma....” Bai karasa ba Mummy ta ɗaga masa hannu har lokacin batayi magana ba ta nuna masa kofa, a maimakon ya juya ya fita sai kawai ya faɗi zaune yana kuka “Dan Allah ki saurare ni nasan ni mai laifi ne amman kiyi ma girman Allah ki saurare ni” Sai a lokacin Mummy tayi masa magana da jan ido, “Sauraren tsawar bakin hadari yafi min saurarenka ganin mutuwa ta yafi min ganin ka, ka fice daga gidan nan tun kamin na kashe ka!” Kallo ɗaya zaka yi fuskata ka tabbatar da furucin dake fita daga bakinta har cikin zuciyarta yake, shi kuma ya wani marairaice ya koma abun tausayi sai kuka yake yana kokarin rika kafarta “Ki kashe ni Salamatu matukar kashe ni zai sa ki sassauta min wallahi a shirye nake na mika miki rayuwa ta Salamatu dan Allah ki saurare ni” “Wallahi ko zan kashe ka ka sake rai na sake kashe ka ka sake rai na sake kashe ka bazan sassauta maka ba dan haka ka fice min daga gida” Kuka yake sosai kuka mai ban tausayi, “Dan Allah ki saurare ni Salamatu ko dan yar mu....!” “Y'a ....” Mummy ta ɗan ja baya tana mishi wani kallo da ba zan iya fassara shi ba, shi dai ba kallon mamaki ba, kuma ba kallon tsoro ba, ba kuma kallon tausayi ba. “Kai baka ji kunyar furta wannan kalamin daga bakin ka ba? ashe kasan kana da Y'a lallai rashin kunyar ka da yawa yake” Mummy ta kalli Talatu tun ɗazu take tsaye tana kallon ikon Allah “Ki ra min Sani da Mu'azu” Cikin sauri ta juya ta fita, bata daɗe ba tadawo tare da su ko wanne sai kallon Dattijon yake da alama ta labarta musu gulmar. Mummy ta nuna musu shi “Kun ga fuskarsa kun ga kamaninsa?” Duk suka ce Eh har talatu, Sani ne ya duka yana kallonsa dan kara tabbatar da kamanin nasa. “Ku fitar min da shi kuma karku sake bari ya shigo min gida duk kuka barshi ya shigo min gida a bakin aikin ku!” Kallonta sukayi suka sake kallonta jin furucinta sannan suka shiga kokarin mikar dashi tsaye. “Idan ke ba zaki saurare ni ba toh ki sadani da Y'a ta, dan Allah ki nuna min ita” Ya faɗa cikin kuka yana kara zubewa. Hannu Mummy ta ɗaga musu alamar su rabu da shi ta nufi upstairs tana faɗin “Biyo ni na nuna maka Y'ar ka” Cike da kwarin guiwa ya tashi ya rufe mata baya har suka shiga ɗakin Minal. Mummy sai da ta kai tsakiyar ɗakin sannan ta juyo ta kalleshi ta nuna masa pictures ɗinta “Ka ganta nan, gaka tufafin nan, kaga takalminta nan, ga gadonta can da kayan kwaliyarta” Duk abunda ta nuna masa kallo yake dan shi sam bai gane inda ta dosa ba, can ya ɗaga kai yana kallon hotunan nata, Wani gurin tana tare da Mummy wani gurin da Kairat wani da Yan makarantar su wani kuma da Deen sai wanda sukayi da abokanta na kasar waje da kuma wanda tayi tare da Mummy da Kairat. Tabbas yarsa ce dan babu abunda ta rage a kamaninsa wani kallo ya bi ɗakin da shi wanda zan iya cewa na farin ciki ne da kuma jindaɗi. “Ina take.?” Ya tambaya yana kallon Mummy idonsa na zubar da hawaye. Mummy kamar mai jira a take ta bashi amsa, “Ta tafi inda zaka je zanje mu tsayu da ni da kai da ita a gaban mahalincin mu ayi mana hisabi na jidaɗin da ba kayi ido biyu da ita ba na jidaɗin da bata raye bata ga wulakantaccen uban ta ba!” Nan take kalarsa ta canja hawayen da ke masa zuba suka tsaya, ya saka hannunsa ya dafe gefen zuciyarsa ya faɗi zaune yana kallon tile ɗin ɗakin kamar wanda bai san inda yake ba. Mummy ta kwala ma Sani kira, yana shigowa ta nuna masa shi. “Ku fitar min da shi karku sake bari ya shigo min gida” “Toh Hajiya” Da sauri ya duka ya shiga kokarin tayar da Dattijon tsaye, daker ya tashi tsaye har lokacin yana dafe da zuciyarsa ya rika tafiya a hankali sani na ruke dashi har suka sauka downstairs. faɗuwa Mummy tayi zaune ta kai hannunta gurin takalmin Minal taja ɗaya ta rumgume ta fashe da wani irin kuka muryarta har rawa take. *** *** *** A hankali Kairat take driving, har ta isa gidansu, bayan tayi parking taja gyalenta ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fito ta nufi cikin gidan. Babu kowa farlon hakan yasa ta nufi ɗakin Hajiya. tun kamin ta karasa take jin shesshekar kukan Hajiya, ta daɗe bakin kofar sannan ta kai hannu ta tura kofar a hankali. Unkurin ɓoye kukanta Hajiya tayi ta maida fuskarta gefe tana share hawaye. Kairat ta karasa kusa da ita ta risina ta ɗora hannayenta saman guiwoyin Hajiya “Ga ni Hajiya gani na dawo” Bayan ya gama share hawayen nata ta juyo ta kalli Kairat “Ai kara da kika dawo ba zaki sake zama can gidan ba” A hankali Kairat ta soma magana “Hajiya yanzu idan na mutu ya zaki ji?” Wani kallo tayi mata “Wace irin magana ce wannan?” “Hajiya ki auna ki gani yanzu idan na mutu ya zaki ji. naga ke baki shaku da ni kamar yadda Mummy ta shaku da ni ba a hannunta na tashi tun ina karama ita tayi ta ɗawainiya da ni har na kawo a inda nake yanzu rana tsaka sai kika ce zaki raba mu bayan mun shaku da juna kuma ni kaɗaice farincikin ta a yanzu shin idan kece ya zaki ji?” Shiru Hajiya ta ɗanyi kamin ta kalli Kairat “Toh saboda me zata sa kije gurin Abban ku kice ya aure ta wane irin halacci ne ba muyi mata ba!” Tashi Kairat tayi tsaye, ta zauna kusa da ita ta yadda zata fuskance ta. “Hajiya na tabbatar zuciya ce a kirjin ki Hajiya ba ko taɓa tausayin Mummy ba? ba ki taɓa mata fata na ta sake samun wasu yayan ba? Mummy bata taɓa yi ma Abbah kallon so ba kullum a uba take ganin shi bata taɓa sha'awar auren mijinki ba tun zaman ta gidan nan bata taɓa cin amanar wani ba baki taɓa jin ance an ganta da wani ba, Duk da hakan zuciyarki bata yi sha'awar ta kasance abokiyar zaman ki ba? Wallahil azim Hajiya Mummy ba ita ta tura ni tasa nayi ma Abbah magana ba nice naga dacewar hakan kuma nayi masa bata sam da wannan maganar ba sai yau sanadin haka yasa tayi min wannan marin” Ta nuna ma hajiya gefen fuskarta gurin da yatsun Mummy suka kwanta mata a kunci. ido Hajiya ta tsura mata tana kallonta kamar mai karantar abu a fuskarta. zuwa can ta ɗauke kai ta sauke ajiyar zuciya. Kairat ta rika hannunta “Na sani Hajiya Mummy ba zata taɓa yarda ta auru Abbah ba. saboda halaccin ta ki kwantar da hankalinki aure ba zai taɓa shiga tsakanin Mummy da Abbah ba” Hajiya dao bata ce mata komai ba, hawayen dake makkale a idonta suka zubo mata a nan ta dantse bakinta. Sun daɗe a haka ganin bata da niyar magana yasa Kairat ta tashi. har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo ta ta kalleta daga gun da take da duka kasa ta haɗe hannayenta kamar mai neman gafara tana hawaye tace “Na haɗa ki da girman Allah Hajiya karki hana ni shayar da Lil Minal, Hajiya ko da Minal na raye ni mai iya shayar da Y'arta ce balle bata raye, Kullum Minal tana faɗa har a gaban ki cewar idan ta haihu ni zan raini yarta dan Allah Hajiya karki hana ni yin wannan shi ne farin ciki ne” Har lokacin Hajiya bace mata komai ba sai hawaye take. Kairat ma bata sake cewa wani abun ba ta tashi jiki ba gwari ta fice. *** *** *** Nasir ya sauke ajiyar zuciya tare da shafa kansa, “Toh kai yanzu ya kake ganin za'ayi?” “Ya za'ayi ban da a kyale ta in yaso sai Safiyyah ta shayar da ita” “No” Nasir ya girgiza kai “Ni kaina ban yarda Safiyyah ta shayar da ita ba Kairat ce ta cancanta ta shayar da ita kuma na tabbata da ta samu damar yin wasiya da sai ta faɗi haka” Shiru Saif yayi yayi ma bakins wani abu alamar damuwa “marry her and make her happy shi ne abunda Minal ta faɗa min lokacin da zata rasu tace min ka auri Kairat dan ku kula min da abunda zan bari that's mean na bar Kairat ta kula da yarta but the problem is ita ta ki aminta” Nasir ya tari numfashinsa “Wannan ba hujja bace kamata ƴyayi ka lallaɓa ta baka san dalilinta ba tun da kaga abun ya kai har gurin iyayenta” Saif ya kalleshi “Lallaɓa ta? karamar yarinya ce da zan lallaɓa ta” “Ba a haka Saif yarinyar yar ka ce bai kamata ka nuna halin ko in kula ba beside ni wallahi Kairat ɗin nan har tausayi take bani yarinya ce mai hakuri da hangen nesa ta raba hankalinta gida biyu ni ina ganin ma ta wannan hanyar zaka iya cika burin ka ka kuma cika wasiyar Minal” Kai Saif ya gyaɗa “I'm not ready yet” Nasir zaiyi magana wayar Saif tayi kara, ganin number Abbah yasa shi saurin ɗauka, “Hello. okey gani nan zuwa” Shine kawai abunda ya faɗa ya kashe wayar ya kalli Nasir “Daddy na nema na” “Ok muje kaji kiran nasa sai muje gidan su Kairat ɗin” Tashi sukayi tare suka shi ya nufi part ɗin Daddy Nasir kuma ya nufi parlour Mummy. Da sallama ya shiga. bayan ya samu guri ya zauna ya kalli Daddy yace “Gani Dad” Sai da ya gama duba jaridar dake gabansa sannan ya ɗago ya kalli Saif. “Akan maganar Huda ne ko ɗazu sai da Mahaifinta yazo gidan nan, ya faɗa min ko abinci bata iya ci a yanzu ta koma wata kalar mace su kansu yanzu abun ya dame su” “Toh ya za'ayi da Kaddara tayi hakuri kawai haka Allah yaso” “Ba haka naso ji daga bakin ka ba Saifullahi ya kamata ace a yanzu ka duba mata nasan iya nadama yanzu tayi ta kuma kaga ko dan yawon da mahaifinta yake a gidan nan ya kamata ka mutun ta shi” Bakinsa ya cika ma iska “Dad ni fa ban gane ma maganar ka ba wannan zirga-zirgar da mahaifinta yake yi ban ga amfaninsa ba kai ma sai naga kamar kana manta babu aure tsakani na da Huda” “Akwai aure tsakanin ku mana ba saki biyu ka yi mata ba?” “Biyu nayi mata a yanzu can farko na yi mata ɗaya kaga babu aure kenan ya cika uku” “Subhanallahi” Daddy ya faɗa yana ɗan nazari “Dad ita kanta tasan da haka sai idan sune bata faɗa ma ba amman Momy ma tasan da wannan” Nisawa Daddy yayi “Bari zanyi magana da Abban nata amman ka tabbata da gaske ne dai ko?” “Wallahi Daddy da gaske ne ka tambayi Momy tasan komai” Kai Daddy ya ɗaga masa yana tunano abubuwan da suka faru. *** **** ***** Kairat na shigowa parlour Talatu ta tashi tsaye da sauri tana faɗin “Yauwa kara da Allah ya kawo ki” Kairat ta kalleta “Lafiya ina Mummy?” “Tana can kuma ina jin kuka take. wani ne yazo mai kama da Minal wallahi fuskarsu ɗaya ina jin Babanta ne ko kuma ɗan'uwan Babanta shi ta shiga ɗakin Minal tun ɗazu har yanzu ta ko fitowa tun ina jin sautin kukan har na daina” Da gudu Kairat ta nufi upstairs. Kwance ta tararda Mummy duk ta watse komai na ɗakin fuskarta a kumbure idonta kuma suyi jawur alamar taci kuka har ta gaji. Sai da Kairat ta karema ɗakin kallon sannan tayi cikin Mummy da masifa “Haba Mummy kefa ba yarinya ce yar da kaddara nai da marar kyau yana cikin imani. Allah baya ɗorawa rayuwa abunda ba xata iya ɗauka ba. duk abunda Ubangiji yayi dai-dai ne Mumny ki yarda da wannan Allah bai raba ki da Familyn ki ba sai da ya baki wasu, bai karɓe miki farinciki ba sai da ya baki wani yanzu kuma ya karɓe miki Minal kin san abunda yayi miki tana di ? dukan tsanani yana tate da sauki Mummy yaushe zaki san da haka?” A maimakon Mummy tayi magana sai kawai ta fashe da wani sabon kuka, nan itama Kairat tasa nata kuka “Kuka kike yi Mummy, Hajiya ma kuka na baro tana yi. ya kuke son nayi da raina ne?. Wayyo Allah na ina ma ni ce na mutu ba Minal ba da baki shiga halin da kike ciki ba yanzu da ran Hajiya bai ɓace ba har ya kai ta gayin saɓani da ke, da Saif bai rasa matarsa da lil Minal bata rasa mai shayar da ita ba Alhamdulillah Allah ni kan na gode maka” Ta faɗa ta karfi sannan ta juya tana kuka ta bar ɗakin. Tashi Mummy tayi zaune ta share hawayenta sai kuma tayi shiru kamar mai tunani zuwa can ta tashi ta nufi ɗakinta. *** *** *** Tare suka shigo parlour ko wanne sanye da farar shadda, bayan sun gaisa da talatu Nasir ya zauna Saif kan tsaye yayi kamar bako. “Ina mutan gidan?” Nasir ya tambaya yana kallon upstairs, Talatu ta tashi tana faɗin “Tana ciki bari na mata magana Kairat kan tana Garden” Kai Nasir ya ɗaga mata Saif kuma ya juya ya nufi hanyar Garɗen ɗin. Sautin kukan ta ne ya sadashi da gurin da take, zaune ya hango ta ta kufa kai da guiwa tana kuka, ya daɗe yana kallonta haka kawai sai ya samu kansa da rashin jindaɗin kukan nata. karasawa yayi kusa da ita rumgume da hannayensa. Kanshin turaren da taji ne yasa tayi saurin juyowa ta kalleshi, sai kuma ta maida fuskarta ta shiga share hawayenta “Me kike yi ma kuka.?” Ya tambaya yana kara gyara tsayuwarsa “Ba komai ba kuka nake ba” “Ba komai kamar ya ko wani abun akayi miki ne?” “Nace maka ba komai” Ta faɗa kamar mai shirin sake yin kukan. Tashi tayi tsaye ta saka takalmin ta ta nufi hanyar parlour abunta ta barshi tsaye. kafaɗunsa ya ɗaga ya rufa mata baya. Da ruwan kuka ta shiga parlour ganin Nasir yasa ta sha jinin jikinta ta ɗan natsu “Ina wuni” Tace dashi tana kokarin ɓoye kuka nata, bai amsa mata ba ya kalli Saif dake bayanta ya sake kallonta ya kalleshi, Saif ya ɗaga kafaɗunsa alamar bashi da ruwa a kukanta, a sannan Nasir ya amsa gaisuwarta “Lafiya kalau ya gida?” “Lafiya kalau” Ta zauna saman kujera tana kallon center carpet, Nan shi ma Saif ya samu guri ya zauna yana kallonta “Saif ya faɗa min Mummy tace masa wai kin fasa shayar da Lil Minal haka ne?” Shiru ta ɗanyi, ita dai bata san tayi wannan maganar da Mummy ba maybe Mummy tace haka ne dan ta hana ta shayar da ita, sai da ta ɗanyi gyaran murya sannan tace “A da ba amman yanzu ni zan shayar da ita” “Ba zaki shayar da ita ba Kairat Saif na faɗa maka ka nemo mai shayar ita Kairat ba zata shayar da ita ba ba matar aure bace ba bazawara bace ba kuma tsohuwa bace ba zan yarda ta shayar da ita ba!” Mummy ta faɗa tana saukowa downstairs, Nasir ya kalleta dai-dai lokacin da ta karasa saukowa “Wannan ba matsala bane Mummy Kairat ba zata fara shayar da Lil Minal ba sai Saif ya aureta. shi kansa yayi tunani akan hakan shiyasa ya yanke wannan shawarar” Daga Saif har Kairat tashi sukayi tsaye suna kallonsa, Kairat ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nasir ya ɗan taɓe baki “Kunyar kake ji ne? ba shine abunda ya kawo mu ba ba kai da kanka ka faɗi hakan ba?” Mummy dai sai kallon Saif take shi kuma ya sakar ma Nasir ido yana masa kallon da shi kaɗai ya san amsar sa.Nasir ma daga zaunen da yake ya tsare Saif da ido yana masa kallon jiran amsa. Sun daɗe suna kallon juna shi da Nasir kamin ya ɗauke kai ya kalli Mummy sai kuma ya saci kallon Kairat da ido sannan ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.+ “Samu guri ki zauna mummy” Ya faɗa ba tare da ya sake kallonta ba, Kairat tayi musu kallon rashim fashimta “Ta zauna kamar ya? ni ban gane nufin wannan abun da kuke kokarin yin ba ni dai na riga na aminta zan shayar da ita dan haka duk wata magana ku ajeta gefe” Saif ya kalletaƙkamar a fusa ce “Ki bamu guri Kairat ba dake zanyi magana ba wannan tsakanin ni da mummy ne” Zatayi magana Mummy ta tari numfashinta “Jeki ɗakin ki Kairat” “Mummy...” Sai kuma tayi shiru, tsaye tayi kamar ba zata ba sai dai kuma ba zata iya yin musu da Mummy ba, ba dan taso ba ta juya ta nufi hanyar ɗakinta. Bayan Mummy ta zauna Saif ya kalleta a natse ya soma magana “Mummy kina da gaskiya na hana Kairat ta shayar da Lil Minal. ni kaina sai da nayi tunani na gano hakan dan haka nima ban bada goyon bayan ta shayar da ita ba. Sai dai kuma Mummy ba zan iya ba wata wanda ba Kairat ba ta shayar da Lil Minal saboda ban san halinta ba ban san ya addininta yake ba, kuma kinga ba wai zata shayar da ita kawai bane zata raine ta ne ta nuna mata tarbiya har na ɗan wani lokacin. Babu matar da na yarda da ita irin Kairat a yanzu, kuma ba zai yiyu ta shayar da ita tana budurwa ɓa dole sai tayi aure. in kuwa haka ne toh ni nafi kowa cancantar na aureta tun da yata zata shayar sannan kuma ina son na rika ganin su karkashin kulawata kuma ta haka ne kawai zan iya cika wasiyar Minal hakan kuma ba zai taɓa samuwa ba sai da haɗin kanki da kuma amincewar Kairat ” Tun da ya ɗauko magana Mummy tayi natsu tana saurarensa, shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗan daɗe kamin ta ɗago kai ta kalleshi “Kayi tunani mai kyau Saif zan kuma goya maka baya ɗari bisa ɗari in har da zuciya ɗaya zaka yi. sai dai kuma ba zan cillas ta yin abunda bata so ba ba kuma zan hana ta abunda take so ba ina fatar ka fahimta” Kai ya ɗaga mata “Bana nufi hakan Mummy, ko kaɗan babu hakan cikin rai na kawai ina son kiyi shawara ne ke da ita ki kuma nuna mata abunda ya dace” Yana kawai nan ya tashi tare da zuba hannayensa cikin Aljihu “Na barki Lafiya Mummy sai naji daga gare ki” Nasir da tun ɗazu mamaki ya kashe shi ya tashi shima yayi mata sallama ya fice. A Mota Nasir yayi ta yima Saif magana yaki ya amsa masa sai tukinsa yake har suka isa gida sai da yayi parking sannan ya kallesa “Dan mi zakayi min haka Nasir? wannan ba shine karo na farko da kake min irin wannan katsa ƙandan ɗin ba ban san miyasa kake min haka ba!” Tuntsurewa yayi da dariya “Ba gashi ka faɗin abunda yake ran ka da kanka ba ni ai soso maka gurin da yake kaikayi ne kawai nayi. Kuma Saif in bakayi auren nan yanzu ba yaushe kake tunanin zakayi shi? kai fa ba yaro bane kasan abunda ya dace” Saif dai bai sake ce masa komai ba ya buɗe Motar ya fice. ganin haka yasa shima ya buɗe motar ya fita. a tare suka shiga parlour Nasir na ta jan Saif da maganar shi kuma ya masa shiru kamar ba dashi yake ba. Guri ya samu ya zauna yana kallon Momy dake kallonsu ya gaishe “Momy an wuni lafiya?” “Lafiya kalau ina kuka fito haka? tun ɗazu na aika a kira min kai akace ƙa fita” Ta karasa faɗa tana kallon Saif, “Eh mun ɗan fita ne” Ya bata amsa yana kallon Dinning dan yasan ba zai wuce maganar abinci ba, dan yanzu ta mauda shi kamar karamin yaro ganin baya son abinci. “Gidan Dr. Salamatu muka fito Momy” Kamar wanda aka matsi bakinsa haka maganar ta fito a baki Nasir yana ɗan Murmushi “Me kuka je yi ko maganar Lil Minal ne?” Nasir ya nuna shi “Zai miki bayani ni yunwa nake ji” Da kallo Saif ya bisa har ya zauna saman kujerar dininning yana mamakin yadda take aron bakinsa yana ci masa albasa, “Lafiya dai ko?” Momy ta tambaya ganin yayi shiru baice komai ba sai hararar Nasir yake. Sai a lokacin ya kalli Momy yana mata wani murmushi daya kara fitar da ramarsa, zaiyi magana Sallamar Safiyyah da Lubna suka katse su. Haɗa baki sukayi da Momy gurin amsa musu sallamar Lubna ta zauna kusa da shi yayinda da Safiyyah ta zauna kasa tana kallon tv. “Ina jinka” Momy ta faɗa tana mai hankalinta gurinsa Sai da ya nisa sannan ya fara kora mata bayani, “Momy akan maganar shayar da Lil Minal ne, toh shine Mummy tace ba zata bari ta shayar da ita ba tunda ba ta da aure. kuma nima ina goyon bayan hakan tunda gaba sai iya zame mata matsala” “Oh yanxu ta fasa shayar da ita kenan?” Momy ta tambaya, “Eh toh ba wai ta fasa bane ita tana son ta shayar da ita matsalan ba daga gare ta bane, Toh shine Nasir ya bani shawarar na aureta kawai ta yadda zata iya shayar da ita tana matata kuma karkashin iko na tun ni daman ba son nake Lil Minal tayi nisa da ni ba.” Annuri ne ya cika fuskar Momy ta jidaɗin maganar sa sosai, daman abunda yake da munta a yanzu kenan dan gani take idan yana da mata wannan damuwar da yake ciki zata ragu. “Kayi tunani mai kyau Saif hakan na nuna ka fara yarda da kaddara kenan. kuma kayi sara kan gaɓa, jiya fa muke magana da Abbah ka yake cewa ya kamata ka samu matarm aure ta yadda zaka rage wannan damuwar” Murmushi Saif yayi “Momy ai yarda da kaddara waji bi ne ga duk musulmi, kawai dai sabo ne da kawa zuci irin na ɗan'adam” Lubna ta rika hannunsa tana murmushin jindaɗi, “Wow Yayana ya kusa zama ango Allah ya tabbatar da alkhairi amman Yaya zakayi mata mai mutunci wallahi ana yabon Kairat da tarbiya nima yarinyar tana burgeni. amman Yaya ta yarda?” “Yardar nata dai nake nema duk da nasan abun zai zame mata wani iri” “Gaskiya kan sai taji daban sai kayi hakuri da ita” “Ko kuma ita tayi hakuri da ni ba” Ya mayar ma Momy da amsa yana ɗan taɓe baki. tashi Safiyyah tayi tana kokarin ɓoye kukan ta, ta nufi ɗakinta. Duk suka bita da kallo har ta shige. Maida kofar ɗakin tayi ta rufe wani irin kuka mai karfi ya zo mata, bata son ta fasa shi su jita duk da tasan sai sun zargeta ganin bata sa bakinta ba, gashi kuma ta taso ta baro musu ɗakin. Makullin Mota ta ɗauka tare da waya ta shiga bathroom ta wanke fuskarta sannan ta nufo downstairs. Ko da ta sauko Momy da Nasir kawai ta tarar sai kuma Saif dan Kairat bata gurin Momy kawai ta kalla “Momy zan ɗan fita naje gidan Gwaggo” “Toh ki gaishe ta Allah ya tsare” Bata amsa mata ba kai kawai ta ɗauke ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga Parlour. Nasir ne ya bita da Ido har ta fice, sannan ya kalli Saif dake aikin dannar waya ya ce “Ina jin maganar auren nan da kayi ne yasa taji ba daɗi” Kafaɗunsa ya ɗaga ya taɓe baki, alamar bai damu ba ya cigaba da abunda yake. Momy ta sauke ajiyar zuciya “Wallahi yarinyar nan tana son ka Saif ni wallahi har tausayi take bani da zaka bi shawara ta da ka aure ta” Sai a lokacin ya aje wayar dake hannunsa ya kalleta “Momy da zan iya auren Safiyyah da tuni na aure ta yun da ba bakuwar fuska ta bace a nan gidan fa ta tashi” “Toh ai ko ɗan haka yaci ace kayi mata wannan halaccin, ina fa maka tsoron kar kaima kaje ka samu mai yi maka haka gaba kayi aure na ɗaya ka barta ka kara wani ka barta yanxu ka zo da maganar wani ai mutane ma sai su zargi abu cewa za'ayi dan ita ba yata bace yasa kake mata haka gashi taki ta tsayar da Miji” Nasir ya ce “Kar hakan ya dame ki Momy nan gaba kaɗan xata fito da mijin aure dan kanta” “Ni abun har mamaki yake bani wallahi wai mace da aka sani da kunya ita zata fito kiri-kiri ta nuna tana son ka ni bana son irin wannan rayuwar” Saif ya faɗa yana taɓe baki Nasir ya karɓa masa “Aiko yanzu mata yawancin su duk haka suke sai ɗaiɗai ku su suke kai tallar kansu da kansu gurin maza musamman in suka ga wanda yayi musu” Momy ta ɗan ɓata Fuska “Toh. miye haramun ne? ai Annabi yace duk abunda kake so ka ce kana son shi, sannan a zamaninsa ma an samu mace da taje tace tana son Annabi (S.A.W) balle yanzu da zamani ya canja” “Momy ai ana barin halal dan Kunya, irin wannan can daban irin wannan daban wannan baya jawo komai sai rage ma mutun kalama da mutunci a idon namiji” Saif na kaiwa nan ya tashi ya nufi dinning area. Kacar Safiyyah taga ta isa gidan Gwaggo, aiko tana shiga faɗi falonta ta fashe da kuka dan fashe kurjin da yake mata ciwo. da gudu Gwaggo ta fito daga kicin tana tambayar “Lafiya? wani ne ya mutu?” “Da mutuwa ce Gwaggo da yafi min sauki” “Miya faru haka ne Safiyyah?” “Gwaggo Saif aure zaiyi” Ta faɗa cikin kuka har muryarta na rawa, “Oh shine kike wannan kukan ? yau kika saba ganin Saifu yayi aure ne? tashi ki share hawayen ki da yarda Allah kece amaryar” Cigaba tayi da rairai kukan tana faɗin “Gwaggo ba zaki gane ba” “Na gane mana Safiyyah babu abunda Saifu da Mahaifiyarsa keso sai ki mutu. ai tasan ta yadda zata iya sashi ya aure ki amman taki kuma tsan yana sonki da yanzu kece baki sonsa cillas ta miki aurensa zatayi. matar nan ko dan tashin da kikayi a hannuta yaci ace tayi miki wannan karancin. amman batayi ba dan tsabar mugunta” Cikin kuka Safiyyah ta kalleta, “Wallahi Momy bata so na Gwaggo bata tausayi na rayuwar yayanta kawai ta sawa gaba ko dan taga bana da uwa ba uba shiyasa take min haka” “Na sani Safiyyah ai matar ɗan uwa ba ɗan uwa bace shiyasa nake son ki daina kuka lokacin kuka ya wuce kamata yayi mu tashi tsaye muyi abunda xai fitar da mu” “Toh Gwaggo me zamu yi? bana ganin akwai wata mafita” “Akwai mafita. nasa abinci ka min wani malamai kwararin kuma an samu mo min ta hanyar su zamu bi har bukatar mu ta biya” tashi Safiyyah tayi tana share hawaye, “Gwaggo yaushe zamu je?” “Ba sai mun je ba su da kansu zasu zo nan gidan zan zuba kuɗi a ɗauko min su daga duk inda suke suyi min aiki” Rumgume ta Safiyyah tayi tana kuka. Kairat ta tashi zaune tana kallon Mummy idonta cike da hawaye “No Mummy ba zan iya ba” “Zaki iya Kairat Saif yana da mutunci yana ɗa karamci bana jin zaki samu matsala a zaman ku dashi” “Ba shi nake nufi ba Mummy ba zan iya auren Mijin Minal ba, ba zan iya auren wanda bana so ba” “Ta wannan hanyar ce kawai zaki iya share min hawaye na ta wannan hanyar ce zaki wanke ni daga zargi, ta wannan hanyar ce kawai zaki iya shayar da yar ki cikin kanciyar dan duk namijin da kika aura ba zai yarda ba taɓa yarda ki shayar da yar wani ba ba kuma zan barki ki shayar da ita kina budurwa ba” “Mummy....” Mummy ta tari numfashinta “Kairat ina son kiyi tunani ki kuma yi shawara amman mummy ki ba zata cutar da ke ba” Kai Kairat ta ɗaga mata tana lasar bakinta idonta kuma cike da hawaye, Mummy ta shafa kanta ta tashi ta fice. Wayarsa ce take ta ringing alamar kira, shi kuma yayi kamar bai jita ba sai tunane tunane yake, sai da aka masa kusan kira biyar sannan ya tado kai ya kalli wayar dake kan mirrow. ɗauka yaƴi bayan ya danna picking ya kara a kunne, shiru yayi bai yi magana ba hakan yasa mai kiran yin magana “Hello Saif....” Muryar Huda ce cikin kuka ta kira sunan nasa. Dafe kai yayi ya ɗan yatsina fuska “Ya a'akayi?” Ya tambaya kamar baya son magana, ta ɗan daɗe kamin ta sake cewa wani abu “Na kira ne naji muryar ka na kuma roki gafarar ka a zaman da mukayi, nasan munyi samun taɓani kuma naci amanar ka dan Allah Saif ka yafe min har abada ba zan taɓa samun miji mai hakuri da juriya irin ka ba Kayi min halacci ta ko ina kayi min adalci Saif baka taɓa cin amana ta ba baka taɓa tauye min hakkina ba ina rokon Allah ya haɗa ka da mata ta gari wanda ba zata ha'ince ka ba Allah ya raya maka abinda Minal ta bari. karka manta da soyayyar Huda a zuciyarka ina Huda na son ka sosai Saif karka manta da wannan.....” Da sauri ya kalli wayar jin kiran ya katse. wani dogon numfashi yaja ya lumshe ido, maganganunta suka tsaya masa a rai. damuwarsa ta karu yana cikin wacan tunani yanzu kuma ga wani dafe kansa yayi jin yana masa wani sara. babu abunda ya faɗo masa a rai sai Happy Island tashi yayi ya ɗauki keys ɗinsa cikin yan mintuna ya bar gidan. *** *** *** “Allah sarki Sweet Friend wai ke da niyarki sai zama zaki yi sai ranar da yazo yace yana sonki? ai an daina wannan yayin yanzu idan kawai kika ga wanda yayi miki zuwa kawai zakiyi a asirce shi shikenan sai yadda kika yi dashi” Shafa ta faɗa tana wani rausayar da kai, “Toh ai ni ba zuwa gurin bane kar sa ka kauce hanya ka kwasar ma kanka zunubi” “Ah lallai sabuwar shiga ce kwace hanyar na yaushe ai tunda kika ce baki yarda da kaddarar son da Allah ya ɗora miki ba na son Saif kika ki hakura kin daɗe da kwance hanyar. Zunubi kuma na nawa? ba ke kika shiga kika fita ba har sai da kika kulla zargi tsakanin mata da miji zama ya gagare su kika ɓata amintar aminai ai kin daɗe da tara wannan zunubin sai dai kawai indan munyi wannan sai mu taru mu tubar ma Allah” Shiru Safiyyah tayi bata ce komai ba kamar mai tunani, hakan yasa Shafa taɓe baki “Ba zai fa taɓa sonki ba tun da kika nuna kina sonsa, bama kece gabansa ba ai maxa sun gware a wannan fannin arkinki ɗaya wannan ba ɗan duniya bane da sai dai yace yayi amfani da wannan damar ya nemi lalata ki” Ajiyar zuciya Safiyyah ta sauke “Toh yanzu ni dai yaushe zamu je?” “Ni idan zaki yarda yau ɗin nan zamu je ba sai gobe ba akwai wani boka a kauyen abujar nan yana aiki sosai kamar hankan wuka sannan ko wane irin aiki yana yi sai dai fa kuɗi” “Toh ko zamu je can ne kamin Gwaggo ta gwada nata? kuɗi ba matsala bane matukar akwai biyan bukata” “Ni kuma nace miki matukar akwai kuɗi to akwai biyan bukata, idan kin shirya kawai ki tashi muje” Tashi tayi tna faɗin “Bari na ɗan watsa ruwa.” *** *** *** Magana take da kanta tana safa da marwa can ta samu guri ta zauna ta dafe kai tana dauke ajiyar zuciya, “Innalillahi wa inna ilaihirraji” Shine abunda ta furta tana lumshe ido, bata buɗe ba duk da tafiyar da take ji a bayata har sai ta taji anyi mata magana “If you need someone to talk to I'm here” Juyowa tayi da saurin jin kamar muryar Saif, shi ko ne ba kama ba ya rumgume hannayensa yana kallonta “Me kazo yi a nan?” Kallon gurin ya shigayi kamar bakonsa “Na kan zo nan wani lokacin dan samun natsuwar zuci. tun lokacin da Minal ta faɗa min nan ne gurin zuwanta sai na samu kai na da sha'awar na kasance a gurin ko da yaushe, Kamar yadda kema nasan hakan ne ya kawo ki dan naga yadda kika shigo hankalin ki ba kwance ba” Yawun dake bakinta ta haɗe ta kalli itace dake gurin, shi kuma idonsa na kanta Yana karantar damuwarta “You can trust me Kairat” Ta Kalle shi “Why should I?” “Cos I'm the only one you can trust” Dauke kai tayi hakan yasa ya zagoyo gefenta ya zauna yana kallon tsuntsayen dake gurin ya soma magana a hankali “Kaiyrat babu ta yadda zaki iya shayar da lil Minal sai kina da aure miyasa ba zaki yarda kiyi auren ba idan har da gaske kike kina son Minal kina kuma son abunda ta bari, taya kike tunanin tarbiyantar da Yar Minal ba tare da ta girma a hannun ki ba? ko kin manta wasiyar Minal ne Kairat?” “A a ban manta ba, naji ba zan iya shayar da ita ba sai ina da aure amman kuma ba zan iya auren Mijin Minal ba, i can't” “Ba Mijin wata zaki aura ba mijin ki zaki aura uban yayanki” Ya faɗa yana kallonta ita, ma shi take kallo. hakan yasa ya kara fuskantar ta “Kairat bana son ki ra a ranki zamuyi wannan auren ne dan so da kauna kisa a ranki zamuyi wannan auren ne dan sadaukarwa. Zakiyi hakan dan Mummy da lil Minal kinsan me? a lokacin da Minal zata rasu ta faɗa min na aure ki na saki cikin farinciki, even on her bed dying ta kula da farin cikin ki misa ke ba zaki iya kula farin cikin yarta ba? ya kike tunanin lil minal ta girma ta buɗe ido taga mahaifiyarta ba raye ba?” Kai ta girgiza idonta cike da hawaye “Ba zan iya auren ka ba, ba zan nuna ma lil Minal bani na haife ta ba” “Taya zaki nuna mata hakan bayan baki auri mahaifinta ba.? banyi wani dogon zama da Minal ba Kairat abunda kike tunani ba shi bane nasan zakiyi rika ga yadda na saba rayuwata da minal ke kuma nayi rayuwa dake no ba haka bane kanun Minal ina da wata matar kin tuna kuma na zauna da ita mukayi tamu rayuwar daban ki sa a ranku saurayi zaki aura wanda bai taɓa aure ba ke zaki koya masa rayuwar aure ki karantar dashi naki karantun a makarantar ki” Kallonshi take tana mamakin yadda waɗannan kalaman ke fita bakinsa kamar bashi ne yake maganar ba sai kuma ta girgiza kai “Still ba zan iya ba Saif ya duniya zata kalleni...? i just can't.” Murmushi yayi mai sauti murmushin da ya kara fitar da kyau da kuma kamalarsa, “Duniya zata rik'a ɗaga ki ne, mutanen cikin ta kuma su rika kallonki karkace kiyi ta tafiya haka har baki ankara ba lokaci ya k'ure miki baki yi abunda zai amfane ki ba. Nasan yadda kike ji Kairat I feel the same way” Hannu ta kai ta ɗauki handbag ɗinta ta rata ya “I need to go home” tashi shima yayi tsaye, “Yes go home Kaiyrat kije kiyi tunani mai kyau kiyi abunda zai fidda ki karki manta da baya Kaiyrat karki cutar da kanki karki cutar kar kuma ki bujirewa Minal” Cikin kwayar idonsa take karantar abunda yake fita bakinsa, kallon kallo suka rika yima junan su kowanne ta tasa sakar a zuciya. ita ce ta fara yin jihaɗin ɗauke nata idon daga nashi ta haɗeye yawun karamin bakinta ta, taka a hankali tana tafiya kamar mai tausayin kasa. Da ido ya bi ta yana mata kallon da shi kansa bai san na minene ba? sha'awa, tausayi, so, ko kuma kauna! wani kalar yanayi nake jin kansa ciki yanayin da bai taɓa jin kansa ciki ba wani kalar yanayi ne mai wuyar fassara. A hankali ya kai hannu ya shafa kyakyawan gashin kansa ya tada kai yana kallon itace dake gurin yana lumshe manyan idonsa a hankali. Mamakin kansa yake yadda yake rokonta ta aure shi bayan bai taɓa yi ma wata mace hakan ba. wani gurin kuma gani yake yana da gaskiya saboda wasiyar Minal da kuma lil Minal. **** *** ***** BAYAN KWANA BIYU.... Safiyyah ce kwance ɗakinta fuskarta ɗauke da murmushi sai juyi take ta kafa tana jindaɗi. yau ne zata fara gwada maganin da malamin ta ya bata kuma ta yarda zaiyi mata aiki. tana jin fakawar Motar Saif ta tashi ta sauri ta leka windo ganin shi ɗin ne ya kara mata jindaɗi, Da sauri ta dawo ta buɗe jakar ta ta ɗauko wani kwalli ta buɗe maciyin ta kira sunan Saif sau uku ta tofa sannan ya shafa. daman haka yace mata duk zata shafa ta kira sunansa dan da sunan akayi aikin. Tana gama shafawa ta mayar a jaka ta nufi madubi ta dauki hoda ta shafa ta gyara jan bakinta ta buɗe wata durowa ta ɗauko wani turare daga ganinsa kasan na magani ta shafa, sannan ta juyo jiki na rwa ta nufo parlour. Ta koyi sa'ah tana saukowa yana danno kai cikin parlour, yana sanye da shada sky blue tayi masa kyau sosai kansa ɗauke da bakar hula. wani fari tayi masa da ido ta sakar masa mirmushi “Ya Saif sannu da zuwa” A maimakon ya amsa sai kawai ya wanke mata fuska da mari. 1 Kuyi Hakuri da wannan Anjima Wani Zai Zo Amman Ban Muku Alkawarin Mai Yawa Ba.😀 just keep voting and commenting on every single line. Stay bless Candy Love you from the bottom of her heart.😍Ja tayi baya da sauri ta dafe junco dan ba karamin mari yayi mata ba, “Lafiya mi tayi maka haka?” Momy ta tambaya tana tashi tsaye, sai a lokacin ya lura da Momy, juyar da fuska yayi ya ɗan haɗe rai. A nan ya shiga neman dalilin marin nata da yayi ya rasa, shi kan shi bai san dalilin marin nata dayayi ba shi dai kawai ya samu kansa da jin haushin murmushin da tayi masa da magana. “Momy parking tayi ba dai-dai ba gurin da nake aje mota na take ta aje” Ya faɗa yana kokarin kare kansa, tunawa da yau gurin da yake parking yaga motar ta fake, “Haba dan Allah dan Annabi sai kuma kayi mata wannan mari haka? Sai kace karamar yarinya, ai sai kaje kace ta ɗauke motar ko.? Ba ma ita ra fita da Mota ba Lubna ce” Shafa kansa yayi yana ɗan yatsinar fuska ya zauna saman kujera, kallonta yayi kamar yace tayi hakuri sai kuma yaji ba zai iya ba, ya kalli Momy data ranta ya ɓace ya ce “Na ɗauka ita ce sorry Momy” Banza Momy tayi dashi tana kallon Safiyyah da ta rufe ido tana hawaye, juyawa tayi kamar kazar da kwai ya fashe ma ta nufi ɗakin. “Ni Wallahi halin naka ya fara isa ta bana son abunda kake yima yarinyar nan ko kaɗan” Momy ta faɗa tana jan tsaki cike da ɓacin rai. Kallonta ya sake yi “Momy kiyi hakuri” “Wane irin nayi hakuri fusabilillahi abun da kake mata kyautawa ne? Ko kuma dan tana zama nan gidan sai ya baka damar yi mata duk wulakancin da kaga dama” “Momy mistake ne fa” “Wane irin mistake daga shigowar ka ka fece yarinya da mari kace mistake haka ake mistake to Wallahi daga yau sai yau ko Kallon banza karka sake mata balle ka ɗaga hannu ka dake ta” Momy na kawai nan, ta tashi a fusace ta shige ɗakinta. Gashin kansa ya shafa ya ɗaga kansa “Oh my goodness Momy ba zaki saurari abunda nazo dashi ba akan na mari Safiyyah, ya salam!” Ya faɗa yana girgiza kai. *** **** *** “Assalamu Alaikum” Yayi sallamar yana kokarin kunno kai cikin parlor, cikin taku irin nasu na manya. Dr Salamatu ce ta amsa masa Kairat kuma ta karasa gurinsa a guje ta rumgume shi “Sannu da zuwa Abbah” Ta faɗa cikin wani irin jindaɗi tana dariya, shina dariyar yayi yana faɗin “Yauwa yar Salamatu ya gidan naku?” “Gida lafiya kalau” Ta masa yayin da take ɗago kanta daga jikinsa, hannunta ya rika suka nufi three sitter suka zauna. “Ina wuni Salamatu” Abbah ya gaishe ta ganin yadda ita ɗin ta kasa masa magana sai wani abu take kamar ba ta jidaɗin ganin shi ba. Daker ta asa tana ɗan murmushi. Kairat ta tashi cike da zumuɗi “Abbah bari na kawo maka Abinci yanzu muka gama ni da Mummy” “Toh yar Mummy ba sai kin kawo min ba ruwa ma ya isa” Kicin ɗin ta nufa tana faɗin, “Toh Abbah” Bata daɗe ba ta fito ɗauke da ture mai drinks da cup, a gaban sa ta dire ta ɗauki lemu ta zuba masa ta mika masa “Gashi Abbah kasha lemon gidan mu” Karɓa yayi yana murmushi ya kurba kaɗan ya aje sannan yayi ma Mummy kallon natsuwa. “Gurin ki nazo ke da yarki” “Allah yasa ba laifi muka yi ba” Mummy ta faɗa tana ɗan murmushi, Abbah ya gyara zaman sa “Jiya ne iyalan Alhaji. Bashir bature suka zo gidana akan maganar Kairat sun ce min daga nan aka turo su kuma yace da amincewar ku, haka ne?” Kairat tayi saurin yin kasa da kanta cikin kunya ta mataa gurin Mummy, Mummy kuma tasa dariya tana shafa kanta “Eh haka ne daga nan na tura su can” Abbah yayi dariya “Ance Saifullahi ne mijin margayiya” “Eh. Haka ne sun daidaita dashi da ita ne sai nace idan har da gaske yake yaje can ya same ka ashe ya je” “Eh sunje Jiya, ni kuma nace ba zan ce komai ba sai naji ta bakin ku, amman naji daɗi wannan abun sosai Allah ya tabbatar mana da alheri” Mummy ta amsa da “Amin” Abbah yayi dariya yana kallon Kairat “Toh ke kina son shi dai ko?” A gudu ta tashi ta shige ɗaki tana rufe ido. Abbah ya kalli Mummy da ta bita da kallo ya ce “Sai a samu su rana kenan?” “Eah a sa musu amman kayi shawara da Hajiya tukuna” “Nayi mata magana ai tace nazo nan na same ki ai kece uwarta” Shiru Mummy tayi tana nazari, ke hakan yake nufi kenan? Babu ruwanta da lamarin auren ko muma me? Maybe bata ji daɗin haɗin auren da aka yi ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Abbah “A sa musu kuma inda hali kar asa da tsawo saboda Babyn ta kasan an kusa sallamo ta daga asibiti kuma kasan ita ce zata shayar da ita” “Masha Allah amman kunyi tunani mai kyau gaskiya dan ba kowa bane zai iya yima ma rokon gaskiya ba, Bari na saka muku wata ɗaya yayi?” “Wata ɗaya bai yi nisa ba?” “Toh bari aka muku sati biyu” “Toh ina madallah da hakan Allah yasa albarka” “Amin” Shiru ne ya biyo baya kowa hankalinsa ya koma kan tv, zuwa can Abbah ya kalleta “Toh ni kan zan wuce inda wata matsalar zaki iya sanar min, duk da akawai wata maganar da nale son yi dake amman ina ganin sai an gama wannan hidimar ta Kairat” Mummy ma tashi tayi ganin ya tashi tace “Na gode sosai ka gaida Hajiya” Ta basar da wacan maganar, murmushi kawai yayi dan yasan da gangan tayi hakan, ya nufi kofa ita kuma tayi masa rakiya har gurin Mota. Kuka Kairat ta samu kanta dayi lokacin da ta shiga ɗakinta kuka marar dalili dan itama kanta bata san dalilin kukan nata ba, ita dai kawai taji kuka yazo mata ba kakkautawa. Kusa da ita Mummy ta zauna lokacin dats shigo cikin ɗakin ta kalleta cikin damuwa “Kairat bana nufin cilasta ki, bana burin kiyi auren da baki so ban roke ki ki auri Saif sai dan ansan akwai ɗigon son shi cikin zuciyarki, na haɗa ki da girman Allah karki auri Saif matukar kina tunanin aurensa zai zame miki matsala ko kuma tursasawa daga gare ni” Dagowa tayi ta ɗora kanta saman cinyar Mummy, “Wallahi Mummy ni kaina ban san dalilin wannan kukan nawa ba, kawai dai ina jin wani abun ne daban, babu cilastawar ki ko ɗaya a wannan auren ni naji zan iya kuma nasa kai na karki taba zargin kanki” “Amman Kairat bana jindaɗin wannan kukan da kike yi yana kuna min zuciya” “Ba zan sake ba Mummy insha Allah” Ta faɗa tana share hawayen ta, Mummy ta shafa kanta. “Allah yayi miki albarka ya biya ki” “Amin” ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ Cikin satin Abbah yasa yanka musu sadaki ya kuma duk wani abun da yace uba yayi ma yarsa, cikin satin kuma akayi komai cikin har da kawo tufafin da Kairat zata saka, Saif yasha mayar nu gidan yana tambayarta ko da wani abun datake bukata tace masa a a. duk wani abu da yan mata suke yi ita kinyin tayi ciki har da kin raba katin aurenta, walima ma dan Mummy ce ta shirya ta shiyasa kawai zata halarta. babu yadda Mummy bata yi da ita ba akan ta ɗan yi wani event ko da ɗaya ne amman taki. Safiyyah kan tattarawa tayi ta koma gidan Gwaggonta wai ba zata iya zama a gidan Momy ba dan ba zata iya jure yadda Saif yake disgata ba, gashi yanzu abu ɗaya da biyu zai sako maganar Kairat ko lil Minal. Duk wani abu da ya dace ya tayi ma yarta sai da Mummy tayi ma Kairat shi, tun daga gyaran jiki zuwa tufafi har kan abunda za a saka mata a ɗakin. hakan sai yasa Kairat ta zama yar gata dan Hajiya ma irin nata gatan take nuna mata, Abbah ma duk abunda aka siyo sai ya nuna mata ya kuma tambaye ta abunda take so, amman hakan bai taɓa sa taji daɗi ko da sau ɗaya ba. Ana saura kwana biyu a ɗaura aure Hajiya Suwaiba ta zo gidan, Mummy taji tsoron ganin ta dan bata san da wace tazo ba, tunawa da zuwanta na karshe a gidan, Murmushi dake fuskarta yaba Mummy karfin gwuiwar yi mata magana “Sannu da zuwa Hajiya Allah dai yasa ba laifi muk yi ba” Hajiya ta zauna tana murmushi tana kokarin zaunawa, “Ya gida ya hidima” “Alhamdulillahi ya naku?” Mummy ta faɗa tana kallon Fusakarta. “Masha Allahu na fito gidan Ramatu ne nace bari na biyo tun da ku baku zuwa ga shirye shirye yayi nisa” Dariya Mummy tayi suka cigaba da fira sai dai kowa bai sake jikin kasancewar Mummy tunanin da wace tazo, ita kuma tana jin nauyin Mummy akan abunda tayi masa. RANAR ASSABAR......... Rana ce da da dandanzon mutane suka shedi ɗaurin auren KAIRAT IBRAHIM AHLAM da SAIFULLAH BASHIR BATURE, anyi taro kosai tun daga kan yan'siyasa yan kasuwa sarakauna malamai da kuma daidai kun jama'ah, Daga garuruwa daban daban, bayan ɗaurun Auren mutane suka ɗugun zuma zuwa gurin liyafar cin abinci. Bayan gama liyafar Saif ya nufo gida tare da wasu abokaninsa, Kallo ɗaya zakayi masa ka ganr shine angon duba da yanayin shigarsa da kuma yadda fuskarsa ke annuri kanshi turare kan ba a magana, kallo ɗaya Safiyyah tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da kallon tv tana wasa da makulin hannunta, “Sannu Ango Allah ya bada zama lafiya” Shafa ta faɗa tana murmushi, Safiyyah ce ta amsa da amin kamar ba komai, sannan ta kalli Lubna take da zuba da Nasir tana faɗin “Ke suda muje ni dai akwai gun da naƙe son zuwa” “Ina zaku?” Nasir ya tambaya yana kallon Lubna dake tsaye kusa dashi ta rike masa hula “Yauwa Ya Nasir muje ma ka kai mu gidan Ya Saif zamu je ɗakin Lil minal zamu gyara” “Ita lil Minal ɗin har an mata ɗaki?” Tayi wani fari da ido, “Taf tun yaushe yau ɗin ma wasu kayan zamu kara sakawa” “Toh masu abu su keci da rana kuna shagalin ku” Duk suka sa dariya har Safiyyah, a nan Luban ta tirsasa shi tasa shi gaba a dole ya kai sai da yayi driving ɗin su har gidan a mota in banda tsokanar Lubna babu abunda yake har ta saka masa kuka. Dukan su sun yaba kyau gidan da kuma yadda aka gyara ɗakunan musamman ɗakin Lil Minal sasancewarsa ɗakin yara yana da ɗaukar hankali idan an gyara shi. A tare suka shiga jera sauran kayan ganin aikin nasu ba mai karewa bane yasa Nasir yayi tafiyarsa yace idan sun maga su buga masa zai zo ya ɗauke su. Ai ko Safiyyah ta jidaɗi sosai yana fita itama ta fita daga ɗakin ta nufi gurin da aka dasa itace dan kwaliya, hannu ta kai ta kalli wani ɗan karamin ice ta duka a gurin tana gina, wani abu naga ta ɗauko ta saka cikin karamin ramen ta rufe waige waige take har taƴi ta gama tana Allah Allah kar wani ya ganta, Tashi tayi tana karkaɗe jikinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya can kuma ta buɗe ta nufi cikin gidan. wani kallo Shafa tayi mata mai alamar tambaya ita kuma ta ɗaga mata kai, sai ko wannenasu ya ɗauke kai suka cigaba da shirya ɗakin. Nasiha Sosai Mummy tayi ma Kairat bayan Abbah da Hajiya sunyi mata nasu, Kuka sosai Kairat ta rikayi kamar ranta zai fita kwaliyar da akayi mata duk ta bace Mummy ma ba karamin kuka tayi ba, saboda tunawa da auren Minal da kuma ganin za a barta ita kaɗai. daker aka ɓanɓare hannun Kairat a jikin Mummy, Motar ma daker aka saka ta, sai wani abu take kamar mai aljannu. ko kuma nace wanda za a cire ma rai, har wani numfashi take saboda kuka. Har a ka isa da ita gidan angonta kuka a motar ma ba karamin yaki akayi ba wajen fitowa da ita a shiga cikin gidan ba, a ɗakin aka wuce da ita kowa sai yaba kyau gidan yake da kuma kayan da ka zuba ma Kairat, masu ɗaukar hoto nayi an video camera ma nasu aikin suke. ita kan bata kula komai ba kuka take har abokanin ango suka shigo dashi. zolayarsa suka rikayi shi dai in banda murmushi babu abunda yake shima kana gani zaka san bai kai zuci ba, Nasir ne kawai ya ware kansa daban yana musu nasiha irin ta zaman aure da kuma hakuri, har sauran abokanin suka rika janshi wai sai kace shi ɗin aure ne dashi. sai da suka canye lokacin su har suka shiga na amarya da ango sannan suka bar gidan bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da. Gyara zamansa yayi ya kalleta yana sauke ajitar zuciya, shi kansa ba wani farinciki yake ji ba, jinsa yake daban yana tuna rayuwar aurensa ta baya, motsin abun warwaronta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ya sake kallonta a karo na biyu “Godiya ta tabbata ga Allah wanda cikin ikonsa da amincewarsa da rahamar sa ya nuna mana wannan rana, wanda yau gani ga ki a masayin miji da mata, wannan lamarin na Allah ne shi kaɗai yasan abunda ya tsara mana da kuma wanda zai tsara mana nan gaba” Ita dai har lokacin kanta na kasa cikin mayafi. “Sai ki tashi muyi ma Allah godiya” ta shi tayi ta nufi kofar bathroom ɗin tana wata tafiya kamar ta faɗi, bayan ta ɗauko alwala ta fito shima ya shiga yayi ya fito. A tare suka gabatar da Sallah raka a biyu suka yi addu'ah, sannan ya juyo ya kalleta “Ga abinci nan nasan baki ci komai ba, ni zanje ɗakina na kwanta” Bata ce masa komai ba shima ɗin bai jira tace masa ba ya tashi ya nufi ɗakinsa. aiko tana jin rufewar kofar ɗakinsa wani sabon kuka yazo mata ta tashi ta koma saman godon ta kwanta tana rera kuka a hankali. da haka bachi yayi gaba da ita1 WASHE GARI....... Sai tara da rabi Saif ya fito daga ɗakinsa, yana sanye da jallabiya baka tayi masa kyau sosai kamar ba wanda ya tashi daga bachi ba, ganinta tsaye gurin dinning yasa ya karasa gurin yana ɗan murmishi kamin yace wani abu tayi saurin dukawa ta gaidashi cike da ladabi “Lafiya kalau kin tashi lafiya” Cikin jindaɗi ya amsa mata. ita kuma ta amsa masa cike da jin kunya, “Ga abincin ka nan” Ta faɗa tana kokarin barin gurin. “Kinci naki ne?” “Aa a ɗaki zan ci” Oka kawai ta faɗa yaja kujera ya xauna, bayan ya kare ya koma ɗakinsa ya shiga bathroom yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin wata shadda Lemon green yasa hula baka ya nufo ɗakin Kaoeat sai kanshin turare yake. zaune ya tarar da ita gefen gado sanye da babban hijab wanda ya suturce mata dukan jikinta, da alama ita wankan ta fito kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai “Ni zan ɗan shiga gari idan kina bukatar wani abun sai ki kirani ko kiyi ma mai gadi magana” Kai ta ɗaga masa ba tare da kalleshi ba, shi kuma ya juya ya fice daman daga bakin kofa ya tsaya. Wunin ranar mutane ne suka rika zuwa gidan tun daga ɓangaren Momy har zuwa yan'uwanta da abokanin arziki, masu zolayarta suna yi masu mata nasiha nayi mata. sai kusan insha kowa ya watse aka barta ita kaɗai aiko taji kamar ta fasa ihu ko kuma ta bisu amman ina ba dama yanzu rayuwa ta sauya. Bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa black and white ta saka bakin hijab ta nufo dinning dan jera kulolin abincin da aka kawo, Tana cikin aikin raji an buga kofa a hankali, sau biyu zuwa uku. yi tayi kamar ba taji ba har sai da aka sake yi sannan tace “Wanene?” Shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta nufi kofar ta buɗe, ga mamakinta sai bata ga kowa ba babu ma mutun balle alamunsa. mai da kofar tayi ta rufe ta juyo zata kunno kai cikin parlour, Buga kofar da akayi yasa ta sake juyowa babu kwankwanto ta buɗe kofar da bismillah. Minal ce tsaye bakin kofar sanye da bakar riga gashin kanta har godon bayanta tana kallon Kairat da wasu irin kalar idanu manya manya, fuskarta ba yabo ba fallasa. Ba shiri Kairat ta buɗe baki, ta zaro ido tana kallonta numfashinta na kokarin ɗaukewa jikinta kuma ya shiga rawa kamar mazari.Ji tayi kamar ana zooming ɗinta saboda tsoro. Daker ta iya rufe idonta ta furta + "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un" Ta daɗe a haka kamin ta buɗe idon ta sake kallon bakin kofar, neman ta tayi ta rasa, tayi ko sama ko kasa, da sauri ta maida kofar ta rufe tana haki Saman kujera ta dawo ta zauna dafe da zuciya, Toh ko dai gizo idonta yake mata ne? Shine abunda ta tambayi kanta tana lumshe, toh idan ba gizo ba kan minene tun dai Minal ba dawowa zatayi ba, wannan tsoro ne da kuma rashin sabo da zama ke kaɗai. Tana haka taji an sake turo kofar a karo na biyu an shigo parlour, kulle idonta tayi gam, har sai da taji sallamar Saif sannan ta buɗe idon tana amsa masa "Wa'alaikumussalam" "Sannu da zuwa" "Yauwa sannu dai ke kaɗai ce a gidan" Ya faɗa yayin da yake kokarin karasawa kusa da ita, ita dai har lokacin kanta na kasa tana doubting abunda ta gani, "Bari naje nayi wanka sai muci abinci ko?" As usual bai tsaya jiran abunda zata ce masa ba ya nufi ɗakinsa ita ɗin bata ce masa komai ba dan abunda take tunani ya isheta. Har yayi wankan ya fito a gurin da ya bar ta ya tararda ita kuma har lokacin kanta a kasa, tsayawa yayi yana kallonta kamar maj karantar abu a fuskarta, "Kaiyrat" Ya furta a hankali, zabura tayi ta tashi tsaye kamar wanda ta razana, "Na'am" Sai kuma tayi kasa da kanta, "Ga abincin ka can ni na ci nawa" Bata tsaya jiran abunda zaice ba ta nufi ɗakinta. Shi dai da kallo ya bita har ta shige sannan ya ɗaga kafadunsa ya taɓe baki ya nufi gurin dinning ɗin. Cike da zullumi da fargaba Kairat tayi bachin ta na biyu a gidan, har garin Allah ya waye tunanin yadda taga Minal take har yanzu ta kasa yarda ita ɗince zigo ne idona suke mani shine abunda take ta maimaitawa tana kawar da tsoron dake ranta, bayan tayi Sallah asuba ne bachi mai daɗi ya ɗauke ta bata farka ba sai kusan goma na safe, "Alhamdulillahil lazi'ahyana ba'adama a matana wa'ilail-nushur A'uxubillahi minasheidanin'rajin"1 Bayan tayi addu'a tashi daga bachin ta mike tana mika ta nufi banɗaki, bakinta kawai ta wanke sai fuska ta fito ta ɗauki hijab ɗinta ta saka sannan ta nufo downstairs. Zaune ta samu Saif a dining room yana cin abinci, karasawa tayi ta risina har kasa ta gaishe shi dan abunda Mummy ta faɗa mata kenan cikin jindaɗi ya amsa yana mata "An tashi lafiya" "Lafiya kalau" "Ga abinci nan ki ci ban tsaya jiran ki dan nasan ba zaki ci dani ba" Ya faɗa yana kokarin tashi tsaye, tana daga duken tace "Yaushe zamu kawo Lil Minal?" Tsayawa yayi yana kallonta, "Wai da cewa nayi sai nan da sati biyu ko uku kinga kamin lokacin kin ɗan saba abubuwa ba zasu miki yawa ba" Jin tayi kamar ta zaburo masa tayi cikinsa da masifa, amman Mummy ta hana ta dan ta faɗa mata wannan ba ɗabi a bace ta matar kirki, bata ce masa 'Eh' ko 'A'a' sai kawai ta tashi ta nufi ɗakinta. Binta yayi da ido har ta shige sannan shima ƴa tsaya yana tunani miye yanke wannan hukuncin bayan saboda Lil Minal ɗin ta aure shi? Dan da kula da ita, amman shi kan gani yake kamar abun zai zame mata wani irin idan aka kawo mata ita yanzu ganin shekaran jiya nan aka kawota a gidan. Amman kuma miye ruwansa tunda ita take son haka ɗin! Dakinta ya nufa yana shiga ya same ta dukunkune can gafen gado kamar marar lafiya, ganin shigowarta yasa ta tashi zaune tana jiran abunda zai ce mata. "Kaiyrat" Ya kira sunanta kamar ba lakka a jikinsa, shi dai baya jindaɗin yadda take kin sake jikin nan dashi ko kuma nace da gidan. Ta ɗan kalleshi kaɗan yayin da take kokarin amsawa "Na'am" Karasawa yayi kusa da ita, cikin yanayi mai kamar ya na damuwa "Yaushe kike son na kawo miki ita?" Shiru ta ɗanyi kamar mao nazari can kuma ta ɗan kalleshi "Gobe?" Ta faɗa kamar mai neman amsa, "Allah ya kai mu" Ya juna ya fice. Wunin ranar wuni Kairat tayi shiru shiru gashi yau gidan ba kamar jiya ba ba mutane sosai, ga kuma abunda yayi mata tsaye a rai tunanin yadda zatayi rayuwa a gidan da kuma yadda zaman ta zai kasance da Saif. Kaɗan kaɗan take ɗan taɓa fira da kawarta, tana cin kankanar dake gabansu. "Sai ɗa kinyi hakuri Kairat ita rayuwar Aure yar hakuri ce musamman irin wannan auren naki, ki kawar da komai da yake ranki ki fuskanci Ubangijinki kisa ni bauta kike ba wai zakiyi rayuwar jindaɗi bane, yadda kake son rayuwa ba zata kasance maka a haka ba baka taɓa samun komai 100%" Kai kawai Kairat ke ɗaga mata tana sauraren nasihohin da take mata kasancewarta matar aure. Ana sallah la'asar tayi ma Kairat sallama, wai mai gida yace kar ta daɗe, Dariya kawai Kairat tayi tana girgiza kai ita kuma ta rika zolayarta tana mata maganganu irin nasu na matan aure. Har gurin Mota Kairat ta raka ta bayan ta fice ta tsaya tana kare ma harabar gidan kallo. Biyar saura kwata, Saif ya shigo gidan ya daɗe a mota sannan ya shigo cikin parlour, "Ummu Minal fito ga Lil Minal ɗin ki" Shine abunda ya faɗa yana kallon kofar ɗakinta yayin da ya kai tsakiyar parlour. Lekowa ta fayi kamar wata karamar yarinya wai ta gani indan da gaske yake, aiko da gudu ta karasa saukowa ganin Baby a hannunsa, A maimakon ya mika mata baby sai kawai yaja baya da sauri yana mata kallon zolaya "Wa zaki fara tarba ni ko ita?" Kallonsa tayi da kyau shi kuma ya sakar mata manyan idon shi, kun kuyar da kai tayi tana murza yatsun hannunta, "C'mon answer me mana idan kina son na baki ita" Ya faɗa yana kallon fuskarta. Sake ɗagowa tayi ta kalle shi sai ta sake sanda kai, wani wasan yana yi mata ne dan ta sake jikinta, amman ina bata da niyar hakan. A dole ya mika mata yar dan yadda taga ta dake ɗin nan tsaye guri ɗaya yasan ba cewa zatayi ba "BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM" Shine abunda ta furta sannan ta karɓi lil Minal ɗin, rumgume ta tayi a kirjinta. Daman can Kairat mace ce mai son ɗiya ballan tana wannan da take da dalilai na sonta. "Na gode" Ta faɗa tana kallonsa idonta cike da hawaye, murmushi yayi mata yace "Dr tace idan zaki bata nono ki bata nonokin na dama kuma ki wanke shi kamin ki bata sannan tace karki bata nono yanzu sai nan da awa bakwai ko kuma ma ki bari har sai gobe tace duk ba matsala bane Momy tace gobe zata zo tare da wanda zata rika lura miki da ita" Kasa tayi da kanta alamar kunya, taɓe baki ya ɗanyi shi kan bai ga abun kunya a maganarsa ba tun da ba wata ɓaran ɓaramar yayi ba, a nan ya barta ya shige ɗakinsa. Sallah ce kawai take sa Kairat ta aje Lil Minal amman duk abunda zatayi tana rumgume da ita. Bayan Sallar i'sha tayi shirin bachinta ta saka hijab kamar yadda ta saba ta hau saman gadon ta kara jan lil Minal kusa da ita tana mai jindaɗi sai kallonta take tana murmushi da alama ma idon ta biyu duk da idon nata a rufe suke amman sai motsi take da baki tana motsa baki. Kamar wanda aka ce ɗago ki kalli windo, tana kallo ta ga Minal da siffar da ta ganta a farko kuma nan ɗin ma ita take kallo, wata razanannar kara da saki ta sauko saman gadon ba shiri ta fisgi lil Minal ta bar ɗakin tana ihu.Da sauri Saif ya ɗago kai daga daga gurin da yake zaune ya kalli upstairs, “Lafiya.?” Ya tambaya yana kokarin aje magazin ɗin hannunsa ya tashi ya nufi upstairs ɗin yana cigaba da tambayar ta, bata faɗa masa gaskiya ba sai ta canja maganar, “Wata na gani gurin windo” Kunna kai yayi cikin ɗakin yana dube dube. ganin bai fahimci abunda take nufi ba “Ba fa a ɗakin ba ta waje a windo na ganta” Windo ya nufa ya shiga dubawa, shikan bai ga komai ba sai kawai yaja windon ya rufe, ya juyo yana faɗin “Ina jin ita cen dake waje ne kika ango iska ne ke kaɗasu kinga garin akwai hadari, kuma kin bar windin buɗe amman ai kinga babu yadda za'ayi wai ya iya haurowa ta wannan windon tun da ba kasa yake ba” Ita dai tana tsaye a bakin kofa rumgume da Lil Minal, “Ba komai kiyi addu'ah ki kwanta” Kai ta ɗaga masa ba dan ta yarda ba komai ɗin ba, har ya fice a bakin kofar take tsaye sai wani abu take da fuska kamar mai shirin yin kuka, can taji ba zata iya jure wa ba, ta juyo ta sauko downstairs. Ba kowa parlour sai tv dake ta aikinsa, haka ta zauna sai kalle kalle take kana ganinta kasan babu natsuwa a tare da ita, sai a jiyar zuciya take saukewa, tana haka Saif ya fito sanye da jallabiya dark blue, “Gate na dawo mikike so a siyo miki?” Ya faɗa daidai lokacin da ya karaso kusa da ita “Bana bukatar komai” Ta faɗa kamar bata son magana. Sai da ya kai bakin kofa sannan ta ce “Please karka daɗe” Juyowa yayi yana murmushi, “Tunda kina jin tsoro ko.?” Kasa kasa ta kalleshi ta ɗauke kai. Shi kuma ya fice yana cigaba da murmushin. Aiko kamar kar ya fita wani irin tsoro ya kara rufeta, ta rumgume Lil Minal a kirjinta gam ta rumtse ido, jin Lil Minal ɗin na motsi yasa ta buɗe idonta ta ajeye ta saman kujera tasan rumgunar ce wata kila bata so, tashi tayi da nufin kashe tv saboda karar da tayi yawa, sai kawai taga an kashe tv ba tare da ta karasa gurin ba, aiko ba shiri tayi baya baya tana haki. “Ashe ki baki da amana Kairat? saboda zaki aurar min miji? kin yaudare ni cin cuce ni Kairat kuma ba zan taɓa barinki cikin kwanciyar hankali ba matuƙar kina cikin gidan nan” A gefenta taji maganar tana juyowa ta ganta cikin bakar siffar da ta saba ganinta, wata mahaukaciyar kara ta saki ta faɗi kasa tana ja da baya sai uhun take ba kakkautawa, aiko sai bin ta take tana son kamota Kairat na ganin ta kusa karasowa kusa da ita ta kara sakin wata irin kara. jin an taɓa ta ta baya yasa ta rika numfashin a jure kamar zai ɗauke “Nine Kairat ni ne” Ina! tayi nisa bata jin me yake faɗi sai kaiwai ta cigaba da ihun jikinta na rawa, juyowa yayi ta ganta yasa bakinshi cikin nata ya rike kanta gam, sunyi minti goma a haka sannan hankalinta ya dawo ganin hakan yasa ya sake mata kai ya cire bakinshi daga nata ya rika kafaɗunta yana girgizata, “Kairat” Bata iya amsawa saboda numfashinta har yanzu rawa yake, “Close ur eyes” Da sauri ta rufe idon kamar mai jiran umarni “Relax, relax ur body” Ba musu tayi yadda ya umarce ta “And stop breathing as long as U can” Dif numfashin nata ya ɗauke ta daƙiƙin tsayar da shi da tayi “Now breath” Ya faɗa yana kallon fuskarta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba da numfashinta, “Open ur eyes” Tana kallonsa ya ce “I m here its me okey” Fashewa tayi da kuka, ya rumgume ta yana mata magana a kunne kamar mai raɗa “Shiiiiiiii ya isa faɗa min miya faru?” “Minal na gani Saif” Bata ɓoye masa ba, ta faɗa masa dan a yadda ra ganta yanzu ya wuce misali gashi har da magana tayi mata. Lil Minal ya nuna “Wannan ?” “A'a Minal dai margayiya” Kai ya girgiza, “Oh no no no Kairat baki ganta ba tsoro dai kike ji kuma kinsa tunaninta cikin ranki” Dagowa tayi daga jikinsa daman ba rumgumar take so ba dan kawai tana jin tsoro ne, “Wallahi na ganta Saif da ido na, ba wai ina tunaninta bane kuma tayi min magana” “No Kairat kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? babu kuma mai rai baya ganin mamace ba ita bace tsoro ne kawai kike ji” Shiru tayi tana hawaye, daman tasan ba zai yarda ba babu ma wanda zata faɗa ma ya yarda da ita amman ita tasan abunda take gani. Unkurin tashi tayi, daker ta mike tsaye kafafunta basa iya ɗaukarta. A nan shima ya tashi ya lakamo hannunshi ya rika kunkurunta “Let me help you” Bata masa musu ba dan tasan ba zata iya kai kanta ɗaki ba, da ɗayan hannunsa ya ɗauki Lil Minal ya nufi upstairs. har cikin ɗakinta ya kaita bayan ya zaunar da ita ya kwantar da Lil Minal, sannan ita ya kwantar da ita ya cire mata hijab ya goge mata fuska. “Ki daina kuka, kiyi addu'ah” Blanket ya lulluɓa mata sannan ya kashe wutar ɗakin ya fice. Yana fita, taji ita ba zata iya kwana ɗakin ba duk wani rashin karfi da take ji sai taji ya cire mata, da wani irin kuzari ta walkato saman gadon ta sauko ɗaukar lil Minal ne kawai ya zame mata dole aiko tana ɗaukarta ta fice daga ɗakin a guje. ɗakinsa ta nufa ta daɗe tsaye bakin kofar sai tunane tunane take, kamar ta koma kuma taji ba zata iya ba.Sam ta manta da ba mayafi jikinta haka ta faɗa ɗakin tare da sallama. yana zaune saman gado laptop na saman kafafunsa yana dannawa ya ɗago ya kalleta “Again?” Kai ta girgiza tana karasa shigowa ɗakin, “A a nan dai zamu kwana ni tsoro nake ji” Wara ido yayi ya kalli gadonsa sannan ya kalleta yana ɗaga kafaɗunsa “Zo ki kwanta” Gefen gadon ta nufa ta zauna kasa rumgume da lil Minal tana faɗin “Nan ya isa” Kitson kanta ya tsaya kallo yana mamakin yadda ta zauna aka tsara mata dashi ta kuma wanda ta tsara mata shi, kanana ne kuma an tsara shi cikin waninsa da sarkaki dan wani kan wani akayi shi gashi kuma ya sauko mata har baya gwanin sha'awa. bai ankaro ba yaga ta sulale kasa kwance, Laptop ɗin ya kashe ya aje saman dorowa ya sauka ya zagaya gefenta ya ɗuka ya ɗauki Lil Minal “Idan ke zaki iya jurar tsayin wannan gurin ita ba zata iya ba, kuma ki tashi ki hau kan gado ko ki koma ɗakin ki idan baki yarda dani ba miya kawo ki ɗakina” Tashi tayi zaune ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka ta kalli gadon. bayan ya kwantar da Lil Minal ya kalleta “Rufe ɗaki na zanyi” Tasan me yake nufi ta fita ta bashi ɗakinsa, ita kan har ga Allah ba zata iya kwana ɗakinta ita kaɗai ba dan jin take kamar kara ganinta zatayi, ganin babu sarki sai Allah yasa dole ta hau saman gadon ta takure kanta can karshen gadon ta kundule cikin nayafin rufa kamar wanda aka cilasta. Taɓe baki yayi yaje ya rufe kofarsa ya kashe wutar ɗakin, yazo ya kwanta ya lulluɓe shi da Lil Minal. WASHE GARI..... Bayan yayi sallah asuba ya tashe ta tana faɗin “Tashi kiyi sallah” Cikin gigin bachin ta tashi, har zatayi mika sai ta tuna ba ɗakinta take ba da sauri ta murza ido ta ɗauki lil minal ta nufi kofar fita. Shi dai kallonta kawai yake har ta fice. Bayan ta kare Sallah, ta sake komawa bachi. bata farka ba sai takwas har da kusan rabin, bathroom ta shiga tayi wanka, bayan ta shirya ta sake komawa banɗakin ta wanke nononta kamar yadda Dr tace bayan ta fito tazo ta ɗauke ta ta ɗaga hijab ɗinta da nufin bata nonon sai kuma ta kasa, ta daɗe a haka sai tunane tunane take, ba karamin jihaɗi tayi ba wajen ɗaurewa ta saka mata nonon a baki, kamar mai nema ta kama da karfi tana sha, runtse ido Kairat ta rikayi kamar mai jin zafi tana dantsar baki tsigar jikinta sai tashi take. Jin motsin shigowar mutum yasa ta buɗe idonta tana ganin Saif tayi saurin sakin hijab ɗin tana faɗin “Sai ka shigo min ɗaki ba Sallama” “Eh ya ranki?” Ya faɗa kamar mai jiranta shi daman tun jiya yaga taken taken ta sam bata yarda dashi gani take kamar wani abu zaiyi nata da ya ɗan motsa sai ta tashi zaune tana kallonsa hakan kuma ba karamin kona masa rai yayi ba. Fitar da ita tayi ta aje saman gadon tana ɓata fuska “Daukarta ki bata nonon” Banza tayi masa. ganin yadda ya nufo ta yasa ta ɗauke ta dan bata san nufinsa ba, ta mayar cikin hijab ta cigaba da bata nonon, Ta ɗai san ba xai doke ta amman kuma zai iya cewa sai ya ba lil minal ɗin nono da kansa. kwafa yayi ya zauna gefen gadon kusa da ita ya tsare ta. ita kuma ba damar tayi masa magana tasan jiraye yake da ita. Jin Sallamar Mummy yasa shi tashi ya nufi parlour yana amsawa, “Sannu da zuwa Mummy kece da safen nan haka?” Ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da murmushi yana karasa saukowa downstairs, tana kokarin zaunawa ta ce “Nice break fast na kawo muku ta kuma mai yima baby wanka ina ya ta” “Tana ciki” ‘Kairat...’ Ya kwala mata kira, sai gata ta fito ɗauke ta lil Minal ɗin, tana ganin Mummy ta sauko da gudu tana murmushi, “Yi a hankali mana” Ya faɗa yana kallon Lil Minal, ita dai bata kula shi kula shi ba har ta karasa gurin mummy ta aje Lil Minal ta rumgume Mummy, sai kuma ta fashe da kuka “Mummy i miss you” “I Miss you too daughter ya gidan?” “Mummy gidan ba daɗi ni ba zan iya zama ba” Mummy ta rika fuskarta, “Zaki saba Kairat komai da sannu sannu ake dainawa” “A a Mummy tsoro ake bani” “Tsoro..?” Mummy ta faɗa tana kallon Saif. Murmushi yayi Yace “Mummy tsoro ne take ji, ta cika tsoro wai Minal take gani ina ganin tasa tunanin ta da yawa ne” Mummy ta rika hannunta suka zauna fuskarta ɗauke ta damuwa, “Minal kuma mafarki dai kike yi ko?” “Mummy ba mafarki bane ganinta nake yi har da magana tayi min jiya” “What .? no Kairat ya za ayi ki ga wanda ta rasu ba zai yiyu ba” “Mummy idan ina ɗakina take zuwa” “Toh da Saif ba ganta ba idonki ne Kairat” “Mummy ba ido na bane ina ganinta a zahiri ai ba ɗaki ɗaya muke kwana da Saif ba” “Saboda me?” Shiru tayi ta ɓata fuska, “Baki san ba kyau raba gado da miji ba ko wani abun ya faru ne” Kai ta girgiza alamar a a, mummy tace “Toh akan me zaki rika kwana ke kaɗai? wannan ai ba ɗabi'ah bace dole ki rika gane gane” Talatu tace “Hajiya karfa kiyi latti kinsan kince tara da rabi zaku shiga meeting” Mummy ta kalli Kairat “tashi ki ɗauko abu Talatu zatayi ma Lil Minal wanka, ita zata xauna a nan tana kula da ita kamin ki iya yi mata wanka” Saif ya ɗauki lil minal ya kalli Talatu, “Muje na nuna miki ɗakinta” Ba musu ta tashi suka nufi ɗakin. Bayan sun shige Mummy ta kalli Kairat tace “Kar na sake jin kun rab gado da mijinki sai kace ba wayayi ya ba idan kika saba masa da hakan ke ce zakiyi nadama nan gaba, baki san babu kyau ba? muharraminki ne fa Kairat ɗan Allah karki sake haka kinji?” Kai ta ɗaga tana kuka mai kamar na shagwaɓa kuma bana shagwaɓa ba. “Ki rika addu'ah kinji? I will do something about it” “Toh Mummy amman ba zaki daɗe ba zaki dawo ko?” “Eh ba zan daɗe ba” “Promise” “I promise” Rumgume Mummy tayi tana wani narkewa jikin mummy kamar zata shige. Saif ya fito daga ɗakin, karaso kusa da su yana kallon Kairat ya taɓe baki. “Tashi ki jera abincin ku a dinning” Mummy ta faɗa tana shafa kanta, tashi tayi ta nufi dinning ɗin tana share hawaye. Mummy ta kalli Saif “Kairat amana ce a gare ka Saif farincikinta shine nawa ka kula da ita sosai kuma kayi hakuri da ita da sannu komai zai zama daidai” Kai ya ɗaga mata ya tashi tsaye ganin itama ta tashi ɗin. da sauri Kairat ta karaso gurin ta rika hannun Mummy kamar wata karamar yarinya “Mummy tafiya zaki yi?” “Eh sai na dawo kinji ki rika addu'ah” Wani irin ɓata fuska Kairat tayi taji kamar ta bita Saif dai sai kallonta yake har Mummy ta fice, sannan yayi dariya yaja kumatunta. “Sagarta ko miyasa baki bita ba?” Rufe fuska ta ɗanyi tana share hawaye. Hannunta ya rika “Muje mu ci abinci” Da kansa ya haɗa mata tea ya tura mata gabanta, sannan ya haɗa nashi. KARFE UKU DA MINTI GOMA SHA DAYA.......... Safiyyah ta digo gidan, da Sallama ta shigo parlour fuskarta ɗauke da murmushi. haɗa baki sukayi da Talatu gurin amsa mata. kallo ɗaya Kairat tayi mata ta ɗauke kai kamar bata san inda ta fito ba. “Amary bakya laifi” Ta faɗa tana kokarin xunawa, Kairat dai bata ce da ita uffan ta sai kallon tv take, Talatu kuma na rumgume da lil Minal. Taɓe baki Safiyyah tayi tana kallon Falon “Yaya na nan” “Baya nan” “Ina yaje?” “Nima bai faɗa min ba” A tsatsaye Kairat take amsa mata tambayarta still bata kalleta ba. Talatu na ganin hakan ta tashi ta nufi ɗakin da Saif yace mata shine nata. Safiyyah ta tsire baki “Wai ya kike min magana kamar baki san wacece ni ba?” Sai a lokacin ta kalleta “Na san wacece ke mana, sheɗaniya kuma makira”5 Tashi Safiyyah tayi tsaye “Wannan wace irin magana ce haka kardai ace kema shaye shayen kike.” “Asibiti nake sha, miya kawo ki gida na?” Kyalkyalewa tayi da dariya “Gidan ki ko gidan yayana daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki tun tafiya batayi nisa ba har kin fara kiran shi gidan ki?” “Akwarai gidana ne saboda ni aka auro aka kawo” “Karki manta kamin ke am kawo wasu, kuma hakan yana tabbatar miki da ana canja mata ba a canja yar'uwa ba” “Waɗan can, an canja su ne ta wani dalili, ni ko zama daram dam kujerar karfe fita ki bar min gida makira annamimiya” Wani irin zaburowa Safiyyah tayi kamar zata mari kairat “Ni ce makira?” “Eh sunan ki ne ko kin canja wani?” Tsaye tayi suna kallon kallo akuya kallon kura, ita Kairat, jin parking ɗin motar Saif yasa ta jindaɗi tana jin motsin taɓa kofar palo ta fashe da kuka. cuke da damuwa ya karaso kusa dasu yana tambayar ba'asi “Lafiya miya faru?” “Mari na tayi tana faɗa min maganganun banza” Kairat najin haka batayi wata wata ba ta watsa mata marin sannan ta nuna ta da yatsa “Ita giwa tafiyar ta bata ɗaya data saura ni makircina a fili nake yinsa kuma babu yadda za'ayi” Zaburowa Safiyyah tayi zata rama Saif ya rike ta, “Wai miye haka ne” Safiyyah kuma dai sai kunce kuncen ta rama marinta take, can Saif ya warguna ta, ya tura ta “Tafi gida Safiyyah wuce” Tsaye tayi tana yima Kairat wani mugun kallon sannan ta juya ta fice cike da jin zafin marin da Kairat tayi mata. bayan ta fice Saif ya kalli Kairat rai a ɓace “Miye haka dan Allah daga zuwanta sai faɗa?” “Toh waya ce tazo dole ne sai tazo” “Dole ne tazo mana tunda ɗan'uwanta kike aure kuma ko bata zo dan ki ba xata zo dan lil Minal” “Bama bukatar ta ni da lil Minal karta sake zo mana gida, bata da wata alaka da mu” “Ni tana da alaka da ni Yar uwata ce ke kuma matata ce ko wacce matsayin ta daban, tana da yanci ta shigo gidana kamar yadda kike da yancin zama, beside Safiyyah ma ba wata mafaɗaciya ba ce i know her sai dai idan ke kika taɓa ta” Hawayen dake makkale a idonta ne suka zubo, ta kalleshi “You take her side” Kai ya girgiza mata, “This is not the right time to take anyone side, Kairat bai kamata a ce kin fara wannan halin yanzu ba, duka duka yaushe kika zo gidan nan?” Bata ce masa komai ba ta juya ta nufi upstairs. Zaunawa yayi saman kujera yana shafa kansa, baya nufin ɓata mata rai sai dai kuma ba zai bata damar ta raina masa yan'uwa ba duk da shi ma ɗin ba son xuwan Safiyyah yake ba, amman ba zai nuna mata ba dan karta raina masa yan'uwa dan da haka ne wasu matan ke samun kofar rai na yan'uwan miji. Da dare tana Zaune parlour tana buga Candy Bom a waya. Saif ya fito daga ɗakinsa rike da waya a hannu ya nufo gurin da take zauna ya ya fisge wayar, tana kallonsa yace “Coffee please” Tashi tayi ta shiga cikin ta haɗa masa ta kawo masa kallonta yayi a hankali sannan ya mika hannu ya karɓa yana faɗin “Mummy ta kira ni yanzu tace kin kirata kina kuka kuma baki yi magana ba kin kashe, miyasa kika kirata?” Zaunawa tayi tana shafa gefen fuskarta “Ba komai” Ta faɗa ta murya kamar ta shagwaɓa. gyara zamansa yayi yana kallonta “Ita gaskiya dole a faɗe ta Kairat, Bana nufin ɓata miki rai kuma ita dole ne na bata rashin gaskiyarta” Bata ce masa komai ba ta aje remote ɗin hannunta ta ɗauki lil minal ta kalleshi “Sai da Safe” Ta tashi ta nufi upstairs. da ido ya bita har ta haye a maimakon yaga tayi ɗakinta sai kawai yaga ta shiga ɗakinsa, Murmushi yayi ya cigaba da kallon yana kurɓa tea a hankali. Ba'ayi minti goma da shigarta ɗakin ba yaji ta fasa ihu ya kalli upstairs ɗin “Oh my goodness” Ya faɗa yana kokarin aje tea cup ɗin ya tashi ya nufi ɗakin. Wannan karon ya tabbatar da gaske Kairat tana ganin wani abu dan yadda ya tarar ana janta tana jan kanta ta rike gado gam sai uhun take, da sauri ya rikata shima tana janta da dukan karfinsa, janta taji ana kara yi sai dai baya ganin mai jan nata ita. komawa a'kayi gurin Hijab ɗinta ana janta da karfi kamar za a fisge mata fuska, cikin sauri ya cire hijab ɗin ya ɗauke ta kamar jaririya ya mai da gefe ya rumgume ta. Hijabin aka fisga ya faɗa ta windon baya, Sai sa kallon ikon Allah yake wai yau a ɗakinsa. ita ko sai kamkamesa take tana faɗin “Saif fitar da ni daga ɗakin nan” “Okey okey” Ya faɗa yana kara rumgume matarsa. saukowa yayi da ita downstairs, har lokacin suna rumgume da juna, a palo suka tararda Talatu sai rabon ido take tana ganinsu tace “Lafiya nake jin ihunta?” Kai ya ɗaga mata “Lafiya kalau Baba jeki ɗakin ki” Ba musu ta shige ɗakinta ba dan ta yarda ba komai ɗin ba, wayarsa ya dake kan kujera ya ɗauka ya shiga dialing wata number. bugu biyu aka ɗauka, “Shigo ina neman ka” Haka kawai ya faɗa ya kashe wayar. ya cigaba da shafa ta, ita kuma sai rera kuka take a hankali. bayi mintu biyu ba aka buga kofar parlour Saif yace “Yes shigo” Yana shigowa ya kalle shi yace “Ka zaga kai da mutanen ka gurin ita cen nan ku duba min gurin komai kuka gani ku faɗa min” “Yes Sir” Ya juya da sauri ya fice. saman kujera Saif ya zauna still yana rumgume da ita sai tunani yake, daker ya samu ta sake shi ta zauna saman kujera amman bata yarda tayi nisa dashi ba dan kunkurunta na gugar nasa sam ta manta da wani abu wai kunya da kuma gudunsa ta take. Bayan kamar mintu na arba'in suka sake jin an buga kofar, “Yes come in” Saif ya faɗa, a nan mutunen ya turo kofar ya shigo bayan ya karaso ya aje hijab ɗin Kairat da wani kololon abu kamar fatar damisa. wani irin tuma Kairat tayi kamin Saif ya ankaro har ta haye saman jikinsa ta rumgume shi gam. “Ga abunda muka gani babu kowa a gurin mun dai samu rame sai muka tona shine muka ga wannan” Mutunen ya faɗa yana kallon Kairat kamar zaiyi dariya kuma bai yi ba, “Okey jeka dashi can gurin ka idan an tashi zan neme ka” Tashi yayi ya fice. sannan Kairat ta ɗago ta sauka saman jikinsa. kirjinta ya kalla yana murmushi, sai tasa hannu ta kare gabanta ta ɗan noce kai. taɓe baki yayi a ransa yana Ba yanzu kika gama rumguma ta ba Tashi yayi. tana ganin hakan ita ta tashi. Daren kin yarda tayi su kwana ɗaki a dole palo suka kwana, kuma guri ɗaya jikinta na gugar nasa, da taji ɗan motsi ta shige masa. Shi kuma ya samu abunda yake so an ba kura fiɗa. lil Minal kuma ta kwana hannun talatu. *** *** *** A tare sukayi sallah asuba, suka koma bachi amman wanna karon a ware sukayi bachi dan taga safiya ce sai ta ware kanta can gefe tana bachinta. Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa bachi, ganin number Momy yasa shi saurin ɗauka cikin muryar bachi. “Hello Momy” Ban ji me akace masa ba na dai ga ya tashi amman gadon yana faɗin “Okey gani nan zuwa” Banɗaki ya shiga bayan ya aje wayar ya watsa ruwa ya fito a gagauce ya shirya, ya fisa turare. har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo ya duka a hankali yayi ma Kairat kiss a goshi ya fice. Cikin yan mintuna ya isa gidan bayan yayi parking ya shiga cikin parlour. Ihunta ne ya amsa masa sallamar da yayi ya kalli Momy da hankalita ke tashe yace “Wai me ya same ta?” “Wallahi ba mu sani ba, ni dai ina ɗaki naji ihunta shi kenan fa abun har yanzu kuma bata magana sai kuka da ihun nan da take”1 Momy ta faɗa kamar zatayi kuka, Hannayesa ya zuba cikin aljihu yana sauke ajiyar zuciya “Da yaushe abun ya same ta?” “Jiya da dare misalin shaɗaya na dare” Tsaki yaja ya nufi ɗakinta yana girgiza kai.

0 Comments