IYA RUWA FIDDA KAI CHAPTER 3

IYA RUWA FIDDA KAI CHAPTER 3
Tun da aka fara waɗannan matsalolin na su Dr Zaid da baby doctor ko kusa Dr Aslam bai da labari bai sani ba kuma bavu wanda ya sanar da shi dan ba ta kan shi ake ba kuma dama ba wayar kirki suke yi da ita baby doctor ɗin ba ko da kuwa tana daidai gaɓar da akwai service yayi nasarar kiran ta toh ba ɗaga kiran take yi ba sai dai ta ƙyale dan mugu mugun haushin sa take ji haka kawai ta tsani ganin lambar sa da sunan sa in yana kira abin suƙin kuma shine uban gayyar ma ya daina kiran sunan Dr Aslam ɗin in suna tare bata san dalili ba... Wata alhamis ya shirya na musamman ya tafi gidan su baby doctor dan sanin ko ana jin labarin su dan fah shi ya ƙudiri aniyar cewa da zarar sun dawo daga outreach ɗin zai mata magana a turo kawai a yi a wuce wurin dan shi babu ranar Allah ta'alah da zai waye bai ji son babyn ya daɗu a ran shi ba dan gaskiya bai taɓa soyayya ba bai san ya ake yin ta shi yasa da ya fara da baby doctor ya ke jin in bai mallake ta ba toh lallai akwai matsala duk rashin bashi muhimmanci da bata yi bai dame shi ba hasalima gani yake yi duk cikin so ne dan bata da baƙi a wurin sa komai tayi daidai ne bat laifi a cewar sa ma in suka yi auren zasu saba ne kaɗan kaɗan... 3 On reaching there ya riski labarin ai ƙalau suke kuma ba wani matsala ko damuwa kawai rashin samin lokaci ne hakan sai ya haddasa masa tunane tunane marasa kan gado da fasali sai yake ganin yanzu shikenan tana chan tare da Dr Zaid abokin hamayyar sa suna chan tana faman yi mai murmushi ko ma heart killer laughter ɗin ta sai ya ji wani baƙin ciki da ɓacimn rai duk sun ziyarce shime yasa ma tun fari bai amince zai bi su ba ai da ya ce shima zai tafi dan he is sure that Bilkisu is not well secured with Dr Zaid hakan ne ya sa ya yanke shawarar da dawowar su zai saka mahaifin shi a gaba a yi mai yiwuwa dan yana ganin rayuwar turai da ya ke kan turbar yi ba zai kawo mai hanya mai ɓillewa ba domin kuwa cutuwa yake yi dan shi jiran ta yake yi ta fara son sa amma sai abin ke nema ya fi ƙarfin tunanin sa dan instead ta faɗa tricks ɗin sa sai ya ga kamar ƙara bata chances yayi na baje kolin soyayya da Dr Zaid which he doesn't welcome it.. Duk matsalolin da ya faru ɗin nan kama daga incidence ɗin da ya faru a koma har dawowar su gida na tsawon 2 weeks ɗin nan har tafiyar su germany bai da labari dan kafin nan mahaifin sa ya tura sa zuwa ƙasar Oman domin yi mai wani babbar assignment wanda hakan zai ɗauke shi sama da wata guda har ma da ɗoriyar sati biyu,bai so ba but ya tafi da zumar in ya dawo zai sanar da mahaifin sa komai dan shi ya matsu bai mallaki Bilkisu ba..... °°°°°°°°°°°°°°°°° A nan gida kuwa bayan tafiyar su Dr Maher da Dr Muhammad Hajiya Zeenat da aminiyar ta Hajiya Madina sun ci kukan su sun ƙoshi ƴaƴan su duk ba su cikin sukuni aka rasa wa zai tsawatar wa wani dan babu ranar gogewar wannan ɓakin babi da ya buɗo masu har sai ranar da Allah yayi sauƙi zai ziyarce su a zuriar, Misalin 7pm Hajiya Zeenat ta fito cikin shigar doguwar rigar abaya silver mix da mayafin ta ƙarama ta yafa dan su basu yarda da hadisin bononon mutani ba na cewa dan ka hayayyafa ka yi jikoki shikenan ka tsufa ba su dan gudun kalmar tsufar ma ya sa auke hole rayuwar su su je chan ƙasar su je chan ƙasar dan fah basu yarda sun tsufar ba in ya kama ma wani tafiyar har da surikar Hajiya Zeenat ake yin shi tun kafin ta sami ciki sai su ce ai ciki baya hana jin daɗin rayuwa toh ko da ta haihun ma zarah ta kai 8months tare ake tafiyar da ita da baban ta in suka tafi a miƙa ta hanun nanny su kuma su hole rayuwar su acewar Hajiya Zeenat idan har zee na ma jamil waɗannan abubuwa toh tabbas babu wata macen da zai kalla ta burge shi dan matsalar matan arewa ne na wai dan ka yi aure an gama amarci an sami ƙaruwa shikenan sai mace ta mai da kanta babbar ƙarfi da gadara toh ita bata amince da wannan haɗubar ba ta fumi yarda da rayuwar jin daɗi dan da shi ta sabarwa prof babu inda ta rage shi hakan yasa ta rinƙa janyo surikar tata a jiki tana koya mata techniques ɗin har dai itama ta hau kan karatun dan zee ba baya ba itama dan kuwa bata son sunan kishiya ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat daɗa dulmiya ta tsundum cikin rafin ƙwato ƴancin ta a wun mijin ta ta yadda babu ma inda zai juyi ya ji un ba zee ba toh kowace mace mujiya ce agare sa ta yi nasarar yin hakan dan a halin da ake ciki kam bayan kasancewar sa soldier baya d lokacin kan sa sosai toh mace ma in ba matar sa ba bashi da tabbacin cewa akwai wacce zai iya kallo ya kira da matar sa.... "Bilal zo ka raka ni gidan Ammin ku"cewar Hajiya Zeenat da ta ke ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.miƙewa yayi daga kan sofa da yake kwance kamar marar lafiya ya ce "Toh mu je umma"daga haka suka fito daga gidan since their houses is adjacent to each other sai basu wani yi doguwar tafiya ba suka iso gidan su Hajiya Madina.ko da suka shigan ba su ci karo da kowa ba a tsakar gidan saboda yanayin rayuwar da ta juyawa jama'ar gidan straight babu dogon juye juye suka shiga main apartment ɗin Hajiya Madina inda a nan ma bata sauya zani ba dan babu kowa a parlorn ce mai tayi ya jira ta ita kuma ta shiga cikin ɗakin Hajiya Madina da ke chan sama. Sallama tayi ta ji shiru ta kuma yi ta ji shiru sai ta tura ƙofar ta shiga bata gan ta ba ta kuma doka sallama still ba response sai ta ɗan jiraye ta na wasu lokutan bata ji motsin ta ba hakan ya sa ta nufi sashen ban ɗakin ta ɗan tura kaɗan aiko sai tayi arba da Hajiya Madina kwance ƙasar tiles ɗin banɗakin Kamar dai a sume da sauri ta ƙarasa ciki ta shiga kiran sunan ta tana jijjiga ta2 "Madina....Madina ki tashi me kija yiwa kan ki,Madina ya zaki yiwa ƴaƴan mu haka in baki da ƙarfin yi masu addu'ar samin lafiya wa zai masu Madina ki tashi dan girman Allah".. Abin duniya duk ya ishe ta ga damuwar ƴaƴan su ga Hajiya Madina da ke a sume bata yi tunanin yayuafa mata ruwa ba sai da ta ga da gaske dai ba farfaɗowar zata yi ba dai ta yi wuf ta ɗebo ruwa ta zo ta yayyafa mata,numfashi ta ja kafin daga bisani ta farfaɗo ta buɗe idanun ta sai kuka kamar me tana ta surutai "Ɗa na Zaid,Zeenat kin ga abin da suka wa ɗa na?kashe min shi suke son yi bai masu komai ba daga taimako sai su lahanta min shi?ba fah rigima ne dashi ba bai da hayaniya ai ke shaida ce,yanzu a ce mutum da ransa tsawon satin biyu bai san inda kan sa yake ba?yana duniyar amma gangar jikin sa ne kawai tare da mu zuciyar sa da rayuwar sa baki ɗaya basu tattare da gangar jikin sa?me suke son yi min?me suke nufi da ni?so suke su tona min asiri?ɗa na Zaid na mawuyacin hali Zeenat ya zan yi"?maganar ta gabaɗaya abin tausayi. Actually both of them are in state of heartache and serious uneasiness amma dole ɗaya ya rarrashi ɗaya juma the strongest ne zai iya ba ma weak ɗin ƙwarin gwiwa wanda Hajiya Zeenat ce ke da ragamar yin wannan ɗin dan haka riƙo Hajiya Madina ta yi suka fito zuwa bedroom ɗin ta suka zauna a nan ta shiga bata magana da hope ɗin inshaAllah Zaid will make it zai farfaɗo kuma zai koma kamar yadda yake da "I hope and pray for that"cewar Hajiya Madina tana share hawayen ta daga haka kiran Dr Muhammad Hajiya Zeenat ta yi dan sanin halin da ake ciki... A chan parlorn ƙasa kuwa zaman Bilal babu jimawa sai ga giftawar Bahajjatu har ta wuce sai ta dawo da baya ta ga eh apple ɗin ta ne sai ta dawo ta shigo falon tana takawa a hankali har ta iso gaf da shi ta kirawo sunan sa "Apple"!!a ɗan firgice ya ɗaho ya kalle ta sai ya sauke ajiyar zuciya yayin da ta zauna kujerar da ke kallon na sa tana son samin natsuwa dan ta lura tashin hankalin da yake ciki yana son fin na ta "Apple yaushe ka zo ban sani ba baka kira ni ba"ƙura mata ido yayi kafin ya ce "Umma ce ta ce in rako ta shine muka zo"shiru ne ya ratsa wurin har dai Bahajjatun ta gaji ta yi bursting abin da ke damin ta "Apple am ill sick of all this shortcomings,na gaji da enduring matsalolin nan,na gaji da wannan wahalar apple ban saba ba,har sai yaushe yaya Zaid da Bilkisu zasu farfaɗo?har yaushe zamu cigaba da zama cikin wannan wahalar da tashin hankalin?apple am sick and tired of all these problems gashi tun da abin nan ya faru Ammi bata fah cin abinci ɗazu da na kai mata sai na gan ta shiru nayi magana har na gaji but bata amsa min ba a haka zamu cigaba da zama apple"?da kuka ta kai ƙarshen maganar wanda ya sanya shi jin duk jikin shi yayi sanyi shi kan shi dan dai namiji ne if not for that tsaf da shima kukan zai yi dan only God knows what is in his mind game da revenge ɗin da zai ɗauka akan wanda ya aikata wannan aika aikar. Tashi yayi daga inda yake ya dawo kujerar da take ya kalle ta ya ce "Wipe them off apple ina raye ban ga me saka ki hawaye kai tsaye ba wipe them off"saka bayan hannun ta tayi ta shiga share hawayen saidai tana sharewa wasu na fitowa daga ƙarshe ma kasa zaman falon tayi sai ta miƙe ta yi hanyar ɗakin ta tana jin ran ta na suya dan abin sabo ne fil a ran ta bata jin zai kankaru har sai an bi an yi maganin wanda ya haddasa abin.. Shima barin gidan yayi ya koma gidan su sai ga Bilal na kuka kukan sosai ba na wasa ba dan abin na taɓa mai zuciya what coukd possibly prompt culprit ɗin yin abin da yayi?lajfin me suka mai da ya aikata masu wannan abin?ya ma suka haɗu da shi kuma me ya haɗa su har suka aikata mai hakan?all these questions have no satisfactory answers dan haka ya cigaba da kukan shi yana ƙudirin abubuwa daban daban game da lamarin.... ************** Da isar su motar asibitin ta kwashe su basu tsaya a ko ina ba sai asibitin inda aka shiga da su separate rooms shi aka yi da shi sashin emergency cerebral room ita kuma aka shigar da ita unconscious and lethargic room yayin da su Dr Maher suka tsaya a waje... Da fari dai an saka shi ne a wani incubator ne wanda zai taimaka yayi monitoring internal organs ɗin kama daga waɗanda suka sami hatsari da waɗanda suke facing trait an saka ne yayi monitoring ɗin sa na tsayin kwanaki huɗu zuwa biyar ta nan ɗin zai rinƙa receiving ƙananan treatments wanda ba zai taɓa lafiyar sa ba har dai a gano ainihin matsalar A nata gefen kuwa ko da suka gwada farfaɗo da ita ƙin farfaɗowa tayi dan haka ana tsammanin ta sami trauma da ya taɓa brain ɗin ta wanda yayi sanadiyar shigar ta temporal comma muddin ana so ta farfaɗo toh sai an yi vibrating ɗin ta sosai dan haka an saka ta under electrification machine yana jijjiga ta kaɗan kaɗan dan speed ɗin machine ɗin is as low as 35.3°c bai kai normal range speed ɗin ba bare a ƙara shi ta yadda zai jijjigata sosai.. Feedback aka ba su Dr Muhammad aka kuma sanar da su cewa as soon as 4 days ɗin suka cika kuma an sami abin da ake so toh za'a yi proceeding amma in akasin haka sai an kuma saka shi a wani machine ɗin dan yi mai differential test ita ma aka masu bayanin nata da haka suka rabu daga nan suka nufi intensive care room ɗin da aka saka shi sai dai ba'a shiga ta transparent glass door ɗin ake iya hango shi gashi nan dai a kwance jikin kamar mai isashiyar lafiya amma duk electrodes ne ke juya jinin jikin shi su ke taimaka mai,a halin nan kuka ne kawai iyayen basu yi ba suka mai addu'ar samin lafiya suka koma part ɗin baby doctor itama dai kwancen take da maƙalallun electrodes a kan ta gabaɗa wayoyin saka kuzari ne a jikin ta sai monitoring machine da ke reading state of wellness ɗin ta in yayi sama yayi kamar zai dawo ƙasa sai yayi pumping electric current wanda yake taimakawa wurin girgiza ta. Suna kallon first move ɗin suka juya baya dan ba wanda zai iya kallon mawuyacin halin da take ciki at least ita tana da chances of surviving kusan 89/90% akan shi da ke da 45/50% of surviving amma a zahiri condition ɗin ta ya fi na sa ɓaci shi complete comma yake ita temporary comma ta shiga kenan shi dama nashi condition ɗin is worsen already but ita duk ta fi wahalan.. Zama suka yi a kujerun da ke kallon ɗakin nata suna kallon ta time to time da zarar electrode ɗin zai bada electric current sai su sauke kan su ƙasa a haka a haka har Dr Muhammad ya ji ƙarar ƙiran matar sa ya ɗaga wayar tare da matsawa nesa da Dr Maher dan kar ya tayar mai da hankali "Hajiya ina Hajiya Madina"? itama matsawa tayi ta amsa mai da "Tana ciki me ya faru ya ake ciki yanzu prof"? Ɗan shiru yayi kafin ya warware mata komai ajiyar zuciya ta yi ta ce "Toh prof muma muna hamyar zuwa ko nan da 3 days ko kuma 4 days dan Hajiya Madina bata cikin hayyacin ta ɗazu da muka shigo ni da Bilal wallahi a sume na riske ta sai da na yayyafa mata ruwa kafin ta tashi ko da ta tashin ma da maganar Zaid ɗin ta farfaɗo prof ina tsoron kar wani abin Allah ya kiyaye ya faru ina ganin zai fi in tana ganin shi"! "Hajiya toh me kike ganin zai fi"?shuru tayi kafin ta ce "A ganina zuwan na mu shi ya fi but kafin nan kun sanar da Afzal kuwa"? "A'a ba'a gaya mai ba dan bamu san a yadda zai ɗauki maganar ba"! "Toh ku bari ni zan kira shi yanzu dan ya kwantarwa da Hajiya Madina rai in ba Zaid shi yana iya dawowa yayi ƙoƙarin da zai yi dan ta sami sauƙin raɗaɗin da take ji a ran ta" "Toh in kin ce hakan ba zan ja ba lemme get going sai mun yi magana gobe" "Toh sai anjima"ajiye wayar suka yi ta koma ciki ta cigaba da rarrashin ta har sai da ta ɗan sami sauƙi sannan ta sallame ta akan washegari zata dawo godiya sosai ta mata da kulawar ta gare ta daga ƙarahe suka ma ƴaƴan su addu'ar samin lafiya.. Da suka fito sai bata ga Bilal ɗin ba hakan ya tabbatar mata da cewa gida ya tafi sai ta wuce zuwa gidan da zuwan ta ɗakin Bilal ɗin ta fara shiga inda ta gan shi zaune a ƙasa hawaye duk sun bushe mai a kan fuskar sa yana scrolling pictures ɗin su shi da twinin sa ba hawayen da ke fitowa amma da gani ka san kukan zuci yake yi dan haka har ta tsaya a bakin ƙofar bai san ta zo ba har ta shigo ta dafa kafaɗar sa sai a nan ya juyo a firgice ya ce "Umma yaushe kika shigo"?yana yunƙurin ɓoye wayan bai san ta gama gani ba sai ta ɗan murmusa ta ce "Let it be my boy na gani just pour ot out"ta faɗa ta na mai kwanto da shi kan kafaɗar ta kamar jira yake ya shiga risgar kuka bata hana shi ba dan shi kaɗai ne solution ɗin halin da yake ciki haka ya sha kukan shi dan ya manta cewa shi namiji ne yayi mai isar sa tana petting bayan sa har yayi shiru ya shiga tambayar ta "Umma apple zata warke ai ko"?sai tausayin sa ya kama ta mutumin da kullum a cikin raha da fara'a yake amma yau guda ya zauna in ban da kuka babu abin da yake yi "Bilal zata warke zata dawo gare mu kamar ma bata taɓa yin rashin lafiyar ba abin da nake so da kai shine ka tafi ka yi alwala ka zo ka yi nafila ka yiwa ƴaruwar ka addu'ar samin lafiya dan a halin da take ciki addu'ar mu kaɗai take buƙata a yanzu ba kukan mu ba dan ba zai yi mata amfani ba humm"?alama ya mata da kai kafin ya miƙe ya nufi toilet duk bai da kuzari ya yo alwalar ya fito ta shimfiɗa mai sallaya ta fita a lokacin da ya tayar da iƙamar sallar. Bata tsaya ko ina ba sai part ɗin Lukman he is used to it already samin shi ta yi yana nafila dan haka ta ja mai ƙofar ta fita ta nufi sashen su a inda ta tabbatar zata sami privacy ta zauna ta yi dialing digits ɗin Afzal ringing uku huɗu ya ɗauka da fara'ar sa ya ce "Assalamu alaikum umma na"kamar ta yi kuka haka ta ji sai ta daure ta amsa mai da "Wa'alaikumul salam ɗan umma ya kuke ya canada"? "Umma lafiya ƙalau da fatan dai an dawo gida ko"? Yayi tambayar da teasing tune sai ta ce "Afzal ka mai da mu kakannin ku"yayi dariya ya ce "Toh ummq in banu yi da ku ba wa zamu yi da"? Sai ta ce "Babu Afzal yanzu dai kana ina"? sai ya ɗan yi jim kafin ya bata amsa da "Umma ina gida but inshaAllah ina son dawowa nan da sati guda saboda ina ji a jiki na kamar Ammi is missing me and we have not been in touch kusan a week +".. Jin haka sai jikin ta yayi sanyi dama tsakanin ɗa da mahaifi akwai strong bond da ke taimakawa wun sadarwar su wanda in ɗaya na da damuwa ɗaya zai ji a jikin sa especially uwa dan haka ta natsu ta warware mai komai sannan ta ɗora mai da dalilin kiran ta.. Iya ƙololuwar tashin hankali ya shiga bayan ya saurari abin da aka sanar da shi sai ya ce da ita "Umma ina hanya gobe inshaAllah su kuma Allah ya basu lafiya"! "Amin sai Allah ya kawo ka Afzal Allah ya kare ya tsare" "Amin umma sai da safe"!! Zama tayi tana ta tunanin yanayin rayuwa few weeks back sune a London cikin kwanciyar hankali basu da damuwa ko matsalar komai sai gashi kwatsam suna tsaka da jin daɗin su kaddara ta sauko masu da wannan tunanin ta daure tayi alwala ta yi sallah bata rintsa ba dan ta san tana buƙatar ibadan a wannam gaɓa sama da kwanciyar barcin.... A gidan babban yaya Jamil tun bayan tafiyar su kid sis ɗin sa da aminin sa ya dawo gidan hankalin shi ba a jikin shi ba duk dabarar da matar sa ta mai dan ganin ya sake ya bi su da addu'ar samin lafiya abin ya ci tura dan kamar ingiza shi take yi akan ya cigaba da saka damuwar a ran sa sai ta zuba mai ido kawai dan ita kanta tana cikin damuwar da tashin hankali wanda ita kaɗai ta san yadda ta ke ji. Bai bar ɗakin da ya rufe kan sa a ciki ba sai chan tsakiyar dare ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita kwance saman sallaya chan kan gadon ga baby Zarah tana barci sai ya ji ta bashi tausayi it takes a loyal,caring and kind wife to behave and act exactly the way she does dan haka ya lallaɓa ya ɗaga ta dama akwai nauyin bacci dan haka bata wani farka ba sai ma ta kuma lamo a hannun sa fita yayi da ita ya kai ta ɗakin sa ya kwantar da ita ya koma ya ɗauko baby Zarah ya kwantar da ita next to her momma shi kuma ya je yayi ablution ya zo ya tayar da sallah ya ɗau lokaci mai tsayi yana addu'a ma ƙanwar sa da aminin sa daga kan sallayar ya hauro ya kwanta shima suka saka baby Zarah a tsakiya ya ja masu comforter haɗe da kashe lamp ɗin ya tofe masu addu'ar bacci... ******************** Kimanin kwanaki uku aka ɗauka ana monitoring patients ɗin germany kafin doctor ɗin ya yanke hukuncin kai treatment ɗin zuwa second stage wanda a gefen baby doctor dole ta yi undergoing electro convulsive therapy ba ƙaramin rikita iyayen ta abin yayi ba dan a gida Nigeria sun gama shirin zuwa ciki har da Afzal da Bilal ƙin barin Bahajjatu aka yi dan in ta tafi tana iya creating scene a wurin nan kuma ƙasar turawa ne basu cika son hargitsatsen abu ba sai aka bar ta a gida,.. Suna airport labarin ya same su Hajiya Zeenat ji tayi kamar tayi kuka ne ko ta kurma ihu ne ko kuma ta zauna ne ta rinƙa rasbihi,shawarar ƙarshe shine ta yi tasbihi dan haka ta yi shiru ta shiga yin tasbihi har jirgin ya tashi dan bata sanar da Hajiya Madina abin da Dr Muhammad ya gaya mata ba sai ta bar wa kan ta. Shi kam abin ba'a cewa komai dan dai duk wasu analysis da diagnosis da likitocin suka yi basu sami gamsashiyar outcome ba sai ma kamar condition ɗin na daɗa yin gaba dan already akwai concealed blood da yayi bleeding tun daga ainihin main root ɗin sai abin ya zama somehow bulky har kan ya fara expanding dan jinin na ta regurgitating ba kama hannun yaro abin da ya rikita likitocin kenan suka ga ya kamata su yi mai gabaɗaya a wuce wurin wato dai brain surgery za'a mai dan haka nemo iyayen shi suka yi bature bai da ɓoye ɓoye straight to the main point ya masu bayani sannan ya sanar da su life rate percentage ɗin in aka yi surgery ɗin either 40/50 ko 50/50 ko mutuwa chances ɗin survival is low which happens to be as low as 30%.. Tashin hankalin da ba'a saka mai rana daga Dr Maher har Dr Muhammad sumumui suka fito in banda fargaba babu abin da ke ran su babu mai ce ma wani komai gashi likitan ya basu space ɗin yin decision har tsawon awa ɗaya da rabi kafin a san abin yi a hakan ne suka zauna shiru babu magana har suka cinye kusan rabin hour a haka a haka suka kuma shafe hour wanda ganin hakan ya sa doctor ɗin yayi reasoning da su ya ƙara masu awa ashirin da huɗu amma ya gaya masu cewa suna delaying survival ɗin ɗan su dan dama ita baby doctor a washegari za'a mata ECT ɗin shi kuma a ranar aka so yi mai sai dai they can't go ahead with the surgery without the permission of the patient relative which have to be his parents with their bold agreement and acceptance + signature da za'a yi stamping a yi forwarding to the board dan a saka a babbar file ɗin brain trauma clients da zasu yi undergoing brain surgery... Dan haka samin wannan damar suka koma lodge ɗin su gabaɗaya jikin su a sanyaye suke babu jimawa suka ji kiran su Hajiya Madina akan sun iso tare suka tafi ɗauko su a cab suka dawo lodge ɗin inda aka masu booking ɗayan ɗakin sai suka koma zaman su na ma'aurata wato kowa ya tare da mijin sa a two rooms ɗin,su kuma Bilal da Afzal next room ɗin suka zauna su biyu. Ordern abinci aka masu but kasa ci suka yi duk sun damu su ga ƴaƴan nasu sai dai a cikin situation ɗin da ake ciki ba su fatan matayen na su su ga tashin hankalin da yaean ke ciki da ƙyar da siɗin goshi suka yarda washegari zasu tafi asibitin amma fah babu kwanciyar hankali a tattare da su kowa na tsoron da fargabar abin da zai gani a goben... _2:50am_ Daidai lokacin da Dr Maher da Dr Muhammad suka fito daga ɗakunan su kenan dan samin mafitar abin da likitan ya sanar da su ƙarfin hali kawai suke yi ba dan sun shirya ba dan haka bayan doguwar nazari da hangen nesan da suka yi sun yi arriving a kan zasu yi signing ɗin a yi surgery ɗin su kuma su bisu da addu'a dan matuƙar babu addu'ar toh ko ma me za'a yi ba lallai bane su yi succeeding a surgery ɗin ba da haka suka koma suka cigaba da tunanin rayuwa... °°°°°°°°°°°°°°°°°° As early as 7am duk sun gama shirin zuwa asibitin dan haka cab ne ya sauke su suka ranƙaya zuwa ciki abu na farko da suka yi shine samin doctor ɗin suka amshi form ɗin kiran matayen nasu suka yi suka nuna masu form ɗin kasa ƙarasa karantawa suka yi sai kuka dan haka su mazan ne suka yi namijin ƙoƙarin saka hannu a papern aka yi submitting zaman jiran likitan suka yi ƙarshe dai ƴaƴan ne suka koma rarrashin iyayen su har zuwa lokacin da doctors ɗin suka iso aka masu bayani babu ɓata lokaci aka fara shirin yin surgery ɗin sai kuka Hajiya Zeenat da aminiyar ta ke yi basu tabbatar da cewa situation ɗin yayi worsening ba sai da aka fito da shi kamar gawa dan bambancin sa da gawa shine shi yana breathing in-out kaɗan kaɗan apart from that bai da maraba da gawar. Basu tsaya ɓata time ba aka shigar da shi iyayen na kuka kamar me daga nan aka shigar da baby doctor ɗaya ɗakin ECT ɗin wanda yake ɗauke da transparent doors and windows ta yadda duk abin da ake yi a ciki ana iya gani daga waje itama haka aka wuce da ita kamar marar rai sai suka mai da duban su gare ta har aka ƙarasa da ita ɗakin setting komai aka yi aka yi testing electrodes ɗin suna tsaye a wurin suka ga an fara dadanna machine ɗin daga haka suka fara witnessing babbar tashin hankalin da basu taɓa gani ba a rayuwar su. Bayan jona mata electrodes ɗin aka danna sai ya fara charging yana bada electical spark da ke shiga directly brain structure ɗin ta suke charging domin bada response ma incoming electrical transmission daga electrode ɗin hakannis equal to her bodily movement first spark ɗin da ya shige ta kawai sai ta shiga jijjiga kamar epileptic patient jijjigan yayi rhyming da saukar hawayen gabaɗayan su da ke kallon procedure ɗin a karo na biyu kuwa hannu Hajiya Zeenat ta saka a baki ta fashe da wani irin kukan ban tausayi sai Hajiya Madina ce ta rungume ta itama tana kukan Bilal kam kasa cigaba da kallon yayi ya matsa chan nesa da ɗakin ya shiga risgar kuka mai ƙarfi babu ƙaƙƙautawa .. Chan ana fama da surgery ɗin Zaid Maher nan ana faman stabilizing baby doctor,a karo na shida da aka ƙara spead ɗin electrode ɗin ne Hajiya Zeenat ta fasa wani ihu haɗe da zamewa ƙasa numfashin ta ya ɗauke cak kanta aka yo ana faman jijjiga ta wannan tashin hankalin koh a mafarkin su basu taɓa encountering da shi ba for crying out loud when will all these be over and done with Zaid is there battling with his life a surgery room mutumin da shi ke yi wa wasu yau shi ake yiwa,baby doctor na ciki ba'a san yadda hali zai yi ba anf now Hajiya Zeenat ruɗewa Dr Muhammad yayi sai da aka fitar da shi daga arena ɗin dan a samu a farkar da Hajiya Zeenat.................. Cikin hanzari Afzal ya ɗauko bottle water ya miƙawa Ammin sa ta yayyafawa Hajiya Zeenat numfashi ta ja kafin daga bisani ta yi ajiyar zuciya wanda ya tafi tare da kuka mai taɓa zuciya ɗagata Hajiya Madina tayi zuwa kan kujeran da ke nesa da ɗakin ECT ɗin ta yadda ba zata gansu ba,ita kanta mai rarrashin danne zuciyar ta take yi dan only a mother can understand the pains that Hajiya Zeenat is passing through.. Fitowa Dr Maher yayi ya tarar da Dr Muhammad yana ta zirga zirga duk hankalin sa baya tare da shi sai kai kawo yake yi dan haka Dr Maher ya dafa shi haɗe da ce mai "Prof"!! A rikice ya juyo ya zubawa aminin na sa ido ya kasa cewa komai dan haka Dr Maher ya ja shi gefe ya fara mai magana cikin faɗa "Habawa prof,yanzu kai abin da ka ke yi kana ganin ka kyauta?idan har kai a matsayin ka na namiji mai riƙe ragamar gidan sa ka kasa handling matsalolin nan then how did you expect others and the rest of your family members to understand this fate?chan ga Bilal yana ta kuka ga Hajiya ta sume and you,,you are here all confused..abin da nale so da kai shine ka kwantar da hankalin ka ƴaƴan mu zasu farfaɗo cikin yardar ubangiji mu cigaba da yi masu addu'a humm"?alama ya masa da kai alamun gamsuwa sai suka rungume juna.. Afzal kaɗai ya rage mai ƙarfin halin kwantar masu da hankali dan haka shi ke ji da Bila ya ji da iyayen sa mata ya kuma ƙarfafawa iyayen maza gwiwa not because he is nit feeling the intense pains sai dan shi kaɗai ke da ƙarfin zuciyar.. Ana haka wani doctor ya fito yana tambayar ina mahaifiyar client ɗin da ake wa ECT,ruɗewa sukawa suka miƙe gabaɗayan su cikin rikicewa duka suka ce "We are here"kallon su yayi dan ya ga yadda duk suka amsa wai sune mahaifiyar ta shi mutum ɗaya yake nema su kuma sun tashi dukan su sai kawai ya koma ciki kusan mintuna biyar ya fito ya ce "Where is apple"?sai a sannan suka gane ɓaranɓaramar da suka yi da fari toh amma ai ba laifin su bane sai suka juya dan kiran Bilal amma suka ga baya nan dan haka excuse Afzal ya ɗauka dan ya kirawo shi,fita yayi daga area ɗin ya tafi chan bayan building ɗin inda ya hango Bilal ɗin zaune duk yayi zuru zuru sai yayi saurin ƙarasawa ya kira sunan sa "Bilal"juyawa yayi suka haɗa ido sai yace da shi "Let's go in someone wants to see you"miƙewa yayi ya bishi kamar bai da lafiya har ciki suka shiga suka wuce mutanin wurin suka shiga cikin main ECT suit ɗin sai a sannan ya hankalin sa ya fara hasaso masa hala Allah ne ya karɓi addu'ar sa apple ɗin sa made it shiru yayi har suka ƙarasa shiga inda ya ga duka electrodes ɗin da aka jona mata an yi dismounting ɗin su ga ta a ɗaya couch ɗin an kwantar da ita saman wani resistable mattress an saka mata oxygen tent idanun ta lumshe kamar dai ta farfaɗo kamar kuma bata farfaɗon ba.. Instead ya jira command daga wun doctorn da ya kira shi ai ko Afzal ɗin da ya kirawo shi suka shigo bai bu ta kanshi ba ya fizge hannun sa ya nufi tent ɗin da take ciki tana numfashi a hankali. Sunan ta ya shiga kira a ruɗe as in is this really real "Apple.....Apple kin dawo mana.. Apple you arw back.. you are back to us"!!!buɗe lumsassun idanun ta tayi ta zuba mai for a while sai ta lumshe idanun kuma kafin ta kuma buɗewa ta kai hannu ta cire oxygen mask ɗin ta buɗe baki da nufin yin magana amma sai ta ji harshen ta ya mata nauyi dan haka sai ta yi shiru ta mai da mask ɗin ta lumshe ido,hakan ya sa twin bro ɗin nata fahimtar cewa magana take son yi ta kasa a hakan ma ya sami relief sai ya girgiza mata kai tare da ce mata "Is okey apple ya isa haka nan i understand you are now safe ki yi shiru kar ki ce komai yanzu zan kirawo likitan ya zo ya kuma duba ki dan bana son ki kuma yin bacci bana so kin ji"?buɗe ido tayi ta lumshe alamun ta ji har da ƴar murmushin ta dan maganar tasa ta bata dariya haka yake da barkwanci ko da kuwa gathering na son juyewa ya zama boring shi zai maida wun ya zama lively dan haka sai ta cigaba da bin shi da ido har ya fita sai ta kuma runtse idanun ta daga nan ta fara tunano abin da ya faru da su kafin yau ɗin yayin da ya fita dan kiran doctor dan wanda ke wurin ya daɗe da barin wurin dan ya ga tsananin kewan junan su and he thought that they needed privacy so he left there a course of tafiya kirawo doctor a hanyar su ta dawowa step uku ya rage su shiga suit ɗin kawai suka ji wani irin razanannen ihu wanda ba kowa bane yayi wannan ihu fave Bilkisu. Tun daga kan iyayen har zuwa ga ma'aikatan babu wanda bai razana da ihun da ta fasa ba except waɗanda suka yi performing procedure ɗin waɗanda a wurin su alama ce ta nasara dan memory ɗin ta is restored back again tsoron amnesia da ake yi ya kau saboda haka likitan na ganin tense grimace a fuskokin su ya ɗan yi murmushi kaifin ya ce da su "Worry not,it went well and everything is now completely successful,congratulations she fought quit good it's a miracle"!!kaiwa nan yayi tafiyar sa zuwa ciki su kuma suka rinƙa juya maganar sa da mamaki meye kuma na congratulations alhalin su sun ji ihun ɗiyar su,bature dai bauɗaɗɗen mutum ne shi bai masu doguwar gamsashiyar bayani ba ya tafi ya bar su da incomplete speech wa zai warware masu?babu dan haka suka biyo bayan su dan tare suka tafi da Bilal a daidai main door ɗin suka dakata suna hango abin da ke gudana a ciki.. Setting mata table aka yi aka shiga goge mata fuska dan ta haɗa zufa sosai daga nan suna iya ganin yadda take magana a uzurce sai dai su da ke wajen basu san me take faɗa ba sai dai ƴan cikin dan haka suka kuma natsuwa dan jin amsar da likitan zai zo masu da shi.. Chan cikin kuwa masifaffen tambayoyi take masu akan ina ne nan ina yake rasa inda maganar tata ta dosa suka yi dan haka suka juya suka kalli Bilal suka ce da shi "Apple did you have any idea about all these questions we can't understand any of her words"saboda da yaren hausa ta yi tambayar bature kuma babu ruwan shi da apple ɗin da suka ji ta kira shi da shi suka yi addressing ɗin sa,sai ya ce "Year i do can you please give me just 5 minutes of privacy"?girgiza kai suka yi suka ce "Yeah sure". Daga nan suka fita suka bar su su biyun,da fari son rikice mai tayi sai da yayi da gaske ya fanne ta a kan gadon yana fincikewa yana kuma danne ta dan kanta da ta gaji ta yi shiru dan har lokacin effect ɗin ECT ɗin bai bar ta ba lokaci lokaci yake fixgar ta dan haka da ya lafa sai ta natsu ta yi shiru shima shirun yayi yana haki kamar wanda yayi dambe iyakan ta kenan amma duk ta jigatar da shi sai da ya ga ta sami kan ta sai ya durƙuso ƙasa yana facing ɗin ta ta zuba mai ido shima ita yake kallo for a while sai ya kirawo sunan ta "Bilkisu"!zuba mai ido tayi tana kallon shi daga bisani sai ga hawaye na bin gefen kuncin ta,saka hannu yayi ya share mata ya kuma kiran ta "Bilkisu kina ji na"?girgiza mai kai tayi dan by then ta fara dawowa hayyacin ta ta san cewa ta bar wild forest ɗin nan for good since tana tare da ɗan uwan ta. "Bilkisu you are now safe and Alhamdulilah kin farka daga baccin nan da kike ta yi that upset us please apple don't sleep again i don't like it" Bata ce da shi ƙala ba sai ido amma maganar ta sa ya shige ta dan da alama ba'ar da ya mata ya saba yin ta sai ta lumshe ido ai a 360 ya ce "Nooooo...apple kar ku mana haka please open your eyes"duk sai ya rasa natsuwar sa dan haka sai ta buɗe idanun ta mai facial grimace ɗin wasa ta ke mai a nan ya sami relief ya dawo ya zauna kusa da ita "Apple let me inform them am coming"ya miƙe da nufin fita sai ya jiyo muryar ta tana ce mai "Where is ge"?dakatawa yayi ya kasa juyowa toh ko ya juyo me zai ce da ita?kawai sai ya ce ai yana surgery room?inaa he can't toh me zai ce da ita?sai ya juyo ya ce "Apple me kika ce"? Da ƙyar ta kuma furta mai "Where is he"?sai ya ce "Apple am coming let me call our parents they are waiting outside"..daga haka ya juya ya fita ba tare da ya bata chance ɗin kuma furta komai ba. Share hawayen sa yayi ya tunkari iyayen su da ke tsaye kamar an dasa su sun kasa furta komai dan tsoron jin me zai faru sakamakon ihun da ta tsala,da zuwan sa suka nufo shi suna rige rigen tambayar sa me ya faru,kasa cewa komai yayi sai ya nuna masu hanyar ɗakin a gurguje suka nufi ɗakin da zuwan su suka tsaya cak suna kallon ta kamar basu san ta ba itama ta maida kallon ta gare su kafin ta ɗan murmusa kaɗan hakan yasa suka ƙarasa ciki suna godiya ga Ubangiji da ya nuna masu wannan moment ɗin the cast the evil that intrude into their lives without invitation. "Baby..baby you are back you are back to life"cewar Hajiya Zeenat tare da rungume ta tana hawaye itama rungume tan ta yi tana jin wani iri duk wanda ya rasa uwa gaskiya yayi babban rashi. Ƙin sakin ta tayi ta cigaba da kukan farinciki tana fatan Allah ya sa kar ta kuma komawa baccin kuma daga haka Hajiya Madina ta zo ta gefen ta ta rungume ta tana mata barka da farfaɗowa iyaye mazan dai kallon su suke yi at least an sani sauƙin ɓangare ɗaya saura ɗayan dan haka fita suka yi dan tafiya jiran jin outcome ɗin surgery da ake yi. Afzal ma fita yayi dan they are making him emotional already Bilal kuwa yana nan zaune bai bar ɗakin ba yana ta kallon ta kamar an hallice ta ne kamar bai taɓa sanin ta ba. Tana da tambaya a ran ta about him where is he?what happened to him?how did they get here?duk a ran ta tambauoyin su ke but sai ta kasa furtawa dan haka ta bar shi ma kanta akan in sun basu space sai ta tambayi ɗan uwan ta.ana haka Hajiya Zeenat ta tambaye ta "Baby akawo maki abinci ne"?shiru ta yi kafin ta amsa da "Eh" da ƙyar ma muryar ke fitowa dan haka miƙewa suka yi su biyun cukun hanzari suka bar ɗakin hakan ya bata damar kiran ɗan uwan nata da ido cikin sauri ya karasa gare ta ya ce "Apple what did you need tell me please"ita tausayi ma yake bata she can tell tun da ta buɗe udanun ta shi ne first person da ta gani yake cikin tashin hankali dan haka ta kai hannu ta riƙe shi dan ya zauna saurin zaman yayi sai ta yunƙura kamar zata tashi wani intense pains ta ji a lumbar region ɗin ta wanda haka ya saka ta sake ɗan ƙara "Auchh auchh"!! Saurin maida ta yayi yana ce mata "Sorry apple sorry kwanta baki gama farfaɗowa ba"gyara mata kwanciyar yayi kafin ya tambaye ta "Menene?tell me please"!!ya zuba mata idanu sai ta haɗa duk wani strength ɗin ta ta furta "Ina Zaid?ya dawo?yana ina"?tambayar kamar dirar dalma haka ya ji ta shi all hus thought ta manta da tambayar seeing their parents dan haka ya ce "Apple ki ji da kanki mana baki da lafiya"!!shiru yayi ta san shi sarai something is fishy dan bai saba ɓoye mata abu ba musamman in ita ta yi tambayar sai gashi a yau yana sauke kan sa ƙasa yana gudun haɗa ido da ita toh me yake nufi?basu bar dajin nan tare ba?ko kuma an....bata bari zuciyar ta ta ƙarasa hasaso mata abin da ke yawo a brain ɗin ta ba ta kallo shi tana mai zazzaro idanu "Don't tell me Bilal"ya gano ta sai ya yi saurin girgiza mata kai ya ce "No noo apple is not what you are thinking no is not"ɗan lumshe ido tayi kafin ta buɗe ta kalle shi Oh gosh why is apple too complicated yana tsammanin zai iya kaucewa tambayoyin ta but she is still on it ya zai yi da ita?kafin ya sami mafita iyayen su suka shigo godiya yayi wa Allah da ya kawo iyayen su a wannan time ɗin dan haka yayi hanzarin fita sai dai bai yi nasarar fitan ba dan kuwa sunan sa ta kira "Bilal baka amsa min ba"!! Dafe goshin sa yayi yana nanata addu'ar *Allahumma ajirni fi musibati* .juyowa yayi ya zuba mata ido dama abincin za'a yi serving ɗin ta sai aka dakata kallo ya koma kan ta ana tunanin amsar menene ba'a bata ba. "Apple he is fine just eat something you have been sleeping for 2 weeks + now ki ci abinci humm"?kasa cewa komai tayi sai ga hawaye na fitowa da ƙwayar idanun ta babu komai a cikin idanun nan in ban da damuwa sai ta bawa ɗanuwan nata tausayi dan haka ya fasa fitar ya dawo ya zauna a nan Hajiya Madina ke tambayar sa "Bilal halan wa take tambaya"?shaf hankalin su bai kai kan cewa Zaid take tambaya ba sai ya yi lowering muryar sa ya ce "Ammi yaya Zaid take tambaya ban san me zan ce da ita ba please help me out"shiru ne ya ratsa ɗakin kafin daga bisani Hajiya Madina ta ce da su "Ku ɗan bamu wuri dan in tana ganin ba dole bane ta yi accepting abin da zan sanar da ita ba"!tashi suka yi jikin su a sanyaye auka fito Hajiya Zeenat sai hawaye take ta faman gogewa yayin da Bilal ya rungumo ta ya shiga rarrashin ta dan shima ya kusa fara kukan,doctors ɗin da suke jiran sa ne suka tate sa suna tambayar sa ko ya gama abin da yake yi a ciki dan suna son ɗaura ta a kan monitoring machine da zai na kula da sleeping pattern ɗin ta saboda gudun kar somnambulism(sleep walk,idan mutum na barci sai ya rinƙa tafiya a gigin barcin fiye da ƙima)ya dame ta. Shi da aka yiwa tambayar kasa bada amsa yayi kawai sai ya girgiza masa kai a nan likitan ya wuce su kuma suka nufi hanyar surgical room.. Maganganu sosai da nasihohi Hajiya Madina ta rinƙa yi wa baby doctor a ƙarshe ta sanar da ita komai sai ga Bilkisu ta shiga shock dan hawayen da Hajiya Madina ke tunanin zata gani daga idanun ta sai bata gani ba ta ga ta yi shiru hakan razana ta yayi har zata fara jijjiga ta sai ga shigowar likitan yana tambayar su me ya same ta "Doctor i don't know...she just transform right now please do something"ta faɗa tana kuka dan ta razana.matsowa doctorn yayi yana mai fiddo heart stethoscope ɗin da ke sagale a wuyar sa ya shiga gwada ta yayin da Hajiya Madina ke ta faman bin sa da idanu dan a dame ta ke sai ya ɗago yace "She needs rest you can excuse her"daga haka ya yi setting mini machine ɗin a hannun ta kamar wrist watch ya bada Hajiya Madina damar fita,kamar zombie ta fitan tana tsoron kar ta kuma kwanciyar baccin da suke tsoro dan a yanzu in akwai abin da suke tsoro shine baccin nan. ************* While the surgery was going on sau biyu Dr Zaid Maher na farkawa dan kuwa local anaesthesia da aka mai bai wani yi tasiri a jikin sa ba kamar su mai general anaesthesia sai dai ɗaya daga cikin surgeon ɗin ya dakatar da su akan what if he reacts to the anaesthetic injection dan haka suka kuma banka mai local anaesthesia ɗin da haka suka samu suka fara surgery ɗin.. Concealed blood da ke cikin internal organs ɗin sa ne suka fara regurgitating kamar an buɗe ɓataccen famfo abin ya ɗan razana su dan haka rage gudun jinin da aka saka mai suka yi dan muddin yana bleeding haka kuma jinin na kan regurgitating haka toh ba amfani dan jinin da ke shiga ne ke fita ta root ɗin sai aka yi regulating at the same time aka yi setting lactate ringers drip dalilin saka drip ɗin kuwa shine yana rasa ɗan ƙarfin da suke samu suna surgery ɗin da shi wanda is of a great help to them ga shi pulse ɗin sa na son diminishing dan ya fara jacking kamar wanda zai tafi. Komai cikin sauri ake yin sa dan any little delay is definitely gonna be dangerous suna yi suna duba time dan amwai exact time ɗin da aka ɗibarwa surgery ɗin in har time ɗin yayi exceeding toh tabbas zasu rasa sa. Hanzari hanzari ake komai,har dai aka gama exposing brain ɗin nasa aka fara tsotse jinin da ke fitowa saboda ya taimaka masu wurun gano ainihin root ɗin da jinin ke bulbulowa. Thank goodness sun gano deep injuring ya sami jijiyar da ke transporting jinin jikin mutum daga brain zuwa sauran part of the body wanda medically ake kiran transportation ɗin jinin da circle of Willis(duk wasu gudanarwar jini a jikin ɗan adam dole ta wannan circle ɗin zai bi kafin ya bayar da jinin a jikin ɗan adam).. "Shiittttt"cewar main surgeon ɗin da ke ƙara spead a procedure ɗin "Anything wrong doc"?tambayar da ɗaya daga cikin surgeons ɗin ya mai kenan sai ya ce "More towel is freaking getting out of control"cikin sauri aka miƙo mai disposable white towel ɗin ya yi amfani da shi ya yi blocking wurin da pressure kafin ya cigaba da aikin. Babu wanda ya natsu a cikin surgeons ɗin dan abin na son fin ƙarfin tunanin su a process ɗin suka gano cewa babu yadda za'a yi yayi recovering completely sai ta hanya ɗaya which they fear it might cause another problem a kan na shi dan haka sun gama concluding yadda zasu yi suturing plan B suka yi amfani da shi suka shiga yin surgery ɗin zanga zanga babu time komai a hanzarce ake yin sa sai da suka kusa cinye time ɗin kafin su yi saurin suturing daga internal organs zuwa nearby structures that were affected har suka fito waje suka ɗinke da kyayu ba tare da sun bar wani leaking space ba. Kimanin awowi 4 ¼ suka ɗauka suna aikin kafin su kammala da suka gama sun yi placing mai wani device ƙarama da zai taimaka mashi wurin jin magana a low tune dan bugun da aka mai ya taɓa hearing ability ɗin sa ta yadda in ba device ɗin aka saka masa ba yana iya experiencing serious crack noises da zai janyo mai bleeding daga kunnuwan sa biyu dan haka suka yi placing abin da tunanin sanar da iyayen client ɗin dalilin saka mai device ɗin dan extra care da cautions da za a na bi to preventing misplacement of the device. Wuraren 12:45pm suka yi wheeling ɗin sa zuwa private room aka yi setting mai drip duk wasu abubuwan lura da shi aka gyara sai da suka tabbatar da cewa sun yi making ɗin sa comfortable sannan suka fita suka bar sa dan ya sami hutun da ƙwaƙwalwar sa ke buƙata. A office aka nemi client relatives dan yi masu bayanin abin da ya faru da kuma wanda zai farun,ba iyayen sa kaɗai suka shiga ba har da su Hajiya Zeenat da prof suka biyo bayan su suka shiga cikin offishin inda likitan ya basu wun zama duk suka zazzauna suna jiran jin bayanin sa ko zasu sami kwanciyar hankali. Da fari dai ya sanar da su surgery went successful sai suka sami relief da ya ga haka sai ya sanar da su matsalar "Firstly a device was mounted at the ear hole to prevent unnecessary noises that might affect the hearing ability of the patient,it will reduce the sharp volume that will penetrate into the ears directly because if it penetrate directly it may lead to bleeding a profuse bleeding that may be too bad because it can lead to death so you have to be very careful and conscious of that device.again the patient has to be under the care of a machine that will help to regulate the movements of the patient because immediately the patient regain consciousness he may tends to wake up with all forces doing so might lead to neurasthenia which is lost of glucose that will cause fatigue,headache, irritability and lassitude this is will finally lead to exhaustion that will end in collapsing the patient which we don't pray for.."daga nan ya ɗan tsagaita dan yana jimamin sanar da su last two final resolutions ɗin but he have to dan su ne iyayen patient ɗin and so they need to know everything ya ɗago ya kae su ya ga suma shi suke kallo sai ya daure ya cigaba "Lastly...the patient will not regain consciousness right away..the patient might be unconscious for a period of 3-4months with positive effects"... Zazzaro idanu suka yi suna kallon sa 3-4months kuma kenan farfaɗowar sa ba yanzu ba kenan?inalillahi wainnailairir raji'un wannan masifa da me tayi kama.seeing their tensed faces sai ya kasa sanar da su masifar da ke gaba muddin patient ɗin ya farfaɗo sai ya bar su akan in suka farfaɗo daga halin da suka shiga sai ya sanar da su final outcome ɗin wanda ya san ba zai masu daɗi ba but dole su karba a haka. "Is okey is a very visible reaction it occurs it happens it's actually normal and you need not worry about the months because we operated directly in the brain and for the brain to heal up completely it need a gradual healing process for it to be able to transform back to it normal functioning state and so i urge you to help the patient in it's recovering process"..su dai kallon shi suke ta yi bai sanar da su amsar ƙarshen ba dan ko ya faɗa ba zai sami attention ɗin su ba dan basu hayyacin su sai ya ce da su "I guess that's all for now you may see the patient in the next 4 hours". Godiya iyaye mazan suka masa dan matan kasa cewa komai suka yi sai hawayen da ya ciko masu idanu dan haka ɗaga su suka yi suka fito ko hanyar ɗakin basu bi ba suka wuce zuwa masaukin su a inda sai a lokacin suka sharɓi kukan su sosai a nan suka tuno ma da source of all this problems dan haka Hajiya Zeenat ta fara haukacewa prof akan ita fah ba zata yarda ba sai an koma Nigeria an san yadda za'a yi da ɗan iskan yaron da ya janyo ma ƴaƴan su wannan fitinar ita ba yafewa zata yi ba an ɗauko hanyar halaka masu ƴaƴa daga taimako shi dai rarrashin ta yale yi dan a cewar sa ɗaukar fansa duk bata taso ba ta ƙara haƙuri har su sami kan ƴaƴan su.mai hali baya dainawa dan haka sai da ta gwada mai iko dan kuwa balbale shi tayi wai dan ba shi ya ɗau cikin ƴaƴan ba bai san azaban da suka ji a lokacin da suke ɗauke da cikin ƴaƴan ba shi yasa zata ce a kamo masu ɗan iskan yaro ya ce a'a,in banda haƙuri babu abin da yake ta bata dan ya san ya takalo kenan maybe ma ta daina sauraron sa har sai yaran sun farfaɗo dan haka ya je ya haɗa mata warm water dan tayi wanka banza ta mai ta ce ba'a yi shi kam dariya abin ya basa dan tun da abin ya faru bata sami natsuwar ta ba sai yau kuma madaɗin ta ɗan samar ma zuciyar ta hutu da sukuni tunda sun ji outcome na komai sai kuma ta ɓige da wani rigimar su kam Allah ya basu mata. A chan apartment ɗin su Dr Maher kuwa rasa abin faɗa Hajiya Madina tayi game da abin iya magana Dr Maher yayi amma bata bashi amsa ba ƙarshe ma da ya ishe ta sai ta ce "Dr"ya amsa mata da "Na'am Hajiya".. "So nake ka sa a kamo min yaron nan"ya ɗan yi shiru na wasu lokutan kafin ya ce "Hajiya wani yaro kuma"a ɗan fusace ta ce "Dr yaron nan yaron ƙauyen nan da ya lahanta mana yara yaron nan da ke son ya kashe mana yaro shi nake son a kawo min shi in gan shi da idanuna dan in tantance ko ya kai matsayin laying hannayen sa aka ɗa na ina son sanin ko he is worthy enough to cause this calamity to my boy did you understand me"!??ta ƙarasa a tsawace bursting into tears of pains sai ya rungume ta yana jijjiga ta shi kansa yana son a hukunta yaron but for now lafiyar yaran su shine major priority ɗin su.. Afzal da ke da niyar shigowa dan sanar da su cewan shi zai koma Nigeria ya turo Hakim dan akwai ayyuka da dama da suke asibitocin iyayen nasu wanda ba mai iya kula da su because Dr Aslam baya nan Kuma jigajigan doctors ɗin duka na nan suna jinyar doctors biyu,jin abin da suke faɗa ya sa ya fasa shigan sai kawai yayi waya da Bilal da ke asibitin ya ce da shi ya cigaba da kula da iyayen su da patients ɗin ya mai bayanin komai,ya mai fatan alheri dan a ranar yake son komawa tsoron sa ɗaya idan Hakim ya zo ya ga yanayin su tun ma na yayan shi it will be hard in bai ɗau law a hannun sa ba dan yaron na da mugun zuciyar tsiya da basu san inda ya ɗauko shi ba shi da Bahajjatu.. A ranar ya bar ƙasar germany ya dawo ƙasar Nigeria shi Hakim ɗin ya zo ya ɗauke sa ya tambaye sa abin da ke faruwa shiru ya mai sai da ya dame sa akan ya mai bayani dan ya matsu ya san halin da suke ciki da fari ya gaya mai yanda likita ya gayawa iyayen su akan surgery was successful har ya fara samin natsuwa kafin daga baya dai ya daure ya sanar da shi gaskiyar maganar yana jan motar ne ya ja wata irin wawan burki da yayi sanadiyar tsorata yayan nasa Afzal da ke zaune a gefen sa dan har mai achaɓa da yazo wuce su sai da achaɓar ta ƙwace masa shi kuma ya juyo a firgice ya cire glasses ɗin idon sa ya zuba yayan nasa idanun sa da suka rikiɗe zuwa wani kalar shi ja shi ba ja ba babu abin da Afzal ke iya hangowa in banda masifa da bala'in da ke yawo a idanun ɗan uwan nasa.. Tabɗijam akwai sauran rina akaba Hakim hmm.................... Tun kafin ya furta wani abin Afzal yayi saurin dakatar da shi ta hanyar riƙe mai hannun sa ya ce "Hakim calm down calm down please"amma bai ko tsaya sauraron sa ba dan ya gama zuciya a wani irin tune mai nuna tsantsar ɓacin rai da fushi ya wani ynƙuro ya damƙo kwalar long sleeve da ke jikin Afzal ɗin ya fara maganganu "What are you saying..tell me what are you saying?huh?my brother?my brother is unconscious?kana son sanar da ni cewa yaya Zaid na chan bai san inda kan sa yake ba har yanzu?aren't you a doctor?can't you make him recover quickly?did you need money?name your price zan biya ka kawai ka farkar min da ɗanuwa na if not..if not Dr Afzal i will sue you..i will sue you..ya ɗan dakata na second ɗaya ya cigaba,,who was that bastard?who is he?who are his parents?huhh?waye iyayen sa a duniyar nan baki ɗaya?wa ya bashi izinin saka filthy hands ɗin sa a jikin yaya na?tell me am asking you"? Ya ida yana mai fitar da hawaye a nan ne idanun sa suka rine ainihin rinewa na kalar ja..+ Riƙe hannun nasa Afzal yayi da niyar sauke su daga wuyan sa sai dai bai saki ba instead ya kuma damƙewa da kyau a zuciye ya ce "Ina tambayar ka wanene banzan da ya taɓa min ɗanuwa na"a ɗan zafafe Afzal ya mayar mai da martani shima "Who knows kid brother!i don't know kar fah ka manta nima yaya Zaid ɗanuwa na ne na jini we all share the same bloodline a jikin mu why don't you understand anything in ka yi fushi ne wai?baka ganin halin da yake ciki ne?addu'ar mu kaɗai yake buƙata ba revenge ba ko ɗaukar law a hannun mu ba did you get it"?saurin katse shi yayi ya ce "No!no Dr Afzal i don't get you"!!a yanayin da yayi maganar one can tell that a sigar da ake kira da gatse yayi maganar shi Afzal ya san da hakan sai kawai ya rikice mai shima ya shiga balbale sa "Come back to your senses Hakim,iyayen na chan basu da kwanciyar hankali,yaya Zaid da baby doctor na kwance bamu dan lokacin da zasu farfaɗo completely ba baka jin tausayin su ne?baka ganin yanzu ba lokacin ɗaukar fansa bane?baka ganin zai fi ma kowa armashi in aka yi reporting case ɗin to authority kuma by then victims ɗin sun farfaɗo?a tunanin ka ni ban damu ba e?a jin ka cikin walwala nake na ganin ɗanuwa na cikin wannan wahalar?gani kake kai kaɗai ka fi kowa son sa a duniyar nan?ce maka aka yi Bahajjatu bata da zuciyar da zata iya kisan kai ne?amma bata yi ba dan ita kanta jiran farfaɗowar yaya Zaid take yi saboda she believes in da hankalin sa komai zai zo da sauƙi wurin kamo wanda yayi wannan abin..i never intended telling you this but saboda gudun kar ka tafi ka ga halin da yake ciki ka dawo ka yi blaming mutani da dama ko ka yi creating scene a wurin nan shi yasa na sanar da kai but just look at you look at your self Hakim duk ka bi ka haukace min har kake min iƙirarin in kuɗi nake so in yi naming price ɗin are you insane?have you forgotten that i am your elder brother?da ina da remedy na matsalolin nan kana ganin ba zan yi maganin sa tun kafin ya kawo nan ba?for God sake Hakim ka bani haɗin kai please am the only one doing all these hustle i myself am tired am fed up already i can't handle and control it all alone i thought i have someone that will understand me but i was wrong babu wanda ya shirya fahimta ta ciki har da kai Hakim why"?kamar zai yi kuka yayi maganar sai jikin Hakim yayi sanyi bai san ya furtawa yayan nasa waɗannan zafaffan kalamai ba dan in har ran shi ya ɓaci babu abin da bai furtawa sai daga baya ya zo yana regretting wasu kalamai... Rungume sa yayi ya shiga rera mai kuka yana faɗin "Please forgive me brother,ka yafe min i failed to understand you feelings i was thinking cewa yaya Zaid yaya na ne ni kaɗai na manta he have a mother a father a sister and brothers even loved ones out there ka yafe min ɗanuwa na ka gafarce ni"hugging ɗin sa back yayi yana rarrashin sa dan shima ji yake kamar yayi kukan dan da halin da ɗanuwan sa ke ciki gwara a ce cikin hayyacin sa yake kullum ana masa allurar kashe zafi har ya farfaɗo gabaɗaya but bai da ikon yin komai dan babu komai da ke hannun sa he can't do anything absolutely nothing especially when it comes to his family affairs he is weak baya iya executing komai game da treatment sai dai ya sa a masu toh dama Zaid ne ke da wannan taurin zuciyar na treating family ɗin sa dan shi baya iyawa gashi Zaid ɗin na kwance banbancin sa da gawa dai shine numfashin da yake fitarwa.. Kuka Hakim ya zage yayi wanda ya yanke hukunci saidai ya barwa zuciyar sa dan inshaAllah ya yi niya kuma baya jin zai iya haƙura dan ba halin sa bane ƙin cika abin da yayi niya sai dai in Ammi ce ta gano ta hana sa amma ko mahaifin sa baya iya mai bare yayyen sa wannan hali na sa da Bahajjatu ya sa Dr Maher nesanta sa da yara abokan wasan sa tun yana yaro da ya girma kuma ya yi ƙoƙarin nesanta sa da abokai dan gudun kar ya ɗauko masu abin yaɗawa a duniya saboda ba dan shi ya haifi Hakim ba kuma shi ya yi conducting delivery ɗin ba tsab yana iya cewa chanza mai ɗa aka yi toh sai abin ya zo mai da sauƙi same attitude da yake yi shi Bahajjatu ke yi su biyun su suka fita zakka a gidan dan ba'a san inda suka kwaso muguwar zuciyar da ke taso masu ba time to time dan Hajiya Madina dai bata da zuciya iyakan zuciyar ta shine tsakanin ta da Dr Maher kuma nasu ne na ma'aurata wanda ya zama very visible kowa ya sani shima Dr Maher ɗin bai da zuciya hasalima bai da damuwa he is gentile wanda ɗan sa Dr Zaid kaɗai ya biyo sa a komai except kamannin da ya ɗauko na mahaufiyar sa dan ko Afzal ma a juye yake wasu lokutan normal wasu lokutan subnormal wasu lokutan abnormal gane mai sai su ƴanuwan sa amma bare sai ya iya cewa ko jinnu ne da shi masu juya shi but in aka haɗa su da Hakim sai a ɗauke sa a bar Hakim though Hakim appear to be simple and quite amma ba hakan yake ba dan abu kaɗan zai harzuƙa shi while Afzal happen to be someone with mood swing shi kan sa ya sani shi yasa baya misbehaving a wuri kuma da zarar ya ga wannan mood swing ɗin zai fara mai sai yayi isolating kan sa dan baya son affecting mutanin kusa da shi unlike Hakim da bai da control of his emotions and anger he break it out bai iya ɓoyewa... "Can we go home now"cewar Afzal "Sure brother"ya bashi amsa daga nan suka cigaba da tafiya har suka iso gidan buɗe ƙofofin motar suka yi suka fito Afzal ne ya fara shiga ciki kafin Hakim ya biyo sa sam fuskar sa babu walwala ko kaɗan dan haka ma masu aikin gidan sun lura suka kama kan su amma still sai da mai girkin ta fuskanci masifar sa dan bata gama arranging abinci a kan dinning ba.. Jiki na ɓari ta rinƙa bashi haƙuri dan ba kasafai ya ke samin saɓani da ita ba bai ma cika shiga sabgogin su ba ya fi yi da masu tsaftace gidan.yau ganin tambotsan sun motsa ta mai uziri Afzal have to calm him kafin yayi shiru "But brother kana fah gani bata gama shirya maka abinci ba kusan an hour aikin me take yi in fact ta tafi she is fired bata da amfani"tarar numfashin sa Afzal yayi ya ce "Common Hakim ina mun gama da maganar nan tun a hanya?ban ce magana ya wuce ba?why must you start the unnecessary blame?kana ganin hakan shine mafita a gare ka?in har ba ka fara controlling fushin ka ba Hakim i fear you won't get a wife trust me"ya juya ya fara hawa kan benen sai ya dakata ya juyo ya ce da shi "And apologize to her she is old enough to be your grand momma humm"?girgiza mai kai yayi bayan ya gama haurawa ya juya ya ba ma matar haƙuri dan kam in bata yi sa'ar granny ɗin sa ba toh zata girmi dad ɗin sa not even his Ammi shima ya san bai kyauta ba zuciyar taaa ce sai a hankali.. Haurawa saman yayi bai tsaya ko ina ba sai ɗakin Bahajjatu da ke zaune tana amsar reports akan boutiques ɗin ta,abunuwan da ake buƙata ake sanar da ita akan an yi placing order sai dai sakamakon bata nan ya sa wasu suka fara zuwa dan withdrawing order ɗin sai dai an basu haƙurin nan da sati ɗaya komai zai daidaita,abin haushi kamar ta janyo kelita da ke mayar mata da zancen ta tablet ta gaggaura mata mari take ji sai dai ba hali technology bai kai nan ba sai ta shiga masife ta "When?when did i hired you to start selling me?when did i ask you to beg some stupid useless costumers for me?when did i agree to pay you for that?huh"?kamar zaki haka ta koma kelita kam ta ga tashin hankali da bata taɓa gani ba dama ma'am na da fushi haka but bata taɓa demonstrating ba tabb ita kam me ya kai ta gaya mata gaskiyar lamarin da ma ƙarya ta mata ko ma juya zancen msybe da bata sha faɗar har haka ba,tana tsaka da tunanin ta ta ji abin da ya girgiza ta "You know what?just go you are fired because i hate working with cheap creatures".. Wani irin ihu kelita ta yi ta tablet ɗin ta fara surutai "Jesus christ madam please spare me don't do this to me i curse the devil that want to see me in hell i reject it madam i beg you in the name of Allah almighty don't send me away because i have no where to go"hanzarin katse ta Bahajjatu ta yi cikin takaicin sunan Allah da ta kira a gurɓace ta ce "Go to hell go there i guess your parents are there waiting for you right?go and meet them right away for calling my creator name with no respect i will have to sue you to court annoying thing get lost and make sure you evacuate that office before i return mtsw"bouncing ɗin ta tayi ta kashe tablet ɗin ta yi wurgi da shi sai a hannun Hakim dan ya ɗab jima yana sauraron conversation ɗin su a zuciye ya zo but ganin itama ta zuciyan sai ya ɗan sassauta na sa fushin ya ƙaraso ciki yana son sanin ainihin matsalar ta. Bata san ya shigo ba sai da ya kira sunan ta "Baha"!!a firgice ta juyo ta ce "Na'am waye"? Ɗan murmushi yayi saboda tsabagen masifa wai da duka hasken da ke haska ɗakin amma bata iya ganin sa har sai ta tambayi ko wanene.. Zama yayi a saman couch da ke gefe kaɗan da gadon ta yayi crossing ƙafar sa ya miƙa mata tab ɗin haɗe da cewa "Me aka maki kike ta masifa bayan kin san na hana ki yawan saurin zuciyar nan"!sai a nan ta gane ko wanene sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Yaya Hakim can you imagine"??sai ya tsaya kallon ta ya ce "Menene"?tsaƙi mai sauti ta yi ta miƙe tsaye cikin jin haushi ta ce "Wai wannan banzar yarinyar mai fuskar shanu wai ita kelita ta je tana roƙan clients ɗi na akan sun ce sun janye order da suka yi placing dan ban kawo masu akan lokaci ba?ta je tana siyar min da dignity a wun waɗancan banzayen ƴan uwan ta masu fuskar shanaye?ni saka ta nayi?ko aikar ta na yi?hala gani take biyan ta na yi na ɗauko ta dan ta rinƙa min iskanci da sunan customer care service provider,my brother is unwell and yet those animals think that i have time for their useless order i have to deal with her dan ta ma gama raina ni firing her won't satisfy me huuuh"!!ta furzar da iska daga bakin ta wanda alama ce ta abin ya ƙuntata mata dan haka miƙa mata bottle water yayi wanda ya tsiyaya mata a glass tumbler ya san ƙanwar ta sa ya san matsalar ta,matsalar yayan ta ne da na aminiyar ta ya sa duk kowa take sauke mai fushin ta kuma shi bai ga laifin ta ba dan is normal a wurin sa Amsar tumbler ɗin ta yi ta ƙwalƙwali ruwan sannan ta ajiye ta koma ta zauna ta na sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi race ɗin 50km,bin ta yayi ya zauna ya ɗan bata time dan ta dawo full senses nata,ta ɗau lokaci kafin ta dawo hayyacin ta sai ta ce da shi "Ina yaya Afzal ɗin"??kallon ta yayi yana jimamin sanar da ita abin da aka sanar da shi shima sai ya ce "Yana ɗakin sa yana freshen up"sai ta girgiza kai ta gyara zama ta ce "And them??are they alright"??tayi tambayar ne cikin tsoro shima ya sani sai ya amsa mata da "Yeah suna cikin ƙoshin lafiya"bata yarda ba dan babu wanda zai gwada mata halin sa sai ta ce "No yaya Hakim ban yarda ba ban yarda ba,ba kuma zan taɓa yarda ba tell me me yaya Afzal ya sanar da kai akan su"?she is out of her conscious mindset already sai yayi amfani da hakan yayi narrating exactly abin da Afzal ya gaya mai dan ya san ta nan kaɗai zai sami abin da yake so.. She was mad she was insane dan maganganu kala kala ta shiga yi wanda a nan yayi nasarar ingiza ta har ta amince da buƙatar da ya zo mata da shi ita kaɗai ce zata amince da wannan buƙata ta shi amma ba Afzal ba. "Thank you baby sis kin gama min komai da kika amshu buƙatata no more cry no more worries from now henceforth hum"?amsa mai tayi da kai tana share hawayen ta ce mata yayi ta tashi au tafi dinning dan cin dinner,she wasn't hungry but saboda yayyen ta sai ta ji kamar ta ɗan sami appetite na cin abincin. Bin bayan sa t yi suna saukowa suna magana ƙasa ƙasa a nan ya ce da ita ta ma kelita haƙuri ta mayar da ita bakin aikin ta dan yarinyar na mata ƙoƙari sosai jin sa kawai ta yi dan kamar ydda yake da kafiya akan abu haka itama ke da kafiya as far as she is concern kelita is fired and that stay final in ba dan ma shi da yake yayan ta ba ne kuma ta san halin sa ba da sai ta ce hala neman kelitan yake yi da ya nace da batun a mai da ta bakin aikin ta,da haka suka ƙaraso dinning table inda suka yi zaman 5minutes dan jiran Afzal kafin ya sauko yayi joining ɗin su,gaisuwa ta musamman suka yi shi da Bahajjatu ta mai sannu da zuwa tare da tambayar sa masu jiki ya ce mata da sauƙi dan shi gudun sanar da ita gaskiyar lamarin yake bai san she is aware of everything ba.. Serving ɗin su aka yi suka fara cin abincin peacefully ya ga har sun yi rabin plate bata ce ƙala ba suka kusa gama cin abincin bata tanka ba sai ya fara suspecting ko dai an sanar da ita ne but me ya sa bai jiyo hayaniyar madness ɗin ta ba daga ɗakin sa?ko dai ta gyaru ne ta daina masifar ta da ke yawo a jikin ta ne?who knows maybe Allah ya shiryar da ita.sai ya basar shima bai ce komai ba har suka gama aka yi clearing table zata tashi ta wuce ya kirawo ta "Baha"!!tsayawa tayi ta ce "Na'am yaya"! "Zo ki zauna ina da magana da ke"komawa ta yi ta zauna kamar wace ba abin da ke damin ta sai da ya gama nazarin ta sannan ya tambaye ta "Wai kin kuwa san halin da yaya ke ciki shi da aminiyar ki"??jijjiga mai kai tayi tana share hawayen ta sai mamako ya kama shi ya ce "Wa ya faɗa maki"?ta ce "Yaya Hakim ne"shiru yayi yana tunanin anya ba sauƙi daga Allah bane ya fara zuwar masu seeing that yayi wa Hakim nasiha ɗazu ya ji yanzu kuma Bahajjatu ta san labarin abin da ke faruwa but yet bata yi reacting ba?what a miracle yayi exclaiming kafin itama ya shiga yi mata nasiha ƙarshe ma haɗa su yayi ya rinƙa yi masu nasihar dan dai ya kwantar masu da hankali daga bisani ya ce da su su je su kwanta su huta.tashi suka yk suka sallame shi kowa yayi hanyar ɗakin sa shima ya nufi nasa ɗakin da relieve na samin chanji a gidan na su daga wun ƙannen sa at least sun girma da zasu iya taya sa wurin taimakon yayan su da baby doctor si yi recovering lafiya ƙalau,with this thought in his mind ya kwanta bacci dan bai so a kira shi a fara tambayar sa dalilin sa na dawowa sai ya kaahe wayar gabaɗaya he believe Bilal can handle everything kafin Hakim ya tafi dan shi a nasa ma in ya gama monitoring Bahajjatu ya ga eh lallai ta yi hankali bata da zuciyar nan da ya san ta da shi sai su tafi tare da Hakim.... Kusan kwanaki biyu yana lura da ita babu abin da ya samo na ganin ido daga gare ta dan haka ya yanke hukuncin yi mata albishir na tafiyar ta da Hakim zuwa ƙasar germany akan da dare in sun haɗu a dinner zai sanar da ita dan da ya so su tafi tare da either Lukman or Jamil but dukkan su babu wanda ke available sai dai in sun dawo daga tadiyar da suka yi. It was in the morning da suka haɗu wun breakfast yana ma sauri zai tafi asibiti yake sanar da su cewa he have a surprise for the both of them in ya dawo suka ce mai sun matsu ya sanar da su amma ya ƙi yayi tafiyar sa.fitar sa babu daɗewa suma suka yi ficewar su.. _10:00pm_ Afzal,Hakim da Bahajjatu,zaune a parlor suna jiran jin me zai sanar da su amma yayi shiru sai chan ya ce "Guess what"?turo baki tayi ta ce "Whattt yaya kana ta ja mana rai"!!ɗan dariya yayi kafin ya ce "Zaki bi Hakim ku tafi germany gobe dan komai naku is well set babu wani abu da ya rage"!!murna ne ya kama su su duka har ta je ta rungume sa tana ce mai "I love you yaya i love you so much thank you for allowing me to go visit them"murmushi suka mata daga baya suka ma Afzal ɗin godiya ya ce da su su shirya tafiyar wuri za su yi,murna ne fal a ran su dan haka cikin nishaɗi suka yi shirin su suka kwanta bacci.... ************* A chan germany kuwa da Hajiya Zeenat ta gama fushin ta sai ta haƙura ta tafi ta yi wankan ta abincin ne dai bai shiga sosai ba dan bata jin zai sami masauki a jikin ta ɗiyar ta na kwance sama da sati biyu bata ci komai ba ina ta ga ƙarfin cin wani abin. Sai da prof yayi dagaske kafin ta chakwalkwala abincin ta ce ta ƙoshi ta matsar gefe.ce mai ta yi ita sallah zata yi kafin su koma asibitin ya ce toh shima bari ya tafi dan yin sallar dan haka kiran Dr Maher yayi a waya akan ya zo su tafi sallah,sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya fita daga ɗakin ta tayar da sallah shi kuma ya sauko ƙasa dan jiran Dr Maher. Da lallaɓa da encouraging words ya samu ta haƙura ta yi shiru ta daina kukan har zuwa lokacin da kiran prof ya shiga ya sanar da ita sallah zasu tafi ta mai Allah ya kiyaye hanya bayan tafiyar sa ne ta yi sallar itama ta zauna roƙon ubangiji da ya ba ma ƴaƴan su lafiya ya ta da kafaɗun su ba dan zunuban su ba,sosai ta masu addu'a dan watanni uku zuwa huɗu da aka ɗebar ma ɗan ta akan adadi lokacin tashin sa ba abu mai wuya bane a wun ubangiji... Da ta idar ne ta nufi ɗakin su Hajiya Zeenat a inda suka zauna zaman jimamin conditions da likitan ya zayyano masu game da farfaɗowar Zaid but sun yi realising cewa komai shall be possible da yardar Allah.ba jimawa suka shirya dan tafiya asibitin inda tare suka fito suka tarar da taxi na jiran su ba ɓata lokaci suka shiga ya wuce da su zuwa asibitin,ko da suka tafi sai suka tarar da Bilal ne kaɗai suka tambaye shi inda Afzal ya tafi bai ɓoye masu komai ba ya sanar da su cewa ya koma Nigeria but ya ce Hakim zai zo dan saboda akwai ayyuka da suka taru da yawa a hospitals ɗin iyayen su and there is no one to take care of them sai shi kaɗai, Abin ya ɓatawa Ammi rai har ta fara bambamin cewa aiki ya fi ƴan uwan sa muhimmanci a gare sa kenan in ba haka ba ana wannan hali har wani aiki mutum zai je yi but Hajiya Zeenat ta yi calming nata ta ce dole ne ya kula da wani fannin since there is no one to do it da haka dai ta yi shiru not because ta yi niyar yin shirun sai dan kar ta janyo magana a hospital premises. Ƙarasa shiga cikin ɗakin baby doctor suka yi inda suka ganta kwance tana bacci kamar dai yadda suka bar ta this is 3 hours da barin su asibitin but bata tashi ba abin ya dame su sai suka koma chan gefen Zaid dan ganin ko an sami improvement but shima still a nan gwiwowin su ya fara sagewa shi Bilal mai kukan ne dai ya ƙarfafa masu gwiwa dan shima jiran zuwan Hakim ya ke yana son komawa gida yayi resuming aikin sa maybe kafin sati ya wuce zai ji an ce da shi an sami improvement dan zaman sa a nan ɗin gani yake kamar abubuwan basu cigaba.. Zaman jiran farfaɗowar baby doctor suke yi dan sun san shi kam Zaid ba tashin yanzu yanzu bane.. Cikin hikimar ubangiji kuwa zaman su babu jimawa suka ji kira daga ofishin likita da suka tafi hints ya basu akan yanda zasu kula da ita yanzu da ta farfaɗo dan gudun kar ta kuma collapsing kamar yanda ta yi ɗazu godiya suka mai suka fita suna murnar ta farka.. She is awake and cool dan a zaune jingine da bed cradles suka riske ta an saka mata soft pillow ta bayan ta tana sipping wani abu da basu san ko menene ba a tea cup rufe da murfi sai straw da take sipping da shi wanda ya ke ta saman kofin.. Hamdala suka yi na ganin ta cikin sukuni har ma tana iya shan abu tana iya riƙewa da kan ta.ƙarasawa ciki suka yi a nan aka shiga tambayar ta me ke damin ta ina ke mata ciwo ita dai murmushi kawai ta rinƙa yi har suka yi shiru ta ce da su "Am fine am absolutely fine you all can see that am good"!!ta faɗa tana masu murmushi dan hankulan su ya kwanta sai suka faɗaɗa fara'ar kan fuskar su.tambayar su ta yi "Ya jikin na sa"?a nan suka ɗan yi jimm sai ta kalle su haɗe da ajiye kofin ta ce "Is okey kar ku damu zai tashi nan ba da jimawa inshaAllah"daɗi suka ji lallai tana da ƙarfin zuciya ita da yanzu ta farfaɗo but har tana da ƙarfin reassuring nasu as a doctor,rungume ta Ammi ta yi ta ce "Allah ya maku albarka ya kuma kare mana ku daga yau sai yau babu ku babu outreach ko da a nan asibitin ku ne ba ku kuma yi"!a halin jimami ake amma sai da maganar ta ya saka kowa darawa kaɗan ciki kuwa har da Bilkisun dan a nan ta fara tunanin shine fah ya natse na maganar outreach ɗin nan ita kuma shegen girman kai ya hana ta ƙin yarda akan ba zata bi shi ba shi dan ya hukuntata ya shirya tafiyan but at the end of the day abin sai ya juye masu he end at the receiving end ohh Allah ka bashi lafiya,,a zuciyar ta ta yi wannan analysis ɗin.. Ranar murnar iyayen baya misaltuwa dan haka a nan ɗakin na ta suka kai har dare ta ce da su zata tafi ganin shi suka ce a'a ta bari har washegari bata gama farfaɗowa ba dan haka ta haƙuran Bilal ne ya taya ta hira har dare wuraren 11 sannan ya mata goodnight ya tafi dan hutawa yayin da Ammi da Hajiya Zeenat suka kwana a nan dan a daren aka so yi mata wanka ta ƙi ta ce zata iya da kan ta har tsiya suke mata wai in bata yarda an mata yanzu ba ma ai akwai na jego dole ma ta yarda jin su ta yi amma ko za'a haɗa ƙasa da sama ba zata yi wannan wankan jegon miyatar da ake yi ba haka kawai ta janyowa kan ta matsala. Da ƙyar ta yi wankan aka saka mata rigar bacci mai kauri da hula abinci ta ce sai washegari dan ta sha energy booster kafin su shigo haka suka ƙyale ta ta kwanta suma suka kwanta. Oh rayuwa wai su ne ke jinyar yaran su biyu a asibiti asibitin ma ta wata ƙasa lallai yaron nan ya guji haɗuwar su da shi... ************ Kwanaki biyu aka ɗauka ana koya mata tafiya dan joints ɗin ta duk na mata ciwo sakamakon doguwar kwanciyar da ta yi a course of minor exercise ɗin ne ta yi saloli wanda ya taimaka mata ta kuma jin jikin ta ya sake mata har take fatan Allah ya sa anjima su fita dan ta samu ta yi sneaking zuwa ɗakin Zaid because tunanin sa ya zame mata obsession tun da ta farfaɗo su kuma sun ƙi kai ta dan ganin sa.. A yammar ranar ne jirgin su Hakim ya iso dama Bahajjatu ta hana kar a sanar da Bilkisu zuwan su she want to surprise her dan Hakim ya sanar da Ammin su tare da Bahajjatun zasu taho har da faɗan kar ya kawo mata ita ta zo tana portraying masu madness a asibiti but sai ya mata bayanin ai ta shiru ƙyale shi kawai tayi.. It was a big surprise to her dan ta ga babbar ƙawar ta da zata iya sharing damuwar ta da ita. After all the oyoyo and everything sai suka keɓe ta sanar sa ita damuwar ta dama ƴar taya ɓera ɓari ce sai ta nemar mata hanyar fita kamar ɓarayi ta yi directing nata zuwa hanyar office ɗin doctor kamar dai yadda Bilal ya nuna masu da suka zo dan bai bari sun ga Zaid ba dan gudun tashin hankalin da zasu shiga a ce da zuwan su sun riski matsala irin wannan bai kamata ba.. Thank goodness ta sami doctor ɗin but he was amused ganin ta bayan ya san cewa ita patient ce sai ya ce ta zauna ta zauna "How may i help you"ya faɗa feeling free da ita sai bata ɓoye mai komai ba akan tana son sanin komai ne game da ɗayan patient ɗin ta kira sunan sa at first the doctor was like can he tell her everything about the patient ko dai ya ɓoye ne da ta ga haka sai ta mai bayanin cewa daga ita har shi ɗin da ke unconscious doctors ne har ta ɗan kawo mai scenario da ya faru da yayi sanadiyar zuwan su,a nan hankalin sa ya kwanta sai yayi narrating mata duka findings ɗin su she was shedding tears but bata san cewa crocodile tears take shedding ba real tears ba sai da ta ji ɓoyayyen solution da likitan ya sanar da ita a nan ta yi zaman dirshan ta shiga risgar kuka ba ji ba gani haka ya rinƙa bata magana har dai ta tashi ta tambaye shi ɗakin da Zaid yake ya mata describing bai da nisa da office ɗin sa ta fita tana haɗa hanya da ba gama warwarewa tayi ba tana dafa bango ana kallon ta ana mata sannu bata amsa kowa har ta iso ɗakin ta hango shi ta waje under control of machineries and devices ta tuna da final solution da likita ya gaya mata sai kawai ta fashe da kuka tana yi tana jujjuya kai tana cewa "Noo noo..Zaid please noo i can't witness that inalillahi wainaillaihir raji'un please Zaid don't accept the defeat fight it please"... Giftawar ta kawai bilal ya gani sai yayi saurin bin bayan ta a hankali ya rinƙa tracing hanyar da ya hango ta har dai ya iso ƙofar ɗakin da take tsaye wato dai ɗakin Zaid,jim yayi yana kallon ta tana bashi tausayi dan duk maganganun da take yi yana jin ta rasa abin faɗa mata yasa yayi shiru har dai ya ga abin na son fita a kan dausayin mai hankali. She was crying with great agony and pains haɗe da hatred na Asma'u dan ita gabaɗaya ta ta'alaƙa laifin komai ne a kan Asma'u because if not for her babu ta yadda za'a ma Zaid wannan aika aikar dan haka with each passing seconds of her life yana tafiya ne da tsananin tsanar Asma'u a ran ta tsana ce mai ƙarfi wacce bata jin zata iya yafe mata saboda taɓa lafiyar Zaid da aka yi daidai yake da hukuncin takura mata walwalar ta da sukunin ta a duniyar ma baki ɗaƴa.+ Any word she speak out rhyme with her heart wishes she just pray that he wakes up at the right time if not da akwai babbar tashin hankali a ƙauyen koma gabaɗaya ba ma gidan su Mudan da Asma'u kaɗai ba.. Tana tsaka da kukan ta mai tsuma zuciya ta ji an taɓa ta sai ta dakata da kukan tana share hawayen ta kafin ta juyo ta kalle sa sai ta ga Bilal ne ba amfani in ta ɓoye masa damuwar ta sai ta cigaba da kukan tana nuna mai ɗakin Zaid tana kuka kamar ba ita ta farfaɗo daga jinyar sama da sati biyu ba jan hannun ta yayi dan su bar wurin saboda kasancewar su a wurin ba komai zai haifar mata ba apart from more heartache da increase hatred wanda is not good for her health. Tana kuka tana fincikewa yana jan ta da kuka da fixge fixge suka koma ɗakin ta inda a nan ne suka yi kiciɓis da Hajiya Madina dan dama daga neman ta ta fito ko da ta ga bata nan babu wanda ya fara zuwar mata rai sai Bahajjatu dan ita kaɗai ce marar jin maganar da zata iya fitar da Bilkisun shi yasa ta rinƙa trying line nata sai dai bai shiga dan ita ma Bahajjatun fita tayi dan neman apple ɗin ta because zuciyar ta fes yake and she is praying for her big bro to wake up as soon as possible,suna cikin hirar ne sai ya ga kamar gilmawar twin sis ɗin sa cikin tashin hankali sai yayi saurin biyo ta inda yayi discovering abin da take kallo har ya saka ta kukan da take yi shi ya sa ya ja ta suka bar wurin gudun kar Bahajjatu ta gano ɗakin da yayan ta ke ciki because he is sure ahe will definitely create a scene dan bai san dalilin da yasa Afzal ya bar ta ta biyo Hakim ba alhalin duk sun san halin ta. Ganin Bilal tare da ita ya sa Ammi sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Bilal ina ka kai ta ka san bai kamata ta rinƙa fita mai tsayi ba ba tare da guidance na kowa ba kuma ka fi kowa sanim halin da take ciki i see no reason why you should take her out of the room"!!ita fah magana take yi ba tare da ta lura da cewa ita Bilkisun kuka take risga ba sai da ta fara wata maganar sannan ta lura "Ni har na fara targeting Bahajjatu thinking ita ce ta fitar da ita daga ɗakin nan ashe ba ita ba ce kai n...."a nan kalmar ta maƙale mata sakamakon fitinannen kukan da ta fashe da shi wanda daga cikin zuciyar ta kukan ke fitowa sai ta yi hanzarin riƙe ta ta shiga tambayar me ya same ta a nan Bilal ke sanar da ita abin da ya faru sai ta yi mamaki kenan dama ranar da ta mata bayanin komai bai shige ta ba kenan ya ɓace mata a memory na ta but kamar wannan kukan ba akan ganin Zaid a halin da yake ciki bane kawai is like there is something hidden beneath the tears but what could it be?rashin samin amsa ya sa ta zaunar da ita a kan gadon ta fara rarrashin ta tare da bata magana ita duk a tunanin ta ganin halin da Zaid ke ciki ne ya saka ta yin kukan though tana suspecting akwai ɓoyayyiya but since she refuse to say a word sai kawai ta ƙyale ta after all bai kamata ta shiga damuwa ba da farfaɗowar ta haka da wuri..rarrashin ta ta ke yi sosai har da gaya mata ai yadda ta farfaɗo ba tare da sun yi tsammani ba haka Zaid zai farfaɗo shima akan ta dai yi mai addu'ar samin lafiya,sauraron Hajiya Madina ya zame mata dole shi ya sa take sauraron ta ba wai dan maganganun ta na tasiri a zuciyar ta ba dan kuwa babu magana ko ɗaya nata da ke shigar ta ko kaɗan har ta kai ayar maganar ta kuka kawai take yi daga ƙarshe dai kiran doctor aka yi ya zo ya mata abin da zai yi seducing ɗin ta ta zamo calm.. Hakan aka yi dan allural anti depressant aka bata wanda babu jimawa bacci mai nauyi yayi gaba da ita sai a nan suka sami kwanciyar hankali,Bilal dai ya kasa ganewa wannan murɗaɗɗiyar al'amari dan shi a iya sanin sa babu wata jituwa tsakanin brother In-law da twin sis ɗin sa kafin su tafi outreach ɗin nan kuwa he can swear that sam ba da niyar ta aka yi tafiyar ba but what later happened bayan tafiyar su?did they manage to get closer to each other?did they understand each other in the course of their outreach?toh wa ma zai ba shi amsa?babu dan haka ya ƙara ba ma Ammi haƙuri akan fitar da ita da aka yi ya sanar da ita shi ke da laifi ba Bahajjatu ba dan sarai ya san halin Ammin sai ta balbale masa apple which he hate more than anything,faɗa ta mai akan ya kiyaye fitar da ita anyhow saboda she is still in convalescence stage bata da damar yin abubuwan da ta saba yi a baya sai a hankali zata mayar da jikin ta,haƙuri ya bata kafin ya mata sai da safe dan yana son tafiya harhaɗa kayan sa na komawa. Fitar sa babu jimawa Bahajjatu ta shigo ɗakin duk a ɗan ɗarare dan tsammanin ta Ammi ta san ita ce ta fitar da Bilkisu har fitar ya janyo mata collapsing she thought Ammi is just waiting for her to give her a sound slap dan Ammi bata tolerating shirme hatta da Hakim da ke babba da ita in ya nemi ja da yawa da Ammin sai ta mare shi babu abin da ya shafe ta sai dai in abin ya lafa ta bi shi ta ja shi a jiki a nan zata mai faɗa da nasiha sannan ta ɗora da rarrashi.. Sai ta ga akasin hakan sai ma ta ga Ammi tana tambayar ta ina ta shiga "Baha ina kika tafi ga Bilkisu har ta famo rashin lafiyar ta Bilal ya fitar da ita ya kai ta ɗakin yayan ku now she has collapsed ban san me yasa Bilal ya fitar da ita ba alhalin ya san halin da ta shiga i hate to see her sleeping bana so it scares me"jin waɗannan bayanai na Ammi sai ta sami sauƙi a ran ta Allah sarki her apple ya amshi laifin da bai da masaniya a kai duk dan yana gudun kar Ammi ta balbale ta. Rungume ta tayi ta ce "Is okey Ammi she will wake up inshaAllah zasu farka mu cigaba da yi masu addu'a kawai kin ji Ammi na"?girgiza mata kai tayi suka kalle ta daga bisani suka fita suka ja ƙofar suka rufe mata dan ta sami peaceful sleep.. ************ A nan hotel apartment Hajiya Zeenat ce kwance tana kallon Dr Muhammad da ke ta faman bincike a laptop dan ya kai kusan awowi uku yana faman binciken da ya ke yi wanda binciken ba akan komai bane face akan remedy na rashin farfaɗowar Zaid Maher dan almost 4 days kenan ya fara research ɗin saboda shi kwata kwata bai gamsu da 3-4months da doctor ya faɗa masu a matsayin period da zai yi spending yana unconscious ba sam bai yi buying idea ɗin ba ya fi yarda da ya binciko makarin matsalar da kan sa a matsayin su na iyayen sa dole su nemar mai lafiya dan wannan duk ba zai kawo masu kai ba time is passing ba zai tsaya jiran kowa ba likewise if care is not taken they might loss him Allah dai ya kiyaye baƙar ranar.wannan shine babbar dalilin sa na takura kan sa ba dare ba rana yana binciken abu mafi sauƙi da zai samo masu hanya mai ɓillewa ba wai ya raina taimakon likitocin bane a'a but yana ganin suna ɓata golden hours da suka samu dan su samarwa da Zaid lafiya shi yasa yake bincike binciken da yake yi with the hope that in an dace Zaid na iya farfaɗowa within a month or less ba sai an cigaba da jiran gafara sa ba'a ga ƙaho ba. Yana tsaka da binciken sai ya ji hannun ta a kafaɗar sa tana mai massage kaɗan kaɗan,lumshe idanu yayi kafin ya buɗe su ya ce "Thank you so much"!! Murmushi tayi da ta daɗe bata yi irin sa ba tace "It's my pleasure my prof". Ɗan shiru ne ya ratsa wurin kamar mintuna biyu sai ta ce. "But prof me zai hana ka kwantawa ka huta in ya so anjima sai in ta da ka ka cigaba da research ɗin or i might even help you you don't know"!!shiru ya mata dan shima ya san yana buƙatar hutun but he just can't he have a task da dole ya ƙarasa dan haka ya ce "Nahh sweetheart je ki kwanta zan cigaba i will join you later saura kaɗan in gama gabaɗaya ma research ɗin dan mu sami hutu da sukuni dukkan mu humm"??ya zuba mata idanu amsa mai ta yi tana mai jin tausayin sa na shigar sa madaɗin ta kwantan sai ta ta gyara kujerar kusa da shi ta zauna ya dube ta da mamaki ya ce "Baccin fah?kin san dai gobe ke zaki tafi asibitin nan dan ya kamata Hajiya Madina ta huta haka nan"!amsa mai tayi ta ce "I know but ba zan iya ba kin ga saura ƙiris in kammala dan Dr Maher bai da sukuni kuma kin ga after all these hallacin da yaron nan yayi mana kafin Bilkisu ta amshi kwatan ragamar ayyukan nan namu ina ganin kamar ta nan kaɗai zan iya saka wa mahaifin sa da family ɗin ma baki ɗaya i just need your prayers and support"rungume shi tayi ta ce "I know your purpose Dr na san dalilin ka kuma ina taya ka addu'ar samin nasarar wannan aiki da kaje yi Allah ya ba su lafiya"da amin ya amsa daga haka suka cigaba da zaman shi yana aikin sa ita kuma tana zaune beside him jefa jefa sukan yi hira. Sallama suka ji an yi a ƙofar ɗakin sai ta miƙe ta nufi ƙofar,leƙawa tayi ta ga mai sallamar sai ta buɗe haɗe da amsawa,bashi hanyar shiga tayi ya shigo ta mayar da ƙofar ta rufe suka ƙarasa shigowa parlorn tare zama yayi ya gaida iyayen sa amsa mai suka yi kafin ya sanar da su dalilin zuwan sa akan komawa gida fatan alkhairi suka mai haɗe da addu'ar kariya daga sharrin hanya da na ƙarfe.. A daren dai sai after 2 na dare suka rintsa dan sai da ya tabbatar da cewa ya samo ainihin doctor ɗin nan wato Dr Ruzu shaharrren herbal doctor ne wanda ya shahara a fannin magungunan gargajiya da sarrafa kayan itatuwa da ganyayyaki wurin samin makarin cuta duk tsananin ta wanda ko da mutum ya kai shekara ashirin yana fama da cuta muddin ya baka magani toh inshaAllah kai da wannan cutar har abada,shine likitan da watanni uku da suka gabata gwamnatin ƙasar china ta miƙo masa gayyatar su akan ya dawo ƙasar ya zama babban likitan gargajiyar su a fadar shugaban ƙasar china saboda ƙwarewar sa da hazaƙar sa da suka ji suka kuma gani wanda a ƙasar germany ɗin ma an san da shi ta fannin bayar da magungunan gargajiya masu inganci,toh a rashin sani aka kusa rasa sa a ƙasar sa ta gado wato Nigeria dan saura ƙiris ya amshi gayyatar gwamnatin ƙasar china sai dai wani mai yaƙi da ha'inci,mai muryar talakawa,mai bawa marasa murya murya,uba ga marasa shi kai har ma da masu shi,adali,zaƙaƙurin shugaba mai taimakon al'uma wato Dr ordinary president Ahmad isah shugaba a gidan radion Abuja mai suna *HUMAN RIGHTS RADIO AND TELEVISION* yayi nasarar ɓarar da katin gayyatar da ƙasar china ta kawowa likitan ya hambaɗa masu hayaƙin tsohuwa ta hanyar yin kane kane wun hana Dr RUZU amsar gayyatar haɗe da nuna mai muhimmanci sa a ƙasar sa da kuma illar tafiya chan dan dama a ƙa'ida bai kyauta a ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi ba wanda a tarihi kowa ya san ƙasar china ƙasa ce da ta shahara a ilimin sanin ganyayyaki da itatuwa masu muhimmanci wanda ya kasance ɗya daga cikin hanyar income na ƙasar dan hikimar su wurin tantance magungunan gargajiya da sanin hanyoyin amfani da su wa marar lafiya kenan in har ƙasar Nigeria ta yi rashin irin wannan babban likitan gargajiya da kafatanin ƙasar china aka rasa wanda yayi nasarar zama likitan gargajiyar fadar shugaban ƙasa kama daga ƙasar har zuwa ƙasashen ƙetare na fararen fata har aka tsallako aka zo ƙasar bakaƙe ƙasar Africa a African na yankin ƙasar Nigeria toh lallai da an yi babbar rashi but with the awareness being created by the ordinary president to the genius herbal doctor Dr RUZU sai aka sami cigaba daga watanni ukun da duniya ta kuma sanin sa sosai sama da da zuwa yanzu an sami marasa lafiya masu fama da cututtuka daban daban kama daga paralysis either unilateral or bilateral paralysis,Diabetes Mellitus,cases related to long hospitalization that can lead to unnecessary comma(kamar dai condition ɗin Dr Zaid Maher) and so many other illnesses da asibiti ta kasa maganin sa shi yana ƙoƙarin sa wurin bayarwa wanda ba shi kaɗai bane ke wannan ƙoƙarin ba wasu lokutan great herbal doctor ɗin nan ma wato pharmaciest Zainab Sharif mai bada nata gudunmawar a fannin magungunan gargajiya har da ma dai ta yi kwana biyu da barin aikin but one of her daughter is on the line wato tana karantar fannin herbal drugs a ƙasar Dubai duk ta hanyar shugaba ordinary president Ahmad isah aka yi exploring waɗannan great herbal doctors namu wanda in banda addu'a babu abin da za'a sakawa wannan great man da shi _(ilimi kogi ne faɗi ne da shi ƙaryar ka ka ce za ka ga ƙarshen sa ba tare da ka samo abubuwa kala kala ba ciki har da na ƙwarai da akasin sa,komai na da sanadi kasancewar Dr Muhammad Sulaiman great and best medical doctor amma bai duba wannan ba ya shiga nemar mafitar matsalar su wato lalurar Dr Zaid bai fah yi girman kan shi ya sani ba ko ma da yayi practising ba he went into research ba dare ba rana dan dama Allah subhanahu wata'ala baya saukar da cuta ba tare da ya saukar da maganin ta ba sai dai in ba'a bincika ba but ko da a birnin sin maganin yake in har ka bincika zaka samu but nowadays we the children of the computer age find it stressful,boring,burdensome,annoying and time wasting mu tsaya bincike especially wai gargajiya sai dai a yi na bature kawai a tsaya jiran adadin da effect zai yi exhibiting but gargajiya ba da mu ba i mean the real gargajiya not muna gargajiya drugs wanda sau da dama muna da su,muna da magungunan cututtukar mu a nan kusa da mu but due to uniform habit na mu na i don't care da ignorance ya sa sam ba mu taɓa sanin komai sai dai mu yi ta ɗura kuɗaɗen mu muna siyo abin da kusa kullum muke kiciɓis da su but sakamakon ignorance na mu ba mu sanin su ne,the long and short paragraph containing the bulky note shine mu daina ko ma mu rage son jiki wurin bincike da son sanin abubuwa a rayuwar mu da zamu ƙaru da su in a positive way mu kasance cikin bincike da bankaɗo abubuwa da dama da bamu sani ba wanda mu kan mu mun san ba mu kaɗai zamu amfani da shi ba the entire nation will benefit from a single introvert and unrecognized individual experiment,dan haka am urging not only us the youth but kowani citizen na ƙasar da yake da ya yi ƙoƙarin shiga chan ciki cikin research dan samo latest update da related histories ɗin su dan samowa kan mu al'uma mai walwala sai tare da haɗin kan mu da hannun mu zamu gyara ƙasashen mu either regarding our health,wealth,safety and security,environment,education and so many other things ina fata Allah zai taimake mu akan portraying waɗannan ƙananun shawarwari da na bayar Allah ya sa mu dace amin)_ _Next morning_ Da sanyin safiyar ranar juma'a Bilal ya nufi asibitin da ganawa da ƴaruwar da nufin in ya kai wata ɗaya zuwa biyu zai kawo masu ziyara dan Hajiya Zeenat kam cewa tayi ƙafar Zaid ƙafar baby doctor na barin ƙasar dan tare aka kai su so dan ta ji sauƙi ba yana nufin zata tafi ta bar sa bane a'a tare zasu koma yanda aka san cewa a tare aka illata su toh ana fatar a taren za'a gan su sun koma lafiyar su ƙalau dan sai lokacin zasu samu su hukunta la'anannen da ya kusa kai masu ƴaƴa inda ba'a dawowa,ƙulluwa sosai suka yi da Mudan sunan sa kaɗai suka ji but anything regarding his personal life affairs basu da labari dan ba ta shi su ke ba kawai jiran farfaɗowar yaran au suke dan hukunta la'anannen zai fi armaahi in suna cikin daidan su. When he opened the door,he felt something strange da bai san dalili ba sakamakon ganin ta zaune ita kaɗai tana cin abincin ta na safe saboda akwai 6am medication da za'a yi serving mata,on normal basis haka kawai bata cin abinci irin haka dan in bai manta baa jiyan nan da ƙyar ma ta iya cin dinner dan sai da aka kai ruwa rana sannan ta tsaƙuri kaɗan ta ce ta ƙoshi but yau,right now she is behaving different kamar wacce ta shekara bata ci abinci ba me yasa?. Ƙarasa shiga yayi ya kalle ta kafin ya zauna ya kira sunan ta "Beelove"!!jin kamar sautin muryar sa ya sa ta ce. "Bilal"tare da ɗagowa dan tabbatarwa because she has been longing to hear his voice. kallon ta yayi cikin sigar tausayi sai ya ce "Na'am apple".da wani irin speed ta jawo hannun sa ta riƙe cikin nata ta fara maganganu "Bilal i missed you,ya aka yi ka san halin da muke ciki har ka sanar da su umma aka kawo mu nan?kana ji na?ka san wa buge Zaid?Mudan ne..Mudan kuma yarinyar nan yarinyar da muka yarda da ita ita ce ta nunawa Mudan hanyar da muka bi shine suka zo..suka zo...suka buge Zaid a ta nan" tayi maganar tana mai nuna mai occiput ɗin ta sannan ta cigaba da magana cikin ƙaraji "Bilal i want to do something..i hate that girl i hate her with passion she caused all these misfortune i hate her"da kuka ta ƙarasa maganar. Me zai ji ya kuma gani?ba dai suspect ɗin sa bane yake shirin zamowa gaskiya?Bilkisu hauka ke shirin kama ta ne ko mai?da ya shigo she was eating without manners and now tana narrating abin da ya faru da su a ƙauyen nan bayan ta kai kusan kwanaki huɗu da farfaɗowa kowa na murnar ta farfaɗo but what is all this?what is he witnessing?sai ya shiga girgiza ta yana magana "Bilkisu are you alright?are you back for real?did you remember every single thing that happened?and she?who is she?waye yayi sanadiyar shigar ku wannan halin Bilkisu tell me"??banda girgiza kai babu abin da take ta yi tun da ya fara maganar har ya ida sai ta amsa kamar mayunwaciya ta ce "She is a villager a low class girl that i trusted and thought,the girl that claimed to be pure but she isn't i...i hate her"!!..ta cigaba da kuka bai gane maganar ba sai ya kuma tambayar ta "Bilkisu look at me..kin tuna abin da na faɗa maki ya faru jiya?kin tuna kin ga halin da brother In-law ke ciki wanda yayi sanadiyar collapsing ɗin ki"?girgiza mai kai tayi ta ce "Yeah..i do..i remember everything..see..am not mad i saw him yesterday..nima tashi nayi na ji na tuna komai..na ga halin da yake ciki kuma na tuna doctor ya sanar da ni condition ɗin sa har ya sanar da ni cewa wai matuƙar muna so Zaid ya dawo hayyacin sa na kankat bayan ya farfaɗo na farko sai an m.a........ "tunawa tayi da cewa she promised not to tell anyone about it saboda tashin hankalin da zasu shiga sai ya fi wannan da suke ciki dan haka tayi saurin kwaɓon bakin ta jin ta fara sauka a kan layi.yin shirun ta ya haifar wa Bilal tambayoyi daban daban a zuciyar sa toh menene final sauƙin kuma?ai likita ya sanar da su komai har da period da zai ɗauki Zaid kafin ya farfaɗo so why is she saying wai akwai zai dawo hayyacin sa bayan ya farfaɗo na farko?ko dai hucin rashin lafiyar ta ne ya sa take maganganu barkatai?yes,haka ne ma dan yanayin ta na yau kawai zai nuna maka cewa duk surutan da take yi a cikin magagin recovering if not wani final farfaɗowa zai yi?she is talking nonsense dan haka sai ya shiga saka ta breathing in and out haka haka har suka yi shi da ita sau biyar sannan ya ce "Apple i believe you duk abin da kika faɗa weren't delusional i understand but please don't say you last word to anyone ki bar shi tsakanin mu ni da ke dan kin san families ɗin mu are passing through a lot already akan wannan matsalar sayin your last word might ignite the range in everyone's heart so please make it be our little promise hmm"??idon su cikin na juna ta amsa mai da ido,godiyar ta ɗaya na ƙin tambayar ta ta ƙarasa sentence ɗin da ta fara ɓaramɓaramar faɗin secrete da ta bar wa kan ta. "Apple zan tafi dan ayyuka na jira na sosai a office i hope idan na dawo zaki gama jin sauƙi kuma zan tarar da brother In-law cikin good state of health"?amsa mai tayi da kai sai ya kuma yi mata wani maganar "Do me a favour apple"!kallon sa tayi sai ta ce "menene"? "So na ke ki taya brother In-law recovering daga shock ɗin nan ta inda in ya farfaɗo kowa zai yi murna mai ɗorewa ke kaɗai ce kika fi kowa sanin hanyoyin da zai saka shi dawowa a matsayin sa na mutum because you are like him,a doctor,su Abba ba za su iya ba please help him kin ji"har da saka fuskar tausayi sai ta amsa da "Toh zan yi"murna yayi sosai har suka rabu yana jaddada mata kar ta bari kowa ya ji maganar da ta fara faɗa ɗazu. Abin na ran sa dan haka da ya kirawo Bahajjatu akan su yi sallama sai ya yi narrating mata komai ƙarshe ya ɗora da "Apple ni fah gani nake Bilkisu ta sami matsala a brain na ta dan tana abu wani iri can you believe wai tana gaya min brother In-law zai kuma undergoing wani matsalar bayan ya farfaɗo?toh a ina ta ji kuma wa ya sanar da ita hakan?she called a name wai Mudan i guess he is the guy that attacked them kuma ta kirawo wata yarinya bata faɗi sunan yarinyar ba but according to her is like yarinyar ce tayi causing duka event da ya faru,but that name Mudan..yana min yawo,zan so sanin shi because i overheard Umma calling that name rannan da aka masu aiki i don't know but am obsess with that name Mudan".da alamar tambayoyi ya ƙarasa maganar wanda bai dawo tunanin sa ba sai da ya ji muryar Bahajjatu tana cewa "Ni na san Mudan kuma about tunanin whether or not shine guy da yayi attacking su Bilkisu shine..ba wani ba..kuma daga kai har families ɗin mu kar ku damu matsalar has been handled already ba sai an ɗau wani mataki ba"shiru tayi ta bar shi da mamaki haɗe da sumewar tsaye har ya kasa tambayar ta me take nufi da 'it has been handled'?? Ƙoƙari yayi ya haɗa kalmar "Me kike nufi da it has been handled"??sai ta ɗan murmusa ta ce "Apple tafi kar jirgin ka ya tafi ya bar ka and about the issue?time shall tell in muna da rai da lafiya hmm"??bin ta da kallo yake sai ya dai yi shiru yau kan sa na son ƙullewa da lamarin ƙawaye biyun. Raka sa tayi ya shiga taxi dan Hakim ne zai raka sa dama zuwa airport,kamar kar su rabu da juna tana ɗaga mai hannu shima haka ko kunyar Hakim ma ba su ji haka suka rabu ta koma ciki su kuma suka tafi,a motar ya kuma tambayar Hakim ko ya san wani wai Mudan amsa mai yayi da eh ya san shi sai ya tambaye shi ko yana da masaniya da matsalar da aka ce yaron ya janyowa family na su nan ma amsa mai yayi da eh ya sani kuma babu wani damuwar son sanin hukuncin da za'a mai dan sun yi handling komai but sai ya ce da shi ya bar maganar a tsakanin su kar ya faɗawa kowa a cikin family members ɗin su,har suka isa airport jirgin su ya tashi bai daina mamakin abin da ya ke gani ba.. °°°°°°°°°°°°°° Around 11am na safe bayan Hajiya Madina ta koma ta yi wanka ta ɗan huta ta dawo asibitin dan bata jin zata iya samin sukunin kanta without seeing her self next to her son shi yasa ta koma asibitin mamakin ta Hajiya Zeenat ta ji sai dai da ta tuna har yanzu Zaid bar farfaɗo ba ba ta yadda zata sami kwanciyar hankali shi yasa suka baje a ta garden ɗin asibiti saman babbar darduma yayin da mazajen su ke ta ɗaya ɓarayin suna tattaunawa game da matsalolin su.a ƙalla ba a kasara ba sau shida Bilkisu na kai kawo tsakanin ɗakin ta,ɗakin Zaid da garden da su Hajiya Zeenat ke zaune,kowani moves ɗin ta Hajiya Madina na ankare da ita duk wasu suspense da tensed looks da ke kan fuskar ta tana ankare so take ta shiga ɗakin Zaid but an saka mata restriction dan jan kunne Hajiya Madina ta yiwa Bahajjatu akan ta kuskura ta bar Bilkisu ta silale ta shiga ɗakin Zaid har ta kuma collapsing masu toh zata fuskanci hukuncin ta mai tsauri ita kuwa ganin ba'a yi discovering ita ba ce ta fitar da Bilkisun a jiya ba ya sa ta ɗau alƙawarin kare ta daga shiga ɗakin a yau dan a zauna lafiya shi yasa ta fito da ita daidai corridor ta inda zata rinƙa hango shi but bata bari ta shiga ba.. Matsaowa kusa da kunnen Hajiya Zeenat Hajiya Madina tayi ta rage murya ta ce "Hajiya kina ganin anya ba za mu yi abin da muka jima bamu yi ba kuwa"?dariyar manyan mata suka yi wanda ya sa mazajen su kallon su sai suka gimtse suma sai suka basar suka juya suka cigaba da tattaunawar su ganin haka sai suka ƙara murmusawa... Gyara zaman su suka yi Hajiya Zeenat ta ce "Aminiya ina jin ki me kuma kika gano mana ba dai ƴan samarin mazajen mu na hararar waɗannan matan turawan bane masu jajayen fuskoki sur pimples da spot ba"?da teasing tune ta ida maganar sai da Hajiya Madina ta dara dan abin ya bata dariya sosai. + "Hmm ke dai aminiya bari ai ba ta kan su muke ba tukunna su zamu koma masu ne bayan mun gama da wannan matsalar da ke gaban mu"shiru ta yi kafin ta mai da idanun ta towards direction na baby doctor wanda har a lokacin ta kasa sukuni sai kai kawo take yi duk hankalin ta taahe sai Hajiya Zeenat ta bi idanun Hajiya Madina zuwa inda take kallon sai ta ga me take kallo juyowa suka yi a tare suka kalli juna Hajiya Zeenat na mata kallon ƙarin bayani sai ta ɗan dara kaɗan ta ce "Hajiya Zeenat me kika hango tattare da yarinyar chan"??sai Hajiya Zeenat ta ɗaga kafaɗa alamun bata hango komai ba sai Hajiya Madina ta ɗan ɓata fuska ta ce. "Kai Hajiya Zeenat kar ki gaya min har kin fara gazawa wun gano abubuwa mana,yanzu wai duk budirin da ke kai kawo cikin asibitin nan ba ki gano komai ba"?ɗaga kai Hajiya Zeenat tayi alamun tunani ta daɗe a hakan kafin ta sauko da kan ta ƙasa ta ce "Wallahi Hajiya Madina na kasa hasaso komai ban san dalili ba dan Allah dai ki saka ni a kan hanya dan ciwon kai kawai zan yi da tinanin nan because i don't think i can bring up anything"!!tafa hannu Hajiya Madina tayi kafin ta fara zayyano mata maganganu "Kin ga yarinyar nan Bilkisu,a baya da na yi zaton hala ƙiyayya ce mai tsanani tsakanin Zaid da Bilkisu wanda har nake ganin anya ba zamu shiga haƙƙin su ba in an haɗa auren nan nasu ba dan duk wata dabara da tarko da muke ɗana masu dan su hau kai ba su hawa but tun da suka tafi wannan outreach sai na ga sauyi sosai dan in na kira baby ina bugar ruwar cikin ta akan Zaid sai ta natsu ta rinƙa bani labarin tambayar da na mata haka shima toh ta nan na fara zargin kamar closeness ɗin su ya daɗu fiye da da kafin su tafi outreach ɗin a haka har wannan ƙaddarar ta sauko mana,ina iya ce maki tun da aka yi hospitalizing ɗin su har kawo ranar da baby ta farfaɗo abin mamaki da sunan Zaid ta farfaɗo tun daga ranar bata da magana sai nashi jiya fah da dare har sneaking tayi ta nufi ɗakin sa sai na ga sun dawo tare da Bilal tana faman risgar kuka suddenly yau yanzu kuma sai gata tana faman zarya tsakanin ɗakin ta corridor da ɗakin Zaid hankalin ta sam baya tattare da ita duk motsin ta ina ankare sai nake ganin kamar fah a matso da auren nan nasu kusa if possible kafin ya farfaɗo su bar ƙasar nan tunda kin ga his personal care is being taken care of by Hakim but kin ga in yana da mata komai ma zata iya yi mai ba physical care kaɗai ba hatta da psychological care wanda zai taimaka masa yayi saurin farfaɗowa dan akwai strong connection tsakanin ma'aurata so i just conclude mu haɗa auren kawai sai kulawar sa ya koma hannun matar sa ta nan ma zai fi samin kula sama da yadda Hakim ke mai dan Hakim ɗin kan sa ban gama kula da shi ba bare ya kula da yayan shi,this is my experience ya kika gani"??Hajiya Zeenat da ta yi suman zaune sakamakon jin maganganun Hajiya Madina wabda ya razana ta a ce ta haifi ɗiya ta raineta har girmn ta but tana cikin wannan halin bata sani ba ba ma ta lura da hakan ba sai da wata ta sanar da ita,is she a bad mother then??ta tambayi kanta,taɓo ta ta ji anyi sai ta dawo hayyacin ta firgigit tare da sauke ajiyar zuciya ta fuskanci aminiyar tata ta ce "Amma Hajiya kina ganin yin hakan ba zai dawo ya haifar mana da ɗa marar ido ba kuwa?dan na ga kamar dai har yanzu ba wai jituwar da kike tunani bane ke gudana tsakanin su ba ni na fi ta'alaƙa wannan halin da take ciki da incidence da ya faru da su a ƙauyen nan dan she is the only one that was with him a lokacin da abin ya faru so is very possible shock da ta shiga ne ya sa da ta farfaɗo ta ga shi bai farfaɗon ba ya sa duk ta damu dan kin san ɗiyar taki da sakawa kanta damuwa ni mamakin rashin damuwar ta ma nayi da aka ce zasu tafi outreach,she didn't complain but still ni dai bana son a ma ɗa na dole dan kawai baya cikin hayyacin sa kuma yana ƙarƙashin ikon mu kar fah ki manta a tarihin rayuwar mu namiji mace ɗaya yake fara rayuwar shi da kuma da ita yake ƙarewa so what if we decide to get the two of them married and it end up that yana da wacce yake so da muradi fah?wacce yake burin aura kuma ita kaɗai ce tsarin sa fah?sai ya farfaɗo ya ji Bilkisu ce matar sa ba wacce yake son ba kina ganin za'a kwashe lafiya?anya ba zamu shiga haƙƙin sa ba kuwa Hajiya"?tayi maganar ƙarshe da alamar jimamin lamarin sai Hajiya Madina ta dara kaɗan kafin ta ce "Me haka kuma Hajiya?ke fah da kanki kin faɗi cewa a tarihin rayuwar mu namiji da mace ɗaya yake rayuwar sa dan haka ki sani Zaid bai da wata matar a duniyar nan illah Bilkisu matuƙar ina raye kuma ni na haifi Zaid a ciki na na raine sa har girman sa toh bai da wata mata a duniyar nan sama da baby either he likes it or not bare ma ba zai ƙi ta ba and about issue na whether or not ita ba taste na sa bane,duk bai taso ba dan ni na hango abin da su yaran basu hango ba,babu namijin da zai kalli Bilkisu ya kawar da idanun sa nare a ce har ya mallake ta sannan yayi yunƙurin cewa bata mai ba wannan ƙarya ne babba ma dan Bilkisu owns everything a proud woman should have ko kin manta hausawa na cewa *_Iya ruwa fidda kai_*,dan haka ina mai miki albishir da ki shirya tarbon jikar ki ta biyu nan da shekara mai zagayowa we will be grannies isn't that a perfect picture"?ta faɗa tana mai fallasa farincikin ta da ta kasa ɓoyewa dan ta gama haɗa komai da yadda zai gudana cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba.Hajiya Zeenat have no choice but to accept the decision being made by her dearest friend. Dariyar manya suka yi sai mazan suka kalli juna cikin mamakin ta yaya matayen su suka san abin da ke zuciyoyin su wanda a halin da ake ciki maganar suke tattaunawa akai dan sun gama da maganar lafiyar Zaid but Dr Muhammad refuse to reveal his intentions akan makarin rashin lafiyar Zaid dan yafi so ya zo masu a matsayin surprise gift daga wun sa sai suka ɗan buɗo idanu alamun what?sai suka kuma kallon matayen nasu sai dai su ba su suke kallo ba hasalima hirar su suke yi. For a long while tana ta kai kawo daga ƙarshe ta gaji ta zauna haɗe da matsowa kusa da Bahajjatu ta yi lowering voice ƙasa "Baha can't you please help me just last help ban kuma roƙan taimakon ki regarding this but please do me this last favour ki taimaka ki tsallake maganar Ammi ki bar ni na shiga ɗakin nan dan ganin sa wallahi am restless bana jin ina iya samin natsuwa matuƙar ban gan shi yadda nake so ba please baha do something i might create a big calamity here"!!a dame ta ida maganar wanda hawaye yayi accompanying maganar ta ta ƙarshe sai tausayin ta ya kama Bahajjatu but ya zata yi Ammi ta gindaya sharuɗɗa ita kuma bata shirya amsar faɗar Ammi ba sai ta janyo ta jikin ta tana share mata hawayen "Beelove ba fah ƙin son shigar ki ake ba a'a,kin ga jiya ɗaya da kika hango sa sai da kika birkice mana kija yi collapsing har sai da aka maki antidepressant kafin mu sami hutu again apple ya amshi laifin da ba shi yayi ba a jiyan nan sannan yau Ammi ta ja min kunne dan Allah kaɗai ya san me zai faru matuƙar kika yi tozali da shi kamar yadda kike son yin kin ga ko ba komai kin jawo min magana da Ammi shi yasa na ƙi barin ki ki shiga ciki ko daga nan ma kina iya hango shi ba sai kin shiga ba ki ƙara haƙuri wataran zaki shiga very soon"!ta cigaba da rarrashin ta dan ita dai bata son shiga matsalar Ammi. Dan ji kam ta ji ta bjmut bata jin tana iya rintsawa ba tare da ta ga fuskar sa ba,kuka take yi sosai wanda ya sa Bahajjatu tambayar ta ko dai wani abin aka mata da bata son faɗa sai ta ce a'a ta share hawayen ta a daidai lokacin kiran Bilal ya shigo wayar Bahajjatu saurin picking ta yi ta matso da Bilkisu kusa dan su gana tare,fuskar sa ne yayi appearing da rabin jikin sa da wanda banda white singlet babu kaya a jikin sa ai yana ganin fuskar twin sistern sa yayi saurin kife wayar yana tunanin me yasa Bahajjatu zata mai haka itakuma Bahajjatun da ta ga bai da kaya sai singlet sai tayi saurin kashe wayar dan kar Bilkisu ta gani saboda lokacin da ta saita wayar ita tana faman goge running tears da ke tsere a kan fuskar ta bata ɗago kan ta ba shi yasa bata lura ba sai da ta gama ta ga an kashe wayar "Me ya faru naga kin kashe wayar"!!tayi mata tambyar sai ta bata amsa da "Babu ina ga matsalar sadarwa ne kin san kayan bature"!jijjuga kai tayi ta share maganar idanun ta na kan sa ta transparent door da ke ɗakin ita in da zasu mata adalci da sun yarda ta shiga ta gan shi. Kira ne ya kuma shigowa wayar Bahajjatu ta ɗauka Bilal ne sai ta yi saurin dubawa sai dai ba shi ta gani ba numbern kelita ta gani kuma video call ne ɗauka ta yi haɗe da ɓata fuskar ta ta ce "Yes"! a halin taimako da agaji kelita ta fara magana "Ma'am how are you,how is your brother's health i was informed this morning"! "Uhumm,,he is fine.anything else"?ta mata tambayar cikin ɓata fuska sai ta ruɗe ta rasa abin cewa tsaki Bahajjatu tayi ta ce "Am hanging up"da sauri ta dakatar da ita ta hanyar ce mata "Ma'am is still on the issue,please do something and save a soul i don't know where to go of i leave here please help me"hmm lallai wasu dai basu iya samun wuri ba in banda haka ke ba gidan ku ofishin ma ba na ubanki ba an kore ki amma kamar karya kin ƙi barin wuri sai ta ran ta ya ɓaci a zuciye ta ce "Hey drama queen i don't have time for your drama as i have said you should evacuate my office before i return back and that's final"katse kiran tayi tana ta jero tsaki dan haushi da takaici wanda ya saka Bilkisu tambayar ta ko lafiya amma ta ce da ita ta share maganar kawai,sharewar tayi dan dama ba a mood na magana take ba so take kawai ta gan sa ko zata sami sassaucin fargabar da ke ɗawainiya da zuciyar ta.. Miƙewa tayi ta kama hanyar shiga ɗakin ta dan tana ganin ko kwana zata yi ba barin ta Bahajjatu zata yi ta shiga ɗakin ba,bin bayan ta tayi tana tambayar ta "Beelove wai ki gaya min wani magana mana"!tana tafe ta ce "Ina jin ki"! "Wannan saurayin naki na asibitin ku Dr Aslam ko wa yake?ina yake halan ko bai san baki da lafiya bane dan tun da aka dawo da ku har aka kawo ku ƙasar nan ban ga ya biyo ba bai kiuma kira ba me yasa"??dakatawa tayi ta tsaya kafin ta juyo ta zubama Bahajjatu idanun ta kamar zata yi magana sai kuma ta shiga tunani,. Aslma?ina ya shiga?ita ta manta da shi kwata kwata saboda last time da suka yi waya da shi ta wayar Zaid ne kuma a ranar ta mai kaca kacan in kiran ta zai yi ya rinƙa yi ta wayar ta ba wayar Zaid ba dan a lokacin basu fara jituwar sosai da Zaid ba kuma tun daga ranar bai kuma kiran ta ta wayar zaid ba sai dai ta nata wayar and if he call bata ɗagawa dan bata da wani sauran magana da shi but still yakamata a ce ko ba dan personal issues da suke da shi ba as professional colleagues kuma ma'aikacin da ke ƙarƙashin ta ya kamata a ce ya zo ya gaida su daga ita har Zaid but bai zo ba bai kuma nuna ya sani ba yana rayuwar sa comfortably lallai ma Aslam za kuwa ya haɗu da ita wani irin mutum ne shi marar sympathy wa mutani,tana cikin tunanin ta ga hannun Bahajjatu na moving kusa da fuskar ta sai ta ɗan lumshe idanun ta ta buɗe su "Bilkisu tambayar ki fah nayi amma kika shiga tunani halan menene"?sauke ajiyar zuciya tayi ta ce "Babu,about Aslam kuma ki manta shi kar ma ki kuma min magamar sa please ba shine a gaba na ba"tana gama faɗa ta juya ta fara tafiya sai abin ya ma Bahajjatu daɗi dan dama so take ta kuma tabbatarwa koh eh Bilkisu na da wani special feelings ma Dr Aslam but thank goodness hunch ɗin ta bai zama gaskiya ba kuma dama hakan take so dan ita kam bata mafarkin wani ya mallaki aminiyar ta sama da yayan ta ta san duk rashin fahimtar junan su ne ya sa suke ganin kamar ba zasu taɓa iya zama inuwa ɗaya ba kuma a rayuwa yanzu *iya ruwa fidda kai* ne in shi bai iya takun sa ba ita ya kamata ta iya in ita bata iya ba shi ya iya kuma ta ma san dole ne zasu saba dan dukkan su masu sauƙin kai ne kawai rashin sanin ainihin hallayar juna ya sa suke ɗaukar junan su a matsayin wani yana da jin kai but a hakan ma ita ta hango rayuwar su nan gaba matsalar dai shine a ɗaura auren but muddin aka ɗaura ko za'a haɗa sama da ƙasa bai isa ya datse auren ba bai kuma usa ya ƙaro wata ba sai dai ya gama bulaguron sa ya dawo kan hanya because she knows her friend more than anyone ita ɗin ƴar son soyayya ne kuma ta san zata samu daga wun yayan ta dan haka bata da wata ragowar damuwa. Saurin rungume ta tayi tana cewa "Apple dagaske ba shi bane a gaban ki"?mamakin tambayar ne ya kamata sai ta ce "Are you alright at all baha"?? "Yes..yess am alright am just happy" "Happy"?ta maimaita maganar Bahajjatun tana kallon ta sai ta girgiza kai ta cugaba da tafiyar ta har suka shiga ɗakin bata kuma cewa komai ba sai da suka zauna Bahajjatu ta kuma tambayar ta "Bilkisu wai ina maganar yarinyar nan da kika ce wai yaya na na so a ƙauyen nan"?sai ta ji ranta ya ɓaci sakamakon tunowa da Asma'u da ta yi sai ta ce "Baha ki daina ɓata min rai please i don't wanna hear or say anything about that ingrate"a harzuƙe ta yi maganar ƙarshe wanda ya bama Bahajjatu damar tantance eh aminiyar ta kishi take yi da so called girl lover na yayan ta kuma ta hango tsantsar so da takewa yayan nata sai dai in ɓoyewa junan su zasu yi but ko ma dai menene what goes around comes around zasu gane hakan nan gaba. Dariya kawai ta yi wanda ya sa Bilkisu kallon ta a tsorace ta ce "Anya baha ba za'a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ki ba kuwa kafin mu koma gida ba"?wani dariyar farinciki tayi kafin ta ce "Friend i saw what you were unable to see for the past few days humm"!!ƙyale ta tayi dan kamar Bahajjatu ta fara zarewa biye mata bai da amfani. Chan wuraren ƙarfe 11pm lokacin kowa ya kwanta babu ma masu taya ta kwanan dan an hana mutani saboda ana takura mata da yawa da unnecessary hirarraki kuma hakan na chaza mata brain jin hakan ya sa Hajiya Zeenat tafiya gida ita kuma Hajiya Madina ta ce babu inda zata tafi a nan zata kwana sai dai ba ta gefen ɗakin Bilkisu ba rather ta ɗakin Zaid hakan bai mata daɗi ba but ta san duk yadda za'a yi dole ne ma kawai ta gan shi yau sai dai a yi haƙuri da Bahajjatu zata tafi ma sai da ta tsaya ta gaya mata wata magana maganar da ya tsaya mata a rai "Bilkisu you are in love but you keep on denying it kin fake da cewa damuwa da shi ne ya sa kika kasa natsuwa again ɗazu mun yi maganar Aslam and you became furious and irritated mun yi maganar Asma'u sai kika sami mood swing immediately kika yi switching and you responded my question by saying you don't wanna talk or hear anything regarding her,,,if you don't have or feel anything about my brother then why did you reacted in such manner?girl don't feel shy i guess abin da iyayen mu suka hango is finally becoming real and reality dan haka ni dai nawa shawarar shine go for it..go for what you want and follow your heart i assure you you will never regret your choice goodnight and take care of yourself as well my brother"!!.. Tafiya tayi ta bar ta da mamakin maganar amma gaske ne wai?ko dai kawai hasashen Bahajjatu ne?but how a ce kana son mutumin da maganar kirki na tsayin mintuna biyar bai taɓa shiga tsakanin ku ba sannan har a ce so ya gitta?no. Wannan ma ba gaske ba ne weighing the distance and differences between the two of them sai kawai ta ga inaa maganganun Bahajjatu shiririta ne ba zai taɓa zama gaskiya ba dan ita ta san in banda tausayin sa da take ji sakamakon halin da yake ciki bata tunanin wani abu mai girma wai shi sunan shi so yana son kutse ya shigo tsakanin su haba a'a wannan shurmen baha ne kawai ba gaskiya ba. Da wannan tunanin ta lallaɓa ta saci hanya ta rinƙa ɓoye fuska har ta iso ɗakin Zaid babu kowa a wurin haka ma a ɗakin babu kowa sai shi kaɗai hasken ɗakin is very deem sai da ta kai mintuna biyu a tsaye tana wasi wasin ta shiga ko a'a shin zata iya hana kanta yin kuka in ta ga halin da yake ciki ko baza ta iya ba.ƙarshe shahada tayi ta tura ƙofar ɗakin ta yi sallama sannan ta shiga jikin ta a sanyaye duk ta ji gwiwar ta ya sage,,takawa ta fara yi kaɗan kaɗan tana jin fargaba. His face is turned laterally ta gefen dama dan ana jujjuya mai position bayan kwana ɗai ɗaya saboda a yi preventing pressure bed sore saboda is very obvious wa masu long hospitalization. A ɗarare ta nemi kujerar kusa da gadon ta zauna tana son ganin fuskar sa a hankali ta leƙa tana fargaba har dai ta sauke idanun ta a kan fuskar sa,gaban ta ne ya faɗi haɗe da tausayin sa dan a normal basis shi ba mutum ne mai ƙazanta ba yana da tsafta he try as much as possible dan shaving excess hairs a fuskar sa but yau sai gashi almost half of his face is covered with hairs though ba a ƙazance yake ba but yana buƙatar gyara,kamar a kira sa ya amsa but babu hali,tuno da rayuwar su ta rinƙa yi tun kafin su tafi outreach har izuwa ranar da abin ya faru. According to doctor ya ce ba zai farfaɗo ba sai nan da watanni 3-4 masu zuwa,sai ta ju kamar ruwa ruwa a kan kumatun ta sai ta kai hannu a hankali ta taɓa ta ga hawaye ne,cire hannun tayi ta shiga rera kuka kukan da ke da ma'anoni daban daban dan a ƙunshe yake da baƙin ciki,tsana,fansa da wani dalilin na daban da bata san yaya zata yi classifying ba.. Magana ta shiga yi mai tana yi tana jan hanci idanun kuwa basu daina fitar da hawaye ba dan zuciyar ta na cikin ƙunci da baƙin ciki. "Zaid me yasa ka mana haka?ba fah ni kaɗai ka saka a cikin halin damuwar nan ba.Ammi,umma su Abba,yaya jamil,yaya Afzal da Hakim ga baha ga Bilal yaya Lukman ka san kuwa ka saka kowa cikin damuwa da tashin hankali..ta ja hanci ta goge hawayen ta cigaba,dan haka ina son sanar da kai Zaid muddin baka tashi ka kwantar mana da hankali i will never speak to you again did you understand"?kamar da mai rai take maganganun tsawon lokaci bata san da kanta kawai take maganar ba da ta ga kuka da surutun ba zai fishe ta ba sai ta shiga yi mai addu'a ta manta dare ya tsala kuma ba a ɗakin ta take ba dan haka tana cikin addu'ar bacci yayi gaba da ita dan kanta tayi leaning a bedside.. Around 5am ta ji kamar motsin mutani sai ta fara buɗe idanun ta tana ɗaga kan ta a hankali har ta ɗago completely sai bata ga kowa ba lumshe idanun ta tayi dan yana da kyau in mutum ya farka especially in a halin figici ya farka kar yayi wuf ya miƙe dan hakan na iya janyo mai ciwon kai da throughout ranar ba zai sami sauƙin sa ba sai a hankal. Idanun ta a lumshe ta ji muryar Ammi na ce da ita "Baby tashi ki yi sallah asuba ta yi"!!a nan ta buɗe idanun ta dan sai a lokacin ta tuno wai ba a ɗakin ta take ba and 'tashi kiyi sallah asuba ta yi'what does that mean?ohh God bacci tayi a ɗakin sa ko me?ya rasulillahi,kasa ɗaga idanun ta tayi har sai da ta ji Ammi ta shige toilet sai ta miƙe da gudu ta ƙarasa zuwa ɗakin ta tana shiga ta ja ƙofar ta saka mai lock ta haɗa bayan ta da ƙofar tana sauke ajiyar zuciya sai mamakin kan ta take ya aka yi ta kwana a ɗakin sa sai wata zuciyar ta bata amsa da "kin manta abokin aikin ki ne kuma abokin yayan ki sannan yayan aminiyar ki?ai ba wani abu bane dan kin taya shi zaman jinya".at the same time other part of her heart ya bata amsa da"maybe saboda tausayin sa da kike ji ne ya sa kika kwana a chan dan ai ba halin ki da ɗabbi'ar ki bace kawai tausayin sa ne"da wannan amsar ta sami ƙwarin gwiwa har ta shiga ta yi wanka kafin ta ɗauro alwala ta fito ta saka doguwar arab El-Mondy gown baƙa mai adon cream colour saka hijabi tayi ta tayar da sallah da ta idar ta yi addu'oin ta sai ta tsinci kanta da yi mai addu'a in a special way addu'ar take yi fiye da yadda ta ke yiwa kanta a kullum ta daɗe tana mai addu'ar samin lafiya kafin daga baya ta idar ta kawar da kayan sallan. Abin mamaki sai ta yafa gyalen gown ɗin ta duba ƙaramar jakar ta da kayan shafawar ta ke ciki ɗaya bayan ɗaya ta fiddo su duka sai dai abin da take nema bata gan shi ba ƴar ƙaramar tsaki tayi sai ta janyo ɗayar trolley ta duba still babu abin sai ya ɓata mata rai gashi har shida na safe yayi za'a zo a bata magungunan ta ciki kuwa har da seductive drug wanda ta san mudfin ta sha shikenan ita da aiwatar da abin da take so sai dare ko ma washegari dan har yanzu ana bata depressive drug twice daily six na safe da six na yamma dan brain ɗin ta bai gama settling ba at any time tana iya collapsing saboda daɗewar da tayi a kwance cikin shock,. Bata gama tunanin mafita ba ta ji sallama ɗaga kan ta tayi sai ta ga Bahajjatu ne wani miƙewa tsaye tayi da sauri ta buɗe mata ƙofar gabaɗaya tace "Hey where us your makeup kit"!??da mamaki Bahajjatu ta ce "Makeup kit Bilkisu?da asussubahin nan me zaki yi da shi?and wait"!!a nan ta ga shigar ta sai ta dawo kamar dai yadda take da wato Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman sai abin ya ma Bahajjatu daɗi dan an sami cigaba sai ta ce "Ki just bani minti kaɗan zan dawo na baro kit ɗin a gida kin san mai jinya ba ta kwalliya yake ba"daga haka ta fita cikin farinciki da jin daɗi ta bar hospital premises ta ɗau cab zuwa hotel apartment ɗin su.bayan fitar ta Bilkisu ta zauna zaman jiran ta amma sai ta ga kamar da gayya Bahajjatun ta ƙi dawowa on time haka ta rinƙa kai kawo a ɗakin ta gaji kawai sai ta fita tana saka ƙafar ta a wahe ta ci karo da mai bata magani da fara'ar ta ta ce "Good morning ma'am you look beautiful"a dame ta ce "Morning Thanks for the complement"sai ta kalle ta alamun mu tafi amma sai ta ce "No not now i need to clear something i will be back in a jiffy"zata kuma yi mata magana ta wuce ta cikin sauri bata tdaya ko ina ba sai ɗakin Zaid sarai fah ta ga Hajiya Madina a ɗakin amma bata san abin da yasa ta kasa jin ɗar ba ta tura ƙofar haɗe da yin sallama ta shiga.amsa mata Ammin tayi suka gaisa ta tambaye ta ko ta sha maganin ta sai ta ce a'a sai anjima "Baby amma kin san kina wasa da lafiyar ki koh?jiya a nan kika kwana dan kin ga babu kowa da zai hana ki futa ko?me yasa ba kya jin magana ne wai baby ba fah haka kike ba da"ƙasa tayi da kanta sai ta ce "Sorry Ammi zan daina" "Hmm Bilkisu kenan toh na ji amma wannan kwaliyar fah?ta mecece"?sai ta ji kunya ta kama ta me zata ce da ita "Anyway in Zaid kika zo dubawa yi sauri ki duba shi dan ki tafi ki sha maganin ki kar lokaci ya wuce dan very soon ma Abban ku zasu zo bana so su zo su ganki ba a ɗakin ki ba hmm"??amsa mata tayi sai ta tashi ta bar masu ɗakin dan dama jiya tana daga ɗaya ɗakin da masu kula da marasa lafiya suke ta ga shigowar Bilkisun girgiza kai kawai tayi sai ta kyale ta dan ta san babu wani abin da zai faru saboda shi marar lafiyar kamar marar rai yake dan haka ba wani damuwar da ta ji sai ta ƙyale su afterall dama tana son closeness nasu ya ƙaru ninkin ba ninkin ita abin armashi yake mata.. Ɗaga ƙafar ta tayi ta fara tafiya sai ta ga kamar idanun ta na nuna mata wani abu daga gefen comforter da aka rufe Zaid da shi sai ta tsaya tana examining but bata kuma ganin abin ba tana ɗaga ƙafar ta ta kuma ganin kamar movement daga cikin comforer ɗin sai ta ƙara girman idanun ta tana mamaki dan movement ɗin yanzu ya fi na ɗazu rufe baki tayi da hannun ta dan saura kaɗan ta fasa ihu sakamakon abin da ta gani...

0 Comments