IYA RUWA FIILDDA KAI CHAPTER 2

IYA RUWA FIILDDA KAI CHAPTER 2
Yana cikin duniyar tunanin sa bai san lokacin da ya ce da ita "You look cute"ba,kawai sai ta dakata da dariyar ta natsu amma da ragowar murmushi a kan fuskar ta wanda hakan ya saka shi gano cewa abin na yawo a kan ta still. Toh amma menene na dariyar?koh dan ya kira Asma'u da budurwar sa shi yasa take ta mai dariya?but ai Asma'u kyakyawar yarinya ce bata da aibu.shi fah ba sani yayi cewa Asma'u na da saurayi mai siffar ƴan daba ba shi yasa ya fara dulmiyawa but nevertheless zai tsawatar wa baby doctor akan me za ta na yi wa budurwar sa dariya dan haka ya ce+ "In kin gama dariyar ki zo mu tafi yamma na yi kuma yanayin ruwa ne".kaiwa nan ya fara tafiya yayin da ita kuma ta biyo shi a baya suna tafiya yana riƙe da kayan da suka raba ya rage wanda yawan jama'an yau har ya ɗare na jiya dan haka sun ɗau lokaci sama da na jiya. Suna tsaka da tafiyar su ta kurame kawai sai ta kuma sakin dariya sai yi take kamar ta sami abin arziƙi abin harzuƙa shi yayi dan haka ya tsaya ka kalle ta kafin ya mata wata muguwar tsawa. "What the heck are you laughing at huh"?shiru ta yi ta haɗe rai kafin ta ce "Excuse me Dr Zaid Maher baka da right din ɗaga min murya dan na yi dariyar abin da bai fice min a kai na ba laifin waye?kai fah ka faɗa min cewa wannan ballagazar ita ce budurwar ka yarinyar da babu tsari babu tarbiya a tattare da ita kai ka sani haka kuma kana gani da idanun ka bata da tsarin da za'a ce ta kai standard ɗin zama budurwar doctor ba doctorn ma kamar kai mai girman kan tsiya da iyayi,iya nan jijji da kan ka ya dakata ashe?dan haka ni ba laifi na bane dan na yi dariya dan abin na dariya ne mana ta yaya zaka ce da yarinyar nan wai budurwar ka kai tsaye,ai kowa ma dole yayi dariyar wannan abin". Tana isa nan ta yi gaba ta wuce shi shi kuma ya tsaya nazarin kalaman ta dan akwai ƙamshin gaskiya a ciki shi kan shi ya kasa ganewa da tantance dalili ƙwara guda da yasa ya ke jin kamar akwai wani al'amari da ke son faruwa da shi game da yarinyar wato Asma'u kenan but ko ma dai menene he don't think Bilkisu should give that bad impression to Asma'u dan ba dan ita ba da an shafe tarihin sa a doron ƙasa ƙila dan bata san da haka bane shi yasa but zai gyara mata tunanin ta akan Asma'u. Shi kaɗan shi yake wannana analysis ɗin har dai ya kamo ta dan dama ba wani sauri take yi ba har suka shiga taxi suka kai madakatar su babu wanda ya kuma cewa kanzil da suka fito ta riga shi shiga cikin gidan yana maganar zuci ya ƙarasa ciki shima a inda yake cewa "Ƙarfin halin yarinyar nan yawa gare shi ita ce da laifi kuma ita ce da fushi"ya cigaba da tafiyar sa har ya kai masaukin sa inda ya yi wanka ya chanzo zuwa ƙananan kaya zuwa lokacin an kawo mai abinci ya ci ya fita abin shi ko ina zai tafi. Ita kuwa da ta shiga ciki dariya ta tuntsire da dan abin gaskiya ya shammace ta ace mutum da izza da iyayi amma ya ɓige da son wannan fanɗararriyar yarinya kuma yana mafarkin mahaifiyar sa zata lamunci wannan shirmen tasa. Har ta gama cin abinci tana alhinin wannan abin yayin da zulfa'u ke tambayar ta dalili sai ta ɓoye mata saboda yadda suke respecting Dr Zaid ba zai kyautu ta faɗi abin kunyar da ya ke yi ba dan mutuncin sa ne zai zube wanda hakan ba zai kyautu ba sai ta ce da ita wata mata ce ta ke sanar da ita wai akan mijin ta zai ƙara aure ita kuma ji take kamar ta yi hauka dan haka wai baby doctor ta taimaka mata su je gidan su yarinyar ta sanar da su cewa ta gwada mijin kuma ta tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar zamani,kuma a zahirin an yi hakan but sai ta lauya wa zulfa'u instead ta sanar da ita ainihin maganar sai ta chanza, Itama dariyar abin ta yi dan matan su akwai duhun kai haka halayyar su take duk baƙon da ya zo sai an gwada mai ƴar hali.. Chan misalin ƙarfe 5:00pm daidai sai ga tarin yara wai sun zo karatu ciki kuwa har da waɗanda basu zo ba jiya kenan yaran gidan sun sanar da abokan wasan su akwai kayan kwalam dan haka yaran suka zo bayan yaran gidan mai gari sun koya masu karatun da aka koya masu jiya, Murna sosai Bilkisu ta yi dan sun yi bitar karatun jiyan har ma yaran makwabtar sun yi_(abin mamaki dama akwai yara masu ilimi da basira a dokan daji waɗanda da za'a bincika da yawa in aka saka ido a kan su aka tsaya masu wallahi za su zama abin alfahari a ƙasar nan baki ɗaya dan baiwar su ta daban ce wato they are exceptionally genius kan su na ja but due to wasu dalilai irin na rashin gata,rashin abin taimako wato kuɗin kai yara makaranta,rashin lura irin ta iyaye akan ƴaƴan su na da special talent sai a kasa fiddo ƴaƴan nan daga duhun da suke, zamani ne na don kai wani mai shi ko da ya lura da hakan daga wun gifted child ɗin nan ba zai taɓa taimakawa ba sai dai ya kawo na shi ɗan yayi tapping daga wun gifted child ɗin nan in suka gama su maida ɗan ɗan daba ko ɗan ta kife ya rasa tudun dafawa bayan sun moru da shi a ƙarshe ma in suka ga yana son kawo masu cikas sai su nemi su salwantar da rayuwar ɗan,ɗaiɗaiku ake samin na kwarai cikin alumman yanzu saboda son kai da son zuciya yayi yawa Allah dai ya sa mu fi ƙarfin zukatan mu ya yaye mana son kai dan wasu da na su ya rasa su taimaki wani mai buƙata gwara sun yi biyu babu wato na sun ya rasa sannan mai buƙatar ma ya rasa)_ "Yauwa toh yanzu tunda mun gama bitar na jiya zamu ɗora da sabo kuma ina so ku tabbatar da cewa duk a shirye kuke saboda gasae jiya da nace zaku yi ban manta ba ga kyaututtukar ku nan a ajiye muddin kuka lashe zan baku kun amince"? Cikin jin daɗi suka ce "Eh mun amince anti"dariya ta ɗan yi kafin ta masu gyara ta ce "Idan muna nan wato wun karatun islamiya da malama za ku na kura na idan kuma muka bar nan da aunty za ku na kira na ba anti ba dan anti wata kalma ce ta daban a yaren ƴan boko wanda na san kuma kuna son ku ji kuma ku iya yaren ko ba haka bane yaran malama"? Da zumuɗi suka ce "Eh muna so malama"cikin farin ciki suka fara karatun nasu yayin da iyayen ke jin daɗi dan wannan bokayen turai da suka zo masu kamar rahama ne a gare su gashi ƴaƴan su na karatun addinin su har ma da ɗoriyar ta boko ake son yi masu basu da bakin godiya sai dai yi masu addu'ar gamawa da duniya lafiya,kafin jiya a bawɗe suke bautar su dan rashin sanin ƙa'idoji but tun da suka ga yadda baby doctor ta ke komai nata cikin tsari da ilimi sai su ka ga ashe sharar fage sule yi a fannin ibadar su dan haka sun ƙudiri niyar samin ta ta koya masu har da dai sun manyanta dan sun yi ƴa da ita amma ilimi amfani ne da shi tunda shine ginshiƙin rayuwa dan haka sun yarda su sauke girman kai da kishin fitinar da suke fama da shi su zo ta koyar da su dan a ganin su kamar dan ilimin addinin da amaryar su wato zulfa'u ke da shi ya sa mijin su ya fi son ta ba wai dan yana rawar ƙafar ita ɗin amarya bace matar da ta kai watanni takwas ai ta wuci gaban a ce miji na mata rawar kan amarci sai dai wani dalilin daban wanda kuma a zahirin gaskiya hakan ne dan zulfa'u akwai ilimi daidai gwargwado bata dai yi zurfi ba amma da babu gwamma akwai ko da kaɗan ne toh ita duk ta fisu dan tana kiyaye sharuɗɗan addinin ta yadda ya kamata har azumin litinin da alhamis take yi ga shi ta ƙware wun iya girki da tsafta toh dole mai gari ya rinƙa mararin ta gata ƴar gidan masu da shi a ƙauyen kuma ita kaɗai ce mai waya a matan gidan dan tun kafin ta auri mai gari mahaifin ta ya siya mata da shi ta zo dan haka da fari da kishin wayar suka fara ta fita harkar su suka koma kan kayan kallon da ta zo da shi a nan ta buɗe masu wuta shine ta sami sa'ida suka rabu da ita aka zo kan haihuwa zasu fara hayayyaƙo mata ta wanke du tass akan ai ita nata mai kyau ne su da sai da suka kai shekara ɗai ɗai har biyar zuwa shida kafin su haihu ai ita nata ya yi kyau toh a nan ma ta yi nasarar fidda kan ta suka dawo suna cewa wai hala kyawun ta ne yake ruɗin mai gari toh a nan shi da kan sa ya tsawatar masu da uwargidan sa kam ta yi ɗiya da zulfa'u dan kwatakwata ba za ta wuce 20-21 years ba a hakan wai ta tsufa bata yi aure ba dan mahaifin ta ya dage sai ta yi karatun arabic wanda yake haɗe da na boko primary ita dai ta fi bada ƙarfi a na arabic ɗin dan ta san ko ta zurfafa da na bokon ba lallai bame mahaifin ta ya yardar mata da na bokon gaba da primary ɗin ba shi yasa tana sauke Alqur'ani mai gari ya ringa sauran samarin zuwa dan kar ya rasa yarinya mai ilimi a gidan sa ai ko ta yarda aka yi aure,toh bayan duk waɗannan gadajen zaren da suke ta haɗa mata sai dai ta ce da su su zo ta koyar da su irin nata ilimin amma fafur suka ƙi wai bata kai wannan matakin ba ta nemi da ta koyawa ƴaƴan su suka hana sannan ƙananan ƴaƴan ɗakin uwargidan aka saka su a islamiyya wai dan su nuna mata suma ba daƙiƙai ba ne haka suke ta yi har dai Allah ya kawo su baby doctor gidan.. Bayan sun kammala karatun sun kuma yi gasar group 2 sun lashe sai group 3 kafin group 1 kuma duk sun sami kyaututtukar su yadda ya kamata a ƙarshe ta sanar da su akan duk ranakun litinin zuwa juma'a za su na yin karatun boko kuma da yamma a rinƙa ɗorawa da na islamiyya hakan ba ƙaramin farinciki ya dulmiya iyayyen su ba yayin da labari ya kai kunnen mai gari rasa abin cewa yayi sai dai Allah shi mata albarka da yaje ta yi, Shi kuwa uban gayyar ko da ya ji labarin wannan daɗin sauyi na koyawa yaran karatun boko da zata yi sai ya ga why not yayi convincing Asma'ur sa ta zo ta yi joining tunda shi bai taɓa kawowa a ran shi ya koyar da ita ba ko ma ya saka ta a makarabtar bokon ba duk zuwan da yake yi ƙauyen ashe daumi kansa yayi wa wannan dabarar zuwa da baby doctor a da so yayi ya haɗa ta da mutanin ƙauyen ya nuna mata bata da daraja sai dai ya ga yanzu tana da amfani sosai a gare shi he just pray that Asma'u ta amince dan ya ga kamar jinin su bai haɗu da Bilkisu ba.. Cikin dare suna hira tare da zulfa'u akan abin da zasu yi ita da Dr Zaid next week ana haka ɗaya daga cikin yaran ɗakin matar mai gari ta biyu mai suna hafiz ya zo ya yi sallama kamar yadda ymta koyar da su akan kar su na shiga wuri kai tsaye babu sallama kuma in sun yi su bari har sai an basu izini kafin su shiga "aunty likita wai ki zo in ji uncle likita yana ƙofar gida yana jiran ki"da mamaki ta kalli time ta ga past 9pm kuma a ƙofar gida ba ma a cikin gidan ba ko me ya faru. "Bara na je na dawo ba zan daɗe ba". "Toh sai kin dawo likiciya". Fita ta yi ta same shi a ƙofar gidan dan haka sallama ta mai ya amsa sai ta ce mai "Ka kira ni a ƙofar gida da daren nan lafiya ko"? Ɗan shiru ya mata yana jin izza izza ita kuma ganin bai da niyar yin magana sai ta juya ta kama hanyar tafiya dan yau itama nata izzan ya motsa. "Wait"!!! Ya dakatar da ita. Inch ɗaya bata ƙara ba ta dakata ya kuma cewa cikin isa "Ki dawo mana magana nake son yi da ke"!! wani irin juyin isa da mulki ta mai kafin ta ce "Ban ga alamu ba in ka shirya sai ka neme ni ni kuma in ina da lokaci sai in amsa kiran naka"!!daga haka ta wuce cikin gida "What have i just done?alfarma fah nake son nema a wun yarinyar nan,oh gosh thank goodness ban furta ba whatt"???ya ƙarasa yana godiya ga Allah da bai bashi ikon furta mata niyar sa ba da shikenan she will definitely look down on him. Yanke shawarar koyar da Asma'un da kan shi yayi dan yana ganin kamar zata fi amincewa since she respect and value him a lot dan haka ya bari akan gobe a wun outreach zai sanar da ita ƙudirin sa,daga haka ya shige cikin gidan ya kwanta, "Hakan me ya ce da ke ne wai"? Zulfa'u ce ta mata wannan tambayar sai ta bata amsa da cewa "A'a kira aka mai wai ana ta kiran layi na bai shiga shine aka gwada nashi ɗazu a wun aikin nan shiyasa ya kira ni dan sanar da ni kin san ba mu samin damar kira dan babu service a nan"cikin hanzari ta tari numfashin ta ta ce "Inaa likiciya ai muna samin sabis a nan gidan zo in gwada miki"ta ja hannun ta zuwa cikin toilet ɗin ta ta nuna mata gefen da zata sami service ai kuwa kamar abin asiri sai full service cikin ɗoki ta danna kiran umman ta da layin ƙasar waje ya shiga sai dai bata ɗauka ba sai ta kuma kiran layin Bahajjatu ringing biyu ta ɗaga "Apple dama zamu gana da ke a cikin dajin nan"! Dariya suka saka tare daga bisani suka shiga hirar su ta aminai sosai suka daɗe kafin su yi goodnight.. Haka ta rinƙa kiran ƴan gidan su suna gaisawa kamar ba gobe sai goma na dare ta fito ta tarar da zulfa'u tana ta jiran ta dan tana so ta tafi turakar mai gari tana jiran ta zo ta rufe ƙofar ɗakin "Kaii likiciya kin daɗe kamar baki da ranar fitowa toh ni dai zo ki rufe ƙofar zan tafi sai da safe" Dariya maganar ta ta bawa Bilkisu ta ce "Toh amaryar mai gari Allah ya tashe mu lafiya"ta raka ta ta tafi ita kuma ta dawo ta rufe ƙofar ta chanza zuwa kayan barcin ta ta haye gadon ta kunna laptop ɗin ta da tun da suka zo bata taɓa bi ta kai ba shiga fannin movies ta yi ta yi playing wani nollywood movie mai suna If i were the president tsantsar siyasanci da ha'incin gwamnati ne a ciki ta yi nisa a kallon ta ji ana buga ƙofar ɗakin da mamaki ta diro tana ƙoƙarin saka falmarar rigar ta ta ce "Wa nene"? Aka amsa mata cikin haɗa baki "Likita mu ne"da mamaki ta ce "Ku?ku su wa"? A karo na biyu suka kuma ce mata "Su hindatu ne likita"a nan ta gano su wato matan mai gari ne hindatu ita ce uwar gidan sai halima sai karime. Buɗe masu ƙofar ta yi suka shigo suna leƙe leƙe kamar marasa gaskiya. "Ku zauna mana"suka zazzauna a kujerar falon ita ma ta zauna sai suka rasa ta ina zasu fara ita ce dai ta yi initiating maganar ta hamyar cewa "kun yi shiru da fatan dai komai lafiya babu wata matsala"? Suka shiga girgiza mata kai kafin hindatu ta ƙoƙarta ta ce "Likiita dama wata magana ce mai muhimmanci muka zo da ita wadda muka ga zai fi mana sirri in zulfa'u bata nan dan yarinyar nan akwai karaɗi da iyayi". Oh ikon Allah mutanin nan ba shiryuwa zasu yi ba kishi har a gaban baƙo. "Toh ina jin ki maman usee me kuke son in maku"?ta tambaye su tana son maintaining eye contact da su dan ta nuna masu cewa tana tare da su kuma maganae tasu na da muhimmanci a gare ta. Cikin sakin jiki hindatu ta ce "Likita wannan karatun ta arabi,shi muke son a rinƙa koya mana in an gama koyawa yaran mu amma a ɗaki na zaki rinƙa koya mana ta yadda wannan ƴar ba zata sani ba dan Allah ki taimaka mana"matuƙa ta ji mamaki dan haka ta ce "Toh maman usee me ya sa ba za ku so zulfa'u ta sani ba kamar abu marar kyau"? Numfasawa hindatu ta yi kafin ta ce "Ƴar nan kin ga dai tun zuwar wannan yarinya ta rinƙa ƙoƙarin tursasa mana akan addinin mu muka ƙi yanzu da kika zo muka ga tsarin ki sai muka ji ran mu ya biya har ma muka yanke hukuncin tunkarar ki dan ki fara koyar da mu tunda hasken rayuwa ya biyo mu har gida kuma da kunya a ce kina koya mana yarinyar nan tana gani ai sai ta raina mu". Ta ida tana ɗan chanza mood ɗin ta abin ya ɗaurewa baby doctor kai wai dama haka jama'a ke yawo da duhun kai?lallai tafiya mabuɗin ilimi duk dan kishin da bai kai ya kawo ba. "Hmm maman usee kin ga ni dai shawara ɗaya zan baku in fah kun ji nawa,tunda dai baku ji kunyar zuwa neman ilimi ba bana jin ya kamata ku ji kunyar ƴar uwar zaman ku duba da cewa gida ɗaya kuke ko mu jima ko mu daɗe wataran zata sani kuma kunyar da zaku kwasa sai ya fi ta wadda in kuka bari ta san da fara koyon addinin ku tun yanzu in kun ji nawa kawai ku basar ai ba'a girma a neman ilimi"daga nan ta yi shiru dan jiran jin opinion ɗin su. Ɗan shiru suka yi suka rahe murya suna ƙusƙus kafin daga bisani ita mouthpiece ɗin su ta magantu "Toh likita mun ji shawarar ki amma ki mana alfarma ɗaya"ta kalle su ta ce "Ina ji". "Yauwwa so muke ki banu daga yanzu zuwa gobe iwar haka zamu sanar da ke shawarar da muka yanke". Jinjina masu kai ta yi suka miƙe suka mata sai da safe sannan suka tafi,dawowa ciki ta yi tana mamakin wai ita da ta zo health outreach kuma ta ɓige da karantar da ahalin gidan mai gari karatun addini har ma da na bokon da zasu fara, "Ikon Allah komai na da sanadi"ta ce da kanta tana mai kwantawa a kan gadon,ƙarasa kallon ta yi sannan ta kwanta barci. ************ First week ɗin su went successful da orientation phase ɗin kuma they were able to picture out matsalolin yankin wanda mafi akasari wife/husband battery,domestic violence kuma akan mace ne da ƴaƴan ta wato ƙuntatawa abokin zama wanda a nan garin matan aka fi ƙuntatawan da ƴaƴan su kuma ta lura akwai matsalolin mata da ya shafi jikin su sosai wanda har yayi affecting mata da dayawa ciki kuwa har da wata marar lura da damuwa da kanta ta ke faɗawa baby doctor cewa in ta zaga bayangida wasu lolutan ta kan ga kamar mahaifar ta ya tulluƙo amma wasu lokutan bata gani sai kawai ta saka hakan a matsayin haihuwar da ta yi ne watanni shida da suka wuce a nata tunanin ai zai tafi bayan watanni takwas ta ƙi zuwa asibiti bare a duba ta toh wannan issue ɗin duk ya fi damin baby doctor dan haka ta sanar da Dr Zaid ya ce da ita dole asibiti zasu tafi kafin a duba a ga degree ɗin annular detachment of the uterus ɗin in wanda za'a iya replacing ne sai a yi in kuma wanda sai dai a yi surgery ne sai su sanar da family ɗin ta su yi. A fannin su hindatu uwargidan su zulfa'u bayan kwanaki biyu na ɓuya da nunnuƙe sun yi finalising zasu na zuwa tare da ƴaƴan na su ana koya masu tare wanda da fari dariya zulfa'u ta masu sai da baby doctor ta nuna mata rashin dacewar hakan sannan ta daina, Ƴaƴa kam ana samin ƙaruwar su dan har ƴaƴan makota da ke zuwa koyon kararun basu ƙirguwa yayin da baby doctor ta zama tamkar tauraruwa a ƙauyen _koma_ kamar su bauta mata ga ta dai very smallish amma akwai ilimi da fasaha,ganin haka ya sa Dr Zaid yanke hukuncin zuwa tare da ita gidan su Asma'u dan su shawo kan ta ta amince da karatun da za'a na koya mata. Tun ranar da suka rabu baram baram basu kuma yin hirar arziƙi ba sai dai abin da ya shafi aikin su da shi ya kawo su garin dama takan yi mamakin sa na rashin son aiki son jiki ya mai yawa dan ko a wun outreach ɗin ita ke major work ɗin baya son yi kwata kwata bata san cewa aikin shi bane wato punishing ɗin ta a garin ko zata rage girman kan tsiyar da ke ɗawainiya da ita shi kuma bai san kan sa yake cuta ba dan ita kam tsakani da Allah ta ke aikin ta babu gajiya ko rangaji a tattare da ita sai ma ta daɗa daraja da ƙima a idon jama'an ƙauyen dan kaɗan ya rage su fara worshiping ɗin ta saboda ire iren kayayyakin da suke kai mata wasu kaji wasu namar dabbobin su wasu fresh milk wasu girki suke yi na musamman su kawo mata duk wannan budirin a idon Dr Zaid ake yin shi ta tafasa sauke bata taɓa ce da shi ba haka take enjoying goodies ɗin ta ita da ƴan gidan.. ********* _Friday evening_ _4:00pm_ Cikin shigar atamfa hollandaise ɗinkin riga da skirt 8 pieces da ɗaurin Aisha Alhassan wato wanda ake turo shi gaba inkiyar ture ka ga tsiya,da mayafin ta na mutunci haɗe da takalmin spline mai ɗan tudu riƙe da wayar ta a hannu ta fito ƙofar gidan inda ta same shi cikin shigar kaftan lilac colour da hular sa ƙafar sa samye da normal skin takalmi yayi kyau ainun dan abin da ya daɗa fiddo da shi shine baƙar speck ɗin da ya saka sai ya haɗe da jikin sa yayi ras gwanin sha'awa She must say that he looks handsome in his cultural attire dan haka tana tafe ta bashi unexpected pic wanda ya bala'in yin kyau a hoton amma on reaching to him sai ta ɗan haɗe rai irin kar ya rainata ɗin nan. "MashaAllah"ya furtawa kan sa da yayi tozali da ita amma shima ganin ta ɗaure sai ya mazge haka suka kama hanya tinƙis tinƙis sai gidan su Asma'u ma'ullen Mudan. A ƙofar gidan su suka tsaya ya aika yaro da a masu iso babu jimawa aka basu damar shiga Tarbo mai kyau aka masu kasancewar shi ɗin ɗan gida ne sai aka karrama su sosai ko da yayi tambayar Asma'u rasa abin cewa mahaifiyar ta tayi dan tun wuraren ƙarfe uku da rabi rabon ta da ita sai ta buɗe baki zata kauce amma sai suka ji bambamin masifar ta "Wallahi wallahi bilahilazimin ba za'a ci bulus da ni ba ni Asma'u ma'ullen Mudan sai sun san sun ɗebo ruwar tafasa kan su tabɗijam bala'i"...... Kasa kunne suka yi suna sauraron ta sau gashi ta bankaɗo labulen zauren gidan na su ai ko ta ci karo da su Dr Zaid tana ganin su ta antaya a guje wai ta ji kunyar ɗaga muryar da ta yi a gaban su,miƙewa yayi yana kwaɗa mata kira tana cewa "Ɗan birni bani sake haɗa ido da kai sai nan da sati guda tabb da ni za'a yi abin kunya inaa".. Sai rafka gudu take ai ko daidai wani dandamalin kwata ta antaya ciki bata lura ba............Asma'u ki dakata mana kin ga abin da kika janyowa kan ki ko a kan wani silly reason"yana maganar ne yayin da yake ƙoƙarin matso ta ai ko ta tsala wata ihu mai razanarwa wanda yayi sanadiyar firfitowar jama'a har da su baby doctor da je zaune cikin gidan su Asma'u tana mamakin rashin hankali irin na ta..+ Taruwa sosai aka yi a wurin ga shi dai ana son yin dariya amma kowa na tsoro dan kana darawa ta san fuskar ka anjima Mudan na zuwa zai keta maka rashin ɗa'a dan haka kowa gimtse dariyar sa yake yi bugu da ƙari ga bokan turai a wurin sai suka rinƙa mamakin abin da ya haɗa shi da ita amma suka yi gum suka bar wa kan su suka tsaya kallon ikon Allah. Dr Bilkisu da fitowar ta kenan tayi arba da aika aikan da Asma'u ta ma kanta ga Dr Zaid a tsaye a kan ta ga jama'a duk ita ake kallo ai bata san lokacin da ta kece da dariyar da bata san dalilin zuwan sa a dai dai lokacin ba sai yi take yi har da ƙwalla. Mahaifiyar Asma'u da ke gefe tana tir da halin ɗiyar ta ta dan irin kunyar da ta ji baya misaltuwa shiru ta yi tana kallon Asma'un yayin da Dr Bilkisu ke ta dariya babu ji babu gani dan haka cikin mugun ɓacin rai da fusata ya daka mata tsawa cikin turanci dan kar a san me yake nufi ya ce "For crying out loud Bilkisu will you stop laughing some one is here crying for her life and you are standing there laughing don't you have human sympathy"? Ya ƙarasa yana mai daka mata tsawa kamar ɗiyar gaban shi. Sai a sannan ta ankare da ɓaranɓaramar da ta yi sai ta ji babu daɗi ko ba komai mahaifiyar yarinyar na wurin kuma ba zata ji daɗi ba dan haka sai ta gimtse dariyar ta ta matsa kusa da su daidai kan Asma'u ta miƙe mata hannu sai dai atafau Asma'u ta ƙi miƙa mata nata hannun wai ita sai dai ɗan birni ya bar wurin shi kuma tsoron matsawa yake gudun kar baby doctor ta wuntsila ta cikin kwatan bayan ta ɗago ta since he knew that ba su cikin good terms. Ganin bata da niyar miƙo hannun sai baby doctor ta gane cewa kunyar jama'a take ji ciki kuwa har da shi saurayin ma'ullen Mudan ɗin wato Dr Zaid sai ta juya ta ce da shi "Please she needs privacy"!! A ɗage ya kaklle ta dan ya san ba tsakani da Allah zata taimake ta ba sai ya girgiza kai alamun ba zai matsa ba. "Are you for real?huh?don't you see that your saviour is sinking in this dirty pit"?kallon ta yayi yana son sanin shin tsakani da Allah ta ke son taimakon Asma'un ko dai ganin ido ne sai dai bai hango komai ba dan bata bashi wannan space ɗin ba so he have no any other option but to give them space... Yana ba da baya Asma'u ta miƙa hannun ta da taimakon baby doctor ta fito daga cikin kwatar duk kayan ta ya ɓaci dan har ƙuƙurjewa ta yi a hannun ta haka ta fito fuskar nan tam cike da bala'i ta hankaɗa masu kallon banza ta ce "Munafukai algungumai annamimai toh ƙwalelen ku ban mutu ba kuma ban kasara ba ku jira ni anjima sai mun zo dukkan ku zaku gane munafurci bai maku rana ba".. Ta ida tana ɓalla masu harara kamar zata zazzago manyan idanun ta haka dai ta lallaɓa suka koma cikin gidan su yayin da su Dr Zaid da mahaifiyar ta suka biyo su a baya bayan ƴar tazarar da suka ma juna dan ce mai tayi ya juya zuwa direction ɗin da aka fiddo ta har su shige ciki kafin ya biyo su hakan ya yi. Da zuwan su direct cikin ɗakin su ta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikin ta dan haka Bilkisu bata bi bayan ta ba ta zauna a tabarmar tana mamakin halin Asma'u ga shi dai a zahiri tsayayyiyar yarinya ce mai kyau amma abaɗini babu halin kirki a ce an fiddo ki daga kwata amma babu kunya kika tsaya fetsa rashin mutunci Allah ya kyauta. Bayan kamar mintuna goma suna zaune ana ta hira tsakanin Dr Zaid da mahaifiyar Asma'u ita dai nata ido sai complains ta ke ta mai a kan Asma'un a nan ta ke sanar da shi abin da ke gudana tsakanin ta da Mudan toh a nan baby doctor ta daɗa kashe kunne dan jin ta bakin mahaifiyar Asma'un ai ko ta sami labarai da kyau har ta tabbbatar cewa eh lallai Asma'u akwai hankali da wayo duk rashin jin na ta akwai mutuncin ta tare da ita dan dama wai shi Mudan ɗin ya daɗe yana maganar a kawo kuɗin aure amma yayyen ta sun ƙi kuma duk iskancin su shi kan sa baya taɓa ta dan yana riƙe mata gyale sai sun yi sati biyu basu haɗu ba ta ɗau gaba da shi kenan kuma kaf gidan su sai sun san Mudan ya taɓa mata gyale kuma ta shaida cewa sai ta ɗau sati biyu kafin su shirya sai dai a ji ta kawai dan ta saba ire iren maganganun but her momma is very conscious of her act a kuum in zata dawo gidan cikin dare sai ta mata full inspection ta duba jikin ta sosai sannan take samin kwanciyar hankali. Shiru Dr Zaid Maher yayi dama shi son maso wani yake yi bai sani ba ashe saurayi gare ta bai sani ba?toh shi yaya zai yi da son ta da yake ji da shi?inaa dole ma kawai shi Mudan ɗin ya yafe mai Asma'u dan da shi ta dace ba Mudan ba da me Mudan ɗin zai raine ta?da talauci ko jahilci?no way he have to stop their relationship.. Ganin ya shiga state of shock sai baby doctor ta ɗan gyara murya ta ce da mahaifiyar Asma'un "Uhmm mama dama wata shawara muka zo da ita wacce in har zaki bamu haɗin kai toh mun miki alƙawarin taimakon Asma'u kuma mu raba ta da shi wannan Mudan ɗin da ba kya so har abada muddin ta hau kan abin da muke son ɗora ta akai toh ba za ta kuma yarda da Mudan ɗin nan ba da fatan za ki mana kyakyawar fahimta mama"?jin maganganun ta cikin hikima sai ya sa mahaifiyar Asma'u amincewa da abin da suka zo da shi har da ma dai bata ji ba but ta sami relief at least ɗiyar ta za ta rabu da wannan gallababben yaro sai ta ce "Ƴa ta ina jin ki menene kike son ɗora Asma'un a kai"daɗi sosai baby doctor ta ji dan haka sai ta ce "Kin ga akwai karatun da na ke koyarwa a chan gidan mai gari karatun biyu ne na addini da na zamani kuma duk yaran gidan har da na makwaftan gidan na halartar karatun kuma har yanzu ana kan taruwa a gidan sai na ke ga in har Asma'u za ta na zuwa wannan karatun toh lallai ba zata na samin lokacin sauraran Mudan ba tunda za ta rinƙa bitar karatun ta haka zata so ta sami kyautar da za'a na ba ta kullum kenan wannan karatun zai ɗauke mata hankali tunda kin ga yau da gobe sai Allah tun ana kiyayewa wataran Allah ya kare wani mummunar abin na iya faruwa tsakanin su kuma ba dole ne ta faɗa ba kin ga tun da an gano abin sai a fara kare shi daga faruwa ko ba haka ba mama"?jijina kai ta yi cikin gamsuwa ko ba komai ƴar ta zata sami ingantacciyar rayuwa ko da kaɗan ne dan haka ta ce "Na yarda ƴa ta shawarar ki ya ba da ma'ana sosai kuma na yarda da shi ko ta amince ko bata amince ba dole in nuna mata iko na na uwar da ta haife ta"daɗi na ya kama Bilkisu dan ita ma yanzu ta fara tausayawa Asma'u duba da yadda take taka tsantsan da rayuwar ta ba dan wauwtar da ta mata yawa ba toh lallai in an natsar da ita zata yi hankali nan abin ne ya mata yawa ga jahilci ga zaman ƙauye babu wayewar kai ga taɓara babu kwaɓo but apart from that yarinyar zata shigo da kyau dan tana da wayo "Shikenan mama na ji daɗi kuma zan fi jin daɗi in Asma'u ta amince wanda na san shi kan sa Dr zai yi farincikin haka ko ba haka ba ne Dr Zaid"? Ta ida tana juyawa gare shi sai ta ga kamar baya tare da su tun da suka fara maganar jin su kawai yake ba wai dan yana fahimtar su ba dan haka ta daɗa ɗaga murya ta ce "Right"? a firgice ya ce "Ye...ee...sss yeeee.... sss"sai ya kuma cewa "Yes yes"abin sai ya bata mamaki toh dama ina hankalin shi ya tafi tana nan tana mai yaƙin sanyin idaniyar sa shi kuma yana wani tunanin dan haka ta ce da shi "Are you okey"?saurin girgiza mata kai yayi kafin ya miƙe tsaye ya ce da ita "Let's get going is getting late"da mamaki ta tashi tsaye ta ce da shi "Me kuma ya faru ba mu fah gama abin da ya kawo mu ɗin ba kuma kake cewa mu tafi"!!! "I said let's go"ya ida cikin nuna halin ya fara gajiya da conversation ɗin. Ƙala ba ta ce da shi ba ta ce da mahaifiyar Asma'u "Toh mama za mu tafi zuwa goben ma ta na iya fara zuwa karatun in ya so shi likitan sai ya rinƙa rako ta gida ba ki da matsala da wannan"murmushin gamsuwa ta yi kafin ta ce "Nagode Allah ya maku albarka ya kare mana ku wannan irin ƙoƙari da kuka min kuka mana a wannan ƙauye na mi Allah ne kaɗai zai baku lada shi kaɗai zai biya ku"ɗan taƙaitaccen murmushi baby doctor ta yi ta ce "Mun gode mama bara mu tafi dare na yi" "Toh Allah ya kuyaye hanya ga shi nan ta ƙi fitowa tabbatacciyan wai kunya take ji"ɗan darawa ta yi ta ce "Hmm mama bara mu tafi"daga haka suka yi sallama shi dai bai ce komai ba har suka yi nisa kafin baby doctor ta dakata ta ce "Wait"sai shima ya tsaya ya kalle ta bai ce komai ba gyara tsayuwa ta yi ta fuskance shi ta ce "Wai tunanin abin da aka sanar da kai kake yi"?shiru yayi bai ce komai ba sai ta ce "Toh ai ba abin mamaki ba ne dan ka ji cewa ta na da saurayi you shouldn't be surprise"ta cigaba da tafiyar ta sai ya ce da ita cikin sanyin murya "Dama kin san da labarin ne"?dakatawa ta yi tana jin wani iri kafin ta ce "Yes i know"!!sai ya ji mamaki kafin ya ce "Tun yaushe"?kasa bashi amsa ta yi dan ya fara bata tausayi dan kuwa ya zurma a son yarinyar da yawa though is something else not pure love but kamar yana wahala.. "tun ranar da na fara ganin ta a wurin outreach ɗin nan"!! daga haka ta yi shiru tana sauraron sa sai dai bai ce komai ba ya cigaba da tafiya itama bin sa ta yi a bayan... ******************* Bayan dawowar su gida sun yi abin da ta dace na yau da kullum wato koyar da karatun da take ma yaran da iyayen su ta basu assignment ɗin su as usual ta kwanta saman ɗaya kujerar falon yayin da zulfa'u ke zaune a ƙasa tana gyara zogale na dambun da take son yi washegari da rana kasancewar ita ce da girki jifa jifa suna hira Lokaci zuwa lokaci takan tuna scenario ɗin ɗazu sai ta yi dariya ita kaɗai countless time zulfa'u na tambayar ta amma sai ta ce babu komai karshe dai shiga toilet ɗin zulfa'u ta yi ta danna wa Bahajjatu kira ringing biyu ta ɗaga. "Assalamu alaikum baƙin ƙauyen koma"dariya suka saka kafin ta amsa da "Wa'alaikumul salam matar mu". Dariyar suka ƙara sakawa dan duk lokacin da zata yi shu'umancin ta toh da shirme suka fara gaisuwar. "Halan me ya faru ne na ga har goman dare ta yi amma kika danna min kira" "Ke dai bari wata labari na kawo maki"gyara kwanciya Bahajjatu ta yi ta ce "Haba da gaske?toh faɗa min ina jin ki"sai da baby doctor ta dara kafin ta ce "Halan Baha wai wacece budurwar yayan ki"? Da mamaki ta ce "Budurwar yaya na?wanne a ciki"? Cikin gatse ta ce "Bilal"! Doguwar tsaƙi Baha ta ja ta ce "Ban son wulaƙancin Beelove wani yayan na wa kike nufi"? Itama tsaƙin ta yi ta ce "Toh shikenan in kin shirya jin ko wanene sai ki kira ni"cikin hanzari ta dakatar da ita ta ce "Tsaya tsaya tsaya,kaii Beelove wai menene na wani ɗaukar zafi?babban yaya kike nufi"? Scoff ta yi ta ce "Toh in ba shi ba dama tare da wa nake"? "Goodness toh yi haƙuri,babban yaya ai bai da budurwa sai ko in a chan ya samo mana new sister in-law". Abin dariya sosai ya ba ma Bilkisu sai ta ce "Ai ko ya samo maku sabuwar sister in-law apple"ta ida tana me kecewa da dariya Shiru Bahajjatu ta yi kafin ta ce "Jokes apart Beelove da gaske yaya ya samo budurwa"? "Hmm Baha kenan na taɓa kawo maki hirar wannan izgilallen yayan na ki in ban da yau"? Ta ce"a'a". "Toh wallahi am serious ya samo wata yarinya kyakyawa mai kyawun kallo sai dai ba natsuwa"! Miƙewa ta yi daga kan gadon ta diro ƙasa ta ce "Mene?budurwa a ƙauyen nan?impossible"? "Hmm Baha kenan wallahi da gaske na ke"a nan ta kwashe duk abin da ya ke ta faruwa tun zuwan su har ma da tarihin yarinyar ta sanar da ita me Baha zata yi in banda Allah ya raba mana jaha,sai nanata shi take yi kamar ba za ta daina ba "Allah ya tsare uhuhm shi kuma yaya haka ya ke son tozarta mu ya daɗe bai yi aure ba sannan ya ce wannan zai ɗauko?toh ba gidan Dr Maher ba sai dai a chan ƙauyen"? "Ha'an toh what if in Allah yayi matar sa ce fah?what can you do"? Da sauri ta ce da ita "Tofar da yawu tun kafin abin ya zama gaske"suka dara kafin daga bisani ta sallame ta ta kira umman ta a waya. Ba ta ɗauka ba sai ta kashe sannan ta kuma kiran ta "Assalamu alaikum umma" "Wa'alaikumul salam baby ya kike ya garin"? "Lafiya ƙalau umma ya na ku"? Sai ta yi shiru alamun tana jin nauyin ta sai ta ɗan yi murmushi kafin ta ce "Common umma am serious ya London ɗin"? A nan ta sani relieve sai ta ce "Lafiya lau baby ungo ku gaisa da Ammin ku"ta miƙawa Hajiya Madina wayar cikin raha ta ce "Baƙin Yola ya kuke"?itama da fara'a ta ce "Lafiya ƙalau Ammi" "Ina my boy ya ke ban ji kun kira tare ba" "Ammi yana ɗakin shi maybe yayi barci nima barcin zan yi" "Noo i need to speak with him akwai muhimman magana da nake son yi da shi please call him".shiru ta yi ta rasa ta yaya zata fara kiran shi zuwa ɗakin mace kuma har cikin privacy ɗin ta sai ta ce "Ammi i can't"!! Cikin damuwa ta ce "But why baby?koh ya ɓata miki rai ne"she was sounding emotional already dan haka cikin sauri ta ce "No Ammi"a nan ta sanar da ita dalili sai ta ce "Alright na fahimta yanzu dai zan sanar da ke saƙobn in kun haɗu sai ki sanar da shi" "Okey Ammi" "Kina ji na,in kun haɗu ki ce da shi na ce amanar nan da na bari mai kar yayi wasa da ni ya riƙe da kyau dan in ya bari na san yayi wasa da amanar toh har abada amanar ta suɓuce mai kenan kuma ba da wasa nake ba". Cikin ɗimuwa da zancen dan she was very serious while saying it sai ta ce "Ammi why me?me yasa ni zan yi conveying mai wannan saƙon"? dariyar manya ta yi ta ce "Bilkisu ki sanar da shi jakan dan le kaɗai gare ni a garin da zan iya aika zuwa wun My boy ba tare da na sami matsala ba dan haka ki sanar da shi shi zai gane me nake nufi"daga haka ta ce "Alright Ammi zan faɗa mai ki gaida mana su Abba" "Za su ji baby and don't forget to take care of yourself humm" "Yes Ammi i will" Suka yi sallama ta kashe wayar tana mamakin wannan saƙo da aka bata, Fitowa ta yi ta ga zulfa'u ta daɗe da yin barci dan haka itama ta kwanta ta yi addu'ar barci ta rufe jiki sai barci.. A fannin su Asma'u kuwa ashe laɓe ta yi ma su Dr Zaid Maher tana sauraron duk wasu kalaman su tana jijjiga kai suna tafiya ta fito tsakar gidan da ɗaurin ƙirji ta saka kuka tana ta ja kamar jiniya mahaifiyar ta dai shiru ta mata tana kallon ta tana jiran ta gama darun ta ta kuma assasa mata nata ƙudirin dan haka ta gama birgiman ta tana surutan ta. "Kee Asma'u ji ni nan wallahi wallahi kin ji na rantse maki babu makawa babu kaffara sai kin fara halartar karatun nan na rantse maki ba ki isa ki take doka ta ba ni na haife ki ba ke ba.. Daga nan tayi shigewar ta ta bar ta tsaye nan tana ta birgima.. ************** Washegari wanda ya kasance asabar wuraren ƙarfe 9 na safe suka shirya zasu tafi wurin outreach sun yi sallama da jama'an gidan sun fito suka shiga taxi a ciki ta fara sanar da shi saƙon mahaifiyar sa kallon ta yayi sai ya mata shiru kawai itama sai bata kuma cewa komai ba har suka iso.. Da zuwan su babu ɓata lokaci suka fara da masu rashin lafiya suna ba su magungunan har dai ƙarfe 2 ya kai suka rufe session ɗin ranar suka dawo gida. Abin mamaki sai ga Asma'u da mahaifiyar ta sun zo wai an kawo ta koyon karatu dan haka babu tsangwama bare hantara baby doctor ta yi welcoming ɗin ta faram faram. Mahaifiyar ta ta tafi ta bar ta ita kuma ta zauna nesa da yaran,ba'a takura mata ba ana karatun hankalin ta na wani wajen sai da aka gama sannan baby doctor ta ja ta gefe ta fara mata nasiha.. "Asma'u kina ganin wani za ki cutar in kika ƙi mayar da hankalin ki a karatun nan?babu fah wanda za ki zalunta sama da kanki,sarai kin san da a ce mu ma irin halin ki muke yi toh ba mu isa mu zo nan muna karantar da mutanin garin ku akan abin da zai taimake su ba babu yadda za'a yi mu zo nan mu tsaya har a saurare mu kin ga duk hakan ilimin mu ne ya janyo mana hakan ke ma ba za ki so ganin kan ki haka ba Asma'u"? A yanayin yadda ta yi maganar sai ya sa Asma'u ta ji jikin ta yayi sanyi dama chan tana da hankalin ta kawai dai rashin samin kyakyawar foundation ne ya sa ta bi ta taɓarɓare. "Ina so mana amma kun ga Mudan baya so dan ya ce ƴan birnin nan cutar da mutani suke yi kuma karatun boko ai dan a sami abin dogaro ne kuma ya ce shi zai tsare min komai ba sai na yi wani kartun zamani ba na je na koyo nasaranci shi ya sa ban yarda da son karatun ba tun farko"! tirkashi lallai wannan Mudan ɗin azzalumi ne wato shi bai yi itama kar ta yi Allah ya raba mu da mugunta,cewar baby doctor a zuciyar ta "Amma ke kina son yin karatun"? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce "Ai ko ina so Mudan baya so kuma in kuka tafi ai shikenan ba cigaba zan yi ba kin ga ai bai da wani amfani"ta yi shiru daga yadda ta yi maganar mutum zai gane cewa tana da zeal ɗin yin karatun amma hindrance na Mudan ya sa ta ke withdrawing.. "Hmm Asma'u kenan ai sai dai in baki ba da haɗin kai ba amma muddin kika amince ni na maki alƙawarin saka ki a makaramtar birni chan cikin Yola ki yi karatu mai zurfi har inda ran ki ke so dan kema ki zo nan ki faɗakar da mutani su ƙaru wannan alƙawari ne daga gare ni kin yarda"?? Kamar bazata ce komai ba sai ta ce "Na yarda amma ina tsoron Mudan kar ya cutar da ku"ɗan dariya baby doctor ta yi kafin ta ce "In dai Mudan ne babu abin da ya isa ya mana sai dai in Allah ya tsara hakan zai faru kar ki ji komai kawai ki bamu haɗin kai"!! Girgiza mata kai tayi kafin ta ce "toh na yarda zan yi karatun"daɗi ne ya kama Bilkisu dan haka ta ce "Yauwa ƴar gidan Mudan toh yadda za'a yi ki rinƙ zuwa kafin lokacin sai in koyar da ke in kuma lokacin koyarwar ya kai sai mu yi tare ko ba haka ba"?girgiza kai ta yi tana murmush. Ita dai bata sanar da ita cewa Dr Zaid na son ta ba dan kar ta yi amfani da wannan ta ƙi yin karatun ko ma ta fara jin wani iri kuma in har suka bari Mudan ɗin ya san cewa Dr Zaid na son ta toh lallai za'a yi ƴar ƙaramar yaƙi su kuwa ba abin da ya kawo su ba kenan.. Dan haka tsara komai suka yi tun a ranar har dai aka fara karatun rumui rumui kafin 6:30pm suka dakata a inda baby doctor ta tafi kiran Dr Zaid dan shi bai ma san cewa an kawo Asma'un ba,da ya fito ya gan ta sai ya ce "Ya aka yi ba dai kuma aiko ki aka yi ba"? Sai ta ɗan murmusa dan ta ga changes a tattare da shi sosai zuwan su nan ɗin a da ba su ga maciji da juna har ji suke kamar su kashe juna dan haushi but now just a week + wai har suna iya tsayuwa su yi doguwar maganar fahimtar juna sai ta ce "A'a ba aike na aka yi ba dama sanyin idaniyar ka ce ta zo muka yi karatu i tried and convince her kuma ta amince"she explained everything to him murna yayi at least koh ba komai ta nan zai raba ta da wannan Mudan ɗin sai ya sakarwa Bilkisu murmushin da ya saka ta ɗauke wuta dan bai saba ba bai kuma taɓa yi mata ba hasali ma ba su jituwa so duk wata murmushin da zai mata na ƙeta ne ba na tsakani da Allah ba amma yau saboda Asma'u har yayi murmushin gaskuya da gaskiya hmm lallai yana son yarinyar koh da ma mix feelings ne gare shi a kan yarinyar ba pure love ba he still feel something special for herdan haka itama murmushin ta mai ta ce "Ga ta chan sai ka raka ta gida". Godiya ya mata by saying "Thanks"daga haka ya wuce ta tana ysaye tana mamakin halayar sa ta burgaggen mutum yanzu sanyi anjima zafi girgiza kai tayi ta wuce abin ta. Koh da ta zo zata shiga daga cikin sashen zulfa'u sai ta gan su suna tafiya he felt something strange sai dai ta bar wa kanta ta shige ciki,. Abincin daren ta ta ci ta yi alwala ta yi sallah zama ta yi ta karanta Qur'anin ta a wayar ta daga nan ta tayar da sallar isha'i ta yi azkar kafin ta ɗora da shafa'i da wutri ta yi doguwar addu'oin ta kafin ta kwanta sai juyi ta ke yi ta kasa barcin duba time ta yi ta ga past 9pm sai ta fito waje ta tsaya a tsakar gidan tana jiran jin dawowar shi dan bai dawo ba ga abincin sa nan ba'a kai masa ba zulfa'u kuma ta wuce turakar mai gidan ta a haka ta cigaba da tsayuwa har dai 9:30pm kafin ta ga shigowar sa zai wuce ta kira shi cikin sanyin murya ta ce "Sai yanzu kake dawowa a cikin daren nan bayan ka san yanayin garin nan"!! Dakatawa yayi ya juyo a hankali suka haɗa ido sai ya ga damuwa a cikin idanun ta he became confused takawa yayi zuwa kusa da ita ya tsaya yana nazarin ta na wasu lokuta before he otter a word. "Are you disturbed"? Shiru ta yi kafin ta ce "Am not am just concern"ganaɗayan su shiru suka yi kafin daga bisani ya ce da ita "Go to bed tomorrow is a new day akwai ayyuka da yawa a kan mu goodnight"daga haka ya wuce ta ita kuma ta tsaya a wurin tana tunanin abin da ta yi is she scared of Mudan that his violence might affect Zaid?koh dai wani abin ne na daban? Babu mai bata amsa dan haka sai ta wuce zuwa ɗakin ta kwanta but still barci bai ɗauka ta ba sai around 12 na dare bata ma san lokacin da barcin ya ɗauke ta ba.. ************* _two weeks later_ Suna last week ɗin su a garin suka fita outreach ɗin su ranar monday a inda suke kuma jaddada masu cewa ranar asabar zasu koma basu ji daɗi ba mutanin garin dan sun saba ga shi zuwa lokacin mutanin ƙauyen sun waye da karatun boko da na islama da baby doctor ke koya masu dan har magana suka yi da Dr Zaid akan why not a yi enrolling yaran a makarantun government sharing suka yi da iyayen yaran iyayen suka yarda a fannin islama kuma a ka nemo malamai da zasu na koyar da su sun dai sami haske sosai a wannan outreach ɗin da aka kawo masu,matar da ta sami annular detachment of the uterus an kai ta city hospital an mata surgery da kyar aka yi replacing uterus ɗin aka bata necessary care har ta warke kafin a yi discharging ɗin ta gabaɗaya family ɗin matar sun godewa su Dr Zaid da wannan taimako da suka masu. A fannin Asma'u da Mudan kuwa abu ya fara ɓaci dan in ya zo hira ko yawon zaga garin shi sai ya ji an ce mai bata nan bincike iya bincike yayi but he couldn't find anything dan haka ya sa aka fara saka mata idon lokacin da take dawowa da lokada take fita tsayin kwanaki uku sannan ya sami labarin ai bokan turai ne ya ja ra'ayin ta ta fara karatun zamani da na addini hakan ba ƙaramin ƙunna shi yayi ba sai ya ƙudiri sai ya mai lahani ko yanzu koh anjima ita kuma Asma'un ya daina zuwar mata yana jiran ranar da zai lahanta shu yayi a gaban ta ta gani dan ta dawo hayyacin ta a haka yake yana kuma jiran perfect timing.. **************** Tun da suka tafi ƙauyen nan baby doctor bata taɓa yarda ta fita after 6 ba saboda garin akwai sanyi ba laifi ita kuma tana son kiyaye kan ta har su koma gida lafiya but tsautsayi sai ya sa yammar litinin ɗin last week ɗin su Dr Zaid ya ce da ita wai ta shirya su shuga cikin gari it was 5pm already sai dai bata jin zata musanta mai dan zuwa lokacin she began to realize that she respect him an so she can't go against his wish ko da kuwa bata da niyar yin hakan bata san dalilin yin hakan ba ita kanta dan shw just develop wani irin dislike ma Asma'u whenever she sees them together with Zaid ko me ya sa Allah ne masani. Cikin riga da wando ta ɗora after dress a kai mai botir ta yafa ƙaramar gyale ta fito ta same shi a waje da wata mota da bata san inda ya samo ta ba sai ta ce "Ina kuma ka samo mota"ɗan murmushi ya mata kafin ya ce "My colleague came here yesterday with his wife so na karɓi motar sa ne dan mu zaga gari da shi"sai ta jijjiga kai ta shiga motar shima ya shiga ya ja suka fara zaga gari Sai wuraren 7pm suka kamo hanyar dawowa gida a inda suka kai tsakiyar hanya motar ta tsaya masu ga hadari ya haɗu sosai saura ƙiris ruwa ya tsuge fita yayi yana son sanin matsalar ai kuwa tana fitowa dan ganin me ke faruwa ruwan sama ya ɓarke kamar da bakin kwarya so ta yi ta koma cikin motar amma sai ta rasa yadda za ta yi ga shi a tsaye a waje ita kuma bata jin zata iya komawa ciki ta bar shi a cikin ruwan dan haka ta ce da shi "Ka dawo ciki mana ruwa fah ake yi"ɗagowa yayi ya ce da ita "Ki shiga ciki ina zuwa"duk ya jiƙe sharkaf da ruwa ita kanta ta jiƙe amma ta ki shiga ciki shi kuma bai lura ba sai da ja kamar faɗuwar mutum sai ya dawo ta ɓangaren me zai gani........A jiƙe jagab ta ke kwance a ƙasa kamar marar numfashi a 360 degree ya nufo ta yana jin fa&uwar gaban sa na daɗuwa kamar ana mai cardiac surgery yana passing. Yana nufo ta ya fara jijjiga ta yana kiran sunan ta "Bilkisu....., Bilkisu....,Bilkisu wake up what is happening to you please wake up what's all this oh goshh"..+ Inaa bata ko yi responding ma stimulus ɗin sa ba ko ɗaya yayi yayi ya farfaɗo da ita amma inaa duk ya ruɗe ya rikice toh dama tana rashin lafiya ne amma ta ƙi sanar da shi ko dai dama tana da wani allergy ne?who could possible answer all these questions babu dan haka ya cigaba da ƙoƙarin reviving ɗin ta by giving a the necessary resuscitation amma inaa chan dai da ya ga ruwan daɗuwa yake yi ba tsaya zai yi ba ga shi kan shi na ƙoƙarin ƙullewa sai kawai ya ɗauke ta ya shigar da ita motar dama ruwa ne ya wa motar ƙaranci ruwan da ke motar yayi amfani da shi wurin tayar da motar bayan ya gama zuba ruwan yayi saurin shiga motar ya ba da motar sai sharara gudu y ke yana addua'ar Allah ya sa b wani mugun abin ne ya faru d ita ba bsi tsaya ko ina ba sai cikin gari babban asibitin garin ya dakatar da motar yana tsiyayar ruwa duk a firgice ya cicciɓo ta suka yi ciki sai kira yake akan a kawo masu ɗauki kamar zai yi hauka haka ya rinƙa kira har dai aka zo aka karɓe ta aka yi ciki da ita sai zirga zirga yake yi a bakin emergency room ɗin duk ya rasa sukunin zuci ya ya zai yi facing Ammi?what if she misunderstand him and his excuse?what if sje thinks that he did this intensionally? What if,,, what if,,,what if,....9 "Goddamn it damn it damn it me ke dami na?toh in wani illness ne da ita fah?kenan carelessness ɗi na kenan ya janyo mata faɗawa cikin halin nan?ya Ammi zata yi reacting in ta ga abin da ya faru da Bilkisu? Ya ilahi please help me out am out of it i can't think of any other way".. Kamar sabon kamun mahaukaci haka ya rinƙa maganganu kamar zararre bai taɓa sanin yana da tausayin baby doctor a zuciyar sa har haka ba sai yau sai yanzu da ya gan ta cikin matsala cikin mawuyacin hali halin life or death ya zai yi if she pass out?a hujajjan ya ce "Noooo she.....sheee can't die she can't just dieeee"yayi maganar cikin wani mawuyacin halin tausayi. Yana tsaka da haka likitan ya fito yana tambayar inda relative ɗin ta suke,yana jin haka ya nufo shi yana ɓarin baki ya ce "Yeee....sss am here am here am her relation tell me what is happening to her is she alright?is she calm?is she stable?why are you keeping silence say something damn it"a mugun haukace yake maganar yana ta jerowa likitan tambayoyi kamar bai da seti. Likitan ya tsinke da lamarin sa dan yadda ya ga ya haukace ya yi tsammanin shi ɗin mijin ta ne sai dai kafin ya ida tunanin sa ya ji wata muguwar shaƙar ban haushi ya jiyo muryar sa yana mai amo a kunne cikin anger yana cewa "how dare you, ina tambayar ka ka min shiru is she alright"!! Ya karasa a tsawace yana huci. Ƙoƙarin ƙwace kan sa ya fara yi da ƙyar dai ya rabu da shi yana wani aiko mai kallon tuhuma shi kuma likitan ya rinƙa sauke numfashi a jere babu ji babu gani. Likitan da ke christian ne mai suna Dr Uche Okoli daga east ya fito imo state ƙoƙarin basirar aikin sa ne ya sa aka mai transfer zuwa nan Yola dan ya san kan aikin sa sosai. Ƙoƙarin calmimg ɗin Dr Zaid Maher yayi yana son ya dawo hayyacin sa dan all his thought go straight to the fact that the young lady is his wife sai ya ce da she "Please come let's go to the office we need privacy calm down"da haka fah ya ɗan sami relief ya bi Dr uche zuwa office ɗin sa suka zauna amma hankalin sa duk a tashe ya ke he just wanna see her he wanna know her state of health. Kasa natsuwa yayi ya ce da shi. "Yess say something am listening"!! Sai da Dr uche ya cire stethoscope ɗin da ke sagale a wuyan shi ya gyara zama sannan ya sauke nannauyar sight kafin ya ce. "Gentleman calm down your wife is okey for now but we don't know what later might say".. Dan fah shi likitan yayi concluding cewa ita matar sa ce. Sam hankalin sa bai kai kan kalmar da Dr uche ya furta ba bare yayi decoding ɗin shi a brain ɗin sa har ya bashi meaning ɗin da zai yi responding ma kalmar ba shi dai ya ji last sentence ɗin sa.. "What did you mean later i don't get it"?? Taysayi ya ba wa Dr uche sai ya ce "I mean she is stable now but she might collapse later"ɗan shiru yayi kafin ya ce "Why did you allow her to bath under the rain"?? Jujjuya tambayar yayi kafin ya ɗago ya kalle sa ya ce "bath under the rain"?? Yayi tambayar da sigar ban san inda ka nufa ba..shima likitan sai ya shiga cikin ruɗu "You mean you don't know that she bath under the rain"?wani irin tambayar rainin wayo ne wannan sai ya hasala ya ce da shi "Will you go straight and hit the nail what is happening to her"a zafaffe ya yi maganar sai Dr uche ya rikice ya ce "Her pneumonic crises attack her and the exacerbation is beyond our capability i suggest you take her to a better facility far modernize than here because our equipments and facilities are very low to handle her am so sorry gentleman"!! Yana kaiwa nan ya ja bakin sa yayi shiru gudun kar ya ji wani damƙar. Shi da ke zaune bai san lokacin da ya tashi tsaye yana ja da baya ba har dai ya haɗa bayan sa da jikin wall ɗin office ɗin yayi shiru ya kasa cewa komai for a while haka shima Dr bai ce da shi komai ba sai ya bar shi dan ya san ya Shiga wani hali ne. Kusan 8minutes yana jingine ba tare da ya ce komai ba daga bisani ya fita daga office ɗin yana haɗa hanya har dai ya kai rest room ɗin da aka kai ta ya shiga ya tsaya a kan ta yana kallon yadda ta koma just hours kawai duk ta fita a hayyacin ta ta na numfashi sama sama gefe ga nurse nan tsaye tana son bata fast pain relieving injection amma ya ƙi matsawa dole ta mai magana,instead ya matsan sai kawai ya ce "No we don't need it just get me the trolling chair"daga haka bai kuma furta komai ba ya cigaba da kallon ta cikin tausayi bai san yaushe ya fara tausaya matan ba but as far as he is concern yana bala'in tausaya mata yanzu da ya gan ta cikin wannan halin battling with her life ɗin. Bai san lokacin da aka kawo trolley ɗin ba sai dai ya ga ana ƙoƙarin cicciɓan ta za'a ɗora ta a kai bata san inda kan ta yake ba,haka aka tura ta har dai suka saka ta a motar ya ɗauko Atm card ya masu transferring ɗin charges ɗin su ya koma ya shiga motar ya fara ja. Kamar kar ya fara driving sai ga kiran Hajiya Madina. Rasss gaban sa ya bayar sai ya rikice ya rasa yadda zai yi haka kiran ya ɗauke bai ɗaga ba kuma kira ta yi a karo na biyu bai ɗaga ba kuma bata haƙura ba ta cigaba da kiran har ta ba shi 8 missed calls bai ɗauka ba the more tana kira the more heart rhythm ɗin shi na chanza rate from regular to irregular sai swinging ya ke yi dan sai ya ke ganin kamar an sanar da ita ne abin da ke faruwa. A tsiyace ya ke jan motar har suka iso cikin ƙauyen cikin hanzari ya shiga cikin gidan ya kirawo zulfa'u dan ita ce kaɗai zaune a tsakar gidan babu kowa tana jiran dawowar su tana ganin ya shigo a wani irin yanayin da bata taɓa ganin sa ba sai ta miƙe tsaye ta na tambayar ko lafiya. "Please ki zo ki taya ni ɗauko Bilkisu tana mota ba lafiya" Ai bata tsaya jin ƙarshen maganar ba ta yi waje cikin sauri tana salati tana ɗaga murya "Ina kuka tafi?me ya faru da ita?ohoh ni zulfa'u na tare su me kuma ya sami likiciya"sai surutu ta ke yi wanda yayi nasaran janyo hankulan mutanin gidan da ke ɗakunan su kowa sai ya fito yana tambayar ko lafiya. Turus suka yi ganin zulfa'u na ƙoƙarin kinkimar ta ita kaɗai dan shi bai saka hannu ba sai hindatu tayi saurin tahowa ta taya ta tana ta salallami a haka dai suka shiga da ita ciki a inda aka kwantar da ita still breathing pattern ɗin ta bai yi regularizing ba.fita zulfa'u ta yi tana kiran Dr Zaid da ya zo ya taimaka ta farfaɗo. Ya ma manta wai shi likita ne dan haka bin bayan ta yayi kamar wani marar laka a jiki ko da suka shiga cikin ɗakin kasa taɓuka komai yayi sai da ta kuma ce mai "Likita baka yi komai ba numfashin ta na raguwa fah"a dame ta yi maganar wanda ya saka shi nemo wayar sa ya rinƙa dialing numbern Afzal ƙanin sa da ke aiki a Canada sai dai da ya dannan sai ya nuna mai cellular network not available kamar zai yi hauka da yake zulfa'u akwai saurin ɗago lamari sai ta gane kamar waya yake son yi sai dai babu service sai ta ce da shi "Kira kake son yi"? Kamar ƙaramin yaro ya girgiza mata kai dan kasa cewa komai yayi sai ta ce "Zo in nuna maka inda zaka sami sabis ɗin"! Ta nuna mai direction ɗin toilet ɗin ta haɗe da gwada mai daidai lokon da zai sami service ai ko sai ya yi appearing fully dan haka babu ɓata lokaci ya fara laluɓar lambar kamar ba za'a ɗaga ba sai kuma aka ɗaga. Daga ɗaya ɓangaren aka ce "Hy big bro kwana biyu baka kira ni ba halan jin daɗin ƙauyen ne ya hanaka neman lil bro ɗin ka"! Cikin jin daɗi yayi maganar amma sai farincikin sa ya maƙale sakamakon jin muryar ɗan uwan sa da yayi cikin wani irin yanayin da bai saba jin ba.. "Afzal me zan mata she is not recovering"!! a dame ya yi maganar sai Afzal ɗin ya rasa ina maganar yayan na sa ya dosa sai ya ce "Big bro she?who is she"? "Her,Bilkisu her crises attack"!! Sai a sannan ya gano bakin zaren sai ya ce "Big bro calm down,calm down,yanzu ina Kuna gida"? Kamar ƙaramin yaro ya ce "Eh muna gida"! "Alright na san ba yadda za'a yi bata tafi da magungunan ta ba dan yanayin garin so yanzu go straight to her luggage and check definitely you will find it humm"? Miƙewa yayi a hargitse ya dawo cikin ɗakin "Ina kayan ta ina jakunkunan ta"? Nuna mai zulfa'u ta yi cikin sauri ya fara hargitsa kayan na ta sai ya hango wani magani me ji kamar ointment ya duba kuma sai ya ga magungunan ta har da inhaler da sauri ya kwaso su ana kallon shi duk matan tausayin baby doctor ne ya kama su dan basu taɓa ganin ranar da ta yi complaining cewa kanta na ciwo ba amma yau ɗazu ɗazu kawai amma an dawo da ita ranga ranga babu numfashi mai kyau. Tafiya ne,super ne duk haɗawa yayi ya isa gare ta ya buɗe ointment ɗin ya zuba a hannu ya fara shaƙa mata ta hancin ta kafin ya dawo ya fara ƙoƙarin dismounting inhaler ɗin ya tabbatar yana aiki sai ya kuma haɗa shi wu guda kafin ya fara ƙoƙarin shaƙa mata tun bata responding har ta fara responding kaɗan kaɗan ta fara tari babu ƙaƙƙautawa haka ya cigaba da inhaling mata har dai ta fara jan numfashi tana ƙoƙarin yaƙi da obstruction ɗin tana ta jan numfashi tuni ta haɗa da ɓarin jiki ga convulsion da ke son kamata ga serious exacerbation da ke ta ƙaru tuni zazzafan zazzaɓi ya sauko mata tana fighting da numfashin ta tana son calming kanta amma abin ya fi ƙarfin ta dan haka a haukace ya ce "Ina blankets ɗin ku"ya manta da irin mutanin da ya ke magana da su cewa ba su ji turanci ba dan haka ya tashi ya koma ya birkice kayan ta har dai ya ga blankets har biyu ya zo ya rufe ta da su duk ya ruɗe kafin ta kuma experiencing wani sharp pains ɗin har ya dannan mata allurar rage zafi ya sa a kawo mai spoon mai kauri aka kawo ya yi saurin sakawa a tsakanin upper and lower teeth ɗin ta kamar dambe tana jacking yana kuma danna spoon ɗin duk ya haɗa zufa yana ta ƙoƙarin raba hakoran da kyar da kyar ya yi nasarar seperating hakoran kafin ta kuma komawa ta kwanta lakwas kamar ba ita ta gama convulsing ba shima zama yayi a ƙasan yana sauke numfashi wani na korar wani su kuma matan wurin na kallon abin kamar alien dan da za'a bar su tsab za su dafa Alqur'ani su ce iskokai gare ta sai dai ganin yadda abin ya faru a zamanance sai suka yi shiru kawai suna jin fargaba na kama su ba dai mutuwa ta yi ba haka kuwa suka antayo mai tambayoyi "Likita menene mun ga ta kwanta kamar marar rai me ya same ta"??yana cikin mawuyacin halin nan amma yayi ƙarfin halin ce masu. "Rashin lafiyar ne ya lafa shi yasa ta ɗan sami barci ku bar ta ta ɗan sami doguwar barci har sai ta farfaɗo da kan ta"!! Cikin gamsuwa suka ce toh dan haka suka koma parlor suka zazzauna shi kuma ya cigaba da zama a wurin yana kallon ta yadda numfashin ta ke fita kamar ta gama gudun tsere he is just restless this is the promise his mom made him took dama?ta saka shi ɗaukar mata alƙawarin zai na kuka da ita ashe dama tana da matsala ne?ashe haka ta ke surfering amma bata taɓa bari an sani ba?dama tana da chronic pneumonia ne tun childhood?but me ya sa bai taɓa sani ba sai da abin ya faru?yanzu me zai gayawa Ammi?what if she says it to Ammi?Ammi tana iya cewa da gangan ya janyo rashin lafiyar ta ya tashi!!! Kawai sai ya ruɗe ya kuma komawa cikin toilet ɗin ya kira ƙanin shi Hakim da ya ɗauka sai ya riga shi magana "Hakim su Ammi...su Ammi sun dawo ne?sun dawo gida ne"? A ruɗe ya ce "A'a big bro basu dawo ba me ya faru"? "Babu babu Hakim je gidan su Bilkisu ka ba ma Bilal wayar i want to talk to him"ɗan shiru yayi kafin ya ce "Big bro it's raining heavily here i can't go out"ras ya ji jin an kira sunan rain sai ya juya ya kalli yadda ta ke barci sai ya ce "Ka ɗau lema ka tafi yanzu dan ina da magana da shi"daga haka ya kashe wayar ya koma ciki bai san lokacin da ya fara tofa mata addu'oi ba yana yi yana duba wayar sa sai da ya daidaici 10minutes ya yi sai ya koma ciki ya kuma kiran layin Hakim ɗin muryar Bilal ya jiyo sai ya ji yayi losing courage ɗin sanar da shi abin da ya faru sai kawai ya ce da shi "Bilal are you alright"??da mamaki suka haɗa ido da Hakim ɗin kafin ya ce "Yes brother am fine me ya faru"? Ajiyar zuciya yayi kafin ya ce "Shikenan ba komai just taje care"daga nan ya datse wayar ya ajiye yana goge zufar da ke tsatsafo mai ya koma ɗakin yana cigaba da kallon ta. A shekaranjiya Hakim ɗin ya dawo yin wani assignment da sai a gida zai iya yin sa tun dawowar sa babu inda ya tafi kullum yana gida toh ana ruwa a ƴan kwanakin shima kuma saurin kamuwa da Rhino virus ne da shi shi yasa baya son fita cikin ruwan jin gaggawan da yayan na shi ya mai sai ya fita ai ko da atishawa ya koma gidan su yana ta rawan sanyi.. _3hours layer_ Sauran matan sun koma zulfa'u ce kaɗai ta fara barci a saman three seaters ɗin falon shi kuma yana zaune in zaman bai mai ba sai ya miƙe tsaye ya rinƙa zirga zirga hankalin sa duk ya gama tashi dan bata farfaɗo ba har expected time dan haka anxiety ɗin sa sai ya daɗu. Ana haka sai ya ji ta fara tari tana jujjuyawa kaɗan kaɗan,da sauri ya nufe ta yana tambayar ta "Bilkisu are you alright?me ke damin ki?ina ke maku zafi"? A hankali ta buɗe idon ta ta sauke su a kansa sai ta rinƙa bin sa da kallo tana ƙoƙarin tunano abin da ya faru kafin yanzu sai ta fara yunƙurin tashi. "Easy take it easy gently"haka yana bata encouraging words tana miƙewa har ta yi leaning da jikin gadon tana numfashi dan bayan ta zama stable yaba da wuri an chanza mata kaya zuwa doguwar riga mai kauri aka saka mata cardigan da hula toh a yanzu da zufa ta farka dan haka sai ta cire cardigan ɗin tana jan numfashi kaɗan kaɗan sai ya je ya ƙunna fan ɗin ɗakin yayi regulating ta yadda ba zai yi yawan da zai ishe ta ba.. Ya dawo ya zauna ya ce mata "Ya kike ji ina ke maki ciwo"?mamakin care ɗin na sa ta ji sai ta ce "Am fine am alright" "Are you sure babu inda ke maki ciwo"? Yayi tambayar yana mai tsare ta da idanu sai ta jujjuya mai kai alamun a'a Numfashi ya sauke kafin ya ce. "Why?why Bilkisu?kina da wannan rashin lafiyar amma baki faɗa min ba kika shiga ruwa kika tsaya for a long without considering your health me ya sa kika yi hakan"?shiru ta mai tana jin wani baƙon abu sai ta juyar da kan ta gefe dan tana da rauni yanzu sai ta fara hawaye dan haka shi sai ya juya zuwa direction ɗin ta ya ce "Bilkisu kin san kina da pneumonia amma baki sanar da ni ba kika yi shiru har muka fita yawo cikin sanyin nan ga shi ruwa ya taɓa ki but.... "Sai ya kasa ƙarasawa ya yi shiru yana kallon ta for a moment sai ya ce "Me ya sa"? Jin muryar sa da yanayin sigar tambayar sai ta ce "Kana cikun ruwan na yi na yi ka dawo cikin motar dan kar sanyi ya kama ka ka ƙi ni kuma zan shiga motar kenan ban san me ya faru ba... "A nan itama ta yi shiru tana son danne abin da ke son taso mata. Wani hali ya shiga dan it is clear to him now cewa shi ne sanadiyar shigar ta wannan yanayin dan haka sai yace "But you should at least consider your health first why are you stubborn?a ko da yaushe you prove your stubbornness i never knew that your stubbornness is up to this degree da har kina gwada shi da health ɗin ki"!? Yadda yayi maganar sai ya bata dariya but bata yi ba sai ta murmusa kawai ta sunkuyar da kan ta shima sai ya ji murmushin ya zo mai a bazzata mamakin kan su ne ya kama su. Miƙewa yayi ya ce "Bara na kirawo maki ita ta ba ki abinci dan you need to take your medication humm"?girgiza mai kai ta yi har ya fita zulfa'u ta shigo bata lura ba dan hankalin ta na wani wurin daban tana jin kamar kar ya tafi. "Likiciya..likiciya ya jikin na ki"?a nan hankalin ta ya dawo jikin ta sai ta yi murmushi ta ce "Da sauƙi" "Me za ki ci a dafo maki"?sai ta ce "Tea kawai zan sha kar ki dafa komai dare ne" "A'a ba'a yi haka ba likiciya ina zuwa"!! Daga nan ta bar ɗakin ta koma kitchen dan samo mata abin da zata ci ita kuma tana nan tana bitar jaridar bunu dan ta kasa haɗa tunanin ta wuri guda sai da zulfa'u ta dawo da tire a hannun ta har ta haɗa mata tea ɗin ta zuba mata indomie ɗin da ke turiri ta na kiran ta amma inaa bata ma jin ta sai da ta ɗaga murya ta ce "Likiciya kina ina"a firgice ta dawo hayyacin ta ta ce "Na'am ina nan"girgiza kai zulfa'u ta yi ta ce "Anya likiciya kin warke kuwa"? Dariya kaɗan ta yi ta ce "Eh na warke mana amaryar mai gari" "Toh gashi yi ki ci ki sha likita ya ce in kin gama a baki magani" Amsawa tayi tana ci,duk wanda zata kai baki sai ta tuna da shi da lokacin da ya ke tambayar ta a ruɗe ɗazu kafin ya bar ɗakin a haka har ta gama bata sani ba. Miƙo mata maganin da ya bata tayi ta ce "Ungo sha"ta karɓa ta haɗiye sannan ta ce da ita sallah zata yi. Taimaka mata ta yi ta shiga toilet ɗin ta yi alwala ta zo ta yi sallar magrib ɗa isha'i lokacin shabiyu saura sai ta kwanta abin ta ta rufe jiki ta rufe ido amma barci ya ce bai san da wannan ba haka ta rinƙa juyi tana tunane tunane barkatai sai 2am ta sami ɓarawon yayi gaba da ita.. *********** _10am_ Ta farka daga barci sai ta yi tozali da su hindatu da ƴaƴan su ga Asma'u nan gefe tana zaune tana kallon ta ganin ta farka sai suka yo kan ta suna tambayar ta ya jiki Murmushi ta masu ta amsa su Asma'u kuma ta zo gab da ita ta ce "Ina kwana aunty Bilkisu ya jikin ki"? "Jiki da sauƙi Ma'ulle"ɗan dariya ta yi jin sunan da ta kira ta da shi dan bata saba ba".. Haka dai suka ɗau lokaci suna ta yi mata hira kafin su ba ta space ta shiga ta yi wanka ta chanza kayan ta,,abinci ta ci ta fito ta sami Asma'u zaune a falon tana kallo cikin lumana kamar ba ita ba ce ke daru satunan baya da suka wuce ba. Zama ta yi kusa da ita ta ce "Asma'u wa ya faɗa maki ban da lafiya"? Da fara'ar ta ta ce "Ɗan birni ne ya zo gidan mu da safen nan ya ce da mi ba ki da lafiya kuma mama ba ta da lafiya shi yasa ni na taho ya jikin na ki"? Wani abu ne ta ji ya tokare ta a ƙirji jin sunan da ta kira a matsayin wanda ya sanar da ita rashin lafiyar sai mood ɗin ta ya chanza out of the blue ta ji duk duniya komai ma bai mata daɗi sai ta ce "Okey,jiki da sauƙi Asma'u nagode,ya kamata ki tafi gida dan ki duba mama in kin tafi ki ce ina gaida ta zan zo in na ji sauƙi"miƙewa Asma'un ta yi ta ce "Toh aunty Bilkisu zata ji ni na tafi Allah ya ƙara sauƙi" "Amin ma'ulle nagode"rakota ta yi har waje sannan ta dawo gida ta zauna tana tunanin abin da ke damin ta a ƴan kwanakin nan game da tarayyar Asma'u da Zaid babu daman tagan su tare sai ta rasa natsuwar ta gabaɗaya sai ta ji duk duniyar ba ta mata daɗi ta rasa me ya ke mata daɗi ko menene wannan ɗin Allah ne masani.. Wunin ranar haka ta yi shi ba ta da walwala bare sakin fuska. Around 4:00pm ya yi sallama ya shigo ɗakin lokacin tana zaune kan sallaya tana azkar dan shi kaɗai take ganin zai ɗauke mata lokacin kaɗaicin da take ciki wanda bata san dalili ba. Jin sallamar sa sai ta dakata ta ta rufe littafin azkar ɗin ta juya da kan ta tana kallon sa shi ya riga ta magana ta hanyar ce mata. "ya jikin ki da fatan babu abin da ya same ki"!! Kasa amsa mai tayi sai ta girgiza kai ta sunkuyar ƙasa tana nazarin yanayin tambayar ta shi.jin muryar shi ta yi yana ce mata "Kin sha maganin ki na yamma kuwa"? Why is he being too caring?does he feel something like sympathy towards her?toh menene na damuwa da ita da yawa haka?ta rasa mai bata amsa sai ta ce "Eh na sha thanks"!!daga haka duk suka yi shiru kafin ya ce "Alright ni zan tafi gidan su Asma'u i want to see her mom's condition"!!ai sai ta ji wani abu na mata yawo a kai bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba ta ce "I want to follow you ina son ganin ta nima dan in gaida ta"!!wani irin kallon ban fahimta ba ya mata ya ce "Kina son fita bayan baki gama recovering ba..?no you can't leave the house ki zauna a gida garin da sanyi when you recover fully ni zan raka ki mu je gidan su but not now".. Chanza fuska ta yi zuwa kalar tausayi ta ce "Ka daina min abu kamar mahaifi na,na ce maka na ji sauƙi i can move around anywhere"! Ta ida tana kallon shi ido cikin ido sai dai shi bai gama yarda da zaɓin ta ba dan bai manta episode ɗin da ya faru a jiya ba he can't risk that. "No you are going no where stop being stubborn".. Haɗe rai ta yi ta ce "Fine ka yi tafiyar ka in yi tawa"daga haka ta juya ta ɗau cardigan ɗin ta ta fara tafiya dan dama da hijabi a jikin ta tana kaiwa tsakiyar ɗakin ya dakatar da ita "Wait"tsayawan ta yi bata juyo ba sai ya tako har inda take cikin izza ya ce "Fine,you will follow me,since you are too stubborn but make sure you don't fall sick again"daga nan ya fita itama ta biyo shi tana murmushin dokar da ya gindaya mata. Sallamar ƴan gidan suka yi akan zasu tafi duba mahaifiyar Asma'u sai suka tambaye su har ta ji sauƙin fita ne sai ya ce masu bata jin magana ne ai ita kuma ta natse akan sai ta tafi so they wished them safe journey, A same car ɗin suka fita har gidan su Asma'u abin daɗin shi ne Asma'un bata nan ta fita an aike ta siyo madara nan gidan maƙota jin hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa baby doctor ba dan haka ta assasa mai akan ya zo su tafi yamma na yi shi kuma bai gane ba yana ganin kamar tana tsoron kar rashin lafiyar ta ya taso ne shi yasa ta ce su tafi dan haka ya tashi suka sallami mahaifiyar Asma'u ta ko yi masu godiya sosai. Lafiya ƙalau suka tafi haka ma lafiya ƙalau suka kamo hanyar dawowa gida suna tafe suna satar kallon juna kamar munafukai ana haka sai kawai ta tsala ihu wanda ya firgitar da shi har yayi sanadiyar kwacewar motar daga hannun shi da kyar ya iya daidaita motar ya ja gefe ja juyo da zumar tambayar ta dalilin ihun da ta yi sai dai ya kasa sakamakon abin da idanun sa suka gano mai......... _Toh ko me Dr Zaid ya gano??sai dai a next page dan haka mu tara a page 9 dan sanin ko menene wannan abin da ya firgita baby doctor ya kuma saka Dr Zaid Maher kasa furta ko da kakmar 'a' ne_Wani wild giant animal ya yi haɗarin ido da wanda daga shi har ita ba su taɓa ganin irin sa ba very giant yana ƙoƙarin fasa glass ɗin ƙofar window ɗin gefen ta she was shivering ta gama sadauƙarwa akan tata ta ƙare dan animal ɗin is moaning for hunger a zaton ta da ya dumfaro su babu wani abin da zai masu sai cinye su dan haka ta gama sadaukarwa ta rufe kunnuwan ta da hannayen ta ta rumtse ido ta dunƙule wu guda tana jiran mai afkuwa ya afku.+ Shi da ke dabaran yi wa motar key dan su bar wurin sai mota ta ce bata san wannan ba yayi yayi ya tayar amma inaa bai tashi ba ƙarshe ma faɗawa a ƙasar motar car key ɗin yayi wanda ya janyo hankalin wild animal ɗin ya kuma yunƙurowa zai kaiwa glass ɗin duka at the same time da ya yunƙuro ya daki glass ɗin a lokacin kuma ta ƙwala ihu wanda har dajin sai da ya amsa. Reras ta koma da baya ta tafi luu sumammiya ko ina na jikin ta ya saki.shi ma duk sai lamarin ya girgiza shi ga sumewar ta ga gurnanin dirty wild animal ɗin ya ƙi barin shi yayi tunanin mafita. Kusa wasu lokuta ma su tsayi wannan dabban bai bar wurin ba shi kuma bai motsa ba yana zaune a hakan sai da baby doctor ta farfaɗo ta kuma sumewa kusan sau uku in ta farka sai ta yi ido huɗu da animal ɗin luu sai ta koma ga shi dara na daɗa tsalawa ga sanyi na saukowa hadari na haɗuwa wild animal ya ƙi barin wurin yana kallon su abin tsoro.. Ganin zaman ba zai kawo masu mafita ba ya sa ya dudduba motar ko zai ga wani abin ya jefe animal ɗin da shi sai dai inaa babu wani abin,gorar table water da ke motar da yayi ƙoƙarin harbawa animal ɗin sai ya janyo masu jangwam dan kuwa wani ƙuwa dabban yayi dajin ya amsa ƙuwar wanda hakan ya saka ta farfaɗowa ai yana ganin ta farfaɗo bai san lokacin da ya fizgo hannun ta ba gudun kar ta juya ta kalli gefen dabban ta kuma sume mai dama ita yake jiran farfaɗowar ta dan su sanu su tsira da lafiyar su,dan haka tana jin irin fizgan da ya kai mata sai ta buɗi baki zata kurma ihu a zafaffe ya rufe mata baki da hannun sa yana mata alama da ido akan kar ta yi ihun amma da yake ta gama tsorata da lamarin kuma ta rigada ta fara yin arba da wild animal ɗin sai ta kasa controlling kan ta bare ta yi shiru. Yana rufe mata baki tana jujjuya kai alamun ya rabu da ita shi kuma yana zazzaro mata ido waje alamun ta yi shiru.sam ba ta fahimci physical gesture ɗin na sa ba sai ƙoƙarin ƙwace bakin ta take yi tana fizge fizge bai sakar mata bakin ba har sai da ya ga zata kuma suman mai sai ya shiga jijjiga ta sai layi ta ke yi tana son fainting kuma. What to do?ya tambayi kan shi "Mutum da syncope attack har haka?ban taɓa gani ba"ya gayawa kan sa yana mai cigaba da preventing ɗin ta from shouting out in ta yi kamar ta natsu sai ta kuma turjewa ta na juye juye.. Da ƙyar da dabara ya samu ya farfaɗar da ita completely har dai ta dawo hayyacin ta shi kuma animal ya ƙi barin wurin. Yana kallon dabban da duk wani moves ɗin sa yana duba time dan lokacin har dare ya fara.. Haka suka cigaba da zaman ya hana ta kallon gefen shi kuma animal ɗin yayi shiru kamar ba shi ya janyo panic ɗin ɗazu ba. Wani daɗewar basira Allah ya saukowa da rabban nan wanda ya juya baya kamar zai tafi sai suka lallaɓa suka yi da kan su ƙasa kaɗan kaɗan suka rarrafa suka fito daga motar a hankali suka fara tafiya cikin sigar gudu gudu suna kaiwa daidai wani hanya da ya raba gida biyu suka rasa ta ina zasu bi kawai sai suka ji gurnanin dabban nan ko da suka juya har ya biyo su a baya da matuƙar speed yana ta moaning suka ƙara saurin speed ɗin su suna gudu yana biyo su ko da suka kai tsakiyar marabar hanyar sai kawai ta yi ɗaya ɓangaren shi kuma ya bi ta right path ɗin wannan dabban ya ko yi left path ɗin yana ta kururuwa kamar mayunwaci sai gudu yake yi yana kururuwa ita kuwa da ta yi cikin dajin ta ga banu shi babu alamun sa ga dabban yana dunfaro ta sai ta nemi wani mafaka ta fake tana haki ga tsoro nan duk ya addabe ta rumtse ido ta yi tana jin faɗuwar gaban ta na increasing linkin ba linkin.. Along the line ya fuskanci cewa shi kaɗai ke gudun babu ita kuma babu dabban bai ma jiyo hayaniyar sa ba kawai sai ya shiga zare idanu yana juye juyen neman ta,tsoro ne ya riske shi babu ƙaƙƙautawa ya fara bin hanyar jikin sa na ɓari yana kiran sunan ta tun yana yi with low tune har ya fara ɗaga murya yana kiran sunan ta.. "Bilkisu........Bilkisu........ina kikeeeee...." Ya kuma ƙwala kiran amma inaa tambayar komo mai yake yi dan yana kiran amma yana echoing back. Ƙara ƙarfafa muryar sa yayi wurin kiran sunan ta dan ta jiyo sa. Daga mafakar ta ji kamar muryar sa ne ke yawo a kunnen ta dan haka ta cire hannuwan ta daga kunnen tana daɗa natsuwa dan ta tabbatar ai kuwa kuma jiyo sautin muryar sa ta yi yana kiran ta,ga wild animal nan yana kallon ta ga shi tana son amsa kiran na sa amma ta na tsoron amsawa gudun kar abin ya yo kan ta dan haka ta yi shiru ga sanyi na shigar ta. A haka suka kai rabin hour a wurin nan babu mafita ganin sanyi yana iya lahanta ta sai ta yi shahada kawai ta miƙe tsaye daidai ya kirawo sunan ta kuma amma a wannan lokacin kusa da ita take jin sautin muryar dan haka ta rufe idanun ta a hankali ta fara matsawa shima dabban na matso ta.tana jin ya kuma kiran kawai sai ta amsa da iya ƙarfin ta "Am here"..jin haka sai ya cigaba da matsowa towards the sound of her voice har ya zo dab sai dai ban gan ta ba sai ya kuma kiran sunan "Bilkisu ina kike".. Ta kuma amsawa da "Am here,behind you".. Ita kanta ba za ta iya cewa ga taƙaitacciyar ɓarayin da ta jiyo sautin muryar ta sa ba dan haka yana daɗa matsowa animal ɗin na nufo ta ita kuma ta ƙi buɗe idanun tana dai shivering sosai. Yana neman ta ya rinƙa bin hanyar da ya jiyo echo ɗin muryar ta.sai zurmawa daji yake yi daidai ya iso tsaƙiyar dajin ya hango kamar dabbar zai ɗaga ƙafar sa kenan ya ji wani irin razanannen kururuwar dabban wanda kafin ya ƙifta ido ya buɗe bai hango dabban ba kuma. Daɗa zaro idanun sa yayi sai ya ga kamar mutum a kwance babu numfashi sai ya dumfaro wurin cikin sauri sauri gudu gudu sakamakon hango hijabin ta da yayi a ƙasa ita kuma tana kwance a gefe. Bai yi wata wata ba ya yi rushing zuwa gare ta directly da wani irin rhythmic motion ba tare da ya yi la'akari da hatsarin da Ke wurin ba ko tsoron kar dabban ya dawo ba. Yana isa gare ta ya fara yunƙurin janyo hijabin yana kici kicin saka mata dan zuwa lokacin shi kan sa sanyin ya fara tsirga sa ba zai iya bari last night episode yayi repeating kan sa ba dan dama lallaɓa ta yake son yi in sun koma gida ta yi receiving intensive care. Ya kawo hannu zai saka mata hijabin kenan ya jiyo wata arniyar dariya daga bayan sa,kasa saka mata hijabin yayi ya shiga kokonton ko dai ba a nan ya jiyo muryar ba yana a haka sai ya kuma jin amon muryar ana dai dariyar dan haka ya juya cikin hanzari dan son sanin me ke dariyar haka.. Maza ne har bakwai masu siffar mashaya marasa tarbiya duk kusan a buge suke sai dai ƙwara ɗaya da ke jin kan sa kamar doki wanda shi kaɗai ne riƙe da wata budurwa a gefen sa tana kuka tana turjewa shi kuma yana dariyar mugunta. Fuskar ta sam bai fito sarari ba dan duhu ya mamaye wurin,sai kuka ta ke tana gunji sosai take kukan kamar wacce zata tsiyayar da hawayen idanun ta. Daɗa ruƙo ta yayi ya kausasa muryar sa ya ce "Kai ɗan birni ko?kai wayayye ko?kai mai son raba soyayyata da yarinya ta ko?ka min shigar kai tsaye kana son yin gasa da ni ko?na ce bana son ta yi karatun zamani magana ta zauna kawai ka zo ka juyar mata da kwakwalwa ko?ga ka isasshe ko ba haka ba?eh ya ne ban gane ba ka min shiru baka magana".. yayi maganar ƙarshen yana wani yunƙuro mai kamar zai far mai sai ita yarinyar ta tsala ihu tana mai cewa "Dan Allah a'a Mudan kar ka mai komai ba laifin sa ba ne ni ce da laifi kar ka mai komai wallahi zan cigaba da bin umarnin ka duk yadda kake so haka zan yi,dan Allah ka bar shi".. Ɗagowa yayi ya buɗe idanun sa da kyau dan son ganin mammalakiyar muryar dan kamar ya san mai muryar bai sami damar ganin fuskar ba dan wani tsawar da ya ji mai suna Mudan ɗin ya daka wa yarinyar "Kina son in halaka ki ne bayan na gama shafe labarin sa halan?eyyyee?kika kuma furta kalma ɗaya za ki bi shi kuma in kika tafi ki bashi albishirin cewa zan zo har nan in kuma halaka sa"?a zafaffe yayi maganar. Ta san shi ta san ko shi ɗin wanene kuma ta san abin da zai iya aikata dan duk daɗewar ka da Mudan ba ka fi ƙarfin ya keta maka tsiyar sa ba tsakanin ka da shi *iya ruwa fidda kai* ne in kuwa baka iya ba toh ka zama abin wulaƙancin sa dan shi ba'a mai gyara ba'a sainsa da shi abin da ya ce shi ne daidai.. Bata kuma furta komai ba sai kuka hakan yayi daidai da farkawar ta daga doguwar suman da ta yi wanda tana farfaɗowa ta ci karo da ƙartin mazan da ke ta faman layi zata kurma ihu ya ce cikin kausasshiyar murya "Yauwa ga ɗayar sa nan,wato har da ke a matsayin ki na mace kina yaƙi da soyayyar mu ni da yarinya ta ko ba haka ba"?ya faɗa yana mai wurga yarinyar zuwa ga sauran mazan yana ce masu "Ku riƙe min ita ku rufe mata baki kar ku bari ta buɗe bakin ta bare ta kuɓuce maku"da sauri suka rirriƙe ta tana ta turjewa yadda ya faɗa haka suka yi da ita suka bar ta da zazzaro idanu waje tana girgiza kai shi kuma ya yi dariyar zalunci ya ce "Kina gani ko ƴan mata na,zan lahanta shi a gaban ki in kashe shi a gaban ki in wurgawa dabbobi namar sa su yagalgala tunda yayi ƙoƙarin shigowa harkata ba tare da na bashi gayyata ba"kuka sosai ta ke yi tana juya kai. Baby doctor da tun da ta farfaɗo ta riski wani muguwar halin da suka kuma faɗawa ciki ta saka kuka duk ta tsani rayuwar ta from yesterday zuwa yanzu,,shi kuwa da tuntuni yake sauraron Mudan da duk wasu abubuwan da ke faruwa dan haka yake ganin ya gaji da sauraron sa dan haka ya miƙe ya ce da shi "Idan kai ɗan ta'adda ne marar ilimi marar hankali baka isa ka lalata rayuwar kamilalliyar yarinya ba yarinyar da bata ji ba bata gani ba,ka gama ɗaura ta a kan mummunar hanyar ka gurɓatacciya ka na son tursasa ta biyewa sharuɗɗan ka dan kawai tana yarinya wacce bata gama girman tantance daidai da akasin sa ba,bari ka ji in faɗa maka da mu da ita za mu bar wannan garin zata tafi chan ta sami ingantacciyar rayuwa da ilimin addini haɗe da na zamani dan ta zama abin alfahari a garin nan a duniya baki ɗaya in ka so sai ka biyo ta chan ka yi abin da kake mafarkin kana iya yi wawa marar tausayin mace"kaiwa nan ya durƙusa dan ɗauko hijabin baby doctor ya saka mata dan su bar wurin amma muryar Mudan ɗin ne ya dakatar da shi "Hmm bokan turai ɗan birni,,toh ai da me rai ake sha'anin duniya ba mutacce ba,sai kana da ran za ka ɗauke ta ku tafi taren ai in baka numfashi kuwa ka ga sai dai kai a ɗauke ka zuwa makwancin ka ko ba haka ba ne"? Juyowa Dr Zaid yayi ya mai kallon wulaƙancin though it is dark but dan takaici ma tsaƙi kawai ya ja ya ce "In ka fasa baka cika Mudan ɗan daba ba kuma ka sa a ran ka daga nan zan tafi in ɗauko Asma'u mu tafi tare sai ka biyo mu"ya mai banza. Dariyar bosawa Mudan yaui dan ya lura shaf Dr Zaid bai san da wa yake magana ba dole ne ma ya koyar da shi ladabi ba ma ladabi kaɗai ba aika shi zai yi inda ba'a dawowa dan haka ya ce "Ma ni kake wa rashin kunya kake gayawa magana son ranka ko"? Amsa ya bashi da "Eh an maka me za ka yi"? Dariya yayi ya ce "Zan maka komai ma,zan maka komai har da wanda ban taɓa yi ba kai zan maka ina da ni kake yi"?juyawa yayi ya ma ɗaya daga cikin yaran na shi alama da ido da sauri suka tafi cika mai umarnin sa. Shi kuma ya cigaba da laluɓo hijabin ta ya yi nasarar gani ya miƙa mata duk ilahirin jikin ta rawa yake yi tana kuka mai taɓa zuciya suna zaman zaman su wannan matsalar ta zo masu sai kuka ta ke yi ya ce da ita "Tashi mu tafi gida sanyi yayi yawa"ta bi umarnin sa tana ɓarin jiki ai kuwa miƙewar ta ke nan wanda yayi daidai da wani direct sharp hit da ya sauka a lower occipital region ɗin Dr Zaid wanda ya tafi daidai Medullar oblongata yayi linking zuwa pons ɗin sa wanda babu yadda za'a yi a yi hitting mutum a wurin nan ba tare da ya sami temporal or permanent dysfunction ko permanent death ba dan wurare biyun nan sune kusan mutum a jikin ɗan adam saboda a nan sinadarin regulating bugun zuciya ya ke,numfashi,haɗiyar abu,amai,shaƙuwa,tari,atishawa,barci da gudanar numfashi daga nan zuwa nan duk sinadarin aiken waɗannan ayyukan na a cikin kwakwalwar ɗan adam wanda kwakwalwar kuma a rufe yake a kan ɗan adam kuma waɗannan sinadaran na daidai ƙeyar ɗan adam wato lower occipital region ɗin kenan inda medullar oblongata da pons suke,bugu ƙwaƙwara mai kaifi na iya illata waɗannan sinadarai in kuwa suka sami matsala toh rayuwar mutum kuma sai dai a sannu ko da zai iya farfaɗowa ba kamar da ba sai dai a events ɗai ɗaya. Jin intense pains a kan sa ya sa ya tsaya cak kan shi da kunnuwan shi na ringing mai ƙarar bugun da aka mai a kan na shi,. Zazzaro idanu ta yi ta tsala ihu mai firgitarwa kafin ta ankara ta ga an kuma kai mai wani strick ɗin a same region saka hannuwan ta biyu ta yi a baki tana zazzaro idanu waje jikin ta na tsananta ɓari sanyi ake yi amma tsabagen firgita da ta yi da tsoro sai kawai zufa ya fara tsatsafo mata ta ko ina. Wannan budurwar ma haka ta tsala ihu ta cikin abin da aka yi amfani da shi wurin rufe mata baki tana fiddo idanun ta waje. Two hits ɗin bai mai ba ya kuma kai mai one final painful hit a same place wanda ya kasa resisting pains ɗin ya faɗi ƙasa reras idanun sa na ƙoƙarin rufewa,fincikewa ta yi ta cire abin bakin ta ta kwala mai kira da iya ƙarfin ta "Ɗan birni kar ka tafi dan Allah ka tashi ka rama abin da ya maka kar ka barshi haka nan ban san ka da karaya ba ka tashiiiii"!!!!!. That was the last word he heard daga nan ya rufe idon sa numfashin sa na ƙoƙarin barin jikin sa.. Wani wawan tsale ta daka ta faɗo daidai kansa tana kiran sunan sa "Zaid...Zaid..Zaiddddd"ta ƙarasa tana mai faahewa da kuka tana jijjiga shi tana cigaba da kiran sunan shi akan ya tashi amma bai ma san tana yi ba. Ruɗu iya iy ruɗu ta shiga dan sam bata tuna da cewa wai akwai wani abu mai suna fainting attack ba dama an ce tsoro kala daban daban ne wani ya sha gaban wani ɗazu sumewa ta rinƙa yi babu iyaka akan haɗa ido da ta yi da wild animal ɗin nan but yabzu da ta ke witnessing murder attempt openly ta kasa ko da rufe idanun ta ne. "Zaid please please please please don't do this to me don't do this to our families don't leave me all alone in this wicked world i can't resist the hardships dan Allah ka tashi ka tashi mu bar wurin nan ka tashi mu bar garin nan Zaid prove to them that you are that strong Dr Zaid Maher the best Dr that deal with so many accidental cases Zaid ka tashi mu bar wurin nan am begging you please wake up"ta cigaba da kukan tausayi wanda ita kaɗai ta san halin da take ciki tun da suke a rayuwar su abu makamancin haka bai taɓa faruwa da su ba basu taɓa jin abu mai kama da haka ya faru da ko wani family member ɗin su ba ko a mafarki bata taɓa yin mafarkin wannan mummunar dare ba a rayuwar ta,they were leaving a happy life very sweet and comfortable babu tsoro amma zuwan su nan garin cikin ƙauyen nan fargaba ne kala kala ya rinƙa riskar su jiya ta faɗa a wata ƙaddarar yau kuma ana son hallaka shi duk dan saboda wannan outreach ɗin da suka zo yi abin da ba su zai amfana ba abin da saboda Allah suka zo yin sa abin da they did it with pure heart amma yayi back firing masu ta wannan sigar,.. Tana kuka tana jijjiga shi amma ba ya responding haka ta rinƙa kiran sunan sa tana jijjiga shi. Budurwar da ke kukan ƙunci ne ta ce "Ɗan birni ka tashi ina roƙon ka da Allah da ka tashi kar ka min haka kar ka tafi ka bar ni da wannan mugun azzalumin ka tashi ɗan birni dan girman Allah".. Da kuka ta ida maganar Wani irin mari ya kaiwa kyakyawar fuskar ta ya ce "Ohhhh wato dama har da saka hannun ki a cikin masu min yankan baya?dama kina sane da duk wani shirin sa?ohh na gane ashe shiryawa kuka yi dan a kashe ni ina tare da ke ina yaƙi a kan ki amma kina son ganin baya na?toh bari ki ji in kwaɗayin zuwa birni kike yi toh babu inda za ki tafi muna nan ni da ke kuma babu mahaluƙin da ya isa ya raba ni da ke ni da ke babu rabuwa ko mutuwa ba zata raba mu ba tare za mu rayu mu kuma mutu tare babu wanda ya isa ya shigo tsakani na da ke Asma'uuu"da isa da gadara ya kira sunan wanda hakan ya sa baby doctor dakatawa na wasu lokutan ta ɗago sai dai bata ganin komai sai dishi dishin mutani amma ba zata iya cewa ga takamanmen mutanin ba but jin sunan Asma'u da aka kira ya sa ta gane cewa ma'ulle ce. "SubhanaAllah me zan gani?ita ta kawo su nan?dama uta ce ta ke biye da su tun ɗazu bata sani ba?ita ta sa aka yiwa Zaid wannan abin"?duk ma kanta take yiwa waɗannan tambayoyi dan dama kamar ta so ta hango wani rickshaw na bin su a hanya kuma ta hangi mutani a ciku sai ta ga mace mai kama da wacce ta sani sai dai bata yi concluding ba dama ita ce a rickshaw ɗin tare da mazan nan??inalillahi wainailaihir raji'um haka ta rinƙa nanatawa hat dai ta ji an ja Asma'un da full force kafin ta sani wurin yayi clearing daga ita sai shi duk sun bar dajin ga duhu ga sautin dabbobi.. shiru ne ya ratsa wurin dan bata san madogara ba sai ta zame ta zauna daɓal tana cigaba da jimamin abin da ya faru tana a hakan for a long while kawai sai ta kurma ihu gabaɗayan dajin ya amsa ta kuma kurma wani ihun mai tafe da kuka ta shiga jijjiga shi tana kiran sunan sa "Zaid...Zaid...Zaid.ka tashi ka tashi mu bar dajin nan please ka daina min wannan taurin kan na ka wake up wake up i beg you"...haka ta rinƙa kuka tana kiran sunan sa ko ta tsoron katsurgin dajin ba ta ji... Lokaci mai tsayi suka ɗauka a dajin nan babu haske ga kukan dabbobi duk yana kuwa a dajin hawayen idanun na ta ma ya daina tsiyayowa sai ya zama kukan zuci kawai take ta yi babu hawaye kuma bata fitar da kukan waje a haka da suke ta rasa ya za ta yi ga shi nan kamar gawa a gaban ta babu alamun akwai rai tattare da shi sai ta ga kamar gilmawar haske da sauri ta bi hasken da idon ta still ta kuma ganin hasken da sauri ta miƙe tana ɓarin baki wurin furta. "Help...help us"gabaɗaya strength ɗin ta ya ƙare muryar ma ba sosai ya ke fita ba sai ta ga hasken na daɗa nufo su haka ta kuma cewa. "Ku taimake mu please ku taimaka mana"!!! Sai ko ga hasken na ta zuwa a haka mutani babu adadi suka rinƙa kutsowa tana daɗa ɗaga muryar ta dan zu yi tracing ɗin ta da kyau kawai sai ta ga haske ya dallare wurin ga mutani nan da yawa kamar a mafarki sai a lokacin hawayen da ke maƙale a idon ta suka fito suka shiga tsiyayowa tana fidda silent tears masu ɗumi yau a rayuwa ko an ce da ita zata faɗo wannan mummunar dajin ba zata taɓa yarda ba sai dai ta ce mafarkin mai faɗar haka ne amma sai ga shi not in her dreams ba kuma wild thought ba reality real picture ɗin komai a kan idanun ta witnessing irin wannan abin tabbas zai bar mata psychological trauma da ba lallai ba ne ya fitar mata a kai ba.. "SubhanaAllahi me na ke gani haka kamar bokayen turai"? Wani elder daga cikin mutanin da suka shigo dajin ya furta haka sai ta ɗago kai ta kalli mutumin wanda zai iya kaiwa 57years a duniya ta kasa cewa komai ta yi nuni da hannun ta zuwa ga Dr Zaid da ke kwance kamar matacce da sauri mutanin suka yi kan sa suna salati maza uku ne suka cicciɓe shi dan jikin shi duk ya saki yayi wani irin nauyi toh dama banza da lada shi ɗin ba mai madaidaicin jiki ba ba ne he is huge very tall and a way giant a tsaye yake gadagam,haka suka ɗaga shi ana haska hanya suka fita daga dajin aka lallaɓa ta tana gaba suna biye da ita kuka sosai ta ke yi tana regretting zuwan su wannan outreach ɗin mai ɗumbin baƙar tarihi a kundin tarihin rayuwar su. Da abubuwa da yawa ta bar dajin nan na ɗaya shine ƙoƙarin kisan da Mudan ya so yiwa Dr Zaid,ga suspencting Asma'u da take yi da cewa ita ce ta nuna ma su Mudan motar su har suka far masu a dajin suka masu wannan aika aikar abu na ƙarshe da ta bar dajin nan da shi shine thought ɗin mummunar sakayyar da Asma'u ta saka masu da shi dan ita ta saka da a ce bata nuna masu motar su ba da babu yadda zasu yi tracing ɗin su har su aikata masu wannan abin yarinyar da ta yi sanadiyar guaruwar rayuwar ta ta ɗaura ta a hanyar da ya kamata yarinyar da Dr Zaid Maher ke mahaukacin ƙauna duk saboda ita ya shiga wannan halin duk saboda ita suka faɗa a wannan tarkon da aka ɗana masu sannan a ce same girl ce ta masu wannan abin?final abin da ke yawo a kan ta da zuciyar ta shine ƙaƙƙarfar tsana marar misaltuwa da goguwa akan Asma'u... Fitar su daga dajin aka saka shi cikin wata doguwar motar ɗeban kaya daga ƙauyen zuwa birni wannan motar ba na kowa ba ne face na mijin matar da ta sami annular detachment of the uterus da su Dr Zaid suka taimakawa aka mayar shi ne mai yawan kai kayan gona cikin gari in an kwashe dan haka a hanyar sa ta dawowa ne ya ga giftawar rickshaw ɗin su Mudan wanda ya san babu alkhairi a tare da su dan da ganin yanayin da suke ga budurwa tare da su babu wanda bai san da zaman ta'addancin su Mudan a ƙauyen nan ba dan haka bayan ganin tafiyar su ya dawo da motar sa baya har zai kutsa dajin sai ya ga wata motar wacce babu irin sa a ƙauyen sai dai in baƙi ne suka shigo da shi dan haka sai ya koma ya kirawo jama'an garin ya sanar da su abin da ya gani shine aka yi dandazo aka shiga dajin har dai Allah ya sa suka yi nasarar haɗuwa da su.. A ƙyar ta iya shiga motar dan halin da take ciki babu wanda zai iya fassara shi sai ita kaɗai da take cikin sa,. Bayan ta shiga motar ne mai motar ya koma daidai wun motar su Dr Zaid ɗin ya ɗauko wayoyin su dan dama motar a buɗe take ya rufe masu motar ya saka key ya dawo ya shiga motar da suke ciki ya rufe yana ta jimamin abin tare da tsinewa Mudan da yaran sa sauran mutanin da ke cikin motar ma duk suna alhinin wannan abin haka aka ja motar tana kuka tana kallon shi kwance muguwar tsanar Asma'u na daɗa bijiro mata. Har gidan mai gari aka kawo su a inda nan ɗin ma kowa cirko cirko a tsaye hankula duk a tashe an bazama neman su kawai sai suka ji tsayuwar mota a waje fita suka yi baki ɗayan su dan suna zaton motar su baby doctor ne sai dai suka ga babbar mota babu jimawa mai motar da jama'ar cikin ta suka fito da sauri suka nufo su suna tambayar ko nan ne inda su likitocin birni ke zama cikin gaggawa suka amsa sai ya nuna masu motar da sauri suka yi motar suka gan su ciki a hargitse tun ma ita da ke ta hawaye babu kuka mai sauti. Fito da shi aka yi daga motar toh ƴan ƙauye me suka sani kawai suka yi cikin gida da shi Hindatu ce ta riƙo ta ta fito da ita daga motar tana kuka jikin ta duk ya gama sanyi aka yi cikin gida da ita kawai tafiya take yi zuciyar ta na ayyano mata abubuwa kala kala mutumin da ya kawo su ne yayi masu bayanin abin da ya faru ya miƙa masu wayoyin su baby doctor da ke hannun sa godiya sosai suka ma mutanin kafin daga bisani suka koma cikin gidan ana ta yaƙin yadda za'a yi a farfaɗo da shi ita kuwa da shigan ta ciki ta miƙawa Hindatu hannu alamun ta ba ta wayoyin da sauri ta miƙa mata haka tana layi wani iri ta shiga cikin toilet ɗin zulfa'u ta zauna a ƙasa duk bata hayyacin ta kira ta yida wayar shi ita kanta ba za ta iya cewa ga takamammen numbern da ta kira ba sai jin murya ta yi ana cewa "My boy ina ka sami service da daren nan a ƙauyen nan na ku"cikin farinciki aka yi maganar wanda ba kowa ba ne face Dr Maher mahaifin Zaid. Jin muryar shi sai ta fashe da kukan da ta daɗe tana so ya zo mata sai rerawa take yi tana shesheƙa jin haka duk sai Dr Maher ya ruɗe ya shiga kiran sunan ta "Baby doctor me ke faruwa ya na ji kamar kina kuka me ya faru ina shi Zaid ɗin"?kasa amsa mai ta yi kawai sai ta fara cewa "Abba.... Abba... Abba!!Zaid Zaid Abba Zaid.... "Daga haka wayar ya sulale daga hannun ta ta faɗi ƙasa sumammiya...........Cigaba da kira yayi but bai ji an ɗaga ba jin kiran yayi yawa ne ya sai ya janyo ra'ayin jama'ar gidan suka shigo suka gan ta kwance ƙasar toilet ɗin sume kamar marar rai da sauri suka shiga yayyafa mata ruwa amma inaa bata farfaɗo ba kira ne ya kuma shigowa wayar da sauri zulfa'u Ta ɗauki kiran inda a nan ya shiga tambaya ba tare da ya san ba mai wayar ne ya ɗauka ba+ "Baby doctor me ya faru ? ina my boy"? sai ya jiyo muryar zulfa'u inda a nan ta ke sanar da shi abin da ya faru wanda hakan ya rikitar da Dr Maher har ya kasa cewa komai ya sauke wayar daga kunnen sa. lokacin ne baƙin ciki ya ziyarce su dan daidai lokacin da tayi kiran gabaɗayan su suna cin dinner toh jin yana ta cewa baby doctor me ya faru ina my boy sai gabaɗayan su suka kasa cigaba da cin abincin kiran layin ya rinƙa yi amma ba'a ɗaga hakan ya kuma ɗaga masu hankali tashin hankalin ma sai da ya sanar da su abin da ke faruwa ai kuwa Hajiya Madina ta shiga tashin hankalin da bata taɓa hasasowa ba a rayuwar ta ɗan ta da ta fi so ɗan da ta fara daga kan shi ɗan ta wanda bata iya ɓoye son sa ko da kuwa a gaban waye duk ta fita a hayyacin ta ganin ana ta kira amma ba'a ɗagawa sai da Hajiya Zeenat ta riƙe ta ta shiga gaya mata sanyayyun kalamai duk dan ta yi calming ɗin ta bata sami sukuni ba.. _Two weeks back_ "Me ya faru da yaran nan me ya same su ina suke"?duk sai hankulan su ya koma kan wayar da yake yi suddenly suka ga ya koma ya zauna kamar an zare mai laka a jikin sa duk sai suka kuma shiga duhu da ruɗu kasa cewa komai suka yi sai da prof yayi ƙarfin halin tambayar sa "Dr me ke faruwa ne ina yaran me ya same su halan"??. Kasa basu amsa yayi sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ce "Zaid ya sami attack presently daga shi har Bilkisu ba su cikin hayyacin su what should we do Dr"?tsit wurin yayi babu wanda ya iya cewa ƙala har tsayin lokaci kafin daga bisani Hajiya Madina ta tsinci kan ta da zubda hawaye masu ɗumi da raɗaɗi,riƙe ta Hajiya Zeenat ta yi ta ja ta suka bar wurin tana mai kwantar mata da hankali dan ita kanta ƙwarin gwiwar take buƙata her baby isn't in good state ga shi wanda yake kamar guardian angel ɗin ta ma baya cikin full senses ɗin sa bare a ce in wani ya kwanta wani zai tada wani. A haka suka zauna cikin jimami da zullumi yayin da Dr Muhammad Sulaiman ya gwada kiran layin baby doctor sai dai bai shiga ba sai ya kira layin Dr Zaid a nan aka ɗaga aka sanar da su cewa har lokacin fah basu farfaɗo ba sai hankalin sa ya tashi ya ce da su su yayyafawa Bilkisu ruwa dan kaf ƙauyen babu wanda zai iya da present condition ɗin Dr Zaid sai dai ita ɗin bayan wasu lokuta ya kuma kira aka sanar da shi cewa bata farfaɗo ba still a nan ne hankali ln sa ya kuma tashi ya kashe wayar ya fita kusan rabin hour bai dawo ba sai chan ya dawo cikin hanzari ya tarar da Dr Maher still zaune a inda ya baro shi a matsayin sa na uba ya san current state ɗin da Dr Maher yake ciki ba sai an sanar da shi ba dan haka sai ya zauna kusa da shi ya ɗan taɓa shi A hankali ya juyo tsantsar tashin hankali ne ya fito ƙarara a kan fuskar sa sai ya ce da Dr Muhammad Sulaiman "Prof ya a ciki yanzu da yaran nan?mu ya kamata mu kasance makusa da su amma mun baro su cikin wani halin muna nan wata duniyar wa zai kai masu ɗauki"?sai yayi shiru cikin wani yanayi hakan ya ba ma Dr Mahmud damar yi mai magana "Dr ka daina saka wani damuwa a ranka dan yanzu na gama booking mana flight zamu bi jirgin ƙarfe 8 na dare there is still time but kafin nan na na saka Lukman tafiya garin dan ɗauko su shi da jibril" Interrupting ɗin sa Dr Maher yayi ta hanyar ce mai "Prof me yasa zaka saka su fita ka san dai dare ya rigada yayi a chan sosai kuma hanya ba lallai bane ya yi kyau". Ɗan murmusawa prof yayi sai ya ce "Dr kar ka damu by air zasu yi tafiyar kuma daga nan direct city hospital zasu fara kai su kafin mu koma gida sai a san where out"rungume sa Dr Maher yayi ya ce da shi "Thank you prof you are a friend am greatful"hugging ɗin sa back prof yayi kafin daga bisani ya ce da shi "We have to inform them abin da ake ciki ko hankulan su zai kwanta"girgiza mai kai yayi suka miƙe suka nufi apartment ɗin su inda suka iske matayen na su a nan suka sanar da su abin da ke faruwa dan haka suka shiga shirin komawa 9ja duk a hargitse suke da an gan su za'a gane cewa kwanciyar hankalin su ya ƙaurace ya kau,shirin gaggawa suka yi babu ɓata lokaci suka isa airport ɗin babu natsuwa a zukatan su a haka jirgin su ya tashi daga ƙasar London zuwa ƙasar Nigeria... °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° A nan gidan mai gari kuwa ganin ba farfaɗowa zasu yi ba sai ɗaya daga cikin ɗan mai gari yayi hikimar karbar wayar Dr Zaid ya shiga contact list ya fara duba sunan abokin aikin Dr Zaid ɗin wato Dr hussain wanda shine mammalakin motar da suke ta yawo a ciki ko da ya buga sai ya shiga amma ba'a ɗaga ba sai da ya tsinke ya kuma dialing amma aka kashe sai aka yi calling back da sauri ya ɗaga wayar yana ɓarin baki ya ce "Ranka ya daɗe dan Allah ka taimaka ka zo ka taimaki rayukan likitocin mu sun fita lafiya ƙalau amma aun dawo duk kamar babu mai rai a cikin su dan Allah ka yi gaggawan zuwan"!! Toh dama dalilin da ya sa shi muktar ya san Dr Hussain shine ranar farko da Dr Zaid ya tafi kai mai ziyara da suka zo garin shi da matar sa tare suka tafi da muktar ɗin kuma a labarin da yake bashi shine shi Dr Hussain ɗin abokin aikin sa ne though ya bar hospital ɗin su kasancewar shima ya fara running nasa hospital ɗin amma sti ana mutunci da juna,toh wannan shine dalilin da ya sa nuktar ya san Dr Hussain kuma abin da yasa ya gane sunan shi a contact list shine times without number ya sha ganin lambar da sunan har da dai ma ba bokon yayi ba bare ya gane amma kullum in suna hira ya ga Dr Zaid ya kira lambar toh ya san da Dr Hussain suke magana yau da gobe sai ya gane kuma dama shima yama da ƙaramar baby nokia so he is familiar with contact list kuma a hausance yakan yi saving numbers. Jin hakan duk sai Dr Hussain ya ruɗe ya kasa zama har dai matar sa ta tambaye sa me ke faruwa a inda ya ma kasa sanar da ita sai dai ya ce mata ta rufe gida shi zai je ya dawo dan abokin sa da abokiyar aikin abokin na sa suna cikin wani hali dama da gidan su a ƙauyen kasancewar hali irin ta fulani ba su wani samin damar sakewa in sun zo hutu saboda kunya shi kuma ba mai kunyar ba ne dan haka ya ga cutuwa yake yi sai kawai ya sa aka fara yi mai gini a ƙauyen far from gidan surukan na sa toh a nan suke hutu in sun zo ƙauyen. "Dr in rufe ƙofa ko dai in biyo ka"?ta faɗa kamar zata mai kuka sai ya ce "A'a ba biyo ni zaki yi ba dan babu mota abin hawa zan shiga bana son ki fita ki zauna a gida kawai and make sure you lock everywhere humm"?sai ta girgiza kai dan bata saba da jan magana ba in bata umarni. Rako shi tayi har bakin gate ɗin su da ya fita ta koma ciki ta rufe tana mai addu'ar Allah ya kai sa lafiya ya dawo mata da shi lafiya dan zuwa lokacin 9 na dare yayi ga tsoron fitar na sa ga tsoron zama ita kaɗao sai abin ya mata yawa ta kasa kwanciya ta dawo parlor da wayar ta a hannu tana duba time.. Da kyar ya sami rickshaw ya tsare ya mai kwatancen inda zai tafi tiryan tiryan ya kai sa y biya shi kuɗin shi ya fita ya shiga cikin gidan inda ya ga jama'a cirki cirko a tsakar gidan da sauri ya tambaye su inda Dr Zaid yake nuna mai ɗakin sa suka yi bai tsaya ɓata lokaci ba ya shiga ɗakin ya gan shi kwance kamar marar rai shi kan sa ba dan likita bane wanda aka kira akan ya bada taimako ba toh baya jin zai iya taɓuka wani abin dan with the physical eye examination da ya ma Dr Zaid ɗin baya jin zai iya concluding cewa Dr Zaid is still existing but he have to put himself ya samo mafita dan haka fita yayi ya tambayi car key ɗin aka miƙa mai ya ce a saka baby doctor a motan kafin su fito da Dr Zaid hakan aka yi dan har lokacin bata farfaɗo ba sai aka saka ta a front seat shi kuma da muktar suka ƙoƙarta suka fito da shi aka buɗe back door suka saka shi ya rufe ya shiga gaban motar kafin ya tayar da motar ya ce da su "Ku harhaɗa masu kayan su zan dawo in kwashe dan muna zuwa asibitin zan bar su in tafi tare masu jirgi dole su bar garin nan a yau ɗin nan"!..ya ja motar yayi gaba dan shi tun farko bai yi supporting Dr Zaid ɗin ba akan kawo outreach ɗin nan ba dan ya sanar da shi ƙauyen akwai haɗari sosai ta yadda mutum ba zai taɓa tsammani ba gashi nan yanzu sun faɗa a tarkon ƴan iskan gari dan yana da tabbacin ƴan iskan garin ne suka masu haka saidai shaf ya manta ya tambayi wanda ya masu wannan abin nevertheless in ya koma karɓo kayan su zai tambaya dan babu abin da zai mayar da su dajin nan sai dai a history dan ko su da ke ƙauyen akwai tazara sosai tsakanin gidan su da na mai gari. Yana jan motar yana ta tunane tunane sai ya ga wayar Zaid ɗin na blinking ya kai duban shi sai ya ga an saka 'Lil bro Luk' bai san ko wanene ba sai ya ɗaga wayar ya kara a kunne "Assalamu alaikum"yayi sallama sai aka amsa mai "Wa'alaikumul salam please ina yaya Zaid"?aka yi tambayar still bai gane mai maganar ba sai ya ce "He is safe yanzu ma asibiti zamu tafi ni abokin aikin sa ne sunana Hussain yanzu ake sanar da ni abin da ya faru kuma nima ina gida mun zo hutu shi yasa na yi hanzarin tafiya ɗauko su yanzu zamu tafi city hospital ɗin Yola daga nan zan tafi booking masu flight dan bana so su kwana a garin nan" Ajiyar zuciya Lukman yayi daga ɗaya ɓangaren kafin ya ce "Mun gode sosai ɗan uwa dama fligt ɗin anjima zamu bi mu zo ɗaukan su daga nan mu dawo gida nut since kai kana nan ina ga sai dai mu yi booking masu jirgin Germany dan na san a yadda aka ce an yi attacking ɗin shi ɗin nan Ammi ba za ta yarda a yi treating ɗin shi a nan ƙasar ba ga kid sis ɗin mu duk an ce itama bata farfaɗo ba ina ga tafiyar su chan zai fi". "Eh toh kai sai ku fara processing masu visa ni kuma zan yi na nan dan abin ya mana sauri"ɓoye mai gaskiyar lamarin yayi dan da zuwan shi ya ɗag kan Zaid ɗin sai ya ga wurin yayi swelling alamun akwai internal bleeding profuse bleeding ma ba kaɗan ba hakan na nufin duk inda aka kai aka komo ba zai farfaɗo nan kusa ba that is in an yi nasarar saving life ɗin shi,sanar da family member ɗin Dr Zaid ɗin da ya kira ba zai taimaka ba instead discouraging zai janyo sai yayi shiru kawai ya bari akan in sun isa chan asibitin a basu taimakon gaggawan da za'a iya kafin ya gama processing komai that means har shi kan sa da matar sa have to leave that same night.. Bayan kamar mintuna arba'in suka iso cikin wani asibitin gari though ba shi ne babban hospital a town ɗin ba amma shine nearby hospital dan haka shiga yayi ya nemi taimakon ma'aikatan aka zo aka ɗauke su aka yi ciki da su zasu fara yi mai surutan police report ya nuna masu licence ɗin sa na Dr ya kuma sanar da su in basu yi sun taimake sa ba yana iya rasa ran sa kuma alhaki a hannun su sannan zasu amshi sammaci daga kotu dan iyayen shi ba zasu bar asibitin ba jin haka suka fara ƙoƙarin su da ya ga sun fara sai ya sako masu labarin abin da ya kawo su ƙauyen da irin taimkon da suka bayar sai hakan ya saka su ƙara himma suka cigaba da aikin taimakon gaggawa daga nan ya sanar da su yana zuwa ya fita ya wuce ya shiga motar sa dare ne dan 10 yayi a lokacin gudu sosai yake ta shararawa har ya isa inda yake son tafiyan bai ji da sauƙi ba dan da ƙyar ya samo visa ɗin mutani huɗu ta POS aka yi komai ya kamo hanya ya dawo gidan mai gari dan kwashe kayayyakin su a nan ya tambayi wanda yayi wannan ta'asar suka sanar da shi sai ya girgiza kai kawai ya wuce suna tambayar sa jikin su sai ya ce shima bai sani ba dan haushi ne ke cin sa sosai ya daɗe yana jin labarin wannan tsagerin Mudan ɗin toh kuwa tunda ya taɓo ɗan gwal zai yi da ya sanin rashin sa'ar sa a duniya dan ya san yadda mahaifiyar Zaid ke ji da shi ɗin nan sam ba zata taɓa ɗaukar wannan shashancin ba sai ta sa an hukunta mata yaron. Daga nan gidan shi ya wuce inda tausayin matar ta sa ya kama shi dan idanun ta duk a kumbure suke alamun dai kuka tayi bayan tafiyar sa ai kuwa tana ganin ya shigo ta miƙe da sauri ta rungume shi ta sakar mai kuka a yanayin da yake ciki shi kan shi kukan ne sauƙin zuciyar sa amma bai bari yayi ba sai ya rarrashe ta ya ja ta zuwa bedroom ɗin su ya zaunar da ita ya ɗauko mata hijabin ta ya saka mata ya ɗauko masu jakar tafiya ya shiga shirya masu kayan su cikin sauri ita dai bin shi da ido take yi dan ta kasa tambayar sa me hakan ke nufi har dai ya gama ya janyo jakar zuwa gaban ta ya riƙo hannun ta ya miƙar da ita tsaye ya ce da ita "Sweetheart am so sorry zamu koma gida my friend is in serious pains da asibitin garin nan ba zasu iya da shi ba in kuma muka yi delaying toh muna iya rasa sa"jin haka sai ta waro idanun ta waje sai ga hawaye saurin share mata yayi ya ce "Is okey Allah zai bashi lafiya"daga haka ya rungumo ta ta gefe suka fito gyara parking ɗin motar yayi suka fito a ciki ya rufe masu gate ɗin suka fara tafiya.. ********** Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya ce "Big bro akwai wanda ma yayi aikin da zamu tafi yi a chan"sai ya ɗago ya kalle shi yana jiran jin ƙarin bayani. Zama yayi ya sanar da shi komai sai ya miƙe tsaye ya ce da shi "Ba matsala ka zauna a gida saboda bana so Bilal ya sani kar hankalin sa ya tashi ni zan tafi in fara processing masu tafiyar"amsa mai yayi kafin su rabu ya wuce gida a inda nan ma ya tarar da matar sa duk hankali tashe ga Zarah ta ƙi barci sai rigima take yi ko da ya shigo sanar da ita yayi abin da ke nan ya kuma ce mata ta kwantar da hankalin ta shi zai tafi dan ya fara processing masu visa dan ya san ko su Abba sun dawo abin da za'a yi kenan instead of delaying is better ya fara kafin su dawo ɗin dan su ma suna hanyar dawowa. Kuka sosai ta yi dan gabaɗayan su wato Dr Zaid ɗin da Bilkisun nata ne shi abokin mijin ta ita kuma ƙanwar ta ƙanwar mijin ta.lallaɓata dai yayi akan ta rarrashi Zarah ta yi barci kuma kar ta tsaya jiran sa su kwanta jin shi kawai ta yi amma ba iya kwanciyar zata yi ba ga yarinya ta dage sai Baban ta ya ɗauke ta shi kuma duk hankalin sa baya jikin sa dan ya rasa me ke mai daɗi a hakan ma ba'a faɗa masu ainihin labarin ba kenan ina ga sun ji root ɗin batun.. A daren nab ya tafi yayi booking masu flight ɗin washegari ya dawo guda very late gabaɗaya family ɗin Dr Maher Mahmud ba'a sanar da su abin da ke faruwa ba except Afzal da ya san labarin pneumonic crises ɗin baby doctor a jiya shima ban da wannan bai san komai ba ko Hakim da yayi waya da yayan nashi bai san komai ba apart from that.babban yaya ne ya hana a sanar da family ɗin Dr Zaid abin da ke faruwa har sai in sun dawo gidan wato jamil... **************** Da isar su bai tsaya wata wata ba ya ce da matar sa ta jira sa yana zuwa haka ta zauna a motar cikin fargabar ko sun farfaɗo ko basu farfaɗo ba da ya shiga dai duk labarin jiya ne dan kuwa kawai first aid treatment suka yi rendering amma babu wanda ya farfaɗo a cikin su a cewar su ma shi Dr Zaid ɗin da aka samu aka ɗan ɗauko hanyar saita numfashin sa sam abin ya rikice masu dan suna da ƙarancin likitoci so the available doctors around su suka yi iya ƙoƙarin su... Bai tsaya jin wani dogon turancin su ba ya ce su saka su a ambulnce car ɗin su aka taimaka aka saka su yayi masu transferring kuɗin su suka fito sanar da security ɗin yayi akan zai yi parking motar sa a nan ya kwana zai dawo bayan kwanaki uku ya ɗauka,fitowa matar sa tayi suka shiga cikin ambulance car ɗin yayi driving ɗin su zuwa airport cikin gaggawa suka fitar da su suka shigar cikin jirgin babu ɓata lokaci jirgin ya gama cika da travellers daga haka suka lula... °°°°°°°°°°°°°°°°°° Sai 7:50pm jirgin su Dr Maher yayi landing dan suna hanya suka dakata saboda yanayin whether ruwa na iya farawa babu notification basu cigaba da tafiya ba har dai da ruwan ya tsaya ko ina ya zama stable. Already jamil ya isa airport ɗin tare da Lukman sun tafi ɗauko iyayen na su already jirgin su baby doctor ya iso tun safe har an ɗora su a intensive care ana jiran dawowar iyayen dan su gana kafin a tafi da su germany ɗin. Rungume Abba Lukman yayi yana ƙoƙarin danne damuwar sa dan tun daren jiyan nan kawai sha'ani aka yi toh tsinkewar lamarin shine yau da suka iso ganin condition ɗin su sai ya sakar mai da jiki ya kasa taɓuka komai dan ƙulle kan sa yayi a ɗaki ya yi kuka ba kaɗan ba mai rarrashin ma jamil bai iya ba dan duk ya shiga ruɗu ganin aminin sa cikin halin life and death ga baby sis ɗin sa cikin temporal lost of consciousness abin bai zo mai a sauƙaƙe ba,ƙwararrun doctors aka kawo gidan a nan aka gano ainihin abin da ke damin sa da abin da ke faruwa a kan sa dan already akwai wuraren da suka sami damage a kan na sa ita kuma baby doctor ta shiga temporal comma ne sakamakon shock ɗin da ta shiga as result of violence ɗin da ta yi witnessing wanda ake saka ran zata iya farfaɗowa any moment from then dan haka na ta da sauƙi amma shi na shi ne sai an kai shi higher facility wanda ke da ƙwararrun likitocin kwakwalwa da zasu iya ɗora Dr Zaid ɗin a kan kula mai tsanani ita kuma ko a gida za'a iya cigaba da bata kula sai dai babban yayan ta ya ce a'a bai amince ba tare za'a kai su a basu kula mai kyau toh tun lokacin ne basu sami kan su ba tun da Bilal ya dawo daga ziyarar da ya kai office kasancewar ranar lahadi ne ba aiki sai ya tafi rage aikin monday ko da ya dawo gidan sai ya ga mitoci ba iyaka duk a tunanin sa iyayen su ne suka dawo sai ya ji mamaki dan ya san holiday ɗin na su bai ƙare ba toh me ya faru? Haka dai ya ƙarasa ciki sai ya ga ana zazzaune jigum kamar ana zaman makoki sai ya ruɗe ya shiga tambayar me ke faruwa ga matar yayan sa a gida aunty zee itama cikin wani yanayin take sai ya dumfari yayan sa jamil ya fara tambayar sa ba'asi.rungume shi kawai ya iya yi yana petting bayan shi dan tausayin sa yake ji apple ɗin sa na cikin halin ƙila wa ƙala daɗa dulmiyawa shi yayan na shi yayi dan haka ya ɗago ya ce da shi "Big bro me ke faruwa ne wai na ga kamar gidan ba'a cikin walwala"!!. "Bilal it's your apple"!! Ai sai ya ji kamar ba a jikin sa ya ke ba apple?what about apple?me ya same ta?a ruɗe ya kalli yayan na sa ya ce "What about apple?me ya same ta"? Riƙe sa Lukman yayi ya ce "Calm down kid bro calm down"fincikewa yayi ya ce "How can i calm down yay Luk?how?it's about apple"!!ya ida yana mai zazzaro wa yayan na sa idanu kamar zai dake sa ba laifi Bilal akwai zuciya sai dai ba kasafai yake yi ba sai in tura ta kai bango dan haka babban yayan dai shine ya riƙo sa ya yi supporting ɗin sa zuwa ɗakin baby doctor. Komawa da baya yayi ya jingina da bango yana kallon twin sister ɗin sa kwanaki biyun nan sam baya jin daɗin jikin sa kawai shiru yake yi bai sani ba but yana ta having strong feelings very strange feelings marasa kyau da bai san dalili ba could it be this?why his apple?sai ga Bilal na kuka kamar ƙaramin yaro a hakan bai ga brother in-law ɗin sa ba kenan. Rungume shi yayyen na sa suka yi suna rarrashin sa kasa tambayar ba'asi yayi sai kuka. Da ƙyar ya natsu ya sarara da kukan da yake yi a nan yayyen shi suka sami attention ɗin sa suka sanar da shi abin da ya faru kasa motsawa yayi haka ya cigaba da zama a wurin.. A ɓangaren su Bahajjatu kuwa tashin ta da safe ta yi mugun gani dan around 9 na safe ta tashi sai ta yi tozali da yayan ta Hakim yana ta shesheƙa duk tunanin ta ya tafi akan iyayen su ne wani abin ya same su shaf bata yi zaton yayan ta ne ba dan ta san lokacin tafiyar su bai yi ba kuma a jiya misalin uku da rabi na yamma suka yi waya da Bilkisu dan haka sam bata saka a ran ta cewa har sun dawo ba. Abin da ya firgitata shine lokacin da ta yi arba da yayan ta rai a hannun Allah sam baya numfashi kamar yadda ya kamata sai ta zube a wurin ta shiga zabga kuka kamar wacce ta rasa iyayen ta her brother Hakim have to take her out of the roon saboda irin loud cry da take yi she couldn't take ot out of her head wai yayan ta ne da gaske ke kwance kamar ba mutum mai rai a jikin sa ba.. Kiran Bilal ne ya shigo wayar ta ko da ta gani sai ta kasa ɗauka dan haka ya cigaba da kira har dai ta ɗauka ta fashe mai da kuka mai taɓa zuciya gabaɗaya babu mai rarrashin wani dan daga gidan Dr Muhammad Sulaiman har nan gidan Dr Maher Mahmud kowa na cikin halin kusan grief na abin al'ajabin da ya same shi. Har daren nan suna a haka until when Lukman ya sanar da yayan sa akan su tafi airport ɗauko iyaten su dan by then jirgin su na iya landing shine suka taho airport ɗin.. Ɗaga shi daga jikin sa yayi yana tambayar sa inda yaran suke cikin sakewar jiki suka sanar da su a nan suka ranƙaya suka tafi gida dama Dr Hussain ne ya ke kula da Dr Zaid ɗin yayin da aka gama bashi immediate care ɗin da ya kamata matar sa na guda dan tun da suka iso bai tafi gida ba matar sa cr ta tafi gidan kuma sau uku tana zuwa duban su kafin daren su tafi tare da shi akan anjima zai dawo in za'a tafi da su Dr Zaid.... Da suka iso gida lamarin ba'a cewa komai dan Hajiya Madina kasa furta komai tayi ta yi shiru duk tsoron duniya ya gama cika ta ta rasa ta ina zata fara an yi nasarar tsayar da external bleeding ɗin toh internal bleeding ɗin fah?internal damages ɗin da aka yi wa internal structures ɗin kuma fah?who could possible do this to their children?da waɗannan tambayoyi a ran ta ta cigaba da zaman kallon ɗan ta wanda kaf wurin ba wanda bai ji tausayin ta ba sai marar imani..1 Possible communication Dr Muhammad Sulaiman ya rinƙa yi har dai ya sami current hint akan cewa babban likitan da ya kamata ya ga Dr Zaid ɗin baya nan ya yi tafiya kuma ba dawowar nan kusa ba sai bayan sati biyu dan haka an basu hanyoyin da zasu bi dan kula da marasa lafiyan har lokacin da Dr ɗin zai dawo dan kai shi wani ƙasar baya tsarin su they believe more akan german Dr ɗin dan ya san aikin sa sosai shi yasa suka amince zasu cigaba da kula da shi a gidan har Dr ɗin ya dawo.. Komai da ya ke gudana a gidan na jin daɗin rayuwa ya tsaya masu cak ga Bilkisu sai dai ta farfaɗo na mintuna kaɗan ta koma na ta ma da sauƙi akan na Dr Zaid da tun da aka ɗauko shi in banda allurai da ake ɗura mai sai body care da ake mai sam baya sanin ana mai ɗin dan yanda aka ɗauko shi haka yake har tsayin two weeks ɗin nan... *********************** Bahajjatu ce zaune tana kallon Bilkisu kamar ta kira ta ta amsa sai dai ba halin yin hakan,hawayen da ya gangaro mata ta goge dan bata san ranar gogewar baƙin cikin nan na su ba ga chan yayan ta kwance nan babbar aminiyar ta twin sister ɗin saurayin ta na kwance bata san dama da hagunn ta ba sai dai a juya ta.. Tana tunanin nata sai ta ga an fara fita da kayan su alamun tafiyar dai za'a yi da su share hawayen ta tayi yayin da Hajiya Madina ke zaune cikin ɗakin ta sai risgar kuka take yi dan har lokacin ta kasa tantance shin da gaske ne wai ɗan ta na kwance bai san kan shi ba har tsawon sati biyu ba kasa rakiyar tayi sai dai Hajiya Zeenat da ta yi dauriyar tafiya tare da su Dr Maher da Dr Muhammad dan su ne zasu tafi tare da yaran chan ƙasar kafin daga baya iyaye matan su biyo su... Ko da jirgin su ya tashi Hajiya Zeenat ta dawo gida kasa shiga gidan aminiyar tata ta yi dan ita kanta tana buƙatar samin sararin fitar da heaviness da ke chest ɗun ta fir the past 2weeks ɗin nan dan bata sami space ɗin zubar da hawaye ba sai a ranar dan haka bata bari kowa ya san ta dawo gidan ba ta ƙille kan ta ta shige toilet ɗin ta shower ta kunna ta shiga yin kuka mai cin rai suna zaman zaman su na jin daɗi da kwanciyar hankali outreach ɗin nan yayi interfering,ƴaƴan su duka na cikin mawuyacin hali halin dilemma halin rai ko mutuwa wannan masifa da me yayi kama,chan gidan Dr Maher Hajiya Madina na kan risgar kuka nan ma gidan prof Hajiya Zeenat na nata kukan ƴaƴan su duk sun rasa sukunin su suma dan daga azumi sai ibada babu wani rayuwar farinciki da suke yi dan suna gani farincikin ya ƙaurace masu kenanhar abada tukunna ba ta kan criminal ɗin suke ba ta lafiyar ƴanuwan su suke kafin su koma kan wanda ya janyo masu wannan baƙar tarihin....................

0 Comments