IYA RUWA FIDDAH KAI CHAPTER 4

IYA RUWA FIDDAH KAI CHAPTER 4
Sauri tayi ta ƙarasa zuwa gadon jikin ta na mazari idanun ta na ƙaiƙayi zuciyar ta na kwaɓon ta a'ah fah halan sakamakon zullumin da take yi da saka abin a ran ta shi yasa deception ya riske ta dan dai ta amince da mafarke mafarken da take yi but unluckily enough for her tana zuwa hannun ya daina motsi zama tayi daɓas a kan kujerar da ke kusa da side drawer sai ga hawaye na tsere a kan kyakyawar angelic innocent face ɗin ta babu kwalliya a fuskar amma is naturally glowing saboda irin hutun da yake samu haɗe da kula,kai hannun ta tayi kan comforter ɗin ta yaye gefen da ta ga kamar yana motsi ta ƙurawa hannun ido sai kallon hannun take yi kamar ta mai magana ta ce ya motsa kusan 5 minutes tana kallon hannun ko zai motsa amma bai motsa ba sai ta cigaba da kuka mai cin rai kukan tsakanin ta da Allah take yin sa dan har shesheƙa take yi kasa furta komai tayi sai kukan dan shi kaɗai ne mafita a gare ta ta ɗau lokaci tana kukan daga bisani ta miƙe ta gyara mai comforter ta juya ta fita ta koma ɗakin ta breakfast ta taɓa kaɗan ta yi saƙo ta telegram dake ɗakin dan a kawo mata morning drug na ta because 6am medication ya wuce sai dai na 6pm jim kaɗan sai ga nurse ta shigo suka gaisa ta miƙa mata medication ɗin ta sha sannan ta fita ita kuma ta kwanta cikin wani hali tun tana iya fidda hawaye har dai bacci mai nauyi ya ɗauke ta..+ Da Bahajjatu ta dawo ta iske ta tana bacci sai tayi mamaki kuma da ganin baccin an san ba na daɗin rai bane na wahala ne dan ga shatin hawaye nan a kan fuskar ta kuma breathing pattern na ta ya chanza ba kamar mai bacci cikin kwanciyar hankali ba sai ta tausayawa aminiyar tata duk a tunanin ta tsaban tausayin ɗanuwan ta ne ya sa ta kasa sukuni sai ta zauna ta zuba mata idanu tana kallon ta shigowar Hajiya Zeenat ne ya sa ta miƙe da sauri ta ce "Umma yanzu ta sami baccin dan jiya a wahale ta yi baccin ba mai daɗi ta yi ba please kar a tashe ta"ta saka fuskar tausayi sai ta bawa Umman dariyar ta ce "Toh Allah ya baku haƙuri dama dubiya na zo yi kafin mu tafi dan jiya Abban ku ke sanar da ni wai in shirya zamu tafi Nigeria mu dawo nan da sati ɗaya kuma late notification ya bani shi yasa na zo sallamar ku but an kora ni shikenan ni na tafi"tayi maganar tana mai dariyar Bahajjatu da ta haƙiƙance akan ita dai kar a tayar mata da aminiya. Dakatar da ita tayi ta hanyar ce mata "Umma please in kun tafi akwai wata yarinya a kusa da da boutique ɗi na da ke kusa da parks and garden suna da babban manicure da pedicure na gargajiya suna ƙoƙari please umma ki ce ni da kai na na ce ta haɗo min items da ake haɗawa a gyara jiki irin dai wanda take min ta haɗo da steps da ake bi dan haɗa su da amfani da su wai na ce first grade manicure treatments nake so ba 3rd grade da suke yiwa mutani ba saboda ina ta trying line nata amma baya shiga kuma private line ɗi na bana son kiran ta da shi please Umma ki aiki Bilal ya amso min dan in na ce ya amso min da kai na ba zai tafi ba kuma ina buƙatar su ne"girgiza kai kawai Umma tayi dan bata gano cewa Bilkisu ake son yiwa gyaran ba sai ta ce "Toh le Baha in ban da abinki kina nan Bilal na chan wa zaki yiwa gyaran jiki"??sai a nan ta jo kunya dan haka ta ce "Laa Umma wallahi ma kaina zan yi ba shi ba..please Umma kar ki bari Ammi ta sani if not sai ta fara faɗan bata yarda ba please"murmushi Hajiya Zeenat tayi dan yaran na su Allah ne ya taya su rainon su bisa tsaftattaciyar tarbiya dan a zamanin yanzu yaran da ke jin kan su waɗanda shekarun su ma bai kai na su Bahajjatun ba muddin suka ga suna aikin kan su basu da wata matsala toh kuwa ganin kan su suke kamar sarakai iyayen nasu ma a hoto suke kallon su but su sai Allah ya kare masu nasu ƴaƴan gasu dai gabaɗayan su aiki suke yi but har yanzu fear da aka yi installing masu tun yarintar su tana nan bata fita ba dan haka basu iya yin abu kai tsaye daga matan har mazan har da ma dai su iyayen sun kasance masu son hutu masu yawon buɗe ido ƙasa daban daban most of the time suna barin yaran ba tare da masu tsaro ko duba su ba saboda sun yarda da tarbiyar da suka basu sun kuma san ba zasu yi abin da zai janyo masu matsala ba. Bayan ta gama tunanin rayuwar su sai ta kalli Bahajjatu ta ce "Alright shi da kan sa zai karɓo miki maybe ma ya kawo da kan sa dan na san dai shi za'a wa kwalliyar kuma ba zai kyautu a ce an yi abu dan shi ba sannan bai gani ba"sai tayi dariya itakuma ta murmusa kafin ta ce "A'a fah Umma ni ba ni zan yi gyaran ba ajiyewa kawai zan yi zuwa wani lokacin"ta faɗa tana mai juyar da fuskar ta sai Umma ta yi dariya ta ce "Kan ku ake ji yaran nan muma mun yi wannan har ma wanda ta fi naku za ma ku dawo kan hanya ne"daga haka ta fita abin ta ta nufi hanyar ɗakin Zaid dan ganawa da Hajiya Madina sabida basu sami damar yin magana ba a daren jiya sakamakon tsalawa da dare yayi kuma a lokacin prof ke sanar da ita batun tafiyar wanda ta ga bai kyautu ba ta kira ta a daren kai tsaye shi yasa ta bari har yau dan ta mata bayanin abin da zai mayar da su gidan On reaching there ta hango ta zaune tana danna wayar ta kamar dai abu mai muhimmanci take yi a wayar sai ta yi sallama ɗagowa tayi ta amsa mata sallamar haɗe da cewa "Hajiya har kun uso da wurwuri haka"?ta faɗa tana mai ajiye wayar a gefe.amsa mata ta yi tana mai zaunawa ta ce "Eh har fah mun iso Hajiya,mun tashi lafiya"amsa mata tayi suka tambayi junan su how their night went bayan hakan ne Hajiya Zeenat ta sanar da ita cewa komawa Nigeria zasu yi ta kuma sanar da ita dalilin komawar su but bata gaya mata har da dalilin maganin Zaid da zasu karɓo ba ya sa zasu tafin "Toh da ƙarfe nawa jirgin naku zai tashi"?tambayar da Hajiya Madina ta mata kenan sai ta numfasa kafin ta ce "Ya ce jirgin ƙarfe tara na safen nan zamu bi shi yasa ma na yi saurin zuwa ina ganin ya sanar da Dr ai" "Eh toh ba shakka maybe sun yi maganar but tafiya da wurwuri haka short notice Allah dai ya kai ku lafiya,kuma kika ce 1week kawai zaku yi"?amsa mata Hajiya Zeenat tayi ta ce "Eh,ni kaina na rasa me yasa ya kasa sanar da ni tun da wuri sai tsakiyar dare nima ban shiryawa tafiyar ba but kin san halin prof komai sharp sharp ne"sai suka ɗan dara dan gaskiya prof duk da tsufar sa na tsayin shekaru dan a wasu yankin mutum mai shekarun sa ba su iya yin abubuwan da yake yi but shi sakamakon agility na sa da tun yana ganiyar shekarun sa ya kasance a jinin jikin sa sai abin ya bisa har tsufar sa ko a asibitocin sa in har aka kawo wasu cases da su yaran yake basu wahala wato young doctors da ke aiki a nan,shi ake kira shi ke iya handling hakan ya sa sunan sa bai bar yaɗa asibitoci ba dan banbancin su da Dr Maher shi ne shi prof komai na ƙarfi ne wanda Bilkisu ta kwaso shi a wannan fannin dan itama haka take komai na ƙarfi ne bata damu wai she is tiny ba all she knows shi ne in har ta saka hannun ta a jikin mutum da sunan surgery ko treatment bata ɗagawa sai an sami sakamakon da ya gamsar da ita while a fannin Dr Maher kuma komai nashi cikin sanyi da lumana yake yi dan shi gani yake lokacin aikin ƙarfi ya wuce a wurin sa dan haka yake barin young doctors na taking over a asibitin sa iyakar sa ya basu shawarwari masu amfani shi gani yake yanzu ƙarfin sa lies only in his wife's wish kuma shine yawace yawacen da suke yi wanda shi kuma Dr Zaid ya ɗauko sa a fannin lumana sai dai shi bai da sanyin jiki when it comes to work he is very active.. Ɗan hira suka taɓa suna cikin hiran ne wayar Hajiya Zeenat ya ɗau ruri,cirowa tayi daga jakar ta ta duba sai ta ga mai kiran murmushi tayi ta kara a kunnen ta ta ce "Gani nan zuwa prof kaii ni Allah nagode ma"ta kashe wayar tana tashi tsaye Hajiya Madina ma tashin tayi tana dariya ta ce "Ba dai har ya gama ba" "Hmm ya gaman kenan shi fah prof akwai asassawa wallahi musamman in ya ga ina ɗaga mai ƙafa"dariya suka yi suka tafa sannan Hajiya Madina ta fara fita ita kuma Hajiya Zeenat ta nufi gadon Zaid ta kalle shi kafin ta ce "InshaAllah zaka farfaɗo Zaid cikin hukuncin ubangiji"addu'ar da ta mai kenan ta fita. A daidai bakin ƙofar ɗakin suka yi kiciɓis da prof yana magana da Dr Maher jiran su suka yi har suka kammala wanda a nan suka yi bankwanan sai sun dawo dan babu wanda zai kula da Zaid in suka ce rakiyar su zasu yi. Cab ne ya kai su har airport bayan ƴan wasu mintuna jirgin ya tashi addu'a suka yi daga haka suka shiga tattaunawa akan batun abin da zai kai su Nigeria wanda muhimmin abin shine maganin Zaid da zasu karɓo,wanda already sun yi wa Dr Ruzu bayanin komai kuma yayi fixing masu appointment wanda shine dalilin dawowar su cikin gaggawa ba tare da sun shirya ba dalili na biyu shine extensive injury da wani yayi sustaining wanda daga Dr Afzal har sauran doctors sun kasa sanin yanda zasu yi suturing for almost a month ana fama da shi da an ɗinke nan sai chan ya kunce da an ɗinke nan chan ya kunce wanda daga baya dai barin sa aka yi dan an gano cewa cutar Human immunodeficiency virus ne da shi(HIV) saura kaɗan ma ya shiga Aids dama duk mutum mai wannan cuta in har ciwo ya ji kokuma aka ce aiki za'a mai toh akan sami matsaloli irin haka sai ayi ta ɗinke ɗinke amma ya rinƙa kwancewa a rasa dalili(Toh dalilin shine jinin jikin su ya rigada ya lalace da ƙwayar cutar wanda a taƙaice dai jinin sa ba mai ƙarfi bane kuma duk inda mutum ke ciwo jini yana ɗaya daga abubuwa da ke taimakawa healing process a nan sai aka sami akasi jinin ya zama marar inganci madaɗin ƙwayoyin sinadarai da ke jinin da ke taimakawa dan ciwon ya warke ya rufu ba tare da an sami matsalar invasion of foreign bodies ba sai ya kasa aiwatar da aikin nan instead sai ciwon da ake ƙoƙarin warkarwa ya rinƙa faɗaɗa yana buɗewa saboda jinin da ke taimakawa wun circulating a area of injury is infectious and non sterile daga haka sai a rinƙa cewa mutum na da ƙan jiki,kokuma a ce ai gado yayi dan duk ayarin gidan su haka suke in sun sami matsalar da ya yi necessitating surgery toh ko an yi ba'a dacewa daga haka maganar so called "our village people" will come to play a nan za'a fara suspecting ana blaming ancestors da cewa they cast a strong powerful curse a family na wani ko na wance gashi nan ɗa ko jikar wani ya sami hatsari an ui ɗinki sau ba adadi amma abin bai yi ba in ba mutanin su ba wa zai janyo wannan rashin dacen blah blah blah sai a ƙarshe in akwai mai zurfin tunani sai ya ce ko dai gwada jinin sa za'a yi dan a ga meye musabbabin ƙin zaman aikin da ake mai toh sai a nan ne za'a gano wai yana da cutar sai kuma zagi da hantara ya dawo kan sa a fara jeopardising nasa a community forgetting that mutum na iya contacting cutar ta hanyoyi daban daban). They arrived safely and Bilal was the one that picked them daga airport yana ta zumuɗin jin ko Zaid ya farka ne amma bad answer ɗin nan ya samu wato not yet sai mood ɗin sa ya chanza a nan ya tambayi lafiyar twinien sa har gida bai bar su sun yi sukuni ba sai da motar ta tsaya suka fito suka yi cikin gida inda gabaɗayan family ɗin ke jiran dawowar su daga jamil da matar sa haɗe da baby zarah,Lukman da sauran ma'aikatan gidan farinciki ne ya luluɓe su ganin familyn na su all present except baby doctor da ke chan ƙasar samin lafiya. Welcome pleasantries aka yi exchanging daga nan baby zarah ta nufo grannyn ta ɗaga ta tayi tana mata wasa har dai ta haura da ita sama tana mata tsiyar kar ta ƙwace mata mijin ta dan idanun nan irin na Bilkisu ta kwaso dara dara,dariya kawai jama'ar falon ke ta yi har shima prof ɗin. A ranar dai sai chan wuraren 10pm suka kwanta inda su Jamil da matar sa suka koma gida yarinya ta tafi wun iyayen ta ta ƙi ita kuwa Hajiya Zeenat ta ce ai sai ta yi dan ba ta kwana mata a gida salon mijin ta ya ve yana so an yi rarrashin amma ta ƙi ji da bori da botsarewa aka danƙwafar da ita aka saka ta baccin dole da haka suka koma gida dan Hajiya Zeenat ta sanar da su in dai yini ne guda ta yarda ƴaƴan su su yi mata amma kwana baza ta lamunci haka ba ta raini iyaye ta raini ƴaƴan su ba zai saɓu ba.. Basu kwanta ba sai da Hajiya Zeenat ta shirya mai komai na washegari dan Dr Ruzu zai fara visiting kafin ya tafi asibitin wanda ya kai su har ƙarfe 12 na dare sai a lokacin suka kwanta,washegari da wurwuri ya shirya shi kaɗai yayi tafiyar sa zuwa HRR&T dan tun 7am ya bar gida bai kai ba sai 8am a hakan ma dan ya saka speed a tafiyar kenan saboda yayi ya gama ya wuce asibitin dan ganin in case ɗin nasu ne in kuma na referring ne sai a yi providing referral means dan abin na worsening each day. Yayi nasarar zuwa har ma ya gana da shi ya kuma mai bayanin dalla dalla Alhamdulilah ya bashi magungunan game da prescription da yadda za'a yi administering komai ya mai bayani suka yi settling da girmamawa suka rabu and yhe very good and sweet paer of it Dr Ruzu ya sanar da shi cewa matuƙar aka fara mai medication yadda yayi prescribing in less than a week yana iya farfaɗowa abin nan ba ƙaramar daɗi ta yiwa prof ba dan har kasa ɓoyewa yayi sai da ya kira Hajiya Zeenat ya labarta mata komai ai ko har guɗa tayi dan murna mata ba'a rabasu da budi'a sai da ya tsawatar mata akan godiya zatawa ubangiji da ya ɓullo masu da waraka a sauƙaƙe ba guɗa ba sai a nan ta ta ɗan dawo kan hanya ta shiga yiwa Allah kirari daga bisani ta rinƙa gode mai.. Daga nan asibitin sa ya tafi inda ya ga patient ɗin ya kuma yi ƴar bincike binciken da yakamata daga bisani ya gano cewa dole ne ayi referring nasa zuwa wata ƙasar dan method of surgery da za'a mai ya danganci fannin amfani da metal seal dan shine mafita a gare sa,an rubuta masa referral later an damƙa mai a hanun sa kuma an yiwa relatives ɗin sa bayanin komai dan haka aka saka masu kwanakin discharging nasu. °°°°°°°°°°°°°°°°° Tafiyar su Hajiya Zeenat da kusan awowi uku zuwa huɗu Bilkisu ta farfaɗo sai bata ga kowa a ɗakin ba dan haka ta shiga ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta zauna tana laluɓar wayar ta,ƙunna wayar tayi sai ga kira nan da sabuwar lamba kuma kamar lambar Nigeria ne dan haka sai ta ɗauka muryar ta a ɗan shaƙe tayi sallama,bai amsa ba sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa da "Wa'alaikumul salaaam baby na"!!har jan salam ɗin yayi kawai saboda farincikin ɗaga wayar sa da ta yi. Ko a magagin bacci ta tashi sarai zata shaida mammalakin muryar wanda ba kowa bane face Dr Aslam. From no where ta ji wani baƙin ciki ya kawo mata ziyara sai ta danne dai bata ce komai ba dan tana son sanin dalilin sa na ƙin zuwa duba su bayan an dawo da su daga ƙauyen nan kafin su zo nan ƙasar.jin bata ce da shi ƙala ba sai shi ya mata magana "Baby ya jikin ki da fatan dai kin farfaɗo garau babu wata damuwa kuma"?shiru tayi kamar bata jin sa shi kuwa ya san tana jin sa amma halin izza da jin kai irin nata ba zai taɓa barin ta ta amsa mai ba ko da kuwa amsawar mai muhimmanci ne sai kawai ya cigaba da maganar sa "Ɗazu Dr Afzal ke sanar da ni cewa Abban mu zai dawo nan Nigeria kuma zai zo asibiti saboda akwai wani babban case da muka kasa handling properly shine na tambayi Dr Afzal ɗin ko ya jikin ki ya ce min da sauƙi but i wasn't comfortable so i asked him to give me your phone digits da na karɓa kuma ban zauna ba sai yanzu shi yasa na kira ki da fatan dai kin warware sosai"?da alama dukkan abubuwan da ya faɗi daga zuciyar sa suka fito but ta yaya iyayen ta zasu tafi Nigeria amma bata da masaniya akai ko lafiya Allah ne masani. Bai yi fushi ba sai ya kuma cewa "Baby ina son visiting ɗin ki saboda lokacin da abin ya faru na sami labari but my dad send me to clear up something a wata ƙasar for almost a month ina chan i couldn't communicate with anyone dan jin yadda jikin ki yake na yi ƙoƙarin kiran ki but it wasn't reaching through,da na dawo Kuma na ji labarin barin ki ƙasar zuwa germany i wanted coming but our twin bro asked me not to worry too much ya ce min kina cikin ƙoshin lafiya and he told me that you have regain consciousness shi yasa na sami sauƙin damuwa ta but still ina da niyar zuwa ganin ki kafin ki dawo dan na san laifuka na sun yi yawa"!!ya ida maganar yana mai lowering muryar sa ƙasa maimakon ta ji haushin da take ji a kan sa ya rafu sai ta ji kamar ƙara ninka mata haushin sa aka yi a ran ta dan abin lura shine tun da ya fara maganar in banda kalmar "ki" da yake amfani da shi baya furta komai toh me yake nufi?zai ce bai san tare da Zaid suka sami matsalar ba kokuma tsabagen wulaƙancin da cin fuska ce urin ta Aslam ya sa bai nuna damuwar sa akan shi Zaid ɗin ba?bata tsaya jiran shawarar da zuciyar ta zata bata ba sai kawai ta shiga balbale sa kamar dai yadda take a da "Dakata mana Aslam..so kake ka ce min baka da masaniya akan cewa ba ni kaɗai na sami wannan matsalar ba amma har da Zaid?so kake ka gaya min an baka details na komai da ya faru da ni but an manta a sanar da kai ciki har da Zaid?koko tsabagen i don't care halin ka ne kake son nunawa a wannan situation ɗin ma?mutumin da tun da abin nan ya faru ko inda kansa yake bai sani sannan wai baka tambayi nasa lafiyar ba ka dage kana son sanin ya tawa lafiyar.toh ka sani ko wani ɗan adam na da jini a jikin sa yadda kaje jin ka ruɗe ka damu da son sanin lafiya ta ni kaɗai toh shima Zaid ɗin miliyoyin mitani ne ka mararin jin lafiyar sa ba ma mutum ɗaya tal ba dan haka ka ga mallam sai anjima you just spoil the moon"..zata kashe wayar ya dakatar da ita "Wait... Waitttt..tsaya,haba baby wannan zafin rai irin taki har tsoro take bani.yanzu saboda Allah bany kin min adalci kenan?i am here sick and hungry of you just your face alone amma kika yi attacking ɗi na da maganar wannan mai kama da basamuden marar tsarin kallon?baby kin fah sani ba dan Allah Zaid yayi selecting naki a matsayin wacce zai tafi outreach da ita ba sai dan ya wahal da ke ya kuma ƙuntata min dan ya san na riga shi shiga a wurin ki kuma na fisa komai duk fah shi yasa ya yi hakan sai gashi a hanyar ƙuntata min cikin ruwan sanyi Allah ya nuna mai he can deal with him duk wayon sa da dabarar sa yanzu fah alhakin zaluntar mu ke bibiyar sa in ba haka ba ta yaya kawai zai zo ya ɗauke li ya kai ki wata uwa duniyar dabbobi da jakai da sunan outreach kawai dai Allah ne ya kama sa shi yasa ma ni ban tsaya ɓata lokaci na dan sanin ko ya nasa jikin yake ba"..ran maza ya ɓaci dan shi tunda ta fara maganar yake hasashen kamar haƙar Zaid ya cimma ruwa dan yadda ta iya rufe idanun ta ta burbuɗa masa masifa akan Dr Zaid Maher toh lallai in har ba wata abu ba ce a tsakanin su ba ba zata yiai haka ba. Tun da ya fara aibata da muzanta haɗe da kushe Zaid da halittar sa sai kawai ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi wanda daidai Aslam na dasa aya a surutun sa ita kuma ta datse wayar dan bata son ƙara jin muryar sa a take ta saka sa a black list ta wurga wayar kan gado ta koma da baya ta kwanta tana nazarin maganganun Baha so take ta tantance ta cire magana ɗaya mai amfani amma ta kasa haɗa maganganun ta maida su kalma ɗaya mai ma'ana ita kanta bata san me take ji game da Zaid ba taysayin sa ne ke ɗawainiya da ita kokuma a'a damuwa da shi da lafiyar sa tayi kokuma wani abin ne na daban Allah ne kaɗai masanin wannan abin da take ji a zuciyar ta dan she become over reactive whenever is about Zaid itama bata san dalili ba.wani juyi tayi akan gadon tana cigaba da tunanin ta sai ta ji sallama ɗago kanta tayi dan ganin ko waye sai ta Ammi ce tashi tayi ta zauna a kan gadon tana mai gaida Ammin amsawa tayi ta tambaye ta ya ƙarfin jiki "Baby dama zuwa nayi in sanar da ke cewa Umman ku da Abban mu sun tadi Nigeria sakamakon wani aiki da ya taso wanda dole sai Abban ku na nan"ta ɗan yi briefing mata komai kamar dai yadda suka sanar da su sai ta ce "Eh Ammi ai yanzu muka gama waya da Aslam ya sanar da ni" "Oh ya kira ki ne ashe"yadda tayi maganar sai ya saka Bilkisu ɗagowa tana kallon yanayin ko in kular da ta saka yayin tambayar ta sai ta girgiza kai kawai. Toh Ammi ƴar ayi a wuce wurin ne dan haka ta gyara zaman ta da kyau ta fuskanci Bilkisu ta fara zayyano mata abin da ke tace da ita wanda ba komai bane face maganar auren su da Zaid A firgice da tsoro tab zuciyar ta ta shiga girgiza wa Ammi kai tana faɗin "A'ah Ammi baku san komai ba kawai abin da idanun ku ya gane maku kuka sani apart from that you all know nothing between i and Zaid"ta ruɗe uya ruɗewa sai Hajiya Madina ta riƙo hannun ta da ɗan force ta ce "Bilkisu Zaid ɗa na ne kuma sai da yarda da amincewa ta zai wulaƙanta ki wanda har duniya ta naɗe ba zan lamunci hakan ba what we see or didn't see doesn't matter abin da ya fi muhimmanci shi ne amincewar ki akan zaki auri Zaid ki kula da shi kafin ya farfaɗo dan kema ki sami lada bibbiyu ga na aure ga na jinyar sa da kika yi ko baki son samin wannan ni'imomi da rahama ta ubangiji ne Bilkisu"?sai ga hawaye na bin fuskar ta dan ita gaskiya ba ta son yin rayuwar aure da mutumin da bai son ta mutumin da laƙaba mai ita za'a yi it will appear like a big disgrace to her yadda take magarki da burin jin daɗin rayuwar aure da mijin ta kamar dai yadda iyayen su ke yi sai a ce She end up with someone she doesn't love someone that doesn't love her wabda basu yi courtship ba kawai daga sama yana ciwo ba ma a cikin hayyacin sa ba a ɗaura masa auren ta inaa impossible ita dama tausayin sa lawai take ji banda wannan babu wani abin. Ganin kukan ba mai ƙarewa bane sai Hajiya Madina ta shiga ƙwabon ta dan ta san in tayi sanya tayi lagwa lagwa toh ba abu mai wuya bane a wun Bilkisu ta ce bata yi kuma in hakan ya faru uta zata cutu dan ta daɗe da yin mafarkin kasancewar su inuwa guda "Bilkisu ji ni da kyau,kin ga Allah in kika bari tunanin zuciya barkatai suka rinjaye ki?toh wallahi babu ke babu samin natsuwa da kwanciyar hankali har abada,haba,Zaid ɗa na ne kamar yadda kike ɗiya a gare ni ko babu komai akwai amintaka da dangantaka tsakanin mu da iyayen ki which equally make Zaid to be your brother,ko ba komai a matsayin ki ta doctor mai kula da kuma kare lafiya da matsalar client ɗin ta in kika dubi Zaid da kyau zaki hango damuwar sa Bilkisu,uhmm,Zaid na buƙatar kula daga wun wanda ya wuce ƙani ko iba ko uwan sa yana buƙatar kula ne mai zurfi daga wun sirrin sa,muharram ɗin sa,matar sa which he have not,amma kin ga yanzu with the little closeness da nake gani a tsakanin ku da yadda kike reacting when it comes to Zaid sai na ga a duniyar nan babu wacce ta cancanta ta kuma dace da zama da amsa sunan matar Zaid sama da ke Bilkisu forget about his jinnkai stuff duk izzar sa sai dai in ba haɗuwa yayi da mace wayayyiya ba kamar dai ke,matuƙar Zaid ya farfaɗo ya ji cewa kece matar sa believe me he will appreciation our effort kuma kar ki saka a ran ki wai in ya farfaɗo ya san cewa ke matar sa ce zai wulaƙanta ki a'a ba zai yi hakan ba dan zaɓi na ce ke kuma ko bana nan Zaid ba zai taɓa wulaƙanta abi na ba dan haka ki kwantar da hankalin ki ki amince tun kafin ma ya farfaɗon ki fara samin ladar bautar auten ki da ladar jinyar sa da zaki fara i can't force you zan baki time ki yi tunani but kae yayi exceeding sama da 48hours".ta miƙe zata fita ta ce "And don't forget to pray to Allah for guidance hmm"?da ido ta bita har ta fita daga ɗakin kafin ta sauke idanun ta masu fidda ƙwaa ƙasa tana maganar zuci "Lallai Ammi bata san komai ba game da su biyun,mutumin da ba son ta yake ba tun asali har ya iya ɗaukar ta ya kaita ƙauyen nan da sunan punishment ina ga in ya san an aura mishi ita in ya farfaɗo?kasbe ta zai yi kawai ya huta..da Ammi ke maganar bata ga macen da ta dace da zama da kuma amsa sunan matar zaid ba sai abin ya bata dariyar baƙin ciki dan tuno da Asma'u da tayi,hmm Ammi bata san cewa ɗan ta na cikin soyayya mai zurfi da wata ba watan ma yarinyar da ta januo mai shiga wannan halin".. Lokaci sosai ta ɗiba tana saƙawa akan batun a ƙarshe dai ta tsaya akan zata sanar da mahaifiyar ta kawai dan ita kaɗaice zata san abin da fi dacewa da ita a rayuwa in ma auren Zaid ko rashin sa.. Tashi tayi ta tafi ta wanko fuskar ta ta dawo ta goge ta gyara gyalen ta ta fito saɗaf saɗaf ta kama hanyar ɗakin Zaid wai duk dan kar Ammi ta ganta ta ɗauka ko dan ta damu da shine bare tayi concluding abin da ke ran ta na cewa tana son zaid har ta zafafa akan maganar auren. Wulup ta shige ɗakin yayin da Hajiya Madina da ke daga balcony na sama tana kallon ta ta saka dariyar wautar ta imagine mai cewa a'ah ba'a san abin da ke faruwa ba tsakanin su su biyun ba kenan tana satar hanya kamar wacce tayi sata ta taho ɗakin sa dan dai ta gansa anjima kuma she will claim ita ba haka ba dariya kawai Hajiya Madina ke yi dan ta matsu bata ga ɗan ta ya fara gwadawa Bilkisun soyayyar sa ba dan kuwa shakka babu matuƙar ya san ita ta yi ɗawainiya da shi tun daga ƙauyen nan har izuwa farfaɗowar sa toh ta san siga da launin soyayyar da zai gwada mata babu makusa da irin tasu da suke yi dan haka ta girgiza kai da ragowar murmushi a kan fuskar ta ta fara saukowa tana nazari a zuciyar ta.. At first da ta shiga ɗakin zuba mai idanu tayi sai daga baya ta zauna ta cigaba da kallon sa azimun babu shakka so take ta fitar da wani abu daga fuskar sa sai dai hakan bai samu ba dan ɓata lokaci tayi tana kallon sa bata san time ya tafi ba sai da ta ji gyaran murya sai tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa,. Ammi ce ta shigo ɗakin dan tuntuni take kallon ta ta transparent glass door dake ɗakin nazarin ta take yi shi yasa bata yi interrupting mata analysis ba har sai da ta ga kamar kan ta zai buga dan dagewa tayi tana kallon sa tana ta wasu abubuwa masu kama da analysis. Kunya ne ya kama ta Ammi caught her again oh no sai ta fara inda inda tun ma kafin Ammin tayi magana wanda ya saka Ammi fitar da dariyar ta fili dan kasa riƙe sa tayi, "Wait Bilkisu,wa ya saka ki a gaba akan sai kin yi explaining dalilin ki na shigowa ganin Zaid?i guess babu right?common dear is a natural feeling feel free and express your feelings is not a crime rather is it a sin,open your eyes and heart,learn to accommodate the stranger in your heart,ki daina ɓoye abin da kike ji game da Zaid,Bilkisu da a ce ban hango wannan abin ba,da a ce ban ga tsantsar so da kike yiwa Zaid ba wallahi tallahi ko da shi Zaid ɗin ne ke son ki amma ke baki son sa toh wallahi ba zan taɓa yarda ya aure ki ba ko da hakan na nufin threat ne ma rayuwar sa dan haka baby,ki amince da abin da zuciyar ki ke faɗa maki"ta ƙarasa maganar tana mai daga kafaɗun ta. Ko uhum bata ce ba sai ta fita abin ta dan waɗannan maganganu da Ammi ta mata kamar watsa mata garwashi tayi saboda yadda take rera kalaman ta sai suka rinƙa taso mata da tunanin Asma'u dan ita kaɗai ta san ya take ji a ran ta a duk sanda ta tuna da Asma'u ta kuma tuna da abin da ya faru da su abin ba ƙaramin rura mata wutar ƙiyayyar yarinyar yake ba shi wanda ya aikata abin ma bata jin haushin sa kamar yadda take jin haushin yarinyar kuma all she can see and say shine Zaid is blindly in love with that villager what if he regain consciousness and decided not to make her his Mrs?what if he develops love for that strange girl and not her?what if he hates her after knowing that she is his wife and life partner?ya salam sai ta zauna tana tunanin mafita gashi su Hajiya Zeenat basu riga sun yi landing ba bare ta kira ta ta sanar da ita abin da ke gudana. Throughout ranar babu wani kuzari ko walwala a tattare da ita iya tayi sallah ta ci abinci ta sha magani sai kwanciya amma baccin ma ba zuwa yake yi ba saboda tsananin damuwa da ta sakawa kan ta duk brain ɗin ta ya ɗau chaji ta rasa menene abin nan da ya ke mata ƙatutu a ƙirjin ta babu damar ta ji sunan Zaid sai gaban ta ya faɗi hatta ita kanta in zata yi yunƙurin kirab sunan sa sai ta yi da gaske if nit kasa furtawa take,toh me hakan ke nufi?wannan tambayar ta tsaya mata a rai sosai duk ta kasa shikir but she knows that damuwar ta zai ƙare da zarar ta yi magana da Umman ta. A haka Bahajjatu ta same ta sai ta kira sunan ta yayin da take ƙoƙarin zama "Beelove"amsa mata tayi ta ce "Na'am Baha"sai ta tashi ta zauna tana son gaya mata wani abin but bata san yadda zata fahimci maganar ba but she have to say it "Baha ni ko na ce me zai hana a yiwa Zaid gyaran fuska he is going out of his usual appearance kuma kamar ba wanda ya shirya gyara shi haka za'a cigaba da kallon sa dan baya cikin hayyacin sa"?tsayawa kallon ta Bahajjatu tayi dan ta bata mamaki wato har lura take da yanayin fuskar sa tsabagen so da ya matu mahaukacin kamu but she doesn't wanna admit it sai ta ce "Toh ke in banda abin ki beelove ai ina ga since babu wanda ya lura da hakan sai ke why not ki tafi ki mai gyaran fuskar coz na ga yanzu ba lafiya kike nema ba dan kin ji sauƙi already sai dai ki yi jinyar marar lafiya and i guess babu zunubi dan mata ta gyara mijin ta for her own satisfactory purpose right"??da teasing tune ta kammala maganar wanda ya sa Bilkisu jefar ta da ƙaramar pillow da aka yi beautifying gadon da shi,gudu tayi tana dariya ita kuma ta ɓata fuska a dole an laƙaba mata abin da bata lamunta da shi ba sai ta ce "Amma dai kin san ban son wannan abin ko Baha?zamu fah ɓata ta yaya zaki rinƙa kiran min matsayin da ban kai ba a ina na zamo matar Zaid stop it please before some could hear you so annoying"!!ta ƙarasa kamar wata ƙaramar yarinyar da ke shirin sakin kuka sai kawai Bahajjatu ta cigaba da dariyar ta kafin ta dawo kusa da ita ta zauna ta ce "Babes,ba fah laifi bane dan kin yarda da abin da kike ji game da yaya na,wallahi kin ji rantsuwar musulm,yau da ace wata ce ba ke ba ta ke ƙaryata feelings ɗin ta akan yaya na toh Allah ban bin ta kanta sai dai ma in daɗa dulmiya ta ta amince akan bata son sa but ke Bilkisu both our parents have agreed to this wedding dan sun san alkhairi ne cike a cikin ta abin da suka hango mu bamu hango ba kuma baki san wani abu ba,kin ga yaya na da kike gani wallahi bai da matsala bai da damuwa ko kaɗan hasalima he is a free person very gentile and kind kawai borin fuskar sa kike gani har kike ɗaukar hakan a matsayin halin sa ne but i will tell you a little secret about my brother"sai ta zama serious haɗe da chanza fuskar alamun maganar da zata faɗa ɗin babba ce mai muhimmanci sai itama Bilkisun ta maida hankalin ta gabaɗaya kan aminiyar tata dan jin me zata sanar da ita "My brother happens to be the most quit caring and gentile out of all my brothers shi kaɗai ne mai hanƙuri da juriyar duk wasu abubuwan da ke tasowa,bai taɓa son wata ba kuma babu macen da ta taɓa gigin kusanto sa da sunan so ko da kuwa tana son sa ne he is committed to his duties abu ɗaya da ya tsaya mai a rai kuma yake damun sa shine akwai wata yarinya da ya taɓa gaya min cewa yana da wani feelings akan ta wanda bai sani ba so ne kokuma shaƙuwa ce bai sani ba amma ya san in har ya ga yarinyar yakan ji wani abu game da ita is somehow mix bai iya tantance menene kuma ya kasa sanar da kowa ya barwa kansa shi kaɗai sai ni da yayi min bayanin kaɗan i guess that girl is the Asma'u girl in that village,wani abin da ya sa na ƙara yarda cewa ba son yarinyar yake ba illah shaƙuwa da tausaya mata da yake yi shine sai da ya gargaɗe ni akan maganar kar ta wuce tsakanin mu mu biyu saboda ya san in har Ammi ta ji toh Allah ne kawai zai taimake shi daga hannun ta dan fushi zata yi da shi and yiu know what?ko da wasa bai taɓa yin maganar da Ammi ba kenan ba son yarinyar yake ba dan da son ta yake toh babu wani abin da zai saka shi jin shakkar nunawa duniya ma budurwar sa har Ammi zai nuna mata but no he is not comfortable with that decision so you see in har yaya bai san matsayin yarinyar nan a rayuwar sa ba i don't think you should play with this opportunity for making him yours kin fah san a family ɗin mu namiji mace ɗaya ya ke rayuwar sa da,which is equivalent to having a single life partner in kuwa ya auri yarinyar nan shikenan ya rasa damar auren ki and our parents dream is for the two of you to get married and leave a happy life wanda nake fatan kafin ya farka ki zamo matar sa because i don't want him to marry that village girl dan bai san abin da yake so ba har yanzu bai san menene taste ɗin sa ba marrying that girl will shatter all his dreams away saboda yaya na ɗan soyayya ne yana son yin rayuwar soyayya ba kaɗan ba da matar da zai aure wanda ko da na duba sai na ga kuna a page ɗaya da juna dan kema ƴar son soyayya ce but kin rasa da wa zaki yi rayuwar soyayyar yadda kika daɗe kina mafarki,Aslam was never your dream guy ni na san ba kya son sa kuma in har kika zuba mai ido yana iya tura iyayen sa su tafi gida a yi maganar auren ku because yadda yake yin abu is like irin kin amince mai ɗin nan ne dan haka Abba might not think twice sai ya amimce though na san shima yana son auren ku da yaya na but he won't force you in ya tambaye ki kika ce mai a'a ba ki son yaya na yana iya barin ki ki zaɓi wanda kike so wanda a gare ni hakan babban asara ne dan i want our friendship to go beyond this so please Bilkisu ki natsu ki duba wannan maganar da na gaya maki ki kuma yi la'akari da future ɗin ki kafin ki zaɓi life partner ba wai kamun ƙafa nake yiwa yaya na ba a'a am here acting like a sister to you saboda na san Umma zaki faɗawa damuwar ki but ba lallai bane ta feɗe maki komai akan rayuwar ki ba kamar yadda ni zan sanar da ke ba just think about our conversation before you make the decision humm"?girgiza mata kai ta yi dan bata sani ba sai yanzu da aka sanar da ita,a yanzu take jin kamar tana da wani abu a ran ta wanda bata tsammanin zata iya sharing nasa da kowa sai mutum ɗaya who could he be?is it Zaid?did she love him kamar yadda ake faɗa?yin wannan tunani na ƙarshe ya sa ta ɗago idanun ta ta ɗora su kan Bahajjatu sai ta kasa furta komai illah kallon da take bin ta da shi daga bisani ta numfasa ta ce "Nagode Baha nagode da shawarwarin da kika bani nagode da kulawar ki gare ni indeed you are a friend and a sister to me a da na yi yunƙurin sanar da Umma danuwa ta saboda Ammi 48hours ta bani dan yanke shawarar maganar da muka yi da ita but you coming at the appropriate time da nake cikin buƙatar shawarar wani ya saka ni jin kai na as the most luckiest kuma inshaAllah i will follow my heart because i was a witness akan maganar Zaid da Asma'u,ko ba komai i don't think i will allow her to marry him koda ban aure sa ba bana jin zan iya zuba ido in kalle sa yana auren yarinyar da ta so ganin bayan sa dan da ita aka mai wannan abin Baha ita ta nuna wa Mudan hanyar da muka bi har suka biyo mu suka mai wannan abin sannan kina tsammani zan kyale ta ta aure sa??i can't i just can't bear to see him leaving with that hippocrate chameleon she is a deceiver he trusted and believe in her but she went right behind his back and stabbed him kina ganin wannan ta cancanci zama abokiyar rayuwar Zaid?ko ba'a faɗa ba yarinyar da bata da tsarin nan za'a bar sa ya aura"?kukan da ya taso mata ne ta fito da shi dan abin na ƙona mata rai sosai. Rarrashin ta Bahajjatu ta ke yi a lokaci guda tana mamakin irin mummunar so da ya kama aminiyar ta wanda yake fizgar ta ta ko ina amma ita ɗin ta ƙi yarda da hakan hasalima har yanzu bata gane cewa son Zaid ne da kishin sa ya mata dabaibayi haɗe da kane kane a zuciya ba dan alamu sun nuna ƙarara cewa mugun kishin Zaid ne ke barazana da zuciyar aminiyar tata. Kallon ta tayi ta ce "Beelove ba kya ganin kina wahalar da zuciyar ki da yawa akan zancen zuciyar ki"?ɗagowa tayi haɗe da share hawayen ta da bayan hannun ta sai ta ce "Baha ban sani ba,wallahi ban sani ba ni kaina ba son wannan halin da nake ciki nake ba sam ban san yadda zan yi ba"!!da cracking voice ta ida maganar wanda ya saka Bahajjatu girgiza kai kawai dan ta san ko shekara zata yi tana mata bayanin feelings da take da shi towards her brother ba ganewa zata yi dan haka ta ɗan yi tapping shoulder ɗin ta tana mai cewa "Beelove zan bar ki ki gano abin da ke damin ki a zuciyar ki wanda ke faman wahal da ke"kallon juna suka yi kafin Bahajjatu ta fita daga ɗakin tana alhinin irin wannan soyayya a da gani take ita da Bilal are the best couples but she has been proven wrong saboda yadda ta ga so da kishin yayan ta a idanuwan Bilkisu abin ba'a cewa komai amma ita sai ta ga kamar son da takewa yayan nata yana so ya mata yawa dan haka wun Ammi ta wuce straight dan shafa mata labarin komai. ********** _NIGERIA_ _1:00am_ Kwance Hajiya Zeenat take tana ta juya juye ta matsu washegari yayi ta ga ɗiyar ta dan tun da suka dawo bata yi magana da ita ba most of the time tana bacci take kira shi yasa da Dr Muhammad ya sanar da ita cewa tunda komai ya tafi masu yadda ya dace ba sai sun kai one week ɗin ba ma just 4 days suka yi already kayan gyaran da Bahajjatu ta ce a karɓo mata ta aiki Bilal ɗin ya amso mata ita kanta ta gama haɗe haɗen ta da zata gyara ɗiyar tata dan an gama fixing ɗauren auren biki ne dai ba za'a yi kasancewar halin da ake ciki ba na wani shagali ko nishaɗi bane,a cikin kwanaki huɗu da suka wuce Dr Aslam yayi nasarar shawo kan iyayen sa akan batun su tafi nema mai auren Bilkisun a cewar sa suna son juna kawai halin ƙyaliyar ta ne ya sa bata iya expressing son ta but suna son junan su iyayen sa sai da suka kuma tambayar sa ko ya tabbatar tana mai so irin wanda yake mata ya ce eh shi yasa suka shirya da abokan baban nasa biyu making them three suka tafi har gidan Dr Muhammad Sulaiman dan nemawa ɗan su auren ɗiyar sa babu sanarwa babu komai hakan ma harzuƙa Hajiya Zeenat yayi har ta so magana sai prof ya hana ta ya ce shi zai yi handling nasu dan haka ƙyale ba dan ran ta ya so ba. bayan gaisuwa ta mutunci da girmamawa prof ya tambaye su ko me ke tafe da su a nan amimin mahaifin Aslam ya mai bayanin abin da ya kawo su sai dai kash rashin sa'a amsar da ya basu ne ya sa suka kasa furta wani abin sai dai suka yi musabaha haɗe da godiya kafin su koma gida ai kuwa Aslam ya haɗu da fushin mahaifin sa ranar dan sai da ya ja mai kunne dan baya son irin hakan ya faru but ɗan sa ya janyo mai ko da Dr Aslam ya nemi sanin ko wanene mijin da aka ce an yiwa Bilkisu sai mahaifin ya sanar da shi wai ɗan gidan aminin mahaifin Bilkisun ne sunan sa Zaid sai ya ji gaban sa ya faɗi ran sa ya ɓaci dama wannan naƙasasshen har da halin da yake ciki sai ya mai shigar sauri ne wai,abin ba ƙaramin girgiza shi yayi ba dan haka ya rinƙa ƙiran layin ta amma bata ɗagawa ƙarshe ma message ta tura mai tana mai kashe mai warning akan ya fita harkar ta takaici ne ya ishe shi but bai haƙura ba ya san shi da Bilkisu are made for each other he saw it countless times in his dreams kuma an ce ai dreams can sometimes become reality shi yasa bai cire tsammani ba. A kwanakin ne kuma Dr Hussaini ya kawowa iyayen Bilkisu ziyara haɗe da tambayar su jikin marasa lafiya suka sanar da shi halin da ake ciki har ma da dalilin su na dawowan dan amsar mai magani godiya suka mai da nuna kulawar sa kafin daga ƙarshe Hajiya Zeenat ta matsu ta tambaye sa ko ya san wani abin akan yaron da ya ma ƴaƴan su wannan abin sai ya ɗan murmusa kawai kafin ya ce da su "Umma ai an wuce wurin tuntuni"!sai abin ya ɗaure masu kai dan ba su fahimci an wuce wurin ba sai prof ya tambaye sa dan ƙarin bayani "Dr bamu fahimce ka ba me kake nufi da an wuce wurin"?sai ya sauke ajiyar zuciya haɗe da fara labarta masu abin da ya faru "Wato bayan na dawo da su nan gida na kuma zuwa visiting na su after 2 days sai Bahajjatu ta tsare ni ta tambaye ni ko ina da masaniya akan abin da ya faru da yayan ta sai na sanar da ita komai da na sani ta min godiya muka rabu,bayan kamar kwanaki huɗu da haɗuwar mu da Bahajjatu sai yayan ta Hakim ya kawo min ziyara ta musamman a inda ya ce da ni in basa cikakken tarihin yaron da ya ma ɗanuwan sa wannan abin a iya tsawon rayuwa ta a ƙauyen koma ban yaɓa jin labarin tsagirin yaro kamar Mudan ba dan haka na sanar da shi komai sai na ga kamar ran sa ya ɓaci amma nayi calming nasa dan na san halin sa na zuciya a yadda muka rabu ya nuna min komai ya wuce ya kuma sanar da ni da zarar sun farfaɗo zai ɗaga ƙara ya shigar da hukuma cikin lamarin lafiya ƙalau muka rabu bai kuma nema na ba ban kuma ƙara jin wani abu ba a ƙauyen mai muni dangane da Mudan,kwatsam bayan tafiyar ku germany da kwanaki na sami kira daga wun mai garin koma wanda a gidan sa su Zaid suka zauna lokacin da suka tafi outreach shi ke sanar da ni wai akwai wasu yara biyu da suka tafi garin suka bi su har gida suka masu alheri daga ƙarshe suka nemi da a kai su gidan su Mudan a lokacin basu yi revealing identity ɗin su ba sai aka haɗa su da babban ɗan mai garin ya kai su har gidan su Mudan a nan ɗin ma alherin suka masu ba tare da sun sanar da su ɗin ko waye su ba sai suka nemi sanin inda shi Mudan ɗin yake akan wai sun zo ne daga birni dan taimaka mai da jari saboda ya daina halin da yake yi na rashin ji a cewar su ma daga hukumar yaƙi da zaman banza suke daga cikin garin Adamawa ai kuwa jin wannan sai mahaifiyar Mudan ta masu kwatancen inda yake zama wanda yake chan bayan gari cikin daji da taimakon babban ɗan mai gari suka yi tracing Mudan sun yi sa'a dan shi kaɗai suka samu a wurin yana shan barasa duk sauran yaran sa basu nan dan haka suka sallami ɗan mai gari haɗe da yi mai godiya har da kyauta ya tafi yana farinciki dan har yayi niyar kirawo samarin ƙauyen akan su zo ga masu yaƙi da zaman banza nan sun zo,sai da suka tabbatar ya tafi sannan Hakim ya cire suit ɗin sa ya bama Bahajjatu ta riƙe mai ya naɗe hannun rigar sa ya shiga jibgar Mudan ba ji ba gani each punch da yake kai mai gani yake kamar heaviness da ke ran sa bai raguwa dan sosai ya rinƙa kai mai punches bai bar sa ba sai da ya mai dukan da ya san dole ne ma ya kwanta jinyar sati ko bai kai wata ba da ya gama ya saka hannun sa a aljuhun sa ya fiddo da allurar kashe zafin gaɓa ya zuƙe kwalbar gabaɗayan sa ya danna ma Mudan a daidai cinyar sa inda ma bai kamata ba bayan ya mai ya kuma zuƙe wata kwalbar ya danna mai a ɗaya cinyar sa daga haka ya hankaɗa sa ya ja hannun Bahajjatu suka bar wurin a nan suka bar Mudan suka yi tafiyar su,toh according to mai gari wai da suke dawowa ne suka biya ta gidan sa suka sanar da shi cewa wai ai da suka tafi neman Mudan ɗin bayan sun gan sa sai tsagerun ƙauyen suka kawo masu hari da kyar suka gudu dan haka su zasu tafi tunda ba'a son taimakon su,sai mai gari ya ce da ni wai yayi yayi su tsaya ya kirawo masu na garin ƙauyen amma suka ce a'a su tafiya zasu yi a nan yake sanar da su labarin su Zaid wai suma da kyar suka sha da shi tsagerin da suka tafi taimaka wato Mudan su dai kawai sallamar su suka yi suka tafi ko ta kan ita Asma'un basu bi ba a cewar su zasu kai mata ziyara ta musamman bayan kwana biyu dan sanin dalilin ta na saka hannu a ta'addancin da aka yiwa ɗanuwan su"numfasawa yayi ya cigaba "Duk wannan ƙarin bayanin daga bakin Hakim na same su dan sai da na kira sa na tambaye sa shin ko su suka aikata hakan sai ya tabbatar min da cewa eh sune kuma muddin yayan sa bai farfaɗo ba toh sai ya koma ya kasara Mudan dan yayan sa ba zai yi jinyar wahala shi kaɗai ba nikuma calming nasa kawai nayi dan dama mutanin garin na neman mai saita yaton ba'a samu ba not until when Hakim and Baha went there and deal with him,toh kun fah ji Hakim dai da goyon bayan sister ɗin su Bahajjatu sun ɗau fansar abin da aka yiwa yayan su ina ga ai ko a haka ma aka bar shi an kasara mai rayuwa dan a halin yanzu yana nan a gida an ma rasa ta yaya za'a fara da treatment ɗin sa duk jama'an ƙauyen murna suke yi yana gida ana gargajiya amma saboda ƙarfin allurai da Hakim ya mai ya sa ya sami temporal lost of function wanda sai a hankali zai warware but before then ya ji jiki gashi a buge yake bare ya ce ya gane waɗanda suka mai dukan dan haka shiru iyayen sa suka yi dan sun san sakayyar mutanin da ya cutar ne ya biyo sa".yana kaiwa nan yayi shiru ajiyar zuciya suka sauke su sun rasa me zasu yi murna ne kokuma akasin haka dan Hajiya Zeenat ta ɗau burin hukunta yaron sai dai yanzu ta sami sauƙi da relief tunɗa an ɗau masu fansa shi kuma prof godiya ya ma Dr Hussaini haɗe da miƙa mai hannu suka yi musabaha sannan suka rabu. Al'amarin ya ba Dr Muhammad mamaki zuciyar Hakim ya kai har haka dama toh dole ne ma ya mai faɗa dan da a ce yaron ya rasa ran sa fa ai sai laifin su ya danne wanda yaron ne yayi masu. Ran Hajiya Zeenat fes dan jin an rama masu abin da yaron yayi wa ƴaƴan su har ɓarin jiki take yi washegari yayi su koma germany dan ta labarta ma Hajiya Madina gwanintar da ɗan su yayi,. A washegarin da wuri Bilal ya raka su airport a inda ta bar mai saƙo zuwa ga babban yayan su wato Jamil akan ya sanar da ƴanuwan su cewa nan da sati za'a yi ɗaurin auren Zaid da Bilkisu saboda Jamil ɗin baya nan ya sami tafiyar gaggawa,bayan jirgin su ya tashi ne Bilal ya kira apple ɗin sa ya sanar da ita aminiyar ta fah zata zama matar brother In-law nan da sati guda kamar ta yi hauka dan murna dan haka ta ce da shi zata bashi goron wannan albishirin da ya mata matuƙar sun haɗu. *********** Already Hajiya Madina ta gama jin bayani daga wun Baha akan tattaunawar su da Bilkisu itama ta zage akan ba ma Bilkisun shawarwarin zaman aure har da nasihohin haƙurin zaman gidan miji,dama bayan 48hours da ta ɗibarwa Bilkisun ta sami ƙwarin gwiwar sanar da ita cewa ta amince zata auri Zaid hakan ba ƙaramin farincikin ya saka Hajiya Madina ba shi yasa ta ja ta a jiki ta shiga yi mata nasihohi because that is all she have for her at that moment duk wasu maganar gyara kuma sai bayan sun dawo gida dan she is absolutely sure cewa babu wani abin da zai shiga tsakanin ta da Zaid that she can guarantee shi yasa ta dage da koya mata abubuwan mata matan ma masu aure waɗanda suka amsa sunan su ota dai jin Ammin take yi ba wai ta gama yarda Zaid zai so ta bane ko da ya farfaɗo and yet bata gama concluding ba a zuciyar ta son sa take kokuma tausayin sa take.. Lafiya ƙalau suka dawo ƙasar germany a inda suka nufi apartment ɗin su abin da ya zamewa Dr Maher da Hajiya Madina kamar almara dan basu yi tsammani ba a nan prof ke sanar da su ai abin da ya kai su ne dama ya zo masu da sauƙi. Bayan wasu lokuta sun huta sai Hajiya Zeenat ta matsawa prof akan ita fah lallai lallai sai sun gana da aminiyar ta dan abin na tsungulin ta ya ya iya da ita haka ya bar ta ta tafi asibitin wanda da ganin ta Bilkisu ta faɗa jikin ta kamar zata yi kuka ta shiga complaining wai tun da suka tafi bata kira ta ba sai ta mata bayani haɗe da ɗaga ta daga jikin ta tana mai ce mata zata dawo anjima bari ta gana da momma ɗin ta girgiza mata kai tayi sannan Hajiya Zeenat ta fita ta nufi ɗakin Zaid inda ta san zata ga Hajiya Madina ai kuwa sun yi murna a karo na biyu wanda Hajiya Zeenat ta kasa haƙura har sai da ta feɗe mata daga biri har wutsiya duk a cikin labarin babu wanda ya fi burge ta sama da fansar da Hakim ya ɗaukar masu daga shi sai maganar maganin Zaid ɗin wanda ya saka Hajiya Madina zubda ƙwallar farinciki after a long while ɗan ta zai farka kuma,hira suka yi sosai a nan Hajiya Zeenat ke sanar da ita ai ta kawowa Bilkisu kayan gyara na musamman sai abin ya bama Hajiya Madina dariya ta ce "In ban da abin ki Hajiya Zeenat ina shi Zaid ɗin ya gama samin lafiya har da zai nemi matar sa kar fa ki manta ko ya farfaɗo bai gama samin lafiya ba"sai itama Hajiya Zeenat ɗin ta dara haɗe da cewa "Hajiya Madina kenan ai yanzu zamani ya zo ma yaran nan da abubuwa daban daban ɗan nan kar kiyi mamakin in ya farka ayan kwanaki kaɗan ya fara nemar matar sa dan fah shi ɗin namiji ne wanda bai san daɗin mace ba the moment ya ga sun keɓe da yarinyar nan ya kuma san cewa matar sa ce a jin ki zai yi ignoring nata ne?ai sai dai bayan ya aikata mai gabaɗayan a maida shi kan gadon asibiti kin ga kenan is inevitable we can't tell"shewa suka yi suna mamakin yaran zamanin nan. A ranar kuwa aka fara bankawa Bilkisu kayan gyara a same day aka fara treating Zaid da maganin da aka kawo daga Nigeria but basu bari asibitin ta sani ba dan suna iya hanawa su kuwa so suke ɗan su ya farka. Askin da ta damu a yi masa kuwa aka ƙi yi aka ce sai ta aure shi sannan ita ta mai dan tsabagen damuwa har Umman ta ta ma magamar askin bata sani ba because wani abu wai kunya kamar ƙaurace mata yake yi in zata yi maganar Zaid. A nan Nigeria ana ta preparation na ɗaurin auren Zaid da Bilkisu a nan germany kuwa ana jiran farfaɗowar Zaid dan ana 4th day kenan da aka fara mai treatment tukunna prof bai sami kan sa ba dan haka bai sanar da Dr Maher abin da su Hakim suka aikata ba kuma bai ma nemi Hakim ɗin ba iyakan abin da suke jira shine farfaɗowar Zaid wanda a tsarin treatment ɗin suna saka ran kafin satin ya ƙare zai farfaɗo wanda kuma ya rage saura kwanaki biyu a ɗaura auren sa da Bilkisu ita kanta bata san me take ji dangane da auren ba daɗi ne kokuma tausayin kanta dan daga Ammi,Umma da Baha duk sai zuzuta mata maganar auren suke yi wai dan ta ji sauƙi da daɗi a zuciyar ta. ranar da ya kasance ranar da su Dr Maher da Dr Muhammad zasu koma Nigeria dan washegarin ranar za'a ɗaura auren ƴaƴan su,a ranar bayan tafiyar su Bilkisu ta kasa sukuni ta rasa me ke mata daɗi gashi tana son ganin Zaid ɗin amma ta rasa yadda zata yi bata gan sa ba sai cikin dare ta sulale ta nufi ɗakin ta zauna tana kallon sa ta rasa me zata yi farinciki ko akasin haka dariyar murna ko akasin haka yanzu fah auren ta za'a ɗaura da shi what if he wakes up and said baya son ta ya zata yi?sai ta kuma mayar da dara daran idanun ta kan kyakyawar fuskar sa ta kasa furta komai ta kasa tantance feelings da take da shi ma Zaid,ƙura mai ido tayi tana kallon sa what is she feeling?the feelings is different is she actually in love with Zaid?sai ta ƙara girman idanun ta ta hanyar buɗe su sosai ta furta a zahiri "Am i in love with Zaid Maher"?.... _promise_*+ Abin mamaki me ke damin ta ne wai haka,ta yiwa kanta tambayar sannan ta ba ma kanta amsa "what else if not love"!!hakan ya sa ta shiga murmusawa ita kaɗai ba tare da ta san tana hakan ba mayar da idanun ta tayi zuwa kan suman kan sa da yayi yawa fiye da da sai ta ji kamar ta masife Hakim da ke kula da shi akan menene ba zai gyara mai fuska da kai ba gashi nan suman kan sa da na fuskar sa sun wuce misali ai hakan sai ya ƙara mai rashin lafiya, Zancen zuci take ta yi ita kaɗai daga bisani ta miƙe ta tofa mai addu'a sannan ta fara tafiya dan komawa ɗakin ta tana tafe tana juyowa tana kallon sa har dai ta kai bakin ƙofar kamar kar ta fita ta zuba mai idanun nan nata tana kallon sa cikin sigar da bata san yanda zata alaƙanta sa ba. Firgigit kamar an tsungule ta sai ta ga kamar baccin da take yi har yanzu bata farka ba haba in ba a mafarkin ta ba dama ta yaya Zaid zai yin yunƙurin yin wani abin ai sai dai a mafarkin dan haka ta saka kan ta zata fita ta kuma jin alamar faɗuwar abu wani juyin bori tayi a zafaffe ta buɗe idanun ta gaban ta na tsananta bugawa tana fargaban abin da zai biyo baya in har bai yi alama ba toh gaskiya ba zata taɓa yafewa zuciyar ta ba for making her imagination go beyond her limits. Sharewa tayi ta yi kamar zata fita sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon jin numfashin mutum kamar yana gasping sai ta juya a rikice tana baza idanun ta dan ganin daga inda numfashin ke fitowa bata san lokacin da ta dira a gaban sa ba sakamakon ganin ɓarin flower verse a gefen gadon sa,saurin yaye comforter ta yi hannun ta na ɓari tana gama yaye comforter ɗin sai ta ga shi ke numfashin kuma taimakon gaggawa yake buƙata dan haka ta fita cikin gaggawa bata tsaya ko ina ba sai a ofishin likita da ƙarfin ta ta shiga office ɗin tana ta kwala mai kira a rikice ya fito daga cikin bathroom da shigar sa kenan yana tambayar ta ko lafiya ta rasa me zata sanar da shi sai kawai ta shiga kirawo mai room number tana faɗin "405...405..405."ganin ta ruɗe sai ya ce da ita "Is okey let's go"da gudun ta ta fita shima ya biyo ta suka ranƙaya zuwa ɗakin da shigan su ya riga ta zuwa kan gadon.ganin Zaid yayi yana jacking yana gasping da sauri da sauri sai ya cire mai mask ɗin ya yi regulating device da zai rinƙa bashi iska,fita yayi cikin hanzari ya nufi office ɗin sa babu jimawa ya dawo shi da wasu doctors biyu a nan ne aka buƙaci baby doctor da ta fita girgiza masu kai ta shiga yi tana kuka tana faɗin ba zata iya fita ba,hayaniyar da ke fitowa daga ɗakin ne ya janyo hankalin Hajiya Madina da Hajiya Zeenat da ke kwance a ɗakin masu kula da majinyata fita suka yi gabaɗayan su zuwa hanyar da hayaniyar ke fitowa,ko da suka tafi sai suka ga abin tashin hankali wato Bilkisu ce ke faman risgar kuka while ga doctors nan uku a ɗakin da Zaid yake kamar dai so suke su yi stabilizing nasa sai Hajiya Madina ta ɗan janyo Bilkisu tana tambayar ta me ya faru. In banda kuka babu abin da take yi hakan ya sa Hajiya Madina jan ta suka bar wurin a inda Hajiya Zeenat ta tsaya tana hango abin da ke gudana a ɗakin duk hankalin ta a tashe yake ko me ya sami Zaid ɗin sai Allah dan haka zirga zirga ta shiga yi a bakin ƙofar Hajiya Madina dai bata dawo ba dan bata jin zata iya cigaba da witnessing abin da ke faru sai ta tsaya tana rarrashin Bilkisu kawai. An hour + kafin doctors ɗin su sami damar saisaita Zaid dan sun fahimci cewa ya farfaɗo ne kuma da ƙarfin sa ya farfaɗo dan kuwa so yake ya farka gabaɗay sai dai ciwon da ke kansa wanda ya janyo masa surgery bai warke ba dan haka dole komai sai a hankali zai saba da shi they were able to seduce him dan ya koma bacci kuma he is calm shi yasa suka fito a nan Hajiya Zeenat ta tare su tana tambayar su ko me ya faru shi babban likitan ne ya yi inviting ɗin ta zuwa office ta bi sa cikin hanzari.bayan sun zazzauna ne ya kalle ta at first moon face ya saka sai daga baya ya murmusa da smiling face ɗin ya ce da ita "I must say,congratulations your son just regain consciousness and he is in good state of mind he will wake up in not less than an hour or more with full strength and ability what a surprise i guess"!!faɗaɗa murmushin sa yayi yayin da Hajiya Zeenat ta tafi ƙasa tayi sujjada bata ce da likitan komai ba sai da ta ɗago sannan ta kalle sa fuskar ta jiƙe da hawaye idanun ta sun yi ja ja zir tana dariya tana fidda hawaye ta ce da shi "Thank you,thank you doctor,thank you"!!shima murmushin ya mayar mata da shi yana girgiza mata kai ya san tana cikin farinciki dan haka bai ga laifin ta ba dan ta zage tuƙuru tana kuka.daga office ɗin ɗakin zaman su ta nufa inda ta ga Hajiya Madina na rungume da Bilkisu tana rarrashin ta ita kanta mai rarrashin ta take nema dan haka ta ƙarasa shiga ɗakin ta ce cikin muryar kuka "Hajiya tashi ki ma Allah godiya our Zaid is back"ba ita kaɗai ba hatta da Bilkisun sai da ta razana dan maganar a matsayin abin almara ya zo masu da mamaki da al'ajabi sai suka tashi tsaye baki ɗayan su hawayen Bilkisu ya ƙafe yayin da Hajiya Zeenat ta buɗe baki cikin mamaki tana son yin magana amma ta kasa Hajiya Zeenat ta gane state of shock da ta shiga dan haka ta matso kusa da ita ta riƙe kafaɗun ta ta shiga girgiza ta tana cewa "Yes yess Hajiya Zaid is back for good yanzu na fito daga ofishin Dr kuma ya sanar da ni cewa Zaid ya farfaɗo kuma any moment from now yana iya farfaɗowa cikin ƙoshin lafiya abin godiya ne ga Ubangiji"!!sai ga hawaye sharr na fitowa daga idanun Hajiya Madina cikin farinciki da jin daɗi ta rungume Hajiya Zeenat ta saki kukan farinciki petting bayan ta Hajiya Zeenat ta shiga yi tana ƙara tabbatar mata da cewa eh Zaid ya dawo masu irin farinciki da suka tsinci kan su a ciki understatement ne sun manta da Bilkisu a ɗakin wacce ta yi suman tsaye sakamakon jin an ce Zaid ya farka a nan ta bar su ita kuma ta nufi hanyar ɗakin da Zaid yake. An saka dokar kar wanda ya shiga ɗakin har sai ya farka amma ita kam kai tsaye ta shige ta rinƙa bin sa da kallo tana jin wani abu a ran ta game da farfaɗowar Zaid a haka ta zauna gwiwa a sage ta kafa mai dara daran idanun ta waɗanda suka chanza launi zuwa jajjaye saboda kukan da ta yi saƙe saƙe kala kala take yi a zuciyar ta mafi akasarin saƙe saƙen sun ta'alaƙa ne ga mafitar rayuwar ta in Zaid ya farfaɗo ya kuma gane cewa shi da ita sun zama ma'aurata wanɗanda zasu rinƙa zama inuwa ɗaya tun farfaɗowat sa har izuwa ƙarshen rayuwar su ya zai karɓi maganar?shin da wani siga zai fahimci maganar?zai amince da ita kokuma a'a?zai ma yarda ya ɗauke ta a matsayin abokiyar rayuwa ta har abada?waɗannan tanbayoyi sun tsaya mata a rai she knows that tomorrow will be her wedding day ranar da ba zata taɓa mantawa da shi ba a rayuwar ta saboda tambari ne that will signifies a new life,a new beginning and a new world to her.but is she well prepared and ready to accept it?sai ta kuma kallo sa ta ga yadda yake fidda numfashi a hankali har yanzu bata san me take ji game da shi ba it's somehow mix the chemistry is over reactive reaction ɗin na boiling ko wani ɓangare da saƙo na jikin ta,kanta ne ya fara ɗebar chaji sai ta tsagaita da tunane tunanen ta cigaba da kallon sa. _1:00am_ Suna a haka shi yana baccin sa ita kuma ta kasa runtsawa tana ta bin sa da kallo already nervousness ya gama yi mata dabaibayi ya hana ta sukuni,tana kan kallon nasa sai ta ga ya fara juyawa da kansa idanun sa a rufe ruf sai ta tashi ta matso kusa da shi tana gyara mai abin numfashin da aka saka mai ɗazu sai ya dakata daga juyawar da yake yi ya tsaya da kan sa a wu ɗaya itama sai ta natsu kamar mai son haddace wani abu kusan 5 minutes bai motsa ba sai ta ji ran ta ya fara mata ɗaci ɗaci ta ji ɗakin ya mata wani iri dan ta gama sadaukarwa ba gaske bane kawai yaudarar ta idanun ta ke yi sai ta haƙura ta koma kan kujerar ta kafe sa da idanun ta wanda zuwa yanzu sun ƙara girma sakamakon takura da suka samu daga gare ta dan kuka ne ba kaɗan ba tayi ɗazu ga rashin baccin da bata yi ba ga tunani duk sai suka taru suka haddasa mata damuwa dan har barkono barkono idanun ta ke mata amma bata cire tsammanin sake haɗa kwayar idanun ta da Zaid ba. Gradually,synchronously ya buɗe idanun sa kaɗan sai ya maida ya rufe duk bata lura ba sai da ya kuma buɗe su a karo na biyu ya sauke su kanta duk bata sani ba sai da ta ji a jikin ta kamar mutum ya kafe ta da idanu sai ta yi wuf ta ɗago with the hope of seeing him fully awake,. Gani tayi kamar idanun ta gizo yake mata ɗan murza su tayi ta tsaya sai ta ga still ita yake kallo abin bai mata ba sai ta rufe idanun ta for a moment ta buɗe su taga ita ce dai yake kallo dan haka sai ta shiga pinching hannun ta but the reality is well set shi ɗin ne dai ba mafarki ba ba kuma imagination ba sai a hankali kamar mai sanɗa ta fara takawa kaɗan kaɗan tana kallon fuskar sa sai ya bita da idon ta kuma dawowa ta gaban sa still ya bita da kallo sai ta dawo gaban sa ta tsaya shima idanun sa suka tsaya a kan ta ya tsura mata idanu kamar bai taɓa ganin ta ba. She was out of words sai kawai ta juya cikin hanzari ta fita ta nufi ɗakin iyayen nasu ta gan su zaune dan tun da ta bar ɗakin suka neme ta suka rasa sai Hajiya Madina ta fita duba ta ganin ta a ɗakin Zaid ya sa ta girgiza kai ta dawo ta sanar da aminiyar ta abin da ta gani sai suka zauna zaman jiran farfaɗowar sa basu koma baccin ba. Da shigar ta cikin extreme euphoria ta ce "Umma Zaid..Zaid ya tashi..wallahi ya tashi baya baccin..idanun sa a buɗe suke zo muje ki gani"tausayi ta bama iyayen nasu dan sun gano mummunar son Zaid ya gama kamata har yana shirin illata ta ba tare da ta sani ba. Sai da ta ja hannun Umman sannan suka biyo ta zuwa ɗakin Zaid ɗin suna fatar ganin abin da Bilkisu ta faɗa. Ko da suka shiga ɗakin ganin sa suka yi a zaune jingine kaɗan da gadon idanun sa lumshe yana fitar da numfashi kaɗan kaɗan sai suka ga kamar a mafarki.ƙarasa isowa kusa da gadon Hajiya Madina tayi tana mai son gasgata abin da idanun ta suka gane mata.da isar ta hannun ta na ɓari ta ɗaga ta kai kan kafaɗar sa sai ya buɗe idanun sa kamar an wanke mata ido dan ganin sa shi kaɗai sai ta yi saurin kiran sunan sa "Zaid baby..Zai..ddd..are you really back..."duk a hargitse take maganar dan haka ya juya mata idanu alamun eh sau ta rarumo sa ta rungume tana mai sakin kuka haɗe da faɗin "Zaid..ka yi baccin doguwar zango ba tare da ka sani ba..you were unconscious for almost a month har ana ce mana zaka kai 3-4months kafin ka farfaɗo..baby i was in great hell of pains i was hiding it not to worsen the situation"sai ta yi bursting into tears shi kuma ya kasa faɗin komai amma yana jin wani abu a ran sa but he can say it out dan haka yayi shiru yana sauraron ta har dai Hajiya Zeenat ta zo kusa da su tana mai taɓa kafaɗar Hajiya Madina akan ta daina kukan da take yi bai dace ba sai ta daina kukan ta ɗago tana kallon sa kamar an ce da ita za'a ɗauke mata shi yayin da Bilkisu ya ƙure sa da idanu tana kallon duk wani motsin sa har dai tayi wani tunani ta bar ɗakin,ɗakin ta ta koma not minding what the time is kawai ta shiga kiran layin Bilal sau biyu tana kira yana ƙarewa ba tare d an ɗaga ba,bata haƙura ba ta ƙara kiran sa cikin magagin bacci ya ɗauka yana tambayar ko wanene dan bai duba lambar ba "Apple wake up you rascal"ta faɗa with great excitement a muryar ta. A rikice Bilal ya tashi haɗe da buɗe idanun sa da kyau ya ce "Apple ke ce?what happened?is brother In-law awake"??duk a jere ya mata tambayoyin. Bata san lokacin da ta sake dariyar murna da jin daɗi ba sai ta ce "Bilal Zaid is back..Zaid ya farfaɗo am happy..am just excited and i feel that i can't take the whole happiness all alone that is why i call you ate you happy"??tayi tambayar da eagerness a muryar ta sai yayi saurin bata amsa ya ce "Damn your second thought apple of course am happy..how could you even think that am not happy..of course i am apple na ma fi ki farincikin farfaɗowar brother in-law"!!murnar su suka yi tuƙuru suna tsaka da celebration ɗin Bilal ya ce mata "Apple gobe fah shikenan zamu daina duk waɗannan wasannin da muke yi because you will become Mrs Maheer and the bond between us will be weaken"sai mood ɗin su ya chanza su duka dan yanzu ta tuno cewa da zarar an ɗaura auren shikenan duk wata ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsaƙanin ta da twin brother ɗin ta sai ta ji hawaye na bin fuskar ta sun ɗau lokaci a hakan kafin daga bisani ya daure ya ce "Apple don't worry muna tare a zuciyoyin mu ko da bamu tare a zahiri kin ji"?amsa mai tayi tana share hawayen ta "Na ji Bilal kuma na maka alƙawari ko da bamu tare son ka a zuciya ta daban take ba zan iya haɗa ta da kowanne ba you are special to me"kasa yin shiru yayi har sai da ya furta mata "Apple am gonna miss you please don't forget about me"tarar numfashin sa tayi ta hanyar ce mai "Common Bilal stop talking like that it makes me feel like crying already"sai ya ɗan murmusa ya shiga teasing ɗin ta ita ma tun bata biye mai har ta fara mayar mai da martanin tsokanar da yake mata.a haka suka ƙarar da ragowar daren basu ajiye wayar ba har sai da ƙarfe 4:30am ya buga a agogon ɗakin Bilkisu sai ta mai bye bye ta ajiye wayar.she was lost in her thought dan haka bata ma san lokacin da bacci mai nauyi gauraye da daɗi ya ɗauke ta ba. _7:09am_ A lokacin ta farka shaf ta sha'afa bata yi sallar asuba ba dan haka a hanzarce ta sauko daga kan gadon tana addua'r tashi daga bacci haɗe da yawning,sauri sauri tayi alwalar ta fito ta tada sallah ta makara ba kaɗan ba shi yasa tayi saurin tada iƙama ta sallame raka'oi biyun ta zauna addua bata bar abin sallar ba sai da ta ɗau mintuna kusan talatin sannan ta sallame ta miƙe tana folding praying mat daga bisani ta shige toilet tayi wanka ta fito abincin ta ta tarar a kan table da aka saba ajiye mata abinci da magungunan ta dan haka shiryawa tayi cikin usual wear ɗin ta wato doguwar riga maroon colour sai bata yafa mayafin ba ta ɗaura kawai,. Zama tayi ta buɗe abinci kallon abincin tayi for a moment kafin tayi bismillah ta fara cin abincin,ba wani yawa wanda ta ci ta tufe ta ɗau magungunan ta sha.har ta kwanta sai ta tuna da bata gan sa ba dan haka ta tashi ta nufi hanyar ɗakin sa babu komai a ran ta ta tura ƙofae ta shiga haɗe da yin sallama ba'a amsa mata ba dan haka kan ta tsaye ta shiga tana raba idanu dan ganin inda yake sai dai bata yi nasarar ganin sa ba dan kuwa an fitar da shi an yi transferring nasa zuwa wani well equipped room da bashi special care tunda ya farfaɗo sai ta ruɗe ta rasa me ke mata daɗi ina kuma ya tafi ta ma kanta tambayar sai ta shiga duba sa ta zaga ɗakin babu shi ta shiga bubbuga toilet door ɗin tana kiran sunan sa bai amsa ba sai ta fito a birkice tana neman sa ji tayi an jata gefe sai ta ɗago a tsorace. Ganin Bahajjatu tayi ashe ita ta ja ta gefen sai ta kalle ta tana son tambayar ta inda aka kai Zaid sai dai Bahajjatun ta riga ta dan sanar da ita tayi fuskar ta tam cike da murmushi tace "I know tambaya ta zaki yi inda Yaya na yake,fine yana chan ɗakin da aka chanza mai very close to yours dan ana saka ran ma an kusa sallamar sa nan da sati biyu sai dai ya rinƙa zuwa check up after 3 months"sai yanzu ta sami relief ta sauke ajiyar zuciya zata yi magana Bahajjatun ta riga ta ta hanyar rangaɗa mata guɗa sai ta shiga rera waƙar "Tazama tazama tazama ɗauko riga tazama tazama ɗauko hula tazama tazama ɗau takalmi tazama"a haka fah ta rinƙa nanata wakar tun Bilkisu bata fahimrar inda waƙar ta dosa har ta fara harbo jirgin sai ta buɗe idanun ta ciki mamaki tana mai cewa "Baha ban gane ba"sai Baha ta ce da ita cikin raha "Ina nufin daga kimanin mintuna arba'in da suka wuce kin zamo mata kuma suruka wato dai kin zama matar babban yayan mu Dr Zaid Maher Mahmud kuma kin zamo suruka a wun Dr Maher Mahmud da Hajiya Madina Maher at the same time kin zamo sister in-law ɗin mu"da annashuwa shimfiɗe a kan fuskar ta ta ƙarasa maganar.. Abin a fizge ya zo mata dan haka sai da ta ɗauke wuta na wucin gadi kafin ta dawo hayyacin ta ta ce "Baha kina nufin an ɗaura auren ne already"?dariya tayi ta ce "Of course mana an ɗaura auren ku in fact ana ɗaurawa Bilal ya korawo ni ya sanar da ni cewa baku jima da gama waya ba shi yasa bai kora ki ba dan kar ya hana ki bacci so presently you are officially Mra Zaid Maher and wani abin da baki sani ba shine we all will be leaving zamu tafi mu bar ku tare saboda ya farfaɗo kuma yana iya motsa jikin sa kaɗan kaɗan no need ma zaman mu,jirgin 8pm na daren gobe zamu tafi dan Abba ma ya ja mana kunne akan mu yi mu dawo since you are now married you can take care of him kin ga tafiya ta kama mu ba tare da mun shirya ba beelove"abin mamaki ya ba wa Bilkisu sai ta kasa furta komai sai zancen zuci yanzu wai ta zama matar wani kenan fah!ikon Allah. Suna tsaye a wurin Hakim ya zo wucewa dan kwaso sauran kayayyakin Zaid da ba'a gama kwasowa ba sai ya hango su dan haka ya kira Bahajjatu ta ce da shi tana zuwa har sai da ta gama maganar ta da Bilkisun sannan ta nufi inda yayan nata yake "Ya aka yi ne yaya Hakim"!?ta tambaye sa sai ya ce mata "Is about askin da za'a yiwa yaya Zaid ke kin san in har Abba ya gano cewa ba'a mai gyaran fuskar nan ba ke kin san akwai damuwa"sai ta ce "Ai yaya ka san umarnin Ammi ne hakan kuma Abba ba zai taɓa yin rigima akan abin ba kawai dai ga matar sa since she is now his life partner i guess zata yi resuming duties nata kuma zata fara ne da gyaran fuskar ko ya ka ce"??murmushi yayi kafin ya ce "Yayi baby sister kin kawo shawara mai kyau".. Daga nan ya wuce zuwa ɗakin Zaid na da dan kwaso abubuwan da aka manto su chan ita kuma ta nufi hanyar fita dan kayan ta da zata fara arranging saboda tafiyar su ma washegari. Itakuma ɗakin ta ta nufa dan bata jin zata iya shiga nasa ɗakin at that moment.tunane tuname take ta yi in su Umman ta suka tafi suka bar ta daga ita sai shi ya zata kula da shi,ire iren tunanin da ta ɓata lokutan ta tana yi kenan har ta cinye rabin ranar dan in iyayen nata sun shigo duba ta sai tayi pretending tana bacci sau biyu suna duba ta dan haka suka rabu da ita su dai burin su ya cika an yi mai kankat. A halin ɓoye ɓoyen ta kai har dare sai dai tana muradin ganin sa but she can't she feel she can't see him at that moment dole ta bari har sai sun tafi.a haka ta kwana ta tashi ba tare da ta saka sa a idanun ta ba,da yake jirgin wuri zasu bi ita kuma tana bacci lokacin sai Ammi ta bar mata note suka yi tafiyar su Ko da ta farka bata lura ba sai ta yi harkokin ta na yau da kullum but ta saka a ran ta cewa dole ne ta gan sa ko da kuwa suna nan dan ta gaji tun shekaranjiya rabon da ta saka sa a idanun ta.she dress in an alluring way shiga mai kyau tayi ta ɗan yi makeup kaɗan ta saka flat Zara pams ta nufi ɗakin sa dama bai da nisa da nata dan haka da zuwan ta shiga tayi kai tsaye ba tare da tunanin maybe iyayen nasu na ciki ba. Zaune yake a kan gadon ana bashi abinci sai ta ƙarasa zuwa inda suke tana kallon mai bada abinci sai ta ga baturiyar mace ce sai ta mai da idanun ta kan sa ta ga yana kallon mai bashi abincin ai tuni ta ji ran ta ya ɓaci ta fara tunani marar kyau a kan mai bada abincin gashi ta ga dai matar yake kallo sai ta zuciya ta karɓe abincin daga hannun matar haɗe da saka fake grin ta ce da ita "Thanks you may leave please"baturiyar sai ta maida mata da murmushin sannan ta fita. Zama tayi a kujerar da ke kallon gadon sa ta shiga ƙoƙarin bashi abinci sai dai ya girgiza mata kai dan dama ɗazu da yake kallon matar nan nuna mata yake son yi akan ya ƙoshi sai dai ita bata gane ba.ita kuma Bilkisu ganin ya nuna alamar ya ƙoshi bayan ta ga yana ta karɓa a wun waccan baturiyar sai ta ji ran ta na suya dan haka cikin ɓacin rai ta ajiye abinci ta tashi da nufin fita ta bar mai ɗakin in yaso Ai ko Baha ko ma ita baturiyar su zo su basa since he doesn't need her help. Ko da ta juya dan fita a zuciye sai ta ji deem voice na sa na kiran sunan ta "Bilkisu come back"!!sai yayi shiru itakuma ta ƙame a tsayen bata juyo ba bata fita ba ta rasa me ke mata daɗi is it her name that he called?or the care he puts in while calling the name?ko dai kawai unique feelings ne?sai ta tsinci kan ta tana mai annashuwa haka kawai... A hankali ta juya ta yi ƙasa da idanun ta ta shiga takawa a hankali har ta iso kusa da shi sai ta tsaya ba tare da ta ce da shi komai ba sai da ya kuma yin magana "Bilkisu zauna"!!sai ta zaunan tana mai kallon ƙasa shi kuma ba hakan yake so ba so yake ta kalle sa dan ya mata tamnayar da yake da niyar yi sai dai sam ta ƙi yarda su haɗa idon sai da ya kuma furta wata maganar "Ki kalle ni mana"!!sai ta ji saukar maganar a tsakiyar kan ta itama bata san me yasa ta ke shakkar haɗa ido da shi ba ita da ta daɗe tana muradin ganin farfaɗowar sa dan dai ta haɗa ido da shi sai gashi yanzu da ya farfaɗon ta kasa kallon sa cikin ido. Bai san menene dalilin ta na ƙin son kallon sa ba sai ya mata shiru ba tare da ya kuma ce mata komai ba har sai da dan kanta ta ɗago a hankali ta sauke idanun ta a kan fuskar sa tana son haɗa courage ɗin magana da shi,dama ya juyar da kan sa gefe sai ya ganta ta gefen ido sai da ya ja lokaci sannan ya juyo ya zuba mata deem eyes ɗin sa da har yanzu basu gama dawowa normal ba sakamakon jinyar da yayi. Sarƙewa idanun su yayi a na juna,doguwar lokaci suka ɗauka suna kallon juna wanda kallon nasu cike yake da ma'anoni kala daban daban wanda su kaɗai suka san ma'anar sa sun daɗe a haka shi bai cire idanun sa ba ita ma bata cire ba dan kasa cirewar tayi ta rasa dalili. Ba su suka daina kallon juna ba har sai da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo haɗe da faɗin "Good morning"da fara'a a kan fuskar wanda ya shigo,ita ta riga sa ɗaga kai ta kai duban ta ga wanda ya shigon sai ta ga Dr ne dan haka ta tashi tana tambayar sa "Morning anything"??amsa mata yayi da "Yeah i want to check his system to assess his body function"sai ta girgiza kai cikin gamsuwa ta matsa mai ya matso kusa da shi yana gaida sa haɗe da tambayar sa ko da akwai wani abin da ke damin sa amsa ya basa da a'a illah son sanin blockage da ke kunnen sa a nan doctorn ya rasa abin faɗa mai dan bai shirya wa tambayar tasa ba kuma dama shi dai duba sa ya zo yi ba wai shine main doctorn Zaid ɗin ba. Sai ta ba Zaid amsa ta hanyar amfani da yaren hausa ta ce da shi "Zan faɗa maka dan ba shine ainihin likitan ka ba zuwa yayi duba ka in ya tafi zan maka bayani"!sai ya tsura mata ido hakan kuma creating mat wani abu yake yi wanda bata iya withstanding sai ta kawar da idanun ta ta mayar ga likitan "Is okey i will explain to him"jijjiga kai yayi ya cigaba da dube duben sa kafi daga bisani ya mai fatan ƙara samin lafiya ya fita ya bar ɗakin sai ta koma mazaunin ta ta zauna ta yi ƙoƙarin danne hawayen da ke cike a ƙwayar idanun ta sakamakon tunowa da tayi da matsalar da Zaid ya ke da shi wanda yayi necessitating masa zama da ear device ɗin for a long period of time ga final healing and recovering stage da ke jiran sa a nan gaba wanda alƙawari ne ta ɗaukar wa kanta babu yadda zata sanar da kowa ita kaɗai zata yi handling komai thank goodness yanzu ita ɗin matar sa ce so ko ma me ta yi ta san is for their own good.kallon sa tayi ta ga shima ita yake kallo sai ta ji ta kasa daurewa dan haka t bar hawayen suka zubo wanda ya saka sbi cikin duhu dan bai san ma'anar kukan nata ba sai ya ce da ita "Menene kike kuka"??muryar sa ƙara saukar mata da tausayin sa yayi sai ta rasa ta ina zata fara kamo zaren bayanin da take son yi mai a kan rashin lafiyar sa.. Share hawayen ta tayi tana saka murmushin dole ra ce "Babu"sai ya juyar da idanun sa alamun bai yarda ba sai ta ɗan yi dariya dan dai kar ya mata tambayar sai ta mai bayanin dalilin ta yin kuka,saidai da yake shi ɗin ɗan boko ne bai bata opportunity na gujewa wayon da take son yi mai ba,kuma yi mata magana yayi ya ce "Ban yarda ba ki gaya min dalilin ki na kuka"!a hankali ya mata maganar sai taji tsigar jikin ta ya tashi at the same time ta ji kamar sanyi sanyi na shigar ta hakan ya bada gudunmawar ƙin ba shi amsar tambayar sa dan haka ta shiga rera kuka ba ji ba gani shi kuma sai ya ruɗe gashi kan sa na banging kamar me sai ya shiga bata haƙuri "Am sorry ban san tambayar tawa zata ɓata miki rai ba ki daina kukan"sai ta ji wani iri mijin ta na bata haƙuri akan laifin da bai sani ba sai tayi saurin ce mai "A'a Zaid ni ya kamata in baka haƙuri dan ni na maka laifi,tambaya ta kayi na ƙi baka amsar tambayar na shiga yin kuka am very sorry am so sorry please forgive me"ta haɗe tafukan hannayen ta wu ɗaya ta shiga ba sa haƙuri tana zubda ƙwalla. She is acting strange but why?ya ma kansa tambayar dan sarai ya san halin ta ba mai saurin karaya bane amma me ya sa take kuka haka dan ya tambaye ta kuma sai ta ƙara yawan kukan nata abin ya ɗaure masa kai sai dai bai ce komai ba dan baya son tursasa ta akan lallai lallai sai ta mai bayanin dalilin kukan ta zai bar ta har sai ta ji kan ta daidai kafin ya tambaye ta,ga tambayoyi da yawa da yake son yi mata sai dai bai san ya zata ɗau tambayoyin ba wannan ɗaya kenan amma ta shiga yin kuka. Shiru yayi yana kallon ta tana kukan har dai ta tsagaita ta kalle sa tana jimamin lamarin ko in ta mai bayanin dalilin kukan ta zai kalli bayanin da fuskar fahimta kokuma zai ƙi amincewa Allah ne masani Ta san yana da tambayoyi da yawa da yake son yi mata dangane da zuwan su nan,wani wuri ne nan ɗin,a wace ƙasa suke,me ya same sa,ina family ɗin sa and she knows maybe a ƙarshe yayi tambayar ina....a zafaffe ta ce "No way"bata san ta furta shi a zahiri ba har ma ya isa kunnen Zaid sai ya kalle ta da kyau yana mamakin halin da take demonstrating dan bai san ta da wannan halin ba me kuma ya dame ta har take magana ba tare da ta san ta furta ba?? Dawowa hayyacin ta tayi sai ta ji kunya ta kama ta bayan ta san a zahiri ta yi maganar da ta yi a haka ta warawre gyalen ta ta ja ta rufe har dai idanun ta suka ɓuya ƙarƙashin mayafin. Shi dai kallon mamaki yake mata ya kasa furta komai dan abin nata ya fara zarce tunanin sa why is she covering her face?ya tambayi kan sa. Zaune suke babu wanda ya kuma furta komai har tsayin lokaci sai ta yanke kawai is better ta sanar da shi a wuce wurin dan haka ta yi ƙarfin halin riƙe hawayen ta ta gyara murya "Zaid"bai ce komai basai idanun sa da ya zuba mata sai dai ta daure bata cire nata idanun daga cikin nasa ba "Abin da ya faru da mu ba yin mu bane haka zalika ba wai mun fi ƙarfin faɗawa a ƙaddarar ubangiji bane..sai ta ja fasali kafin ta ɗora da,satin ka kusan huɗu kana unconscious sakamakon abin da ya faru da mu a ƙauyen koma ban sani ba ko ka tuna da abin da ya farun but bana fatar ka tuna dan ba abu mai daɗin ji bane ina so ka sani ba da gangar na bari aka kai maka harin da ya illata ka ba kuma ina so ka sani am always ever ready dan kare ka daga wani harm ba'a fata but i promise never to let any harm come your way again,,,a last two weeks aka maka cerebral surgery wannan shine dalilin saka maka ear device da aka yi saboda accident da ka samu ba a iya cerebral region ɗin ka ya tsaya ba yayi affecting maka pineal gland wanda ya tilastawa kunnuwan ka amfani da device ɗin nan dan taimaka maka wun rage shigar sharp and lousy noises amma doctor ya sanar da mu cewa akwai tsawon period da amfanin shi zai yi elapsing sai a cire maka and you will be back to normal but before then please kar ka sakawa kanka damuwa da yawa in ka ga ba zaka iya ɗaukar damuwar kai kaɗai ba ka yi sharing da ni am at stand by now and always kuma dama doctor ya ce ba nan kusa zaka farfaɗo ba sai ka kai 3-4months but ikon Allah sai ka farfaɗo in less than 2weeks ka ga kenan tunda har ka iya farkawa kafin expected time wannan ear device ɗin ma ana iya cire sa kafin lokacin da suka ƙiyasta ka ga ba sai ka shiga damuwa ba dan am here and our parents are also here to help us da fatan ka fahimce ni and please don't react i know you will get well soon and all these minor pains will be done and over with just trust me"!!ba ƙaramin dauriya tayi ba a yayin da take sanar da shi dan kuka ne ke ta son taso mata ta sani it won't sound superb a kunnen sa dan ba abu mai daɗin ji bane a ce da kai ga abubuwan da suka same ka kuma yet baka gama warkewa ba especially ga wanda shine ya saba sanar da wasu sai a ce yau ana sanar da shi abin babu sauƙi definitely ta san he will be hurt amma gwara da ta sanar da shi tun yanzu dan bata san me zai faru ba in aka ɓoye mai asalin abin zai iya jin zafi in aka jinkirta sanar da shi but yanzu ta san ta sauke wani ɓarayi na nauyin da ke damin ta a zuciyar sa but inda gizo ke saƙar shine ta yaya zata sanar da shi matsayin ta a gare sa as his wife will he wacce or reject her bata sani ba kuma bata san lokacin sanar da shi ba har da ma dai tana tunanin by now either Bahajjatu,Hakim or Ammi must have inform him but a yadda yake yi sai take gani kamar bai da masaniya. Ko da ya gama jin jawabin ta sai ya tsinci kan sa da son sanin cikakken labarin dan ya san ba duka labarin ta ba sa ba saboda je can sense phobia da ke damin ta dan har a muryar ta hakan ya nuna,he barley remember what happened that night but ya san ko ma dai menene it must be awful and ugly dan tsoro ne taf a tattare da ita sai ya yi interrupting tunanin da take yi ta hanyar kiran ta "Bilkisu ba duka labarin ba kenan,ina son sanin cikakken labarin"!!dumm ta ji gaban ta ya faɗi dama zagaye ta mai dan ta tsani ta kai kan gaɓar labarin inda Asma'u came to play dan sam bata so ya tuna da yarinyar saboda ba ƙaramar hatred take da shi ma yarinyar ba and she thinks bayan hatred akwai wani abin da take ji game da yarinyar wanda bata san ko menene ba. sauke idanun ta tayi ƙasa dan tsakani da Allah sai dai yayi fushi da ita amma ba zata taɓa gaya mai gaskiya ba.. "Ka ga Zaid ka daina sakawa kan ka damuwa saboda wannan labarin da na baka iyakar ta kenan babu wata believe me"tana gama faɗa ta tashi ta yi hanyar waje tana jin sa yana kiran ta amma ta ƙi dawowa dan bata shirya sanar da shi ainihin labarin ba sai dai peripheral ɗin. Da kuka ta ƙarasa ɗakin ta kuka mai tattare da cin rai take yi dan pains da agony da ke zuciyar ta bata iya riƙewa kanta ita kaɗai gashi bata so ya san abin da ke damin ta dan kar ya gane cewa maganar da ta sanar da shi ba cikakkiya bace. Tana tsaka da kukan ne ta ji ƙarar wayar ta sai ta yi kamar ta share amma wata zuciyar na bata ta ɗau kiran sai ta kai duban ta ga wayar cikin saurumi ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnen ta tana mai sakin wani kukan "Yaya Zaid zai fasa min zuciya ta da son sanin abin da ni kaina nake kan binnewa tun kafin yanzu,sai tambayoyi yake min i can't withstand it na gaji please yaya help me am too young for all these problems"ta fashe da kuka mai tafe da shesheƙa sai yayan nata da ya kira dan yi mata congrats saboda jiya wayar ta a kashe take kowa ya kira sai a ji wayar a kashe toh yana gwadawa ya ji ya shiga sai ya saka a speaker dan tare da Bilal,Lukman da Zainab matar Jamil ɗin suke da fari ma video call yaso yi sai dai ya chanza ra'ayi ya kira kawai,jin abin da ta furta sai yayi saurin cire wayar a hands free ya tashi daga inda yake zaune yayi isolating kan sa a waje ta gefen pool side cikin natsuwa ya kira sunan ta "Bilkisu calm down talk to me and stop crying me ya faru"??cikin kukan ta ce da shi "Yaya tambaya ta yayi in gaya mai abin da ya faru and i narrated everything bayan na gama ya ce bai yarda ba sai na sanar da shi komai,,,yaya ba zan iya ba akwai ugly parts da ba zan iya sanar da shi su ba amma ya natse sai na gaya mai Yaya i have to leave him all alone in that room dan ba zan iya cigaba da kallon sa yana cikin pains ɗin da ya shiga ba but i know by now su Ammi sun ba shi haƙuri na san zai haƙura in suka mai magana kaima in ka mai magana zai janye son sanin labarin please yaya help me na kasa composing kai na"!!tausayin ta ne ya kama sa dan duk a halin ruɗani take maganganun gashi bata da labarin dawowar iyayen nasu dan daga dukkan alamu bata san cewa sun kamo hanyar dawowa ba,daga ita sai Zaid a ƙasar germany babu wani ɗan uwa ko aboki dole su yi tolerating juna haɗe da nunawa junan su kulawa har Allah ya sa Zaid ya sami lafiya su dawo gida. "Baby kina ji na"??ta ansa da "Eh ina jin ka yaya"!!sai ya ƙara sassauto da mutyar sa ta yadda zata ji komai cikin sauƙi "Baby kin ga su Ammi sun kamo hanyar dawowa gida already yanzu a ƙasar nan babu kowa naku daga ke sai shi kuma kin san shi ɗin ba lafiya ce da shi dole ya rinƙa samin kula daga gare ki dan ke kaɗai ya sani bai san kowa ba duk wasu lalurorin sa da ɗawainiyar sa sun komo hannun ki daga jiya har izuwa ƙarshen rayuwar ku kin chanza daga abokiyar aiki,makwafciyar sa kin zamo matar sa abokiyar shawarar sa abokiyar rayuwar sa,,nauyi ne ya ƙaru a kan ki ba kaɗan ba dan haka ina so kiyi concentrating wun bashi kula dan sai kin bashi isashiyar kulawa ne zai sami natsuwa ya warke yadda ya kamata ba tare da an sami mishkila ba,kar ki damu da individual differences da ke tsakanin ku duk waɗannan zaku iya mending nasu in har kuka cigaba da zama tare dan haka ina so ki sani in har kika saba mai da rayuwar ƙarya tun yanzu a kan sa zai ginu in ma na gaskiya ce duk a haka zai ginu so i guess tun yanzu ki sabar masa da faɗin gaskiyar lamari ko da kuwa ba zai mai daɗi ba gwara ya sani daga gare ki than ya ji daga wun wani ko outsider da fatan kin fahimci maganganu na baby sis"??ƙamewa tayi a zaunen dama sun tafi ne ba su sanar da ita ba??yanzu ita ya zata yi da Zaid?yaushe ta gama kula da kanta har da zata fara kula da Zaid all alone?me yasa suka mata haka ne yanzu ko Baha bata tsaya ba suka tafi suka bar ta ita kaɗai tayi nursig kanta sannan tayi nursig Zaid??ta ina zata fara?.. Duk a cikin zuciyar ta taje waɗannan tunane tunanen mantawa tayi da yayan ta na kan layi har sai da ya kuma yin magana "kina ji na kuwa Bilkisu"firgigit ta dawo daga tunanin ta ce "Eh na ji yaya,,amma yaya su Umma basu kyauta min ba ta yaya zan fara kula da kaina in kula da Zaid nima fah convalescence patient ce ba gama warkewa nayi ba ina buƙatar kula ta musamman daga wun wani ta ina zan fara i can't...i just can't do it all alone brother please do something"...sai ya rasa abin faɗa mata gashi sai kuka take yi "Baby stop panicking stop crying komai zai zo maki a daidai da yardar Allah all ypu need to do shine ki natsu kiyi studying Zaid da kyau ki san abin da ran sa ke so da wanda baya so sai ki fara exhibiting but crying won't solve the problem ki natsu zaki iya handling komai baby sis you have to learn how to start leaving alone dan zaki fara family ɗin ki ne so bai kamata ki fara da tsoro ba henceforth be back completely dan Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman da na sani is a conquerer despite the fact that her tittle is Baby doctor but she is actually not a baby when it comes to fighting for her goal she ain't a loser she always win humm dan haka ki daina faɗin wai ba zaki iya ba sure you can kin ji"?? Jan hanci tayi tana jin ta sami ƙwarin gwiwa.. "Nagode Yaya Allah ya saka da alkhairi you are special to me nagode yaya bari in duba shi dan ban san su Umma sun tafi ba" "Shikenan baby sis Allah ya shige mana gaba" "Amin yaya nagode sai anjima"ta kashe wayar haɗe da sauke ajiyar zuciya ta kwanta da baya tana kallon sama.tunanin maganar su da yayan ta take yi sai t ga gaskiya ƙarara a zancen nasa tabbas dole a kan abin da ta ɗora sa zai ginu dan dama namiji da abin da ka sabar mai zai cigaba da gudanar da rayuwar sa. A baya tayi tunanin jan jikin ta daga nasa ta so ne ta rinƙa guje mai ko da wani abin ne ya taso sai ta yi sama sama ta nisance sa sai dai yanzu da ta ji babu wanda ke tare da su da zai taimaka mai akan harkokin sa wanda ya haɗa da su lalurorin sa kama daga cin abincin sa kula da jikin sa shan maganin sa hira tare da shi ta yadda zai ƙara mai kuzarin farfaɗowa gabaɗaya sai ta ga ya kamata ta rinƙa ɗauke masa waɗannan abubuwan he have no one to do it sai ta ji tausayin sa na tsirga ta dan haka wuf tayi ta tashi tana duba jakar kayan shafawar ta ta fiddo ƙaramar abin powder ta buɗe mirror ta ɗan yi touching kwaliyar fuskar ta kaɗan dan bata so ya gane cewa tayi kuka sai ta ɗan shafa lip moisturizer ta kuma bin jikin ta da turaren jiki mai sanyin ƙamshi sannan ta ta chanza kayan jikin ta zuwa riga da wandon Dior pink colour ta ɗora after dress mai igiyar ɗaurawa black colour mai adon duwatsu ƙanana ta nemi ƙaramar gyale baƙa ta yafa a kan ta takalmin valentino na mata ta saka mai ɗan tudu kaɗan sai ta kuma bin jikin ta da perfs kala biyu kacal sannan ta ɗau wayar ta zata fita kenan ta hangi takardar da Ammi ta ajiye mata sai ta koma ta zauna ta ɗau takardar ta warware tana duba abin da ke ciki cikin natsuwa. Har ƙarshe ta karanta wasu kalmomin da Ammin tayi amfani da su sun mata nauyi har take jin kunya ita kaɗai.. Most of the things contained in the later shawarwari ne akan zaman ta da Zaid haɗe da tunatar da ita matsayin ta a wun Zaid ɗin sai kuma shawarar kar ta yarda wani abu ya shiga tsakanin su muddin bata gama amfani da kayan da aka saba bata ba ta sanar da ita unda ta ɓoye mata su cikin trolley ɗin ta ne da ke waldrop na ɗakin chan cikin ma'ajiyar ƙarshe a nan ta ɓoye mata.. Da ta gama karanta wasiƙar sai ta nannaɗe ta nufi waldrop haɗe da budewa ta ajiye papern a back zip ɗin jakar sannan ta mayar ta rufe ta ɗan ƙara kallon kan ta a wayar ta sannan ta nufi hanyar waje,tunani ne fal a ran ta dan sai yanzu ma ta tuna wai bata sanar da shi matsayin ta a gare sa ba ko ya zai ɗau maganar Allah ne ya sani.. Da fargaba ta doso ɗakin tun daga ƙofar ɗakin take kallon sa ya jingina da pillow idanun sa a buɗe yana kallon gefe ɗaya so she felt awkward abin da ta mai bai dace ba shi kaɗai ta bari tayi tafiyar ta ba tare da ta tsaya ta saurari damuwar sa ba what if he hasn't taken his drugs mr kenan tayi a matsayin ta na matar sa ai wannan babban abin kunya ne a gare ta sai dai ta daure ta shiga ɗakin fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali she is feeling clumsy already dan ta san bata kyauta mai ba wai ma tukun me ke damin ta ne haka she get confuse easily kuma duk saboda tunanin Zaid ne. Tsaye tayi daga tsakiyar ɗakin ta ƙi ƙarasawa sai ya lura ya kira ta "Bilkisu akwai wata matsala ne"??very calm and gentile yayi maganar and so he drove her crazy and insane ita dai bata san ya zata yi da Zaid ba sam she doesn't feel comfortable in har ya kira sunan ta kai tsaye haka kuma gashi yanzu kamar da gangan yake kiran sunan dan ya ga yana causing mata effect.. "A'a babu wata matsala dama so nake in sani ko ka sha magungunan ka na safe na ga har 11am na son gotawa"!! Na sha magunguna na na safe??strange ya faɗa a zuciyar sa shi so yake ma ya san a wace ƙasa suke but bata yarda ta bashi opportunity ba hakan ba ƙaramin danuwa ya janyo mai ba shiru dai ya mata yana jira ya ga iya gudun ruwan ta. Jin bai ce komai ba sai ta ji ta tsargu dan haka ta bar shi a ɗakin ta nufi inda nursing personnel suke ta masu kwatancen ɗakin sa haɗe da tambayar ko an yi serving masa morning drug nasa.. Dubawa suka yi suka tabbatar mata da cewa ba'a bashi ba dan bacci yake yi sai ta ji mamaki wani irin bacci bayan ta san idanu biyu ta bar sa kuma ta dawo ta tarar da shi a jingine alamar dai ba baccin yayi ba maybe he pretended to be asleep dan kar a takura shi,,umartar su tayi akan su zo su bashi ya farka dan haka ɗaya daga cikin su ta bi ta har zuwa ɗakin sa a inda suka gansa kwance shiru fara harhaɗa magungunan tayi har ta gama ta matsa zata nufe sa dan bashi ya sha ai Bilkisu bata san lokacin da ta dakatar da ita ba cikin kakkausar murya "Excuse me young lady,,no need for all the unnecessary care just give it to me i will make sure he take the drugs hmmm"?babu ko tsilin fara'a a kan fuskar ta sai baturiyar nurse ɗin ta mata wani irin kallo irin kallon are you okey at all ɗin nan ke kika kirawo ni sannan kina min wani irin kallo??sai dai bata furta ba ta bar ma kana ta yi gaba abin ta tana tunanin anya yarinyar nan bata da matsala a ƙwaƙwalwar ta kuwa.. Da harara ta raka bayan nurse ɗin kafin ta sake tsaƙi ba tare da ta san ya kufce mata ba kafin ta kai inda ruwan shan maganin yake tayi ƙwafa ya fi a ƙirga shi dai da ido yake ta bin ta dan shi kam yau ya ga abin mamaki daga gare ta as smallish as she is amma ta iya yiwa matar nan rashin kunya what did she mean?mr mme actions ɗin ta ke nufi?he have to ask her. Kyaketa yayi ta gama zuba ruwan ta matso haɗe ce mai " tashi ka zauna sai ka sha maganin"bin umarnin maganar ta yayi babu musu ko jan magana ya zauna ta miƙo hannun ta ta ce mai ya buɗe bak,buɗewar yayi ta zuba mai haɗe da bin maganin da ruwa ya haɗiye sannan ta gyara mai pillow ta mayar da kofin ruwan ta ajiye. Dawowa tayi ta zauna ttana tunanin tambayar sa ko yayi wanka amma hakan ta daure ta tambaye sa cikin sanyin murya "An maka wanka ne"??sai ya ji abin banbaraƙwai dan haka ya bi ta da idanun sa wanda ya saka ta yin ƙasa da nata idanun tana tsoron kar ya zarge ta akan abin da ba shine ba. For a While sai ta ji sautin muryar sa "A'a han yi ba me ya faru"??faɗuwar gaba ta ji sai ta kasa cewa komai har dai ya gaji da shirun ya ce "Me ya faru na ce ban yi ba"!!cikin fargaba ta ce "Toh dama zan taimaka maka me in ba zaka damu ba"da mamaki ya kalle ta ya girgiza kai ya juyar da kan sa grfe sai ta ji ba daɗi dan haka ta ce mai "Zaid taimakon ka zan yi ka yi wankan ka ga Hakim baya nan duk sun koma please let me help me dan ka sami bacci mai daɗi humm"??shiru ya mata yana kallon ta ita bata son yadda yake kallon ta sam dan haka sai ta kaear da fuskar ta gefe shi kuma ya ce da ita "Kina so ki taimake ni saboda kina wa kenan"cikin tsoro ta ce "Zaid am your wife and am here to help you get bath ka ga har chanza kaya na nayi dan in kaika wajen building ɗin nan saboda ka yi saurin farfaɗowa gabaɗaya am not here tk harm you daga ni sai kai ne kawai a ƙasar nan kuma saboda ina matar ka ne yasa aka bar ni tare da kai dan in kula da kai please Zaid let's get you clean up dan mu fita ka ga waje ka ji"??ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba yayin da take maganar dan saura kaɗan tayi fainting masa a wurin sakamakon yawan faɗuwar gaban da take ta samu yayin yin maganan da shi ƙasa ma taje kallo dan ba zata iya cigaba da kallon sa ba.. Wani irin kallo ya ke mata wanda ya saka ta jin akwai idon wani a kan ta sai ta ɗago suka haɗa ido ta ga irin kallon da yake binta da shi irin kallon nan can only mean one thing oh ya salam what did she get herself into?ita da ke son dagewa dan kar ta yi ƙasa saboda ta taya shi farfaɗowa amma yake mata irin wannan kallo haka?ya zata yi ina zata kalla ta sami sauƙi dama ta sani za'a sami matsala amma wannan kallon da yake mata duk ya fi hargitsa ta da tsorata ta dan ita kaɗai ta san ma'anar kallon..Cigaba da aika mata da kallon ɗaure jijiyoyin jik ya ke yi sai ta rasa ya zata mai bayanin itama ba da son ran ta aka masu auren ba sai dan dalilai da dama kuma a yanzu ita bata son ya ji abin da zai ɗaga mai hankali ko ya firgita sa dan bai kamata yana ƙoƙarin warkewa ba sannan ta ƙara danƙwafar da shi ba. Tunowa tayi da maganganun yayan ta na fara ɗabbaka responsibilities ɗin Zaid a kan ta sannan tayi resuming wifely duties nata ba tare da ɓata lokaci ba dan kula na musamman yake nema daga wun makusancin sa wanda babu wani makusancin da ya fita a yanzu dole ko zai cigaba da yi mata wannan murɗaɗen kallon sai ta yi abin da zai faranta mai.+ "Zaid baka amsa min ba ka yi shiru..."!ƙarfin hali tayi har ta mai tambayar sai bai ce mata ƙala ba ya cigaba da kallon ta. She just hate the way he stairs at her bata jin sauƙi a zuciyar ta,bata ƙara second ba ta tashi ta shiga toilet ta hau neman abubuwan da zata haɗa mai dan ya sami warm bath,bathing lotions ɗin sa ta harhaɗa tayi regulating mai ruwan wankan a right temperature dan har sai da ta nemi bath thermometer ta gwada ruwan wankan sannan ta shiga haɗo abin guaran fuska kama daga shaving cream zuwa liquid face cleaners da su shaving stick,face mask da ake mannawa bayan an gyara fuska saboda ya taimaka wun smoothening fuskar,mirror da cucumber paste duk ta haɗe su a cikin ƙaramar tray da ke ɗakin wanda a ciki ake zuba kayan datti kamar sachet na magunguna da su kwalayen drips Fitowa tayi da su sannan ta koma ta ɗauko warm water a bowl haɗe da ƙananan towels biyu ta dawo. Ɗarɗar take ji amma ba zata iya cigaba da kallon sa yana son losing appearance ɗin sa ba kawai saboda yana kan jinya a gadon asibiti ko ba komai ai shi ɗin mai matsayi ne a gare ta tunda har hukuncin Allah ya sa ta zamo matar sa.. Ko kallon kwayar idanun sa bata yi ba ta shiga mixing abin buƙata har ta kammala sannan ta ce mai cikin tsare gida "Zan maka gyaran fuska ne kafin ka yi wanka please cooperate"..bin ta da ido yayi kamar wanda bai da bakin magana sai ido,haɗa ido tayi da shi ko second bata ƙara ba ta cire nata idanun daga nasa haɗe da cewa "Let's begin"bata tsaya jiran sa ba ta hau ɗeban shaving cream na kamfanin aloe vera ta zo dab da fuskar sa tana tsoron kar ya dakatar da ita sai dai ga mamakin ta sai ta ga ya ajiye mata fuskar ba yabo ba fallasa hannun ta na ɓari ta kai kan fuskar sa wanda ba ita kaɗai ba har shi sai da ji electrification da ya haɗe a yayin da hannun ta ya taɓa fuskar sa. Kasa janye hannun ta tayi sai ta bar shi wu guda tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo,kallon kallo suka tsaya aikawa juna har suka ɗau lokaci mai tsayi ba tare da sun sani ba,bata farga ba sai da ta ji sautin muryar sa cikin gajiya ya ce "Auchhh"!!a nan ta tuna cewa ta bar hannun ta mai ɗauke da cream a kan fuskar sa a wu ɗaya,cikin sauri ta cire hannun bakin ta na ɓari muryar ta na karyewa ta shiga ce mai "Am...a...m...amm so.oo..rrr...yyy"kallon ta yayi ita kuma tayi saurin ɗaukar hand towel ɗaya ta shiga hoge mai part ɗin da ta bar hannun nata,ko da ta kai towel ɗin da nufin goge cream ɗin sai ta ga har suman wurin ya karye yayi laushi sai ya fita,cire towel ɗin tayi daga kan fuskar sa tana kallon towel ɗin shima towel ɗin ya ƙurawa ido,at the same time suka ɗago suka zubawa junan su idanu sai chan ta cire nata idanun daga nasa tayi ƙasa da idanun cikin in ina tace "Kayi haƙuri ban lura bane".. Ci kanki bai ce da ita ba sai ya kawar da fuskar sa dan haka ta bi sa ta direction ɗin da ya juyar da fuskar sa ta kai hannun ta cikin tsantsene da hikima ta shafa mai cream a fuskar,a hankali ta shiga murza mai cream ɗin tana yi tana kallon reaction na sa dan tana gudun kar ta kuma maimaita abin da tayi earlier on. Da ta tabbatar cream ɗin ya bi ko ina a fuskar sa sai ta koma kan suman kansa da ya taru har ya wuce misali,in bata manta ba gyaran suman sa yayi shige ne da na boys scout mai fasali na zamani dan haka tayi picking scissors da ta ɗauko musamman dan gyara mai sumar. Yana kallon ta da idon sa kamar wani saƙago wanda aka sassaƙa sai an bashi umarni yake iya aiwatar da abu,kaɗan gently ta fara bin suman tana yankewa a hankali dan kar wani wun ya fi wani wun tsayi ko gajerta,a haka a haka har ta yi leveling suman zuwa desired look da ta gama ne ta dawo kan fuskar sa tayi amfani da hand towel ta goge mai fuska sannan ta bi sajen sa ta yi amfani da brush ta rinƙa taje shi a hankali har ta kammala sai ta ɗau face mask ta manna mai sannan ta koma kan suman kan sa ta shafa mai wani exotic hair wash ta cuccuɗa tana gamawa ta cire mai face mask ɗin ta shafa mai cucumber paste sama sama shi dai yana kallon ta ƙala bai ce da ita ba hakan kuma ya mata daɗi dan ta sami ɗaukewar kashi casa'in a cikin kashi ɗari na fargabar da ta rinƙa samu kafin ta fara mai gyaran ga irin kallon ƙur da ya rinƙa mata ɗazu sarai ta gane ko kallon menene sai dai ita kam tayi alƙawarin enduring duk wani maganganun zafafa zuciyar da zai mata dan dole a matsayin ta na matar sa ta koyi shanye duk wasu rigingimun da zai taho mata da su addu'ar ta ɗaya kar Allah ya bashi ilimin tambayar ta Asma'u dan ji take kamar zuciyar ta zai buga a duk lokacin da ta tuno yarinyar abin da ya faru da su bai mata daɗi ba ko kaɗan hakan ya sa ta ɗau tsanar duniyar nan ta ɗora shi akan Asma'u dama chan jinin su bai haɗu ba bare yanzu da take ganin itace ummul aba'isin na janyo masu matsalar da suke ciki dan haka bata jin zata iya yafe ma yarinyar so soon dan yanda take jin zafin abin da yarinyar tayi ko shi da ya aikata ta'addancin bata jin zafin sa kamar yadda take jin na yarinyar.. Kusan tun da ta fara har ta ida a halin kurame suka yi gyaran fuskar sai da ta kammala ta mai kallon tsanake ta ga ya fito a ainihin Dr Zaid Maher ɗin sa though akwai wasu tranaformational changes da ya faru a jikin sa kamar ramar da ya ɗan yi alamomin jinya da ya nuna a fuskar sa sai gajiya da yake tattare da shi.. Magana ta mai cikin ruwan sanyi ta ce "Na gama duba ka gani in akwai wani wurin da kake so a ƙara gyarawa sai ka sanar da ni"!!kallon mamaki yake mata dan maganar ta na kan yi mai yawo a ƙwaƙwalwa wai ita ɗin matar sa ce gaske ne ko ko rainin hankali ne dan ta ga he is helpless. Kallon sa itama take yi tana jiran jin amsar sa sai dai har ta gama ƙiyastin ta bai amsa mata ba ya ƙyake ta kuma wannan guilty look ɗin yana nan yana bin ta da shi kasa jurewa tayi sai ta miƙe tsaye tana mai gyara mayafin ta. "Wanka zaka yi bari in taya ka ka shiga toilet"!!wani razanannen kallo ya bita da shi she must admit that ta gigita da kallon saidai bata bari ya gane hakan ba ta ɓoye ta cigaba da abin da take yi "Mu je kar ruwan yayi sanyi"!!kai hannun ta tayi ta riƙo nasa a hankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga sa with the hope that zai taya kan sa tashi in yaga effort da take yi sai dai bai taya ta ɗin ba dan daɗa ƙara weight ɗin sa yayi a kan gadon tayi tayi ya tashi ya ƙi sai ta ɗago ta haɗa ido da shi ta mai alama da ido akan ya tashin mana amma yayi shunning nata sai ta gane ashe ba wai weakness ne ya sa ya kasa taimakon kansa dan tashi ba a'a kawai ra'ayin sa me yin hakan sai ta haɗiyi wani abu da ta ji ya taso mata ta cigaba da trying dan dai ya tashin amma ya ƙi. Bai tashin ba ita kuma bata karaya ba ta cigaba da ƙoƙartawa dan kan shi ya tashin dan ya ga kamar ta fara gajiya har zufa take yi,yana tashi tayi tanga tanga kamar zata faɗi sai dai ta yi saurin regaining balance shi kan sa ya tsorata da ya ga zata faɗi sai dai da tayi regaining balance ɗin ya sami relief amma bai nuna ba ita kuwa ko a jikin ta ta matso ta riƙe sa ta baya ɗaya hannun ta na riƙe da nasa hannun a haka suka fara takawa har ta kai shi bakin toilet ta rasa me zata yi shin ta raka sa har ciki ne kokuwa ta bar sa ne a bakin toilet. Tsayuwar ya fara gundurar s sai yayi tsaki hakan ne ya fargar da ita har ta ruɗu bata sani ba ta cigaba da tafiyan yana bin ta suna takawa ta kai sa har kan bathtub ɗin ya zauna dama komai ta tanadar mai wanda zai baƙata ta kawo mai bath throb kusa da shi ta ajiye su sponge da bath liquids daga haka ta kalle shi cikin tausayi ta ce "In ka gama ka sanar da ni sai in zo mu fita".. Wannan kallon baƙuwar ya bita da shi ita dai tayi gaba dan gani tayi kamar tunda ya farfaɗo bai da wata ɗabi'ar da ta wuce na kallon ta dan ko sauran mutanin da ke kewaye da shi baya masu kallon da yake mata takan rasa ma'anar kallon. Dawowar ta ɗakin ne ta shiga gyara mai gadon sa ta canza bed linen ɗin ta share ɗakin da electric cleaner ta biɗe waldrop ɗin sa ta shiga kallon kayan nasa dan tantance wannene zai fi masa sauƙi sakawa,bayan dube duben da ta yi sai ta fiddo mai da Tom ford tuttle neck top ash colour ta haɗa da black jeans,white singlet ta ɗauko,muffler ash colour ta haɗo da sai head warmer ash mai tuntu baƙi, takalmin sneakers baƙa mai tambarin NBA da aka yi shi da ash colour gyara shoelace ɗin tayi daga yadda aka saka shi zuwa wani iri ta yadda zai ƙayatar.mayar da waldrop ɗin tayi ta rufe ta dawo da kayan a hannun ta a kan gadon ta zuba su daga nan side drawer ta buɗe ta duba kayan shafar sa ta fito da su ta ajiye a saman drawer ɗin. Zaman jiran alamar gamawar sa take yi time to time takan kalli agogon hannun ta dan ganin time in ta haɗa duka time ɗin da yayi spending a toilet zata iya cewa ya sami kyawawan mintuna arba'in a toilet ɗin nan wanda ta san ko da wani irin wanka ne wannan da yake yi ya ci a ce ya kammala but me yasa bai yi alerting nata ba wata zuciyar ce ta bata amsa da cewa ta yaya zai yi alerting ɗin ki bayan ke kanki kin san kallon da yake miki ba irin kallon ya gamsu da ke a matsayin matar sa bane sai ta yi tunanin in har kuwa so take Zaid ya amince cewa ita ɗin matar sa ce toh dole sai ta yi mai abin da zai fahimci hakan har ma ya gamsu da haka. Wannan tunanin ne ya ingiza ta ta taka har zuwa bakin ƙofar toilet tana mai tambayar sa a hankali "Zaid ka gama wankan ne"!!sai da ya ɗau lokaci sannan ya amsa da "Uhum"kamar dai marar baki haka ya amsa mata. Tura ƙofar tayi ta shiga kan ta a ƙasa har ta zo kusa da shi dan zaune yake a inda ta bar sa kafin ta fita kenan bayan ya gama wankar ne ya koma ya zauna a gefen bathtub ɗin ɗaure da bath throb da ta bar mai ƙafar sa sanye cikin slippers bath throb ɗin bai kai mai har ƙasa ba amma da kaɗan ya rage ya kai ƙasan space ɗin da yake expose a ƙafar sa abin kallo ne dan suma ne kwance sakamakon ruwan wankan da ya taimaka wun kwantar da suman fatar jikin sa sai glowing ƙafar ke yi. Kai hannun ta tayi ta riƙe sa suka fito tare daga nan ta zaunar da shi a kan kujera ita kuma ta ɗauko towel dan goge mai kai daga tsayen ta bayan sa ta riƙe towel ɗin ta shiga goge mai kan tana yi tana massaging kaɗan kaɗan gently har ta gama sannan ta dawo ta zauna a saman gadon suna kallon juna ta ɗauko body lotion da ta fito da su ta matsaa hannun ta ta murza tsugunawa tayi ta shiga shafa mai a ƙafar sa ta dama ta ɗago ta kuma matsowa ta murza ta tsugun ta shafa mai a ƙafar hagu daidai inda towel ɗin ya rufe da kaɗan wato gwiwar sa a nan take jan burki dan bazata iya shafa mai duka ba da ta gama ta hau shafa mai a hannun sa shi kam abin na bashi mamaki ba dan komai ba sai dan farin sanin da yayiwa yarinyar dan first class ce wun girman kai da izza amma sai gashi yau ya nuna mata attitude ta hanyoyi daban daban duk dan ta san cewa shi fah ba yarda yayi da abin da ta gaya mai ba wai ita matar sa ce amma bata nuna ko a fuska ba akan abin ya mata ciwo ko ya ɓata mata rai ba me yasa haka. Jin muryar ta yayi tana ce da shi "Na gama saura saka roll-on gashi saka"ta miƙa mai kallon roll-on ɗin yayi kafin ya kalle ta ta amsa mai da kai akan ya karɓa ya shafa,karɓa yayi ita kuma ta shiga mayar da cream ɗin leaving a little gap da zata mayar da roll-on ɗin in ya gama amfani da shi ko da ya gama shafawa bata jira sa ba ta karɓa haɗe da miƙo mai fogg body spray ta ce "Ungo ka fetsa"she behave gentile and kind it amuses him. Karɓa yayi ya fetsa haɗe da miƙa mata ta ƙarba ta haɗa da roll-on ta mayar a drawer daga nan ta tashi dan miƙo mai kayan sa da zai saka sai ta tuna bata ɗauko mai boxers basai ta koma ta buɗe ta hau dubawa hangowa tayi an yi hanging nasu a wasu hangers sai ta ɗau ɗaya ta juyo da shi ta miƙo mai kan ta a ƙasa. Nan ma sai da ya mata kallon stranger sannan ya karɓa sai ta juya mai baya dan ya sami privacy ya saka hankali kwance. Da ya gama sakawa bai mata alamar ya gaman ba sai ya cigaba da saka sauran kayan ya saka inner wear ya ɗau top ya saka ya ɗau jeans har ya fara sakawa sai ta ga kamar ya kamata a ce ya gama saka boxers by now sai ta juyo dan miƙo mai rigar da zai saka sai dai tana juyowa idanun ta bai sauka a ko ina ba sai kan jeans trouser da yake hannun sa ga rabi ya wuce rabin ƙafar sa sai tayi gaggawar runtse idanun ta tana jin faɗuwar gaba oh ita me ya kai ta juyowa yana cikin halin nan har zata juya ya dakatar da ita ya ce "Get me a belt"!! Da sauri ta isa gaban waldrop ɗin ta buɗe ga belts ɗin nan a gaban ta but abin mamaki shine sam bata lura da shi ba sai da ta gama kalle kallen ta sai chan ta ga belts ɗin a gaban ta dan haka ta ɗau ɗaya daga cikin belt ɗin ta ɗan tsaya gudun kar ta kuma yin gamdakatar da abin da ta gani ɗazu, Ya san tsayawa tayi dan kar ta gan sa a halin da ta gansa ɗazu sai yayi gyaran murya.hakan ne ya bata damar juyowa dan alama ce da ya gama saka kayan. Miƙo mai tayi tana sinne kai ƙasa karɓa yayi ya shiga sakawa ita kuma tana kallon ƙasa da ya kammala sai ta kwaso takalmin ta kawo mai kamar dai ta bar shi ya saka da kansa sai kuma ta fasa ta durƙusa ta shiga saka mai takalmin da ta gama ta ɗaure shoelace na takalmin tana gamawa ta miƙo mai oud perf mai ƙarfin ƙamshi ya fetsa sannan ta karɓa ta mayar muffler ta saka mai a wuyar sa ta ɗau head warmer ta saka mai sannan itama ta gyara gyalen ta ta ɗau wayar ta da nasa ta riƙe a ɗaya hannun ta da ɗaya hannun ta riƙe sa tunda ta ga kamar yana da ƙarfin jikin sa baya buƙatar much help haka nan tashi yayi da taimakon ta daga haka suka shiga takowa har suka fito kamar kurame bata ce da shi a ba bai ce da ita uffan ba da suka fito ta saka ma ɗakin security pin ya rufu sannan suka cigaba da takawan. Ta baya suka bi suka fita daga asibitin baki ɗaya akwai wani garden mai ɗauke da park na wasanni chan suka nufa tun daga nesa take son fara jan sa da magana sai dai hakan ya ci tura dan bayan kallon gaban sa da yake yi baya kallon ko ina gashi fuskar kamar an mai dole. Daurewa tayi dai ta ɗago da maganar "Ni kam Zaid in tambaye ka mana"cikin taushin murya tayi maganar wanda ƙaryan mutum musamman ɗa namiji ya ce an mai magana ta wannan siga bai ji shi har cikin tsokar jikin sa ba amma da yake Dr Zaid Maher is almost back to his Dr Zaid Maher sai yayi pretending bai ji abin da ta ce ba and so she have to ask again "Zaid na cein tambaye ka mana"!! Sai a nan ya ce "Uhhhnn"irin ina jin ki ɗin nan tsabar jin haushi bata san lokacin da ta ce da shi "Damuwar ka"ba abin sai ya so bashi dariya amma ya mazge kamar dariyar bata taso mai ba saboda out of frustration tayi maganar ba tare da ta san zai fito da sautin haushin da ta ji ba. Sai da suka yi nisa a takawar sannan ta ji sassaucin abin haushin da ya mata har ma ta tuna da abin da ta yi mai na demonstrating ɓacin ran ta a gaban sa. Bata ce da shi komai ba ta ƙyale sa kamar dai yadda yayi shiru shima. Da suka ƙarasa cikin park ɗin ne suka nemi wun zama ta bar sa a nan ita kuma ta ƙarasa zuwa ciki wun masu saida kayan sanyi dangin su smoothies,icing,vinegar icing,ice creams,da dai sauran su ordering vinegar icing tayi ma kanta shi kuma ta karɓo masa smoothie,master card ɗin ta ta miƙo masu suka yi transferring haɗe da miƙo mata card ɗin ta ce da su thanks. Daga nan wun masu siyar da kayan ciye ciye ta nufa inda akwai abubuwa da dama kamar su cookies,spring rolls,sandwich,hot pizza,hamburger,da sauran easy chops. Hamburger ta karbawa kanta shi kuma ta kaeɓo mai cookies though bata sani ba ko yana ci ko baya ci. Nan ma transferring aka yi aka miƙo mata card ta juyo ta nufo inda ta bar shi tana ɗan murmushi dan tunowa da ranar da suka haɗu a theater room yana surgery babu assistance sai anaesthetics ran nan a haɗe ita kuma ta rantse ba zata taimaka mai ba dan bai nemi taimakon nata ba gashi babu wasu likitocin kaf suna off ranar ma emergency surgery ne ya taso ita kuma ta zo duba patient ɗin ta sai ta ga yana buƙatar taimako amma rashin tambayar alfarma daga gare ta ya sa ta shiga surgery room ɗin tayi zaman ta tana kallon sa har ya gama da taimakon anaesthetic nurse yana gamawa tayi tafiyar ta shi kuma ya rinƙa bin ta da kallon takaici. Tana isa kusa da shi annurin fuskar ta ya kau ta zauna haɗe da miƙo mai abin da ta siyo mai karɓa yayi ya ajiye a gefen sa sai ta juyo ta kalle sa ta kalli gefen da ya ajiye abin da ta kawo mai sai ta juyar da kai ta ce "Uhumm"daga haka ta fara shan ice vinegar ɗin ta tana sipping kaɗan kaɗan babu wanda ya ce komai a cikin su shi ya zuba ma park idanu yana kallon wasannin yara dama ƴaƴan turawa da rashin ji in an ce su bari basu bari,wani ɗa ne ke faman throwing tantrum kawai saboda an hanasa shiga cikin anaconda na wasa da ke park ɗin, uwar tayi tayi ta rarrashe sa amma ya ƙi jin ta sai kuma uwar ta koma bashi haƙuri madaɗin yayi shiru sai ya ƙi yin shirun ya saka mata kukan banza Duk event ɗin nan a kan idanun Bilkisu da Zaid ake yin su,gajiya Zaid yayi da kallon rashin ta ido irin ta ɗan sai ya miƙe a hankali ya shiga takawa har ya isa gaban su a hankali ya durƙusa ya riƙe hannun ɗan yana kallon sa yana son sanin damuwar sa "Hey kiddo whats up"sai yaron ya kalle sa idanun sa cike da hawayen shagwaɓa ya ce "Momma doesn't wanna let me play with the anaconda she didn't allow me to play with the cobra all my buddies are there play with the anaconda but momma isn't listening to me she doesn't want me to play around i just wanna go home".. Kwata kwata yaron ba zai wuce 5years ba a shekaru kuma daga dukkan alamu yana da tsiwa da rashin ji sai ya murmusa ya shafa kan yaron yana cewa "Common cobra tell me when momma says you shouldn't play and stops you from playing what does it signifies"??sai yaron ya ƙurawa Zai ido kafin ya ce "It signifies that something dangerous is there"cikin gamsuwa ya tari yaron ya ce "Good cobra,that's it momma have seen something bad and that is why she didn't allow you to play there with your friends"sai yaron ya kyaɓe fuska ya ce "But i wanna play buddy"abin dariya one sided smile Zaid yayi sannan ya ce "Tell me kiddo are you sure you not scared of anything"??sai yaron yayi shiru yayin da mahaifiyar ɗan ke kallon su cikin admiration dan dai ta san wannan stranger ɗin ba ɗan ƙasar su bane but yana da kirki gashi har ya fara gano matsalar ɗan nata da ita kanta ta kasa rarrashin sa but ga wannan yana ta jan sa da hira shiru ta yi tana kallon su tana murmushi. Amsar da ɗan ya bashi ne ya sa ya ji tausayin yaron "Buddy am scared of darkness"sai ya ce da shi "And i think the anaconda is dark what did you think"??a rikice yaron ya ce "Yeah the anaconda is dark"sai ya ce "And you are scared of"?? ai a mugun tsorace yaron ya ce "Darknesssss"da gudu ya shige bayan mahaifiyar sa yana ɓoyewa tsabar tsoro sai ya shiga cewa "I don't wanna go i hate darkness i hate anaconda"sai Zaid yayi murmushi cikin ruwan sanyi yayi handling abin da mahaifiyar ɗan ta kasa yi wai dan ma ɗan turawa ne in ba dan haka ba da da iron hand zai yi handling ɗin sa dan shi ya tsani rashin kunya kuma that is exactly what the boy is doing kuma uwan na kallon sa imagine.. Miƙewa yayi ya juya zai yi tafiyar sa sai mahaifiyar yaron ta dakatar da shi ta hanyar ce mai "Thank you young man,my son Andrey is having a disorder he have claustrophobia he get scared easily and that is why i don't allow him to play all alone his friends are used to playing alone and they might forget him while playing he can get into harm i don't hope for that"sai ya gyaɗa mata kai alamun ya gane sai ya ce da ita "I understand Ms... "?sai ta ce "Mcsantos am Elina Mcsantos nice meeting you"sai ya ce "Me too"da murmushi ya juya zai tafi ta kuma dakatar da shi "And you are"sai ya ce "Call me Zaid"sai ta ji abin banbaraƙwai dan haka ta ce "Just Zaid"?da murmushi ya ce "Dr Zaid Maher"cikin amusement ta ce "Wow nice name but i will address you by Dr ZM did you like it"??sai ya ji mamaki kamar an sanar da it ɗaya sunan sa da aka saba kiran sa da shi a asibiti sai ya ce "Sure"da fara'a a kan fuskar sa ya juya zai tafi sai ta kuma ce mai "That beautiful lady..is she your spouse"??abin sai ya ɗaure mai kai ya manta shaf wai ta gaya mai shi ɗin mijin ta ne sai ya rasa me zai ce ma Ms Mcsantos ga ta da surutu ta ya ma aka yi tambayar ta ta kawo wannan gaɓar ya ma aka yi ta hango baby doctor sai ya ji bakin sa ya mai nauyi me zai ce wa matar dan shi kam bai yarda da zancen baby doctor ba wai ita matar sa ce haka kawai kai tsaye ake yin aure. Jiyo muryar ta yayi cikin fushi tana cewa "Yes am his spouse you have problem with that"??ta faɗa tana mai zaro mata rikitattun idanun nan nata da suka fara canza launi dan ɓacin rai sai matar ta tsorata ta ce "No..i don't but you got a good and caring husband"cikin gundara da maganar matar da gajiya da kallon mummunar fuskar ta kamar dai yadda ta laƙaba a ran ta ta ce da ita "I know"da murmushin haushi ta bi matar sai matar ta tsorata da irin kallon da ta bita da shi sai ta ce "Just complimenting"a harzuƙe ta riƙo hannun sa suka fara tafiya tana mai ce ma matar "We don't need your compliment"a haka suka tafi sai bambami take yi wai matan turawa basu da kamun kai da mazajen su but da zarar sun ga wasu mazan jikin su ya shiga ɓari kenan ko abin da ta siyo masu bata bari sun ɗauka ba ta ja shi suka koma asibitin yana binta da kallon mamaki why is she behaving so strange in ta gan sa tare da mata...

0 Comments