IYA RUWA FIDDAH KAI CHAPTER 5

IYA RUWA FIDDAH KAI CHAPTER 5
Fincike hannun sa yayi daga nata da suka shiga ɗakin ya na mazurai maganar dai bai yi ba ita kuma bata fasa haɗe fuskar da ta ke yi ba.zama yayi yana nazarin ta but me yasa take mai haka?ɗazu da safen nan ta zo ta hau nurse da faɗa ta kirawo wata kafin su fita dan ta bashi magani amma ta hau matar da faɗa and now....this nice woman Ms Mcsantos again tana gaya mata and she is comfortably saying basu buƙatar compliments ɗin ta again she claims to be he spouse why is she doing all these?babu wata wata ya shiga buɗe mata wuta+ "Bilkisu wacece ke da har zan rinƙa mu'ammala da mutani kina son datsewa?wacece ke da har zaki rinƙa underestimating min dignity a gaban jama'a kai tsaye?ko dan kin ga na sake miki fuska ina maki shiru ne ya sa kike ɗauk na for granted?saboda kin ga ina binki da kallo bana maki magana ya sa kike kallo na kamar wawa?ko dan kin ga am hospitalized shi yasa kike mim kallon rascal?tell me me dalilin ki na min shishigi"?da ɓacin rai ya ƙarasa maganar dan shi bai ga dalilin da zai sa ta raina sa ba ko da kuwa saboda disability ɗin sa ne na rashin lafiyar da ya ke ciki. Cikin halin ko in kula cikin halin damuwar ka ne wannan ta kalle sa ido cikin ido ta ce "Ni ban hanaka mu'ammala da mutani ba da mata na hanaka matan ma matan turawa da baka san su ba baka haɗa wata alaƙar jini da su da su nake hanaka mu'ammala dan ubangiji ma bai lamunce maka da yin mu'ammala da wanda ba muharramin ka ba ciki kuwa har da waɗannan masu fuskar shanun dan ita ɗin ai ba muharramar ka bace arniya ce tana iya jan ra'ayin ka you mever can tell ka ga ka aikata laifi babba dan sai da aka ce 'La taƙrabul zina' kar ku kusanci zina and that woman...that os exactly what she is trying to induce you to do using her child as her entry point ni kuma ba zan so Allah yayi fushi da kai ba ka ga ai ban da laifi dan na taya ka kuɓutar da kanka daga shiga kaifin arniyar baturiya.sannan ni bana underestimating maka dignity ina ma rising maka dignity ne dan duk responsible man in ya kalle ka ya san kai ɗin ɗan gidan masu hankali ne zai ji takaicin ganin ka kana zubda mutuncin ka a bainar jama'a shi yasa na hanaka cigaba da hirar da kake yi da matar kuma ni bana ɗaukar ka for granted kawai dan ina tausaya maka ne shi yasa nake hana ka mu'ammala da matan turawa haka zalika ni bama ɗaukan ka a wawa dan kai ɗin miji nane akan me zan maka kallon wawa,kuma ni ma nan ai i was hospitalized kuma har yanzu ban gama warwarewa ba dan haka in saboda in har dan baka da lafiya ne ya sa kaje ganin kamar ina ɗaukar ka a rascal then nima maybe haka kake kallo na dan nima ai patient ce finally ba shishigi nake maka ba as a responsible wife haƙƙi nane kare ka daga faɗawa a cikin ko wani irin sharri ko halaka dan haka you owe me no explanation"... Kamar an dasa sa a wun haka ya koma bai yi tsammanin zata bashi amsoshi daki daki kamar yadda ta bashi yanzu ba dama ta iya gasa magana haka ne ko dai dan shi ne da ta raina??. Ko a jikin ta ta yi kamar zata durƙusa ta cire mai takalmin sa sai kuma ta fasa ta tashi tana mai kallon ƙur idanun ta na nuna alamun wani gagarumin magana "You know what??just undress yourself i guess you are now physical and mentally fit....goodbye Dr Zaid Maher"...daga haka ta juya a zuciye tayi tafiyar ta lo waigo sa bata yi ba ita fah danne zuciyar ta take yi da attitude ɗin da yake bata haka kawai tana kan nemawa kan ta lafiya kawai dan tana tausaya mai sai ya rinƙa mata wani gani gani dan ma ya gode su Ammi da Umma sun yi convincing nata kan ta aure sa if not me ma zata yi da shi... Tsaƙi ta ja a yayin da ta hankaɗa ƙofar ɗakin ta ta shiga sai kumbure kumbure take faman yi,wurgi tayi da gyalen ta a kan gadon ta kwanta da full force tana sauke ajiyar zuciya for a while tana a haka sai can ta fara hasashen fuskar wannan baturiya sai ta shiga jero tsaki ba iyaka ƙarshe dai ɗauko wayar ta tayi ta yi dialing numbern Baha ba'a ɗauka ba sai ta laluɓo na Abban ta dan tun kusan kwanaki uku kenan rabon ta da ji ko ganin sa. A karo na biyu ya ɗaga yana mai teasing nata dan su babu ruwan su da wata kunyar ƴaƴa da iyaye they are well socialize akwai wani babbar jituwu tsakanin iyayen da ƴaƴan su wanda ya sa ƴaƴan basu da aminai sama da iyayen su dan sukan buɗe ma iyayen damuwar su hakan kuma shi ke janyo jituwa mai ƙarfi a tsakanin.. "My baby Mrs Zaid Maher how are you doing over there"!??? bata bari ma ya sauke numfashi ba ta ce "Abba am sick and tired of what Zaid is doing to me can you believe that yau na fitar da shi zuwa park da ke nan bayan asibitin ya taƙarƙare yana ta faman zuba hira da matar turawa wata mummunar mata wai dan na hana sa cigaba da kwasar zunubin da ya ɗauko hanyar yi shine kawai ya rinƙa buɗe min wuta wai ina mai shishigi can you believe this Abba wallahi shi yasa na ƙi yarda da auren nan tun farko dan gudun rana irin ta yau amma su Umma da Ammi sun ƙi sauraro na"!!ta ida kamar zata yi kuka.. Ga mamakin ta coz ta zata sympathising zai yi da ita akan abin da Zaid ya mata sai dai kuma ta ji muryar sa yana dariyar manya sai ta ji mamaki toh ita me ta yi da yake mata dariya she reported Zaid to him at least he should sympathize with her and not laughing at her. "Baby yanzu dai me kike so a yi dan na ga kamar kin haura sama da yawa"!!sai ta tsinci kan ta da sakin kukan sakalci "Abba so nake ka mai faɗa ya daina yin abin da Allah ya haramta wallahi Abba kasa gayawa mai fuskar shanun nan ni matar sa ce dan bai ɗauke ni a matsayin matar sa ba"kuka take sosai sai abin ya daɗa ba Abban dariya ƙarara kishi ke ɗawainiya da ƴar sa amma bata sani ba sai ya ce "Baby na ji zan mai faɗa yanzu dai na san kin yi fushi kin bar sa shi kaɗai toh ina so ki koma ki ko baki mai magana ba ki dai zauna in kin ga yana buƙatar wani abin me sai ki taimaka mai da shi kin ji"!?kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce "Fine Abba amma ka ja mai kunne dan yana aikata haramun"!!abin dariya sai dai bai yi ba ya share ya ce "Good baby sai kin ji ni"da toh ta amsa mai kafin ta tambaye sa inda Umman ta take "Zata kira ki gobe baby we are busy right now"shaking kai tayi mai hali baya fasawa watoh for the period of their hospitalization iyayen sun natsu amma yanzu da suka tabbatar sun farfaɗo sai suka koma jin daɗin su. "Abba watoh baku daina yawoce yawocen nan ba ko"!!sai ya fara inda inda dan bai san ta gano su ba. "Baby kin ga....you see...oh common zan mata magana ta kira ki just take care of your husband for the main time"ƙitt ya kashe wayar sai abin ya bata dariya har ma ta dara sosai. Juyi tayi a kan gadon sai tayi wani tunani dan haka ta tashi ta ɗau gyalen zata fita aka shigo kawo mata magani sauri sauri ta amsa ta haɗiye ta fita. Ɗakin sa ta nufa sai dai a yanzu fuskar ta da ɗan walwala unlike yadda ta fita,tura ƙofar tayi ta shiga ta same sa har yayi undressing kan sa ya koma daga shi sai jeans da singlet sai ta ji wani iri bata ji daɗin abin da ta mai ba. Shiga tayi jiki a sanyaye yana kallon ta dan mamakin ta bai bar sa ba tun ɗazu.neman wun zama tayi ta zauna tana noƙe kai ƙasa shi kuma ya mata shiru kamar wani kurma sai guilty conscious ya ishe ta ta rasa ta ina zata fara. Daga baya dai ta yi nasarar yaƙitar da tsoron a ran ta ta tambaye sa "Lokacin sallah ya kawo ko kana buƙatar taimako na"??idon sa ya zuba mata daga bisani yayi nodding kai sai tayi saurin tashi ta nufi hanyar bayin dan haɗa mai ruwan alwalar. Ruwa mai ɗumi ta haɗa mai dan yanayin garin akwai sanyi sanyi shi yasa ta mai mixing ruwan ita kuma ta yi da normal water sai ta fito ta ce mai "Na gama haɗa ma ruwan alwalar yana bayi"daga haka ta matsa mai ya tashi a hankali yayi hanyar bayin ta bi shi da ido ba dan wulaƙancin da ya mata ba da ta taya sa but nevertheless. Juyawa tayi ta nemi sallaya ta shumfiɗa mai haɗe da ɗauko mai jallabiya coffee brown ta haɗa da casbaha ta ajiye mai ko da ya fito bayan ya gama alwalar sai ta miƙo mai rigar ya saka ta tabbatar ya tayar da sallar sannan itama ta koma nata ɗakin dan gabatar da sallar zuhur. Bata bar ɗakin ba sai da ta yi wanka ta canza zuwa normal gown chocolate colour mai baza daga sama har ƙasa siffar sa dai kamar irin karan miski ne dan ya lafe mata jiki sai ta ɗora mai nylon puffer jacket mai hula dan zuwa lokacin yanayin garin ya rigada ya rikiɗe hadari ne sosai alamun nan ba da jimawa ba ruwan sama na iya saukowa ta san yanayin ta shi yasa ta yi tanadin kayan tarar sanyin tun wuri.. Ɗakin sa ta koma ta same sa kwance yana riƙe da wayar sa kamar yana video call sai dai murmushi kaɗai yake yi baya magana bata san ko da wa yake maganar ba sai ta ƙarasa ciki ta zauna a kan kujera sai ya bita da kallo sai da aka kira sunan sa sannan ya mayar da idanun sa kan wayar yana mai cewa "Armm....ahhmmm..Ammi am sorry"..sai yayi shiru ita kyma Ammin sai ta ce mai "Halan likita ce ta shigo duba ka"??sai yayi saurin cewa "A'a Ammi,,Bilkisu ce"!!daga haka yayi shiru sai Ammi ta ɗan ui murmushi kafin ta ce "Eh ai dama ita nake nufi ko ka manta ko ita ɗin wacece??ai likita ce ita ko ba haka ba"??. sai yayi shiru dan abin ya shammace sa kiran sunan sa tayi ta ce "Zaid ba ni ita mu gaisa mana"kallon ta yayi kawai toh dama tana jin su da duk hiran da suke yi sai ta tashi ta dawo kusa da shi tana son goge damuwar ta dan kar Ammi ta gani. Juya mata wayar yayi sai fuakar Ammi ya bayyana suka gaisa ta tamnaye ta ko da wata matsala amsar da ta bata be ya bama Zaid ɗin mamaki saboda yayi zaton zata faɗi abin da ya mata sai ya ji ta ce babu komai tambayar ta Ammin ta kuma yi dan ta tabbatar ta san halin ɗan ta yana iya bijirewa da ƙin yarda akan Bilkisu matar sa ce,sai dai yadda ta tabbatar mata akan babu komai kuma bai yi abin da take zargin ba sai ta ji daɗi all her thought ɗan ta ya gyaru ne ya gyara halin sa,, Magana ta mata cikin yin ƙasa da murya ta ce "Matsa daga wun da mijin ki yake i need to tell you something"..tashi tayi ta fita daga ɗakin gabaɗaya tana tunanin me Ammi zata gaya mata haka.. Shikuwa tunani ya shiga yi kar dai Ammi ta saka ta gaba akan sai ta aanar da ita komai dan in har ta faɗi abin da ya mata toh tabbas Ammi zata ce ya watsa mata ƙasa a ido dan sai bayan ta kira sa ɗazu ne da Bilkisu ta fita ta ke sanar da shi komai kuma a nata bayanin nuna mai tayi akan su suka tursasa Bilkisu auren sa dan ba budurwa gare shi ba da za'a nemo ta a haɗa auren ba but tunda ga Bilkisu kusa sun yi ƙoƙarin convincing na ta ta anince ba dan ran ta na so ba sai dan ta masu biyaya sosai Ammi ya ɗagawa Bilkisu darajar ta a idanun Zaid dan kar ya ɗauke ta for granted ya kuma raina ta,ya ji mamaki sosai dan bai yi tunanin hakan ba dama ashe dole aka mata ba wai ra'ayin ta bane kamar yadda yayi zargin ta... Da ta fitan sai ta nemi wani wuri da ke da privacy ta zauna tana mai kallon Ammin sai ta ce "Ammi ina jin ki"murmushi Ammin tayi kafin ta ce "Baby so nake in ƙara ja maki kunne akan abin da na daɗe ina gaya maki game da Zaid,,kin dai san baki gama shan magungunan ki ba bana son ki kuskura ki yi sakacin barin Zaid ya san ki a mace har sai kin kammala da magungunan nan gabaɗaya kin dai san ƙa'idojin su dan haka ina mai ƙara ja maki kunne kar ki yarda da duk wani daɗin bakin da zai maki dan na san halin sa sarai saukar da kai ne gare shi muddin yana buƙatar wami abin kar ki yarda har sai kin gama shan maganin nan kuma ki kula da lafiyar ki kin dai san garin nan akwai yanayi na sanyi ba kaɗan ba bana son jin labarin pneumonic crises ɗin nan did you understand me"??duk kunya ya gama rufe ta yayin da Ammi ke maganganun nan sai bata ce komai ba illah nodding kan ta da tayi tana mai jin nauyin Ammin ita kuma bata fasa ba ta cigaba tana cewa "Toh ni dai na gaya maki again baki da danuwa in dai Zaid ne dan na ja mai kunne kuma na gaya mai matsayin ki a wurin sa dan kar ma yayi gigin ɗaukar ki for granted ki dai ƙara haƙuri da juriya dan muma nan da kika gan mu tare da iyayen ku maza ba wai ba'a samin matsalar bane ana samu amma saboda fahimtar da ke tsakanin mu da su ya sa kuke ganin mu tare har yanzu kuma baku iya sanin ko akwai misunderstanding a tsakanin mu dan mun san takun mu mun iya handling matsalolin mu ba sai an mana ba i want you to use your capabilities as a woman,,mace da ta amsa sunan ta mace,ki tafiyar da Zaid yadda shi da kan sa zai yi falling mKi sosai na san na takura ki but please ki min haƙuri ki kular min da shi ba dan hallayar sa ba dan ni please kin ji Bilkisu"?ya salam Ammi asking for favour she can't believe it sai tayi saurin dakatar da ita by way of saying "Ammi dan girman Allah ki daina roƙo na ni kunya ma nake ji ni ya kamata in roƙrme ki a matsayin ƴa a gare ki ba ke ki roƙe ni ba bai dace ba Ammi please ki daina kin ji"??sai ta ji tana ƙara son yarinyar dan kindness da gaskiyar ta. "Nagode Bilkisu inshaAllahu ba zaki yi kukan da kin sani na auren Zaid ba dan zai so ki fiye da yadda kike tunani alƙawari ne wannan"!!a zuciyar ta tayi magana ta ce "Hmm Ammi har yanzu baku gama sanin wanene Zaid ba da a ce kun san yarinyar da yake mutuwar so da ƙauna da baku ma fara mafarkin haɗa mu ba bare har a kai ga yin alƙawarin tabbatuwar zaman mu a tare ba"a fili kuma ta ce "Nagode Ammi ki gaida min Baha na kira ta ɗazu bata ɗaga ba"sai Ammin ta ɗan yi shiru dan su tun da suka bar germany suka nufi paris a chan su Dr Maher da prof suka same su dan haka bata da masaniya akan whereabout na yaran. Shirun ta ya tabnatar wa Bilkisu da cewa basu gida kenan ma gabaɗaya sai ta tuna da ai ɗazu tayi waya da Abban ta kuma bisa ga dukkan alamu sam ba a Nigeria suke ba kenan tare suke a wata ƙasar oh su dai Allah ya basu iyaye sai ta ce "Fine Ammi na gane a huta lafiya in na koma ciki zan ba Zaid wayar"tana gamawa ta kashe tana mai girgiza kai. Da maganganun Ammi ta shigo ɗakin inda ta same sa kwance nan inda ta bar sa ba bacci yake ba but ya lumshe idanun sa sai ta mai sallama ya buɗe idon sa yana kallon ta. Miƙo mai wayar tayi ta ce "Gashi mun gama amma na kashe sai ka kira"karbar wayar yayi yana jujjuyawa yana jiran ganin reaction nata akan maganar da suka yi da Ammin sai dai bai hango komai ba dan bata bari ya ga alamun zargi tattare da ita ba. Bai yi kiran ba sai ya ajiye wayar a gefen sa ya juyo gare ta ya ce da ita "Am sorry...i was harsh on you ɗazu am sorry"!! Abin ya bata mamaki da ta ga ya sauko da wuri ta ɗauka zai cigaba da ciccin magani ne har sai ita ta roƙe sa akan yayi haƙuri sai ta ga yayi saurin saukowa dan haka sao ta ce "Is okey"daga haka basu kuma cewa komai ba har tsawon lokaci da a da ne da suke ƙauyen koma da hira zasu yi dan sun saba a lokacin but yanzu they are more of strangers to each other sai suka zauna shiru kamar kurame Da ta gaji da zaman shirun ne ta tashi ta ce "Zan je in dawo"sai yayi saurin tambayar ta "Ina zaki je"da mamaki ƙarara kan fuskar ta tace "Am going to my room"sai yayi tsammabin hala fushin ɗazu ne bai sake ta sai ya ce "I wanna apologize"abin mamaki sai ta juyo tana kallon sa ta ce "Apologize???..about what"??he is a straight forward man dan haka sai ya ce "Akan ƙin yarda da nayi da ke when you told me that you were my wife...am sorry Ammi ta min bayanin komai"sai ta ji kamar an tsunduma ta a ruwan sanyi dan haka ta ce "Hmm ya wuce zan tafi in dawo"!!daga haka ta fita bata tsaya jin komai ba kuma sai ta barshi da tunanin ƙila wa ƙala. A nata fannin kuwa da ta shiga ɗakin ta sai ta kasa natsuwa ta yi nan tayi chan tana tariyo maganar da ya faɗa mata da yanayin yadda ya bata haƙuri abin sai ya rinƙa birge ta. Komai bata yi ba sai tunane tunane ta kwanta ta shiga nazarin maybe as time pass by zai amince ya bata lokacin da ya kamata ya bata a matsayin sa na mijin ta. Bacci ne ya ɗauke ta bata sani,bata farka ba sai da la'asar tayi sannan ta tashi tana mamakin abin da ya saka ta yin doguwar bacci har haka. Gabatar da sallah tayi sannan ta ɗau wayar ta ta yi dialing numbern sa dan bata jin zata koma ɗakin sa nan kusa Bai ɗauka ba sai da ya katse sannan yayi calling nata back sai da ya kusa tsinkewa sannan ta ɗaga suka gaisa ta tambaye sa ko yayi sallar la'asar ya ce eh yayi sai ta ce abinci fah nan ma ya bata amsa da eh an kawo mai daga haka ta mai sai anjima ta kashe wayar ta ajiye. 6 hours later Ba ta koma ɗakin sa ba sai 10pm lokacin har ya fara bacci sai ta kyale sa ta koma ɗakin masu kula da marasa lafiya nan kusa da ɗakin sa,a nan tayi kwanciyar ta har bacci ya ɗauke ta. Washegari da ta tashi yin sallar asuba ta je ta tashe sa yayi nasa a ɗakin sa ita kuma ta koma nata ɗakin tayi. For the whole of that day cikin calmess da respecting juna suka yi shi babu hayaniya tunda kowa an Ammi tayi clearifying nasa a wun ɗan uwan sa As a wife tayi discharging duties ɗin ta a ranar wato kula da wankan sa cin abincin sa shan maganin sa da dai abubuwan da suka kamata cikin ruwan sanyi suka yi spending ranar su kan su abin ya masu daɗi. Bata manta ba tana kula da lafiyar ta haɗe da shan magungunan da Ammi ta umarce ta da sha sai dai bata shan su a ƙa'ide dan kaɗan take sha ba kamar yadda aka ce ta rinƙa sha. Ko da dare yayi a nan ɗakin kusa da nashi ta kwana bayan ta mai abin da ya kamata ta mai sai da safe ta ui wucewar ta... *_2 weeks later_* A yau ne za'a sallame su sai dai za'a rinƙa kawo sa check up every after 2 days kenan zaman ƙasar ya kama su dole saboda likitan ya sanar da su cewa bayan tsayin sati biyu da zasu ɗauka suna zuwa checkup ba zasu kuma zuwa ba sai after 3 months dan duba lafiyar hearing aid ɗin sa saboda a cire mai ear device da aka saka.. For this 2weeks da suka yi tare a asibitin sun fahimci juna sosai dan sun fara sakewa suna ɗan hira tare amma bata yarda ta kwana a ɗakin sa iyakan ta da shi shine ƙarfe goma na dare daga haka kuna sai washegari,kafa kafa suke da junan su komai cikin ilimi ale yin sa. A zaman nan nasu daidai da rana ɗaya bai taɓa taso mata da maganar Asma'u ba ko ma wani abin da ya shafi garin ba lafiya ƙalau suke zaune kuma tun bayan fitar da shi da tayi zuwa park nan bayan asibitin bata ƙara fita da shi ba iyakan su ta zagaya da shi cikin hospital environment su dawo ciki shi kuma baya takura mata akan dole sai ya fita. A lokacin ta sami ragin ayyukan sa dan yana iya yiwa kansa most of the things da a da ita ke mai improvement ɗin ya mata daɗi dan har ƙaramar celebration ta mai wai ya gama warkewa but anytime she remember that akwai babban abin tausayi da ke nan zuwar masu sai ta ƙara jin mixed feelings ɗin nan na taso mata sometimes bata iya controlling kan ta sai ta shiga kuka ita kaɗai wasu lokutan kuma sai ta mai addu'ar iya tsallake ƙaddarar da zai riske sa bayan ya gama mantawa da wahalar da ya shiga. Wani hotel apartment ne suka tafi wanda yake medium ba luxurious ba dan ba zama ya kai su check up ɗin sa ne ya sa zasu ƙara sati biyu. Shi zai yi processing zaman nasu but sai ta hana sa ta ce ita zata yi kar ya damu ya jira ta. Tambayar unoccupied room tayi mai complete abubuwan buƙata ta yadda ba sai an fito waje nemam wani abin ba. Room number 208 aka basu ta amshi keys na ɗakin ta juyo ta mai bayani sai dai yayi shiru dan ya ga kamar key ɗaya ne wato dai ɗaki ɗaya take son su zauna. Wucewa ɗakin suka yi sai ya ga two rooms ne sai ya ji relief dan yana tunanin yadda zai rinƙa gudanar da activities nasa gaban ta but seeing two rooms sai ya ji sauƙin abin Zaɓar mai ɗaki tayi itama ta zaɓi nata suka shige tare da kayayyakin su,basu fito ba sai da aka shigo kawo masu abinci nan ma karɓa tayi ta miƙa mai ita kuma ta shige da nata sai da suka gama cin abincin sannan ta fito ta mai sallama ya amsa sai ta tura ƙofar ta shiga. he is already dressed in blue pyjamas na bacci dan har ya kwanta a kan gadon sa baccij ne dai bai kai ga yi ba. Duƙar da kanta ƙasa tayi haɗe da ce mai "Maganin ka na zo baka"sai ya ce "Okey"daga haka ta ƙarasa ciki ta ɗauko kit da ta saka magungunan sa ta buɗe ta ciro mai sannan ta mayar. Da maganin a hannun ta ta juyo ta ɗau bottle water ta iso kusa da gadon ta miƙo mai,karɓa yayi yana kallon ta sai tayi murmushi ta ce. "Sha mana i wanna go and sleep"sai ya kai maganin bakin sa ya haɗa da ruwan ya sha sai ta amshi bottle water ɗin ta mayar sanna ta ce da shi "Goodnight"da kai ya amsa mata yana kallon ta har ta kai bakin ƙofar tana waiwayo sa suna haɗa ido da ta kai inda zata tura ƙofar sai ta dakata ta kashe mai light haɗe da jan ƙofar gently ta wuce zuwa nata ɗakin ta kwanta...First move Next morning 8:45am Shigar white Burberry slim-fit shirt ne da wandon Calvin Klein baƙa sai takalmin Jason of Beverly hills mai silver white colour hannun sa saƙake da agogon Daytona Rolex baƙa wuyan sa kuwa saƙale yake da muffler baƙa sai hular sanyi da ya saka na kamfanin Balmain kalar ta ɗaya da takalmin ƙafar sa idanun sa sanye cikin black goggle,ga doguwar jacket mai kalar ƙasa da ya riƙe a hannun sa daga dukkan alamu dai sakawa zai yi in ya fito,tsaf ya fito cikin shirin fita yawon zaga gari wanda shi dan kan sa ya haɗa fitar ba tare da sanin taba dan kamar abin shammaci zai mata sakamakon alkhairan da take mai tsakanin ta da Allah wanda ya san ko da wata nashi ce ta jini iya abin da zata mai kenan dan haka da wannan ƙudirin ya kwana a ran sa sai dai bai nuna ba bare ya sanar da ita. Kwance take ɗaure da towel orange colour mai ɗan girman kan ta lulluɓe da hular wanka,komai bata saka a jikin ta ba dan tun da ta fito ta kwanta a nan a ƙalla ta kai awa guda tana kwance kamar bata ɗakin tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa lokaci zuwa lokaci. Bata ankara ba ta ji an turo mata ƙofar ɗakin a 360° ta yi wani juyin masa ta jawo bed sheet ta naɗe kan ta a ciki tana ta faman zazzaro idanu waje dan ta san babu wani mai shigo mata kai tsaye daga ita sai shi ne a apartment ɗin in ba shi zai shigo mata ba babu wanda zai yi barging mata kai tsaye haka. Tana kai duban ta ga ƙofar ɗakin tayi arba da shi cikin shigar da ba kasafai yake yin su ba sai lokaci lokaci. Wani ihu ta tsala dan ganin yadda ya kafe ta da ido alamu dai ya nuna ya gama kalle ta tun ɗazu bata sani ba dan ya sakankance ne a yayin da ya zuba mata idanun sa abin da ya tada mata hankali kenan har ya sa ta sake ihun dan a wun ta kamar ta cutu ne kallon ta da yayi kusan gakf naked babban abin cutuwa ne a gare ta. A rikice cikin rasa abin yi ya ja dabaya haɗe da turo mata ƙofar yana panting kamar wanda yayi tsere yana mamakin dalilin ta na yin ihu ana zaune lau anya lafiyar ta ma ƙalau kuwa.??+ Kuka zata yi ko hauka ta rasa toh shima me ya kawo sa ɗakin ta kai tsaye babu alama ko sallama,ita bata taɓa yi mai shigar kai tsaye ba gudun kar tayi tozali da abin da bai kamata ba amma shi ya shigo kai tsaye kuma ai ita ta saba zuwa duba sa ba shi ba dan me zai mata shigowar bazatta?ya gama da ita... Wani zuciyar ke sanar da ita ai ba laifi bane dan ya gan ki a haka kin manta shi ɗin mijin ki ne kuma ya halasta ya gan ki a halin da ya fi wannan??sai kuma ta ji kunya da haushin kan ta why did she react in this way.. Haushin kan ta taji sosai dan ba girman ta bane at least she is 25 ai ta san do and dont's na ma'aurata dan ta sha gani haka zalika tana da ilimi da hankalin tantance fari da baƙi.. Daga wajen ya ɗan ɗaga murya ya ce "Good morning"!!!bata amsa ba sai ta ce "Uhmm"what?ya tambayi kan sa dan mamaki ta ba shi sai ya kuma cewa "In kin gama ki fito zamu tafi wani wuri ina jiran ki" Sai tayi kasaƙe tana tantaman anya daidai kunmuwan ta suka jiyo mata Zaid na faɗin in ta gama ta fito wani wun zasu?da wa?da shi?sai tayi shiru bata sauko daga kan gadon ba tana nan nannaɗe da zanin gadon kamar dai tana ganin sa a ɗakin har lokacin. Shiru shiru bata fito ba ya kai duban sa ga agogon hannun sa ya duba ya ga mintuna ashirin da shida sun wuce kuma bai ji alamun ta ma sauko ba bare ta shirya sai ya tashi daga inda ya zauna zaman jiran ta ya nufi ƙofar ɗakin ta ya shiga danna mata alarm bottom. Cikin firgici ta ɗago ta mai da idanun ta kan ƙofar tana jin faɗuwar gaba take huɗubar Ammi ya dawo kan ta inda take sanar da ita wai kar ta yarda Zaid ya san ta a ƴa mace sai har ta kammala shan magungunan ta dan Zaid ya iya tsara zance muddin akan abin da ya gani yana so ne. Wannan huɗubar ne ya kuma ruɗa ta da tunanin ta har dai tayi making mind ɗin ta akan in ta kuskura ta biye mai toh ba shakka zai kai ta ya baro dan haka ta mai banza sai da ta ji ya kuma pressing bottom ɗin sannan ta ɗaga murya ta ce "Zaid i can't come with you....,,just go alone am sick"jin ta kira sunan sick a kalaman ta sai ya turo ƙpfar gabaay ya shigo yana nuna alamun mamakin rashin lafiyar ta dan lafiya ƙalau suka rabu jiya toh me kuma ya same ta hala shi yasa ma bata zo ta tashe sa da asuba ba. Ko da ta ga ya bankaɗo ƙofar sai ta tsala ihu ta shiga masife shi tana cewa "Zaid get out...out...how can you be barging into my room without my permission...get lost....you wanna see me naked or what...arrrrggg..ka fitar min a ɗaki nace bana zuwa ba zan je ba just go out"!!!da matuƙar fushi ta ƙarasa maganar wanda ya ɗan yi shaking nasa kaɗan sai dai bai biye mata ba instead ya tsaya clearing kan sa a wurin ta ta hanyar faɗa mata shi bai gan ta ba ko ɗazu da ya shigo amma ina ta tuɓure ta ƙi yarda ta kafe akan lallai lallai ya gan ta shi kuma na natse da rantse mata a kan bai gan ta ba "I swear i didn't see you"ya faɗa with sincerity a idanun sa sai ta natsu bata ce komai ba har sai da ya kuma nanata mata sannan ta ce "And now?ka ganni"??sai ya kuma zama serious kafin ya ce idon sa cikin nata alamun assurance "Not at all baby doctor...ban gan ki ba"!!sai ta cigaba da kallon ƙwayar idanun sa kafin ta ce "Ka tabbata baka ganni ba"??cikin gaskiya da gaskiya ya ce "I swear"..... Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske wanda ya bashi mamaki toh me na ɗaga hankalin ta dan ya gan ta?sai yayi bouncing maganar ma ya ce "It's her perception and hallucination"a zuciyar sa yayi maganar yana mai furzar da iska. Kusan mintuna uku suna a haka ya fita bai fita ba ta tashi bata tashi ba sai daga bisani tayi gyaran murya haɗe da ce mai "Excuse me"!!cikin sauri ya ce "Sure"!!amma me?sai bai tashi ba ya cigaba da maintaining eye contact da ita sai da ta kuma nanata "I said excuse me Zaid"da ɗan ɗaga murya ta yi maganar wanda ya saka shi dawowa hayyacin sa sai ya tuna ashe fah hide and seek puzzle ake yi shi kuma ya zauna.. Tashi yayi cikin daburcewa yana in'ina yana faɗin "Errrmmm..so...sorrry..ina jiran ki a waje sai kin fito"!!ya fita cikin sauri,ko kallon sa bata yi ba dan a takure take da zarar yana kusa da ita shikenan natsuwar ta ya kau haka ma tunanin ta ya tsaya har sai ya bar wurin.. Halan ba sai ta tafi wun psychologist an duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta ba kuwa?.. Miƙewa tayi ta nufi waldrop ɗin ta ta buɗe ta fito da wata Chloe top and trouser cream colour ta ɗau ƙaramin gyale baƙa amma haɗe yake da hijabi ana iya yafa shi a naɗa kamar gyale mai hula. ta ajiye a kan gado haɗe da ɗauko pins da zata kama gyalen da shi,takalmin boot na fata mai kalar ƙasa ta ɗauko mai tsayi wanda ya kai har kusa da gwiwar ta mai siraran rope lace da ake ɗaura takakmin da shi dan samin comfort a ƙasar takalmin kuwa tsini ne kamar dai hills haka yake,ɗaukar babbar Alexander McQueen jacket mai tsayi har gwiwar ta ta haɗa da muffler cream colour. Bayan ta gama saka inner wears ɗin ta ta saka kayan sai da ta yi rolling veil ɗin ta saka ta ciki sannan ta ɗora jacket ɗin sai gyalen ya kasance yana rufe cikin jacket ɗin,naɗa muffler ɗin tayi a wuyan ta ta ɗau ƙaramar side bag cream colour ta saka wayar ta da tablet a ciki sai room keys da ke hannun ta ba wani make up sosai tayi ba kaɗan ne amma ta fito dan hidden angelic beauty ɗin ta ya fito a sihirce beauty ɗin ta ke haskawa yana glowing a fizge.. Rasa yadda zata fito daga ɗakin tayi sai da ta gama juye juyen ta sannan ta yi shahada ta turo ƙofar ya buɗu sannan ta fito kan ta a ƙasa kamar marar gaskiya.a yayin da take ƙoƙarin rufe ɗakin shi kuma yana zaune yana jiran fitowar ta jin ƙarar buɗe ƙofar ne ya sa ya ɗago sai ya gan ta tana rufe ƙofar. Ƙura mata ido yayi yana kallon ta dan gani yayi kamar ta sami process of hypertrophy saboda transformation da ta samu dan ta ƙara weight compared to yadda take da in a baya tana weighing 50kg a yanzu yana iya cewa ta kai 58-59kg dan ba kaɗan ba canjin ya nuna a jikin ta.. har ta gama rufe ƙofar sannan ta juyo kan ta a ƙasa ta ce da shi "Na gama"!!sai ya miƙe tsaye ya tako a hankali har ya iso dab da ita sannan ya dakata ya matso da fuskar sa kusa da nata a hankali wanda hakan ya janyo mata faɗuwar gaba tana tunanin Zaid ai babba ne ba zai yi shirmen samarin zamani ba sai ga shi yana mata wani irin abu da bata san dalilin sa na yi mata hakan ba. Jin numfashin sa tayi yana sauko mata daga gefen fuskar ta sai ta ji intense obsession ya shige ta but bata iya furta komai ba Cikin ruwan sanyi da kama aji ya ce da ita "Kin yi kyau and......you....smell..gooood"a haka ya jero maganar sai ta ji jikin ta na wani iri kamar yana son programming ɓakon abin da ya kawo mata ziyara a lokacin da Zaid ke jero mata maganganun nan dan ba a maganar kaɗai ya tsaya ba sai da ya haɗa da sauke mata numfashin sa wanda abin ya zo mata out of the blue.. Jin muryar sa tayi yana cewa "Shall we"sai ta ɗago ta kalle sa haɗe da yin murmushin ƙarfin hali ta ce "Yes"...daga haka ta shiga gaba yana bayan ta har suka fito ya rufe ƙofar suka shiga takowa a hankali har suka iso reception inda ya sanar da su cewa fita zasu yi ba yanzu zasu dawo ba da kyakyawar fahimta receptionist ɗin tayi wishing nasu good day dan ta ga alamun kamar newly couples ne faɗa ne kawai bata yi ba but tayi alƙawarin dhk dare in har suka dawo zata sanar da su how much she admire them ga shigar su kusan iri ɗaya dan jacket ɗin su kala ɗaya ne because suna fitowa daga ɗakin ya saka nasa but rashin kwanciyar hankali ya sa Bilkisu bata yi noticing ba but shi yayi tun lokacin da ta fito hakan ne ma ya sa ya yi complimenting nata but sai ya ga bata yi responding yadda yayi tsammani ba kenan bata lura cewa kaya iri ɗaya suka saka ba ko me ke damin ta ne haka bai sani ba... Da fitan su suka shiga cab da ke tsaye a wajen hotel ɗin dama basu ci abincin safe ba dan haka da mai cab yayi tambayar inda zasu tafi sai ya ce da shi ya kai su nearby eatery sai mai cab ya ja suka yi tafiyar da bata wuce mintuna ashirin ba ya ja ya tsaya ya yana mai ce da su sun zo. Fitowa suka yi ya miƙo mai kuɗin sa ya ja yayi gaba su kuma suka shiga takawa har suka iso glass translucent four sided sliding door ɗin eatery ɗin suka yi sliding yayi ciki da su a juyi na biyu wurin madaidaici ne ba babba ba ba ƙarami ba ga wun regular nan a gefe ga vip a gefe nesa da wun regular sai kuma vvip da ke saman upstairs. A ran sa ya fi son su tafi saman wun vvip dan yana da sociophobia when it comes to eating in public hakan na ɗaya daga cikin dalilin sa na ajiye ice da ta kawo mai the other day dan baya iya cin abinci a gaban jama'a da yawa ko family ɗin sa ba kasafai yake son zama suna cin abinci tare ba dan baya taɓa sami comfortability in yana cin abinci ana kallon sa ko ba'a kallon sa yana samin nervousness. Dan haka yana gama ƙare ma wurin kallo ya mata alama da su haura sama,ita dai bata san dalilin sa na cewa su haura saman ba dan ta ga akwai tables a ƙasa but ya ce su haura sama. Gently suka haura saman inda ɗaya daga cikin host ɗin ta yi leading nasu har zuwa desired choice ɗin Zaid dan shi ya nuna inda yake son su zauna. Wurin rufe yake dan wanda yake zaune a nan fannin ba zai iya shaida wanda yake zaune a chan fannin ba saboda yanda aka yi designing wurin an yi designing nasa ne cikin yanayin sirri privacy is ensured a wurin sosai komai naka a tsare yake dama baturi na ba ma tsari haƙƙin sa sai wurin ya ma Zaid sosai har yake tunanin for the main time of their staying a germany nan zasu na zuwa cin abinci dan wurin ya birge shi sosai. Round glaas table ne mai ɗauke da attracting bouquet a vase ƙanana ƴan gudil gudil sai light candles dake cikin glass container gefe kuma sparking lights ne masu different colours suna walwal bayan already akwai hasken farin wutar lantarki dake fitowa daga bulb dake sagale daga saman vvip ceiling arena ɗin wanda shi kansa ado aka mai abin kallo dan glass ne mai kalar golden da silver yayi kamar oval ta ƙasa sannan yayi curving daga sama kujerun na mutim biyu ne kawai sai dai in mutum na buƙata sai a ƙaro wasu like in case of family eating outing treat.. Ba shi kaɗai ba har ita wurin ya birge ta har take tunanin sanar da shi ko nan zasu rinƙa zuwa cin abinci kafin su koma because privacy na gaba da komai kuma su biyu ɗin na son privacy sosai.. Shi yayi gaba ya iso kan ɗaya daga cikin kujerun ya ja mata baya alamun ta zauna sai ta kalle sa da murmushi a saman fuskar sa ya ce "Ladies first"sai itama ta mai murmushi ta zauna a hankali tana wani basarwa kamar ba mamaki ne ke damin ta ba sakamakon manly treats da yake ta mata tun da suka fito har zuwan su nan ba.. Juyawa yayi ya koma fannin ɗaya kujerar yana mai ƙoƙarin cire jacket ɗin sa kafin ya zauna. Hanging jacket ɗin yayi a wani abin hanging kaya da ke bayan sa sannan ya kalle ta haɗe da ɗaga mata gira ɗaya sama kafin ya ce "You"??yana mai nuna jacket ɗin ta da chin ɗin sa sai girgiza kai alamun a'a "Okey"ya bata amsa sannan ya zauna yana mai miƙo hannun sa ga host da ke tsaye a daga gefen sa dan jiran ya nuna ordern sa kafin ta ba ma bBilkisu itama ta nuna nata sannan a kawo masu. Bayan ya karɓa sai ya kalla kusan sau biyu sannan ya ɗago ya miƙo mata ba tare da ya ce komai ba sai ta tambaye sa cikin sakin fuska "What did you need sir"?kallon ta yayi for a second kafin ya buɗe baki ya ce da ita "Give her let her choose"!!daman haushi ya fara kama Bilkisu ganin yanda ta wani tsaya mai a kai tana murmushi but jin ya ce a bata ta yi zaɓin sai ta ji sauƙe kenan bai ma san host ɗin na kallon sa ba kenan. Miƙo mata tayi tana murmushi ta ce "Here ma'am"karɓa tayi a ɗan fusace ta kalla sai ta ɗago ta kalle sai sai ya juyamata eye balls na sa haɗe girgiza kai alamar ya bar mata zaɓi dan haka sai ta kirawo host ɗin da hannu ta nuno mata abin da suke so wato black apple mixed with meant flavour tea marar sugar sai hamburger haɗe da wani African dish course wato Passion La Braise wanda ta mata alama da ta kawo masu su biyun. Da murmushi ta yi nodding kai haɗe da fita suka rage su biyun su ta fiddo wayar ta ta shiga searching security na wurin sai ta ga akwai full security safety dan haka ta mayar ta ajiye a kan table ɗin ta ɗago sai ta ga ita yake kallo ɗan murmushi ta yi ta ce "Da matsala ne"??sai ya girgiza kai sai tayi shiru itama. Babu jimawa host ɗin ta dawo da order da suka yi placing saman trolling table da zuwan ta ta sassauke su a saman table ɗin duka rufe suke da food covers manya manya saboda gudun kar wani abin cutarwa ya faɗa cikin abincin unknowingly. Da ta gama jere masu sai ta matsa ta ce da su "Have a nice breakfast"babu wanda ya tanka mata har dai ta juya ta tafi dama akwai alarming device handle da ke ajiye a saman table ɗin dan in sun kammala su danna sai a zo a kwashe plates da dirts ɗin dama mostly da disposable items suke amfani dan kar wani mai cuta ya yi amfani da wani abin sannan marar cutar ya kwasa wannan yana ɗaya daga cikin abin da ya sa eatery ɗin ya fito sosai a cikin Berlin city na ƙasar germany ɗin. Da host ɗin ta so tsayawa buɗe masu covers ɗin amma Bilkisu ta nuna mata ba komai ta tafi kawai basu buƙatar hakan shi yasa ta tafi. Daga zaunen Bilkisu ta shiga bubbuɗe food covers ɗin har ta kammala. Ƙamshin tea ɗin ne ya bige shi sai ya shaƙi ƙamshin duk Bilkisu na kallon sa sai ta ji daɗi choice ɗin da ta masu ya mai daidai a nan ta gano cewa yana son black apple mixed meant flavour tea ta sami exposure ɗaya sai ta ga ya zurfafa a son jin garɗin abin furtawa ne kawai bai yi ba dan haka ta ce da shi cikin tsokana "Dr Zaid Maher...your breakfast is ready feel free"!!! Buɗe idanun sa yayi yana jin wani yanayi na ziyartar sa a yayin da ta kirawo sunan sa sai dai bai san dalilin da ya sa ya sakar mata murmushi ba Silently suka fara cin abincin su hankali kwance garɗin abincin na riskar su a hankali har suka yi rabin abincin babu wanda ya ce ƙala a cikin su iyaka dai sun ɗago sun haɗa idanu a tare sau huɗu a course of cin abincin nasu in sun haɗa idon sai su sakarwa junan su murmushi su cigaba daga dukkan alamu abincin ya masu daɗi dukkan su.. _1 hour later_ Sun kammala cin abincin suna goge bakin su da tissue sai ya kalle ta ya ce "Are you okey..i mean you're satisfied"??sai ta gyaɗa mai kai sai suka zauna zaman jiran zuwan host ɗin dan yayi pressing alarm bottom ɗin some seconds ago. Babu jimawa sai ga ta ta iso da fara'ar ta ta nuno mai bill ɗin su ya miƙa mata master card tayi amfani da shi a manual pos transaction machine device ta tambaye sa pin ya bata ta ce thanks daga haka tayi abin da zata yi ta cire ta miƙo mai haɗe da ce mai "Hope you enjoyed and you will make a return next time"!!!abin takaici harara Bilkisu ta banka mata haɗe da jan tsaki wanda ya saka su su biyun kallon ta sai dai ta basar ta miƙe tana mai gyara jacket ɗin ta. Shima miƙewar yayi yana mai ɗaukar hanged jacket ɗin sa dan sakawa. Ta riga sa barin wurin shi kuma ya biyo ta a baya bai dai ce komai ba but he can sense the mood swing that occur in her just a while ago.. Rai a ɗan ɓace ta ja ta tsaya a bakin cab da ke jiraye a wajen eatery ɗin,ko da ya fito ya same ta a tsaye tana jiran sa sai yayi joining nata a tsayuwar bata ce da shi komai ba har sai da dan kansa ya ce sa ita "So where should we go now Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman"wato rama abin da ta mai ɗazu acikin eatery ɗin nan yayi amma nashi har da ƙarin sunan grandpa ɗin ta. Instead ta bashi amsar tambayar da ya mata sai tayi shaking kan ta tayi shigewar ta cab leaving him smiling all alone. Biyo ta yayi ya shiga ciki sai mai Cab ya tayar da mota ya fara ja suka hau tafiya basu ce da shi ga inda zasu tafi ba har sai da ya tambaye su sai shi Zaid ɗin ya ce da shi ya kai su museum da ke a cikin Berlin city. Tafiya ce me ƴar tazara daga eatery da suka fito kusan tafiyar mintuna hamsin suka yi kafin su iso babbar museum ɗin inda a nan mai cab ya dakata ya sanar da su kan cewa sun iso. Biyar sa kuɗin sa Zaid yayi suka fito daga motar suka nufi hanyar shiga babbar museum ɗin wanda ya kasance one of the best historical museum in Berlin city of germany. Museum Island Berlin ya kasance kamar magnet ma American travellers with nearly 5 millions of travellers ftom other countries each year which made it the best and most special museum a duniya.  Sun shiga ne yayin da wasu ke fitowa daga museum ɗin fuskokin su tab da annashuwa sai hira suke yi wanda ya saka Bilkisu jin dama su ma happy couples ne then the outing could have been more interesting but nevertheless zata yi iya ƙoƙarin ta dan saka outing ɗin lively.. Tiryan tiryan suka rinƙa zaga museum ɗin..da island site ɗin suka fara,,zagawa suka yi tun daga farkon Island ɗin har suka isa ƙarahen Island ɗin sannan suka koma suka shiga cikin main museum building ɗin wanda yake ɗauke da abubuwan ban sha'awa saboda building ɗin ya kasance kamar 4-5 throne tower building. Ɗauke yake da ɗakunan tarihi daban daban wanda yake cike da abubuwan al'ajabi da ban mamaki saboda kowani abin tarihi ɗauke yake da abin al'ajabi wanda ya samo asali daga ainihin abin da ya faru shekarun baya da suka shuɗe. Da fari ɗakin wani babban chameleon da ke dashe an ƙira shi da concrete iron rod sannan aka yi mai zanen ado da brass mai ƙyalli gabaɗaya tun daga saman kan chameleon ɗin har ƙasa inda ƙafafun sa yake lulluɓe yake da wani medallion mai ɗaukar ido haɗe da sace zuciya da tunanin mai kallon sa.ado sosai aka cancaɗawa chameleon ɗin saboda faranta zukatan masu kallon sa. Suna tafe suna karanta tarihin duk abubuwan da ke wurin.ba su kaɗai bane akwai jama'a da dama da suka zo dan kallon suma hakan ya ɗan yi discomforting Zaid har ma ya rinƙa addu'ar kar Bilkisu ta ce zata tsaya sai ta ga ƙarshen museum ɗin. Tana lura da yanayin sa da ya chanza sakamakon ganin mutani da suka fara yiwa wurin yawa sai dai ita kam bata ga damar fita ba again tana son amfani da wannan rana ta fara exposing nasa a public yadda zai rinƙa jin kan sa free a cikin jama'a ba wai ya ce dole sai a isolation zai rinƙa sakewa ba. Da dai ya ga bata da niyar bin abin da ke ran sa sai ya matso kusa da ita tana tsaye tana snapping chameleon from no where ta ji an yi grabbing mata waist sai kuma ta ji kamar an kwanto ta bayan ta an kuma saukar da fuska a ta wuyan ta ga numfashin mutum na fita a hankali yana penetrating skin ɗin ta har yana shiga cikin tsokar jikin ta,out of words ta tsaya cif ta kasa motsawa bare ta ƙwaci kan ta daga riƙon da ya kaiwa waist ɗin ta.. Sassauta murya yayi cikin kunnen ta ya ce da ita "Can we get out of here Ms Muhammad"??tsit kamar an yi ruwa an ɗauke bata iya ce mai komai ba dan ya shammace ta fiye da yadda tayi tsammani wannan abin da ya mata shi ya sage mata gangar jikin ta gabaɗaya har ya sa ta so bada mata dan ƙiris ya rage ta lumshe idanun ta sai dai ta hana kan ta yin abin da zuciyar ta ke umartarta da ta yi. Mintunan su biyu a haka sai ya kuma yi mata maganar cikin sigar da ya ɗaga mata hankali ba a iya maganar ya tsaya ba har da riƙon da ya mata sai da ya sauya., Abubuwan da yake mata yana saka ta cikin wani yanayi dan haka ta yanke shawarar haƙura da son kalle kallen da take muradin yi ga hotunan da take son ɗauka da chameleon ɗin duk bata ɗauka ba har shi kan sa tana son su ɗau hotuna tare but ya hana bata da wata zaɓi illah na ta bi maganar da ya mata dan samin sauƙi.. Cikin sauke murya a hankali ta ce "Amma Zaid ban gama kalle kallen ba ga hotunan da nake son yiwa chameleon but duk ban yi ba ka ce in zo mu tafi ka bani ko mimtuna huɗu ne in ma chameleon ɗin pictures"kamar bai saurari maganar ta ba tana direwa ya kuma cewa "Can we get out of here"??ya faɗa yana mai ƙara kai mata tensed grab bata da zaɓi dole ta girgiza mai kai sannan ya rabu da ita. Kamar ta yi kuka haka ta yi da fuskar ta ba dan ran ta na so ba suka bar museum ɗin ai kuwa har suka shiga wani carriage da zai kai su wani wurin bata ce da shi ƙala ba dan ran ta ya ɓaci Shi ya san damuwar ta but yana son privacy a rayuwar sa hakan ne ma yasa ya yanke hukunci nemar masu quite and noise free visitation place dalilin da ya sa ma suka shiga carriage ɗin kenan instead of shiga cab. Ko a jikin ta tambaye sa inda suka dosa sai da ta ga sun dakata a wani wuri da ke ɗauke da shuke shuke tun daga bakin titin da ya yanka yayi ciki can cikin dajin babu wani abu face shuƙin nan da yayi tsayi sides biyu dama da hagu daga ƙasa sun bada hanyar takawa da suka kai daga tsakiya zuwa sama kuwa sai suka haɗe ɗaya na overlapping ɗaya suka rufe ruf creating a deem suitable atmosphere. Babu abin da wurin ke fitarwa illah ƙamshin shuƙe shuƙen nan dan wani abin ma sai an shiga daga ciki inda a nan ne filawowi kala daban daban ke bada ƙamshin su iri iri ƙamshin da ke kwantar da hankali. Wurin dai ba wun jama'a bane dan ba kasafai ake visiting wun ba sai time to time hakan ne ya sa wun ya zama special. Da suka sauko daga carriage ɗin sai ta kai duban ta ga wurin abin sai ya bada ma'ana dan yanayin wurin ba ƙaramin birge ta yayi ba but saboda fushin da take yi da shi sai bata nuna ba shi kuma yana kallon duk moves ɗin ta sai bai ce mata komai ba. Tana tsaye ta ƙi tafiya sai ya kawo hannun sa ya saka cikin nata haɗe da ɗan murzawa kaɗan hakan ya bata wani sensation mai rikitarwa but she didn't allow him to see it out. "Mu shiga ciki i bet you will enjoy it more than the museum"daga haka ya ja hannun ta suka fara tafiya suna takawa tana experiencing fluorescence dake cike a wurin mai kama da babbar lambu radiation ɗin na shigar ta sosai sai ta ji ran ta na mata daɗi ba kaɗan ba Wannan wurin ba ko ina bane illah Nature Reserve da ke cikin Black forest a Baden Württemberg wanda ya kasance beautiful hilly forest ne mai ɗumbin tarihin hole rayuwa by seeing the nature da creatures da ke wurin kawai. Daɗi sosai ta ji a ran ta sakamakon zagayawa da ya rinƙa yi da ita a wurin bata buƙatar haƙurin sa at that moment har sai sun bar wurin shi yasa ma bata bari ran ta ya ɓaci ba ta yi enjoying kan ta sosai shima kuma ba laifi ya sake jikin sa da ita sun shaƙata duk wanda ya gansu tare zai rantse akan they are happy couples. He impressed her sosai dan surprises from no where ya rinƙa yi mata kamar ɗaukar ta hotunan bazatta ba iyaka tun bata sani har ta gano sai ta shiga yin dariya hakan ma ya faranta mai rai at least ya faranta mata.. Daga ƙarshe ma janyo ta yayi suka shiga yin selfie tare hotuna kala kala suka yi wanda ya dasa tarihi a rayuwar su dan hotunan smya dasa tambari daban daban a zukatan su. Sai yamma lis suka kamo hanyar dawowa gida inda a nan suka yi shopping wasu abubuwan da zasu buƙata da waɗanda zasu yi amfani da su a daren a hanyar su ta dawowa ne suka yi take away na dinner meal ɗin su daga nan suka dawo gida cikin nishaɗi kamar dai wasu masoyan asali..Sai wuraren 8:40pm suka iso gida already sun tsaya a Nature Reserve sun gabatar da sallar zuhur da asir dan haka da dawowar su kowa ɗakin sa ya nufa ya yi freshen up suka gabatar da sallar magrib da isha'i daga haka suka fito falon cikin shigar kayan barci nata coffee colour mai ƙyalli na sa red colour mai laushi duk da takalman su ita ta saka gyale ta yane kan ta shi kuma ya fito da wayar sa a hannu yana latsawa kamar dai waya yake son yi da wani ko wata. Kusan a tare suka fito dan jubilation ɗin da suka yi yau ya saka su deciding cin abincin dinner tare a falon shi yasa ma suka bar abincin a falon. Saman centre carpet da ke shimfiɗe a falon suka zauna yayin da ya ajiye wayar sa a gefen su. Shi ya buɗe well packaged pack ɗin ya yi unwrapping foil papers da ke lulluɓe da wasu abin ciye ciye,a gaban ta ya baje mata nata haɗe da miƙo mata spoons da ke nanaɗe a cikin toiletry yana mai ce da ita "Bismillah"!ɗan murmushi tayi sannan ta amshi spoons ɗin ta buɗe bata wani tsaya jiran sa ba tayi bismillah ta fara cin abincin,shima sai ya fara ci. Sun yi maintaining good table manner babu magana har sai da suka kammala sannan tayi clearing wurin shi kuma yana zaune ya ɗau remote yayi booting plasma dake falon. Kafin ta dawo daga disposing dirt ɗin already ya hakimce saman kujerar yana kallon wani program na shirin doctors suna surgery an kai tsakiyar shirin dan bai ƙunna da wuri ba. Har zata wuce ta ma buɗe baki da niyar ce mai sai da safe sai ta ga abin da yake kallo,abu nasu maganin a kwaɓe su sai ta dawo da baya ta zauna kan ɗaya kujerar dake fuskantar nasa dama a tsakiya plasma ɗin yake sai kujerun a gefe da gefe. Ko da ya ga ta dawo ta zauna sai ya kalle ta ya ce "Ba zaki yi bacci bane?aren't you tired"??kallon sa tayi kamar ba tare suka yi yawon ba after all shi ke buƙatar hutun ba ita ba dan shine marar lafiya kuma gobe suna da zuwa asibiti wun doctor saboda zai fara checkup ɗin sa. Da murmushi shimfiɗe kan fuskar ta ta ce "No..not at all...in fact,kai ya kamata a ce mawa ya huta,dan gobe zamu fara zuwa checkup"!!sai a nan ya haɗa ido da ita dan she speak to him so nicely ga tausaya a muryar ta yayin da tale maganar. Glance yayi sai ya gyaɗa kai ya cigaba da kallon kamar yadda itama ta mayar da hankalin ta kan plasma ɗin suka cigaba da kallon. Basu bar falon ba sai da suka ga abin da ya turewa buzu naɗi dan a idon su aka yi suturing komai aka gyare patient ɗin kafin a tafi short break wanda yayi daidai da ƙarfe goma shaɗaya da mintuna hamsin da biyar. Kashe tv yayi ya juyo gare ta ya ce da ita "Sai da safe"itama ta ce mai sai da safen,kowa yayi ɗakin sa dan barci ne cunkushe a idanun su kawai son ganin ƙarshen theater ɗin suke son yi shi yasa basu kwanta ba. Da baya ta kwanta a kan gadon tana mai lumshe idanun ta sai hamma take ta yi akai akai tana son tambayar sa hotunan da suka yi ɗazu but barci ya hana ta sai kawai ta bari akan washegari zata tambaye sa kafin su tafi asibitin. Babu jimawa bacci yayi gaba da ita ai kuwa a yadda ta kwantan nan a haka tayi baccin hankali kwance ta ke baccin ko ƙofar ɗakin bata ƙulle ba iya turawa tayi ta bar shi a hakan.. A nasa ɓangaren ma kusan hakan ne ya kasance dan bayan ya shiga ya kwanta sai ya janyo wayar sa da nufin saka alarm dan so yake ya riga ta tashi dan tun da aka yi hospitalizing na sa bai dawo daidai ko ba sallar dare ba kasafai yake tashi yin ta ba hakan kuwa ya samo asali ne a sakamakon effect na maganin yamma da yake sha a kullum again ear device ɗin da ke sagale a kunnen sa ya taimaka wun saka shi yin bacci har fiye da misali dan sosai device ɗin ke taimaka mai wun rage jin sauti sai ya ke saminbacci sosai wanda hakan ke shagalar da shi. Yana danna hasken wayar dama ba a security pin take ba,fuskar su ne ya fito a hoton da suka yi na ƙarshe a Nature Reserve wanda hoton ya kasance kamar selfie ne wanda ya ɗauke su suna murmushi sai ya shagala yana kallon hoton kawai sai kira ya shigo mai wayar kai idanun sa yayi ya sauke kan sunan mai kiran sai ya ga Ammin sa ce dan haka yayi saving sunan my Ammi ɗauka yayi yana mamakin ko lafiya cikin daren nan take kiran sa. Kafin ya ce wani abin har ta riga sa ta hanyar ce mai "My boy ina ɗiya ta take ne wai tun ɗazu nake ta kiran layin ta but bata ɗauka kai kuma taka wayar bai shiga sai yanzu na yi sa'a ina fatan dai bata fara barci ba"?haka ya ji tambayar daga sama sai ya yi shiru yana tunanin me zai ce mata dan kam bata da masaniyar ba ɗaki ɗaya suke rayuwa ba shi da Bilkisu ba hala ma ta rigada ta fara baccin tun ɗazu yanzu me zai ce da ita in ta nemi sanin ba'asin rashin haɗa ɗaki ɗaya da basu yi ba a matsayin su na ma'aurata,idan ta yi tunanin raina ta yayi fah me zai ce da ita dan ta fahimce sa.. Jiyo muryar ta yayi tana kiran sa "Zaid kana ji na kuwa"?firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi cikin sarƙewar murya da ruɗu cikin zance ya ce "Na'am na...aa.mm Ammi..Am..mi ina jin ki"..da mamaki ta ce "Zaid lafiyar ka kuwa"??da sauri ya tari numfashin ta ta hanyar amsa mata da "Ehh..Ammi,lafiya ta ƙalau"??sai kuma ta yi wani hangen a matsayin ta na babba tunanin nan ne yasa ta basar haɗe da sakin murmushin manya wanda ya fito fili har yana iya jiyo ta sai ta ce "Oh common my boy is normal it happens guess what?i understand your state of being ba damuwa gobe ka haɗa ni da Bilkisun ok,goodnight my boy"zata sauka a kan layi sai yayi saurin hana ta dan ya gano abin da take nufi wanda sam baya jin Ammi ta ma san matakin auren su da ba zata yi wannan doguwar tunanin ba. "Ammi tsaya bara na tashe ta dan ta fara bacci"a karo na biyu da ya ma Ammin sa ƙarya na fari akan Bilkisun ne dai ranar da ta kira sa a asibiti tana tambayar ko ya sha maganin sa ya ce a'a ta tambayi dalili dan ta san alhakin Bilkisu ne bashi nigh medications ɗin ta but sai yayi ƙarya ta hanyar cewa itama ai rashin lafiyar ta ne yake son tashi saboda sanyin da ake yi a garin gashi yau a karo na biyu ya kuma yi mata ƙarya all because of Bilkisu. "My boy ku kwanta abin ku gobe zamu yi magana".sai ya ce "No Ammi lemme wake her dan gobe zamu tafi checkup bana jin zamu sami time mu yi waya"..sai ta ji daɗi wato har closeness nasu yayi nisa haka hala ma ba fitan kaɗai suke yi zuwa asibiti ba maybe har zaga gari suke yi tare sai kuma ta ji wani excitement ya shige ta ko dai yaran nan sun kai wani mataki ne a rayuwar auren su??sai ta shiga juyi a ɗakin nata dan Dr baya kusa yana ƙasa suna zantawa da Prof ita kaɗai ce a ɗakin. Yin wannan tunanin ya saka ta jin kamar ta janyo su su dawo nan kusa da ita ta rungume Bilkisu and thank her for introducing her Zaid to the real world.. Ko kafin ta sani har ya datse kiran ya tashi ya nufi ɗakin ta babu tantama ya turo ƙofar bai sauke idanun sa akan komai ba sai a kan kyakyawar surar jikin ta da ke ɗaukar hankali dan bata da girman jiki haka bata da ƙanƙanci sosai dan ta ƙara weight akan tiny structure ɗin ta na da. Kasancewar rigar mai santsi ne sai ya ɗan yaye sama kaɗan exposing her navel but iya nan kaɗai ya fito waje sai gyalen da ke yashe gefen ta a saman gadon idanun ta luf sai sharar bacci take yi tana fidda numfashi a yadda ya kamata. Zuba mata idanu yayi yana kallon fuskar ta da ke nan so smooth babu taɓo sai dai wanda ba za'a rasa ba eyelashes ɗin nan zara zara kamar lema suman kan ta dama a ɗaure yake da robber band ta naɗe shi ta yadda ba zai takura ta ba dama ba wani cikan cunkus bane da suman it is scanty and silk soft and tender to touch dan yana da tsayi daidai misali bai fi ƙarfin jikin ta ba dan a ƙiyastin masana an gano yawa yawan masu ƙananan jiki ko sirara sun fi albarkatun suma toh a wurin Bilkisu ma haka ne dan suman mashaAllah cika ne kawai bai da shi amma tsayi na nunawa kuwa akwai Alhamdulilah.. He was lost in his imaginations sai ya ga ta juya ta cigaba da baccin ta hakan ne ya ankarar da shi yayi saurin ƙarasawa gare ta ya kai hannun sa cikin son nuna darajawa gare ta a matsayin ta na ɗiya mace ya ɗan yi tapping nata a hankali. Bata da nauyin bacci sai ta buɗe idanun ta ta sauke su kan na sa idanun mayar da idanun tayi ta lumshe sai ta kuma buɗe su tar sai cikin nasa ta gwalalo idon zata maimaita abin da tayi da safe sai dai bai bar ta ya ce "Hey calm down Ammi wanna talk to you"sai ta fara neman gyalen ta at the same time tana rufe jikin ta da bed blanket da ke kan gadon. Abin dariya sai ya shiga taya ta rufe jikin ta da blanket ɗin har yana ma fin ta saurin lulluɓe jikin,hakan ya bata mamaki and she began to wonder is he this gentile dama?wow he is a nice guy.tayi exclaiming a ran ta sannan ta ce mai "Thanks"da little smirk ya amsa mata sannan ya yi dialing numbern Ammi,babu jimawa ta ɗaga sai ya saka wayar a hands free ta yadda zasu jiyo ta sosai Tana ɗagawa ta shiga yi masu ba'a "Zaid wani irin ɗaukar alhaki ne wannan na ce maka ka bar ƴar nan ta huta da wanne zata ji gajiyar yi maka aiki ko gajiyar aikin da kake saka ta"!??sai suka haɗa ido suna kallon juna. Cikin su babu ƙaramin yaro kowa ya mallaki hankalin kan sa sun gano manufar Ammi sai suka juya at the same time suka girgiza kai kamar haɗin kai. Dariyar Ammin suka jiyo sai suka gyara zama suka shiga gaishe ta ta amsa masu tana tambayar lafiyar su,ƴar hira suka taɓa da ita a ƙarshe ta nemi Bilkisu da ta bar inda Zaid yake dan tana son yin maganar sirri da ita saboda ta kalli Zaid ɗin ya mata alamar zai fita da ido dan ya bata privacy na yin magana da Ammin. Bayan fitar sa ne hirar su da Ammi ya canza layi dan ita duk ganin ta ai Bilkisu ta zama babar mace dan haka ta shiga yi mata manya manyan maganganu irin na cikakkun mata a wun mazajen su ciki har da yadda zata canza shigar ta,yanayin zaman ta in suna tare,irin kallo da murmushin da zata na aiko mai in suna tare,irin takun da zata na yi in ta gan sa ƙarshe ma mai kankat ta mata wanda a nan Bilkisu ta fara tarin ƙarya wai ta shaƙe sai hankalin Ammin ya tashi ta shiga tambayar ta ko lafiya ta mata ƙaryar zata sha ruwa ta shaƙe ne. Kashe wayar tayi ta zauna shiru tana tunanin maganganun Ammi wai ita kallon hapoy couples take masu ne da har take tunanin sun zama ɗaya? Dafe goshin ta tayi da hannun ta biyu tana jujjuya kai dan bata mafarkin akwai ranar duniya da zai zo da zasu haɗa shimfiɗa da Zaid sai dai in an wata duniyar amma ba a nan ba dan ba son juna suke ba kawai umarnin iyaye suke bi.. Tana zaune a haka ta ga kiran Ammi ya shigo sai tayi salati ita sam bata son jin wannan wa'azi da huɗuba ta Ammi basu ƙaran ta da komai sai sha'awar samin life partner da zata iya yi mai duk shawarwarin da Ammin ke bata dan dai kam in har Zaid ne,ta san ta rasa wannan mafarkin na son experiencing irin epics da suka shuɗe a tarihin gidan su da ahalin su baki ɗaya. Barin wayar tayi har ya ƙaraci ƙarar sa ya mutu daga wannan bata kuma kira ba hakan ya ma Bilkisu daɗi sai ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.. Ganin Zaid bai dawo karbar wayar sa ba sai ta yi swiping sama ta ga bai da security lock dan haka tayi tunanin shiga gallery ɗin sa sai dai ta ga already a gallery yake dan haka ta shiga kallon hotunan tana zooming wasu tayi dariya wasu tayi murmushi sai ta shiga tunanin toh ko dai yana da wani abu ne game da ita dan in ba haka ba ta san ba zai shiga kallon hotunan da suka yi tare ba. Wani irin juyi tayi wanda yayi daidai da sallamar sa a bakin ƙofar ɗakin ta kai idon ta tayi ga ƙofar ta ce da shi "Wa'alaikumul salam,shigo". Turo ƙofar yayi kan sa a ƙasa sai ya tsaya mata a kai yana mai tambayar ta "Kun gama wayar"?ta amsa mai da cewa "Eh mun gama gashi"ta miƙo mai wayar ya kai hannu zai karɓa kenan hannun su ya haɗe da na juna sai electrification ya shige su at the same time suka ɗago suka zuba ma juna ido sun ɗau lokaci a haka suna kallon juna kafin daga baya yayi namijin ƙoƙarin janye nasa idanun ya shiga yin wasu moves na rashin gaskiya yana sosa giran sa da yatsa ɗaya yana son basarwa.. Ganin hakan ya sa ita ma ta shiga basarwa ta yi kamar bata ji baƙon yanayin da ya shige ta ba a lokacin da hannayen su ya sarƙe tare da na juna ba. "Sai da safe calm sleep"ya faɗa kamar yadda nurses ko doctors ke ce ma patients ɗin su in zasu kwanta baccin dare. Abin sai ya saka ta murmusawa kaɗan sannan ta ce "Thanks goodnight"daga haka ya juya ya fita yana zuwa daidai bakin ƙofar ta ya dakata ya yi switching mata light na ɗakin haɗe da kuma yi mata sai da safe ta amsa da "Uhumm"jan ƙofar yayi sannan ya nufi nasa ɗakin ya kwanta wai dan yayi bacci amma kuma sai me?bacci ya ce bai san haka ba, gizo idanun sa ke faman yi mai akan shigar da ya riske ta ɗazu haɗe yanayin suffar jikin ta,juyi yayi sai ya tuno da sarƙewar hannayen su ɗazu da irin electrification da ya shige sa ɗazu ne ya rinƙa dawo mai sai ya tsinci kan sa da son ƙara ganin fuskar ta a halin da ya gan ta ɗazu sai dai wani hanzari ba gudu ba,not all we want we get dan haka ya sakawa zuciyar sa haƙuri da dangana dan ya san ba zai ma iya komawa cikin ɗakin ba at this very moment. Rufe idanun sa yayi dan dole yayi forcing kan sa baccin dole ba wai dan yayi niyar yi ba dan da fari ya matsu yayi baccin but after what happened earlier sai ya ji baccin ya ƙauracewa idanun sa a haka a lalace yayi spending daren sai kusan ƙarfe uku saura na dare ya sami ikon runtsawa amma ciwon kai mai tsanani ya gama kama sa dan haka baccin wahala yayi a daren. A chan ɗakin baby doctor ma kusan haka labarin ya kasance dan har nata tunanin ya ɗare nasa da kusan ɗigo cas'in da biyar,sosai ta lasa saƙat sai tunanin abin da ya faru a safiyar ranar zuwa ɗazu da ya bar ɗakon take ta faman yi,ta juya nan ta juya chan har dai ɓarawo ya sace ta ba tare da ta sani ba. 8:45am Cikin sauri sauri ta fito dan sun makara dan ya kamata a ce suna asibitin by now but sakamakon rashin baccin da basu yi ba da wuri a daren jiya shi ya sa suka makara wun tashi. Zuwa tayi ƙofar ɗakin sa bata tsaya jiran izinin sa ba ta shige wuluf tana mai kiran sunan sa "Zaid ina kake mun yi late fah zo mu tafi kar mu kai yamma"maganar take yi cikin nuna halin fara ƙosawa san lattin ba kaɗan bane. Yayin da ta shigo mai ɗaki kai tsaye babu excuse bare ta natsu ta san yana tsaye tuntuni yana kallon ta. Gyaran murya yayi wanda ya saka ta ankara da shi sai kuma ta juya mai baya cikin jin kunyar sa dan he is almost half naked daga boxers sai singlet dake jikin sa wandon da yake sakawa ma bai rigada ya ƙarasa saka shi ba, ga blazers da zai saka haɗe da accessories ɗin sa nan kan gadon. Shi kan sa mamakin ta ne ya kusa shagalar da shi dan ya rasa ta ya ma za'a ce ga mutum a gaban ka amma ka ce baka gansa ba how comes? Ganin juyawar da ta yi ne ya saka shi girgiza kai kafin ya ce da ita "Is okey i understand..we are now even na gan ki almost naked yesterday and now...,kema kin gan ni almost naked..is okey just sit and wait for me".. Kamar ya mare ta haka ta ji saukar maganar na sa har cikin zuciyar ta ta ji ba daɗi dan ita ba niyar ta ba kenan tsakani da Allah ta shigo kuran sa ba wai dan wannan dalilin ba. Cikin ɓarin baki ta shiga yi mai bayani "Zaid ka yarda da ni wallahi ba haka bane,shigowa nayi dan in kira ka mu tafi asibiti saboda time ya tafi kuma ban son mu kai dare bamu dawo gida ba shi yasa na shigo maka kai tsaiye believe me ba intentions ɗi na ba kenan wallahi"..kamar zata yi kuka haka ta ƙarasa maganar sai kuma ya ga rashin kyautawar sa dan he was little bit hard and his words weren't respectful hakan ya sa ya ce da ita cikin tausasa murya "Is okey na fahimta and am sorry just wait for me ina zuwa"kamar jiran sa ya kai ƙarshen ayar maganar sa tayi hanzarin barin ɗakin. Shine da abin jin kunya amma ita ce da jin kunyar sa saboda yadda ta gan sa babu kaya cikakke a jikin sa.zama tayi a parlor tana jiran fitowar sa sai kallon kan ta take yi shigar ta dai ba shigar tsiraici tayi ba dan doguwar riga ce mai igiyar ɗaurawa simple gown ash silver colour sai gyalen da ta naɗa kan ta da shi wanda ya kasance milk colour haka jakar da ta sagala ƴar ƙarama itama milk colour ce takalmin ta kuma mai tsini ne kalar gyalen. Tana zaune tana jiran sa sai yanayin da ta riske sa ya shiga dawo mata sai yawo a idanun ta abin ke yi,gyara zama tayi tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta tana cigaba da tuno halin da ya gan ta jiya and yau kuma reverse is the case ita ce ta gan sa almost naked. Fitowa yayi yana mai gyara botirin blazer da ya saka,botir ɗaya ya saka ya bar ɗayar sai ya ce da ita "Tashi mu tafi"buɗe idanun ta tayi ta sauke a kansa sai ta kasa ɗaukewa dan wani irin special kyau ya mata da safen sak ya fito a ainihin Dr Zaid Maher ɗin sa da ta sani da chan. Tafa hanun sa yayi yana faɗin "Excuse me Ms Muhammad,na ce ki tashi mu tafi"cikin jin kunya ta tashi tana son riga sa fita sai dai bai bari ba dan dawo da ita baya yayi by means of holding her hand firmly yana faɗin "Kar ki damu in dai akan ɗazu ne feel free feel comfortable ba komai,,ya ɗan ja fasali kafin ya cigaba..after all you are my wife so ba komai bane dan kin gan ni a halin da kika gan ni ɗazu"!!!ɗif ta ji wuta ya ɗauke mata shin kunnuwar ta daidai suke jiyo mata maganar ko dai ƙarya ne kawai gizo maganar ya mata??his wife?strange,,a zuciyar ta tayi maganar sai tayi saurin ɗago kai daidai shima ya ɗago dan ganin me ya hana ta yin magana Cak suka haɗa ido,kallon juna suka shiga yi ido cikin ido suka ƙi cire idon tsawon lokaci,sai da yayi ƙarfin halin juya idon sa sannan itama ta sami damar juyar da nata idon har dai ya sami damar yi mata magana "Shall we"??ta amsa mai da kai daga haka suka ɗau niyar fita.. Har zasu fita wannan receptionist ɗin ta tare su da fara'ar ta tana cewa "Good morning Mr and Mrs Maher,you look perfect i couldn't keep my compliments to myself,i must say that you are the best couples i have ever seen you are just too perfect for each other"ta faɗa da sincerity sai dai walwalar fuskar Bilkisu ya daɗe da ƙauracewa fuskar ta dan matar ta wani zaƙe a dole sai tayi impressing nasu ko wa saka ta. Haɗe girar sama da ta ƙasa tayi ta kai hannun ta kan na Zaid haɗe da ce mai "Mu tafi"sai ta juyo ga receptionist ɗin cikin isa da gadara ta ce "We don't need your compliments we know that already humm so keep it to your self"daga haka ta ja hanun sa da matuƙar haushi suka fita,suna fita ta ware kamar ba ita tayi displaying little madness ba ɗazu ɗazu a cikin hotel ɗin,shima dai kam yana da ƙudirin tambayar ta dalilin dasawa mutani magana son ran ta ba tare da sun mata komai ba. Ko breakfast basu tsaya sun yi ba suka ɗauki hanyar zuwa asibitin ya so su tsaya a eatery na jiya su ci abincin but ta dage akan sai dai in suna dawowa su yi branching nan ɗin. Tafiyar kusan awa suka yi kafin ya sada su da asibitin,tun daga bakin asibitin ta hango wata na kallon su sai ta kalli Zaid ɗin ta ga shi ta mai cab ma yake yi sai ta sake ran ta ta tsaya jiran sa har ya gama sannan suka shiga ciki. Without much waste of time suka doshi ofishin Dr wanda shi ke da alhakin kula da Zaid in zai rinƙa zuwa checkup. Bayan gaishe gaishe da tambayar lafiyar su suka ɗunguma zuwa ɗakin da za'a duba sa,ana kaiwa ɗakin ta ja ta tsaya a bakin ƙofar dan ba zata iya tsyawa kallon sa ba a yayin da ake gwada accuracy na brain na sa ba. Murmushi ya mata dan ya gane gudun ganin checkup ɗin take itama sai ta maida mai da murmushin ta zauna su kuma suka shige ciki. Gudun kar ma ta jiyo hayaniyar su ya sa ta saka ear piece ta shiga danna wayar kawai sai ga kiran Bahajjatu,ɗagawa tayi tana mai nuna ɓacin ran ta ta ce "Babu ruwa na da ke yauwa"!!shewa Baha tayi kafin ta ce "Excuse me Mrs Zaid Maher kar fah ki manta matar yaya na kike ba yayar tawa ba"da dariya ta ida maganar sai Bilkisu ta ce "Lalalalaaa,,Baha kin gama raina ni,,wato ni ba yayar ki bace right??ohh na gane,toh bara in gayawa yayan naki maybe shi zai raba gardamar"ta faɗa kamar da gaske zata yi hakan. Da sauri Baha ta ce "Kee Beelove kar ki haɗa ni faɗa da yaya na na janye furuci na"sai suka saka dariya baki ɗayan su sai Bilkisu ta chanza murya ta koma serious "Amma Baha kin san baki da kirki?tun yaushe rabon da ki kira ni ko message ba kya turo min haka rayuwa take?ashe dama akwai ranar da zata zo da har zaki iya kwana ki tashi ba tare da kin nemi sanin lafiya ta ba?tun fah baki yi auren ba kenan amma kina distancing kanki da ni"?sai Bahan ta yi shiru dan ta san bata kyauta ba she is her only friend wacce take iya sharing damuwar ta da but sai gashi wai kusan sati biyu da ɗoriya ta kasa neman ta but ita so tayi ta bar su su mori rayuwar auren su dan hakan ne zai sa su sami fahimtar juna sosai ita da yayan ta Zaid saboda kaf iyayen su sun hana su kiran su sun ce a bar su su sake dan ta nan zasu fi yin kusa da juna shi yasa bata kira ta ba. "Am sorry Beelove wallahi ba haka bane"sai ta mata bayanin dalilin ta hakan ya ba ma Bilkisu mamaki wai su gani suke kamar zaman masoya suke yi kenan hmm "Toh amma har da haka Baha kin san a yanzu na fi buƙatar ki dan ina neman shawarwari daga wun friend but you abandoned me"!!sai tausayin Bilkisun ya kama Baha but she apologized and promised never to let it happened again. Haka suka taɓa hirar su har Baha ke tseguntawa Bilkisu saka bikin yayan ta da aka yi wato Afzal ta ce Ammi ta rantse ta ce ko ya fito da mata ko ta mai auren dole shi yasa ya kawo ƙanwar Zainab matar babban yayan su Bilkisu Jamil wanda takurawar Hajiya Madina ne ya sa ya ce ta zaɓo mai matar kawai ita kuwa ta ce Hajiya Zeenat ta tuntuɓi mata gidan su Zainab ko suna da budurwar yarinya da ba'a mata miji ba ai kuwa aka samu. safiya ita ce ke bin matar Jamil kuma yarinyar ba laifi ko ta ko ina ta yi ba mishkila kuma an yi sa'a bata da wani she is single sai abin ya zo daidai hakan ma ya sa aka saka bikin na su nan da watanni huɗu wai dan su fahimci juna dan son komawa canada yake kuma Ammi ta kasa ta tsare akan sai da mata zai koma by then ta san Zaid ya warke sosai ta yadda zai iya ɗaukar responsibilities ɗin asibitocin tare da taimakon Bilkisun. Wannan gulma da Baha ta ma Bilkisu ya mata daɗi matuƙa har ta ma manta da wai fushi take da ita. Har aka gama dube duben da za'a mai bata sani ba sai da suka fito tare da likitan sannan ta cire ear piece ɗin ta tashi tsaye a ɗan ruɗe tana tambayar sa "Are you okey....are you alright?da fatan dai baka ji wani pains sosai ba"?duk ta ruɗe sai ya janyo ta kusa da jikin sa ya ce cikin sassauta murya ƙasa "Am good...humm!!babu komai am fit"sai a nan ta sauke ajiyar zuciya tana mai kallon gefen doctor tana mai ce mai "I hope there is no serious problem doc"?sai ya gyaɗa mata kai da murmushi kwance kan fuskar sa ta kuma ce mai "Thank you so much"ya amsa mata sannan ya bata wata white plain paper mai ɗauke da sunayen drugs da za'a siya mai dan ya dakatar da waɗanda ake ba sa ya ɗora sa a kan wasu ƙwaya uku kacal kuma duka sau ɗaya ale sha a rana. Godiya ta musamman ta mai sannan suka bar asibitin bayan ya masu fixing next appointment day after tomorrow. Nearby pharmacy suka tsaya suka sayi magungunan,daga nan suka tafi eatery ɗin jiya dole lunch suka ci kawai at that same privacy part wato wun vvip lafiya ƙalau suka ci suka gama wanda daga nan suka kama hanyar tafiya gida dan doctor ya ce ya kamata ya huta kafin ƙarfe biyar na yamma yayi. Suna dawowa bayan sun gabatar da sallar zuhur ya zauna a falon ya ɗau remote zai ƙunna tv ta wufce remote ɗin sai ya ɗago ya kalle ta da mamaki ita kuma ta saka murmushi ta ce "Just obeying the doctor's orders"!!sai yayi murmushi kawai ya kwanta saman kujerar ya rufe idon sa kamar mai jin baccin hakan ya sa ta ɗan tsaya ta yi observing nasa ta ga kamar da gaske baccin yake yi sai ta wuce ciki tana leƙo sa dan wanka take son yi kafin ya farka. Tana shiga ɗakin ya buɗe idon sa ɗaya ya ga ta wuce sai ya girgiza kan sa yana murmushi ganin tana son mai da sa kamar wani ɗan ta,fiddo wayar sa yayi ya shiga kallon hotunan su na jiya yana ta kallo bai sami ba har ta turo ƙofar sai da ta rufe sannan ya ankara a ruɗe yaayar da wayar ta gefen sa ya mayar da idon sa ya rufe ruf kamar yadda ta bar sa taimakon sa ɗaya bata kama sa ba. Kamar mai bincike ta gama kallon sa sannan ta matso kusa da shi ta ƙura mai ido sai ta ga baccin yake yi da gaske dan haka ta koma ɗakin sa ta ɗauko mai blanket ta dawo ta rufe shi sannan tayi shigewar ta ciki. Abin dariya amma ba damar yi dan abin shi dariya ya bashi har da lulluɓe sa gani take bacci yayi..,sai ya yi dariyar sa a cikin sa ya ƙara jan duvet ɗin har fuskar sa ya ɗau wayar sa yana dannawa yana murmushi shi kaɗai...Bond+ Wanka take amma ƙwaƙwalwar ta na dawo mata da abin da ya faru tun jiya har kawo yau sai ta shiga yin murmushi ita kaɗai kamar ana tickling nata in tayi murmushin sai ta kalli kanta a mirror tana mamakin irin abubuwan da ke gabata tsakanin ta da Dr Zaid bata taɓa kawowa ba ko a mafarkin ta bata tunanin in aka ce ita da Zaid zasu zauna inuwa ɗaya zata gasgata sai gashi daga ita har shi ɗin babu wamda ya yi jayayya da ra'ayin iyayen sa haka babu wanda ya ja da hukuncin ubangijin sa. Wankan da ya kamata ta yi sa cikin mintuna ƙalilan sai gashi ta kai mintuna goma sha bata kammala ba sai shiririta da shirme take faman yi daga ta yi tunanin lokacin da yake kallonta sai tayi tunanin lokacin da yake kai mata seducing touches in tayi wannan tunanin har wani lumshe idanun ta take. Ko da ta kammala wankan zama tayi a kan tub na wankan tana tunani wanda wannan tunanin ya zurfafa mata duk ilahurin hankalin ta,tunani take akan abu ɗaya wanda take ganin in har ta bari ta amince da hakan toh abu biyu ne ko dai tayi gamo na alkhairi mai matuƙar garɗi da burgewa ko kuma ta tafka babbar kuskuren da ba zata iya goge sa ba a cikin kundin shafunan rayuwar ta wanda bata fatan hakan ya faru da maƙiyin ta bare ita kan ta. Tambayar kan ta ta shiga yi tana ba ma kanta amsa dan tana son sanin menene mafitar rayuwar a nan gaba in har tayi accepting defeat daga zuciyar ta dan ita kan ta ta san ta kai mataki,matakin da bata jin kiran wani mahaluƙi zai iya dakatar da ita dan hanyar da ta ɗauko hanya ce miƙaƙƙiya mai tsananin tsayi da ita kanta bata san ranar da zata ga ƙarshen ta ba amma tana fata akan tafiyar da ta ke yi bisa hanyar ya zamo mata tafiya mai alkhairi wanda zai zamo kamar ƙarin fitila ne a rayuwar ta ba mutuwar haskwn da take tafuyar tare da ba sannan tana fatar tafiyar ya kai ta matakin da zai sada ta da madagora dan in har ita kaɗai ke tafiyar a wannan shararriyar sharahararriyar hanya toh tabbas ta ɗauko dala babu gammu.. "Bilkisu kina ji a jikin ki kamar abin da zaki bar zuciyar ki da jigilan yi zai iya ɗaukar nauyin ta?kina ganin ba zaki cutar da rayuwar ta nan gaba ba in har kika bi shawarar zuciyar ki ba?har ya kai matakin da zaki gasgata tunanin ki ba tare da kin ƙarasa yin gwajin ki ba?anya ba babbar asara kike shirin tafkawa rayuwar ki ba kuwa?what if you welcome his love whole hearted and then he ends up breaking and tearing your heart apart?what if he still have that girl in his heart?what if he remembers her and decide to throw her away in a garbage bin?tuno wannan abin ne ya saka ta miƙewa a 360 tana zazzaro idanu waje tsabar masifaffen kishi ta hau cewa "Tir...tir..tir...Allah ya kiyaye Zaid haɗa hanya da wannan yarinyar maƙiyayr mu,,,i reject this thought,,haba,inaa...babu abin da zai yi da ita"..posting tayi tana panting tana son calming kanta sai furzar da iska take yi tana sauke ajiyar zuciya sai numfashi ke faman tsere a tsakankanin kowani second da take shaƙar iskar dake shiga cikin alveoli nata.. "Bilkisu ki natsu ki bi zuciyar ki,Zaid ya zama naki har abada har abada dan ko babu komai aure ya haɗa ku wanda kike fatar ta ɗore har abada,ba laifi in ki amshi abin da kike ji game da shi a zuciyar ki da hannu bibbiyu,,stop the unnecessary hide and seek stop relating your misery to your perfection,no it was meant to happened baki da laifi kuma dan kin yi kishin sa ba abin kunya bane,mijin ki ne fah,ke zaki bada ƙofar da har wata zata buɗe ta shigo rayuwar ku,ke ke da maƙullin zuciyar Zaid dan haka in kin rufe kin adana a keɓaɓɓen wuri babu wacce zata iya zuwa ta ɗauka har ta buɗe kai tsaye ta shige ba tare da shakka ko fargaba ba".. Shiru tayi ta dakata tana kallon kanta a madubi sai ta ji kamar akwai wani abin dake taso mata daga ciki cikin zuciyar ta wanda har yake son fasa tsakankanin ƙirjin ta saurin kai hannun ta wurin tayi ta dafe tana sauke ajiyar zuciya. Kusan awa tayi a bathroom tana yanta da warwara,bata fito ba sai da ta gama concluding kuma ta amince da final decision da ta yankewa kanta.. Bath throb ne a jikin ta a haka ta fito daga bayin tana gyara ɗaurin igiyar rigar hankalin ta yayi nisa so take ta ɗau wayar ta ta shiga google dan samin gamsashiyar amsar da take nema dan abin kunya ne ta tambayi Bahajjatu wannan abin is gonna be too childish of her.. Ko da ta shiga falon bata lura da hasken dake fitowa daga cikin blanket da ta rufe Zaid da shi ba kawai wayar ta ta ɗauka ta yi saurin ƙunna data ta shiga google ta yi typing abin da take nema. Ba jimawa ya fito mata da amsoshi har da hotuna abin ya bata mamaki.,,tun da ta zauna a kujerar bata tashi ba sai da ta ji kiran sallar wayar ta na ƙasar madina da tayi setting kasancewar bai da yawan musulmai sai tsitrarai. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana mai kai idanun ta gare sa da zuwa lokacin baccin gaske ya ɗauke sa sakamakon daɗewar da tayi zaune a wurin tun yana tsimayen ta har bacci ya ɗauke sa. Share hawayen da ya silalo mata tayi tana kallon sa in complete shock dan bata san abin da ke ɗawainiya da ita for all these while sunan sa Love ba,dama haka abin yaje ko dai ita nata ne ya zo mata a haka da wahalarwa?sai ta ji duniyar ya mata ba daɗi komai ma bai mata daɗi wannan wace irin rayuwa ce haka so zai mata tana zaman zaman ta?ya rasa lokacim da zai kama ta sai lokacin da suka fara samin fahimtar juna lokacin da suka fara fahimtar juna?ta yaya ma so zai mata haka alhalin ya san wanda yake kaiwa harin sam bai san da zaman sa ba??share hawaye ta kuma yi tana kallon sa sai hakan bai mata ba har sai da ta tashi ta nufi kujerar ta zauna a hankali tana son hana kukan ta fitowa fili dan kar ta tashe sa ya farka ya ga tana kuka.. A hankali kamar mai jin tsoro ta shiga yaye mai blanket ɗin idon ta kyar a kan innocent gentile face ɗin sa da ke nan so calm and good looking. A hankali ta kai hanun ta dake shaking kan fuskar sa,,hannun ta na kaiwa kan fuskar sa ta lumshe idanun ta sai ga hawaye na silalo mata dan ba komai take tunani ba illah kanta da take tausayawa dan Zaid....bata gabar sa ita ta sani taimakon ta ɗaya ne Allah bai bashi izinin tambayar ta Asma'u ba dan ta san da zarar ya san halin da take ciki shikenan tata ta ƙare sai dai ta haƙura dan ita ta ɗorawa kanta lalurar da ta san ba zai kawo mata hanya mai ɓillewa ba.. Har bakwai saura tana kallon sa tana hawayen tausayin kanta haka shima tausayi yake bata dan ta san in har ya gano Asma'u ta taimakawa Mudan har yayi achieving kai su ƙasa toh zai zama so shattered kuma he will be heart broken ko zai iya ɗaukar wannan abin?Allah ne masani.. Share hawayen tayi a karo marar adadi sannan ta yi calming kanta ta ja iska sannan ta furzar kusan sau uku tana breathing exercise kafin ta mai wani kallo wanda ke tafe da tsantsar tsananin so mai zafi zafi dan hucin son na kan huro mata yana huro mata zafin sa wanda ke ratsa jikin ta har ya fara melting mata jinin jikin ta. Ita wannan ne kuma ƙaddarar ta a rayuwa ya zata yi da irin zazzafar son sa da ya shige ta ya ɓula ƙowani gaɓa a jikin ta??jan hanci tayi sannan ta hau kiran sunan sa tana yi tana gyara muryar ta dan ya fara rawa kuka ke son kwace mata but she didn't allow it.. Sau biyu tayi tapping nasa sannan ya juyo da corny looking face nasa ya sauke kan nata already falon is spread with light sai hasken ya so tona asirin halin da take ciki but ganin zai gane sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sam ta manta banu kaya a jikin ta sai rigar wanka. Shiru shiru ta ji bai ce komai ba haka bai yi attempting tashi ko moving ba sai tayi zaton ko baccin ne bai ishe sa ba ya koma dan haka ta ɗago dan kuma tada shi sai dai abin mamakin shine tangaras ta gan sa a kwance ya kafe ta da idon sa yana mata kallon ƙurilla sai ta rasa abin faɗa dan haka ta bi inda yake kallon da ido sai ta ga ƙirjin ta ya kafe da ido ɗan buɗaɗɗen wurin da yayi exposing ƙirjin ta sakamakon rashin haɗewar rigar wu guda saboda kamar falmarar riga yake haɗawa ake yi a ɗaure toh nan space ɗin yake kallo kamar his life is laid on it sai dai the most surprising and amazing things is that she didnt react,bata yi wani silly reaction ko response ba illah maida idon ta kan sa da tayi tana mai cewa "Lokacin sallah ne yayi ka tashi kar ka makara"a yanayin maganar ta one can see the misery she is in presently ga alamun karaya daga muryar ta. Kallon ta ya shiga yi cikun ɗaurewar kai yana mamakin rashin responding ko reacting ma kallon da ya mata. Tashi yayi daga kwancen ya ɗan zauna haɗe da haɗa hannayen sa biyu yayi cupping fuskar sa yayi zugum kafin daga baya kuma ya tashi yana mai ce da ita "Thanks"ta mai murmushi haɗe da saukar da idon ta ƙasa dan bata son haɗa ido da shi kallon sa kaɗai na increasing venom da je yawo a jikin ta wanda ya sami kafar shiga ne sakamakon son sa da yayi poising ɗin ta because his love at this moment have no difference with a poison dan ya shige ta ba a lokacin da ta shirya ba ba da sanin ta ba ya shige ta so she consider his love as a poisoning element that convert and react to her chemical electrodes that moves and perform their functions by each passing second and she have no justification to this love she have for him indeed this is the love saga.... Tana kallon sa yayi shigewar sa ita kuma ta zauna a wurin tana tausayawa rayuwar ta ko ya zata kasance in har ta gama tabbatarwa da ita kaɗai ke shawagi cikin son sa amma ban da shi.. Da yake tana fashin sallah ɗazu da ta shiga wanka ta ga ta fara staining pant ɗin ta sai ta gane monthly period nata ne ya zo hakan ne ma ya sakata zama ba tare da ta saka kaya ba dan ko ta saka ɓaci zasu yi kuma wahala take sha ba lallai bane ta iya wanke su ko a gidan Umman ta ke mata wankin in ta fara but now she is married kuma ba so take Zaid ya san halin da take ciki ba because they are still different basu zama abu ɗaya ba.. Tashi tayi ta nufi table da landlune ke ajiye,so take tayi making order na dinner ɗin su,har ta kai hannu ta ɗauka sai ta ga ya leƙo daga shi sai towel da yayi tying around his waist jikin sa jiƙe da ruwa ga kumfa nan a wasu sassan jikin sa kamar ya sani har ya fara soaping kansa sai ya fito dan bai so su ci abincin hotel ɗin he wanna give her a special treatment for taking care of him. "Don't bother calling,a waje zamu ci abincin dare humm"!!ya ida yana mai assuring nata da idanun sa sai ta ɗan murmusa sannan ta mayar da wayar ta ajiye shi kuma ya koma ciki dan ƙarasa wankan sa.. Zama tayi duk jikin ta ya saki ga matsalar menstrual cramps ga damuwar abin da tayi discovering just a while ago,shiru tayi ta daɗe a hakan sannan daga bisani ta tashi ta shige nata ɗakin tayi freshening kanta haɗe da saka kaya ta ɗan yi kwalliya kaɗan ta dawo falon ta zauna tana jiran sa. Abin na ɗaure mata kai wai dama haka shi so yake ko dai tata ne ta zo mata da wannan sigar?tukunna ma ita kaɗai ke wannan abin da ita kaɗai ke jin wannan abin game da shi but him...,baya jin wannan abin towards her abin da yake ji ya zama mallakin Asma'u.. Wuf ta tashi ta tsaya hankalin ta tashe dan har zazzaɓi take ji kamar zata yi hauka wannan abin ya shammace ta haka ya yaudare ta ta ya ma za'a yi zuciyar ta ta kamu da matsanancin son Zaid a lokacin da bai dace a lokacin da shi bai yi realising ya gane ainihin taste ɗin sa ba,in aka bar shi da yarinyar nan da tayi silar faɗawar sa halaka yake son cigaba da rayuwar sa har ƙarshe.. Tana tsaka da tunanin mafita sai ta ji sound ɗin takalmin sa ta bayan ta sai ta juya ta kalle sa,,for the very first time ta mai kallon so kallon da bata taɓa mai ba kallon da ke ɗauke da abubuwa daban daban kama daga zazzafar son sa,tausayin sa,sadaukarwar da zata iya yi akan sa at any cost,baza ta iya rasa sa ba haka zalika ba zata iya haƙura da shi ba ko da kuwa me za'a bata.. Twinkling fingers nasa yayi a daidai saitin idon ta wanda hakan ya saka ta lumshe idanun ta sannan ta buɗe su tarr a kan nasa fuskar straight to his charismatic eyes da ya kafe ta da su,jin wani irin son sa take a cikin jikin ta chan ciki cikin jikin ta dama ba lafiya ne da ita ba sai abin ya haɗe mata bibbiyu tuni ta ji sanyi na shigar ta silently sai ta hau karkarwa da rawar ɗari wanda ya fallasa har ya saka Zaid gano hakan da idon sa sai shima ya shiga ruɗu a ruɗen yayi saurin kawo mata agajin gaggawa dan shima ganin yanayin ta ya saka sa cikin duhu ko dai bata jin daɗi ne sai dai bai kai ga samin amsar tambayar sa ba ya ga amsar a gaban sa. Rungumo ta yayi sosai dan gabaɗaya jikin ta ya saki kamar bata da laka,ya tsorata ba kaɗan ba dama bai da masaniya akan rashin lafiyar da tayi a lokacin da yake nasa rashin lafiyar dan haka bai san bata gama jin sauƙi sosai ba ya ɗauka kawai sudden collapse ne. Saurin kwantar da ita yayi saman 3 seaters leather chair ɗin falon idanun ta lumshe ta fara losing consciousness nata cikin ruɗewa ya shiga kiran sunan ta yana jijjuga ta in yayi ya hau tapping kumatun ta duk ya ma ras abin yi yanzu yanzu ana zaune ƙalau me ke damin ta ne "Bilkisu...Bilkisu..wake up,,,ki tashi me ke damin ki..common wake up you were fit and sound just some seconds ago what happened....tashi mana Bilkisu stop all these kin san bana son ire iren waɗannan puzzles ɗin ko...wake up".. A haka fah ya share mintuna yana girgiza ta ya manta da wani abu wai first aid treatment bare ya ɗauko ruwa ya yayyafa mata lallai wannan shine rule da ke magana akan ma'aikatan asibiti akan "you should "NOT" treat your family member" saboda a duk lokacin da ma'aikacin asibiti zai kawowa family member na sa agaji in yana cikin wani hali toh abu biyu ne zai fari ko ya ruɗe ya rasa samin mafita kokuma yayi overreacting har ya zamo ya kasa treating abin da ke damin sa ya je yana treating wani abin daban. Sai da ya ga ba sarki sai Allah sai ya tuno da ana yayyafawa sumamme ruwa dan farfaɗar da shi.. Da sauri ya tafi kitchen dake apartment ɗin ya ɗebo ruwa da zuwan sa ya shiga yayyafa mata yana kiran sunan ta sau shida yana yayyafa mata ruwan sannan ta ja numfashi a hankali ta yi ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanun ta ta sauke su kan fuskar sa sai ya shiga tambayar ta "Me ke damin ki Bilkisu?baki jin daɗi ne dama kokuma sudden collapse ne"?tsakanin sa da Allah yake tambayar ta sai ta shiga duhu ta kasa tantance reality ne ko kuma wild dreams ne Zaid asking her abin da ke damin ta strange.. Sai tayi faking facial expression nata ta saka fake grimace ta ce "Bana ɗan jin daɗi ne Zaid but..,,na ji sauƙi yanzu,thanks for the care". Ɗan boko ne dan haka sai ya ce "A'a Bilkisu ban yarda ba you collapsed suddenly out of the blue sannan ki ce min kin ji sauƙi...no no way dole ki zo muje a duba ki a asibiti ban yarda ba"zata yi magana ya miƙe yana faɗin "And that's final bana son jin komai daga bakin ki ki zo mu tafi asibiti a duba ki bana son taurin kan nan naki"ya faɗa yana wani tsare gida irin he is the boss ɗin nan sai abin nasa ya bata dariya har ta ɗan fidda murmushin ta fili wanda ya saka sa kallon ta yana mamakin dalilin ta na mai murmushi sai ya saku yana kallon ta kafin yace "Hey baby doctor listen up...,am the boss here ba a gida muke ba daga ni sai ke a nan ƙasar in ban kula da ke ba Ammi ba zata yafe min ba dan she warned me not to make you feel uncomfortable and insecure dan haka dole ne in kai ki asibiti"!. Yayi maganar ne da iya gaskiyar sa amma sai ya ga ta saka dariya dan dariyar ya bata sai ta ce "Boss huhh??toh me zai hana ka kasa treating nawa a nan ba sai mun tafi asibiti ba i guess hakan ya fi ai ko the boss".. Sosai ya ji mamakin moral da ta samu har take daring nasa sai ya karkata wuyar sa ya ce "Kenan kina daring na"??ta ce cikin kafe sa da ido cikin idanun sa "Ina ganin haka"ta faɗa tana ɗage gira ɗaya sama yayin da take bin sa da kallon in ka isa tana murmushi..abin da tayi ne ya saka sa jin dole ya gyarawa yarinyar nan tunanin ta dama ɗaga mata ƙafa yake yi dan ganin yadda take kula da shi but yanzu tana son ta ƙure sa. Takawa yayi har gaban ta ya shiga durƙusowa har ƙasa yana kallon ta tana bin sa da ido tana kallon abin da yake yi,yana kai gwiwar sa ƙasa ya kawo hannun sa ya kai saman kumatunta a hankali ya shiga yawo da hannun sa a kan fuskar ta,ita dai tana kallon sa har ya kawo kan bakin ta ya sauke hannun,yatsar sa a kan lips ɗin ta yana jujjuyawa kawai sai ta tsinci kan ta cikin wani hali ta shiga lumshe idanun ta har ta hau sauke ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba sai ta ji ya dakata daga yi mata abin da yake yi hakan ya saka ta buɗe idon ta ta sauke kan sa. Shima ita yake kallo da wani irin siga wanda shi kaɗai ya san ma'anar hakan bai furta komai ba yana kan kallon ta kamar bai san ta ba haka itama tana kallon sa,idanun ta har sun fara cikowa da hawayen tausayin kanta dan wani salon son sa ne ke fizgar ta kai tsaye tana ji a jikin ta kamar nan ba da jimawa ba zasu rabu rabuwar da Allaj kaɗai ya san lokacin haɗuwar su.bata kai ga saukar da hawayen ta ba sai ta jiyo muryar sa a hankali cikin sanyi yana tambayar ta "Kina daring ɗi na ne Bilkisu"??yayi mata tambayar yana mai kallon bakin ta zuwa ƙwayar idanun ta.tsabar sanyin maganar da izzan da ya haɗa cikin muryar sa yayin da yake furta kalamomin bakin sa ya saka ta jin faɗuwar gaba mai tsanani wanda ya haifar mata da fargabar gaba mai ƙarfi dan tana jin kishin sa a ran ta tana tsoron rasa sa sai ta saka idanun ta cikin nasa idon ta buɗe baki ta fara magana "Eh...,,,Zaid...,i..amm...dari...nn..,,.bai bari ta kai ƙarshen maganar ba ya haɗe lips ɗin su wu ɗaya attraction ne mai gauraye da tsantsar affection ya shige su su duka sai suka lumshe idanun su at the same time this being their first time to experience such thing sai suka rasa sukuni a zukatan su daga ita har shi heartbeat ɗin su yayi increasing yayi elevating sosai dan da za'a gwada su da stethoscope toh lallai ƙarar "Lup Dup" da ventricles na heart ɗin mutum ke bayarwa za'a tantance banbancin ƙarar da tasu ke bayarwa dan a haɗe ya gauraye ya rinƙa bada ƙarar at the same time hankulan su a tashe yake bata taɓa yi ba haka shima bai taɓa yi ba abin ya zamo masu alien a duniyar su. For some seconds lips ɗin su na haɗe ba tare da sun yi komai ba haka idanun su na lumshe kamar masu bacci sam basu so su dawo duniyar a haka suka ɗau lokaci sai daga baya tayi ƙoƙarin buɗe idanun ta a hankali kamar mai tsoron gamuwa da mugun abu. Tana buɗe idanun ta sauke kan nasa lumsasdun idanun da ke rufe ruf gab da nata idanun tana ganin yadda yake fidda numfashi in-out and she can say that tun da suke basu taɓa yin kusanci da juna kamar yau ba and the only time she sees him panting like was once ranar da yayi surgery shi kaɗai ba tare da assistance ba wato ranar da ya ƙi nemar taimakon ta alhalin gata ga shi a cikin theater suit ɗin. Lips ɗin su na kan maintaining position da suka masu wato lock up position,sai ta fara jan nata lips ɗin baya baya har ta raba da nasa lips ɗin sai kuma ya buɗe lumsassun idanun sa da suka komo kamar wanda ya tashi daga bacci babu abin da ke cikin ƙwayar idanun nan nasa sai buƙatuwa,tsantsar buƙatar mace ne ke taso mai amma abin mamakin shine bai san hakan ba bai san yana buƙatar mace ba duk tunanin sa strange illness ne ya same sa ba tare da ya sani ba dan ya san lafiyar sa ƙalau kuma shi so yake ya nunawa Bilkisu kuskuren ta na daring nasa and he wanted using a positive reenforcement in her but he end up hurting his self ko ina dalilin hakan?? Cikin lumana ya raba fuskokin su haɗe da tashi daga tsugunnen da yake hankalin sa a ɗan tashe dan ya ji abin da bai taɓa ji ba a iya rayuwar sa,kansa a ƙasa ya shiga gyara collar na rigar sa da ya ɗan canza position ita kuma bin sa da ido take yi tana son tantance abin da ta karanta a google sai dai bata ida analysis ɗin ba ta ji muryar sa na faɗin "Let's go"daga haka ya fita dan yana so ya bar ta ta ƙara kimtsawa..bayan fitar sa sai ta shiga yiwa kanta murmushi tana bin lips ɗin ta da yatsar ta tana tuno abin da ya faru tsakanin su was that a reality act ko dai mafarkin ta ne sakamakon saka abin da tayi a ran ta gashi tayi googling ɗazu ta ga abin da take buƙata abin da ya faru da su na ɗaya daga cikin alamomin da ta karanta but in their case can she call that as a strong sign?girgiza kai tayi tana jin kunyar kanta sai ta tashi ta gyara rigar jikin ta haɗe da gyara gyalen ta sannan ta fita. A step na huɗu ta same sa tsaye yana latsa wayar sa sai ta tsaya kallon sa again kamar bata san sa ba,imagining take yi ya rayuwar su zai kasance in har Zaid na jin abin da take ji?ko zai nuna ko zai barwa kan sa?.. Shi da kansa ya gane presence ɗin ta saboda ƙamshin ta ya iso sa sai ya ɗago idanun sa ya sauke a kan ta wani irin munafukin kallo yake bin ta da shi wanda yake ganin kamar bai da lafiya ne in ba haka ba ta yaya zai tasa ɗiyar mutani a gaba yana kallon ta he thinks he need to see a physician.. Ƙarasa saukowa tayi tana ɗan aika mai da murmushin da bata san tana yi ba sai da taga shima yana mata sannan ta gane cewa ita ce ke yi shi yasa shima ya mayar mata da martani. A sukune suka ƙarasa saukowa har suka bar hotel province,. Yau basu tafi wannan eatery ɗin ba wani nan kusa suka tafi inda suka ci light dinner tsaf suka kammala suka fito pretending not to remember what happened between them earlier on,a hanyar su ta komawa hotel ɗin ne ya canza ra'ayin sa ta hanyar ce mata trekking zasu yi sai ta juya ta gwalalo mai idanun nan nata "Trekking kuma?sai ta ɗan ɓata fuska kafin ta ce ni kam a'a ban iyawa kawai mu tafi a cab am tired already"surprising look ya bita da shi bakin sa buɗe yana murmushin mamakin ta ita kam ko a jikin ta tsakani da Allah take dan kam ta san tata ta ƙare in har basu koma gida da wuri ba cramps ɗin ta zai ƙaru ta ga azaba a gaban sa ita kuma ba haka take so ba.. "Me kike nufi?in fah ban manta ba ke doctor ce mai kaiwa awa huɗu zuwa shida a tsaye kina surgery toh why the sudden change and weakness?just trekking na how many minutes da zamu yi mu koma kina faɗin baki iyawa"?ƙyale sa tayi har ya dire ayar maganar sa ita kuma tayi picking up "Zaid i can't..gaskiya bazan iya ba bana jin daɗi and anything can happened if care is not taking i can't afford seeing myself being demoralized in front of you i just can't so please ka min rai mu shiga cab mu koma gida"har ta gama kawo dalilin ta shi linking yake yi da issues na crises nata dan garin akwai alamun saukowar ruwa any moment but ai suna iya kaiwa gida ruwan ma bai fara ba dan haka sai ya janyo ta kusa da shi yana mai ce mata. "Kar dai ki ce min har kin fara tsoron crises naki ne?kar ki damu har mu kai gida babu abin da zai faru trust me"girgiza kai ta shiga yi tana jin pains ɗin na increasing intensively ta shiga ce mai "Baka gane ba kuma ba ganewa zaka yi ba Zaid ni na san abin da ke dami na ba tsoron crises nake ji ba.."kasa ƙarasawa tayi dan wani irin unexpected cramp da ya riƙe ta hakan ya saka sa kasa furta abin da yake son furtawa sai ya hau tambayar ta ko menene ke damin ta amma ta kasa basa amsa ƙarshe ma faɗi ta kusa yi but yayi nasarar grabbing nata ya riƙo ta firmly ya hau girgiza ta but idanun ta har sun fara lumshewa alamar sume mai zata kuma yi for the second time a 360° ya dakatar da mai cab ya shigar da ita sannan ya shiga a rikice ya ce da mutumin ya wuce da su asibiti. Tafiyar 15minutes suka yi ya kawo su wani asibiti inda da shigar su ya tsaya a emergency ya kirawo masu kula da lafiyar dake wurin suka kawo mai agaji aka shigar da ita ciki dan duba ta shi kuma ya hau yin zirga zirga a tsakankanin ɗakin yana iya hango su a ciki. Almost 25minutes sannan doctorn ta fito haɗe da kiran sa gefe ya tafi jikin sa na bashi wani abin gaban sa na faɗi but sai ya ga ta ɗan murmusa ta ce da shi "She is your wife"?a cikin tsantsar damuwa yake dan haka bai san lokacin da ya shiga girgiza mata kai ba sai ta ce da shi. "She is fine and she will be fit as soon as she wakes up just experiencing her cycle cramps i guess you know that already,so right now we were able to stabilize her and she is calm by 9 you can take her home if she wakes up because she need yo rest adequately but fir now,she is good"godiya ya mata sannan ta tafi shi kuma ya koma ya shiga ciki haɗe da zaman jiran ta har ta farka,shu tausayi ma take ba sa ya ɗauka ba duka mata ke shan irin wannan wahalar ba sai gashi bayan baby sis ɗin sa Bahajjatu a yau ga matar sa ma na experiencing cycle pains hala ma shi yasa ta yi collapsing ɗazu.. Tausayin ta ne ya kama sa sosai dan haka ya shiga yi mata fatar samin lafiya as soon as possible.. Awar sa ɗaya yana zaune yana jiran farfaɗowar ta amma bata farka ba sai ya bar inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya tsura mata idanu yana mata kallon tausayi a ce da ran ka da lafiyar Ka amma kayi losing consciousness naka har tsayin awa ɗaya he really felt bad and he curse this pains.. Yana kan kallon ta yana jin tausayin ta sai ya ga ta fara mutsu mutsun farkawa,da sauri ya kuma matsawa kusa da ita yana mai riƙo hannun ta cikin nasa har dai ta gama buɗe idanun ta ta ga inda suke ta kalle sa zata yi magana ya riga ta "Kar ki yi magana,,am sorry i couldn't understand you ɗazu har sai da na bari kika zama helpless am so sorry,doctor ta ce zamu iya tafiya in kin farka dan kina buƙatar hutu shall we?can you walk or i should support you"?da iya gaskiyar sa yake nuna kulawar sa gare ta sai ta girgiza mai kai alamun zata iya tafiya. Taya ta tashi yayi sannan suka fito haɗe da yi ma doctorn godiya haɗe da yi mata sallama sannan suka fita. 35 minutes later Tana kwance ya shigo ya same ta haɗe da tambayar ta ko akwai wani abin da take buƙata ta ce mai a'a sai ya mata sai da safe sannan ya koma ɗakin sa but sai me??he couldn't sleep he kept on thinking about her yana ji kamar he is connected to her dan haka ya tashi ya bar ɗakin nasa ya nufi nata ɗakin,ko da ya isa har ta fara bacci but he can't leave her all alone what if ta farka cikin dare tana buƙatar wani abin kuma babu mai yi mata kusa. Da wannan tunanin ya nemi wuri ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta cikin nasa yana ɗan murzawa duk tausayin ta ya ishe sa he can't wait to see her fit again dan mood nata duk ya canza har maganar da suke ɗan yi basu yi ba wannan ciwo ai wahalarwa ne. Shi kaɗai yake ta zancen zuci in yayi ya kalle ta ya ji sabon tausayin ta na kuma shigar sa haɗe da wani abin da shi bai san ko menene ba..Conspicuous Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin. Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar "IYA RUWA FIDDA KAI" amma bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da za'a iya alaƙanta kalmar da ba.. Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura. Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin. Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai. Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta. Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane.. A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita.. Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa. Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba? A wannan karon da ya kalle ta sai ya ji yana son kwanciya next to her maybe zai sami sauƙin raɗaɗin da yake ji a ran sa dan haka ba tare da wani doguwar tunani ba ya saki hannun ta ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta a left side adjacent to her ya juyo fuskar sa daidai nata fuskar yana kallon ta. Akwai wani maganaɗisun da ke ingiza sa yin abubuwa da dama da bai gama yin shawara da zuciyar sa akan halascin su ba amma yana jin in bai yi abin ba toh kamar a takure zai kasance wannan ne dalilin sa ma na barin ɗakin sa ya shigo nata kenan ba tare da ya tsaya yayi doguwar tunanin abin da zai yi ba sannan yanzu da yake zaune ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta next to he,kuma ikon Allah sai ya ji faɗuwar gaban da yake experiencing ya ragu kusan kashi talatin cikin ɗari,yana kallon nata ne yana tunanin zuci har bacci mai naiyin gaske ya ɗauke sa wanda bai san ba a ɗakin sa yake ba dan he feel very comfortable and free a inda yake sanadiyar samin lafiyayyiyar baccin da yayi kenan.. 5:14am A daidai wannan lokacin ne ya juya da nufin gyara kwanciyar sa sai kuma ya dakata daga komawa baccin dan ya ji different scent ba kamar wanda ya saba ji ba in ya juya a ɗakin sa,a hankali ya shiga buɗe idanun sa har ya gama buɗe su duka sai a nan ya fara tuno abin da ya faru da shi a daren jiya,dafe goshin sa yayi yana mai lumshe idanun sa kusan mintoci kafin ya buɗe su ya juya ta ɗaya gefen sa sai ya ganta kwance lafiya ƙalau tana kwasar baccin ta juyawa yayi ya ɗauko remote ɗin air split na ɗakin ya rage yawan shi dan yana gudun wani abin da zai janyo mata ƙaruwar zazzaɓin da take ciki already. Tashi yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin,ba sallah take ba bare ya tashe ta sai kawai yayi tafiyar sa zuwa ɗakin sa ya yi alwala ya zo yayi sallah.. Wani baƙon lamarin da ya same sa shine yadda ya taƙarƙare ya rinƙa yi mata addu'ar samin lafuya haɗe da yi mata addu'ar tsari daga yin wani rashin lafiyar dan shi kaɗai ya san yadda ya ji a jiya da ta shiga halin nan sam baya so ya kuma witnessing.. Sai da haske ya fara haska ɗakin nasa sannan ya tashi daga saman sallayar nasa ya dawo kan gadon sa ya kwanta daga haka ne wani session ma baccin ya kuma yin awon gaba da shi kuma a cikin wannan baccin nasa ne ya rinƙa mafarke mafarke marasa daɗi dan kaf abin da ya faru da shi ne a dajin nan ya shiga dawo mai sai ya shiga karkarwa yana haɗe jikin sa wu ɗaya at the same time yana karantar add'uar tsari da kariya bai farkan ba haka bai daina yin add'uar ba har sai da hotunan mummunar ranar takau daga baccin sa sannan ya cigaba da yin baccin duk ya gama haɗa zufa gashi ya rufe kan sa da blanket kuma ba ƙaramin zufa yake yi ba.. Juyawar ta ke da wuya taji ƙarar wayar ta sai ta fara laluɓo wayar har da ta kai hannun ta kan wayar ba tare da ta duba sunan ba ta ɗauka haɗe da karawa a kunnen ta ta kwanto ta gefen da ta ɗauko wayar idanun ta rufe da ragowar magagin bacci cikin muryar ta ta ce "Hellooo"..haka ta ja kalmar wanda ya saka Umma kallon aminiyar ta Hajiya Madina sai suka ɗan yi murmushi dan dama sai da Ammi ta hana ta kiran ta ce da ita maybe fah basu tashi ba amma Umma ta ce ita kam tana jin yin waya da su.. Jin ba'a ce komai ba sai ta kuma maimaita kalmar "Hello"sai a wannan karon ne aka amsa "Goodmorning Mrs Zaid Maher"muryar da ta ji ne haɗe da sunan da aka kura ta da shi ga kuma ƙamshin da ta ji su suka haɗu suka saka ta warewa da kyau ta tashi a birkice tana zazzaro idanu waje cikin rikiɗewa ai a sittin ta ce "Umma please can i call you back in the next 15minutes"??tayi tambayar gaban ta na faɗi sai Umma ta ce mata "Yeah...sure...why not...just..just take your time okey baby bye"wani irin ajiyar zuciya ta sauke idanun ta na daɗa buɗuwa da kyau kan ta na sara mata kamar ta kwana biyu tana rashin lafiya. Dafe kanta tayi ta zauna kam gadon tana son tuno abin da ya faru jiya.. Iya abin da take iya tunawa shine jiya sun yi sai da safe ita da Zaid kuma distance dake tsakanin su da ɗan tazara tana kwance ne shi kuma daga bakin ƙifar ya sallame ta but how come take jin ƙamshin turaren sa a saman gadon ta gashi nan dai babu alamun mutum ya shigo dan gadon is neat babu wani canji daga yadda yake.. Ganin zata wahal da kan ta garin nemo amsar da bata san inda zata samo shi ba ya sa ta tashi ta nufi hanyar bayi dan gyara kanta. Wanka tayi ta gyara jikin ta sannan ta fito ta buɗe closet na kayan ta duk ta ma rasa abin sakawa sai kawai ta ɗau wata bum short da one single hand shimi ta saka ko bra bata saka ba da ta gama saka kayan sai ta ɗauko wata doguwar riga mai hula orange colour blended with red touches ta saka ya kuwa sauko mata har ƙasa sai ta nemi room slippers ta saka kasancewar babi inda zasu tafi ranar dan next checkup nasa sai washegari zaman gida zasu yi a yau.. Turare kala kala ta feshe jikin ta da shi sanna ta ɗau wayar ta tayi dialing digits na Umman ta,tana tafe da wayar a hannun ta har ta iso falon ta nemi wuri ta zauna haɗe da ɗauko remote ta ƙunna tv,tana ƙunna tv Umma na ɗaga wayar sai ta riga ta yin magana ta hanyar ce mata "Umma na ina kwana"dariyar manya Hajiya Zeenat tayi kafin ta ce "Bilkisu kenan shikenan cikin waɗanda zaki manta har da ni a ciki baby?,,ki ce kawai in kama baby Zara dan ina ganin in kuka yi naku ƴaƴan hana su zuwa wun mu zaku yi tunda gashi tun yanzu kun manta mu"murmushi tayi kaɗan kafin ta ce "Umma ni na isa,,wallahi ba haka bane Umma kin ga jiya gabaɗaya ban yi baccin daɗi ba rashin lafiya duk ya saka ni gaba dama kwanannan kawai managing kai na nake yi dan bana so Zaid ya zama demoralize saboda ni but am really sick please Umma ki min haƙuri inshaAllah hakan ba zai kuma faruwa ba kin ji"?tun da ta fara wannan maganar babu gaɓar da ya taɓa Umma sai inda Bilkisu ke faɗin"jiya bata yi baccin daɗi ba kuma ganaɗaya satin managing kan ta take yi" what does that implies? Cikin jan wani irin ƙara Umma ta ce "Baby you pregnant"tari Bilkisu ta shiga yi har tana wani shiɗewa tsabar mamakin abin da Umma ta faɗi kuma ya zo mata ne kai tsaye daga sama. Sorry Umman ta shiga yi mata sai Bilkisun ta tari numfashin ta ta hanyar ce mata "Umma is not what you think,,ban da lafiya ne saboda monthly cycle ɗi na was about coming ne and jiya da na ce maki ban yi baccin daɗi ba,cramps nake ta experiencing a bacci na shi nake nufi ba abin da kike tunani bane"sai kuma anmashuwar fuskokin su ya kau Hajiya Zeenat ta kalli Hajiya Madina suka girgiza kai su duk tunanin su ko sun kusa zama grannies ne especially Ammi da yanzu ta ɗora buri akan babban ɗan ta Zaid tana bala'in son samin jika daga gare sa time is flying any moment za'a wayi gari babu su and she can't help her self but say it out to her friend wato Hajiya Zeenat and she made her a promise that inshaAllah ba zasu bar duniyar ba ba tare da sun ga jikokin su ba waɗannan kalamai kaɗai ke kwantar mata da hankali.. "Kina nufin har yanzu baki fara jin alamomin masu ciki ba baby"?da mamaki ta ce "Strange Umma,,why are you asking me such question"??kamar jirar ta Umman take ta ce "Saboda na matsu in sami jika why are you people delaying it"??ya salam su kam Allah ya albarkace su da iyaye sai ta ce "Umma in dai har irin tambayar da zaki na yi min kenan toh i wi stop picking your calls i promise you"babu alamar wasa a muryar ta sai suka kuma kallon juna suka girgiza kai sai Hajiya Zeenat ta ce "Fine na daina kuma ba zan sake ba but ina dai fata baby ba planning kuke yi b?dan Allah kar ku bi hanyar yaran zamanin nan masu cewa sai sun gama enjoying honeymoon kafin suyi conceiving please kar ku mana haka mu muna buƙatar jikoki as soon as possible"shiru Bilkisun tayi tana sauraron mahaifiyar tata cikin rashin sanin abin da zata ce da ita dan abin nasu ya fara takura mata 2 days back Ammi ta yi nata part ɗin and now,,her mom is portraying her own pattern.. "Oh ya Allah Umma,dan Allah ki daina ke da Ammi have to stop all these things you are doing,seriously kuna takura ni i can't please,,,sai anjima i will call you when the need arises"ɗiff ta kashe wayar ta ajiye saman kujerar haɗe da kwantar da kanta saman pillow dake bayan kujerar,shiru tayi tana tunani.. She was lost in her thinking har ya fito bata lura ba tana kan tunanin abubuwan da ke faruwa da ita a ƴan kwanakin nan ga matsananncin son Zaid da ke juya ta ga asassawar iyayen su da wanne zata ji.. Ya kai minti ɗaya tsaye kan ta bata sani ba shi kuma a nasa tunanin gani yake kamar she is still in pains shi yasa take zaune haka.. Zama yayi a same chair da take zaune ya kai hannu ya taɓa gefen wuyar ta sai ta buɗe idanun ta a ɗan birkice sai ta ga shine hakan ya janyo mata baƙuwar yanayi tun ma bai tambaye ta ba kenan ina ga in ya tambayi health ɗin ta. "Good morning"da ɗan murmushi ta ce "Morning"sai ya kuma tambayar ta yana mai kawo hannub sa kusa da goshin ta "How was your night"?imagine Zaid is a good pretender kamar ba ɗakin ya kwana ba sai ta bashi amsa da "Alhamdulilah"ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Your health"??sai a nan ta haɗa ido da shi dan shima abin da yake so kenan,so yake ya haɗa ido da ita ko zai sami wani amsa cikin idanun nata dan shi ya rasa gane abin da ke damin lafiyar tunamin sa. Cikin sanyin murya da ke tattare da tsantsar so da ƙaunar sa ta ce "Alhamdulilah nagode"sai suka yi shiru suna kallon juna kafin daga bisani ya tambaye ta "Waya...da wa kike waya..na daɗe a nan baki sani ba"cire idanun ta tayi daga nasa tana gyara zaman rigar ta sannan ta bashi amsar tambayar sa cikin unexpected response "Hmmm i see,,me kuma ya sa kake son sanin ko da wa nake magana"?wani irin kallo ya mata mai nuna tsantsar mamakin sa da irin amsar da ta basa har ma da tambaya a ƙarshe. Bai so amsa mata ba but wani sashe na zuciyar sa na ingiza sa akan dole ya amsa mata dan haka ya ce "Babu,kawai gani nayi hankalin ki ya koma kan wayar gabaɗaya"!!ƴar murmushi tayi sannan ta rausayar da kai gefe kafin ta ce "Da Umma na yi wayar"sai ya gyaɗa kai yana mai kai hannun sa kan teburin da ke mafi kusa da ita,landline ya kira ya masu ordern breakfast har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalle ta cikin kulawa ya ce "Sorry ban tambaye ki abin da kike so ba na bayar da ordee,what would you like"??kallon sa tayi kafin ta miƙe tana tafiya a hankali zuwa ɗakin ta ta ce da shi "Abin da zaka ci shi zan ci ko ka manta a ƙarƙashin ka nake"??ta juyo ta mai kallon da ya saka jikin sa sakewa,kasala ce ta sauko mai a bazata ba zato ba tsammani ya ji kawai ita yake son kallo sai dai kafin yayi wani yunƙuri har tayi shigewar ta ciki. "Damn it...Zaid common man up man up..."ya furzar da iska mai ɗauke da ɗumi daga bakin sa dan hucin iskar alama ce ta yamayin da zuciyar sa ke ciki but why all these me ya sa haka me ya kawo haka he thinks he should visit a doctor seriously.. Da dariya ta ƙarasa shigewar ta ɗakin dan ta san ta ƙunna sa dan dolen sa ma ya ji a jikin sa saboda ta san yanayin maganar da ta mai sai ya ji wani abin all she need is for him to realise and keep her in his head kuma ba zata iya yin hakan ita kaɗai ba dole sai da sanin sa da kuma yardar sa.. Kwantawa tayi bisa kan gadon ta tana jin wani sassanyar annashuwa na shigar ta from no where,juyi tayi tana tuno wasu moments da suka yi tare da shi most especially jiya da ya nuna damuwar sa gare ta,tunowa tayi da lokacin da ya ruɗe a jiyan yana ta tambayar ta ko me ke damin ta sai ta tsinci kan ta da yiwa kanta dariya lallai ta shiga sabuwar duniyar da bata san da akwai shi ba a duniyar nan the feelings is extraordinary abin ya mata nauyi da yawa tana buƙatar mai taya ta riƙon abin da take ji a zuciyar ta.. Tana duniyar tunanin ta ne ta ji an turo ƙofar ɗakin kamar ba'a son turowa hakan ya tabbatar mata da Zaid ne dan shi kaɗai ke tare da ita a gidan. Tashi tayi daga kwanciyar riginginen da tayi tana mai kallon sa da murmushin son da take mai shi ko shagala yayi yana kallon ta yana jin wani abu na fizgar sa sai dai yayi ƙoƙarin controlling kan sa dan yana ganin kamar yana overreacting da yawa. Gyaran murya yayi game da riƙe ƙofar ɗakin yana mai sauke mata idanun sa cikin wani salo hakan kuwa yayi tasiri a kan ta dan kallon yayi affecting nata sosai sai dai itama tayi controlling kanta dan so take ta gama tabbatarwa ko shima yana jin abin da take ji ko ita kaɗai ke jin abin.. "an kawo mana breakfast zaki yi joining ɗi na ne a parlor ko in kawo maki nan"?cikin salon jan ra'ayin sa ta ce "Hmm Zaid kenan..,ai duk inda kake nan nake duk inda ka zaɓar min nan zan zauna" Ya ilahi,me yarinyar nan ke son yi mai ne haka shin?sam yakan kasa ganewa kan sa in har tana kusa da shi shi dai ya san abu ɗaya ne tak wanda ya san ko a baccin sa zai iya shaidar sa sai ya sami mai warware mai.. Kallon kallo suka shiga musayar yi da juna kafin ya ce da ita "Toh ki zo mu tafi parlor in yaso sai mu kalli theater show"tashi tayi da fara'ar ta ta ce "Hakan ma yayi"!!ta rigasa fita falon shi kuma yana biye da ita a baya yana saƙe saƙe.. Shi ya ɗauko plates biyu da spoons ya zo ya juye masu abincin cikin different plates ɗin sannan ya zuzzuba masu chill drink a tumbler,tana bin sa da kallo har ya kammala tana kallon sa bata ce da shi ƙala ba sai da ya kammala duka ya ɗago ba yabo ba fallasa ya ce "Bismillah"!!...wani irin kallon kashe jiki ta mai dan ƙanƙance idanun ta tayi tana mai kallon ƴan boko,shi kuma ya kasa furta komai sai bin ta da ido da yake yi kan sa duk ya ƙulle ya rasa dalilin ta na nuna mai wannan attitude ɗin. Bai gama tunanin nasa ba ya ji muryar ta kamar mai jin baccin tana faɗin. "Bismillah??toh bismillah"ta faɗa cikin halin ko in kula haɗe da ɗaukar spoon da side table knife tana kallon sa dan kamar statue ya koma a zaunen yana mamakin ta sam bai san ta shahara har haka ba sai yanzu. Alama ta mai da ido irin ina jiran ka ɗin nan dan kuwa babu alamar wasa a fuskar ta kenan bata ji daɗin yadda ya mata tayin abincin ba. Kallon ta yake kyar dan dai ya fara shiga duhu da ɗabi'un da tayi adopting tana displaying mai. Saka cokalin yayi cikin plate ya fara ɗibawa zai kai bakin sa sai ya ƙaƙare ya kasa sakawa ya tsaya kallon ta sakamakon ganin nata cokalin cikin plate ɗin abincin sa hankali kwance ta ɗibo sai ta dakata bata saka a bakin ta ba ta aika mai da wani kallon kashe jiki sannan cikin taushin murya ta ce "Bismillah"ai bai san lokacin da ya fara tari repeatedly babu tsagaitawa ba sai ta ɗan nuna alamun damuwa a kan fuskar ta sannan ta tashi cikin kula ta ɗauko mai ruwan sha dan organic drink ɗin na iya increasing mai rate na tarin bit water will be more suitable for him. Bashu ruwan tayi a baki ya ɗan yi sipping sannan ya ɗaga kan sa yana kallon ta,haɗa ido suka yi ta mai sannu da idon haɗe da gyaɗa mai kai irin it is well ɗin nan sai kawai ya sauke idon sa haɗe da furta "Nagode"sai ta ce mai "Ba komai ai aiki na ne"da murmushin ta ta faɗi hakan sannan ta dawo ta zauna ta ɗebi abincin ta kawo bakin sa haɗe da ce mai "Haaa"sai ya kalle ta a kasale bai buɗe bakin ba har sai da ta mai alama da kai sannan ya buɗe bakin yana mai yin bismillah,saka mai cokalin abincin tayi a baki ya karɓa sai ta cire ta kuma ɗebo wani ta ƙara bashi ya karɓa,a taƙaice dai ita ta ciyar da shi har ya ƙoshi sannan ta ɗau nata plate ɗin ta saka same spoon da ta bashi abincin da shi ta ɗauka zata tashi dan komawa ɗakin ta cin abincin. Yana ganin haka kuwa ya kawo hannun sa ya riƙe nata hannun da take da nufin ɗaukar tumbler,dakatar da ita yayi yana mai cewa "Zauna mana ina kuma zaki tafi"??sai ta ji gaban ta ya ɗan faɗi dan riƙon da ya kawo mata ya shige ta ba kaɗan ba. Haɗa ido suka yi sai ta kawar da nata idon kamar marar gaskiya ta ce "Dinner zan yi having"!!still yana kallon ta ya ce "Wayo dai zaki min,kin gama bani na ci sannan ke ki ce guduwa zaki yi ki ci alone dan kar in ga menene"?dariyar mamakin sa tayi sannan ta ce "Ban gane ba?abinci zan tafi in ci,,ina son shan magani kai ma ya kamata ka sha night medicine naka"sarai ya gane so take tayi dodging tambayar da ya mata dan haka shima sai yayi claiming ai bai ma san inda maganar tata ta dosa ba yayi pretending dan dolen ta ta dawo ta zauna ta ɗau cokalin zata fara ciyar da kanta sai ya riga ta riƙo cokalin,ta zuba mai idanun ta bata ce komai ba sai ta ga yana ƙoƙarin fara feeding nata abin ya ɗaure mata kai but bata dai ce komai ba. Sai da ya ɗibo iya bakin ta sannan ya ce da ita "Haaa"kamar dai yada ta mai sai abin ya saka ta darawa wato shi ba'a mai bai rama ba.. Share ta yayi dan shi dai duk abin da yake yi ji yake kamar ingiza sa ake yi yayi su dole dan haka baya jin wani damuwa ko da ta mai dariya in dai zai sami sauƙin damuwar da yake damin sa he is okey.. Buɗe bakin tayi ya saka mata,a ƙalla sai da ta yi rabin plate ɗin nan sannan ta shiga girgiza mai kai alamun ta ƙoshi sai ya tambaye ta "Are you sure"?ta kuma girgiza mai kai sai ya miƙo mata drink ta sha haɗe da karɓa daga hannun sa tana ce mai "Thank you"ya ɗan murmusa sannan ya tashi ya kwashe kayan dama tana da niyar taya sa kwashen kayan amma ya ce ta bari ita da ba lafiya sai ta yi zaman ta haɗe da ƙunna plasma ta kamo tashar da ya kamo ranar da suka kalli theater da dare. Zama tayi haɗe da crossing ƙafafun ta tana ɗan kaɗa su a hankali ta natsu tana kallon yadda ake feɗe wata mace ana son cire mata fibroid mayomas,ta zurfafa a kallon har ya fito bata sani ba sai da ya zauna yana mai faɗin "Interesting"sai a nam ta kalle sa tana mai yin murmushi haɗe da gyaɗa mai kai,daga haka suka mayar da hankalin su kan kallon har aka gama sai dai ana gab da ƙarasa ɗinke feɗan suka shiga yiwa kan su tambayoyi a course of tambayar ne suka shiga arguing da juna har ma da abin ya masu sugar suka koma yin raffle draw sai da aka kammala show ɗin sannan suka natsu sai suka koma yiwa kan su dariyar shirmen da suka rinƙa yi,gaskiya ta ji daɗi abin nan dan ko ba komai yana copping da internal response nasa ta ji daɗi ba kaɗan ba.. 3 hours later Bayan sallar azahar ya shirya cikin ƙananan kayan shan iska ya duba ta a ɗakin ta dan yana son su ɗan zaga hotel ɗin tare since they have no where to go.. Ganin ta yayi kwance babu doguwar rigar sai ƙananan kayan da ta saka a ciki,bacci take sosai hankali kwance sai ya mata kallon ƙurilla tun daga ƙasar ƙafar ta har ya kawo kan sumar kan ta yana kallon ta yana admiring jikin ta sai ya ji baya son takura ta sai kawai yayi tafiyar sa shi kaɗai ya zaga ilahirin hotel ɗin baki ɗaya yana zagawa yana tunanin ta har dai la'asar ta yi sannan ya dawo ya yi sallar sa ya kuma komawa ɗakin ya ga still baccin take sai yayi murmushi haɗe da girgiza kan sa irin wannan bacci nata haka ina zata kai sa.. Bayan kamar awa huɗu a tsakani lokacin har an fara shirin bacci dan sun gama cin abinci har sun yi sai da safe sai ya ga kawai ba zai iya ba dole ya dawo ɗakin nata ya tura yana doka mata sallama daga kwancen da take ne ta amsa mai tana mamaki dan har tayi addu'ar bacci. Lighting ɗakin yayi sai ya hango ta kwance ta ɗan leƙo ta blanket ɗin tana kallon sa,rasa abin faɗi yayi sai ya faƙe da cewar "Dama zuwa nayi dan ƙara yi maki goodnight"da fara'ar ta ce "Alright goodnight"sai ya tsinci kansa da waving nata yana murmushi itama martanin hakan ta mayar mai,ya ja mata ƙofar haɗe da kashe hasken ɗakin. Komawa baccin ta tayi shi kuma ko da ya isa ɗakin sa baccin kasa ɗaukar sa yayi dan haka ya rinƙa juye juye shi bai san me ke damin sa ba sam wannan baƙon al'amari bai mai adalci ko kaɗan. Da ƙyar da yaya baccin ya sace sa babu labari,baccin kusan baccin wahala ne dan kan sa ya kusa bugawa tsabar takura mai da yayi da tunani marasa mafita... 7 days later Last night in Germany Misalin ƙarfe takwas da mintuna ashirin da biyar na dare tana kwance da ƙaramar nightie tana tsara abubuwan da zata yi a washegarin in sun koma gida saboda daga Ammi har Umman ta sun gama zuzuta mata kyawun gidan ta sun sanar da ita yadda aka tsara masu gidan very portable kuma an gyare ko ina jiran zuwar su kawai ake yi dan har abincin da za'a masu washegarin an gama harhaɗa su a row suna kamo hanya za'a fara dafa masu,duk sun saka mata kwaɗayin gidan nata a ran ta ga ƴan uwan ta sun gama kwaɗaita mata jin daɗin rayuwar da zasu yi a gidan su dan gida ne mai tsarin gaske wanda yake situated a Apo Hills birnin tarayya na ABJ.. Juyawa tayi bisa kan gadon tana ƙara tuno rayuwar da suka yi a gidan har zuwa goodnight da suka yi da juna cikin ƴar kwanakin nan da suka zauna inuwa ɗaya. Wato wano irin zama ne suka yi wanda ke tattare da tsantsar kulawa da daraja juna haɗe da taka tsantsan dan gudun ɓacin ran wani a cikin su ga so da ke girgiza su a karkace for her,she is aware amma shi kam bai ɗaukar hakan a bakin komai ya fi dangana hakan da zaman taren da suka yi wa da shi ya janyo masu jituwa mai tsananin gaske.. Ita kaɗai ta rinƙa analysis ɗin ta sam babu wani abin da ya shiga tsakanin su tun da aka ɗaura auren har kawo yau da yake masu daren ƙarshe a ƙasar,kuma abin bai dame ta ba dan ta san duk wani abin da zai rikita sa ta mai kuma ta san ya ruɗe ba kaɗan ba.. Tana nan kwancen ta ji ya turo ƙofar ɗakin dama akwai haske a ɗakin dan haka ya sami direct access na kallon ta,ƙare ma jikin ta kallo yayi sai ya ji wani abin na taso mai from nowhere sai ya haɗiye yawu haɗe da buɗe baki da nufin gaya mata abin da ya kawo sa amma sai me?kasa magana yayi dan kayan jikin ta have tempted and seduced him already. Tana kallon sa gaban ta na faɗi shi kuma ya ƙi cire idanun sa daga kan ta wani mugu mugun muguwar sha'awar junan su ne ya taso masu,strong desire ne ke ɗeban su but sun kasa aiwatar da komai sai idanun su da ke aikin aiken da sukewa junan su mai ɗauke da saƙonni daban daban masu girman gaske..

0 Comments