IYA RUWA FIDDA KAI CHAPTER 1

IYA RUWA FIDDA KAI CHAPTER 1
"One... two...three.. start" "Again "One...two...three.. place"!!!+ "Goddamn it again"! "One.. two.. three.. place" "Take it easy baby" Cikin hanzari Circulating nurse ɗin da ke tsaye tana ta zazzaro idanu outside sterile surgery field ɗin ta buɗe baki tana cewa "Breathing pattern diminishing" Daɗa himma nurse anaesthetic ɗin ta yi tana ƙoƙarin reestablishing numfashin patient ɗin wanda ke kwance kamar marar rai yayin da take iya ƙoƙarin ta sauran theater team ɗin na ƙoƙarin resuscitating patient ɗin ta hanyar bayar da chest compression at a higher rate of 4:1 sai dai still patient ɗin didn't pick up ƙara rikicewa suka yi a inda ɗaya daga cikin su ta juya ta ce "Increase the speed to 220"gwalo idanu suka yi suna mamaki amma bata ko bi ta kan su ba ta ce a ƙara instead a ƙara zuwa 220 da ta ce sai aka kai 190 wani irin wawan tsawa ta dakawa anaesthetic ɗin "Are you out of the team will you increase the damn speed" muryar ta was a little bit pieced off da alamun anger but atill hakan bai hana cool cracking voice ɗin ta bayyana ba tun kafin ta ɗora da wani kalmar tuni anaesthetic ɗin ta ƙara spead ɗin har ya so ya wuce misali sai da aka mata alamar ta rage yayi yawa jiki na kyarma ta rage tana sauke ajiyan zuciya wani na korar wani. "One...two...three..place"ta manna electrode ɗin a bare chest ɗin patient ɗin ya zaburo ya koma a nan heart beat ɗin ya fara motsawa yana regularizing wanda hakan ya nuna a jikin monitoring machine device ɗin da ke theater suite ɗin,bata daddara ba haka ta cigaba da placimg electrical electrode ɗin nan duk sauran team members ɗin sun sadaukar akan the patient is passing already dan haka a ganin su wahal da kanta kawai take. Ɗagowa tayi ta kalle su ta ga alamun lost a fuskokin su wani irin harara ta banko masu kamar zata duddulo kwayan idanun waje dama ga su nan tubarkallah jiki na rawa suka fara gwaje gwaje yayin da wasu ke gwada blood pressure wasu ke gwada temperature wasu ke auscultating ita kaɗai ke faman resuscitating ɗin babu irin wanda bata yi ba CCM,Mouth to nose,air bag,ƙarshe mouth to mouth resuscitation ta yanke hukuncin yi kallon ɗaya daga cikin team members ɗin tayi ta mai alamu da ido wanda da gani assistant ɗin ta ne ya gane me take nufi ya so ja amma yanayin kallon da take mai ya sa yayi saurin fiddo sterilized gauze ɗin da ke cikin galipot rufe da murfin shi yayi saurin yin amfani da forceps ɗin da ke kan instrument table ɗin yayi amfani da ɗaya forceps ɗin ya warware ya yi place gauze ɗin a daidai bakin patient ɗin yana gamawa ta ɗauke numfashin ta ta nufi daidai bakin patient ɗin bayan ta sa an yi mata ƙasa da face mask ɗin da ta saka babu wata wata ta saita bakin ta akan na patient ɗin ta sakar mai da numfashin da ta ƙumsa jan numfashi yayi ta kuma breathing in-out ta ɗauke numfashi ta kuma saita bakin ta daidai na patient ɗin ta busa mai iskar bakin ta sai ga shi patient ɗin ya numfasa da ƙarfi tuni sauran suka cigaba da aikin suturing da suke yi gudun kar a sami invasion of infection a cikin incide cut ɗin haka ta cigaba da bada mouth-mouth resuscitation ɗin nan har sai da circulating nurse ɗin ta ce "Perfectly done"a sannan suka sauke ajiyar zuciya especially ita dan wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke na samin nasara 5¼ hours ana abu ɗaya duk an fitar da ran samin nasara dan kuwa ba su taɓa yin complicated surgery irin wannan ba first step approach ɗin was successful amma second approach ɗin ya zo masu da inevitable complication wanda babu wanda zai ga patient ɗin ya ce zai rayu dan duk signs of dying patient has been exhibited by the patient dama tun kafin a fara patient ɗin has gave up already sai dai good rapport da ke tsakanin theater team ɗin da patient ɗin ya sa ya sami ƙwarin gwiwar cewa zai fito da ran shi after surgery ɗin.. Akwai wani particular theater team member ɗin da tun da aka fara surgery ɗin yake tsaye ƙeƙam kamar an dasa wani live statue ƙwaƙwaran juyin nan bai yi ba movements ɗin shi was restricted iya wall mounted white latrine da ke haska ko ina a cikin surgical suite ɗin bai ƙara gaba ba haka bai koma baya ba yayi folding hannayen shi cikin shigar complete surgery attire ɗin shi wato dark green surgical gown da hular shi iri ɗaya hannun shi cikin elbow surgical glove ƙafar shi sanye da surgical suite flexible booth wanda ya rufe mai ƙafar shi tun daga tafukan ƙafar sa har zuwa dab da gwiwar sa yayin da sauran theater team ɗin suka saka boot ɗin yakai masu har gwiwa shi a iya gwiwar ta tsaya mai dan tsananin tsayin shi fuskar shi ɗauke da operating google ya haɗe fuskar nan tamau kamar wani wanda bai san abin da ake kira da murmushin fuska ba duk waɗannan tashi faɗin da ta rinƙa yi yana kallon ta cikin tsananin izza da dakiyar zuciya ƙala bai ce da su ba har suka kammala suturing ɗin suka yi cleaning patient ɗin aka gwada temperature,pulse,respiration da blood pressure ɗin shi sannan aka saka shi a wheel table couch aka yi wheeling ɗin shi zuwa post operative room. Scrub nurse ce ta ƙarasa gyara wurin surgery ɗin yayin da circulating nurse ta shigo ta fara praising ɗin su sun amsa mata except surgeon ɗin da ta mata banza ta wuce zuwa tap ɗin surgery room ɗin ta fara cire elbow hand glove ɗin ganin haka ya sa ta yi shiru ta ƙarasa zuwa cikin part ɗin surgeon preparation room ɗin ta yi saurin unbuttoning mata surgical gown ɗin tana yi tana son mata sannu amma ganin babu fuska ya sa ta mazge ta ja bakin ta tayi gumm but dole ne ma ta mata sannun nan dan duk sauran doctors ɗin sun cire hannun su a case ɗin except su theater team ɗin da suka yi performing recent surgery ɗin cikin izza ta goge hannun ta ta cire face mask ɗin,ya salam wata kyakyawar slim innocent creature ta bayyana wacce fuskarta ya kasance doguwa dai dai ƙima ɗauke da dara daran idanuwa masu ɗauke da breathtaking light blue eyeballs yayin da fararen eye sclera ɗin ta suka zagaye attracting eyeballs ɗin ta making them to appear so angelic and uniquely perfect hancin nan karan shi tun daga marabar frontal bone ɗin ta har zuwa gab da upper lip ɗin ta inda a nan ya dakata bakin nan daidai fuskar ta so cute ɗauke yake da lip bam marar shining daga fuskar ta kawai mutum zai gane cewa ilahirin jikin ta haske ne tass dan kuwa fuskar nan babu taɓo ko kaɗan ga alamun hutu nan da ya bayyana a fuskar dan the face is looking so smooth and rough free babu spot ko ɗaya kamar a taɓa jini ya fito ko da ta cire hular kanta dan saka ƙaramar headwear da ke gefen ta well parked neatly appeared dark curly hair ne ya bayyana wanda shi bai kasance a cike ba daidai dai bai yi kaɗan da yawa ba haka bai yi kaɗan ba parking ɗin an bi shi ne da pony style wanda ya sauko har gefen kafaɗar ta baƙi ƙirin ne babu abin kushewa ko da aka gama cire mata gown ɗin ma glowing skin ɗin ta ne ya bayyana mai ɗaukar ido da hankalin mai kallo,scrub wear ne a jikin ta navy blue riga da wando ta cire surgery boot ɗin ko da ta cire surgical boot ɗin sai ta fito doguwar ta samɓal very slim kamar wacce bata cin abinci dan ba wani jiki ne da ita ba sai tsayi da doguwar fuska mai ɗaukar hankali,saka flat surgery shoe tayi wanda yayi covering mata ƙafar ta gabaɗaya da ganin ta ka ga mace marar damuwa a rayuwar ta, ta fito tana ɗaɗaure fuska babu wasa ko kaɗan a fuskar ta ta fito tana mai cewa "Let's meet at the conference room in the next 15minutes"daga haka ta cigaba da tafiya bata kuma furta komai ba takun ta biyar a na shida da zai sada ta da transparent tinted glass full operating room door ɗin ta ji saukar muryar shi a kunnen ta cikin gadara da nuna isa na shi ɗin wani ne ya ce mata "You are a loser and you will always be a loser ki rubuta ki ajiye"za ka rantse ba magana ya gaya mata ba dan duk ƙwazbar ka ƙarya ne ka ce ka ji sautin muryar sa bare ka ce ga abin da ya gaya mata dan he made his voice to be as lower as anything ta yadda daga ita sai shi zasu iya jin maganar. Kallon tsana ta aika mai da shi ta harare shi harara irin na takaici kamar idanun zasu faɗo ƙasa ta buga tsaki ta tura ƙofar ta fita kamar zata tashi sama dan haushi.. Bayan fitar ta daga theater suit ɗin sauran team members ɗin suka fara shiga taitayin su dan sun san yau sun takalo fitinar baby doctor haka suka rinƙa undressing theater wear ɗin suka wanke hannayen su suka fito a nan suke lura da shi shaf sun sha'afa yana ciki dama chan basu da wata kyakyawar jituwa tsakanin shi da baby doctor a duk ranar da aka ce ita ke da surgery toh fa zai zo amma stitches wannan ba zai taya ta da shi ba haka ita ma in dai shine on call kuma yana da surgery toh zata halarci wurin sai dai kuma babu ruwan ta da shi sai dai su rinƙa muzurai wanda shi kuma wawan doctor da ke son ta ya tsani ya ga suna kallon juna a yanzu ma hakan ta kasance dan bayan an gama za'a fita daga theater room ɗin ya dakata yana kallon shi ya ce "Ɗazu me kake gayawa baby na na ga ran ta a ɓace ta bar wurin nan"? Cikin fushi yayi maganar yayin da shi kuma ya mai kallon tsanake kafin ya ce da shi "Well doc,ka ga shiga hurumin da ba naka ba bai dace da kai ba a matsayin ka na wanda yayi rayuwar turai i guess it will be safe for you if you learn how to mind your business in you little world"kaiwa nan ya bar wall ɗin ya shiga cire kayan jikin sa shikuma kamar yayi hauka dan takaici ya tsani ya ga ana raina ma babyn shi ɗazu a wun surgery ɗin nan duk ganin ƙoƙari da himmar da take yi yasa shima ya sami ƙwarin gwiwa amma da fari ya yi losing hope gabaki ɗaya. Juyawa yayi ya kalle shi kafin ya ce "Kuma ka dai ji abin da ta ce mu haɗu a conference room"banza ya mai dan shi fa ya tsani takura kwata kwata a rayuwar sa dan haka amsa ɗaya ya bashi wanda ya san duk daƙiƙancin sa dole ya rabu da shi "Wasu dai haka suke daƙiƙai ana ƙin su suna nacewa"daga haka ya sa kai ya fice Kenan shi ne daƙiƙin wato shi ke ɗawainiya da son baby doctor amma ita bata damu da shi b?toh ai babu komai ko da zagin shi zata na yi ba laifi bane duk a cikin soyayya ne moreover yadda yake ganin doctor ZM ke da shegen siffar ɗaukar hankalin nan ya sa shima ya fara zuwa gym duk dan ya buɗe ya haɗa abs ɗin karfi da yaji koh zai kai kamar shi dan a tunanin shi ta hakan kaɗai zai iya ɗauke hankalin baby doctor ɗin shi alhalin ya san ba ta kanshi take ba amma shegen kishin tsiya ya sa yake son haɗa kan shi da doctor ZM thinking that he can beat him after all shima ai ɗan masu kuɗi ne in ma kyau ne toh dakaɗan doctor ZM ɗin ya fishi amma shi ya ma fushi hasken fata kyau kaɗai zai nuna mai da well developed body structure ɗin da yake da shi da ɗan banzan muscles kamar basamude dan shi haka yake kiran shi da basamude he just hate him so much kawai bai da yadda zai yi da shi ne da ya sa an nesanta su da baby doctor ɗin sa.. Bayan kamar mintuna 15 suka hallara a conference room ɗin gaba ɗayan theater team ɗin. Juyawa tayi ta kalli ko ina bata gan shi ba dama ta san ba zuwa zai yi ba dan haka ta fara zazzaga masu kwandon bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba sannan ta hana su furta kalma ko ɗaya lallai sun janyowa kan su ruwan dafa kansu da kansu dan masifar yau tafi ta kullum gata nan dai ƴar tsirit babu wani jikin da mutum zai gani ya ce zai tsorata amma fuskar nan da ke ɗaure tamau a kulliyaumi ya sa dan dole a rankwafa a daraja ta dan bata son raini duk wata mu'ammala ta mutunci concerning her work tana kiyaye shi bata shiga sabgar da ba tata ba haka itama ta tsani a shiga sabgar ta in ba ita ta gayyace ka ba shi yasa ba su jituwa da doctor ZM saboda kowa na da principles da policy kamar sarkin kansa da suna da hali ma da sun saka an raba masu wun aikin saidai iyayen su sun hana dan haka a dole kawai suke aiki tare ba dan ransu na son hakan ba. "Baby ga ruwa ki sha na ga ran ki ya ɓaci da yawa"ya miƙa mata glass tumbler wani irin kallon wulaƙancin da ta aika mai da shi haɗe da buga tsaƙi ya sa sauran durƙusar da kawunan su suna mai dariya ƙasa ƙasa dama sun san za'a yi haka on normal basis ma da ba'a taɓa baby doctor ba ya aka ƙare bare yau da aka taɓo ta shi kan sa rashin kamun kai ke damin sa if not ya dage dole sai ta saurare shi ita kuwa yadda take ji da izza da kan ta bata da lokacin sauraron samari duk wani kyau da izzan ka baka kai matsayin ta sakaya maka saboda waɗannan qualities ɗin ba,sau nawa sauran male doctors ke kawo mata gayyatar son su amma tsagaben yarfata su da take yi kamar ba mutani masu ƙima ba yasa kowa ya ja girman shi ya fita harkar ta duk wata mu'ammala da zai shiga tsakanin su baya wuce na aikin subayan wannan babu ruwan su.shi shi kaɗai ya nace dan haka shi ɗin ne ya zama garbage bin ɗin ta madaɗin ya kiyaye ta sai ya ƙi ya amince da karbar duk wata wulaƙancin da ta ke mai shi yasa a duk sanda ta mai hakan mutani kan mai dariyar wautar sa saidai shi ko a jikin sa dan shi bai ganin laifin baby doctor ɗin shi. "Me kuke ma dariya"?ya faɗa yana zazzaro masu idanu kamar wani damisa,dan haka suka yi shiru suna mai danne dariyar su amma da sun sami sarari lallai zasu sheƙe da dariyar shiriritar sa. Kallon shi tayi cikin jin haushin shashancin sa ta ce "Daga yau sai yau in ka kuma kira na da sunan baby a yayin da ake abu mai muhimmanci duk abin da na maka kai ka ja wa kanka wawa kawai"ta zabga mai tsaki instead yayi fushi sai ya bige da murmushi yana washe baki "Yes baby"wani hararar ta zabga mai sai yayi saurin rufe bakin shi ya ce "Sorry baby doctor na daina"a nan ta mai kallon wofi ta cigaba da masifar tana ƙin haɗa kan da aka yi a theater suit har da alƙawarin dakatar da su zuwa ranar da suka koyi rashin yin panicking a middle of surgery haƙuri sosai aka shiga ba ta ta ƙyale su kwatsam sai suka ji buɗewar ƙofar conference room ɗin gabaɗaya juyawa suka yi dan ganin wanene ya shigo a makare sai dai ganin wanda ya shigon ya sa suka miƙe baki ɗayan su suna gaida shi cikin girmamawa da gani dai shi ɗin babba ne wanda ya cancanci ban girman da aka mai,murmushi ne fal fuskar shi ya ce da su su zauna suka zazzauna. A kiyasti dai mutumin ba zai wuce 60years ba fari ne da shi tass kasancewar sa tsoho wanda shekaru suka fara ɗan ja masa bai nuna a jikin sa ba dan jin daɗi da hutu sun runfe hakan sai ma wani yarinta da ke nunawa a jikin nasa dan in aka gan sa za'a yi tsammanin ɗan kimanin shekara 49-50 ne sam 60years ɗin bai yi fitting ɗin shi ba in ba wai faɗa yayi ba to a ɗan 50years za'a na kallon shi,kyakyawan dattijo ne wanda ya kasance cikakken dan boko da sanin ilimin zamantakewar ɗan adam dogo ne shi sosai kuma tsufar shi da tsayin shi basu saka shi rakwafawa ko kaɗan ba yana nan a tsaye cur abin shi idan mutum ya kalle shi ya kuma kalli baby doctor ɗin nan toh babu tantama koh second thought za'a iya concluding cewa jini guda ke running through vein ɗin su dan kamannin ya ɓaci da yawa kama ce ta sosai wanda za'a ce wannan mahaifi ne ita kuma ɗiya ce bambancin ɗaya ne shi fuskar shi da rahama ita kuma masifa ce fal a kan fuskar ta. Bayan ya zauna ta gaida shi "Good day dad"amsa mata yayi da murmushi dan ya ji rahoton scene ɗin da ya gudana a surgical suit kuma ya san mai kwatar surgical team a hannun ta yau sai ikon lillahi ko kuma shi shi yasa yayi takakkiya ya zo har conference room ɗin "Baby doctor me aka miki ne yau na ji muryar ki har waje da fatan dai ba failure aka samu a process of surgery ɗin ba"?wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin calming kan ta dan ta san duk bambamin ta she can't include her father in it sai dai ta sauke shi akan su. "Dad talk to them because am tired of warning them to stop panicking whenever a surgery is going on amma yau ɗin nan sun wuce limit ɗin sa dan haka duk hukuncin da na masu no one among them should question my act"kaiewa nan ta zauna tana sauke numfashi. Murmushi yayi irin na manya kafin ya kalle su cikin sakin fuska ya ce da su "And me kuke cewa a duk lokacin da kuka yiwa boss ɗin ku laifi"? Cikin chorus suka ce "We are sorry forgive us"jinjina kai yayi cikin gamsuwa ya kalle ta ya ce "Baby doctor kin ji abin da suka ce"? girgiza kai ta yi ta haɗe girar sama da ta ƙasa "Good what did you do as the chief head then"? Bata so furtawa ba amma haka ta daure ta furta "Let it be"cikin jin daɗin ɗiyar ta shi ta ji maganar shi ya ce "Allah ya maki albarka"ya juya gare su ya ce dasu "You guys can go amma kar ku bari hakan ya sake faruwa again ina dr ZM"? Suka rasa abin cewa yayin da ita kuma ta ɗan yi leaning da kujerar da take zaune jira kawai take su fita ta saka mai kukan gajiya da tayi da aiki tare da su ita ya haƙura ya tura ta ɗayan asibitin sa ta yi aikin ta a chan in ya so sai shi dr ZM ɗin da na nace mai ya bar shi a nan.jin yayi tambayar shi yasa ta daɗa mayar da hankali dan jin amsar da zasu bayar sai dai kafin su ba da amsar ya riga su ta hanyar cewa "Am here sir"cikin mamaki suka juya auna kallon shi ita kanta buɗe lumsassun idanuwar ta tayi ta zuba su a kan shi shima kallon seconds ya mata ya ɗauke fuskar sa ya mayar kan wannan dattijon wanda ya faɗaɗa murmushin sa ya tambaye shi "Where were you ban gan ka cikin conference room ɗin ba tun da na zo"kallon sauran yayi sun gane me yake nufi dan haka suka fita ya tura ƙofar ya zauna kusa da shi ya ce "Dad ban sami damar halartar meeting ɗin ba ne sakamakon emergency call da aka min a skylight yanzu na dawo"mamakin ƙaryar da ya zabga take yi mutumin da yake asibitin nan tun ma kafin a fara meeting ɗin zai ce wai ya wani tafi skylight lallai wasu lokutan al'amurar shi na bata mamaki gashi dai namiji a tsaye amma some times yakan bata mamakin kare kansa da yakan yi in ya aikata ba daidai ba gashi mahaifin ta baya ganin laifin sa Murmushi ya mai kafin ya ce"Zaid Allah ya maka albarka irin ayyukan da kake yi da ɗawainiyar da kake yi between this three hospitals ban da komai na cewa gare ka sai albarka da maka fatar alkhairi indeed my friend has trained and raised a kind hearted son ina fata wataran alaƙar mu ta ƙara ƙarfi fiye da haka"haɗa ido suka yi shi da ita wai me yasa addu'ar iyayen su bata wuce wannan ne?basarwa suka yi kamar babu komai yayin da shi kuma ya amsa mai da "Amin dad"daga haka ya juya ya kalle ta ya ce "Baby ya maganar outreach ɗin da zaku tafi a garin Adamawa have you finish your preparation"? Ya ilahi wai me Abban ta ke nufi ne da batun wannan outreach ɗin a ce gabaɗaya asibitin an rasa waɗannda zasu tafi outreach sai su yau da ita da wasu ne abin zai zo da sauƙe amma ita da shi how?ina ba zata yarda ba,ɗagowar ta kenan dan sanar da shi cewar itafah ta fasa amma kuma sai ya rigata magana "Dad ta gama tun last week muka gama komai da yadda abin zai gudana within 3week ɗin baka da damuwa in dai ta nan ne"ya ida yana mai sakar mata da murmushin mugunta dan ya rantse sai ta tafi outreach ɗin nan ko tana ra'ayi ko bata ra'ayi kuma ya san ya gama ɗaure ta da jijiuoyin jikin ta dan bata iya jan magana muddin yana wurin dan izza da jiji da kan ta ya sa bata son yawaita magana a gaban sa dan haka shiru ta yi tana kallon ikon Allah "MashaAllah Alhamdulilah toh ai ina ganin babu wata magana kuma tunda kun gama komai about your accommodation kuma komai has been settled jiran ku kawai ake"ɗagowa yayi ya kalle shi cikin girmamawa ya ce "But dad ai har accommodation ɗin has been taken care of by me in ba zaka damu ba nake ganin tunda ni na kawo shawarar ai ni ke da alhakin kula da lafiyar ta dan haka na yi booking mata accommodation already sai dai in ita ce ta ce bai mata ba"taɓdijam wai me ya maida ta ne a gaban mahaifin ta ya ke shararo mata zance cikin zance bayan ya san ba zata iya ja da maganar Abban ta ba amma ya mata shigar sauri?kamar ta fashe dan haushi "Ikon Allah wannan yaro da ƙoƙari ka ke ai babu wani abin da zai saka ta ƙin girmama alkhairin da ka mata dan haka babu komai with you my baby is safe na sani so nan da 10days zaku tafi outreach ɗin Allah ya maku albarka ya raya mana ku"da amin suka amsa shi kuma ya miƙe ya fita yana cewa "Baby mu haɗu a gida in kin huta akwai maganar da zamu yi ok"? "Yes dad sai na dawo"murmushi yayi ya fita abin shi,yana fita ta daɗa haɗe fuskar nan tayi kicin kicin da fuskar ta yi kamar bata san da zamar sa ba sai da ya gyara murya shima ya haɗe fuskar sa "Idan kin gama shirin naki just let your foolish boyfriend know about it"yana kaiwa nan ya miƙe ya fita ya bar ta cikin tunani ta yaya ma zasu zauna inuwa ɗaya da shi shi jin kai itama jin kai hmm abin da kamar wuya. Ko da ta chanza kayan ta zuwa fashionista black joude arabian gown ɗin ta sai kyawun ta ya daɗa bayyana ta fito a siririyar doguwar ta yarintar ta ya fito sarari sosai doguwar heel ce a ƙafar ta sai jakar da ke hannun ta ɗaya hannun ta riƙe da maƙullin motarta ta fito ta nufi car park ta buɗe motar ƙirar toyota corolla XL ta saka jakar a kujerar zaman banza ta dawo ta buɗe ɗaya side ɗin zata shiga kenan ta hango shi shima zai shige cikin tasa motar harara suka bankawa juna kowa ya shige motar sa suka fita yana gaba tana baya har suka isa inda zasu tsaya a inda shi ya shige ɗaya gate mai kallon inda ta shigw kenan makwafta ne su kamar zasu tayar da anguwar da horn ɗin da suka saka cikin sauri kamar haɗin baki aka zo aka buɗe masu gate ɗin a fusace suka shige ciki aka mayar aka rufe. Shigar ta falon kenan ta tarar da su suna abin da suka saba yi ita dai Allah ya bata kyautar iyaye a ko da yaushe kamar wasu yara suke yanzu ma dai umman ta ce cikin shigar fitted gown an sha kwaliya an zubo suman nan har gadon baya she is just looking perfect kamar wata wacce bata manyanta ba yayin da Abban ta ke cikin shigar ƙananan kaya kamar ba shi yazo hospital ɗazu ba cikin shigar manya duk sai suka koma mata wasu teenagers "Prof na gaya maka baby ba zata tafi wannan outreach ɗin ba muddin ba tare da company ɗin wani ba i can't risk that"tana maganar ne tana wani mammatsewa yayin da shi kuma cikin son impressing ɗin ta ya ce "Haba no heart she is not going alone tare da zaid zasu tafi that is in kin amince amma in bai maki ba sai a yafe tafiyar"kamar wani wanda yake bauta mata haka yayi maganar ga mamakin sa sai ta saka dariyar manya ta ce "Common are you serious"? Cikin jin daɗi yayi impressing ɗin ta ya ce "Yes of course"ta rungume shi tana cewa "Na amince zaid is a good boy zai kular min da baby na"daɗi ya ji sosai inda ganin abin na su ba mai ƙarewa ba ne ya sa ta gyara murya wanda hakan ya dawo da su daga jubilation ɗin da suke yi da sauri suka gyara zama murmushi ta masu ta ce "Good evening love birds"hararar wasa mahaifiyar tata ta mata ta ce "Baby me yasa kike da son yi mana shishigi ne wai kin dawo instead ki tafi apartment ɗin ki sai kuma kika tsaya kallon mu gashi kin hana mu ƙarasa hirar mu ko prof"? Ta ƙarasa tana kallon direction ɗin shi inda yayi saurin girgiza mata kai. Dariya kawai ta masu ta wuce tana jin daɗin ganin farincikin iyayen ta ko da kuwa sun ɓata mata rai ne da zarar ta birkice masu zasu sauko su fara rarrashin as if ita kadai ce ƴa a gidan tana alfahari da su duk da ma dai Abban ta na yi wa umman ta total obedience kamar wani wanda bai girma ba ita kuma umman ta na ruling gidan according to her desire sai dai ta san duk a cikin soyayya ce dan da babu soyayya duk hakan ba zai faru ba.karasa haurawa tayi tana fatan wataran in ta shirya neman abokin rayuwa ta sami kamar Abban ta dan a tarihin gidan su irin rayuwar da ya gabana kenan she just pray that the epic will repeat it self a kan ta... Shima da shigar sa kenan ya tarar da iyayen shi zaune bakin swimming pool an sha ƙananan kaya ana zuba soyayya ko ba'a faɗa ba a nasu fannin dai kusan abin da ke faruwa a gidan su bany doctor ke faruwa a nan dan mahaifiyar shi ce ke faman bayar da command akan abin da za'a kawo masu in suka tambayi mahaifin sai ya ce duk abin da ta zaɓa ya mai alhalin bai da niya amma dan gudun ɓacin ran ta sai ya basar girgiza kai yayi ya nufo su ya tsaya masu a kai kamar soldier sai da mahaifiyar ta sa ta juyo ta lura da dawowar shi cikin sauri ta miƙe tsaye tana cewa "My boy yaushe ka shigo ban sani ba me za'a kawo maka kafin ka yi wanka"? Instead ya bata amsa sai ya haɗe rai kamar bai iya dariya ba ya ce "Ammi sau nawa nake hana ki ke da Abba yin irin waɗannan shigar?ban ce maku in zaku yi ku bari sai ba mu nan a gidan ba"? Ya ida maganar cikin sanyin murya Cire hannun ta tayi daga kan kyakyawar fuskar sa wanda yake nan exactly irin nata ta juya ga mahaifin sa ta ce "Only ka ma ɗanka magana yana mana shishigi a rayuwar mu da yawa in bai son ganin soyayyar mu me zai hana shi zuwa ya samo tasa matar ta yadda ba zai rinƙa ganin namu soyayyar ba"ta ida tana batsewa a dole ya ɓata mata rai cikin hanzari ya miƙe tsaye dan cika mata umarnin ta ya ce "Haba zaid ya zaka na saka Ammin ka da ni a gaba kamar kai ka haife mu tare fah ka gan mu ta yaya kake son raba abin da Allah ya haɗa?toh kar ka sake ka jini ko"? Ya gama maganar yana mai signal irin yayi haƙurin nan murmusawa yayi dan yasan Ammin sa ce ruler ɗin gidan dan haka Abban sa has no say sai abin da ta ce well duk a cikin soyayya ce ya faɗa a ran shi yayin da ya juya ya fara tafiya ya tsinƙayo muryar ta tana cewa "Ni wai only yaushe yaron nan ka ce zai yi tafiya ne"? "In the next 10days kuma tare dababy doctor zasu tafi ai yayi ko"? Cikin murna ta ce "Kana nufin da ɗiya ta zasu yi tafiyar"? Cikin murna ya ce "Eh tare zasu tafi" "Ohh Allah ya kai su lafiya i have to call hajiya Zeenat dan mu raba wannan farinciki tare miƙo min waya ta"ya miƙa mata yana farinciki shima yace "I have to call prof mu raba farincikin mu"hararar wasa ta mai ta ce "Whatever ni damuwa ta ma yaron nan ya tafi ya bar mu mu sake" Murmushi kawai yayi ya wuce zuwa ciki dan iyayen shi are always behaving so childish bai san yadda zai yi da su ba......... _Toh ya kuka ji takun farkon?mu cigaba ne ko dai mu dakata? yawan amsoshin ku da sharhunan ku su zasu bada cikakkiyar amsoshin ku da amincewar ku_ Dr Zaid Maher Mahmud shine cikakken sunan sa ɗa ne ga Dr Maher Mahmud retired Dr mammalakin asibitoci biyu da ɗan sa ke running wato Dr Zaid,ya kasance babban ɗa ne ga Dr Maher Mahmud wanda ya ke da ƙanne uku Afzal wanda ya ke aiki a Canada da wani babban asibiti a inda mahaifin sa ya matsa akan sai ya dawo nan ƙasar Nigeria amma ya ƙi a cewar sa tunda yayan sa na kula da asibitocin sa na nan no need ya dawo haka ya ƙyale shi kasancewar mahaifiyar su ta saka bakin a bar shi har sai yayi deciding, Hakim shine ɗa na uku wanda ya ke kan yin masters ɗin sa a science and technology a ƙasar Qatar sai autar su Bahajjatu wacce ita ce sa'ar baby doctor kuma babbar aminiyar baby doctor tun yarinta kasancewar tare suka taso har rana ita yau amintakar su na nan tana running babban fashion company na kan ta wanda mahaifin ta ya buɗe mata. Gidan su ya kasance strict free home very simple and unique home babu takura da hantara na kasa na girmama na gaba da shi akwai ginanniyar ƙauna da shaƙuwa a gidan tsakanin su ilimin addini da na zamani daidai gwargwado akwai fahimta mai ƙarfi a tsakanin iyaye da ƴaƴan na su. Dr Zaid da ya zama babban ɗa a gidan ya lashe gurbin babban yaya a gidan kuma babban ɗa very simple and jovial brother and a son bai haɗa ƙaunar kid sis ɗin sa da na kowa dan haka ma duk mai neman wani abu a wun shi a cikin ƴanuwan na ta ke bi ta wurin ta dan ita ce ƴar gwal ɗin sa since she is the only girl a gidan she is just 24years amma a hakan a wun shi a ƴar 5years yake ɗaukar ta ta yadda yake zuba mata sharuɗɗan irin saurayin da zata saurara a haka kuma ta ke bi dan duk hutu da arziƙin ki muddin ka zo mata da abin da baya cikin sharuɗɗan yayan nata toh ta haƙura da kai kenan sai dai ka nemi wata dan yadda yayan nata ke ji da ita haka ma ita kanta.. abu ɗaya ne ya kasa hana ta shine amintakar su da baby doctor dan kuwa ya buga ya buga har fushi yayi da ita sai dai haka ya haƙura ya bar ta dan ƙarshe shi ya koma rarrashin ta as strong head ɗin ta in ya motsa baya jin lallami shi kuma bai iya ɗaukar fushin da take yi da shi he just doesn't know how amma jinin shi ne kawai bai haɗu da na baby doctor ba dan tun yarintar su yake ganin taurin zuciya irin na ta kwata kwata when it comes to him ba ta da sauƙi ko kaɗan bata raga mai in ya ce 'a' sai ta mayar mai since they are all neighbours kusan a gidan su take yini dan mahaifiyar su Hajiya Madina na bala'in ƙaunar ta saboda ƙaƙƙarfar friendship relationship da ke tsakanin ta da mahaifiyar baby doctor wato Hajiya Zeenat,ganin hakan ya sa ya ke raga mata but in da ta shi ne yarinyar ta daina kusanci da ahalin shi but unluckily for him hatta mahaifin shi na ji da ita being his best friend only girl child ga ƙannen shi na son ta saboda hazaƙar ta da ilimin ta tunda both houses ɗin gidan boko ne sai relationship ɗin su ya yi ƙarfi daɗin ƙarawa irin career ɗin iyayen su suke yi sai abin ya burge iyayen har ma suke fatan wataran ala'ƙar su ta karfafa ta fi haka fatan su kenan amma ga su waɗanda ake ɗorawa hope ɗin ba haka ba ne dan a kulliyaumi idan zasu haɗu da juna toh babu alkhairi is either a rabu da juna ana dasa ma juna magana ko kuma a rabu ana aikawa juna mugayen kallo, Dr Zaid ya kasance mutum ne shi mai son girma da kamun kai hakan ya samo asali ne sakamakon zurfin karatun da yayi a ƙasar balarabe wato Dubai dan sanin mutunci da ƙimar ɗan adam ya ƙare a ƙasar larabawa sai dai ɗaiɗaiku da ba za'a rasa ba masu ɓata ƙas, rayuwar sa a chan ya sa ya yi adopting halayyar su dan fah shi bai cika son raini ba bare shishigi a al'amurar mutani over 12years yana ƙasar dan ko da ya kammala karatun sa da su ya fara aiki until his momma mounted pressure on him kafin ya dawo ƙasar shi ko da ta ga abin na son repeating kanshi akan Afzal sai bata wani damu ba since her boy is close to her kuma shi Afzal ɗin ya nuna mata bai da niyar dawowa yanzu shi yasa ta sa mahaifin su ya bar shi kawai tunda bai ra'ayi. Kwata kwata bai wuce 33years ba very young gentile and hard working guy dan shi ke handling hospitals ɗin iyayen na shi da na mahaifin shi da na aminin mahaifin nashi wato Dr Muhammad Sulaiman dan duk ƴaƴan shi babu wanda ya karanci medical line ganin haka ga shekaru na ja ya sa Dr Maher Mahmud bashi shawarar ɗora Zaid akan wanda za kular mai da asibitocin sa har kafin baby doctor ta kammala karatun ta ya ko ji daɗin shawarar dan haka ya tuntuɓe shi da maganar akan in babu takura sai dai ya ji daɗin amsar da ya bashi na ce mai da yayi ai shima ɗan shi ne dan haka duk yadda ya ga ya dace a wun shi ba matsalar komai tun daga lokacin ya cigaba da kular mai da asibitocin sa +na mahaifin sa it wasn't that easy for him gashi ɗan uwan shi yaƙi dawowa sai lokacin da baby doctor ta dawo sannan abubuwan suka mai sauƙi but still wannan baƙar tambarin ƙin da ke tsakanin su ya sa instead of them to be close and work hand in hand with each other sai suka kuma tsanar juna because shi yana nuna mata ya rigata zuwa system ɗin muddin girman kan ta ba zai saka ta saukowa ta nemi assistance ɗin sa ba toh kuwa sai dai ta rinƙa yin abubuwan ta ita kaɗai dan shi ba zai taɓa saka hannun sa a abubuwan ta ba hakan ba ƙaramin ci mata rai yake yi ba ganin ita da asibitin mahaifin ta amma ana mata iko da mulki gashi mahaifin nata bai shirya ganin abin da ke cikin duhu ba mahaifiyar ta kuwa bata son jin negative side ɗin Dr Zaid sanar da ita abin da ke faruwa is a total waste of time. Bilkisu Muhammad Sulaiman shine ainihin sunan ta wanda aka fi sani da baby doctor,ita ce ɗiya ta uku a wun iyayen ta su biyu aka haifa lokaci guda ita da twin brother ɗin ta mai suna Bilal akwai babban yayan ta mai suna Jamil wanda yake age mate ɗin Dr Zaid kuma aminin sa but shi ya yi aure har ma da baby ɗin su Zarah kuma shi ɗin navy ne tun fari mahaifin shi ya so ya karanci medicine amma ya nuna interest ɗin shi ba a nan yake ba shi yasa ya rabu da shi,mai bi mai shine Lukman mai aiki da Nigerian custom shima haka mahaifin sa ya so ya bi medical line amma ya ki,abin ya dami mahaifin na su dan shekarun sa sun fara ja but babu mai jan ragamar asibitocin sa not until lokacin da Zaid ya fara tafiyar mai da abubuwan sa ganin haka ya sa yayi ƙoƙarin ganin ɗiyar sa ta dage a medical line ɗin dan dai ta zama mai share mai hawayen shi wani abin dole sai naka daman toh a nata ɓangaren ma haka ne she dearly loves her dad dan haka ta tashi da ƙudirin maye mai gurbin da yayyen ta suka kasa because even her twin brother bai amince ya hau medical line ɗin ba instead ya je ya karanci banking ita kaɗai ce ta bi line ɗin mahaifin ta shi ya sa ya fi fifita son ta akan yayyen ta bugu da ƙari sunan mahaifiyar Dr Muhammad gare ta. Yarinya ce ƴar shekaru 24 wacce ta sami takardar zama cikakkiyar likita at early age yarinya ce mai kaifin basira da ilimi wanda ilimin nata ya ke zame mata makamin yaƙar samari masu kawo mata hari da farmaki dan duk ilimin ɗa namiji muddin ya kawo mata shiriritar wai son ta yake toh tun daga lokacin ya zama marainin wayon ta dan fah ita maza sam ba su layin ta as for now tana da burin farantawa mahaifin ta dan haka batun saurayi bai gan ta ba. Fitinannen da ya addabe ta ya ishe ta a rayuwa kuma bai da niyar rabuwa da ita duk wulaƙanci da cin kashin da take mai amma ya naniƙe mata shine Dr Aslam yaro ɗan gatan Mama da Baban shi shi kaɗai suka haifa a duniya dan haka suka yi over pampering ɗin shi abin da yake so shi za'a mai in fact bai da self discipline a haka ya taso a gidan su yayi karatun sa a ƙasar barure ƙasar London ya taso da ratuwa irin ta masu jajayen kunne bai san wannan abin yayi ba mo a'a bai yi ba in dai shi ya mai toh shikenan.dawowar shi ƙasar ya haɗu da baby doctor a wani medical conference meeting wanda zallan doctors ne suka haɗu dan ƙarawa junan su ilimi a inda a nan ya ji kawai ta mai he thought it would be an easy task since shi ɗin ɗan gidan manya ne not knowing that ita ɗin men headache ce yayi yayi ko friendship ne su haɗa ta mai banza ƙarshe dan fitina sai da ya san yadda yayi ya sa mahaifin ta ya bashi gurbin zama ma'akaci a asibitin da take running actually shi kan shi mahaifin nata ya ji mamaki kasancewar ya san shi kuma ya san irin gata da daular da yake ciki toh dan me zai zo neman alfaar yin aiki a ƙarƙashin shi. Tun da ya sami aikin nan ya rinƙa ɓarin ƙafa since he is from a free home babu wanda ya takura ko ya tsaurara wa decision ɗin sa tunda ya ce yana jin daɗin aikin da zai fara so let it be suka yi supporting ɗin shi a gefen baby doctor kuwa abin bai mata daɗi ba sai dai da yake ta kasance ƴa ce mai biyayya ga umarnin mahaifin ta sai ta amince amma ba wai dan ran ta na muradin hakan ba..haɗuwar su ta farko a office da shashancin ya tunkare ta ta ɗaga mai ƙafa thinking that he will change amma haka abin ya cigaba da repeating kanshi sai a wani faithful thursday da ta kwance mai notice ɗin bala'in ta ya ga fah muraran fitinanniyar kan ta ne sai ya ɗan yi sanyi madaɗin ya fita harkar ta sai ya cigaba da bibiyar ta ita kuma mutunci mahaifin ta da take gani ya sa bata kuma warware mai tsakanin zare da abawa ba dan ko na farkon da ta mai an kai ƙararta wanda take da tabbacin Dr Zaid Maher ne dan shine mai liver ɗin kwashe stuff ɗin office ya mayar gida ma mahaifin ta gashi he knows that her dad is her weakness bata iya jayayya da shi.toh fah tun daga ranar da ya ga ya kira ta da Beelove bata yarfa shi ba sai ya cigaba wataran ya ce mata Beelove wataran ya ce mata baby abin na baƙanta mata rai dan dai ita ta san babu inda zata kai shi dan waɗanda suka fi shi tsari,fasali da hankali ma ta watsa su bare shi da ba cikakkiyar ilimin addini gare shi ba. Wani abu da ke harzuƙa Dr Aslam shine ganin irin special attention da mahaifin baby doctor ke bawa Dr Zaid dan komai ya taso sai ya ce a nemi Dr Zaid ko Dr Bilkisu da ke ɗiyar shi bai wani cika kiran sunan ta ba sai Dr Zaid ganin kusancin su yayi yawa gaahi shi kuma so yake ya share wa kan sa hanya a wun Dr Muhammad Sulaiman dan ya amince ya bashi auren baby doctor amma ya ga hankalin sa ya karkata ga Dr Zaid sai ya fara kishi marar dalili da Dr Zaid duk a tunanin sa hala akwai wani hidden relationship ne tsakanin Dr Zaid da Dr Bilkisu wanda ya sa Dr Muhammad ke karkata akalar shi zuwa ga Dr Zaid kuma abin da ya kasa ganewa shine babu wata kyakyawar jituwa da fahimta tsakanin Dr Zaid da Dr Bilkisu a haka yake masu kallon kamar masoya ne su saboda tsabagaren girman kai da izza da ke ɗawainiya da su su biyun da haka yake ƙoƙarin ganin ya ƙure Dr Zaid a komai tun daga dressing har kwarewa a aiki sai dai ya makaro dan duk moves ɗin shi Dr Zaid ɗin ya gano da yake shima ɗan kan shi ne sai ya bar shi a haka ya ta wahalar da kan shi ya mai biris kamar bai ɗago komai ba shi haushi ma yake bashi ganin wannan ƙanƙanuwar yarinyar yake ma wannan haukar yarinyar da bata ma san da zaman shi ba abin da yake saka shi sakar mai maganganu kenan a duk haɗuwar da zadu yi amma da yake sakarai ne bai wani ɗaukar abin chan ciki. Sunan ta na baby doctor kuwa ya samo asali ne daga mahaifin ta wanda shi ya laƙaba mata shi kasancewar ta very smallish and young and she was able to acquire a doctorate qualification at a very tender age she tressure and value the name sosai hakan ya sa tun mahaifin ta ke kiran ta da sunan tana amsawa har ya kai ga sunan ya bi ta ko a gida ne,family ɗin su ne,neighbours ɗin su har office da sunan ake kiran ta dan fah ko fushi take yi aka kira ta da sunan takan huce dan tana respecting sunan sosai shi yasa da Dr Aslam ya gane ya ke mata abu son ranshi dan ya gano makarin ta sai dai still in tana jin zazzagar ta bata ɗaga mai ƙafa ko da kuwa sau dubu zai yi bitar sunan ta a bakin shi ba sassauta mai take ba sarai ta san tarihin shi abin da yake daɗa ƙara mata ƙarfin wulaƙanta shi kenan wai ko zai yi fushi ya rabu da ita amma ya ƙi dan jaraba ƙarshe fita a harkar shi ta yi ko da theater take da shi bata kiran shi yayi assisting ɗin ta yadda bata gayyatar Dr Zaid sai dai in dan kashin kan sa ya zo ya mata tsayuwar sojoji toh haka shima wannan yadda ya zo ya saka hannu haka zata share shi babu uhm ko uhuhm illah in ya harzuƙa ta da zarar sun fita ta balbale shi ta wuce abin ta haka zai rinƙa bata haƙuri kamar marar zuciya abin ba ƙaramin ƙona ran Dr Zaid yake yi ba shi yasa ya ji ya ƙara ƙin baby doctor gashi ya rasa ta inda zai ƙuntata mata dan ta dawo cikin hayyacin ta ta daina wulaƙanta maza ta rigada ta siye imanin family ɗin shi baki ɗaya dan kamar wasar asiri duk babu mai son jin laifin ta they believe that she is a genus dan haka sun fi alaƙanta rashin jituwar Dr Zaid da baby doctor a matsayin rashin fahimtar junan da basu yi ba ne dan shi ya kasance irin natsatsun mazan nan masu hankali da sanin ya kamata haka Itama ta kasance quite simple lady marar son jayayya da maganr manya especially iyayen ta in akwai abu na farko da Hajiya Madina ke matuƙar so shine respect wanda tuntuni ta hango hakan tattare da baby doctor shi yasa ta aminta da abotar su da ɗiyar ta Bahajjatu tun yarinta har yanzu again silently she is praying for a special day that will come da zata haɗa zuri'a da ahalin Dr Muhammad Sulaiman bata san cewa iyaye mazan sun riga iyaye matan yin wannan tunanin ba tuntuni dan haka itama Hajiya Zeenat ta gama haɗa nata tunanin suka sanar da juna murna suka yi sosai ganin tunanin su ya zo ɗaya sai dai basu bari mazajen su sun sani ba wai tunda su ke juya su su zuba masu idanu kawai dan jin me zasu ce in sun tuntuɓe su da batun auren ƴaƴan separately akan in amsar bai zo masu yadda suke so ba sai su juye maganar sun san dole su amince da su a kan wannan yarjejeniyar suke.. Ana zaune ƙalauya ƙirƙiro da wani tafiyar outreach har zuwa Adamawa a Adamawar ma chan cikin yankin Koma inda ya san babu wanda ta sani a chan dole shi da ya ƙirƙiro tafiyar shi zata na bi a lagwas har su gama su dawo wanda da biyu yayi arranging ma tafiyar na farko shine ya haɗu da sanyin idanuwar sa na biyu kuma ya saita baby doctor kafin su bar ƙauyen. Ko da ya sanar da iyayen shi akan outreach ɗin sun jI daɗi ƴaƴan su sun yi kaifin basira dan shi ce masu yayi decision ne that was made between the two of them da labari ya isa kunnen ta rasa abin cewa ta yi dan dai the last time she checked ba su taɓa samin conversation mai ma'ana a tsakanin su ba na good 2minutes sai dai yaɗeyaɗen maganganu na ban haushi toh ta yaya zai mata wannan saurin shiga haka and she can't say no to her dad bayan albarka da ya gama duldula mata but in har tafiyar ta tabbata lallai zata gwada mai taurin kai irin nata dan komai ba zata yi ba har su gama su dawo a haka ake wanda duka ƴanuwan su ke murna thinking that sun fara jituwa ne especially Bahajjatu da Bilal waɗanda ke tsokanar su da cewa wataran wannan rashin jutuwar tasu na iya rikiɗewa ya koma soyayya sai dai ta ji su ta kyale dan tana da wannan ɗabi'ar ta kyale mutum in yana mata magana.. Despite all this her attitude tana da disability ɗaya she is cold blooded saboda tana da chronic pneumonic patient ce ita for so long tun da ta cika shekaru shida a duniya abin da ya ɗaga ma iyayen ta hankali da yayyen ta dan shi twin brother ɗin ta ma har kuka yakan yi akan shi a dawo mai da rashin lafiyar as a young child back then bai san komai ba sai da suka girma a nan ya dage akan kula da ita har wasu lokutan takan tasa shi gaba da masifar ta akan he is being overprotected kamar shine Prof ɗin gabaɗaya bai biye mata sai dai ya rarrashe ta as she is the eldest shine hussainin ta haka ta ke mai big sis stuff kamar ta bashi wasu shekaru ne.. Yayin da ƙiyayya ke ruruwa tsakanin Dr Zaid Maher da Dr Bilkisu Muhammad soyayya ce ke gudana tsakanin Bilal twin brother ɗin baby doctor da Bahajjatu ƙanwar Dr Zaid babbar aminiyar baby doctor daga gida wun iyayen su Bahajjatu an san da labarin soyayyar su dan haka ake jiran ranar da za'a saka bikin su at first abin banbarakwai ya ma baby doctor but tunda ta ga ita kanta Bahajjatun tana ji da soyayyar twin brother ɗin ta sai ta zuba masu idanu moreover ya fi ta girman jiki dan shi lafiyayye ne unlike her da ke fama da rashin lafiyar sanyi shi yasa take very tiny but very attractive and cute ba za'a ce ita ce ke farke cikin mutani sama da shida a rana ɗaya ba in ba gani mutum yayi ba.. A wun Dr Zaid tiny structure ɗin baby doctor ke ƙara hasala sa in ya ga yadda take yarfa sauran abokan aikin sa akan kawo mata tayin soyayyar su shi ba dan ma ƙaddarar kasancewar ta mace ba kuma ɗiyar mutumin da yake respecting da tuntuni ya tsage mata. Akwai wani daɗɗaɗen tarihin families biyu ɗin wato family ɗin Dr Muhammad Sulaiman da family ɗin Dr Maher Mahmud wannan tarihi kuwa shine tun zamanin kakkanin su iyaye matan ne ke ɗaukar ragamar bada umarni a gidajen su kuma mazan ke bada total obedience ma duk decision ɗin da matan suka yi hakan ya samo asali ne a sakamakon ƙulalliyar soyayya da ƙauna da aka gina ta akan yarda,aminci da tsaftattaciyar ilimin addini da na zamani dan haka a wun mazan ba wani abin aibu bane dan sun biye wa ra'ayoyin matan su ba su ɗau abin a matsayin wani abnormal issue ba since suna zaune lafiya da iyalan su toh ko da yauan baby doctor yayi aure wato jamil da matar sa zainab momma in-law ɗin ta Hajiya Zeenat ke ƙara koya mata yadda zata tafiyar da gidan ta a cewar ta itama haka mother in-law ɗin ta ta koya mata da ta zo gidan as a newly bride dan haka itama take koyawa sarkuwar ta yadda zata yi ruling gidan ta a gaskiya zainab bata taɓa tunanin her momma in-law will be as simple as this ba dan haka take respecting ɗin ta kamar ta bauta mata ita kuma ta mata alƙawarin in har zata na kular mata da ɗan ta ba tare da ta cutar da shi ba toh zata ji daɗin zama da ita this epic is applicable to the other family that is Dr Maher Mahmud family hakan ne ma yasa duk a cikin matan abokai sun fi kusa Hajiya Madina da Hajiya Zeenat dan sun fi baje kolin mulkin su yadda suke so haka kawai in ya ɗebe su sai su yi tafiyar wata guda su da mazajen su wai an tafi yawon buɗe ido ƴaƴan su kam sun gaji da masu faɗa sai zuba masu idanu suka yi at last suka bar su toh ganin kamar ƴaƴan sun fita a harkar su yasa suka haɗa ma ƴaƴan kai suna murje soyayyar su a gida ta yadda ƴaƴan da kansu zasu kora su su rinƙa zuwa yawon buɗe idanun su amma ƴaƴan suka ƙi sai dai in suka ga suna yi a gidan su tsawatar masu wanda hakan bai masu shi yasa suka kuma haɗawa ƴaƴan tarko ba tare da sanin su duk dan su bar su su wala.. All in all shine akwai strong bond tsakanin duka ahali biyun kuma ya faru ne sakamakon kyakyawar soyayyar da aka gina ta akwai yarda da kulawa a tsakanin two families ɗin wanda ya sa suke ganin kamar haɗa zuriar su wu guda zai haifar da kyakyawar unbreakable bond wannan buri kuwa ba akan kowa bane face Dr Zaid Maher da Dr Bilkisu Muhammad baby doctor...... _Toh koh burin iyayen zai cika?sai a hankali za'a warware murɗaɗɗen al'amarin.._ Da shigar ta ɗakin ta ta yi wurgi da jakar hannun ta ta faɗa kan gadon ta wanda ya ke lailaye da white and silver bed linen ya sha kwaliya kamar ba'a kwanciya a kai ta ɗau kimanin mintuna goma a kwance kafin ta yi wuf ta miƙe ta shiga bathroom dan yin wanka ba wani daɗewa ta yi a bathroom ba ta fito ɗaure da mini towel ɗin wanka da bath net tunda ta kwanta a kan gadon bata farka ba sai 6:25pm garau ta farka da full strength ɗin ta sauri sauri ta shirya cikin Adidas straight pepper red gown ta saka flat adidas pams shoe ta yafa veil ta ɗau maƙullin motarta ta sauko ƙasa ganin duk dinner suke yi yasa ta zauna ta yi joining ɗin su har sun kai rabi kafin Hajiya Zeenat ta ɗago ta ɗan kalle ta ta ce "Baby anya gajiyar surgery ɗin nan ya rabu da jikin ki kuwa"? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce "Eh ya sake ni umma me kika gani"?ɗan numfashin relieve Hajiya Zeenat ta sauke ta ce "Gani na yi kamar son fita kike"!! cigaba da cin abincin ta tayi tana girgiza kai dan overprotective attitude ɗin umman su na bata dariya tana 24 amma she is still being treated as a child of 5years..dakatar mata da tunanin ta ta kuma yi ta hanyar cewa "Baki bani amsa ba fah fita zaki yi"? Ajiye spoon ɗin hannun ta tayi ta buɗe baki dan son yin magana amma Abban su ya rigata "Heart nake ga ai aikin ta ne kuma tun around 4 da ta dawo bata fito ba sai yanzu kenan ta sami hutun da take buƙata right baby"? ya ida yana maida duban sa ga Hajiya Zeenat wace ta haɗe fuska kamar wacce ta haɗu da mummunar furuci, ta juya kenan da nufin yi mai sababi akan bai damu da babyn ta ba shi kuma ya juyar da tasa fuskar ta ɗaya bangaren,me yaran zasu saka in ban da dariya in da sabo sun saba da dramar iyayen na su tare da aminan su makwaftan su gidan su Dr Zaid gashi baka isa ka shiga tsakanin su ba kana saka baki zasu gwasale ka. Hararar wasa ta jefa mai a lokacin da ya kuma juyowa dan ya ga reaction ɗin ta suka sakarwa junan su murmushin ƙauna. Gyaran murya Bilal yayi ya ce "Toh ke apple ina zaki tafi by now kin dai ga time it's already 8pm ina ga kamar ki huta"!! haɗa ido suka yi ta mai alamar yayi shiru kar umman su ta hana ta fita dan abin kamar wani sabon abu a duk lokacin da zata tafi dubo patient ɗin ta muddin dare yayi toh tsoro ba zai bar Hajiya Zeenat ta amincewa ɗiyar tata zuwa dubiyar ba sai an sha fama shi yasa bata ƙaunar gaya mata tana da morning theater sai dai ta ce theater ɗin zai yi commencing by 1-2pm dan in dare yayi ta bar ta ta tafi dubiyar patient ɗin ta. A yau ɗin ma dramar kenan gashi apple ɗin ta na son jaza mata dan haka ta yamutsa fuska ta yi shiru abin ta ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat ta yi saurin miƙewa ta isa kujerar kusa da tata ta zauna ta fara taɓa jikin ta duk ta ruɗe "Baby jikin ne?ina ke damin ki?ba dai sanyin air split ɗin theater ɗin nan ne ya maki yawa ba"?duk ta ruɗe wanda hakan ya janyo attention ɗin sauran family members ɗin suka mai da duban su ga baby doctor.,ita kuma ganin hankalin umman ta ya tashi ya sa ta ɗan sasauta tamke fuskar da ta yi ta ce "Babu ko ɗaya umma"daga haka ta yi pim haka fah yayan ta Lukman ya rinƙa tambayar ta ƙarahe hawaye ta fara matsewa daga idanun ta ta miƙe ta ce da twin brother ɗin ta "Apple ungo zo ka raka ni"ta wurgo mai maƙullin motarta ya cafe ya na mata alamar ya zata mai haka daidai lokacin ya ke samin damar ganawa da Bahajjatun sa itama kallon tashi mu je kawai ta mai dan bata jin wani doguwar surutu dan kar ma a gane faking fushin ta take yi, Zai yi gardama ta ce mai "Ka tashi mu tafi kawai kokuma wallahi in jaza ma babu abin da ya shafen"ta juya baya ta fara tafiyar ta sumsum ya miƙe ya sallame su wai sai sun dawo yaya Luk kawai ya amsa yana murmushi dan ya san borin gwal ɗin gidan ya tashi yau babu ji babu gani. Bayan sun fita babu daɗewa ya kammala cin abincin sa ya ma iyayen na sa goodnight dan ya ba wa Abban su space ɗin rarrashin Hajiya umman su sakamakon chanjin yanayi da ta shiga tun bayan fitar ƴan biyun ta Abban su kaɗai ya amsa goodnight ɗin yayin da umman ta kyaɓe fuska Lukman na barin wurin ta saka ma prof kuka mai haɗe da shesheƙa tana cewa "Prof ka ga yadda Bilkisu ta bar gidan nan kamar fah ran ta a ɓace yake ta fita na ɓatawa ɗiya ta rai ka kirawo min ita ta dawo in rarrashe ta i didn't mean to offend her emotions"sai kuka shi kuwa da ya san halin abin shi ya san darun ta sarai yanzu akan ƴaƴan ta sai ta fita hayyacin ta in har ita ke da laifi toh babu sukuni har sai sun daidaita dan haka ya ɗaga ta suka bar falon suka wuce bedroom ɗin su inda ya bata assurance ɗin cewa komai zai yi daidai ai Bilkisu mai hankali ce da kyar fah ya rarrashe ta akan da safe zata bata haƙuri har da kwanciyar bacci amma tana ganin ya ɗan yi nisa a baccin sa ta miƙe ta koma falon zaman jiran dawowar su duk ta rikice.. _Back to Dr Maher's house_ Da ya shiga ciki da tarikicin Hakim ya fara karo suna mai sallama tsaƙi ya ja ya wuce ya rasa dalilin da ya sa muddin Hakim ya dawo gida duk gyaran da za'a kwana a yini ana yi ma gidan tas sai ya hargitsa shi in aka yi magana ya ɓige da cewa experiment yake yi shi a dole ga kwararren scientist hatta da kula da kan shi ma sai Ammin su ta yi kamar zata mai wanka da kan ta kafin ya yi dan shi in ta tashi ne bai ƙi sai 12 ɗin dare ba dan tsabagen aikin dan a gaskiya shi ɗin haziƙi ne akwai brain ba laifi a ko da yaushe jiye mai da yayan shi ke mai shine yadda matar shi zata iya zaman haƙuri da shi dan fah shi kullum a cikin utilizing time yake kamar sanƙiran hanzari..yana da wani abin da yake so yayi inventing dan haka yake cikin charging kwakwalwar shi babu ji babu gani. "Hakim!!! Hakim!!! da ɗan ƙarfi ya kira shi yana mai banko mai ƙofar ɗakin sa.duk dai bata sauya zani ba dan nan ɗin ma kacakaca da kaya da ƙyar ya kutsa ya shiga ciki ya hango shi kan reading table da babbar computer system ɗin sa gefe ga manyan pamphlet babu iyaka ɗan tsayuwa yayi a kan sa na mintuna kafin ya ɗan taɓa shi,a ɗan firgice ya ɗago suka yi ido huɗu da yayan na shi. Bambancin su tazarar shekaru ne dan kamannin su sak iri ɗaya ne da juna. Miƙewa yayi yana murmushi ya cire glasses ɗin da ke idanun sa masu rage mai kaifin haske ya gaida yayan nashi "Good day big bro wallahi tun ɗazu nake ta jiran ka ka dawo akwai wani chemical combination ne da ya shige min i couldn't sort it out"!kallon sama zuwa ƙasa ya mai kafin ya matso da doguwar hancin sa gab da jikin ɗan uwan ya shiga sunsunawa sannan ya ɗago ya tsaya ya ce da shi "You stink go get shower sai ka dawo mu cigaba da magana and make it snappy coz i will be going out"daga haka ya juya ya fita leaving Hakim a tsaye yana shafa kanshi yana murmushi kafin shima ya wuce toilet ya fara wanka.. Shima wankan yayi ya fito kenan ya tararda missed calls har huɗu bin kiran yayi ya sanar da cewa nan da 15 minutes yana zuwa sauri sauri ya shirya ya fita ya manta shaf da ɗan uwan sa da ya ce mawa ya same sa. Da sauri ya fita daga gidan ya wuce iyayen su da ke zaune a pool side har lokacin kiran sa suke yi amma ya wuce yana mai cewa "Yanzu zan dawo"motar shi ya shiga ya fige ta sai asibitin da zuwan sa cikin sauri ya sa aka yi setting mai theater suit saboda emergency caesarean section da zai yi. Babu wani time dan haka aka yi saurin haɗawa yayi changing zuwa kayan aiki wani Dr Mark ne ya yi assisting ɗin shi suka yi lafiya suka gama lafiya bayan ƴan observation aka wuce da matar zuwa ga post-op room sannan ya koma office ɗin sa ya ɗan yi relaxing.. Kiɗa ya saka a motar ta yi saurin mangare hannun shi ta chanza zuwa wani wa'azi sannan tayi lowering volume ɗin chan ƙasa zai taɓa ta hayayyaƙo mai "Kana taɓawa zaka fita wannan motata ce ba taka ba yauwa"! Ta jingina kan ta da kujera tana tunanin yadda tafiyar ta su zata kasance. interrupting ɗin ta yayi ta hanyar magana "Apple kenan kun shirya da brother in-law"!? Wani kallo ta kwashe shi da shi ta juya kai kawai ya kuma ƙoƙarin furta wata kalmar ta riga shi "Apple wallahi kana takura ni"shiru yayi dan yau kam laifin asibiti na son shafar kowa..ƙala bai kuma cewa ba har sai da suka isa asibitin ya zaga ya buɗe mata ƙofa ta fito ya mayar ya rufe suka tako har cikin asibitin tare da yake dare akwai restricted movements sai ƴan tsiraru da ba za'a rasa ba. Gaisawa suka yi da receptionist ɗin ta masu barka da dare suka wuce ciki,ɗakin patient ɗin ta ta wuce apple ɗin ta na bayan ta,ƴanuwan patient ɗin ne suka gaida ta ta amsa cikin girmamawa shima Bilal ya gaida su suka amsa suna mamakin kamanin su kallon yayan ta suke mai since shi ɗin jibgege ne tun daga girman jiki har tsayi ya fi ta sai suka kasa yin shiru har sai da suka tambaye ta "Doctor wai wannan ɗin ɗanuwan ki ne"? Kallon junan su suka yi suka murmusa dan an saba yi masu ire iren waɗannan tambayoyi "Eh ɗan uwa na ne"!sai suka ce daga gani ai sun shaida,dariya kawai suka saka daga haka ta tambayi matar patient ɗin ko ya farfaɗo "Eh doctor ya farfaɗo ɗazu ba ki nan sai ɗayan likitan nan ne ya zo wucewa daidai ya farfaɗon sai muka kirawo shi shine ya zo ya duba shi"! da mamaki ta tambaye ta "Wani likita kenan"? "Wannan ɗin nan doctor ZM naji ana kiran shi ko menene"! Ɗan exclaiming ta yi ta ce "Oh yeah shi,ok toh yanzu ya jikin nashi"? "Alhamdulilah doctor har fah ƴar hira muka yi da ya farfaɗo"suka ɗan dara kafin ta jadadda masu kar fah su takura mai har sai ya taso da kan sa suka amsa mata haɗe da yi mata godiya daga haka ta sallame su. Fitowar su kenan ta ja shi zuwa office ɗin ta ta zaunar da shi ta fara mai tambaya "Apple,wai am i that bad"?natsuwa yayi ya bata hankalin sa kafin ya amsa mata da "Not at all apple me yasa kika yi wannan tambayar"?ɗan shiru ta yi kafin ta miƙe tsaye tana ɗan zagawa na wasu lokuta sannan ta cigaba da magana "Apple ka san tafiyar nan ba da niyya ta za'a yi shi ba"!!juyawa yayi ya kalle ta kafin ya ce "Ban gane ba apple"zama tayi ta ƙura mai ido kamar wacce ke son fiddo Wani abu a kallon da take mai "Apple Zaid mugu ne he must have planned something bad da ya sa ya matsu sai mun yi wannan outreach ɗin tare i don't trust him"a nan ta kwashe labarin abin da ya faru da safen ta sanar da shi Madaɗin ya nuna damuwar sa sai ya share ya ce mata "Apple kin san dai da brother in-law na da mugun hali da tuntuni an gano hakan but ni nake ga kawai hanyar shiryawa yake nema if not ban ga me zai sa ya bar family ɗin shi da career ɗin shi a nan ba ya tafi wannan dajin Koman dan ya maki mugun abu ba"shiru tayi tana kallon shi kafin daga bisani ta miƙe ta ce mai "Tashi mu tafi ypur brain always boot about bank stuffs baya nuna maka reality da ke gaban ka talking to you is always a waste of time apple"wucewa tayi ya biyo ta yana dariya. Suna hanyar su ta fita bata sani ba ta bangaje shi da sauri ta furta "Oh goodness am so sorry"ɗagowar da zata yi ta gan shi a tsaye wani mugun takaici ne ya ziyarci zuciyar ta kamar ta gasa mai magana sai dai ta share ta yi gaba yayin da Bilal ya tsaya suka gaisa dan ya baƙanta mata ya rinƙa jan Bilal ɗin da hira dan dai kawai ya bar ta tsaye tunda ya san bata night driving definitely Bilal ɗin ne ya kawo ta kuma ya san in har yana wurin ba za ta iya magana da ɗan uwan nata ba gashi Bilal ba laifi akwai surutu kamar alƙalin aku.bai tashi releasing ɗin Bilal ba sai da ya ga ta gaji da tsayuwar sannan ya ce da shi "Ga fah ƴaruwar ka chan na jiran ka"shaf ya manta da ita a tsaye da gudu gudu ya ƙarasa wun ta yana bata haƙuri ya yi saurin buɗe ƙofar motar ƙala bata ce da shi ba ta shige suka kama hanya yayi ta magana komai bata ce da shi ba ya bata haƙurin har ya gaji haka suka dawo gida ta riga shi shiga tarar da Hajiya Zeenat ta yi a zaune ta yi mamakin rashin baccin da bata yi ba 9:34pm amma bata yi barci ba ta manta sun yi faɗa da umman na ta kafin ta fita Da ganin shigowar ta ta miƙe ta nufe ta tana ce wa "Baby kin yi fushi da ni ki yi haƙuri i was so concern about your health shi yasa nake tsoron barin ki kina fita da dare ga sanyin yau yayi yawa please forgive me baby i never meant to offend you am sorry"!! rungume ta tayi tana ce mata "Haba umma sau nawa nake hana ki zaman nan akan wani fake anger ɗi na and i know that you cried why are you behaving like a baby"?rungume ta tayi itama sosai dan tana tsoron rasa ɗiyar tata akan condition ɗin ta shi yasa tafi tsaurara mata ƙaidoji.Bilal da shigowar shi kenan ya gan su zai yi magana ta yi pulling daga jikin umman su ta fara tafiya "A word from you will increase my anger ba zan yi having conversation da kai ba sai gobe"ta ce da Hajiya Zeenat "Umma je ki kwanta sai da safr na gaji".. Ta yi shigewar ta leaving them staring at her inda umma ta balbale shi me yasa zai ɓata mata rai shima ɗin wucewa yayi Hajiya Zeenat ma ta wuce bedroom ɗin su tana sababi.. Bayan ta shirya cikin kayan bacci ta yi setting laptop ɗin ta ta ɗanna kira babu jimawa yayi connecting aka ɗauka wata kyakyawar budurwa ce sanye cikin chiffon mini top babu ɗan kwali a kan ta ta yi sallama tana murmushi "Wa'alaikumul salam" "Beelove ya kije ya apple ɗi na"? Harara ta danƙara mata ita kuma ta kece da dariya tana cewa "Haba Beelove wai laifin me aka miki ne yau na ji apple na complaining temper ɗin ki yau ya ɓaci"!tsaƙi ta yi ta ce "Rabu da shi zan yi maganin shi ne ai yanzu ba wannan ba yaushe zaki dawo Baha"?ɗan dariya ta yi kafin ta ce "Don't tell me you are missing me already" "Yes i am kuma akwai maganar da nake son yi da ke shi yasa na matsu ki dawo"! Ɗan juya ido tayi kafin ta ce "Nan da 5 days kayan ne ban ga taste ɗi na ba da tun jiya na dawo"da murna ta ce "Alright till then sai da safe headache na dami na yau surgery huɗu na yi i need to rest"daga haka suka yi goodnight.. ************** A lissafi saura kwanaki 6 su tafi outreach ɗin su wanda har lokacin babu wata kyakyawar maganganu ko alaƙa mai kyau tsakanin su amma da haka ake kan bakan za'a yi tafiyar outreach zuwa Adamawa. Da safen ranar wacce ya kasance asabar,al'ada ce ta gidar akan duk asabar haɗuwa ake yi wu ɗaya a yi spending saturday ɗin tare da juna dan haka bayan sun gama breakfast suka shirya zasu tafi Nija Motels dan cikasa ranar,prof ne da Hajiya Zeenat cikin shigar kayan beach iri ɗaya nashi na maza nata kuma na mata hatta da kalar iri ɗaya ce babu bambanci da hulunar cowboy sun mammaka a ka za'a yawon buɗe ido chan ma Dr Maher da Hajiya Madina shiga iri ɗaya suka yi kamar dai irin na su Prof suka haɗe a gate cikin motocin su komai an yi packaging ɗin shi an saka masu a mota horn suka yi wa junan su suka hau kan titi babu wasu drivers dan ba su buƙatar su tafiyar holewar su ne masu kallon asiri are not needed,ƴaƴan kamar su fashe dan haushi haka dai suka bar su kowa ya cigaba da sabgar sa.. Fitar su babu daɗewa Hajiya Madina ta kira Bilkisu a waya wai sun manto earpiece ɗin su a gida da headphone ɗin Dr Maher dan Allah ta je ta ce da Zaid ya kawo masu yanzu. "Oh ni Bilkisu i can't say no to this woman in ba haka ba a rasa wanda za'a kira ya je aike sai ni"haka dai ta fito daga gidan su ta saka slippers ɗin ta fito daga gidan su ta shiga cikin gidan su Zaid duba shi ta yi bata gan shi ba ta cigaba da zagaya gidan har dai ta iso pool side inda ta hango shi kwance saman couch ɗin pool ɗin idon shi manne da sunglass gefen shi apple ice ne ga hand towel a gefen shi daga shi sai boxers babu riga a jikin shi,gwalalo idanun ta tayi tana ƙoƙarin juyawa kenan ta ci karo da mai aikin gidan zai kai mai wani drink ɗin kafin ta hana shi magana har ya rigata "Hey goodmorning baby doctor how may i help you"?runtse idanu ta yi tana jin haushin sa ai ko ya miƙe jin an kira sunan baby doctor Neman rigar shi yayi ya saka cikin hanzari yana roƙon Allah ya sa bata gan shi a haka ba "What could she be doing here"ya tambayi kanshi. Kasa ba ma mai aikin amsa tayi kawai sai ta cigaba da tafiya da nufin in ta koma gida sai ta aiko Bilal ya faɗi saƙon amma tana fara tafiya ta jiyo muryar shi cikin ɗan fushi yana cewa "Hey me ya kawo ki gidan mu by this time"? bata juyo ba amma ta tsaya haushin ɗaga mata muryar da yayi ta ji sai ta ce mai "Gidan masu gida dai, kuma ni Ammi ce ta ce in sanar da kai sun manto earpiece da headphone ɗin su ka ɗauko ka kai masu"tana kaiwa nan ta wuce tana tsaƙi.. Mamaki yake yi ga wayar shi nan kusa da shi babu missed calls ko ɗaya bare ya ce kira suka yi bai ɗauka ba suka kira ta toh me suke nufi na aiko ta by this time ga Hakim nan a gida ba'a kira shi an aiko shi ba sai ita lallai there parents are up to something Tsakin yayi shima ya saka takalman shi dan dubo masu abin da suka ce sun baro a gidan, Ita kuma da ta koma gida ta rufe ƙofa ta shiga zirga zirga tana ƙoƙarin calming kan ta in any way possible dan kuwa tun da ta gan shi ɗazu har yanzu yanayin da ta riske shi ya ƙi daina yi mata gizo da kyar ta yakice abin ƙarshe ma shiryawa ta yi ta wuce zuwa gidan yayan ta Jamil dan ta rage wani abin tunda ayyukan ta na ranar are less daga chan sai ta wuce zuwa hospital ɗin may be zata rage damuwar da ke ɗawainiya da ita. Shi kuwa da ya koma cikin gidan dan ɗauko masu saƙon su ya duba ya gani sai ya chanza kayar sa zuwa ƙanana ya fito da saƙon a hannun sa ya wuce zuwa wun motar sa ya shige ya ja har chan kiran su yayi a waya dan jin inda suke suka mai kwatance ya tafi.abin haushi sai yi suke kamar wasu yara gaida su yayi kan shi a ƙasa ya miƙa masu saƙon ya juya zai wuce sai ya ji muryar Ammin sa tana cewa "My boy please ka tafi ka dubo min lafiyar baby doctor dan umman ku ta ce tun jiya bata ji daɗi ba gashi na aiko ta wun ka ban sani ba sanyi ya taɓa ta please go check on her huhh"rasa abin cewa yayi dan he can't believe that his parents are for real,girgiza mata kai kawai yayi ya wuce Jan motar yaje yi kamar motar ce ta aike shi bai tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan su yana fita daga motar ya shiga cikin gidan yayi tambayar ta aka ce mai ta fita hamdala yayi ya koma cikin motar shi ya ja zuwa cikin gidan su ya shirya shima ya fita. Sai dare families ɗin biyu suka dawo gida inda suka sha faɗa da ƴaƴan nasu musamman Hajiya Madina da ta takurawa Zaid ɗin a ranar haka yayi ta faɗa kamar zai yi me ita dai shiru ta mai har ya gama sannan ta ce "Zaid ka daina shigar min ido fah da yawa ba fah hanaka auren nan na yi ba ga abokin ka nan Jamil da mata har ma da ƴar ƴar shekaru biyu da rabi kai baka yi ba ban hanaka jin daɗin ka ba sannan a ce kai ban takura ka ba amma kai kana son amputating min farincikin rayuwa ta ba zan ɗauka ba yauwwa"tana gamawa ta kalli Dr Maher ta ce mai "Only talk to your boy"ta yi wucewar ta a dole an ɓata mata rai,bayan wucewar ta mahaifin ya kalle shi cikin taarguwa kafin ya ce "Zaid we are sorry ka san halin Ammin ta ka"kallon tsaf ya ma mahaifin na sa dan ya san har da laifin sa a yawan yawon nasu dan haka ya zauna kusa da shi ya ce "Abba toh wai dole sai kun fita yawon nan ne zaku nunawa duniya cewa kuna son junan ku"? ya girgiza kai "Toh me yasa ba zaku rage ba at least not always koh da once in a month ne"ya kuma girgiza mai kai kamar wanda ya ɗau shawarar ta sa shi so yake ma ya rabu da shi ya wuce ya rarrashi heart ɗin sa lallai yaro man kaza su da suke planning tafiya ƙasar London dan buɗe ido zai wani kawo masu tsarin su rage yawon buɗe idanu hmm Zaid bai san me ake kira da soyayya da ƙauna ba anyway he didn't blame him bai san daɗin su ba shi yasa, Da haka suka rabu kowa ya wuce shi Dr Maher ya tafi rarrashin Hajiya Madina shi kuma Zaid ya koma ciki yana mamakin rayuwar mahaifin sa wai a ce mutum da girman sa amma mace ke juya shi kamar ƙaramin yaro a ce mahaifin at his early 60's amma mahaifiyar su sai yadda ta yi da shi sannam in aka yi magana su ce soyayya ce to he with the word soyayya meye gamon shi da kalmar,shi ba zai yi tolerating wannan shirmen a gidan sa ba.haka ya kwanta yana mamakin halayar iyayen su na both houses ɗin. _Monday morning_ 8:50am Sauri saurin shiga office ta ke dan ɗauko important files ɗin da ta bari tun friday she was in a hurry so bata lura ba kwata kwata ta take shi da takalmin ta,ja da baya tayi tana jin damuwa gashi ita kuma ba zata iya ce mai yi haƙuri ba dan haka ta tsaya shima ya tsaya yana kallon ta ga shi dukkan su suna da uzirin da ke gaban su amma izza ta hana su motsa fatar bakin su dan haka suka cigaba da tsayuwar har sai da Dr Aslam ya zo giftawa ya tsinkayo su wani kishi ne ya taso mai wanda yayi sanadiyar chanza hanyar tafiyar shi zuwa direction ɗin su ya iso su yana kallon su afar dan son jin me suke cewa amma har shafewar mintuna biyu bai ji sun ce komai ba dan haka ya yanke hukuncin tunkarar su dan ganin irin kallon da suke aikawa juna a tunanin shi kallon so ne bai san wuta ne ke ruruwa a cikin kallon ba, Da zuwar shi ya yanke kallon ta hanyar kiran sunan ta "Beelove good morning how was your night"?jin muryar shi ya sa ta sami kafar barin wurin ta ƙara gaba abin ta ta bar su a wurin yayin da shi kuma Dr Zaid ɗin ya bankawa Dr Aslam harara yana cewa "Wawa yarinya ƴar ƙanƙanuwa na juya ka kana abu kamar wanda bai da tunani mtsw"ya yi tsaki kafin ya bar wurin shi kuma ya raka shi da harara yana cewa "Eh na ji ɗin haka kawai in bari ka sami lafiyayyiyar yarinya haka ɓagas inaa ba zai yiwu ba"shima ya wuce abin sa. Throughout ranar a hide and seek suka yi ta Bahajjatu was supposed to return back yesterday amma ta ɗaga har sai yau dan haka da wuri baby doctor ta yi closing komai nata dan ta tafi tarbar aminiyar tata,.. A airport ɗin da ta ke jiran isowar ta ne ta hangi Dr Zaid ɗin yi tayi kamar bata san da zuwar shi ba yadda shima ya basar kamar bai gan ta ba haka suka yi zaman jira har jirgin su ya sauko aka gama firfitowa daga baya ta fito itama da yayan ta ta fara tozali dan haka ta yi saurin ɗaga mai hannu har dai ya hango ta shima suka sakarwa junan su murmushi har suka iso dab da juna ya bata side hug yana tambayar ta ya hanya "Very hectic journey yaya na gaji sosai"ya ɗan murmusa kafin ya ce "Then you need to rest"ta ce "Yeah sure"suka cigaba da takawa har suka zo zasu shiga motar sa sai ta hango aminiyar tata tana kallon su da sauri ta ƙarasa wun ta ta na "Ohhh my God Beelove dama kin zo ne ban gan ki ba"hararar ta tayi ta ce "Ban sani ba"ta rungume ta tana ce mata "Ya hanyar"? "Babes babu daɗi tafiyar yau na gaji da yawa" Kallon ta tayi tana cewa "Anya ko dai fever ne ke son kama ki"jan jikin ta yi ta ce "Zaki fara kenan da zarar mutum yace nan na zafi sai kun yi analysis" ɗan dara suka yi kafin ta ce "Mu je ma a motar ki zamu tafi"juyawa tayi ta ce da yayan ta "Yaya na mu haɗu a gida zamu biyo ka"ɗaga mata kai kawai yayi ba dan ya so ba da haka suka wuce shima ya biyo su a baya. Ta so barin har sai sun isa gida kafin ta sanar da ita maganar da ta ke ta jiran ta ta dawo ta sanar da ita amma abin na damin ta dan haka ta fayyace mata saidai rashin nuna kulawar ta ya sa Bilkisu ƙara tsarguwa da tafiyar har dai ta ajiye ta a gida ta ce mata anjima zata dawo suka rabu. Da tunani fal a ran ta smta kwana tafiyar will be friday kuma ita she is not just comfortable with the outreach kuma mahaifin ta bai son fahimta babu ma wanda ke son fahimtar.. ***************** A daren da yake washegari ne tafiyar ta tafi asibiti dan ɗauko wasu abubuwan da ke da muhimmanci a tafiyar tata ta fito tana kallon office door ɗin shi a buɗe kamar ta shiga ta tunkare shi da maganar dalilin shi na son tafiya tare da ita outreach ɗin sai dai girman kan tsiya ya hana haka ta rinƙa kallon ƙofar har ya fito ya ja ya rufe zai tafi kenan ya hango ta tsaye da kayan a hanun ta tana kallon shi.babu alamun damuwa a tattare da shi dan shi matsuwa ma yayi ya je ya ga sanyin idaniyar sa he use to take soyayya a matsayin abin da bai da wani ƙima though yana da wacce yake son yin rayuwar shi da ita sai ya ke mutunta kalmar son har da dai ba chan sosai ba amma ya san dai yana son ta but ba irin blind love da iyayen su ke ma juna ba he cursed that type of love. nufota yayi yana tsare ta da ido ita kuma ta kasa cire idanun ta daga nashi har ya ƙaraso ya tsaya yayi folding hannayen sa ya ce "Are you prepared"? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce da shi "Why?me yasa ka min haka a wun mahaifi na bayan ka san ba zan iya ƙin amsa duk umarnin sa ba why did you do that to me"? Murmushin ƙasaita yayi ya ce. "Hmm baby doctor kenan ba dai har kin fara tsorata da outreach ɗin na mu ba"? ɗan rausayar da idanu ta yi cikin takaici ta ce "Ni dai tambayar ka na yi me yasa ka min hakan"? saka hannun sa yayi a waist ɗin sa ya rage tsayin sa ya ce *_"iya ruwa fidda kai_* yana kaiwa nan yayi gaba abin shi ita kuma ta bi shi da kallo har ya ɓacewa ganin ta kamar zata yi kuka haka itama ta bi bayan shi ta wuce zuwa gida tana tunanin yadda zaman su inuwa ɗaya zai kasance a ƙauyen........... A ranar kasa rintsawa ta yi sakamakon zullumi da fargaban ko me zai wakana washegari kiran Bahajjatu ta yi a waya bata ɗauka ba an saka mata number busy kuma kira ta yi har sai da ta ɗauka "Haba Beelove wani irin fitina ne da daddaren nan kin kira kin ga am busy kin kuma kira na saka ki a on hold wai menene"? Gauron numfashi ta sauke kafin ta ce "Baha ina tsoron tafiyar nan"ɗan shiru suka yi kafin ta ce da ita "Me ya sa zaki ji tsoro Beelove bayan kin saba zuwa outreach ɗin nan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba toh nervousness ɗin na meye"? "Ban sani ba Baha amma ina da atrong feelings akan cewa babu alkhairi a outreach ɗin nan i don't know maybe is because of your brother am not just comfortable Baha"!! ta ida kamar zata yi kuka dan haka Bahajjatu n ta ɗan saurara mata kafin ta ce "Beelove calm down please you are being over reactive na ke ganin kamar ki yi magana da yaya Zaid kafin goben saboda ki sami relief ko me kika ce"?Bahajjatu is always putting a bilnd eyes ma duka abubuwan da ke wakana a tsakanin su haka take da halin ban san kuna da misunderstanding ba which hurts baby doctor ba kaɗan ba.. "Alright fine tunda haka kika ce nagode good night take care".. Tana kaiwa nan ta datse kiransau uku Bahajjatu na kiran ta ta ƙi ɗagawa dan ta san ta mata sallamar da ɓacin rai shi yasa ta rinƙa calling back amma ta ƙi ɗagawa haka ta haƙura ta tura mata saƙon safe journey akan washegari zasu yi goodbye proper ignoring message ɗin ta yi ta tashi ta saka slippers ɗin ta ta nufi ɗakin Bilal wanda ke ta faman rarrashin apple ɗin sa dan ta ƙi magana da shi laifin Bilkisu ya shafe shi,bata wani tsaya buga kofar ba da yin sallama ta turo ƙofar luckily yana buɗe, Da sauri ya leƙo daga cikin comforter ɗin dan bai yi tsammanin ganin kowa ba..haɗa ido suka yi ya ga yanayin ta ya chanza sai ya bama Bahajjatu haƙuri akan zai kira anjima ya katse wayar yayin da ita kuma ta ƙarasa shigowa ɗakin tana taku a hankali kasa haƙura yayi har sai da ya tambaye ta me ke damin ta. zama ta yi a saman hannun kujerar ɗakin tana ƙoƙarin danne hawayen ta "Apple me ke damin ki har kike ƙoƙarin zubar da hawayen ki"? ai kuwa sai ga hawaye sun gangaro ta yi saurin goge su "SubhanaAllah apple wai menene"? Juyar da kan ta gefe tayi ta ce "Bilal bana jin akwai alkhairi a tafiyar nan da za'a yi amma babu wanda ya fahimce ni nayi nayi in fahimtar da Abba amma baigane ba ya yarda da Zaid Maher sama da misali umma ma ba'a magana dan bata son jin laifin sa Bahajjatu ma bouncing ɗi na take yi saboda yayan ta ne tauraron ta bata ganin illar abubuwan da yake aikatawa kai kuma tun farin maganar nan na sanar da kai yadda nake ji amma baka taya ni jimami ba toh duka waɗanda na amince da su basu yarda da ni ba wa kuma zai yarda da ni"? ta ƙarashe tana sakin silent cry wanda ya karya zuciyar ɗanuwan nata har shima ya ga rashin kyautawar sa out of all peoplr he should understand sama da kowa but bai bata wannan chance ɗin ba ya biye ma halin ta na sanyi ya ƙi fahimtar damuwar ta. "Bilkisu am so sorry please forgive me ban san abin ya dame ki da yawa har haka ba ni duk a tunani na maybe kun sami masalaha ne a tsakanin ku but believe me apple wallahi wallahi ban san har yanzu akwai matsala a tsakanin ku ba but since it turns out to be this way ki zo mu je wun Abba a san na yi dan shi kan shi ba zai yarda ki tafi outreach ɗin da hankalin ki bai kwanta da shi,lets go"! ya miƙe tsaya yana ƙoƙarin jan hannun ta su tafi dan abin ya ƙona mai rai. Dakatar da shi tayi ta hanyar dawo da shi ya zauna ta fuskance shi ta ce "Bilal duk duniya ban da wanda nake da burin farantawa kamar Abba,zuwa sanar da shi wannan maganar kamar janyo mai ɓacin rai ne wanda hakan na iya janyo masu saɓani tsakanin su da daddy Maher wanda duka iyayen namu ba za su so ba dan haka ka bar maganar kawai i accept defeat zan tafi tare da shi muyi outreach ɗin mu dawo kuma inshaAllah zan rufe idanuna kuma in rufe kunnuwa ta ga duk wasu abubuwan da zai min a garin har mu dawo ban san dalilin shi na ƙi na ba but ko ma dai menene ba zan taɓa ɓatawa mahaifi na rai ba"ta ida tana share hawayen da ke tsilalowa daga idanun ta wanda ya kuma karyar da zuciyar ɗan uwan nata. "But apple are you comfortable with the decision you just made"?? Kallon shi ta yi tana jinjuna kai "Alright,just always remember that am with you ko ina kusa ko bana kusa da ke huh"? jinjina kai tayi tana jin sanyi a ran ta ɗan uwa ɗan uwa ne dan tun da maganar ta taso bata taɓa jin sauƙi da sanyi haɗe da kwarin gwiwa ba sai yau da ta fitar da abin da ke ɗawainiya da ita a ran ta. "Thank you apple"comforting smile ya mata ya raka ta har ƙofar ɗakin ta suka yi sweet dreams har sai da ta rufe ƙofar ya koma ɗakin shi ya kwanta koh Bahajjatun bai kira ba da kyar yayi bacci yana tsoron tafiyar twin sis ɗin ta sa. A nata ɓangaren ma haka ne dan ta sami courage ba laifi a haka ta harhaɗa abubuwan da zata buƙata a trip ɗin ta gama ta kwanta bacci with less worries... ************* Tun 9am suka gama packaging kayayyakin tafiyar ta su wanda Hajiya Zeenat ta haɗa mata kayan cime cime kala daban daban dangin su dambun nama alƙubus cupcakes plantain chips dried smoked fish da dai sauran kayan fast food da ba zai wahal da ita wun dafawa ba. Bayan breakfast suka ranƙaya gabaki ɗaya har da yaya Lukman suka raka ta dan zuwa airport inda a nan suka haɗe da su Zaid suka ƙarasa har airport ɗin dan by air zasu yi tafiyar saboda sauƙaƙa gajiyar hanya. Sosai Hajiya Zeenat ta nuna jin kewar ta ga ɗiyar tata haka Hajiya Madina ma duk ta damu saboda pneumonia ɗin ta shi yasa ta jadadda ma Zaid akan ya tabbatar ya kula da baby doctor though bata sanar da shi cewar tana da pneumonia ba but ta ja mai kunnen ya rinƙa kula da ita sosai ya amsa mata da cewar inshaAllah.. Bilal kamar kar ya rabu da ƴaruwar sa haka ya rinƙa ji.wata ƴar drama aka yi a airport ɗin dan wani koke koke iyaye matan ke yi yayin da iyaye mazan ke rarrashin su abin sai ya zama abin dariya ga ƴaƴayen nasu Lukman da ke kallon su ya kasa haƙura ya ce "Alright drama over a tafi gida haka nan"hararar wasa Hajiya Zeenat ta aika mai da shi suka kuma yin dariya da haka suka shige jirgin ya ɗaga zuwa ƙasar Adamawan Yola su kuma iyayen suka koma gida. Tun da suka shiga jirgin nan babu wanda ya kalli juna a cikin su kowa harkar gabar sa yake yi har jirgin yayi landing safely suka shiga taxi zuwa inda zasu tafi uhum bai shiga tsakanin su ba shi da ya san wuri shi ya rinƙa kwatance har suka yi tafiyar kusa 2¼ hours kafin su kai ciki cikin yankin _koma_ inda aka masu masauki a gidan mai gari tuni labari ya zaga gari bokan turai ya zo tare da wata wacce ake tsammanin itama bokar turai ce ai kuwa aka fara tururuwar zuwa ganin su dama shi ɗan gari ne ita ce sabuwar zuwa dan haka suka rinƙa zullumin ko likitar ce ita ko dai ƴar rakiya ce ita dan haka suka rinƙa tambayar samarin garin wanda suma jira suke washegari yayi su ji cikalen labari daga bokan turai sun so yin takakkiya su tafi har gidan mai garin dan jin rahoto amma mai gari ya hana ya ce a bar su su huta har gobe dan haka suka haƙura. Matan mai gari suka karɓe su hannu bibiyu tun ma ita baby doctor wacce ta kasance mace ta ji daɗin tarbar da suka mata har da dai basu da wani ƙarfi amma sun yi ƙoƙarin su abinci kala kala daidai ƙarfin su shi da ya zama ɗan gida ya ma manta da wata wai Bilkisu dan samarin gidan mai gari sun ja sa da hira kuma yanayin sauƙin kan sa ya sa suke son sa har suke mai kirarin bature ya ƙi halin turawa dan su sun san ƴan birni na da ƙyanƙyami da tsantsene akan ɗan kauye amma ta fannin bokan turain nasu ba haka bane.hira sosai suka sha har aka kawo mai abinci suka ci suna hira har lokacin sallah yayi suka tafi suka yi daga nan ma ɗan zaga gari suka ui har sai bayan sallar isha'i suka koma gida inda a nan mai garin ya ce a bar shi ya huta haka nan dan haka suka bar shi akan gobe zasu dawo. A gefen ta kuma haka dai suka so sakewa da ita amma ganin kamar bata saba da hayaniya ba yasa suka rabu da ita sun fi dangana hakan da gajiya akan gobe zasu yi hira itama hakan ya fi mata dan so take ta huta gyara mata wurin kwanciya aka yi a ɗaya ɗakin matar mai gari wacce ita ce ta fi su wayewa dan ita ce ƴar gaban goshin mai gari kasancewar ta amarya kuma ɗiyar mai kuɗin garin so komai nata tsaf tsaf yake watannin ta 8 kawai da aure bata kuma da ciki bare ɗa ko ƴa.lafiyayyen gadon ta da ya sha gyara da zanin gado mai kyau ga blanket mai kyau ga ƙamshi na tashi a ɗakin,kwantawa ta yi tana tunanin gida dan tun da ta zo babu network a garin shi yasa bata sami damar yin waya da ƴanuwan ta hakan ya dame ta sosai gashi shi ɗin da ya kawo ta garin bai ma damu ya san halin da take ciki ba which hurt her a lot but bata cire rai ba akan gobe zata kuma ƙoƙarin ganawa da ƴanuwan ta... ************* Basu tashe ta ba sai wuraren ƙarfe 6 na safe godiyar ta ma ba sallah take yi ba dan haka tashin farko ta ankara da cewa gidan nan akwai ƙarancin ilimin addini dan haka shima yana cikin aikin da zata yi a garin ba ma a gidan ba kawai, Komawa tayi ta kwanta bayan ta sanar da su cewa fashin sallah take yi ai kuwa tun lokacin da ta koma basu tashe ta ba sai da ta tashi dan ƙashin kan ta which is 1:45pm ta ji mamaki ba kaɗan ba su kuma haka suke rayuwar su. Ita amaryar mai garin wato zulfa'u ita ce ta kai mata ruwan wanka a toilet ɗin ta na ɗakin wanda ya sha gyara ba laifi yana ƙamshi dan dama zulfa'u ba laifi wun gyara da ajiye ƙamshi a sashen ta,wankan ta shiga ta yi ta fito ɗaure da towel a ƙirji tana goge fuskar ta cikin sakin fuska ta karasa wun zulfa'u ta ce mata "Ina yini"amsa mata tayi ta na ce mata "Likiciya ya baƙunta"?murmusawa tayi dan jin sunan da ta kira ta da shi wai _likiciya_ "Alhamdulilah kuma sai kika bar ni ina ta barci madaɗin ki tayar da ni in taya ki aiki"hangame baki tayi kafin ta saka dariya tana cewa "Likiciya rufa min asiri ina ni ina saka ƴan birni aiki likiciya?a'a wallahi ni jira ma nake ki ci abinci ki koma barcin dan gajiyar hanyar kamar bata sake ki ba likiciya"ɗan darawa ta yi ta ce "Ki kira ni da Bilkisu sunana kenan ba likiciya ba "shiru tayi kafin ta ce "Toh ai ba zan iya kiran sunan ba ne tun jiya na san sunan amma ya min nauyin kira shi yasa nake kiran ki da likiciya"da mamaki ta dakata da shafa man da take yi ta ce "Me yasa ba zaki iya kiran sunana ba"?ta ce "Sunan mahaifiya ta gare ki likiciya"ɗan darawa ta yi ita fah wannan sabuwar suna nata na bata dariya "Kin san me"?ta ce a'a sai kin faɗa "Ki kira ni da wani sunan ba likiciya ba"ɗan shiru ta yi tayi sukui alamun tunani kafin tace "Ni kuwa jiya bokan turai ya faɗa mana ɗayar sunan ki amma da yake sunan dai kamar ta ƴan nasara ne ban riƙe ba ni ko me ma ya ce sunan naki"??ta cigaba da nazari Tsaf ta san da baby doctor ya yi introducing ɗin ta shi yasa suka kasa riƙe sunan wannan wace irin wulaƙancin ne kuma shi bai neme ta ba hmm a haka ta shirya cikin atamfa wanda ya mata ɗas a jiki har ya sa zulfa'u kasa ɓoye maganar ta tace "Kaii amma kin yi kyau dama kuma kuna saka atamfa har haka likiciya"? Ohh matar nan ba zata kashe ta da kayan dariya ba a iya zaman su daga jiya zuwa yau ta lura matar akwai son jan mutum a jiki kuma duk tafi wayewa a cikin matan maybe dan itace amarya shi yasa "Ai muma kamar kowa muke duk abin da kuke yi muna yin shi muma"sai ta saka dariya ta ce "Kai amma na ji daɗi da ni duk kallon da nakewa ƴan birni basu da kirki kuma basu saka ire iren kayayyakin mu ashe ba haka bane" daga haka ta kawo mata abinci cikin tray babba ga kunun fulani da ya sha kindirmo ga sugar a ɗan ƙaramin kwano mai murfi ga alale mai rai da lafiya a food warmer ga soyayyun kaji nan an masu pepper chicken sai ƙamshi suke yi ga plate nan da spoon haɗe da ruwan wanke hannu komai dai MashaAllah Zama tayi a dardumar da aka shimfiɗe mata ta zuzzuba ta fara ci tana kaɗa kai alamun girkin ya mata daɗi ta ɗago ta ce "Amma wa yayi girkin nan hala"?dariya ta yi ta ce "Ni ce na yi ya miki daɗi"? Jijjiga kai tayi tace "Ya min sosai gaskiya zaki koya min"daɗi ne ya kama ta tace "Ai ko zan koya miki kala kala"rage murya tayi ta ce "Kin san kuwa saboda iya girki na ta sa mai gidan mu ya fi so na?duk sauran tsohuwar hannu gare su basu iya girkin zamani ba in kuma aka ce badu yarda ba su ƙi yarda"dariya maganar ya bata dan haka ta dara ta ce "Yayi kyau toh ai zaki koya min dai ni"ta ce sosai ma "Yauwa toh bari in yi in gama" "Toh likiciya"darawa tayi dan sunan dariya yake bata daga haka suka cigaba da hira kaɗan kaɗan har ta gama lokacin har 2 ya wuce a nan ne kuma matan gidan suka rinƙa zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya kowa na son samin shiga a wurin ta ita abin ma mamaki yake bata kishi muraran babu ɓoyo sai dai ayi ta dariyar fatar baki Bayan fitar su ta tafi wun mai gari suka gaggaisa ya mata ya hanya suka ɗan taɓa hira sai duddubawa take dan ganin ta inda zai fito amma bata hange sa ba kuma babu wanda ya sanar da ita inda yake dan haka bayan sun koma ciki suna tsaka da hirar su ita da zulfa'u aka shigo kiran ta wai ta zo su tafi Ta zo su tafi ina kuma?ta ma kanta tambayar dan haka ta ce da zulfa'u tana zuwa ta fita Ɗan duba shi tayi kafin ta hango shi cikin half jumfa da hula baƙaƙe kallon seconds ta mai kafin ta fara takawa zuwa wurin shi ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta ce "Gani"sai da ya ƙare mata kallon ƙuril har ta fara tsarguwa kafin ya ce "Ba cewa nayi ki zo empty handed ba cewa nayi ki zo mu tafi hakan na nufin ki zo da kayanki mu tafi ainihin masaukin mu"! Kallon shi ta yi ta ce "Akwai wani masaukin da ya fi wannan ne"?ɗan jan aji yayi kafin ya ce "Yeah cikin ƙauyen zamu tafi inda a nan zamu gabatar da outreach ɗin nan kawai somintaɓi ne ai kin fahimta"? Ya wani sha mur wannan abin da mamaki yake cikin ƙauye kuma?jin kai irin nata ya sa bata kuma mai tambaya ba ta juya ta koma cikin gidan cikin wani yanayi ganin haka ya sa zulfa'u tambayar ta ko lafiya bata ɓoye mata komai ba ta sanar da ita ai kuwa ta ce bsta san da zancen ba babu inda zata tafi da haka ta wuce zuwa wun mai garin bayan mintuna ta dawo ta ce da ita "Ai an gama mai gari ya ce babu inda zaki tafi tunda kin ce nan ya miki kuma shima bokan turan ai nan ya kamata ya zama masaukin sa ba chan da yake son ku tafi ba"wani sanyi ta ji at least ba zai kai ta ƙauyen da ya fi wannan typical ba dan haka ta share zancen nasa ta cigaba da sabgogin ta har dare bata kuma ji daga gare sa ba bata kuma damu ba. A ƙaida ranar monday zasu fara gabatar da outreach ɗin wanda zai ɗauki steps uku ne a cikin sati ukun da zasu yi,satin farko zasu binciko su zaƙulo matsalolin mutanin garin dan su yi creating rapport da mutanin garin a sati na biyu kuma zasu gabatar da outreach ɗin sai satin ƙarshe kuma zasu ƙara koyar da su abubuwa dangane da lafiyar su. Bata sami network ba ma a ranar haka ta kwanta washegari da ya kasance litinin kuma ranar zasu fara wanda zai yi taking place ne a wani primary school ɗin ƙauyen tun safe ta gama shiryawar ta ta zauna zaman jiran sa ya zo su tafi bai aika a kirawo ta ba sai da ƙarfe tara na safe ya buga sannan ya aika a korawo ta,sallama suka yi da ƴan gidan ta fita cikin shigar mutunci doguwar riga maroon da gyalen ta ta yafa ta ɗau ƙaramar jaka inda ta saka wayar ta da pens ɗin ta tana jiran sa babu daɗewa aka aika kiran ta har ƙofar gida zulfa'u ta rako ta suka yi sallama "Goodmorning"tace da shi ya ji mamaki dan haka ya tsaya kallon ta kafin ya ce "Morning"daga haka suka kama hanya babu uhm babu umumh haka suka cigaba da takawa har suka iso inda zasu sami abin hawa suka shiga ya masu kwatancen inda zasu sauka ba wata doguwar tafiya suka yi ba suka iso inda zaau sauka dama mai gari ya aika a sanar da su cewa ga bokayen turai nan tafe su haɗu a inda suka saba haɗuwa dan haka a cike suka tarar da wurin. A hankali suka taka zuwa gare su sai hayaniya ake ta yi dan ganin mace tare da tsohuwar fuskar da suka saba gani murna sosai matan suka yi dan akwai matsaloli da dama da suke son a magance masu amma rashin ƴar uwar su mace yasa ba su son sanar da Dr Zaid Maher gashi su ba wani ƙarfi ne da su ba bare su rinƙa zuwa asibitin cikin gari wahala suke sha sosai dan sai sun yi dakon mazajen ke samin abin masarufi matan kuma sune sai da kayan gida dangin su waran fulani, barkono, kindirmo da dai sauran su dan haka kullum akan sana'ar abin da zasu rufawa kansu asiri suke dan haka cuta na cin su amma da ya fara sai dai a yi na gida ya lafa da zarar ya tashi a kuma banka concoction a lafar da rashin lafiyar,ƴaƴan su babu makarantar boko ba wai dan basu da burin saka ƴaƴan ba sai dan basu da hali toh mutanin da lafiya ma bai gimshe su ba ina wani karatun boko ga matsalolin mata da ke ɗawainiya da matan yankin amma babu wasu ƙwararru sai na gargajiya Toh a wata tafiyar da Dr Zaid Maher yayi ne zuwa garin Adamawan ɗaurin auren wani abokin aikin su wanda ya zaƙulo matar sa daga cikin garin dan ko da yake ba su labarin inda ya samo ta mamaki suka ji ba kaɗan ba sai da ya masu bayanin kirki da dattako irin na ƴan garin wanda shi ɗin ganau ne ba jiyau ba shi yasa ya ga match ɗin sa a nan she was just 16 years da ya aure ta ya ce da su zai saka ta a makaranta a kan rainon shi zata taso wanda hakan ya ja ra'ayin Dr Zaid har ya yi takakkiya zuwa garin _koma_ a nan ko ya shaida dan tun daga gidan mai gari ya ga kara da martabawa har dai ya ci karo da sanyin idaniyar sa kamar yadda ya laƙaba mata dan haɗuwar su ta farko kare shi ta yi daga ƴan iskan gari da suka kawo mai hari a hanyar sa ta komawa masaukin sa kasancewar ta budurwar mudan ɗan gayu sai suka rabu da shi da ta ce masu tare suke kuma duk wanda yake cikin ƙauyen _koma_ ya san labarin ta da mudan kuma kowa ya san mudan babu kirki dan akan budurwar sa yana iya shukawa mutum rashin mutunci duk kusancin ku kuwa, Tun daga lokacin ya tambayi gidan su ta mai kwatance har dai ya kai mata ziyara kafin ya bar garin wanda sai da ya bar garin ya fara zargin kamar a kwai shaƙuwa mai girma a tsakanin su sai dai bai yi concluding ba outreach ɗin shi huɗu a garin kuma ko wanne a gidan su ake masa masauki wanda hakan ya kuma janyo kusanci tsakanin shi da sanyin idaniyar sa sai dai still bai sanar da ita abin da yake ji game da ita ba though bai gama yarda ba kuma bai jin giyar son na fixgar sa ko me yasa ohon mai,toh a wannan tafiyar ne ya yanke hukuncin gaya mata not knowing she have a man da take mugu mugun so da ji da shi. Toh ko a tafiyar da ya so su yi a daren jiya da baby doctor gidan su sanyin idaniyar sa ya so su tafi dan hankalin shi ya fi kwabciya a chan amma kuma alfarma da mai gari ya nema a wun shi a daren jiyan ya sa ya ji wani iri ya amince akan zasu zauna a nan but da sharaɗin zai rinƙa tafiya chan gefen da ya fi wayo. ko da ya koma ɗakin sa ya fi dangana laifin da baby doctor ya yi fushin ita ce ta hana sa zuwa gidan da ya saba zuwa but babu komai ita ta jiyo dan shi chan zai rinƙa wuni in ta gan ta zaume ita kaɗai ta yi bayani ai,sai ka ce wani abin ya ke mata dama chan.. "Sannun ku da zuwa bokayen turai muna maku barka lale lalen ku"da murna suka masu sannu da zuwa suma suka gaida su inda suka natsu dan jin da me suka zo "Ni sunana Dr Bilkisu Muhammad kuma ni ce sabuwar fuskar da ta zo tare da likitan ku da kuka saba zuwa ni maɗin likita ce zan mayar da hankali da kuma aiki na a fannin mata shi kuma zai yi fannin maza da fatan zaku bada haɗin kai"?jin daɗin su ya kasa ɓoyuwa har sai da suka nuna dan kamar haske ne ya bayyana a birnin rayuwar su ganin likita mace. "InshaAllah likita zamu baki haɗin kanmu"first impression last long dan haka ta yi murnar haɗin kan da suka bata dan haka ta kalle shi ta ce mai "Ina ga mun yi creating rapport mai ƙarfi so we can commence"murmushin fatan baki ya mata ganin jama'a sai ya ce "Yes we can" Daga haka suka fara shirye shiryen gabatar da abin da ya kawo su from no where suka ji an ce "Wai farawa za'a yi ban da ni"? Juyawa suka yi daga shi har ita sai ta hango wata ƴar yarinya ƙarama dan ba zata wuce 14years ba fara kyakyawa kamar am zana ta doguwa ƴar mai jiki da ita tana tafe tana taunar chewing gum tana tafe kamar wacce bata san tsarin tafiya ba cikin rashin kunya da fitsara ta tako har inda suke ta buɗe baki tana jujuya idanu "Wai toh ba dan na zo ba shikenan babu wanda zai aika a kirawo ni"!? ta faɗa cikin izza kamar wata sarki,gabaɗaya mutabin wurin shiru suka yi suna kallon ta dan in da sabo toh sun saba da halayar nata na rashin girmama na gaba da ita gashi ba'a isa a mata faɗa ba da a mata faɗa gwara a yi shiru a zuba mata idanu dan bata da kunya ko kaɗan "Wacece ke kuma me yasa tun lokacin da aka zo ke ɗin baki zo ba alhalin tun jiya aka sanar daga fadar mai gari"cewar Bilkisu cikin ɓacin rai dan babu sallama babu gaisuwa kawai fatam fatam faransa kamfani ba oda Instead ta bata amsa sai ta ja tsaƙi ta na cewa "Hmm bokan turai ko?toh ki je ki tambaya a baki gamsashiyar labarin ko ni ɗin wacece hatta da ƙaramin yaro ya san da labari na dan haka ni ban da lokacin baki labari na yauwa"daga haka ta juya tana tattauna chewing gum ɗin ta tana sarrafa shi yana bada ƙarar ƙas ƙas ƙas.. Duk mamakin yarinyar ya gama cika baby doctor dan haka ta juya ga Dr Zaid dan tambayar ko ita ɗin wacece tunda shine tsohon zuwa dole ya san ta "Who is she"? Cikin ko in kula ya ce...........,,,,,, "Sunan ta Asma'u kuma ƴar nan yankin ce again bai kamata ki tsare ta kina mata ihu ba kawai dan ta zo ƙarƙashin ki neman abu a gare ki ba"daga haka yayi shiru yarinyar ta kada baki ta ce "Ɗan birni baka faɗa mata ɗayar sunan ba"sai ta juya ga Bilkisu ta kalle ta cikin fitsara ta ce "Ma'ulle"inkiya ta kenan kuma bana ɗaukar raini ban ma san abin da ya sa na kyale ki kika gasa min magana har haka ba ba tare da na nuna miki ko ni ɗin waye ba"ta juya kai tana rakaɗi Tsyawa kallon ta tayi cike da alhinin wannan fitsararriyar yarinya marar tarbiya ta juya ta kalle shi ta ce da shi "What ever her name is ba business ɗi na bane dan bata gaba na iya abin da na sani ba zan ɗauki rashin kunya daga wun ƴar ƙanƙanuwar yarinya ba kai da ka san ta sai ka nuna mata muhimmancin zuwa na dan bata isa in zauna orienting ɗin ta ba"a zafafe ta karasa maganar wanda hakan ya bashi mamaki dama ta na da masifa har haka?shi kam bai taɓa gani ba sai dai ji a hospital a ce ta masife su a asibitin but shi bai taɓa witnessing ba "Me ya sa ba zaki iya mata magana da kanki ba alhalin kin san ke ce da laifi"ƴar ƙaramar scoff tayi ta ce "Are you for real"? Ɗage mata gira ɗaya yayi daga haka ta mai banza ta cigaba da abin da take da niyar yi "Ku yi haƙuri fah kun san a wuri dole mutum ya haɗu da masu tarbiya da marasa shi in kuma mutum ya haɗu da marasa sanin ina ke masu ciwo dole ya daidaita su domin samin kyakyawar sakamako a wun aiki ko ba haka bane"?cikon chorus suka amsa da "Haka ne likita"ta yi murmushin gamsuwa ta ce da su "Toh yanzu dai zamu fara abin da ya kamata saboda yanayi na gari tunda ruwa ake yi yanzu gashi akwai ayyukan gida da za'a yi in an bar nan dan haka ba tare da ɓata lokaci ba zaku gaya min sunayen ku ne da shekarun ku haka ma da ayyukan da kuke yi"murna suka yi sosai dan she tried as much as possible ta wurin bringing kan ta so low wanda ya saka su jin kamar ta saka kan ta a shoe ɗin su ne dan haka babu ɓata lokaci suka fara gabatar da kan su ɗaya bayan ɗaya yayin da ita kuma yarinyar mai suna Asma'u ta haɗe rai tana ta faman kumbure kumbure yayin da shi kuma ya ke ta bata haƙuri,sam ta manta da su a wurin ma kwata kwata sai da aka yi rabi da introduction ɗin ta fara duba shi,chan wani bakin bishiya ta hango su zaune abin ya firgitata dan haka ta juya ga ɗaya daga cikin matan da suka yi introducing kan ta ta ce mata "Wai ni kuwa baba waccan yarinyar wacece ita"?ajiyar zuciya ta sauke ta ce cikin jimami "Kin ga waccan yarinyar"? ta girgiza mata kai sai ta cigaba "Sunan ta dai kamar yadda bokan turai ya sanar da ke Asma'u ɗiya ce ga mamman mai rasuwa dattijon kirki da kamala mutum mai haƙuri duk faɗin yankin nan ana daraja shi ba kaɗan ba dan bayan sarki da mai gari sai shi halin dattako irin tasa yasa ko matsala aka samu wun shi ake zuwa dan ana mutunta shi ba kaɗan ba..ita kaɗai ce ƴar shi mace yayyen ta biyu maza duk yaran kirki ne su ita kaɗai ce ta fito bare babu hali dan uwar ta ta yi ƙoƙarin tarbiyartar da ita haka mahaifin ta ma yayi ƙoƙarin sa sai dai albasa bata yi halin ruwa ba dan daɗin taɓarɓarewar tarbiyar ta wannan tsagerin saurayin nata mai suna Mudan yaron nan babu hankali gashi dai a fuska kamili daga shi har ita sai dai babu halin arziƙi toh a faɗin ƙauyen nan ko wani lungu da saƙo an san su dan tare suke zaga garin kuma duk wanda ya san Mudan ya san shi da jarabar tsiya da fitina toh haka duk wanda ya taɓa Asma'u ya taɓo jaraba dan kusan kowa tsoron sa yake ji ba kaɗan ba shi yasa ƙarfe shida na yamma na bugawa zaki ga yaran gari sun koma gidajen su amma a lokacin Asma'u take cancaɗa kwaliya ta fita ita da Mudan su zaga garin nan sai karfe tara na dare suke dawowa an daka har an gaji amma bata daina ba dan haka aka zuba mata idanu kawai toh kamar dai yadda muka ji shi wannan bokan turai shine yayo dare a hanyar sa ta dawowa daga cikin gari tsageran garin suka tare shi a hanya itakuma sun rabu da Mudan kenan zata dawo gida ta ci karo da su a hanya ai kuwa shine ta masu kaca kaca kuma sun san ko ita ɗin wacece sai suka gudu ba dan haka ba da sun mai kisan gilla dan ba su son harkar asibiti a cewar su duk ma'aikatan asibiti bankaɗo sirrikan su na shaye shaye suke yi daga haka gwamnati sai ta saka masu ido har a tono asirin su a hukunta su wanda hakan ba daɗi ke masu ba,toh kin fah ji labarin wannan botsararriyar ƴar wacce ta fi ƙarfin jama'an gari... Gwauron numfashi baby doctor ta saukeyayin da jama'ar wurin ke jinjina kai dan gabaɗayan su sun san da wannan rikitacciyar yarinya mai sigar marasa kunya. Kuma kallon su tayi sai ta shiga mamakin yadda aka yi rasa yarinyar da zai saurara duk jiji da kan nan nasa da fa'ili iya nan ya tsaya lallai dole ta raba shi da wannan fetsararriyar yarinya dan sam bata ma da gurbin zama cikin rayuwar su saboda bata da tsari bare tarbiyar da zata taki matakin zama cikin ahalin su. Hmm ji ƙarfin hali irin na baby doctor. Cigaba da aikin ta tayi a ƙarshe ta aiki wani yaro ya kirawo mata su sai da ya ja lokaci kafin ya taso ya zo Tana gaba yana baya suna tafe suna ɗan zantawa kallon su take yi ta mayar da idanun ta kan yarinyar da ke tafiya cikin iyayi tana mamakin rashin ji irin na yarinyar har dai suka nufo su sai ya dakata ya ce da ita "Kin kira ni"cikin tsare gida yayi maganar itama sai ta haɗe rai ta ce "Am done with today session sai ka zo mu ɗau evidence"bai ce ƙala ba ya ɗan rage murya ƙasa ƙasa ya ce mata yana zuwa tana dariya ta ce mai toh haushin ta baby doctor ta ji ta ce "Na fah gaji"dakatawa yayi ya fiddo wayar sa ya saita ya fara videoing ɗin su yana yi yana tambayar yadda suka ji daɗin abin haka har suka gama da zasu tafi gida aka basu packs ɗin ktautar su kayan wanki da na wanke wanke as an incentive duk dan su dawo washegari da murna haɗe da addu'oi suka tafi gidahen su su kuma suka kama hanyar komawa gida bayan ya ɓata mata lokaci yana hira da Asma'u sun dai rabu akan da yamma zai kawo mata ziyara da haka ta raka shi har wurin da take tsaye ta kalle ta ƙerere ta ce "Toh likita ni na tafi a huta gajiya lafiya"ƙala bata ce da ita ba wanda bai mata daɗi ba dan so tayi ta tanka mata sai ta juye mata fitsara sai dai hankalin wayayye da ƙidahumi ba ɗaya ba dan haka ta ƙudiri yi mata rashin kunya duk dan ta ƙure ta dan ta amsa mata. A hanyar su ta komawa gida ne ya ce mata ɗazu an kira ta bata ɗauka ba an kira shi wai ina take. Cikin hanzari ta tsaya ta fiddo wayar ta ta ga full service da sauri ta bi kiran da aka mata wanda ta riski 10 missed calls daga family ɗin ta sai na Hajiya Madina da na Bahajjatu kiran farko kiran mahaifiyar ta tayi da ta ɗaga sai ta yi kamar ta saka kuka ta ce "Umma ina yini ya gida ya Bilal da su Abba kin kira muna orientation ne sam ban gani ba"dariya Hajiya Zeenat tayi daga ɗaya ɓangaren ta ce "Ohh su baby an girma babu dai wani abin da bai maki ba ko"?girgiza kai tayi kamar tana gaban ta ta ce "Umma komai yayi mutanin na da kirki" "MashaAllah toh yanzu ina kuke na ji Zaid ya ce min motar ku ta sami matsala a hanyar ku ta tafiya dan haka a taxi zaku koma gidan"cikin kaɗuwa ta ce "Uhumm umma ina Bilal ki bashi wayar"murmushi ta yi ta ce "Bilal na gida baby"da mamaki ta ce mata "Ke kuma ina kike umma"ɗan sukwui tayi kafin ta ce "Errr....mm..baby muna airport ne"!! tsit communication ɗin ya yanke kafin ta ce "Umma ba dai wannan tafiyar zaku yi ba"? Cikin jin nauyin ɗiyar tata ta ce "Eh baby tafiyar za mu yi kin ga ai ba mu kadai da baban ki bane har da su Hajiya Madina da Dr zamu tafi"cikin ɗari ɗari ta ƙarasa maganar. Kasa furta komai ta yi dan in suka cigaba da bin halin iyayen su toh tabbas wataran zasu haɗiye zuciya dan haka ta ce mata "Alright safe trip umma ki gaida su Abban"kitt ta kashe wayar tana ƙoƙarin kiran twin brother ɗin ta wanda ringing biyu ya ɗaga "Haba apple tun jiya nake ta kiran layin ki bai shiga me ya faru"sanyi ta ji a ranta kafin ta ce "Apple garin ne babu network sai yanzu a hanyar mu ta dawowa daga wun outreach ɗin ne na lura shi yasa na kira" "Ohh i was very scared toh ya garin ba dai sanyi sosai ko"?murnusawa tayi ta ce "Stop acting like my father sanin kan ka ne zan iya kula da kai na ba sai an gwada min ba"dariya yayi kaɗan ya ce "A'a fah apple kar ki yarda da mutanin ƙauyen nan na san su da son zuwa rafi kar dai ki rinƙa bin su tohm"!! dariya ya bata dan haka ta ɗan dara "Yes sir"gabaɗaya suka dara kafin daga bisani ta ce "Bilal kana ina su umma suka kama hanyar tafiya yawon buɗe idon nan bayan na ce duk yadda zasu buga kar ku bar su har da yaya Luk bai hana ba gashi yaya Jamil baya gari bare ya tsawatar masu why did you allow them"? "Hmm Bilkisu kenan ke kan ki kin san halin mutanin nan ba fah wannan ne na farko ba da suke sneaking su gudu toh ko wannan ma bayan tafiya ta office na ji kiran sweet wai ko su umma na gida na ce mata eh ta e basu nan na ce mata na baro su gida ta ce in kira in ji toh ko da na kira apple wallahi ce min aka yi bin baya na suka yi da na fita suma suka fita tare da su Abban su sweet wai sun tafi airport i have no clue akan tafiyar nan ta su forgive me"sauke numfashi ta yi kafin ta ce da shi "Alright gobe zamu yi magana inshaAllah dan yanzu a gajiye nake"!! "Alright apple i missed you"ɗan murmushi tayi ta ce "Me too bye"suka yi sallama a nan ta tuna da mutum na tsaye na jiran ta. "Ban fah gama abin da nake yi ba kana iya tafiya in na gama sai in biyo ka"ɗaga kafaɗa yayi kafin ya fara tafiya bata ji mamaki ba dan dama bata saka ran samin security daga gare sa ba kiran layin Bahajjatu ta yi bata ɗaga ba daga nan ta kira Hajiya Madina "Ammi ina yini" "Ƴa ta lafiya ƙalau ya yanayin garin kuma ya baƙunta"? "Alhamdulilah Ammi har yanzu jirgin ku bai tashi bane"? Da mamaki ta ce "Baby wa ya gaya maki muna airport"? Murmushi kawai ta yi ta ce "Umma ce dama kawai kira na yi dan in yi wishing ɗin ku safe journey"sai ta ji nauyin ta amma still dan kar jikin su yayi sanyi su ce sun fasa tafiyar sai ta ce "Alright baby mun gode i promise to call you da zarar mun sauka da fatan dai Zaid na kula da ke kamar yadda ya kamata"? Abin mamaki ya bata amma sai ta ce "Eh Ammi,toh ni zan ajiye wayar sai dai kun kira mu"! "Ok take care dear" "Uhum bye"ta datse kiran yayan ta Lukman ta kira bai ɗauka ba sai ya kashe ya kira ta "Baby sis tun jiya nake neman layin ki bai shiga da fata dai komai lafiya"? Ɗan murmushi ta yi tana ƙara son ƴanuwan ta dan irin kula da suke nuna mata "Yaya Luk ina cikin lafiya mutanin na da kirki sosai babu network ne a inda muke shi yasa ban kira ba jiya sai yanzu da muka baro accommodation ɗin mu ne na ga full service shi yasa na kira" "Toh shikenan da fatan dai babu damuwa"? "Hmm yaya Luk ni na rasa me kuka maida ni kowa sai tambaya ta yake da fatan babu komai of course babu komai babban yaya na" "Toh na yarda but ki kiyaye sanyi kin sa yanayin garin akwai sanyi kar ki rinƙa shan kayan sanyi fah kin ji ko"? Darawa ta yi kafin ta ce "Yes sirrrr"ta ja sir ɗin ta yadda abin ya zame masu abin dariya har suka daran kafin ta mai sai anjima akan washegari zasu sake yin waya. Daga shi sai babban yayan ta Jamil ta kira ya fi sau huɗu bai ɗaga ba ƙarshe matar sa ta kira zainab a karo na biyu ta ɗaga tana tambayar ta "Haba Bilkisu tun jiya hankalin yayan ki ya tashi wai baki ɗaga kiran shi ba ashe ma kwata kwata kiran ne bai shiga ba sai fah da umma ta ce mai Zaid ai ya gaya masu babu service dan haka kar a damu da kiran su akan in ku kuka kai inda zaku na reaching juna zaku kira tukunna fah ya sami damar yin barci har zarah ta kasa barci dan hankulan mu a tashe yake toh yanzu ya lafiyar ku"? Dariya sosai tayi irin tata gatar daban ce dan haka ta ce "Aunty zee ai ko ɓata nayi sai haka baki bari mun gaisa ba kawai kika hau magana toh ina yini"itama dariyar ta yi kafin ta ce "Kin raina ni Bilkisu toh lafiya ƙalau ya kuke ya baƙuntar"? "Hmm Alhamdulilah zamu ce aunty zee mutanin na da kirki gaskiya da fari i was scared amma yanzu ba laifi na ma fara sabawa da su" "Toh na ji daɗi da fatan ba wankan ruwan sanyi suke yi ba ko"? "Haba aunty zee ko wankan ruwan sanyi suke yini sai in yarda in yi"? "A'a dai wai saboda lafiyar ki ne kar fah ki rinƙa fitar yamma kin ji"? Dariya ta yi kafin ta ce "Na ji aunty zee zan kiyaye ina zarah"? "Tana falo yanzu muka gama darun cin lunch"suka saka dariya daga bisani ta ce da ita "Na kira yaya bai ɗaga ba in dai ya dawo ki sanar da shi" "Eh ba zai ɗaga ba da yake sun tafi wata meeting akan tafiyar da zasu yi next week but zai kira ki ai" "Noo koh ya kira ba zai samu ba dan babu network a chan ni dai zan kira shi gobe in Allah ya kaimu" "Ohh Bilkisu wai babu service a chan ɗin"? Darawa ta yi ta ce "Eh babu aunty zee sai goben dan ga chan Dr Zaid na jira na zamu yi wayar gobe bye" "Toh take care please" "I will bye"suka ajiye wayar ta ɗaga kai ta hango shi chan tsaye bai tafin ba instead ya jingina da bishiyar wurin yana waya ga kayan su a ƙasa grfe kaɗan da shi.. Karasawa tayi zuwa wurin shi ta ce da shi "Na gama"daga haka ya sauke wayar suka cigaba da tafiya yana riƙe da kayan har suka iso kan titi inda suka tari mai adaidaita ya kai su har masaukin su wanda ba wani nisa ne da shi ba daga wun outreach ɗin da suka fito zasu shiga cikin gidan ya tsare ta ya ce mata "Baki kira sakaran saurayin nan na ki ba halan dan ya kira ni yana umartata da in baki waya kuyi magana dan naki a user busy yake saka mai me yasa kike son saka min ciwon kan ki"? Mamakin shi ta ji sai ta ce "Hmm da sauƙi tunda sakarai ne yana da tarbiya da ilimin zamani ba kamar wasu da ke tafe a baibai ba babu kwaɓo"daga haka ta yi gaba ta bar shi da mamakin ta dama ta iya magana haka bai sani ba lallai mijin ta na da aiki toh wacce bata da kwaɓon?ba dai da Asmien sa take ba?no ai bata san labarin su ba toh wacce bata da kwaɓon? Ya ɗaga kafaɗa ya shige cikin gidan shima sai barka da zuwa ake masu da abinci aka fara tarbon su sai da ta yi wanka sannan ta ci abincin ta ta ƙoshi sannan aka dasa hirar abin da ya faru a ranar sosai suka sha dariyar labarin Asma'u dan a nan zulfa'u ke kuma gaya mata ai suma sun san da labarin yarinyar na rashin jin ta har yamma kafin ta ce da zulfa'u ita fah yau karatun islamiyya take jin yi mamaki sosai ya kama zulfa'u ta ce da ita "Ke koh likiciya a ina zaki yi karatun islama da ɗanyen daren nan"?murmusawa tayi ta ce "A nan gidan zamu yi shi yanzu haɗo kawunan yaran gidan nan su zo nan shashin naki mu fara kin ga yanzu biyar ta yi zuwa shida da rabi sai mu tashi kafin lokacin sallar magrib sai mu ɗora bayan sallar isha'i zuwa takwas da rabi sai washegari ko ya kika gani"? Ta zuba mata idanun ta shiru ta yi tana tunanin ta yaya za'a fara wannan sabuwar tarba wacce ƴan gidan basu saba da shi ba iyakan yara su tafi makarantar allo tun ƙarfe biyu zuwa bakwai na yamma toh babu wani tsatsauran saka ido da suke ma yaran bare su san ya yanayin karatun nasu yake gudana dan haka ta ce mata "Anya likiciya wannan sabuwar aƙida za ta karɓu kuwa a gidan nan"?darawa tayi kafin ta ce "Me zai hana kuwa zulfa'u?ke dai kawai ki tafi ki sanar da su su zo nan akwai labari"miƙewa tayi ta fita tana fargabar Allah dai ya sa su amince su biyo ta amma abin da kamar wuya... Bayan fitar ta sai ta yi saurin fiddo cupcakes ɗin ta ta jere su saman dardumar ɗakin ta fiddo ƙananan goodies ɗin ta ta baje su a wurin ta ɗau wayar ta ta na latsawa kusan mintuna goma sai ga yaran sun fara shigowa ɗai ɗai har dai suka ƙarasa shigowa daga baya iyayen yaran suka biyo su sai zulfa'u da ta tafi kiran yaran. Dakatawa da latsa wayar ta yi ta ce da su su zauna,suka zazzauna suna kallon kayan kwalam ɗin dama abin da take so kenan ta janyo ra'ayin su kuma ta yi nasara dan haka ta fara da cewa "Yara manyan gobe sannun ku da zuwa"cikin fara'a ta yi maganar suma cikin zalama suka ce "Yauwa sannu anti"cikin turancin su da take irin wanda suka tsinta a bakin manya, Murmusawa tayi ta ce "Yauwwa toh yau dai ga kyauta nan na kawo maku sai dai ba zan baku ba"ta ida tana haɗe rai sai yaran suka yunƙuro suka ce "Me yasa ba za ki bamu ba anti"? Ta ɗan tsare gida kafin ta ce "Kuna son kyautar kenan"? Cikim sauri suka haɗe baki wun cewa "Eh muna so mana anti"point ɗin gyara kenan kalmar _'mana'_ da suka yi amfani da shi wannan kalmar na rashin tarbiya ne dan haka tace "Cewa zaku yi eh ba rh mana ba" Sai suka yi saurin gyara maganar ta hanyar cewa "Eh muna so aunty"sai ta sassauta fuskar ta ta ce "Toh zan baku sai dai da sharaɗi"suka hayayyaƙo suka ce "Menene anti"? "Karatun islamiyya zamu yi wanda in har kuka bani haɗin kai toh inshaAllah kullum zaku rinƙa samin kyautar da ta fi wannan ma kun yarda"cikin zumuɗi suka ce "Eh mun amince anti"tafawa ta yi ta ce "Yauwwa yaran anti toh ku gyara zaman ku"ta yi demonstrating masu zaman tarbiya suka kwaikwaye ta ta fiddo Qur'an ɗin ta ta ajiye ihzu biyu ta buɗe shafin baƙi ta ce da su "Kun san wannan"? Suka girgiza kai alamin eh ta ce "MashaAllah toh kun iya karanta shi"? A wannan karon kaɗan ne suka amsa wanda hakan ya bara ikon gane cewa ba su da yawa da suka san Qur'anin dan haka ta ce ma waɗanda suka iyan su fara ai kuwa ba laifi ta sami kaɗan kaɗan daga cikin su da suka kawo alif zuwa nunun babu tangarɗa kuma yaran duka ƴan ɗakin uwargidan mai gari ne dan haka sai uwar ta fara alfahari kenan kishin ma har da ƴaƴa ake yin ta lallai akwai aiki dan haka ta ce da su "Yanzu dai zamu yi karatu tun daga alif har zuwa ƙarshe bayan sallar isha'i sai a yi maimaici wanda a nan kuma zan baku kyautar ku kun amince"? Suka amsa da eh daga haka suka fara kaɗan kaɗan har ƙarshe suka maimaita sau uku sannan ta ce su tafi masallaci in sun dawo sai su cigaba yaran da murna suka tafi bayan fitar su iyayen suka fara tambayar ta "Likita mun gode fah wai dama bayan karatun siddabarun naku har na islama kuka iya"? Dariya kawai tayi ta ce "Ai da sannu zaku tantance hakan yanzu dai ku tafi ku yi sallah in yaran sun dawo sai mu ɗora"da toh suka rabu yayin da zulfa'u ta rinƙa yabawa baby doctor da irin ƙoƙarin da ta yi akan Allah kadai zai bata lada dan dama tun zuwan ta gidan ta so gyara tarbiyar amma iyayen yaran suka ƙi bada haɗin kai toh gashi yanzu Allah ya kawo ta abin sai godiya. Bayan sallar isha'i yaran suka dawo ta saka su maimaitawa ashe dai yaran na da brain gyara kaɗan aka ci su daga haka ta basu kyaututtukar su sannan ta raba su gida uku a inda tayi mixing ɗin yaran ɗakunan uku ta ce da su washegari gasa za'a yi duk group ɗin da suka lashe gasar za'a basu kyauta mai girma dan haka ta raba masu inda zasu yi bita yaran suka tafi da murna da ƙudirin lashe gasar washegarin iyayen su sai murna suke ashe dai ƴaƴan su na da hazaƙa cutar da kansu suke ta yi basu sani ba wai suna kishi. Bayan fitar iyayen suka cigaba da hira tare da zulfa'u a inda take ce mata har karatun boko zata fara koya masu kaɗan kaɗan murna sosai zulfa'u tayi ko ba komai sun sami hasken duhun kan da suka daɗe a ciki suna tsaka da hirar su mai gari ya aika a kira baby doctor dan haka ta tafi ta same shi a falon shi yana zaune shi da Dr Zaid hira suke yi,suka gaisa ya jinjina ma ƙoƙarin ta na ranar da godiya dan matan shi sun sanar da shi komai cikin jin daɗi da farinciki dan haka ya mata godiya ta musamman "Haba ai ba komai yi wa kaine kuma ai ƙanne na ne babu komai ai mune da godiyar karamcin da kuka mana na bamu muhalli a ƙarƙashin inuwar ka Allah ya saka da alkhairi". hira suka taɓa har zuwa ƙarfe tara na dare jifa jifa yake saka masu baki dan shima ya ji daɗin sabuwar rayuwar da ta ke son kawowa ahalin gidan,9:15pm suka yi sallama ta wuce ko da ta koma tea kawai ta sha da cupcake ɗaya ta kwanta bacci. ************** _Next day_ Kamar jiya haka yau ma ya kasance sai dai a hanyar dawowar su ya ɗan ja ta da hira "Jiya kin yi ƙoƙari i must say good job"ta kalle shi cikin mamaki dama ya iya complement hmm "Thank you"daga haka suka cigaba da tafiya sai dai a daidai bakin titin suka yi karo da Asma'u tana tahowa babu tsari "Ɗan birni"ta kwala mai kira suka dakata suka juya kallon ta a hujajjan ta ke tafe da zuwar ta ta yo kansu kamar zata faɗa masu da sauri Bilkisu ta dakatar da ita ta hanyar saka hannu tsakanin su da ita "Malama kina da matsala ne"?kallon raini ta mata kafin tace "Ni da ɗan birni nake magana ba ke ba" Murmushi ta yi ta ce "Ai duk ɗaya muke ni da shi dan haka in kina da abin cewa faɗi ina jin ki" Abin ya bata haushi dan haka ta ce "Chan maki ban da lokacin ki"ta juya ga Dr Zaid ta ce "Ɗan birni sai ka zo anjima ai zaka zo koh"? Sai yanzu ya san bata da tsari sosai sai dai bai jin zai iya yi mata faɗa dan haka ya girgiza kan sa ta juya ta yi tafiyar ta. Kallon sa Bilkisu ta yi ta ce "Allah ya shirya"bai amsa ba sai ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya ce "Ya zaki rinƙa yi ma budurwa ta ɓatanci a gaba na wannan ai cin fuska ne"dakatawa tayi da tafiyar da take yi ta juya tana kallon shi ido cikin ido ta nuna shi da yatsa ta ce "You?her?budurwar ka"? Sai kawai ta fashe da muguwar dariyar da bata taɓa yi ya gani ba dan haka sai abin ya bashi mamaki dan haka sai ya sake jiki yana kallon ta abin gwanin sha'awa he never knew she is this beautiful ita kuma sai dariya take mai babu ƙaƙƙautawa dan abin ya bata dariya ta yaya zai ɗau wannan ballagazar ya ce budurwar sa ce hala bai da labarin saurayin ta Mudan ne taɓdijam abin abin bada dariya ne ɗagowa tayi ta ce "Sorry forgive my manners but i can't help it but laugh"ta cigaba da dariyar sho kuma kamar zombie ya rinƙa kallon ta...............

0 Comments