ANYI WALKIYA CHAPTER 7

ANYI WALKIYA CHAPTER 7
A mota ya jefata ya rufe murfin motar be jira cewarta ba yaja motar a guje.....Hagen fitarsu bilkisu tayi Tana murmushin mugunta....ta juya abinta, Saida suka hau Kan titi sanan ya waigo ya Dan kalleta har yanzun kuka takeyi kamar wadda akaiwa mutuwa gashi ta dunkule waje daya Tana rawar sanyi alamar zazzabi ne ke damunta.... Kada kansa kawai yakeyi minti minti Yana juyowa ya kalleta tausayinta ke ratsa sassan jikinsa, Be tsaya ko inaba sai asibitin su Ahmad,parking space yayi parking motarsa sanan ya Ciro wayarsa ya Kiran ahmda minti kadan sukai magana ya kashe.... Kallonta yakeyi yadda ta juyar da kanta gefe Tana hawaye yakai minti biyu a haka sai da ya gaji yace "muje ko?" "Bana bukatar taimakon kowa sai na Allah da ka maidani kawai ai Allah Yana sane Dani tunda mantawa Kayi Dani" Kamo hannunta yayi ta kwace "Fatima dama abinda ya janyo Miki zazzabi kenan?abinda yasamun ke rashin lafiya kenan?kika rame kikai baki tamkar wadda tayi ciwon shekara daya?....dafe kansa yayi take tausayinta ya Kara ratsa zuciyarsa cikin sanyin murya ya cigaba da magana "kiyi hakuri banyi hakan da ganganba sai Dan wani uzuri,Kuma Allah ya rubuto hakan zai faru insha allahu bazan sake barinki ba kinji?na tuba bintu"...ya karashe maganar cike da lallashi. Sai yanzun ta juyo da dubanta gareshi idanuwanta na fidda hawaye...."karka sake yimun haka idan ka barni bansan yadda zata kasance da rayuwata ba Kaine jigon rayuwata,idan ka nisanceni Yaya zanyi inyi rayuwa Babu Rabin rayuwata a tare Dani?"kafesa tayi da ido har yanzun hawaye ke zuba a idanuwanta Hannunsa yasa ya shiga share Mata hawaye cikin sigar lallashi yake fadin "ya Isa bintu Nima na shiga halin da kika shiga kanki kikasani juriyace kawai da jarumta irin ta da namiji Amma kiris ya rage in zubar da hawayena"...ya kashe Mata ido daya Cike da shagwaba ta langabar da kanta a jikin seat Tana jifansa da wani irin mayen kallo da idanuwanta ko kiftawa batayi yayinda yaji wani shaukin soyayyarta na dibarsa ji yakeyi tamkar ya rungumeta ya lallasheta,ji yakeyi tamkar ya dawo da kwanaki ukun da sukayi ba a tare ba....dakyar ya saita kansa ya matso daf da fuskarta Yana jiyo sautin futar numfashinta Mai zafin gaske "bintu Anya zan iya rayuwa da wata mace bayanki kuwa?" . Kada Masa idanuwanta tayi hade da murmushin karfin Hali "Dole zaka koyawa kanka rayuwa da wata mace bayan ni dikda naso ace nice kadai zan mallakeka" Hancinta ya ja cike da zolaya "matsoraciya keda kikace bakiso Mai martaba yasan da ke?cewa kikayi Kar infada Masa saboda kina tsoron Kar deejah ta zauneki ni bansan yadda zaayi ki koyi zama jaruma ba" Turo baki gaba tayi Tana Masa hararar wasa"nidai muje kaga ka kawoni a dubani ka cikani da surutu" "Malama kin fa warke dama ciwon soyayya ne Ashe dai haka akesona" Hannu tasa ta rufe idanuwanta Tana dariya,lokaci daya sukaji Ana kwankwasa glass din motar..... Da sauri yarima ya zuge glass din ya motar gaba daya,Ahmad ne tsaye sanye da labcutt wuyansa rataye da abin daukar numfashi irin na likitoci,hararar yarima ya shigayi "malam ka kirani tun daxun zaku shigo Kun kwashe kusan Awa daya bangankuba nagaji na harhado Mata magungunan zazzabi na biyoku dashi Dan nasan soyayya kukeyi.... Tabe baki yarima yayi hade da dage kafadarsa sama sanan ya Mika Masa hannu ya karbi ledar "zamuyi maneji Amma na rigada na Bata maganin ciwonta dama ciwon nawa ne ko bintu" STORY CONTINUES BELOW Sadda kanta kasa tayi kunya ta lullubeta ganin yadda jikinta yayi dauda haka ta fito Babu kyaun gani wani ma sai yace ta shekara batayi wanka ba....murmushi kawai takeyi kasa kasa.... "Kaidai kasani sai nazo Mata allura" Da sauri ta dago ta kalleshi,dukansu suka kwashe Mata dariya ta sunkuyar da kanta da sauri.... Hannu yarima ya dagawa Ahmad hade da tayar da mota ya jasu a guje.... Tunda suka hau hanya gabanta ke tsananin faduwa Dan ta manta da shaff cewa wannan gidan zasu koma,idan Tana hare da yarima jinta takeyi a wata duniyar ta daban.... ****** "Ranki ya dade a idona ya dauketa suka fice Kuma motarsa yasata ya ja da kansa suka fita" Kaiwa da komowa kawai hajiya babba takeyi hannunta rungume a bayanta.....tsananin takaici ne ya hanata cewa komi tunda saade ta Soma magana, Kasa gasgata maganar saade tayi Saida tasa Mami ta binciko Mata ko Ina ta tabbatar Mata da Bata gidan, Iska Mai zafi ta furzar daga bakinta "lallai yaron Nan nema yakeyi ya nuna mun iyakata,lallai kabiru ya cika Mara kunya ya tabbatar mun da shi Dan halak ne ni Kuma zanyi maganinsu dukansu su biyun bawai na rasa yadda zanyi dasu bane...." ******** A parking space yayi parking motarsa ya kashe motar ya kunna fitilar cikin motar ya dan kalleta Yana nazarin yanayinta,ya lura da dik yadda take a tsorace a firgice,shi mamakinta yakeyi yadda takejin tsoron wadanan bayin Allah Jin shiru yasa tasa hannu zata bude kofar taji a rufe ta juyo da sauri suka hada ido ya sakar Mata murmushi kasa mayar Masa tayi sai kallonsa da takeyi cike da kosawa tace"yaayah Dan Allah ka budemin in fita kafin wani ya ganmu" "To meye idan anganmu nidin ba mijinki bane?Mai martaba ya mallakamin ke ya yarjemun da aurenki" Raurau tayi da idanuwanta Tana kallon yadda yake magana hankalinsa a kwance....ita ko dik inda hankalinta yake a tashe yake "haba mana yaayah Dan Allah ka budemin kofar Nan infita" Key yasa yayi unlocking motar da sauri ta bude kofar jiki na rawa tasa kafarta ta jiyo muryarsa "tunda kika tafi baki tsaya nagama kallon kyakkyawar fuskarki ba to tabbas wajen wata zanje yanzun Nan " Cakkk ta tsaya zuciyarta na harbawa sauri da sauri take wani Abu yazo ya tsaya Mata a kirji dakyar ta hadiye miyon bakinta ta karasa fita har zata rufe kofar ta leko da kanta Tana kallonsa cikin ido ya kashe Mata ido daya "idan har kaje to tabbas kasani kabar sake ganina sai Nan da sati biyu" Dage kafadarsa yayi Yana murmushin mugunta tarkon daya Dana Mata ya kamata Nan da Nan ta nuna Masa kishinta a Fili.... Juyawa tayi da sauri tabar ledar maganin cikin motar saboda kidimewar da tayi hantar cikinta dik a Kade take addua kawai takeyi Allah yasa Babu Wanda ya ganta.....ga takaicin maganar da yarima yake fada mata Wai zaije wajen wata ,to yaje Mana ai ko be fadaba tasan cewa Yana son deejahmah boye Mata kawai yakeyi.... Har ta doshi shiga ta babban parlor ta fasa dabara ce ta fado Mata tabi ta kofar baya da sauri ta kwaso shanyar da tayi ta nufo cikin gidan kirjinta na bugawa.... Sashen hajiya ta shiga da sallama sai Raba idanuwa takeyi dakyar ta Tattaro jarumtar ta tayi sallama cikin sassanyar murya... "Kin dawo daga yawon iskancin kenan?kin manta na baza idanuwana cikin gidan Nan Kuma dik akanki suke?...ya daukeki ya fita dake kunyi abinda zakuyi kundawo ko ?ai na dauka daga can wani waje zashi dake ya ajiyeki ya fiye Miki sauki Akan dawowa cikin gidan Nan"... Wani mugun miyau Fatima ta hadiye a fakaice"Babu inda naje Ina bayan can anan nayi sallah na zauna har akayi ishai sai yanzun na dawo ai bilkisu ta taganni lokacin " STORY CONTINUES BELOW Da sauri hajiya ta juyo ga bilkisu wadda ke faman zare Ido "bilki Wai kinganta?" "Naganta ranki ya dade niba shiga sabgarta nakeyi ba shiyasa nayi wucewata Kuma bansan maganarta kukeyi ba Dan ni ko sunanta ma bansaniba".. Kwafa hajiya ta sauke ta wurgawa Fatima wata uwar harara "ficemun daga daki" Mikewa tayi ta fice abinta har yanzun gabanta be daina faduwa ba ta fito ta babban parlor, Hajiya karama ta gani zaune hannunta dauke da carbi Tana ja ta karaso ta tsugunna a gabanta ta gaidata ta amsa Mata Babu yabo Babu fallasa.... Dakinsu taje ta nemi waje ta zauna ta fada duniyar tunanin yarima....zuciyarta ke ayyana Mata yanacan tare da deejahmah suna Shan soyayya ke tsoro ya hanaki nuna Masa yadda kike sonsa,ki tsaya kallon ruwa kwado yayi Miki kafa, Yatsanta ta ciza hade da Jan tsaki lokaci daya, A gaggauce bilkisu ta shigo ta sameta daidai tanajan tsaki "ke kuma tsakin me kikeyi?angamo soyayya an dawo kinzo kina zare idon banza bayan ba tsoron da kikeji tunda kika iya awanni biyu tare dashi" Duka Fatima ta Kai Mata "ni ki kyaleni abinda ya dameni ya dameni Dan yanzun fa fushi yayi Wai zaije wajen wata" "Kadan kika gani wallahi inhar bazaki cire tsoroba kiyi yaki to watarana Zaki wayi gari ki nemesa ki rasa yanzun gogayya yakamata kuyi ta tsaya Jin Kai ke Kuma ki kwace miji dik kallon baiwa kuyanga da akeyi Miki ki barta a Tasha" Dariya Fatima tayi "ni Bilki idan kina magana kamar wata uwar Mata mamaki kike bani" Harararta bilkisu tayi "Dole inbaki mamaki ai tunda kin Gama koke koken kin warke yanzun ai Dole ki fadamun magana " Toshe baki Fatima tayi tanawa bilkisu dariya wadda ke magana cike da kulewa, "ni yanzun babban tashin hankalina be wuce ranan da zata kasance an rabamu da yarima ba maana ranan da zaa daura Masa aure" "Ki shirya kibishi gidan matar" Tsaki bilkisu tayi ta juya tai tafiyarta tabar Fatima Nan..... ********* Shiko yarima Yana ganin shigewar Fatima cikin gida ya fito ya rufe motarsa ya shige bangarensa Yana murmushi Domin Harga Allah dariya ma abin ya bashi.... ********** Bayan kwana shida, Ya kasance befi kwana takwas bikin yarima da deejah ba gida ya fara rikicewa da baki na cikin gida da waje saura kwana biyu a fara event kamar yadda deejahmah ta tsara itada aminiyarta teemah dollar..... Zaune Fatima take can bayan gida inda ya kasance Nan ne wajen zamanta Nan take makalewa taita kukanta dik ta fige ta rame ta shiga matsananciyar damuwa hakika sabo turken Wawa ne ta tabbatar da hakan Dan ta Saba dashi sosai fiye da tunanin Mai karatu, Durkusar da kanta tayi Tana kuka Mai ban tausayi Wanda batasan dalilinta na yinsa ba,.. Nemanta bilkisu takeyi tun safe Bata gantaba har ta cire Rai da ganinta saita tuna da inda suke Zama saboda mutane da suka fara yawa cikin gidan.... Yarima ta gani yanata dube dube tamkar me neman wani Abu can ya hangi bilkisu ta nufi bayan gidan su inda bishiyoyin mangwarori suke....bayanta yabi har suka Isa a tare wajen bishiyar da Fatima ke tsugunne Tana kuka Ganinsu ya sanyata saurin mikewa Tana share hawayenta hade da wayancewa, Kallon yadda ta canja yakeyi dik ta rame tayi bakin Kirin idanuwanta sunyi zuru zuru.... Tsugunnawa yayi a gabanta ya rike kunnuwansa alamar ban hakuri.....kuka ne ya taho Mata lokaci daya kawai ta durkushe a gabansa Tana kuka Mai ban tausayi.....besan lokacinda hawaye ya shiga fita a idanuwansa ba,....ita kanta bilkisu dake jingine jikin bishiya hawaye takeyi Domin dik Wanda ya kalli Fatima a wanan yanayin saita bashi tausayi..... Dakyar ta tsagaita da kukanta ta matso kusa dashi tasa gefen rigarta Tana share Masa hawaye hade da girgiza Masa Kai...."...banason ganin idon jarumin namiji Yana fitar da hawaye,....idan har bakayi shiru ba bazan gafartawa kainaba"tana maganar ne Tana kuka.... Hannu yasa ya share hawayensa sanan yasa hannunsa Yana share Mata hawaye "banason ganin kyakkyawar fuskar Nan cikin damuwa, kiyi shiru ki dainamun asarar hawayenki Fatima,hawayenki sunfi komi tsada da kima a idanuwana da inada Hali da na hanasu zuba har abada meyasa kike nisanta kanki Dani cikin kwanakin Nan".. Cikin shasshekar kuka taja hancinta "nafara koyawa kaina rayuwa batare da kaiba,kukan Nan da kaga inayinsa inayine saboda zan rasa farin cikina.....banida gatan daya wuceka a rayuwa,...ka manta Kaine inuwar dake zagaye Dani a cikin gidan Nan?babu wata inuwar da nake rabawa insamu farin ciki in samu sassauci daga zafin Rana sai inuwarka....banida uwa bani da uba sai Kai ya bazanyi kuka ba?ya bazanyi kukan rashin masoyi ba?"..... Tunda ta Soma magana hawaye ke gudu a idanuwansa tausayinta shine abinda ya mamaye ilahin sassan jikinsa.....hakika Fatima a bar tausayi ce Fatima batada gatan daya wuceshi cikin wanan duniyar..... Kammo hannunta yayi ya rike Yana murzawa yayinda take durkushe a kasa Tana kuka Mai ban tausayi..... "Ki dago kanki kidaina wanan kukan Domin idan kinayinsa ji nakeyi na tsani kaina a rayuwa ji nakeyi tamkar na cutar dake naci amanarki ki dago ki fadamun abinda kikeso inyi Miki nayi alkawarin yi Miki ko meyeshi a fadin duniyar Nan matukar Zaki daina zubar hawaye".... Dago Kai tayi tana Kare Masa kallo har ya Kai karshen maganarsa,Kara damke hannuwansa tayi cikin nata,dayan hannunta ta Sanya ta share hawayenta+ "Kaima ka share hawayenka kaji ?kaga Nima na share nadaina kuka kaji?".. ta langabar da kanta Tana kallonsa, Hannu yasa ya share hawayensa ya maida dubansa gareta "Ina sauraronki fadamin bintu na mekikeso umm?" "Ni tsoro nakeji kada kayi aure ka mance Dani ka manta da wata Fatima na rayuwa a doron kasa,gashi ka sabamin da rayuwa da Kai ba lallai bane kullum inganka shiyasa na shiga damuwa" "Idan har zan mance dake faty to tabbas zan mance da kaina da rayuwata,kisawa zuciyarki ninakine ke kadai harabada bazan taba rabuwa dake ba numfashina" Kallon yadda yake motsa bakinsa takeyi soyayyarsa na yawo cikin jinin jikinta,ta shagala da kallonsa har ta mance da wani bacin Rai da take ciki a wanan lokacin, Duko da kansa yayi Yana kallon cikin idonta ,da sauri ta kauda Kai Tana murmushi "yaayah Dan Allah ka rinka zuwa wajena kaji?"ta marairaice fuska, Mikewa tsaye yayi Yana kakkabe jikinsa "rigimarki yawa ne da ita Fatima Allah Ina gab da fara zaneki don wanan kukan da kike yi wata rana hawayenki zasu Kare" Mikewa tayi tsaye tana murmushi "inhar kukan Nan ne bakaso to na Bari ".. Gira daya ya dage Mata "kin tabbata?" Daga Masa Kai tayi tana dariya. Aiko Dole inbaki chocolate,ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya Ciro chocolate guda biyu ya bare da hannunsa "oya taho ki amshi kyautar soyayya" Tana dariya ta Miko fuskarta ta Dan bude baki ya tura mata chocolate baki ta hade da yatsansa ta rike Tana dariya... "Aushhhh da zafi Mana wallahi kinci bashi saina Rama" Kada Masa idanuwa tayi "yanzun sai ka Rama?"... "Ehh Mana kibari indawo daddare zan Rama zan siyo muku kayan da zaku canja kuci biki dashi keda bilkisu da Maryam" Gyada Masa Kai tayi "Allah ya tsare" Waige waige ya shigayi hade da leka bayan bishiyar sanan ya juyo Yana dubanta "Ina bilkisu?".. Sai lokacin Fatima ta tuno da wata bilkisu itama waige waige ta shigayi sanan ta juyo tace mishi "Ashe ta wuce" Jan hancinta yayi kadan "yaushe zakisan ta wuce kinatawa mijinki rigima?umm?"...yasa hannu ya zagayo kungunta ya riketa sosai Yana kallon fuskarta,itama shi take kallo Tana murmushin sannan taja da baya cikin dabara ta kwace daga rukon da yayi Mata "saika dawo" Gyada Mata Kai yayi ya juya cikin sauri Yana kallon agogo ya bar wajen,kallo ta bishi dashi hade da sauke ajiyar zuciya.... Ta Dade zaune wajen Tana tunani kala kala yadda zuciyarta batayi Mata Dadi kwata kwata..... ********** Yau ta kasance Ana gobe zaafara event din biki yayinda gida yake cike makil da jamaa na ciki Dana waje Kuma yau ne hajiya zainab da tawagarta suka sauka daga Saudi Arabia bangaren mama karama ta sauka Domin sunfi shiri da ita,.. Tunda garin Allah ya waye ake girke girke kala kala dik wata baiwa da ke cikin gidan Bata Samu tsugun ba saboda aikace aikace da suke famar yi yayinda deejahmah da tawagarta gabaki daya suka dawo gidan sarki Nan ake biki sosai.... STORY CONTINUES BELOW Zaune da kawayenta can wani daki Wanda ya kasance Nan anyisa Domin masaukin baki dakine safe content da bayi biyu ciki a Nan suka sauka suke lalle itada kawayenta da kannenta ciki kuwa harda su khausar afnan,faizah da fauziyya sai wasu friends dinta guda uku,.. Taunar chewing gum takeyi cike da yanga da kasaita yayinda ake Zane Mata kafa da hadadden lalle Mai shegen kyau domin ita kanta me lallen daga wani gari aka daukota musamman don tayiwa Yan biki lalle,.. Gefen kawarta teemah ta kalla ta Dan yatsina fuska "ka'wata nake ganin kamar lallen Nan ya bushe ko?ya kamata a baremun na kafafuwan sanan akawo ruwa a wankemun kafar" Jinjina Kai teemah tayi tana kallon kafar "ya kamata Kam ai sai ayi Miki,...juyawa teemah tayi gefen da rahane kuyangar deejahmah take tsugunne ta Dan kalleta a wulakance "Rahane ki kawo Mana ruwa" Yunkurawa Rahane tayi zata Mike da sauri deejahmah ta dakatar da ita "Rahane wanan ba aikinki bane aikin tsintacciya ne,kije dik inda take ki kiramun ita tazo ta kankaremun lalle ta wanke kafar matar uban dakinta"...ta karashe maganar Tana murmushi hade da hada ido da teemah dollar ta daga Mata hannu hade da jinjina 👍🏼"yayi ranki ya dade ya kamata ta fara bautawa uwargijiyata kafin ta fara ainihin bauta Nan gaba" Kallon juna faizah sukai da fauziyya wadanda suke gefe waje daya idan ka kallesu zasu iya juyar maka da Kai saboda tsabar kamanninsu, Fatima na cikin kitchen suna hakilon aikin abinci dik tayi zufa tayi bakin Kirin ta gaji Domin aikin da takeyi yafi karfinta, Direct wajenta Rahane ta nufa ta tabota,da sauri ta juyo "uwar gijiyata nada bukatar ganinki yanzun a sashen baki"....Bata jira cewar Fatima ba ta juya abinta.... Dafe kirjinta tayi tana tambayar kanta a zuciya "wacece Kuma uwar gijiyarta?"...jiki a sanyaye tabi bayan rahane da sauri har tana tuntube gudun karta bace Mata,.. Sashen dataga Rahane tabi ne ya Sanya gabanta ya yanke ya fadi take taji wani Abu na Shirin tasowa a kirjinta tabbas yanzun ta Gane fuskar Rahane Dan ta taba ganinta tare da deejahmah, Dakewa tayi tabi bayanta har cikin dakin da sallama dauke a bakinta ta nemi gefe ta tsaya batare da tace komiba, Dukan wadanda ke cikin dakin suka zubowa Fatima na mujiya wasu nayi Mata kallon wulakanci wasu nayi Mata kallon ko in kula, A fusace deejahmah ta kalli Fatima dake tsaye kikam zuciyarta na tafasa "ke kinfi karfin ki tsugunna a gabana nasa a kiraki?ko kin manta matsayinki na kaskantacciyar baiwa ne?Koko ni saarkice da zankiraki ki tsayamim a Kai batare da kin rage tsawoba?" Batare da Fatima tace komiba ta rage tsawonta ta tsugunna Amma fuskarta a daure tamkar Bata taba dariya ba, Da yatsa deejahmah ke nunata Tana fadin "ba yanzun Zaki wannan iskancin ba kibari sai Kinga cikar burinki,..sanan ni ba kaunar kallon wanan mummunar fuskar Taki nakeyi ba infact ko ganinki banason yi yanzun ma dalili ne yasa nakiraki aiki zansaki ,kije kisamo ruwan zafi ki sirkashi kizo ki kankaremun lalle sanan kisa kafata ciki ki wankemun yanzun Nan idan ba hakaba kinsan sauran" Tsananin bacin Rai ya Hana Fatima cewa komi Banda idanuwanta da suka kada sukai jajir tamkar zata fashe da kuka haka ta Mike tsaye ta fice,....deejahmah tabita da uwar harara tamkar idonta zai fado kasa.... "Niko deejahmah Ina suka samo wanan kyakkyawar yarinyar tamkar ita tayi kanta kuma a matsayin kuyanga?gata yarinya karama wallahi"... Harara deejahma ta watsawa kawarta da tayi wanan maganar sanan tace"tsintacciya ce shegiya uwar ta da tai cikinta yarda ita tayi a bakin kwata Yan gidan marayu suka tsunceta suka sata cikinsu shine mijina ya daukota a matsayin baiwa Yar aikina" STORY CONTINUES BELOW Daidai Nan Fatima ta shigo hannunta dauke da Dan karamin baho ta ajiye a gefe ta shiga kankarewa deejahmah kafa,....tanayi zuciyarta nayi Mata Kuna takaici da bakin ciki duka suka lullubeta a haka har ta Gama,ta sa hannu Tana Shirin tsoma kafar cikin ruwan zafin,...da sauri deejahmah ta dago Kai ta Kai Mata Mari cikin tsawa tace "kin taba kinji zafinsa ne da kike kokarin samun kafa cikin ruwan zafi?konani kikeson yi?kin kashemun tsoho mijina dik be ishekiba Nima sai kin konani kenan" Aikuwa idon kowa dake dakin ya dawo Kan Fatima wadda tayi tsumu hade da sunkuyar da kanta kasa,take kwallar bakin ciki suka shiga silalowa a kumatunta,....daurewa tayi tasa hannu cikin ruwan sanan ta dago Kai ta kalleta hawaye na zuba a idanuwanta "Babu zafi na surka kafin inzo" Murmushin nasara deejahmah tayi Domin burinta be wuce ta nuna mulki da Isa a gaban kawayenta ba burinta be wuce ta wulakanta Fatima taga Tana hawaye ba,...tabe baki tayi sanan ta watsa Mata harara "ki samun" Haka tasa kafar cikin ruwan Tana wankewa hawaye na gudu a idanuwanta har ta Gama ta Mike ta fice a dakin.... Tausayin Fatima ne ya lullube faizah dake zaune a gefe Tana ganin dik abinda ya faru,wayarta da Jakarta ta mikawa fauziyya ta Mike ta kalleta fuskarta Babu walwala tace"rikemun fauzy Ina zuwa".. Da sauri deejahmah ta kalli faizah cikin Isa tace"ke Kuma Ina Zaki?ko kin fasa lallen ne?bakiga k'awata ake mawa ba yanzu?shine kikai fushi Zaki futa kika canja fuska?" Girgiza Kai faizah tayi tana murmushi "ah ah wallahi anty deejah Ina Dan Jin yunwa ne zanje insa a zubomin abinci".. Murmushi deejahmah tayi tana kallon faizah "kiyi sauri fauziyya Dan idan tagama ku zaayiwa Dole ayiwa Yan biyun innah,...." Dariya sosai faizah tayi "anty deejah ga fauziyya Nan gefenki"...duka Yan dakin suka sa dariya...yayinda deejahmah ta tabe baki "ni ba ganeku nakeyiba kamanninku yayi yawa kiyi sauri dai" "Owk"shine abinda faizah tace a takaice ta fice.... ******* Kitchen ta shiga tanata dube dube Bata ganta ba ta fito ta kofar baya na kitchen sai ta ganta tsaye ta hada Kai da bango Tana hawaye hannunta daya dafe da jikin bango,...ta Dade tsaye a bayanta sanan dakyar ta karfin Hali ta ambaci sunanta cikin sanyin murya "Fatima"... Jimm kadan Fatima tayi sanan ta juyo fuskarta jike da hawaye da sauri tasa hannu ta share hawayen ta tsugunna gaban faizah "ranki ya dade me kike bukata?" Dukawa faizah tayi ta dagota ta mikar da ita tsaye fuskarta dauke da murmushi ,....kallo itadai Fatima ta bita dashi batare da tace komiba, Faizar ce ta fadada faraarta "sunana faizah,....na Dade inaso inzo in kebe dake inyi magana dake ta fahimta ni bazan cutar dake ba Domin Harga Allah ni Ina kaunarki tsakanina da Allah ne bansamu nazo ba saboda makaranta da muke zuwa nida Yar uwata,ni Yar waziri ce Nan bayanku kadan gidanmu yake kusan gida dayane Amma kofa CE ta rabamu" Murmushi Fatima ta kirkiro dikda bacin ran da take ciki a wanan lokacin ta mikawa faizah hannu su gaisa,babu kusu faizah ta mikawa Fatima hannu suka gaisa sanan faizah ta cigaba da magana "kiyi hakuri dik abinda ya sameki mukaddari ne daga Allah kinsan bawa baya wuce kaddararsa a rayuwa sanan kiris ya rage kema ki fara farin ciki kamar kowa,ki daure ki jure anzo karshe Domin kema Nan gaba kadan Zaki fara zuba mulki har mu da muke a matsayin kannen mijinki dole muyi Miki biyayya".... Murmushi Fatima takeyi Tana kallon faizah....ya fito ta kofar kitchen hannunsa dauke da leda yanata waige waige Dan sauri yakeyi zai fita sai yaji magana kasa kasa ya juya da sauri gefen da yakejin maganar take sukai Ido hudu da Fatima ta sakar Masa murmushi, STORY CONTINUES BELOW Bayan faizah yakebi da kallo don besan ko wacece ba Saida ya karaso wajen ya bita da kallon mamaki,murmushi faizah tayi take yarima ya Gane itace ya maida Mata da murmushi hade da nunata da yatsa cikin wasa yace "idan banyi batan Kai ba faizah ce ko?Domin kece sarkin murmushi" Dariya faizah takeyi Tana gyada Masa Kai "nice Yaya barka da zuwa" Cikin kosawa ya Dan kalli Fatima ya kalleta "me kukeyi a Nan ne? injidai lafiya"...faizah zatayi magana Fatima ta rigata cike da shagwaba ta amsa da "nida faizah ne Yaya tazo Tana lallashina itace sabuwar k'awata Tana Sona" Dadine ya cika yarima Jin Fatima tasamu kawa me kaunarta bayan bilkisu koba komi zata samu sassauci..."gaskiya naji Dadi faizah Dan Allah ki rikemun amanarta ki rinka kulamin da ita kinji?Kinga ita zan aura Kuma marainiya ce batada kowa saini saike yanzun da kike kaunarta kinji' Gyada Masa Kai faizah tayi tana murmushi "insha allahu zaka sameni da rukon Amana yaayah Domin inason halin Fatima" Murmushi yayi ta mikawa Fatima ledar hannun sa "ankon wajen kamu ne da zaayi gobe Kuma a gidan Nan zaayi nasan sauran kuyangin ma sarki ya bada kudi a siya musu Kaya su sabinta saboda biki shine na siya muku keda bilki" Wani irin kallon soyayya take jifansa dashi Tana murmushi Wanda ganinsa ya mantar da ita bakin cikin da take ciki "mungode Allah ya saka da alheri Allah ya Kara girma" Dadi ne ya kamashi yayi murmushi "ki kawomin ruwan zafi daki zan Dan Sha in warware cikina tun safe banci komiba" "Angama ranka ya dade"... Hannu yasa ta Ciro wallet dinsa a aljihu ya Ciro kudi Yan dubu dubu ya kirga dubu goma ya mikawa faizah "ga wanan faizah kema ki siyi abinda baki siyaba na biki" Ta Dan durkusa "nagode Yaya Allah ya Kara girma" "Ameen"kawai yace ya wuce ya barsu Nan tsaye da Fatima, Kamo hannunta Fatima tayi ta hada "Allah ya barmu tare faizah nagode da kauna....Allah yasa ki rikeni Amana" Ta bayansu bilkisu tace "Fatima me kikeyi a Nan tun dazun hajiya na nemanki nazo kitchen bangankiba shine na biyo ta baya ko zan ganki" Karasowa bilkisu tayi tanabin faizah da kallo yayinda ta maida dubanta ga Fatima tanayi Mata kallon tuhuma,itadai faizah batasan tsakaninsu ba yasa tayiwa Fatima sallama tace Tana zuwa zata Kara dawowa ta wuce, Harara bilkisu ke jifan Fatima dashi "Mara zuciya wanan Kuma wacece tazo kika ruko hannunta kdmar wata Yar uwarki" "Ke da'alla faizah ce Yar waziri tanada kirki sosai yanzun aka Gama wulakantani a gabansu shine ta biyoni Tana bani hakuri take cemin ta Dade tanaso tazo wajena Domin Tana kaunata" Girgiza Kai bilkisu takeyi hade da rike kugu "kauna fa kikace Fatima?dama wadanan mutanen zasu kaunace ki?a tunaninki ba wani tuggun ake son hada Miki ba" "Ah ah bilkisu ka kyautata zatonka Akan kowa,kuma yadda tazomin ban kawo komi a rainaba Dan bakiga abinda deejahmah tayimun a gabansu ba"...Nan ta kwashe komi da ya faru tsakaninta da deejahmah ta fadawa bilkisu, Ajiyar zuciya bilkisu tayi murya a raunane tace"Allah yasa dagaskene " "Ameeen"... Ta kalli bilkisu Tana murmushi tace "Bari insa ruwan zafi inje inyi sallahr laasar kafin Nan ya tafasa yarima keso sai inzo mu zanta ko?" Jiki Babu kwari bilkisu ta amsada "toh shikenan ki sameni wajen magwarori" "Naga jikinki dik yayi sanyi ne ko akwai wani Abu ne Yar uwa?" STORY CONTINUES BELOW Girgiza Kai kawai bilkisu tayi ta juya abinta.... ********** Sauri sauri tayo alwala ta zo inda ta Saba zuwa tayi ibada ta shimfida dankwalinta ta tada sallah cikin natsuwa take sallahr ta ta fuskanci alkibla Tafe suke Tana rike da hannun yaronta karami sun fito sashin Mai martaba yaron ya kalli mahaifiyarsa Yana nuna Mata Fatima dake sallah "ummu laa duba sallah takeyi ankira sallah ne?".. Juyawa hajiya zainab tayi tana kallon inda yaron ke nuna Mata tabi yarinyar da kallo wadda ke sanye da Kaya irin na kuyangin gidan "sadik ankira yanzun zamuje muyi muma kaji?".. "Toh ummu muyi sauri" Batace masa komiba takebin Fatima da kallo Tana jinjina Kai cike da mamaki ta furta a Fili "ikon Allah "...haka suke tafe Tana saka da warwara har suka shigo sashen hajiya karama ko Zama batayiba ta kalli hajiya cike da al'ajabi tace"hajiya dama maaikatan gidan Nan suna sallah ne?ni tunda nake bantaba ganin wata baiwa ko kuyanga na sallah ba a iya rayuwata a cikin gidan Nan sai yau Naga wata Yar farar yarinya bandai lura da fuskarta ba Tana sallah can baya" Fuska dauke da damuwa hajiya karama ta kalli hajiya zainab sanan ta kauda kanta gefe tace"wacece kika gani Banda Fatima?yarinyar da kikejin labarin ta kashe Miki d'a habibu ?itace wadda danki yake Shirin jajubowa a matsayin matar aure tsintacciya Mara asali itace surukarku" Zama hajiya zainab tayi gefen hajiya karama sanan ta nisa tace "hajiya insha Allah wanan yarinyar alheri ce a rayuwar kabiru Domin naji hakan a jikina,Koda ta kasance Mara asali tsintacciya ba yin kanta bane laifin iyayenta ne sanan ba ita ta halicci kanta ba Allah ne ya halicceta yasa kaddararta tazo a hakan....sanan maganar kisan Kai kusan gaskiya saidai ku take sani tunda kungani a video lalata danku yajeyi da ita Allah ya Aiko Masa da ajali,be Dace ku tsaneta ba Dan Babu Wanda yafi karfin kaddara ta fada Masa wallahi tunda ta kasance Mai ibadah ni Ina kaunarta Ina sonta a matsayin suruka kema Kuma inaso kada kibiyewa tsegumin mutane ki riketa amana bakisan me Allah ya boye a wajenba bakisan tarin baiwar da Allah yayi Mata ba" "Aike dama dik abinda kabir yakeso to fa kina sonsa,komi kabiru yayi daidaine a wajenki" Dariya wanan karon hajiya zainab tayi "saboda shi din yarone Mai biyayya da hankali da sanin ya kamata shiyasa,Kuma ninasan Dole yanada hujja da dalilinsa na yin hakan,nidai Ina kaunarta Kuma inayin suruka da ita" Ajiyar zuciya mama karama ta sauke "ai sai kiyitayi" Girgiza Kai kawai hajiya zainab tayi tana murmushi... ******* "Wai bintu sai wani sauri kikeyi kin hadamun tea ko ki tsaya kibani ma insha sanan kitafi" Dariya yabata Tana kallon yadda yayi maganar tamkar wani yaro karami "inbaka tea sai kace jariri".. "Toh ni ba jaririnki bane?ai mijinki tamkar jaririnki ne Domin kece keda hakkin kula dashi"... Mikewa tayi tana dariya"kaga tafiyata" Da sauri ya Kai Mata cafka zille cikin azama ya damkota da dayan hannunsa ya janyota Yana dariya itama dariyar takeyi "kaga bama saika rikeniba zauna da kyau inbaka,Amma kanaganin zaka iya Shan tea kana kallon wanan jikin nawa Mai dauda?"ta dage Masa gira daya hade da kyafta Masa Ido.. "Babu ruwana da dattinki ko cikin ruwan kwata kike kwana ke nakeso ba dattin ba" "Shikenan"ta dakko kofin tea din Tana juyawa Tana kallonsa ta dibo a cokali takai bakinsa Babu kunya yarima ya kurbe Yana dariya kasa kasa haka taita bashi har tea din yakai Rabin Kofi ta Mika hannu ya karba Yana fadin "oya Dole a ramawa kura aniyarta kema ki bude baki in baki naki" Rufe ido tayi yabita da kallo ya dibo tea din yace "oya ha baki"aikuwa Fatima ta bude Tana murmushi yasa Mata a baki yayita Bata harta shanye sanan ya ajiye kofin Yana kallonta Yana dariya, Turo baki gaba tayi hade da Dan canja fuska "yanzun da ka koyamin ciyar Dani idan katafi wajen matarka waye zai rinka bani abinci?bayan nasaba da yayana ke bani" Da sauri ya amsa da "nine Nan zan rinka zuwa Ina baki bintu,lokacin cin abinci nayi zanzo" Ta saki fuska Tana murmushi ta Mike ta dauke cup din ta juyo ta Dan kalleshi "ni natafi bakin aikina kaga bilkisu na can Tana jirana nasan ta cika tayi famm" Dage mata gira yayi batare da yace komiba ta juya tayi waje yabi bayanta da kallo,komi na Fatima na Burgesa... ****** Kicibis sukayi da bilkisu "malama nagaji da jiranki kintafi soyayya ko ?kunje satarwa sarauniya deejahmah hanya ko?Tana can tana kuri ku Kuna Nan Kuna soyewa".. Dariya Fatima tayi hade da yin kasa da murya "ai tunda ta bullo da hakan ni zata rinka tozartawa ni Kuma zan mantar da mijinta ita" Mamakine ya kashe bilkisu ta rike habarta Tana jinjina Kai Tana fadin "Allah ya kawomu Fatima tayi baki haka nakeso ta wajena jeki Kai kofin kidawo" Fatima ta shige Tana dariya.... ******* Maryam dake dakin hajiya karama Tana rabe a gefe hajiya zainab ta kalleta tace "ke,kinsan wata kuyanga Fatima?" Da sauri Maryam ta daga Mata Kai "ehh ranki ya dade" "Tashi ki kiramun ita"... Ta Mike da sauri, Hajiya karama tace dake gefe ta ce "hajiya lallai kinason surukar Nan Taki yanzun me zatayi Miki?".. "Inaso inganta ne sanan insata ta je bangarena ta bude ta gyaramun Kinga yamma tayi...." Jinjina Kai kawai hajiya karama tayi cike da gamsuwa... ******* A zabure deejahmah ta Mike daga kishingiden da take cikin tsananin tashin hankali take duban Rahane dake durkushe a gabanta tace"kikace takai awaya a dakin yarima? Kin tabbatar da maganar da kika fadamun ?" "Bana baki labari saina tabbatar ranki ya dade" Da sauri ta Mike tsaye tana zura flat shoes dinta, "Dakata princess ai martabarki da kimarki ta wuce kibita a matsayinta na baiwarki kece Zaki sa ai kiranta kici zarafinta yadda ya Dace" Huci kawai deejahmah takeyi Nan da Nan fuskarta ta canja kala ta dubi Rahane "kiramun ita"... Da sauri rahane ta Mike ta bar dakin ta barta Nan tsaye Tana huci hade da girgiza Tana furzar da iska a bakinta cike da bacin Rai... A parlor suka hade da Rahane Fatima na biye da Maryam Dan zuwa Kiran hajiya zainab Rahane ta tsaidasu "Fatima kizo inji uwargijiyata" Wani kallo Fatima tayiwa Rahane wanan karon sanan ta kauda Kai tace"zan fara zuwa Kiran hajiya zainab kafin inzo nata"....Tana Gama fadin haka ta wuce....Maryam tabi bayanta... Jinjina Kai Rahane tayi ta juya zuwa dakin da deejahma suke Tana shiga ta zube a gaban deejahmah "ranki ya dade tace ankirata saita Gama wancen uzurin zatazo naki" Cikin tsawa deejahmah ta ce"ita a wa?nidin inyi kiranta tacemun bazakazoba?lallai yarinyar Nan ta Kira Mai alewa batada kudin siye".....a fusace deejahmah ta wuce tamkar kububuwa har tana bangaje Rahane dake gurfane a gabanta ta fice a dakin.... Kallo suka bita dashi ko wanne da abinda yake rayawa a zuciyarsa..... Cike da natsuwa ta shiga dakin yayinda zuciyarta ta tsananta bugawa,fargabar abinda zai biyo baya takeyi Dan batasan laifin da tayiba ake Kiran nata...+ Gefe kadan ta tsugunna hade da sunkuyar da kanta kasa,..zuciyarta na tsananin bugawa ta bude baki a hankali tace "gani ranki ya dade ance kina nemana" Hajiya zainab wadda ke gefe ta kafe Fatima da Ido tunda suka shigo take binta da kallo har ta nemi waje ta tsugunna,...kallon yadda kayan jikinta sukai makal makal takeyi saboda datti sanan ta maida dubanta ga fuskarta wadda take a sunkuye ta kafeta da Ido.... Shigowa dakin yasa dukkansu suka daga Kai su kalli waye ya shigo Babu ko sallama bare neman izini, Deejahmah Bata damu da wadanda ke wajenba Dan batasu takeyi ba Fatima kawai takeso ta ciwa mutunci saboda yadda idonta ya rufe,....tsaye tayi Akan Fatima hade da rike kwankwaso jikinta har rawa yakeyi savida masifar dake cinta, "NA aika akiramun ke shine kika dawomin da Yar sakon kikace bazakizo ba saboda ninayi Kama da Saar ubanki?shegiya har ta Kai matsayin da Yar sunnah zata kirata tace bazatazo ba?ko kuwa aikin bautar da kikeyi an yantaki ne?"cikin tsawa take magana, Bude baki hajiya karama da hajiya zainab sukayi suna kallon ikon Allah, Dakyar Fatima ta hadiye wani mugun miyau na bakin ciki sanan tace cikin sanyin murya "kiyi hakuri lokacinda kika Aiko kirana,Nan anrigada an Aiko kirana ko kafin tazo shiyasa nace Mata tace Miki zanzo idan nazo Nan naji Kiran da akemun" Fincikota deejahmah tayi ta baya ta Fadi kasa,da sauri hajiya zainab ta Mike tsaye cike da masifa "dakata Mara kunya,kibari idan tazo saikiyi Mata cin mutuncin da zakiyi Mata Amma baa gabanmu ba wallahi tunda rashin kunyarki takai kishigo Mana daki Babu ko sallama,sanan ki rufe idonki kina kokarin ciwa Yar mutane mutunci to baki isaba kinyi kadan Khadija ai mafarkina be taba bani fitsararki ta Kai haka ba,Dan haka ki bacemun daga gani tun kafin nawa borin ya tashi insauke akanki".... Takaicine ya lullube deejahmah wani kululun bakin ciki yazo ya tokare Mata wuya Wanda yasa idanuwanta suka rufe ruf saboda tsananin bakin cikin abinda hajiya zainab tayi Mata gaban Fatima Amma dikda haka be hanata bude baki tayi magana ba "Ummu karya takeyi tun dazun na aike kiranta Taki zuwa saboda ni ta rainani shiyasa" "Da kika aika kiranta batazoba sai kika shigo Mana ko arzikin sallama bamu samuba ballantana gaisuwa dagani kuwa har uwar mijin Taki Anya Khadija wannan halin naki Zaki canjashi kuwa?rahina tayi Miki muguwar tarbiyyar da sai kinyi danasani Mara amfani a rayuwarki Nan gaba kadan,ki bacemun daga gani tunban gaggaura Miki Mari ba Mara kunyar banza" Jikin a sanyaye deejahmah ta juya batare da tace komiba zuciyarta nayi Mata suya,Bata da wani damar daukar hukunci a gaban ummu saboda sanin halinta Bata daukar raini haka ta fice cike da takaici,Mai makon tayi sashen da friends dinta suke sai tayi sashin hajiya babba..... Juyowa hajiya zainab tayi tana zazzaga masifa "wallahi wanan yarinyar da ake Shirin aurawa kabiru an hadashi da aiki,Domin batada tarbiyya ko kadan tun suna yara nasan halin deejahmah Bata laifi komi tayi daidaine a wajen rahina,banji Dadi ba ko da can da akace zata auri habibu balle yanzun da lamari ya juya Kan kabiru mutumin kirki" STORY CONTINUES BELOW Tsaki taja ta juya ga Fatima wadda ke durkushe ko motsin kirki takasayi,zuciyarta cike da fargabar abinda zai biyo baya,muryar ummu ce tadawo da ita daga tunanin data fada "Makulli zan baki kije wancen sashin na can cikin gida ki bude ki gyaramun shi,tun shigowarmu nasa aka kaimun kayana can,Amma kafin kije kiyi aikin ki tabbatar kinje kinyi wanka kin cire wadanan kayan na jikinki kin wanke su dan bana kaunar datti ko kadan bazakije gyaran gidaba kema jikinki kaca kaca"...ta karashe maganar da kafe Fatima da idanuwa.... "Ranki ya dade kayana guda daya ne idan na cire wanan Babu Wanda zan canja sai Kuma kayan gida da nake dashi" Juyowa ummu tayi ta dubi Maryam dake durkushe a gefe "ke jaki kitchen kisamu lantana kice nice nace taje wajen jakadiyya tace a Bata Kaya irin na jikin faty ki kawomin yanzun Nan" "Toh ranki ya dade"..... Cikin mintuna da Basu wuce goma ba saiga Maryam ta shigo hannunta dauke da Kaya jajaye irin wadanda kuyangin gidan ke sawa ta shigo ta durkusa ta mikawa ummu "Mika Mata su" Hannun Fatima na rawa tasa ta amshi kayan,sanan hajiya zainab ta Miko Mata makulli ta Mike da sauri ta fice..... ********** Kuka sosai deejahmah keyi a jikin mahaifiyarta Tana fadin "kamar ni mama a wulakantani gaban baiwa kuyanga?baiwar ma kaskantacciya cikin sauran bayi?wallahi bazan yardaba sai na dauki fansa a wajen Fatima" Cikin tsananin bacin Rai da tashin hankali hajiya rahina ta ture deejahmah daga jikinta ta Mike Tana huci ta fice a dakin hajiya babba ta rufa Mata baya basu zarce ko inaba sai dakin hajiya karama,.. Koda suka shiga ummu na zaune da mama karama suna taba Yar hirarsu suka shigo dakin Babu ko sallama, Daga tsaye hajiya rahina ta juya baya cike da rashin mutunci tace "nazo inji baasin wulakanta Yar sunnah Akan shegiya" Murmushin kasaita ummu tayi ta dago Kai ta kalli rahina kadan sanan ta girgiza Kai "banyi mamaki ba da Khadija ta shigo Mana daki kerere babu ko sallama ta zuba rashin mutunci Ashe gado tayi a wajen uwarta,shiyasa masu iya magana ke cewa barewa bazatayi gudu ba danta yayi rarrafe yanzun kinzo ramawa yarki ne kenan rahina?to Bismillah"....ummu ta cigaba da kada kafa, Hajiya babba ce a fusace tafara magana "haba zainab wanan abin da kikayi kin dauka abune Mai kyau?a tunaninki bare yafi Dan uwanki ko?baren ma shegiya tsintacciyar mage?ke har kinada bakin wulakanta diyar Yar uwarki a gaban bayi?".... "Dakatamun hajiya,ke matar Dan uwana ce Kuma Dole in mutuntaki saboda haka ki rike bakinki wanan abinda ya shafi Yan uwa ne ki rike matsayin da Allah ya baki"... Takaicine ya lullube hajiya rahina jikinta har kyarma yakeyi ta juyo ga ummu Tana fadin "ai ni dama nasan cewa bakya kaunata baki kaunar abinda na Haifa,wayasani ma ko bakin ciki kikeyi da deejahmah kikai Mata wanan wulakancin a gaban wanan matsiyaciyar yarinyar" "Rahina matsiyaci shine Wanda zai tashi ranan tashin kiyama bashida komi na ladan ubangiji,ke baki Isa ki kalli wani kice Masa matsiyaci ba wallahi,sanan yarki gyara nayi Mata na dauka ta dauki gyaran Ashe wuta taje hasowa to tayi daidai Kuma zan gamu da ita,saboda haka ki bacemun daga gani tunban Bata Miki Rai ba kema Dan niba saarki bace "... Gyara tsayuwa hajiya rahina tayi tana tafa hannu Tana fadin "kome Zakice kice Amma a kiyayarmum yarinya Babu ruwanki"...Tana karasa magana ta fice Tana surfa balai ,hajiya babba juyawa tayi ta bi bayanta cike da takaici.... ******* Deejahmah kuwa ganin tijarar da iyayenta sukayi yasa tasamu sassaucin takaicin da takeji a zuciyarta dikda ta kudiri aniyar Rama abinda akayi Mata a Kan Fatima kota halin Yaya, STORY CONTINUES BELOW Dakin kawayenta ta shiga dukkansu suka bita da kallo,saboda dik Wanda ya kalleta babu tantama sai ya fahimci Tasha kuka, Neman wajen zamanta tayi ta zauna,....teemah dollar ta Dan kalleta cike da tsaigumi tace "haba ranki ya dade,daga tafiya sai Muji shiru?kodai kinfara kukan rabuwa da momy ne Kinga yadda kyawawan idanuwanki suka canja kala?"....takaicine ya lullube deejahmah Jin abinda kawarta ke fada, Shiru tayi Tana girgiza kafa minti minti Tana sauke kwafa daga bakinta sanan ta juyo gefenta ta ruko hannun teemah tafara magana cike da bakin ciki muryarta a dishe"wallahi tallahi saina wulakanta yarinyar Nan saina tabbatar da ta Zama abar kwatance saitayi data sanin shiga Ramin damusa"... Cikin rashin fahimta teemah ke kallon deejahma yayinda ilahirin Yan dakin friends dinsu suka baza kunnuwa Dan Jin kanun labari,....cije lebe deejahmah tayi "Zaki fahimci abinda nake nufi Nan gaba kadan idan na aikata Mata abinda na kudura a zuciyata" Matse hannun deejahmah tayi tanadan girgizata"haba princess bai Dace ki tsaya furta Zaki dauki fansa akan baiwarkiba wadda kikeda yancin sawa a tsireta ma kowa ya huta fadin Zaki dauki fansa tamkar cewa tafi karfinki ne yasa kike wanan ikirarin,ai aiwatar da abinda kikeso a lokacin da kika gadama saboda ita mallakinki ce" Takaici ya Kara rufe deejahmah tamkar ta fashe da kuka,babban bakin cikinta be wuce tunanin abinda Fatima sukayi da yarima ba a dakin da akace ta shiga,....bisa alamu ta rigada ta fahimci Yana son yarinyar soyayya suka makale sunayi kenan?....Nan da Nan fuskarta tayi jajir saboda takaici da bakin ciki.... ********* Gyaran sosai Fatima keyi a bangaren hajiya zainab Wanda yasha Kura saboda dadewa da yayi baa budeshiba,...dakuna uku ne cikin sashin dik Saida tabi ko wani daki tayi gyara na musamman ta shimfida musu zannuwan gado tayi mopping dik inda wata kura ta makale ,sanan ta shiga ko wani toilet ta wankeshi tass suka fita, Har kitchen Saida ta fidda duka wanke wanken sashen ta wankesu Tass ko wanne ta jera shi a mazauninsa, Fadin yadda ta gyara parlorn hajiya zainab Bata lokacine dik uban kurar da dattin ciki Saida ta share tayi goge goge,..wajen drawer din gadonta taga burner da turaren wuta Nan da Nan ta hada ko Ina ya dauki kamshi cikin gidan Wanda tamkar be tabayin dattin da yayiba, Koda ta Gama aikin can barandar bayan dakin hajiya zainab ta nema ta zauna Tana maida numfashi,minti minti takan tsinci kanta cikin faduwar gaba Wanda batasan dalilinta na yin hakanba,har magriba ta risketa a Nan tayi sallar magriba sanan ta rufo gidan ta fito ta nufi sashen cikin gida.... ******** Suna zaune sun idar da sallah suna zazzaune da wasu kannen hajiya karama wadanda sukazo biki daga kasar Sudan ta shigo bakinta dauke da sallama, Ta zube a kasa ta gaida kowa a dakin,sanan ta juya inda hajiya zainab ke zaune tanajan carbi ta tsugunna hade da Mika Mata key din gidan tace cikin sanyin murya "na Gama ranki ya dade" Daga Mata hannu hajiya zainab tayi batare da ta amshi makkulinba Saida ta shafa adduar ta sanan tace "yauwa Fatima ko ki dauki wata daga cikin kuyangar gidan Nan kice nace kuje ki dafamin abinda zanci Dan bazanci abincin gidan Nan ba Kuma nawa nakeso a dafa min".. "Mai zaa dafa Miki ranki ya dade".. "Jeki min couscous da miyar hanta kije friege din gidan Nan ki dauki hanta Dan yau na dawo Babu komi a gidana kuje ki dafamin".. Fatima ta Mike Dan cika umarninta ta juya hajiya zainab ta dakatar da ita "kin ma iya abincin kuwa?karkije kimun shirme " Tsugunnawa Fatima tayi daga inda take sanan tace"na iya ranki ya dade a kitchen nake ai a Nan din " STORY CONTINUES BELOW Daga Mata Kai tayi hade dayi Mata nuni da hannu da taje..... ********* Fridge Fatima taje ta bude ta ciri dik abinda take bukata sanan ta juya ta nufi sashen hajiya inda bilkisu ke Zama, Can ta taddata rakube gefe daya da sauri ta karaso cikin kasa da murya tace "kizo muje wancan sashin na waccen bakuwar tasani inyi girki Amma tacemun in nemi Dan rakiya saboda duhu ya farayi" Mikewa bilkisu tayi tana waige waige sanan tayi kasa da murya tace "jeki zanzo akwai abinda nake saurare a Nan"...batare da Fatima tayi musu ba ta juya tai tafiyarta, Daga can cikin dakin hajiya babba bilkisu ta kasa kunne Tana sauraronsu, "Inhar tayi amfani da wanan ya kwanta da ita to tabbas shida wata mace harabada,sanan babu makawa zata dauki ciki Kinga burinmu ya cika dan wata Fatima ma mantawa da ita zaiyi" "Amma hajiya Naga wanan abun tamkar ruwa beyi kamada magani ba"... "Ehh Mana bazakisan amfaninshiba sai deejahmah Tasha komi ya faru zakice nabaki labari tafiyayya aka kawoshi daga can a balaq garin buzaye nasa akayoshi ga Yar aminiyata Nan shiru a gidan miji Kuma infada Miki anayi tasamu ciki" "Kai hajiya nagode Allah ya saka Miki da alheri banida kamarki a rayuwata wallahi.....burina ya kusan cika kenan yata zata haifawa sarki jikan fari" Dariya Suka kwashe dashi sanan hajiya babba tace "bude drawer dincan kisa shi ciki gobe bayan sungama kamu sai tazo Tasha ta wanke fuska,to harshi tsoronta zai rinkaji" "Hajiya kin tabbatar idan ansaka a drawer din can bawani Abu?" "Babu karki damu Babu me shigomin daki sai bilkisu itama na amince da yarinyar ne don ko shiga shirgin sauran bayin gidan Nan batayi kullum muna tare da ita,itakadai yanzun nake Bari ta shigomin daki Kuma idan ta ganshi zata dauka zam zam ne,...yanzun ki tashi mune fada wajen sarki Dan ya Aiko jakadiyyarsa kiranmi inaji anfada mishi abinda ya faru ne dazun" "Owk".... Jin alamun zasu fito da sauri bilkisu ta koma can cikin parlor inda babu Wanda zaiyi zargin taji wani Abu... Zuciyarta ke tsabanin harbawa sauri da sauri tunanin yadda zatayi takeyi take mafita tazo Mata... A parlor suka taddata a rabe tayi shiru,hajiya babba ta kalleta tadanyi murmushi tace"bilki bakije cikin Yan uwanki ba tunda Babu abinda zakimun?" Cike da ladabi bilkisu ta kakalo yake tadan durkusa "ranki ya dade Ina Nan,nayi gyaran parlor ne nace Bari idan kinfito in tambayeki idan kinada bukatar a kakkabe Miki cikin daki saboda yau Naga gidan ya kacame ko Ina da Dan datti " Jim kadan hajiya babba tayi "kinyi tunani to a kakkabemun daki kafin mudawo idan kingama ki rufemin bedroom din da makulli ki bude waccan drawer din kisa makullin ciki sai kije abinki tunda dare yafarayi" "Toh ranki ya dade" Wani kallo hajiya rahina takewa bilkisu sanan ta rufawa hajiya babba baya suka fice, Kamar jira takeyi ta fada dakin a guje direct drawer ta bude ta shiga waige waigen neman abinda suka ajiye,daga idonta sama tayi ta sauke idonta Akan gorar swan Wanda bashi da maraba da ruwa,jikinta ne ya Kama rawa tunani kala kala ta shigayi sanan daga karshe ta yanke shawarar canja ruwan ciki, Da sauri ta nufi bayi ta bude ta shige ta rufo kofa jikinta sai kyarma yakeyi zufa na zuba a jikinta dakyar ta bude ta antayar da ruwan ciki,ta samu ruwan fanfo ta maida yadda ruwan yake ta goge gorar ruwan ta fice ta ajiye inda ta gani gabanta na tsananin faduwa.... STORY CONTINUES BELOW A gaggauce ta kakkabe ko Ina ta gyera gadon ta rufo kofar yadda aka Bata umarni tayi ta fice,jikinta be bar rawaba tunanin tonuwar asirinta take.... ******* Kwankwasa kofar gidan tayi,da sauri Fatima tazo ta na kici kicin budewa sanin tasan bilkisu ce, Tana bude kofar sukai Ido hudu da yarima wani kallon tuhuma yake binta dashi hade da mamakin abinda ya kawota Nan gidan, Wucewarta tayi ciki ta nufi kitchen batare da tace Masa komiba kirjinta na tsananin bugawa, Ciki ya shigo Yana kwalawa hajiya zainab Kira "ummu"(yadda suke kiranta dashi)shiru yaji ya shiga leka dakunan dik Babu ita Amma komi a gyare, Mamakine ya kasheshi Tana tsaye ganan standing gas Tana juya miyar da takeyi kamshi ya karade ko Ina ya shigo ya tsaya a bayanta,gabanta ya tsananta faduwa saukar hannunsa taji a kafadarta ya juyo da ita Tana facing dinta Yana jifanta da wani irin kallo Wanda ita kanta taji ta kasa aiwatar da komi "bintu shine akayi banza Dani aka wuce aka barni bazaki tarbi mijinki ba ko "Yana Shirin janyota jikinsa taja da baya Tana fadin "Haba yaayah nidai kabari kada hajiya tazo Dan Tana gab da shigowa ta ganmu a Nan " Ta juya ta kashe gas din ta Mika hannunta Tana kokarin Ciro kuloli ya fizgota jikinsa ya rike ta sosai "to tazo Mana bakisan ni Dan ganta bane a wajen ummu?inda zata ganmu ma ba abinda zatace".. Turo baki tayi tana kunkunai hade da ture hannunsa'naji kabari inkwashe abincin Nan sai kace dik abinda zakace" Makale kafada yayi ya sauya murya cike da shagwaba "umm umm naqi" Dariya ta kamayi Masa Dan yadda yayi da muryarsa Dole ne ko waye yayi dariya, Batare da tace komiba ta shiga kwashe abincin fuskarta dauke da murmushi,Yana tsaye a gefenta ya kafeta da Ido yadda take aikin Yana gefenta sai zuciyarsa ke ayyana masa sundace da juna tamkar Miji da Mata, A bangarenta mamakinsa takeyi yadda yakeyin abubuwa tamkar ba Dan sarautaba,mafi yawancin masu mulki akwai kasaita da ji da Kai Amma Banda yariman ta ko dai itace yakewa haka oho a haka ta Gama gwashewa ta dibo kulolin tazo parlor ta jera dik inda tayi Yana biye da ita kamar bindi Tana faman kyalkyala Masa dariya a haka sukazo parlor ya jona tv ya kunna ya koma kujera ya zauna tazo ta bayansa ta durkusa da kanta daidai kunnensa cikin rada tace "yaayah barka a Nan ni zan wuce kafin hajiya tazo"....lumshe idanuwansa yayi Yana Jin wani Abu nayi Masa yawo a jiki yadda takeyi Masa rada a kunne hannunsa yakai daidai fuskarta ya shafa "kina nufin tafiya zakiyi?" Ta bude baki zata amsa aka kwankwasa kofa ....da sauri ta Mike daga durkuson da tayi jikinta har rawa yake Tana adduar Allah yasa dai ba hajiya bace... Tana budewa sukai Ido hudu da bilkisu ta sauke ajiyar zuciya, Kallon kallo suke yo da bilkisu "meye kikemun kallon rashin gaskiya" Murmushi Fatima tayi takai Mata duka a kafada "kema yau kinamun kamada marasa gaskiya"....dariya Suka sa su duka a tare suka shigo da bilkisu,.tsayawa tayi turus Tana kallon yarima da ya hade Rai Yana kallon tv Kallon Fatima tayi da tambaya a fuskarta ,....dage Mata gira tayi sanan ta rada Mata a kunne "tunda bakizo ba shi yazo jiran matarsa"ta kashe Mata ido daya Tana dariyar keta, Tabe baki bilkisu tayi "aikinku kenan kamar chewing gum"...dage Mata kafada Fatima tayi tana dariya kasa kasa Mikewa yarima yayi ya kalli Fatima ta gefe "Bari inje tunda kinsamu Yar Taya Hira dama na dauka ummu Tana Nan ne" Ido ta kifta Masa Tana dariya ya wuce, Waje suka samu suka zauna bilkisu na murmushi tacewa Fatima "wato yanzun kin Kuna bakijin tsoro ko?kin manta ke baiwace kaskantacciya inji su" Dariyar takaici Fatima tayi sanan ta fuskanci bilkisu da kyau tace "a zahiri ni baiwace kaskantacciya ,Amma a badini ni yace cikakkiya Mai yanci,bazasu fahimci hakanba sai Nan gaba kadan zasu fahimci hakan lokacin da deejahmah ta koma baiwa ni nakoma uwargijiyarta" Dariya sosai bilkisu keyi lokacinda sukaji karar zaa bude Kofa da sauri suka saisaita kansu, Hajiya zainab ce hannunta dauke da sadik da sauri Fatima ta Mike ta amsheshi Tana fadin "barka da zuwa hajiya" Kallon yadda Fatima ta gyara gidan hajiya zainab keyi Tana murmushi sanan ta nisa tace"Kar inkarajin kin kirani da hajiya ko ranki ya dade ki kirani da yadda kowa ke kirana ummu". Sunkuyar da Kai Fatima tayi ta juya taje kwantar da sadik,minti kadan ta fito ta tadda hajiya zainab ta baje a parlor bilkisu ta Mike Dan su wuce ta kallesu ta gefe "dare yayi bazaku iyabin hanyar Nan ku kadaiba Nima kabiru nasa ya dakko mota ya kawoni Kuma Koda zai dawo sai anjima Dan akwai maganar da zanyi dashi,yanzun dai kusamin abinci kuyi zamanku anan da sassafe kwa koma cen din" Kallon kallo bilkisu sukeyi da Fatima sumaiwa juna murmushi sanan Fatima ta tsugunna tafara serving ummu da abinci.... ******** Wajen Sha daya na dare yarima ya shigo sashen hajiya zainab Yana sanye da jallabiya don har yayi Shirin bacci takirasa tanason magana dashi... Suna zaune a parlor take shaida Masa Taji dik abinda ya faru tun daga farko har karshe har maganar aurensa da Fatima....shine ma yasa takeson magana dashi... Ajiyar zuciya ta sauke ta sanan ta dubesa ta Soma magana kasa kasa Dan bataso su Fatima su jiyo "a yadda Naga yarinyar tanada natsuwa ga ibadah sanan jikina ya bani aurenku alheri ne Amma naji Mai martaba yace Wai sai ansamu lokaci kafin ayi bikin" "Ehh ummu haka yace".... "Toh ni zanyi karambani Dan zansamu shi Mai martaba mu tattauna Akan ayi auren nan karshen shekara tunda yanzun muna watan biyu ko?" Dadine ya lullube yarima ya shiga faraa yace "ehh ummu da zaayi hakan da zaifi" Ta juyar da Kai fuskarta a daure "insha allahu zan nemi Mai martaba da maganar nasan zai saurareni Allah ya zabi abinda yafi Zama alheri Amma kayi shiru ko yarinyar karka fada Mata" Yarima ya sunkuyar da Kai Dadi na ratsashi "insha allahu".... "Tashi kaje dare yayi"....Dan Dadi dakyar yarima ke taka kafarsa ya fice.... ****** Washe gari da wuri wuri su bilkisu suka gyarawa ummu gidan ummu sukai Mata abin karyawa sukayiwa sadik wanka sanan sukai Mata sallama suka wuce..... Shirye shirye yau kawai akeyi na kamu har masu decorations aka Kira sukayi sukayi decorations a babban filin da aka ware Dan yin shagalin biki suka sassaka kujeru da runfuna sosai wuri ya tsaru tsayawa fadar yadda wurin yayi kyau Bata lokaci ne..... Tunda Fatima ta wayi gari take faduwar gaba haka kawai saidai ta ambaci innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,hasbinallahu wa niimal wakil kawai takeyi..... ******* "Na Gama shirya dik yadda komi zai wakana a wajen Nan ranki ya dade yadda kika zubar da hawaye Akan shegiyar Nan itama saita zubar akanki saitayi danasanin shiga hurumin da ba nataba"cewar Rahane dake tsugunne gaban deejahmah wadda ke faman shiri Mai kwalliya zatayi Mata, Murmushi deejahmah tayi ta jinjina Kai alamar gamsuwa sanan tayi Mata nuni da ta fita.....ta Mike ta fice a dakin.... Shirye shirye kawai akeyi gida ya rikici da Yan uwa da manyan masu kudi wadanda akeji dasu su kawai ke shigowa gidan ana parking hadaddun motoci.... ***** "Fauziyya ki tabbatar kinyi abinda ya Dace yadda na fada Miki kada asamu matsala,Dan inaso ingama da karamar alhakin ne kafin inkoma Kan babbar dikda itama cikin sauki zanyi yadda yadace" Fauziyya tayi murmushi tace"insha allahu innah ai bazata ganeba" "Nasani shiyasa ma nasaki ki tabbatar kin Bata Kuma kinyi yadda nace" "Insha allahu" "Tashi kije faizah tun dazun ta shirya Tana jiranki "..... Yan matan amarya uku ne tare da amarya a wani kebabben daki inda nan ne ake tsarawa amarya kwalliya wadda ta fito da ainihin kyawunta Domin ita kanta deejahmah ba baya ba wajen kyau da diri wadda fatarta ta kasance ita ba faraba ita ba baka ba fatarta tamkar mutanen Etopia ga manyan idanu da take dasu farare tas da yalwar Zara zaran gashin idanuwa sanan ita ba doguwa bace ba gajereba Tana cikin matsakaitan Mata Mai Dan jiki da shape dai dai ita....doguwar Riga ce jikinta kalar golden da kyalli kyalli na net da stones Wanda akai kwalliyar rigar dashi head dinta ma golden colour tayi matukar kyau na kece raini fuskar Nan Tata wadda ta kasance Koda yaushe a daure take yauma hkn ya kasance Amma hakan be tsantsar kyawunta bayyana ba...+ Mayafi aka kawo Mai tsadan gaske aka lulluba Mata akanta wayarta ce ta fara Haske da sauri ta cire pin din wayar Tex ne ya shigo kamar haka ... _HELLO IN D NEXT 5 MINUTE IDAN BAKI FITOBA WALLAHI BAZANJE WAJEN TARON BA WAYE YARONKI DA ZAKI SHANYA...MTSWW_. wani mugun takaicine ya rufeta wato yafi karfin ya kirata a waya ma saidai yayi Mata Tex,kwafa tayi hade da girgiza Kai cike da takaici a cikin ranta tace "zaka shigo hannu Dan rainin hankali"...a zahiri kuwa dago idanuwa tayi cikin mayafinta tana kallon su teemah dollar suna kashe selfi,haushi ne ya lullubeta dakyar ta bude baki cike da takaici tace "Sunita kubar daukar hoton Nan haka mu ake jira a wajen Nan yanzun haka prince ya turomin Tex suna waje" Dariya Sunita ta kamayi "soyayya wanan wani irin ango ne da baya Kira sai Tex" Teemah dollar ta karbe zancen "kedai Bari zee baby wanan amgon da abokanansa Yan Jin Kai ne domin Basu nemanmu sai amaryarsu zamu Rama wajen siyan baki"suka sheke da dariya suka tafa A k'ule deejahma tace"Kun fiye son magana muje da Allah" Saida suka kakkashe hoto da deejahmah sanan suka fito Tana tafe tamkar bazata taka kasaba ga wani uban takalmi me shegen tsini da kyau Wanda tasa Tana takawa a hankali mutum biyu suka tsaya gefe da gefenta daya na biye dasu a baya... A kofar harabar gidan sukaga motoci reras na abokanan ango cike da xumudi Sunita ta bude bakar mota zata shige Ahmad ya juyo da sauri ya dakatar da ita "motar amarya da ango ce wanan".turus tayi ta juya Tana kallon yarima Wanda ya hada girar sama da ta kasa tamkar be taba dariya ba haka ta juya ta wuce, Deejahmah na sako kafa cikin motar kamshi ya baibaye motar tamkar anyi barin turare,..ta gyara zamanta a baya kusa da yarima ta zauna Ahmad ya rufo kofar ya zagayo gefen driver ya zauna ta glass din mota yake kallonsu Yana dariya kasa kasa cike da zolaya yace "ranki ya dade,sarauniya deejamah amaryar sarki Mai jiran gado Allah ya Sanya alheri" Murmushi cike da kasaita Sanan ta amsa cikin sassanyar murya "nagode"... Fuska a daure yarima yace "Ahmad ka manta uwar gida ce?nan gaba kadan amaryarta zata shigo Wanda zataci girma ta barwa amarya Zama sarauniya tunda ita babba ce"...ya waigo ya kashe Mata ido... Takaicine ya lullubeta suna tafe a hankali a mota kusan second talatin tamkar bazatace komiba tsulum yaji tace"sai na so na bada kofa wata zata shigo gidan mijina,Domin mijina nawa ne ni kadai Kuma baayin sarauniyoyi saidai ace sarauniya,mulki da sarauta na ya'yan asaline ba tsintattu ba" Ta wurga Masa harara daidai lokacinda suka karaso wajen mota ta tsaya tayi parking .... ********* Da sauri sauri Fatima tayi wanka ta fito bayan sunkammala ayyukansu dikda ranta da yake abace Amma bazai hanata zuwa wajenba kodan farin cikin yarimanta, STORY CONTINUES BELOW A dakinsu ta tararda bilkisu rike da Kaya Tana jujjuyawa,...turus Fatima tayi tana kallon kayan dake hannun bilkisu Tana juyawa Wanda akanbisu akayi musu sala Sala yankan wulakanci da almakashi, Dafe kirji Fatima tayi zuciyarta na tsananin bugu "innalillahi wa yayi wanan aikin?".. Girgiza Kai bilkisu tayi tace "ninasan zaa Rina Wai an Ari zanin mahaukaciya Domin dazun da safe Naga lokacinda rahane ta shigo dakin Nan Kuma zato zunubi Koda ya kasance gaskiya itace ta shigo tayi mugun aikin Nan" Hankalin Fatima ba karamin tashi yayiba ta karaso inda bilkisu ke zaune hannu rike da Kaya ta amshi kayan ta shiga jujjuyawa Tana girgiza Kai ,take hawayen bakin ciki suka shiga zubowa a idanuwanta tasa gefen dankwalinta ta goge sanan ta dago Kai ta dubi bilkisu wadda ta tsareta da idanuwa... "Wai dik wanan wulakancin da akemun saboda na fito a matsayin shegiya ne?ko ko saboda kaddara ta fadamun Akan habibu shiyasa ake kokarin aga bayana?shin Nina dorawa kaina rayuwar gidan marayu?ko ko ganin da sukamin a can sunada tabbacin nidin shegiya ce?kaddarar data fada mun Nina dorawa kaina?Koko Allah ya Riga ya kaddara cewa mutuwar habibu a hannuna take?menayi haka wani irin balai ne wanan?tsirara akeson a ganni a wajen kenan?"ta rushe da kukan ta kaici tayi jifa da rigar hannunta,hade da durkushewa a wajen Tana kukan bakin ciki... Janyo jiki bilkisu tayi ta matso kusa da ita ta shiga lallashinta"haba Fatima ai ya kamata zuwa yanzun kisaba da dik wani bakin ciki da takaici da ake kunsa Miki saboda kabiru,azabarki ta Karu ne saboda Kabir Yana sonki da badan haka ba da wani Abun zaa raga Miki,nasha fada Miki Akan ki Zama jaruma wanan koke koken dik ba naki bane ya kamata ki Zama idanuwanki sun bushe kema ki fara Rama wasu abubuwan" Dago Kai Fatima tayi tana jinjinawa idanuwanta manne da guntun hawaye "bilkisu lokacinda zan Rama wanan bakin cikin da nake kunsa Yana Nan tafe,lokacinda kowa na gidan Nan zai fara tunanin Anya nice kuwa Yana Nan zuwa Domin nayi alkawarin dik Wanda ya zalunceni ya cutar Dani bazan cuceshiba bazan zalunceshiba Amma inada hanya mafi sauki da kowa sai yaji a jikinsa wallahi zakice na fada Miki ko yanzun ma ba tsayawa zanyi a cigaba da cutar daniba abinda yake tauyeni be wuce kasantuwata a matsayin baiwa ba" Jinjina Kai bilkisu tayi cike da Jin dadin kalaman Fatima tace"Ina goyon bayanki dari bisa dari Yar uwata Allah ya cika Mana burinmu" "Ameen bilki"tasa hannu ta share hawayenta sanan ta Mike taje inda kayanta suke ta Ciro wata doguwar Riga baka Mai adon fulawas farare Yar kanti ce ta say a jikinta da Dan mayafinta Mai girma ta yane jikinta dashi ba karamin kyau tayi ba.... Itadai bilkisu sai bin Fatima da kallo kawai takeyi Tana girgiza Kai hade da guntun murmushi... Uniform dinta bilkisu ta mayar a jikinta ta shirya tsaf suka fito yare suka nufi wajen bikin.... ******** Isowarsu wajen wuri ya kacame anata famar ciye ciye da lashe lashe masu serving mutane abinci sai kaiwa da komowa sukeyi, Idanuwan rahane ne suka sauka Akan Fatima wadda take tsaye can gefe Tana karewa kowa kallo a cikin gidan Tana murmushin takaici, Yarima kuwa tunda ta kallesa sau daya Taji wani mugun kishi ya taso Mata ta Kauda kanta saboda Yar kwallar data ciko a idanuwanta, Durkusawa rahane tayi ta bayan deejahmah inda dama Nan ne wajen tsayuwarta kasancewarta baiwarta ,ta danyi kasa da murya kadan tace"ranki ya dade ga Fatima cen tsaye ta gefen hannun Daman mu a bangaren da aminanki suke" Da sauri deejahma ta dago Ido ta maida dubanta inda rahane ke fada Mata aikuwa direct idanuwanta suka sauka Akan Fatima wadda ke tsaye tamkar balarabiya tayi matukar kyau Wanda ita kanta deejahmar Saida ta shagala da kallonta sanan ta danyi tsaki ta kwanto da kanta cikin izzah tacewa Rahane "kiramun ita"... STORY CONTINUES BELOW Rahane jiki na rawa ta kukkutsa cikin mutane ta karasa wajen da Fatima ke tsaye tasa hannu ta tabata hade da cewa "ke hawainiya Mai rikida?kije uwargijiyarki na kiranki" Murmushi ne ya subucewa Fatima Jin abinda Rahane tace"nakoyi rikida ne kafin lokacin rikidar tawa yayi Domin Nan gaba kadan zan rikida in koma hawainiya kamar yadda kikace"....galala Rahane tayi tana kallon Fatima wadda ta soko wadanan maganganun fuskarta dauke da murmushi, "Muje ko?"ta daga Mata gira daya,jiki a sukwane Rahane tayi gaba Fatima na biye da ita suna kukkusawa cikin mutane,take idon fauziyya ya sauka Akan Fatima wadda take ta Raba Ido tun tuni Tana nemanta dama, Har inda suke zaune Fatima da Rahane sukaje.... Dan durkusawa rahane tayi tace "gata ranki ya dade"... Dago Kai deejahmah tayi ta watsa Mata wani mugun kallo sanan ta bude baki cike da wulakanci da gadara ta Soma magana "waya baki umarnin canja Kaya daga kalar ja zuwa wani kala?....ko kinsamu yancine daga bauta zuwa cikakkiyar ya'" Daurewa Fatima tayi ta danne abinda takejin zuciyarta ta bada amsa da "ya kamata in sabunta kayan jikina ranar bikin iyayen gijina Domin intayasu farin ciki a wanan Rana data kasance ta farin ciki a garesu"... Amon sautin muryar Fatima ne ya sauka a kunnen yarima Wanda ke zaune a wajen kamar mutum mutumi,Jin muryar Fatima ya haddasa Masa faduwar gaba Wanda besan dalilinsa na hakanba,kasa jurewa yayi ya juyo gefen da yakejin wanan satin juyowarsa tayi daidai da dagowar idanuwan Fatima Wanda suka hadu Dana yarima take yaji wani Abu tamkar shocking na yawo cikin jikinsa tozali da kyakkyawar fuskar Fatima ya haifar Masa da hakan,...ajiyar zuciya ya sauke Yana Kare Mata kallo yayinda ita kanta fatimar dakyar ta Tattaro natsuwarta ta kawar da idanuwanta daga cikin nasa, Yan matan amarya dake gefe idanuwansu suna Kan yarima da Fatima da sauri Sunita ta zunguri teemah dollar "Wai Kinga kallon da prince yakewa waccen kyakkyawar yarinyar kuwa?Kuma a gaban deejahmah" Cikin kasa da murya teemah dollar ta Bata amsa "tsohuwar budurwarsa ce wadda take a matsayin baiwa a gidan yanzun haka,ni naji a majiya Mai karfi ma ita zai aura Nan da watanni kadan" Zaro ido Sunita tayi tana jinjina Kai "tabdijan Aiko deejah ta Gama yawo dik ranan da wanan yarinyar ta shigo gidan,Dan daga ganin yadda suke jifan juna da kallon soyayya kinsan Yana sonta" Dariya suka kamayi kasa kasa suna karewa deejahmah kallo wadda ta cika tayi famm tamkar zata fashe... Juyawa Fatima tayi da tafiyar Nan Tata Mai daukan hankali,yarima yabita da kallo hade da lumshe idanuwansa ya saki sassanyar ajiyar zuciya sanan ya juyo da kallonsa ga deejah wadda idanuwanta suka kankance saboda tsantsar kishi "ya kamata ki koyi yadda ake kallon soyayya kodan mijinki saboda gaba"....abinda ya rada Mata a kunne kenan ya koma ya jingina da jikin kujera... Can gefe Fatima ta nemi table ta zauna Tana sauke numfashi minti minti Tana sauke ajiyar zuciya wadda batasan dalilinta nayin hakanba murya tajiyo a gefenta Ana magana da sauri ta waiga cikin masu kawo abincine ya tsaya "ranki ya dade me xaa kawo Miki" Khausar dake tsaye a gefe ta karbe zancen da "waya ce maka bakuwa ce a wajen Nan?baiwa ce ta canja kamanni ta shigo Domin yin basaja saboda haka ba sai ka kawo Mata komiba matsayinka yafi nata a wajen Nan"ta karasa maganar da watsawa Fatima wata uwar harara hade da Jan tsaki tabar wajen....takaicine ya lullube Fatima batare da tace komiba ta cigaba da Zama wajen, Minti kadan fauziyya ta karaso table din Fatima taja kujera ta zauna hade da Mika Mata hannu Tana murmushi "assalamu alaikum" "Waalaikumussalam"Fatima tace hade da maida Mata da nata murmushin sanan tace"sai yanzun nake ganinki?haba faizah nadauka zakizo muzo tare?" STORY CONTINUES BELOW Gyara Zama fauziyya tayi tana fadin "kiyi hakuri banzo wajen Nan da wuri bane wallahi Kuma sakonki shi ya zaunar Dani a gida wallahi " Cike da rashin. Fahimta Fatima tadan kalleta , "Ehh wallahi tsarabace aka kawowa mamanmu daga nijar shine na tsaya diba Miki kilishi da wani turare Dan agadaz Kya rinka shafawa idan kinyi wanka" Dadine ya cika Fatima "Kai Amma nagode wallahi inason kamshi banida yadda zaayine insamu turare inrinka shafawa kodan shiga mutane" Jinjina Kai fauziyya tayi tana kallon kyawun halitta da Allah yayiwa Fatima wani haushine ya turnuketa take taji tamkar ta shaketa,jinjina Kai kawai takeyi Tana kallonta Tana murmushi zuciyarta kawai ke Raya Mata "matukar kika shafa turaren Nan kin Gama yawo yarinya Domin jaba saita fiki mutunci a wajen Wanda kikewa rawan Kai" Dan kallonta Fatima tayi ganin yanayinta dik ya canja yasa tace "faizah kodai bakida lafiya ne yau?" "Mekika gani?" "Yanayinki ne Naga dik ya canja bakida annuri a fuskarki Babu faraa kamar jiya"ta tsareta da idanuwa Tana karantar yanayinta.... Girgiza Kai kawai fauziyya tayi "no bakomi yau hayaniya tasamun ciwon Kai wallahi" "Allah ya sauwake" Daga Mata Kai kawai tayi batare da tace komiba,dik yanayinta ya canja ba kamar jiyanba sanan yau tanayi Mata magana a takaice... Shagali kawai akeyi Yan matan amarya sai cashewa sukeyi yayinda hajiya babba da tawagar kawayenta suke zubar naira suna liki,fitowa dubu da amarya zatayi tai rawa yarima baya fitowa dik abinda sukeyi a zaune yake tamkar an dasashi... Haka akaita shagali wajen Nan Wanda dik inda Fatima tasa kafa fauziyya na biye da ita tanayi Mata basaja .....komai dake faruwa akan idon bilkisu ne tunaninta gabaki daya ya karkata wajen abinda ke hannun Fatima ne a jakar leda.... Baatashi taro ba sai karfe takwas na dare sanan jamaa suka fara watsewa suna tafiya gidajensu yayinda wasu ke shigewa cikin gida ciki kuwa harda baki wadanda dama yau suka sauka a gidan saboda biki.... ******** Hayaniya ce ta kacame sai surutu akeyi ta ko Ina saboda mutane dake cike a gidan ta ko wani bangare cike yake da mutane.... Sashen Yan matan amarya ne ya kacame da hayaniya ko wacce ta fiddo wayarta Tana kallon hotuna da videos din da akayi a wajen suna Hira suna dariya yayinda deejahmah zuciyarta take bakin Kirin Tana gefe a zaune Tana cika Tana batsewa da gudu kawarta tazo gefenta ta dafata Tana nuna Mata video dai dai inda yarima ya kafe Fatima da idanuwa wajen a slow yake tafiya "ranki ya dade kalli wani abu a wajen Nan wanan kawar mijin naki yadda suke jifan juna da wani kallo tamkar masoya" A fusace deejahmah ta juyo ta kalli Mai maganar Wanda dama a cike take famm tace "ba soyayya sukeyi ba Amma zan nuna Mata tayi gangancin hada Ido da idanuwa masu tsada a duniya saina shayar da ita mamaki ,sanan sai ta Zama baiwa a gareni Mai hidimar cikin gida na"...Tana Gama maganar ta fice a fusace dakin yayi tsitttt kowa ya bita da kallo.... Dakin hajiya babba ta shige a Nan ta taradda Fatima ansata aiki bayan ta tube Kaya sai mopping takeyi Tana hada zufa tana Ana kyararta hade da hantararta ai deejahma nayin tozali da Fatima tayi kanta Wanda hakan yayi daidai ta shigowar ummu dakin "Munafuka kin gamo karuwancin kindawo asalinki na baiwa?wallahi dik abinda kikeyi inasane dashi nasan cewa kin mallakeshi ne yasa yake kulaki Amma yafi karfinki" Rirriketa kawar mahaifiyarta tayi tana fadin "lafiya deejah meyafaru?meke tsakaninki da Yar aiki Kuma" Daga gefe hajiya babba ta sakarwa Fatima rankwashi a tsakiyar Kai ta shiga dukanta ta ko Ina Tana fadin "munafukar Allah kin zame Mana karfen kafa wallahi Dole ma ki hada kayanki kibar gidan Nan Dan ke balai ce annoba" A fusace hajiya zainab ta daka tsawa cikin dakin "meye haka kukeyi?Tara Mana mutane kukeso kuyi?Koko so kuke ku fallasawa duniya asirin da yake rufe a kasa kowa yaji?" "Wani asiri Banda Wanda itace tayi sanadiyyar mutuwar Dana daya tilo sanan saboda cin Amana aka dauko shegiya aka kawota cikin gidan Nan Wai ita marainiya bayan munji komi a gari cewa karuwa ce to wallahi saita bar gidan Nan tabar Mana zuriah yau din Nan ba sai gobe ba" Kuka sosai Fatima keyi yayinda hayaniya ta kacame cikin daki Wanda hakan yasa jamaar cikin gidan suka cika bangaren hajiya babba kowa na tofa albarkacin bakinsa,wadanda suka hayi maganar a sama suka shiga yiwa Fatima tofin Allah tsine, Jin hayaniya tayi yawa yasa yarima shigowa cikin gidan a guje yayo sashin hajiya babba Yana shigowa yayi tozali da Fatima Tana famar rizgar kuka,bece komiba yasa hannu yajata yayi waje da ita... A haukace hajiya babba ta Soma surfa balai Tana fadin "kamar yadda kakeson ganin karshena kabiru sai Naga karshenku a cikin gidan Nan daga Kai har ita matsiyaciyar yarinyar wallahi tallahi yau din Nan saita bar gidan Nan Kuma kaida aurenta saidai a kiyama" Yadda take kumfar baki kawai hajiya zainab ke kallo Tana watsa Mata wani irin kallo dakyar ta bude baki cike da takaici tace "Haba hajiya wanan wani irin Abu kikeyi haka kamar karamar yarinya sai a shigo cikin gidan Nan aga da yaran cikinki kike balai saboda waccen haddasanar ta kunno balai ko?to wanan rantse rantse da kikeyi na banza ne Domin Babu abinda zai yuwu a cikin maganar da kike fada,wanan yarinyar da kuka dau Karan Tsana kuka Dora Mata saboda Bata da gata ku kune masu gata Kuna ganin Allah ba zai saka Mata ba?to wallahi Allah zaiyi Mata mummunan sakayya sanan Ina Mai gargadinki Akan ki gaggauta canja tunaninki idan ba hakaba zan shayar dake mamaki"..... Dik jamaar dake wajen shiru akayi tamkar anyi ruwa an dauke sautin muryar ummu kawai ke tashi a wajen,.... Takaicin maganganun ummu ne ya lullube hajiya babba ta zaburo ta tsaya a gabanta Tana fadin "Akan kabiru da wanan tsinanniyar yarinyar kikeson yimun rashin kunya zainabu?kikeso ki nuna mun Isa?me kika Isa kiyi a wajen Nan Koko kece kikeda damar yanke hukunci Akan baiwata kutanga ta" Dariya kawai hajiya zainab keyi Tana tafa hannu Tana kallon hajiya babba ido cikin ido sanan ta nisa tace"zan nuna Miki isata kuwa,Domin Fatima baiwarki ce kuyangarki ce Amma yau cikin bainar jamaa kowa zai shaida cewa na ya'nta ta zuwa cikakkiyar ya'sanan rukonta kacokan zai dawo hannuna Kuma ko kinki ko kinso Dole kibi wanan umarni" "Karya kikeyi zainabu baki isaba wallahi kinyi kadan..... Bata karasa maganaba yarima ya shigo dakin fuskarsa Babu walwala dakyar ya iya bude baki yace "Mai martaba Yana kiran taron gaggawa yanzun a fadarsa".... Yana Gama fadin haka yayi ficewarsa kowa ya bishi da kallo yayinda hajiya zainab ta rufa mishi baya...... Hajiya zainab ita tafara Isa fada bayan yarima,a can ta iske fatima a gaban Mai martaba Tana faman zubar da hawaye tamkar an bude famfo kallo daya tayi mata ta kauda kanta saboda tsananin tausayin yarinyar da ya lullubeta take taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta nemi gefen da Fatima ke zaune ta zauna da kyar ta bude baki tace "ya Isa haka Fatima kiyi Shiru insha allahu komi zaizo karshe Domin wannan cin zali yayi yawa na tabbatar da Mai martaba adalin sarki ne zai duba lamarinki kinji share hawayenki"ta kamo Fatima zuwa jikinta ta shiga goge Mata hawaye,a haka su hajiya babba suka shigo kowa ya hallara cikin fadar...+ Wanan karon sarki ransa yayi mummunan baci a fusace yake sai kaiwa da komowa yakeyi Saida kowa ya Gama zuwa sanan yanjuyo da kakkausar murya ya Soma magana "Kun bani mamaki kun zubarwa kanku da mutunci sanan Kun dauki wuka Kun dabawa cikinku yadda kuka taru waje daya Kuna hayaniya kuka kokarin fallasa asirin cikinku na tabbatar cikin gidan Nan ba zallar Yan uwa bane ciki harda na waje,yau Koda Yan uwane bai kamata kutaru ku nemi zubarwa da wanan masarautar mutunci ba " Gyara Zama ummu tayi ta ce cikeda ladabi "Allah ya huci zuciyar Mai martaba baa kyautaba sharrin shaidan ne" "Babu ruwan shaidan a wanan lamari sai sharrin zuciyoyinku wadanda gabaki daya Babu abinda kukasa a Rai sai son Kai da son zuciyane" Ya juyo inda hajiya babba ke zaune kanta a kasa Tana famar hura hanci "hajiya safiya kinbani mamaki ban taba tunanin ko kowa zaiyi rashin hankali ke zakiyi ba" Da sauri ta dago "ranka ya dade..." "Dakatamun hajiya Babu abinda kowa zaicemun a wajen Nan Domin ba yarda zanyi daku ba tunda kunci amanata kunci amanar marainiyar Allah Kuna neman aikata lahira to na yanke shawarar dauketa daga gidan Nan kafin ku kasheta" .. Jin haka yasa hajiya zainab saurin fadin "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade ai idan aka Bari har aka fita da yarinyar Nan zuwa wani waje Domin rukonta munyi asarar ladan da muke samu ta sanadiyyarta bazan taba bada goyon baya a fita da yarinyar Nan daga gidan nanba"... Harara kawai hajiya babba ke jifan ummu da shi,Jin furucin da tayi, "Yanzun ke zainabu nasan kinada hankali Kuma kin girmi rahina kinsan ya kamata inaso ki fadamun yau abinda ya faru a cikin gidan Nan a gaban kowa Dan banaso daga baya inji wani gutsiri tsoma Yana tashi... Murmushin Jin Dadi hajiya zainab tayi sanan ta gyara Zama murya kasa kasa ta kwashe kaf abinda yafaru Wanda tagani a idanuwanta ta fadawa Mai martaba sanan ta Kare maganarda "dama da Naga haka shine na yanke hukuncin yanta yarinyar ta dawo hannuna da Zama tunda ni dama Allah be bani haihuwar ya mace ba sai in riketa har zuwa lokacinda zaayi aurenta da shi kabirun,...shine nakeso a yanta ta" Ran Mai martaba ba karamin baci yayiba a fusace ya karbe zancen da "ai yarinya ya'ntacciya ce Domin yace kamar kowa tunda baa yaki aka siyota a kasuwar bayi ba balle a kirata da baiwa sanan maganar kikeso a yantata?aike kin Isa ki yanta kowa a gidan Nan Domin inda ke macece da idan na mutu banida da' namiji kece Zaki gaji mulki bayan ni Domin bayan yayana da Allah ya saukarwa kaddarer rashin lafiya ai saini saike sanan ita rahinar saboda haka ni da kaina na ya'nta Fatima na Kuma danka Miki amanarta halak malak harabada nabaki Fatima diyarkice" Juyowa hajiya zainab tayi ta kalli Fatima ta bude hannuwanta ta fada jikinta ta rungumeta Fatima ta fashe da kuka Mai ban tausayi, Mai martaba ya dubi Fatima wadda ke faman kuka yace "ke Fatima daga yau na mallaka Miki kanwata jinina ta Zama mahaifiyarki Niko dama a matsayin ubanki nake Kuma harabada a haka muke har karshen rayuwarmu idan Allah ya nufemu da ganin iyayenki shikenan idan bamu gansuba kina Nan a Yar amanarki kinji?ki share hawayenki inajin kaunarki cikin jinin jikina kamar khaussr da ummul khairi".3 STORY CONTINUES BELOW Tsittt fadar tayi bakajin karar komi sai karar AC da fankar sama dake aiki a hankali..... Murmushi kawai ummu takeyi Tana jinjina Kai "nagode ranka ya dade Allah ya bani ikon rikon wanan Amana da aka bani"... "Ameen"..yarima ya amsa sanan Mai martaba ya shigayi musu nasiha Mai ratsa zukata Akan muhimmancin Amana da rikon maraya Wanda Saida jikin kowa yayi sanyi a wajen Banda hajiya babba da rahina wadanda inda zaasa takadda a zukatansu sai sun Kama da wuta.... Saida ya Gama nasiharsa sanan ya bawa kowa damar yin magana Amma kowa yace bashida abin cewa sanan yasa suka yafi juna gaba dayansu sanan akayi addua aka watse a wajen.... Ummu ce ta ruko hannun Fatima ta fito tare da ita daga fadar wajen goma na dare taron ya tashi.... ******** "Wanan makircin shiryayye ne yanzun na gano inda suka dosa Amma in Allah ya yarda bazasuyi nasara ba,idan zainab tayi nasara wanan karon to tabbas zamu hadu a Wasa na gaba"...cewar hajiya babba dake faman sunturi cikin dakin zuciyarta tamkar ta fashe Dan takaici, Kuka kawai deejahmah takeyi ta kifa kanta jikin mahaifiyarta Wanda Nan da Nan jikinta yayi zafi rau zazzabin Dole ya rufeta, Hannu hajiya rahina taka jikin deejahmah Taji yadda ya dau zafi tamkar wuta ga kuka da deejahmah keyi Wanda hakan ne ya haifar Mata da zazzabin tsabar kuka muryarta har dishewa tayi, Tunda Taji hukuncin da Mai martaba ya yanke tayi jifan bori a tsakar dakin hajiya babba tamkar Mai aljanu ta shiga rera kuka, Dago fuskarta tayi wadda tayi jajir saboda tsananin kuka ga hawaye ya wanke Mata fuska tace cikin dasasshiyar murya "mama da hajiya kuyi wani Abu Akan wanan lamarin,banaso Fatima ta shigo gidana a matsayin kishiya hakan babban ci bayane a wajena" Hajiya babba na tsaye hannayenta goye a bayanta ta sauke gwauron numfashi "ni saina haddasawa zainab da Fatima takaicin da har su mutu bazasu manta ba Domin wanan abun da zainab tayi ta farkar Dani daga gyangyadin da nakeyi da farko na farka Kuma din sainaci uban Yan iska".... "Hajiya yanzun me kike ganin zaayi"hajiya rahina tace cike da kosawa, "Akwai abinda na rigada na amso wanan ruwan wanda a lissafi gobe zatasha ta wanke fuskarta dashi,sanan akwai abinda zansa ayi, Wanda ba sai wani yayi amfani da shi ba, turen aljanu kawai zansa ayiwa shegiya ta haukace tabi bola uban kowa ma ya huta" Ruko kafar hajiya babba tayi tace"ki taimakeni hajiya Kar wanan auren ya yuwu"ta rushe da kuka durkusawa hajiya babba tayi ta zauna ta janyo deejahmah jikinta Tana lallashinta..... Ko wannensu sakawa kawai yakeyi Yana warwarewa yayinda ko wani sashe na cikin gidan Shiru kakeji kowa da gulmarsa cike da cikinsa,haka bayi da kuyangin gidan suka hade kansu suna famar gulma sai kuss kuss ke tashi cikin gidan,dik wata hayaniya da akeyi a cikin gidan biki ranan Babu ita daddare tamkar anyi mutuwa.... ******** Bayan sun shiga sashensu hajiya zainab ta umarci Fatima da taje ta dauko kayanta wadanda tace Mata tanadasu, Babu musu Fatima taje dauko kayanta dik inda ta gifta sai a bita da kallo tamkar wata sabuwar halitta,ita kanta sai takejin kanta wani iri haka ta ciccibo akwatinta tayo gidansu dashi ciki kuwa harda jakar ledar da fauziyya ta Bata ta dawo ... Wani daki Mai dauke da madubi da gado madaidaici da bayi a ciki hajiya zainab tacewa Fatima shine mallakinta Dan dadi Fatima batasan lokacin da ta rungume hajiya zainab Tana kukan farin cikiba"Allah ya bani ikon faranta Miki Rai kamar yadda kike faranta mun,Allah ya bani ikon yi Miki biyayya tamkar uwar data tsugunna ta haifeni nagode Allah ya saka Miki da mafificin alherinsa uwata"....ita kanta hajiya zainab Dan Dadi batasan lokacinda kwallar farin ciki ta taru a idanuwanta ba take kaunar yarinyar ta Kara shiga zuciyarta ta shiga bubbuga Mata baya Tana shafawa a hankali sunkai minti uku a haka kafin hajiya zainab ta zaunar da ita a gefen gado Tana murmushi tace "ke bakisan nauyi garekiba ai saiki yarda umman Taki" STORY CONTINUES BELOW Murmushi Fatima tayi"Kai ummu ya zaayi in yardake bayan banida nauyi" Dariya sosai hajiya zainab keyi lokacinda Taji kwankwasa kofa ta tsagaita ta waigo ta kalli agogo Sha daya saura na dare tace "bintu tashi kije kiga wake buga Mana kofa" "Toh ummu"ta yunkura zata Mike ummu ta dakatar da ita da cewa "ko shiga kiyi wanka dare nayi ki tsaftace jikinki kicire wanan muguwar rigar idan kinfito ki duba waccen drawer akwai sababbin kayan bacci irin na Yan Mata kala kala ki duba ki dauka kisa Ina zuwa Bari inje" Ta fice daidai Ana kwankwasa kofar Tana fadin "waye wanan zai karyamun kofar gida"ta karasa ta sa key ta bude,tayi tozali da yarima tsaye Yana yatsina fuska ta watsa mishi wani kallo "me Kuma ya kawoka gidana daddaren Nan me kazoyi".. Ratsa gefenta yayi ya wuceta Saida ya shiga parlorn yake fadin "wallahi yinwa nakeji tun safe banci komiba".... "Saikace wani jariri dik bayi da kuyangin dake sashenku a rasa Wanda zai dafaa maka abinci sai kazo Nan da tsohon Daren nan?to uban wa zai dafa maka anan din badai niba ko?" Sosa keyarsa ya shigayi Yana dariya kasa kasa "Kai ummu ga Fatima a Nan?" "Au Yar aikinka ce ita?Koko ka aureta ne da zakazo kace tayi maka dahuwar abinci?" "Ummu Wai yau kadai kin canjamun saboda kinsamu Diya kin yaye yaronki?haba ummu nine fa kabiru autan ummu" "Kaidai kasani kaji da gulmarka diyata wanka take saita fito" Ta wuceshi ta shige dakinta,Jim kadan ta fito da Shirin bacci ta zo parlor ta zauna ta dauki remote ta canja Tasha sanan ta kwalawa Fatima Kira... "Bintu"....Jin sunan da ummu ta Kira yayi sauri ya kalleta Domin a iya saninsa shi kadai ke kiranta da hakan,Koda yake ba abin mamaki bane don yaji hk a bakin nata Domin kusan halayyarsu daya.... Fitowa tayi sanye da Wando da Riga na kayan bacci milk colour masu taushi da shegen kyau fuskarta fayau ko Mai Bata shafaba Amma hakan be hanata yin kyau ba, Sarai hancinta ya sanar Mata da kamshin turarensa Amma saita kauda kanta wajen da ummu take ta Dan durkusa cikin ladabi tace"gani ummu" "Wanan fitinannen ne Mai kamar Dan yaye yazo ya fitineni Wai yunwa yakeji shine nace ki dafa Masa ko indomie ne" "Akwai Miya a fridge wadda nayi shekaran jiya nasan batayi komiba Bari a dafa farar taliya".... Mikewa ummu tayi tana zabga hamma "to Bari inshiga ciki idan kin Gama Masa kisa mishi a flask ya tafi Dashi don dare yayi" "Owk".. kawai tace ta wuce ya bita da wani mayen kallo,ummu na kallonsa ta gefen ido ta girgiza Kai Tana murmushi ta shige dakinta.... Kusan minti uku da shigan Fatima kitchen ya kurawa kofar kitchen din Ido ko zata fito shiru tsulum ya Mike ya shigo kitchen din ya tokare hannunsa a kofa Tana fadin "Wai har yanzun baa Gama abicin bane?" Batace masa komiba ta cigaba da aikinta,ya karasa shigowa ciki ya tsaya daf da ita ya tsareta da idanuwa kamar zai cinyeta dik inda ta motsa sai ya kalleta,.. Gajiya yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "malama sarautar ta motsa kenan yau baajin kulani?".. Harararsa tayi ta gefen ido batare da tace komiba ya ko Kai hannu ya rike hannunta ta kwace hannunta tace cike da tsiwa"kaje ka rike hannun matarka cikin mutane ni ka lallabo kazo zaka rikeni kayimun wayau bayan aure zakayi ka barni wayasani ma ka Gama tabani kazo baka aureniba" Da sauri yasa hannu ya toshe bakinta da hannunsa"idan nasakejin wanan kalmar a bakinki saina datse harshenki" Tasa hannu ta cire hannunsa daga bakinta ta turo baki gaba "ni kazo ka Hana mutum bacci kanasani aiki" STORY CONTINUES BELOW Yar dariya yayi hade da gyara tsayuwa "Kuma Dole kiyimun ba Kuma ki bani abincin inba haka ba inje wajen wata tunda na fahimci kishi kikeyi"... Dago Kai tayi tana kallon fuskarsa tana sauraron abinda yace Wanda Nan da Nan ranta ya baci wani kishi ya turnuke ta da kyar ta janye idanuwanta daga fuskarsa Wanda yake jifanta da murmushi,ta kada Kai kawai ta kashe gas ta tsiyaye ruwan taliyar ta wanke Tass ta tsane a kwado ta ciro flask ta zuba Miya daban taliya da ban da Dan karamin flask na ruwan zafi Wanda yaji citta da kayan kamshi ta harhada Masa ta janyo basket ta sasu ciki ta ruko ta wucesa a bakin kofar kitchen ya bita da kallo ya dage kafadarsa sama ya biyota a tsakiyar parlor ta dire Masa ta dago jajayen idanuwanta ta jefesa da wani mugun kallo tace "Allah ya ta shemu lafiya"....Bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ta shige dakinta ko kafin yayi wani yunkuri ta rufo kofar dakin garammmm Kamar wani Wawa haka yake kallon kofar dakin ya Dade tsaye sanan ya dauki basket dinsa ya fice ya rufo musu kofa.... Kwance take Tana juyi wasu hawaye masu dumi suna bin kumatunta saboda takaicin abinda yarima ya fada Mata,Aiko Dole t Rama Domin bazaici bagas ba,tun kafin ayi aure ya fara fada Mata idan Bata kula dashiba kenan yanada Mai kulawa dashi?yasan yanada ita yazo wajenta kenan?to meyasa beje deejahmar ta dafa Masa abincin yaciba yazo wajenta?....da tsaki tayi ta juya ta kifa kanta a pillow takaici ya hana bacci daukanta...."aikuwa zakasha mamakina Domin bazan yarda da hakan ba tun kafin a daura ko?"...Dole in Rama Dan ya kamata Nima kasan darajata kasan abinda zaka rinka fadamun Wanda bazai rinka batamun Rai ba....sai sambatu takeyi ita kadai bacci ya kauracewa idanuwanta sai maganganu takeyi ita kadai saboda tsabar takaicin yarima.... ******** Washe gari da safe bayan ta Gama ayyukanta ta hada musu breakfast itada ummu da sadik tayi Masa wanka ummu tayi wanka tacewa Fatima idan tayi wanka ta sameta cikin gida kasantuwar yau dinner zasuyi don gobe daurin aure ne kawai... Bayan tafiyar ummu Fatima ta fada bayi tayi wanka Mai Rai da lafiya ta fito tazo wajen kayanta ta Ciro wasu Riga da sket na atamfa jajaye da adon yellow yellow a jiki ta ajiye a gefen gado ta wawwaiga Babu kayan kwalliya dakin ta shiga dakin ummu taci Karo da body spray ta fesa sanan ta dauko powder da lip gloss ta fito ta shiga dakinta ta shirya tsaf tai kyau tamkar wata Yar baby har ta daura dankwalinta ta warware tayi parking din gashinta da dankwalinta ta nade ta shafa hodar tasa man baki ta zizara kwallin man da ta shafa a bakinta ya karawa bakinta kyau ya canja kala zuwa pink Wanda dama haka kalar bakinta yake...gyalenta ja medium size tayi rolling dashi Wanda ya tsaya iya kafadarta ta zura flat shoes jajaye ta fito tayi mugun kyau ....ta kukkule ko Ina sanan ta Miki hanyar cikin gidan... Tunda ta doso harabar cikin gidan kallo ya koma kanta wasu maaikatan gidan sun ganeta wasu Basu ganetaba haka take keta jamaa Tana tafe Tana kada makullin hannunta fuskarta a Dan daure haka ta shiga babban parlorn cikin gidan inda dik Yan matan gidan ke zaune suna breakfast ciki kuwa harda Yan matan amarya da amaryar ita kanta...kamshin turarenta da sallamarta yasa kowa juyowa ganin wacece, Deejahmah dake kishingide ta dago kanta suka hada ido da Fatima take ta kauda kanta gefe,ganin haka yasa Fatima karasowa wajensu ta zauna gefen kawar amarya tace cikin zazzakar muryarta "sannunku da hutawa Kun tashi lafiya" "Lafiya kalau"Sunita da farida suka hade baki suka amsa Mata Banda khausar da teemah dollar wadanda ke jifanta da kallon Tsana, Ko a jikin Fatima ta gyara zamanta Tana cigaba da wasa da makullin hannunta ta waiga Sukai arba da rahane,take tayi murmushin mugunta tacewa rahane "kawomin abin karyawa".. Rahane kallon inda deejahmah ke kishingide tayi wadda idanuwanta suke lumshe tamkar me bacci, Shiru rahane batace komiba Fatima ta Kara magana a karo na biyu "ki kawomin abin karyawa Nima don babu abinda naci na fito sauri nakeyi" STORY CONTINUES BELOW Jiki Babu kwari rahane ta Mike Sumi Sumi ta shiga kitchen,Jim kadan sai gata da plate da cokali da cup a hannunta tazo inda flask din suke tasa mata siyayyen dankalin turawa say kwai da ketchup a gefe ta dire Mata a gabanta sanan ta hada Mata tea Mai kauri Rabin Kofi ta mikawa Fatima, Babu kunya Fatima ta amsa ta faracin dankalin a hankali Tana kurbar ruwan tae din Wanda tayi hakan ne Dan kawai ta muzanta rahane ... Ajiyewa tayi a gefenta ta kalli wadanda ke wajen kowa ita yake kallo sanan ta Mike tsaye ta Tana duban rahane da dik abin duniya ya isheta tace "ki kwashe kayan ya isheni haka idan kuma zakici to Bismillah Bari Inga ummu" "Aikin banza Kare da gudun layya,Wai samin yancin bawa yasa kwana daya kacal yake neman yiwa mutane iskanci bayan ba gidan ubansa bane"khausar tace cike da masifa da takaicin Fatima kamar ta shaketa... Bude idanuwa deejahmah tayi "bedace ace idan dabba yanayin Abu ki rinka kulasaba little Domin akwai banbanci tsakanin cikakken mutum da dabba,sanan akwai banbanci tsakanin bawa da Mai yanci,sanan akwai banbanci a tsakanin Dan asali da shege Kinga bedace ki tsaya kina maidawa shegiya martaniba" Har Fatima ta juya batace komiba ta juyo ya dawo ta Dan durkusa daidai kusa da deejahmah da khausar wadanda ke zaune waje daya tace"cikar Zama mutum ne yasa ya aikata dabbancin daya jefashi a cikin danasani Wanda awanni kadan da faruwar hakan yasa wanan cikakkem mutum din ramewa da fada babban tashin hankali,sanan Kuma shi Wanda ake Kira dabban shine akejin shakkar yin kishi dashi Domin a wajen mijinsa cikakken mutum ne kamar kowa,Ina Mai shawartarki da ya kamata ki zauna kiyi nazarin abinda wanan dabban yakeyi ake kaunarsa fiye da cikakken mutum yantacce Dan asali....idan har kin iya dabbancin to tabbas Zaki samu soyuwa a zuciyar mutum daya tamkar da dubu"Tana Gama fadin haka ta Mike tsaye tana faraa Wanda har hakoranta Saida suka bayyana, Cikin azama khausar ta Mike ta daga hannu zata wanke Fatima da Mari da sauri Fatima ta rike hannun khausar tace "kullll da taba kyakkyawar fuskar sarauniyar masarautar barayar Zaki?wanan fuskar tafi karfin Mari a wajenki Domin fuskar matar yayanki ce"ta yarfe hannun khausar kaasa ta juya tai tafiyarta ko waiwaye Babu.... Rike kugu khausar tayi Tana sauke numfashi cike da takaici "yau kadai yarinyar Nan ta canja salo?tabdijan zataci ubanta kuwa Domin wallahi tallahi saita Raina kanta"... Tsabar takaici ya hana deejahmah motsin kirki sai jinjina Kai kawai takeyi maganganun Fatima sunayi Mata yawo a tsakiyar Kai.... Bayan yarima yayi wanka ya shirya ya shigo cikin gida Domin gaida iyayensa,babu kunya ya wuce sashen hajiya babba da sallamarsa Tana zaune suna tattaunawa da mutanen dakinta ya shigo da sallamarsa,a ciki suka amsa Masa Koda ya gaishesu dakyar rahina ta amsa ita kuwa hajiya babba ko kallonsa batayiba ya mike har zai fita ya juyo muryar hajiya rahina Tana fadin "ya kamata kasa a kawowa Deejahmah magani Domin batada isasshiyar lafiya" Da sauri ya juyo ya durkusa Yana fadin "meyasameta?".. "Inaga gajiya ce kasai tasa Mata zazzabi da ciwon Kai jiya daddare" "Owk Bari indubata sai inkira waya akawo Mata magani"..harara ta bishi tashi batare da tace komiba ta saki kwafa ya fice.... ******** Suna zaune a parlor ya fito Yana tafe Yana takama har ya karaso inda suke zaune har zai wuce ya tunada cewar deejahmah batada lafiya ya dawo ta wajensu ta nemi gefe ya tsaya dukkansu suka shiga gaishesa daya bayan daya tanaji Taki bude ido, Kallonta yakeyi kawai yadda idanuwanta ke rufe sanan fuskarta kanta ta Dan fada jiya zuwa yau kadai wannan kadai ya shaida Masa da batada lafiya kamar yadda uwartata ta fada Masa, Ganin Taki bude ido yasashi Dan tsaki kadan yace "deejah ya jikin naki"....Saida yayi magana sanan ta bude jajayen idanuwanta ta sauke akansa Tana yatsina fuska da kyar ta bude baki tace"naji sauki".. STORY CONTINUES BELOW "Allah ya Kara lafiya".... "Ameeen"tace a takaice.... Har ya juya zai tafi ya juyo ya dubeta kadan yace "zaa kawo Miki magani anjima kadan ki tabbatar da kinsha"...yayi wucewarsa... Sashen mahaifiyarsa ya nufa a can ne ya tararda gwaggwaninsa da ummu da Fatima dake gefenta Tana ganinsa ta kauda kanta gefe shima bai lura da itaba ya durkusa har kasa ya shiga gaida iyayen nasa wadanda ke amsa Masa cike da kulawa... Ummu ce tace "kabiru waye zakasa yakaimun diyata Fatima wajen telar ya gwadata dinkin lace na wajen dinnar Dan inaso itama ta shiga anko kamar kowa" "Sai in kaita ai wajen telan inace wajen inda nake Kai su afee ne ake musu dinki" "Ehh Nan ne" "Owk toh ta shirya sai muje "... Kallon Fatima ummu tayi tace Mata "ya kamata kije gida ki shirya kizo ya kaiki ko" Jimm kadan Fatima tayi sanan tace cikin sanyi murya "ummu ni banjin Dadi dama anyimun girma daya Dana afnan idan yaso sket din sai a Kara innci hudu Kinga ba sai munsha wahalar zuwaba ki kirashi kinji" Tunda ta Soma magana yaji wani Abu nayi Masa yawo a sassan jikinsa,cikin dabara ya dago idanuwansa ya sauke akanta.....Aiko idanuwansu suka hade waje dayata wurga Masa harara ta kauda kanta gefe,shi kuwa gogan mutuwar tsugunne yayi Dan tunda yake da Fatima bai taba ganinta da Koda Hoda ba ballantana kwalli da man baki kwalliyar ta amshi fuskarsa,take ya nemi dik wata natsuwa ta jikinsa ya rasa kokari yakeyi ya dago idanuwansa ya Dora Akan nata Amma Koda ya dago batashi takeyi ba juyar da kanta tayi Tana Wasa da sadik dake gefenta.... Dakyar ta yunkura ya Mike yaja kafarsa ya fice a dakin ya nufi sashinsa.... Koda ya shiga dakinsa ya nemi natsuwarsa gabaki daya ya rasa Fatima keyi Masa yawo a kwayar idanuwansa lokaci daya ya nemi natsuwarsa ya rasa babu abinda yake bukata kamar yayi tozali da ita a idanuwansa.... ******** "Ummu Bari inje gida inyi sallah in sake wanka in Dora Mana abinci ko?".. Jinjina Mata Kai ummu tayi tana murmushi,Fatima ta Mike tayiwa jamaar dakin sallama tayi ficewarta A hanyar fita suka hade da fauziyya da afnan sundawo daga cikin gari,dukkansu Saida sukai shock ganin Fatima a haka take hassadar fauziyya ta bayyana karara a fuskarta ta kasa boyewa tace"iyyeee k'awata an fita a kangin bauta gaskiya nayi Miki murna" Ruko hannunta Fatima tayi Tana murmushi "nagode k'awata"....itadai afnan wadda ta gaji murmushi kawai taiwa Fatima ta wuce yayinda fauziyya ta cigaba da jifan Fatima da wani irin kallo Wanda yasa Fatima yin mamakin hakan Amma sai batace komiba.... "Ashe haka kike da kyau?gaskiya kin hadu gashi kinsha kwalliyarki,Allah yasadai kinsa turare Dan cikon kwalliya Saida turare" "Laaa Kinga dazun inata neman turare na mance da Wanda kika bani gara da kika tunamin kuwa Dan anjima idan anyi Shirin dinner shi zan shafa" Takaicine ya lullube fauziyya najin har lokacin Fatima Bata shafa turaren ba saita danne tace "gaskiya ya kamata"... "Bari inje gida inyi sallah inyi wanka,ke inayin wankan ma shi zan shafa turaren aminiya".. "Yauwa gaskiya ki rinkasa turare kafin mamanki ta siya Miki"...fauziyya ta shige gida ta dagawa Fatima hannu... Fatima tayi nisa bilkisu ta biyota Tana kwala Mata Kira cakkk ta tsaya har bilkisu ta karaso "wallahi tun dazun ke nake nema Ina kika shiga ne?".. Dariya bilkisu ta kyalkyale dashi sanan tace "Ina makale Ina kallon dramarku a parlor gaskiya kinyimun daidai kinyi yadda nakeso Ashe kinsan Kan zance kika tsaya da anacin ubanku?" "Malama sun Gama cin ubana watan cin nasu ne ya tsaya Dan dik saina Rama abinda sukamun".. "Yayi daidai ta wajena haka nakesonki"... "Wai meye tsakaninkine da wadancan Yan biyun?Naga daya daga cikinsu Tana shige Miki nifa tsoron mutanen Nan nakeyi " Dafa kafadar bilkisu tayi tana jinjina Kai "karki damu wadanan basuda matsala sunada kirki babu abinda zai faru kinji?Bari inje inyi wanka sharp sharp" Ta kada Mata Kai kawai ta juya cikin gida itama ta wuce, Tana shiga dakinta t shiga cire kayan jikinta ta taciro wadanda zata canja kafin lokacin dinner ta Ciro turarenta ta Dora Kan kayanta ta fada toilet dinta don yin wanka....

0 Comments