DAN MAKAHO COMPLETE

DAN MAKAHO COMPLETE
Kamar kullum, zaune suke kan Benchi daidai shagon Eskaley dake farkon layi, zaman banzan da suke yi ke nan duk bayan Sallar La'asar, daga gefenshi Haruna ne ke shan Sigari. Haruna ya mik'o mishi Sigarin da ke dab da k'arewa, ya karba ya sa a baki zai zuk'a ke nan suka hada idanuwa da halitta daya da yake jin kunya duk duniya, da sauri ya tura karan sigarin cikin doguwar hannun rigarshi ya kawar da kai kamar ba wani abu. K'arasowa ya yi bakin shagon ya musu sallama. Haruna kadai ya amsa tare da gaishe shi sai Eskaley, shi dai gudan kawar da kansa ya yi. Naira Dari ya fiddo daga Aljihun gaban rigarshi ya ce da Eskaley "Barka dai! Maggi za ka bani Mai Star da Farin Maggi" karban kudin Eskaley yayi, ya hada mishi kayan daya bukata ya ba shi chanjin Naira Goma Sha Biya(15) bai amsa ba sai cewa ya yi a bashi Ashana da sauran. Sallama ya sake yi musu ya wuce cikin layin don tafiya gidan shi. Haruna ne ya lura da Zufar da abokinshi ke yi, d'an zungurar shi ya yi da hannu yace "Ya dai Mankas?" Da sauri wanda aka kira da Mankas ya zura hannun shi cikin doguwar hannun rigarshi ya zaro karan Sigari, ya jefar kasa tare da sa kafa ya murjeshi. kafin kuma ya hau nannade hannun rigar. Haruna da mamaki yace "Mankas? Kana da hankali kuwa? Sigari mai wuta ka tura cikin rigarka? Mtss! gashi nan har ya taba fatarka". Mankas ya kauda kai daga kallon fatar hannunshi da ya yi bororo lokaci guda saboda wutan da ya taba fatar, abunka da farin fata, tuni wurin ya yi Ja. Garin wata hoda Eskaley ya wurgo ma Haruna ya ce "jik'a ka shafa mai a wurin" Haruna ya bude 'yar takardar, ya dauki fasasshen ruwan ledan da ke gefenshi ya dan jik'a ya kamo hannun Mankas zai shafa, Mankas ya janye hannunshi, da k'yar ya iya cewa "Ka barshi, ba damuwa". Haruna cike da damuwa ya ce "kai fa Mankas gardama gare ka, ka tsaya don Allah." Bai ce komai ba, sai ya mik'a masa hannun. Hakan ya ba Haruna daman Shafa masa Powdern a wurin da ya fara tashi. Suna fira jefi-jefi sauran Abokan zaman kashe wandon suka karaso, nan unguwar ya kaure da hayaniyan yan benchin Eskaley , rabi da kwata duk gardama ce. Da Sallama ya shiga Gidanshi, Ameera da Sabit suka rugo wurin Mahaifinsu dan taren shi "Baba Sannu da dawowa" kansu ya shafa ya ce "Yauwa sannu, ya makaranta?" suka amsa mi shi, "Barka da Dawowa Yaya" ya kalleta da fara'a ya ce "Barka dai Labeeba, ya Makaranta?" murmushi ta mishi tace "Alhamdulilah" shiga ciki tayi ta dauko Tabarma ta shimfida mi shi, ya cire takalminshi ya hau kai, Sabit ya zauna kan kafar Babanshi Amira kuma ta jingina da jikinshi yana musu tambayoyi suna amsawa. Aunty Asiya ta fito daga Toilet da Buta a hannu, ta ce "Barka da dawowa Baban Amira" wani murmushi me k'ayatarwa suka ma junansu, da ba dan idon yara ba da sun rungume juna, da kallon kauna ya ce "Asee, ya Gida ya Yaran?" ta ce "lafiya lau, ya Kasuwan?" ya ce "Kasuwa Alhamdulilah, kin san sai da na bar kasuwa na ga message dinki? Sai da na shigo Unguwa na tsaya shagon Eskaley dinnan na siyo Magunan" ya k'arashe tare da mik'a mata ledar Maggin. Murmushi tayi ta ce "Maggin ke nan nayi amfani dashi a Abincin rana, shi ya sa na ce bari na maka text ka taho mana da shi" ta karba tare da isa kitchen inda ta iske Labeeba na jera Cooler din Abincin Baban Amira a Tray, karban Tray din tayi ta ce "Fasa k'ankarar nan cikin Sobon" Labeeba ta amsa mata da "To" ta bude dan firij din da ke kitchen din ta dauko kankarar ta fasa ta juye a Jug. Duk da su Sabit sunci Abinci sai da suka taya Babansu cin na shi. Ya ce "Wai ya ba a je Islamiya ba yau?" Ameera ta ce "Baba yau fa Alhamis" yace "Afuwan na shafa'a, to ina Homework dinku, na tabbata an baku" Amira ta ce "Sai da daddare zanyi nawa" Baban Amira ya ce "Aa, kuyi yanzu tun ido na ganin ido, ba sai dare ya yi ba, ba wuta a rasa yadda za'ayi" Aunty Asiya ta ce "tashi ku dauko Aunty Labeeba ta koya muku" Rige-rigen tashi suka yi suka shiga dakinsu. Baban Ameera ya ce "Labeeba to ya Makarantar?" ta ce "Wallahi Yaya Ranar tsiya, kaji zafi, ga nisan tsiya" Aunty Asiya tace "nan ta shigo min kamar zata kife" dariya ya yi yace "Haha, yarinya yanzu kika fara, baki ga komai ba" tace "Wai Allah!" duk suka yi daria. Ta danyi kewar Gida, tana kewar Mamarta, da yanuwanta, sosai take kewan mahaifarta inda ta girma, amma tana jin dadin zaman Gidan Yayanta sosai, tana sha'awar yadda Yayanta ke tafiyar da Gidanshi, bata da damuwar komai, to damuwar me za ta yi tana gidan Ɗan'uwanta Shak'iki, ga kuma Matarshi da ko kusa ba ta da matsala, ga Yaran Yayanta masu matuk'ar kaunarta, zama da su kan dauke mata duk wata kewa. Haka yanzu ta zauna ta ci gaba da koya ma Amira Homework dinta, sai da ta gama kafin ta ma Sabit da yake shi Tracing ne. *** 6:35pm Baban Amira ya tashi ya shiga bandaki ya fito tare da daura Alwala, ya kalli Sabit ya ce "Mallam Sabit muje Masallaci ko?" Sabit ya mik'e da murna ya yi alwalarshi duk da ba daidai bane, ya rik'o hannun babanshi. Aunty Asiya da ke kitchen tana tuk'a tuwon dare Baban Amira ya lek'a ya ce "Asee, mun tafi Masallaci, sai bayan Isha'i in Allah ya kaimu" fatan dawowa lafiya ta musu, Labeeba ma haka suka fita daga gidan rik'e da hannuwan Juna. Suna nan zaune har aka kira Sallar Maghrib, cikinsu babu wanda ya yi yunkurin tashi zuwa Sallah duk da Massalacin na gefensu. Har Baban Amira ya ketara su ya dawo baya ya ce "Dan Makaho, kuna ji ana kiran Sallah, kuna nan zaune, haba kuji tsoron Allah mana" Tero yace "kai Mallam kaga an Sallame Sallar ba muyi ba ne?" Baban Amira ya ce "ai gani nayi baku da niyya shi ya sa na ce bari na muku tuni" Haruna yace "Zamu yi anjima" Baban Amira yace "Haba, da hankalinku? Anjima? Yanzu me kukeyi? Kun san hukuncin masu Tarrikus Salat? Jinkiri wurin yin Sallah? Kunsan fallalar Jam'i" Master yace "Kaga ba ruwanka da mu, in kai ke karban Sallahn kar ka karbi namu". Dan Makaho ya mik'e yana kallonshi da mak'allelen idonsa da k'yar yace "Yanzu za mu tafi". Baban Amira ya kalli Master yace "Aa bani ke karban Sallar ba, tuni ne nawa, Allah ya shirya" ya ja hannun Sabit suka wuce tare da k'etara Titi suka wuce Masallaci. Cikin muryan yan shaye-shaye Master yace "Kai Mankas naga sai wani lallaba Gayen nan kake, daka barshi dan uwattai, kallon kafirai yake mana" Dan Makaho yayi tsaki yace "Eskaley bani Ruwa leda biyu" Eskaley ya mik'o mai Ledar Pure water dan gefe ya matsa ya fara Alwala. Haruna yace "kai ma dai Master, bak'ar magana ka gaya mishi, ni ban ga laifinshi ba" Tero yace "Yan Unguwanan Gulma buroba ne dasu, Master ka min daidai" Haruna ya mik'e shima ya karbi ruwan ya matsa inda Dan Makaho yake shima yayi Alwalarsa. Master kuwa da Tero zamansu sukayi, suna kuna Sigari. Har Eskaley ya fito ya kulle Shagonsa, Master da Tero suna nan zaune. Su uku suka nufi Masallacin Unguwansu da ake ma lak'abi da Sharp-Sharp. Vote and Comment line by line #1love #DM #anatare #FWA #nagode Biebee Isa. [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Biyu 2⃣ (SHARRI) 4/05/2013 Kan'nannen Idonshi ya dago ya kalli Sady da ta ke zaune a gaban dakinshi, da alama shi take jira, ya dan k'araso da sauri yace "Ya akayi ne Sadiya" ya tambaya fuska cike da damuwa, kamar ba zata amsa ba tace "Barin Gidan nan zanyi" ido ya dan ware kafin ya murza Idonshi yace "me ya faru?" bata amsa shi ba, ta sake jadadda mai da "Gidan nan zan Bari" dan mur ya sha kafin yace "ba inda zaki, ba ki da inda yafi nan, ni a matsayina na miji ban bar gidan nan ba, kema ba zaki bar gidan nan ba" kuka ta fashe dashi ya matso gareta ya janyota jikinshi ya rungume yana shafa bayanta alamun lallashi, ya sama magana a hankali "Sady, komai zi wuce--" Be karashe maganar da ya so mata ba sukaji ana rafka sallati a bayansu "Inallillahi wa ina ilaihir rajiun, DanMakaho kanwarka kake runguma haka? Kana shafa mazaunanta?" cike da tashin hankali suka sake juna suna kallon Aunty Shafa'atu Matar Babansu. Bambamin da ta hau yi ne ya sa mutanen Gidan suka firfito, Aunty Shafa bata bar tafa hanaye tana jefansu da mugayen kalamai ba. Jikin Sady na bari ta karasa gunta tace "Aunty Shafaatu donAllah kiyi shiru, wallahi ba wani abu bane, kin manta Yaya Zaid Yayana ne Muharramina Shakikina?" hannu Aunty Shafa'atu ta sa ta buge bakin Sady tace "yi min shiru Munafuka, yau kuka fara shafar juna kuna iskanci? Shegia Yar Shegia Karuwar Yayanta.". Ran Mankas ya baci ainun, be san lokacin da yayi wani tsalle ba ya shak'o wuyan Aunty Shafa'atu ba ya danganata da bango, k'aninta Hudu ya yo kanshi, be saketa ba, k'ak'arin mutuwa take tana jin azaba tace "DanMakaho kasheni zakayi? Hudu ci man ubanshi" kamar umurninta yake jira, nan ya fara dukkanshi yana kai mai naushi ko ta ina, ko motsi beyi ba illa kara matse hannunsa da yayi a wuyanta. Fati da Annah suka rufe Sadiya da duka durkusawa tayi tana kuka ba su bar dukanta ba, kukanta yaji ya tsananta, ar yanzu su Hudu ba su bar dukkanshi ba kuma be saketa ba, kukan da Sadiya keyi ne ya sa shi sakin Anty Shafaatu ya karasa gun su Fati ya finciko su yana kai musu duka ko ta ina,. Sarkin yawa ya fi sarkin karfi, nan suka hadu gabaki daya suka ma Sadiya da Mankas dukkan tsiya. **** Bangon Kantangarsu daya, ko meke faruwa a cikin Gidan Alhaji Zaki musamman ta wurin BQ suna ji kamar a cikin Gidan akeyi, suna zaune baki daya kan darduma sukaji muryar Hajia Shafa'atu na cewa "Inallillahi wa ina ilaihir rajuun, DanMakaho kanwarka kake runguma haka? Kana shafa mazaunanta?" zumbur suka mik'e tare da matsawa kusa da bangon Gidan. Suna nan tsaye jigum-jigum, sunji komai kamar gabansu ake, jikinta sai bari yake, baki na rawa tace "Aunty Asee kar su kashesu, muje mu rabasu DonAllah" Aunty Asee tace "hmm, Labiba ina mu ina shiga fadan Gidan Alhaji Ali Zaki? Haka suke, ai sun dade ma basuyi ba, haka suke wallahi". Muryar Alhaji Ali sukaji yana fadin "Me ke faruwa a gidan nan ne? Da alamu yanzu ya shigo Gidan, da sauri suka tashi daga jikinsu Mankas. Anty Shafaatu ta fashe da kuka ta matsa kusa dashi cike da kissa "Nagaji Alhajina, nidai ka sakeni, ba zan iya ba, har sai yaushe Dan Miji zai bar dukana? " Hankali tashe yake tambayarta me ya faru, ta ja majina tace "Zuwa nayi baya naga DanMakaho na ta latsar Sadiya yana mata wasu abubuwan da na kasa hakuri sai da na mishi magana na nusar dashi Kanwarshi ce Muharamma, in kuma aure yakeso ya fada sai a mai, bansan ya akayi ba sai dai kawai naga ya kaini k'asa yana dukana Sadiya na tayashi da kyar su Hudu suka zo suka karbeni daga hannunshi". Labiba ta bude baki tana kallon Aunty Aseeyah tace "Laah Aunty Karya takeyi, wallahi karya take musu, ba abunda ya faru ba kenan, karya ne" Aunty Aseeyah ta tabe baki ta koma kan dardumanta ta zauna tace "Labiba, meye naki? Sharri ai ba yau ta saba k'ala musu ba, In Allah ya tashi saka ma DANMAKAHO da k'anwarsa wallahi sai Hajia Shafa'atu ta wulakanta ta shiga hakkinsu sosai, wata irin Mata ce da muke neman tsarin Allah daga garesu". Jin muryar Alhaji sukayi yana cewa "Allah ya tsine maka Zaid, matar tawa ka buga? Allah ya tsine ma ban yafe ba, watsatsse kawai" Labiba ta fashe da wani irin kuka, kamar ita a ka tsinemawa Aunty Aseeyah ta kallota tace "Labiba" cikin kuka tace "Aunty Asee Mahaifinshi ya tsine mai, Mahaifinshi ya laanceshi, be san gaskiar abunda ya faru ba, ya hau kan maganar matarshi, zanje in gaya mai gaskia, wallahi zan gaya mishi matarshi k'arya takeyi" ta zabura Aunty Asee ta taso don kamota, amma bata ci nasara ba, har ta kusa k'ofar Gidan Baban Sabit ya shigo, hakan ya sa tayi turus. "Ina zakije?" kamar bata cikin hayyacinta tace "K'arya Auntynshi take mishi, wallahi ba haka akayi ba, ina bakin katanga, naji komai, yaya Babanshi tsine mishi yake" Baban Ameera ya kalli Aunty Aseeya, girgiza mai kai, ya sa hannu ya rik'o Labeeba ya jawota har tsakar gida ya zaunar kan tabarma yace "me ya faru" a hankali Aunty Aseeya ta bashi labarin abunda suka ji, jinjina kai yayi yace "to ke me zai dameki?" Majina ta ja kafin tace "Yaya, wallahi Allah sharri suka mishi, k'arya suke" ganin tana magana kamar me shirin fita hayyaci, ya ma matarshi alamu da ta shiga da ita ciki. Aunty Aseeya ta kamo hannunta ta ja ta zuwa daki, bakin Gado ta zauna ta rafka uban tagumi, Aunty Aseeyah ta fita gun Mijinta, Kubra ta rasa me ke mata dadi, bata da kuzari, ko da suka zo bacci, hakan tayi ta juyejuye, haka Labeeba ta k'arashe darenta. Washegari da safe idanunta sunyi luhuluhu saboda kukan da taci, bata san shi ba, amma abunda aka mishi ya tsaya a ranta, to shi wani iri ne da ba zai iya kare kanshi ba? Meyasa ba zai iya furta k'arya ake mishi ba? Shi sakarai ne? Haka ta tashi tayi shirin Makaranta, ta shiga ta gaida Aunty Aseeyah, Baban Ameerah ya kai yara Makaranta, Aunty Aseeya tace mata ta tsaya ta yi kalaci amma tace sauri take ta makara, adduan samun nasara ta mata, ta rakota har bakin k'ofar gidan, Adduan fita daga Gida Labiba tayi ta fice ta bi dogon hanyar unguwarsu ta Tudun Matawalle inda zata neman abun hawan da zai kaita National inda zata hau Motar Makaranta (School Bus). Kasancewar Safiya ce, Unguwar bata cika sosai ba kamar yanda take cika wurin k'arfe 11 na rana, tafiya take cikin dan sauri, unguwar sai an fito bakin Titi ake samun abun hawa. Daga chan nesa ta ke hango wani zaune na busar sigari, da sauri ta zaro wayarta don ganin lokaci, 8;17am, mamaki ya cikata, wanene ke banka ma cikinshi hayak'i da sassafe haka, da ta k'araso gurin sai ta ga matashin saurayine, daidai nan ya murje guntun da k'afa ya sake kyasta wani da ya zaro daga aljihun gaban rigarshi ya fara zuk'a. Labiba ta dan yi jim tana kallon bawanAllahn nan, Zuciyarta na tunzurata kan taje ta mishi magana. Har tazo ta gabanshi ko kallonta beyi ba, haka ta tsallaka titi tana waigenshi har ta samu kekenapep da zai kaita National don tafia Hassan Usman Polythecnic. #1love #DM #SonSo #anatare #Fikrawriters #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Uku3⃣ ('YAN MAKARANTA) Har lectures din ya k'are Labeeba bata fahimci komai ba, a hanyarsu na zuwa Masallaci yin Sallahr Azahar, Aisha Usman K'awarta take tambayarta lafiya yau ta ganta wani sukuku da ita, jim tayi kafin tace "Kaina ne yake dan ciwo amma ya bari yanzu" Aisha tace "haba ni dai ince, yau na ganki ga ki nan, Allah ya sauwak'e" murmushi Labiba tayi tana kara k'allon k'awarta. Kafin su k'arasa Masallaci suka ji ana k'wala musu kira ta baya, dakatawa suka yi tare da dan waigawa, cikin hanzari ya k'araso yana me sakin su da k'ayattacen murmushi. "Aisha, Labeeba, ya kuke?" a tare suka amsa masa da Ina wuni Captain Abu Sideeq? Ya amsa tare da cewa "kun gama lectures din yau ai?" Aisha ta gyada kai, Labeeba tace "eh mun gama" yace "Good, to kuje kuyi Sallahr, ku sameni a Ajinmu, sai mu duba karatun yau ko na 1hr ne" amsawa suka yi tare da wuce shi don nufar Masallacin. Aisha tace "Son ki yake" Murmushi Labiba tayi, tace "na sani" da doki Aisha tace "I knew it, kema kina sonshi?" Labeeba ta sake wani murmushin kafin tace "ina dai ganin mutuncinshi, yana kuma burgeni, ina son naga mutum me k'wazo da basira" Aisha ta dan tafa hannuwanta tace "a sannu kema zaki fara son shi, ai ya hadune ya hada komai, ga bokon, ga addinin, ga kuma Kyaun". Labiba tace "ba k'arya". Daidai nan suka iso Masallaci, ko waccen su ta d'auki buta ta nufi Fampo. Sun idar da Sallah suka nufi ND2 inda AbuSideeq yake, yana ganinsu ya k'araso yana jefan Labiba da wani irin kallon da shi kawai ya san ma'anarsa. Murmushi kawai Labiba tayi, yace "muje daga k'arshen Ajin, yana gaba suna bin shi a baya, daga can suka samo Bench suka zauna, shi ne a tsakiyarsu, ba bata lokaci suka hado masa Jotting din Lectures Biyu da suka yi yau, dubawa ya yi kafin ya shiga yi musu bayani cike da k'warewa. K'arfe 2:30 ya ce su dakata haka. Godiya suka masa me tarin yawa, ganin yadda AbuSideeq ke bin Labiba da wani irin kallo ya sa Aisha ta dan mik'e ta ce "bari na dan amsa waya". Ganin haka yasa AbuSideeq fara magana "Labiba..." sai kuma ya yi shiru, ya sake fadin "Labiba ina... ina..." sai ya sake yin shiru, sai da, mintuna kusan 4 suka wuce kafin ya ce "bansan ya zaki dauki maganar nan ba, amma ina so in fada miki wani abu, amma kuma dai na kasa, k'ila rashin faden shi ne Alheri, bari kawai in bar shi, tashi muje na rakaku ku samu abun hawa". Dago idanuwanta tayi ta kalle shi, kafin ta saukar da kai ta fara magana cikin sanyinta ta ce "So na kake yi, kana jin nauyi na, kana tsoron yadda za ka gaya mini, kana gudun kar hakan ya zaman silar bacewar kyakyawar Alak'ar da ke tsakaninmu?" da sauri ya kalleta. Kai ya fara gyadawa kamar k'adangare. "Haka ne, wallahi haka ne Labiba, tun farkon haduwarmu a office din HOD, lokacin da Yayanki ya rakoki Registeration na kamu da sonki" Labiba ta danyi murmushi ta ce; "Ban yi mamaki ba, its obvious ai". K'arfin guiwa ya samu, ya ce "Ina fatan zaki amince mini?" murmushi tayi ta ce "wallahi ban sani ba, bansan me nake ji a kanka ba, bansan me zanji nan gaba a kanka ba, amma nasan cewa ina matuk'ar ganin girmanka, sosai kake burgeni Captain, bansan ko nan gaba wata alak'a da ta wuce wannan zata shiga tsakaninmu ba, amma ko me ke nan, Allah ya zaba mana abin da yafi Alheri a rayuwarmu". Kallonta kawai ya tsaya yi, sosai ta burgeshi, sonta na k'ara ruruwa a zuciyarshi, bai taba ganin irinta ba, bai taba sanin Matan Katsina na iya kallon Namiji haka su gaya masa gaskaya ba tare da wani 6oye-6oye ba, ba ta rufe mishi komai ba, ta gaya mishi iyakar gaskiyarta, hakan da tayi ta matukar burge shi, yana da tabbacin da wata ce, yaudarar shi za ta yi, ko ta ce mishi eh itama tana sonshi ko don wani abu, ko kuma ta bata mishi lokaci, ko kuma ta ja mishi aji, haka yake so Mata su kasance Straightforward, in ana haka, da ba a samu Yaudara da cin amana a cikin Soyayya ba. Mik'ewa yayi yace "tashi muje na nema muka abun hawa" murmushi tayi tare da sa6ar jakkarta, ta bi bayanshi, a bakin kofa suka ga Aisha, tace "muje ko?" Labiba ta gyada kai, a haka har suka fita bakin makaranta ya tsaida musu keke Napep, fadin inda zasu sukayi, mai Keke Napep yace "ke ta tudun Matawalle ciki zaa shiga?" Labiba tace "eh ciki ne ta wurin Makarantar Hope" yace "150 ne kudinki, ke kuma ta k'ofar k'aura layout ki bada 250" da yake hakan suke badawa ba su tsaya ciniki ba. Aisha ta fara shiga kafin Labiba, Labiba na ganin AbuSideeq ya sa hannu cikin Aljihu tace ma Adaidaita sahu, mu tafi kaji" ba tare da bata lokaci ba ya ja Kekenshi, ta dan juyo ta daga ma Captain hannu, shi ko yatsarshi ya nuna mata alamun "ke ko" kafin suka sakar ma juna murmushi. Aisha tace "Bawan Allah, be gajia" Labiba ta gyara zamanta tace "kullum cikin Hidima yake". ** Abu Sadeeq Abu, dan Department of Engineering HUK Poly, wani irin Yaro ne me matuk'ar k'okari, HND2 yake, a nan ya gama ND ya jona HND dinsa, a Dept din kowa na sonshi sabida kyakyawar Alak'ar da yake dashi da Malamai da Dalibai, k'okarinshi be daura mai Girman kai ba. So da yawa in ana darasi, kace ma Mallami ba ka gane darasin yau ba, zai ce "ka sa min AbuSideeq a HND2 ya ma bayani zaka fi ganewa" hakan ne ya faru da Labiba a ranar da suka samu Mallama Amina bayan darasi, tace "ta sake mata bayanin wani fannin da bata fahimta ba" mallamar tace "Wallahi sauri nake, amma kije HND, ki samu a AbuSadeeq a HND2, kice ni na aiko ki, ya miki bayanin topic din". Labiba ta mata godia ta ja Aisha suka tafi inda Mallama ta mata kwatance. Ko da sukaje sukayi tambaya, nuna musu shi akayi, yana tsakiyar maza biyu da mata 3 daga gani 'yan ND2, yan gaba da ajinsu Labiba, yana ta faman musu bayani. Aisha tace "mu jira ya gama, ko muje mu dawo" Labiba ta girgiza kai ta musu Sallama" suka amsa tace "ina wuninku? DonAllah Abu Sadeeq muke nema" kallonta yake yi sosai, yarinyar nan ce da Yayanta ya kawota office din HOD ranar da yake ciki, murmushi ya mata yace "Ga wani Abu Sadeeq nan" Murmushi tayi sosai, ta ganeshi, shine HOD yace mata in tana da matsalar karatu ta zo gurinshi zai mata bayani". "Sannu da Aiki, Mallama Amina ce tace na sameka, wani abu ne ya shige min duhu a course dinta, shine nakeso in kana da lokaci ka dan min bayani" Agogo ya kalla, kafin yace "Alright ba damuwa, amma ga yayyinki nan muna karatu, saidai in mun gama" tace "lahh dama ai sai kun gama" yace "to nam da 30mins InshaAllahu" murmushi ta sakar masu duka, sosai ta burge duk na wurin, tace "bari mu dawo" ta ja hannun Aisha da ba tace ma kowa komai ba. Ya musu bayani yanda ya kamata, Labiba da Aisha sun fahimta, suka mishi godia sosai, yace musu daga yau duk bayan ko wane lectures suzo ya sake musu bayani, hakan zaisa su fi fahimta. Godia suka sake mishi, tare da exchanging numbers. Tun zuwansu Poly Aisha ke tare da ita, tana son Labeeba sosai, duk da a Ajin Maza sunfi Mata yawa, matan basu wuce sha biyar (15) amma Aisha bata da k'awar da ta wuce Labiba, ko wata daya basu rufe a Makarantar ba, amma Aisha na jin Labiba har ranta. Labeeba za ta iya rantsuwa Aisha na sonta matuk'a, kodayake ita dai haka take, indai ta zauna a wuri, to tana da farin jinin mutane, kowa na sonta, ba za a ce don Kyau ba, don ba fara ba ce, a'a, don kyauwun zuciyarta ake sonta, ta iya zama da jama'a, kowa nata ne, bata da zabin mutane da take mu'amala dasu. Wannan kenan. Labari suke da Aisha kafin a shiga layin Unguwarsu Labiba, Aisha ke hada ta da Allah tazo gidansu don Mamarta na son ganinta, har k'arya ta mata cewa Mamar ta ce in ita Labiban bata je ba to ita za ta zo gidansu Labiban da kanta, duk dai don taje Aishar ta ce mata haka. Dariya Labiba ta yi tace "Insha Allahu zanzo wannan Satin, ki ce Mama tayi hakuri. "Allah ya sa kana da chanjin dubu daya" cewar Labiba, mai Adaidaita ya buga tsako yace "Hajia sai kiyi magana tun wuri ni banda chanji" Aisha tace "nima wallahi dubun ne" mai A daidaita ya fara mita da ya san Chanji ne da be dauko su ba, gashi har ya kusa shiga Tudun Matawalle, Labiba tace "Afuwan, akwai shago a ta wurin zasu samu Chanji" mai Napep yace "ga unguwanku ba dadin shiga, balle jiya anyi ruwa" Labiba dai hakuri ta sake bashi, Aisha dai tsaki tayi tace "ya cika mita". Daidai Shagon Eskaley ya ci burki, Aisha ta mik'a mishi dubu daya tace "gashi ka samo chanji ka cire duka" ko waigowa beyi ba yace "Yo Anguwarmu ne? ko sani na sukayi da zasu bani chanji?" Labiba ta lura Mai Keke Napep dinnan dan tijara ne, ta sauka tace "bari na samo" Aisha ta bude baki tace "ya za'ayi kije gurin 'yan Shaye-shayen chan? Haba Labiba ba mutuncinki bane a ga kinje chan shagon, ki bari ya samo" Labeeba ba ta tsaya ba, illa ta karasa bencin Eskaley da Sallama. * Zaune yake kan plastic chair, cikin wata longsleeve shirt da 3 quartern Sojoji, face cap dinshi wanda ya rufe kanshi har wurin idonshi ruf ma irin wandon ne, kayanshi kenan duk dunia, ya dora k'afa d'aya kan d'aya, Idonshi lumshe. Yana shak'ar k'amshi, yana jin dadin yanayin da World ke sashi, World shine sunan da 'yan bencin Eskaley ke kiran Tabar Wiwi, a cewarsu, Ita Wiwin Duniya ce, ma'ana komai, in suka zuk'eta, jin kansu suke daidai da Saraki, Sarauta Wiwin ke sasu. In ka zuk'i World, kafi kowa, wannan ma ya sa Zaid zama shi kadai tare da ba su Master baya, wanda suke fama buga Whot ko na Sigari basu dashi. Duk k'ullin Worlda naira dari biyu Eskaley ke saidawa, yana bada bashin Sigari, amma be yarda ya bada bashin World ba. Tunda suka ga ta nufosu suka k'ura mata ido, Eskaley ya amsa yana washe hak'oranshi jajjaye, da murmushi ta kallesu tace "Ina wuninku, DonAllah chanji naira dubu nake son ka taimaka min dashi" ta maida hankalinta gun na cikin shagon, Eskaley yace "Ahhh, chanjin dubu da sauk'i, basu kai ba wallahi" Labiba tace "akwai Credit? Mtn?" "Aa wallahi ya k'are" dubu dayan ta mik'a mishi tace "to DonAllah ka dan ara min #350 na ba me keke Napep" Eskaley yayi daria yace "Hajia yau wallahi da sauk'i, yau ba ciniki" "Oh Allah!" ta fada a gajiye, ta musu Godia ta juya. "Ga 350" taji an fada murya a dakushe, ta juyo ta ga wa ke magana, bata samu kallon fuskarshi ba sai gani tayi wani ya fincike kudin da aka mik'a mata. "Shege Mankas, kana da kudi a aljihunka kasa Eskaley ya hana ni World, kai mik'o min World dinnan" ran mankas 6ace yace "donuwarka bata kudin" master ya kalleshi yace "mankas ni zaka ma wulakanci don nace ka siya min World, don ni ba mace ba ce, banda kayan dadi ko? to ranta min uku da hamsin dinnan, zan baka" daidai nan mai Napep ya sake buga horn, Labiba dai ikonAllah take kallo. K'yallararen idonshi ya dago ya kalli Master bece komai ba, Master ya buga tsaki ya matsa kusa da Labiba yana cewa "Danmakaho ya ga Chikala" da sauri Labiba ta kalli mazauna gurin don ganin dan Makaho, amma bata samu nasarar ganinshi ba don ya juya mata baya, dubu dayan ta mik'a ma Master, tace "ka bashi, na biyo shi chanji, zan zo na amsa" master ya yashe jajayen hak'oranshi yace "Yayata, donAllah ki bar min chanjin mana" tace "aa gaskia ni ba zan baka kudina ka k'ona su ba" da sauri Master yace "wallahi ba Sigari zan sha ba, abinci zanci Yunwa nakeji". Labiba tace "ban yarda ba, nidai ka ba DanMakaho chanjina". "Haba Babbar yaya kin fi k'arfin dari bakwai da hamsin, nidai Godia nake" Horn mai Napep ya sake buga mata har yana mata masifa, da k'arfi master yace "dallah ware Mallam, zaka ishemu da Oda, ka bita a hankali ko na ci uwarka, Yayarmu Allah ya kiyayeki" Mai Adaidaita tuni ya shiga taitayinshi, kar ya sha duka a banza, Labiba na shiga ya ja Napep dinshi suka shiga cikin Unguwa. "Master, bani" cewar DanMakaho, "me zan baka?" master yayi kamar be san me yake nufi ba, Haruna yayi wuf yace "kai Master, muna gani fa ta baka 1k, kuma muna ji tace ka ba DanMakaho chnajinta, kawai kawo kowa a bashi world daidaiya" DanMakaho ya dago k'yallararen idonshi yace "ku bani nan" Master yace "haba Mankas, yawa kakeyi wallahi, kai ma fa World dinnan ka taba, kuma ka hanani, ka bari mana Eskaley ya bamu daidaya". "DonAllah Mankas ka bar mana kudin nan, haba mana yawa kake" mik'ewa yayi ya fizge kudin, tare da cewa "In tazo k'arbar chanji ta uwar me kuke so na ce mata?" Master yayi wuf yace "ta fa bani" DanMakaho ya zira kudin Aljihun gaba inda Kwalin Sigari ke ciki, tare da fadin, "in na bata ta baku". Barin gurin yayi, ya shiga cikin unguwa, su Master suka bishi da Ashar kala-kala ransu bace. ** 5:20pm Baccin Awa 2:30 yayi, yana farkawa World ta sakeshi, ko da yake be shak'eta duka ba, Kewaye ya shiga ya dauro alwala, yazo ya hada Azahar da La'asar, rigarshi ya shinshina yaji tana warin zufa da rana ga kuma k'aurin hayak'i, guntun tsaki yayi, be yarda ya zauna da dauda ko k'azanta ba, duk da wadan nan sune suturunsa, sai wata bak'ar jallabiya da yake sawa a duk lokacin da zai wanke riga da wandonshi yana iya k'okarinshi wurin tsaftace su, be son shiga cikin Gida amma dole ya shiga ya dauko sabulu, ya ga dan Shegiar da zai hanashi. Straight ciki ya shiga, da Hudu ya ci karo ya fito kamar mara gaskia, yana zare ido, da sauri ya wuce boysquaters, da dan mamaki DanMakaho ya kallesh yana mamakin saurin da yakeyi kamar wanda yayi k'arya, amma da yake ba damuwarshi bane sai yayi gaba ya shige Store ya dauko Klin. Ya na fitowa daga Store yaji Aunty Shafa na cewa "Uban wa ya dauke min Naira Dubun da na aje kan Center Table" Annah ta fito daga daki tace "nidai Wallahi Aunty bani bace, tun dazun ina daki" Fati tace "ni kuma wallahi ban ma san kin aje kudi ba" "duk dauke dauken da ake min bana magana, yau abun ya isheni, daga in aje kudi in shiga in fito sai na nema kudi na rasa? ina Sadiya?" Fati tace "tana cikin dakinta ko?" Aunty shafa tace "na san itace, ya zaayi dama ku dauka, aiko ko ta bani kudina ko na mata mugun bugu, kuma Ubanta yazo ya biyani kudina" Mankas be gama jin sauran zancen ba ya banko labulen Parlo ya shigo, ya na bude idonshi ganin ina Sadiya, ganin bata cikinsu ya kutsa cikin dakin ya ganta chan gefen gado me kama da na 'yan boarding durk'ushe tana karkarwa, ga dukkan alamu ta ji zantuttukan su Aunty Shafa, kuma ta tsorata, be tsaya kwantar mata da hankali ba ya finciko hannunta ya ja ta har Parlo gaban Aunty Shafa ya tsaya. "Uwar da ta fasa taba ta, ta raina Uwar da ta haifeta" duk suka yi cirko-cirko ba me motsi, ya juya ga Annah da Fati, yace "duk randa kuka sake daga mata hannu, sai na sassareku" Aunty Shafa tace "Dubu daya ta ta dauka, kuma sai an biyani, DanMakaho ka fita idona, ni ba sa'arka bace, Uwarka ma bata fara yi dani ba, wallahi ku firdo min Kudina kafin Daddynku ya dawo, kaga duk inda yake yana daf da Gida, ku bani kudina, ba zai ji komai ba". Baki na rawa Sadiya tace "Wallahi Aunty bamu dauka ba" Mankas ya daka mata tsawa yace "dallah kyaleta, munje mun dauka, ba za kuma a bayar ba, in ya dawo me zaiyi? Tsine min? Wani irin tsinuwa ne zai min wanda be min ba? Mtswww" ya buga tsoki kafin ya ja hannun kanwarshi suka fita daga Parlorn. Daidai nan Hudu ya shigo yana zare ido, "Wai meye ke fariwa nake jin Hayaniya Hajia?" Kwafa Aunty Shafaa tayi tace "dani Dan Makaho yake cikin Gidan nan, wallahi zaman Gidan nan sai ya gagareshi fiye da yanzu, bari Alhaji ya dawo". * Zaunar da Sadiya yayi gaban k'ofar dakinshi ya dan bata baki, tare da kwantar mata da hankali ta hanyar gaya mata zai rok'i Babansu kan ya barta taje Gidan Mamansu hutu, sai da ya ga ta saki ranta kafin ya koma daki ya dauko Bak'ar jallabiyarshi ya zura, ya kwaso Riga da Wandon da zai wanke tare da bucket a toilet, cire abubuwan gaban Aljihunshi yayi, da Mukulli, da kwalin Sigari, da Naira dubu daya ya ajiye k'asa, Klin ya Jik'a ya fara tsoma rigar ya fara cudawa. Be gama wanke Rigar nan ba yaji muryan Daddynshi yana fadin "Ina Dan Makahon yake?" dago idonshi yayi ya kalli Daddynshi da ya nufosu kamar Zakin da ya kwana 7 be ci abinci ba, duk 'yan Gidan sun rufa mai baya, kafin ya ankara Daddynshi ya sakar mai nushi kala biyu a gefen baki, ko motsawa beyi ba, Sadiya ta fashe da kuka. " Sata? A gidana DanMakaho? Dama duk sace-sacen da akeyi kai ne? Yau dubun ka ya cika, yau wallahi sai ka kwana bayan Kanta" wayarshi ya dauko ya latso DPO, Sadiya ta zube gabanshi tare da rikon kafarshi, tace "Daddy Wallahi ba shi ya daukar mata Dubu dayanta ba, wallahi bashi bane, Daddy, Klin kawai ya shigo ya dauka, Daddy ka yarda damu" Haurinta yayi dai da ta matsa gefe, da sauri Mankas ya karasa gunta ya durkusa tare da dagota yana watsa ma 'yan Gidan mugun kallo, ya tsaida kallonshi ga Mahaifinshi ido cikin ido yake kallonshi. "Zaid Mahaifinka ne, Zaid kar ka manta Soyayyar da ya wanzu tsakaninku, Zaid kar ka sake ka yi ma Mahaifinka ba daidai ba, duk yanda zuciya ke tunzuraka kan ka mishi wani abu, Zaid ba zan yafe ma ba, kar ka ga tsinuwan Mahaifinka kamar baya tasiri a kanka, Zaid a ranar da zan juya ma baya, Zaid ka rasa Lahirarka wanwar, Zaid Mahaifinka ne, ba komai tsakaninku sai k'auna da kyautatawa" muryar Mahaifiyarshi yaji na mai kuwa kamar a lokacin take magana. Runtse ido yayi sosai, muryar Hudu ta katseshi inda yake cewa "Lahhh, ga Dubu daya chan" da sauri ya bude idonshi, ya ga Hudu har ya durkusa ya dauka, da azama ya karasa shima ya rik'o kudin, idonshi duk biyun ya bude su yace "Sake min kudi". Aunty Shafaa ta karade da "Wallahi dubu daya tace, ashe dama kai ka dauka, in kace kana so ai DanMakaho dubu daya ba komai bace, zan baka, amma meyasa zaka daukar man kudi?". Daddy yace "Zaka sake kudin nan ko sai ranka ya baci?" sai da Daddy ya sake maimaitawa kafin ya sakar, ran Daddy a bace yace "Shege Barawon Banza, kaji haushi" halbi Zaid yayi da Bokitin Wanki, ya shige daki rai a dagule. *** Zaune suke gaba ki daya , Fira sukeyi har Yara suna dariya, daga bisani sukaji an fara iface iface, sosai su ke jin abunda ke faruwa daga kan tabarmar da suke zaune, Labiba ta mik'e da sauri ta k'arasa jikin Bangon Gidan, nan taji komai, Girgiza ka ta farai kamar k'adangaruwa, "Wallahi ba sata yayi ba, Aunty Aseeyah wallahi dubu daya ta ce, kudina ne, ni na bashi, Aunty DanMakaho ba Barawo bane, Ya Illahi". °°°°°°° Kindly Vote and Comment Line by Line #1love #DM #anatare #™SonSo #FWA Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DANMAKAHO 😉 4⃣ Rikota tayi da hannu biyu, "Labiba, ki yi min magana". Naunayar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bata labarin abun da ya faru dazun. Aunty Aseeyah tace "Labiba, akwai abubuwa da yawa dake faruwa gidan Alhaji Ali Zaki, tun kafin zuwanmu Unguwar nan, ba zaki gane ba, amma akwai 6oyayyen alamari tsakanin duk wani rai da ke cikin gidan, wanda ba hurumin mu bane, ba mu da wata alak'a dasu da ta wuce makwafataka". Labiba ga kalli Matar Yayanta " Aunty, Hakkin Makwaftaka fa? wannan babban hak'k'i ne, ya kamata a yi wani abu a kai, so biyu ina jin Makirar Matar nan na hada makircinta, ba zata tsaya a nan ba, ba za kuma ta bari ba, ya kamata Aunty a tari Alhaji Zakin". "Hmm, Labiba, fadan da ya fi k'arfinka sai ka maida shi wasa, ba abunda za mu iya yi. Hajia Shafa, ta zarce tunaninki, bana son matsala da Hajia Shafa, yanda ba abunda ya taba hada mu, bana son komai ya hadamu, amma tabbas Dan Makaho da k'anwarshi na buk'atar Addu'a, shi kawai zamu taya su". Hannu ta sa ta ja dankwalinta baya, murya k'asa k'asa tace " Sakarai! Kamar ba namiji ba, ba ya iya kare kanshi? Meyasa be iya k'aryatasu in sun mishi sharri? Mts" Aunty Aseeyah tace "Magana kike?" girgiza kai tayi tare da mik'ewa ta shige daki 5/5/2013 1:30pm Tunda garin Allah ya waye zuciyarta ke mata kitse-kitse, DANMAKAHO k'wak'walwarta ke kwada ma kira, baza ta iya shaidashi a hanya ba don ba saninshi tayi ba, dalili take so ya sa ta ga DanMakaho, kamar shekaran jiya, da tunaninshi ta tashi, ta damu da lamarinshi, abu kamar a film ko a littafan hausa, so take ta shiga rayuwarshi, so take taji damuwanshi, abun da kamar wuya, amma sosai take so ta hadu dashi, haduwarsu ta farko in brief ne, ko ganin fuskarshi ba ta samu tayi ba, gashi yau ba ta zuwa Makaranta balle ta sa ran ganinshi a Waje, haka kurum ta tsiri zuwa Gidansu Aisha. Yara na Tahfiz, Parlo ta iske Yayanta da Matarshi, a gefen Kujera ta zauna tana musu murmushi "Yaya, ina neman izinin zuwa Gidansu Aisha Usman, Mamarsu ke son ganina, har cewa tayi in ban zo ba, ita zata zo". Dan dariya sukayi kafin Yayan yace "Kinsan Gidan ne?" Girgiza kai tayi alamun aa kafin tace "kwatance ta min" yace "to bari naci Abinci na saukeki" tace "to shikenan nagode". * Da kwatance suka gano Gidansu Aisha, dari biyu ya bata yace " ki hau Adaidaita sahu, kuma kar ki kai Maghrib" Godia ta mishi, Aisha ta gaisheshi sannan suka shiga Gida. Ina za'a saka Labiba don murna, tunda ta tako cikin gidansu Aisha ta ke cin karo da Soyyayar mutanen gidan, har Mai aikinsu ta san Labeeba, da kaunar da ke tsakaninsu. Ya Illahi, haka suke sonta? Barin ma Mamar Aisha da take ji kamar ta goyata, kayan mak'ulashe a ka cika gabanta, daga bisani a ka kawo mata Abinci mai rai da lafia, ita dai Labiba daria take tayi, tana cikin cin Samosa Aisha ta k'atseta da cewa "Zo muje ki gaida Daddy". Kunya ya kama Labiba, "DonAllah ki bari sai anjima" Aisha bata saurareta ba, sai jan hannunta tayi don ta mik'e tsaye tare da janta ta na gaba Labiba na bin ta a baya. Har k'asa ta durkusa ta gaida Daddy, Daddy ya amsa cikin kulawa ya dauko dubu biyu ya bata, bata iya amsa ba sai dai Aisha ta amsar mata sukayi Godia suka koma dakinsu Aishan. Sai da Laasar yayi suka yi Alwala don yin Sallah. Labiba na adduointa ta ji kamar ihu daga waje, sai da ta kasa kunnuwanta sai taji ashe Ihun murna ne da alamun bak'i sukayi, tashi tayi ta ninke Darduma, ta zauna gami da tsiyayo kunun Aya a Cup. Aisha ce ta shigo fuskarta dauke da murna. "Besty kinsan me? Cousins dinmu ne sukazo daga Abuja wallahi dadi kamar ya kasheni". Labiba tace "Inye, fatan sunzo Lafiya" "Lafiya lau wallahi, taso muje ku gaisa" hararar wasa ta jefeta dashi, ta dan muskuta tace "tafiya zanyi ni, banason marace yayia ina waje, kuma dai zaun daura Sanwar dare" Aisha ta san ta mata tunda tun bayan Azahar tazo, don tace zata tafi yanzu ba wani abu ne. Mikewa tayi tace to "barin sanar da Mama". Labeeba tace "ke dai jira mu tafi tare, katon gyalenta Khashka me kauri ta yafa, Aisha kuma ta janyo wata yar gyale bayan ta mata packaging su Samosa da Springrolls tace a kai ma su Ameera. Ba ta Parlor inda ta barsu, ba dai har sun tashi ba? Da sauri ta ja hannun Labeeba sukayi tsakar Gida, inda ta gansu tsaitsaye, kallo ta bisu dashi kafin tace "Yaya Hafeez ba dai kun fito ba". "wallahi kuwa A'i, gwara muje mu gaida Hajia Kaka kafin ta kira Abba tace Munfi Awa 8 a katsina bamuje mun gaisheta ba". Dariya sukayi gabaki daya, Mama tace za kuci Gidanku, Sirrikar tawa kuke ma iyashege?" daria suka sakeyi. Mama tace "Af! Labeeba ba dai kin fito ba" ta dan k'araso garesu cikin takunta tace "Wallahi Mama gwara na tafi, Marece yayi" Mama tace "eh Gaskia ne". Dukkansu Maza Ukun idanuwansu suka zuba ma Labeeba, idanuwa taji a kanta, ta dan dago ta kallesu su ukun a lokaci daya tace "Ina wuninku? Kunzo lafiya?" amsawa sukayi a tare suna kallonta sosai, Aisha tace "Besty, wadannan sune yanuwana rabin Jikina, kika tsaga tsokata Jininsu kawai zaki gani". Dariya Labeeba keyi wanda ke k'ara ma fuskarta kyau, ta cigaba da sauraron Aisha, "ga Yaya AbdulHafiz ga Yaya Abdulmajeed kuma ga Yaya Jawad, yau yau dinnan suka zo daga Abuja don Sada zumunci" wani murmushin ta sakeyi, tace "Barkanku da zuwa Katsina ta dikko Ya Abdulhafiz Ya Abdulmajeed da Yaya Abdul-" ta dan yi shiru tana son tuno sunan gudan, wanda suka kurawa junansu ido shi da ita, murmshi ya mata ya girgiza kai yayi yace "ba Yaya Abdul bane, Yaya Jawad ne" kamar bitar karatu ta maimaita "Yaya Jawad". Aisha ta katsesu tace "Brothers, ga Besty ta, Labiba Ahmad" a tare sukace "Labiba" Mama ta dan murmusa tace "cikinku wa zan ba Diyata?" ta fada tana dafa Labibar da tayi saurin sadda kai k'asa". Yaya Abdulmajeed yayi karaf yace "Ni zaki ba Antisco, Yaya Hafiz na da Mata, dama nine online, kinga sai in hada da Aminiyarta na aure, kinga no kishi". Aisha ta harareshi, tace "sai me don na hada Miji da Besty ai ba wani abu bane, ba dai kai bane Mijin" Dariya Ya Majeed yayi yace "to ni nace ke na ke nufi ne? Nidai Antisco ina so" Mama ta yi Daria, ta maida dubanta ga wanda take ma Labiba kwadayi tace "Jawad fa?" murmushi kawai yayi da ya sake kallon Labiba. Ya Hafiz yace "nifa bangane ina da Mata ba, don ina da Mata sai aka ce ba zan iya sake ta biyu ba?". Antisco tayi daria tace "to zan raba gardama, kuzo ayi tseren gudu, wanda ya riga zuwa bakin Gate, shi zan ba damar daidaitawa da Diyata Labiba". Kafin ta rufe baki tuni Jawad ya ruga a guje ya isa bakin gate daria suka sa baki dayansu, Abdulmajeed yace "Cheating! Ni fa Mancy ban shirya ba, gaskia a sake" Mama tace "Wani ya hanaka shiri da wuri? Ni Jawad na ba dama" Ya Majeed ya cubune fuska yace "dama Antisco na lura kin fi san Jawad" Daria suka sa baki daya. Labiba tayi saurin katsetsu da cewa "barin tafi, yamma na k'arayi" Mama tace "ki tsaya su Jawad su sauke ki sai Aisha ta raka ki" Labiba tace "Baban Amira Zaiyi fada, bari dai in samu Keke Napep" duk sai ta burgesu duka. Mama tace "Gaskia ne, to besty mungode, mungode Allah saka da Alheri, ki gaida Aunty Aseeyar da yaranta" Labiba tayi murmushi jin sunan da Mama ta kirata dashi wai 'Besty' tace "sai anjimanku" tayi Gaba Aisha ta bita a baya. "Nidai Antisco wallahi tayi min ina so" Jawad ke fadin maganar nan, Antisco tace "dagaske Jawad?" "wallahi Antisco" Mama tace "maza je ka karbo numberta, gwara ta baka da hanunta" da dan gudugudu ya bi bayansu, har sun fita bakin gate, k'arasawa yayi gunsu yana dan haki, Aisha tace "Ya Jawad ya akayi ne kake gudu?" wani kallo me wuyar fassaruwa yabi Labiba dashi tare da cewa, "Zuciyata na biyo, zuciyata, ta tafi dashi" tafi Aisha tasa, ita kuma Labiba ta rufe fuskarta da hannu biyu. Dan gefe Aisha ta tsaya don basu wuri su dan tautana. Kallonta yake cikin ido, duk jarumta irin tata sai da ta kasa jure kallon, sadda kanta tayi k'asa, cike da shauk'i Jawad yace "Labee" da sauri ta dago ta kalleshi, jin sunan da ya kirata dashi, murmushi mai nuna jin dadi ta mishi. "Ba zan tsayar da ke ba, Yamma nayi, ki bani numbernki DonAllah" "ka karba gurin Aisha" girgiza kai yayi da sauri yace "Haram, ke zaki bani da hannunki, in kuma hanani zakiyi shikenan" yayi fuskan tausayi kamar mai shirin kuka. Dan daria tayi me k'ayatarwa tace "be maka kyau ba" ya dan kallota yace "mene?" tace "shagwabar mana" dan bubbuga k'afa ya fara yi kamar dan yaro, da sauri tace "Ya hakuri Baby kar ka tara min jama'a kawo wayar na sa ma". "Baby,Wow, sunan da aka bani yayi dadi" da sauri ta girgiza kanta da hannuwanta bibbiyu kamar mai yin bye bye tace "ni fa ba wannan Babyn nake nufi ba, naga kana abun yara ne shiyasa na kiraka da Baby". Kafadunshi ya daga " Oho, nidai zan dauka a matsayin Dayan, yanzu dai gashi ki samin number" karba tayi ta sa Numberta. Tsaida mata Keke Napep sukayi, Jawad ya bude mata k'ofa yace "kin k'i yarda na kaiki Gida ko?" murmushi tayi tace "Bye Ya Jawad" lumshe ido yayi ya bude "Good bye Labee" Aisha ta bude baki ganin yanda Bestynta da danuwanta suka shagala da aika wa junansu sak'onni, "Hello! An manta dani ko? To ina wurin besty?" Kunya ya sa Labeeba rufe fuska tana daria, ta umarta mai Keke Napep da su wuce. *** 5:45pm Tuk'i Yaya Hafiz keyi cike da nutsuwa, sun fito daga Unguwar Alk'ali Gidan Kakarsu, zasu tafi su aje Sak'o kafin su wuce Masauki don Gobe zasu wuce Abuja. Yaya Hafiz yace "Yauwa Majeed, kira Yaron Mancy mu biya mu kai mai sak'on nan don ni gaskia nagaji ni da fita sai gobe". AbdulMajid ya ciro wayarshi daga Aljihu ya latso numbern da Mancy ta bashi, har wayar ta katse ba a dauka ba, sake dialing yayi nan ma ba answer. "Ba ya dauka fa" cewar Majeed, Hafiz yace "Kira Mancy ka gaya mata" dialing Numbern Mancy din yayi ringing na biyu ta dauka. "Assalam Majeed" ta fada cike da Murna, "Hello Mancy ina wuni, dama mun ta kiranshi dan mu bashi sak'on be dauka ba" "Oh Allah, sorry na wahalar daku, ko ku barshi" Majeed yace "haba Mancy, har muzo gari kuma mu juyo da sak'o? Ba wani abu bari na sake kira InshaAllah zamu sameshi". "Nagode sosai, bari nima in kira k'anwarshi in ba ya nan sai ta amsa" nan suka katse wayar. Tudun Matawallen suka nufa kamar yanda Mancy ta gaya musu. Majeed be fasa trying numbern shi ba, Jawad har ya k'ulu, shi fa be son bacin lokaci, tsaki ya sake yi, shi ba Fan din Mancy bane, be kuma k'inta, kawai dai bata cikin 'yan kayanshi kamar yanda yayyunshi biyu ke yinta. Sun fi minti 10 a cikin Tudun Matawalle basu san inda zasu ba, sake kiran Mancy Majeed yayi tace "kuyi hakuri, wallahi wayar k'anwar tashi kashe take, na kuma ta kiranshi be dauka ba wallahi, kuyi tafiarku kawai Majeed". "To Mancy ya sunan Maigidan sai muyi sallama mu bada a ajiye musu" dan jim tayi na wasu sakwanni kafin tace "kawai Majeed ku dawo ba wani abu" ba ya so ya matsa sai cewa yayi "to Mancy, amma banji dadi ba" ya kashe wayar ya ce masu "tace a bari kawai, amma banji dadi ba wallahi". A k'ufule Jawad yace " to ya zamuyi, nan zamu lallace? Ya Hafiz mu tafi please" ta Mirror Hafiz ya kalli k'aninshi da harara yace "Jawad!!!" kawar da kai yayi, Hafiz yace "Majeed sake kira" Majeed yace "for the 14th time, Allah ka sa ya dauka". Bencin Eskaley World DanMakaho ya zuk'a, sarauta ta sa mai, k'afa daya kan daya ya daura, yana kallon kowa a dage, me tsautsayi kawai zai shiga harkanshi yau, yanda yake jin kanshi tsaf zai kakarya mutum. Master da su Haruna ke buga Whot, suna yi suna busar sigari, yau ma basu da arzikin siyan World,sunyi ma Eskaley Magiya amma fir ya k'i basu". "Wai Mankas ba wayarka ke k'ara ba tun dazun, kusan so 10?" Haruna yace "yo ina zai iya dauka, World fa ya ta6a" Master yace "yo in baka dauka ka kashe shegia mana, ni nan ta cikan kunne" Tsaki Eskaley ya buga ya mik'e ya nufa Mankas hannu ya sa a Aljihun gaba inda Wayar ke k'ara, dauka yayi kafin ya amsa da "Hello?". "Eh Hello, Zaid?" daga bangaren Eskaley yace "Eh to ba Zaid din bane" daga dayan bangaren a ka ce "DonAllah gamu a Tudun Matawalle, sak'o aka bamu daga Abuja mu kawo ma Zaid, don Allah ina zamu sameshi?" Eskaley yace "kuna ta ina?" "mun dan shiga cikin Anguwar" "Ayya, ku dawo farkon Anguwar, akwai wani kiosk nan Yellow". Eskaley ya kalli su Master yace "Daga Abuja aka aiko wasu gun Mankas, gashi Mankas na birnin Sin ya zaayi?" Master yace "to ya fa? Uban kowa ya san Mankas na eh ya ne". Horn sukaji na wani mota bak'a k'irar 507, duk suka tashi don yau kakarsu ta yanke sak'a. Wayar Mankas ta sake ringingin Eskaleh ya dauka " Hello? Kaine a bakar Mota? Eh nan ne, barin zo" Eskaley yayi gaba, su Master na binshi a baya. Ta Window suke kallon masu tunakaro su, "'Yan Shaye-Shaye ne" cewar Jawad "Mai ya hada yaron Mancy da Shaye-Shaye?" inji Hafiz, ba su da wannan amsar illa fitowa da sukayi gabaki dayansu. Musabaha sukayi da dukkansu harda Jawad da ya mik'a musu hannu a kyamace, su ko 'yan bencin Eskaley kamar su musu Sujjada don biyayya, Hafiz ya kallesu daya bayan daya, ya lura duk ba na kirki cikinsu, duk warin Sigari suke, daurewa dai yayi magana yace "Ina Zaid?" Master da Haruna suka kalli juna suna tunanin waye Zaid? Shaf sun manta da wani Zaid". Kafin Master yace "au Mankas? Gashi chan baya, in sak'o ne ku kawo a bashi" Majeed yace "Aa, hannu da hannu zamu bashi" Haruna yace "Ai Mankas ya hau network, ba zai gane bayanin da zaku mishi ba, mune Aminnanshi". " DanUwarku Mahaukaci ne ni da ba zan gane bayani ba?" gabaki dayansu suka juya, Mankas ne ke tunkaro su, tuni Master da Haruna suka matsa mai ya k'araso yana k'are musu kallo duk a dage, ya tsaya kan Jawad mai kallonshi a k'yamace, Mankas ya wurga mishi mugun kallo shima kafin ya kalli su Master yace Duk ku ware?". Hafiz ya mik'a mishi hannu, k'in amsa yayi, ran Jawad ya mugun baci, Majeed yace "Zaid, Mancy ce ta bamu sak'o mu baka". Runtse ido yayi da k'arfi ya bude, tuni ya dawo hayyacinsa, Hafiz ya nufa da sauri ya dan durkusa " DonAllaj kayi hak'uri babban Yaya kuyi hakuri, wallahi akasi aka samu" daga yanda yake magana sun san a buge yake, yana dai k'okari ya dawo hayyacinsa ne. Hafiz ya girgiza kai yace "Zaid, Mancy Mutuniyar kirki ce, donAllah ka bar Shaye-Shaye" da sauri Zaid yace "Wallahi na bari, ba zan k'ara dama yau na fara" sun san ba gaskia ya fada ba amma dai suka share" Majeed ya bude Booth ya dauko Ghana MustGo dan k'arami ya mik'a mishi. Karba yayi, yace "nagode, Allah tsareku, ko uban wa ya tabaku ku gayan naci uwar mutum, duk garin Katsina, ko da kuwa Sarkin Katsina ne". Takaici ya sa Jawad saurin fadawa Mota, Majeed ya girgiza kai yana mai fatan shiriya, shiko Hafiz da yake Ustazu ne sai da ya sake masu Mankas da abokanshi nasiha kan su bar Shaye-Shaye. Nan suka fara mishi rantsuwar kaffara kan sun daina ba za su sake ba. Master har yana k'arawa da cewa dama don rashin abun yi ne ya sa suke Shaye-Shaye. Hafiz kudi ya ciro kusan 10k ya basu. Master yayi wuf ya amshe tare da zuba Godia kamar zasu goyasu. Addua suka dinga zuba musu har Hafiz ya shige Mota ya ja suna mishi byebye. Mankas be tsaya bin ta kudin da aka basu ba ya dauki ghanar nan ya danna a guje yayi Gida kamar wani zararre. Su ko su Master yau take Sallah, World suka siya kowa qulli biyar biyar. Washegari 5/05/2013 Tashi sukayi yau ba ruwa a Gidan, Drums dinsu empty, dama da k'yar suka samu Ruwan Alwala da Asuba, ko ruwan da zasu dafa suyi kalaci basu dashi. "Oh ni Labiba ya zamuyi? Gashi Baban Amira bacci yake yi balle yaje nemo mai ruwa, bansan tadashi wallahi" Labiba tace "to Aunty Aseeyah ko in fita inga in zan samu mai Ruwan?" dan shiru tayi tace "Oh, ko zaki dan lek'a Gidan Alhaji Zaki ki samo mana a Kettle? Naga su borehole garesu". Ba tare da wani tunani ba tace "eh wallahi barin shiga, ina zuwa" da sauri ta fita. Aunty Asee mamakin Labiba take kawai ta ga fuskarta da walwalwa daga cewa taje Gidan Alhaji Zaki debo ruwa. Maimakon Kettle wani Plastic Bucket na fenti taga ta dauko. "Aa Labiba, ina zaki iya daukan wannan Bokitin, ki dibo a Kettle din zai isa kafin Yayanki ya tashi, ya nemo mai ruwa". Da murmushi tace "Anty Aseeyah kar ki damu, zan debo daidai ni" bata tsaya jin me zatace ba, tafita da sauri tana jin wani annashuwa a tattare da ita burinta daya, Allah ya sa ta Hadu da DanMakaho. ** Tun jiya da ya kwanta bayan Maghrib be farka ba sai yanzu, fitowa yayi don ruwa be zuwa a toilet dinshi, Alwala zaiyi ya hade sallah tun Maghrib din jiya zuwa Asubar yau. Fitowa yayi zuwa Babban Tankin Gida. "Hajia masu Gidan bacci suke, nikuma banda hurumin barin ki diban ruwa, aikina Gadi kawai". "Yauwa ga DanMakaho nan" karasowa yayi gunshi yace ya akayi ne Manu?" yauwa wannan yarinyar Gidan Baban Amira take, ruwa suke so a tsammasu" juyawa yayi ga Labiba da ta shagala tana kallonshi, da kannennen idonshi ya kallota yace "ki shigo ki diba, Manu barta ta diba". Kamar sakara ta bi bayan dan Makaho har bakin Tank din gidan, karban Bucket din Labiba yayi ya tara a Fampo ya bude fampon, hankalin Labiba na gun karantarshi, fari ne, amma wahalar rayuwa ta maida Fuskarshi bak'i, bayan hannunshi da dan haske amma tafin hannun da duhu, bakinshi ma yayi duhu, ganin kallon k'urillan da Labiba ke mishi ya sashi cewa " Chanjinki na nan, in na chanza zan kawo miki". Wani irin kallon da be san na meye ba take binshi dashi, ji yayu ta fara magana tace "Meyasa?" dan kallonta yayi da kannenen ido me kama da bacci yace "Meyasa sai nayi chanji zan baki chanjinki?". Da sauri ta girgiza kai tace "Meyasa baka iya kare kanka? Meyasa kake tsayawa ana daura maka laifin da ba naka ba? Meyasa kake daukan laifin wasu? Duk a zatona DanMakaho nakasasshene da ba zai iya tabuka ma kanshi komai ba, a zatona Dan Makaho bai da karfi da ikon kare kanshi, ashe ba haka bane, ashe kawai Dan Makaho Matsoraci ne, ashe dan Makaho ba zai iya tsayawa garkuwa ma k'anwarshi ba" baki bude yake kallonta cike da dumbin mamaki. "Yanzu ba lokacin bude baki bane ka kalleni kamar Photo, ina jinka jiya da aka ce ka dauka naira dubu dayan da na baka, ba sai ka min k'arya ba, na san baka da ko sisi, ina kuma ji ranar da akace kana iskanci da k'anwarka, ina son sanin dalilin da ya sa baka iya kare kanka". Da k'yar yace "Wacece ke?" •••••• Yay!!! Late night post Afuwan Dont forget to vote and comment line by line #1love #DM #anatare #FWA #SonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Biyar (RUWAN SAMA) Barka da Sallah Bibilicious freaking fans, da fatan anyi Sallah Lafia? Allahu ya maimaita mana na badin badada. Okay, please, before you start reading Vote first, number of Votes na decreasing, ku bani barka da Sallah ta hanyar voting kafin karatu Nagode. "Dan Makaho ba tambayar da zaka min ba kenan, ka gaya min mene dalilin da ya sa ba ka iya kare kanka?" shiru yayi be da niyyar amsata. "ba fa shiru zaka min ba, amsa nake so ka bani, meyasa kake daukar laifin da ba naka ba?" Hannu ya sa ya shafi sumar kanshi "first of all ki daina min magana kamar wata uwata, secondly ba zaki ta6a ganewa ba, everything is beyond your expectations (komai ya zarce zatonki)" wani kallon mamaki take bin shi da shi, turancinshi mai kyau ne kalar na turawa. Mamaki ya gani a fuskarta "Oh wow! kallon jakki, dak'ik'i kike min. I'm a Graduate Miss, thank you very much for asking, in kinaso zo in daura miki ruwan a kai, in ba kya so kuma sauri nake Sallah zanyi". Bata gama mamakin da yace shi Graduate ba ne kuma taji wai Sallah zaiyi da mamaki tace "Asuba?" ba tare da jin komai ba yace "da Maghrib da Isha'i ba". "Auzubillahi, haba Dan Makaho, me kake yi haka da ya hanaka Sallah? Me kakeyi da ka tara Sallah haka? Kai banji dadi ba wallahi, ka bari bana so" fada ta fara mishi sosai. Cike da Mamaki ya dubeta kafin yace "To Hajia Maryam, zaa bari". Kallonshi ta danyi tace "wacece Hajia Maryam? Ni sunana Labiba?". "To ai naga kin tasani gaba kina ta min fada, in ba uwata ba, ba uwar da ta isa ta tasani gaba tana min fada, kuma ni bandamu da sanin sunanki ba, kuma ki daina labe kina jin gulma, duk randa kika sake tsareni kika titsitseyeni da tambaya sai naci Uwarki". Ya dauki Bokitinshi yayi gaba ya barta tsaye cike da mamakinshi, dan bude murya tayi yanda zai jiyota tace "ai dai ban tsoronka, zamu sake haduwa kuma" ba tare da ya juyo ba yace "aiko zakici Uwarki". Da sanyayyar guiwanta ta dauki handle din bokitinta ta fita guiwa a sage. Tana shiga Gida ta diba ruwan a tukunya ta kunna Risho. Aunty Asee na lura da ita, yanayinta ya chanza, ba kamar da ta fita ba "Labiba? Wulakanci suka miki halan?" da k'yar ta girgiza kanta, tace "kai na ke dan ciwo" "ki shiga ki dan kwanta zai bari" kamar jira take ta fada daki, ta zube kan Gado kafin ta mik'e zumbur ta zauna. K'wak'walwarta ta shiga tana sak'a da warwara. Gidan Alhaji Ali Zaki Babban Gida ne, duk Anguwar ba Gidan da ya kai Gidanshi Girma da kyau. Zaid na da k'anwa Sadiya? To ina Mamarsu? Ko ta rabu da Alhaji Ali ko kuma ta rasu. Tabbas Hajia Shafa Matar Ubansu ce? Sauran muryoyin da take ji kuma na yaranta ne, ta san 'yan uba da matar uba, don ta na dasu, Gidansu gidan yawa ne, amma tsakani ga Allah ba sa irin zaman Gidan Alh Zaki. To shi DanMakaho tunda Iliminshi meyasa ba zai nemi aiki ba? Meyasa yake shaye-shaye? Meyasa ya bata rayuwarshi haka?. A baiyane tace "Ya Rabb! Ina son sani, nasan ba hurumina bane, amma ina son sani" Wayarta ne ya katse mata tunanin da takeyi. Jawad ne, murmushi ya dan su6uce mata kafin ta dauka da Sallama. "Labee nah, ina son ganinki kafin na koma Abuja" abunda ya fara ce mata kenan. Murmushi ta saki mai laushi kamar tana gabanshi, kafin tace "Ina kwana? Ka tashi lafiya?". Da sauri ya katseta "Wallahi ba Lafia ba, ina ta tunaninki, let me see you please". Sausauta murya tayi tace "kayi hakuri, ni bansan me zance ma Baban Ameerah ba, amma nan gaba zan mishi maganarka, sai kazo Gida ko?". Jim ya danyi kafin yace "Alright, Zamu biya ta Gidansu k'awarki kafin mu dau hanya, i will call you later, Ina Sonki Labiba". Bata taba sanin ana shiga irin wannan yanayin ba, ba ta taba saurayi ba, da yawa nace mata suna Sonta, ba ta taba samun kalaman da sukayi tasiri a zuciyarta ba kamar na Jawad, Ina Sonki Labiba. Maganar ta sake dawo mata katseta yayi "kinyi Shiru" tace "to me zan ce?" "kice kema kina So na" murmushi tayi tace "ka cika shagwaba, kai dan Auta ne?" yace "Ehmana, ashe ana ganewa, OK gotta go, zan kiraki in na isa Abuja". "Allah ya tsare ya kaiku lafiya" ya amsa mata da Ameen. Gab da zasu katse wayar. Yace "Labiba, a hankali zan koya miki So na, I love you". Kaste wayar sukayi, Ruf da ciki ta kwanta, wani irin yanayi ta shiga, wannan ne yanayin da ma'abota soyayya ke shiga? Wannan ne yanayin da ke ta6a zuciya. Pillow ta janyo ta rungume a k'irjinta tare da lumshe ido, Mantawa tayi da duk wani abu, ta manta da komai, har DanMakaho, ba abunda zuciyarta ke aiyana mata sai JAWAD. Shin Son so ne?. Jawad da Yayyinsa sai da suka biya Gidan Kakarsu, kafin sukaje Gidan k'anin Babansu suka musu sallama. Jawad ya sake jadadda ma Aisha son da yake ma Labiba don ta kafa mishi Fada a wurin kawarta, yayi alk'awarin dawowa ba da dadewa ba, daga Gidansu Aisha ba su tsaya ko ina ba sai a Shagalinku Restaurant dake Zaria sukaci Abinci sukayi Sallah kafin suka sake daukan hanyar Abuja. ABUJA Da Marece suka iso Garin Abuja, Gidansu da ke Garki suka nufa, a tare suka fito daga Motar, Autarsu Mimi ta hangosu, da gudu ta kwasa ta na musu Oyoyo, AbdulMajeed ya dagata sama yana chafewa, Jawad shafa kanta yayi kawai ya shige ciki ya barsu, yarinya ce 'yar shekara uku, amma akwai surutu da shiga rai, cikin muryarta tace "Yaya Ina kukaje? Mancy tace kunje Katsina, ni meyasa bakuje dani ba?" Abdulhafiz yace "Sorry Mimi, da mu ka fita bacci kikeyi next time OK?" gyada kai kawai tayi. A jikin AbdulMajeed suka k'arasa cikin gidan. A main Parlor duka zube, sai ga Jawad ya fito daga wani Daki, Mahaifiyarsu na biye dasu, bakinta har kunne saboda murmushi. "Sannunku da zuwa Boys" a tare suka gaisheta da "mun same ku lafiya Hajia? Ya gidan" da murmushi ta amsa musu da "Lafiya lau, ya mutanen KT?" suka amsa mata, tayin abinci ta musu. AbdulHafiz ya mik'e yace "bari dai na k'arasa Gida Hajiya, Ummita ta min Waina" Hajia tace "to ba matsala ka gaidasu, muje na rakaka ma" ta k'arasa gunshi tana dan turashi kamar mai gudun kar yaga wani abu ko kuma kar ya tsaya yin wani abu, ranta ne ya dan sosu da taji yace "bari na Gaisheda Mancy" AbdulMajeed ma yace "Mimi sauka muje mu gaida Mancy" yarinya ta k'i sauka, haka ya dauketa a jikinshi, ya bi bayan yayanshi suka wuce Hajiyarsu da Jawad da je tsaye suka nufa hanyar dakin Mancy. Abunda bata so kenan, abunda take gudu kenan, bata so yaranta suna ba Kishiyarta muhimmanci, suna nan tsaye sai ganin fitowarsu sukayi su duka har bakunansu na motsi da alamu wani abun ta basu, ranta ya baci, don me suka maida zuwa gaishe da kishiyarta Wajibi, itace Uwarsu ba Mancy ba, amma don me zasu dinga raba musu matsayi? Har suna cin abun hannunta?. Muryan Mancy sukaji "Jawad, ashe an dawo, ya hanyan?" ba yabo ba fallasa yace "lafiya lau" tace 'Abdulhafiz, Allah ya huta gajia, a gaida Ummita, ke kuma zo nan ki bar Yaya Majeed yaje ya huta" Mimi ta mak'e kafada. Abdulhafiz ya musu sallama ya fita don tafiya Gidanshi, AbdulMajeed ya ba Mancy Mimi da k'yar shima ya wuce daki, Jawad ya ja Hajiyarshi suka shige daki, ita kuma Mancy ta ja hannun diyarta suka wuce daki. Jawad ya zauna kusa da cinyar Mamanshi, ya na mai bata labarin Labiba, da irin son da yake mata, da kuma gaskia shi aurenta yake sonyi, Hajia Luba tayi mamaki matuk'a, ita ta san yaronta Miskili ne a wani fanni, ta san halinshi da kyale mutane, so da yawa kawayenta ke so su hadashi da 'yaransu amma fir yake nuna ba ya da raayi, tayi mamakin yanda ya furta da bakinshi kan cewa ya samu Mata. Hajiya tace "to zan kira Antisco din na tambayi hallayar yarinyar" Jawad yace "to Hajia, bari ma na kira miki ita ku gaisa" Hajia tayi murmushi ganin zumudin Jawad. KATSINA Labiba ta lek'a dakin Yayanta inda matarshi ke kishingide tace "Aunty Asee barin je in siyo kati, duk yau bamuyi waya da su Mami ba" mik'ewa tayi "tace yauwa nima siyo min na dari" Labiba tace "to" fita tayi tana gyara zaman mayafinta. Daidai da fitowarshi daga Gida, karaf suka hada idanuwa, dauke kai ya fara yi, ya fara tafiya, da sauri ta bi bayanshi tana fadin "DanMakaho Chanjina, zanyi amfani dasu" chak ya tsaya ya dan juyo, kafin yace "wai ba kince kin san Kudin be wurina ba? Ban dasu yanzu ban da dalilin samun su, na san inda kike, da na samu zan kawo miki har Gida" Yana kai wa nan ya juya ya cigaba da tafiyarshi, dan jim tayi kafin tayi saurin binshi tana cewa "Dan Makaho, tsaya tsaya DonAllah" dan dakatawa yayi "ka rakani wurin siyan Kati, kaga dai shagon Oga kulle yake, dole sai chan Bencin Eskaley, kuma 'yan shayeshaye ke wurin, nikuma ban san zuwa, ka sansu ban so su ci mutunci na, ko su min magana bana son magana da su wallahi, ni tsoron su ma nakeji, donAllah ka rakani" ta k'arashe kamar me niyyan kuka. Ya harzuk'a yace "wai ke don Uwarki me kika daukeni? Zan fa ci uwarki, zan babbala ki, ki fita harkana" fuskarta ya dan chanza amma murmushin be gushe da ga kan fuskarta ba tace "dazun da safe ka zagi Uwata so biyu, yanzu ka sake Zaginta, shin me ta maka? Ba ma fa ta sanka ba? Amma kake ta zaginta, don nace ka raka ni?". jikinshi yayi dan sanyi, shafa kai yayi da hannu kafin yace "to ai duk cikin 'yan bencin Eskaley na fisu shaye-shayen don me zakice na rakaki, ba kya tunanin na miki wani mugun abun yanda kike shishige min haka?". Kallonshi tayi ta ga yanda yake kallonta da kannennen idonshi tace "I'm safe with you, na sani, in zaka rakani muje". Gaba tayi da sauri ya cin mata suna tafiya kafada-kafada ba mai ce ma wani komai har suka iso shagon Eskaley. Tuni su Master da Haruna suka fara shewa "Shege Mankas, wo kai Mankas" Master yace "Yayar mu ina wuni, ya kwana biyu? A dan dari biyu inci abinci donAllah" Tero yace "amma wallahi kin hadu fa, kina da kyau, Labiba ta kawar da kanta kawai tana mai da na sanin zuwa shagon nan, ina ma yaro ta samu ta aikoshi nan, kamar tayi kuka, jin irin maganganun da suke mata. "Zan ci uwarku ku ka sake mata magana, danuwarku kalarku ce? To danuwarku waninku ya sake cewa wani abu game da ita, zai kwana Asibiti billahilazi" Tero yace "Kai ji Mankas, yo kai ka shiga wurin sai ka hanamu shiga, indai ba kalarmu bace kaima ba kalarka bace, ai tunda muka ganta tare da kai, ai mun san 'yar hannu ce, Eskaley bata World, dan na san shi tazo saye, ba sai an tsaya mana wani kwane kwane ba, mun san kina Eh-Yaneh Malama". Kafin Labiba ta gama gano inda Zancen Tero ya nufa, tuni DanMakaho ya kai Tero k'asa ya na kai mai nushi ko ta ina, ba wanda yayi yunk'urin rabasu don sun san halin Mankas, Labiba da tashin hankalin yayi yawa sai ta rasa me zatayi, tana waigawa inda zata ga jama'a don a samu mai rabasu, kowa harkan gabanshi yake , sai da Mankas ya ma Terro Ha6o kafin ya barshi, ya tashi ya nuna su da yatsa yace "duk daniskan da ya sake mata magana sai na ci uwarshi" fizge kudin hannun Labiba yayi yace "Eskaley bamu Kati" Tero ya mik'e a wahalce yace "Wallahi Mankas sai na rama, ko ba yau ba" Mankas yace "zo rama dan uwarka" ya nufoshi da gudu Tero ya bar gurin. Be ko kalleta ba ya amshi Katin daga wurin Eskaley, gaba yayi ganin haka ya sa ta bishi a baya, sai da suka zo har k'ifar Gidajensu kafin ya mik'a mata katin, amsa tayi tace "Nagode, meyasa kayi Fada?" kallonta yayi ya kawar da kai, tace "Fada be kamace ka ba, be maka kyau ba, komai be maka kyau, ka bari donAllah " a fusace tace "Danuwarki bana ce ki bar shiga harkata ba" shiru tayi ta sadda kanta kasa, sai daga baya yayi laakari da zaginta da ya sakeyi. Hannu ya sa ya murza idonshi na hagu, yace "kinga ke ke sa ina zaginki, kiyi hakuri, ki kyaleni, ki fita harkata" kallonshi take sosai kafin ta daura hannunta saitin k'irjinta tace "bansan menene ba, Zuciyana daidai nan, na min Zafi, bansan meyasa nake son saninka ba, ba son meyasa na damu da lamuranka ba, dagaske banson meyasa ba, amma dagaske Zuciyana na min Zafi, yana azazzala min, yana tafasa, zakayi mamakin don me ko? Nima mamakin nake, don me, so ka taimakeni, ka gaya min, ko zan samu sausauci". Kafin yayi maganar Wayarta ta fara ruri, dubawa tayi taga Jawad ne, har ya katse bata dauka ba, ya sake kira DanMakaho yace "ki dau ka wayanki, zan sake ganinki, za kuma ki san ko Ni Waye, ban taba maganar nan da kowa ba, amma zanyi dake, ki shiga ciki, zamu sake Haduwa". Da duk wata kalmar da ta fito bakinshi suka samu zama a Zuciyarta, samun kanta tayi da bun umurninshi, ba tare da ta ce mishi komai ba ta shige Gida tare da amsar Wayar Jawad. "Haba Labee nah, ina kika aje waya ina ta kira?" dan guntun murmushi tayi "sorry na fita siyo Kati ne" "God, laifina ne, by the way, Hajiyata zaki gaisar" Dakinta ta fada, tace "Haba Jay, is too early" wani darian farinciki taji yayi, yace "Zamuyi maganan sunan da kika bani Anjima, amma ga Hajiar" kafin tace wani abu ya sadata da Hajiarshi. Da Sallama ta amsa "Hello Assalam Alaikum" Labiba ta saki murmushi kamar tana gabanta "Ummanmu ina wuni?" dama a handsfree wayar take dadi ya kama Jawad, "Lafiya lau Labiba, ya kike ya su mamanku?" Labiba ta amsa mata, Umma ta tambayeta ya Makaranta, kafin ta mata addua sukayi Sallama. "Ameen Ummanmu, Nagode Allah ya k'ara Girma ya kuma ja Kwana". Labiba mai Farinjini tuni Umman Jawad taji ta na sonta sosai, tace "Jawad, Labiba wayayya ce, ba ruwanta" Jawad yace "sai ma kin ganta a fili" Umma ta kai mai dukan wasa tana cewa "wuce ka zubo abinci Ja'iri". ALHAJI ABU SHAMSU Asalinshi dan Garin Katsina ne, Alhaji Abu Shamsu na da k'ani daya rayyaye, sauran duk sun Rasu, Alhaji Abu Shamsu fitattacen dan Kasuwa ne mai zaman kanshi wanda ake damawa dashi a k'asa, Hajiya Lubabatu itace Uwargidanshi tun auren saurayi da budurwa, itama 'yar Katsinar ce, tun Abu Shamsu na 'yan buga-buganshi sukayi Aure har Allah ya mishi budi. Alhaji Abu Shamsu da Hajiya Luba na da yara Uku, duk Maza, Abdulhafiz shine babba, sai AbdulMajeed sai auta a cikinsu Jawad. Amaryar Alhaji Abu Shamsu wacce basu rufe Shekara 4 da aure ba Sunanta Hajia Maryam, diyarta daya Aminatu ana ce mata Mimi. Wannan kenan Ruwan Sama akeyi ba k'ak'autawa, tun k'arfe 10 dare, har wayewar Gari, da Asuba Baban Amira ya fito don yin Alwala don tafiya masallaci yin Sallahr Asuba, gabanshi ne ya fadi ganin bangon da ke tsakanin gidanshi da Alhaji Ali Zaki ya rushe, "Subhanallah, Inallillahi wa ina ilaihir rajiun" ya furta, da kyar ya daure ya shiga kewaye ya dan zagaya tare da yin alwala ya fita masallaci. Bayan Sallahr Asuba suka hadu da Alhaji Ali Zaki, Baban Amira ya karasa wurinshi sukayi musabaha cikin mutuntawa. Alhaji Ali yace "Mallam ya Iyali?" Baban Amira yace "Alhamdulilah, sai ga tsautsayi kuma" Alh Ali yace "Subhanallah, me ya auku?" be yi mamakin rashin sanin da yayi ba saboda bangon ta baya ne, ta inda Boysquaters yake, Baban Amira yace "jiya Ruwa yayi Gyara, Bangon da ke hade dade da Gidanka ne ya fadi". Alhaji Ali yace "Subhanallah, IkonAllah, wallahi ban gani ba, ko don ban lek'a bayan ba, ta wurin DanMakaho ne kenan, InshaAllahu zaa gyara, bari gari ya waye" Baban Amira yayi Godia suka taho Gida tare, "ai Alhamdulilah tunda bangon be fado ma wani ba" "Ai don dare ne, amma wurin Iyalina suke shimfida don wurin akwai inuwa" Alhaji Ali yace "IkonAllah, Allah ya k'ara tsarewa" A haka suka iso Gida, Baban Amira ya shigar dashi ta Gidanshi ya gani, suka sake jajantawa juna Alhaji Ali kuma ya tabbatar mishi da cewa da Safe zaiyi waya a siyo Bulo da k'asa da Siminti sai a gyara. Godia ya sakeyi kafin ya bi ta dan hanyar ya shige Gida. Aunty Aseeyah haka ta tashi ta ga Ikon Allah, da mamaki, Baban Ameera ya mata bayani, ya kuma gaya mata yanda sukayi da Alhaji Ali, jinjina lamarin tayi kafin ta k'ara da Allah ya tsayar nan, dan tautaunawa sukayi, Baban Amiran ya yanke Shawaran su fita gabaki daya, sai ita Asiyar ta tafi Gidansu, in Yara sun tashi daga Makaranta sai a kaisu gidansu Aseeyar, Labiba Sallah tayi ta shiga dakin Labiba da Yara, Labiba na fashin Sallah. Aunty Aseeya ta fara tada yaran don suyi shirin Makaranta yau Monday. Labiba ta farka ta gaida Aunty Aseeyah, ta amsa tace "sai kika ga Bango ya fadi ko?" Wuf Labiba ta mik'e zaune tace " "Bango? Na ina? Inallillahi, ya akayi?" Aunty Aseeyah ta mata bayani, Labiba ta jajanta abun, Aunty Asiya tace "to yanzu dai k'ofar k'aura zamu yini, zuwa anjima InshaAllahu anyi gyaran. In kin tashi daga Makaranta ki wuce chan, yayanki yace zai gaya ma Mai Adaidaita sahun su Ameera da ya kaisu chan in sun tashi" Labiba tace "to shikenan Allah shi kyauta ya tsare". Yara suka fara tafiya Makaranta, kafin Baban Amira ya fita Kasuwa, Aunty Aseeyah tace "karfe nawa kike da lectures?" Labiba tace "9 ne" "Ohh, na zata yanzu ne, bari na jiraki sai mu fita tare" Labiba tace "ki tafi kawai Aunty, in na gama sai na kulle Gidan ko?" sai da suka danyi mahawara kafin Aunty Aseeyah ta amince. Itama 8 daidai ta shiga wanka, ta fito ta shirya cikin riga doguwar Riga Bak'a, Jan gyale medium ta sa ta yane kanta, ta kulle kofar Dakin, dama Aunty Asiya ta rufe Dakinta da Parlo da kitchen. K'ara saba jakkarta tayi ta yi hanyar fita, bata san dalilin juyawa ba, sai juyawa tayi ta hada Ido da k'ofar dakin da ke kallonta na Gidan Alhaji Zaki, kuma tana da tabbacin daya daga Ciki na DanMakaho ne, Kila ko Sallahr Asuba beyi ba cewar zuciyarta, har tayi gaba, zuciyarta ta tunzurata da ta je ta kwankwasa mai, ya tashi yayi Sallah, samun kanta tayi da bin umurnin Zuciyarta, tsallake rusassun bulo din ta dinga yi har sai da ta dangana da Gidan Alh Ali Zaki, amsa kuwar zuciyarta take yi , duk da faduwan gaban da take jin zuciyarta nayi, bata fasa tafiya ba har ta k'arasa gaban k'ofar dakin. K'wank'wasawa tayi amma ba amsa, Zuciyarta na harbi da sauri sauri, gabanta na tsananta faduwa, ta lek'a ta window, kwance ta ganshi ruf da ciki. Sake k'wankwasawa tayi, tare da murda handle din k'ofar. "A bude take, k'ofar a bude take, ki shiga ki tadashi yayi Sallah" cewar Zuciyarta Girgiza kai tayi tare da runste ido, amma zuciyarta na sake tunzurata. Ki kiyaye mutuncinki Labiba, ki tsare mutuncinki, a kullum maganar Maminta kenan a duk lokacin da sukayi waya. Ta san abunda take shirin yi is wrong, babu Macen arzik'in da zatayi hakan, ba Macen da zata shiga dakin Namiji Baligi ba Muharamminta ba, duk abunda ya faru da ita, ita ta jawa kanta, ita ta kai kanta, ko dakin Yayyinta Mahaifinta ya masu iyaka da shiga sashensu, balle wannan da ba zatayi shaidarshi a kan komai ba, bata san menene ke sa tana biyewa zuciyarta a 'yan kwanakin nan, ba halinta bane, amma bata san yanda zata tsayar da abun ba, Bude k'ofar tayi tare da sa Kanta, tattaro Natsuwarta tayi kafin ta bubbuga kan Katifar da yake kwance tace "DAN MAKAHO" Firgigit ya tashi, k'anannen idonshi ya dago ya kalleta da mamaki, kafin ya mik'e tsaye kyam yana binta da wani irin kallo, cikin Labiba ya bada k'ulululu, ta zabure zata ruga a guje, da sauri ya sha gabanta fuska daure yace "Ina kuma Zaki?". Yayyyyyy people, Labiba ta kawo kanta fa.. Ba shi ya kirata ba, ita ta kawo kanta Yau Mankas zai Angwance Rengyem Me kuke tunanin zai faru? Drop your thoughts here Biko Vote Vote and Vote. #1love #DM #SonSoFWA #anatare #nagode Biebee Isa. [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Shidda (WACECE KE?) Vote before reading please don ku kai karshe kun manta da wani zancen voting, just vote now. Thanks "Saurin me kikeyi? Ina zaki ba wurina kika zo ba? To ina kuma Zaki? Ba so kike ki san ko ni waye ba, to yau ko zaki sanni, ba ke 'yar iska ba, kin san yanda ake zuwa dakin Namiji ko? Aiko zaki gaya musu, kwanta dan ubanki, yau sai na miki lagalaga" ya fada yana me yunk'urin tu6e riga don ya tsorata ta. Runtse ido tayi cike da kidima, hawayenta su ka soma kwaranyowa, tana girgiza kai da k'yar ta lalubo kalmomin nan "ni Sallah na zo tadaka kayi, kuma wallahi ni ba 'yar iska bace". Hanayenshi ya rungume a k'irjinshi, yana kallon yanda take rantsuwan ita ba 'yariska bace, iyakar gaskiyarta ya gano, daurewa yayi yace "yanzu in zagi uwarki kiji haushi, ni yaro ne da zakizo tadani yin Sallah? Bude ido tayi a tsorace, bata son ganinshi ba riga, amma da rigarshi. Baki na rawa tace jiya fa naga sai daga garin Allah ya waye ka hada Salloli har Maghrib da Isha'i, shine nayi zaton ko bakayi ba, shine nace barin zo na tadaka ,ko zan samu lada, in ba haka ba, ba abunda zai kawo ni nan, saboda na damu da kai, ina so mu tsira tare ranar gobe k'iyama". Kallonta sosai yake yana nazarinta, daga bisani yace " kin damu dani? Ni k'anin uwarki ne ko na ubanki?". Kai ta girgiza tace "Aa, kai ba daya daga cikinsu bane, k'annen Mahaifana ba haka suke ba, kuma na lura Zagi kamar a jininka yake, na san na maka shishigi, ina kan maka shishigi a rayuwarka, amma ina rok'onka, wannan ya zama karo na k'arshe da zaka Zageni, kar ka k'ara zagina DanMakaho, babu mai ganin Mutuncinka a duk Unguwar nan, ni kam Ina ganin mutuncinka, inshort ni kadai ke ganin mutuncinka, so be kamata ace kana danno min Ashar ba" ta fada cike da sanyi, murmushi be kauce daga fuskarta ba. DanMakaho ya kalleta sosai, yana mamaki, be taba sanin a Arewacin Nigeria akwai Mata masu Confidence irinta ba, be taba sanin akwai Matan da zasu iya expressing kansu kamarta ba a Katsina ba, yana mamakinta sosai. Kallo ya bita dashi a hankali yace "WACECE KE" Ta amsa mai da "Labiba Ahmad". Ya Girgiza kai yace " Aa, wacece ke, kamar yanda kike son sanin Ni wanene haka nake so ki sanar dani ke wacece, sai na san ko ke wacece kafin zan iya sanar da ke ko ni waye". Murmushi tayi tace "Makaranta zanje, nidai kaje kayi Sallahr Asuba". Jim ya danyi, yace "Nayi" ta kalleshi da alamun rashin yarda, yace "ke ni fa bana k'arya, ba Bango ya fadi ba?nagani da Asuba". Murmushi ta sakar mai tace " tabbas kayi Sallah, to ni na tafi School". Bai ce da ita komai ba, ta raba shi ta wuce, har ta kai bakin k'ofan ta dakata, zuciyarta na kitsa mata da ta tsaya suyi magana, opportunity ne ta samu, k'ila daga yau ba zata sake samun irin damar nan ba. Dakata wa tayi ta juyo gareshi tace "lets talk Dan Makaho". Ya dan waigo yana mamakin rashin tafiyarta yace " lectures din fa?". Wuri ta samu daga gefe ta zauna, ta dago ta kalleshi, ta sakar mishi da murmushi tace "We are going to have our lectures here". Bata jira yace komai ba ta fara magana; Alhaji Ahmad Dakata Alhaji Ahmad Dakata dan asalin k'asar Nijar ne, Maraya ne, baya da kowa, ya zo ya fara 'yan bugabuganshi a Garin Katsina, da yake yana kaifin basira da fasaha, nan ya fara shigeshige yana samun k'anannun kwangiloli. Baiwa gareshi, yana da Ilimin Hak'a Rijiya da gina mugudanun ruwa, da ilimin Quantity surveyor amma be taba shiga Aji ba ma'ana beyi karatu ba, a shekaru da yawa a baya saboda kwarewarshi ya sa ake daukan shi gari gari don yin Aiki, Da ya dan samu kudi yake zuwa Maradi gurin Tsohon da ya tashi a gidansa, a nan ne aka aura mishi Wata buzuwa Zaharau, marainiya ce itama, ya taho da ita Katsina. Da Likafa ta cigaba mai, a ka dinga fita dashi garuruwa don yin kwangilar Tituna da Hak'on rijiyoyi, da janyo ruwa daga wani kauye zuwa babban Birni. Babban kwangila ta sameshi inda zaiyi aikin kusan Shekara a Garin Edo Benin City da Zara'u ya tafi, lokacin tana da jaririn ciki, nan ya dan kama musu dan karamin Gida, ya hau aikinshi. Ganin aikinshi ba ha'inci, ya sa shi kafin ya gama wannan aikin ya samu wani aikin, haka zaman Edo ya kamashi, sai ya zama ya fara jin dadin Edo fiye da duk wani garin da yake zuwa, a nan ya kafa Iyalinshi. Alhaji Ahmad Dakata Yana da Mata Biyu, Hajia Zahara'u, da Hajiya Jamila wacce ya aura bayan dawowanshi Edo kwatakwata, ko wacce da iya adaddin yaranta don Haihuwa suke MashaAllah. Hajiya Zaharau itace UwarGida ta haifi yara Sha daya amma Uku ke da rai Mata 2 namiji daya , Yaya Muhammadu, Yaya Hajara, sai Auta Labiba daga kanta Mami kamar yanda suke ce ma Mahaifiyarsu bata sake haihuwa ba. Hajiya Jamila itace Amaryar Alhaji Ahmad, Yaranta 7, 3Maza Yaya Aminu, Yaya Muntari, Mata Yaya Salisu, Yaya Fadime, Yaya Zaliha itace tsarar Yaya Hajara, sai Samira tsarar Labiba duk da ta girmi Labiba da 'yan watanni sai Auta Halisa. Gidan Alhaji Ahmad kamar yawancin Gidaje ne Masu mata biyu maana mai Kishiyoyi, akwai kishi tsakaninsu, sa'anan akwai 'yanubancin. Alhaji Ahmad yana tsayawa tsayin daka akan hade kawunan iyalanshi, amma abun da kamar wuya, a cikin kaso Dari, suna zaman lafiya kashi Tamannin, amma dai ana iya cewa na ciki na ciki, akwai ganin k'yashi da hassada musamman wanda 'yan wannan dakin ke ma wanchan. Muhammad da Aminu suna da Shekaru 18 aka haifi Samira ba da dadewa ba aka haifi Labiba. Sun taso kamar 'yan biyu, amma Labiba ta faye wayau, ganin tana da Wayau sosai, ga Shegen tambaya Muhammadu yayanta ya kwadaitu da son autar mamanshi ta shiga boko, don ba zai bari Babansu ya ma yarinya mai saurin daukan abu kamar Labiba abunda ya musu ba. Alhaji Ahmad Dakata be damu da sanya yara a Makarantar Boko ba yana dai sanya su a Islamiya, in Namiji ne in ya kai shekara 10 yake fita dashi wurin aiki ya koya musu Aikinshi, in kuma Mace ce, da kin samu Miji zai maki aure, . Daga Samira sai Labiba da Auta Halisa ne kawai basuyi aure ba, yawanci ba Hausawa suke aure ba, amma Maza kuwa daga Yaya Muhammad da Yaya Aminu wanda ke zaune cikin Gidan Alhaji Ahmad Dakata da matarshi. %%%%%% Da yaje wurin Baban da bukatar sanya kanannun yaran Makaranta, Baban fir yak'i, bayan Muhammadu ya kwantar da kai ya ma Baban bayani sosai kan Muhimmancin Karatu musamman ga 'ya Mace, sai suka tafka muhawara, daga k'arshe Baban ya amince. Aka sanye Labiba da Samira wani Private school. Samira bata da passion din karatu, Labiba kuwa tana son k'aratu sosai, har suka gama Primary School. A lokacin ne Zamani ya fara dakushe tauraron Alhaji Ahmad Dakata, sai ya rage samun Kwangiloli, a nan ya Umurci yaranshi da su fita su samu Aikin hannun da zai ma kowannensu, ko wanne ya kama gabanshi, Muhammadu ne yayi Arewa a garin Katsina, yanemi izinin Babanshi da ya bashi hayar Gidan da yake Katsina zai zauna Baban yace yaje dai ya zauna in ya mutu a sa Gidan a Gado. hakan kuwa akayi amma hakan ya taba zuciyar yan uba. Muhammad ya tafi katsina da ya fara 'yan bugabuga, ko shekara baayi ba da zamanshi Katsina, ya samu mata ya aura a Katsina, har Allah ya sa mishi Albarka a kasuwancinshi ya bude dan madaidaicin Provision store a Kasuwa. Samira ta tsani karatu, daga JSCE tayi ta zillewa bata son karatun, Mamanta ta biye mata, shi kuma Alhaji Dakata tunda be da damuwa kan Karatun boko, be matsa mata ba. Amma Labiba ta dage da bada himma a karatunta ta shiga Senior Secondary School. Labiba ta ke kutsawa cikin 'Yayan kudun nan ta dau ilimi, bata fiye k'awaye Mata ba saboda gulma da fada, yawancin abokanta Maza ne kuma Kiristoci, don Musulmai basu fiye yawa ba, a nan ne ta koyi tambaya akan komai, ta iya mu'amala da kowa, tun tana primary ake fita Debate da ita, bata jin komai Magana gaban dubannin mutane, ba kuma ta kunyar tambaya. Labiba tafi so ta sanya dogon Wando budadde, da rigar da ta wuce mazaunanta, tana da burin zaman Injiniya saboda duk abokanta Maza da tunanin zama Engineer suka tashi, duk tunanint irin na Maza ne amma ko so daya bata taba tunanin kwace hanyarta ba, tana da ilimin addini, bata wuce gona da iri ta fanin nan, ko hannu namiji ya bata sai ta galla mishi harara. Wayon Labiba ya girmi shekarunta, shiyasa take samun laifi da Mama kamar yanda suke cema Mamansu Samira, Mama tana son lak'afa mata sharri, ita kuma in ta san batayi abu ba, ba zata taba amincewa ba, ko me zaa mata. A lokacin da ta gama Secondary School Samari suka mata chaaa, ba sa gabanta, in sun zo zata fita ta sha hira dasu, amma kar take gaya musu ba wanda zata aura cikinsu, burinta dai tayi karatu ta zama Injiniya, in har suna sonta su jirata in ta zama Injiniya zata dawo, sai ko wannensu ya gwada bajintarshi, a hakan ta samu suke shafa mata lafia . Result sun fito, duk sunyi kyau, ta kira yayanta Muhammad ta na kuka sosai kamar ranta zai fita, ta nuna mai tana son cigabawa da Makaranta amma tasan Babansu ba zai taba bari ba. Yayan ya kwantar mata da hankali ya shaida mata zaizo k'arshen Wata.. Bata gaya ma kowa ba burin son cigabawa da karatu, harta Maminta bata sani ba, sai da Yaya Muhammad yazo da Iyalanshi, Aunty Asiya da Ameera da Sabit, murna wurin su baa magana don sai sufi shekara 3 ba suzo Edo ba sai dai waya, Aunty Asiya na san Mami don bata surukkuta da ita, tana son k'annen Mijinta, Labiban ma na sonta, da ta shiga gaida Mama, a dage ta amsa, gani take kamae Muhammad yafi yaranta kudi da arziki. A lokacin da Muhammad ya shiga da bukatar son Labiba ta cigaba da karatu, ran Baban ya baci, yace shi aure zai musu karatun da tayi a baya Allah ya amfana. A nan ma wata Muhawarar suka sake tafkawa amma Baban yace shi sam Diyarshi ba zatayi Jami'ar Edo ba, ba zatayi karatun gaba da Secondary cikin Arna ba, muma shi tsakani ga Allah aure yake son musu, ya lura kan Labiba na rawa, wai rannan nan har tistitsiyeshi tayi da tambaya don me be sa sauran yaranshi Makaranta ba. Muhammad dariya yayi, yace in zai yarda zai tafi da ita Katsina ya sanyata a Polytechnic, kuma ya mishi Alkawari da ta samu Miji, zai dawo da ita a mata Aure da k'yar Baban ya yarda, tara su yayi gabaki daya ya shaida musu hukuncin da ya yanke, nan Mama ta fara jin zafi, tace "Haba Alhaji, anya kuwa? Duk cikin 'ya'yanka, Maza da Mata, ba wanda ya taba karatu sai Labiba yanzu kuma kace zaka kaita wani gari tayi karatun Jami'ah? Ina guje maka dana sani Alhaji, Wallahi AbdulFatah ya nuna ya na sonta, gwara ka mata aure". Labiba tace "Allah ya sauwak'e in auri mai shan taba, ki aura mishi Samira" Mami ta wurgeta da harara, Samira tace "Kinga Labiba Mama na ba tsaranki bane, wallahi ki daina maida mata magana in tayi" Alhaji Dakata yace "to nidai na amince Muhammad ka tafi da Labiba, amma idan Labiba ta kwaso abun kunya, ko tayi wani abun da zai kunyatani a idanun jama'a, to ba ruwana da kai da ita da Mahaifiyarku" Mami ta kalleshi cikin tashin hankali, Labiba kuwa ko a jikinta dom ta san ba zata taba basu kunya ba, dadi ya rufeta tace "Niko wallahi sai na baka Mamaki Abbah, zan zama abun alfaharinku, da Allah, ba zakayi dana sani ba, Mami karki damu, wallahi karatu kawai zani Katsina, sai na kula muku da jikokinku" wasu sukayi dariya wasu ko sukayi fuska. Hakan kuwa akayi, Muhammad ya koma Katsina ya mata Appying HUK poly, don bin sharrudan uban, tunda Diploma Shekara 2ce, kuma akwai sharadin in ta samu Miji za tayi aure. Labiba na daga cikin wanda aka dauka da farko, saboda ko Jamb dinta Mark din yan jami'ah ne, ya gama mata preparation nan da wata biyu zata zo katsina fara lectures. Abbansu ya kirata daki, ya mata nasiha sosai, ya bata kudi Naira dubu ashirin yace kuma InshaAllahu zai dinga turo mata ko da dubu uku ne duk wata, godia tayi sosai, ta rungume Abbanta. Maminta ta ki rata daki tace "Na zauna a Katsina shekaru da yawa, na san yanda suke, yanda suke ma'amala da mutane ya sha bamban da yanda mukeyi a nan, baki taba barin Edo ba, Arewa zaki Labiba, dole ki koma halaiyar 'yan Arewa, kije kasuwa ki dinko atamfa da ankara, ki dinga shigan Hausawan usul, ba zasu miki uzurin ba a chan kika taso ba, zasu miki fassara in kikayi wani dabi'ar da ba tasu ba, ke ke son Karatu, dole ki zama irinsu ba zan so ki fito da wani penti duk kankantashi ba, kingane? Labiba ta gyada kai, Mahaifiyarta ta dade ta na mata nasiha kan kare Mutuncinta. Tana son karatu, tana son fidda mahaifiyarta kunya, zatayi komai don ganin ta cimma burinta, ta shiga kasuwa ta siyo manyan gyaluluwa da atamfofi, ta dinka su. Lokacin zuwa Katsina Yaya Muhammad ya zo da kanshi don tafiya da ita, kowa na alhinin tafiyar Labiba, don tana da shiga rai, harta Samira da ba sa shiri tayi kukan rabuwa da ita, haka suka ma Edo Sallam suka taho Katsina ta dikko dakin Kara. Gidan Yaya Muhammad dakuna biyu ne sai Parlo, da kitchen da toilet a waje, k'aramin Gida ne, Dakinta Aunty Asiya ta bar mata da Amira babban diyan Yaya Muhammad, ita kuma Aunty Asiya da Sabit suka koma dakin Yaya Muhammad. Yaya Muhammad ya raka Labiba Registeration ba wai don ya san yanda ake ba, Sati guda ya kashe yana kaita Makaranta, ta hanyar bin School Bus, ya kuma koma ya daukota, ce mishi tayi ya bari hakan nan, ta gane hanya, zata iya zuwa ta dawo da kanta, a sati na biyu ne ta fara zuwa da kanta a lokacin har tayi k'awa Aisha Usman. Wannan kenan. Zaid ya gama jinta lokacin da ta gama bashi tak'aiceccen labarinta da murmushi dauke a fuskanta, kallon da yake binta da shi ne ya sa tace "ya akayi ne?" mur Zaid ya sha "are you stupid?" kallon mamaki ta mai tace "me ya faru?". Hannu ya sa ya murza idonshi "wai ke lafiyar ki lau? Alk'awarin da kika daukar ma Maminki kenan? Don me zaki shigo dakina? Kare mutuncin kenan? Kinsanni ne? Yanzu in na danne ki, na miki abunda ba kya zato, me zakice mata? Kin san me kikayi risking? Farincikin ki, na Yayanki, na Mahaifiyarki wanda barazana ne ga aurenta, to kinyi risking kin shigo dakina, for what? Is it worth it?". Labiba tayi shiru "nasan ban yi daidai ba, but kamar yanda nace ma, wallahi kamar ana controlling dina, bansan meyasa when it comes to you, nake yin abubuwa da yawa, i am just curious, Ya Rabb, amma kasan me? Wallahi banyi dana sanin shigowa dakinka ba, bansanka ba, bansan what you are capable of ba, amma na san ka san abunda kayi, shi za'ayi ma, na san kana da k'anwa Sadiya, na san in ka shiga gonan da ba taka ba, itama zaa shiga tata, nasan ba zaka min abunda ka san ba zaka ji dadi ba in an mata ba, na san fandarewarka a busa ma ciki hayak'i ne, kuma ina da tabbacin kai ba mazinaci bane". Idon ya sake murzawa ya kwantar da murya, kamar zaiyi kuka, damuwa taji a muryarshi yace"Labibaah, you cant be so sure, ba a gane daniska a fuska, baki san abun da wani zai miki ba, ba kowa ke da irin zuciyar da kike tunani ba, wasu suna da abun ban mamaki, baki gane bak'in halinsu, nidai please kar ki kara shiga dakin kowanne namiji, ina tsoron abunda wani zai miki". Ido ta lumshe ta bude ta sakar mai murmushi, tana me jin dadin muryar nan, tace "ka damu dani?" hannu ya sa a cikin gashi kafin ya daure yace "ke dallah, tashi ki tafi School" raurau tayi kamar me shirin kuka, nifa ba inda zani, already an fito 1st lecture, kawai na baka labarina sai kuma kace zaka koreni, ai ba haka mukayi ba?". Tsaye yayi yana kallonta, itama kallonshi takeyi, sun dau mintuna fiye da uku suna kallon kallo, ko wannensu fa da abinda yake sak'awa, Wayarta ne ya katse su. Aisha ce, dauka tayi "Hello Aisha? Ya kike, eh wallahi Ruwan Jiya ya mana gyara. Bangon Gidanmu ya fadi, shiyasa banzo ba, Ayyah Allah sarki, ya lectures? Ok to". Ashe Aisha na tare da Abu Sadeeq, bashi wayar Aisha yayi suka gaisa ya mata jaje, ya shaida maya da yana missing Dimta, murmushi ta mishi kawai ta kashe wayar. Har yanzu be fasa kallonta ba, wani kiran ya sake shigowa, kallon screen din wayar tayi taga Jay mamaki ta ba kanta da ta kasa daga wayar har wayar ta tsinke, don me zata k'i daukar wayar? ta tambayi kanta, kafin ta ba kanta amsa wayar ya sake ringing, sai ta daga ido a hankali ta kalli DanMakaho da sauri ta ajiye idonta k'asa tana wasa da hanayenta, wayar na kan Katifa tana ruri. Wayar ta katse ta sake ruri, DanMakaho ya cire idonshi daga kanta, ya ga Jay a screen din, da kyar yace "Saurayinki na kira". Da sauri ta daga kai ta kalleshi da kuma sauri ta sauke kanta kasa ta kawar da kai gefe, "Oh baki iya dauka a gabana?bari na fita" ta san in ya fita nan zai barta, ganinshi aiki ne tayi saurin cewa "aa, donAllah ka tsaya zan iya dauka". Da sauri ta dauka "Hello Jay, zan kiraka, ina lectures ne" tayi saurin katse kiran, DanMakaho ya kalleta da mamaki. Da murmushin mugunta yace "Lectures? Seriously? Wow, ashe kin iya k'arya" itama tayi mamakin k'aryan da ta sharara amma sai ta dake ta daure fuska tace "Ina Jinka, ka gaya min wanene kai?" Wuri ya samu ya zauna daga gefe a sanyaye yace "Labarina bai da dadin ji" gyara zama tayi tace "zan iya saurarenka" yace "Labarina akwai tsawo" ta gyara zama tace "i have the whole day. (Ina da dukkan rana). Murmushin takaici yayi Yace "Sunana Zaid, Zaid Aliyu Zaki" Da sauri tace "Meyasa ake ce maka DanMakaho? Meyasa ake kiranka da Mankas?" A fusace yace "Zaki man shiru ko kuwa? in azarbabi zaki min tashi ki fita". Hannu ta sa ta kama bakinta "Afuwan, nayi shiru". A hankali ya soma Magana. °°°°°°° Wa zai iya mana hasashen Labarin Zaid? Vote Vote Vote please. #1love #DM #SonsoFWa #anatare #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Bakwai (ASALIN SU) Alhaji Aliyu Umar Zaki tsohon dan Siyasa ne da yayi tashe a Da. Yana da Shekaru 28 ya auri Shafa'atu 'yar mutanen Jos. Ya hadu da Shafa'atu ne lokacin da yaje Gaisuwar Mamar wani Abokinshi. A GURGUJE A lokacin, Mamar Shafa'atu na da Gidan Abinci, kafin Ali yaje Gidan Rasuwan ya fara zuwa Shagonsu Shafa'atu dake bakin hanya don cin Abinci. Shafa'atu ce ta zo ta same shi, a natse ta gaishe shi ta tambayeshi abunda za'a kawo mishi, kallonta yayi yace "ki kawo min Shinkafa da Miya da Wake, sai kan Kifi" Shafa'atu ta dago ta kalleshi da mamaki tace "babu kan Kifi, saidai gangar Jiki da Bindi". Ya dan tuburne fuska yace "ni kuma Kan Kifin nakeso" ta dan sa yatsar ta a baki tana nazari, su ba sa ba Customers kan kifi, amma wannan ya buk'aci da a bashi, tace "ka dan bani mintuna na soya maka" murmushi yayi don sosai 'yar budurwar ta burgeshi. Bayan wasu 'yan mintuna ta dawo da abunda ya buk'ata, sosai ya ci Abincin nan, don ya sha tafiya, rabonshi da abinci tun kafin ya baro Katsina, sai ruwan da ya sha a Tasha, tambayar kudin Abincin yayi, tace mishi "kudinka naira dari da hamsin ne" cirowa yayi ya bata. Ali sai ya manta da abunda ya kawo shi garin Jos, ya ja Shafa'atu da fira, haka ta biye mishi, da yaga Maghrib na neman yi baije yayi abunda ya kawo shi ba, ya ciro takardan da aka rubuta Adireshin Gidan Rasuwan, ya gwada mata "ko kin san Anguwar nan?" tace "eh ba nisa" nan ta sake mai kwatance. Sallama sukayi tare da shaida mata zai dawo Gobe, murmushi suka sakar ma junansu, Ali ya tafi kwatancen da ta mishi da taimakon wani mai a kori kura ya gane Gidan. Sosai Abokinshi yaji dadin ganinshi, ya mishi godia sosai. Washegari Ali ya koma Shagon su Shafa'atu, tun wurin k'arfe 10 na safe, dama da tunaninshi Shafa'atu ta kwana, taji dadin ganinshi yau, nan suka zauna suna ta fira, ba abunda ke tadata sai in Customers sunzo da ta basu abincinsu take dawo gurin Ali, Mamarta bata damu ba in dai kudi na shigo musu bata da matsala. Maimakon kwana 1 da Ali yayi niyyan yi, sai gashi har kwana Uku be koma Katsina ba, duk da yayi Sallama da Abokinshi. A cikin 'yan kwanakin nan Shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakanin Ali da Shafa'atu don Soyayya har ta shiga tsakaninsu kamar Almara. Ranar da yace zai koma kar hankalin 'yan Gida ya tashi, Shafa'atu ta sha kuka sosai, a cewarta in ya tafi ba zai dawo ba, shi kuwa ya mata Alkawarin dawowa nan bada jimawa ba don zuciyarshi na wajenta a k'arshe ma ya tabbatar mata da cewa da labarin Aure zai dawo Mata. Da wannan batu suka rabu Ali ya dawo Gida Katsina. Ali ne Babba a Gidansu, yana da k'anne Maza da Mata. Yayi karatun Arabi da Boko a Kano, be da wani aiki takamaime, amma yana da shige-shige da kutse-kutse, in yaje wuri sai ya tabbatar da an san shi a wajen kafin ya bar gurin, shiyasa abokan shi ke mai Inkiya da Ali Zaki ko suce Zaki kawai. Tunda ya dawo Katsina yake ta tunanin Shafa'atu, hankalinshi dungurugum na gurinta, zuciyarshi na gaya mai ya koma Jos, nan ya bi zuciyarshi, ya sanar da Mahaifiyarshi zai koma Jos don ya samu Mata a chan, Mamarshi tayi mamaki sosai, amma sai tace "yanzu Ali duk Matan da ke garin nan da k'auyen garin nan basuyi maka ba sai ka dangana da Jos? Da dai ka bar maganar ta Jos ka zo ka bincika cikin Dangi, kasan Babanku dai" nan ya hau mata Magiyan donAllah ta goya mishi baya, zai samu amincewar Baban in har ta goya mishi baya, bayan ya dan sha wahala ya ci nasarar convicing dinta daga k'arshe. Bayan 'yan kwanaki ya Koma Jos da Babanshi da k'anenshi sukaje ma Maman Shafa'atu da maganar Aure. Ta amince da hannu bibbiyu, Baban Shafaatu be da ta cewa don sai abun da Mamar tace, abu dai kamar wasa aka daura Auren Shafa'atu da Aliyu Zaki. Bisa Alada aka rakota nan Gidansu Ali da ke Katsina inda a ka kaita dakin Ali. Sosai Ali ke Son Shafa'atu, itama haka take sonshi, tana kyautata ma Mahaifiyanshi da k'anenshi, zaman lafiya sukeyi sosai. Ali na dan fita yayi 'yan buga buganshi ya samu na cefane, ya kawo Gida a dafa kowa ya ci, zama suke na tsakani da Allah. Bayan wasu yan Shekaru Har Shafa'atu tayi shekara 3 a gidan bata taba ko da bari ba, wannan ya ja hankalin Dangin Mijinta gareta, abun ya soma damunta. Alin ne ke kwantar mata da hankali yana sake tunatar da ita kan Haihuwa ta Allah ce, yana ba wanda ya so a duk lokacin da ya so. A lokacin ne Ali ya fara Shiga Siyasa, da yake yana da baki, ya iya magana sai hakan ke jawo mai Alheri daga Manyan 'yan siyasa, nan ya siya fili dan madaidaici ya fara gini, don su koma tare Matarsa duk don ya kwantar mata da hankali don ya lura rashin haihuwar nan, na damunta sosai. Har wasu Shekarun suka k'ara shudewa, Shafa'atu bata yi ko da batan wata ba, abubuwa da yawa sun faru, Baban Ali ya rasu, duk nauyin Gidansu ya dawo kan Ali. A Lokacin Ali ya shiga Siyasa tsundum don a yanzu ya wuce dan kwarako, a nan ta buk'aci da ya kaita Jos don a ganinta bata da Lafiya, ya kan ce mata "ta bar irin maganganun nan, don Haihuwa ta Allah ce, k'ila lokacin Haihuwar beyi ba" bata saurarenshi sai tayi ta kuka don danginshi sun sanga mata udo, habaibaici sukeyi mata, don Matan k'anenshi daga mai yara daya sai biyu, ita dai ya taimaka ya kaita ta samu magani". Ba don ya so ba, ya kaita Jos da Motarshi, ya barota chan, nan Mamarta ta shiga dirka mata magungunan samun ciki. Watanta daya a Jos Ali ya dawo daukarta don yayi kewar Matarshi sosai. K'ulle mata magungunan akayi, har da na hayak'i, a ka kuma hadota da k'aninta Hudu dan shekara 4, Ali bai damu ba, don zai iya yin komai don Matarsa.. Shiru-Shiru bayan Watanni babu wata alama, hankalinta yayi mugun tashi da taga ba sarki sai Allah, sai ta bar yin maganin ta zubawa sarautar Allah ido. BAYAN WASU 'YAN WATANNI Alhaji Ali yayi suna, ya lula cikin siyasa tsundum, a lokacin shine Dan Majalissar dake wakiltar Katsina a Birnin tarayyah Abuja. Tunda Allah ya buda mishi yake kai danginshi aikin Hajj.Ya hada da Mahaifan Shafa'atu. Wata rana, Alhaji Ali na hanyar zuwa Katsina daga Abuja shi da Drivernshi, suka tsaya a Masallacin Matafiya da ke Zaria. a gidan mai Masallacin yake. Bayan sun idar da Sallah ya hadu da wani Abokinshi Alhaji Usman Shehu da suka yi Karatu a Kano tare. Da Murna suka rungume juna, bayan sunyi gaisuwa, Alhaji Ali yace "Haba Abokina ka boye" Alhaji Usman yayi dariya yace "Ina talaka zai ganka kana dan majalissa, ai ka zarce ni" Dariya sosai Alh Ali yayi yace "kai har yau baka bar iskanci ba" sukayi dariya baki daya. "Daga ina zuwa ina?" Alh Usman yace "daga zariya zamu koma Kano , chan nake zaune da wallahi iyalaina" Alhaji Ali yace "yaranka nawa?" "su 3 ne muje ku gaisa na san sun idar da sallah suna Mota" Tare suka je inda yayi parking Motar shi, ya bude yace ma matarshi ta fito su gaisa da abokinshi, fitowa tayi daga mota yaran suka fito su ma suka gaisheshi, daya bayan daya ya daukesu yana tambayan sunayensu yana mai sha'awarsu, sosai yake son yara, barin ma na k'annenshi, so yake ya dauki wasu daga cikin yaran k'annen nashi, amma da yake suna da yawa be son daukan dan wani ya bar na wani, kar ace ya nuna bambanci ko fifiko ga wani da kuma be so Shafa'atu taji an mata ba daidai ba don ita bata haihu ba, shiyasa be taba bijirowa da son rike 'ya'yan kanenshi ba. "Kaifa yaranka nawa?" dan murmushi yayi yace "tukunna dai Allah bai kawo ba" Alhaji Usman sai yayi nadamar tambayarshi don kar yaga kamar yana son ci mai fuska ne, Alhaji Ali ya lura da yanayin da abokinshi ya shiga yace "kai daniska, kar ka damu, haihuwa ai ta Allah ce, idan da rabona zan samu D'an cikina ko ba dade ko ba jima zan samu, kawai ka tayani da Addu'a" InshaAllah Abokina inji Alh Usman. Alhaji Usman ya kalli matarshi yace "wai ina Maryama ne?" dan murmushi tayi tace "ta na cikin masallacin mata muka barota bata idar ba" da mamaki Alhaji Usman yace "k'assarun?" tayi dariya tace "shi fa, ka santa da dadewa gun sallah" yace "danAllah je kirata muna kan hanya kar muyi marece" kafin waninsu ya sake magana hankalin Alhaji ya kai bakin Masallaci da wata halitta fara ta fito daga ciki tana gyara zaninta wanda shine matsayin mayafi. Yauwa gata nan ta fito cewar matar, bude baki yayi yace "sallatu yi sauri ko?" da murmushi ta k'araso, ta kalli Alh Usman da ya shagala wurin kallonta tace "ina wuni" kasa amsa mata yayi sai da abokinshi ya lura dashi ya sa hannu ya zunguro shi kafin ya amsa mata. Oya a shiga mota, ya umurce su. Alhaji Ali yace "Abokina wacece wannan?" yace "Maryama ce kanwata ko" dan shiru yayi kafin yace "indai har baku yi mata miji ba ina so, zan aureta". ############# Dariya Alhaji Usman yayi "kai wallahi Ali ba ka rabuwa da shiririta" tamk'e fuska Alhaji Ali yayi yace " kai ni wallahi dagaske nake, in dai wallahi ba kuyi mata Miji ba, ina so". Kallonshi Alhaji Usman yayi sosai yaga iyakar gaskiarshi kenan, yace "in har dagaske kake, to wallahi ka samu Maryam, kai dai kawai ka zo Gida, sai mu sake tautaunawa". Hannunshi ya rike yace "Wallahi zanzo, kawai ka bani full address dinka." Alhaji Usman yace "ba damuwa". Paper ya fallo a cikin Motarshi ya rubuta mishi Adireshin Gidanshi a Kano, shi ko Alhaji Ali hannu ya sa a Aljihu ya ma yara Alheri suna ta Godia, a nan ne kowanensu ya shiga Mota suka ma juna Oda kafin suka wuce. Tunda ya zauna yake lumshe ido yana sake hasaso ma kanshi Maryama, haka Driver ya ta shatata gudu Alhaji Ali na ta begen Marayama a zuciyarshi. Ya iso Katsina lafiya, sai da ya fara zuwa Gidansu ya gaida Mahaifiyarshi, kafin ya sauke mata tsarabar da yayi mata, ya ma Matasan Gidan Alheri kafin ya wuce Gidansi. Shafa'atu ta tarbeshi kamar yanda ta saba, cikin shiga ta alfarma, suka rungume juna don sunyi kewan juna, sai da ta kaishi yayi wanka, kafin ta zubo mishi Abinci suka ci tare. WasheGari, ya dauki hanyar Kano. Alhaji Usman Aminin Alhaji Ali ne tun suna Makaranta, Maryama k'anwarshi ce, kasancewar Mahaifansu sun Rasu, Alhaji Usman ne ke rik'on Maryama tun bayan Rasuwar Mahaifiyarsu, yana kula da ita sosai don har makarantar Unguwanzomanci ya sakata(Midwifery). Da Azahar suka karbi bak'uncin Alhaji Ali, Alhaji Usman yayi mamakin ganinshi, don beyi zaton zai zo nan kusa ba, lallai ya nuna mai dagaske yake. Abinci Matar A. Usman ta gabatar mai da shi, ya ci sannan ya gabatar mai da buk'atarshi, Alhaji Usman yace "ba damuwa, shi dai ya bashi ita, kuma ya san yarinya ba zata bashi kunya ba, don Matsayin Uba yake a gunta" ya mik'e tare da cewa "bari ya turo mishi ita". A daki ya isketa tana zaune kan wata kujera tana duba wani littafi, zama yayi a dan nesa da ita, tana ganinshi ta gyara zamanta tare da kulle littafin da ke hannunta. "Maryama, ina so ki Saurareni, a Parlo, akwai abokina Alhaji Ali, wanda muka hadu jiya a Zariya a Masallaci! Na san kin ganeshi, to shine ya zo neman aurenki gurina, ni kuma na bashi ke, saboda na san kyawawan halaiyanshi, na san ba zaki watsa min k'asa a ido ba". Shiru tayi batayi magana ba, yace "Maryama, ba dai bijiremin zakiyi ba ko?" da sauri ta girgiza kai tace "Yaya, kai ne Uwana kai ne Ubana duniya banda sama da kai, na san ba zaka zaba min abinda zai cutar dani ba, Nagode da zabinka gareni, Allah ya shige mana gaba". Da fara'a ya amsa da "Ameen, ni na san ba zaki bani kunya ba, ina Alfahari da ke Maryama, maza tashi, ki sanya Mayafi kije gareshi yana jiranki". Kanta a k'asa ta ciro Zaninta ta yafa ta fita waje. Da Sallama ta shiga Parlorn kanta a k'asa, zama tayi a kan kujera daga farko, kafin ta dan rusuna ta gaisheshi, shi ko da kallon So da Kauna ya bita, ya amsa gaisuwarta cikin shaukin soyayya, a hankali a hankali ya ke tambayarta tana bashi amsa, sun dau lokaci suna zantawa, daga bisani yace "ta shiga ciki ta turo Yayanta". Alh Ali ya gaya ma Alh Usman shifa ya samu Mata, ba bata lokaci yace "suje ya gabatar dashi wurin Kawun su". Alhaji Ali be bar Kano ba sai da ya tabbatar an bashi Maryama. Da farinciki ya koma Katsina, ya je ya sanar da Mahaifiyarshi yana neman Aure, ta sa mishi Albarka, Danginshi ko sunfi kowa Murna don su na son su ga gudan jininshi, k'ila Auren Rabo ne ke zuwa, nan fa aka fara shirin Biki. Ba wanda ya sanar da Shafa'atu game da Auren. Kudade ya biya masu dimbin yawa aka fara gina Mishi Katafaren Gida a wani Anguwa da kusan shi kadai ya fara Gini a wurin wato Tudun Matawalle, Shafa'atu kuwa tausayinta yake sosai, yana shakkar gaya mata maganar Aurenshi, be so taji kamar zai kara aure ne saboda haihuwa, baya so ta ga kamar ya gaji da ita ne, baya son bata mata sam, karshe dai ya biya mata kudin Umra ta tafi Makka, kuma ya siya mata 190, a lokacin da wuya kaga Mace na tuk'a mota, amma ita ya mallaka mata Motar kanta, Bayan tafiyarta Makka ya samu ya fara shirin bikinshi a tsanake. Ana saura Sati 3 Biki Shafa'atu taje Gidan Surikanta da Akushi dauke da Tuwo Miyan Kubewa busassa dominos uwar Mijinta, tunda ta shiga ta ji gabanta ya fadi, da Sallama ta shiga k'urya, zaune k'annen Alhaji Ali suke su 9 suna diba kaya, da alamu lefe ne, akwati 2 manya, da fara'arta ta gaishesu, da Hajiyarsu, Hajiya ta amsa tana dan jin nauyinta, basu san zata zo ba. Shafa'atu ta kallesu tace "to, lefe ne ake kallo? Karime wa aka kawo wa lefe bamu sani ba?" Karime ta dan kawar da kai gefe tana yak'e ta rasa me zata ce mata, Shafa'atu ta sa hannu tana daga kayayyakin tana gani tana yabawa "wai Kayan waye? Wa aka kawo mawa?" Ladidi tace "wa dai zaa kai ma wa ko?" Karime ta zungurota da hannu, da yake Ladidi ta fi ki jinin Shafa'atu tace "har sai yaushe zaa boye mata? Ke Shafa'atu lefen Yayanmu ne, za'a kai Kano Gobe in Allah ya kaimu" Shafa'atu da dan yak'e a fuskarta tace "Ahh, Yaya Shehu Aure zai sake? Waiyo Allah shi kaimu, ashe muna da biki". Ladidi tace "Iyeeee, wato Shehu kadai ne yayanmu? To babban Yayanmu nake nufi" Hajia tace "Ladidi kiyi shiru" Shafa'atu da bata fahimci komai ba tace "bangane ba, Babban yayanku? Wanne kenan?" Ladidi tace "baki gane ba? To Yaya Ali nake nufi" tsalle Shafa'atu tayi ta dire tace "Ba ku da hankali, kun ga dai bana san irin wasan nan" Asabe tace "wake miki wasa? Tunda kin kasa haihuwa, zaa auro me haihuwa". Karamin bori Shafa'atu ta hau, ta hau facali da kayan cikin Akwatunan, kafin ta wawuri Akushin Miya ta bude Miyan ta juye a jikin kayayakin, nan suka yo kanta, ta dire ta yi kan Hajiyarsu. "munafuka, ke kikace yayi aure ko?" aiko su Ladidi sukayo kanta, suka hau dukanta wai ta zagar musu mahaifya da k'yar Hajia ta hanasu dukanta, har tace "zata tsine musu in suka sake bugunta" Ina bakin shafa bai mutu ba, ta dinga surfa musu Zagi, tana laantarsu, tana cewa itace Ajalinsu, shegu k'azamai, talakawan banza, duk kyautata muku da nakeyi? Ni zakuyi wa butulci, biye nake da ku kamar na muku sujadda shine zaku saka min da wannan? Aiko zaku sha mamaki, ayi auren mu gani, ta fita fuuu, ko zaninta bata dauka ba, ta ci karo da Ali a hanya ko kallonshi bata yi ba ta fada motarta ta danna a guje, Ali ya ji gabanshi ya fadi. Ya shiga Gidan da sauri Hajia ce tace "ta ga kayan lefen ne, ka bita ka lallasheta" kallon kayan yayi yace "meye wannan kamar miya?" Ladidi ta chafe tace "Wai baka ga ruwan wulakanci da tayi a gidan nan ba, har ta na zagin Hajia, kanta farau kishiya?" ran Ali ya baci yace "Ta zageki Hajia?" Hajia ta girgiza kai tace "aa ba fa ta zageni ba ladidi" tana wurgar Ladidin da harara, kai dai ka je ka san me za ka ce mata kasan mata ba sa son Kishiya. Tashi yayi jiki a sabule ya nufi Gida, ya jima a bakin gate kafin ya shiga, zaune ya ganta har ta bashi tsoro don ta ci kuka har ta gaji, k'arasawa yayi a tsorace, be san ta inda zai fara ba, yana karasowa ta ci kwalarshi, tana jijigashi tana dukanshi ko ta ina, ni zaka yaudara Ali don kayi kudi, ni da nake zaune da kai tun baka da komai, ni zaka ci amanata Ali? Kasa magana yayi, ya kasa motsi, ta cigaba da dukanshi kafin ta fashe da wani irin kuka, rungumeta yayi tsam tun tana motsi har tayi lamo a jikinshi tana mayar da ajiyar zuciya, sai da ta daina motsi kafin ya soma magana. "Shafa'atu na san ban kyauta miki ba da na boye miki maganar Auren nan, amma ki san cewa ina sonki fiye da zatonki, duk wata Macen da zan aura a bayanki take, kar ki manta irin Son da nake maki, ki dauka wannan Auren k'addara ce, ki bani goyon baya nayi auren nan, wallahi ba zan taba wulakantaki ba, wallahi Shafata kin fi karfin wulakanci a wurina, Shafa'atu ba ayi macen da take karshena da zata wulakantaki ba, in naga ba zata girmamin ke ba, wallahi ina iya rabuwa da ita, ki taimaka min" abun mamaki hawaye ta gani kwance a idanuwanshi tana son Mijinta sosai, kalamanshi sun darsu a zuciyarta, bata da wani zabi illa ta danne zuciyarta. Bayan ta gama kumburinta ta sauko, hakan ya bashi kwarin guiwa ya cigaba da sabgarshi, amma walwalarta sam bata dawo ba, da tsanar danginshi da ya darsu a ranta, danne zuciyarta kawai take. ***. Ba wai don tsoronta yake ba kawai don a zauna lafiya ya sakar mata ragamar bikin gaba ki daya, sai yadda tace ake yi, harta dakin da Amarya zata zauna ita ta za bar mata, ya so ta ba Amarya daki biyu, amma tace nata ne kawara daya ne na amarya, be damu ba don ya san da ya gama gininshi zasu koma sabon Gida kowa da Dakinshi da Parlornshi, shiyasa be ce mata komai ba. A ka zo jere, da katifa da kujera da kayan kitchen duk aka jera a daki daya kasancewar dakin k'ato ne. Tun daga jere dangin Maryama suka gano matsala daga gun Abokiyar zaman Maryama, amma basu ce komai ba gudun sa mata tsoro da fargaban kishiya, kuma sun lura Dangin Ali na son Abun. "Kinsan Shafa'atu, ki bi a sannu, kinsan Mijinki yana daidai gwargwado gurin kyautata miki, to in kika faye zak'ewa kika kureshi, zai bar bi takanki, ke dai kawai ki bi ta bayan fage ki kori amaryar nan, ki mata zagon k'asa, kishin mimik'e zakiyi, kar ki yarda a gane ba kya sonta kin gane?" ta jinjina kai tana kwasan karatu gurin Aminiyarta Hajiya Er Rabi, Nan ta kwantar da kai ta bi har Gidansu Hajiar Ali ta basu hakuri, kan haukan da tayi sharrin shaidan ne, Hajia tace ba komai ya wuce dama an san mata da kishi, balle ita da aka boye mawa. Jumu'ah na zuwa aka daura Auren Alhaji Ali Zaki da Maryama Adamu a garin Kano ta dabo, an kawo Amarya dakinta. Uwar Dakinta Matar Yayanta ta dade tana jadadda mata nasihan da yayanta ya mata, kafin suka bar Katsina, Maryama ta sha kuka kamar idanuwanta zasu fadi. Murmushi ya mata yace "nagode Allah ya miki Albarka Maryama" Shafa'atu kamar ta fashe amma sai ta hau yak'e tace "bari ta dauko musu Abinci". Da sauri ta mik'e ta fice hanyar kitchen, Ali ya dinga bin Maryama da kallo ita ko kunya ma yake bata. Tare sukaci abinci kafin suka gama, Shafa'atu tace bari ta shiga ciki ta musu sai da safe. Shiga daki tayi ta dinga gwala kanta a bango, tana kukan bakinciki, anya hanyar nan mai bullewa ce? Anya zata cigaba da nuna komai lafiya lau ne alhalin ba haka bane? Gaskia da sake. Su ko maaurata tuni suka shige dakinsu. A GURGUJE Bayan wasu 'yan Satittika Zaman lafiya suke kadaran kadahan, Maryama dama sanyi gareta, biye take da Shafaatu, sun raba kwana bibbiyu, ko wacce burinta ta zama tauraruwa wurin Mijinta, sosai Shafa'atu ta danne zuciyarta don su zauna lafiya da Maryam, barin ma da ta ga bata da matsala. **** Ta gane tana da ciki, saboda sauyin da ta ji jikinta nayi, bata ce ma kowa komai ba ta cigaba da harkokinta. Sosai Mijinta ke nuna mata k'auna, a gaban Shafa'atu ya kan nuna kawaici, amma in suka kebe kamar ya hadiyeta. Sannu a tashi alamun Ciki ya fara bayyana a jikin Maryam, tara miyau a baki, da amai in taji tashin zuciya, daga Shafa'atun har Alin ba su dago cikin bane don ba sani sukayi ba. Ita dai Maryam ta san ciki ne da ita, in ta fara kwarara Amai kamar ta amayo hanjin cikinta. Wata Rana Hajia Er Rabi, k'awar Hajia Shafa'atu tazo gidan, Maryam ta fito don gaisheta, kallo daya ta mata ta san cewa tana da shigar ciki, da ta shiga ciki, tace "kawata, ashe mutuniyar har ta dau ciki" Shafa'atu ta mata kallon rashin fahimta. Er Rabi tace "kar ki ce baki san tana da ciki ba?" ta dan zamo daga kujera tace "kar ki ce man ciki gareta, wallahi ban sani ba, shima Alin bai sani ba" Er Rabi tace "lallai kam, ban yi mamaki ba don ko bari baki ta ba yi ba, ba ki san yanda ake gane ciki ba, to Kishiyarki Ciki ne da ita". Dam gabanta ya fadi "yanzu Maryam ciki ne da ita? Bata gaya mani ba?" Er Rabi tace "ke ya ma fi haka, kinga yanzu da kika sani, sai mu 6arar da cikin ba tare da kowa ya sani ba, balle mu shiga zargi" ido ta zaro tace "a barar da shi fa kika ce?" ta girgiza kai da sauri, tana da kishi sosai amma rashin imaninta bai kai nan ba, ta san Mijinta ya dade yana neman haihuwa, kuma amfanin Maryaman kenan ta haihu, bata ji dadin cewa ba ita zata haifa ma Ali 'ya'ya masu kama dashi ba, amma ba za ta taba halaka dan Cikin Maryama ba. Ta kalli k'awarta tace "ba wannan maganar, duk da bana so ta haihu, ba abunda zan mata gaskia, Cikin Mijina ne, farincikinshi nake so, don gaskia be rageni da komai ba" baki sake take kallon Shafa'atu tace "lallai Shafa'atu, kina tafka wauta, wayace miki Dan Miji Da ne? Kinga zaki tafka kuskure, a duk ranar da Maryama ta haihu musamman Namiji ti kashin ki ya bushe, ba mai kara kallonki da daraja, ke ce Uwargida, amma gida zai koma nata. Dangin Mijinki kuwa dama sun tsaneki da ta haihu sunanki abar tausayi". Hajiya Shafa'atu tace "nidai gaskia a bar maganar zubda cikin" Er Rabi tace "an bari, amma zakiyi kuka da kanki, ni kinga tafiyata" ta mik'e ranta a bace "haba kawata ina zaki?" tace "yo zaman me zanyi? Ana gwada maki annabi kina runtse ido". Hajiya Er Rabi ta fita, Shafa'atu ta bi bayanta tana magiyar ta tsaya amma tak'i. Da daddare wurin cin Abinci, suna zaune su uku kamar yanda suka saba, Shafa'atu tace "Alhaji, Albishir ne dani me zan samu" ya tsaya da cin tuwo ya kalleta yace "Shafata duk abunda kike so zan baki, gaya min" Maryama ta zuba mata ido, tana tunanin abunda Shafa'atu ke tafe dashi, murmushi tayi tace "Maryama Ciki gareta, akwai danka a Mahaifarta" mamakin ya sa Maryama kallonta, shi ko Gogan wani Yammm yaji a kunnenshi, ba zai iya fasalta abunda yakeji a tattare da shi ba a cikin wannan lokacin, duk suka zuba ido don ganin halin da zai shiga. Mamaki ya basu duka, da k'yar yayi murmushi yace "Allah Sarki, to Allah ya raba lafiya" ya mik'e tare da cewa bari ya wanko hannunshi, Shafa'atu ta bishi da ido, a matsayinshi na wanda baa taba mishi irin wannan Albishir din ba, tayi mamakin yanda ya karbi zancen, to ko baya son Haihuwan ne shiyasa bai taba mata k'orafi kan rashin Haihuwar ta ba, tunaninka da yawa suka darsu a zuciyarta. Ita ko Maryam ba ta ji dadin yanda Mijinta ya karbi Zancan ba, ko da ace ya saba haihuwa aka ce tana da ciki ya kamata a nuna farincikinshi, ita da take da burin haihuwa duk shekara don ta cika mishi Gida da 'ya'ya, amma ba komai, ta tashi ta kwashi kwanonin ta kai kitchen ta dauraye kafin ta koma daki. Alh Ali Zaki na shiga dakinshi ya fada kan Kujera tare da fashewa da wani irin kuka, kuka ne mai dauke da ma'anoni da dama, shi ne Zai haihu? Shi Allah ya azurta matarshi da ciki? Shekara fiye da bakwai da aure? Yau shi matarshi ke da ciki? Farincikinshi ba mai fassaruwa bane. Alwala yayi ya jera nafilfili don nuna farinciki ga Allah SWT. Watanni sun shude Tun Safe ta ke jin nak'uda, amma sai ta daure, ganin ciwon na k'aruwa yana sake yawa ya sa ta fitowa ta kwankwasa dakin Shafa'atu tana cije baki. "Yaya Cikina kamar zai balle, mutuwa zanyi" da sauri Shafa'atu ta kamota tace "gashi Alhajin be nan, ko zaki sake daurewa har ya dawo?". Maryam ta riko hannunta tace "ki taimakeni, wallahi mutuwa zanyi, nidai ki kira Unguwanzoma". Kamar daga sama sukaji Sallamarsu Ladidi da Asabe, Shafa'atu ta manta rashin jituwarsu ta karasa gunsu tace "yauwa ina jin Maryama nak'uda takeyi" Ladidi tace "to da me zaki mata? Ke zaki karbi haihuwar ki danna kan yaro ya koma?" ran Shafaatu ya baci "ai da banson a haihun da tun lokacin da take da ciki na barar da shi" Ladidi tace "ai ko ba ki fada ba na san bakincikin cikin nan kikeyi, to ta Allah ba taki ba, sai an haifeshi munci moriyar Magajin Yaya Ali da yardan Allah". Asabe tace "kinga muje mu taimaka mata, tana cikin mawuyacin hali". A daddafe suka kaita dakinta, haihuwar ce dama, bayan yan mintuna ta santalo danta jazur dashi, bayan Ladidi ta gyara Da da Uwan ta aiki Asabe zuwa chan GidanGandunsu taje ta fadi haihuwar. Shafa'atu na nan tsaye gefe tana jin kukan jariri tsoro ya mamayeta, kasa shiga dakin tayi sai ta wuce dakinta ta fashe da wani kukan da bata san ko na meye ba, fargaba ne fal ranta. Kamar daga Sama sai ga Alhaji Ali da Kanenshi, yana Gidansu Asabe ta je ta fado haihuwar, Shafa'atu na jin muryan Mijinta ta fito waje, "Alhaji sannu da dawowa" be ko kalleta ba ya wuce ya barta tsaye, gabanta ya fadi, me kenan? Ta tambayi zuciyarta, bayanshi ta bi da ido, kafin ta rufa mai baya. Yana shiga ya amsa Jaririn daga hannun Ladidi ya rungumeshi tsam a k'irjinshi, tsigar jikinshi suka mimike, wani yanayin da be taba shiga irinshi ba ya shiga, hawaye suka soma kwaranyowa daga idanuwanshi, hamdala yake yi yana godewa Allah, addua ya ma yaronshi, kafin ya karasa gun Maryama yana ta jero mata sannu yana sanya mata Albarka. Duk a kan Idon Shafa'atu, hawayen bakinciki ta fara ta fita daga dakin da sauri. Labarin Haihuwa ya Zagaye Gari, sai zuwa barka akeyi, ana taya Alhaji Ali murna, kullum Gidan ceike yake da Danginshi da yan barka. Shafa'atu ta zama kamar bakuwa, don da ta zo wuri ake mata habaici, ita Maryama bata da ta cewa sai yanda dangin Miji sukayi da ita don ma suna sonta, kowa so yake ya burgeta, daga masu dafa mata abinci, sai masu ina zaa saka da ita. Alhaji Usman da Iyalanshi da Dangin Maryama sunzo barka, da yawa sun tsaya Suna. An san Alhaji Ali da kyauta, amma tunda akayi haihuwar nan, ya Soma kyauta kamar baya son kudadenshi, kyautata ma Makwaftanshi yake. Ranar Suna aka radawa yaro Suna ZAID ALI ZAKI. Zaid ya sha kyaututuka daga manyan 'yan siyasa. Anyi babban liyafan Sunan da baa taba yin irinshi ba a Anguwar. Wani sabon kulawa Alh Ali ke ba Zaid da Mahaifiyarshi, dan kawaicin da yake ma Shafa'atu a da yanzu babu shi, gabanta yake nuna tsantsar soyayarshi ga danshi, in yana tare da Zaid ba ya da lokacin kowa da komai, Abujan da yake yawan zuwa yanzu ya bari, in ko Zaid na kuka da kanshi yake zaro Nono daga Jikin Maryama ya ba Zaid ko gaban waye. Ba ya kawaici ko shariya wai don Zaid ne dan fari, mutane na mai uzuri ganin be taba haihuwa ba. Shafa'atu ta fara jin ba daidai ba, Alhaji Ali ya rage damuwa da ita, kacokam hankalinshi ya koma kan Zaid, tun tana daurewa har ta tare shi wata rana da maganar a parlo. Yana rike da Zaid a k'irjinshi "Alhaji, magana nake so muyi" ya dan kallota amma be fasa ma Zaid wasa ba, hakan da yayi ya nuna mata yana sauraronta tace "Alhaji, wai kai baka da lokacin kowa da komai sai na Zaid? Kai ko dan kawaicin Dan fari bakayi? Alhaji, ba ka gudun bakin mutane? Komai Zaid komai Zaid?" baki sake yake kallonta yace "Shafa'atu wace irin magana ce wannan kike? To in banyi lokacin Zaid ba lokacin wa zanyi? Don mutane kar suce banda kunya, ko kuma kar suce banda kawaici sai na k'i nuna ma yarona So, Kauna da kulawa? To mutane sun dade ba suyi magana ba, aj dade baa zageni ba, banda kamar Zaid wallahi, kuma zan iya rabuwa da kowa ta kan Zaid ko da Mahaifiyarshi ce balle ke". A tsorace ta kalleshi, mamakinshi take, tace "Alhaji Ni? Sai ka rabu dani ta kan Zaid? Me na mishi?" yace "Yo sai na rabu da ke nana Shafa'atu, haka kurum kinzo min da wani soki burutsu, ni da Dana? Duk mai son ganin bacin raina to ya kawo kushe ga Zaid, kika cire Mahaifiyata, Wallahi na fi sonshi fiye da kowa a Duniyar Yanzu, to ki bi a hankali". Hankalinta ya tashi sosai, sum sum ta tashi ta shige dakinta tana fashewa da kuka Sosai. Haka ta kwanta zuciyarta na k'una, tunaninka kalakala, washegari ta ma Gidan Hajia Er Rabi diran Mikiya, Matsalarta ta karanto mata. Er Rabi tayi dariya, "ba ke dadi Miji ba? Ba yanda banyi dake kan a barar da cikin nan ba ki ka ki, gashi ya zame miki ciwon Ido, mai makon ace kinyi Kishi da Kishiyarki, kin kare da kishi da Dan Mijinki, ai wallahi kuka yanzu kika far yinshi, ba zaki san tsakanin Mahaifa da Gudan jininsu ba tunda ba haihuwa kika taba yi ba". Bata rai tayi tace "abun 'yar gori ce?" tace "aa, ina dai gaya miki ne, kashin ki zai k'ara bushewa a duk lokacin da Maryama ta sake haihuwa, in ko ta cika mishi Gida da yara to wallahi zaki zama Almajira a cikin gidan aurenki, kar ki yarda ta sake haihuwa, ki tashi tsaye Shafa'atu, ki kwatar ma kanki 'yanci". Jin saukar maganganun Er Rabi take kamar Darma mai zafi, dole ta tashi tsaye, da ta bisu ta arziki ba abunda ya kare ta dashi, zata bisu ta tsiya, duk sai ta ci uwarsu, nan Hajia Er Rabi tayi ta zugata tana gaya mata abubuwan da ya kamata tayi. Tun daga ranar Hajia Shafa'atu ta chanza ma Maryama, a gaban Mijinsu kamar ta goya su ita da Zaid, amma a bayan idonshi Kashi ya fisu daraja. Zaid na da Wata 5 Maryama ta sake daukan Ciki, hankalin Shafa'atu ya tashi ya a ka k'are da Zaid balle an yi mishi kanwa, kila Alhaji Ali ba zai samu lokacin yi mata magana ba. Samun Er Rabi tayi, ta gaya mata ai Maryama na da ciki, wani magani ta bata tace ta zuba mata a cikin Abinci. Ta ko ci saa cikin ya zube, bayan Maryama ta sha bak'ar wahala. Tun daga lokacin nan, ciki ya bar Zama a jikin Maryama, da tayi da cikin ya zube, kusan bari 9 tayi a shekara 4. A cikin Shekarun nan Hudu da suka shude, Alhaji Ali yayi wani irin kudi mai ban tsoro, ya koma Sabon Gidanshi da ke Tudun Matawalle, Gidan Sama ne, a Sama akwai Dakuna 3 daya na Maryama daya na Alhaji Ali, daya na Shafa'atu, sai a k'asa Akwai K'aton Parlo da dakuna biyu, sai k'aton Kitchen din da duk mai sanwa take shiga. Sai kuma ya na da masu dafa Abinci a baya inda Boysquaters suke, Gidajen da ke kusa dashi kullum suna da kwanon Abinci a Gidanshi, tunda ya dawo Anguwar kullum yana da 'yan maula masu jiranshi a k'ofar Gida, bai taba gajia ko kosawa da su ba, yana musu ihsani. Kullum hannunshi rik'e da na Zaid, duk inda ya sa k'afa to Zaid na biye dashi, mutane kuwa sai su dinga wasa Zaid da kirari ko don ya musu Alheri, Zaid na da matuk'ar wayau, baya da k'uiwa, duk yan Unguwa na sanshi, yana da son mutane kamar Mahaifinshi, yana da shekara 4 yayi wani irin wayau. Shafa'atu tsanar ta ga Maryama da yaronya karuwa yake.ta yi ruwa tayi tsaki dai gun hanata sake haihuwa, duniya ba abunda ta k'i jini irin Zaid, abunda ke bak'anta ranta, sai ta dage tayi abinci domin Mijinta, sai Alh Ali ya kira Zaid wai tare zasuci, ko kuma ya kwashe mishi namomin yace "maza cinye Zaiduna" abun nan na ci mata tuwo a kwarya, ji take ta na iya harbeshu da bindiga. In ko ranar Girkin Maryama ne sai tayi sanadin bata mata sanwa, ko ta k'ara mata gishiri, ko yaji, don dai suyi fada da Alhaji, amma bata taba jin kansu ba. Yaran Yayan Maryama na zuwa mata hutu sosai, in har Alhaji Ali baya nan, to Abinci a cikin Samira take ba Maryama wai da ita da bak'inta, ta kuma kulle kitchen din CIkin Gida don kar Maryama ta dafa komai a cewarta ai ana abincin gandu, zai zama albazaranci ayi ta dafuwa kalakala. Maryam bata taba kaima Mijinsu k'orafi ba. Da ta hadu da Zaid to sai fa ta hada shi da wani Rankwashi, ko tsunguli, in ko yana bacci har razor ta ke sawa ta fasa mishi jiki dan k'eta. Ran da ya ba kowa mamaki, randa suke zaune gabaki daya su hudu suna cin Abinci, Zaid na kan cinyan Babanshi yana sa mishi doya a baki kamar an tsunguleshi yace "Yauwa Baba, kaga kullum mama sai ta tsunguleni ta min haka akai" ya Rankwashi baban a kanshi a hankali yace "amma ni mai zafi takeyi min, me na mata baba?". Mama kamar yanda yake ce ma Shafa'atu, kowa ya san ita kadai ce Mama don Maryama Minyama ya ke ce mata. Alhaji Ali ya kalli Shafa'atu, Maryama kuwa kau da kanta tayi, yace "Shafa'atu? Ke kin Rankwashi shi da tsungulinshi? A kan mene?" Shafa'atu da tayi zaune kamar gawa ta kasa motsi, mamaki ta hanata motsawa. Sai da ya daka mata tsawa kafin ta fara borin kunya, haba Alhaji, kai ka san yanda na dauki Zaidu kamar dan cikina, don me yaro dan shekara hudu zai ma magana ka hau kai? In tsunguleshi inji me? Daga jin maganar nan an san kitsa mai a kayi, kuma ban yafe ba, Zaid ni na san ba kayi wayon hada maganganun nan ba, na san gaya maka akayi, ba wani abu, don ban taba haihuwa ba shine ake ta min abubuwa a gidan nan". Jikin Alhaji Ali yayi sanyi, shi ya san Yaronshi beyi wayon yin karya ba, amma kuma maganganun da Shafa'atu tayi sun shiga ranshi. Sai dai ya share ya cigaba da cin Abincinshi, amma ya kudurta a ranshi duk wanda ya matsa ma Zaid shima zai matsa mishi. Wannan kenan nagode.. Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Takwas (WANENE SHI?) Bibilicious freaking fans, Vote before reading please, thank you. Ya kalli Labiba yace "A zaman Gidan Kishiyoyi, ko a auro Amarya tazo ta takura ma Uwargida, ko kuma Uwargida ta takura ma Amarya, a gidanmu ba haka bane, Matar Ubana , ni ta takura mawa, da yaron Gidan take kishi, ni ta sanya wa Ido". Idan har ta bude idonta ta ganni, ji takeyi kamar ta kasheni. Ba zan manta ba wata rana Baba ya tafi Lagos wani Taro, a lokacin ina da shekara 5, na shiga Makarantar Boko, ranar da Baba zai dawo Mama ke Kitchen, ta dade tana hada Abincicika kala 2 masu dadi, da farko tuwo miya taushe, sai na biyu Shinkafa da ya ji kaza ko ta ina, kuma don rowa sai tayi don cikinshi kadai. Kamshin Abincin ya cika Gidan gabaki daya, har na kasa hakuri na bita har kitchen nace "Mama zanci Abinci" kora na tayi har da dan biyoni da gudu. Fadawa nayi daki kan Minyama, ta kasance ta na jina da Mama a kitchen, rik'oni tayi tace "Zaid, ba fa yunwa kakeji ba" nace "Ni Abincin Mama nake son ci, kuma ta hanani, bakomai, ai da Baba ya dawo tare zamuci" Minyama ta kalleni sosai kafin ta rik'o hannayena duka tace "Zaid, kana ja min matsala, DonAllah in Babanka ya dawo kar kaje wurin ci Abincinshi, zan maka irinshi ranar Girkina kaji DanAlbarka?" sai da Minyama ta dade tana lallashina kafin na amince ba zanje gun Babana ba in yana cin Abinci. Da Baba ya dawo, kamar ko da yaushe da tsarabata ya shigo, ya dauke ni ya tillani sama ya chafe "Farincikina" kamar yanda ya saba ce min, ni ko na mak'alk'aleshi ina dariya, yace "Kayi Kewana?" nace "Sosai ma". Ina kallon Mama ta galla min harara, da yake ita ce ta biyoshi daki, tuni na shiga taitayina na dan zame na bar musu dakin. Nan suka sake gaisawa, sai da yayi wanka kafin suka fito Parlo tare, ta gabatar mishi da shagalin da tayi dominshi, ta zuzzuba mishi a Plate. Baba ya lumshe ido yace "wai kin san yanda nayi kewan Girkinki Shafata?" Murmushi tayi tace "ai gaka ga shi, sai kaci ka k'oshi, nayi dominka kai kadai" Baba yayi murmushi yace "nagode k'warai". Da Bismillah ya fara cin Abinci, Shafa'atu ta zuba mishi ido cike da so da kauna, tana ganin yanda ya lumshe ido ta san cewa yaji dadin Abincin ta fadada murmushinta. Loman da Baba zai k'ara ya dan dakata, bude baki yayi yace "Ina Zaid?" Da sauri tace "yana gurin Minyamanshi ko, yi sauri ka ci kar ya huce Alhaji" Kamar zai mik'e tsaye yace "Kira min shi yazo muci Abinci". Ranta a bace tace "be fa jin yunwa, na bashi, bari na k'ara mai wani, akwai saura a kitchen kai dai ci" Fuska ya dan bata yace "kinsan dai bana iya cin Abinci ni kadai in ba da shi ba" ya mike tsaye ya nufo dakin Minyama. Ina daga chan rakube ina zaune, ban saba zama haka ba in Babana na Gida, a ko da yaushe ina jikinshi in dai aka ce yana Gida. Yana shigowa ya ganni zaune daga gefe, yace "yana ganka a nan? Bayan ga Abincinmu chan" Na dan kalli Minyama ta min ido nace "na k'oshi" be tsaya wata-wata ba ya cicciboni. Minyama ta dan ci gabanshu tace "Alhaji, da dai ka barshi, ba ya jin yunwa" Baba ya harareta yace "sai ki gaya min yaushe na fara cin Abinci a KT ba tare da Zaid ba, kai Matan Gidan nan ku fita idona fa" ya fita tare dani a jikinshi ya koma Parlo inda Mama ke zaune ranta a Jagule. "Shafata kinga ga Zaid din, ashe Maryama ce ta hanashi fitowa, zauna kaji Farincikina mu ci Abinci" ko kallon mu Mama ba ta yi ba, illa hucin da take yi, shi ko Baba be lura ba, ni kuma abunki da kwadayyaye, na zauna da na sa a cokali daya a baki sai naji kamar ban taba cin Abinci mai dadin wannan ba, sai kuma na ga kamar Abincin ya min kadan. "Baba In cinye?" da sauri Baba yace "Cinye tas Zaiduna". A hasale Mama tace "Haba Alhaji, ba fa ka ci komai ba". "Zaid ya nuna ya na so, a kawo min na Gandu in ci" ran Mama yayi kololuwa gun baci. Sanwan da ta dauki Awowi ta na yi, wanda tayi domin shi be ci ba, sai dan loma dayan da yayi, fuuu ta tashi ta bar wurin kamar zata tashi sama. Shi ko Baba hankalinshi ya maido guna cewa yake "Yi Sauri ka cinye Zaiduna" ni ko na zage na cinye Shagalin nan tas. Dan Makaho ya tsagaita yana dariyan takaici kafin ya dan sha mur tare da murza kanannen Idonshi. Labiba kuwa zuba mishi ido tayi tana sauraronshi tana son taji k'arshen Labarin, ta k'agu taji amsoshin tambayoyinta. Ya cigaba da cewa "Shi fa Baba har ga Allah bai san Mama ta ji haushi ba, in Baba na tare da ni kowa yake mantawa, ba ya karantar damuwa a fuskan Mutum, haka ya rik'o hannuna muka shiga Dakin Mama, inda muka ganta zaune, da alama Kuka ta sha, ko bi ta kanta Baba beyi b ya fada toilet din Dakin, ya barni zaune tare da Mama. "Ni ko na matsa gunta "Mama me ya faru kike kuka? Baba ya miki fada ne? Zance ya daina miki fada" tureni tayi daga jikinta, na sake tashi na nufota "Mama wai" kafin na gama maganar da zanyi, Zuciya ta ci Mama ta riko min kunne ta fitar dani daga dakinta ta wurgar dani a Parlo." "Da yatsa ta nuna ni "Zaid ka fita idona, ina tausayinka duk ranar da na kama ka, dan Ubanka Abincin kai na dafa mawa? Da zaka zauna ka cinye? Maye ne kai da duk k'oshin da kayi in na dafa ma Babanka abinci sai kaci, kai baka k'oshi ne? Wallahi duk randa na sake dafa mai Abinci kaci sai na ci ubanka, shege Maye, na tsaneka Zaid, da na sani da na barar da cikinka tun kafin a haifeka" ta juya fuu tayi hanyar dakinta." "Kalamanta kenan a gareni, ba zasu taba gushewa a k'walwata ba, ban manta su ba tsawon Shekarun nan, kinsan me nace mata?" da sauri Labiba ta gyada kai alamun "aa" ya dan murmusa yace "yarinta ma dai to, ce mata nayi nima ban sonta kuma zan sa Babana ya koreta". "A hasale ta juyo, ta san zan aika, ji take kamar ta shak'eni na mutu, a gefenta ta wawuro wani Cokali mai yatsu, fork, daga inda take ta saito ni ta wurgo min cokalin nan cikin bacin rai tare da cewa "in ka fasa ka ci Ubanka, shegen yaro ka zame min alak'aik'ai, wallahi sai nayi maganinka". "Cokalin nan be tsaya ko ina ba sai a cikin Idona na hagu, wani gigitacen k'ara na saki wanda ya tsorata Mama, "Allah Sarki Babana ashe duk abunda ke faruwa yana kallonmu, a guje ya k'araso gareni inda na ke zube a k'asa, ya tariyo ni jikinshi yana jijjigani, ni ko ihu nake ina ambaton idona". "Minyama ta fito a rude, ita kanta Mama ta mugun rudewa, Baba ya ciccibeni, yayi waje dani, Mama a rude ta bi bayanshi, Minyama ma binmu tayi a baya". Baba be tsaya jiran Direba ba ya figi mukuli ya fada mota, itama Mama da Minyama Mota daya suka shiga, hankali a tashe suka bi bayanmu da mu kayi General Hospital. "A Emergency a ka karbeni, a lokacin Jini ya taru a cikin Idon, likitoci suka karbeni. Suka hau aiki, Alhamdulilahi ba wani ciwo a can cikin Idon, dama kin san ido baya son bak'on abu nan dai suka diga min magani a idon, suka rufe da bandage bayan Minti Talatin zasu dawo na bude in na bude ba wani abu InshaAllahu". "Bayani suka ma Baba da su Mama kan cewa ba wani abu, jini ya taru sakamakon wani abu da ya shiga, amma sun diga magani, a hankali zai washe" Godia Baba ya musu tare da zama, be kalli Minyama ba da ke kuka ballantana Mama da ranta ke cike da Fargaba, tsoro, dana sani, suna nan zaune har Minti 30 suka dawo don bude idon, a lokacin nima na farka daga dan baccin da na samu bayan kukan da na sha". "Warware Bandage din Likita yayi tare da cewa Zaid Bude idonka, sai labari ya sha bambam, da nayi yunkurin budewa sai nayi sauri na rufe, na yi hakan fiye a k'irga amma na kasa budewa, ba wai don idon ya manne ba, sai don tsoro, tsoro ya hanani budewa, Likita yayi, yayi amma na k'i budewa, fita Likita yayi don ya kira su Baba, kila in Baban ya min magana zan bude, nan su Baba suka shigo har da Minyama da Mama." "Rungumeni Baba yayi, kamar jira nake na fashe da kuka idona na mai radadi fiye da zato, Baba shima kukan yakeyi, rik'e dani sosai ya ke magana a hankali "Zaid ka bude idonka, ka ganni Baba ne, Girgiza kai kawai nakeyi, hawaye na zuba daga idona, Baba ba zan iya ba". "Baba yana kuka Sosai yace Zaid kar kace ba zaka iya ba, ba ka so mu cigaba da zuwa Filin Polo kallon Wasan Polo? Zaid in baka bude idonka ba, ta ya zaka ga na sa riga a bai-bai? Wa zai ce Baba ka zubar da miya a rigarka? Wa zaice baba-- Baba be k'arasa ba ya fashe da wani irin Kuka, duk mai rauni sai da ya tayasu". "Jarumina, ka bude idonka kaji? A hankalina na fara bude idon ko second 3 beyi ba nayi sauri na rufe don ji nake kamar ana barbada min barkono a ciki". Hannu Baba ya daura a kai kamar dan yaro yace "ta nakasa min shi, shikenan yaro na ya zama Makaho". Likitoci dai sukayi bakin k'okarinsu don ganin na bude Ido amma na kasa, sun sake bincika idon sun tabbatar ba komai a ciki, tsoro ne kawai, sai suka yanke shawaran bari na na dan kwana biyu, k'ila kafin lokacin tsoron ya fita a raina. "Ba inda Baba yaje a Asibiti yake kwana, ba ya cin Abinci, dangi sai tururuwan zuwa gani na suke duk da an hanasu shiga, Mama duk ta fita hayyacinta, tana tsoron abunda zai faru, har yanzu Baba bai ce mata komai ba, duk da itama da ita ake zaman Asibitin, rashin mata magana na damunta matuk'a". Har a kwana biyun ba wani Cigaba, haka suka sallamoni, sukace da Baba a hankali zan bude Idon, Baba ya ji haushi sosai har ya kusa dukan daya daga cikin likitocin, be koma dani Gida ba, sai wucewa dani Abuja da yayi, ba wanda ya san inda muka nufa, hankalin kowa tashe yake. Lokacin Duniya a kwance take, ya mana processing zuwa k'asar Italy don zuwa Asibiti, ba a jima ba mu ka tafi Italy daga ni sai Baba, ba wanda ya san inda muke a Gida, Minyama Kuka, Mama Kuka. Satinmu 2 a k'asar Italy, wanda suma kamar a kasar mu Najeriya, ba su ga komai a idon ba, illa tsoron da suka gani a tattare da ni, pediatric vision therapist shine ya duk'ufa wurin ganin na bude idon ta hanyar exercising idon kuma Alhamdulilah tsoron ya ragu sosai don yanzu ina dan bude Idon hagun amma ba completely ba. sai ya zama ina kanne idon kamar wanda ke tsoron wani abu zai shiga. Ba yanda zasuyi dani don hakan ya zame mini Habit (Dabi'a) sallamarmu sukayi muka dawo Nigeria Abuja muka dan huta. Daga kallon Baba ka san cewa bai ji dadin sakamakon da muka samu a K'asar italy ba to amma ya zaiyi? hakan yafi da ace danshi ya makance gabaki daya, da ya kalleni sai yace "Zaiduna kayi hakuri, an nakasa min kai" ni sai dai na kalleshi. Haka muka dawo Katsina, kowa yayi farincikin ganinmu, barinma Minyama da ta kasa kawaicin sai da ta rungumeni tana hawaye, Mama kuwa tsoro ya hanata magana har yau bata san Matsayinta ba, nima ban saki jiki a gabanta ba. Baba ya rik'eni yayi dakinshi dani, mukulli ya a ma dakin, don bai yarda da kowa ba, toilet ya fada, don yin wank, su Minyama kuwa suka shiga kitchen tareda Mama don yin abincin bak'i. Minyama ta lura da dari-dari da Mama keyi, ita fa har yau bata san me ya faru da ni ba. Dangi sai zuwa mana Barka suke, a lokacin da Baba ya fito daga wanka, ina nan zaune yace muje na ma wanka, tubeni yayi ya min wanka kafin ya shafa min mai, ina da kaya a dakinshi, ya ciro min riga da wando tazarce irin nashi, anko mukayi, sai da yayi rubutu a 'yar takarda kafin ya rik'o hanuna ya jani zuwa babban Parlo inda yake cike Mak'il da 'yanuwa da abokan arziki, harta hajiyansu Baba su Mama Asabe sun rik'ota sun kawota. Sai da Baba ya je gabanta ya gaisheta kafin ya fara amsa gaisuwan mutane, har yanzu yana rik'e da hanuna idona daya bude daya a kanne. Baba Sani yace "wai yaya Ali me ya samu Zaid a ido, daga asibiti ba mu kara ganinku ba?" Baba yayi murmushi mai zafi yace "Zaidu ka gaya musu meya sameka a ido ranar nan da na dawo daga lagos" idanuwa suka dawo gurina na dan sa hanuna na murza idon, na kalli Minyama da ta yi kasak'e don son jin me ya samu idon, nayi imani kuma gaban mama na ta faduwa ganin yanda tayi firifiri. "ba Mama bace ta wurgo min cokali me yatsu a ido don wai naci abincin da ta ma Baba" Daki ya kaure da Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, Minyama ta bude baki cike da mamaki, ko da wasa Mama bata taba gaya mata abunda ya faru ba. Ita ko Mama kamar kasa ta bude ta shige ciki, ta rasa mai zata yi, dangi sun samu abunda suke so, nan kowa ya samu abunda yake fada. Gyara murya Baba yayi, yace "In Zaid yace Mama to kuwa kun san Shafa'atu yake nufi, auren Soyayya mukayi da Shafa'atu, na aureta ne saboda ta na So na, nima ina Sonta, amma meye amfanin Zamanmu in har bata son abunda na haifa?". Wasu sukace ba amfani. Baba yace "ba na tauye mata hak'k'inta, ina biya mata buk'atunta, laifina, na ba Zaid abincin da ta girka min, wai Abinci, ta kan abinci ta nakasa min shi. Da kunne na na ji Shafa'atu na ce ma Zaid ta tsaneshi, da kunnena wallahi naji tace da ta san hbaka zai zame mata da ta markade cikinshi tun kafin ya zama gudan jini, wai yaro kamar Zaid ake ma wadannan maganganun". Magana daya ce, ba zan iya zama da wacce bata son Gudan jini na ba, ba zan iya zama da wanda ta tsani farincikina ba, kin nakasa mishi ido nan gaba ban san me zaki nakasa mai ba, Shafa'atu na tsaneki kamar yanda kika tsani Zaid, a yanzu kuwa na Sakeki SAKI UKU ga takardarki. Jikin kowa sai da yayi sanyi, Minyama na can rakube sai da gabanta ya fadi, ita ko Mama jikinta sai rawa, idanuwanta na ta ambaliyar hawaye, kana iya karanta tashin hankali daga fuskarta, bakinta har wani rawa yakeyi hak'oranta na bugun junansu da karfi, durkusawa tayi a gabanshi, tace "Alhaji, donAllah kayi hakuri, kar ka sakeni, kayi hakuri, wallahi ina son Zaid, dama sharrin shaidan ne ya sa nayi abinda nayi, kuma wallahi tsautsayi ne, ba ma da niyya nayi ba, amma tun lokacin Alhaji banda wani kwanciyar hankali, donAllah ka yarda dani, muje ciki na maka bayani, nidai kawai ka janye, ba zan iya rayuwa ba kai ba". Mik'ewa Baba yayi yace "kin taba ganin inda aka janye Saki 3? To in baki sani ba, ba aure tsakaninmu, Aurenki ya gama a kaina. Baba ya ja Hannuna ya yi ciki dani ya bar kowa zaune Banda Mama da ta ke burgima a k'asa tana wasu surutai mai kama da Sambatu. Ni Ali zaka wulakanta? Ni ke tare da kai tun kafin ka san kanka, yau ta kan yaronka ka wulakantani gaban matsiyatan k'anenka, ni Ali? Bayan son da nuna maka? Sai chan ta fashe da wani irin kuka mai karfi, da yawa sun tausaya mata, haka suka fara fita daya bayan daya. Da k'yar Minyama da ke daskare wuri guda ta taso don lallasanta, amma cikin zafin nama Mama ta tureta wanda hakan yayi sanadin faduwar Minyama akan wani table dake kusa da kujera, Minyama ta sak'i yar k'ara, su Asabe da suka rage a parlon suka yo kanta. Dukan Shafa'atu suka fara yi don har ga Allah ba sa sonta, Ladidi ce tayi dakin Yaya Ali don sanar dashi Minyama na fitar da jini ta goshi. A sittin muka fito, Baba ya kamata ya rik'e don zuwa Asibiti, bayan ya kira Securities dinshi suka fitar mai da Shafa'atu daga gidan a wulakance. A Asibiti a ka ma Minyama Dressing muka dawo Gida, ta birkice ma Baba tana kuka tace "Alhaji, ba ka kyauta ba, irin sakin da Manzo baya so, shi kayi haba Alhaji" ranshi bace "wai ke wace iri ce? Ba kiji abubuwan da tayi ta kuma ce game da Zaid ba? Kurma ce ke? Kika san tun yaushe take mai mugunta yanzu da Asirinta ya tonu ba sai ki gode ma Allah ba da a nan abun ya tsaya, Allah kadai ya san abunda take mishi, kwanaki da yake cewa tana rankwashinshi yar barikin ba karyatawa tayi ba harda kukan munafunci? Nifa da ba ke kika haifeshi ba da na ce ba kya sanshi. Tace Alhaji wallahi Kishi ne, duk macen da zaka aura dole tayi kishi da Zaid ba laifinta bane yace Shiyasa ba zan sake Auren ba, ke kadai kin isheni, ta dan sausauto da murya tace "ko in ta sake aure zaka Maidota?" ke Hajia Maryama ki fita Idona, ke Hajia Maryama ki kiyayyeni, zan mugun bata maki rai, a duk randa kika sake min maganar Shafa'atu, na dai saketa ko? Na kuma wuce gurin, ke kuma in da Dan Cikinki zakiyi Kishi zaki sha Mamaki, zan manta da Usmanu abokina ne na miki Rashin Mutunci, haka Baba yake yi in har yana fada a kaina idonshi rufewa yakeyi, Son da Baba ke min ya wuce tunaninki Labiba, ba zaki iya gane adadin Son da yake min ba. Minyama jikinta yayi sanyi, kar fa garin neman gira ta rasa ido, garin gyara auren wata ta bata nata, tun daga ranar bata sake maganar Mama ba, Mu dai ba mu san ya take ba, ko ta zo Gidan ba ma sani don Already Baba ya sa matakan tsaro na kar ta sake zuwan mai Gida. Haka muka shafe Mama a rayuwanmu. YanUnguwa, Abokanan wasana, Manya da yara suka koma ce min DANMAKAHO, don da Ido daya nake amfani, abun har ya zame min jiki, don ko da yaushe ido daya a bude daya a rufe, Baba ba ya son sunan amma ya ya iya? Niko yarinta a lokacin har kidi a ke min ana min Wakan Zaidu DanMakaho me rijiyan naira niko inta rawa na ba tare da wata damuwa ba. Duk wanda ya kirani da DANMAKAHO amsawa nake bai dameni ba, da yawa kan ce ina da wautar 'yan fari, amma fa sosai nake da farinjini, in dai na fito, to ko ina na shiga zakiji ana DanMakaho, DanMakaho manya da yara. Wai kin san abun mamaki?bayan sakin Mama da shekara 2 Minyama ta samu ciki har ta haifeshi bayan wata 9? Labiba ta jinjina kai tace "ikonAllah your Sister?" kai Zaid ya daga mata yace "lokacin aka haifi Halimattu Saadiya taci sunan Hajiyar Baba, tsakanina da ita Shekaru 11, kuma wani ikonAllah daga nan Minyama bata sake ko da batan wata ba. Darling kamar yanda Baba ke ce ma Sadiya, ta fini haske, ta na kuma da shiga rai kinsan yanda mu ke sonta kuwa?" Sosai ta samu Soyayyar mu 3, ni Baba, Minyama sai kuma dangi, wallahi ta tashi cikin So da K'aunar kowa. Ta yi Girma da Wayau, ta shiga Makaranta lokacin nikuma nagama na shiga Secondary. Zaid ya dan murza idonshi tare da yin wani guntun murmushin da ya burge Labiba da alama wani abu ya tuna, ta nutsu tana kallonshi ta ji muryarshi ya cigaba da cewa "wai kinsan In Baba yace mata Darling ita mai tsiwa sai tace ba Darling ba Dalo, nikuma sai ince Dalo wai kuma sai tayi ta kuka" Labiba ta murmusa itama, murmushin ya sake yace "Ni dan Boko wai sai na ke cema Minyama Momcy"Dalo bata iya cewa Momcy ba amma da tsamin bakinta sai da ta sa mata sunan da har gobe ya bita, kinsan me take ce mata?" da sauri Labiba ta girgiza kanta tace "Momso?" dariya ta ba Zaid wanda yana yi yana murzan idonshi kuma hakoranshi sun bayyana". Tace "Atoh, ai naji ance mata Darling tace Darlo, Mumcy kuma sai Momso ko?" Kayyatacen murmushi yayi yace "Mancy, Mancy ta ke ce mata". Sunan da Darlo ta sanya ma Momcy kenan, ni Mancy, Baba ma Mancy, kowa ma Mancy, rayuwarmu gwanin ban shaawa, muna da Gata, kudi, kwanciyar hankali, muna kyautata ma Makwafta da danginmu, muna taimakawa duk wanda yazo mana da kukanshi, muna sharewa ma wanda ya tunkare mu da matsalarsu hawayensu, kuma ko wani Gida a Anguwar na da kwanon Abinci rana da dare. Labiba wallahi ba mu san akwai wani abu wai shi damuwa ba, Baba da Mancy na biya mana ko wace irin bukata. Motoci na sunfi 3 wanda duk baba ya mallaka minsu, kudi a account dina kuwa sai na rasa me zanyi dashi. Bamu san komai ba sai Jin Dadi, Farinciki Annashuwa. Da lokaci yaja Baba ya sake fantamawa cikin Siyasa, Mancy ta zama Sister a General Hospital, ni kuma na tafi karatun Degree a London bayan an sha fama da Baba wanda da k'yar ya yarda na tafi karatun, amma kinsan duk hutu ina dawowa Gida, in ban zo ba su zasuje, duk a lokacin duniya na kwance. Wani dawowa hutu da nayi na san Yayanki, Baba ya aikeni da dubu 10 Gidanku, yace ka shiga gidan da ke jikin gidan nan, ka kaima Muhammadu kace gashi ya siya Rago yayi hidimar Suna inji ni, da na tambayi Mancy waye shi sai ta ce min wani Matashi ne mai sanin ya kamata, Ba su dade da dawowa garin ba, matarshi ce ta haihu, nace "ayyah Allah sarki, barin kai mishi sakon Baba" Lokacin aka haifi Ameera diyarki. Na koma Makaranta na hada Degree dina, mai makon na dawo gida kawai sai na Jona Masters dina bangaren abunda na karanta wato Engineering. "Ke nagaji" Ya fada ya na me fito da kwalin Sigari a gefen Wandonshi, kallon mamaki ta bishi dashi, a ranta tace "ba dai Sigari zai sha a gabanta ba, aa ba shi bane, ya zai sha Sigari a daki?" a sannan hancinta ya jiyo mata warin sigarin da ya dade a dakin wanda sai yanzu ta ankare da warin meye. Ba ta lura ba sai ganin hayak'i tayi na tashi, zabura tayi ta kalleshi, ashe tuni ya kyasta sigarin nan yana bankama cikin shi hayak'i. Baki sake Labiba ke kallonshi, DanMakaho ya wuce tunaninta, kasa daurewa tayi sai da ta tanka tace "yanzu a daki ka ke shan Taba?" banza yayi da ita, sai ma kara kunna wata da yayi. Ba ta yi shiru ba tace "ina laifin ka fita daga waje, ni gashi hayak'i ya isheni, kasan ina da athma" tarin k'arya ta fara yi. A tak'aice yace "Fita" Da sauri ta tsaida tarin k'aryanta, ta na son jin karashen labarinshi, akwai tambayoyin da take son ya amsa mata tace "ai bance zan fita ba, gani nayi bai kamata ace kana shan Taba ba a daki ba". "Dakinki ko nawa?" ya soko mata tambaya da sauri tace "aa nakane, Allah ya baka hakuri". "Kinga bansan wannan san iyawan da kike min ko?" Murmushi tayi tace "kayi hakuri". Jikinshi yayi sanyi "Ok, kina ji ba? Komai ya chanza ne a ranar da na dawo Naija, wani hutu mukayi na dawo Gida". Ranar da ba zan taba Mantawa ba, muna zaune a Bukkar waje Ni,Mancy da Dalo muna shan Fruits, dama Daddy yayi tafiya kwananshi 8 ba ya gida yaje Abuja wani aiki. Sai ko ga Motocin Daddy sun shigo harabar Gidan, gabaki daya muka tashi don murna, mu uku muka hau rigerigen karasawa ga Daddy. Sai ya fito kanshi a dage, maimakon ya kula mu da muka zak'u da ganinshi, sai dauke kai yayi ya zagaya ta dayan side din motar, a lokacin muka fahimci cewa bayan Odilenshi akwai mutum a Motar. Wata Mata muka ga ta fito daga bangaren da Daddy ya bude k'ofa, ta fito ta na mana kallon kaskanci, gabana ya fadi na kalli Mancy wanda itama na rantse gabanta ya fadi, duk tsawon shekarun nan, duk rashin wayau na a wannan lokacin fuskar nan bata taba gushe min ba". A kagauce Labiba tace "Wacece?" Zaid yace "Wacce tayi sanadiyar da ake ce min DanMakaho" Labiba ta zaro Ido tace "Aunty Shafa'atu?" Zaid yace "Exactly" labiba tace "Ya akayi? How comes? Wai itace dama Aunty Shafa ta yanzu? Ba saki uku Babanku ya mata ba?". Sigari Zaid yaja Sosai ya furzar cikin bacin rai ya cigaba da cewa "Ni da Mancy muka tsaya kallon kallon, Dalo bata santa ba, da gudu ta karasa gun Daddy don ta rungumeshi, yanda kika san wanda Kashi ya taba, haka Daddy ya zabura da da Dalo ta nufoshi, Dalo bata fahimci yanayin Daddy, ta kara kusantoshi, da wani Zafin nama Daddy ya ture Dalo ta fadi k'asa" Mamaki ya rufe mu, da sauri na k'arasa gun Dalo na dagata don ta fara kuka, da murmushi a fuskana mai dauke da mamaki nace "Daddy sannu da zuwa" wani irin muguwar hararar da ban taba ganin Irinta ba Daddy ya wurgeni dashi, gabana yayi mugun faduwa a lokacin da na hango tsana a idon Daddy, lokaci daya wallahi Allah na fita hayyacina". Mancy na tsaye fa, mamaki ya gama kare mata, da k'yar ta iya daga k'afa ta karaso tace "Sannunku da zuwa, Hajia Shafa, Baban Zaid,Sannunku da zuwa". Kamar jiranta Baba yake "Baban Zaid? Kar ki sake kirana da wannan sunan, ke ki ma fitar min a Gida Na Sakeki Saki Uku Maryama bana sonki bana son ganinki". Wani tsalle nayi na rik'o Mancy da ke niuar zubewa,Hankalina a tashe, Mancy kuwa kasa motsi ta yi, Dalo kuwa ta fashe da kuka ta karasa gun Daddy tana jijjiga shi "Daddy me kake cewa? Me ya faru? Daddy wacece wannan?". Turetan Daddy ya sake yi, yace "muje Hajia Shafata" Hamshakiyar sai yanzu tayi magana tace "yi gaba Alhajina gani nan zuwa" kamar jiran umurni yake yayi gaba, takowa tayi kusa da mu tana murmushi mai kama da na mugunta. Idonta a kaina tace "Zaid, ko ince DanMakaho, ina fatan baka manta ni ba? In ka manta ni zan tuna maka, ba zan so ka manceni ba, yanda ban taba mantaka ba, kaima ba zaka taba mance ni ba, yanda na tozarta a sanadiyarka sai ka wulakanta a sanadiyata, sai ka zama abun kwatance a garin Katsina" Ta kalli Mancy tace "Alkawari nayi, duk randa na shigo cikin gidan nan ke kuma zaki fita" Ta kalli Sadiya tace "Dalo ko? Ba a taba baki labarina ba? Nice Aunty Shafa dinki,Matar daddy dinku, shekarunki sha biyar? Shekaruna 16 rabona da gidan nan, na kuma dawo ba fita". Ta na kaiwa nan ta wuce ta barmu tsaye, kowannenmu hankali tashe yake, bamu da wani sauran farinciki daga ranar, galihun mu ya bace, komai ya watse mana, duniyarmu ta koma k'ankanuwa". Labiba ta fashe da kuka tace "ni fa ban gane ba, Ina Mancy? Me ya faru bayan nan? Ni har yanzu banji me nake son ji ba, donAllah ka gaya min". Kuka take sosai. Zaid ya tashi tsaye yace "kinsan Allah nagaji, yunwa nikeji, ya dade da nayi magana mai tsawon haka, kar ki damu wata rana zan idasa gaya miki labarin, kawai dai a gurguje Mancy na aure a Abuja ta na da diya daya". Kina son sanin meyasa na tsinci kaina a yanayin nan? Its obvious amma na miki alkawarin ida baki labarin, but a takaice zan iya shan kwalin cigari biyar a rana shisa 'yan bencin Eskaley suke ce min MANKAS. Hello Bibilicious fans, afuwan, komai ya daidaita nagode da adduoinku da fatan alherinku gareni. #Ilove #DM #SonSoFWA #anatare #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Tara (ABUNDA YA FARU) Labiba na ta girgiza kai tace "donAllah ka gaya min mai ya maidaka haka?". Dan kallonta yayi lafij yace "are you not listening? Ba ki fahimci duk abunda na fada miki ba yanzu? Isnt it obvious? Matar Uba ta maidani haka, ke ko komai sai an gaya miki kafin ki fahimta?". Sausauta murya Labiba tayi tace "naji, ina son sanin Meyasa ka fara shaye-shaye? Wacce rana ka fara shan Sigari? Meye dalilinka na shan Sigari?" Kallonta kawai DanMakaho yayi, mai take so ya sanar da ita baya ga abunda ya gaya mata yanzu? Ya lura ta na da naci sosai, tsaki yayi ya yayi hanyar k'ofa yace; "Nagaya miki yunwa nakeji, ina da buk'atar cin abinci". Gunguni tayi tace "da kana jin yunwa da ba ka banka ma cikinka wuta da sassafe ba". Waigowa yayi yace "me kikace?" Baki ta zumburo tace "fa banyi magana ba". Kai ya girgiza sosai yace "kina wasa dani Labiba, zan miki hankali" Ya sa kai ya fice, da sauri ta mik'e tsaye ta figi jakkarta ta bi bayanshi. "Tsaya, ya zaka barni a nan?" Be juyo ba yace "dama ni na kawo ki?" "To wai ta ina zan fita?" Bai fasa tafiyar ba yace "ta inda kika shigo". "Seriously?" Bai amsata ba yayi gaba abunshi, ba ta da zabin da ya wuce ta tsallaka fasassun bulo ta ketara zuwa Gidansu. **__**_**_**_**_**_**_ Wannan Sakin da Alhaji Ali ya mata, ya girgiza duk wani gabban jikinta, ta san dole ya dau hukunci, ta san shirun da ya mata yana neman hukuncin da ya dace da ita, amma Saki? Saki har uku? Ba ta tunanin ta canchanci Saki Uku, ita da ta soshi tsakaninta da Allah, tun bai kai haka ba, ta zauna dashi da dadi ba dadi, ta shanye bakincikin da danginshi suka ta k'unsa mata, wai ita ya saka saboda danshi? yanzu ya zata yi? Ita fa ba ta so ta yarda, don tunanin na barazanar fasa mata kwanyar kai. Yunk'uri tayi daga inda take durk'ushe a tsakiyar unguwa ta nufa Gidan da niyar shiga, sai dai kash akwai masu tsaron Gidan, suka sa mata fullstop daga bakin gate, tayi magiyar ta yi haukan amma a banza, wani ma daga cikin securities din ya shaida mata in ta sake zuwa zai ya daureta. Kuka Shafa'atu keyi sosai, kallo daya zakayi mata ka san tana cikin tashin hankali, da ta ga ba sarki sai Allah, sai ta ja kafarta ta nufa Unguwarsu Aminiyarta Er Rabi. Hankali tashe ta isa Gidan, jikin kawarta ta fada ta fashe da kuka mai ban tausayi, hankalin Er Rabi ya tashi, ta shiga lallashinta da kyar ta samu ta bata labarin duk abunda ya faru. Kirji Er Rabi ta dafe, Saki uku? Yau an shiga uku, a kan wani dalili zai sakeki? Shi be san tsautsayi ba? Hmm Shafa'atu, wallahi banga laifin kowa ba sai laifinki, tun yaushe nake binki kan ki barar da cikin Maryama? Tun yaushe nake ce miki a batar da Zaid, saboda ni wallahi na san yaron nan shi zaiyi Sillar barin gidan ashe Hassashe na ya tabbata, yau mun shiga uku, sai da Alh Ali ya fara mahaukacin Azziki zai sakeki?" Kuka Shafa ta fashe dashi tace " nidai ki taimaka min in koma, magiya ta fara yi mata, Er Rabi ta lura kawarta na son zarewa, dawowa kusa da ita tayi, ta tariyota jikinta tana lallashinta tace "kinsan dai a yanzu ba aure tsakaninki da Ali, sai kin sake wani auren". "Wallahi ina da wanda zai aureni ya sakoni a yau dinnan" Er Rabi tace "dakata Hajia, ina ke ina aure yau? Ko kin manta shari'ah ne? Akwai Idda a kanki, bayan nan ma dai ina so na farko ki kwantar da hankalinki, na biyu kuma ki yarda dani ki bar min komai". Share hawayenta tayi tace "eh na bar miki komai, na yarda dake". Washegari Er Rabi ta fita tun kan gari ya waye, Shafa'atu ba ta tashi ta ganta ba, kasa hakuri tayi tayi wanka ta fita zuwa Gidan Alhaji Ali, kamar jiya masu gadi suka ci mata mutunci, suka hanata shiga, wuri ta samu ta rakube a inda marok'a ke zama don jiran fitowan Alhaji Ali duk safiyya, ta san ya kusa fita Office, bayan 1hr sai ga Motocinshi sun fara fitowa, da sauri ta mik'e tsaye ta nufe Motar da take da tabbaci yana ciki don ya tsaya yana sallamar marok'a, yana hangota ya ciro kudadden da be san yawansu ba ya ba wani Yaronshi yace ka raba ma kowa, ya kallo driver yace mu tafi, kafin ta karaso tuni driver yayi gaba, sauri sauri gudu gudu ta bi bayan motar, daga bisani ta tsaida kekenapep tace ya kaita Office din Speaker, tana isa kuwa ta iske karnuka irin police dogs dinnan, securities suka sake mata su bisa umurnin Ogansu, a guje ta bar gurin da kyar ta tsira ta koma Gidan Er Rabi tana haki Rai a bace. Daidai da dawowan ErRabi, rik'ota tayi ganin tana neman kifewa "Hajia Shafa'atu meya faru? Lafiya?" Tana haki tace "Karnuka Ali ya sa aka sakar min, da kyar na tsere". Ran Er Rabi bace tace "yanzu wurin shi kikaje Shafa'atu? Gashi ya wulakantaki a banza". Sai da nace ki bar min komai" ita dai Shafa'atu bata bar kuka da kumbure kumbure ba. Er Rabi tace "saurareni da kyau, daga gurin mallamina nake, na kai mishi kukanki, amma yace na kaiki, don ya kalli kwayar idanunki ya karanto miki matsalolinki, kinsan shi baa mai katsalandan, shiyasa banje dake tun wuri ba, in ba shi yace azo da mutum ba, ba a mishi jaye-jaye, aikinshi kamar yankan wuka, kuma ba kya fadin damuwarki da ya kalleki ya san damuwarki ta mecece" Shafa'atu da ta natsu tana sauraronta tace "Er Rabi, kina da tabbacin zai magance min masalata, shi da bai santa ba ta ina zai maganceta?" Shafa'atu tace "La Ilah, ya kike magana? Wai baki yarda dani bane?". Hawayenta ta share mata ta kwantar mata da hankali, sai da ta ga hankalinta ya dawo gareta kafin ta fara magana, "Banda haufi kan Mallam, sai dai in ban kai mai kuka na ba, da naje yake magance minshi" "Yace inje dake" wuf Shafa'atu tayi tace "to wai jiran me mukeyi ne? Danallah mu tafi" Er Rabi ta mike, suka fita gabaki daya basu tsaya ko ina ba sai tashar da zai kaisu kauyen Marmara. Babban Gidane don Gidan kadai ne gini bulo, maigadi bai tsaya musu iso ba don Er Rabi yar Gida ce. Mallam na zaune a wani parlorn da yaji kayan alatu, rik'e yake da wani zungureriyar chasbaha a hannayennshi biyu. Daga wani tuntun Er Rabi ta zauna, ganin haka yasa Shafa'atu zama kusa da k'afar ErRabi. Er Rabi tace "Mallam kaga nadawo ko? Mutuniyar ce ba ta da sany shiyasa muka taho yau ba gobe ba". Mallam da tun da suka shigo yake bin Shafa'atu da wani kallo, cikin rashin sabo da irin kallon da ya ke mata ta gaisheshi, ya amsata da faraarsa. Ya fara magana ba tare da ya daina jan Chazbaharsaba "A gurguje Sunanki Shafa'atu, kin auri mai girma Speaker Alh Ali Zaki tun baida komai, kin so shi tsakani da Allah, ba ki taba haihuwa ba, kin shanye bakin cikin dangin Miji, kin zauna da kishiyarki lafiya ba wai don kina sonta ba, sai don Mijinku, ta haihu, son duniya Alhaji Ali ya daura ma dan nan, kika zo kika fara kishi da dan, kika nakasa mishi ido, Alhaji Ali ya miki Saki uku, yanzu kina sonshi, kina so ki dawo gidanki, kina so wannan karon in kin dawo ki mallake komai,ki juya komai kuma kar wanda ya kalleki ya ce miki don me, ko ba haka ba?". Da mamaki yanda ya karanto mata labarin Rayuwarta take gyada kai "hakane wallahi, ka taimakeni, da na sake aure zan kashe auren in koma ya aureni, bana so na samu matsala, bana so wani ya bani matsala wurin komawa Gidana, bana son kowa ya sake daga kai ya kalleni a wulakance". Mallam yace "kije ki gama Idda ki dawo" ba gardama ta tashi tayi gaba Er Rabi kuwa ta tsaya suka danyi magana da Mallam kafin ta fita. Bayan ta gama Iddah Er Rabi ta jadadda mata kan Rashin yi ma Mallam Gardama, da kuma bin duk wani abunda yace tayi, ka nan suka koma Gidan Mallam. "Shafa'atu aikina ba kamar na saura bane, bana aikin Ammaja, ina da kudi, bana karyar aiki, bana aikin da zai warware bayan shekaru dubu, ko mai zai faru aikina nike warwareshi da hannuna, ki gaya min, zaki iya bin sharrudda na?" Da sauri ta gyada kai, don ita ta matsu ta koma Gidan aurenta, a yan watanni hudu, ji take kamar an rura mata wutan son Alh Ali tace "Mallam na shirya, zanyi duk abunda kace" "Aikina ba a hadashi da na kowa, ni na fara sa hannuna cikin Alamarinki, ni na bude aikin ki, in kika koma gun wani ya miki aiki daga yanzu, aikin da na riga na sanya hannu, to zaki biya da ranki, mutuwa zakiyi". Baki na rawa tace "Ni wallahi ban san kowa ba" Yace "kamar yanda na gaya miki a zuwanki na wanchan karon, in har na karanceki daidai, a yanzu kina so ki koma gidanki, kina so wannan karon in kin komaki mallake komai,ki juya komai kuma kar wanda ya kalleki ya ce miki don me, ko ba haka ba?". "Eh haka ne, haka nake so" A takaice yace "to hakan ba zai faru a yanzu ba". Gwalalo ido tayi hankalinta tashe yace "na duba sosai, ba wani abun kirki da na hango, ba Alheri, ko kin koma ba zaki tarar da komai ba sai bakinciki da kunci, kyara, hantara da tsangwama, ke babu ma hanyar komawarki a yanzu don ba karamar tsana dangin suka miki ba, kuma akwai kariya sosai a Jikin Alhaji Ali da Iyalenshi, so a yanzu ba zai yiwu ba, shawara, ko kiyi hakuri har sai lokacin da zan dubo daidai, ko kuma shi Alhaji Alin ki hakura da shi baki daya". Fashewa tayi da kuka tace "Bangane ba, wallahi ba zan iya hakuri da shi ba, zan jira har sai lokacin da ka gano Alheri, ko nan da shekara 50 ne". Dariya mallam yayi yace "be ma kai shekara50 ba, shekara sha biyar(15) ne ba yawa". Fargaba, tsoro suka dura a kirjinta a yayinda ta hango iyakar gaskiarshi, cikin rudu take cewa "bangane shekara 15 ba, Mallam donAllah bar wasa muyi maganar da ya kamata". Dariya yayi yace "Kina ganin kamar wasa nake, kije ki gwada auren Alhaji Ali, ai ba ma zaiyiwu bane, in kina son burin ki ya cika, ki daure ki cika shekaru 15 dinnan zaki ga ribar hakuri, har ki dafa dutse ki sha romonta". "Mallam wai wani irin Shekaru 15? In na mutu kafin nan fa? In shi ya mutu fa? Kai in akayi K'iyama kafin shekarun su zagayo fa?" "Ke ki bar wannan tunanin bana so ki hango komai sai nasara, ki kallo nasara har kin sameshi, a lokacin Arziki ninkin ba ninkin, kuma sai yadda kikace, kuma a duk inda kike, in dai shekarun suka cika, sai ya nemoki, ko da kina kasar sin". Shiru tayi tana wasu tunani, ta waiga ta kalli ErRabi wacce take daga mata kai alamun amincewa, basirarta ta dode, zuciyarta ta bushe, hangen dogon buri take, take zuciyarta ta dinga hasko mata abubuwan jin dadi da ke jiranta nan da shekara Sha biyar. "Na fahimta Mallam, shekara wata rana kwana ce, kamar gobe ne, Allah ya kaimu". Mallam ya murmusa "to akwai wasu maganin da zan dinga rubuta miki a, ke da kanki zaki dinga wanke shi" Ido ta gwalalo, tsoro ya rufeta. "Kwantar da hankalinki, ni zan aureki, kinga kawai da nagana aiki a kanki, da na sakeki, kawai sai ki aure tsohon mijinki". Da yake zuciyarta ta dakushe, ba ta da mafadi, ta amince da bukatar Mallam, Mallam ya aureta, ya cigaba da aiki a kanta a cewarshi, sakinta yayi bayan Sati 1. Abun mamaki wai don auren da sukayi na kwanan 7. Shafaatu ta samu ciki, murna Shafaatu tayi harda kuka, gani take aikin Mallam ya fara ci, bata son Mallam ko kadan, amma inta tuna nan da shekaru sha hudu da rabi zata auri masoyinta na asali sai ta ji dadi. Ba yanda Mallam beyi kan ta zubda cikinta ba ta ki, son cikinta take sosai, kuma ita da ba ta taba ko da bari ba akan me zata zubar da cikinta, aiko ta na son abunta". Mallam yace "shi ko ba ruwanshi" tace "ta yarda". Yace "Kiyi tafiyarki, ki cigaba da rayuwarki kamar kowa, 18/10/2008 Alhaji Ali zai zo wurinki a duk inda kike,ki rubuta ki ajiye, ki fara irga kwana daga yau". Da Murna ta bar Gidan Mallam ta koma Gidan Er Rabi, ta hade kayanta da yan kudadden da take dasu ta koma Gidansu da ke Jos. Uwarta ta shiga tashin hankali da ta gaya mata sakinta a kayi, amma ta kwantar da hankalinta ganin hankalin diyarta a kwnace yake. Zaune suke da dadi ba dadi, lokacin haihuwarta ta yayi ta haifi diya Mace suka sa mata suna Amina suna ce ata Annah. Bata damu ta gaya ma mallam ba don ya riga da yace ba ruwanshi da diyar, don shi mallam bai san iya adadin yaranshi ba. Haka Shafa'atu tayi rayuwar Jos da dadi ba dadi,duk da son Ali Zaki beta bacewa ba. Shafa'atu na da Labarin Gidan Alhaji Zaki kaf dinshi, duk abunda suke ciki Er Rabi na gaya mata. Tare take da Mahaifiyarta, da diyarta da k'aninta Hudu da ba zai wuce tsaran Zaid ba, ko ya girmeshi ba da yawa bane. A shekararsu ta 5 ne Mamarta ta fara wani irin ciwo, sosai rashin Lafiyarta ya kwantar da ita a babban Asibitin Jos, bincike ya nuna Hantarta ce ta kumbura, kuma tana buk'arta a mata open surgery. Hankalin Shafa'atu ya tashi, ta rasa inda zata neman kudi, gashi ba kudin nan, damar duk buga buga ce. Duk inda zata aron kudi sai ace babu. Ta kira Er Rabi a waya tace ta ara mata dubu dari3, Er Rabi tace "wallahi bata dashi babu" hankalinta ya tashi, ErRabin ce hope dinta, yanzu ya zatayi? Katsina zuciyarta ke kira mata, kawai taje gurin Alhaji Ali. Ba doguwar Shawara washegari ta shirya Annah, suka bi Motar haya zuwa Garin Katsina, shi kuma Hudu zai zauna wurin Mama kafin su dawo. Suna isa duk a gajiye, Annah ta fita hayyacinta, ga yunwa ga gajiyar Mota, direct ta nufa Offishinshi duk da Marece yayi. Wurin Secretary dinshi ta buk'aci ganinshi, Secretary tace "ba ki da appointment, kuma 4 ya wuce, baya ganin visitors, kuma he is about to leave, ki bari sai gobe" magiya ta fara yi mata, Annah ta fara kuka. "Meke faruwa a nan?" Muryarshi ta doki kunnuwanta, da sauri ta waiga inda yake tsaye, ya fito daga office ga wasu mutane masu bakin suit da bakin Gilashi suna gefenshi. Idonshi ya sauka kanta, nan da nan fuskarshi ta hade, kafin ta yi magana yace a kausashe "me kikeyi a nan? Bana ce kar ki kara fitowa gaban idona ba? Bance miki bana son sake ganinki ba? Bance miki na tsani ko da kalonki ba? At this instant, bace min daga gani kafin na sa a Wulak'antaki". Dama tuni take zube gabanshi, kuka take tana girgiza kai "Alhajina, ka taimakeni, Mama na chan kwance bata da lafia" Bai saurareta ba yayi umurni da a fitar da ita. A wulakance a ka fitar da ita, tana kuka ta karasa Gidan Er Rabi, ErRabi ta basu Abinci, ta tausheta da cewa nan da shekara 10 zata dawo Gidanshi sai ta fanshi bakincikin da ya kunsamata na shekaru, a haka ta dinga lallabata. "DonAllah muje ki rakani wurin Mallam, kila zai taimaka min, ga Annah ma, be ma san ya take ba, kuma diyarshi ce" Er Rabi tayi saurin katseta, "aa Shafa'atu ba haka kukayi ba, sai da yace zai baki magani ki zubar da cikin Annah kikace aa, kikace ya bar miki cikinki, harda kuka, yace kar ki taba zuwa gabanshi da diyrki, kar ki taba ambatonshi a matsayin uban diyarki, kikace kin amince, yanzu kuma kice muje gurinshi? Karki manta yace ya gama aikinshi kanki rana kawai zaki jira, yace duk randa kika zo mishi da maganar diyarki zai kwance komai da ya kulla kinga kinyi jiran banza, Shekara 5 ta tafi a banza, komai ya tashi a banza, ke dai kiyi hakuri yanzu, gobe ki koma Jos a fara ma Mama maganin hausa zaa dace". Kuka Shafa'atu kawai take, Washegari da Asuba tayi Sakkon komawa garin Jos ranta 6ace, ta na dawowa da kwana daya Mamarta tace ga Garinku nan, ta girgiza da mutuwar Mahaifiyarta ta sha kuka son ranta tana tausayin kanta da na kaninta Hudu, basu da kowa, basu da komai. Rayuwa ya mata zafi, dole ta rayu kafin Burinta ya cika, dole ta zama karfin Annah da Hudu, dole duk su rayu, mikewa tayi tsaye ta fara Abincin Saidawa kamar yanda sukeyi a da, kasancewar ta iya Girki, kuma akwai Tsafta ya sa take samun Customers. Kuddirinta na nan, ranta chunkushe, Ganinta Ali zaki ne yayi sanadiyar mutuwar Mahaifiyarta, da ya taimaka mata, da amma Uwar ta aiki da ta warke, Ta k'agara Shekaru 10 su cika ta fanshe Bakincikinta. Bayan Shekara Goma 18/10/2008 Yau take Sallah a gurin Hajiya Shafa'atu, kwalliya ta ci ta sa tsaddaden leshin da Allah kadai ya san inda aka samu kudin dinkawa, harta lalle sai da aka K'unsa mata, yanda ka san Sabuwar Amarya. Da karfe 1 na rana Annah ta shigo dakinsu, tace "wai ni Mummy ina Baban nawa? Har yanzu bai iso ba?" Shafa'atu ta fara girgiza kafarta, ita fa a ganinta ko garin yau be idasa wayewa ba zata ga Alinta, gashi har an fara kiraye kirayen Sallah. Ba ta so ta sa shakku a Aikin Mallam, Shekaru 15 tayi tana jiran Ranar nan, ga ranar tazo, gashi ranan ya mata kama da sauran ranakun da suka shude, ba wani abu special game da ranar yau, ko dai tayi wauta da sakaci da ta yarda da maganganun Mallam? Ko Annah bata amsa ba ta ciro wayarta ta latso Er Rabi, Er Rabi na dauka ta fashe da kuka. Yau waya kala kusan 10 sukayi, Er Rabi tace "Yaya ne? Ya iso ne?" Shafaatu ta fashe da kuka tace "wani isowa? Har yanzu shiru, sai da nace miki zanzo Katsina kila gidan ya mai wahalar ganewa, er Rabi ya zanyi? Ko dai mallam ya wanke mu ne?" Er Rabi tace "ke dai baki da hakuri, ki bari ranar yau ta kare mana kafin kiyi korafi, kinsake hakuri, kar ki sake kirana sai yazo" dif Er Rabi ta kashe waya, ran Shafaatu a bace. ABUJA Zuciyarshi ke mishi Zafi tun bayan Sallahr Asuba, Ji yake kamar a na yankar Naman jikinshi. Meeting sukayi , amma be fahimci komai ba. Meke damunshi? Ya tambayi Zuciyarshi. "SHAFA'ATU" A takaice zuciyar ta amsa mai. Yana son ganinta, ta na ina? Tayi aure? Akwai auren wani a kanta? Ta mutu? Da sauri ya girgiza kanshi da ke barazanar tarwatsewa, tunanin Mutuwarta na neman dauke mishi numfashi, in ta mutu sai ya bita, in kuma tana da aure ko zaiyi yawo tsirara sai ya raba auren nan ya dawo kanshi, zai biya Mijin da duk wani k'addara tashi. "Ina zan fara nemanta?" Ya tambayi zuciyarshi. JOS ta amsa mai, kamar ana karanto mishi abunda zaiyi haka yake ji, kurum ya kira PA dinshi yace a siya mishi ticket din Jirgi zuwa Jos, haka ko a kayi, a gurguje suka isa Airport, suka nufa Jos bayan Mintuna da basu kai 50 ba suka isa Jos. Akwai Convoy din da suka zo tarbenshi, be manta Unguwarsu ba, ya gaya ma driver cikin 30mins suka iso Unguwarsu Shafa'atu. Kamar ana ingizashi ya fada Gidan, ko Sallama babu, abunka da me jira, ta na zaune tsakar Gida, tana ganinshi ta mik'e tsaye, murna ya sa ta fashewa da kuka, da niyarta in yazo ta dan gasa mai gyada a hannu ta ja aji, amma ganin yanda ya shigo, ta manta da duk wani bacim rai da ya taba kunsa mata a rayuwa, Son shi ya goge mata komai, daga inda yake ya choge tsaye, hankalinshi ya dan tashi ganin ta na zubda hawaye kai ya girgiza mata tare da ware hanayenshi Biyu, da gudu ta fada jikinshi ya rungumeta gam yana samun wani irin natsuwa. Murya a dishe yace "Shafata, ina kikaje kika barni cikin kewanki, Shafata me na miki kika barni?" Kiyi hakuri kizo mu cigaba da Zamanmu, Ina sonki, kece wacce na fara so a rayuwata" ganin yanda yake sake rungumeta ya sata cewa "Yarinya na kallonmu,Alhajina ai Sakina kayi, Saki Uku ma" da sauri ya tureta yace "Inji Ubanwa yace Sakin ki nayi? Nifa ban sakeki ba, ta ya zan rabu da rayuwata? Baki da labarin kece Rayuwata". Dan tabe baki tayi tace "Ya kayi da Shekaru 15 da suka wuce?" Yana son yin dogon tunani amma ya kasa cewa yayi "Ni bansani ba, kar ma ki tambayeni, abunda na sani shine, san karashe rayuwata dake, ba zan taba bari kiyi man Nisa ba". Wani Farinciki ya ziyarceta, dadi kamar tayi tsalle, "Shafata, Katsina zan tafi dake, ba zan iya kwana ba da ke ba, yau dare yayi, gobe zamu dau hanyar KT kinji?" "To wa ya ce maka zan bika? Ina da Auren wani a kaina" ganin yana neman haukacewa tayi saurin cewa "Wallahi wasa nake maka hahaha" kamar yayi kuka yace "kina son wahalar dani ne? Ki zo mu tafi Masaukina" Cike da shagwaba tace "Auren fa? Ba zaa maida ba?" Yace "Yanzu kuwa zaa maida, Da anyi sallahn maghrib sai a daura" Dadi kasheta, nan ta mishi introducing Annah a matsayin diyarta da Babanta ya mutu, Hudu kuma kaninta. Yace "duk baki da damuwa, Annah Diyata ce, Hudu kuma kanena, dukkansu na dauki nauyinsu na tsaya musu, tare zamu tafi dasu". Godia tayi mai sosai, bayan Sallahn Maghrib aka daura Aurensu sadaki dubu dari 5, a ranar duk basuyi kwanan Gidansu ba, sai a kayattacen Hotel dake Jos. Washegari da Sassafe suka hau Jirgi suka nufi Kano, daga Kano suka hau Mota zuwa Katsina. Suna isa KT ya bada Umurni a kai Annah da Hudu Shopping Mall suyi siyayyan Kaya. Shikuma suka nufi Gida tare da Amaryarshi. ^^^^^^^ Kiraye kirayen Sallahr Azahar akeyi, ashe ta dade a wurin Dan Makaho, ita ina ta lura lokaci ya ja? Wuri ta samu ta buga tagumi, tana ta nazarin Labarin danMakaho, wayarta tayi k'ara Jay ta gani a gaban screen. Numfashi ta ja ta saki ta dauka wayar da Sallama "Labeenah, ina kika shigane? Nayi missing dinki sosai" In Ina ta fara "Eh wallahi lecture mukeyi, nima nayi missing dinka" "Yaushe zaki ban lokaci na zo Katsina?" Murmushi tayi tace "duk lokacin da kazo, ina maraba da kai" Hangoshi tayi daga inda take, ya dawo dauke da wani abu a hannu, mancewa tayi da Wayar da take ta mike zuruf ta kuka tsallaka fasasssun Blocks din ta bishi daki har ta kusa bashi tsoro. "Ke wai meyasa baki da hankali ne? Ta ya zaki ta shigo min daki ne? Wato ba kiji warning din da na miki ba ko?" Baki ta tabe ta kalli ledar hannunshi, Bread ne sai Sardines, tace "ni karashen labarina nazo ji" "To ba zaa bada ba" Wuri ta samu ta zauna harda daura kafa daya kan daya tace "gama ci dai". Tsaki yayi, gardama da ita aikin banza ne ya bude Kifin gwangwaninshi, ya na dangwala mai din da bread yana ci, be kulata ba, ita kuma latsar wayarta kawai take. Daga waje kuwa Blocks aka kawo da Cement da Yashi zaa fara aiki. "Kina ji ba?" Da ya gama kenan, da sauri ta ajiye wayar tace "eh ina jinka. "Jikin Mancy Rawa kawai yake, rik'ota nayi na mata garkuwa da kafada na" ban bi ta kan Dalo da ke kuka ba, Mancy ta zare jikinta daga gareni tayi hanyar cikin gida duk sai muka bita. A parlo muka tsaya inda muka ga Baba da Anty Shafa'atu suna magana, ce mishi take ita ba zata iya zama a dakunan nan ba, bata san surkullen da ke ciki ba, kafin ya bata amsa ya hngo mu, Baba na ganinmu kamar an aiko mai da mutuwa, dif annurin fuskarshi ya dauke, ya ja hannunta ya fita, muma muka bishi riiiiiii, Mancy ta dan Matsa kusa dashi tace "ka riga da ka furta, ba aure tsakaninmu, aure ya k'are, ina so na san me na maka da na chanchaci Saki Uku gaban Yarana?" Kamar jira yake ya hau kan Mancy da duka, hankalina ya tashi na shiga tsakaninsu, na janye Mancy ina ma Baba Kallon Mamaki. "Ki fitar min A Gida Maryama, ki kwashi yaranki ki bar min Gida bana son ganinku ku duka, na tsaneku" Mancy ta share hawayenta, nikuma ina tsaye kamar gunki, Dalo kuwa na zaune dirshen a k'asa. Mancy ta matsa kusa da Dalo ta tallafota gabaki daya. Yanayin da ban taba ganin Mancy a ciki ba, ta bude murya tace "Zaid, Sadiya, zamana ya k'are a gidan nan, rabonku ne dama ya kawoni gidan nan, ku sani Nan Gidan Ubanku ne, ba ku da inda ya fi nan, ko ma mai zai faru, i mean no matter what will happen, this is Your Father's house, kar ku taba mantawa, kar ku manta da kalar Soyayyar da ke tsakaninku, kar ku bari kowa ya shiga tsakaninku" Hannayenta ta daga Sama "Ya Allah, ga Bayinka nan, Allah ga Zaid, Allah ga Sadiya, Allah kaine gatansu,Allah ka sakama duk wanda aka zalunta" Shafa'atu ta fashe da Ihu "Ni Alhaji sai dai ka Sakeni, Matarka so take ta kafurtani". Aiko ya yunkuro zai bige Mancy nayi saurin tareshi ina girgiza kai don ban ma da k'arfin magana. Ki tafi da yaranki" Baba ya sake jaddada mata, tace "ba inda zani dasu, nan ne gidansu, gidan ubansu, Ba inda zani dasu, kamar Zaid? Yana Masters? Ina zani dashi? Dalo da ba nono take sha ba ina zani da ita? Ai suna gidan ubansu, su ba Mata bane balle a sake su, 'Ya'yane su". Nan suka fara hayaniya, da karfi, ban taba sanin Mancy ta iya fada, don ko an kure hakurinta ne. Kinsan mai hakuri in an taboshi. Shafa'atu tace "kinga Maryama rufin Asirinki ki tafi dasu, kika san me zan musu in suka zauna? Ba kya tsorona ne? Ki tafi dasu, wannan Gidan daga ni sai yaran da zan haifa ma Alhajina Magada Babansu". "Huh tsoro? Bana Shafa'atu, bana tsoron makircinki, ko da ba tsoronki nake ba, kawai na fi so a zauna lafia, kuma yarane gasu nan, ki sa kansu gabas ki yanke, suna Gidan Ubansu, haihuwa kuma Allah ya kawo miki 100, duk dai yaran da zaki haifa ba zaki taba haihuwan Yayan Zaid ba, koma Sadiya, dole sai Kannensu zaki haifa". Sosai kalaman Maryama suka bata haushi, me zata mata ta bak'anta mata rai? Alhaji wai tsayawa zakayi tana gaya min magana? Wallahi sai dai ka sakeni". Yana jin haka ya rufe Mancy da duka a karo na biyu, na shiga tsakani ya hada dani, Dalo ma ta shiga tsakani aka hada da ita, ya dinga dukanmu ko ta ina yana halbemu, mu ko muna rungume da junanmu, Dalo sai kuka mai sauti take. ::::: Zaune yake da 'yar Matarshi, da jaririnsu, wani abu yake ji daga Makwaftanshi kamar hayaniya, kasa kunne yayi sosai, Gabanshi ya yanke ya fadi, Gidan da ya sani a matsayin Gida da suka kansu a kan Soyayya, Aminci da juna, abunda be taba ji ba, hayaniya, ya ji kamar ana maganar Saki, ya ji kamar maganar Barin Gida ake, wacece Matar nan da ta shigo tsakanin Gidan nan da basu son komai ba sai SO?. Matarshi ya kalla yace "Aseena, akwai matsala". A tsorace tace "Wai Sakin Mancy aka yi? Inallilahi" kafin ya bata amsa sukaji kamar kuka, da suka kasa kunnensu sai sukaji ashe dukansu yakeyi, da sauri suka tashi a sittin sukayi Gidan Alh Ali Zaki. Kamar an tara Mutane don wurin cike yake, kowa mamakin Alh Ali yake, yau shine yake dukan Farincikinshi? Da girman Zaid yake dukanshi, yake dukan Sadiya diyar da yake gani itace Yar Gwal, ga matar da yake so kamar ranshi, yau itace yake duka da hannu duk ya galabaitar da ita, rigarta har ya yage har kana iya hango abunda ke ciki, da Zaid ya tashi taimaka mata sai ya sa security su rik'eshi. Manyan Unguwan sai magana suke mishi suna rokonshi da ya barsu haka, amma be tanka kowa ba. Muhammad ya shigo da Matarshi Asee, kutsawa sukayi tayi, gidan kamar ana shooting film, kutsawa yayi ya shiga, matarshi ta bi bayanshi, daidai nan Alhaji Zaki ya daga wani katako zai kwala ma Mancy kenan ya karasa da gudu. "Haba Alhaji, Haba, menene haka? Meya sameka Alhaji? Wallahi ba Girmanka bane? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" Hajiya Shafa'atu ta dago ta kalli Muhammad da tsana, shi ko Alhaji samun kanshi yayi da maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" waigawa yayi yana kallon su yashe a k'asa, abun alfaharinshi, dukkansu yashe a k'asa. Hajia Shafa'atu tace "nifa su tafi, ina son na huta" kamar an ingiza shi yace "duk ku fitar min daga Gida, yan iska shegu, duk na tsaneku". "Alhaji ina kake so suje? Basu fa da inda ya wuce nan" ni wallahi sai sun fitar min a Gida, Muhammadu, ba na k'aunar ganinsu" DanMakaho ya kalli Labiba sosai yace "Kinsan Unguwar nan kaf, ba wanda nake ganin mutuncinshi irin Yayanki?" Labiba ta murmusa tace "Yayana na da kwarjini" yace "ya min abunda ba zan taba mantawa ba, zuwa yayi ya dago ni ya rungumeni, ya lallasheni ya rada min a kunne, ka zama k'arfin Mahaifiyarka da kanwarka, tashi ka rik'o Dalo, muje gidana muyi magana". Umurninshi na bi, na tashi na mik'ar da Dalo da ke kwance magashiyan a k'asa. Yayanki ya matsa kusa da Matarshi, ya karbi jaririn hannunta yace ki taimaka ma Mancy, bin umurninshi tayi, ta daga ta ta riko hannunta, ta ja ta, ba gardama Mancy ta bi bayanta. Sosai mutane suka tausaya mana, ina jiyo muryar wani yana cewa "Me ya samu Gidan nan? Me ya samu jin dadi da walwalar Gidan nan" wani yace "ko nayi rantsuwa ba kaffara, wanchan ce, itace Ummul Abais" Wallahi DanMakaho Allah ya saka muku, Allah ya bi muku hakkinku". Ba mu ce komai ba muka fita zuwa Gidan Yayanki, kan tabarman da suke zaune na kwantar da Dalo, na yi hanyar fita Mancy tace ma Yayanki donAllah kamo min shi, a wahalce take magana. Mallam Muhammad yace ina zaka?" Zuwa zanyi ya gaya min dalili? Me muka mishi ya tsane mu, Mallam Muhammad Babanmu ya wulakanta mu gaban mutane, Babanmu ya daga hannu ya dake mu gaban mutane, me muka mishi? Me ya chanzashi". "Zaid" Mancy tayi kirana. Na dan choge na tsaya tace "kazo ka zauna, donAllah, kana da Uwa, and i promise you, ba za ku bar Gidan Ubanku ba" "Mancy, zaman me zamuyi ba kya ciki? Ta ya zamu fara rayuwa a Gidan nan ba da ke ba, Mancy kafarki kafarmu Allah". Mancy ta girgiza kai, ta kawar da maganar "Maman Amira DonAllah kina da Panadol a ba Sadiya?". Eh barin dauko mata, ta shiga Ciki, baban Amira ya bi bayan Matarshi. Mancy ta matso kusa dani ta rik'oni tace "Stay Strong, kaine Gatan Dalo in bana nan". "Mancy". Ta katseni "Zaid, kayi min Alakawari, no matter what happens, ba zaka taba barin Gida ba, aure kawai zai rabaka da Gida, zaka kula da Sadiya, zaka kula min da kanku" "Mancy" "Zaid, DonAllah". "Mancy, ba ki ga kallon da Baba ke mana ba? Ya tsanemu fa" "Still Zaiduna, you wont leave home". Kai na gyada mata nace "I wont leave home". Dalo ta sha panadol, amma masassara ta rufeta, kinga yanda muka damu, lokacin Maghrib Yayanki ya sani Alwala don zuwa masallaci, na bar Mancy da Dalo tare da Antynki. A waje sai kallona ake tayi, wai kinsan me nagani kofar Gidanmu? Labiba ta girgiza kai yace "Katuwar Mota nagani, tana kwashe kayayyaki wanda kallo daya na musu na san kayan dakin Mancy ne da nawa" nufansu nayi, amma yayanki ya rikoni tare da girgiza min kai, yace mu tafi Masallaci kaji?" Jikina rawa yake, idona ya ciko da hawaye, lallai baba yana son Wulakanta mu. A gidan Yayanki muka kwana, daki daya ya bamu, Mancy tayi ta mishi godia, yace "haba Mancy, ai kowa ya san ke Uwa ce a Anguwar nan, duk me zamu miki ba zamu taba biyanki Alheranki ba". Washegari Mancy tace "Zaid, Sadiya, yau zan koma Kano gidan Yaya" Nace Mancy Dalo bata da karfin jikinta Masassara takeyi, ina zaki tafi ki barta? Ni ya zanyi? Mancy karki tafi? Kar ki juya mana baya donAllah, kar ki barmu, atleast not now, kina ganin korar da ya mana, na gya miki an fitar da kayayyakinmu tas". Mancy tace "Zaid ya zanyi? Wa ke gareni duk dunia in ba Yayana ba? Ina zanje? Sakina yayi fa, saki 3, ina na nufa? Nan gidan zan ta zama? Ai ba zaiyiwu ba, kuna da Mahaifi, da ranshi, yanzu ba anjima ba zan raku Gida, nikuma na wuce, ina so kuyi hakuri da duk yanda rayuwa ta zo muku, donAllah kuyi hakuri, ina sonku sosai, fiye da rayuwa da kanta". "Mancy" Ta katseni tace "Zaid mun riga da mun gama maganar nan, dole ku koma Gidan ubanku, whatever happens he is still your Father, ku tashi mu tafi, so nake kafin karfe 11 in isa Kano". Labiba banson ma Mancy gardama don wallahi a daren ranan bata runtsa ba, a kan idona tayi ta kuka, zuciyata ta karye amma sai nayi kamar bacci nake, banson ta sha wahalata shiyasa kawai na share, na rike dalo sosai ta ma Yayanki Godia, muka fita muka nufa Gida, dukkanmu gabanmu na faduwa. Karfe 8 saura muka shiga Gida. Da sallama Mancy ce me k'arfin halin Rafka Sallama. Wata Yarinya da bata wuce saar Dalo ba ta fito daga kitchen tana mana kallon wulakanci, sai ga wani shikuma ya fito daga daki wanda nawa ne. Hannayenmu Mancy ta ja, har cikin parlo, ta zaunar damu, Nasiha ta cigaba da yi mana. Sallama aka sake yi muka amsa Yan Gidansu Babanmu ne, su Aunty Asabe da Baba Sani, Maza da Matansu, sun kai su 15. Wurin mu suka nufa, Mancy ta tashi ta taryesu da faraa, suko kallon tausayi suke mata. Ina kwananku muka gaishesu, suka amsa Baba Sani yace "Maryama ashe abunda ya faru kenan? Wallahi sai yau da asuba wani abokina ke gaya min" tace "Ya muka iya da k'addara Baba Sani, zama ne ya k'are" duk su Aunty Asabe suka ma Mancy Jaje don sosai suke sonta. Wannan yarinyar tayi hanyar Dakin Baba da gudu ta na kiran Mummy, Mummy zo kiga wasu sun shigo mana Gida. Da ido duk muka bita, ba da jimawa ba sai ga shi sun fito Mama da Anty Shafa'atu. Da Mamaki kowa yace "Shafa'atu" Ita ko ta shigo ta na yatsuna Baba na binta a baya kamar Rakumi da Akala. "Su waye suka shigo mana Gida da farar safiya kamar masu bin bashi?" Kamar kare baba ya fara haushi "Eh.. su waye suke mana Sauko da sassafen nan?" Asabe tace "Yaya mune, mai Shafa'atu takeyi a gidan nan?" "Shafa'atu Matata ce, Jiya aka daura mana Aure a Jos, dama chan kune munafukan da kuka sani Sakinta" Nan aka fara kallonkallo. Mancy ta mik'e da alamu ba su ma lura da mu ba tace "Alhaji ka sa an firda min kaya ina aka kaisu?" Kamar wuta ya taso, Gidan da na daukoki chan nace a kai maki, don maita ashe baku tafi ba?". Tace "Nagode da ka sa a kaimin kayyayakina, tafiya kuma yanzu zan wuce Kano, ga dai Yaranka nan". Shafa'atu tace "Alhaji nan zata bar maka su" nan ya hayayyak'o "Kai ku fitar min a Gida, Wallahi ba zasu zauna min a Gida ba". Baba Sani yace "Ahh Yaya, ina zata kaisu? Tunda ka saketa, ai yara nakane, Ina zata da Zaid dan Shekara 25 Sadiya yar shekara 15?". Wani abu kamar Hauka Baba ya fara "Sani ka fita Idona, ina ruwanka da Sabgar Gidana? In yaran kake so ka dauke su ka tafi dasu, nidai ku fita harkana, banda 'ya'ya in ba Annah ba ita kadai ce diyata". "Wacece Annah?" Injisu. Aunty Shafa'atu tace "Our Only Daughter ga ta tsaye" kowa ya bi Annah da ido, sai faman harare harare take. Su Asabe suka fashe da kuka, Waiyo Yayanmu me aka maidaka? Zaka dauki diyar da ba taka ba kace itace kadai diyarka? Yayanmu ka manta yaranka mafi soyuwa gareka Zaid da Sadiya?". Shafa'atu ta fashe da kuka cike da kissa "Yanzu haka Alhaji yanuwanka zasu dinga min gori?ni gaskia ka sakeni ba zan iya ba, dama chan yanuwanka sun tsaneni". Hargagi ya fara "Kai Buhun Uban da ya k'ara cewa Zaid da Sadiya ne mafi soyuwa a gareni, kai zan fa kulleku, ku fitar min a gida dukkanku, wallahi duk ku fice min, na sake ganin kafar dayanku a cikin Gidana sai na sa a kulle ku a Cell, yan iska, Matsiyata". Ya juya garemu yace "Ku kuma na sake bude ido na ganku a gidan nan wallahi zan iya kasheku, don baku san yanda nakeji game daku ba na tsaneku sosai". Wuf Mancy tayi ta mik'e tsaye "Alhaji Sai ka Kashe su fa kace?" Kina waswasi ne? To ki bari na k'ara ganinsu a cikin Gida kika ga mai zan musu. "Alhaji ban san mai sihiri ya maidaka ba, Yaya Asabe sai kun tashi tsaye kan Danuwanku, a baiyane kunga dai ba yin kanshi bane, sai kuna sanya shi a addua, nima zan taya ku da Addua a matsayinshi na Uban 'ya'yana amma a yanzu zan dauki mataki, duk abunda ya sami yarana a cikin Gidan nan to shine". Shafaatu tace "to ki tafi dasu mana in ba kya son komai ya samesu, ai rufin Asirinsu su biki kawai, don ko be kashesu ba, zaman gidan nan sai ya gagaresu, ba Ubanda zai tsaya musu duk fadin Kt, so kinga da su biki daga baya gwara kin tasa keyarsu kun wuce yanzu". Mancy tace "Abunda ba ki gane ba Hajia Shafa'atu shine, Zaid da Sadiya ba inda zasu, ba wanda zai rabasu da Gidan Ubansu, ko da Uban nasu ne kam, kuma in kinga dama duk ranar Allah ki dinga sa wuk'a kina yankar namansu kuna miya, sai kuma wanda zai tsaya musu? Allah, shi zai tsaya musu, ki ja dashi in kina iyawa". Ta juya ta kalli Yanuwan Baba tace "DonAllah wa zai kaini Gidan Sarki? Ai in ba wanda ya isa da kai Alhaji, ai baka fi k'arfin hukuma ba" Baba Sani da ranshi ya gama 6aci yace "Muje hajia Maryam, muje ni zan kaiki". Baba Aminu yace "nima zanje, don wallahi wannan Makirar Matar ba zamu barta haka ba" Su Aunty Asabe sukace muma zamu. "Wai ni zaku kai k'ara? Ni zaku hade ma kai? Ni zaku tona ma Asiri?". Hajia Shafa'atu tace "Dallah, duk burga ce, suje muga zasu iya Ja da kai" kamar sakarai yace "to ku tafi din, matsiyata, bani ba ku, kar shegen da ya sake zuwa min Gida". Ba wanda ya kulashi, sukayi gaba, Dama Motoci kusan 4 suka zo, kowannensu ya samu Wuri ya zauna, suka nufi Gidan Sarki suna sake yi wa Juna Jaje. Da suka iso Gidan mai Girma Sarkin Katsina, ba su sha wahalan shiga ba don Amaryar Sarki kawar Mancy ce, tun zuwansu makka suke zumunci. Sasshenta ta shiga, ita kadai, duk sauran na Mota, bayan su gaisa ta gaya ma kawarta tazo ganin Sarki ne. Gimbiya tace "kin ko ci saa yau kwanana ne, ya kusa shiga Fada, barin ga in yana iya ganinki yanzu". Mancy tace "ba ni kadai bane, sauran na Mota". Gimbiya tace "toufa, bari naje naga" Bayan kusan minti 40 sai ga ta ta dawo "Afuwan Kawata, ashe yana Karamin Fada, yana ganin wasu baki ne, duk da haka kuna iya shiga" Mancy ta mik'e tace "barin je na kira sauran". Sun samu shiga Fadar, da biyayya suka gaida Sarki. Wasu tsofi Mata guda biyu na zaune, sai kusa da Sarki wani mutum ne, sai dogarai 4 sai magatakarda. Mancy ta zauna kusa da k'afar daya daga cikin tsofin ta gaishesu, su Aunty Asabe duk a ka gaigaisa. Gimbiya tace "Mai Martaba, wannan k'awata ce, ta buk'aci ganinka, duk da na san yau ba ranar ganinka bane na nemi a mana alfarma aji da me tazo" cike da izza ya gyada kai". Daya daga cikin dogarawa yace "Gyara Kintsi, matso gaba ki fadi damuwarki". Ko dar Mancy bata ji ba ta matsa kusa da Kafar Sarki, wanda gefenshi wani mutumi ne sanye da Babbar Riga. "Sunana Maryam, wanchan babban da na ne sunanshi Zaid, waccan itace auta ta sunanta Sadiya, wadannan k'annen Mijina ne na da". Sarki ya gyada kai alamun yana ji "Muna zaman lafiya da Uban yarana, tafiya yayi, yana dawowa ya min Saki Uku, yace kuma dole da yarana zan tafi, ina zani dasu Mai Martaba? Nace mishi da yara kanannene sai na tafi dasu amma ni ba zan tafi da baligai ko ina ba, banda kowa sai Yayana, ina yake so naje dasu? Wannan shekararta 15, wannan shekarunshi 25 masters ma yakeyi, ina zan kaisu? In ya sakeni me zai sa ya koresu, har yana ikirarin ya bude ido ya sake ganinsu zai iya kashesu?". Sarki yace "Wanene Mijinki? Yana gari? In yana gari a kirawo manshi yanzu, in be gari na bashi kwana biyu yazo ina kiranshi". Wani bafade yace "Kiran Sarki Doka". Mancy tace "Yana Gida, Alhaji Ali Zaki". Mutumin kusa da Sarki yace "Speaker?" Sai a sannan ta kalli mutumin, daga kai tayi tace "eh shine". Sarki yace "A aika ma Ali Zaki Sammaci, ace ina kiranshi yanzu". Baba Sani yace "Harda Matarshi wacce itace ummulabaisi, ita ce ta sa ya saketa, muma yanuwanshi ya wulakantamu, sihiri ta mishi" Sarki yace "A zo da matarshi". Suna nan zaune jugumjugum magatakarda ya fita da wani zuwa aiken Sarki. Da Sak'o ya je musu, Shafa'atu taso ya bijire ya k'i zuwa, amma kiran Sarki ba wasa ba, lallashinta yayi ta hanyar nuna mata illan rashin zuwan, rashin zuwan na iya kawo mishi cikas a Siyasar shi, kuma shi Sarki Uban kowa ne. Da k'yar ta zura wani minnirin mayafi suka bi bayan dogarai bayan tace Hudu ya kula da Annah. Bayan Zuwansu ne Alhaji Ali kunya duk ta rufeshi ganinshi gaban Sarki, ga kuma Alhaji Ibrahim Iroro, ita uwar gayyan sai da ta ji shakkun Sarki duk da tsagerancinta. Sarki ya bada umurni, a ka buk'aci Mancy da ta sake fadan abunda ta fada, kamar yanda ta fada dazun haka ta sake fada. Sarki ya tambayeshi "meye dalilinka na cewa ba zaka rik'e yaranka ba?". Alhaji Ali ya keta zufa, gaban Shafa'atu na faduwa Allah ya sa kar yace ita ce bata so. "Allah ya kara ma Imani, wallahi bana kaunar bude idona na zuba kansu, wallahi banson ganinsu, na tsanesu". Sarki yace "Aiko ba ka isa ba, wani yace ka haifesu? To ba tare da bata lokaci ba, wannan abun mai sauki ne, a Addinance, tunda Yara Baligai ne, kai ke da hakkin daukarsu, da ace yaran k'anana ne sai ta daukesu, amma wadannan yara gurinka zasu zauna Alhaji Ali". Da sauri yace "donAllah aa, zan bata ko nawa ne na kula dasu, zan dauki nauyinsu, nidai kawai su bar min gidana". Sarki yace "to ke kinji, yace zai dauki nauyinsu, amma su tafi da ke". Mancy tace "Aa Allah ya kara maka Imani, Saki Uku ya min, shari'ah ta bashi damar rik'e Baligai, Shari'ah ta hutar dani da gajaniyarsu tunda ba yara kanana ne dani ba, Allah ya ja nisan kwana, in na samu Miji aure zanyi, ya zanyi in be amince da na zauna da Yarana ba? Ya zanyi in yace na zaba ko aurenshi ko yarana? Ya zanyi in ya fasa aurena saboda Ina da Yara Baligai? Ban k'i su dinga zuwa min ziyara ba, Allah ya ja nisan takawa, ban amince ba, hankalina zaifi kwanciya in Yarana na gidan Ubansu". Sarki ya jinjina kai yace "Alhaji Ali, Yara zasu zauna a gurinka, zaka dauki nauyinsu kamar yanda duk wani Uba zaiyi, cin su, shan su, suturarsu, iliminsu, tarbiyarsu, komai, duka, kayi maganar zaka iya kashesu, zan sanya ido a kanka, in ka karya doka, doka zata taka ka, kasan kai sananne ne, kayi tunanin mai zai faru a rayuwarka ta siyasa in nace zan tona asirinka, Yara naka ne, amma Girma ya bani Iko a kanka da yaranka da duk wani rai da ke cikin garin katsina da kewaye, ina fatar ka fahimceni". Kan Alhaji Ali a k'asa ya kasa magana, sai da wani dogari ya daka mai tsawa kafin ya amsa baki na rawa "to to rankai dade". Mancy ta murmusa tace "Allah ya kara ma Girma da daukaka da daraja, nagode kwarai, ka gama min komai, Allah ya ja da rai ya kera lafiya, Ina neman alfarma a bani kudin motar zuwa Kano". Duk suka bita da ido, Asabe tace "Maryama yo ai baki gama ba, ko kin manta da Shafa'atu ce silar sakinki, ba kiyi maganar cin kashin da ta sa Yaya ya mana ba". Mancy tace "Yaya Asabe, damuwata sune 'ya'yana tunda na kwatar musu 'yancinsu banda sauran damuwa, kuma Saki dai ya riga da yayi har uku ba kome, sauran kuma nakune, Allah ya sa a dace". Mamakinta suke gabaki daya, rana daya ta rikide musu, kamar ba Maryama mai hakuri da kawaici ba. Sarki yace "a bata kudin Mota zuwa Kano" na kusa da shi yace "ai kano din mukayi, ni da su Hajia sai mu sauketa". Hajiya da kawarta sukace "aiko dai sai muyi ta tafiya". Sarki yace "to barka". Mancy ta tako har gaban Zaid da Dalo inda fuskokinsu sunyi ja saboda kuka, ta dago su gabaki daya tace "Ina Sonku, kar ku taba mantawa" Dalo na kuka tace "Mancy karki tafi ba dani ba" Mancy a girgiza kai tace "mun gama magana Sadiya, ki kula da kanki, Allah ya miki Albarka". Ta rik'e hannun Zaid da yake ta faman murzan idon Hagunshi tace "sai Idon ya kara kankancewa Zaidu? Kabar murzan idon nan, bana so" Gyada kai yayi alamun to, bubbuga kumatunshi tayi a hankali tace "Stay Strong". Zan kiraku kunji?. Ta rungumesu sosai kafin tace ku zauna. Umurninta suka bi suna kuka ita kuma ta fita daga Fadar da sauri, Zaid ya dago kannennen idonshi ya bita da kallo har ta bace ma ganinshi. Abokan tafiya suka tashi suka ma Sarki sallama suka bi bayan Mancy. Zaid ya runtse idonshi ya kalli Labiba da ta ke ta sharan hawaye yace "ki tafi Marece yayi" karfe 5 da ta duba agogonta. Majina ta ja tace "Oh Allah, ban san lokaci ya ja haka ba, zan dawo gobe, zan idasa jin labarin kaji Yayana?" Banza yayi da ita ya dauko sigari ya sa a baki ya kyasya lighter ya fara zuk'a. Jakarta ta dauka ta bude kofar sai dai me? Gani tayi har an gama Shafe, an gyara passage dinta, duk an gama gyran bulo din, suna ina har aka gyara wurin? Duk suna aikinme basu san a gyara ba, lallai ta shagala da yawa. Kofar ta bude sosai yanda Zaid zai hango Bangon gidan. Jinjina kai yayi yace "Wow, har an gyara". "Yanzu ni ta ina zan bi?" Yace "ta Gate mana ko zaki fasa bangon ne ki fita sai a sake gyarawa?". Tace "muje donAllah ka rakani" "saboda ni na shigo dake?" Ya tambayeta cike da tsageranci. "DonAllah nace Yayana" Banza yayi ya kyaleta, ganin tana k'ara bata lokaci ne ya sa ta sakin kofar ta fita tana mai tafiya sadaf sadaf kamar mai shirin Sata. Gabaki dayansu suna zaune a Bukka, nan suke zaune duk yammaci su sha Fruits, ganin wata sukayi ta wuce sutana tafiya kamar barauniya tana tafiya tana waigen baya, a tare suka mike tsaye. Hudu ne ya daka mata tsawa yace "Keeee" Sai da hanjin Labiba suka kada, chak ta tsaya ta kasa juyowa, jikinta sai rawa yake. Duk suka nufota. "Uwar wacece ke? Daga ina, barin zo in ga fuskarki" cewar Anty Shafa'atu. Labiba a tsorace ta fara juyowa taji muryanshi na cewa; "Beebs, donot turn". Fasa juyowan tayi ta tsaya tana mai kallon gate, su kuma hudun suka juya suna kallon DanMakahon dake nufosu sauri-sauri gudu-gudu". Yana zuwa daidai Labiba ya finciko hannunta ya yi gaba ita ko ta bishi a baya hannunsu rike da juna. Muryan Aunty Shafa'atu sukaji tana cewa "Yau Mun Shiga Uku Alhaji, Karuwa har cikin Gida". Hello Lovers, Vote and Comment line by line please. #1love #DM #FWASonSo #anatare #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: BABI NA GOMA1⃣0⃣ Kalmar Karuwa shine sanadiyar tsayawarta cak, duk wani lakka na jikinta ji tayi kamar an zaresu, a lokaci daya kuma jikinta ya fara rawa. Baki na rawa tace "ka tsaya, ni ba karuwa bace, wallahi ni ba ita bace" K'ara damk'e hannunta yayi ya jata har sai da suka yi daf da fita Gidan. Muryar Alhaji Zaki sukaji na cewa "Shege, Tsinanne, karuwa kake kawo man Gida ko? Kanwartaka bata isheka ba? Sai ka kawo na waje Gida?". "Ya Rabb" ta furta da k'arfi, be sake hannunta ba ya cigaba da janta, togewa tayi, ta k'i gaba ta k'i baya, gabanta ya tsaya, ya rik'o kafadunta da duka hanayenshi, Kai ya girgiza mata, da dan karfi tace "Tsine maka fa yakeyi, Shegantaka yakeyi, ko baka ki bane? mu koma in mishi bayani, mu koma na gaya mishi ni ba karuwa bace". Hannunta ya rik'e ya cigaba da janta har suka fita daga gidan baki daya, ko da suka fita Gate be sakar mata hannu ba, haushinshi taji karo na farko a rayuwarta, da kyar ta samu ta fincike hannunta daga nashi. Ta waiga ta kalli Unguwarsu da ke busy asaboda marece yayi, ta sa hannu ta shafi goshinta ta da ya danyi zufa. "Baba ba karuwa bace, abunda ya kamata kace kenan, amma ka kasa, har sai yaushe zaka cigaba da karban laifin da ba naka ba? Shiru na nufin fa ka amince da kayi abunda ba kayi ba". Hannu ya sa ya murji idonshi "Ba zaki gane ba, yin maganata bata da wani amfani". Ta katseshi ta hanyar cewa "sai kayi, kayi magana ko bata da amfani, yafi ace ka yarda da abunda bakayi ba, maganarka yafi ace ka na neman k'anwarka da lalata, ya fi ace kana kawo karuwa Gidanku". Gashin kanshi ya dan shafa kafin ya murje idanun duka biyu, sannan ya koma kallonta yana karantarta, ya fada a ranshi "ta na da gardama kuma bata ganewa". A fili yace "nayi rantsuwa na daina cewa banyi abu ba, duk wani abu da zai fito daga bakinsu, hakan ne, banda k'arfin jayayya, yau ko kisa sukace nayi, kawai hakan ne, they are right". Takaici ya sa Labiba yin gaba, da sauri bata ma da abunda zata ce mishi, tafiyarta kawai tayi, don tana ganin Zaid be ma da hankali. Bin bayanta yayi yana kwala sunan "Beebs" amma tayi burus dashi, ta ci sa'ar samun Keke Napep ta hau ta fadi sunan Anguwarsu Aunty Asee. Tsayawa yayi ya bi Keke Napep din da ido, ya juya ya kalli Gidansu, kurum yaji Garin Katsina ya mai zafi duk da ni'imtaccen iskar da ke bosowa, garin da alamun hadari. Ya buga tsaki da ya ciro sigari ya kyasta ya koma Gida, suna nan tsaye kamar yanda ya barsu, maganganu suke wanda yake da tabbacin La'antarshi sukeyi, straight hanyar BQ yayi, yana jin Baba na faman kwala mai kira amma yayi burus da shi ya wuce dakinshi. Yana shiga Daki ya sa mukulli ya rufe ya fada kan Gado yana mai tunanin Labiba. Labiba ma da tunanin Zaidu ta isa Gidansu Aunty Aseey, jikinta duk a mace,ta shiga Gidan da Sallama su Ameera su ka taso don yi mata oyoyo, da yak'e ta taryesu, ta karasa ciki ta gaida Hajiar Aunty Aseey da 'yan Gidan. Aunty Aseey tace "Labiba ya makaranta?" Dan jim tayi, yau ko hanyar Makaranta bata bi ba,amma sai tayi karya tace "Alhamdulilah" Hajiyar su Aunty Aseey tace "ya mukaji da wannan abu? Bango ya Fadi" Labiba tace "eh wallahi Mama, an ma gyara". Aunty Aseey tace "Kin biya Gidan ne?" Da sauri tace "Aa, nasan dai angama saboda marece yayi, yaya kuwa yace aikin be da wuya". Aunty Aseey tace "haka ne, tashi ki ci Abinci". Mik'ewa Labiba tayi tana mai jin haushin kanta, wai itace yau da k'arya har so 2, Allah ka yafe min". Gab da Maghrib suka koma Gida a Keke Napep, sun tarar da an gama gyaran Bangon, Labiba ta share tsakar Gidan ta shiga kitchen don daura musu taliya, bayan sunyi Sallahr Maghrib, suka ci Abincin, gabaki dayan su suke zaune kan tabarma kasancewar ba Wuta. Hadari ya taso, iska mai karfi ya taso, da sauri suka nade shimfidarsu, suka shige dakunansu. Baban Amira yace "Oh Allah ka ci da ginin bangon nan kar ya rushe" Anty Aseeyah tace "ai sai yanda ta yiwuwu dai kawai" Jugum-jugum suka zauna suna sauraron ruwan Sama, sai ga ruwa kam da bakin kwarya, suna jin ginin ya sake faduwa wurin da aka gyara, ta window sukayi ta lek'e suna jimami. K'arfe har k'arfe 10 saura ruwa bai tsaya ba, duk sunyi bacci banda Labiba da ke daki tana waya da AbuSideeq inda yake tambayanta dalilin rashin zuwanta makaranta. Karya tayi Kamar yanda ta gaya ma Aisha da sukayi waya dazun haka ta gaya mishi, bata lafiya. Sannu ya mata ya mata sallama da fatan samun sauk'i. Ruwan saman nan na kawo ma duk wani bawa mai rai nutsuwa, saboda yanda yake sauka cikin wani yanayi mai sa Nishadi. Jugum tayi zaune tana latsar wayarta kadan ne babu cikin karfe 10. Me ya keyi? Bacci? Ya koyi Sallahn Isha'i? Ko ma ya ci abinci? Ko ya suka k'are dazun da Babanshi? "Ya Rabb" ta fada da ta tuna yanda sukayi dazun, shaf ta manta da wani fushin da tayi dashi. Haka kurum Zuciyarta ke k'yank'yasa mata Zaid cikin daren nan, Son ganinshi take son yi, son sanin halin da yake ciki takeyi, kawai tana son ganinshi da daren nan, har ya kai ga ta na ji kamar ba zata iya bacci ba in har bata saka shi a Idanuwanta ba. Juyi ta koma yi kan Katifarta, da duk numfashin da ke sauka daga kirjinta tana mai hasassho halin da Zaid yake ciki a wannan Dak'ikan. Wuf ta tashi kamar an tsikareta, ta yanke hukuncin da bata san ko ya kamata tayi abunda take shirin yi ba. Dakin DANMAKAHO zata. Hijabinta ta dauko ta daura kan Rigar baccinta ta fita sadaf sadaf tayi hanyar bangon da zai sadata da Gidansu DanMakaho kamar barauniya. Chogewa tayi ta tsaya kuma tana wani tunani. Bai ka mata ba ko kadan ace taje Dakinshi a wannan daren, ba ta san halin da yake ciki ba, ba ta san mai zai mata ba, it is wrong, so wrong, daya daga cikin zuciyarta na cewa "Dont Labiba, Dont". Dayar ko Ingizata takeyi. Zai rantse be taba jin wannan yanayin ba, zai rantse bai taba zama yayi tunanin wata haka ba, tunanin wata bai taba lik'ewa a k'wak'walshi ba, tun dazun ya ke tunaninta, yanda ranta ya baci ne ya dameshi, duk abubuwan da yake gaya mata ko yake yi mata bata taba fushi dashi ba, ba ya so ya chanzata, ba ya son ya k'ure hakurinta, tunda har ta shiga rayuwarshi, gobe InshaAllah zai bata hakuri. Ji yayi kamar ana taba k'ofarshi, duk da bai sanya sakata ba amma kofar datse take,ba wanda ya damu da dakinshi, wa zai zo yanzu? ko dai iskan ruwan da akeyi ne yake hurowa? To ai Kofar datse take, kuma kofar irin ta manyan wood din nan ne, iska ba zata budeshi ba, da sauri ya tashi ya bude k'ofar. A kallo na farko ya zata Dalo ce, sai da ya kalleta sosai ya gano Labiba ce, a cikin sakwan kadan ya finciko hannunta ya jawota cikin dakin ya rufe kofar kamar mai tsoron kar wani ya gansu. Hannu ya sa ya murji idonshi, tana tsaye tana farfar da ido tana rawan sanyi, Hijab dinta duk ya jik'e. "Bibbs ba kya jin magana meyasa ba kya ji? Me kika zo yi nan?". Murmushi tayi tace "Bango ya sake faduwa". Ba wannan yake sonji ba "how could you be so reckless? Don me zaki dinga zuwa min daki? Ba kya tsorona? Ba kya tsoron ina iya danneki cikin daren nan? Baki ga tsinuwan mahaifi a kaina ba? Ba ki san mutuncin mutum na zubewa ba idan aka ganshi da ni ba? Ba ki san dazun da sun ganki ba sai sun bata miki suna ba? Don me zaki dinga zuwa inda nake? Da daddare, wai ke baki san ni Namiji bane of 28years? Baki san me ke faruwa ba in Namiji da Mace suka kebe? Are you not worried about yourself? About your Family? About Mami? Kin manta Gidanku baa karatun boko amma mahaifinki ya yarda ya turo ki karatu saboda ya yarda dake? Ya yarda zaki kama mutuncin kanki, ki kare martaban gidanku, amma zuwa dakin Namiji mutunci ne? In yayanki ya kamaki ya zaiji?". Kyafta idanuwa tayi, tace "Ya Zaid, na yarda dakai, ba zaka cutar dani ba" ba tare da ya tanka YaZaid din da ta kirashi dashi ba yace "baki sani ba Bibbs, baki san ko zan iya cutar dake ba ko ba zan iya ba, World fa nake sha...Uhm Wiwi". "Dagaske na san ba zaka cutar dani ba, ba zaka min abunda zakaji haushi ba in anyi ma Dalo". DanMakaho ya tsura mata ido kafin yace "DonAllah DonAnnabi me kike so, its late, ki koma Gida, gobe zamuyi magana". Kai ta girgiza tare da zama kan kujerar dakin tace "ni bana jin bacci, ba kuma abinda zanyi, so yafi ka idasa bani labarin". Idonshi ya murza sosai kafin ya zauna yana harararta, ita ko sai murmushi take sakar mai. Sarki ya mana Nasiha kuma yace in muna da wata damuwa da Babanmu ko Matarshi muzo mu gaya mai, sarki ya sallame mu. Baba da Aunty Shafa suka fita daga fada ransu a bace, Baba Sani ya dauke mu ya maidamu Gida nida Dalo bayan ya mana nasiha sosai ya bamu hakuri. Daga wannan rana komai ya chanza mana Beebs. Da muka Shiga Gida mun tarar da Baba, Aunty Shafa, Hudu da Annah zaune a Parlo, jikinmu yayi sanyi yanda mukaga suna kallonmu, jan hannun Dalo nayi zan sadata da Dakinta amma na jiyo Ihun Baba. Danubanku kuzo nan. Beebs, bamu saba ba, Babanmu baya zaginmu,Babanmu ba ya daga mana murya, k'ara matse hannunta nayi muka shiga Parlon sosai. A gefe muka dan rakube, ran Baba bace yace "yanzu ni Maryama ta tona ma asiri ko DanMakaho? Kuna ganin uwarku ta kaini k'ara Gidan Sarki, bayan duk abubuwan da na mata, duk hallacin da na mata ta rasa da me zata saka man sai ta kaini Kara a Fadar Sarki? Ni Alhaji Ali Zaki?". Mu dai ba muce komai ba Baba ya cigaba da cewa "to tunda Maita ta hanaku bin Uwarku, ku zauna, amma ba ruwanka Zaid da cikin Gidana, Boysquarter zaka koma, ban yarda da kai ba, ina da Diya Mace, kar kazo ka keta mata haddi, wani irin yammmm naji a jikina, na dago kai na kalli Babana, wanda banda tabbacin ko shine ko ba shi bane,anya Baba na ne Mahaifi? Me ji dani? Me yin duk wani abunda nakeso?". Ya cigaba "Ke Sadiya, Annah tace dakinki take so, so ki koma BQ tare da Yayanki, ko ki koma gunsu Raliya masu dafa Abinci". Dalo ta dago baki zatayi magana sai kawai ta fashe da kuka. Ni ko na fara girgiza kai alamun rashin yarda nace Baba ta ya Dalo zata koma Boysquaters? Dakuna nawane a cikin Gidan nan da har sai ta koma BQ? Haba Baba kar ka juya mana baya". Hayyayakowa yayi "DanUbanka DanMakaho ina fada kana fada? Rashin da'a zaka min? Danubanka nace ba ku zama min cikin Gida, ku koma BQ, bana son ganinku, ina laifi ma da na barku a BQ din". Zaid ya tashi inda yake rak'ube yace "Baba, wallahi ba zata yi zaman BQ ba, in ka matsa yanzu sai naje Gidan Sarki na gaya mishi " Baba ya tunzura, danubanka ni zaka tona ma Asiri? Kaje ka gaya mishi to, tsinanne watsattse, da sauri na tashi hankalina a tashe ban ma ganin gabana na dinga jefa kafata kasa na fita daga Parlon. Aunty Shafa tace "barshi Alhaji, kaga dai abunda Sarki yace, kar a kama mu da saba ma Umurnin sarki, Baba ya amince, Anty Shafa tace ke Sadiya ki koma dakin kusa da naki, naki Annah ke so, Sadiya bata da rigima duk da ta san Dakin da ake so ta zauna ba komai ciki daga Gado sai toilet amma na ta har Tv akwai bayan decoration din dakin da akayi da pink and purple color. Kai ta gyada alamun ta amince, Anty Shafa ta koreta cewar zasuyi magana ta zauna musu, sumsum ta mik'e ta wuce dakin da aka ce ta koma. Ni kinsan abun bai dameni ba zaman boysquaters don na san in 2days zan koma makaranta so Dalo ma ne nake jiye ma zaman bakincikin da zatayi. Duk ranar wayar Mancy a kashe yake, na kirata yafi so dari naji ya take, me take ciki, karamin hauka na kusa yi. A waje na zauna bayan Sallahr Maghrib, ga yunwa ina ji bana ma son shiga Gida balle naga kayan bacin rai, kawai na wuce gunsu Raliya masu dafa Abincin Unguwa, aiko na samu Jollof din Shinkafa a wurinta, ta na tausata da bani baki kan mu jure duk wani abun da zamu gani daga yanzu. Washegari da safe na tashi na tafi cikin Gida don ganin yanda Dalo ta tashi, kallo daya na mata na lura da tsantsar ramar da tayi na kwana daya, tausayinta ya kamani, na karasa gunta ta dago da murmushi mai kama da yak'e. "Ya Zaid, har yanzu ba ka samu Mancy din ba? Wayarta a kashe" ta fada cike da karaya, ka sa amsata nayi, na durkusa daidai tsawonta nace "ba kiyi breakfast ba, tashi mu shiga kitchen na hada mana kalaci". A Gidanmu kowa ke hada breakfast dinshi da kanshi, saboda rarrabuwan raayi, in kuma k'osai da koko din Raliya kake son ci sai kaje baya kaci. Na rik'o hannunta muka shiga Kitchen, muka kalli juna cike da mamaki, ba wai ba komai cikin kitchen din ba, aa sai ganin babu abubuwa da yawa, trolley din kayan tea, ba komai, ba kwai ba komai cikin fridge dana duba, yanda na lura duk wani abunda zaa sarrafa a sa a baki babu, da mamaki muka kalli juna, yaushe akayi wannan kayekayen? Dalo tace "maybe suna a Store" da sauri na karasa store na jishi a gark'ame. Da karfi na kwada ma Raliya kira, sai ko gata nan da saurinta, tnace wai ina kayan Abincin gidan nan? Ta duba kitchen din da idonta tace "toufa, kamar an kwashe komai, na jinjina kai na san aikin matar chan ce, nace Raliya Yunwa mukeji, tace ai DanMakaho akwai Kalaci a kitchen din baya, bari na kawo muku. Parlo muka zauna muka jira Raliya ta kawo mana Breakfast. Dadi kosai da koko dinta, sosai mukaci don jiya rabonmu da abinci tun rana. Muna cikin breakfast sai ga Aunty Shafa'atu ta shigo da nightgown jikinta. Da mamaki ta kallemu tace "ina kuka samu Abincin nan?" Daga kai nayi na kalleta nace "meye amfanin kwashe kayan abincin kitchen da kikayi? So kikayi kiyi starving dinmu da yunwa? Ko so kikayi ulcer ma ta kama mu? A gidan ubanmu? To ba zai yiwu ba, wallahi baki isa ki horar damu yunwa ba a Gidan Ubanmu". Fuuu ta wuce ta banka dakin da Baba ke ciki, ko bacci yake ko zaune yake oho, amma da karfi naji tana cewa "ni yanzu a sallami su Raliya masu Abincin Gandu". Baba yayi dan jim kafin yace"Shafata, Abinci sukeyi wanda ake rabama yan Unguwa, da yawa da nan gidan sukayi relying, in aka Sallamesu wa zai dafa Abinci har a ba Makwafta? Kicinkicin tayi da fuskarta tace "nidai Alhajina kana shagwaba talakawa, in ka dinga basu abinci kullum ta ina zasu samu zuciyan neman na kansu? Zuciyarsu bushe take, su a ganinsu sun samu bati ni dai kawai ka sallame su Raliya, daga yau an gama Abincin Badawa". Da sauri Baba yace "kuma fa? Hakane mutane son banza garesu, daga yau ba zaa k'ara Abincin badawa ba, ko wani shege ya tashi ya nemi na kanshi, ai maza a kira man su Raliyan". Well ina gaya miki Beebs, baba ya ma su Raliya da masu taimaka mata wurin dafa Abinci, Sallaman Wulakanci Aunty Shafa na tunzurashi kamar wani robot take control dinshi, ni kuma da na ga haka, nace su jirani naje Bank, da sauri na dauki Motata na nufi Bank, na zaro dubu 200 na basu nace su ja jari, godia suka dinga min kamar zasu min sujadda, suka dinga min addua suna mana fatan Allah ya karemu daga sharrin Matar Uba, Raliya da yake zata girma Mancy, ta dinga min Nasiha da kuma na kula da Kanwata, suka min Sallama suka kwashe kayayyakinsu. Ashe Hudu ya ga lokacin da na mik'a ma Raliya Kudi, ashe ya je ya barar ma Yayarshi, yayarshi ta tada ma Baba rigima da haka yake barina ina kashe kudi? Be san kudi na bata yaro ba? Ita gaskia ba zata yarda ba?. Hahaha Labiba Babana ya kira Manager ya sashi freezing account dina, bayan ya kwace makulan Motanshi, da wayar hannuna a cewarshi da kudinshi na siya, God, to ban ma dai yi mamaki ba sai da bayan kwana biyu na samu Baba game da son komawa Makaranta. Nan ne Baba ya min Wulakanci gaban Matarshi da Diyarta da k'anenta. Da farko banza yayi dani ya k'yale sai da na sake magana nace "Baba lokacin da ya kamata na koma Makaranta yayi, jarabawa zaa fara da sati 2, zan koma na fara shiri". Baba ya dan kallo Anty Shafa, da ido ta mishi magana, haba sai baba ya fara Spark, wani irin Makaranta, Kai dan iska ina sane da duk wata burobar da kake a k'asar Ingila ba, Shekarar 6 a chan amma ka kasa hado degree, sai dai kaje ka shek'e ayarka da yanmata, ka dawo Nigeria ka kuma koma London san da kaga dama, to ba zaiyiwu ba wallahi, ba zai taba yiwuwa ba". Nan ne ya kasheni da Mamaki, baki na nauyi nace "Baba, wani Degree kake magana? Ina Degree din da na amsa ranar da kukaje London kai da Mancy da Dalo? Baba har fa Graduation Dinner sai da kukaje, ko kuma ka manta na riga da nayi joining Masters, befi min Wata daya nagama ba? Yanzu da na koma nayi Exams fa na gama". Baba ya dinga zare ido "kai ni ban san wannan ba, ni sisi na ba zan k'ara kashewa a kanka ba DanMakaho" hankalina ya tashi amma na daure nace "kayi hakuri babana, ka bude min account dina, akwai kudi na, ni zan dauki nauyin kaina, i need to go back Baba". Tsawa ya daka min yace "Bazan ba, nace bazan ba, na cire kudadden Account dinka tas, London kuma ba zaka kara zuwa ba". Guiwowina na dire a kasa ina kuka "Baba ka min rai donAllah, kar ka hanani komawa, Baba in wannan shine abu na karshe da zaka min a duniya donAllah ka maidani London, don Girman Allah baba". Kafa ya sa ya shure ni sai da na k'ume, a kausashe yace "bazan kai ka ba, naira daya ta gama kuka a kanku". Shafa'atu tace "kaima Alhaji ka rabu dashi, tunda shi ya fi so a yi ta magana daya". Raina ya baci ban san sanda nayi wani kukan kura ba na chakumo wuyanta, na mak'ureta kamar zan kasheta, Hudu da Baba suka yo kaina, suka rufe ni da duka amma ko gezau banyi ba, na cigaba da matse hannuna a wuyanta ita ko sai k'akarin mutuwa take. Dalo ta fito daga daki da gudu da ta ga hayaniya tayi yawa, ni ko wani karfi ya zo min na ingiza Baba da Hudu, na hau dukkan Aunty Shafa'atu, Dalo na kuka tana Yaya donAllah ka rabu da ita, ina sam ban ji ta ba, ita ko a galabaice take kukan wahala, Hudu ya rikoni ta baya, Baba ya dunkula hannunshi ya dinga kai min naushi ko ta ina kamar zararre, itama Aunty Shafar ta mik'e ta nufoni tana dukana Dalo ta rike mata hannu ta wurgar da ita. Kamar daga Sama mukaji ana Sallami, muryar tsohuwa ce ke cewa "Ki kori Mahaifiyarsu ki juya kan ubansu yanzu ku mishi rubdugu? To wallahi baki isa ba, sai na ci uwarki, yau sai na ga Bokanki, daga nan har Pilatu sai na ga Uban da ya tsaya miki a Najeria". Dalo ta dago kai ta kalli Tsohuwar da ta ke niyar cin danmara, a wahalce tace ; NENE.. Ai Nene ba ta bi kan dalo ba ta shiga cikin fadar nan ta finciko Shafaatu ta kaita k'asa, ta dinga kilarta kamar Allah ya aikota, Baba yazo shiga tsakani ta sa hannu ta tsokale mishi ido, ganin haka na maida hankalina kan Hudu, ni da Nene muka kaisu k'asa ina kilar kani Nene na kilar Yayar, baba hankali tashe ya wawuro wayarshi ya latso kiran Police Station. Wai tsohuwa Nenen nan sai da ta ma Shafa habo kafin ta tureta, ta rik'o hannuna da na Dalo tayi gaba, tana maida numfashi, tana haki tana cewa "ni ai ko bokon Saude sai da ya tantance Aminene Mamman, zaki zo ki shiga tsakanin da Da Mahaifi, shegia K'abilar banza". Muna jin Aunty Shafa'atu na cewa "wacece wannan Alhaji?" Kafin Baba ya bata amsa Nene tayi karaf tace "Uwarki ce, kaii a'a ni ban haifi Azzaluma ba, Sunana Aminene Mamman kije kiyi tambaya kaina". A tsakar Gida muka tsaya ta kalleni rai bace tace "kai danubanka sai kayi tsaye suyi maka taron dangi?" Ta kalli Dalo tace "ke kuma sakara kin tsaya kin bare baki kamar famfo kina ta kuka ana dukan Yayanki, baki dauko wuka ki watsa taron?" Baki bude nake kallonta na san Matar kamar zararra take amma me take nufi? Nace Nene fa harda Baba fa, kai dallah arr, ni sai na bugeshi tunda ni ba ubana bane, sai na mushi mugun bugu tunda shi sakarai ne shanyayye". Kai ni ina Gida Raliya ta kawo min zance abunda ya faru, to wai danuban Maryaama tana da wadda ta fini ne duk garin Katsina, ashe cin kashin da Ali ya mata kenan? Bayan ya wulakantata harda bugu? Ni ina me baa zo an sanar dani ba? Wato ni hoto ce, banda wata amfani". Zaid ya dafe kai, matar nan tana son saka mishi pressure da yamman nan, ni yanzu kiyi hakuri Nene, wallahi ban ma cikin hayyacina cikin yan kwanankin nan". Kai dallah ar raggon maza, ba ka biyo masu Sunan ba, Zaidu Bawan Allah jarumi ne". Labiba ta share hawayenta amma yanzu murmushi na dauke a fuskarta tace "Wacece wannan? Kakarku ce?". DanMakaho ya murmusa shima yace "Ba dangin Iya bara ne Uba, wai kawar Mancy ce, amma fa tsohuwa ce kuma a haife ta haifi Mancy". Labiba da mamaki tace "Kawa kuma?" Yace "Eh kinsan Mancy na yawan zuwa Hajj da Umrah, to a chan suka hadu, dakinsu daya a cewarta Mancy ta taimaketa sosai da hidima a Makka shiyasa suke kawance, to tunda suka dawo suke zumunci ko muje ko tazo, tsohuwa ce amma bata da hakuri, karfinta kamar na garada Goma". Sosai Labiba ke daria. Ya cigaba Kafin wani yayi magana sai jin siren din Motan yansanda mukayi. Baba ya fito Shafa'atu na biye dashi a baya, ke wai Baba ya shigo da YanSandan nan yace a tafi damu a rufe mu bayan karta harda Nenen. Nene kuwa tayi kukan kura tace "duk uban da ya tabani sai naci kutumar ubanshi, yara ba ku sanni ba" ta zaro wayarta a purse ta mik'o min tace "latso min Zaidu Bawan Allah, kai ba ma shi zaka kira ba, latso min Habibu Lema, in na tuna da kyau harda shi yayi silarka ka zama abin da ka zama a yau". "Yo ku kadai kuka san manya? Nima dana Habibu ai suke da gwamnati, kuma shi ba tsaranka bane, kai soko maza kira man shi" ko mai Baba yayi tuna oho sai cewa yayi "ku bar tsohuwan, ku tafi dashi ku kulle, ku lallasa min shi". Haka yan Sandan nan suka kamani kamar barawo, Dalo ta fashe da kuka. Nene tace "oho, nidai ba uban da ya isa ya kulleni, shi da ka isa dashi ka sa su tafi dashi, ke kuma ki ma mutane shiru komai kuka, kai kuma Danka ne, ka barshi a chan bayan karta kar Allah ya sa ka firdoshi, ka barshi chan ya mutu Sakarai shanyayye, ke kuma a juri zuwa rafi". Ta fizgo wayarta daga hannuna ta wuce fuuu kamar zata tashi sama. Ba su jira wata ba suka tusa k'eyata suka sakani a bayan motarsu suka tafi dani, hankalina tashe, yau nine haka a wulakance, ba wani wata wata a ka wurgani bayan karta. Wani zauri ya bugi hancina, ga k'uda, ga k'azanta daga wani bangare, hawayen bakinciki suka soma kwaranyo min, yau ni ni ne a Cell? Yau ni ne a wulakance, meyasa na ma dawo hutu? Meyasa nake da rabon ganin wanan rana? Kuka nake sosai ban damu da kallon da yan bayan kartan ke bina dashi ba, ban damu ba. A sannu na yi ta hasasso rayuwarmu a da, da rayuwarmu a yanzu, komai ya chanza Alkalamin k'addararmu tayi zanen da ba zata kankaru ba, sosai nake kuka, na dade kuma ina kukan, bansan minti ko awan da dauka ba ina kuka. "DanMakaho" naji an fada Da sauri na dago kai don ganin me min kiran nan wanda tabbas ya sanni tunda ya kirani da sunan da yan Unguwa kadai ke ce min. Na sanshi, ina ganinshi a Unguwa, Dan shaye-shayene, ya sha rokona kudin da zai ci abinci duk da na san karya ne shaye-shaye zaiyi dadu ban taba hanashi ba, da shi da yan bencin Eskaley na sha raba musu naira dubu dubu. Da kyar na ambaci sunashi "Haruna, me kakeyi a nan?" Haruna ya danyi daria yace ai ni nan bana sati 2 k'warara banzo nan ba, kai ne dai zan tambaya me kake anan. Ban iya ce mishi komai ba na duk'ar da kaina. Gaskia DanMakaho Babanku ya kwafsa, ji yanda ake ganin mutuncinshi amma wa shine zai yi wannan kwafsin? Harda dukan Hajia Mancy gaban kowa, Kai ya mugun kwafsawa. Kamar jira nake na fashe da wani sabon kukan, be lallasheni ba, bai hanani ba, bai kuma tafi ya barni ba". Sai da na tsagaita kuka na kafin na dago kai na ga hannunshi a mik'e alamun wani abu yake so na karba daga hannun. World kenan, ka sha shi, wallahi ka sha shi damuwar da kake ciki zai bace bat, ka dan ta6a world ba ka da wata matsala. Kallo daya na ma kullin garin na kauda kai. Zama yayi kusa dani Kagane ko ka sha taimaka min, ka sha fiddo ni cikin damuwa da yanayi, in ka bani kudi, kaga abunda nake siya nan, dagaske in na sha shi wallahi bana da wata sauran damuwa, wallahi World duniya ne, duk yanda kake cikin damuwa, bakinciki, kuncin rayuwa, da ka zuk'a so daya damuwar zata kwaranye, zuk'a ta biyu kuma zakaji kanka a kan gajimare, ka gwada zuk'a daya, da kanka zaka nemi k'ari, in kuma ka zuk'a damuwarka bata gushe ba kayi kan duk abunda kake so". Runtse Ido na nayi, na yarda gajeran tunani gareni, shaidan ya buga min ganga, a cikin Cell dinnan na zubdar da duk wani tarbiyan da Mancy ta min shekara 25, Wallahi Beebs da na bude World na fara zuk'a ta hanci, sai da na zukeshi tass, Haruna ya so ya kwace amma na hanashi, burina damuwa na ta kau". Ido na a runtse na ji ni a wani irin yanayin da ban taba shiga ba, wani yanayi mai wuyar fasali, wani yanayin da ban taba saninshi ba. Wanda suka dade a harkar da wuya su ja World fiye da biyar, ni ko na ja shi ya fi so 20, mamaki na Haruna keyi yanda ya ga nayi bagas a k'asa ido na a runtse in rausaya da kaina hagu in rausaya da shi dama. Haruna na tsoron kar na haukace, don in yayi yawa yana sawa a zare, sunana ya fara kira DanMakaho DanMakaho shiru ba amsa ido na runste A kira na uku ne na bude ido tare da sakin wani irin murmushi. Cikin jin dadi haruna yayi wani juyi, tare da jinjina hanayenshi guda biyu alamun ya sara min gami da cewa; MAANNNKAAAASSSSS....... Yes Guys your one and Only Nene is here Who's happy? Vote and comment line by line please #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Sha Daya1⃣1⃣ (MANKAS II) (Note: wannan Events din ya faru ne Bayan dawowan Nene daga London lokacin da Nasiban Rafeeq ta Haihu. Fahimt?) A kan idonta a ka wuce dashi cikin motar yan sanda, ranta a bace, sai dai ya ta iya? Fuuu ta shige bayan motar da aka kawota, ko magana bata iya mishi ba ta wuce Gidan Lema. "Banda Sakarai shanyayye, wa ke tura yaronshi police station?" Haka tayi ta fadi har ta shiga cikin Gidan Lema, Mami ta mata sannu da zuwa, Nene tace "ke yau ni naga k'awar Saude". Sai da Mami ta dafe k'irji tace "a ina Nene?". "Wannan Kishiyar Maryaman" "Nene dagaske an Saki Hajia Maryam?" "Ke ina baki kina k'in karba, Makira ce Matar nan, wai ke in gaya miki Yaro na samu bakin gate ya bani labarin duk abunda aka ma Maryama, ke fa da naje samu nayi sun ma Takwaran Zaidu Bawan Allah Rubdugu, aiko na shigar mai, na tsokale wa Uban Ido, ita kuma na lallasata". Mami tace "yanzu Nene fitanki har kinyi Dambe?" Nene tace "aa fa ni fa ba dambe nayi ba, bugun tsiya na mata, ke dallah ina kaiki. Ke shaida ce irin So din da Alhaji Zaki yake ma Matarshi Maryama da Yaranshi, kina zuwa Gidan Kema, kinga kyakyawar Alak'a tsakaninsu, ke kawai sai rana daya, ya auri tsohuwar Matarshi, ya zabure ya ma Matarshi duka gaban 'yan anguwa, ya cika mata saki 3 ya sa aka kwashe mata kaya, ya zo ya tsani yaranshi, ya shigo da Agola su biyu, ya fifita su fiye da yaran cikinshi, me zakice? Me kike ganin ya faru?" Mami ta danyi jim kafin tace "ta na iya yiwuwa Chanji ne kawai, ko dokin sabon auren da yayi ne". Hannu Nene ta sa a kai dauke da takaici tace "ke wai bakiji me nace ba, don yana dokin aure sainya juya ma Yaran cikinsa ba? Ya kike magana ne kamar ba ki san aikin asiri ba, ke da Saude ta rafka muku asiri ke da Mijinki aka rabaku tsawon shekaru?. Mami tace "kawai banson zargin Asirin ne, tunda bamu da hujjah". Nene tace "wai ya kike magana? In ba asiri ba meye? Hujja ya wuce wanda na karanto maki, ke wai don uwar yaron nan da ni zai sa a kulle a pirisin?". Mami ta zaro Ido, tace ya akayi? "Aa wai mun bugar mishi Mata, ya kira YanSanda wai su tafi dani da Zaidu Bawan Allah, nace mishi ya kira min Habibu, da yaga uwar bari, sai cewa yayi a barni amma a tafi da Dan, yanzu dan na chan kulle, ki latso min Mijinki". Sai ko gasu shigo tare da Uncle Zaid. Nene ko ta tarbesu "Oyoyo Sannu da zuwanku" Uncle Zaid ya murmusa yace "Nenemu ni da Seebi". Jawo hannunshi tayi ta zaunar dashi tace "wai Zaidu Bawan Allah, ina kawata Hajia Maryama da ke Tudun Matawalle wanda ka taba kaini Gidanta?" Cikin fahimtarta yace "Matar Speaker Ali Zaki?". Tafi tayi cikin jin dadi tace "itafa" Uncle Zaid da neman k'arin bayani yace "me ya sameta?". Nene tace "to asiri kishiyarta ta ma Mijinta ya saketa saki 3 bayan ya lakada mata na jaki, ya kuma juya ma yaran Baya, kai wai jiya suka kori su Raliya masu abincin da na kai ma Maryama, aiko Raliya tazo ta gaya min duk abunda ke faruwa, ni ko na wanke kafa na sa Sabitu ya kaini Gidan. Kai wai daga isa na naga sun saka takwaranka Zaidu a tsakiya suba ta jibgarshi, ni ko naci dammarata nayi kansu". Kai wai sai ga 'yan Sanda sunzo wai tafiya da mu, wai zasu samu bayan Karta, wai mun bigi Matarshi, niko nace wallahi bai isa ba, sai dai a tafi da danshi ba dai ni ba, kuma nace a latso min Habibu ai ba su kadai bane Manya". Daddyn Rafeeq ya jinjina kai yace "Gaskia da Ali Zaki yayi Babban kuskusre da yayi gigin Kulleki" Nene ta yi darian jin dadi tace "yo shiyasa na bashi tsoro wallahi, shegen ya tsorata, ai gaba da gabanta". Uncle Zaid ya girgiza kai yace "wai Nenenmu ni da Seebi yanzu dambe kikayi? wai ba ma na hanaki Shiga abunda bai shafeki ba?". Gimtsa baki tayi tace "yi hakuri Mamman". Mami tayi daria tace "yau Zaidu Bawan Allahn zaa watse?". "Yo ai naga Zaidu Bawan Allah ko meye nama Hajia Maryama ban fadi ba, matar da ta soni kamar Uwarta, ke Aisha da muke Makka wani ciwo da nayi, wallahi ita ke hidima dani, duk nisan Samanmu sai ta sauki ta siya min abinci da magani, ta rirrikeni in zan fadi, ni ko gani da raki da fada, yanda kika san diyata haka nake watseta , duk tsarabar da na maku ita ke zabar maku kuma so dayawa ita ke biyan kudin, karamcin Maryama mara misaltuwa ne, to yanzu don na taimaka ma yaranta sai ace nayi shiga sharo ba shanu?". Duk suka jinjina kai, tace "Alhaji Habibu DonAllah kayi man taimako, kaje polis station ka sa a firdo Takwaran Zaidu Bawan Allah, kuje kuyi belinshi, wallahi dan gata ne, be saba irin rayuwar nan ba". Daddyn Feeq yace "InshaAllah Nene, bari inyi waya inji yana a wani Police Station ne". Ba jimawa yace "yana Police Station din Tudun Matawalle, barin je inji". Nene tayi wuf tace "muje". Gardama da ita bata lokacine, fits sukayi su Uku, Nene da Alhaji Habibu da kuma Zaid BawanAllah. Ko da suka isa Police Station din tuni DPO ya fito ya tarbesu, ba bata Lokaci Alhaji Habib ya buk'aci a saki dan Gidan Alhaji Ali Zaki da aka kawo dazun". Jim DPO yayi kafin yace "anya kuwa Alhaji? Alhaji Zaki yace mu rik'eshi kar mu sake mu ba kowa Bail dinshi, kayi hakuri Sir yaron kangararre ne, Mahaifinshi ke da rights akan shi kuma yace a hukuntashi". Nan Nene ta fara surfa musu ruwan Bala'i wanda Su Haruna da ke bayan Karta sun ji banda Zaid da ya dade a duniyar da World ta kaishi. Da k'yar Uncle Zaid ya firda Nene daga police station din don da har ta fara maganar dukan DPO. Daga Station basu wuce ko ina ba sai Gidan Alhaji Zaki, iso aka musu har parlo, tare da hamshak'iyar suka fito, suna ganin Nene Shafaatu ta sha mur, riko hannunta Alhaji Zaki yayi suka karasa cikinParlon, hannu ya ba Zaid da Daddyn Feeq sukayi Musabaha". Alhaji Habibu yace "Alhaji Ali, Nene ta zo mana da wata magana wai ka sanya an kulle Zaid, munje muyi bailing dinshi sunje ba bail, Alhaji komai yayi zafi maganinshi Allah, kayi hakuri ka firdoshi". Kallon Hajia Shafa yayi ta banka mishi harara, lokaci daya ya fara bala'i "Haba Alhaji Lema, wai ni ina ruwanku dani da iyalina? Shin Zaid din ba yaro na bane? Ina ruwanku ko yanka shi zanyi? DonAllah ina ganin Girmanka, ka tsaya a nan, ba zan dauki shiga sharo ba shanu ba". Nene ta katseshi ta hanyar cewa "Kai dallah sakarai rufa ma wa mutane baki, ka na zaune sai juya ka ake kamar Masa, kai Asirin ma sai fa sakarai take ma tasiri, shiyasa da ta kamaka tayi maka mugun kamu, to wallahi ka natsu kayi wa kanka kanka fada". Ta matsa kusa da Shafa'atu ta sake mata wani zazzafan Rankwashi wanda ya sanyata ihu, a tare Alhaji Zaki da Zaid Lema suka tashi, Zaid yayi kan Nene, Zaid ya janyeta yana "Haba Nene". "Ni Zaidu wallahi ban san harka da Stupid, nidai a Sako min Amanar da Allah ya bani". Shafa'atu wanda rankwashin ya shigeta ta fara kuka "wallahi Alhajina sai ka sakeni, ba zan iya ba, ace har Gidana wata tsohuwa zata dinga bina tana duka na? Kamar yar yarinya? Ni wallahi ba zan iya ba". Hankalin Ali Zaki ya tashi da sauri yace "Alhaji Habib Lema, ba gaya ma ina mugun jin kunyarka, ku fitar min daga Gida, ku fita daga harkan Gidana, wallahi in Mamarka ta sake taba Matata wallahi ba zamu kwashe da kyau ba". Aiko ya tunsura Nene tace "Allah ya tsine maka in har ka bari muka kwashe da kyau, Shege, mara hankali". Zaid ya ja hannunta tayi ta fizgewa, da k'yar ya iya fitar da Nene daga Parlon, ga Nene da karfi. "Alhaji Habib Lema, ka ja mata kunne, ta fita daga harkan Gidana, ko kuma hukuma ta shiga tsakaninmu, ai mata Iyaka da Gidana". Daddyn Feeq be iya magana ba sai dai fitan da yayi a zucciye. A Mota yace "Don Girman Allah Nene ki fita daga harkan Gidan Zaki, Nene ta ya zan iya dauka in wani ya miki rashin kunya, Nene ki sa mishi ido, duk daren dadewa gaskia zata bayyana, Dan shi ne, chan cikin ranshi akwai sonshi a cikin shi, donAllah kar ki sake zuwa Gidan". Zaid ma ya shiga lallashinta da tausassun lafazi, yana cewa ta bisu da addua, Allah ne zai kare ma Maryama Yaranta. Takaici ya hana Nene cewa komai sai Girgiza k'afar da takeyi tana tunanin yanda zata shigo Gidan Alhaji Zaki karfe ukun dare ta ci ubansu daga shi har Matar. *** Kwana na 2 a Cell, banda wata damuwa, saboda me? Saboda World, sosai yake batar min da duk wata damuwata. Baba bai zo ba, bai kuma ce a sakeni ba, so ba ranar fita daga wannan wurin. A kwana na ukun ne Ina zaune kawai naga wani kurtu ya lek'o yace "kai Dan Gidan Zaki fito" mamaki ya cikani, to Baba ya hakura kenan, ya sa an firdoni, tashi nayi na fita sai ganin Dogarawa fiye da uku tsaye da dorinarsu. Dogarawan nan suka tisa k'eyata bayan sun sanar dani cewa mai Martaba Sarkin Katsina ke nema na. Motar Emirates muka Shiga Har Fadar Sarki dake K'ofar Soro, wani dogaribya fara shiga bayan Mintuna Goma sai gashi ya dawo yace mu shiga. Ina Shiga Fadar gabana ya fadi, ganin Dalo durk'use gaban Fada, daga gefe kuma Baba ne da Aunty Shafa, sai Hudu da Annah, sai wata da ke Durk'ushe tana ta bayani ta bawa Fada baya". Muryarta kawai ya ankarar dani ko wacece. "Nene ce". Kwakwalwata ta fahimci cewa Nene ce dai ta kawo Baba k'ara. **** Tun bayan dawowar su Nene daga Gidan Zaki ta rasa sukuni, bata da wani madafa ga shi Zaidu kamar yayi kuka wurin rokonta a kan kar ta sake zuwa Gidan Alhaji Zaki. Bata san ya zatayi ba har kwana 2 suka shide bata da wani dabara, duk tayi sukuku, bari ta kira Seebinta ko zataji sanyi. Zuwa yanzu Nene ta iya kiran Mutanen London a waya da taimakon hotunan su wanda Zaidu Bawan Allah ya sa a jikin ko wani Contact, Hoton Seebi ta lalubo cikin contacts din ta danna kira don tana da kudi fiye da Dubu 10 cikin wayar duk don kiran Mutanen London wanda Zaidu BawanAllah ne ke sawa". "Hellooo Neh-Neh" taji muryarshi Da sauri tace "Dunkum. Kai na kira?" Ta na mai dauke wayan daga kunnenta tana sake duba screen din don ganin wa ta kira kuma dai hoton Nasibar ne. Mur ta sha kamar yana gabanta tace "kai dallah ba mai wayar wayarta". Dan daria yayi yace "Neh-Neh kinyi missing dina ne? Baki nemeni kwana biyu ba". Yau bata da lokacinshi cewa tayi "kai Arr, ina Nasibar?" Dan daria ya sakeyi yace "Sunje wani Birthday Party ita da Yarona". Tsaki Nene tayi tace "Wani yace ba yaronka bane? Rasa kunya beran kitchen, kace ta kirani in ta dawo". "Wai ya Neh-Neh yau sai gwasuleni akeyi? Wai ba mun shirya ba? Ai mun bar fada ko? Ko yau kin tuna kanki a Airport ne wurin masu Red din Kunne" ya karashe yana daria. "Wallahi Dunkum ubanka zanci" Guntun tsaki yayi yace "kinga Matsalarki ko Zagi? Wai ba Uncle Zaidu ya hanaki Zagi ba? Barin kirashi in gaya mai". Da sauri ta katseshi "kai dallah tsaya kaji, ka tuna Hajia Maryama Mamarsu Takwaran Zaidu BawanAllah da Dalo?". Rafeeq yace "Eh na tuna kawarki da kike bamu labarinta, me miki Wanki a Makka". Cike da jin dadi tace "Good, good Dunkum, to wallahi Mijinta ya mata Saki Uku, ya mata dukkan tsiya gaban Mutane" nan ta shiga bashi labari kamar a gabanta akayi, har zuwa zuwanta na farko da dukan da ta ma shafa, da kulle Danmakaho da akayi da zuwan su karban bailing dinshi". Ran Rafeeq ya baci, wai yaushe mutane zasu bar zama Victim din Matar Uba? Karon shi da Saude ya tuno, abubuwan da tayi da yanda ta shiga tsakaninshi da Mahaifiyarshi ya tuno, guntun tsaki yayi yace "Neh-neh Wai are Women Selfish?". Nene tace "Uwar me? Hausa zakai man dallah". Tsaki yayi yace "Neh-neh tunda Baban bai dubi Girman Daddy ba ya ci muku mutunci, ai yana da magabata, in ya fi karfin Magabata ai bai fi karfin Hukuma ba, in ko yafi karfinsu bai isa ya fi Karfin Baban Kowa na Katsina ba". Nene tace "Sarkin Katsina". Rafeeq yace "Shine Magana kawai, Neh-neh ba tare Kukaje Makka da Amaryar Sarki ba?". Nene cikin Jin dadi tace "ehmana dakin mu daya da matar sarki da Maryama". Rafeeq yace "ki samu ganinta ta miki hanya kawai". Allah Dunkum? Yace "wallahi kuwa" Tace "Zaidu Bawan Allah ya rokeni kan na fita daga harkarsu wallahi". Rafeeq yace "Nene sharesu wallahi, ki taimaka musu, ni na san sharrin Matar Uba, DonAllah kar ki karaya". Cikin Samun Karfin Guiwa tace "tankiyu Dunkum, i lobiyu, i miss you Dunkum". Yace "Yeah Right i miss you too My Amazing Granny". Ji yayi tace "Uwarka ka zaga" Tsaki yayi yace "kina da damuwa wallahi, ke fa kika fara turancin, kuma in an miki sai ya zama laifi?" "Oho dai kace ma Matarka in ta ga dama ta kirani" dif ta kashe wayar. Ta yanke Hukunci, Washegari karfe 8 na safe tafita, bata gaya ma kowa ba balle a hanata, ko driver bata bi ta kanshi ba ta samu A daidaita Sahu ta hau sai Gidan Sarki, Part din Gimbiya, aka ma Nene iso, bayan wasu mintuna Gimbiya ta fito, aiko ta rungumo Nene, suka gaisa cike da mutunta Juna. Nene tace "mai Martaba na nan? Shi nazo gani? Ko yana da bak'i?" Gimbiya tace "ko da bak'i ai zai ga Nenenmu ina fatan Lafiya?" Nene tace "k'aran Sakaran Mijin Maryama na kawo". Gimbiya tace "wani abun ya sakeyi? Ko sati biyu baayi ba da Maryama ta zo nan maganar rik'on yaya wai don ya saketa sai dai su bita". Nene tace "kinji Gilu ko? Ashe kun ma san da maganar, to shekaran jiya wacchan naje Gidan, naga matar da kanenta da uban sun mishi taron dangi sai bugunsh suke wai bayan nan kuma ya kulleshi a Police station, ke cin kashi kala kala ake musu a gidan nan, nace aiko suna da Gata, shine na garzayo don Ganin Mai Martaba". Gimbiya ta mik'e tace barinje in mai bayani. Bayan Sarki ya saurari Nene ya aika a Kira Mishi Alhaji Ali Zaki da Iyalanshi Gabaki daya, sannan ya tura Police Station a sako Zaid. Wannan Kenan ***** "Aa Allah ya kara ma Imani, Matata suka tarar mawa, Nene kuwa harni ta tsokale wa ido" Nene tayi karaf tace "ba gaskia bane, kaine dai kuka taran mashi, ni ina ni ina dambe? Ina neman shekara Saba'in da dori? Ta ya tsohuwa kamata zata iya Dambe da kai da wanchan matashin da kuma Matarka? DonAllah Mai Martaba duk wanda yaji wannan ai ya san karya ne". Duk da ina cikin tashin hankali sai da na murmusa da jin zanttutukan Nene. Bayan Sarki ya ji bayanan Nene da kuma na Baba da na Shafa'atu, aka min tambayoyi aka ma Dalo tambayoyi Sarki ya yanke hukunci. "Alhaji Ali Zaki, wannan ya zama karo na karshe da zamuyi zama kanka da yaranka, na saurari komai, na fahimci komai, ba ruwan Matarka da Yaranka, ba ruwanta da su, ke shafaatu ba ruwanki da duk abunda zai ma yaranshi, ba ruwanki da hanashi, ba ruwanki da sa shi, na miki iyaka da su, yauwa ba kuma da k'ayyade musu abincin cinsu, gidan ubansu ne, yana iya sakin ki, amma bai iya sakinsu, kina jina?". Shiru tayi bata amsa ba, bata ankara ba sai jin Dorina tayi a bayanta, wani irin bank'arewa tayi tare da sakin ihu, haka wannan dogarin ya sake shada mata a baya yace "kinji ko ba kiji ba?" Da sauri tace "naji wallahi, wallahi naji". Hankalin Alhaji Ali ya tashi amma ba abunda zai iyayi da ya wuce sanya ido, Sarki ya ja ma Baba kunne sosai, kafin ya tambaye in akwai mai magana. Nace ina da magana "Masters nakeyi, saura kwanakin da ba su wuce 3 na fara jarabawa, Baba yayi freezing accounts dina, ya kwace duk wani abun da ya bani, ya hanani komawa don kammala karatuna". Sarki yace "Alhaji Zaki hakane?" Baba ya fara in ina yace "Wallahi Mai martaba, ba kudi ne, amma inshaAllah da komai ya daidaita zan maidashi". Sarki yace "to madallah, duk da zaiyi wuya ace kai baka da halin maidashi karatu ba damuwa bane wannan, indai be rasa ci da sha ba to komai mai sauki ne, wannan tsakaninku ne, ku tashi ku tafi, ku kuma in akwai wani abu kuna iya zuwa Fada ku sanar dani, akwai mai magana?". Baba yace "eh ni, mai Martaba, donAllah ace ma wanchan Tsohuwar kar ta sake zuwa man gida, tayi nesa da iyalina donAllah, ayi mata iyaka da Gidana". Nene ta murmusa tace "indai Gidanka ne ba zan kara zuwa ba". Murmushin da takeyi ne ya fadar ma Baba da Aunty Saude Gaba, ba su yarda ba, wannan tsohuwa akwai bariki". Sarki yace "to Madallah" A haka ya sallame mu, ko ba komai Nene ta kwatar mana yanci ta siya mana mutunci, ta nuna mana muna da sauran gata. Nene ta rik'e hannuna da na Dalo ta ja mu waje tace "ku je Gida, da kunga abunda bai muku ba ku kirani, ka kula da kanwarka" sosai hankalinmu ya kwanta.Nene ta tsaida abun hawa tayi tafiyarta Gida abunta. Mu kuma da Motar Emirate a ka maidamu Gida, ba wanda yace ma kowa komai sai ni da Dalo da ke fira jefi jefi. A ranar Baba yaje Gidan Alhaji Lema don kara ja mishi kunne kan Uwarshi, lokacin sun fito daga Masallaci shi da Abbii(baban Nasiba) a nan ne ma ya san Mamarshi na wani Case, shi kuma Alhaji Lema a nan ne ya san cewa Nene taje Gidan Sarki, hakuri Abbi ya ba Baba. Nan suka shiga tattaunawa tsakaninsu. Abbi yace "wallahi ko me zaa ma Nene ba zata fita daga harkansu ba, oh Allah Nene ita bata damuwa taje ta siya fada da kudinta". Alhaji Habib yace "kawai Zaidu gobe ya wuce da ita Kaduna kawai, ta dan kwana biyu chan". Abii yace "anya zata yarda ta bishi? Alhaji Habib yace "wannan kuma aikin Zaidu bawan Allah ne". Dariya sukayi baki daya. Da kissa da kissina zasu bar Gidan ba tare da sun sake waiwayan gidan sarki ba, ki kulla makirci da duk wani sharrin da zaki iya musu, fadan ba naki bane, ya zama na Uba da yaranshi, ke kawai ki zama 'yar kallo. Hudubar yar rabi kenan da tazo Gidanta, haka kawai zatayi dole tayi taka tsantsan bata son duk abunda zai sake hadata da gidan Sarki don ta ji Dorunar nan, ta san me zatayi. Da kansu zasu bar Gidan baki alekum. SAI DAI ME? Rayuwa ta cigaba mana, ba dadi, ba mu taba waya da Mancy ba tunda ta bar katsina, tunda na dawo ni ke shiga kitchen in dafa Abincina, ban yarda na ci abincinsu ba, wani community school Baba ya maido Dalo wai be da kudin biyan makarantar da take a da, amma kin san me? Chan ya maida Annah, ga hudu da ke fantamawa cikin Motocin Gida ni ko nawa kallo. In naji Bakinciki kamar ya kasheni, na kanje dakin Haruna na shak'a World, a hankali na dinga taba Sigari har ya zame min jiki, a rana sai in sha kara fiye da biyar, komai ya cigana da wakana Babanmu na fiffita Bare kanmu, kashi ya fimu daraja, banda Abinci da wurin kwana ba komai na Babanmu a wurinmu, ke sai yazo ma na daina damuwa da komai, na daina shakkun Baba, na fetsare, na koma abota da su haruna na zama wani dan jagaliya, na koma Taraiyya da yan Bencin Eskaley. World din na batar min da duk wata damuwa, sai likafa ta cigaba sai in zuqi World na bi da kwalin Sigari guda, to fa Sigar Zuk'i daya nake mishi ya kare na cillar na kunna wata, shiyasa suke ce min Mankasssss... Ke kwatsam wata rana ina daki Dalo ta shigo dakina Hankalinta tashe, tana kuka wai ance mata ina shaye-shaye, ni abokinsu Eskaley ne. Hankalina ya tashi bana so ta taba ganin wannan side din nawa, nima kukan na sa nace mata "wallahi zan bari, ba zan karaba". Da kyar na samu tayi shiru na lallasheta. Rakata nayi har dakinta a cikin Gida, tausayinta ke kamani, duk ta fige ta lallace ta kuma yi duhun bak'i". Nazo wucewa daidai dakina na da na ji muryar Hudu na cewa "eh na saka mai a karkashin katifar shi" sai na ji Aunty Shafa tace "Yauwa kawai ai shi ya dauke su" sai kuma suka sa darian shewa. Kafadu na na daga, ba su dameni ba, na wuce dakina da ke baya, na dauko ragowar World na zuk'e, na zauna ina recieving current din da World ke bani a lokaci daya ina busar sigari, ina jina a gajimare naji an banko kofar Daki. Baba, da Anty Shafa ne, a dage na kallesu na watsar na cigaba da bankan Abuna". Cike da hargowa Baba yace "Kai DanMakaho, ina Sarka da yan kunnen Zinarin Matata da ka shiga ka sace a dakinta?" Duk da Maganar ta buga zuciyana ban dago na kallesu ba na cigaba da busar Sigarina". Aunty Shafa ta fara kukan munahinci tace "wallahi da idona naga ya fito dashi daga dakina, na mishi magana kan ya bani abuna ya min zagi ta uwa ta uba, shime nace ni ba zanyi komai ba balle ace ban kyauta ba, bari kai ka dawo tunda kai ka haifeshi sai ya baka". Wani murmushin bakinciki nayi wanda ya sa na zuk'e ragowar Sigarin, ido na ya kada yayi jazir, amma dai tak bance musu ba. Cin kwalar rigata Baba yayi "Danubanka yana ina? Hudu duba min dakin nan". Don rainin Wayau Hudu ya daga Katifata kawai sai ga sarka da yan kunne? Kutumar. Wai sai suka shiga rafka Salati. "Wallahi kai ba dana bane ba, ni ban haifi Barawo ba, Maryama ta dade tana haintata, cikin shege tayi ta lakafa min Da, ashe Barawo ne, Allah ya isa tsakanina da Maryama, ta sa na raini Barawo, shege dan shegia, Allah ya isa na, Allah ya tsine ma Maryama". Da sauri na kwace kaina nayi hanyar Fita. Muryar Makirar naji tana cewa "dama Alhaji baka san DanMakaho Shege bane? Be da Uba, kai a ka dauka sakarai a ka lakafa maka shi, kai kuma ka raineshi tsakaninka da Allah". Wani kukan Kura nayi na finciko hannun Baba na tillashi waje, kafin su ankara na sa mukulli na kulle Dakin, kafin ta farga da me nake niyyan yi na ciro Charger Laptop dina na dinga laftarta ta da shi, ihu takeyi na sa k'afa na tande kafafuwan ta, shi ko Baba daga waje Hankalinshi a tashe yana ta kokarin budewa, ya rasa yanda zaiyi. Sai da nagaji da kaina na kyaleta, duk tayi laasar, fuskarta tayi suntum, wannan shine ba a rabu da bukar ba, ita zaman shekara 15 din da tayi ba wai don ta zo dan Miji na dukanta bane, ita bata ma ga wani chanji ba, bata ga ribar shekarun da ta dauka ba, zuwa zatayi ta samu Er Rabi dole a sake sabon Zama. Ni ko na kyasta Sigarina na hau busawa, bude k'ofa nayi na bi ta inda Baba ke tsaye cike da tashin hankali, ya na ko ganina ya hau la'anta ta. "Allah ya tsine maka DanMakaho, Allah ya watse maka Karama, Allah ya kwashe maka Albarka, Allah ya laance ka" ya dinga tsina na. ••••• Kalar kukan da Labiba keyi ne ya sa shi tsaida labarin, murmushi mai cike da tarin takaici da bakinciki yake yace "Kefa kika dameni da na baki labarina, kuma da na fara sai kuka?". "INA SONKA" Ta tsaida duk wata na'urar da ke jikinshi daga aiki. Da kyar ya iya lallubo kalmar "Sha biyu Saura, dare yayi sosai, tashi muje na rakaki Gida". "DAGASKE, Ina Sonka". Cikin ido ya kalleta ya hango tsantsar Gaskiarta tsakani da Allah, wannan wace iri ce? Wace kala ce cikin Mata? Ya san ba da dabi'ar 'yan arewa, don babu wata 'yar arewa da zatayi abubuwan da Labiba keyi, ba 'yar arewa mai ajin da zata kalli Namiji gatsau haka ta gaya mishi kalmomi masu tsada, dauke kanshi yayi sakamakon binshi da wani kallo da takeyi. Ba tare da ya kalleta ba yace "Its Late, ki tashi na rakaki Gida". Hawayenta ta goge ta mik'e tsaye yayi gaba ta bishi a baya, da hasken Torchlight ya haska Fasassun Blocks ya tsallakesu, ya haska mata itama ta tsallake. Har tsakar Gidansu Labiba ya shiga. Da taimakon Hasken Farin Wata suke kallon juna cikin Ido. "So na kikeyi? Ko tausayina kikeyi?" Ya tambayeta kwayar idonshi kan nata. "In tausayina kike ji, nagode, ki bari, ni bana bukatar tausayin kowa" "In kuma sona kikeyi, shima ki bari, bana bukatar a So ni". So biyu ta kyafta idanuwanta kafin ta tsaidasu a kanshi tace Dagaske Sonka Nikeyi. Bata ganewa ya fada a ranshi, ya juya ya barta a tsaye, tafiyanshi yayi, ya sake tsallaka Fassassun blocks ya shige Gidansu, kan idonta ya bude kofar dakinshi ya shiga ya maida ya rufe. Zubewa tayi a kan guiwowinta biyu a k'asa a hankali ta furta YA RABB..... INTERMISSION.Runtse ido tayi ba tare da ta ga mai yake shirin yi ba, ta tsorata matuk'a da yanayinshi, Idonta a runtse bakinta kawai ke motsi, girgiza kai yayi ya ciro Jallabiyarshi ta Gado ya zura, chan gefen Gado ya zauna yana shafa Mai. Jikinta rawa kawai yake daga inda yake yaji adduar da takeyi "Allah ka tsareni da tsarewarka, Allah ka kubutar dani, Allah ka yafe mishi na san ba halinshi bane". Wani murmushi ya subuce mishi mai kama da na takaici, ita ko ganin shirun yayi yawa ya sa ta dan bude ido, ba ta ganshi ba, ware idonta tayi ta duba gefe, abun mamaki zaune ta ganshi yana shafa Mai. Murmushi tayi tare da gyara zamanta, tace "har raina na san ba zaka min komai ba". Mur ya sha "Me kika zo yi?" Da murmushi a fuskarta tace "nazo ganinka ne" a tak'aice yace "Fita" tashi tayi ko a jikinta tace "to bari naje, dama ba dadewa zanyi ba, na ganka ai". Kallon Mamaki ya bita da shi, wai ta yaya take a haka? Wulakanci ya mata fa, amma Dubeta ko a jikinta, tsakaninta da Allah babu abunda ya dameta. Tashi yayi ya sha gabanta yace "Okay kina ji ba, duk randa kika sake zuwa min daki, sai na tari Yayanki na gaya mishi kullum sai kinzo min daki". Kamar doll baby, haka ta kyafta idanuwanta tace "ashe kenan kullum zaka tare shi ka gaya mishi, don ni ba zan bar zuwa ganinka ba, sosai nake sonka Yayana". Cike da takaici yace "Huh!! Wai ke bakya jin nauyin ce ma mutum kina sonshi? Ko haka kuke a Kudu? Ashe haka Matan kudu suke? Kenan a Kudu, Mata ba su da Aji? Mata ke tallan kansu? To ki saurareni da kyau, in wannan haukan da kikeyi ne kike kira da So, ki sani ni ba zan taba son Mace Mara Aji ba, ba zanso ballagaza irinki ba mai tallan kanta, Macen da zan so ko nan gaba zata kasance mai Aji, mai kunya". Sake kyafta idonta tayi tace "Ka So ni donAllah". Da takaici yace "Are you not listening? Maganar da na gama miki kenan, ba zan taba sonki ba, don baki da aji, bana son classless person, kina zuwa dakin Namiji, wa ya san ko dama haka kike? Wa ya san iya adadin mutanen da kika kai kanki wurinsu? Ohh, tunda kike nuna rashin tsoro a duk abunda nake yunkurin miki wayasan ko kin saba? Waya san ko ke yar hannu ce? Dallah ki fice min a daki, ki koyo kamun kai, ki zama mai Aji da har ni zan kawo kaina wurinki ba ke ki kawo kanki wurina ba kingane?". Har ga Allah bata ma jinsa, hankalinta na gun yanayinsa, komai nashi abun burgewa ne, yanayinshi, yanayin maganarsa, yanayin fushinsa, ba abunda ya fi burgeta kamar yanda yake sa hannun damanshi yana murzan idon Hagunshi. Murmushi cike da fuskarta tace "Har raina nake Sonka". Takaici kamar ya kasheshi ya sa hannu ya tura mata kafadunta duka biyu yace "Dallah Mallama ki fitan min a daki" ya mata koran wulakanci, ita ko, ko a jikinta tayi murmushi ta wuce gida sadaf sadaf. WasheGari ta sake fakar Idanun Aunty Asiya ta fada dakinshi, ba ya nan, bata ji dadi ba ko kadan, ta so ganinshi, da tunaninshi ta kwana jiya ta kuma tashi dashi jiya. Da kallo ta bi dakin a hargitse, katifa ba gyara, duk lungu da sak'on dakin akwai karan sigarin da aka sha, ta bude toilet ta ga shima datti, ba ta son k'azanta. Hijab dinta ta aje gefe ta hau gyaran dakin. Ta waiga ta waiga bata ga tsintsiyar shara ba, ta fita da sauri ta fada gidansu, kasancewar bango ya rushe ya sa suka daina zaman tsakar gida. Labiba ta dauko tsintsiya da abun kwashen shara, da ledar Aerial, ta koma dakin, share dakin tayi tas, in har aka auna bolan dakin Mankas sai tayi tiya uku, kuma ba wani datti ke ciki ba illa ragowan sigari da kwali kwali, bak'ar leda ta samu ta juyesu tas ciki. Toilet ta shiga ta wanke tas, ta bude Wardrobe din, Ghana Must Go ne, hannu ta sa ta bude zip din ta ga atamfa da laces sai shadda da yards na maza. A ranta tace "ji kayayyakin da ba a dinka ba" a fili kuma ace "toh meyasa be dinkawa?" Wani tunani ya zo mata, ta tuna ya ce mata Babansu ya hanasu karban kayan Mancy, in ma ya gani k'onawa zaiyi, "Allah sarki, ba halin dinka kayan da Mancy ta turo muku, abun tausayi". Kwashe su tsintsiyar tayi ta koma Gidansu. BENCIN ESKALEY Su 3 ke zaune a Bencin sai Eskaley da ke cikin shagonshi. Safiya ce amma ko wannensu na banka ma cikinshi hayak'i, ba su da wata damuwa, sigari kawai suke zuk'a. Mankas daga gefe yake zuk'ar tabarshi, ganin Mota yayi ta ajiyeta a inda ta saba ajiyeta ya kalli su Tero yace "ga Jarabarban chan tazo". Baki daya suka bi gun da kallo. Mikewa Master yayi yace "wallahi warewa zanyi kafin ta iso" Ya tashi yana niyyan guduwa yaji ta na cewa "Master gaban Babarka zan bika na lakada maka na jaki". Chak ya tsaya tare da juyowa yana yak'en dole "Na matsu, Zan dan zagaya ne" mur ta sha tace "zagayawan uwarka, ban sigarin" kallonta ya tsayi yana kallon sigarin da yanzu ya kunnata, zaiyi asarar naira gomarshi da ita kadai ta rage mishi a dunia ya siya sigarin, muryarta yaji "za ka bani ko kuwa?" Tsaki yayi ya mik'a mata karar. Kafa ta sa ta murje shi tas, kafin ta matsa gun Haruna ta kwace nashi ta yar a kwata. Na karshen Mankas ya zuk'a ya busa hayak'in, cikin fada yace "ka zuk'i uwarka, kuma ita ka busa ma hayak'i a fuska ba ni ba". Murmushi yayi ya tashi tsaye tare da furta sunanta "NeNe". Iya k'arfinta ta sakar mishi Rank'washi a kai tace "Allah ya shiryeka Zaidu, nidai Wallahi—-" shiru tayi don Master, Haruna da Eskaley suka hada baki wurin k'arasa mata maganar da ta yi niyyanyi na "Zaidu Bawan Allah ba haka yake ba" kallo ta bi su dashi, so milliyan in zata ce haka, to so milliyan zasu karasa mata saboda maganar kenan "Zaidu bawan Allah" ba haka yake ba, kullum indai har ta zo to inshaAllahubsai ta fadi haka. Mur ta sha tace "Uwarku kuke kwaikwaiya bani ba". Gum sukayi suka ja bakinsu sukayi shiru, zama tayi kan bencin cike da isa don haka suke kullun. Eskaley ne ya fara gaidata kafin sauran suka gaisheta har Mankas din, ta amsa tare da kallon Zaid tace "kai dai baka ji ko? Ka cigaba, kar ka fasa wannan bushe-bushen, kai ko kunya bakaji? Bakinka yayi bak'i dubeka donAllah". Kai Zaid ya shafa yace "InshaAllah Zan bari Nene, ki tayani da addua, kai arr makaryaci, kullum haka kake cewa kuma baka bari, wallahi Zaid ka fita idona, randa zan tona maka Asiri wurin uwarka zaka sha mamakina, ka san dai ban tsoronka ko?". Da sauri ya rude ya fara rantse ranste "wallahi Nenenmu na bari, ban k'arawa, dagaske bazan k'ara ba". Ko a jikinta don ta san k'arya ba yau ya fara shi ba, ta kuma san ba bari zaiyi ba, amam ba zata fasa mishi addua ba, harara ta galla mishi tace "ka je ka dauko Abincin cikin mota ko kuwa?". Be tsaya tunanin yaushe tace yaje ya dauko abinci ba sai ma nufar motar da yayi da gudu. Kallo ta bi Haruna, Master da Eskaley tace "Ce muku ku bar Shaye-shaye bata baki ne ko?". Eskaley yace "Nenenmu zamu bari" Kamar ta mareshi tace "dallah rufa min baki, ba kai ne dan iskan da ke saida musu ba". Eskaley ya ja baki yayi gum. Tsautsayi yasa Haruna cewa "ai daga yau mun bari, ba zaki taba kama mu da shan wani abu ba". "ka min shiru ko sai na gwala kanka da bango? Kullum haka kuke cewa, banga laifinku ba, tsinuwa ke kanku, ta ya zaku bari uwayenku na tsinanku kullum". Master zaiyi magana, daidai zuwan Mankas dauke da Basket ya girgiza mai kai alamun yayi shiru. Ajiyewa yayi gabanta, kamshi ya bade wurin, waina ce da miya da taji naman miya tantakwashi, ta zuzzuba musu a plate kowa. Cike da jin dadi suke ci. Hannu ta nade a kirjinta tana binsu da kallon tausayi, ta san yanayi ne ya sasu halin da suke ciki yanzu, ta san takaici da bakinciki ya jefa da yawansu a halin da suke ciki yanzu, har ranta take son su kuma har ranta take tausayinsu. Barin ma Zaid wanda tafi so da tausayinshi, hawayenta ba kusa suke ba, amma ranar da ta fara ganin Zaid a hali na shaye shaye sai da ta zubar mai da hawaye bayan ta saka an rufeshi a Cell. A shekarun da suka shude, bayan Alhaji Zaki ya ma Alhaji Habib warning akan zuwa Nene Gidanshi, Zaid ya tafi da Nene Kaduna, Watanta Biyu ta saka daru dole a maidota Katsina. Zaid ya amince zai maidata amma ya bata sharadin ba zata sake zuwa Gidan Alhaji Ali Zaki ba, haka ta amince. Bayan Zaidu Bawan Allah ya dawo da ita, washegari da safe ta fita, tayi Unguwar Tudun Matawalle kan Keke Napep, daga farkon Anguwan taga samari yan matasa na shaye-shaye, su kuma wadannan ba sa tausayin kansu ne suke shaye-shaye da farar safiya? Nene da shiga sharo ba shanu sai da ta tsaya wai zata musu nasiha. Saukar daga Napep ke da wuya taga wani mai kama da Zaid na kokarin kai Sigari Biyu lokaci Guda Baki. Da gudu ta k'arasa wurin tana salati. Su 6 ne, dagowa sukayi suna kallonta cike da tsageranci. DanMakaho ya hau network, be ma ganeta, World ya dan taba kafin yake bi da sigari biyu. Da karaji tace "takwaran Zaidu bawan Allah, kai ne nan ke shan Sigari? Da kayan Maye?" Banza yayi da ita ya cigaba da suburbudar sigarinshi yana sake hawa network". A fusace Nene tace "danuwarka ina kaduna Hankalina na gunka, na matsa aka dawo dani don kawai naga halin da kake ciki ashe kana nan ka zama dan duniya, kana cikin yan banza kana shan sigari, don bariki guda biyu kake hadawa lokaci guda kai tak'adari ko?". Banza yayi ya kyaleta. Terro yace "kai mankas dallah wacece wannan tazo tana mana haushin kare?" Cike da murya ta yan shaye shaye yace "yo wa ma ya santa? Ke dallah Mallama ware". Ran Nene yayi mugun baci, bata san lokacin da k'walla ya cike mata ido ba, ranta ya baci ta wuce ta tsaida Keke Napep, ta yi gaba bata tsaya ko ina ba sai a Police Station, cewa tayi ta kawo k'aran Jikanta, shayeshaye suke suna taamali da kayan Maye, so take a rikeshi a ci ubanshi har sai ya tuno ko ita waye". Mota Guda aka ba Nene, bayan ta shiga ta musu kwatance har gaban Bencin Eskaley, kafin su Mankas su farga, tuni anyi ram dasu, daga inda take take ta faman Mita "ni zaka ce baka sani ba? Officer ku ci man uwarshi donAllah" haka akayi gaba dasu tas aka rufe a cell. Kwanansu Biyu kafin Nene ta koma, lokacin sun jigata sunyi laasar. Zaid na ganinta ya mike tsaye "Nene kiyi hakuri donAllah, hankalin dalo na chan a tashe, ba ta san halin da nake ciki ba, kice su sake mu". Hararshi tayi tace "sakarai, ka san da Dalo ka wofintar da rayuwanka, har kai dan mitsitsi da kai ka san shaye-shaye? To yau sai na gaya ma Dalo ko kai waye, ta daina girmamaka, don kai ba kowa bane face dan shayeshaye, gwara ta ganka a asalinka". Hankalinshi ya tashi ya hau magiya yana mata alkawarin ba zai k'ara ba. "Ka gaya musu ko ni wacece?" Da sauri ya gyada kai yace "wallahi na gaya musu, na gaya musu ke kakata ce" ta kallesu tace "to don uwarku sunana Nene, kar ku bar shaye-shayen, in na sake zuwa na ga kuna shaye-shaye, sai na sa an k'ara kamaku" da sauri suka fara rantsuwar sun daina basu k'arawa. Haka ta saka a ka sake su. Wani zuwan da ta sake yi ne ta iske suba gidan jiya, wato ba su bari ba, ta zagesu tas, ta ranrankwashi Mankas ta juya cikin Motar Gidan Lema. Ya zamana duk zuwan da zatayi don ganin Zaid a nan Bencin Eskaley ta ke tarardashi, ranar ko ta zauna kan Bencin tace "don uwarku kuzo ku ban labarinku duka, ta yaya kuka fara shaye-shaye?" Da Haruna ta fara, sai Terro, Master, Eskaley, Gayu, Bororo da Big loma. Dukkansu sun bata tausayi, kowa da irin labarinshi, wanda kusan dukkansu suna da irin matsalar Zaid. Wato matsalar Matar Uba, yawancinsu Matar Uba ce Silan fara shaye-shayensu, Nene ta tausaya musu, ta musu nasiha ta nuna musu suma 'ya'yane, Alkawari suka mata sun bar shaye-shaye amma ina Sam. Ba alamun dainawa. Nene bata kyamarsu, haka take jan su a jiki, ba kullum take zuwa ba, ta kan dade bata zo ba, amma in zata zo, da safe take zuwa kuma zata dafo Abincinta mai rai da lafia, ta zauna cikinsu, su ci ta kwashi kwanoninta ta tafiyarta Gida. Duk zuwa sai tayi fada dasu amma hakan bai hanata sake zuwa inta samu dama. Ba wanda bai son Nene a Bencin Eskaley gashi duk sun santa, indai kana zuwa Bencin Eskaley to ka san Nene, in ma yunwa ta koro su sai su zo Bencin Eskaley su zauna suyi ta adduan Allah shi kawo Nene da Abinci. **** Santi Haruna keyi yace "Wai Nene, Siyo Wainar nan kikayi?" Mur ta sha tace "Uwar ka ke saidawa?" Haruna yace "daga tambaya?" Nene tace "daga amsa? Dan wulakanci tun Asuba nake aikin wainar nan, zaka ce siya nayi, aa ka manta". Zaid yayi daria yace "Neneeee, mungode kwarai" kar ma ku gode "'yan tananiya, Allah ya shiryaka wallahi, ba haka Zaidu Bawan Allah yake ba" su Haruna suka karasa mata, sun san next statement din suka ce "uwarku kuke kwafa" duk suka kwashe da daria har Nene, wato kun daukeni Kaka, to ni ba kakarku bace ni uwarku da ubanku ce, don duniya baku da me sonku sama dani. Baki suka hada suna "wallahi gaskia ne, Sai Nene, Allah ya kare mana ke, ya ja kwana, dariya tayi tace "Allah ya shirya ku" haka suka rakata bakin mota suna jiran ta basu wani abu duk da sun san da wuya ta basu". Tace "kun dai san ko sisi ba zan baku ba ko? Ba zan baku kudina ku k'ona ba. sai Allah ya kuma min dawowa". Haba Nene ai mun bari, ba ta tsaya amsa su ba ta shige Mota ta rufe, Zaid ya bude dayan wurin ya saka Basket suka daga mata hannu Driver ya ja suka wuce. Zaid daga nan ya wuce Gida, straight cikin Gida ya nufa, dakin Dalo ya kwankwasa kafin ya shiga da Sallama, gaidashi tayi da Ina kwana Yaya? Da fara'a ya ansata yace "Yanzu Nene ta bar Unguwan nan" fara'ar Dalo ya fadada tace "haba? Shine ba ka kirani mun gaisa ba?". Murmushi yayi yace "ta na gaidaki, kinsan dai kika fita Baba zai dakeki, rannan da nace ta shigo ku gaisa Baba ma ya manta da ita cewa tayi aa gwara ta tsaya waje, don in ta shigo baba ya mata wani magana bugun tsiya zata mishi, Dalo ta fashe da daria tace "yanzu sai ta bigi baba? Zaid yayi hanyar k'ofa yace "tab ko nima sai da aka rankwasheni yanzu". Daria sukayi ya fita dakin yayi Boysquaters. Gabanshi ne ya fadi a lokacin da ya daura kafarshi cikin dakin, komai ya chanza, ba haka ya bar dakin ba, wa ya gyara? Da sauri ya fada toilet ba abunda ke tashi sai kamshi Aerial, wa ya gyara mishi daki? Wa ya wanke mishi toilet? Da sauri ya fita don koma wa cikin Gida. Inda ya bar Dalo chan ya isketa, kallonshintayi da mamaki tace "yadai Yaya?" Rasa abunda zai ce yayi. "Erhm Dalo, nace ke kika gyara min Daki bayan na fita?". Sadiya ta girgiza kai tace "aa Yaya, me ya faru?". Dan jim yayi yana dan tunani kafin yace "no karki damu" tare da fita. Dakin ya koma yana tunani mai tsawo, wacece a gyara mai daki? Ko Yesmin ce don ita kadai ce ke mishi wannan karambanin, amma a iya saninshi Yesmin bata zo Gidan ba tun last 4months, waye zai mai haka? Who could have possibly done this?". Idonshi ya kai ga Gidan Mallam Muhammad, da sauri ya girgiza kai yana fadin "Kai No, Aa gaskia, ba ma ita bace, ta ya ma zaayi in yi zargin itace? ba ita bace. Ba ya son yarda, ya tabbata ta zuciyya ga koran wulakanci da yayi mata jiya, ba ya tunanin zata taba dawowa har ma da farar safiya har ta mishi gyara haka, Hannu ya sa yana murza idonshi. Muryarta yaji tana cewa "Ya Zaid, har ka dawo?" Firgigita yayi kafin ya tsura mata ido yana mamakinta. Fuska a daure yace "Ke ce kika shigo min daki?" Karasowa tayi ciki da fara'arta tace "eh wallahi, nazo ba ka nan, shine naga dakin yayi kacha kacha, shine na dan share" mur ya sha yace "wa ya saka ki?" Murmushi kan fuskarta ta dan kalleshi, nace "wa ya sa kaki sharan? Ni na sakaki gyaran daki? Don me zaki gyara min daki? Ni Mijinki ne? Kar ki sake shigo min daki, ke wai wata irin Mara Aji ce? Bayan tallar kanki da kikayi, har bauta kike yi ma samari? Lallai kam Ajinki ya zube, ko da yake ba Ajin balle ya zube". Hannu ta sa a baki ta mishi alama da yayi shiru "shhh, menene abun tada jijiyoyin wuya? A kan me kake ihu? Saboda na maka shara? To kwantar da hankalinka Masoyi, ba zan kara ba, zan nema izinin ka kafin na maka shishigi, kai ba Mijina bane amma ina fatan wata rana zaka kasance Miji a gareni, lokacin zan share ko ina ba tare da na nema izininka ba". Zaid yayi shiru don ta gama kasheshi da Mamaki, bata zuciya bata fushi, me zaiyi da zai sa ta rabu dashi ne? Tsaki yayi ya sa hannu a aljihun doguwar jallabiyarshi bak'a dake Hange, sigari ya dauko ya cinna mata wuta. Labiba bata ida bashi mamaki ba sai da ta tako kusa dashi ta zare Sigarin hannunshi ta girgiza mai kai. "Ka ga dai ina da Athma, bana son hayak'i in na tafi sai ka sha abunka kaji Masoyi?" Kamar yayi ihu don haushi da takaici, wai me zai ma yarinyar nan ta rabu dashi ne? Ko Yayanta din zai samu ya gaya mishi yanda take bibiyarshi kila shi ya tsawatar mata, amma Aa ba zaiyi haka ba, ya san tarihin Gidansu, ya san dalilin da ya sa aka barta zuwa karatu Katsina, ba zai so zama silar batawar da Wanta ko Mahaifanta ba". Guiwowinshi ya sa a k'asa tare sa hade hanayyenshi duk biyu yace "DonAllah Biebs, don Girman Allah, kar ki k'ara zuwa min daki, na hadaki da Allah, ina jiye miki abunda zai faru a duk ranar da aka ganki a dakina, wai ba kya tunanin wata rana a ganki a nan? Wallahi people will have other impression, ki cece mu duka". Murmushi be kauce ma Fuskarta ba tace "wai ni ka durk'usa a gabana? Don na bar zuwan maka daki? Nima barin durk'usa mu dawo daidai, hakan tayi yanda yayi. "tsaya kaji maganar Gaskia, wallahi Billahi har raina nake son ka, ina matuk'ar son ka, sosai nake sonka, wallahi a cikin zuciyata ina wahala in ban ganka ba, zugi zuciyata ke min in har ban ganka ba, Ban taba jin son wani abu ba a raina kamar yanda nake jin Sonka, zaka ga kamar na matsa maka, amma Wallahi So gaskiya ce, samun mai son ka Abun Alfahari ne, ina Sonka, ka min uzuri, ka min izini na cigaba da Sonka". Sosai maganganunta suka kashe mishi jiki, zama yayi dirshan a k'asa, tare da lumsa idanunshi, wani irin yanayi yake tsintar kanshi a ciki, a hankali ya bude idonshi ya zuba mata su, sai faman murmushi takeyi yace "ki fa kyaleni, ni bana sonki I have a Girlfriend". Irin zaman da yayi tayi da murmushi tace "to wa ya ce maka Ina son zama budurwarka? I dont want to be your girlfriend, i want to be your wife, ban damu da wanda suke sonka ba ko kai kake sonsu, abu daya na damu dashi, shine ni ina sonka, kuma zan cigaba da sonka ba tare da amincewarka ba, ka min uzurin wannan". A duk lokacin da zata bude baki tayi magana, to inshaAllahu sai ta kwance mishi duk wani Noti na jiki, sai ta kashe mai jiki. "Yaya Sunanta?" Ya kalleta da mamaki tace "ita budurwar taka" Ta na ganin tantanin makwalatonshi yayi sama da k'asa kafin yayi magana yace "Yesmin". Tashi tayi tsaye kan kafafunta ta dauki wayarshi da ke kan Gado tayi dialing numberta, ya ko shiga ta duba numbern, ta ajiye mai wayar inda ta dauke shi duk yana aikin kallonta, ta kalleshi sosai. "Ba ta kaini Sonka ba" ya dago sosai don kallonta, jinjina mai kai tayi tace "Yesmin bata kama kafata a Son Ka ba, ni ina sonka kuma ba zan daina son ka ba, ka rok'eni kan na bar shigo maka daki? Kayi hakuri ba zan iya ba, na dauka numberka, zan dinga kiranka a duk lokacin da nake buk'atar son jin muryarka, kuma dai ga numberta nan, zabinka ne kayi saving ko kar kayi, ni dai zan dinga kiranka, ka ji dadin ranar yau kaji Masoyi? ina maka Son So Fisabillilahi". Juyawa tayi ta tafi abunta, ta barshi da mugun mamakinta, tambayar da shi kanshi zai so ya Amsa ma zuciyar yake ma kanshi, ta yaya ta ke haka? Why is she like this? She's too blunt Oh Allah, ita kamar makauniya, wai bata ga shi dan iska bane? Bata ga be chancaci soyayyarta ba? Ko kawai ita ta makance da son shi, shin bata hango ranshin dacewarsu bane? Ita bata san ya kamata bane? Bata san ya kamata tayi nisa da shi as far as she can? Wai harta ta ma fatan aurenshi? Tsaki yayi yace "tana ma hauka". Sigarin da ta aje ya dauka ya cinna ma wuta ya fara banka ma cikinshi hayak'i. Yana cikin banka ma cikinshi wuta wayarshi tayi ringing, dauka yayi ya kalli mai kiran, tsaki yayi gami da daura wayar a kunne. Da muryarta mai dadin sauraro tace "Hello Masoyi?" Lumshe ido yayi ya bude yace "Waye?" Ya na jin sautin murmushinta tace "Sunana Labiba Ahmad, kuma ina Sonka". Ji yayi kamar yayi ihu, da ta san yanayin da take sashi a duk lokacin da ta furta kalmar So a gareshi da ta rage Fada, ko kuma ta bar fada gabaki daya. "Ka dan fito wajen dakinka" kamar yana kallonta yace "menene?" Cike da shagwaba tace "donAllah Masoyi ka fito Kofar dakinka, wani abu kawai zaka gani" kamar ba zai tashi ba ya tashi dai ya fita, yana fita ya ganta zaune kan dakalin tsakar gidan Yayanta, murmushi ta mishi tare da kashe mishi ido, bai san sanda ya zauna shima a bakin kofar dakin nashi ba ya na kallonta, taku 30 zai kaishi gareta, itama haka. "Yauwa Masoyi, ka zauna a nan ina kallonka ina waya da kai". Mur ya sha yace "mai kike so ne?" Da jin dadi tace "good question, kai nake so". Tana ganin harararshi daga inda take, tayi dariya tace "komai kyau yake maka" yace "zan kashe wayata fa" " ka kashe amma ka tsaya na cigaba da kallonka". Ido cikin ido suke kallon juna, bai kuma kashe wayar ba, sun dau minti daya a hakan kafin yaji tace "ko ban shigo dakinka ba, in na samu ganinka irin haka ya wadatar dani". Dif wayar ta mutu sakamakon k'arewar credit dinta, da sauri Zaid ya duba wayarshi ya ga call ended, shi ya san bai kashe wayar ba, baya so ya katse wayar, ya na so su cigaba da magana, ya na jin dadin muryarta, so yayi ya sake kiranta, ya ma manta tana gabanshi, ta na lura dashi sosai, har ya dago kai ya kalleta, daria tayi ta mishi alama da katin wayar ne ya k'are, kunya yaji don gani yake ta dago damuwa a fuskarshi, tashi yayi ya shige daki. Ita ko farinciki kamar an mata kyautan kujerar Makka, ta na cikin jin dadinta ne wayar Jay ya shigo, murmushi tayi ta dauka da Sallama. Da korafi ya fara. "Labee nah, anya kin damu dani kuwa? Ba kya nemana, ba kya kirana, in na kiraki ba kya dauka, ko laifi na miki Labee?" Kamar yana gabanta ta girgiza kai tace "ko daya Jay, wallahi issues ne suke ta faruwa a gida, ruwan sama akayi kwana biyu, bangon Gidanmu ya fadi". Jawad ya jajanta mata, yace "yau Saturday kuna gida" tace "eh wallahi" "ina zakije to?" A ranta tace dakin Masoyi amma a fili tace "babu fa, ina gida ba wurin zuwa". Cike da shauk'i Jawad yace "ya kamata ace ina kallonki a halin yanzu, wallahi Labiba nayi missing dinki sosai, murmushi tayi tace nima nayi missing dinka". Jawad yace "ki saurareni nan da nextweek ko ta sama inshaAllah, zanzo naganki farincikina". Murmushi Labiba tayi tace to nagode. Firan Soyayya sukayi kafin ya mata sallama, tashi tayi ta fada kitchen don daura Sanwar rana. Kullum Sai Labiba taje dakin Zaid ta ganshi kafin ta tafi Makaranta, so da dama har ta gama surutan ta ta fito bai ce mata komai, ba ta kuma zuciya don banzan da yake da ita baya hanata dawowa gobe, in kuma ta dawo Makaranta zata tsaya a Bencin Eskaley ta ga in ya na nan, in ko bai nan da ta dawo Gida zata kwala mai kira a waya ya fito waje suna kallon juna daga inda suke suna waya. Yau Talata sun fito daga Aji ita da Aisha, suna zaune a Caf suna cin Abinci sai ga Abu Sideeq, da murmushi ya k’arasa gunsu, su ma suka mayar mai da martannin Murmushin, kujera ya ja ya zauna yana jefan Labiba da kallon k’auna, tana cin Abinci ta waigi ta kalleshi tace “ba zaka bar kallona haka ba sai ka k’ara So na? Bayan na ce maka ka daina So na”. Shafa dan gemunshi yayi yace “ba ni zan yanke hukuncin daina Son ki ba Labiba, ba yin kai na bane”. Cokalin hannunta ta ajiye tace “Na sani, ba yin kan ka bane, So ne, ba kayi laifi ba, ba kai ka zabi ka so ni ba, zuciyarka ce, wanda baka da damar controlling dinta in har ta kamu da Soyyaya, za ta iya kamuwa da Son Fari, bak’i, mai kyau ko mara kyau, nakassashe ko mai lafia, mashayiya ko mazinaciya, So ba choice dinka bane, bakai ke zabar So ba, So din ne ke zabanka, amma ina kiranka da kayi So domin Allah”. Abu Sideeq yace “Kinga wannan dalilin ne ya sa nake jin Zuciyata ba zata iya daina Sonki ba Wallahi bana son weekends ta yi saboda ba na samun ganinki, kin hanani kwatancen gidanku, ya zanyi?” Jinjina kai tayi tace “na san yanda kakeji trust me, wani lokacin zaka ji zuciyarka kamar ta dare a duk lokacin da baka tare dani ko? To So ne, shifa haka So yake, baida hakuri kamar Zawo, ina maka Uzuri, nima ka min uziri, Abokantaka kawai zan iya baka, wallahi kafin karfin wulakacin gu na, shiyasa na ke gaya ma iyakar gaskiana”.. Baya son maganar nan, mik’eewa yayi tare da kallon Aisha da ta cika da takaicin Labiba, yace “Sholy, barin je Class” da kyar Aisha ta murmusa tace “to Abu Sideeq bye”. Ba tare da Labiba ta lura da Aisha ba ta cigaba da cin Abincinta, Aisha ta zundureta ta k’afa. Labiba tace “Yadai?” Aisha tace “wai ke Labiba me ke damunki?” Da mamakinta kalli Aisha tace “me ya faru?”. A hasale Aisha tace “Why are you so Blunt? Me ya sa ba kya kauda Ido? Meyasa kike fadan abu kai tsaye? Mace fa kike fa, da kike ma Abu Sideeq magana haka wallahi ji nayi kamar na kashekinda mari don kunya da takaici, kin sake baki sai mishi bayani kike a kan Love, aa ke ga Dr din Soyyaya, kinsan me ke damunshi kaza da kaza, ki dinga sa wa bakinki linzami, dazun ma na ji su Hamza na gulmanki wai kince ma Yusuf kayan da ya saka ya mishi kyau, Labiba Ahmad ina ruwanki da kyaun da Yusuf yayi? Meye ruwanki da kayan da ya saka? na san you are a straightforward person, amma ba komai bane yazo bakinki zaki fada most especially Maza, ban san ya kukeyi a kudu ba amma mu a nan Arewa ba haka mukeyi ba, yanayin maganar mu da Namiji daban yake. Ji fa daga randa Abu Sideeq ya zo gaya miki sirrin ranshi tun kafin ya fada kikace kin san yana sonki, haka fa kika ce mishi na son kana sona, gaba da gaba fa, haba Labiba, donAllah ki dinga Jan Aji, in namiji ya zo miki da wani bukatam So ki nuna ma baki san me yake nufi ba har sai ya furta da bakinshi, duk da Ya Jawad Yaya na ne, amma wallahi kin yi saurin ba da kai da yace yana sonki, baki bashi wahala ba, Mace ga kike, Labiba i am not criticising you, ba zan dauka ba in aka cigaba da yi da ke don kawai kina fadin raayinki ba wanda tsakaninki ne daAllah, but don Allah ki sai ma kanki mutunci, Mace da yanga, nuna isa da Aji aka santa, ba saurin ba da kai bori ya hau ba, a haka maza na Sonki ina ga kin fara jan Aji da yanga?”. Labiba da take sauraron kawarta ta na jin abunda take cewa tace “Aisha Usman, Kina ta fadan Aji Aji, me kike nufi ne da Aji? Wai meye shi Ajin?”. Aisha ta kalleta sosai, ta karanci har ranta bata san me take nufi ba, ta gyara zamanta tace “Labiba, You are a treasure and you are priceless, donot give anyone reason to look down on you, do not let anyone stomp on your Pride, its Ok to be straightforward, But Here in the North, a Girl’s Ego Comes first Okay?”. Ta dade tana nazarin maganganun Aisha kafin tace “Aisha so a Arewa zubar da aji ne in ka fara approaching Guy, like kace kana son Namiji maybe don yana burgeka or something?” Da sauri Aisha tace “What? Ai da in tareka ince maka ina sonka, gwara Sonka ya kasheni tab, wannan ai zubar da Aji ne, ba girma”. Murmushin Takaici tayi tace “To, dalilin kenan? Shiyasa in tace ma DanMakaho ta na sonshi ya keji kamar tace “zo mu yi zina ko zo mu kashe wani, Abun Mamaki ba zai taba k’arewa ba. “Aisha yanzu in nace ma Namiji “Ina Sonka, ina kaunarka DonAllah ka So ni fa?” Aisha ta zare ido kamar Labiba tayi sabo tace “nace miki da kika gaya ma Namiji haka gwara kin koma gun mahallicinki da sonshi, ai zaki sha gori tunda ke ki kace kina sonshi, zai ta tutiya kan cewa ba shi yace yana sonki ba ke kika rok’eshi da ya soki, za kuma ki ga wulakanci kala kala indai Namiji ne”. Labiba da tambayoyi kala kala a bakinta tace “Zai ta miki wulakanci yace baki da Aji ko?” Da sauri Aisha tace “Ehmana, zai ce ke dai baki da Aji, kin kawo min tallar kanki, ballagaza kawai”. Da sauri Labiba tace “meye Ballagaza?” Aisha tace “Worthless person with no self respect” wani murmushin takaici ya subuce mata a hankali tace “WOW!!” nan ne kalaman shi suka dawo mata; “KI SANI BA ZAN TABA SON MACE MARA AJI BA, BA ZAN SO BALLAGAZA IRINKI BA MAI TALLAN KANTA, MACEN DA ZAN SO KOBNAN GABA ZATA KASANCE MAI AJI, MAI KUNYA”. A yanzu ne ta fahimci duk wata kalma da ta fito bakinshi, mai ya sa bata fahimci hakan ba? Ya Rabb, kallon da ya ke mata kenan?. Tashi tayi ta saba jakkarta tace “Aisha Gida zanje” Aisha da mamaki tace “Gida? Lectures din 2-4 din fa? Labiba ta girgiza kai tace “ ba zan yi ba, gida dai nake son Zuwa”. Nan da nan Aisha ta shiga damuwa tace “Labiba kinji haushin maganar da na miki ne? Kiyi hakuri donAllah” Labiba ta murmusa tace “ko kadan Aisha, baki bani haushi ba, illama taimaka minda kikayi kika firdo ni a duhu, sai dai in gode miki. Aisha zan ganki gobe inshaAllahu”. Da sauri Labiba ta fita daga Cafteria ta bar Aisha, straight ta fita Makaranta ta ko ci saan samun abun hawa ba ta tsaya ko ina ba sai Gida. Tun zuwanta Katsina Yau ne karo na farko da ta ji ranta ya baci, ita ya ke ma kallon Ballagaza mara Aji? Wacce bata da kamun kai? To Laifin me tayi? Son shi shine Laifi har ya ke danganta ta da ballagaza mara Aji? Saboda Son shi? Ya Allah, tayi mamaki, sakamakon da kake samu kenan in ka fada son wani? To indai haka so yake, Allah ya wadaran So, ba ta so kuma, ba ta so ta yi Soyayyar kuma. Runtse idanunta tayi da ta tuna ya fa gaya mata bak’ak’en maganganu da yawa, tunanin wanda ta yi ya fi bata ranta fiye da ko wanne inda yake cewa {“ba zan taba sonki ba, don baki da aji, bana son classless person, kina zuwa dakin Namiji, wa ya san ko dama haka kike? Wa ya san iya adadin mutanen da kika kai kanki wurinsu? Ohh, tunda kike nuna rashin tsoro a duk abunda nake yunkurin miki wayasan ko kin saba? Waya san ko ke yar hannu ce? Dallah ki fice min a daki, ki koyo kamun kai, ki zama mai Aji da har ni zan kawo kaina wurinki ba ke ki kawo kanki wurina ba kingane?}•. Duk da Hausan da yake yi ya girme ma hausanta tayi amanna wannan ba abun Alheri ya fada ba, ba ta san me yake nufi ba, amma ita ta san zata koyi kamun kai kamar yanda ya bukata, zata yi Aji, za kuma ta daina kai kanta gun shi har sai ya kawo kanshi gunta, zata bi kalamun Aisha, sai dai Sonshi ya kasheta in yana kisa, amma zata sai ma Kanta mutunci. *** Yau tun k’arfe 3 yake Gida don dazun da safe tace mishi 4 zata dawo, har 4 ta wuce, yana zaune bai ga Gitta wanta ba, har 5 yayi ta lek’e ya ga ta ina zata fito, shiru ba alamunta, ba Wayarta kuma, sai 6 saura ya ga ta fito daga Dakinta amma ko kallon Bangon Gidansu ba tayi ba, mamaki ya kashe Dan Makaho, hakan na nufin ta dawo Gida Kafin 4, amma bata nemeshi ba kamar yanda ta saba. Ya dai share, ya fita, bayan maghrib yayi ta tsumayin wayarta, ba shi ba alamunshi, ya damu, meyasa yau bata nemeshi ba tun safe, ko bata da credit ne a waya? To meyasa bata zo gunshi ba, ko bata samu dama ba? Da tunaninta ya kwanta tare da k’agara safiyya tayi don ya san dole tazo ganinshi kafin ta tafi School. Ita Ko Labiba tunda Uwata ta haifeta, ba ta taba kasa bacci ba irin daren ranar, zuciyarta har wani zugin zafi takeyi, Alwalarta na nan, kawai ta hau Sallaya ta fara Sallah don ta samu sauk’i. Washegari da safe ta tashi ta yi ma yara wanka ta basu breakfast ta fita ba tare da ganin Zaid ba, karo na farko tun bayan rushewan bango, duk jinta takeyi wani iri. Shi koyana zaman jiranta har 10 don zuwa ta gaya mishi zata tafi makaranta, amma shiru fa,har 11, wayarshi ya duba ya ga ba kira balle nessage, mamaki ya kasheshi, tashi yayi da sauri ya fita ganin 12 saura. Bencin Eskaley ya nufa, Eskaley kaga wucewar Yarinyar nan? Eskalay da neman magana yace “wace yarinya kenan?” Mur danMakaho ya sha yace “Beebs mana” Eskaley yace “yo ai ina bude shago naga wucewarta tun wurin 8 da minti 40”. Hannu ya sa cikin sumar kanshi, tunanin goma da ishirin a kwanyarshi, da kyar ya koma Gida, don jiran dawowarta, still be ga dawowanta ba ba kuma kira, damuwa ya shiga fiye da zato ganin har suka kwana suka tashi Labiba ba ta kirashi ba, ba ta kuma nemeshi ba, hankalinshi ya tashi, to ko wani abu ya mata? Ko ta ji haushin maganganun da yake mata ne? Amma yaushe rabon da ya mata wata magana? Ai ko bayan nan tazo dakin ya fi so nawa, kuma shekaran jiya sun dade suna waya, me ya faru ne?. Haka suka cigaba da Wasan Buya, har sai a kwana na ukun wanda shine Jumuat, ya fito ya zauna kan dakalin da suke waya tun bayan Sallahr Asuba yake zaune a wurin, yau sai ya ga fitar ta, a gaban idonshi ta ma Yara Shirin Makaranta, a gabn idonshi ta shiga da kalacinsu kasnacewar Kitchen da toilet duk a tsakar gida suke, yana zaune Yaya Muhammad ya fito rike da hannun yaran bayan Aunty aasiy ta rakosu suka fita. A gaban idonshi Labiba ta fito daga dakinta sanye da Zani da Hijab da kwandon Wanka ta shiga Toilet, mamaki yake yanda ko ta gefen ido be ga ta kalla Bangon Gidansu ba, harkarta kawai takeyi, bata damu da ta kalli gefenshi ba balle ta san akwai hallitta a gurin. Nan Damuwa ya baiyyana fuskan Zaid, wanda yanzu ya tabbatar something is wrong somewhere.?” Ya na ganin ta fito ta lek’a dakin Aunty Asee ta mata sallama yayi saurin tashi shima ya fita daga Gidansu sauri sauri gudu gudu don ya cin mata, tafiya take yi kawai, shi ko ya bi bayanta, ta ji kamar ana binta, ta juyo ta mishi kallo daya ta watsar, daidai nan zuwan wani mai Keke Napep, ta hau ba tare da tace ma mai KekeNapep din fga inda zata. Turus Zaid yayi, menene hakan? Bata ganeshi bane? Ita ta gani ta watsar? Gabanshi ya dinga faduwa, zuwa yayi shagon Eskaley ya karbi World ya hau zuk’a sai da ya ji shi tatul. Gida yaje ya hau bacci bai tashi ba sai karfe 4 na rana, fatanshi ya ga missed call dinta amma babu, gabanshi ya tsananta faduwa, karo na farko a rayuwarshi ya samu kanshi da kiranta a waya amma sai dai me wayar har ta gama ringing baa dauka ba, ya na da tabbacin ta dawo saboda yau jummuaa, sake kira yayi no answer, kamar zaucacce ya cigaba da kiran layin baa dauka 27 missed calls ya mata, daga baya sai jin wayar yayi a kashe. Sosai ya ga tashin hankali, messages ya tura mata yana son sanin me ke faruwa? Da me yasa ta bar nemanshi, meyasa ta bar kiranshi amma ba reply. Haka yayi kwanan bakinciki da tararabi. Weekends ya shigo DanMakaho ya fige ya kajame, kofar dakinshi ya zama wurin zamanshi, Aunty Asiyah ta sha ganinshi zaune a wurin sai dai ta murmusa mai daga inda take, amma bata son zamanshi wurin yana kalle musu gida, ya zamana dai kullum cikin Hijab take, su Sabit kuwa sai da ya musu alamu da suzo suka tsallaka, ya rike su yana musu hannunka mai sanda yana ina Mama? Amira tace tana Dakinta, Ina Baba? Sukace yana Kasuwa, ya danyi jim yace “Ina Bibs?” Sukace wa? Sai da ya sosa kai yace “Labiba” Amira tace “Aunty Labiba? Ta na daki”. Zaid yace “Ok ku koma Gida” suka tsallaka suka wuce, wato shine bata son gani? Take kulla kanta a daki, yanzu inda take zama ta bari ko? To me yasa ta fara abunda ba zara iya jurewa ba? Wani yace ta shishige mai in ta san zata bari? Uban wa yace ma ta shigo rayuwarshi, danuwarta don ta ga ya damu shiyasa take azabtar dashi ko? To dole yau ya samu mafita, ba zai iya ba wallahi, ya gaji kuma. Karfe 12:30am na dare ya tabbatar duk sunyi bacci, ba tare da tunani biyu ba ya tsallaka Gidan Mallam Muhammad, ba fargaba ko wani tsoro ya fada dakin Labiba, Dakin na warin mosquito coil, wayar shi ya haska yaga inda zai ganta, be ganta ba, sai Amira da Sabit da ya gani kan Gado, ta na ina? Ya tambayi kanshi yana waigawa ya ganta kanta a k’asa tana Sujjada, idonshi ya murza, ya kunna wutan dakin kasancewa da wuta, Labiba na cikin Sallah tayi zaton Aunty Asee ce, sai ba ta damu ba ta cigaba da sallahnta, don Aunty Asy kan shigo daukar wani abu a wardrobe dinsu. Ta na Idarwa ta daga kai ta kalleshi, gabanta ya yanke ya fadi, zuciyarta ta karaya, da kyr tayi na maza ta mik’e tsaye ta linke dardumanta ta wuce shi ta kashe Hasken Wutar Lantarki, dama torchlight din wayarshi be mutu ba, dakin da dan haske, ganin ta na niyyar hawa gado ta kwanta, tana so ta gwada mishi cewa bata san da wani hallitta a wurin ba ya sashi kiran sunanta, muryarshi cike da yanayi madu wuyan Fassaruwa. “Beebs” Chak ta tsaya ba tara da ta juyo ba illa fasa hawa gadon da tayi. “Beebs me na miki ne?” Ba amsa A tsorace yace “Ko kin dai na So nah neh?”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO Babi na Sha Biyu1⃣2⃣ (MANCY 🤱🏻) Daga kai tayi ta kalli Farin Wata da ya haske tsakar Gidan, ta sa hannunta daidai saitin zuciyarta ta karanta: Allahumma La Sahla illa ma ja'altahu Sahla, wa anta taj alal hazna iza shi'ita Sahla. Saboda wani radadin da taji zuciyarta na yi ba tare da wani dalili ba. Da kyar ta isa dakin, ta bude k'ofar a hankali ta raba ta shiga, sai dai zama tayi dabas kan Katifar, zuciyarta ba komai ciki sai tunanin DanMakaho. Muryarshi ya dawo kwakwalwarta inda yake cewa "tausayina kike ji ko Sona kikeyi? In tausayina kike yi, ki bari bana bukatar a ji tausayina, in kuma Sona kikeyi shima ki bari bana buk'atar a so ni". Kamar yana gabanta tace "ni fa ba tausayinka nakeji ba, kai din ne nake So" ta idasa hawa kan Katifar don yin bacci. Sai dai me? Tunanin Dan Makaho na nan mak'ale a zuciyarta. "Huh!!!" Ya fada Cike da mamaki da takaici. Ta ya tace haka? Ta yaya ta iya fada mishi haka? Wani irin guts ne da ita? Karfe sha biyun dare? Ta yaya ta iya kallonshi har cikin kwayar ido tace mishi tana sonshi? Wace irin Macece? A ina aka taba haka? Haka sukeyi a Kudu? Tambayoyi ya ta ma kanshi. Daga bisani kuma Ranshi kuma ya soma baci, don me za tace mishi tana Sonshi? Don me zatace dagaske take sonshi? Ko zolayarshi takeyi? Was she mocking him?" Hannu ya sa a cikin tulin sumanshi ya zube kan Gado don yin bacci, sai dai me? Tunanin Labiba da kalamanta ba su bar zuciyarshi ba. Asuba ta gari ZaiLab ***** Alhaji Abu Shamsu na Tuk'i cikin kwarewa da iyawa, a lokaci guda yana taya Mamanshi da kawarta fira, a wani bangaren kuma yana daga kai ya kalli madubi daidai saitin Maryama da ke ta kuka a hankali. K'awar mamarshi ta juyo tace "Ki bar kuka Maryama, ki gode Allah wallahi da bata nakasa ki ba, kishiya ai bala'i ce, nima haka na sha wahalarsu, aure na 4 duka banji dadi kishiya ba, amma da nayi hakuri, wallahi gashi na ci ribar hakuri". Hajiya tace "kiyi hakuri, na san tunanin yaranki ke damunki, inshaAllah ba wata damuwa, kin ba Allah ajiyarsu shi zai kula miki dasu, ki kwantar da hankalinki kije kiyi Iddah ki samu miji kiyi aure. Mancy dai murmushi tayi ba tace musu komai ba, suka dinga tafia har suka isa Kano, Unguwar Yayanta ta fada, da kwatance suka isa har Gidan Yayan, an ci saa ya na nan ta shiga Gidan, suna ganinta duk suka tashi, Matarshi ta rik'ota. Maryama Lafia? Mun ga motar kaya akace daga Gidan Alhaji Zaki, shin Lafiya?" Wani kuka ta fashe da shi wanda ya tada hankalin Yayanta Umar da Matarshi. "Yaya Baban Zaid ya Sakeni, Saki uku ya min Yaya" a tare suka rafka salati "Maryama me kika mishi?" A gurguje ta basu labari, sosai suka jinjina ma lamarin, ran Yayanta ya baci, har yana ikirarin sai yaje Katsina ya ma abokinshi rashin mutunci. Hakuri ta hau bashi tana gaya mishi ba yin kanshi bane, sannan ta tuna mutanen da ta bari a waje, da sauri ta mike tace ba ita kadai bane, Yayan ya fita ya isa gurinsu Alhaji Abu Shamsu, Maryama ta shigo da Hajia da kawarta, ta basu ruwa a buta suka kama ruwa sukayi Sallar Laasar. Alhaji Abu Shamsu ya ba Yaya Umar baki, ya mishi nasiha, Yaya Umar ya ji dadin dattakon Alhaji Abu ya mishi Godia sosai, ya tambayeshi in shi dan Kano ne, Alhaji Abu yace "Abuja yake da Iyalinshi, sun zo bin Jirgine zuwa Abuja don Mamarshi ba zata iya zaman Mota ba daga Katsina har Abuja, sai kuma kawar mamarshi da zasu aje a Rijiyar Zaki, Yaya Umar ya jinjina kafin suka dan yi fira, sukayi musayar number kafin suka musu Sallama. Bayan tafiansu ne tayi wanka ta yi sallah, ta kulle kanta a Daki ta cizga kukanta son ranta, Yaranta sune damuwanta, wani hali suke ciki? Bata ma son sani, ta fi so ta yarda da cewa suna nan lafiya lau, bata son ta karaya har ta kirasu su ma ta karya masu da zucia don tana da htabbacin in har dai ta kira daya daga cikin Dalo ko Zaid to shakka babu sai sun sa kuka, har ta biye musu ba za a samu mai lallashin wani ba daga cikinsu, nan ne ta dau alkawarin kashe wayarta har sai ta samu natsuwa a cikin ranta. Bayan Wata 5 Har ta gama Iddah bata nemesu ba, duk da Yayanta yayi ta rokonta kan ta rok'esu amma ta k'i, ko Zaid ya kira ta wayan Yayan yace a ba Mancy kin k'arba takeyi. Haka ta kasance a Gidan Yaya Umar, ta na k'okarin ganin cewa ba ta zauna cikin damuwa ba, yaran Yayanta na debe mata kewa, har tau bata kunna wayarta ba, yanzu so take ta fara ko da neman aiki ne dama da kwalinta na nursing, dama shi Alhaji Zakin ne yace be yarda da aiki ba shiyasa batayi ba, yanzu ko dole ta nemi aiki don ba za ta zauna haka ba. Gabaki daya suke zaune a Parlon cikin Gida, wayar Yaya Umar yayi Ringing, cirowa yayi daga Aljihunshi ya ga mai kiran. Alhaji Abu Shamsu ne. Bayan sun gaisa ne yake sanar mishi da cewa ai yana kofar Gidanshi. Zumbur Ya Umar yayi "Ah aha, ka ja zance da yawa, ga ni nan fitowa". Ya kallesu yace "Bak'o mukayi, Alhaji Abu Shamsu ne". Mancy da Matar Yayanta suka kalli juna suna neman karin bayani, amma yayi gaba don shigo dashi. Parlornshi ya kaishi, suka gaisa sosai sukayi firan bayan rabuwa. Yaya Umar ya tambayeshi yaya Mahaifiyarshi? Ya sanar dashi cewa ai har ta gama hutun a Abuja tana Katsina, yanzu ma daga Katsinan yake yaje gunta. Yaya Umar yace "Allah sarki, Allah ya ja kwana". Alhaji Abu ya amsa da Ameen. Shiru suka danyi kafin Alhaji Abu yace "Alhaji Umar ina Maryama?" Da murmushi yace "aff kaga na shafa'a ban kirasu kun gaisa ba". Yace "bakomai, dakata dai kaji Alhaji Umar, tun tuni na so zuwa Gidan nan amma na dakata saboda Maryama na cikin Iddarta, na yanke hukuncin zuwa bayan Iddarta shiyasa na zo yau, hak'ikanin gaskia tun randa muka dawo da Maryama take cikin tunanina, na tausaya mata, kuma ina son Aurenta in har zata amince dani". Yaya Umar da murna yace "me zai hana in har Maryama ta amince da kai, barin turo maka ita dai ku tautauna in har ta amince sai ayi wallahi" Alhaji Abu Shansu yaji dadin hakan ya gyara zamanshi shi kuma ya shiga ciki. Maryama dauki ruwa kikai parlo, akwai bak'o na nan na jiranki. Da mamaki ta kalli Yayanta tace "Yaya Bak'o kuma? Daga Ina?". Murmushi yayi yace "Yi Maza kije Maryama, ya na jiranki". Mik'ewa tayi ta shiga kitchen don hado tray dama akwai Hijab cikinta straight parlon Yayanta tayi, tun daga k'ofar Parlon take jin wani daddan kamshi, nan gabanta ya shiga dukan uku-uku, kafanta yayi sanyi amma haka ta shiga da sallama, ganin mutumin da ke zaune ne ya sata karasawa cike da mamaki, amma sai ta dake ta fara mai murmushi. Gaishe da shi tayi sosai da faraa a fuskarta, ya amsa shima cike da jin dadi, tambayar Hajiarsu tayi ya gaya mata tana Katsina lafia, shima tambayan mutanen gidan yayi ta amsa da Lafiyar kowa lau. Shiru suka danyi kafin yace "Mancy" Da sauri ta dago kai ta kalleshi cike da Mamaki, murmushi yayi yace "haka naji Zaid ya ce miki rannan a Gidan Sarki". Sadda kanta tayi tana wani murmushi sakamakon irin kallon da Babban mutum kamar Alhaji Abu yake mata. "Nasan zuciyarki na cike da tambayoyi kan me ya kawo ni ko? Ba tare da bata lokaci ba Mancy, so nake na shiga cikin jerin Zaurawanki don neman Aurenki, hak'ika bayan rabuwan mu na kamu da sonki duk da a farko tausayinki nakeyi amma daga baya na lura So ne, shiyasa ko da na ba Mamata labari ta karfafa min guiwa kan na nemeki". Mancy tayi shiru ta cigaba da wasa da yatsunta. "Uhmm?" Ta dan dago tace "ni yanzu har wani aure zanyi? Ina da kamar Zaid? Sai dai in jira aurenshi". Yayi yar daria yace "Shekararki nawa?" Dan turo baki tayi tace "43" murmushi yayi yace "duka nawa kike? Ni ina da 65 shekarun babban Dana 32, amma bance na tsufa ba sai ke? Kuma ni fa ban ma yarda kin kai ko 25 ba". Dariya ya sata sosai tace "Shekarun Zaid fa kenan". Ji yayi ta sake burgeshi, har ranshi yake jinta cikin sanyin murya yace "Maryama, mu ba yara bane, bakiyi tsufa ba, koma kin tsufan nikam gani nakeyi kamar yar shekara 18 kike, ina so naji ta bakinki, in baki amince dani ba ba zan miki dole ba". Shiru tayi ba tace komai ba Ganin Shirun na neman yawa ne ya sashi cewa "ina iya baki Lokaci, kiyi shawara kiyi tunani, har zuwa jibi da nake shirin komawa Abuja". Tace "to shikenan nagode". Ba jimawa ya mata bankwana sukayi sallama ta shiga ciki ta ma Yayanta magana ya koma wurinshi ya rakashi har Gate ya sake jinjina mai dagaske yake sonta yake da Aure. Da daddare ne Yaya Umar Ya kirata suka yi maganar Alhaji Abu Shamsu, Shawara ya bata a matsayinshi na Yayanta, yace "kar ta dakusar da kuruciyarta, kar ta manta Alhaji Ali saki Uku ya mata in ma tana tunanin koma mishi ne, tace "haba Yaya, tana sonshi amma wallahi ya fitar mata a rai, ba ta tunani ko aure ta sake ta fito zata iya sake aurenshi, ta hakura dashi" yace "to Ina ganin ya kamata kiyi tunani kan Alhaji Shamsu, ba zan miki dole ba, amma kar ki bari Alhaji Abu Shamsu ya subuce mata". Godia tayi ta tashi ta koma dakinta. Ta san ba zaiyiwu tayi ta zama a gidan Yayanta ba, duk da Uwa daya Uba days, yau da gobe sai Allah, Alhaji Abu baida wani aibu a zahiri, Zuciyarta tayi ta karanto mata shawarwari, har tayi naam da Alhaji Shamsu. A ranar da zai tafi ya dawo, nan ta mishi Albishir da ta amshi bukatarshi, sosai ya nuna murnan shi, yace "zai basu Wata Biyu su Fahimci Juna, kuma ya na fatan suyi Bincikenshi kafin nan don da Wata biyu ya cika zasuyi Aure. Ita gani take kamar anyi gaggauwa amma shi cewa yake bata lokacin me zaayi. Haka Alhaji Abu Shamsu yake zuwa Kano duk bayan Sati bibbiyu, har Mancy ta sake jiki suka shak'u sosai, suna fahimtar juna a lokaci daya kuma Yaya Umar na binciken Alhaji Abu Shamsu. Wata rana suna tsakar Gida suna Zance kan Carpet, Alhaji Abu yake ce ma Mancy, in sunyi aure ta karbo su Zaid, Mancy tayi murmushi tace aa su yi zamansu a chan abunsu, yace "wai saboda me? Tace haba ina zani da manyan yara kamarsu? Dan shekara 25 da 'yar shekara 16?" Yace " to menene? Zan dauki nauyinsu, zan kula dasu a matsayin nawa" tace "aa Alhaji, ka barsu wallahi nagode sosai". Yace "to a dauko Macen" tace "aa ba wanda zaa dauko cikinsu, zasu dinga zuwa mana hutu". Ya juya kai cikin rashin jin dadi yace "to shikenan". Ba su san shigowan mutum ba, sai dai suka ganshi tsaye kansu, hawaye ne ke kwaranyowa daga idanuwanshi, duk yayi bak'i ya rame ya jeme. Da sauri Mancy ta mik'e zata rik'oshi yayi saurin yin baya kamar wanda wuta zai taba. Alhaji yace "lafiya wanene ne wannan?" Baki na rawa Mancy tace "ZAID". Alhaji da faraa yace "Mallam Zaid muna lafia?". Ba tare da yace ma kowa komai ba ya juya zai fita daga Gidan. Mancy ta bi bayanshi tana kwala mai kira amma yak'i tsayawa. Murya a kausashe tace Zaid Aliyu Zaki kar ka sake ka fita daga gidan nan. Chak ya tsaya. Ta taka har gabanshi ta tsaya tana kare mai kallo, idanuwanta suka ciko da hawaye amma sai ta dake, hannu ya sa zai murza idonshi ta rike hannunv. "Baka ganni da bako bane Zaid?". Juyawa yayi ya karasa inda Alhaji Abu ke tsaye yace "Ina Wuni?". Alhaji Abu Shamsu ya amsa da Fara'arsa. Zaid ya juya ya kalli Mancy kafin ya dawo da dubanshi wurin Alhaji Abu yace "Daddy, ka aureta ka tafi damu Gidanka DonAllah". ZAID mancy ta fada a kausashe. Alhaji Abu yace "zan so hakan Zaid, zan so na hadaku da nawa 'yayan, kuma 'yayane, InshaAllah zan ga hakan ya faru". Mancy tace "to lallai ka manta da maganar Aurenmu, na fasa ba zanyi ba kuma". Alhaji Abu ya rikide yace "haba Maryama mai yayi zafi? Kiyi hakuri, dama ai sai da amincewarki zan daukesu, kiyi hakuri, ni niyyata masu kyau ne". Da sauri tace "Allah ya baka ladan Niyya, amma zasu tsaya Gidan ubansu" "Faqat". Wani murmushin takaici Zaid yayi yace "Mancy, kina son mu kuwa? Mancy? Wace irin Uwa ce zata dafkar da Yaranta kamar wasu kayan wanki, ta tsallakesu ta yi tafiyarta, ta k'i waiwayonsu, ta ki nemansu? Ko sun nemeta ta guje musu? Mai muka miki? Ko mai na miki? Mai dalo ta miki? Eh Mancy?" "ZAID mu shiga ciki mu gaisa ya kake?" Ta na mai nuni da Alhaji Abu da ke tsaye da Ido. Bai damu da ba su kadai bane ba, yace "Mancy,kika tafi kika barmu, bai isheki ba, kika kashe wayarki baki neme mu ba, Mancy Mu kira Baba Umar, ko su Walid da Ummi, su baki wayar ki kashe ki ce zaki neme mu, baki taba neman mu ba? And now zaki ce min Ya nake? Really Mancy? Ya nake? Do i look alright to you? Bakiga nayi bak'i na rame ba? Bakiga na k'azance ba? To na ma fi kyan gani kan Dalo, ita in kika ganta so daya ba zaki so sake daga ido ki kalleta ba, saboda rama". "Mancy Gidan Ubanmun da kike ta ik'irari bamu da wani gata ko galihu, Idi yafi mu matsayi a Gidan, Mancy ba wahalar rayuwar da ba ma gani, ba kallar Sharri da kazafin da baa mana, Mancy me muke ci a Gidan Uban da ba zaki bari a dauke mu ba, nan Kano zanzo sai da naci bashin Naira dubu daya wurin Eskaley, Mancy kamar ni yau ni ke ci bashi? Huh. DonAllah ki firda mu daga wannan k'angin, ki tafi damu duk inda zaki, Babanmu ba sonmu yake ba ba zai damu da duk inda zamuje ba, bai k'i mu shiga dunia ba, think of our Future wanda nawa ya fara rugujewa, da kanshi wanda kike son Aura ya miki tayin daukar mu amma kin hana, wai saboda me? Anjima sai kice kina Sonmu, kalar soyayyar taki kenan?". Ganin yana magana ba tare da ya tuna wa yake ma magana ba ya sa ta daga hannu ta mareshi. Dakata wa yayi tare da matse kuncinshi. "Har Gobe, har abada ni Mahaifiyarka ce, ka san yanda zakayi man Magana". Kai ya sadda k'asa yace "kiyi Hakuri Mancy, ki yafe min, amma DonAllah ki tafi damu". Alhaji Abu yayi tunanin tafia ya barsu don yana ganin kamar zasu zo su kebe, yayi hanyar Fita da sauri Mancy ta dakatar dashi ta hanyar cewa "dakata Alhaji, donAllah ka dawo, akwai abunda nikeso dukanku ku fahimta, mu zauna". Alhaji ya dawo ya zauna Shima Zaid din Zama yayi a bakin Carpet. Mancy ta fara "Alhaji Nagode kwarai da kala Soyayyar da kake nuna min, na san Son da kake min ne ya shafi Yarana, nagode kwarai amma donAllah indai bani nace maka ina so ka taimaka ma Yarana ba kar kayi komai". Alhaji yayi mamakin Mancy Sosai, shakka babu bata da kwadayin abun dunia. Ta kalli Zaid tace "Zaidun Babanshi, Mancy bata kyauta ba da bata nemeku ba, Mancy tayi laifi ku yafe mata kaji?" Kauda kai yayi yana son murza idonshi ta rik'o hannun tace "Haba DanMakaho na" murmushi ya subuce mishi don Mancy ba ta kiranshi da sunan sam sai in tana son sa shi daria. Tace "to ka fahimceni, wallahi duk runtsi duk wuya baku da Gidan da ya wuce na Mahaifinku, kun fiso na tafi da ku Agolanci? Kama san meye hakan? Kana da Shekara 25 kake so ka bar Gidan Ubanka ka koma Gidan Mijin Mamarka? Haba Zaid kayi tunani mana, ban yi hakan ba don bana sonku, na yi hakan ne don na kwatar muku yancinku, ku zauna Gidanku, ku ma Mahaifinku Biyayya, ku maido da sonku zuciyarshi, ku samu albarkarshi". Murmushi Zaid yayi yace "Ya riga da ya Tsine min, ta sa ya tsine min Mancy". Ba ta san lokacin da ta fashe da Kuka ba. Ganin haka Alhaji Abu yayi saurin Mik'ewa ya zaro kudi a Aljihu wanda zasu kai dubu 20 ya damk'a ma Zaid a hannu yace "barin tafi Zaid, kangaida Dalo, ku cigaba da Addua, Allah baya bacci". Yayi Gaba Zaid ya mik'e ya bishi a baya, Mancy kam bata yi yumkurin mikewa ba. Sosai Zaid ya ma Alhaji Abu Godia, ya rakashi har Mota kafin ya dawo Gun Mancy dake durkushe a gurin, Zaid ya cigaba da bata labarin tun bayan rabuwar su zuwa yau da ya yanke hukuncin biyo Mancy. Sosai take Kuka kafin ta share hawayenta, Zaid ya yi zaton ta janye qudurinta amma da yaji tace "Allah ba ya bacci, ku cigaba da hakuri, gaskia zatayi halinta, kuma in dai ba saba mishi kayi ko addininka ba, to bakinshi ba zai bika ba, ba zai kamaka ba" ya gane cewa tana kan bakanta. "Mancy ya maida tsine min fa kamar wak'a ko karatu, wata rana ko zai kamani". Mancy tace "Allah yana tare da ku Zaidu" sanin Mancy yar magana daya ce ya sashi mik'ewa don shiga ciki, ya san Magiyarshi da duk abunda zaiyi ba zai chanza mata raayinta ba, Mancy kaifi daya ce, ajiye mata kudin da Alhaji Shamsu ya bashi yayi, riko hannunshi tayi ta bashi kudin, tace na kune, ni banda kudin da zan baku da na k'ara maku, muje ka ci Abinci ka koma Katsina". Murmushin takaici Zaid yayi yace "ba ma zan kwana ba?" Ta gyada kai tace "eh ba zaka kwana ba". Mai makon yaji haushinta sai cewa yayi "Ya Rabb" zuwa yayi ya rungumeta sosai yace "nayi Kewanki da Yawa Mancy, ki kunna wayarki ki kira Dalo donAllah". Kai ta gyada mishi ya shiga ciki gurin Danginshi, sun ko ji dadin ganinshi sukayi ta rungumeshi suna fira, Ya gaida Kawunshi da Matarshi, Walid ya jashi zuwa Dakinsu, Ummi ta zubo mai Abinci, yayi Sallah Asahar da Laasar kafin ya mike don haraman tafiya, Walid ne ya fito don saukeshi a tasha, yaso sake kebewa da Mancy amma tak'i yarda. Haka ya musu Sallama Walid ya daukeshi zuwa Tasha. Sai Gab da Isha'i Zaid ya isa Katsina, tun a hanya yace yau shagali zaiyi shi da kanwarshi, daga tasha ya wuce Chimex don siya musu Shawarma, ya tsaya a Mansho Suya ya siya Gassashen Kaza, ya siya musu Lemu da ruwa, kafin ya tsaya a Wani Shago ya siya ma Dalo Chocholates kafin ya hau Machine ya wuce Gida, sai da ya tsaya ya biya Eskaley dubu dayanshi kafin ya karbi World na dubu biyu, ya dan zuk'a kafin ya wuce Gida. Yana Shiga Gida ya hau kwala ma Dalo Kira, babban parlo ya shiga ya gansu gabaki daya banda Dalo, hanyar Dakinta yayi yana kiranta da k'arfi, fitowa tayi da murna ta rungumeshi cike da jin Dadi "Ya Zaid ashe gun Mancy kaje baka tafi dani ba? Ya Zaid nayi waya da Mancy na, Mancy na ta kirani" Zuba musu ido yan Parlorn Sukayi, Shafaatu bakinciki kamar ya kasheta, wannan farincikin da sukeyi ya fi daga mata hankali, bata so ta ga ko da hakori daya ne ya fito da sunan daria, ranta ya baci. Kasa hakuri tayi tace "DanMakaho tafiya kayi? Wa ka gaya ma zakayi tafiya?" Kallonta DanMakaho yayi yace "Kar naje gun Uwata? Sai na nemi izini? Kin yi kadan na nemi izininki" ya kalli Dalo da ta ki bari ranta ya baci yace "muje daki Dalo, muje kiga abunda na siyo miki" tsalle ta daka tace "Allah Ya Zaid naji dadi ko ba ka siyo min komai ba, da Mancy na nayi waya, kuma tace za mu dinga waya kullum" daria yayi wanda ya kara bak'anta ran Shafa, yace "muje Daki kar su huce. Binshi Dalo tayi sai ji sukayi tace "ina zaki da daren nan? Dakin Yayanki? Ke karuwa ce zaki bi namiji dakinshi?" Zaid ya mika mata ledojin yace jeki gani nan zuwa ta bi umurnin Yayanta. Zaid ya taka har Parlo inda suke tsaye yace "Uwarki Ce Karuwa" Hudu ya taho Zaid yace "kar ka soma, Agolan banza, ka san kayi gigin wani Abu bugun burauba zan maka yanzu". Ya kalli Annah, yace "kinyi Asarar Uwa, Agola". Ya kalli Shafa da take tsaye kamar an disata yace "Ni da Dalo muna nan zama daram a Gidan Ubanmu, baki isa ki koramu ba, ba ki isa ba wallahi, ko me zakiyi kiyi, ko me zaki sa ya mana ki sashi, amma baki isa ki sa ya koremu ba don ba inda zamu wallahi, in kinga mun bar Gidan nan, to Aure mukayi". Ya juya yayi tafiyarshi, sai huci rai bace tace "bari Ubanka ya dawo" daga bakin kofa ya dakata yace "sai dai shi da kika raina, kar ki fasa hada mu da Mahaifinmu nikuma ba zan fasa miki duka ba, kinga ba wani abu bane don DanMiji ya bigeki" ya sa kai ya fice. Wani ihun Bakinciki Shafa ta sake, Hudu da Annah sukayi kanta, bangaje su tayi ta wuce daki ta rufe. DanMakaho Ya iske dalo a daki har ta fara cin shawarmanta dadi kamar ya kasheta. "Yaya nagode nagode this is the happiest day of ny life tun bayan tafiyar Mancy". Daukan shawarman yayi shima ya zauna yace "Nasani Dalo, i know". Alhaji Abu Shamsu ya isa Gidanshi da Dare, yau ne yayi shirin gaya ma Uwargidanshi Hajia Lubabatu da Iyalanshu batun Aurenshi wanda zaizo a sati 3 masu zuwa. Da Sallama ya Shiga Parlon Inda suke jiranshi gabaki daya. Hajia Luba da Yaranta biyu Abdulhafeez da AbdulMajeed suna sanye cikin shiga ta alfarma. Sannu da zuwa suka mishi gabaki daya, ya amsa da fara'arshi. Direct Dinning Area suka wuce don yin Dinner. Suna ci suna sha suna fira cikin jin dadi da soyayyar junansu. Alhaji yace "nikam Abdulhafiz ina Ummita ne? Kazo kana cinye min abincin gida" daria sukayi gabaki daya yace "Abba ta tafi Biki Kaduna sai ranar Lahadi zata dawo" Hajia tace "Ai Gauro ne bai da mata" suka sake daria. AbdulMajeed yace "Abba da kaje Katsina ka ga Aisha?" Abba ya kurba ruwa yace "na ganta wai har ta kai SS2, ikonAllah yara suna ta girma". Umma tace "amma ka dai san dalilin da yasa Majeed ya tambayeka ko ka ga Aisha ko?" Majeed ya fara shurin Umma da kafa kan tayi shiru ta fara Dariya tace "to ba zan fada ba" Abdulhafiz yace "ni zan gaya ma Abba in ke baki gaya mishi ba". Abba yayi daria yace "na san Zancen, ai sai ta gama Secondary zamuje ayi magana". Shidai Abdulmajeed kunya ya kama shi. Suka cigaba da cin Abinci kafin suka gama, suna niyan tashi ne Abba ya dakatar da ita, ta zauna su kuma suka wuce parlo. Ya kalli Ummar yace "Hajia Luba, akwai abunda nake so na gaya miki". Ta tattaro nutsuwanta ta bashi, "Hajia Luba, kin tuna Maryama wacce na baki labari? Da muka zo Abuja da Hajia?" Kai ta gyada tace "eh naganeta wanda Mijinta ya saketa ko" Alhaji Abu ya gyada kai sannan yayi dan Jim, kafin yace "So nike na Aureta". Dimmm taji kafin ta dafe kirjinta tace "Aure kuma Alhaji? Wani irin Aure?" Yace "afuwan, donAllah kar ki daga hankalinki". Nifa bangane ba, a kan wani dalili zakayi aure? In tausayinta kakeji ka bata jari mana, ba sai ka aureta ba, baka sakr aure tun kuruciyarka ba sai yanzu? Haba Alhaji". Lallashinta ya fara yi, amma bata tausu ba ta cigaba da bude murya har sai da Abdulhafiz da Abdulmajeed suka zo. Abdulmajid yace "Abba meke faruwa?" Kafin Alhaji Shamsu yayi magana Umma tayi karaf tace "Majeed ni Abbanku ke son tonawa asiri, wai aure zaiyi, yana da Yara kamarku wai zai sake aure, ko Autanshi Jawad na neman shekaru 25 shine yake son tona min asiri". Duk da sun ji maganar wani iri amma ba su nuna ba AbdulMajeed ya karasa gunta ya dafa kafadarta yace "Umma donAllah kar ki tada hankalinki". Cikin karaji tace "Aure fa zaiyi, mai na rageshi dashi?" Abdulhafiz yace "Haba Umma, menene haka kike shirin yi? Ba mu taba jin kanku ba, menene don Abba zai kara aure? Umma ba a kanki zai ajeta ba, Umma Abba ba zai ki yin adalci tsakaninku ba, in Abba yau ya kawo wacce zata raina ki, kinsan mu Yaranki ba zamu yarda ba, donAllah ki kwantar da hankalinki, kiyi fatan a kawo maki ta gari wacce zaku zauna ku sake kwantar ma mahaifinmu da hankali" Abdulhafiz ya kalli Abbansu yace "donAllah Abba in wacce kake son aura zatazo ta tarwatsa maka farincikin Gidanka ne DonAllah kayi watsi da lamarin, amma in har zata kwantar maka da hankali ta k'i tada hankalin Mahaifiyarmu to Allah ya kawota Lafiya". Fuuu Hajia Luba ta wuce daki, Da sauri Alhaji Abu yace "wallahi Maryama ba ta daga cikin Mataye masu tarwatsa farinciki Gida, in kuka ji labarinta zaku tausaya mata kuma zaku so ta kasance Aunty a gareku". Abdulmajeed yace "In har ba zata daga Ma Mahaifiyarmu hankali ba to kana da goyon bayanmu Abbanmu, zamu tayaka shawo kan Ummanmu". Hadesu yayi ya rungume yana sanya musu Albarka, Madallah da yara masu hangen nesa. Da ban baki da Nasiha suka shawo kan Hajia, aka dai samu ta sauko daa fushin da tayi da Abbansu. Biki ya matso aka sake gyara Gidan aka ware mata dakuna Biyu a cikin Gidan. Zaid da Dalo kullum sai sunyi waya da Mancy, sun san zatayi aure, Mancy tace "suyi zamansu ba sai sunzo ba. Haka aka daura Auren Maryama da Alhaji Abu bisa sadaki naira dubu 30 a nan kano, kamar auren Fari haka abokan Alh Abu suka zo. Danginsu sunzo, Abdulhafiz da AbdulMajeed suka dauko Matar Babansu tun daga Kano har Abuja, ba ruwansu da taya Mamansu kishin haukan nan wanda yawancin mata keyi in aka ma Mahaifansu kishiya. Nan aka danyi Walima wanda da shawararsu Majeed Hajia Luba ta hadashi. Dangin Maryama suka damk'a ma Hajia Luba Maryama, ba yabo ba fallasa sun karbi dangin Mancy, aka musu adduar zama lafia. Da dare Alhaji Abu ya hada iyalanshi ya musu Nasiha ya musu fada ya masu fatan Allah ya hada kawunan su. Abdulhafiz ma ya musu Nasihan zama lafia don kwanciyan hankalin Mahaifinsu, ya gargadesu kan su toshe kunnuwansu da ga jin tsegumin mutane. ** Zama sukeyi da juna tsakani da Allah, ko wacce burinta ta burge Mijinta, Kishi irin na Yan Bariki sukeyi, Hajia Luba ta lura Mancy bata zo da raini ba, bata da matsala ko kadan, shiyasa ta kwantar da Hankalinta suke zamansu, Mancy ko ta na biye da ita, abunda yake dan sosa ran Hajia Luba shine yanda Abdulhafiz da AbdulMajeed ke son Mancy, komai Mancy Mancy, harta Matar Abdulhafiz ko ta zo Gidan da sun gaisa da Hajia Luba sai ta wuce dakin Mancy ta shantake, in Abdulhafiz yazo daukarta da ya shiga gun Mancy to fitowarshi ba lokacin ba sai sun sake bata lokaci, ta rasa mai suke cewa. Duk da ta san Mancy da son labari da jan fira shiyasa ta saye zuciyan kowa. A duk lokuttan da suka shude tun bayan Sabon auren Mancy, ta kan tura ma su Zaid kudi duk wata, shiyasa ba ya rasa kudin zuk'an World. Akwai wani Rana da Mancy ta aiko musu da kaya Shadda laces da atamfa kai harda provisions cike da Ghana Mustgo, Zaid yaje Tasha ya karbo, yana zuwa Gida ya kira Dalo ya na nuna mata Sak'on Mancy, kamar daga sama sai ga Alhaji Ali da Hajia Shafa. Hajia Shafa tace "wannan kayan fa?" Banza Zaid yayi da ita ya cigaba da firdo da kayan ya na nuna ma Dalo, daka mishi tsawa Alhaji Ali yayi yace "bakaji ana magana ba? Wadannan kayan daga Gidan Uban wa suke?" Shiru yayi bai da niyyar amsawa. Dalo tace "Mancy ta aiko mana dashi". Sai da gabanshi ya fadi ya bi kayan da Ido. Hajia Shafa tace "ina ta samu kudin siyan wadannan kayayyakin tana zawarci?". Dalo ta zuro baki tace "ta fa yi Aure". Gaban Alhaji Zaki ya fadi da sauri yace "Maryamaa Tayi Aure?" Hajia Shafa da tsoronta kar ace Mancy Auren Kisan wuta ta yi don ta dawo dakinta, da sauri tace "to sai me in Auren tayi?" Nan ya fara "Sai me in Aure tayi? Ina abunda ya damemu da aurenta, zancen banza zancen hofi?". Zaid tsaki yayi ya fara maida kayan cikin Ghana, Aunty Shafa tace "wai yanzu kai Alhaji ce mata sukayi kai baka daukar nauyinsu ne? Baka basu ci ba ka basu sha da zata aiko musu da provisions? Har da kayan sakawa, harta lipton don tonan asiri? Duk k'okarin da kakeyi a kansu ba sa gode ma ba sa godeAllah? Sai sun ce baka musu?" Ran Alhaji yayi dubu ya baci, yace "Allah ya tsine muku marasa gode Allah, duk abunda nike maku ba kwa gani?" To wallahi ba ku isa ku tona min Asiri ba, kamana ace ana turo da irin kayyayaki nan kamar na Mabuk'ata a gidana, ina Samson, kuzo ku k'onemin Kayayyakin nan". Da Gudu Samson yazo don cika Umurnin Alhaji, Zaid yayi yunkurin hanawa amma Alhaji tuni ya fara tsinanshi, Dalo ta runtse Ido ta riko hannun Zaid, ta jashi baya, suna hange aka cinna ma Kayan Wuta. Fargaban Hajia Shafa ace Mancy auren kisan wuta zatayi, ta samu Sarari ta kira Er Rabi ta gaya mata fa Mancy tayi aure a yi bincike a ga wata aure. Nan ErRabi ta kira Hajia Shfa tace "ke Maryama ta fi karfinmu don tana Auren Wani k'usa" nan kuma sai bak'inciki ya kaure. ** Ran Mankas ya baci Ainun, amma Dalo ta taushe shi, ba su gaya ma Mancy ba, itama bata daina turo musu Sak'o in ta samu dama ba. Ba da dadewa ba Mancy taje Dubai ita da Alhaji da Hajia Luba, ta musu Tsaraba, ta aiko musu dashi bayan dawowan su. wani Jallabiya Dalo ta saka cikin tsaraban Dubai, Annah na ganin kayan taji Kayan sun mata kyau, cewa tayi ta je ta cire ta bata, dalo ta kalleta da mamaki, kafin ta bata amsa sai dai ji tayi Hajia Shafa tace "ina kika samo rigarnan? kije ki ciro ki bata kafin ranki ya baci, don munafunci ba Babanku ya hanaku karban abubuwa daga gurin Mahaifiyarku ba? Kije ki cire ki kawo ma Hannah ko yau Babanki ya tsine miki a karo na ba adadi. Jiki na rawa ta shiga ta ciro ta ba Annah, Annah ko ta fuzga taje ta chanza. Annah ta ci kwalliya wai zata Gidansu kawarta, ta fita tana karairaya wurin inda ake prking Mota, kamar daga Sama sai ga Zaid, a Hak'e yake don yanzu ya zuk'i world yace "Ke wannan ba rigar Dalo bace? Tace "Aa" hr yayi gaba ya dawo baya yace "danubanki ba rigarta bace? Uwar wa ya siyo miki? Zaki gaya min gaskia ko sai na yankaki?" Da sauri tace "A ra min tayi" damk'o wuyarta yayi yace "cire don ubanki" jiki na rawa tace "barin je daki zan bata abunta" daka tsawa ya mata yace "a nan zaki cire danubanki". Ihu ta kwala "Mummy" Mari ya katse mata hanzari, ya ja rigar tun daga Sama har kasa ya dire, ya fincikota ya kwabe mata rigar tas, kuka ta fara sosai ga cin mutunci gashi ya farka rigar. Allah ya so ta da vest a jikinta amma sharara ne har ana ganin Bireziyarta. Shafa ta fito hankali tashe tana tambayar Annah me ya faru? Be bi ta kansu ba ya barsu a gun bayan ya dauki farkaken rigar ya saka a Bolan kusa dashi yayi hanyar dakinshi yana cewa da kuci arzikinmu gwara kowa ya rasa. Ranan Har Daki Baba ya bi Zaid ya na ta tsinanshi kamar zai ari baki, shi ko Zaid din ko a jikinshi. *** Watan Mancy 9 ta haifi diyarta Mace mai kama da Babanta, sosai akayi murnar samun karuwa a cikin Dangi balle duk yaran Alhaji babu Mace, dangi daga Katsina da Kano sukayi ta zuwa barka. Hajia Luba ma ba a barta a baya ba don ta nuna Son Jaririyar. Ranar Suna diya taci sunan Hajiar Alhaji Abu wato Halima amma ana ce mata Mimi. Mimi na da Wata Biyar Autan Hajia Luba ya dawo daga Makaranta da sakamonshi na Masters wanda ya hado a Malaysia. Jawad Miskili ne, shine Autan Umma, yasan Babanshi yayi aure amma ba ruwanshi da Mancy, daga gaisuwa shikenan, be iya shiga wurinta ya zauna kamar yanda yayyinshi keyi, indai Sun hadu a Parlo yana mik'a hannu ya karbi Mimi don Mimi son kowa ce, baya ganan bai da matsala da Mancy. Wannan Kenan. Jaje suka sake yi ma Juna a Massalaci, Alhaji Ali ya sake tabbatar ma Mallam Muhammad kan cewa kar ya damu shi zai sake gyara Bangon Gidan. Kamar jiya Aunty Aseeyah ta tafi Gidan Iyayenta ta bar Labiba da niyyar in 10 tayi zata wuce Makaranta. Kamar Jiya haka ta sake sando ta shiga dakin Mankas, yana zaune yana cin Bread da k'wai. Kallo daya ya mata ya dauke kai, ko sau daya tunaninta bai fita daga kwakwalwanshi ba. Da murmushi ta ce "Ina kwana YaZaid". Shareta yayi ya cigaba da Breakfast dinshi ta k'araci zamanta bai tankata ba, ta mik'e da murmushi a fuskarta tace "ni na tafi Makaranta sai na dawo". Tak bai ce mata ba, haka ta fita ta barshi zaune ya bi bayanta da ido,ta tsallaka blocks ta fice abunta. Runtse ido yayi ya bude, zuciyarshi na mishi wani irin zugi, sigari ya dauko ya fara zuk'a cikin Zafin nama. Washegari Haka aka sake Wani Ruwan Saman Ginin ya sake Rushewa, sau 3 kenan kasancewar lokacin damina ne kusan kullum sai anyi Ruwan Sama. Hajia Shafa tace da Alhaji "wai kai ke da kudin banza? Kar ka sake ka kara gyarawa, in banda son banza shi ba zai gyara ba? Kuma su ma ake rufa ma Asiri tunda tsakar Gidansu ake gani, in abun ya dameshi ya gyara, kai kar ka k'ara Gyarawa kaji ai?" Da sauri Alhaji yace "Ba zan kara gyarawa ba, ai Muhammadu akwai son banza, ai kudin ba a bishiya nake katso su ba, in bai gyara ba ruwanshi". Da murmushi tace "yauwa Alhajina". "In har ba damuna ta tsaya ba, Ginin nan ba zai bar rushewa ba" Cewar Yaya Muhammad cike da damuwa. "To ya zaayi" inji Aunty Asiya. Baban Amira yace "wallahi ni kunyan Alhaji Zaki ma nike, ace duk rushewan da bangon yakeyi ko so daya ban taba gyarawa ba?" Tace "Ai ya san baka dashi kar ma ka damu". Yace "bari InshaAllah zan gaya mishi a bar gyaran haka har sai ruwa ya tsaya, in ba haka ba Allah na tuba asara zaayi tayi, anayi yana rushewa" Aunty Asiya tace "eh gaskia, Allah dai ya rufa Asiri". A zuciyar Labiba kuwa ba ma taso a gyara, ita bata k'i a zauna a haka ba, hakan ne zai sa ta ga Sanyin Idaniyarta, sosai take jin shi a ranta, yanzu ma Jira take Baban Amira ya fita ta faki Idon Aunty Asiyah ta shiga. Aiko yana fita tayi sadap sadaf ta fada Gidan Alhaji Ali. Ba tare da jira ba ta fada dakin Zaid wanda daidai yake da fitowanshi daga Toilet daure da Towel a k'ugunshi. Da sauri ta runste Idonta shi ko cikin zafin rai ya fincikota ya wurgata kan Gado yace "yau sai kin ci Ubanki, Wallahi yau ba zan daga maki ba". Gadangadan yayo kanta... Ghen Ghen. Whats about to happen? Anyone? Vote and comment line by line please #1love #DM #FWASonSo #anatare #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 Babi na Sha Hudu1⃣4⃣ (FUSHI😒😏) Jin tambayar tayi wani iri, shi kuma gani yayi kamar ba ta ji bane, ya sake maimaita mata, "kin bar So na ne? Me na miki to da zaki bar So na? Ki cigaba da So na, kar ki daina". Baki ta hangame ta na sauraro zantuttukan bakinshi, takaici ya turniketa, bai zo don ya fada mata yana sonta ba, ko kuma don yayi kewanta sosai, ta zata ya zo nemanta ne kamar yanda ya gaya mata cewa in tayi Aji k'ila ya kawo kanshi gareta, shin ba ta yi Ajin ba? Ko yin Ajin ya wuce Kama kanta na kwana biyu? Cikin daren nan zuwa yayi kawai ya gaya mata ta cigaba da sonshi? Seriously? Ya ma mugun raina mata wayau cikin zafin nama ta k'arasa wurin k'ofa ta bude ta sosai tace "Fita". Sosai yayi mamakinta amma abun mamaki shine yanda ta rikide ta chanza lokaci guda. A kausashe tace "ka fitar min a daki, kar kuma ka sake shigo min daki, duk randa ka fado min daki haka kamar yanda kayi, wallahi zan maka Ihun Barawo, tun muna Shaida Juna yanzu, ka fitar min a daki". Sosai yayi mamakinta, jiki a sanyaye ya daga kafaffunshi da kyar ya fita ta gabanta, yanayi yana waiwayonta, ya na sa k'afa ya fita daga dakin ta datse kofar da k'arfi tana numfashi samasama, hawaye ta fara, ta ba kanta wahala , ta wahalar da zuciyarta. Tashi tayi maimakon ta kwanta, sai ta cigaba da Sallolinta har bacci ya kwasheta a gurin. Zaid kam tunda ya bar dakin k’afafuwanshi suka mishi nauyi, da k’yar ya isa dakinshi, ya zube kan Gado. Hannun damanshi ya sa ya murji idon hagunshi, a baiyane yace “Mai ke faruwa da Beebs? Ya Allah!”. A haka ya yi bacci. Washegari bayan Asuba, be shiga dakinshi ba ya tsaya bakin kofa ya kwala mata kira a waya, no answer. Yana tsaye ya ga fitowarta daga daki, ta shiga toilet dauro Alwalan Asuba, minti 10 ya bat, ya tabbatar da idar da Sallahn, ya sake kira, bata amsa ba, haka yayi ta trying amma ba amsa karshe sai jin wayan yayi a rufe. Tsaki yayi ya ji kamar ya fada Gidan. Zama yayi dabas, a kan idonshi gari ya waye, kan Idonshi Yayanta ya fito dauke da dan karamin jaka da alama tafiya zai yi, kan idonshi Labiba ta fito don yi mishi sallama, tana fitowa kuwa ta kalli Inda Zaid yake, idanuwansu ne suka sark’e ma juna. Musayar Kallon kallo sukeyi ma junansu, ko wannensu da abunda yake kitsawa a ranshi, daga baya Labiba ta watsar ta bi bayan Aunty Aseey suka raka baban Amira har kofa yana ji suna mai Fatan sauka lafia kafin suka dawo suka shiga dakin Aunty Aseeyah. Muryar Dalo ta katseshi “Ina kwana Ya Zaid” firgigit ya juya ya kalleta murmushi suka sakar ma junansu kafin yace “Sadyn Mancy” karasowa tayi ta na kallon gidan Mallam Muhammad bayan ta zauna kusa da Yayanta tace “Mai ya faru nan?”. Zaid ya dan Kalleta yace “Sadiya Ali Zaki, anya kina Gidan nan kuwa?” tace “Yo Yaya yaushe rabon da nazo Boysquarters? Baka zama, kuma ko da yaushe kai ke zuwa, kafin nazo ka riga kazo cikin gida” yace “haka ne, ruwan saman da akayi last 2weeks me ya rushe bangon, an gyara amma ko kwan beyi ba ya k’ara rushewa, am not sure whats taking so long da ba a k’ara gyarawan ba”. Tace “ya kamata a gyara, wurin is too open, komai fa na gidan ana gani, they need privacy, ka san har tsakar Gida suke zama, bansan yanzu ya sukeyi ba”. Zaid ya murji idonshi yace “Na san Mallam Muhammadun bai da kudin siyan sabbin blocks da ya siya, don shine a takure” Dalo tace “ai baba ya kamata ya dauke mishi gyaran”. Zaid yace “ba wuya Matarshi ta hanashi gyaran”. Dalo tayi murmushin takaici tace “Allah shi kyauta”. “Ya gidan? Wa ke takura miki?” Daura kanta tayi kan kafadunshi tace “Ba kowa, sai dai Yaya, Uncle Hudu yayi ta sani dafa mai tea yana sa ina kai mishi daki, i dont like it”. Zaid ya cije baki har jijiyan gefen kunnenshi ya taso, yace “kar ki sake ce mishi Uncle, ba k’anin uwarki bane, kuma ya sake kiranki dakinshi karki je, ya sa annah, itace diyarshi ba ke ba, God meyasa ban ma ga hatsarin zaman shi cikin Gida ba? Da sakel, ba zaiyiwu ba ma, wait, dalo, tsaya, tun zuwan su Hudu Gida, ya ta ba miki wani maganar Banza, ko ya tabaki ko ya rik’eki?” Da sauri ta girgiza kai tace “aa” yace “Ko so daya?” ta gyada kai tace “eh be taba ba, da fa baya min magana, ko Aunty na zagina tayata yakeyi, amma just recently ya fara sa ni aiki, yana cewa in kawo mishi daki”. Murmushin takaici yayi yace “He is developing intrest in you, aiko zai ci ubanshi, wallahi billahi ya tabaki sai na kasheshi”. Firgita tayi sosai, Tsoro yayanta ya bata, bata taba ganinshi a irin yanayin nan ba, yanzu ta ankara da wani irin magana yakeyi irin ta ‘yan sara suka, yan daba. Sai tayi nadaman gaya mishi, tace “Yaya, be fa min komai ba” Zaid yace “Stay the hell away from him, duk randa yace ki dafa mishi ruwan zafi kice ba zaki iya ba, ke ba yar aikin uwarshi bace ba, in kuma ya matsa ki zo ki gaya min kinji ai?” Yaya “ba zan iya mishi rashin kunya ba” tureta yayi yace “nikuma ki bijire min, zan ko ci uban Hudu”. Da sauri tace “yaya kayi hakuri, ba haka nake nufi ba, kayi hakuri donAllah, yaya wallahi be ta ba min wani magana ba, ruwan zafi kawai yake cewa inkai mishi, i am not complaining, i just dont feel comfortable entering his room, amma in ya min wani abunda ba shikenan ba, yaya zan gaya maka, kayi hakuri donAllah, ban son tashin hankali kuma”. A hankali yake sauke numfashi, zuciyarshi na danyin sanyi, kallonta yayi, suka sakar wa juna da murmushi, tace “Yaya ka kira min Mancy, banda kudi a wayata” ‘yar nokia dinshi da ta ci robali ya miqa mata ta bi wayar da kallo, bata ce komai ba ta kira Mancy. Da farinciki suka fara waya da Mancy, aka bata Mimi suka gaisa da gwalondonta. Shima ya amsa wayar suka gaisa da Mancy da Mimi. Kamar kullum Mancy ta tambayeshi akwai wata damuwa? Sai yace “aa” sai tace “zan aiko maku da sak’o a account Allah ya muku Albarka” suka amsa da Amin. Fitowa Labiba tayi idonta kan wata wanda ta jingina da kafadun Zaid, gabanta ya yanke ya fadi, zuciyarta ya fara dukan uku-uku. Aunty Aseeyah da ke bayanta ta karasa fitowa daga Dakin, inda Labiba ta ke kallo ta bi da kallo. Ameerah da Sabit ne suka fito suma, hayaniyansu ya sa Dalo da Zaid maida kallonsu ga Gidan Mallam Muhammad. Da sauri Dalo ta mike da faraa a fuskarta ta tsallaka zuwa Gidan. Labiba kam ta hade girar sama da k’asa, wacece kuma wannan? Itace Yesmin ko? Me za ta zoyi? Kafin ta ankara taji muryan dalo na “Allah sarki Ameera da Sabit nayi missing dinku”. Labiba ta waiga taga Sabit da Amira jikin budurwar Zaid, suko sai dadi suke ji suna murna. Labiba ji take kamar ta finciko yaranta. “Sady ya kike kwana biyu?” Dalo tace “Allah sarki Aunty Asiya, ina kwana?” “Lafiya lau ya kuke?” Wallahi lafiya lau, ta juya ga labiba da murmushi a fuskarta tace “Ina kwana?” Labiba fuska murtuk ta raisayar da kanta kamar bata ji ba, dalo kam bata lura ba ta juya ga Aunty asiya tana tambayarta ina baban su amira, “be dade sa fita ba, Maradi zaije” Abunda Labiba tayi tsaf kan Idon Zaid, sai ya ji haushi, wato fushin da ake dashi ya shafi k’anwarshi ko?. Aunty Asiya tace “yanzu Sadiya zumunci yayi wuya? Kina nan? Bakya lek’o mu duk tsawon shekarun nan? Tunda Mancy ta bar unguwar nan ban k’ara ganinki ba Sadiya, sai dai Baban Amira yace min yana ganin DanMakaho a hanya ko Masallaci”. Dan yak’e Dalo tayi tace “ Aunty Asiyah Wallahi ba inda nake zuwa, ina gida ko da yaushe, baba ya hanani fita, ya sa tsaro a kaina, tunda nayi Candy ko bakin gate ban zuwa wallahi, kin san yanda abubuwan suke, wallahi ko gun Ya Zaid bana zuwa shi ke zuwa inda nake, ni na ma fi san zaman daki, kin san komai Aunty Asee, amma da na san bangon nan ya rushe ai wallahi da zan dinga zuwa ana gaisawa, sai yanzu fa da na zo gun YaXaid naga wai ashe bango ya rushe”. Aunty Asiya ta jinjina kai cike da tausayin Dalo tace “na san Komai Sady, ba wani abu, ku cigaba da hakuri, mahakurci mawadaci”. Yak’e mai kama da kuka Dalo tayi tace “barin koma kafin ya zama wani abun, sai anjimanku” ta kalli Labiba da ta daskare a lokacin da ta fahimci Dalo ita ce Kanwar Zaid, wanda kishi? Eh kishi ya hana gane wacece”. Aunty Asiya ban gane wannan ba, Aunty Asee tace “Labiba ce Kanwar Baban Ameera, karatu take a Poly”. Dalo tace “Ayyah, Allah ya bada saa, sai Anjimanku”. Labiba ta sakar mata da murmushi mai kayatarwa, tayi dana sanin rashin amsa gaisuwarta, ta na so ta samu lolaci da Dalo, tana so su saba, ashe haka take? Tana kama da Zaidunta, son da take ma Zaid ya shafi Dalo, sosai ta ji tana k’aunar k’anwar Masoyi. Sauri-sauri gudu-gudu Dalo ta koma inda Zaid yake, har yanzu yana nan tsaye inda ta barshi, hannu ya daga ma Aunty Aseeyah da yaranta, suma suka daga mai hannu, ya kalli Labiba ya riko hannun Dalo, yace “oya wuce ciki kafin Baba ya tashi ya ga ba kya nan, kinyi breakfast?” Ta girgiza kai “Aa” yace “barin je in siyo mana K’osai, ki dafa mana tea sai mu sha da bread da kosai”. Tace “Okay Yaya, barin je kafin ka dawo, daki ya shiga, ita kuma ta wuce cikin Gida, sai gashi ya fita kuma, duk kan Idon labiba. A kitchen ta iske Aunty Asee ta na hada Tea a k’aton Jug. Kafin tayi magana tace “Lab kece ke ta son ganin Dan Makaho, to wannan shine dan Makahon” wani murmushi tayi tace “Aunty, ashe wannan itace k’anwar DanMakaho kenan” “Eh Labee, itace, Sadia, kai Allah ya isansu, wallahi duk tayi bak’i ta rame, baiwar Allah”. “Aunty, meyasa ba kya shiga Gidan” Aunty Aseeyah ta zaro ido tace “niii Lab? Ni gidan Alhaji Zaki? Wurin wa? Wurin Hajia Shafa? To har gobe ban san kamannin Matar ba, ko mum hadu be wuci randa aka saki Mancy ba, da duk yan unguwan suka shiga Gidan, amma wallahi ba zan iya shaidata ba, to wannan matar Anamimiya mai zanje na mata? Matar da bata tsoron Allah? Ba abunda zanje yi Gidanta wallahi”. Labiba ta jinjina kai tace “haka ne, amma zumunci ai daban yake, yanda kukayi zaman kirki da Mancy, ya ci ace ba ku hofintar da ‘yayanta ba, kamata yayi ace kuna duba yaranta, musanman ma Sadiyan da take mace. Kallo daya Aunty Asee ta mata ta juya ta cigaba da motsa sugar, wata sa’in Labiban bata ganewa, kamar mai jin magana ta guiwa. Labiban ma shiru tayi tana tunanin Yanayin da ta gani a idon Masoyi dazun. Da Yamma Zaid yayi ta kiran Labiba, ta k’i dagawa, ta na gani, shikuma duk inda ranshi yake ya baci, wai meye haka? Wai don me zai dinga kiranta? Mai ya sa ma ya damu? Dan uwarta, don ta ga yana bibiyanta, shine zata dinga ja mishi Aji? Murmushi ya subuce mishi ba tare da ya sani ba. AJI? Aji? Hahahah Aji? Ajin kenan? Fushi tayi wai dama? Hakan ne? Ko kuma wani abun ne? Tsaki yayi ya jefar da wayar tare da kwance k’ullin World ya hau zuk’a. Bayan Maghrib ya farka, jikinshi duk ya mutu, da k’yar yayi wanka, ya rama sallolin da ake binshi, ya kasa hakuri, ya lalubo wayarshi ya fara dialing wayarta, ringing take tayi, tana rejecting, sosai ranshi ya baci, ya buga tsaki ya dauko Sigari ya kunna mata wuta, ya fito waje yana zuk’a don yana da tabbacin ba zai ga Dalo waje a daren nan ba, waje ya fita, zaije benchin Eskaley, don in ya tsaya a gidan nan, ba abunda zai hanashi afkawa gidan Mallam Muhammad. 7:50pm A bencin Eskaley, Mankas ya daura k’afa daya kan daya yana shan Sigari na 11 tun bayan fitowanshi daga Gida, Yana kallonsu suna ta gardamansu kamar yanda suka saba. Kamar daga sama ya hango wata daga nesa mai irin tafiyarta, rike da yara biyu, ko idonshi ne? Da sauri ya girgiza kai, ita ce, zumbur ya mik’e, me ya fito da ita da daren nan? Ina zata? Ita da Amira da Sabit, ina zasu, jira yayi ta k’araso, amma abun mamaki, wurin su ta nufa, Bencin Eskaley ta tunkaro, mamaki yake, mai ya kawota? Ko ta kasa hakuri ne ta biyo shi? Ko taje daki ta ga baya nan sai tace bari ta biyo shi Bencin Eskaley? Bari dai ta k’araso”. Da Sallama ta k’araso gurin, bata kula su Master da ke ta fadin “yayarmu barka da fitowa” ta wuce gaban kiosk din Eskaley tace “Akwai Shafto?(Mosquito Coil?) Eskaley yace “eh akwai” “ a bani Kwali daya” ta mik’a dari biyu ya dauko ya bata, ta amsa ta juya, ba tare da ta kalli gefen da Zaid yake ba, ta san yna wurin, jikinta ya bata lallai Zaid na wurin”. “Wai ya? Ana miki magana kina jinmu? Haba yayarmu yawa kike” cewar su Master. Dan Makahon da ke zaune, Mamaki ya gama kasheshi, wato ba shi ta zo nema ba, ba ta shi take ba?tsaki yayi mai karfi ya murje guntun sigarin da ke hannunshi ya rufa mata baya, mai su tero zasuyi? Shewa suka fara suna tafi. “MANKAASSSS” “Sai Mankassss, shawo mana kanta, ita yar jami’ah bata wa mutane magana, saito mana ita”. “Uwarku!” Kadai yace ya cimma Labiba da ta gama jin duk abunda suke cewa. Sabit ya daga Sama, Labiba bata ce komai ba, a jikinshi ya kwantr da Sabit, ya dinga binta, Amira tace “Ya Zaid me kakeyi a Bencin Eskaley? Da sauri yace “Uhm Uhm Amira, naje siyan maganin sauro ne” tace “lahh muma shi mukazo siya” yace “Me yasa baku zo tun dazun ba sai dare? Kuma ina babanku? Mai yasa bai zo ya siya da kanshi ba?”. Amira tace “Abba yayi tafiya, Aunty Lab bata san ya k’are ba, sai yanzu da zamu kwanta, tazo daukowa taga ashe ya kare, kuma sauro dakinmu, in ba da shafto ba cizonmu zasuyi, kuma ba mai siyowa, shine Aunty Lab tace Umminmu ta bada kudi mu siyo, Ummi tace ko ta fito muje tare duka, sai Aunty Lab tace aa, ta bari muje mu siyo, umminmu tace mu bi a hankali, bencin Eskaley ba mutanen Kirki, shine Aunty Lab tace “ita ina ruwanta da su? Shafto kawai zamu siyo mu dawo”. Labiba tayi mamakin surutu na Amira shi ko Zaid ya jinjina kai yace “Aunty Lab, kika ce ba ruwanki da yan Bencin Eskaley?” Banza tayi ta kyaleshi ta cigaba da jan Amira suna tafia, daidai kunnenta yayi kasa da murya yace “har ni ba ruwanki dani?” Tak bata ce mishi ba, yayi ta magana tak’i amsawa yace “baki min magana wai? Fushi ake dani? Eh Beebs? Fushin ne har yau? Ki gaya min ne na miki? Beeeebs kina fa jina, mai Masoyi yayi? A ma Masoyi hakuri to, Daria ta so kufce mata amma ta dake daidai isowarsu Gida, mik’a mishi hannu tayi alamun ya bata Sabit. Sake mata Sabit yayi yace “Seriously? Seriously Beebs? Ba zaki ce min komai ba?DonAllah Fushin ya isa haka”. Bata amsa shi ba ta shige Gida ta barshi tsaye a wurin. Gida ya wuce shima rai a jagule, be samu zuwa gun Dalo ba ya shige daki ya banki World ya kwanta ruf da ciki bai farka ba sai k’arfe 9 Washegari Lahadi. Ya Tashi ya fada toilet yayi wanka yayi Alwala, ya dauko Jallabiyarsa yayi Asuba, yana idarwa ya chanza zuwa Riga Body Hug da 3quater wandonshi irin na sojoji, ya dauko Face Cap ta k’wama a kanshi ta baya, ya fita don shiga Cikin Gida. Suna kan Dining Table gabaki dayansu banda Dalo, dakinta ya wuce Straight, ya ganta zaune tana shan Shayi da Bread, gaisheshi tayi da murmushi a fuskarta ya amsa yace “kin tashi Lafia? Ta amsa da lafia lau” yace “zakici abunda suke ci kan table?” Da sauri ta girgiza kai tace “aa wallahi, na k’oshi da wannan ma” ta san in tace eh zataci zuwa zaiyi ya debo mata, kuma ayi rigima Babba. Yace “Okay, kun gaisa da Mancy yau?” Tace “eh munyi waya da Asuba” yace “ naga missed call dinta ina bacci, zan kirata zuwa anjma”. Barin je in nemi abinda zanci” be jira amsarta ba ya fita yayi hanyar Kitchen. Baba, Aunty Shafa, Hudu, Annah ne kan table suna cin Shagali, kallon table din yayi baida niyyan gaida uban nashi balle matarshi, haka kurum yau yaji yana son cin Abincin. Kitchen kawai ya shiga sai gashi ya fito da Plate da fork, duk suka zuba mishi ido, coolern ya bude ya zuba Dankali, ya zuba sauce din Hanta, ya dauko kwai, baki bude shafah ke kallonshi, baba ko daure fuska yayi ya cigaba da cin Abicinshi. Shafa tace “na shiga Ukuna, Alhajina kana kallonshi ko gaisheni beyi ba zai ci min abinci, ni baiwarshi ce? Ni banda matsayi a gurinshi na girmamawa ina matar ubanshi? Gaskia ya ajiye min Abinci”. Haba Kamar an kunna TV baba ya fara Bambamin bala’i Yo ina zai gaishe ko? Ya gaisheki yana watsatsatse? Kina gani ko ni Mahaifinshi be min kallon kirki ba balle ke matata? Tsinanne, shege, Allah ya kwashe maka albarka Zaid”. Ko a jikin Zaid don daukar Plate dinshi yayi, fork din ya sa cikin plate din Shafaatu ya chaki hanta ya sa a baki, ya karama wandonshi iska, kamar an kunna baba, ka dawo da abincin nan dan shegia, ka ci Abincin nan Allah ya isa tsakanina da kai, ina Zaid ko waigowa beyi ba, ya wucewar shi dakinshi. Dalo kuwa ta fashe da kuka a daki. Shafa ko in ranta yayi dubu ya baci don raini harda caka mata fork a plate dinta? Lallai Zaid dan duniya ne, wallahi maganinshi zatayi, shi ko Baba yayi ta haushi kamar tsohon Kare. Bayan La’asar Yara na Islamia Labiba ta dauki wayarta da ke Ringing taga Abu Sideeq ne ke kiranta, da sallama ta amsa yace “Hajajju, ya kike?” Daria tayi tace “Lafia lau Alhaji bu Sideeq” yayi daria yace “wallahi Baba ya aiko ni wani Gida a Tudun Matawalle, har na kawo sak’o na tuna Unguwar fa kike, niko nace ba zan bar Unguwar ba sai na ganki sanyi idona”. Tayi daria tace “rigima, kai da zamu hadu da kai gobe?” Yace Uhm Uhm, ban yarda ba, ni gaskia ki mun kwatance, in zo mu gaisa, ko 10mints ba zamu wuce ba donAllah don Annabi”. Bata so yana mata magiya, tace “to sarkin Magiya, ka tambayi Gidan Alhaji Ali Zaki, in kazo ka kirani” yace “to shikenan”. Aiko da kwatancen ya k’araso Gidan Ali Zaki, don gidan a Unguwar Tudun Matawalle ba 6oyayye bane. Kiranta yayi yace mata yazo, tace to gani nan zuwa, hijab dinta ta saka ta shiga dakin Aunty Aseey tace “aunty bari in dan gaisa da dan makarantarmu, gashi wai yana waje”. Daria tayi yace “ke dai ko dan samrayin ne?” Labiba tayi daria tace “haba dai” ta fita. Baki Gate ta sameshi, ta mishi alama da ya karaso kofar gidansu, ya dan tako ta murmushi dauke a fuskanshi. Ko gaisawa ba su kai ga yi ba, sai ga DAN MAKAHO kamar an jefo shi, bai ganeta ba daga nesa, sai da ya zo kusa ya ganeta, daga nesa yake hango dariyarta, kamar gudugudu ya karaso garesu kamar zai bugeta, da sauri tayi baya. Abu Sideeq yace “Mallam Yadai?” Labiba tace “kar ka kulashi, kyaleshi Abu Sideeq, dan shaye shaye ne” DanMakaho bai damu da maganganun da ke fita daga bakin Labiba yace “Beebs, waye wannan?” Maimakon ta amsashi sai cewa tayi “Yanzu Abu Sideeq saura kwana nawa a fara Exams?”. Abu Sideeq yace “less than 2 months fa” tace “wow ashe bamu da time sosai”. Su ka cigaba da firansu ba tare da kula DanMakaho ba, yanda Labiba ke daria ya fi k’ona ran Dan Makaho. Yace “Beebs kice mai ya tafi please” Labiba ta ki cewa komai, Dan Makaho ya juya ga Abu Sideeq yce Mallam ka bar nan Unguwan nan yanzu” Abu Sideeq yace “Meyasa? Unguwar Babanku ne?” Labiba tace “Haba, nace kar ka kulashi kaima”. Dan MAKAHO yace “Eh, kalli chan, ka ga sign an saka Ali Zaki Street ko? To Ali Zakin Babana ne, so ka bar Unguwar nan”. Abu Sideeq yce “kinga Labeey ki rabu da irin yan shaye shayen nan, haka zasuyi ta uttering nonesense in ana shiru ana kyalesu”. Yace “to ka fitar dani in kana iyawa” Zaid yace “my Pleasure” Gefe ya matsa ya ciro wayarshi, suna kallon yana waya ba su tanka mai ba, ba su san da wa yayi waya ba, sai kawai su ka cigaba da firansu. Cikin Mintunan da ba su kai 5 ba sai ga Yn Bencin Eskaley kusan su 9 a guje, kowanensu da makamin shi a hannu, masu Gora, sanduna, Wukkake, Zarto da wasu Makamai irin na ‘yan sara suka, ganinsu ya sa yan Unguwa rugawa, ganin wurinsu suka nufo Abu Sideeq da Labiba suka hada baki wurin Fadin “Inalillahi wa ina ilaihir rajiun”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉 BABI NA SHA SHIDA1⃣6⃣ (Zumunci🤝) Hannuwanta ta daura a kan k'ugunta cike da masifa tace "wai menene haka? Meyasa kake min haka DanMakaho? Dazun ka tozarta bak'o na, yanzu har kana da guts din threatening dina? Zaka sha Giya? Really DanMakaho? Zaka sha Giya? To ka sha mana, ai naga ba a cikin Littafina zaa rubuta maka zunubi ba ko? Sai abu na k'arshe, kar ka sake gigin shigo mana daki". Sosai ya ke kallonta, ya sasauta murya yace "why are you doing this? Meyasa kike yin haka?". Cikin dan daga murya tace "meyasa nake mene? Me na keyi?". "Da bakinki ki ka ce kina So na, da bakinki kika ce ba tausayina kike ba, me ya faru? What happened?". "Huh, da bakinka kace in Sonka nake na bari, baka bukatar a So ka". Da sauri yace "amma ai ko da nace haka baki bar So na ba. Ko da na ce haka ai ba kiyi paying mind to it ba, baki damu da abunda nace ba, kawai kin cigaba da sona baki fasa abunda kike ba why now?". Cikin Zafi tace "nagaji, na daina, ba zan iya ba kuma". Shima cikin zafin yace "Uban wa yace ki fara dama? Ban sanki ba, kika nema na sanki, ki ka shiga rayuwata, ki ka kutsa sai da kika san labarina, ki ka sa na fara sabawa dake, kika min sabo dake, sai yanzu na saba da ke, zaki ce min wani kin gaji? Meyasa kika fara abunda kika san ba zaki jure ba? Uban wa yace ki shishige min, uban wa yace ki ce kina sona ba tausayina kike ba? Uwar wa yace ki min sabo da kanki in kin san akwai ranar da zaki toshe ni?". Chan kuma yayi dan jim, kafin ya ja numfashi ya karya harshe cikin sanyi k’wayar idon shi a nata “look, i’m sorry i lost it, kin saka na daga miki murya, please, in ma wani abu na miki, kiyi hak’uri, we can sort it out, kinji”. So biyu ta kyafta idanunta kafin tace “Haqqun, So Gaskia ne, bani na daura ma kaina Sonka ba fa? Allah ne, kuma shi zai yaye min, yana kan yaye min ma” ta juya da sauri ya sha gabanta yace “DonAllah kar ki bari, kar ki bar So na”. Cike da fada tace “nikuma in Allah yayi dunia don Manzo”. Da sauri ya sa hannu ya rufe mata baki yace “ba zaki bar so na ba, zaki cigaba da So na, zan ji dadi in kika cigaba da So na kinji,?”. Takaici kamar ya kasheta, ba abun da ta ke son ji ba kenan, ba ta fito don ya ce mata kar ta bar sonshi ba, ina laifin ya bata hakuri yace “yana sonta shima, ko bai ce haka ba ina laifi yace “zan koya son ki? Ya dai nuna mata tana da mahimmanci a rayuwarshi, ko bata da shi ya nuna mata nan gaba zata iya zama mai mahimmanci a wurinshi, ba wai ya kalleta yace kar ta daina sonshi ba, ko kuma ta cigaba da sonshi, wato bata da wani amfani, ta cigaba da bibiyanshi yana jin dadi yana ya6a mata maganganu, abunda yayi kewa kenan, ko kadan be yi kewanta ba, bak’ak’en maganganun da yake gaya mata ita kuma bata zuciya yake missing. Taku biyu tayi da baya da baya kafin ta juya, hannunta ya rik’o, tana juyowa ta kamtse shi da mari, kafin ta juya da sauri don komawa Gidansu, bai damu da Marinshi da tayi ba, sunanta ya fara kira. “Biee, bieebs beeebs tsaya mana kiji”. amma bata tsaya ba sai da ta shige dakinsu ta datso da karfi kafin ta sa hannu biyu ta rufe bakinta saboda wani kuka mai k’arfi da ya zo mata. Cikin Bacci Aunty Aseey tace “Labs, kece?”. Labiba ta saita kanta tace “Uhm,toilet naje” Aunty Aseey bata tanka ba ta koma bacci, ita ko Labiba kuka take a hankali, zuciyarta na mata zafi, bata taba jin kwatankwacin abunda Dan Makaho ya sa ta ji ba, ba komai. Mankas fa? Zaune yake kan dakali yana kallon hasken farin wata, me yace? Me yayi zafi? Me ya mata ne ta tsaneshi kwana biyu? Bibbs dinshi, to shi fa be san me yayi ba, and she’s not even talking balle ya san me yayi so wrong” da kyar ya samu ya shiga daki ya banki world dinshi kafin ya kwanta bacci. Washegari Da Misalin k’arfe 10 na safiyar ranar Litini, Wanka Zaid yayi kafin ya shiga Gida ya hada breakfast dinshi ya shiga dakin Dalo ya tambayeta in akwai wani damuwa, babu ta ce mishi, yace “ni yau ziyara zanje” dariys tayi tace “da ina da ina zaa?” Yace “yau ai sai inda mai ya k’are”. Daga Dakin Dalo ya fita daga Gidan, daidai da fitowar Labiba daga na su gidan don yau Lectures din rana gareta. Ido cikin ido suka kalli juna, ita ta fara dauke ido kafin shima ya cire nashi, gaba tayi kafin ya rufa mata baya har ya cin mata ba tare da daya daga cikinsu ya ma danuwansa magana ba, kuma duk bakin titi suka nufa, ba su kula junansu ba, daga nesa zakayi tunanin jerawa sukayi amma wai nan fushi sukeyi da junansu. A bakin titi suka rabu inda Labiba ta hau Keke Napep, shi kuma ya tsaida Okada ya hau. Tunda ta shiga Department take baza ido neman Abu Sideeq, wayarshi bata shiga, a daddafe tayi lectures, suka fito Aisha tace “ke wai ya? Duk baki da sukuni,Lafia?”. “Hmm, Wallahi Besty jiya Abu Sideeq yazo Anguwarmu, kinsan ‘yan shaye shaye, suka tareshi suka mishi barazana, wai kar ya sake zuwa Anguwar, to tun jiya nake ta kiranshi na bashi hakuri sam wayar tashi bata shiga”. Aisha tace “Ahh, lallai kila yayi zuciya” labiba tace “muje donAllah ki rakani Ajinsu”. Suka fita tare. Abu Sideeq bai zo ba, hankalin Labiba ya tashi, ko dai Mankas karya ya mata, sai da suka ma Abu Sideeq wani abu, aiko ranta ya baci, ga fargaba kuma. A daddafe ta koma Gida. Family House din Alhaji Zaki ya nufa, Gida ne da duk k’annen Alhaji Ali ke zaune saboda part part ne a gidan wanda Alhaji Alin ya gina ya mallaka ma k’anenshi. Da sallama ya shiga Gidan Gidan Baba Sani ya fara Shiga, immediate din Babanshi, da yake baya aiki ya iskeshi, sosai ya gaida kawunshi, ya tambaya ‘yanuwanshi akace sun tafi makaranta. Baba Usman ya shigo yace “Ahh lale, mallam Zaidu ne a gidan namu” da faraa Zaidu ya gaida Baba Usman, Ya amsa, kusa da yayanshi ya zauna. Baba Sani yace “Zaid ina Sadiya? Yaya take rayuwa a cikin Gidan nan?” Murmushi Zaid yayi, yace “Kawu ta nan lafiya, ya dai hanata fita,jiya na mishi maganar ya barta ta fara zuwa koyon sana’a ya k’iya”. Kawu Usman ya girgiza kai yace “Allah ya isa tsakaninmu da Makirar Mace irin Hajia Shafa’atu, wannan mata ta cuce mu ta zalunce mu”. Kawu Sani ya murmusa yace “Shi Allah fa baya bacci, wallahi koman nisan Jifa, k’asa zai duro, a dade anayi sai gaskia, ku dai muje zuwa” Kawu Usman yace “kullum ina k’ara godewa Allah da ya sa Inna ba ta rayu ta shaida wannan kayan bak’in cikin ba, sai bayan ranta abubuwan nan ke faruwa, Yayanmu Gatanmu rana daya aka shiga tsakaninmu” ya karashe kamar zaiyi kuka. Kawu Sani yace “wai Yaya Ali ace bai da mak’iya sama damu? Mu shak’ikanshi? Ace mune baya son gani, mune ya hana zuwa inda yake, bama Gidanshi ba, anguwan da yake ya mana iyaka? Hmmm”. Charaf Baba Usman yace “ka tuna min lokacin da ya sa aka kullemu a police station wai don munje Gidanshi, Matarshi ta sa ya datse duk wata alak’a damu, babu zumunci, ‘ya’yanmu ba sa zumunci da ku, wannan Matar Allah ya tsine mata yanda ta shiga tsakaninku, ni tsorona kar Dalo tayi tunanin Dangin Ubanta sun yadasu”. Zaid yace “Kuyi hakuri Kawu, ba wani abu ai Dalo ba yarinya bace, ta san an fi karfinku ne, ta san komai tunda ko nan da kofar gate din Gida an mata iyaka, kuma maganar zumunci ni zan dinga zuwa InshaAllahu ina sada zumunci da ku da ‘yanuwa na, mun san cewa baku yada mu ba”. “Haka ne, Allah ya isar mana” kawu Usman ya amsa da Ameen. Kawu Sani yace “Ya Hajia Maryam?” Zaid yayi murmushi yace “tana Abuja”. Yace madallah in kunyi waya ka gaisheta donAllah” Zaid yace “zataji”. Hannu ya saka a Aljihu ya zaro kudi naira dubu biyu ya ajiye gaban Baba Sani yace “Kawu kwayi Cefane”. Da sauri kawun ya ture kudin yana “Allah ya sauwak’e, Allah ya sauwak’e mu karbi kudinka Zaidu, muna k’annen mahaifinka bamu baka ba, bamu taimaka muku ba shine kai zaka bamu kudi?Aa sam, ko alama”. Kawu Usman ya chafe yace “wallahi Zaid bamu da shi ne shiyasa bamu taimaka muku, to dama Yayan ne gatanmu shine k’arfinmu, to Shedaniya ta shiga tsakaninmu ta rabamu dashi, buga buga muke, da k’yar muke samo ma iyali Abincin da zasuci, wallahi shiyasa bamu tsinana ku da komai alhalin kune abun tausayi, donAllah kar ku ga kamar mun yardaku”. Zaid ya gyara Zama yace “Ko Daya Kawu, ku ji da kanku, mu wallahi a wadatace muke, duk wata sai Mancy ta turo mana kudi, wallahi ba komai, haba kawu, mu duka victims ne, akwai ranar da Baba zaiyi kuka da idanunshi, zai durukusa gabanku ya rok’e Ku gafara kan abunda ya maku, yanda ya wulakanta zumunci Allah...” bai samu ya k’arasa ba sakamakon rufe mishi baki da Kawu Sani yayi. “Kul Zaid,kul kar ka furta mugun Alkaba’i kan mahaifinka, wlh ba yin kanshi bane” “Allah ka tsine mata, ka kwashe mata Albarka, kai dama bata da wani Albarka, Allah ka watsar da ita”. Cewar Kawu Usman. Zaid dai ya juya kanshi karin ya mik’e tsaye yace “barin shiga gidansu Kawu Labaran”. Karan Sigari Kawu ya hango a Aljihun gabanshi. “Yanzu Zaidu baka bar Shan Sigarin ba? Har wannan tabar ta wiwi ba ka bar sha ba ko? Anya Zaidu” Shafa kai yayi cike da kunya yace “Na bari ban k’arawa” Kawu yace “karya kake, haka kace kwanaki da kazo” Zaid yace “InshaAllah zan bari, donAllah ku min Addua”. Cike da tausayi kawu Sani yace “Allah ya sa ka bari, Wallahi hayak’i mugun abu ne, na san illarta tunda nima gashi nan ina fama da ita, in na fara Tari kamar zan taro hak’ark’arina, kai ko da kuruciyarka, Allah ya shirya ka Zaid”. Ameen ya amsa tare da fita da sauri. Albarka suka sa mishi tare da daukan kudin da ya bari. Haka Zaid ya zagaya duka gidajen K’annen Babanshi, suna sa musu Albarka shi da kanwanshi, kuma duk Gidan da ya Shiga sai an kwashe ma Shafa Albarka an tsine mata, da Alama kullum sai an tsine mata a gidan nan. Sallama yayi dasu duka kafin ya kama hanyar Gidan Goggonshi Asabe daga nan zaije Gidan Goggo Ladidi. Da Murna Goggo Asabe ta taryeshi, ta rasa mai zata bashi, kame kame kawai take, ita mijinta ba mai k’arfi bane, dama duk Alh Ali ne gatansu, tunda ya zame hannu kan lamarinsu duk suka tagayare, ina Shafa zata da duk hakk’in wadannan mutanen?. “Kai Allah ka tsine ma Shafa’atu, dan Uwar Matar nan da Girman Ubangiji Allah sai ta wulakanta tun duniya kafin ta je Lahira, Matar nan bata tsoron Allah, k’iri k’iri ta juya mana kan Wanmu mai k’aunarmu? Ta rabamu da ku? Ba mu da halin zuwa ko da Anguwarku balle Gidanku? Allah ka isar mana” shidai Zaid yak’e kawai yakeyi, yau ya san baida labarin da zaiji da ya wuce tsinewa Aunty Shafa’atu” haka suka danyi fira ya bata naira dubu itama kafin ya hau Achaba zuwa Gidan Goggo Ladidi. Sosai ta ji dadin Ganinshi, da ban hakuri ta fara na rashin kiransu a waya ta ji ya suke, kafin ta la’anci shafaatu. “Hmm Zaidu, da Inna na nan da kila da bakincikin Mahaifinka zata koma ga Mahallicinta, duk da ba yin kanshi bane Allah ka ma Matar nan abunda ta mana, wai ni zanje gurin Yaya neman taimako kan ya ma Hajara Gado da Kujera lokacin da zatayi aure? Matar nan ta sa Yaya ya min Wulakanci, ya sa aka firdani kamar kayan wanki, tare da bige min warning kar na sake zuwa Anguwar? Aka sake gani nan sai na kwana police station? Ni Ladidi ciki uwa daya uba daya? Rannan na kwana kukan bak’inciki”. Zaid ya bata hakuri, suka jajanta wa juna kafin ya mata ihsani yayi sallama. Haka kurum yake jin dadi, ya sada zumunci, ya samu Albarkan Magabata. “Uhhh, yau kunanshi ya dade yana jin tsinuwa da la’anta kalakala, its time for nishadi”. Ya murmusa tare da tsaida Okada yace “ka kaini Layout Gidan Habibu Lema”. Wayarta ya kira, sai da ya matsa da wayar gefen kunenshi saboda hargowarta wurin kiran “Helllo” idonshi ya juya yace “Nene, ina k’ofar Gidanku” “to to gani nan fitowa”. Ba jimawa sai gata kuwa “Takwaran Zaidu bawan Allah” ya gaisheta ta amsa, tace “uban me ya sami idonka naga sun kara k’ank’ancewa?” Murza na hagun yayi ta sa hannu ta daka mai duka. “Wai ba nace bana so kana taba idon nan ba?” “Nene wai sai yaushe zaki bar dukana?”. “Sai randa ka bar shan wall yake ko uban wa?”. Yace “World”. “Oho, ina ruwana da shi tunda ba sha nike ba? Meyasa me ka ne? Kayi bacci kau jiya? Ko baka lafia? Ka kara bak’i ka sake kazancewa” “Kai Nene banson Wulakanci”. Dan shiru yayi kafin ya gyara tsayuwanshi yace “Nene, akwai wata makwabciyarmu” Charaf tayi tace “Son ta kake?” Da sauri ya girgiza kai yace “AA ita ke Sona fa, ita fa ta furta min So, gatsau fa tace min Sonka nake, dagaske nake sonka, can you imagine” Nene ta bishi da wani kallo raini ta na mai bura hanci tace “to sai me? Nace sai me? So nawa akayi? Allah ya ji k’an Mamman, da bakina nace mishi yana burgeni, kuma na gaya ma Mahaifina, Babana ya samu Babanshi yace ya ba Mamman ni, har ya mutu yana gode ma Babana”. Zaid da mamaki yace “Nene kece kika kai kanki wurin Namiji?” Tace “kai Arr yi man shiru, in son Labarin kake ka zo na baka, amma yanzu gaya man kana sonta?” Yace “kawai na damu da ita ne, haushi na takeji, banson ko ta bar so na ba”. Nene tace “to me zai dameka in ta bar sonka? Ai ba sonta kake ba ko?”. Da sauri yace “aa ai na saba da ita ne”. Nene ta buga tsoki tace “kai Gele, sonta kake, ko ka furta mata So, ko ka rasata gabaki daya, kai ni nagaji da tsayuwa, sai munyi waya tunda baka shigowa”. Shigewa zatayi ta barshi tsaye baki a bude, “Nene wai meye haka? Ke da nazo wurinki muyi fira?” “Nagaji nace,gashi warin sigari kake, amai nikeji” ta shige ciki yace “lallai tsohuwarnan ta ci uwar rainin wayau” daga ciki ta bude murya yanda zaiji tace “Uwarka”. Tsaki yayi ya banka ma Gate din harara kamar ita yake harara, hakan bai sa yayi nadamar zuwa gurin Nenen ba, don sosai yake son tsohuwar. Bakin titi ya tsaya don samun abun hawan da zai maidashi gida Laasar ta kusa. Ta fito da buta kenan ta tsugunna don yin Alwalar Sallahr Laasar. Ta ganshi tsaye yana waya, so daya ta kalleshi ta cigaba da alwalarta. Shima wayarshi ya cigaba yana mai kallon Gidan Mallam Muhammad. Ji yayi an rufe mishi ido ta baya. Hannu ya sa ya daura kan hannun da aka rufe mai fuska. Laushin hannun tabbas mace ce K’amshin turarenta ya ziyarci hancinshi, k’wak’walarshi tuni ta gaya mishi ko wacece, shakka babu itace, ita kadai ya sani wacce zata iya mishi wannan abun. Labiba na dagowa ta ga abunda ya sa ta sake butan hannunta, jikinta rawa yake kamar mazari, wata ce ta sa hannayenta ta rufe ma Zaidunta Ido, haushi ya bata da beyi yunkurin janye jikinshi ba, to ko ya zata Dalo ce? Ranta ne ya sosu ganin wani murmushin da bata taba gani ba gurin Zaid, bude hanayensu yayi tare da juyawa ga yarinyar. Lumshe idanuwanshi yayi ya bude, sosai suke sakar ma junansu murmushi mai k’ayatarwa. A hankali ya furta sunanta “YESMIN”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 Babi na Sha Biyar1⃣5⃣ (KE TAWA CE😍) Kafin su idasa k'arasowa gunsu tuni ta sha gaban Abu Sideeq, ta kare shi da hanayenta, tuni su Master suka zagaye su. Mankas da isa da tak'ama yace "ki shiga Ciki, ko in sa suyi gunduwa gunduwa da namanshi". Hankalinta a tashe ta kalli su Master tace " donAllah kar ku mishi komai". Tsawa Zaid ya daka mata yace "ki shiga Gida ki rufe k'ofar kar ki tsaya ko ina sai daki". Tsoro sosai Zaid ya bata, ba ta san wannan Zaidun ba, wannan ba shine Zaid din da fara So ba, wannan ba Dan Makahonta ban, wannan wani ne daban, wannan shine MANKAS. Da sauri ta juya ta shige cikin Gidan gudun ta tsaya gardama su ma Abu Sideeq wani abu, ba za ta iya dauka ba in har wani abu ya samu Abu Sideeq ba, bata san mai zatayi ba. Abu Sideeq ido ya raina fata, jikinshi sai rawa yake, Zaid ya kalleshi cike da tasha yace "yan shaye-shaye ko? Uwar meke faruwa in ba a kula su ba? Kace me?" Shi dai Abu Sideeq ba bakin magana. Zaid ya matso kusa dashi ya sausauta murya. "Beebs Yarinyata ce, Beebs Tawa ce, kar ka sake zuwa inda take, wallahi ka sake zuwa Unguwar nan, hmmm, zan gwada maka Tudun Matawalle na Mankass ne". Wuce su yayi tare da ma Master inkiya da su rabu dashi, Gidansu ya wuce ba tare da damuwan mutanen da ke kallonsu ba, afin kace wani abu Haruna ya finciko Abu Sideeq ya bashi mari kala Uku, ya gwada shi da hannunshi "kar ka sake taka k'afarka cikin Unguwar nan kanaji?" Abu Sideeq ya gyada kai da sauri. Hannu Haruna ya sa cikin Aljihun Abu Sideeq ya zaro ya ciro kudin da ke cikin Aljihun dubu-dubu guda 7, Haruna da jajjayen hak'oranshi yace "mu raba? In dau 3 in baka 4?" Kafin Abu Sideeq yayi magana Master yace "dan uwarka mu fa?" Haruna yace "to kai Ware" da sauri Abu Sideeq ya hau Abun hawanshi ya burka ya bar unguwar a sittin. Terror ya kalli Unguwar, cike tap kamar kallonsu suke kamar ana shooting film, yace "duk ku ware, ko in sareku magulmata" da sauri kowa ya dare suka bar wurin. Su ko suka wuce bencin Eskaley da murnan sun samu kudin siyan World. Hannunta rawa yake tayi, safa da marwa take tayi, Aunty Aseey na toilet, hankalinta ya gaza kwanciya sai da ta lek'a ta k'ofa ta ga ba kowa wurin sai tsiraran mutane, ba su Mankas, gabanta ya tsananta bugu. Chan sai gashi ta hango shigowarshi BQ, wurin ta tsura ma ido hawaye na neman kufce mata, shima tsayawa yayi yana kallonta idonshi cike da wasu abubuwa, wani abu yake ji game da ita da yake fizgarshi, dagaske yakeyi da yace "ita tashi ce, bai san ta yaya zata zama tashi ba, amma tabbas ita tashi ce shi kadai, dama kwanaki kadan ya rage mishi a duniya, zai kasance tare da ita kafin ranar rabuwarsu tazo, kafin tazo, in dai yana lumfashi, babu mamijin da ya isa ya zo kusa da Labs, ko tana so ko ba ta so, zai iya saran duk wani namijin da zai rab'i Beebs dinshi. Wayarshi ya zaro ya tura mata text, tana kallonshi, yana kallonta ta bude message din. "Saurayinki is fine, ya tafi Unharmed, ki gaya mishi, kar ya sake zuwa Inda kike, ke TAWA ce Beebs, You Are Mine alone, kin fahimta?". Ba ta san wani sanyi na ratsata ba, sai da taji wani yanayi na neman rufeta, ba za ta so ya ga reaction dinta ba, kallonshi tayi ta galla mishi harara tare da buga wani tsaki ta shige daki. Tana shiga ta fara latsar wayar Abu Sideeq amma wayar a kashe, duk ta damu, amma hankalinta ya dan kwanta da Mankas yace mata ya koma Gida ba tare da sun mishi komai ba. Tsaye yayi ya bi bayanta da kallo tare da murzan idonshi ya wuce Cikin Gida. "Kai Dan Makaho, mai nake ji ne a cikin Unguwa? Fada kayi da wani a kan Mace?" Mankas ya kalli Babanshi da ya shigo yana huci, be kula shi ba ya shiga kitchen don dafa indomie, sai kuma ya fasa, ya bude k'ofar dakin Dalo, ya ganta zaune jigum, murmushi ya mata tare da kashe mata ido daya, murmushi ta mishi, ya rufe mata k'ofa. Baba da Aunty Shafa’atu na tsaye inda ya barsu, yazo zai wuce “Baba yace Don uwarka ba magana nake maka ba? Wallahi Zaid in ka nemo magana kar a sake a tunkareni a matsayina na Ubanka, duk wanda ya kawo min kararka zance kai ba dana bane a tafi da kai chan Police Station, shege har ka san yanda ake fada kan Mace”. Wucewa yayi yaji Shafa’atu na cewa “ni tsorona Alhaji kar yayi ma Diyar Mutane Ciki, ka san halinshi” daga waje inda yake ya bude murya don ya tabbatar zata ji yace “Uwarki Zan Ma Ciki”. Ihu Shafa ta sake, Alhaji ya bi bayan Zaid wai zai bigeshi yana tsinanshi amma ko a jikin Zaid ya buda daki ya shige ya rufe k’ofar a fuskar Alhaji Zaki. Nan kamar an kunna shi ya hau bambamin Fada “Allah ya tsine maka Zaid, Allah ya k’untata maka yanda kake k’untata min da matata”. A sukwane Labiba da Aunty Asee suka fito daga Daki, tsinuwar da yake mishi ba dadin ji, Aunty Aseey bata ankara ba, sai ganin Labiba tayi harta k’etara Gidansu Zaid”. Da k’arfi Aunty Aseey tace “Uhm uhm Labiba”. Amma Labiba tuni tana gaban Baban Zaid da tunda ya ga Aunty Aseey ya ji wani irin mugun Kunya. “Ina Wuni?” Alhaji Ali ya amsa mata da “lafiya lau” tace “Baba, sunana Labiba, ba ka san Bakin Iyaye halaka ne ga yaransu ba? Ka san tsinuwan Mahaifi ga yaro ba zai taba sa yaro ya dace a rayuwa ba? Shin baka san mugun alkaba’i na janyo halaka ga mutum balle dan da ka haifa? Shin baka son Yara amanar Allah ne a wurin Uwayensu ba? kuma tabbas Allah zai tambaye ka yaya ka yi kiwonsu, in rai ya baci hankali ke nemoshi. Magana mai dadi sadaka ce, in yau Zaid ya maka ba daidai ba, ka zaunar dashi kace “Zaidu Eh, ka min ka za kamin kaza ban so, don Allah ka bari” wallahi zai bari, in ka janyo shi a jiki a hankali zai shiryu, kai ka sa Dan Makaho ya kangare, tsinuwan da kake mishi ya bar damunshi, ya giga, wallahi duk mai zaka mishi yanzu ba zai dameshi ba, daga ranar da ka fara La’antarshi, daga ranar rayuwarshi ta chanza, ka samu gurbi Babba wurin durkushewar Rayuwarshi, kana da kwamasho Babba, Wallahi Baba Allah sai ya tambayeka”. Juyawa tayi ta barshi tsaye a nan. Wannan Aljannace? Daga ina ta fito? Matar Muhammadu kadai ya iya ganewa, be son wacece ba. Maganganunta, sosai sukayi tasiri a ranshi. Kanshi yayi nauyi yana barazanar rabewa biyu, wani irin yanayi yake tsintar kanshi a ciki, sosai maganganunta suka shigeta, tambaya daya kawai zuciyarshi ke wurgo mishi, MEYASA? Meyasa mene? Shine bai sani ba. Na dan lokaci guda ya dawo daidai sai da ya ji muryar Shafa na cewa “taho Alhajina rabu dashi”. Kamar robot da ake controlling da remote ya juya yace “ai da kin bari na lallasa shi, tsinanne”. Zaid na ciki bai san wainar da ake toyawa ba. Anty Asy tace “me kikace mishi Labeeba?” “Waazi na mishi Aunty, bai kamaya yana tsine ma dan cikinshi ba” “Labiba ba yin kanshi bane” “Yana iya yak’ar Asiri” “Nidai Labiba da bakije ba, yanzu in yayanki ya ji fa?” Labina ta yi gaba tace “shi yasa ba zaki gaya mishi ba”. Aunty Aseey ta bita da ido. Ran Labiba k’al ta shiga daki, wayarta ta shiga lalubar numbern Abu Sideeq, kamar dazu wayar kashe, zama tayi ta shiga rubuta message na ban hakuri a kan abunda ya faru ta tura mishi. Shiko Mankas Wanka yayi ya zumbula Jallabiyarshi ya fita daga Gidan. Alhaji Ali Zaki duk yayi wani sukuku, kamar mara Lafiya, wani iri yake jin kanshi, Hajia Shafa na lura dashi, ba ta san meke samunshi ba, amma zata sa mai ido ta ga iya gudun ruwanshi. Bayan Maghrib Zaid ya shiga duba Dalo, ya ga Alhaji Ali zaune shi kadai a Parlo, har zai wuceshi yaji muryanshi na kiran ZAID. Chak ya tsaya saboda rabon da ya ji Babanshi ya kira shi da Zaid har mantuwa ta mance, ya dau seconds kafin ya juyo ga inda Baban ke zaune, daga inda yake ya hango wani abu mai wuyan fassaruwa a idon mahaifinshi. K’afarshi ta mai nauyi, ya k’arasa jiki a mace. “Zaid” Ya k’ara fada wannan karon muryanshi cike da fargaba. Hawaye ya cika idon Zaid, Hamdala ya farayi a zuciyarshi Mahaifinshi ya dawo daidai, duk da ya san Tashi ta k’are, atleast kafin ya bar duniya zai samu soyayyar Mahaifi. Muryar Hajia Shafa ta chanza Mood din Baba nan da nan ya rikide kamar wanda aka jona ma Charge “Uban me kake so ka tasani gaba kana kallo?” Runtse Idon da zaid yayi yayi daidai ta fitar hawaye daga idanunshi, for a moment, yayi zaton babanshi ya dawo hayyacinshi, har ya fara celebrating da zuciyarshi, ashe bai chanza ba, ba zai taba chanzawa ba in har matar nan na kusa dashi. Kafin ta k’araso yayi saurin share hawayenshi, da yardan Allah Anamimmiyar matar chan ta bar ganin hawayenshi. Dakewa yayi yace “Dama Maganar Dalo ne, ta gama makaranta, zaman gida kawai takeyi, so kafin ta samu admission, ya kamata ta fara wani abu, ko ta dinga zuwa koyon Dinki, ko cakes, ko wani abu dai haka, zaman Gida is depressing her”. Baba yayi shuru yana kallon Hajia Shafaa, ya na jiram Go ahead dinta, aiko ta girgiza kai, yace “banda kudin enrolling dinta a ko ina” Zaid yace “ni ina da kudin, kawai permission dinka nake so saboda fita zata dinga yi, kuma ka hanata fita”. Hajia Shafa na son magana amma sosai take tsoron tashan Zaid sai ta rada ma Baba abu a kunne. Baba yace “ Uban wa ya baka kudi? To eh din na hanata fita din, salon ta zubar min da mutunci ta ja min abun kunya, ka gama maidata karuwa ta je ta janyo min magana a waje”. Zaid ya cije bakinshi tare da kallon Shafa’atu yayi k’wafa yace “In ba zaka bari ta fara training ba, ka bari taje hutu wurin Mancy”. Shafaatu tace “a kan mene? Ba inda zata” Zaid ya juya gareta yace “zan zubar miki da hak’ora Wallahi” Baba yace “zo ka fara zubar min da nawa, DanMakaho wallahi ka fita idona”. Tashi yayi ya bar musu wurin ranshi na soyuwa, ya san Dalo ta gama jin komai, be son ganin kukanta kawai ya fasa shiga wurinta ya fita daga Gidan Baki daya. A B U J A Mimi ke kwance Ruf da ciki tana buga game a wayar Mancy, a shekarunta ta iya bude wayar Mancy ta kunna game. Wayar Mancyn ne ya fara ringing, ba tare da ta san waye ba tayi swiping ta amsa cikin muryarta da “Hello” Kamar jira take ta fashe da kuka, “Mimi ina Mancy? Ki bata wayar” muryan addanta Dalo taji, Mimi ta fara kuka tace “Adda Dalo are you crying? Stop crying, barin kaima Mancy wayar” da kuka ta fita daga dakin tayi hanyar dakin Abbansu. A babban Parlo Jawad ya ci karo da Mimi, kuka takeyi sosai wayar Mancy a hannunta, da sauri ya rage tsahonshi ya rungumota jikinshi ya na tamabayarta Lafia? Cikin kuka da muryarta na yara tace “Adda Dalo Is Crying” yace “Who is crying?” Maimakon ta amsashi sai ta mik’a mishi wayar, ganin DALO yayi a rubuce, kara wayar yayi a kunnenshi yace “Hello?” Dalo batayi magana ba sai sheshek’ar da takeyi, bata san waye ba, kawai sai ta kashe wayar. Haka kurum ya samu kanshi da swiping wayar ya bude ya sake bin number da kira. Ta dauka da Sallama, yace “Meyasa kike kuka?” Maimakon ta amsa sai cewa tayi “Ina wuni?” Daidai fitowar Mancy da Abba daga Daki, kamar mara gaskia Jawad ya tashi, kafin Mancy ta ankara wayarta ke hannun Jawad Mimi ta fara zubo zance. “Mancy, Adda Dalo is crying out loud” Abba yace “a ina?” Jawad yayi saurin Mik’a ma Mancy wayar ta amsa, ta ga wayar is still on call, da sauri ta kashe tana murmushin yak’e tace “Dalo na da reason din kuka ne? Ai komai sai ta mai kuka” jawad dai ya yi gaba yana sak’a wani abu a ranshi. Abba yace “Mancynsu, ko zaa ma Alhaji Ali magana ne? Ko hutu Dalo ta zo mana?” Mancy tayi jim tace “bari dai mu gani Abbansu,sai mutane biyu sun Amince” yace Dawa dawa? “Da Alhaji Alin, da kuma Hajia(Ummansu Jawad)” Alh yace “saboda gidanta ne?” Mancy ta girgiza kai tace “saboda tana da hakki” yace “shikenan zamuyi maganar” tace “to shikenan ina zuwa barin sa Mimi bacci” ta saba mimi a kafadarta tana babanta byebye, shi kuma ya zauna don kallon Channels. Mancy na shiga daki tayi dialing numbern Dalo jikinta na rawa, Dalo na dauka ta fashe da kuka, Mancy hankalinta ya tashi, da kyar ta lallashi Dalo ta samu ta gaya mata abunda ke faruwa, ran Mancy ya baci, tace “kiyi hakuri Dalo, sharri kayan kwalba, Alhaji ya buk’aci zuwanki Hutu Abuja, all we need to do is convince your Father, inshaAllah zaki zo wurina, kuskurena daya da na k’i tafiya da ko kece, amma inshaAllah, komai zai wuce, zan samu Alhaji ya kira Babanku ya nemi alfarma gunshi, inshaAllah ba zai hana ba”. Tayi ta lallashin Dalo, har sai da ta sa ta Daria. “Mancy dazun waye ya karbi wayar daga Hannun Mimi?” Mancy tace “Oh Autan Hajia ne, Jawad” Dalo tace “Oh Okay”. A haka suka cigaba da firan Uwa da diya har sai da Dalo ta sake, Mancy tace “Barinje gurin Alhaji” sukayi Bankwana. K A T S I N A 10:45 pm duk sun kwanta, Aunty Asee ma dakin yau zata kwana saboda Baban Amira baya nan, Labiba ce ke chatting, tana ganin wayarshi ta yi ringing ta katse ta kara shigowa bata tabawa. A karo na kusan Goma ya kira Wayarta a kashe, duk kiran da ya mata bata dauka ba sai ya zuk’i sigari, da ya ga abun na neman zautar dashi, ya fito waje kan Dakalin da suke waya. Yafi karfin Awa daya zaune wurin, sauro duk sun cijeshi, amma ko a jikinshi. Haka Ya cigaba da kiran Wayarta, Message ya tura mata. “Ban taba Shan Giya ba, ban taba siyan Giya da hannuna ba amma yau na siya, Beebs, Ki na da Zabi uku, ko ki zo dakina yanzu, ko ni nazo dakinki yanzu, ko kuma na sha Giyar nan, kuma in na shata Alhaki a kanki, kina da ikon hanawa, in baki hanani ba, ko me ya faru, its on you, have your self to be blamed”. Tirkashi, ta karanta message din ya fi so nawa, gabanta na faduwa, kar fa yazo dakin nan don yau harda Aunty Aseeyah, ya zata yi in ya zo?” Message ya sake shigowa yana mai tambayarta “In zo ne? Ko zaki zo ne? Ko in sha giyar? Which is Which?”. A ranta tace “to ya sha giyan mana ina ruwana? To kuma kar Allah ya kamata tunda tana da ikon hanashi ta ki hanashi kar ace tana da kwamasho, ko be sha giyan ba be da hankali yana iya zuwa dakin nan, kuma kar Aunty Asee ta farka ta samu wrong impression. Bata da wani zabin da ya wuce ta je ta iskeshi, cikin sando ta mik’e a hankali ta bude k’ofar ta fita a hankali. Nanauyar ajiyar zuciya ya sake a lokacin da ya sanyata a idonshi, da taimakon hasken Farin wata ya ga fuskarta daure yake tamau wai ita fushi take, wani murmushi ya subuce mai daga baki. Gyara tsayuwarshi yayi, a hankali take takowa gareshi, har ta iso gareshi ta tsaya a gabanshi. Chan k’asar mak’oshi yace “Bibbbssss, KE TAWA CE”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 Babi na Sha Bakwai 1⃣7⃣ (K'AMSHI☺) Cikin wata iriyar murya yace "K'AMSHI" Dariya tayi tace "Zaid dina ni kadai" hakan da ta fada ya sa shi tunawa da Labiba, da sauri ya waiga ya ga bata wurin da ya barta dazun, ya sake juyowa ga Yesmin yace "yaushe kika dawo?". A tak'aice tace "jiya" "Ba ki gaya min zaki zo ba?"y "Ba zai zama zuwan bazata ba in na gaya maka" Dan guntun murmushi yayi yace "K'amshi". Itama murmushin tayi tace "Zaidun k'amshi". Daga gefe ya ga travelling bag dinta yace "oh baki ma shiga cikin gidan ba?" tace "eh zuwana fa kenan" yace "okay kije, zan zo cikin Gidan, barin yi Sallah" Gaba tayi tace "alright sai ka shigo" tafiya tayi ta bar wurin da k'amshinta kamar ko da yaushe, ciki ya shige shi kuma don yin sallah. Daga Window Labiba ke lek'ensu, jikinta rawa yakeyi sosai, ranta ya sosu, kallon fuskokinsu ya tabbatar mata da cewa akwai tsantsar soyayya a tare dasu, "uhmm wannan itace Mai Aji? Gashi nan suna ta zabga k'walisa, dama ya na da kamar wannan mai zai yi da ita Mara Aji? Uhm su masu Aji". Da k'yar ta bar wurin ta kabbara sallahr La'asar, zuciyarta na mata zogi. Da sallama ta shiga Parlon duk suka hau shewa , Annah ta rugo ta rungumota "oyoyo Aunty Yesmin" itama ta rungumeta tayi "oyoyo Annahn Aunty Shafa" sukayi daria baki daya, "Dr Yasmin" Hudu ya fada cike da k'auna da Bege. Murmushi tayi tace "Uncle Hudu muna lafia?" Ba ta jira amsar sa ba ta zauna kusa da Aunt Shafa tace "Aunty Ina wuni?" Shafa ta amsa ta na tambayarta mutanen Gidan. Sunyi Minti 10 suna magana kafin Zaid ya shigo da Akwatin Yesmin. Cewa yayi "K'amshi, ga Box dinki" da sauri ta tashi yan parlon suka bita da muguwar harara, tace "har kayi Sallahn?" yace "Yup" tace "sai ina?" yace "zan shiga na ga Dalo sai na dan fita". Gaba tayi don zuwa dakin Dalo tana fadin "wai har yanzu Dalo baki bar zaman daki ba? Haba sai kace wata Mata mai Takaba?" Zaid ya rufa mata baya yana daria, a tare suka shiga dakin, aikam Dalo taji dadin ganin Aunty Yesmin dinta, Zaid yace "nidai ma fita, sai bayan Maghrib kuma" byebye k'amshi tace, dalo ta gyada mai Kai. "Wai ke ba nace ki dinga fita parlo ki na zama ba? taso muje" da sauri Dalo tace "donAllah ki barni a wurin zamana, please" Yesmin tace "Waye yace daki shine wurin Zamanki? My friend taso muje Parlo inda mutane suke". "Dalo tace banyi sallah ba" Yesmin tayi hanyar k'ofa tace "kiyi sallah ina jiranki kizo, in baki zo ba, ni zan zo". Dalo tace "Yes Ma". Tunda ta fito daga dakin Dalo "Aunty Shafa take tarbanta da harara har sai da Yesmin ta zauna kusa da ita taja zabga murmushi. Aunty Shafa'atu tace "Kinga Abunda ke hada ni dake kenan ko Yesmin? Na gaya miki ba ruwanki da yan iskan chan, wurina kike zuwa, ba wurinsu ba, ni kika sani ba su ba, haka wanchan zuwan da kikayi sai da mu kayi fada da Mamanki ta kanki, indai abunda zaki dinga ja min kenan ki bar zuwan man Gida gaskia". Nan da nan Yesmin ta chanza fuska tace "Kinga Aunty Shafa ba sai kin min gorin Gida ba, yanzu zan bar miki Gida, kuma ki sani wallahi sai nace Mommy ta zame hannunta a cikin Lamarinki kaf". Da sauri tace "haba Yesmin, ni ba gorin Gida na miki ba, baki fahimceni ba, kiyi hak'uri, kin san you are always welcome, kawai dai banson ganinki da Dalo daDan Makaho". Harara ta zabga mata ta ja akwatinta ta yi dakin da take sauka in tazo. Hudu kam bin bayanta yayi cike da k'auna. Shafa ko ranta a bace ta zaro waya don Kiran "Er Rabi". YASMIN wacce aka fi sani da k'amshi a Jami'ar Oxford University dake England. K'amshi kamar yanda 'yan Nigeria masu karatu a England suke ce mata, k'amshi kyakyawa ce doguwa sosai mai dan diri, kamar sunanta K'amshi 'yar k'amshi ce, in ta zauna a wuri ta tashi shikenan gurin zai dauka da k'amshinta, ko handshake tayi da friends dinta to sai fa ta bar tambarin k'amshinta a hannun mutun K'amshi yar gayu ce sosai. Akwai wani K'ungiya na 'yan Nigeria masu karatu a UK (UKKSA) United Kingdom Kastina Students Association, ne ta ke haduwa da Zaid Ali Zaki wanda shine Vice president of the Association, k'amshi ce Treasurer. Suna gaisawa don baida shariya ko kyaliya, sosai Guy din ke birgeta, daga gaisuwa ba abunda ke hadasu amma ta na so alak'arsu ta wuce gaisuwa. A hankali a hankali haduwarsu ta fara yawa don akwai wani gaggarumin taron da zasuyi na (UKKSA) wanda Taron zai hada da Shugaban k'asn Nigeria, Gwamnan Katsina, Director na Scholarshi board na Katsina, shiyasa suke haduwa sosai a kwanankin nan, aikin da suke yi ne ya sa suke yawan haduwa tare. Kowa na son shishige ma K'amshi amma ita yar shan k'amshi ce, sai wanda ta za6a take magana, amma sai gashi tana son shige ma Zaid amma bai wani bata fuska ba bayan gaisuwa, a hankali taji ta na matuk'ar son shi, sosai take so ya furta mata kalmar so don ba za ta iya gaya mishi tana sonshi ba. Ajinta take ja, don abun kunya ne ace kamarta K'amshi yanda tayi suna a universities din England musamman Cambridge da Oxford ace ta bada kanta wurin Namiji ai yawa ne, shiyasa take kama kanta, bata bari son Zaid ya fito fili ba balle a gane, Makarantansu ba daya ba balle ta dinga ganinshi har ta kasa hakura wata rana ta tareshi ta furta mai So, sauk'inta kenan ba su faye haduwa ba sai sunzo Meeting suke haduwa, bayan anyi Taron kuma bata sake ganinshi ba. Wannan Kenan. SHEKARA BIYU DA SUKA SHUDE Hajiya Shafa'atu ta kalli Hajia Er Rabi ranta na k'una tace "wallahi ba zai yiwu ba, shekaru 15 nayi a banza?" Er Rabi ta katseta da cewa "Aa fa Shafa'a, bukatar da kika rok'a an biyaki fa, kince kina so ki dawo Dakinki kuma ki mallake mijinki, ba ki dawo ba? Baki mallakeshi ba? Sai dai in ba ki saka Alhaji Ali wani abu ba, ba tunanin zai maki ya biya maki buk'atarki, Ai wallahi in baki gode mai ba, ba kya butulce ba". Da fada Shafa tace "Yo ina amfanin mallake mijin, Tunda dan sa na daga hannu ko abun duka ya dakeka? Ina amfani? Kalla fa jikina duk shatin Belt, wallahi yaron nan haka ya hadeni da Hudu ya shaude mu da Belt, nidai wallahi ai man maganinshi, ba fa zata yiwuwu ba". "Yanzu dai shima zai dawo k'ark'ashinki, sai yanda kikayi dashi, burinki ma zai cika na ganin ya bar Gidan, don shima zaki mallakeshi kamar Ubanshi, tashin farko ki mai umurni da barin K'asar gaba ki daya ba tare da ya k'ara dawowa ba, ita wannan kanwar ta shi kuma karamar Alhaki ce, murjeta kawai zakiyi". Shewa sukayi tare da chafe wa "Allah ko kawata? To yanzu meye abunyi?" Er Rabi tace "kar ki damu kawata, zan hada maganin zuwa gobe, zan turo miki Yass gobe" Sake chafewa sukayi Shfa tace "Shegia kawata, wasa wasa kin fa zama wata bokanyar kanki". Dariya tayi tace "ke ko yau da gobe ko? Da su dinga cinye mana kudi ai gwara mu mun ci ma Mata kudi, ai kinsan samu nayi Baban Annah ya hadani da Aljannah guda wallahi Miliyan Ashirin na sayeta". Ran Shafa bace tace "wallahi kar na sake jin kin kara furta Baban Annah, salon taji? So kike ace baban diyata boka ne? Banson iskanci fa Er Rabi". Wayan cewa Er Rabi tayi tace "yi hakuri kawata, gobe zan aiko Yass barin tafi". Sum sum ta tashi ta bar Gidan Alh Zaki tana mai borin kunya. WasheGari Uwa Uwa ce ko da uwar banza ce, ita ta san ba tayi dacen Uwa ba, ita ta san Uwarta na daga cikin Matan da ke cikin Halaka in har Allah bai shiryar dasu ba. Uwarta ta kasance Matsafiya kuma Bokanya mai yin Shirka, ita kuma tana da kwamasho wurin taimaka mata wurin isar da sakwannin ga masu yin shirka kawai don kyautata mata kamar yanda ta ke kyautata mata itama. Uwarta ce gatanta tunda har ita ce take biya mata bukatunta, Ubanta bai da mararraba da Mattace tunda baida say a gidanshi, mamarta itace Gidan, itace ke musu Providing komai na buk'atunsu, ita ke dawainiya da ita da Uban nata,ita kadai ce diyarta to Son duniyarta ta daurama tilon gudan Jininta, shiyasa tayi muk'u muk'u ta turata karatun Likitanci a Oxford University, ta bata Mota, ta kaita kasar waje karatu, ta bata duk wani jin dadi na rayuwa meyasa ba zata mata abunda take so ba?. Tana yin ma Uwarta Biyayya don ta kyautata mata kamar yanda take kyautata mata. Ta san tana cin haram tana rayuwa irin ta haram, amma son Mahaifiyarta ya rufe mata komai bata ji bata gani. Murza Sitiyari tayi cikin k'warewa har ta isa Gidan Alhaji Ali Zaki, honk tayi a ka bude mata ta shiga da Motarta, sak'on ta dauko a wata paper bag ta shiga Gidan da Sallama. Ta na shiga Cikin Parlon, shi kuma ya fito daga Kitchen dauke da Plate a hannu. Idonshi na hagu ya murza a hankali yace “Yesmin K’amshi?”. Bakinta wanda ya dade a bude tace “Zaid?? Kai ne? Me kakeyi anan?” Murmushi yayi yace “Me nakeyi a Gidan ubana?” Da mamaki tace “You mean this is your House?” Girgiza kai “This is My Father’s house”. Nan da nan K’wak’walwarta ya kaita ga tunani, maganar mamarta taji a kwanyar kanta kamar a lokacin ake gaya mata. “Ki ce ta saka mai wannan a k’ark’ashin Gado, wannan kuma ta barbada mishi a gaban daki da ya tsallaka shikenan zai shiga Duniya”. Wannan kuma a yi hayak’i dashi, duniya zata manceshi, ba wanda zai tunashi balle ya damu da inda ya shiga, ita kuma Sadiya a bata wannan ta sha itama zata shiga duniya, ba zata ma hadu da yayanta ba a duniyar da zata shiga balle su shaida juna balle su tuna Gida”. Wani zufa ya keto mata, bakinta na rawa tace “Aunty Shafa’atu mamarka ce?” Fuskarshi ya sauya , kamar ba zai amsata ba yace “Matar Babana ce” Baya baya ta fara yi, kafin ta juya da gudu ta bar wurin, da sauri Zaid ya bi bayanta yana kiranta “K’amshi” amma bata juyo ba. Kafin ya k’arasa gunta har ta shige mota, ta yi horn aka bude mata ta fita daga gidan a sittin. Mamaki kamar ya kashe Zaid a tsaye, lafiyanta kuwa?”. Tuk’i take cike da ganganci, Allah ya kaita Gidansu Lafia, tana shiga ta wuce dakinta straight. Tunani barkatai. Istighfari ta fara yi, kuskure daya, kuskure daya zatayi ta kai Zaidun ta ga Halaka, saura kiris ta batar da Zaid a shafin Duniya, Inalillahi, yaron da Mamarta da Aunty Shafa’atu suke son halakawa Zaidunta ne, Zaidunta fa, kai bata yiwuwa wallahi, sai inda karfinta ya k’are”. Ta dade zaune kafin ta shiga toilet tayi Alwala tayi sallah, ita bata taba shirka ba, amma tana yadawa, Allah ka yafe mata. Knock taji a kofarta, da k’yar ta bude. Mamarta ce. “Yasss yadai? Munyi magana da Hajia Shafa’atu tace “bakije ba, baki kai saqon ba? Ya akayi?”. Dan guntun tsaki tayi tace “Oh Mommy wallahi ban dan jin dadi, har na fita kuma najini wani iri, shiysa na dawo” Er Rabi ta kamota “ayyah sorry Yass baby, sannu muje in baki paracetamol” Yesmin tace “Mommy karki damu nasha, ina so na kwanta ne”. Er Rabi tace “Ayyh my baby shiga ki kwanta kinji, ki huta sorry”. Er Rabi ta kira Hajia Shafa’atu ta shaida mata diyarta bata da lafia amma da ta warke InshaAllah zatazo aikota. Bayan kwana biyu Yesmin ta fito tace “zata kai ma Hajia Shafa’atu sak’o”. Er Rabi tace “Yass dauko kayan na k’ara miki bayani” k’amshi tace “ban manta ba, amma tuna min” haka Er Rabi ta sake mata bayani. Yasmin ta fita daga Gidan a Motarta bata tsaya ko ina ba sai a wani Islamic Chemist, ta buk’aci a bata garin Zogale da garin habbatus sauda, da garin tazargade dana ‘da’d’doya, fasawa tayi ta hadesu guri gura tace wani sassak’e garesu? Sukace akwai na baure akwai na mangoro, tace duk a bata. Haka tayi hadadden magungunan ta biya ta shiga Mota ta wuce Gidan Alhaji Zaki. Hudu na Parlo ya daura k’afa daya kan daya ya jiyo wani k’amshi na k’amshi, da sauri ya mik’e tsaye gami da hade miyau da ya ci karo da kyalyawar halitta na K’amshi, cike da shan k’amshi tace “Aunty Shafa na nan?” Baki na rawa Hudu yace “barin kirata ta na ciki”. Samun wuri tayi ta daura k’afa daya k’an daya, tana kadawa a hankali. Jim kadan sai ga Aunty Shafa ta fito da sauri hards rungumeta, itama ta rungumota. “Yass ya kike ya jiki? Ashe bakiji dadi ba?” “Wallahi kam Aunty amma da sauki” “Ya sSchool ko an gama?” “Aa da saura, saura shekara daya” “Inye Doctor Yesmin, yanzu ina sak’ona?”. Cike da bariki k’amshi ta kalli Hudu, hudu yayi saurin cewa “kar ki damu Baby, ni k’anin Aunty, na san komai”. Aunty Shafa tace “kar ki damu Yasmin”. Ta ciro k’ullin da ta siyo yanzu a Islamic Chemist kamar yanda Mamarta ta mata bayanin wadan chan magungunan, haka ta mata bayanin a wannan “gasu Aunty, wannan a ba yarinyar aAbinci, wannan shi zaa saka a krkashin gado, wannan shi za a barbada a k’ofar dakinshi”. Aunty Shafa tace “Hudu Dan Makaho na nan?” Yace “eh ya na nan” tace “to sai ya fita sai mu shiga dakin. Hudu yace “to hakan zaayi”. Mikewa tayi tace “barinje in adana” Hudubya zauna kusa da k’amshi, tayi saurin tashi ta rufa ma Shafa’atu baya. K’amshi ta musu Sallama ta tafi, ta so ganin Zaid amma bakomai, ta san inda yake, zata cigaba da kareshi, wannan shine son da take mishi. Mankas na barin Gidan Hajia Shafaatu da Hudu suka shiga dakinshi, suka daga Katifarshi suka wurga Sassaken iccen Mangoro da na baure. Gaban dakin kuma suka barbada Garin Habbatus Sauda mai Zogale, ta dafa Abinci ta barbada garin Hibban a cikin Abincin Dalo ta mik’a mata ransu k’al yau zasu shig duniya. Har bayan Isha’i bata ga Dalo ta fito ba, Zaid ya dawo, bin bayanshi sukayi suka ga ya shiga daki. Su ka tsaya jiran tsammani amma shiru, a kan idonsu Dalo ta fito da plate din Abinci alamun ta cinye tas. Mamaki ya kamasu. Har kwana biyu ba wani labari, cike da damuwa ta kira Er Rabi tace “ke ba wani bayani, yara na nan kamar mayu, ba wanda yayi yunkurin barin Gidan”. Da mamaki Er Rabi tace “Be yiwuwa, maganin da Er Lale da kanta ta hada fa” cikin fushi Shafa’atu tace “koma Er dada ce magani beyi ba” Er Rabi tace “kwantar da hankalinki, yesmin zata kawo miki wani hadin, ki turo 800k”. Shafa’atu tace “Er Rabi dubu dari 5 na baki fa shekaran jiya”. Er Rabi tace “Yo Shafa’atu wannan maganin babba ne, zaifi aiki wallahi, ke ko miliyan ne in zaki samu biyan bukata ai sai kiyi ko?”. Hajia Shafa’atu tace “Hmmm, zan miki transfer”. Haka Er Rabi ta sake hada wani Maganin ta ba Yesmin, Yesmin ta zubar a hanya taje ta sake hado wasu tarkacen wannan karan hardasu dakakken Citta da masoro, bayanin kadai take kaiwa. Har Sati daya ya wuce Ba wani bayani. Cike da Masifa tace “Er Rabi ban fa san Iskanci da kutumar uba, don iskanci sai tura miki kudi nake kina cinyewa ba kya biya min buk’ata, 1.4 fa kikace ma tura maki”. Er Ravi tace “wallahi kina ban mamaki, indai burinki zai cika ko nawa na ce ai kya bada ko? Da danake miki aiki baya ci? Wannan DanMakahon akwai babban kariya a tattare dashi, shiyasa asiri be kamashi, shine fa wannan karon nake son aika Er lale taje da kanta ta karya Asirin ta dauke shi ta kai birnin Sin ta dire”. Shafa’atu ta yi jim tace “zan turo Miki 1.4 amma donAllah ki tabbatar Aikin nan wannan karon yayi”. Er Rabi tace “shikenan ba ki da Matsala, zuwa nan da sati daya zan turo Yesmin”. Sukayi Sallama. Bayan Sati daya Yesmin tazo Gidan da sak’on Mamarta wanda ta chanza a Islamic Chemist. Da Zaid ta fara haduwa ta bishi da kallo taga duk ya wani kazance, kamar ba Zaid mai k’walisa ba. Da murmushi yace “K’amshi” “Zaid Ali Zaki”. “Wai me kike zuwa yi Gidanmu, rannan kinzo daga ganina kika ruga a guje” Tace “sorry Zaid, ya kake?” Yace “baki amsani ba, me kike zuwa yi gidanmu?”. “Ina zuwa gun k’awar Mamata ne” Dan hade rai yayi yace “wacece kawar mamanki? Anan gidan?” Tace “Aunty Shafa’atu” Fuskarshi ya daure tamau “yace wurin Shafa’atu kike zuwa? Itace kawar mamarki? Nice”. Ya yi gaba ta bishi a baya tana cewa “zaid menene? Ka saurareni”. Yace “ke nifa ba ruwana dake, i have nothing to talk to you about”. “Ka tsaya menene don na zo gaida kawar Mamata?” Yace “Bakomai, kar ki kara nuna kin sanni, banda wata alak’a dake, na tsani duk wanda ke tare da Shafa Algus, ko da kuwa kece”. Shan gabanshi tayi tace “Allah? Uhm Zaid? Tsana? Da ka sani da ba kace haka ba, ko da yake i dont blame you”. “You have no idea what i have been doing for you, what i am still doing for you”. Ya kalleta da dan mamaki yace “Uwar me kike min? To ki bari mana, in ma wani abu kike man uban wa ya saki?”. Cike da bakinciki tace “Really Zaid? Really?”. Yace “Yes K’amshi Really”. Murmushi tayi tace “ba zan bari ba, you will thank me someday”. Ta wuce ta shige cikin Gidan ta barshi tsaye, da mamakinta ya bita da kallo, da ya ga kanshi zai fashe ya dauko world ya hambada kafin ya fara wani tafiya kamar tsallen kwadi har ya shige boysquaters”. Da Sauri Shafaatu ta taryo Yesmin ta na mata sannu da zuwa, murmushi ta mata ta zauna. "Yesmin ina Sak'o na? Dauko min naji dadi, wallahi na kagara naga aiki da cikawa" Yesmin ta bude jakkarta ta firdo da wasu k'ullin magani ciki harda jan dutse da ta saka aka dake mata shi, bayani ta mata ta amsa jiki na rawa tace bari ma na kira mamarki ta sake min bayani gudun kar a samu Matsala, don wannan ya ki biya min bukata ta bansan me zanyi ba kuma, na kusa fa kashe miliyan uku ta kan aikin nan. Yesmin ta jinjina kai tace "kaii aikin da wuya kam, shiyada kudin ke tsada, amma wannan zaiyi in Allah ya yarda" cike da jin dadi Hajia Shafa ta tafa hanayenta tace to "Allah ya sa". Yesmin tace "Amin a fili" amma a bayyane tace "zanga yarda jar k'asa zata sa mutum ya shiga duniya". Annah ta fito tana hawaye hankalin Shafa'atu in yayi dubi ya tashi da sauri ta taryeta "me ya sameki Annah?" Cike da shagwaba tace "Mommy wai Sadiya nace ta ban doguwar rigar da ta saka Jiya, shine tace ba zata bani ba wai Mamarsu ta siyo mata". "Ba Alhaji yace kar su k'ara Karban kayanUwarsu ba, je kira mini ita" ta koma ta kira Dalo. A tsorace Dalo ta fito Parlorn, tun kafin a mata fada jikinta ya fara rawa. Kallo daya ta ma inda Shafa take gabanta ya yanke ya fadi. Cike da Umurni tace "je dauko rigar". Da sauri Dalo ta koma daki ta dauko Riga ce ta larabawa mai kyaun tsiya. Danubanki yaushe aka kawo Rigar nan? Ba babanku ya hanaku karban kayan gurin Uwarku ba? Ce mata kukeyi baya da kudin siya muku kaya ne? To bata Ba Annah rigar yanzu kafin na sanar da Uban naku". Jiki na rawa Dalo ta k'okarta cewa "Mancy fa tace rigar in aje in nayi aure na haihu na ba yarinya na". Hannu ta shiga tafawa tana cewa "yanzu har kin san meye haihuwa? Shekararki 16 kinsan zaki haihu? Da wa zaki haihu? Da Yayanki ko? DanMakaho shi zai miki cikin ko? Shegiya karuwar Yayanta. Sadiya ta runtse ido, ita bata son masifa da bala'i amma cin fuskar nan ya fara isa, wannan zagin da kazafin yaushe zaa bari? Cin fuska, hantara, kyara, tsana a gidan Mahaifinsu yaushe zaa daina? To wallahi wannan rigar ba za ta bayar ba, ko zasu kasheta, kyautar Mamarta ne, ta kuma ce ta ajiye ma jikarta to hakan zaayi, tsaye tayi k'am ba tare da ta yi yunkurin ba Annah riga ba. Tunda Dalo ta fito daga dakinta K'amshi ta k'ura mata ido, yanayinta sak na Zaidu, kurum taji yarinyar ta mata, duk badak'alar da akeyi a kan idonta amma bata iya cewa komai ba sai binsu kallo da tayi kafarta kan daya da alama tana mamakin karfin hali irin na Haj Shafa da diyarta Annah. Gani tayi yarinyar ta sa Gudu da sauri ta fita rik'e da rigar, Shafa da Annah sun rufa mata baya a guje, itama Yesmin ta tashi ta bisu, baya sukayi da alamu BQ ne. Daga nesa ta ke kwala mai kira. Zuciyarshi ke mai wani irin zugi, kamar world din da ya zuk'a ta bi mishi ta wurin da be kamata ba, sosai yake bugun k'irjinshi don kwarewa yayi. Muryar Farincikinshi yaji tana kiran sunanshi cike da tashin hankali. Durowa yayi kan gado ya fita daga dakin suka hade gabaki daya. Rik'ota yayi tare da kallon masu binta a baya. Mur ya sha tare da hade girar sama da k'asa. Yace "me kika musu?" Kamar jira take ta fashe da kuka. "Wai saidai na ba Annah Rigar da Mancy ta siya min" karbar rigar yayi kafin ya kallesu ya har sai da ya ba Yesmin tsoro yace "Saboda uwar babbansu ta siya? Sai su kwata in suna da k'arfi". Ki tafi daki ki rufe, zan shigo ba da dadewa ba, da dan gudu ta wuce cikin gida, shi kuma ba tare da ya sake kallonsu da ke tsaye ba ya shige dakinshi dafe da k'irjinshi da ke mai zafi. Shafa ta kalli Yesmin tace "kinga yanda dan mijina ya raina ni ko?" Yesmin tace "ke da kike da maganinshi a hannu". Tace "ke dai bari, ai sai dai wasu ba su ba, chance nike nema, da ma samu zasu zama tarihi a mance su a rayuwa". Yesmin ta jinjina kai. A tare suka koma ciki, yesmin ta dau jakkarta ta musu sallama ta fito. Mai makon ta yi hanyan parking lot sai tayi BQ. Samun shi tayi kwance ringingine, idonshi na fitar da kwalla, wuri ta samu ta zauna a hankali ta kira sunanshi. "Zaid" Sai da ya dan bata lokaci kafin ya dan kallota "me kike so?" K'amshi tace "Zaid, can we talk?". A fusace yace "talk about what? How My step mother is your Aunty?". Dan bude murya tayi tace "Zaid ya kamata ka san cewa ba zan taba yin wani abun da zai cutar da kai ba ta kowani fanni, wallahi in wani abu zai cutar da kai ko wani naka sai inda karfina ya k'are, right now i need you to trust me". Dan jim yayi kafin ya tashi zaune yana kallonta, bakinshi na rawa da k'yar ya iya cewa "Meye alak'arki da Hajia Shafa'atu?". A takaice tace "Aminiyar Mamata ce". Zaid zaiyi magana tayi saurin katseshi ta hanyar cewa "Eh Zaid, kawarta ce kuma Halinsu yazo daya shiyasa suke abota, ba zan iya fada maka exactly what is happening ba, saboda wasu abubuwa zasu fi kyau in ba a fadesu ba, suna k'ulla wani abu game da kai da kanwarka amma ba zan bari su cutar da ku ba na maka alkawari". Zaid ya kalleta kaifn yace "ta ya zan yarda da ke?". Tashi tayi tsaye tace"Zaid i just told on my Mother, na ci amanarta ne fa, na yaudari yardanta, zaid kana ganin zan yaudari uwata ne in ba akwai kwakwaran dalili ba, dole akwai dalili?". Shima tsayen yayi yace "nikam kinsan banda komai, i lost everything, banda abunda zan biyaki dashi". Daria tayi tace "lallai kam ka manta k'amshi, ka manta k'amshi ba matsiyaciya bace ba ko? Ka manta ko a school k'amshi ke treating kanta bata yarda a siya mata ko da cup daya ne na coffee, so Zaid bana bukatar kudi ko wani abun duniya,abu daya nake bukata shine "in ka ganni, ko ka ji sunana, kayi murmushi a bayyane ko a boye kace "Na Santa". Da mamaki yace "Yesmin ban gane ba" tace "ba zaka gane ba, hakan kawai nake buk'ata, yanzu ba wannan ba, gaya min meyasa baka dawo School ba Last year, me ya faru da Zaid mai Zabga K'walisa? Mai ya faru da kai, why are you a complete mess now?". Ya dan kalleta ya na so ya karanceta tace "Zaid ina son na taimakeka but ina buk'atar ka yarda dani, how can i help you when i dont know what happened to you exactly, please Zaid, Yesmin is not your Enemy, trust me". A hankali ya soma karanto mata duk wani abu da ya gifta tsakaninshi da Hajia Shafa'atu tun yana dan Shekara bakwai, da Silar komai, har i zuwa yau, babu abunda ya boye mata. Sosai take kuka kamar zata shide, ya zaayi Mutum yayi haka? Ya zaayi Mace ta yi irin wannan rashin imanin? Ina zata kai Hak'okin bayin Allah? Ta san Uwarta na da babbar sa hannu a cikin lamarin nan, ba abun mamaki bane in ma Uwarta ta sata bin boka, don ta san Uwarta Shedaniya ce. Ganin kukan na neman yawa ya sa Zaiid cewa "K'amsshhiii, to yane? Ya school? Saura Months ko ki gama?" Itama ta na son mantawa da abun for a while ta share hawayenta tace "eh saura 7months" yace "inye Dr K''amshi Allah sanya Alheri" murmushi tayi kanta na wani irin sarawa. Mik'ewa tayi tace "barinje Gida, I wont let them hurt you or your sister again, zan kuma bincika naga if theres anything i can do, da zai dawo da babanku cikin hayacinshi". Murmushi Zaid yayi yace "nagode". Tun daga ranar Yesmin ta maida Gidan Hajia Shafa'atu wurin zuwanta, duk wani Makirci da bak'ar aniyya da suke kullawa Yesmin sai ta kwance ta bata musu aiki, in ta zo Gidan, attimes sai dai ta wuce BoysQuaters wurin shi or in ta karyo Motarta a Unguwar ta ganshi bakin Bencin Eskaley, oda take mishi sai ya taso ya shigo motar su sha labarinsu ba tare da ta k'yamaci kaurin da yakeyi ba. Tsakaninta da Dalo sai k'auna da janta a Jiki. Har sai da wata rana Hajia Shafa'atu tace "wai ke Yesmin, na ga wani haba-haba kike da wanchan figigiyar yarinyar, baki san itace nake so na raba da gidan nan ba abun ya cutura, har gobe mamarki ta kasa hada min magani me k'ark'o? Ni ban so kina zuwa kusa da ita balle ki jata a jiki". Dariya Yesmin keyi bata cewa komai. Ba da dadewa ba Yesmin ta fara shirin komawa makaranta. Bata koma Makaranta ba sai da ta tabbatar Shafa'atu ta hak'ura da batar da Zaid da Kanwarshi. Don da bakinta take cewa "Aunty Shafa, kinga wai Mummy ta kasa biya miki Buk'ata, inada shawara, ki bar kashe kudinki wallahi, tunda ke ke da gida, babansu kuma sai abunda kikace mai zai dameki?". Hajiya Shafa'atu tace" wallahi na kashe fiye da Miliyan Biyar kan wannan maganar, magana ta kici ta ki cinyewa, ba wannan ba Yass, ni tsagerancin yaron nan ne ya ke isata, har hannu yake sawa yana dukana" tace "abu mai sauk'i da ya tabaki ki fanshe a wurin Ubanshi?". Tare suka fashe da daria harda kashe hanaye kamar wasu kawaye. Yesmin tace "ba da dadewa ba zan gama Makaranta, zanje India yawon Bude Ido, akwai wani hatsabibin Boka, wallahi daga India zai dauko su ya batar dasu, ba tare da kinyi shakka ba, kinsan Bokan India ya miki aiki, sai godia kawai". Cike da jin dadi da gamsuwa tace "shegia Yas, kin ko tsotso nonon Er Rabi, wallahi zaki fi Er Rabi tsula tsiya don a idonki naga ba Wasa". Da wannan Yesmin ta koma London don kammala karatunta. *BAYAN WASU 'YAN WATANNIN DA BASU KAI SHEKARA BA* Yesmin ta shigo Gidan Alhaji Zaki da Sallama. Hudu ya zo taryanta, guntun murmushi ta mishi ta wuce shi tsaye, Annah ta rungumeta tana Oyoyo Aunty Yesmin. "Annah ya kike ya school? tace "lafiya lau gobe zanyi Jamb ma" "inye Allah ya bada saa" Aunty Shafa tazo da murnarta tace "Oyoyo Mutanen Ingila, sannunku da zuwa" Gaisawa sukayi sosai bayan duk suka mata murnan kamalla karatun Likitanci da tayi, ta kuma yi Qualification Exams ta ci, yanzu saura HouseManship sai ta tafi Service. Hudu yace "Aure fa?" Yesmin tace "Lokaci ne" Hudu da mummunan murmushinshi yace "In fito?" tace "daga Mota?" Annah Ta fashe da daria, ya kalleta rai bace yace "Zanci Uwarki" Shafa ta hade rai tace "Ni kenan". Zaid ne ya shigo ko Sallama babu, ba tare da ya kalli inda suke ba ya wuce kai tsaye dakin Dalo. Yesmin ta bishi da kallo ganin ya chanza kama, ba da dadewa ba ya fita ya wuce ko kallonsu beyi ba, Hudu da Hajia Shafa suka bi bayanshi da ashar da zagi. Haka kurum taji gabanta ya fadi, da sauri ta tashi tace "barinje gida" a tare sukace "tun yanzu?" Bakinta ya fara rawa wai "eh wallahi dama zuwa nayi na gaisheku" kafin su sake cewa ta figi jakkarta ta fita tana "sai anjima" Shafa tace "ki gaida Mamarku" ba ta amsa ba. Hudu yace "kai aunty ban yarda da Yesmin ba, muje mu gani". Bayan Zaid ta bi ta na kiranshi Chak ya tsaya ya juyo da murmushi yace "tun a Parlor naji k'amshinki". Tace "shine baka juyo ba?" Yace "kina tare da wanda bana k'aunar hada ido dasu, wurin dalo naje". "Lahh dalo na ciki ba ta zo mun gaisa ba?" "Eh aikam tana ciki, ba zata fito ba? Ke dai barta da zaman daki" "kamar mai takaba?" Dariya sukayi baki daya. Kallonshi takeyi sosai tace "Me ya sameka?" Murmushi mai kama da yak'e yayi yace "mefa?" tace "Zaidd, me ya sameka? Are you sick? You look pale" yace "maybe I am just tired" tace "ba wani gajia, you are sick, ka zo in dubaka" dariya yayi yace "Dr Yesmin, you dont have a License" tace "yet, amma a hankali zan samu, kazo in dubaka donAllah, in baka yarda dani ba Akwai friends dinka ai a General Hospital muje su duba ka". Yace "su waye?" Da mamaki tace "kar ka ce min baka da whereabouts din kowa?". Kai ya girgiza alamun aa tace"har Aliyu A Aliyu?" Ya gyada kai alamun "eh" ta bude baki tace "your bestfriend Zaid, you dont have contact with him...this is serious". Kafin yace wani abu sai ji sukayi cikin fushi ance "Yesmin, me kikeyi a nan?". Ta waiga taga Aunty Shafa, Hudu da Annah, dama Zaid na kallonsu, Yesmin ta maida kallonta kan Zaid tace "zan dawo dubaka, ko ka gaya min matsalarka or i force you to a hospital". Ta juya ga su Aunty Shafa tace "dama yanzun zan tafi". Ta wuce ta barsu cike da mamaki. Zaid ya hade gabas da yamma ya hade rai ya shige daki. Hudu bakinciki kamar ya kasheshi ya ga Zaid da Yesmin dinshi tare Yace "Aunty ko sun san juna ne?". Cike da fushi tace "a gidan ubanwa suka san juna? K'ila ganinta yayi ya tareta kasan dan akuya ne". "Shege" cewar Hudu. Washegari ta dawo, ko cikin Gida bata yi ba ta wuce BQ, ta na shiga taga Zaid na wani irin Tari mai hade da Jini. Wani tsalle ta daka kan gadonshi inda yake zaune "Zaid Jiniii?" Ganinta ya sashi fara kauda kanshi. "You are coughing out blood" "Yesmin it's nothing please" "Kana tarin jini kuma kace min its Nothing, ka tashi we are going to the hospital ?" "Yesmin calm down, you are over reacting". "Oh haba dai? To yi hakuri i am over reacting, you are coughing out blood and you are so stupid to realise what that means". "Yesmin na kusa shekara ina tarin Jini". Mutuwar tsaye tayi, duk wani lakka na jikinta ya mutu, ta dade a k'ame kafin ta samu da kyar ta bude jakkarta ta ciro Tissue pape bata damu da Kazantar da ke bakinshi ba ta sa tissue ta dinga goge mai baki. Hawaye na zuba daga idanunta ta ki yarda ta hada ido dashi, har sai da ta gama ta kwashe dattin ta je waje ta zubar ta dawo. Fuska daure tace "ka tashi mu tafi Asibiti, bana son gardama Zaid, ka tashi kawai mu tafi". Murya chan kasa yace "Yesmin..." Ta katseshi ta hanyar cewa "Zaid, zamuje Asibiti yanzu da kai, gardama ko jayyaya bana so". Jim ya dan yi kafin ya Tashi, jallabiyan da ke kan Gado kawai ya zura, ta fita ya bita a baya. A parking lot suka tsaya. Hudu ya fara ganinsu tare kafin ya tabo Hajia Shafa, da mamaki Shafaatu tace "Yesmin?? Yaushe kika zo?" Hankali tashe tace "Aunty Ina Zuwa, barin kai Zaid Asibiti". Hajia Shafa ta figo Yesmin ta ja ta gefe tace "yesmin me kike shirin yi?" A rude tace "tarin jini yakeyi, ya kamata na kaishi Asibiti". Shafa tace "ya mutu ma, ina ruwanki dashi?". Wani kallo ta mata tace "ba zai mutu ba, asibiti zan kaishi, kuma zasuyi treating dinshi, da yardan Allah zai warke". Kafin tace waniabu ta fincike hannunta ta iske Zaid tare da bude mai gaban Mota ya shiga ta mayar ta rufe kafin ta zagaya wurin kujeran driver ta shiga ta kunna mota tareda barin Gidan a sittin, barin su Hajia da tsananin Mamaki". Cikin Gida suka koma rai a bace Kasuwar da basu je ba kenan. A hanya ta finciki Motarta ta zaro waya ta kira Dr Aliyu. "Hello Dr Ali kana ina donAllah?". "Hello K'amshi, ina Doctors Quaters". "DonAllah yi maza ka fito Asibiti, gani kan hanya" Ba ta tsaya jin me zaice ba ta kashe waya. Zaid yace "Yesmin duk wannan is not necessary, ki tsaida motar muyi magana" banza tayi dashi ta k'yaleshi, ta cigaba da Jan Motar. "Atleast kiyi tuk'ia hankali". Bata kulashi ba har sai da suka zo Asibiti, ta sake kiran Dr Ali taji ana ina. Nan ya ce mata yana consultation Room na Opd. Chan suka nufa. Dr Ali ya gansu ya k'araso don su hade yana cewa" "Yesmin Emergency ne? Ya Illahi wani kamar My Guy Zaid Ni" Murmushi Zaid yayi yace "Sunana Zaid Kai, babana ya kake". A tsorace ya kalli Zaid kafin ya waiga ya kalli K'amshi wanda tayi saurin kawar da kai". Tuni Dr Ali ya rungume abokinshi yana kiran "abokina meya sameka, rana daya kawai ka bace bat no contact nothing, what happened to you man?". K'amshi tace "nikam kar ma ku fara hiran bayan rabuwa dinnan. Dr Ali donAllah mu shiga kayi checking dinshi". Shigewa tayi cikin CR din ta bar su tsaye, ko wannensu da abunda yake sakawa a rai suka bi bayanta. Dr Aliyu ya zauna Zaid ya zauna shima. Dr Aliyu yace "Zaid, ina so na san meke maka ciwo, i need you to tell me the truth akan duk wani tambayan da zan maka". Zaid ya jinjina kai duk da ya san ba wani reason da zai sa ya kasance a nan tunda ya riga da ya san matsalarshi, kawai nan zaa yi ta jan magana ne ana maida shi wani big deal. "Zaid me ya sa kuka zo Asibiti" "Tari nakeyi" "Akwai Mura?" "Aa" "Wani kalar tari ne?" "Green ne attimes yellow" "Akwai Jini?" "Eh" Dr Aliyu yayi dan jim kafin yace; "In kana tari k'irjinka na ciwo"? "Eh". Sosai Dr Ali ke kallon Zaid ido cikin Ido, ya san Zaid for long, Zaid jajirtace ne, duk da Course dinsu ba daya ba don Shi Zaid Civil Engineering ya karanta shi kuma Ali ya karanta Medicine amma wurin kwnanan su daya, banda wauta na dan fari bai san Zaid da wani shashanci ba ko halin banza amma bari ya tambayeshi yaji. "Zaid kana shan Giya?" "Aa bana sha" "Sigari fa?" "Eh ina sha" "Sosai ko kadan" "Sosai" "Ka na shan kara biyu a kwana 1?" "Ina shan Kwali daya ko fi a rana daya". A tsorace Dr Ali yake rubutu yace "Inalillahi, Zaid Akwai investigations din da zaayi yanzun nan, zaa ja jininka, zaka bada sample din kakinka, zaa dau hoton Kirjinka da na Huhunka" Wata nurse ya kira yace Zaid ya bita. Yesmin ta shigo ciki tace "Yadai Alee?" Report sheet din ya bata ta karanta hannunta chushe cikin kitson attachment dinta. "Zaid is getting himself in real trouble, Ya Allah". Dr Ali yace "K'amshi, donAllah me ya faru da Zaid? He is no longer Zaidun da na sani". A tak'aice tace "He is no longer that kam". Zaune sukayi jugum jugum suna jira Zaid su dawo har 1hr ta shure, fargaba fal kirjin k'amshi amma son ta samu sauk'i tace "Dr Ali baka da patients ne, ba ka zuwa rounds?" Shima jiki a sanyaye yace "ba nike call ba yau". Zaid ya shigo da Sallama yace "yadai kamar masu zaman makoki?" Yesmin tace "an gama investigations din? "Yeah wai sai gobe zaa karbi duka results din Muje ki maidani Gida." Dr Ali yace "HELLO Ina son sanin abunda ke faruwa, donAllah muje Dr's quarters". Zaid yace "muje to" Tare suka fita, Yesmin na gaba suna binta a baya, jikinsu duk yayi sanyi, suka nufi Doctor's Qtrs, fira suka sha Sosai har bayan laasar suna Gidan Dr Ali, nan dai suka taru suka bashi shawara, suna bashi bakin wannan shaye-shayen ba me bullewa bane, ya bari, yace "to zai bari InshaAllah". Yesmin ta dawo da shi Gida, ta shiga wurin Aunty Shafa, ta cika tayi pam. "Wai Uban meye hadinki da Zaid? Ko ba ki san duk dunia banda abun k'i kamarshi ba?". Yesmin tace "Nikam banda abun So kamar shi". Aiko ta daga hannu ta mare Yesmin, Yesmin tace "ni kika mara? To ki tabbatar kamar kin daga hannu ne kin mari Mommyna". Ta fice da sauri Hajia Shafa'atu ta biyo bayanta tana kwala mata kira amma tayi banza da ita, sai Shafa'atu ta fara nadamar marinta, motarta ta fada ta figa sai gida, tana isa gida ta tasa mamarta tama mata kuka wiwi, hankalin Er Rabi yayi mugun tashi, tace "uban wa ya mareki na batar da mutum". Tace "mommy kawarkice Hajia Shafa'atu" cikin daga murya tace "Shafar ce ta mareki? Aiko zata ga tashin hankali". Er Rabi ta iske Hajia Shafa har Gida, abunda Shafa ke tsoro kenan, ta manta Er Rabi bata da mutunci in aka taba yayanta, bata hada yranta da kowa da komai ba. Kika dauki hannunki ki ka mari diyata? Ni Shafa? Bayan duk abubuwan da na miki? Kinsan sirrinki babu wanda babu a hannuna ko?wallahi kiyi a hankali duk randa kika sake gigin taba min yarinya wallahi daidai yake da tonuwar Asirinki". Ta juya ta barta tsaye jikina na rawa. Bayan Maghrib ta kwashi jiki ita da Hudu da Annah ta nufi gidan Er Rabi don basu hakuri. Er Rabi tace "me kuka zo yi min a gida?" Kwantar da kai Hajia Shafaatu tayi tace "haba Kawata, ina diyata Yesmin? Zuwa nayi na bata hakuri, Er Rabi ki fahimceni, wai Yesmin DANMAKAHO take so, wai nace ta rabu dashi wai ba zata rabu dashi ba, shine zuciya ta ci ni na mareta, amma kinsan wallahi ba da san raina bane, ina Yesmin din take na bata hakuri". Er Rabi tace "ai lallabata zaayi har ta rabu dashi, ba wai ki sa mata karfi ba, nidai kar a sake taba min yarinya, sai a zauna lafia". Tace "na yarda". Er Rabi ta kira Yesmin ta fito a yangace "Er Rabi tace baby meye hadinki da Dan Makaho?" A wulakance take kallonsu tare da yatsina fuska tace waye haka?" Tace "yaron gidan Anty Shafa'atu" "Oh wai Zaid?" Suka kalli juna gami da tabe baki tace "eh shi". "Okay Zaid Ali Zaki Friend dina ne tun yana London, yana Cambridge ina Oxford so we know eachother for long, and relationship that i have with you ba zai hanani cigaba da abotana da shi ba, so incase kin ganni a gidanki to wurinshi na zo ba wurinki ba". Duk da ran Hajia Shafa'atu bace yake ta kwantar da kai tace "yi hakuri diyata, ai gidana gidanku ne, kina iya zuwa duk lokacin da kike so kinji diyata?" Bata amsata ba ta tashi ta shige ciki. Hajia Er Rabi tace "lallabata zaayi har ta rabu dashi, ban son matsi kin gane?" Da sauri ta amsa da eh ranta a bace. Washegari kuwa Yesmin ta dira gaban gate din Gidan Alhaji Zaki. Wayar Zaid ta kira tace tana k'ofar gida Dama ya shirya yana fitowa suka wuce Asibiti bayan ta shaida ma Ali zuwansu yace yana Consulting room din da suka hadu jiya. Jiki a sanyaye ya amsa sallamar su, zama sukayi suna kallon juna. Da kyar suka gaisa. Dr Aliyu yace “anyi compiling results din duka gasu nan” Zaid da karfin hali yace “gaya min me ke samun danka baba?” Yesmin ta mike zata fita Zaid ya rik’o hannunta yace “haba madam, ki kawo ni Asibiti kuma ki tafi ki kyaleni sam” “Zaid please” Dr Ali yace “K’amshi gashi ki duba kigani” Ta girgiza kai Zaid yace “come on, take it, duba kigani mana” Hannu ta sa jikinta na dan rawa Ta duba paper na farko Ta duba na biyu Ta duba paper na ukku Ta duba Xray din Sai ta fashe da wani irin kuka. Murmushin takaici Zaid yayi yace “Nifa na sani, i know”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DANMAKAHO 😉 BABI NA SHA TARA 1⃣9⃣ (ILLAR SIGARI 🚬) Dr Ali yace “haba k’amshi, kar ki tsoaratar da Patient, soon fa zaki fara HouseManship, haka zaki dinga sanar musu da results? K’amshi, ina so ki kama kanki yanzu, ki kwantar da hankalinki donAllah”. Zaid yace “Huh, to meye? Ni ai na san ciwona, na san matsalata, ba sai kun sakaya komai ba”. Dr Ali yace “Zaid, you are sick” Zaid yace “i know” Dr Ali yace “Busan hayaki na illata kusan ko wani gaba na jikin mutum kamar ciwon Huhu, ciwon Zuciya, cutar Mak’ogaro wato Bronchitis, cutar jijiyoyin jini, hak’ark’ari ko awaza, ido, baki, gabar haihuwa, k’ashi, mara da sauransu”. Numfashi ya aje yace “Zaid, munyi investigating jikinka, sakamakon busan hayakin da kakeyi wanda ba sigari kadai bane har da wiwi, Daya daga cikin jijiyoyin dake bada jini ta samu matsala, gab take da ballewa, a yanzu baka da Athma amma rashin daina shan sigari na iya janyo maka Athma, Alhamdulilah lafiyar Huhunka kalau, amma rashin daina shan sigari na iya taba maka Huhunka wanda wallahi Zaid akwai mugun damuwa in ba ka daina shan Sigari ba. Zaid akwai Tuberculosis a tattare da kai, duk da dai minor ne, possibility of it becoming major da yawa ne, tunda you are on the verge of coughing out blood, kuma abinci bai dameka ba, so TB din can be cured tun kafin yayi worsening”. Yesmin k’amshi hawaye ke kwaranyowa daga idanunta, shi ko Zaid cewa yayi “nifa nasan banda lafia, but bansan haka abun yake ba”. Dr Ali yace “kaje Asibiti? Ko mene?” Zaid yayi murmushi mai ciwo yace “banzo Asibiti ba, kawai tuna watannin da suka wuce nasan jikina ya chanza, in nayi tari k’irji na na ciwo, to nasan wallahi banda lafia, kuma its obvious Sigari ne, tunda ina mishi Shan fitan hankali”. Dr ya fara mai fada “haba Zaid, da tun a lokacin kazo Asibiti ai da an rage wani abun, da komai ba yi worsening ba, ciwo ba a mishi zurfin ciki, da anga slight change, kamata yayi a garzayo Asibiti”. Zaid yace “nifa Its Fine” Cikin muryan kuka Yesmin tace “dallah, its not fine, Ali donAllah ka rubuta mishi magani, and advice him as a Doctor and as a friend”. Rubutu yayi sosai a Wani takarda kafin ya dago ya kallesu, mik’a ma Yesmin takardan yayi yace “gashi magungunan ne, a siya ya fara Medication ASAP”. Yesmin tace “InshaAllah kam, yanzu zaa siya”. Tashi tayi tace barinje na siyo kafin ku gama magana”. Tashi tayi ba wanda yace mata komai. Gyara Zama Doctor yayi yace “Chronic obstructive pulmonary disease (COPD) is a chronic inflammatory lung disease that causes obstructed airflow from the lungs. Wannan shine yake kama duk wani rik’ak’e a shan Sigari, wanda in ya kamashi, in Allah be sauwake ba sai dai mutuwar mutum. Alamominshi sune; Karancin Numfashi musamman wurin yin ayyukan yau da kullum kamar tafiya, Atishawa, k’ank’ancewar k’irji, kaikayin mak’ogaro da farin safiya, chronic tari da mura da zai haifar da majna da tasono wanda zaa ganshi yellow, fari ko green k’arara, baki zai zamu blue yatsu ma haka, yawan gajia da kasala, rama, kumburin kafa, guiwa da duk wani gaba na jiki”. “Kafin yazo ga haka Zaid, donAllah ka yi ma kanka fada ka datsar da wannan dabia ta shan sigari a busawa jiki hayak’i, Zaid, nasan its hard, you are addicted to smoking, it would be hard for you to stop now, amma zakayi duk yanda zakayi ka rabu da Sigari rabuwa na har abada, medication dinka donAllah ka dinga yi, kar ka aje magungunan nan, you have to be strong for your Sister Okay?”. Zaid yace “InshaAllah zan bari”. “Allah ya baka iko” ya amsa da “Ameen” Haka yayi ta mishi nasiha da k’ara karanto mai illolin hayak’i har Yesmin ta dawo dauke da Ledoji. Dr Ali ta ba, nan ya ware duka magungunan ya masu bayani da yanda zaiyi amfani da su, godia suka mishi, Zaid ya kwashi ledojin suka fita. A cikin Mota ya ga duk ta wani damu yace “Yesmin” da sauri ta katseshi tace “donAllah kar ka ce min komai in har ba zaka ce min kayi quitting Sigari ba”. Numfashi ya ja ya sake yace “Yazz banson miki k’arya, amma its not easy, i am addicted fa”. Hannu ta sa a bakinshi tace “shhh, kar ma ka saka a ranka wai ba zaka iya ba, wallahi zaka iya, let me help you please”. Hannu ya sa ya murza kannanen idonshi yace “Okay” kafin ya maida kanshi kan kujera ya kinshingida, ganin haka ya sata saka seatbelt tare da yi ma Motan Key. Sai da ta tsaya Yusrah’s Kitchen ta musu Take away din Abinci kafin suka wuce Gida, straight dakinshi suka nufa, sai da suka ci Abinci kafin ta ballo mishi magungunan kamar yanda Dr ya musu bayani, ba gardama ya karba ya afa duka kusan guda Goma a baki ya sha. “Yesmin kije Gida ki huta donAllah” kallonshi tayi cike da so da kauna tace “aa zan tsaya tare da kai”. Yace “aa donAllah, ki tafi, na ji sauk’i, dama chan ba abunda ke min ciwo, kawai kece da over reacting” harararshi tayi cike da k’auna tace “naji din”. Yace “dagaske kije Gida, in tsoro kike, na miki Alkawarin ba zan sha sigari ba”. Murmushi tayi tare da mik’ewa ta dau jakkarta gami da cewa “I trust You, zan kiraka every minute of every hour”. Murmushi yayi yace “kar kuma a dameni, zan sha magani a lokaci”. Murmushi sukayi a tare bata san lokacin da tace “I Love You” ba. Sosai ya k’ame k’am yana kallonta yana san karantar fuskarta, ita kam dan daburcewa tayi ta rasa gaba zatayi ko baya. Murmushi yayi yace “ki kula da kanki K’amshi, kiyi tuk’i a hankali, kar ki damu da yawa a kan Zaid, Zaid ba zai sha Sigari ba”. Wani farinciki ke ratsa zuciyarta tace “Madallah da Zaid, zan zo na ganshi Gobe, Sai Allah ya kaimu”. Yace “Allah ya kaimu” Sallamar kenan ta tafi ba tare da ta shiga Gidan Anty Shafa’atu ba. Zaid kam kamar yayi hauka, burinshi ya sha Sigari, ji yake ko wani gaba na jikinshi na kira mishi Sigari, safa da marwa yayi tayi, kwashe Sigarin yayi duka na dakin ya fita dasu zuwa Bencin Eskaley. Ganinshi ya sa su Tero ihu da murna, mik’a musu yayi yayi saurin juyawa don kar su fara sha gabanshi ya ji shima yana son Tabawa. Ranar a dakin Dalo ya yini don kar ya kadaice har zuciyarshi ta fi karfinshi ya sha Sigari. Haka ma washegari, har akayi kwana uku Zaid be sha Sigari ba, amma da ka ganshi kasan bai lafia, duk ya tsomare, kullum sai Yesmin tzo duba shi, kuma tana jin dadin yanda yake responding to treatment. A rana ta hudun ne Alhaji Ali yace an mishi Sata naira dubu dari 5, nan take Shafa’atu tace “ai Zaid ne, ta ganshi ya fito daga Dakin”. Ba Bincike Alhaji Ali ya Bi Zaid daki ya hau dukanshi ko ta ina, yana laantarshi yana tsine mishi ba tare da ya damu da yanayin da Zaid din ke ciki ba. Nan take ya kira Police Station aka zo aka tafi da Zaid, rannan Dalo ta yi kuka kamar zata mutu. Alhaji Ali yace da DPO ku nakasa min Shi har sai ya fito man da kudina, ana kai Zaid bayan karta aka rufe shi da duka ko ta ina, ga rashin Lafia shi kam Zaid be san dukan me ake mishi ba, kuma ya k’i furta kalman Bani bane. Yesmin tayi ta kiran wayarshi be dauka, hankalinta ya tashi, ta k’araso Gidan, dakinshi ta wuce straight bashi ba alamunshi. Sai wayarshi da ta gani kan gado,a sukwane ta shiga cikin Gida dakin Dalo ta isketa durkushe tana kuka, da sauri ta taryota jikinta tana tambayarta baasi. Dalo ta kwashe komai ta gaya mata, hankalinta ya tashi, ta fita da sauri, ta shiga Motarta ta wuce Police Station don amsan bailing Zaid, amma fir aka k’i bada bailing shi. Tunda case din gidane wai sai wanda ya sa aka kulleshi yake da daman firdoshi. Rasa abunyi Yesmin tayi. Taci kuka ta gode Allah Sauro bata so ya tabashi balle wani abu babba da sunan duka. Ya zatayi? Taya zata fitar da masoyinta daga cikin wannan k’angin?. Riii daga Police Station ta wuce Gidan ALHAJI Ali. A cikin gida daga inda ake parking Mota ta iske Dalo ta hade kai da bango. Ta na ganinta ta rugo ta rungumeta tana kuka. “Aunty Yesmin donAllah bani wayarki na kira Nene taje ta firdo min da Yayana, Nene kadai ce zata iya fito dashi, bamu da kowa sai ita”. Yesmin ta kalleta tace “Dalo ina so ki yarda dani kingane? Yanzu ba Nene kadai ne da ku ba, ina nan tare da ku, i want you to trust me”. Hannunta ta ja zuwa cikin Gidan inda Hudu da Hajia Shafa’atu suke zaune, suna ganinta da yanayinta suka mik’e tsaye. Kallon Dalo tayi tace “je ki daki ina zuwa”. Da sauri ta wuce daki tana haki. Kallon Hudu tayi a kyamace kafin ta waiga ta kalli Anty Shafa’atu tace “kina jina, ina so ki ba Mijinki Umurni ya firdo min Zaid” Aunty Shafa tace “Yesmin, ki yi hankali dani, ni ba tsararki bace, kar ki dinga ganin ina lallabaki kice zaki kawo kin raini, ba ruwanki da duk abunda ya faru a gidana”. Yesmin ta kankance idonta tace “kece zakiyi hankali dani, ina da sirrinki a tafin hannuna, sosai na san komanki, shekarunki 15 zaune kina zaman jiran Alhaji Ali, ke harta mahaifin Annah wanda kuka...” da sauri ta toshe mata baki ta na huci don sirri ne daga ita sai Er Rabi suka sani, bata san Er Rabi sakara bace tana tatauna sirrinta da diyarta, ya zata yi mata haka? Meyasa zata mata haka? Wannan maganar ko Hudu bata so ya sani. A dakile tace “Yesmin, me kike so ayi yanzu?”. Ture hannunta tayi daga bakinta tace “ki sa Mijinki ya firdo Zaid daga Cell”. Wayarta ta ciro a charge ta lates wayar Alhaji Ali, cike da umurni tace. “Alhajina, ka sa su sake Zaid” “Aa kar ka damu, ya dawo gida kawai bakomai”. Ta kalleta tace “Angama” Yesmin tayi murmushi tace “barkanki” Ta juya ta fita daga Parlorn Hudu da mamaki yace “Aunty, maganar me takeyi?” Banza Shafa tayi dashi ta wuce daki tana hucin tana so ta san ta yanda zatayi maganin Yesmin. Yesmin ta jira a Dakin Zaid kusan hour daya, sai ko gashi ya shigo rai a bace, dauke da kwalayen sigari kusan 5, jikinshi ko ina bari yake, wai shi zaace ya saci kudin babanshi? Shi Zaid zaa lakafa ma Sata?”. Yesmin ta zo rik’eshi ya daka mata wani irin tsawa wanda ya kada mata yan hanji, janta yayi ya fitar da ita waje tare da rufe kofar yana jin magiyarta na ya bude k’ofa amma fir ya k’i. “Don Girma da Darajan Allah kar ka sha Sigarin nan, Zaid akwai hanyoyin da zaka mance damuwanka ba tare da kasha komai ba,donAllah Zaid” be ma san tana yi ba. Kamar mayuwanci ya kunna sigari ya fara Zuk’anta irin an dade baa hadun nan ba, ya shanye kwali daya. Ya kwance kullin world ya hadeta ya fara zuk’anta ba sassautawa sai da ta kai mai karo sannan yayi Mankass kan gadonshi. Baccin Awa Hudu yayi, kafin ya tashi jikinshi duk a mace, amma kafin ya bar kan Gadon sai da ya kunna ma wata sigarin wuta, sai ya tashi ya bude k’ofa da niyyar fita, Yesmin ce zaune kan dakali tana waya da sauri ya murje sigarin da k’afa yana fadin “Ohh Yesmin”. Taci kuka harta gode Allah. Riko hannunta yazoyi ta ja da baya Ya sake yunk’urin rikota tace “ka k’yaleni” Chan kasan mak’ogaro yace “Yesminnn” Tace “ni ka barni” Hannunta ya ja suka koma daki. “Yesmin i am sorry” Yesmin tace “Zaid donAllah ka rayu, live healthy, if your life is meaningless to you ni it means the world to me, don Girman Allah live well”. Zaid ya murmusa ya rik’o hanayenta duka yace “Yesmin kinga irin life din da nake living? Babana Mahaifina ya lak’a min Sata, ya kaini Police station, aka min dukan mutuwa, babana mahaifi fa, tsinuwa, laanta suna kaina,to wani jin dadi ya rage min? Gaya min, meyasa ba zan sha abinda ya fi sigari ba?” Kuka Yesmin take sosai, harda Majina, ya girgiza mata kai yace “Aa, Yesmin, ki tayani addua, dont stress yourself, na san kina min k’okari, nasani kina kan yi min kokari, amma donAllah kar ki ba kanki wahala, ba zan iya daina shan sigari ba, cikin kwanaki ukun nan i felt like i am dying, na san ba zan wuce yau ban sha world ba, Yesmin i cant thank you enough, amma wallahi in lokacina yayi ko da shan sigari ko ba da shi ba, zan mutu, everything is formality, in lokacinka yayi ba makawa sai ka tafi, donAllah just pray for me Okay?”. Kuka takeyi ta kasa magana, da kyar ya lallabata tayi shiru. Tun daga ranan Yesmin sai tazo Gidan tare suke yini, sunyi mugun sabo da Dalo, har ta sai mata waya. Zaid da Dalo na son Yesmin sosai, tun Aunty Shafa na ma hajia Er Rabi mita har ta hakura, ba yanda zata yi da ita, hajia Er Rabi kuwa tace duk ranar da ta bata ma wa yesmin rai karshen alakarsu yazo. Yesmin ta zame mata ciwon ido. Zaid ya kan ji nauyin Yesmin sanin cewa ta na sonshi amma shi baya jin komai game da ita, tana da wuri mai girma a zuciyarshi da yafi karfin soyayya, yana sonta kamar yanda yake son Sadiya Dalo. Bata taba nuna mishi wai tana so ya sota ba, a cewarta ganinshi cikin farin ciki ya fiye mata komai, ta kalleshi ta ga murmushinshi ya isheta rayuwa. Yesmin Kamshi ta zamo wani jigo a gun Zaid da k’anwarshi Sadiya. Ta fara HouseManship dinta a General hospital for 10months kafin aka turata Ondo Akure tayi Service kafin ta dawo Katsina a Matsayin Dr Yesmin Hamis. C I G A B A N L A B A R I LABIBAAAA....... #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 BABI NA ASHIRIN2⃣0⃣ (KALLON KALLO👀) Yesmin K'amshi ta fito sanye da wata doguwar jallabiya mai kyaun tsiya, daga bacci ta tashi a dakin Aunty Shafa, k'amshinta ya cika gurin. Hudu ne kadai a Parlo, Auntyg Shafa'atu sun fita da Annah. Hudu na ganinta ya ji wani abu ya fizgeshi, da murmushi ya taryeta har ta zauna ta daura k'afa daya kan daya. Bude hak'oranshi yayi yace "Yas Yas, Allah ua miki kyau wallahi kamar ke kikayi kanki". Guntun murmushi tayi tace "aa ba ni nayi kaina ba, Allah ne yayi ni" Yak'e Hudu yayi, ya san Yesmin da datso magana dole sai yayi taka tsantsan. Yace "wai Dr Yas nayi ta kiranki baki dauka, ba kuma kya calling back, kuma na san kina ganin Missed call". Bata tanka shi ba, ta ciro wayarta tace "wai har yanzu baka gama ba? To ina jiranka a ciki please". Ta saka wayar cikin jakka tace "Uncle Hud, wallahi ina ganin missed calls dinka, attimes ma akan idona kake kira, but attimes kawai am not in the mood to pick your call kagane? Don na san usual surutanka zaka min, kuma ni banda energy din jinsu over and again kagane?". Kafin Hudu yace wani abu, ya shigo, babu wani abu sabo a jikinshi amma sosai ya ma K'amshi kyau. Tuni ta mik'e tsaye har ya tako har gabanta, kallon kallo suke wa juna, Hudu na zaune ya gama k'ullewa ya kalli wannan ya kalli wannan. Gira Zaid ya daga mata yace "Ya Da Kallon?". Murmushi ta sakar mai tace "Sosai kayi Kyau Zaiduna". Kafin Zaid yayi magana Hudu ya fincike Zaid ya mayar dashi gefe ya sha gaban K'amshi yana huci yace; "Yanzu ke Yesmin ta kan wannan Dan Makahon mara gata kike min wulakanci? Ta kanshi kike k'in saurarana?". Zaid yace "kai so kake na maka mugun bugu ko? Ka manta bugun tsiyan da na maka ko". Hannu K'amshi ta daga mai tace "kash Zaid, rabu dashi, ba girmanka bane magana da Agola, akwai rashin gata da ya wuce agolanci? Yana kasan kafar yayarshi yana fadanci kamar wani marok'i sai abunda ta dauka ta bashi, kamarshi yazo yayi katokato, cima zaune, ba cis ba as, duk randa babanka ya rabu da yayrshi ba baida sauran gata, bai da amfanin komai, kar ka sake ranka ya baci ta kan wannan cima zaune, barin kira Dalo, don Outing dinnan da ita zamu". Wuce su tayi duka, shi ko Zaid kashe ma Hudu ido yayi tare da rufa ma K'amshi baya. Wani Ihun bakinciki Hudu ya sake ba wanda ya kallo inda yake suka shige dakin Dalo a tare. K'amshi tace "Hajiya Sadiya tashi muje Yau outing zamuje" Ido ta zaro tace "ina zaku?" K'amshi ta dagota daga kwancen da take tace "dake zamu ko ma ina zamuje". Dalo ta sake ware idonta tace "ni ina zanje? Baba ya hanani fita fa". K'amshi tace "come on my friend get up and dress up". Dalo tace "Aunty Yasmin ki rufa min Asiri donAllah, wallahi Baba yace kar na sake na taba fita, ya Zaid gaya mata donAllah". Zaid ya murza idonshi da murmushi a fuskarshi yace "Ai fa Dalo Yesmin ba zata ji ji ba, tunda tace da ke zaaje da ke zaaje din, sai ta san yanda zatayi da baba in ya kama mu, ki tashi dai kafin ya dawo muje mu dawo". Dalo tace "in suka gaya mishi fa?" K'amshi tace "i know how to shut them up, trust me". Numfashi Dalo ta ja ta sake a hankali kafin ta bude Wardrobe ta ciro wani doguwar rigar da Mancy ta aiko mata dashi, gudun magana ne ya sa bata taba sakawa ba, Zaid yace "zan jiraku a waje" ya fita. Sai da ta shirya suka fita tare gaban Hudu wanda yana ganin fitowar Dalo ya dauko waya don shaida ma yayarshi. Zaid a gaba Dalo a baya Yesmin a seat din driver suka fita daga Gidan. Wayar Dalo ke ringing ko da ta duba Aunty shafa ce, sai da hanjin cikinta suka kada, ba kasafai Aunty shafa ke kiranta ba, in har ta kirata to ita Aunty shafa ta fita kuka tana so Dalo ta mata wani abu sai ta kirata. A daddare tace "donAllah ku maidani Gida bana son problem, ga Aunty shafa na kirana". Yesmin ta cigaba da tuk'inta tace "answer and put the phone on speaker". Bin umurnin Yesmin tayi ta kawo mata wayar daidai gemunta. Muryan Aunty Shafa ya karade Motar "Ke Sadiya Gidan Uban wa kika tafi harda sa sabbin kaya, karuwancin da kika saba zaki ko?". K'amshi tace "Wai ya Aunty Shafa? Dalo na tare dani, ko akwai matsala ne?" Da sauri ta sauta murya tace "kingane Yesmin Babanta ne be so tana fita a gidan". Yesmin tace "to muna tare ba wani wuri zataje ba". Yesmin ta ma Dalo alamu da ta katse kiran. Zaid na gaban Mota bece musu komai ba, ya san akwai wani abu da Yesmin ta sani wanda Shafa take tsoron a sani shiysa take daga mata tana kuma bari tana takata amma ko so daya be taba son sanin ko meye ba, abu daya ya sani shine ya yarda da Yesmin dari bida dari. Chimex Shawarma ta nufa dasu, su ka bada order aka gasa musu guda biyar duk chicken and sausage ta biya kafin suka je Havillah Ice Cream. Anan suka ci Shawarman bayan ta siya musu icecream. Fira sukayi su uku cike da kaunar Juna, sukayi pictures kafin suka koma mota, yawo kawai sukai tayi a Garin Katsina, Girman Yesmin ya k'aru a idon Zaid, don ya dade be ga Dalo cikin farinciki irin na yau ba, sai da ta tsaya a Dadin Kowa ta siya ma Dalo Chocolates kafin suka koma Gida gab da Maghrib. A kusan tare suka isa Gidan da Baba. Ganin Sadiya da Zaid a tare ya sa zuciyarshi nauyi, Yesmin tace "Ina wuni Daddy" ya amsa da murmushi "lafiya lau Yesmin yaushe aka zo?" Tace "dazun da safe na zo, na zo muku weekends" yace "ayyah mungode sosai ina sukayi posting dinki bayan service?" Tace "General hospital na Kankia" "Allah ya taimaka" yana kallon Zaid da ya dauke kai ita kuma Dalo ta na jiran saukan fada ko duka a daddare, be ce musu komai ba, gaba yayi zuciyarshi na mai nauyi, yaranshi.. ya Allah". Yesmin ta kallesu duka tace "muje ko?". Tayi gaba suka bi bayanta. Suna hanyar parlo sukaji muryan shafa'atu na cewa "Alhaji kaga Sadiya tun dazun ta fita, har yanzu ba ta dawo ba". Nan da nan fuskar baba ya chanza " Ina Sadiyar, ba zata huta ba sai ta jawo min magana cikin Gidan nan ko? To kafin ta kasheni ni sai na kasheta". Tuni Dalo ta koma bayan Yayanta a tsorace, shima Zaid ya tsorata da sudden change din baban, yanzu fa ya gansu, ya san tare suke, amma be ce komai ba, amma matarshi tayi magana duk ya koma wani zararre, matar nan ta maida masu mahaifi kamar wani toy. Yesmin ta kallesu tace "Relax, ba abunda zai faru" parlorn ta k'arasa shiga ta wurga ma Aunty Shafa'atubwani mugun harara mai ma'anoni da yawa. Hajia Shafa ta dan tsorata tace "Laah kaga Alhaji na manta, ashe Sadiya da Yesmin suka fita, na ma manta, kar ka damu". Kamar wani pagal ya washe hak'ora yace "au haba dai? To to to ashe suna tare da Yesmin, ai ba damuwa, barin shiga daki" yayi haba Hajia shafa tayi saurin rufa mai baya don bata shirya haduwa da Yesmin ba. Sai da suka kai Dalo har daki kafin suka fito a tare. Hudu da Annah suna tsaye a Parlo. Don Zaid ya k'ular da Hudu don ya san yana son Yesmin yace "Yesmin ayi rigegen zuwa dakina" da daria tayi saurin fita ya rikota ta fizge hannun ta arta a guje shima ya bita a gujen, bakinciki kamar ya kashe Hudu. Yanzu shi ke gaba tana biye dashi a baya sukayi BQ. Ita kuma ta fito daga dakinsu da Plates a hannu ta ga wata na bin Zaid suna gudu suna daria. Zuciar Labiba ya halba. Chak Zaid ya tsaya yana kallonta yanda itama take kallonshi, hakan yasa Yesmin chogewa itama don kallon abunda yake kallon. Budurwa ce ta gani tsaye daga chan bangaren tana kallonsu, daga inda take ta hango fushi a idon yarinyar da bata wuce 18 ba, kallon Zaid tayi ta ga hankalinshi kacokam na gun yarinyar da wani expression a fuskarshi da ta kasa gane ko menene. Yarinyar ta ga ta share wani abu a idonta kamar hawaye, ta wuce kitchen sauri sauri gudu gudu, a kan idonsu ta sake dawowa a guje ta fada daki. Wani jijiya Yesmin ta hango a kan Zaid duk ya damu. Jiki a sanyaye tace "Zaid who is She?" Murya chan k'asa yace "Noone". Kafin tace wani abu tuni yayi gaba ya wuce dakinshi tare da barinta tsaye. Gidansu Labiba Yesmin ta kalla kafin ta tsaya wani nazari kafin ta shiga dakin Zaid ta ganshi kwance rigingine duk yanayinshi ya chanza. Murmushi tayi tace "Yau ko ka tashi ka min Fira ko na je shagon Eskaley na zuk'i world". Dariya ya fashe tare da mik'ewa yana fadin "Me zanyi in babu ke k'amshi?". #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 BABI NA ASHIRIN DA DAYA 2⃣1⃣ (KISHI🤨😏) Labiba ta katse tsaye ta kasa zaune, girgiza k'afa kawai take, binibini sai ta lek'a window amma ba wani alamun sun fito, har yanzu suna ciki. Zaid na cikin daki tare da wata Macen da ba ita ba, sosai zuciyarta ke mata zafi da zugi. Da ita ce tayi yunkurin zuwa dakinshi da yace mata Mara Aji, to ita wannan me za a kirata dashi? Tunda har yunk'urin taba shi take. Tsaki ta buga mai k'arfi tare da cuno baki cikin k'unar rai chan kuma ta tashi ta sake lek'awa. Kiraye kirayen sallah taji na maghrib, hamdala tayi a zuciyarta ta na me murnan dole su fito suyi Sallah. Shiru shiru har ta fito tayi nata alwalan bata ga sun fito ba, yayyafi aka fara dama garin tun bayan laasar hadari ya hadu, da sauri ta shige daki tana fatan ya fito ya je Sallah. Har dai ta idar da Sallah tana ayyanawa a ranta sun fito a yayin da take sallahnTa na idar da sallah tayi tasbihinta a kan dardumanta take har aka kira Isha'i, ta tashi tayi Ishai ta hada da Shafa'i da Wutr. Ta na ji yayanta ya shigo tare da kullo Gidan alamun yau ya gama fita, tashi tayi ta shiga dakin Yayanta da Sallama. Zama tayi kusa da Amira ta sake gaidasu kamar yanda takeyi duk bayan sallahr da tayi sai ta gaidasu. Yayanta da Aunty Aseeyah suka amsa.Ameerah da sabit suka gaidata. Mallam Muhammad yace “nikam Labiba wani abu naji a cikin anguwa wai ko hatsaniya ya shiga tsakaninki da DanMakaho da ‘yan bencin eskaley” dumm gabanta ya yanke ya fadi, mak’ogaronta ya bushe da k’yar tace “waye kuma danmakaho?” Yayan yace “wannan yaron da ke nan Gidan Alhaji Zaki wanda ya samu matsala da matar babanshi kwanaki”. “Tabb yo ni ina na ganshi balle in samu hatsaniya dashi” ta shirgo karyan da ita kanta tayi mamakinta, yayan yace “wallahi kin dainji abunda ke yawo a Anguwa, yanzu bayan Masallaci Mallam Na’abba ke ce min ya ga kanwata na sa’in sa da dan makaho da yan bencin eskaley, ni dai na sha mamaki sosai har ina cewa me ya hada labiba da DanMakaho?”. Aunty Aseey ta chafe tace “wai baban Amira yanzu baka san gulman yan unguwan nan ba? Ana ganinta ta na zuwa makaranta har sun fara kawi ma gulma da k’arerayi, tunda kayi tafiyar nan ba fa inda muke zuwa, da ta dawo daga makaranta muna gark’ame a daki, to wallahi in ma sonta sukeyi su fito su fada ba wai su dinga hado k’aryan da bai da wani amfani ba, in banda k’arya mai zai hada Labiba da ‘yan shaye shaye?”. Mukut Labiba ta hadiye bak’in miyau, hankalinta na dagawa a duk lokacin da akace me zai hadata da dan shaye shaye? Amma a fuska yak’e takeyi. Mallam Muhammad yace “in ma gulma ya je musu kan har yau baa gyara bangon chan ba to inshaAllah zan gyara da na hada yan kudaden nan, bulo tsada yake shiyasa, amma ni k’anwata ba ruwanta da yan bencin Eskaley. Cike da rashin sanin yanda zaayi ta tashi tace barin shiga daki. Zuciyar Labiba na tsinkewa har yanzu hankalinta na ga dakin Danmakaho, zuciyarta na ingizata da taje ta ga su nan ko ba sa nan ko don hankalimta ya kwanta amma ina ba zata iya ba, Yayanta na gida, ba zata bashi dalilin gasgata maganganun yan Anguwa ba. Yesmin na fashin Sallah, ganin an fara yayyafi ya sa Zaid yin Maghrib da Isha’i a gida, nan suka cigaba da fira har karfe 10:30. Anty Aseeyah ta shigo da Sabit da yayi bacci dakin babansu, ta koma ta dauko Ameerah har zata fita ta tsaidata ta hanyar cewa “Aunty Asee” Aunty Asiya ta dan tsaya tace “yadai Aunty Labs?”. Labiba tayi murmushi tace “wai dama Jawad mukayi waya yanzu wai yace zaizo gobe” hak’ora Aunty Aseey ta yashe tace “ahh Mallam Jawad, aikam sai yazo Allah ya kawo shi lafia, zan gaya ma Yayan naki yanzu kuwa”. Murmushi Labiban tayi tace “to Aunty, in yace wayeshi? Kice mai cousin din besty Aisha ce” “kar ki damu, ki ba danuwan Aisha bane ai yasan wata rana dole a zo wurinki” murmushi kawai ta mata tace “sai da safe” “Allah ya kaimu Ameen” Aunty Aseey ta fita ta wuce dakin Mijinta. Labiba kashe datanta tayi ta mike ta rage kayan jikinta zuwa kayan bacci, ta fita don zuwa toilet. “Ki tashi na rakaki gida Yas dare na sake yi” fuska ta danyi tace “Zaiddd” girgiza kai yayi yace “Yesminnn to 11 fa, get up” a shagwabe ta tashi ya mik’e shima yace “oya” ganin tana niyyan sake zama ya sa shi rik’o hannunta ya ja, ita ko ta cigaba da bubbuga k’afa kamar ‘yar shekara4. “Zanyi Mafarkinka” yace “nikuma zanyi mafarkin kinyi mafarkina daria sukayi gabaki daya. Fitowarta daga Toilet saitin idonta kan su biyu, da taimakon wutan lantarkin da ke tsakar gidan da kuma hasken farin wata ya hasko mata Zaid da Yesmin suna tsaka da tsinkar fure a ganinta. K’irjinta ke barzanar fitowa, kenan tun kafin mangariba suke tare har yanzu? Me suke cewa? Hawaye masu dimi suka cigaba da gangaro mata, kasancewar garin akwai sanyi don yayyafin be dade da tsayawa ba atishawa yazo mata mai k’arfi. Da Zaid da Yesmin sukayi saurin kallon inda sukaji sautin Atishawan. Ganin ita suke kallo ya sata saurin shigewa daki har da dan tuntubenta. “Beebs” ya fada cikin wata irin murya wanda yake chan k’asan mak’oshi. Yesmin ta kalloshi tace “Wa?”. Be san maganar da yayi ba ya fito Yesmin tace “Ehen? Wacece?”. Zaid ya dan murji kanennen idonshi yace “Mak’wabtan mune” Yesmin tace “eh ai nagani, sai me kuma?” Bangon Gidansu ya fadi saboda ruwan da akayi kwanaki, to so kusan uku ana gyarawa ana sake wani ruwan yana rushewa-” Zaid “ba wannan ba cewa nayi wacece?” Kafadunshi ya daga sama yace “a gidan take, k’anwar mai gidan ce” yayi gaba, juywa tayi ta kalli Gidan, ta rantse tana ganin alamun mutum a daidai window din wani daki alamun kallonsu ake, ba ta da zabin da ya wuce tabi bayan Zaid din. Har bakin Parlorn cikin Gidan ya rakota inda Hudu ke zaune yana kallo, da mamaki ya bisu da kallo, ya kalli agogon dake sak’ale kan bango, duk zatonshi Yesmin na daki, ashe tana chan suna iskanci da DanMakaho. Yi sukayi kamar basu ganshi ba Yesmin tace “Zaid, kamar ya kamata na san ko wacece”. K’ura mata ido yayi sosai kafin yace “sunanta Labiba Ahmad, tana karatu a HUK Polytechnic, kina buk’atar sanin yanda tayi yarintarta ko abunda take so ta zama in the future?”. Duk da faduwan gaba ya Ziyarci Yesmin amma sai da ta murmusa tace “hakan ya isa, Goodnight Zaid” shima murmushin yayi yace “Goodnight Yas Yas” ta juya ta shige dakin dalo don nan take kwana, be shiga ba don ya san Dalo ta yi bacci ya juya shima ya fita ba tare da ya kalli Hudu ba. Hudu ya bi bayanshi ta zaguna marasa dadi amma beyi da karfi ba don ya san Mankas yanzu zai tada duk wanda yayi bacci a gidan da Tashancinshi. WASHEGARI Tunda yara suka tafi Tahfiz bata zauna ba, aiki takeyi, a ranar sai da ta cire duk yanar dake a saman ceiling, aka zo aka share Gidan. Mallam Muhammadu ya fito don tafiya kasuwa yace “Ahh su Aunty Labs yau fa ba zama saurayi zaizo” kunya ya bata ta sa hannu ta rufe fuska” Aunty Aseey tace “ai dai ka dawo ku gaisa ko?” Yace “eh to bari dai muga kasuwan” addua suka mishi a tare kafin suka rakashi har bakin k’ofa. “Labiba, kije kiyi baccin safenki, Abuja ba nan kusa bane” Labiba tace “wani bacci Aunty Asee? Yace fa ya taho” “ahh to ai dai koma meye sai dai Yayan naki ya aiko da cefanen ko?” Hakane “amma bari dai na dora sobon in yaso sai na hada na saka a fridge don yau da alama rana zaa k’wala”. Aunty Aseey tace “nidai barin je na kwanta” “to shikenan Aunty”. Labiba ta kasa tsaye ta kasa zaune ta je nan taje chan, ta goge nan ta goge chan. “Ki fito wallahi muje kan dining muyi breakfast” ta fada ta na jan hannunta. Dalo tace “Aunty Yas donAllah ki bari nayi kalacina a daki yanda na saba” Yesmin ta harareta tace “ba nace miki bana son musu ba, just standup muje muyi breakfast”. Dalo ta numfasa ta san gardama da Aunty Yasmin ba amfani ya sa ta tashi suka fita. Suna kan Dining table gabaki daya har Alhaji Alin. Kan dalo a k’asa suka isa bakin table, tunda suka fito idon Hudu ke kansu, sosai Hudu ke ganin kyaun Yesmin amma yau sai ya ga Yesmin tayi muni, ya ga Kyaun Dalo sosai ganin Yesmin da Dalo ya sa ya hango munin Yesmin a lokaci daya, ta fiye tsawo kuka tsohuwa ce, dalo kuwa bata fiye gajarta ba amma yarinyace shakaf, cikin seconds da ba su wuce 30 ba ya ayyano dalo a zahirance yana ayyana wasu abubuwa a zuciyanshi. Aunty Shafa ranta ya baci ganin Yesmin ta tunkaro table tare da Dalo. Da ido Yesmin ta mata magana ta jawo kujera ta zauna tare da cewa “Ina kwana Baba?” Alhaji Ali ya kalli Shafa ta galla mai harara yayi saurin kawar da kai ba tare da ya amsa gaisuwan dalon ba”. Dalo ba ta damu ba ta gaida Aunty Shafa tace “sannu ‘yar sarki jikan galadima, sai yanzu zaa tashi ba aikin fari bare na baki, anzo an zauna zaa cika k’undu”. Dalo ta daga ido ta kalli Aunty Yesmin, kamshi ta murmusa ta girgiza mata kai. Yesmin tace “Daddy ina kwana?” Da fara’a Alhaji Ali ya amsa, ta gaida Aunty shafa itama ta amsa, Annah tace “ina kwana Aunty Yas”. Aunty Yesmin tace “Lafiya lau Annah, ke kikayi breakfast dinnan hala?” Annah ta kyabe baki tace “ni zanyi abinci chabda, mommy ce tayi”. Yesmin tace “auu na zata ke kikayi, ashe ba banbanci ke da Dalon, duk ba aikin fari bare na baki sai dai a dafa kuzo ku cika k’undu ko Daddy?” Ta fada tana kallon Alhaji Ali, Alhaji Ali yak’e kawai yayi don baida ikon magana. Aunty Shafa ta san cewa bak’a Kamshi ta gaya mata tace “ku ci abinci kin tsaya jan mutane da surutu sarkin magana”. Dariya k’amshi tayi tace “Ok lets all eat”. Yesmin ta zuba ma Dalo Dankali da kwai da sauce din k’oda ta tsiyaya mata ruwan tea a cup, dalo duk a tsorace take bata ko son daga ido, godia ta mata kafin ta fara tsakurar abincin a hankali. Ba ka jin k’aran komai sai k’aran cokula, ji tayi wani abu na bi mata k’afa, ba ta biye ba ta cigaba da cin Abincinta. Amma sai ta ji abun na yawa har wurin guiwanta, gashi kuma bata sonyi kwakwaran motsi tayi laifi wurin babanta ko aunty Shafa. Sai ta share duk yanda take jin abun na damunta bata yi motsi ba, ashe wai Hudu ne ke shafar kafarta, kasa cigabawa tayi da cin Abinci, ta mik’e tsaye. K’amshi tace “yadai? Ina zaki?” Dalo ta kalli Hudu da sauri ta kawar da kanta don wani irin daniskan daga gira ya bi ta dashi tace “na k’oshi ne” Yesmin tace “come on my friend zauna kici Abinci” Dalo ta marairaice kamar zatayi kuka tace “dagaske Aunty Yas na k’oshi” Aunty Shafa tace “kema dai Yesmin tunda ta k’oshi ki kyaleta mana” kafin yesmin tayi magana Dalo tuni ta isa daki. Yesmin ta dauki plate and Cup din Dalo ta bi bayanta dashi ta shiga ta ganta zaune tace “ke wai ya?” Dalo tace “wallahi kawai i wasn’t comfortable” Yesmin ta harareta tace “in har bakya zama kusa da Mahaifinki ta ya kike so ku saba? Ansa ki cinye”. Da sauri ta amsa plate din Aunty Yesmin kuma ta fita ta cigaba da kalacinta, ta riga su gamawa ba tare da tace da kowa komai ba ta fita daga Parlorn, sun san BoysQuaters ta nufa. Tafiyarta takeyi wa ta hango? Labiba ce ke kai kawo tsakanin kitchen da wajen diban ruwa, tsayawa tayi tana kare ma yarinyar kallo, yarinyace karama, ba zata wuce shekarun su dalo ba, kishinta ya turniketa, a hankali ta fara takawa har sai da tazo boarder tsakanin gidaje biyun Labiba na waigowa ta ga mata tsaye. Bata karasa ciki ba ta murmusa mata, labiba ta kawar da kanta kamar bata ganta ba. Yesmin da murmushi tace “Labiba, ki gaisheni” da sauri Labiba ta kalleta, ta san cewa wannan ta girmeta nesa ba kusa ba, a k’alla zata bata shekaru 7 ko 8 chan kasan murya tace “Ina kwana” K’amshi ta murmusa har ta samo answer tambayarta, tace “Lafiya lau, aiki kikeyi ne?” Uhm kawai tace, murmushi ta sake mata tace “oya ayi aiki da kyau kar mama tayi fada” bata jira me labiba zatace ba ta juya ta shigewanta dakin Zaid. In ran Labiba yayi dubu ya baci, bata kin mutane, ranta sai yayi kuri yake baci, amma sosai Yesmin ta bata mata rai, haka kurum take jin haushinta, ta dade tsaye da roba a hannu, abunda yafi bata haushi shine ganin Yesmin ta shiga dakin Zaid, kamar ta janyota ta daba mata wuka takeji, zuciyarta Zafi Zafi zafi, kishi kishi kishi. Yesmin na shiga dakin Zaid ta danne kirjinta, zuciyarta kamar ya fito, tabbas yarinyar nan na son Zaid, ta karanto son Zaid a idanunta, tambayar shine Shin Zaid na Sonta? Waigawa tayi ta kalli Zaid da ke sheme kan Gado, da alama ko asuba beyi ba, kuma duk ta k’are ya banki shegiyar wato World jiya da daddare ba ta san sadda ta daka mata duka a baya ba. Kamar jira yake yayi firgigit ya tashi ganinta Yamutsutsuke idanunshi, hararshi tayi tace “bakayi sallah ba” yace “Uhm” ta sake galla mai uwar harara tace “ai sai ka tashi kaje kayi” sum sum ya wuce toilet ta samu wuri ta zauna zuciyarshi cike da tunanin Labiba, sai da yayo wanka kafin ya dauro alwala, ya shigo ya kalli gabas yayi asuba. Ya kallota yafe “ina kwana yas yas kamshi” Ba ta iya fushi dashi tace “ka kwana ladiya?” Yace “Alhamdulilah” tace “munyi breakfast na san ba zaka ci Abincin cikin gida ba shiyasa ban diba ma ba”. Murmushi yayi yace “zan hada da kaina” tace “ni yanzu kankia zaka rakani”. Yace “yadai?” Tace “lafiya lau, kayana zan kwaso, wai yajin aiki ake”. Yace “to daga yajin aiki sai a kwaso kaya?” Tace “to zaman me zamuyi?” Yace “ku kuma haka kuke? Tayi daria tace “nidai mu tafi”. Yace “Okay barin yi breakfast” Tace “muje mu siya a crispy sai mu wuce” Yace “Okay muje” “Wai kai baka da kaya ne sai wannan jallabiyan” Yace “Yesmmmin mu tafi” Dariya tayi tayi gaba ya bi bayanta tare da rufo dakin. A kan idonta suka fito suka tafi, hawaye masu dimi suka ziyarci idanunta. Jin motsin Aunty Asee ya sa ta goge hawayenta da sauri. “Baban Amirah be aiko ba?” Labiba tace “eh wai be kai ga aikowa ba”. Okay. Ba da dadea ba sai ga yaro da cefane daga kasuwa Labiba ta amsa ta gyara kayan miya ta yi blending. Aunty Aseeyah ta taimaka ta. Bayan Azahar sun gama tuwo miyan ogu da yaji stock fish da ganda ” Aunty Aseey tace “maza ki shiga kiyi wanka”. Labiba tayi wanka tayi alwala, bayan tayi sallah ta shirya cikin wani Swiss Lace black and red. Ta na cikin shiri Jawad ya kirata yace ya shigo Katsina zai yi Sallah a Masallacin matafiya da ke dandagoro sai ya karaso. Da kwatance Jawad ya iso Gidansu Labiba, be sha wahala ba don sun taba zuwa Tudun Matawalle da yayyinshi, har k’ofar gida Jawad yayi parking. Ta fito don tarbanshi. Sam be ganeta ba, wani irin kyau ta kara, hotunan da take turo mishi kwata kwata basuyi kama da ita a bayyane ba, sai gani yayi ganin da yayi mata a farko bata kai haka kyau ba, MashaAllah, tsarki ya tabbata ga sarkin da ya k’agi wannan hallitar. Takowa tayi cike da murmushi tace “Assalam Alaikum Jay, barka da zuwa Katsina ta dikko dakin kara” kasa amsata yayi sai murmushin da yake cizga baki zuwa wuy, da hannun ta mishi Alama da Bismillah. Tayi gaba, ya bita a baya kamar rak’umi da akala, har suka shiga gidan da Sallama, kasancewar ba wuta parlon akwai zafi ya sa ta shimfida musu babban darduma a waje. Zama yayi suka gaisa sosai. Labiba ta shiga daki tace ma Aunty Asiya su fito su gaisa. Hijab dinta ta saka suka fito tare, cike da girmamawa Jawad ya gaidata, ta tambayesu ya ya bar su Umma ya amsa da Alhamdulilah. Ciki ta shiga Labiba taje kitchen ta gabatar mai da Abinci a kan tray. Serving dinshi tayi, Jawad baya cin tuwo, amma yau sai da ya bude ciki ya ci tuwon nan mulmula daya da rabi, zobo da ya fara sha sai da ya shane kofi ya kuma kara, anya baby ba Aunty Aseey tayi abincin nan ba? Dariya tayi tace “ ta taimaka min da kwashe tuwo da tukawa, amma ni nayi miyana nayi sobona”. Dariya yayi yace “amma abincin yayi dadi sosai, baby wallahi kin k’ara kyau” Hannu ta sa ta rufe fuskarta. Binta kawai yake da mayattaten kallo, be iya surutu ba, be da hayaniya, sai ya zamana ma in ta ga kallon yayi yawa sai ta tambayeshi ina kaza ko ya kaza?. Jawad miskili ne, kallon kallo da murmushi yafi firan su yawa, suna zaune aka kira Laasar tace “muyi sallah ko?” Yace “eh k’asaru zanyi, amma yanzu zan tafi gidan Baban Usman sai naje na gaida Grannynmu sai naje masauki, anjima zan dawo na gaida Yaya”. Murmushi tayi tace “to shikenan” Aunty Asiya ta fito ya mata Sallama, Labiba ta rakashi har bakin Mota. Tsayawa sukayi suna kallon juna suna murmushi. Motarta ta danno layin, tun daga nesa ya hango ta tana yashe hak’ora kamar audaga, ita ko kamshi tukinta takeyi ba tare da ta san meke going ba, waigawan da zatayi taga jikin Zaid na kyarma a tsorace ta taka birki tace “Zaid are you Okay?” Kasa magana yayi amma jikinshi ba inda baya rawa, idonshi kan su, Yesmin ta maida idonta kan inda yake kallo. Kallo daya ta masu ta gano Labiba ce, ta kalli Zaid da ke tafasa a ranta tace menene haka? Kishi kenan?. Tuni Zaid ya fita daga motar ya nufesu, tafiya yake be san inda yake jefa kafanshi ba, wani abu Jay yace mata da ya sata daria sosai tana kallon gabas ta hango Zaid da ya tunkarosu kamar wani zaki, cikinta ya bada kululu, gabanta ya fadi, jawad ya juya mai baya be san me ke tunkaroshi ba, Labiba kam tsoro da fargaba sun mamayeta, bata san me zaiyi ba, nan take ta tuna karon Yan Bencin Eskaley da AbuSideeq basu kwashe da kyau ba, har yau bataji daga Abu Sideeq ba, tsoro ya sake mamayeta, tuni zufa ya keto mata, ganin yanayin Labiba ya sa Jawad saurin juyawa ga abunda take kallo. Hango wani yayi ya tunkarosu kamar namijin zaki... “Me ke shirin faruwa?” #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 BABI NA ASHIRIN DA BIYU 2⃣2⃣ (ZANCE 👫 ) "Me kake shirin yi? Meke kake tunani Zaid? Menene haka?" Tambayoyin da ke zuwa mai a kai kenan, daf da su ya tsaya chak, yana kallonsu daya bayan daya kafin ya dawo da kallonshi ga Yesmin da tayi saurin shan gabanshi tare da fadin "Sweetheart, saurin me kake haka?". Bakinshi ya mai nauyi da k'yar yace "bakomai, dama so nake na rigaki shiga Gida". Hannunta ta sagala ana shi ta jashi tace "nak'i wayon mu shiga a tare". Yace "motar fa?" Tace "na rufeta". Wuce su sukayi suka shige Gida, da Jawad da Labiba suka bi bayansu da ido kafin suka juyo suna kallon juna. Jawad mamakin abunda ya faru yanzu yakeyi, zai iya rantsewa da Allah cewa wannan tunkarosu yayi, wurinsu ya nufo, to ya akayi ya chanza akalan abun? Menene haka? Ya kalli Labiba da sauri ta girgiza mai kai! Da yake wani miskili ne be tsawaita abun ba sai yace ta shiga gida zai dawo anjima. Da yake a k'agare take da sauri ta juya ta shige Gida. Jawad ya kira wasu Almajirai biyu ya bude booth yace su kwashe kayan da ke ciki su kai cikin gidan chan, jiki na rawa suka kwaso kayyayakin cikin booth. Ya basu 200 sabuwa dal, sai da ya ga shigan su kafin ya shige motarshi ya mata key zuwa Gidan k'anin Babanshi Baba Usman. Isan Zaid da Yesmin BoysQuaters yayi daidai da shigowar yara dauke da kaya nik'inik'i suna shela "Sallam Alaikum wai ance gashi a ba Labiba". Dakatawa Zaid yayi daka shiga daki ya ga Labiba tayi wuf ta fito ta nufa yaran tace "wai inji wa?" Hade baki sukayi sukace "wani ne a waje a mota". Labiba ta bude baki tace "tohhhh" karban ledar tayi yaran su ka fita a guje tana waigawa ta hade ido da Zaid da Yesmin, wani mugun kallo ta karanta a Idanuwan Zaid. Ganin tafasan da Zaid yakeyi ne ya sa Yesmin riko hannunshi ta jashi zuwa dakinshi, labiba tsaye tayi nan ta bisu da idon da ya cika fal da hawaye. Muryan Aunty Asee taji ta na cewa "mai muka samu?" Da sauri ta mayar da hawayenta ta mik'a mata ledar tare da shigewa daki ta bar Auntyn tsaye a tsakar Gida, Auntyn bata dau komai ba ta biyota baya tare da zazage ledojin kan Gado. Leda daya kayan Zak'i ne kama daga Chocolates ne kalakala da biscuits cookies irin wanda taga ana talla a MBC2, dayar ledar kuma kayan shafa ne da turaruka masu k'amshi kala kala sai atamfar da taga an rubuta Juilius Holland sai wani Leshi. A tare suka kalli juna ganin kayan da ke zube kan Gado, Labiba ta budi baki tace "wannan irin kaya da yawa haka? Anya Aunty zan karba kuwa? Gaskia bari ya dawo Anjima zan mayar mai" Aunty tace "uhm uhm, kayan sunyi yawa ga tsada kuma, bari dai yayanki ya dawo a gwada mai, duk mai yace hakan zaayi". Labiba ba tace komai ba, Aunty Asee ta dauki chocolate diary milk ta fita tare da barin Labiba a daki ita kadai. Kallonshi kawai takeyi, yana zaune sai ajiyar zuciya yake sauke lokaci zuwa lokaci. Sosai ta tsura mishi ido, sai da ya lura da kallon da take mishi ya dawo dubanta. Yesmin tace "KISHI kenan?" Zaid ya murje idonshi na hagu yace "bangane ba" K'amshi tace "ba zaka gane ba, ni ai nagane" "Son yarinyar chan kake" Borin kunya ya fara "So? Wace yarinya? Ni bansan me kike magana akai ba". Yesmin ta yi wani murmushi mai takaici tace "ni na san maganar da nikeyi ai, kana son yarinyar chan, ka ganta tsaye da wani, zuciyanka na maka zafi, ranka na baci, bakinka na rawa, kishinta kakeyi". A hankali yace "I dont know what you are talking about Yas". Mik'ewa tayi tsaye ba tare da ta kalleshi ba tace "Bari inje Gida" ta fita. Kiran sunanta yayi "Yesmin" Ba ta juyo ba, bata tsaya ba ta bace wa ganinsa, bai da k'arfin bin bayanta, bai da karfin dawowa da ita, in shi a matsayinshi na Namiji yaji haka, ita ya take ji? God, me zaiyi yaji dadi? World kawai ya dauko ya zuk'e k'ulli uku yayi shameshame kan Gado. Tana a daki taji Sallaman Yayanta, shimfida matarshi ta mai a waje ta gabato mai da Abinci, yana ci yana santin dadi chan yace "ba dai bak'on Abuja ya tafi ba" Aunty Assy ta bashi amsa da "zai dawo bayan Isha'i" yace "ya dai ci tuwo ko?" Tayi daria tace "yaci kam". Daga waje taji Aunty Aseey na cewa "Labiba firdo ma Yayanki tsaraban Jawad". Sai da ta bata lokaci kafin ta fita jiki a sanyaye "Yaya sannu da zuwa" tsokanarta ya fara yi ta rufe fuska tana daria, bubbude mai kayan Aunty Aseey tayi tace "ka dai ga abun Arziki shine Labiba ke cewa sunyi yawa ko za ta mayar" yace "Aseeyah ba rokonshi akayi ba ai, ko rokonshi kikayi?" Da sauri ta girgiza kai yace "to kinga, abunda zaayi, in yazo anjima, zan yi magana dashi, zan tambayeshi in dagaske yakeyi aure ya kawoshi, tun wuri zan turashi chan gurin su Baba, kar ki manta Alkawarin da nama Baba cewa da kin samu Miji zakiyi aure, kema da amincewarki na da kin samu Miji zaki tsaida Karatu, to in dagaske yake tunda yazo har gida to yaje chan Asalinki ya nemi aurenki ba mu son dogon soyayyan zamani". Tunda ya fara magana ta sadda kanta k'asa ta ji zuciyarta na wani irin zugi, Aure? Aure? Da wani ba Zaid ba? Ya Illahi. Sai da ta tabbatar yayan ya gama magana ba tare da tace komai ba ta tashi ta shigewarta daki, Aunty Asee ta k'ara da cewa kasan amincewar Yanmata masu kunya shine tashi ba tare da sunce komai ba". Yayan ya murmusa yace "MashaAllahu, bari dai yazo muji". Jawad kam yana barin Gidansu Labiba ya wuce Gidan Uncle Usman gidan 'kanin babanshi, Aisha tace "Ya Jawad fa tun dazun ka iso sai yanzu muke ganinka?" Antisco tace "sai da yaje ya ci girkin diyata" Jawad yayi murmushi yace "kyaleta Antisco, so take na fara ganinta kafin naje na ga matata?" Aisha tayi shewa tace "Allah ya baku hakuri yaya, shegia Besty an samu Miji a sama" harara ya zabga mata yace "wallahi ki kayi wasa sai na ma Yaya Majeed budurwa" hararar ta rama tace "shi kuma makaho baya iya budurwa da kanshi sai ka mashi?" Antisco dai tayi ta daria, sai da ya huta kafin yaje gidan Kakansu ya gaidasu kafin ya tafi masauki, yayi sallahr Maghrib ya jira Isha'i kafin ya kira Labiba yace gashi nan zuwa. Tunda ta bar Gidan Alhaji Ali Zaki ta koma gida ta kulle knta a daki take ta riskar kuka, ranta a jagule, ta isa gida cike da tashin hankali, yanayin da ta gani a tare da Zaid dazu, yanayin da ta dade take buri ta ganinshi a ciki amma a dalilinta, ta dade tana mafarkin Zaid na Kishinta, Zaid na shiga yanayi a dalilinta, Sai gashi yau a gaban idonta Zaid ya shiga yanayi ta kan ‘yar karamar yarinya da take aji 1, yau Zaid dinta ke kishin wata ba ita, Allah ka kawo mata sauk’i, Allah ya yaye mata wannan damuwa nata, Allah ya iyakance mata Son maso wanin da takeyi, rannan taci kuka har ta gaji. Er Rabi ta sameta tana kuka sosai hankalinta a tashe take tambayarta waye ya sa ta kuka, wani mai gangancin ne ke sanya tilon diyarta kuka. Tarayota gabaki daya tayi jikinta tace “Baby me ya sameki? Me aka miki? Waya tabaki?”. Da kyar ta samu tayi magana, “Mummy Zaid ba ya sona, ba ya sona Mummy, duk son da nake mishi be sona sai wata yarinya wanda da kyar ta kai shekara 17 a duniya, mummy ni Zaid zai ma haka? Bayan duk abunda na mishi?”. Tuni Er Rabi ta shiga huci kamar Zaki tace “donuwar Dan Makaho ke zai ma haka? Don har yanzu na barshi yana jan numfashi a doron kasa, saboda kene fa baby, saboda ke, amma har yana iya yaudararki? Ya zabi watan ki? Lallai Dan Makaho, wannan shine babbar kuskuren da ka tafka a rayuwa, sa yesmin kuka shine ajalinka”. Wani tsalle Yesmin tayi ta duro gaban Mamarta tana haki tace “Mummy, wallahi aa, kar ki sake, kar ki taba yin wani abun da zai taba min Zaid, kar ki sake wallahi, wallahi ki ka taba Zaid wallahi daidai yake da rasani, Mummy kikayi ma Zaid wani abu ba zan taba yafe miki ba kuma sai na kashe kaina”. Da sauri Er Rabi ta girgiza kai tace “aa baby, ba ma zai kai ga haka ba, ina kokarin kare matabanki da cin mutuncin da ya miki, ba zan dauka ba, ba zan iya dauka naga ana saki kuka ba Yesmin”. “Mummy ina mugun son zaid fiye da kaina, rayuwana na cikin garari in har Zaid ya mutu ko ya bace, ba zan iya rayuwa babu shi ba, shine farincikina, Mummy ina sonshi fiye da rayuwa da kanta”. Kalaman Yesmin sun fara ba Er Rabi tsoro, tana tsoron irin mutuwar son da diyarta ke ma mak’iyin aminiyarta, wannan lokacine da zata zabi farincikin diyarta ko kuma na aminiyarta. Lallashin Yesmin ta fara yi, da k’yar ta samu tayi shiru, tace “zan baki wani kwalli, ki shafa in zakije gidan Shafaatu, da kin hada ido da shi, zai ji duk duniya bai da abunda yake so sama dake, zai so ki fiye da uwar da ta haifeshi”. Yesmin tayi murmushi tace “Mummy, bana bukatar irin wannan Son daga gun Zaid, ba na son kazamar soyayya irin wanna, bana son kyamataccen so irin wannan, bana so Zaid ya so ni ta hanyar nan, ina So Zaid ya so ni daga zuciyarshi, da niyyarshi da yardanshi, Mummy Zaid ne farincikina, farincikina shine farincikinshi, in kuma kina son ki ganni cikin farinciki kar ki sake yi ma Aunty Shafaa aiki a kanshi, shi kuma farincikinshi itace Labiba? To bari a samo mishi farincikinshi” magana Yesmin kawai takeyi kamar baa hayyacinta ba. Er Rabi kallon diyarta kawai takeyi cike da tsoro, fargaba da mamaki, ya zaayi diyarta ta ma wani mahaluki irin wannan Son? Ta yaya? Kuka yazo mata da sauri ta fita daga dakin Yesmin ta rufe tana fargaban rasa diyarta. Lokacin da Jawad ya iso Gidan Mallam Muhammad ba wuta a Gidan, kuma basu da Generator, amma gidan babu duhu saboda hasken Gidan Alhaji Zaki ya shigo tsakar Gidan, ga kuma farin wata, ga kuma rechargeable lantern. Yaya Muhammad ya tarbe Jawad don Labiba na cikin daki Aunty Aseey ta tsareta kan sai ta chanza wanka da kwalliya, to tayi wankan shafa takeyi. Zaune suke a kan Carpet daya, Yaya Muhammad yace “Mallam Jawad ka ga Gidan sai duhu, sai hakuri” kan Jawad dai a k’asa shi bai ma san me zaice ba, yo shi ina ruwanshi da gidansu tunda yarinya yake so?. Baban Amira yace “Yaya sunanka? Kuma kai dan ina ne?” Jawad ya hadiya kafin yace “Sunana Jawad Abu Shamsu, ni ne na uku a gidanmu, ina da yayyi biyu da k’anwa daya, iyayena ‘yan Unguwar Alkali ne a nan garin amma muna Abuja zaune, ina aiki a wani Company kuma ina bussiness”. Baban Amira ya jinjina kai yace “Mallam Jawad naji tak’aiceccen tarihinka, to an dai san wata alakar mace da namiji wanda ba muharamai ba bai wuce aure ba, amma duk da haka ina son ji daga bakinka, mai ke tafe da kai? Meye k’udurinka a kan kanwata Labiba?”. Jawad yace “Ni Sonta nakeyi da aure, kuma na ma gaya ma Mamana”. Baban Amira ya murmusa daga jin shi ya san akwai shagwaba a tattare da shi Auta ne, yace “Yaron Mama, Mama za ta maka aure yanzu?” Murmushi yayi don yaji alamun zolaya a tare dashi. Niyyar tashi baban amira yayi yace “to dai duk yanda kayi da manyanka ka gayama Labiba, sai ta gaya min sai kuje chan gida Edo, don uwayenmu na chan”. Jawad yace “InshaAllahu, nagode kwarai Yaya” Baban Amira yace “Mu ke da Godia munga dawainiya” Jawad ya sadda kai k’asa yace “bakomai” Daki ya koma ya kira Labiba. Labiba ta fito rike da Amira da Sabit suka iso gaban Jawad, gaishe shi sukayi, jawad ya dauki sabit yace “dazun nazo kuna hadda”. Sabit ya gyada kai yace “Eh, kuma munada Chakulats da yawa”. Ameera tace “Sabit ummi tace mu gaisheshi mu koma daki, tashi mu tafi”. Mak’e kafada yayi alamun ba zaije ba. Labiba tace “yi tafiyanki amirori barshi” Amira ta ruga ciki da gudu. Jawad ya maida hankalinshi dungurgum wurin Labiba da ya lura da chanjinta, ya lura da yak’en da takeyi, amma tayi iya k’okarinta na ganin bai fahimci akwai wata damuwa ba. Fira suka danyi ba yabo ba fallasa yace “gobe so yake yazo da safe kafin ya tafi” Allah shi kaimu kadai ta ce. Har Sabit yayi bacci ta dauke shi ta kaishi daki saboda sauro ta dawo, su ka dan zauna na wani lokaci. Hamman k’arya ta fara yi yace “bacci ko baby?” Ta gyada kai tace “eh wallahi Jay, ga kuma sauro” Shima ya gaji don sauron sun cijeshi. Yace “to barin in tafi InshaAllah zan zo muyi Sallama k’arfe 10 gobe”. Tare suka mik’e tsaye, wanda yayi daidai da fitowar Zaid wanda yanzu ya tashi daga baccin asaran da ya sha ba mangariba balle ishai, fitowarshi yayi daidai da dawowan wutar lantarkin da ya karade Gidan da haske. Idon Zaid kansu, idonsu kan Zaid wanda yake sanye da dogon riga kawai, babu riga har ana ganin saman boxers dinshi. Da sauri Labiba ta kauda kai, shi ko Zaid zuciyarshi ke ingizashi kan ya je ya nakada musu duka dukansu biyun. Tafiya ya fara yi yana doso su, nan da nan cikinta ya duri ruwa, me Zaid zai shigo gidansu yi? Mai zai ma Jawad, me zata ce ma Yayanta meye hadinsu da shi? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun. Zaid ya k’etaro Gidan Mallam Muhammadu bai tsaya a ko ina ba sai a gaban makunnin hasken lantarkin Gidan dake daidai k’ofar dakin Labibar, hannun shi ya sa ya KASHE FITILAr. Ya sake wuce su ya koma gidansu ba tare da yace da kowa komai ba. Kallo suka bishi dashi Jawad dai ya ga abu yayi yawa ya daure yace “Baby waye wannan?” Shiru tayi Ya sake cewa “baby waye wannan wai?”. Tace “Zaid ne” Yace “Zaid” Tace “ka tafi barin shiga akwai sauro”. Jawad bai ja magana ba yace “Good night Baby” Tace “Good night Jay”. Ya juya ya bar Gidan a kan idon Zaid, ya juya ya shige dakinshi, ganin Dalon da ya so yi ya fasa. Ita kuma Ranta bace ta kunna Fitilar Gidan ta shiga dakinsu Yaya tace ya tafi. Yaya yace kinji kinji yanda mukayi. Sadda kai kasa kawai tayi kafin ta tashi ta koma dakinta. Wai meyasa Zaid ke mata haka ne? Wai meyasa yake kada mata gaba haka, wai meyasa yake nuna kamar yana kishinta, donAllah ya bari, wannan dabiar da yake yi, hakan da yakeyi yana sa ta na ji kamar tana da damar samunshi, nuna irin wannan kishin zai sa ta kasa kwantar da hankalinta ta rungumi Jawad a matsayin Mijin Aure, ta na tsoro, kar ta sa ma ranta dogon burin samunshi amma ta rasashi ta wahala daga karshe, kai bata yiwuwa, yau dole ta sama ma kanta mafita dolen dole. Jawad kam suffar Zaid yake ta tunanowa, shine wanda Mancy ta taba aikosu wurinshi, dan Mancy ne, tabbas shine, dama baida hankali, yana shaye shaye, banza ne ba zai bari ya dameshi ba balle yayi tasiri a kanshi, nan da nan ya kawar da tunaninshi. Karfe 11:30 Labiba ta tashi ta zura doguwar abayarta ta tabbatar kowa yayi bacci, tayi sando zuwa gidan Alhaji Ali. Tura k’ofar dakin Zaid tayi ta sameshi a bude, yana zaune yana zuk’ar sigari. Yana ganinta yayi saurin mik’ewa tare da kashe karan sigarin. Kallon juna sukeyi suna k’okarin karantar juna, ganin kallon da yake jifatar dashi na neman tasiri a zuciyarta ya sata daure fuska tace “Wai me kake nufi ne dani? Menene haka kake min, baka tashi yin wulakancinka sai ka ganni da wani? Me hakan ke nufi? Ba kai kace na fita daga harkanka ba? To na fita daga harkan ka meyasa kake son shiga nawa? Ina abunda ya kwalaka da k’asa da duk wanda na tsaya da shi sai ka so bani kunya, haka kai da abokanka kuka tozarta Abu Sideeq, kuma Zaka zo kana wasu abubuwa gaban Jay, to wallahi ka fita harkata, ba ruwanka da duk wanda zaizo wurina balle ka sani jin kunya, kar ka sake nuna fuskar ka a inda nake ka gane?”. Ta na gama magana ta fita daga dakin bata tsaya ko ina ba sai dakinta ta rufe ta sa sakata tare da zubewa kan gado tana mamakin jarumtarta, lallai tayi kokari, ba ta fushi bata fada bata masifa amma yau Zaid ya sa tayi, numfashi take mayar wa a hankali, har ta dawo daidai, haka bacci yayi awon gaba da ita. Shi kuma Zaid idanuwanshi na nan k’yam ba alamun bacci, world din ma kasa sha yayi ya tsaya yana nazarin kalamanta yana juyasu, sigari kadai ya iya sha har gab da Asuba inda naunauyar bacci yayi awon gaba dashi. K’arfe 10 Jawad yazo Gidan sukayi Sallama ya kama Hanyar Abuja. Kafin 12 rana sai ga Yasmin ta dura a Gidan Alhaji Ali Zaki. Sai da ta shiga cikin Gida inda ta iske Amna da Anty Shafa’atu a Parlo. Anty Shafa tace “Ke ‘yar hutu haka akeyi? Sai kawai naga wayar mamarki wai ‘yar hutuna ta koma gida, haka ake hutun?”. Murmushi tayi din ta san bariki ne kawai don tasan Hajia Shafa’atu kwatakwata bata son zamanta a gidan don ta hana ta rawan gaban hantsi. “Wallahi Aunty jiya na shiga wani rububi amma ai gani na dawo” yak’e kawai Shafan tayi tace “dama Kasuwa zamu, ko zaki bi mu” Yesmin tace “sai dai kun dawo, a siyo min Agwaluma” sukayi gaba tare da fadin “Allah sa mu gani”. Dakin Dalo ta shiga suka gaisa tace “ashe Aunty Yesmin ba nan kika kwana ba” tace “eh wallahi Dalo, barin dubo yayanki ko ya tashi”. Tace “eh ya tashi , ya ma shigo”. Yasmin ta fita ta nufi BoysQuaters. Sai da ta k’are ma Gidan su Labiba kallo kafin ta shiga dakin da sallama. Yana ganinta ya mik’e tsaye tare da fadin “Yasminn” Murmushi ta mishi tare da daga mai gira “Yadai nawan?” Ya mike tsaye ya matso kusa da ita yace “I am soo sorry Yas”. Giran ta sake dagawa “forr?” Shiru yayi Tace “kayi wanka?” Yace “Eh” Tace “beyi kama da kayi wankan ba, ni fa wannan Jalabiyar sai na k’onata”. Yayi daria ta bude wardrobe dinshi ta ga ba komai ciki sai wata Ghan Must go Ta sa hannu ta bude ta ga duk kayyaki ne wanda baa dinka ba. Tace “na wa ye?” Yace “nawa ne da na Dalo” Wani tunani tayi ta ciro wani Yard mai kyaun gaske navy blue da skye blue tace “zo muje” Yace Ina? Tace “bansan tambayoyi” Hannun shi ta ja ba su tsaya ko ina ba sai cikin Mota Horn tayi Mai gadi ya bude Gidan suka fita MeelaMeerna Stitches ta tsaya suka shiga, ta bada Yards dinnan biyu tace “Ku auna shi yanzu ku dinke su duka”. Zaid zaiyi magana ta harareshi tace “bana Son gardama” Haka ya tsaya aka auna shi suna zaune kusan Awa Biyu aka dinke mishi kaya kala biyu a ka goge, ta tsaya ta sai mai Hula k’ube, da wasu turaruka, yana zaune a mota. Ta shigo da kaya ta ja yace “Yasmin” Ta katseshi ta hanyar cewa banson surutu Shiru yayi har suka isa Gida ta turashi toilet tace kayi wanka wannan kayan zaka saka zan dawo nan da 30 mins. Ta fita ta koma cikin Gida wurin dalo, baayi minti 15 ba sai ga Zaid ya shigo cikin Gida Console din Parlon ne ya hasko mai kanshi a jikin madubu, sai da gabanshi ya fadi, mantuwa ta mance ranar da yayi shiga ta kamala irin yau, mantuwa ta mance randa ya ga yayi kyau kamar haka, madallah da Yesmin, madallah da ta tuna mishi wannan part din na nan. Dakin Dalo ya shiga Da Yesmin din da Dalon duk suka bude baki suna kallonshi Yayi kyau sosai A tare suka ce “wallahi kayi kyua” Daria yayi yace “Dalo It was all Anty Yas dinki” Tayi murmushi tace “na sani, thank you Anty Yesmin Allah ya biya miki bukatunki na Alheri”. Basarwa tayi kawai tace “Muje ko?” Da Zaid da Dalo suka hada baki suka ce “Ina?” tace “Zance Zamu” Dalo tace “Zance? Ahh a dawo lafia”. Daria tayi ta ja hannun Zaid suka fita daga cikin Gidan tace “kasan zai fi sauk’i in muka ketara ta nan?” Ta na mai nuna gidan su Labiba”. Zaid bai fahimceta ba yace “meye?” Tace “well never mind, ba zamuyi scaling ba, its illegal, bari mu bi ta gaban Gida”. Janshi tayi, shi kuma binta yakeyi kamar wani soko. Yaga sun wuce parking lot yace “motar fa?” Tace “inda zamuje zance ba sai mun shiga mota ba” Zaid mamakinta yake kawai, bata gama bashi mamaki ba sai da ya ga sun toge a kofar Gidan Mallam Muhammadu gidansu Labiba”. Cike da mamaki yace “Yesmin me mukeyi a nan?” Murmushi tayi tace “Zance mu ka zo” “Zance wani irin Zance?” Ba ta amsashi ba, sai kiran wani Almajiri tayi tace shiga gidan nan kace ana sallama da Labiba a waje. Tana Kallo ita da Aunty Aseey yara na makaranta suka ji ance “wai ance ana sallama da Labiba a waje” Labiba tace wai “inji wa?” Yaron yace “ni bansani ba su biyu ne dai” Labiba da mamaki tace “ko wanene?” Aunty Aseey tace “sai ki tashi kije ki duba”. Zaid ya juya da sauri zai koma Gida ta yi saurin shan gabanshi tace “Rai na ya baci jiya, amma zai fi baci yau in ka tafi ka barni tsaye ni kadai anan”. Zaid ya juyo gareta cike da tausayawa yace “Yasminnn, yasmin you are hurting yourself” Tace “ban san surutu, bansan gardama, ban kuma son tambaya” ta ko rik’e hanunshi gam. Daidai da fitowar Labiba ta choge ta tsaya ganin wani mai kama da Zaidu amma wannan Babba ne don sanye yake da manyan kaya, kuma wannan ya fi Dan Makaho kyau, kallon kallo sukeyi ba ma ta lura da wata a gun ba, hannu ta ga ya sa ya murji idonshi na hagu. Zuciyarta ta kawo mata kuwa a kwakwalwarta “Shine, wallahi Shine, Dan Makaho ne”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 BABI NA ASHIRIN DA UKU 2⃣3⃣ (INA SONKI❤) Tare yake da wata zuciyarta ta ankarar da ita, ido ta kai wurin Yesmin da ke tsaye tana zabga murmushi, fukarta ba yabo ba fallasa. "Labiba" Labiba ta kalleta ba tare da ta ce komai ba. K'amshi tace "Zance fa muka zo, haka zaki tarbemu?". Labiba ta rausayar da kai kafin tace "Zance kuka zo? Wurin wa? Ko kuma zance kuka zo yi a gidanmu? Chan be isheku ba har sai kunzo gidanmu?". Yesmin tayi murmushi tace "zance muka zo dai wurinki,ciki zamu shiga? Ko nan zamu tsaya?". Tsayuwa Labiba ta gyara tare da hade hanayenta guda biyu bisa k'irjinta tace "ban gane ba? Zance kuka zo wurina? Wani irin zance kum?". K'amshi tace "Zance irin wanda saurayi ke zuwa yi Wurin budurwa, zancen soyayya, ni 'yar rakiya ce". Labiba da mamaki Ta juya ga Zaid tace "Kai gaya mata kayi so na kakeyi ko meye?". Ta kalli k'amshi tace "Wanda ake so, ake zuwa zance gurinshi, nikam ba so na yakeyi ba, you got it all wrong". Yesmin tace "ba sai ya gaya min ba ai, i got it right, sonki yakeyi sosai wanda zuciyarshi na zugi in ya ganki tare da wani, jiya munji haushi sosai da muka ganki da wani, shiyasa yau mukazo don kar mu tsaya kallon ruwa kwado ya mana k'afa". Labiba tace "ke ba budurwarshi bace?". Yasmin tace "kar kiyi kishi dani". Labiba tace "aa ba zanyi kishi da ke ba, naki ne ki rikeshi kinji? Ku bar zuwa mana gida kuna mana sallama, Zan shiga gida" ta juya da sauri zata koma. Yasmin ta yi saurin rikota tace "dagaske kar kiyi kishi dani, ni ba damuwarki bace ba, damuwata shine ki bamu dama, mu shiga cikin masu nemanki mu fafata, don ba zamu yarda wasu su dinga zuwa gunki ba, jiya saura kadan zuciyarmu ta fashe da ta ganki da wani tsaye". Labiba tayi dariyan takaici tace "wai waya ce miki so na DanMakaho keyi?". Yasmin tace "Sonki Zaid keyi". Labiba tace "ba so na yakeyi ba, yana kishin ganina da waninsa ne kawai" Yasmin tace "ashe ma yana sonki sosai, don sai abun da kake so kake yima kishi, ba ki sani ba ke yarinya ce". Cike da zafi Labiba tace "gaskia ne, a yarintar na tareshi da k'okon barata a kan ya soni, da yarintar fa na kamu da son shi, kinsan da Allah da Annabi nake rokonshi ya soni?kinsan me yace? Cewa yayi banda Aji, ni ballagaza ce, ba zai taba son yarinya mai tallar kanta ga da namiji ba, ni yar kudu ce banda kamun kai, ni kaza ce, ni kaza ce, be san so ba, bai ma so adalci ba, in har wai don mace ta ce tana son namiji shine rashin kamun kai, to bai chanchanci furta kalmar So ba". Yasmin ta dafe gefen kirjinta tace "kiyi hakuri, bamu kyauta ba, mun gane kuskurenmu". Bakinciki ya turnuk'e Labiba da ta kalki Danmakahon da ke tsaye kamar ya tsohon soja ba motsi sai binsu da kallo da yakeyi daya bayan daya. Tace "kurma ya koma? Be iya magana? Kinga hakan na nufin zuwanku nan ma was all your idea, ke kika tilastashi yazo, wannan zuwan naki ne, so donAllah ina ganin girmanki Aunty, kar ki sake zuwa min da irin maganar nan, ni dai DanMakaho na dade da yakice shi a zuciyana, babu wani abu tsakaninmu da ya wuce makwaftaka". Kafin Yasmin tayi magana, tuni Labiba ta shige Gida da sauri ta maida k'ofa ta rufe. Yasmin ta Zabga ma Zaid harara tace "wai kai wani iri ne? Kaga abunda ka ja ko? Kai da zaka lallasheta a wuce wurin amma ka tasamu gaba kana ta kallo kamar wanda ya samu Tv? Haba?". Tausayinta ya mamayeshi, ba komai ya sashi kasa magana gaban Yesmin ba sai jim nauyinta da yake da kuma girma da darajan da take dashi a idonshi ya kasa ce ma Labiba komai, ai ana barin halas don kunya. Yace "Yass, ba sai kinyi haka ba donAllah, kina ba kanki wuya, nifa wannan yarinyan ba abunda kilke tunani bane, 'yar karama da ita me zanyi, kawai kinsa yarinya ta gama mana rashin kunya". Yasmin tayi wani guntun murmushi tace "kamar na chanchanci sanin gaskiar lamarin nan, na tafi Gidanmu". Gaba tayi yayi saurin binta a baya yana kiranta amma tayi banza ta kyaleshi, har ta bude mota tayi shigewarta ta tafi Gidansu ranta na k'una da zafin jarumta irin na abunda tayi don neman farincikin abunda takeso, tuk'i takeyi har ta isa Gida. Labiba na shiga gida ta rufe k'ofa tare da jingina jikin k'ofa tana mayar da numfashi, ba namijin kokari tayi ba wurin gaya musu magana, duk da bata tsoron magana gaban ko waye amma Zaid daban ne, shine weakness dinta. Ta na jin Yasmin na mishi fadan ya zo yay tsaye ya kasa magana, ta na jin ansar da ya bata ma cewa ita yarinya ce ba abunda zaiyi da ita, k'wallah ta matse da ta ji muryan Aunty Asee na tambayarta waye ke sallama da ita "wani dan ajinmu ne" tayi k'arya, ba ta san meyasa ba in dai kan Dan Makaho ne, to ta zama expert wurin k'arya, jiki a sanyayye ta shige daki. Maimakon ya shiga Gida, sai ya wuce center, shiganshi Gida ya san World kawai zai taba, duniyar ta juya mai, yana dauke da damuwa, zafi biyu, yana so ya yi clearing kwakwalwarshi, tafiya kawai yakeyi zuciar shi na ga Yasmin don ba ta Labiba yake ba. Ba ya son yanda take k'untata ma kanta kawai don ta burgeshi ko don ya samu farinciki, kwatakwata baya son yanda take zaban farincikinshi kan nata, hakan ba adalci bane. Wayarshi ya dauka a aljihu ya kira Yasmin din kamar ba zata dauka ba ta dai dauka tare da fadin "Yadai?" Yace "donAllah ki dawo" Tace "me zan maka Zaid? Baka yarda da ni ba, ban san komai game da zuciyanka ba, to wani irin zama kake so muyi? Baka yarda dani ba, ta yaya kake so na taimaka maka". Numfashi ya ja yace "na san baki isa gida ba, DonAllah ki dawo, ina son miki magana, zan jiraki bakin gate". Dif ya kashe wayarshi. *** Da ta ji Gidan Shiru ta san cewa ba kowa, mutanen gidan sun fita, Fitowa tayi don ta gaji da zaman Daki, sanye take da riga da skirt na material, ba ta daura dankwali ba saidai ta yafa shi a kanta. Parlo ta shigo tare da kunna TV ta kamo tashar ZeeWorld. Daga Daki ya fito, ba aikin fari bare na bak'i, bacci ya tashi, idanunshi suka sauka kanta, ya san ba kowa a Gidan, zuciyarshi ta raya mai wani abu, ba ta san da fitowarshi ba, takowa yayi har gabanta tare da zama kusa da ita ji tayi kamar an jingina da ita, da sauri ta waigo ta kalleshi, zumbur tayi zata mik'e yayi saurin mayar da ita ta zauna, tuni jikinta ya duri ruwa, tuni jikinta ya fara rawar mazari. Da wani murmushi mai sa kuka ya kira sunanta "Dalo". Kasan motsi tayi sai rawan da Jikinta keyi. Sake yunkurin tashi tayi a karo na biyu ya sa hannu ya janyota tare da zuba hanayenshi kan cinyoyinta biyu. Murmushi yake mata "Dalo, wai meyasa kike dari dari da ni? Ni ba uncle dinki bane, ki saki jikinki dani, zan zame miki gata a gidan nan, i will do anything you want" Murmushin da yakeyi ne ya na daga nata gira ya sata fashewa da wani kukan bak'inciki. Da sauri ya tariyota jikinshi yana fadin "Oh No Dalo, kar kiyi kuka? Uncle Hudu ne ya saki kuka? To zan hukunta shi kinji? Amma kar ki sake zubar min da hawayenki". Da sauri ta tureshi ta tashi da zafin nama ta ruga dakinta tare da saka sakata ta rufe, jikinta rawa yakeyi, wannan wani sabon hali ne Uncle Hudu ya tsuro dashi, bata saba da wannan dabia tashi ba, ta fi sabawa da dabiar kyara da hantarar da yake mata, bata son yanda yake son fara shige mata, bata so ko kadan. Shi ko jinta a jikinshi ya kashe mai nasa jikin, kasa yunkurin binta yayi, kawai ya ayyana ma ranshi sai ya samu yarinyar nan ko ta halin k'aka amma dagaske yake sha'awarta don wannan ba wani abu bane illa sha'awa kuma sai ya ja ta a jikinshi ta sake dashi kafin ya cimma burinshi, ya lura tsoron shi kawai takeyi, amma ya san yanda zai bullo wa lamarin. Inda ta barshi nan ta iske shi, yana ganin Motar ya karasa gunta da sassarfa, gani yayi ta hade gabas da yamma ta murtuke fuska, bude gaban motar yayi ya zauna tare da cewa "Yas Yunwa nikeji". Bata kulashi ba ta ja motar ta bar Anguwan. Royale Restaurant ta nufa dasu, su ka shiga ciki suka siya abinci suna ci. Zaid yace "wai fushin me akeyi da ni?" Banza tayi ta kyaleshi. Yace "Okay Okay inaji, zan amsa miki duk wata tambayar da zaki min, ina jinki Yas". Girgiza kanta tayi alamun aa tace "Aa, ni ai ban kai na san gaskia ba, Nayi zaton na chancanci na son abubuwan da ke boye a ranka, ashe baka daukeni a bakin komai ba, ashe baka ma yarda dani ba". Da sauri ya girgiza kai yace "Yass, i dont want to hurt you" Da sauri tace "hurt me with the truth" Numfashi ya ja yace "Ki tambayeni Yas, tambayeni". Da sauri tace "Ina son sani, kana son Labiba ko ba ka sonta". "INA SONTA". Numfashinta ne ya dan tsaya kafin ya dawo ta boye damuwarta da murmushi tace "Meyasa ka kasa ce mata komai dazun? Mai yasa ka kasa kare kanka, meyasa kaki gaya mata kaima kana sonta?". Hannu ya sa ya murji idonshi na hagu yace "saboda yin maganar bai da amfani, kare kaina baida wani amfani, haka nan fada mata kalmar so ba zai amfaneta da komai ba". "Inji wa? Wa yace maka haka? Ka san tun yaushe nake son jin kalmar So a bakinka? Ka gwada gaya mata, ita ta san amfanin da zai mata, fada mata sauke nauyi ne kai zaka ji sak'at, itama hakan, i think kaje ka gaya mata, zaku kasance cikin farinciki ku duka". Kallonta yakeyi sosai kafin yace "Yas, wani irin abu kikeyi haka? Ba kya jin haushina? Na kasa biyanki kwatankwacin abunda kika min? Ba ki tsaneni ba kan ina son wata ba ke ba? Ba ki ji na fita ranki ba ina kallonki ina gaya kiki ina son watanki, Yesmin ya zanyi da ke? Kina turani wurin wata bayan ke mai so na ce, ba kya kishi na? Ba kya jin zafin turani ga wata?". Murmushi mai ban tausayi tayi tace "Sosai nake sonka, ina kuma kishinka fiye da zatonka, burina shine samunka, na rikeka ni kadai, amma a dayan bangaren farincikinka shine nawa, in har Labiba ce farincikinka, ina maraba da sadaka da ita, in So daya tak Labiba kake ma ita, zanyi yanda nayi ka sameta, don dai ka kasance cikin farinciki, irin son da nake maka kenan, haka ne adadin son da nake maka, in har kana son ganin farincikina to ka kasance cikin farinciki". Ji yayi idonshi ya ciko da ruwa, zuciyarshi na zugi. "Yasmin how could you love me this much?" Murmushi tayi tace "wallahi fa, nima ina tambayan kaina wannan." Yace "dagaske ba abun daria bane, Yas kina sa ina jin haushin kaina, na kasa baki abunda kike so, amma wallahi ki sani ina sonki kamar yanda nake son Dalo, kina da Girma da daraja a idona, k'imarki kullum karuwa yake a zuciyana, bana son k'untata miki, yin soyyaya dake wallahi kunci zai jawo miki, kuma ina sonki da ba zanso wani kunci ya kusanceki ba, bana son bata miki rai, bana kuma son abunda zai bata ranki ko menene, bana son saba miki, shiyasa dazun na kasa cewa komai, ana barin halas don kunya, Haka ne zan biyaki hallacin da kika dau shekaru kina min, zan ga kin auri wanda zai so ki fiye da tunaninki, wanda zai kula min dake, wanda zaku kasance tare har k'arshen rayuwarku". Sosai take son fashewa da kuka, amma ta dake tace "Awwn so touching, to in ka gama maganganun ban tausayi ka tashi muje ka ba Labiba hakuri, ka kuma gaya mata kana sonta fiye da zatonta, kuma zaka shiga layin manema aurenta". Zaid be san lokacin da ya fashe da wani irin dariyan takaici ba. "Aure? Aure fa kikace Yas" "Wa zaiyi aure? Ni? Ni Mankas zanyi aure? Hahah funny". Yasmin da mamaki tace "what is funny kuma?" Ya dan tsagaita darian marasa lafian da yakeyi yace "ai na jiki da wani magana ne kamar almara, wai zan shiga layin manema aurenta". Yasmin da mamaki tace "Yes, what is wrong with that?". Zaid ya gyara Zama yace "Okay let me make this Straight". "Kinsan ina iya amincewa da Soyayyarki ko da ba kece Yasmin k'amshi ba? Ina iya ganin wata ince ina so, wata na iya ganina tace ta na so, na amince na kuma bata mata lokaci don wallahi zan bata lokacin duk wanda maganar So ya shiga tsakaninmu yanzu, Amma But No ba zan fara wani abu mai suna Soyayya ba, ban amince miki mun fara Soyayya tun farki saboda kin fi karfin na ci amanarki kin fi karfin na hainceki, kin fi karfin wulakanci a guna, duk yanda da zuciyata ke ingiza ni kan mu fara soyayya na ki saboda na san ba hanya mai bullewa bace, ba zan taba bata lokacinki ki ba shiyasa Yesmin ban taba jin wani abu da ya wuce na Yanuwantaka game da ke ba, saboda bata miki lokaci kawai zanyi, na hanaki samari, kuma ni ba zaki sameni ba, bana cikin jerin samarin da suke soyyaya da biyu, bana cikin samarin da ke bata lokacin Yanmata kuma sun san ba aurensu zasuyi ba". Duk yanda zuciyar ta ta karaya bata fada murmusawa ba ta gyada kai tace "na sani, na san da haka, amma Labiba fa? Abunda kakeji game da ita daban ne dana Yasmin K'amshi, ita me ke hanaka? Meyasa?". Ajiyar zuciya ya saki yace "Yasmin kina sa ina ta maimaita magana daya". Yasmin tace "Labiba fa?" Yace "Labibaa, Labiba, to ita Labiba yanzu kinga ai tana da tsayyaye, da idonki jiya kinga wanda yazo gurinta" Tace "kaima zaka fara zuwa gunta". Yace "Yasmin so kike na bata mata lokaci itama, shi wanchan da Aure yazo mata, nikuma bata lokacinta kawai zanyi, to meye amfanin zuwa in the first place?". Yasmin tace "inji wa? Kaima da Auren zakaje mata". Yace "wai wani irin aure? Wanda ke da lafiya, kamala da tsawon rayuwa fa shi yake planning jin dadin rayuwa har ya sa Aure ciki". Galala ta kalleshi tace "kai kuma baka da tsawon rai ko?" Ya gyada kai yace "Kin fi kowa sani ai". Tace "kul, kar ka sake ka ce min na sani, ban sani ba, na san kai Namiji ne kamar kowa, na san kana da rights to love and to be loved". Ya katseta "Yasmin, kar ki maida mu baya, kin fi kowa sanin i am sick, kin fi kowa sanin how sick i am, meye amfanin zuwa in the first place, meye amfani fara abun da nasan it wont last, meye amfanin fara abunda zai taba zuciyar yarinya, what if we started all that sai nazo na mutu, kinsan damage din da hakan zaiyi mata? Kinsan illar da zai mata? Kinsan yanayi da hakin da zata shiga sanadiyar rashina? Son da nake mata ba wai yanzu bane, har gaba da zata shiga wani hali bayan ba ni a doron kasa, kinga ko na zalunceta na sa ta saba dani bayan ni ba rayyaye bane". Cikin zafi tace "to sai aka ce ka kusa mutuwa? Sai a ka ce kar ka ji dadin rayuwanka kamar mutane? Sai akace kar kayi planning future dinka? Kai Allah musuru ne? Ka san ranar mutuwanka? Ko ance maka cuta na kisa? Wa ya san gawan farin? Mutane nawa suke da ciwo more worse than you and are living happily? Mutane nawa ne suke fit and sound ba tare da ciwo ba mutuwa ke zuwa musu farat daya, eh yes Your liver is infected, your lungs are damaging, and you are not taking your medications sai ka ga dama, kai baka da plans saboda you believe you are dying, ba ka da wani hope, kai kana zaune kana jiran mutuwan ka, haushin da kake bani da kake irin surutan nan, ban dade a Islamiya ba, ban da sani sosai a addini amma tun ina karama na san cewa ba a so bawa na yankewa daga rahamar Allah, Zaid wake up, you deserve to be happy". Shiru yayi yana nazarin duk maganganunta. Maganganunta sun ratsa shi. Yace "Yas ta ya zaayi a barta ta soni? Ta ya zasu yarda da dan Shaye Shaye? Dan zaman kashe wando? Ta ya zaayi ta aure wanda bai da aikin fari bare na bak'i sai zaman bakin hanya?". Yasmin tace "ka tashi tsaye, ka gyara, ka chanza, ka kimtsa kanka, and komai zai zama tarihi, ba decision din danginta bane, decision din zuciyarta ne, kar ka manta kafin ka sota ta soka, ta san ko kai waye, amma ta zabi da ta soka a matsayinka na wanda ta san dan shaye shaye ne, i think shes ready for what to come, ina dai so ka ma kanka karatun ta nutsu, since you are planning to love, i think you need to work on how to live". Kallonta kawai yakeyi yana neman karin bayani tace "ehmana, Maganin da kayi watsi da su su zaka dawo ka sha in har kana son kasancewa tare da ita, you strive to survive, or tunda baka son hurting dinta, zan sameta na gaya mata matsalarka kila in ta saka shan magani dole ka sha tunda ita ake so". Da sauri ya girgiza kai yace "dont be like this, kar kice haka mana, ki sani Son da nake miki yafi karfin Soyayyan maaurata, so ne na jini fa". Kafadunta ta daga tace "i am not complaining ai ina dai fada ne, duk da haka zan mata bayanin ciwon ka, na gaya mata ka bar shan magana saboda ka cire rai da rayuwa yanzu haka mutuwarka kawai kake jira". Da sauri yace "aa donAllah, kiyi hakuri, na bari wallahi, muje ma ki siya min magani yau zan fara sabon medication". Da mamaki da jin dadi tace "Ahh Lover Boy Allah ya baka hakuri, yanzu dai ka jira monday a sake ma tests a ga me zaa ma prescribing". Dokinshi ya kasa boyuwa yace "Nagode Yasmin, Allah ya biyaki da Aljannah , Allah ya saka miki da Alheri. Allah ya faranta miki yanda kike faranta min". Yasmin tace “Ohhh you are so sweet, dallah mallam tashi mu tafi you are making me emotional, kafin ka sani kuka”. Daria yayi yace “Okay okay muje”. Ganin jin dadinshi ya sa Yasmin jin dadi itama har suka tafi Gida. Gab da Maghrib Jawad ya isa Gida, isowarshi kenan don ya tsaya a Kaduna, Babban Parlorn Gidan ya shiga, daga Mancy sai Mimi,da sallama ya shiga Mimi ta karasa da gudu tayi hugging dinshi, murmushi kawai ya mata tace “Ya Jawad ina kaje?” A takaice yace “Katsina naje” Mancy ta fadada murmushinta tace “Ashe KT kaje Jawad” ba yabo ba fallasa yace “Eh” tace “lafiya dai ko?” yace “Uhm, naje ganin wasu ne” Ayyah Allah sarki, ai bansani kayi tafiya ba” a kagauce yace “Umma kadai ta sani, ai ba dadewa zanyi ba shiyasa ma ban fada ma ko Abba ba” tace “uhm hakane, Allah ya huta gajia dan Umma”. Wucewa yayi cikin Gida don sanar ma Ummanshi dawowanshi. Tun dazun take kiran wayar Zaid ba ta shiga, sai tace bari ta kira wayar Dalo kila tana kusa. Ringing daya ta dauka, amma yanda ta ji muryarta ta san cewa akwai wani abu. “Sadiya me ya sameki?” Dalo tace “bakomai Mancy, ya gida”. Mancy tace “uhm uhm sadiya, muryarki cike take da tsoro, wani abu suka miki?” Dalo ta fashe da kuka, hankalin Mancy ya tashi, ta hau tambayarta abunda ya faru. Dalo cikin kuka tace “nidai Mancy don Girman Allah ki zo ki tafi dani, i dont like it here, mancy kinga Uncle Hudu dazun” sai tayi shiru kuma. Hankalin Mancy ya tashi tace “me ya miki? Gaya min Sadiya, me ya miki?”. Ba ta san me za tace mata ba, nauyin maganar taji, duk da be mata komai ba, tattabatan da yakeyi ne bata so, amma ta ya zata ma Uwarta bayani? Ba tayi wannan sabon da ita da zata iya gaya mata komai ba, ganin Mancy zata isheta da tambaya kuma ita bata san me zata ce mata ba ya sa ta kashe wayan. Mancy ta shiga tashin hankali, ta sake kiran wayan ta ji switched off, nan da nan cikinta ya duri ruwa, ta nemo numbern Zaid wanda suke daf da Gidansu Labiba. “Assalam Alaikum Mancy” “Waalaikum Salam Zaid, Ina Dalo?” Yace “Mancy tana Gida” “Yanzu muke waya da ita tana kuka, wai ko Uncle Hudu ya mata wani abu? Ta dai k’i magana yanzu kuma na sake kira naji wayarta kashe”. Mai makon Gidan su Labiba sai ya wuce Gida a guje Yasmin ta bi bayanshi tana son jin mai ya faru. Dakin ya nufa a guje yana kwankwasawa Dalo fito nine da sauri kuwa ta bude kofar ta fada jikinshi tana kuka. Alhaji Abu Shamsu ne ya fito daga Dakinshi zai tafi masallaci ya ga Mancy tsaye yace “wani abu ya samu Sadiya Maryama?” Kai ta shafa tace “aa wayarta ne a kashe, shine danuwan ya dubota” girgiza kai kawai Alhaji Abu yayi be san irin wannan zurfin cikin irin na Mancy ba, wato ba ta daukeshi a matsayin Uba yaranta ba, shikenan ido kawai zai sa mata” ya sa kai ya fita don zuwa Masallaci. Yasmin tace “gaya min Dalo, me Hudu ya miki?” Zaid ya fara huci yace “Wallahi sai na kashe Hudu” da sauri Dalo tace “me yayi? Be fa yi komai ba, dazun ne fa na fita naga bakowa shine naji tsoro, shine fa nayi waya da Mancy taji ina kuka nace mata ina tsoro sai ga Uncle Hudu ya shigo sai naga ashe akwai mutane fa, tsoro kawai nakeji in nikadai ce”. Zaid da Yasmin suka fara lallashinta tare da cewa ba zasu sake barinta ita kadai ba, Zaid ya kira Mancy ya mata bayani, yace da Yasmin bari yayi Sallah. Dalo kam ajiyar zuciya kawai takeyi wani na bin wani. Yasmin tace “yau mutanen Gidan dare akayi a waje kenan” Dalo tace “uhm gashi kam har yanzu ba su dawo ba” Yasmin tace “muyi Sallah mu dafa abinci” Dalo tace “to Aunty Yas”. Suna kan Table suna cin Doya da sauce Hudu ya fito daga daki ya yo kan table din yace “abun solo ne? Mu fa?” Jikin Dalo ya fara bari, Zaid ko kallonshi beyi ba, Yasmin tace “Ayyah abincin mutum 3 ne”. Hudu da bariki ya sa hannu cikin plate din Dalo yace “bari na ci na diyata” haba tuni jikinta ya hau bari jin hanayensu sun gogu. Wani mugun Kallo Zaid ya watsa ma Hudu amma Hudu ya dauke kai irin be ma san kallon da Zaid ke mai ba, sai ma Kashe ma Dalo jiki yake da kallonshi. Haka suka gama Dinner, su Hajia Shafa sun dawo Zaid da Yasmin sun tafi baya ita kuma dalo ta shige daki ta sa key. Yesmin tace “yanzu ka zo muje Gidansu Labiba ayi magana once and for all” Yace “aa Yas, its late, 9 ta wuce, bro dinta ya dawo, kuma ni i am already nervous, ni tsoro ma take bani”. Yasmin tayi daria tace “ji fa, nawa labin take? Ko ta girmi dalo befi ta bata 1year ba, yanzu ita ke kada maka gaba? Haba jarumina kar ka bani kunya mana”. Yace “oho dai nidai wallahi wani iri nakeji” Tace “yanzu dai meye abunyi, ba zamu je ba ?” Yace “dare dai yayi, akwai gobe” Tace “Allah shi kaimu, nima dai yau bacci zanyi da wuri, barin je na kwanta, goodnight”. Har tayi gaba ya tsaidata ta hanyar kiran sunanta “Yasmin”. Ta tsaya tare da waigowa Yace “Thank You, Thank you for Everything”. Har ta dan karaya don idonta ya ciko tayi saurin mayar da hawayenta tare da jefanshi da murmushi tace “Goodnight Zaid”. Tayi saurin tafiya har ta hada da gudu gudu. Zama yayi kan dakali yana tunanin abubuwan da suka faru tun daga safiyar yau zuwa yanzu, “Yasmin, Yasmin ta chanchanci Farinciki, yasmin ta chanchanci ta ji dadi, baya mata irin Son Soyayya, bai so kuma ya so ta saboda tausayi zai zalunceta in yace yana sonta, amma InshaAllah zaiyi duk abunda zai sata farinciki zai kuma tsaya mata gwargwadon ikon shi”. Sai kuma Chanji, ya san shan World da sigari a jikinshi ne dolen dole ya bari in har yana son kasancewa tare da Labiba, dole ya watsar da duk wani mummunar dabiar da ta zameshi Jiki, amma tambayar shine ta ina zai fara?. Ya dade yana sakawa da warwara, ya ga fitowarta daga Daki rike da wayarta wanda take amfani da fitilar jikin wayar wato torch light. Kallonta kawai yayi ya sake murmushi, a ranshi yace “Biebbs kenan, akwai wuta fa ko me zatayi da torchlight?”. Kitchen ya ga ta shiga kuma chan ta fito, yana ganinta ta shiga toilet ta fito, ta tsaya kamar tana neman abu sai taji wayarta yayi ringing. Tana ganin waye tayi saurin kallon Sashen Da yake, a zuciyarta tace “tun yaushe yake zaune a nan? Ban lura dashi ba”. Zuciyarta ta kwadaitu da ta dau wayar, dauka tayi tana zabga mai harara daga inda take. Cikin wata irin murya yace “Bibbs”. Cike da Masifa tace “What? Meye?” Yace “INA SONKI”. Dif ta dauke wuta, duk wani na’ura na jikinta suka tsaya chak suka kasa motsi, k’irjinta kamar ya fito, wani yanayi ta shiga da bata san ko wani iri ne ba, jikinta murus ya mutu jin muryarshi tayi chan k’asa da k’yar ta saita kanta don jin abunda yake cewa. Da dukkan numfashin da na ja, da dukkan numfashin da na sake kina cikinta, rufe idona da budewarshi kina cikinshi, kullum kina tsungunne a cikin zuciyata, bansan me zanyi kuma ba, bansan ko ina da damar jin haka game dake ba, bansan ko matsayina ya kai na ji haka game dake ba, ba laifina bane, ba yin kaina bane, haka na tsinci kaina, tun daga ranar da na sanyaki a idona nake jin haka game dake, ban san ko daidai bane jin haka game dake amma ina so na yarda da cewa banyi laifin jin haka game dake ba, ina so ma yarda ba laifi bane Sonki, sonki ba sa6o bane da zaa hukuntani a kai, INA SONKI SOSAI , Ina sonki Labiba Ahmad Dakata”. #1love Dif ta dauke wuta, duk wani na'ura na jikinta suka tsaya chak suka kasa motsi, k'irjinta kamar ya fito, wani yanayi ta shiga da bata san ko wani iri ne ba, da k'yar ta iya furta "YA ALLAH". K'yafta idanunta tayi sau biyu tana juya kalamanshi, bata san mai ya kamata ta ji ba, dadi? Ko akasin haka. Ba zata taba bari kalaman yaudara irin ta maza suyi tasiri a wurinta ba, da k'yar ta iya ce mai "ka bar yaudaran kanka, ba so na kakeyi ba, bakincikinka Ka ganni da waninka, wanda yanzu kam ba yanda zakayi, tunda dai ina da wanda nake so, dole kam yazo guna, kuma in har muna makwaftaka musamman da wannan rufzazen bangon to dole ka ganmu, amma zan sake gaya ma, ba ruwanka da duk wanda zaka ganni tare dashi, ba zai yiwu ka dinga kora min samarina ba, so ina rok'onka da ka fita daga rayuwata yanda ka buk'aci na fita daga rayuwarka". Cikin wani murya mai kama da hankali tashe yace "Biebbs, me kike so kice? Me kike so? Ba kya so na kuma?" Da sauri tace "Eh, haka nake so nace, bamu da wata alak'a da ta wuce na Makwaftaka, ni da kai bamu dace ba". Gani tayi ya tashi tsaye daga zaunen da yake, ya tako har gaban fasassun blocks amma be ida shigowa gidansu ba yace "Aa kar ki ce haka donAllah, biebbs ya kike so nayi? Sonki ya shiga jikina, ya zagaye tsoka da bargona, ya kike so na cireki a zuciyata? Wai manSai da kikayi nasarar chusa ma zuciyana sonki zaki ce baki sona kuma? Wani irin abu ne wannan? In fushi kike dani kiyi hak'uri donAllah". Ji yayi ta tsinke wayar, da sauri yayi yunk'urin karasowa gareta tayi saurin shigewa daki tana haki, dirshan ta zauna a k'asa, zuciyarta na barazanar fitowa, a halin yanzu bata san me ya kamata tayi ba, ta dade tana son jin kalaman nan a bakinshi, ta dade tana so ya furta mata kalmar so, yau ya furta mata, meyasa bata gaya mishi yanda take sonshi ba itama? Message ya shigo wayarta da sauri ta bude ta ga Zaid ne. "Akwai Sauro, zan kwana a nan in har baki fada min wani abu mai dadi ba". Tashi tayi da sauri ta lek’a ta window ta ganshi a takure, A fili tace “ina abunda ya dameni? Ka kwana nan mtss, kalaman yaudaranka ba zasu yi tasiri a kaina ba”. Hayewa tayi Gado tayi adduar Bacci kafin baccin yayi awon gaba da ita. Sauron Katsina marasa kunya a gaban idonka ma sai su cijeka balle bayan idonka, haka Saurayen Tudun Matawalle sukayi dinner da DanMakaho, tun yana sosawa, yana kashesu da hannu, yana tsaki gashi bai da abun rufa, taurin kai da ya sa ma ranshi, shi ya hanashi shiga daki ko da ya dauko abun rufa ne, haka dan MAKAHO ya kwana a waje wanda bacci rabi a bude ya yishi, sai gaba da Asuba bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi. Alarm dinta ya tadata, bude dakin tayi ta fito, idonta tsaye yayi chan sashen, wani murmushin takaici tayi tare da mamaki, wai dagaske kwanan yayi a nan? Sai taji zafi kuma, bata ji dadi ba, kamar ta karasa gunshi ta k’yaleshi ta shiga Toilet ta wanko bakinta tare da dauro Alwala, ta shiga kitchen ta dauko babban tukunya ta cikashi taf da ruwa sannan ta janyo risho (stove) ta kunna ta daura tukunyan kafin ta fito daga kitchen din sai da ta sake kallonshi kafinta shige daki k’irjinta na mata nauyi. Rakaatanil Fajr tayi kafin tayi Asuba tayi zikrorinta na safe kafin ta tashi don tada yara ta musu Wanka yau Monday. Ta fito rik’e da hannun Ameera, yana nan bai motsa ba. Itama ta rasa abunyi, yau ko Asuba be yi ba, yana nan yana baccin asara a waje. Baban Amira ne ya turo k’ofar Gidan hannu shi dauke da Bak’in Leda wanda shakka babu Breadi ne da madara da lipton da milo na sachet, wanda duk rannan da zasu sha tea baya dawowa daga Sallahr Asuba sai gari ya waye ya tsaya siyansu. Ganinshi ya sa Labiba dawowa daga tunaninta kar yace DanMakahon take kallo, tace “Yaya Ina Kwana” ya amsa da “Lafiya lau Aunty Labs” Amira tace “Baba ina kwana” yace “Lafia Amirori wanka zaayi ko?” Tace “uhm” Labiba tayi saurin shigewa Kewaye da Amira ta dauki bokiti ta shiga kitchen ta diba ruwan zafi ta k’ara a na tukunyan ta sirka kafin ta shiga yi ma Amira Wanka. Kamar dai kullum in yana Gida, Baban Amira ya dauko tsintsiya don Share tsakar Gidan, Aunty Aseey na Kitchen tana hada Tea a dogon Jug, Labiba ta shiga da Amira ta fito da Sabit dan mishi wanka taji muryan Yayanta yana “SubhanAllah, DanMakaho ne chan?”. Da sauri ta kallesu taga Yayan na k’okarin k’etara Gidan Alh Zaki. Ta naji Aunty Aseey na cewa “yanzun haka shaye shaye yayi ta kai mai karo shiyasa yayi Mankas a waje”. Labiba tayi saurin dafe kai. Mallam Muhammad ya fara bubbuga shi tare da cewa “DanMakaho, tashi gari ya waye fa” firgigit ya tashi a dan tsorace tare da murzan idonshi na hagu. “Dan Makaho ba dai anan ka kwana ba? Ji cizon sauro ko ina a jikinka”. Zaid ya bi jikinshi da kallo, ya ga cizon sauro runtuma runtuma. “Kayi Sallahr Asuba kuwa?” Ya ji Mallam Muhammad na tambayanshi “Aa” ya girgiza kai. “Haba DanMakaho, ka san k’arfe nawa yanzu? Bakwai ta yi fa, me ya ja maka rashin Sallah har gari ya waye”. Idonshi na hagu ya sake murzawa kafin yace “barin shiga ciki”. Labiba ya kalla wacce tayi saurin kauda idonta kafin ya juya ya shige dakinshi. Mallam Muhammadu cike da tausayawa ya girgiza kai ya cigaba da sharanshi. Aunty Aseey ta shige kitchen don cigaba da hada kalaci. Ita kuma Labiba ta shige daki don shirya Sabit. Ko da ya shiga Daki, toilet ya wuce direct yayi wanka kafin ya doro Alwala, yazo yayi Sallah rakaa biyu kafin ya zauna a kan kujera yana tunanin Labiba. Ta tsaneshi har haka? Har yace mata zai kwana a waje ta ki furta mishi kalma mai dadi? Dagaske ta bar son shi? To ko daman ba son shi din takeyi ba tausayinshi take? “Ba tausayinka nake ba, sonka nake, sosai nake son ka” Kalamanta ne suka dawo mishi kamar a lokacin take ambaton su a lokacin da yake tambayarta in tausayinshi take. To ko dai ta sadak’as ne? Son da yake mata ba zai saka ta dole ba, ba zai tilasta mata wurin dawo da son shi a zuciyarta ba, tunani fiye da dubu a kanshi ya rasa abun yi. Tunda ta shiga daki, take tunani, hankalinta baya wurin shafa man da take yi a jikin Sabit. “A waje ya kwana?” Don me zai kwana a waje? Baida hankali ne? Yanzu in malaria ta kamashi fa? Akan me zai kwana waje? Akan me? Ya burgeta ya kuntata ma kanshi a kan me? Oh Allah, ya zatayi? Dagaske ya fara sonta?”. Muryar Amira taji inda ta ke cemata “Aunty Labs, kina lafta ma Sabit mai a jiki” da sauri hankalinta ya dawo jikin Sabit da aka kusa kwashe rabin roban Vaseline a jikinshi” “Ya Rabb” kawai ta iya cewa. A B U J A Suna Zaune gabaki daya kan Dining Table suna breakfast Umma ke cema Babansu “Abba wai kasan Jawad Zance yaje Katsina ranar Asabar?”. Jawad ya ma Umma wani kallon “haba Umma ya zakiyi irin maganar nan a gabana”. Dariya tayi ta maida hankalinta gurin Abbansu Abba ko yace “Lallai Autan Umma an girma, har ana zuwa Zance wani gari?”. Murmushi Mancy tayi tace “ai Ya isa Aure, sai a mishi”. Abdulmajeed yace “to wai kana nufin Overtaking dina zakayi ne?” Mancy tace “ai gwara yayi tunda kai ka tsaya wasa”. Abdulmajeed yayi dariya yace “kai Mancy”. Abba yace “to ya sukace gidansu Yarinyan?”. Jawad yace “Abba haka yayanta yace in tura manya na aje neman izinin chan Edo State”. Abba ya aje kofin Shayinshi yace “Edo state kuma?”. Da sauri Umma tace “Aiki ya kai babansu chan shine suke zama har yayi retire, yarinyar ma chan aka haifeta, amma yan arewa ne”. Abba yace “kuma kana sonta?” Ba tare da ya kalleshi ba Jawad yace “Eh Abba”. “Ya sunan Babanta?” “Alhaji Ahmad Dakata”. “Cikin garin Edo?” Jawad yayi jim yace “bansani ba Abba, sai na tambayeta”. Abba yace “Aa ba maganarta bane, kace ta hadaka da Yayanta, sai ka hadasu da Yayanku suyi magana, yayanku should report to me, ko ya kira Baba Usman dinku suyi magana”. A ladabce yace “To Abba” Mimi da ke wasa da dankali a baki tace “Abba nima ka min Aure”. Dariya suka saka baki daya. Yasmin ta fito sanye da doguwar riga mai kama da ‘yar kanti ta wuce dakin Zaid, daidai da fitowar Labiba rik’e da jakka da alamu Makaranta zata, Labiba tayi saurin dauke kai ta shiga dakin Aunty Asee don mata sallama, murmushi Yasmin tayi ta shige dakin Zaid. Zaune ta ganshi cikin yanayi. Da sauri ta karasa gunshi tana tambayarshi “Lafiya Zaid?” Hanayenshi ya nuna mata ta bi hannun da kallo. “Wani abu kamar cizon sauro” Murmushin takaici yayi yace “ba kama bane, cizon sauron ne”. Yasmin na bin duk ilahirin jikinshi da kallo tace “to me ya faru? Ji fa yanda suka cijeka har fuska, garin yaya? Bakayi fleeting bane? Ko maganin sauron nan da kake kunawa ya k’are ne? Ji fa kamar ka kwana a kwata, chabda har saman goshi”. “Beebs ce, Labiba ce”. “Meya sameta Zaid?” Kamar zaiyi kuka ya kwashe komai ya gaya mata. Yasmin ranta ya baci tace “saboda bata gaya maka magana mai dadi ba ka kwana a waje? Ji ciwon sauro a jikinka sunfi dari, ji yanda suka ma ja da fata, sun sha jininka, Zaid Malaria ta kamaka already, kuma kasan da wani abu yayi triggering ciwonka it will only worsen, Zaid what were you thinking? You had to prove that to her? Oh Allah, ba zan ga laifinka ba don So ne, So banzan abu ne, it makes us do stupid things, nikam tashi muje Asibiti, mu fara treating Malaria tun kafin ta mana mummunan Kamu”. Ganin yanda ta tashi hankinta ne ya sa shi nadamar gaya mata dabara ta fado mai yace “Na sha Anti Malaria fa” tace “wanne?”yace “ACT” ina kwalin?” Yace “baki yarda dani bane?”. Kafin tace wani abu ta hango Labiba ta window zata fita Gida. Da sauri tace “Ina Zuwa” Yace “Ina Zakije?” Ta fara yafiya tace “ka jirani yanzu zan dawo”. Da sauri ta koma cikin Gida ta dauko Wayarta da Key ta fita. Sauri sauri gudu gudu ta karasa inda motarta take cewa “kai bude min gate” Yau zaayi ta ta k’are ni da Labiba, makarantar zan kaita. Bude gate akayi ta kunna motar ta fita da saurinta. Labiba kuwa tafiya takeyi da sauri don bata so ta makara, yau 9 zatayi lectures gashi 8:30 ta yi, kafin taje School 9 tayi k’ila ta wuce, a zuciyarta take fatan akwai bus da taje zata tashi kar kuma ayi tsaye tsaye direct ta samu har batagarawa. Bata kai ga isa shagon Eskaley ba Motar Yasmin ya sha gabanta. Da mamaki ta kalleta. Yasmin ta zage Window tace “Shigo” Labiba tace “Makaranta Zanje fa”. Yasmin tace “Hassan Usman Polytechnic Department of Animal Health and Production Technology, chan nayi nima”. Labiba tayi jim, kaafin ta zagaya ta bude gaba ta zauna. Wani irin sansanyan k’amshi taji ya bugi hancinta, k’amshin motar ya hade da k’amshin jikinta, zata iya bambance na motar da kuma na jikinta, don zata rantse ta ji kamshinta daga inda take dazu a gida da suka hadu, lallai kam wannan ‘yar kamshi ce, da Ita da Zuciyarta kawai suke wannan firar. Yasmin ta gyara kan sitiyari ta fita daga Unguwan tana juya sitiyari cike da k’warewa. Labiba ta fara shawara da zuciyarta chan ta yanke shawaran gaisheta tace “Ina kwana Aunty”. Yasmin ta maida hankalinta ga Titi ba tare da ta kalleta ba tace “Lafiya lau”. Ba wanda ya sake magana. Yasmin shatata gudu takeyi cikin minti da bai wuce 10 ba tana gaban K’ofar Batagarawa, mai makon ta shiga School din sai tayi parking gaban Gate din. Labiba ta kalleta da dan murmushi a fuskanta tace “Nagode” ta sa hannu zata bude k’ofar ta fita taji Yasmin ta danna Lock kofar ta datse ta ki buduwa. Labiba ta kalleta da mamaki tana jiran bayani. Yasmin fuska ba annuri tace “karfe nawa kike da lectures?” Labiba tace “karfe 9” Yasmin ta kai idonta ga agogon motarta tace “muna da sauran Minti 11, i will make it fast, Labiba, kin san cewa Zaid waje ya kwana Jiya?”. Labiba ta dan kau da kai kafin tace “ni ban sani ba”. Yasmin tace “Oh baki sani ba? To bari na gaya miki, Zaid waje ya kwana, a daren jiya ya furta miki Kalaman da na dade inaso na ji daga bakinshi, a daren jiya ya tona asirin zuciyanshi da na dau shekaru ina son ji daga bakinshi, a daren jiya ya furta miki abunda bai taba furta min ba, ya buk’aci ki ce mishi ko da ‘thank you’ ne amma kin faskara, ya rok’i ki gaya mishi magana mai dadi amma sai kika jefe kalamanshi da kalmar Yaudara”. “Zaid bai cire rai ba, ya miki barazanar kwana waje in baki mishi magana mai dadi ba amma ko a jikinki, to ashe ba barazana bace ba, Kwanan yayi a waje, mosquitoes kuwa suka samu Abincin Dinner suka far mai, jikinshi yau ba ma tsaka tsinke duk cizon sauro ne wanda ina da tabbaci malaria ya kamashi lokaci kadan zai kwanta ciwo, ke ce sanadi kuma, kuma Wallahi wani abu ya samu Zaid, ba zan yafe miki ba”. Labiba tace “kema son shi kike ai, to meyasa kike son ganin kin hadamu?”. Yasmin tayi murmushi mai ciwo tace “ba ruwanki, na gaya miki kar kiyi Kishi dani, ni ba damuwanki bace, as long as kina zuciyarshi, to sai nayi yanda nayi ya sameki”. “Zaid na Sonki sosai, yana matuk’ar kaunarki, in har kikayi amfani da son da yake miki wurin wahalar da zuciyarshi, baki yi wa SO adalci ba, ba ki chanchanci ki furta kalmar SO ba”. Labiba ta turo baki tace “nifa ba sona yakeyi ba, haka kawai yake cewa yana sona, kema kin yarda dashi, haushi fa kawai yakeji don yana ganina da wasu”. Cike da takaici Yasmin tayi tsaki, ji take kamar ta rufe labiba da duka. Wayarta ta ciro ta danyi latse latse kafin ta daga wayar sama. Labiba ta ji muryan Yasmin na fitowa daga jikin wayar da alama recording ne tayi playing inda taji muryan Zaid na cewa; “Ki tambayeni Yas, tambayeni". Taji muryan Yasmin din na cewa “Ina son sani, kana son Labiba ko ba ka sonta?". "INA SONTA". Labiba ta fara kaita bango a kausashe yace “ki bi a hankali Labiba, shawara nake baki yanzu, kuma dai lallabaki nakeyi, ina da halin maida Zaid nawa nikadai, amma ba zanyi ba saboda yana Sonki, bana so inyi Son kai, i dont want to be selfish, in har kika bari na sa Selfishness a cikin lamarin nan, Labiba in har ki ka bari na zabi kaina akan kowa, wallahi Zaid ba zai sake kallonki ba, Zaid ba zai sake bi ta kanki ba, ko iskar da ya deboki Zaid ba zai sake kallo ba, Zaid zai zama nawa, nikadai in har kika kaini bango Labiba, Fitar min a mota”. A sukwane ta bude k’ofar ta fita, yanayin Yasmin ya bata tsoro, da sauri ta fara tafiya tana yi tana waigen Yasmin, Yasmin ta bude wuta ta yi wani irin reverse ta hau kan Titi, Labiba tsoro ya kamata, ganin yanda ta bude wuta a fili tace “Allah ya tsare” wani irin So Yasmin take ma Zaid da har zata sadaukar da kai haka ta nema mishi abunda yake so? Lallai in itace wallahi saidai ya mutu, in be sonta ba zata taba hadashi da wacce yake so ba. Shiru tayi kafin Zuciyarta ya tambayeta tambayar da take son amsarta “Amma dagaske Zaid din na Sonta? Muryarshi ta tuna Radam ta wayar Yasmin inda yace “INA SONTA” zata rantse gaskia ya fada, ba zai ma wacce ta tambayeshi karya ba, ta aminta da kalamanshi, zuciyarta tayi naam dashi”. Ta dafe saitin Zuciyar tace “Ina Sonka Zaid, Wallahi ina Sonka”. #1love #DM %anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 BABI NA ASHIRIN DA BIYAR 2⃣5⃣ (SON SO ❤💖) Tana shiga aji ta zauna, Besty bata kai ga zuwa ba, wayarta ta cire a jakka ta latso numbern Aishar, ringing biyu ta dauka "Hello Besty kina ina ne?" Daga bangaren Aishar tace "muna first gate gani nan karasowa. Ta window Labiba ta hango Mallam na nufowa Ajinsu, daidai da rurin wayarta, ta duba ta ga Jay ne, ga kuma Mallam nan zuwa, ta san in bata dauka yanzu ba, ba zai damu da tana Lectures ba zai ta kwala mata kira, dauka tayi tare da sa kai kan desk. "Hello Jay, Goodmorning". Jawad daga bangarenshi yace "GoodMorning Baby, ya kike? Bacci kike halan?". Labiba tace "Jay, yau Monday ka manta ne? Gani nan cikin Aji, ga ma Lecturer dinnan ya shigo, zan kiraka in na fito" "Okay okay donAllah yi min sending Numbern Yaya Muhammadu, yanzu donAllah, kafin a fara lectures din". Labiba bata son jan magana, ga Lecturer ya shigo ajin, ya fara cewa a shirya ya sa tace "Okay" tare da datse kiran. Labiba ta tura ma Jawad numbern Baban Amira daidai da shigowar Aisha ta shigo class din da sauri ta ma kanta mazauni kusa da labs tare da tsunkulinta, gira Labiba ta daga mata tare da maida hankalinta gurin Lecturer da ke bayani. A B U J A Jawad kamar zazzabi tuni ya ma Office din yayanshi diran mikiya. Bayan Secretary ya mishi Iso Jawad ya shiga farfajian offishin yayanshi suka gaisa. Yaya Abdulhafiz yace "yadai autan Umma?" Jawad yace "Yaya dazun ne Abba yace na baka numbern Yayan Labiba ka kirashi shine na amso numbernshi". Yayan ya murmusa yace "Jawad, Abbanka ya kirani, ya min bayani". Cike da jin dadi Jawad yace "Yauwa Yaya, ga numbern kirashi donAllah". Yayan yace "tun yanzu Jawadb? Kamar jira ake" Yace "Eh wallahi Jira akeyi, nidai call him now". Yayar ya yi dialling Numbern Baban Amira Ringing daya aka dauka, Jawad ya ma yayanshi nuni da ya saka handsfree haka kuwa yaya Abdulhafiz yayi. "Hello Assalam Alaikum" Daga chan bangaren Mallam Muhammadu ya amsa da "Waalaikum Salam" "Sunana Abdulhafiz Abu Shamsu, nine Babban wa a guri Jawad mai neman k'anwarka Labiba". Baban Amira yace "to to, muna lafia?" Suka sake sabon gaisuwa. Yaya Abdulhafiz yace "Mahaifina ya Umurceni da na tuntubeka da Maganan Jawad". Baban Amira yace "MashaAllah, kamar yanda na gaya ma Jawad, nace mai Inda gaske yake da Aure yazo, ya turo Manyanshi ga Manyanta, sai su nema mishi izinin zuwa zance kafin ayi na neman Aure". Yaya Abdulhafiz yace "dama haka ya kamata, to yaushe zamu iya zuwa?" "Ko yaushe kuka Shirya". Yaya Abdulhafiz yace "shikenan zan tuntubi magabatarmu da maganan, kaima ka tuntubi naku, tunda ga waya sai mu ji yanda zaayi, amma for now muna son sanin Asalinku, Abbanmu ke tambaya". Baban Amira yace "Mahaifanmu na cikin Garin Edo,a unguwar Uromi, Bari zan maka Text" Yaya Abdulhafiz yace to shikenan mungode kwarai dagaske, ba, mu yan Anguwan Alk'ali ne, da ka tambayi Gidan Shamsu Abdulrahman Alo, zaa gwada maka gidan kakaninmu, sunan Mahaifin Alhaji Abu Shamsu, nima haka zan maka text gudun mantuwa". Baban Amira yace "Ba laifi mungode kwarai". Yaya Abdulhafiz yace "Sai kun jimu". Sukayi Sallama. Jawad baki uwa gonar audugu don burinshi na kan cika. E D O "Muhammadu kace akwai yaro mai neman Labibata?" Daga bangaren Baban Amira yace "Eh Abba, suna ma maganar zuwa gunku neman Izini". Alhaji Ahmad Dakata yace "MashAllahu, ya maganar mu?" Duk da ya san maganar yace "Wacce Abba?" Yace "Muhammadu Alkawarin da ka min na cewa da Labiba ta samu Miji zaka cireta daga Makaranta ka maido man Ita Gida na mata aure". Baban Amira yace "ban manta ba Abba". Abban yace "yauwa, auren shine rufin asirin duk wata diya mace, wanda tayi Allah ya sa mai Albarka, in Mijinta na da raayin karatu sai ya sakata in baidashi kuwa sai tayi yar sanaa tunda haka sauran yayyinta sukayi, amma Labiban ta amince ko?". Baban Amira yace "Eh Abba, ita ta bashi numberta ya ba yayanshi ya kirani ai, kuma da yazo Gidana na gaya mata zan turo muku su, kaga ko tanayi tunda ta barshi yazo Gidana". Baban yace "MashaAllah, wallahi naji dadi sosai, sai kaima ka fara naka binciken yanda suma zasuyi, in babu wata matsala sai a hade da bikin Yaruwarta Samira kafin Azumi". Baban Amira yace "to InshaAllah Abba, a gaida su Mami da mutanen Gidan". Sukayi Sallama. K A T S I N A Strike Din Likitoci bai dade ba, a hanyar Yasmin ta komawa Gidan Alhaji Zaki ta samu wayar sun dawo Yajin Aiki, ta garzayo Kankia she's on call, kuma akwai patients da yawa suna jiranta. Gani tayi zata bata lokaci in taje Gidan Alhaji Zaki kuma ta tafi Gidansu ta kwashe kayanta, ya sa ta kira Zaid kamar jira yakeyi ya dauka nan da nan. "Yasmin, ina kikaje you got me worried". Murmushi tayi tace "Kankia zani, ana jirana a Asibiti, in aiki yayi yawa sai Weekends, in kuma ba aiki sosai zan dawo within the week, ka kula da kanka, kayi duk wani abun da ka san zai saka farinciki da jin dadi". Zaid yace "InshaAllah" Suka katse wayar. A nan ne ya tashi ya shiga Cikin Gida don ganin Dalo kuma yayi Breakfast. 3:07 ta shigo Anguwar cikin Keke Napep, da 'yan Bencin Eskaley ta ci karo, ce ma mai napep din tayi ka tsaya nan. Ba ta fito ba sai da ta k'are musu kallo, ko wannen su da karan Sigari banda Mankas, ko ya gama shan na shi ne oho. Fitowa tayi daga Keke Napep din ta k'arasa gun su, kanshi a k'asa, hayaniyar da suke mata ne yasa shi dago kai a hankali ya sauke a kanta. Itama shi din take kallo. Da sauri ya kauda kai, shi yanzu Labiba tsoro take bashi, kar ta mishi wani magana mara dadi, kar ta mai wulakanci gaban mutanen shi. K'in kallonta yayi amma tana kallo yana dan satar kallonta, bata ce ma kowa komai ba. Eskaley ne yace "Mankas wurin ka aka zo fa". Kallonta ya danyi yaga tabbas shi din take kallo, to me ya faru? Me take so? Sai da ya dan bata lokaci kafin ya mik'e tsaye ya tako har gabanta. Ido cikin Ido suke kallon Juna, 'yan Bencin Eskaley suka zuba musu ido. Chan Labiba tace "Kai kace Kana Sona?". Ido ya k'ura mata sosai kafin yace "Ni na ce ina Sonki. "Har yanzu kana So na?" Hannu ya sa ya dafe Zuciyarshi yace "Har gaban Abada zan So ki". Idanuwanta ta lumshe ta budesu kafin tace "ina Sonka Fisabilillahi". Murmushi yayi sosai har hak’oranshi suka bayyana tace “kaga Sauro ya cijeka, kar ka ya k’ara cizon man kai, bana so”. Shewa 'yan Bencin Eskaley suka hau suna tafi, murna suke yi. Terror yace "to wallahi Yayata ke gonarmu ce, duk wanda muka gani yazo gunki sai na sare mishi k'afaffu". Murmushi tayi, ganin fuskokinsu da farinciki, its genuine, farincikin da ba kudi ya basu ba, farincikine na Solidarity da ta musu na son Danuwansu. Ta gwada musu cewa Suma fa ‘yan Shaye Shayen mutane ne, suna da damar So, suna kuma da damar a So Su, Labiba kam ta tabbatar musu da hakan. Zaid ya kallesu kafin ya dawo da kallon gareta yace “mu tafi Gida” murmushi ta mishi tace “mu tafi”. Ba magana sukeyi ba, kallon juna sukeyi sai su dauke ido, sai su sake kallon junan, sai su kuma kawar da kai, sai suyi murmushi, sai suyi dariya, shine jin dadi da farincikin da suke ciki, duk wanda ya kallesu sai ya k’ara, kallo daya zaa musu a san cewa masoya ne cike da Soyayya da shaukin juna a lokacin.,basu damu da kallon da yan anguwa ke musu ba, don bama sa ganin kowa, junansu kawai suke gani, sauran mutanen dont matter, in dai zasu kasance tare, ba su da damuwa. A bakin Gidansu Labiba suka toge suka tsaya. Sama da k’asa ta kalleshi tace “Ka san kayi kyau Jiya?” Daria ya subuce mai, be yi kokarin hana dariyar fitowa ba, bata taba ganin expression dinnan a tattare dashi ba, kawai sai ta jita cikin farinciki da walwala ganin ya sake da ita. DanMakaho ya ga dai har nuna su ake ya lumshe ido ya budesu yace “Shiga Gida”. Ta gyada mai kai alamun Amincewa. Sai da ya ga shigewarta kafin shima ya shige Gidansu. In har wani abun Farinciki ko na Bakinciki ya sameshi, world yake sha, amma yau kawai sai ya fadi kan guiwowinshi yayi Sujadda raka’a biyu don kam yaji dadi fiye da zato. Ko da Yayanta ya dawo Gida suna zaune bakin daki akan tabarma suna cin Ayaban da ya kawo, Idonta kan Gidan Alhani Zaki so take taga ta inda zai bullo. Baban Amira yace “dazu su Jawad sun kirani”. Ita ina ruwanta? Ba ta shi take ba, ta Zaid take, bata damu da tambayan mai ya kira yi ba sai cewa tayi “dazun ne ya kirani wai na tura mishi numbernka”. Don ma kar ya ja wani magana ya sa ta mikewa ta shiga Dakinta. Aunty Aseey tace “ke kuma da an fara magana sai ki fita? Baban Amira ya kuka kare?” Baban Amira yace “eh yayanshi ya kira, na dai basu Sunan baba da Adireshin Gida kuma sun bada nasu, yanzu haka a kasuwa na tambayi wani abokina dan Anguwan Alkali a kasuwa, yace ya san Family din, kuma Alhamdulah naji bayani mai kyau, amma duk da haka ba zan tsaya nan ba, zuwa gobe InshaAllah zan shiga Anguwar Alkalin na tsananta Bincike kan Mahaifin yaro da shi kanshi Yaron duk da ba tashin nan bane, ba zai gaggara ba, da ka san wani wani ya san wani haka komai zaizo da sauk’i”. Aunty Aseey tace “hakane, Allah ya sa a daidaita a yi damu”. Amsawa yayi da Amin. “Amma ka kira su Baba?” Yace “eh munyi magana, ya bar min komai yace in fara bincike saboda su san wa zai zo neman diyarsu, in ma an daidaita so yake a hada da na Samira, kuma ya tuna min Alkawarim da na daukar mishi na da ta samu Miji za ta bar karatu, to muna Addua Allah ya sa shine Mijin”. Guda Aunty Aseey ta sake tace “Ameen Wallahi, Karatun wa? Haba dai ai aure shi ne kan Gaba, ai wallahi Allah dai ya tabbatar”. 8:50pm Ko da Jawad ya kirata sai taji yau duk haushinshi ma takeji, ko mai ya fada sam baya burgeta, a k’agare take ta katse wayar, da ya dauko magana a dokance sai ta sace mishi guiwa. Ko da ya ce mata dazu Yaya ya kira Baban Amira. Da sauri tace “Eh ya gaya min”. Ita burinta ta katse wayar, shima ya lura kamar yau bata cikin yanayin, so sai bai matsa ba yace bari ya barta ta huta, haka suka aje waya”. *** Ta na jin fitar Aunty Aseey daga dakinsu ta koma nasu dakin, tana ji ta saka sakata ta tashi ta dauko wayarta ta ma Zaid text. Yana cikin shan sigarin shi yaga shigowar message dinta “Kayi bacci ne?” Daria Yayi kamar tana gabanshi ya ja sigari ya fesar cikin jin dadi yace “haba dai ko 11 batayi ba fa” “Me kakeyi?” “Zaune, missing dinki” Tace “buri daya” Yace “In kasance tare da ke daga yau har har abada”. Batayi reply ba sai yayo zaton ko katinta ya k’are ya yanke hukuncin kiranta. Ya zuk’i Sigarin karshe ya hangota ta window da sauri ya yarda ya murje be kai ga fesar da hayak’in bakinshi ba ta shigo dakin da murmushi a fuskarta. Kallo daya ta mai ta san cewa baida gaskia sai tace “Yadai nawan?”. Kai ya gyada mata, tace “ka zama kurma ne?” Ya sake girgiza mata kai tace “fito da hayak’in zai maka illa”. Cike da kunya ya juya mata baya ya fitar da hayak’in ba tare da ya bari taga yanda hayakin ya bar bakinshi ba”. Zama tayi tace “its obvious, na san shan sigari kake, tun daga Tsakar Gidanmu na jiyo hayakin, kunya yaji sosai ya shafa k’eyarshi yace “Sorry”. Ba ta damu ba tace “Well, burinka na son kasancewa tare dani daga yau har abada nazo ka ganni na yau din kafin kayi bacci”. Sosai yake kallonta yana nazarinta ganin kallon yayi yawa tace “Yadai?”. Yace “Ina tsoro” “Tsoron me?” Yace “ni dake bamu dace ba” Tace “ah haba dai?”. Ganin tana son maida abin wasa yace “dagaske nake, i am serious, bamu dace ba, wallahi gani nake kamar ma na kwareki, kamar cin mutunci ne nace ki Soni, kamar na zubar miki da kima nace ke nake so, ina jin kunya harga Allah”. Tace “DonAllah ya isheni, ashe a goshi ake rubutawa ace wance da wane sun dace, ashe a goshi ake rubuta wane da wance basu dace ba, ashe baka yarda da Son So daga Allah bane, ashe baka yarda domin Allah nike sonka ba”. Ya girgiza kai yace “ba haka nake nufi ba donAllah, wallahi bakiji kunyarki da na ji ba da kika kamani redhanded ina shan sigari, naji kunya, kuma ina tsoron abunda zai faru nan gaba in mutane suka son cewa soyayya mukeyi” Tace “huh, yaushe ka fara damuwa da abunda mutane ke cewa game da kai?da zaka damu da abunda mutane ke cewa da ba ka taba fara shan sigari ba, da baka taba zama a bencin Eskaley ba, da baka yi abota da mutanen da sukayi kaurin suna ba, to kar ma ka sake kaji kunyata wai don kayi shayeshaye, in har ba zaka ji kunyan Allah ba, waceni Labiban Dakata?” Kai ya sadda k’asa ta hango nadama da da nasani a cikinta sasauta murya tayi tace “ba a film ko novel bane balle na ce zan chanza ka kafin na soka, banda ikon chanzaka, kai kadai ke da ikon chanzaka, kai kadai zaka iya chanza kanka, Sigari, addiction ne ko? Fine ka saba, ba zaka iya daina sha ba, okay, regulate in kana shanta so dari a sati, ka shata so sha biyu a sati, in so 10 kake shanta a rana, ka shata rabi a rana, in so daya kake shanta a kwanaki 3, ashe zaka ma iya bari kwata kwata, na san da wahala, i know its hard, i know amma regulate, ba umurni nake baka ba, shawara ce, ba don Labiba ba, don Lafiyarka, na san kana shayeshaye amma na furta maka kalmar so, which means ban damu ba”. “Allah ne ya dora min sonka, to ya zanyi? Cizgeka zanyi a raina bayan Allah ne ya dasa min Sonka a raina? Ba fa zabina bane, in zabi na ne Makka zanje na So Sudaiz, so ina so ka san its Natural, Ina sonka saboda Allah, fissbilillahi wallahi, kafin na furta maka kalmar So, na san akwai k’alubale da yawa, da complications kala kala da zasuzo, akwai abubuwa da dama wanda na san Sonka zai ja min, i damned the consequences and chose to love you, so ka min adalci ka bar cewa bamu dace ba, ni da kai mun dace fa, ban cire rai zaka daina shan sigari ba, ka ceci unborn kids dinmu kar a dinga jefansu da maganganu marasa dadi saboda haka, so you need to change for good”. “Labiba zaki iya aurena?” “Toh zancen kake so, wai kai baka da android phone? Da kana dashi da video call zamuyi whenever you miss me, ba sai na sha wuyar zuwa ba kamar wata baraniya”. Murmushi ya mata yace “tashi na raka ki Gida”. Ba musu ta fito ya rakota tare da jaddada mai tana sonshi din, ya gasgata din,ya dawo zuciyarshi wasai tare da k’uddirtawa zai rage shan Sigari kuma ya bar shan world”. Washegari Zaid ya tattara kudin Account dinshi Tas ya siyo Android phone ba don komai ba don ya dinga Chatting da Bibbs dinshi. Aikam cikin kwana dayan nan sukayi wata irin Shak’uwa, son junansu suke sosai, har ya jirata ta dawo daga makaranta, ta tsaya Shagon Eskaley, suna faman yin selfie da wayarshi, ya na ganinta ya nufota yau ma shigar Yard akayi Ash wanda K’amshi ta dinka mishi Labiba tace “wai hotuna akeyi da sabuwar waya? Inye, kayi kyau sosai wallahi naji dadi da na ganka haka”. Yayi murmushi yace “naji dadi da kika ji dadi, nima zan dinga saka irin kayan nan don in miki kyau kiji dadi” Tafi tayi cike da jin dadi Yace “na san kin gaji ko? Muje Gida ki huta”. Sallam sukayi da su Eskaley suka fara strolling, ba su damu da masu binsu da kallo ba, kawai son junansu suke ba su damu da kowa ba”. *** Yana son kiranta amma bai da kudi, sabuwar waya na gun Tero da ya koma an so wayar ba ya nan, baya so kuma ya matsa mata kar ta ga kamar so yake tazo gunshi irin na jiya, shiga yayi cikin Gida ya bata lokaci wurin Dalo kafin ya dawo Daki. Yasmin ta kirashi wurin k’arfe 10:30 waya suka hau yi tana bashi labarin gajiar da tayi, sai wurin 11 suka aje wayan. Mai ya kamata yayi? Baya jin bacci, fitowa yayi wajen daki, ya zauna kan dakalin gaban daki yana tunanin karon su da Labiba dazu kalar farinciki da ta sakashi, kai ya daga sama yana kallon kyawawan taurari. “Fitsari ta fito? Ruwa ta fito Sha? Allahu Aalam, shidai kawai yaga Labiba ta tako har Gidansu ta zauna a kan Dakalin da yake zaune a kai tare da daga kai sama suna kallon sararin samaniya a tare. “Suna da kyau” tace mishi cikin wani murya. Yace “taurari? Suna da kyau sosai kam” Wani irin dadi ke ratsasu yana shiga kowani sassa na jikinsu. Idonshi ya murza ta girgiza kai tace “ka daina, ka daina murza idon nan” kallonta kawai yakeyi, kamar ya hadiyeta don So yace “Ina Sonki Bibbs”. Cike da shagwaba tace “wannan Auntyn fa?” Zaid ya murmusa yace “ta koma Aiki” Ta dan maido hankakinta gareshi ta “Son ka takeyi ko?”. Dan jim yayi kafin yace “Yas ba matsala bace”. Labiba ta turo baki tace “wace iri ce ita? Tana Sonka kuma take son ganin ta hadamu?”. Murzan ido ya sakeyi yace “yin maganarta dake, ban mata adalci ba”. Labiba ranta ya dan sosu ganin Antyn na da mahimmamci a rayuwanshi tace “Fine, ni son iyawanta ne bana so, tana acting kamar ta fi kowa Sonka a dunia, ga feleke da iyayi, shekaran jiyan nan da tace ta rakoka zance wurina kamar na mutu wallahi saboda da takiaci, kai ma ka fi ban takaici duk ka ban haushi da ka biyota wani zololo kai an rakoka zance, dont you have legs?”. Ji yayi ta burgeshi Ainun yanda take magana cike da sanyi amma ita a ganinta ranta bace yake. Zaid yace “Kishi kenan?”. Baki ta turo tace “oho, nidai kar ta sake wani cewa ta rakoka Zance”. Dariya yayi yace “Yes Ma”. Kema wannan da yazo gunki rannan Sonki yakeyi, kuma har daria kike mishi, you look happy, harda murguda baki.. Daria tayi tace “Jayy dina kenan” Hararta yayi yace “meye kuma Jay”. Tayi daria tace “J for Jawad”. Baki ya tabe “meye wani J? Aa H ne, you are so Unromantic” Tayi daria tace “why are you like this?”. Yace “point is i dont like him, kuma dagaske kar ya sake zuwa wurinki, kin dai ji ai mai su Terror suka ce miki jiya? Wallahi they will hurt him suka ganki dashi, and I cannot stop them, don ba ji zasuyi ba, so in ba so kike su karya mai k’afa ba, he should never come back again” ya fada yana dage kafada. Harara ta zabga mai tace “kaga kai da mak’arabanka su fita daga hanyan mutane na? Poor Abu Sadeek tun ranar bai sake bari mun hadu ba, ina ta so mu hadu na bashi hakuri baya bari, kuma yayi blocking din chance din haduwar mu, bai ma zuwa School din sosai, ko yana zuwa wallahi nidai ban ganinshi”. Dadi Zaid yaji ya tafa yace “weldone yaro yaji warning, so same thing will happen to that spoilt brat, dagaske kar ya sake zuwa”. Dadi maganganun shi ke mata, ashe yana kishinta haka tace “nifa ka daina kora min samari”. Ya hayyak’o yace “Labiba Ahmad i am dead serious, kar wanda ya sake zuwa wurinki, ke tawa ce nikadai”. Kamar ta narke don jin dadi ta lumshe idanuwanta ta bude tace “I am dead serious Zaid Ali Zaki, ni taka ce, kai nake so har cikin raina”. Cikin wani yanayi ya kalleta yace “har ranki?”.. Ta murmusa tace “Ehh, har chan cikin raina nike sonka”. Yace “Ina Sonki Wallahi, ina Sonki nima”. Tace “to dai Jawad kam ba matsala bane, abunda ya faru Cousin din Bestyta ce, kuma ni dama wallahi Girmanshi nake gani, and other days da muka samu sabanii, ji nayi zaman Katsina ya isheni, ni kawai i was desperate na yakiceka shiyasa nayi tunanin maybe i could give him a chance, and still babu wani abu da ya chanza game dashi, ina girmamashi, ina kuma ganin mutuncinsa, kuma dama ina da niyar gobe inshaAllah na gaya mishi ni kai nake so, yayi hakuri kar na bata mishi lokaci ya nemi wata yayi hakuri kam, so Mr Zaid kai kadai nake so, kuma ni na amince Ni taka ce”. Zaid ya ji ta gama burgeshi matuk’a, wani girmanta ya sake girma a idonshi, she’s so matured ya Allah, wato ba ta iya cewa ranakun da ya mata wulakanci ba sai dai ta ce rannakun da suka samu sabani, gaskiarta na burgeshi, ya san tunda tace zata tsaida Jawad, zai ranste zata tsaida shi din don ya lura she is so honest and straight, ya san zata dakatar da Jawad din, ganin zata saka shi kuka saboda murna yace “Mallam kika sake kika min saving sunan as wani Z or kikace min Z sai na cijeki, wai J aa F” Daria tayi sosai harta na rufewa don ta na tsoron kar ta yi harta ta tado masu bacci” Tace “amma fa duk daya ne, sounds the same Z or Zaid duk daya ne”. Yace “ke ni fa ba ABCD nace ki min ba”. Tayi daria ta latso contact dinshi ta nuna mishi tace “daga ranar da nayi saving number dinka, har yau this is what it has been”. ‘SOULMATE’ ya gani barobaro a jikin Screen din wayar. Lumshe idonshi yayi, ya dau seconds yana jin wannan yanayin kafin ya bude ido, k’aunarta na sake kunnuwa a zuciyarshi yace “Zaki kasheni da dadi, its late, tashi muje na rakaki, ki tafi daki, ga sauro duk ya cije mana kafafu?”. Daria tayi tace “naji dadi da yau ba kai kadai ya ciza ba, gwara da suka hada dani, we are in this together”. Daria yayi yace “Sannu Lover Girl, zaki gaya min wa ya koya miki Soyayya, wannan H dinne ko?”. Daria tayi tace “heyy, ya kake bata ma saurayina suna, jay ne fa”. Yace “Allah zan rankwasheki kika sake ce mai saurayinki, ni kadai ne saurayinki”. Tace “heyy, you havent even asked me out yet”. “Haha oh Oh, Labiba Ahmad Dakata will you be my Girlfriend?”. Tace “Uhmmm sai nayi tunani”. Ya hararega cike da kauna yace “Shutup and get up, muje ki shige daki”. Batace komai ba ta mike, suna tafia cikin sando kar a ji su kamar barayi na shirin shiga sata Sai kuma Zaid ya dan tsaya chak duk ya jin rashin dadin yanayinsu, juyowa tayi cikin muryar rada tace “yadai?”. Shima cikin muryan radan yace “Ba sai kin sake zuwa Gidanmu ba daga yau, ni ne namijin, daga yau ni zan dinga biyoki Gidanku, but we are going to do it Legal, zan zo miki kamar ta yanda duk wani Namiji ke zuwa wurin abar sonshi, i will come through the gates not the walls, lets do it legally ko?”. Kamar ta maidashi ciki don So tace “Lets do it legally”. “I love you” “I love you so much babe shiga ciki”. Bata juyo ba ta shige daki, shima sai da ya ga ta shige daki ya koma nashi dakin yaga 1am har ta kusa yace “lallai lokaci na gudu in kana tare da masoyi”. Kan katifarshi ya haye yana tunanin Labibarsa. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉 BABI NA ASHIRIN DA SHIDDA 2⃣6⃣ (BAIKO 💍) Da yake duk sun sa ma kansu abun, cikin kwanaki biyu su ka binciki Juna, akwai wani Mutum a Benin City, shi Abban Jawad ya tura ma Details kan Alhaji Ahmad Dakata yayi mishi background check kan family dinnan kuma ya samu gamsasshiyar Amsa. Yace mishi Mutumin babban mutum ne datijo kuma bai da matsala, gidan shi Gidan Mutumci ne. Haka nan Baban Amira ya binciko Asalin su Jawad a Unguwan Alkali, kasancewar Family dinsu ba boyayye bane, babu wani abun Assha da ya ji game da Family din, ya kira Mahaifinshi ya sanar dashi, baban yace "to Alhamdulilah, kace su turo". To kafin ma Baban Amira ya kira Yayan Jawad yace mai su turo sai ko ga dan Halak din ya kira ya sanar dashi cewa "Akwai wani Uncle dinsu da yazo Abuja, zai koma ran Friday, to sauk'i suke so ba sai an tado kowa daga Katsina ba a tura su chan Edo neman Izini why not su tafi gobe Alhamis? Ba tare da an wahalar da mutanen katsina ba? Amma fa sai in ba matsala a wurinku be san ko its a short notice ba?". "Bakomai" Yaya Muhammadu yace, zan gaya musu suyi shirin tarban ku Gobe in Allah ya kaimu, suka rabu a mutunce don yin shirin tafiar su kuma da tarban bakin. Yaya Abdulhafiz ya gaya ma Abbansu yanda sukayi da Yayan Labiba, shi kuma Abban ya kira k'aninshi ya gaya mishi, k'anen yace bakomsi suna iya tafia gobe su dawo goben Friday sai ya dawo Katsinan. Abba yace "akwai stress, bari na aiki Abdulmajeed naga ko zamu iya samun tickets to Edo" A hakan suka rabu. Yaya Muhammadu ya kira Gida ya musu bayani cewa gobe zasu zo saboda wasu dalilai, Babansu Labiba yace "haba bakomai su zo, ita kuma ka saka ranar kawo min ita Gida, tunda dai ga Miji, a bar karatun haka nan". Mallam Muhammadu yace "InshaAllah baba, bari dai suzo muga yanda zaayi ba zai gagara ba InshaAllah". A hakan suka rabu. WASHEGARI EDO STATE Kamar yanda Abba ya tsara su 5 suka ya tafiar zuwa Edo Benin City, Abba, Daddy Usman, Yaya Abdulhafiz, Yaya Abdulmajeed da shi kanshi Jawad din, a cewar Abba gwara su ga wanda zasu ba diyarsu tun yanzu. Tafiya ce mai nisa, sun iso Edo after 12, kamar yanda aka umurcesu, Dan Achaba suka tsayar su ka bashi adireshin gidan yayi gaba suka bishi a baya har kofar Gidan Alhaji Ahmad Dakata. Yana a bakin Gate din Gidanshi tare da Manyan Yaranshi su 4, suka tarbesu cikin mutunci, Sukayi ma juna Musabaha cike da farinciki kafin Alhaji Dakata ya ja hannun Alhaji Abu Shamsu har cikin Parlo suka zauna. Bayan 'yan gaishe gaishe, aka ci abinci don sosai Alhaji Dakata ya sa aka musu Abinci har kala 3, sunci sun gyaste. Alhaji Abu Shamsu ya gabatar da Daddy Usman a matsayin kaninshi kuma waliyi madaurin auren 'yayanshi. Ya gaya mishi yana da mata biyu da yara 4 Abdulhafiz shine babban danshi sai mai bi mishi Abdulmajeed sai auta a mazamai neman diyarshi kuma Jawad, sai miemee yar shekara 3. Alhaji Dakata yace "MashaAllahu, Allah ya raya mana zuria, nima dai Matana 2, ko waccen su na da 'yaya takwas, ni mai tarin zuria ne, Babban yaro na shi ne Labiba ke gunshi a Katsina, wannan sunanshi Hamza, sai wannan sunanshi Faruk, ga Aliyu wannan kuma mai sunan babana ne Lawal. Da faraa suka sake gaisawa. Daddy Usman Abba yace yayi magana. "Alhamdulilah kamar yanda ka sani munzo ne don muga tushen Yarinya kuma mu nemi a ba dan wurinmu Izini ya dinga zuwa gunta su fahimci juna". Alhaji Dakata ya murmusa yace "Mallam Jawad, kai ne ke son Diyata Labiba? Fada min naji daga bakinka". Jawad ya dago kai ya sauke da sauri irin kwarjinin da mutumin ya mishi. "Eh nine". Alhaji dakata yace "ka shirya aure?". Jawad ya kalli Babanshi kafin yace "eh na shirya". Alhaji Dakata yace "to MashaAllah, abu yayi kyau, Itama nayi magana da Yayanta yace tana sonka tunda ta barka kazo gida wannan alamace ta yarinya na sonka din, nikuma gaskia a tsarin gidana, ban yarda ayi ta zuwa zancen nan ba, in aka ce yaro na son diyata, in na bincike yaro na binciki halinshi da asalinshi, sai in kirasu a daura aure, bana son bacin lokaci, amma naji dadi yanda ka kwaso min Iyalinka na gani, naji dadi wannan ya nuna halin girma, na amince da ku dari bisa dari, na ba danku Labiba, kuzo duk lokacin da kuka shirya ayi auren". Alhaji Abu Shamsu ya murmusa yace "Alhamdulilah mun ji dadi sosai da karamci, amma so muke ka gaya mana cewa ga ranar da kake so muzo ayi maganar Aure, diya taka ce, magana ma takace". Alhaji Dakata yace "wallahi bakomai, ni da kuka nuna kuna son nawa? Ko yaushe kuke so sai ayi, ku dai da kun shirya kuzo". Alhaji Abu yace "dagaske Alhaji kafada, mu fa a shirye muke, ko yaushe ne, Mu ko yanzu kace a daura ai sai a daura". Daria sukayi gabaki daya. Alhaji Dakata yace "to shikenan, faduwa tazo daidai da zama, akwai yaruwar Labiba wato Samira, an saka ranarta, auren nata nan da kwana 45, in babu matsala, ina so in hadesu su biyu na aurars". Alhaji Abu ya fadada fara'arshi yace "ba wani abu InshaAllah, mu da aka ma gata? hakan ma yayi, ba amfanin raba biki biyu a shekara, gwara kawai a hadesu". Dadi kamar ya faso zuciyan Jawad jin shi zai yi niyyar aure nan da kasa da wata 2. Daddy Usman yace "aikam bari in bada kudin neman Aure" Ya ciro naira dubu dari a Aljihu ya kawo ma Alhaji Dakata har gabanshi. Ya sa hannu ya karba, yace "naira dubu dari? Ai tayi yawa Alhaji Usman". Daddy Usman yace "aa bata yi ba, bikin Autan Umma ne fa". Alhaji dakata yace "aa gaskia tayi yawa, nifa aladar nan wai ta bada kudin neman aure da ina da yanda zani yi dana hanata" Daddy Usman yace "haha, to tunda dai anayi, shikenan muma munyi". Alhaji Dakata yace "wallahi sunyi yawa, amma abunda zanyi, na dauki dubu hamsin na neman auren, dubu hamsin na sadakinta". Alhaju Abu Shamsu yace "shikenan an raba gardama". Duk sukayi daria suna masu ganin mutuncin juna. Da zasu tafi aka cika musu booth da Doya da Makani da jarkan Manja, suka rabu suna sambarka da junansu. Bayan tafiyansu ya kira Mallam Muhammadu ya sanar dashi duk yanda sukayi. Baban Amira yace "hakan yayi Abbanmu, ina kasuwa sai anjima zan koma gida na sanar dasu yanda akayi, MashaAllah abu yayi kyau". Gidansu ya kachame da Abbansu ya sa bikin Labiba rana daya dana Samira, 'yan uba kam ba su ji dadi ba, balle da labarin yazo muso cewa gidansu mai son auren Labiba mai kudi ke, duk surukan gidan babu mai kudinsu mijin Labiban, a da suna ta jin dadi Samira zatayi aure Labiba batayi ba, yanzu ko ransu ya baci jin ta samu Miji dan Babban gida kuma. Mamin Labiba kam godia take ma Allah da zai nuna mata bikin Labibarta. K A T S I N A A Masallacin Anguwar yayi Sallahr La'asar, Mallam shehu ya tareshi a hanya yana tambayarshi. "Wai ni Mallam Muhammadu wannan k'anwa taka ya ma sunanta?". Baban Amira ya murmusa yace "Labiba Sunanta". Mallam Shehu yace "ita fa, ni ina mamaki, meye hadinta da wannan yaro dan gidan Alhaji Zaki" Baban Amira bai gane zancen ba yace "wai wa? Yace "wannan yaro mana DanMakaho" Da mamaki yace "DanMakaho kuma? Ita fa ko saninshi batayi ba, me ko zai hadssu?". Mallam Shehu yace "ya zakace ko saninshi batayi ba bayan kullum sai na gansu tare, jiya da tsaye na gansu a shagon Eskaley kuma suka ketaro Anguwa tare, duk wands ya gansu ya san masoya ne, kuma sai da suka tsaya kofar Gidanka sukayi zance kafin ta shige gida". Mamaki duk ya bayyana a fuskarshi yace "Anya dai? Ba dai Labiba ba". Mallam Shehu yace "hmm, baka yarda ba ko? Ka dai bincika ka gani, dama nace in gaya ma ne don ka san yanda zakayi ka datse Alakara su tunda dai kowa ya san DanMakaho dan Shaye shayene kafin ta zubar maka da mutunci gwara ka katse ma hanzarinsu gudu". Baban Amira ya ma rasa abunyi don shifa bai yarda ba, haka ya k'ama hanyar gida jiki a sanyaye. **** Fitowar ta kenan daga Gida, ta ganshi tsaye ya rungume hannu a kirji kafarsa daya kan bangon gidansu. Suna hada idanuwa suka murmusa ma Juna, kusan a tare suka ce “Kinyi kyau, kayi kyau”. Sukayi daria a tare yace “ai ban kai ki ba”. Tace “ka fini mana” Yace “ya makaranta? Are you stressed out?” Tace “i was, amma ganinka ya sa gajiar duk ta tafi”. Ya dago kai da murmushinshi kafin yace wani abu ya Hango Mallam Muhammad na nufosu. Ya dan tsorata yace “Shiga Gida Biebbs” da mamaki ta kalleshi tace “meyasa?” Murya k’asa k’asa yace “ga Yayanki nan”. Ta dan waiga ta ga shi dinne, ko a jikinta don ma murmushi take mishi da ya zo gabansu ya kallesu daya bayan daya. Labiba tace “Yaya sannu da zuwa” Baban Amira yace “DanMakaho mai kakeyi a kofar gida na?”. Zaid ya dan fara in ina yace “bakomai, dama wucewa zanyi”. Labiba tayi karaf tace “Yaya wurina yazo” Mallam Muhammadu ya kalleta da mamaki yace “wato maganganun da ake fada game da ke a anguwa”. “Gaskia ne” Ba tare da ta san me yake nufi ba ta amsa shi. Mallam Muhammadu yace “Labiba shiga Gida”. Tace “To Yaya” Ta kalli Zaid tace “Barin shiga ciki, sai munyi waya”. Zaid sadda kanshi k’asa kawai yayi, wai ya ta ke haka? Ta ya take iya fadan abunda ke ranta ba tare da ta sakayawa ba? Ai a irin yanayin nan k’arya ya kamata tayi, ansan bata k’arya, amma dai yanda bata ji nauyin yayanta ba ya sa shi jin wani iri. Yana jira yaji Yayanta yace wani abu amma bai ce ba illa ce mishi sai anjima da yayi. Ya shiga Gida ya ga Labiba tsaye, kwala ma matarshi kira yayi. “Asiya, Asiya”. Sai ko gata ta fito da sauri jin kiran Mijin nata “Wai dama kinsan Yaron nan DanMakaho na zuwa gurin Labiba?” Ido ta bude tace “wallahi ban sani ba, DanMakaho kuma? Wani irin dan Makaho? Tare ka gansu?”. Ta tambaya tana kallon Labiba. Labiba tace “Yaya fa bata sani ba”. Yace “yi min shiru”. Aunty Aseey tace “dagaske ne? Ke ko me zakiyi dashi?”. Baban Amira yace “bude kunnenki kiji, kar na sake ganinki da Yaronnan, kuma an sanya ranar aurenki da Jawad, sadakinki dubu hamsin na gun Baba, dazun sukaje neman aure Baba kuma ya amince musu, tunda ya ansa sadakinki”. Labiba jin abun take kamar Almara tace “Yaya chabda, lallai kam”. Yace “kin dauka wasa nike?” Kallonshi ta tsaya yi tana karantarshi, iyakar gaskia ta karanto a idanunshi. “Yaya ta ya akayi bansan shiryshiryen nan ba?” Yace “kinyi waya da Jawad jiya zuwa yau?” Tunawa tayi rabon da suyi waya tun ran Tuesday, kuma messages dinshi a whatsapp suna chan tayi hanging. Tace “Huh, Yaya har kai baka min maganar ba”. Yace “tunda kika kawo minshi Gida magana ta k’are”. Ko a jikinta tace “nikam ba a daura ba ai? To ku mayar mai da sadakinshi, nikam DanMakaho nike so, kuma ni shi zan aura”. Ta shige ciki ta barsu da mamaki, barin ma Baban Amira, Labiba bata taba mishi rashin kunya ba, shekara 26 ya bata, amma yanzu ita take mishi rashin kunya akan Namiji? Namijin ma DanMakaho?. Zuwa yayi yana kwankwansa mata amma ta ki bude dakin, ran baban Amira ya baci, ya shige daki. Itama Labiba ranta a jagule ta kira Mamarta ringing daya ta dauka tace “Mami, dagaske an kawo sadakina? Dagaske bikina rana daya dana samira?”. Mami tace “Eh Labiba, aikam mutanen Kirki”. Labiba tace “Mami nifa ba zan aureshi ba, so daya yazo nan gidan, kawai suka zagaya suka ma Yaya Muhammadu magana shine ya turasu chan gun Baba”. Mami tace “Labiba mai kike son cewa? DonAllah nidai ki rufa min Asiri, bakiji me ake ta cewa a cikin Gida ba”. “Mami su fada abunda suke so, nikam ba zan auri Jawad ba, ina da wanda nake so”. Mami tace “Labiba kiyi hakuri donAllah, kinsan babanki kaifi daya ne, ya amince musu, ki rufa min asiri”. Labiba ta lura Maminta ba zata gane ba yanzu tace “Mami zan kiraki, ina zuwa” ta kashe wayarta. Sukuku ta karashe ranar Alhamis, ba wandata ma magana har yaran yayanta, da daddare ta sha zancenta da Zaid a waya ba tare da ta damu da komai ba, don ba mai mata auren dole so wannan ba matsala bace, ta cigaba da harkan gabanta. F R I D A Y. Daddy Usman yazo musu Sallama, Doya da makani damanja Galan Biyu da suka samo jiya a Edo AbdulMajid ya saka mai a booth, yayi breakfast, sukayi dan fira da Yaran Yayanshi kafin yayan ya fito, sannan yayi sallama yace "bari ya tafi". Gabaki daya Iyalan Alhaji Abu Shamsu suka rakoshi har bakin Mota suka mishi fatan Allah ya sa a isa lafia suna mai mai fatan Alheri. Daddy Usman ya kama hanyar ta dikko dakin Kara. *** Tsautsayi ne ya faru da Alhaji Usman a hanyarshi ta komawa Katsina, yana daf da shiga Katsina a Charanci yayi hadari inda Shanu suka gitta mai garin kauce musu ya bige wani Mutumi tare da fadawa wani kwalbatin da ya sa shi buguwa a kai. Mutanen Anguwa suka kawo dauki, da aka duba sai aka wanda Alhaji Usman din ya bige ya cika don ko shurawa beyi ba. Da yawa kan idonsu abun ya faru sun san cewa ba laifin Alhaji Usman bane, nan da nan yan garin suka taimaka suka kai Alhaji Usman Asibiti mafi kusa. Wayarshi wani ya ciri ya cire sim din ya saka a wayarshi don wayar Alhaji Usman din akwai Pattern. Duba contact list yayi yaga dai ba wani suna Mama ko Baba, sai yaga Contact din My Son. Da sauri mutumin ya latso numbern. A B U J A Abdulmajeed cike da shagwaba yace "Yanzu kai shikenan Abba ka yarda Jawad ya rigani Aure?" Mancy tace "to tunda baka da niya ba gwara ya yi overtaking dinka ba?". Abdulmajeed yace "fa Mancy ba laifina bane, ko dazun sai da nace ma Ya Abdulhafiz yama Daddy Usman magana a hada bikin da nawa da na Jawad Abba ya hana, wai ba ya so ya shiga hakkin Daddy, kuma wai karatu takeyi sai ta gama ND1, afterall wallahi cireta ma zanyi daga Poly, Haba Polyn lafia". Abban ya harareshi yayi saurin sadda kai, Umma tace "gaskia Abbansu da ka bari an hadasu, ai ba shiga Hakkin Aisha diyarka ce kaine waliiyyinta, in ka yanke hukunci kanta ba mai ce maka don me?". Shiru Abban yayi kafin yace "shikenan, bari Usmanun ya isa zamuyi waya, sai mu ji in zaa iya hadesu". Abdulmajeed ya gallawa Zaid harara yace "mallam sai ka bar mi gwalo hakan nan, inshaAllah ba zaka rigani aure ba". Jawad yace "hahah aiko zaka sha madaran mamaki". Sukayi daria baki daya. Suna cikin firansu mai dadi ne wayar AbdulMajeed yayi ringing, Ya kallesu baki daya da murmushi a fuskancshi yace "Daddy Usman ne" Jawad yace "kace sirikinka ne" Ya jefeshi da harara. Mancy tace "kai wani irin Gudu Daddy Usman keyi haka? Har ya isa kenan". Jin tashin hankali sukayi a muryan Abdulmajeed. "Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, mai ya sameshi? Yanzu yana ina?". Kowa na cikin parlorn ya fara tambaya mai ya sami Uncle Usman. Kasa magana yayi sai da Abban yace "Kai Abdulmajeed, ka gaya mana mai ya samu Daddyn naku?". Abdulmajeed kamar yayi kuka yace "Abba hadari Daddy Usman yayi a Charanci, ya bige wani mutjmi har mutumin ya mutu amma shi Daddyn yana Asibiti ba abunda ya sameshi sai dai wai ya bugu a kai". Tunda ya fara magana suke Salallami da Salati. Abba cike da kidima ya ciro wayarshi ya kira chan Katsina gidan Iyayenshi ya sanar dasu, da su je Charanchi yanzu yana nan tahowa gobe InshaAllah. Ya Kalli Iyalanshi da sukayi saye cirko cirko yace musu "ku shirya, gobe inshaAllah zamuje Katsina". Amsa mishi sukayi duk jikinsu a sanyayye K A T S I N A Ai yayewa akayi a Unguwar Alkali harta Hajiarsu Alhajin suka kwasa suka nufa Charanci har su Aishan. Kafin su je an gano Gidansu Mamacin, suka shiga akayi magana, Allah ya sa Saurayi ne, baida Iyali, Mahaifiyarshi kam taci kuka sosai amma ta yafe Wanda ya bamkeshi yayi kaffara, aka rufo mamacin. Basu kwana a Charanci ba suka wuto Katsina. Asibiti zaayi dashi yace shi dai donAllah a kaishi Gidanshi don ya tsorata sosai da abunda ya faru. Tunda suka dawo Gida ake zuwa yi musu jaje ko wani lungu da sak'o, gidanshi ma bude ya kwana saboda masu shiga da fita, wasu sun kasa hakura safiya tayi su zo, abunku da 'yan dangi. * 'Yan Abuja tun safe wurin 8 suka fito, Mota biyu sukayi, AbdulMajeed ke jan Abba da Matanshi Umma da Mancy, sai Abdulhafiz ke jan Matarshi Ummita da Jawad da Mimi, a tare suke taafiya ba'a gudu da Abba, shiyasa suke dadewa akan hanya, sai da suka tsaya a Zaria suka ci Abinci a Shagalinku kafin suka sake daukan hanya. Sun iso Charanci wurin Karfe2, tambaya sukayi gidan da aka banke wani Jiya, har kofar Gidan aka kaisu, suka shiga, sai kallonsu ake tayi aka dai gaigaisa. Abba yace "ina Mahaifan yaro?" Aka gwada musu Uwarshi. Yace "Uba fa?" Akace ya dade da rasuwa. Abba ya gabatar da kanshi a matsayin Yayan wanda ya banke mata da, ya roke su gafara, mahaifiyar yaro tace "wallahi Alhaji, lokacin Saminu ne yayi, K'anenka ne sila, amma lokaci yayi ba wata dabara da zai tsaida tafia". Matar ta burgesu, nan aka musu karamci aka kawo musu ruwa fiya wota (pure water) da damammen fura. Ba wanda bai sha furan nan ba sai mimi da bata shan fura, suka sha suka sake musu gaisuwan mutuwa kafin Abba ya cika Mahaifiyar yaro da Alheri. Godia ta hau yi ta na kuka tace "Saminu ya tafi, amma sanadiyar shi sai samun Alheri nakeyi, Dazun ma Maidakin Mutumin tazo da tawagarta, wallah sun cika mu da abun Alheri, mungode mungode, Allah ya ji kanka Saminu". Da kyar suka bata baki ta bar kuka, suka musu rakiya har bakin Mota kafin suka dau Hanyar Katsina kuma. A Garin Katsina. Zaune ta isketa a babban Parlo tana kallon dadin Kowa sabon Salo na karfe 3. "Nene Jaje zanje Unguwan Alk'ali kafin yara su dawo Islamiya" Nene da ke tamnar cingam tace "Jaje na me? Me ya auku?". Hajia Aisha tace "wallahi Mijin k'awata ne yayi hadari, yayi banka a hanyar charanci, har wanda ya banke ya Rasu". Nene tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Allah sarki, kije dani nima nayi musu jajen". Hajia Aisha Lema tace "Eh sai muje Nene, abun ba dadi wallahi ". *** Welcome to Katsina ta gani a tollgate, gabanta ya yanke ya fadi, Katsina...bayan ta auri Babansu Jawad tazo katsina so uku zuwa hudu, bata san meyasa wannan karan ta ji faduwar gaba ba, jikinta ya soma rawa, haka kurum ta ke jin faduwar gaba a zuciyarta, Zaid, Sadiya, ya kamata ta gansu, amma ina bata shirya ganinsu ba, ba yanzu ba, shiyasa kamar zuwanta na baya har taje ta dawo bama zasu san ta zo ba. Straight Gidan Daddy Usman suka nufa. Aisha ta rugo da gudu ta rungume Umma kafin ta rungumi Mancy. Ta gaida Abba da yayyinta ba tare da ta kalli AbdulMajeed ba. Suka karasa har Parlon Daddy Usman, Parlorn cike yake da mutane, aka gaigaisa aka ma Juna Jaje, Alhamdulilah jikin da sauki sai ciwon kai, akayi wa juna barka ba abunda ya samu Daddy Usman, Antisco tace "Abinci na Parlo na, ku muje kuci kun kwaso hanya". Abba yace "ai mun tsaya Charanci gaisuwa sun bamu fura munsha". Antisco tace "ai abun bai yi dadi ba, nima dazun da safe mukaje muka sake musu gaisuwa, duk da lokacinshi ne yayi harda sila dai". Suka sake jajantawa juna kafin suka dunguma baki daya Parlon Antisco, Mancy ta shiga toilet din Parlorn. Sai Ga Hajia Aisha da Hajia Nene sun shigo Parlon Antisco, Antisco ta musu maraba, suka tarbi juna suka zauna don yi ma juna Jaje da Barka, Alhaji Abu Shamsu ya gaida Nene ta mishi Jaje, Suka gagaisa duka harda Umman su Jawad, Antisco ta rakasu chan Parlon Daddy suka mishi Allah kyauta, suka koma Parlornta don parlon Daddy cike yake da 'yan anguwan alkali. Jawad da yayyinshi suka zuba Abinci suka fita waje wai Mota zasu. Fitowar Mancy daga Toilet ta hada ido da Nene, tare suka zare ido suna mamakin ganin junansu, Mancy tace "Nene?". Nene ko ta buga muguwar tsaki ta tashi ta fita daga Parlorn. Duk suka bi tsohuwar da ido Umma na ma Alhaju Abu magana da ido ya mata alamun baisan ko wacece ba. Mancy da Hajia Aisha Lema suka bi bayan Nene. Nene na daga kofar parlo a hakimce tana jiran Mamyn Rafeeq ta fito su wuce amma a zuciarta mamakin chanzawan Mancy take, da alamu duk inda take tana jin dadin Aurenta. "Hajia Aisha Ina wuni? Ya yara? Ya wurin su Rafeeq da matarshi?" Mami ta amsa mata da fara'a, "lafiya lau Hajia Maryam ya bayan rabuwa?" Mancy tace "Alhamdulilahi". Kallon Gogiyar tayi, gogarku sai tamnar cingam ake kachalkachal ana kallon gefe irin bata san akwai mutum a gurin ba. Murmushi Mancy tayi tace "Haba Hajia Neneta" Nene bata amsata ba, tace "Hajajju Nene mutanen Makka, Allah ya sake hadani dake a Makka na goyaki bayana" yanzun ma ko kallonta bata yi ba, hannu Mancy ta sa ta na taba cinyar Nene ta na kiran sunanta. "Nene, Nene, Nene, haba Nene" Nene ta mik'e cike da masifa tace "haba Mallama, ya zaki ta sani gaba kina min Noiiiiise? Is Stupid? Ke tsaya ma is no me ne? Nace is no me?". Mancy ta murmusa tare da rik'o hannayenta biyu tace "I know you very well Nene" hannu Nene ta fizge ta bugar ma Mancy baki tace "Ni kike ma turanci? Dan iskancin kin sa k'afa kin bar Katsina, ba waya ba komai, kika maidani wata mara amfani ashe yanda na daukeki ba haka kika daukeni ba, kin take duk wani abunda ke tsakaninmu da k'afa, bayan shekara kusan 4 kinzo kina cika min kunne da surutu, har da karfin halin turanci, Allah ya tsine miki kika sake furta man kalmar turanci". Mamin Rafeeq tace "kiyi hakuri Nene, kina daga Murya, kar 'yan Parlo suji" Nene ta sake bude murya tace "Su ji, nace Su Ji, ai gwara su ji". Mancy ta murmusa ta sake rik'o hannun Nenen tace "kiyi hakuri donAllah, ban kyauta ba, nasani ni mai laifi ce wallahi, Nene banda zabi ne, abubuwa sun fara da sauri ne, wallahi a lokacin ban san me nayi ba, kuma ni wallah kunya ma nikeji, ki yi man hakuri donAllah, fushinki na sosa min rai donAllah Nene". Nene ta dan sha mur tace "kinsan na gaji Yafiya wurin Mahaifina, na yafe miki, amma banji dadi yanda kika watsar dani ba, kika nuna ma duniya baki da gata a Katsina, ni yanda aka ci maki mutunci a garin Katsina da kin gaya man sai na sai miki mutunci kuma in ci uban mutum ko uban wa ya tsayar mai daga nan har gaban ko wani dan shegia amma kika tsallakeni, ke kika sani". Mancy tayi ta kallon Nene da mamaki, ta san Nene bata da hakuri bata da ragowa amma yanzu ta ga Nene ta koma kamar wata 'yar Tasha. Nene tace "yana ga kina kallona? Ko zagin uwata zakiyi?". Mancy ta hau Girgiza kai tace "Nene ki rufa min Asiri, wai ba ma kince kin hakura ba?". Murmushi tayi tace "oyoyo Maryama, nayi missing dinki". Mancy tace "Hajia Aisha kinga Nene ko? Turanci tamin, nikuma in na mata a zageni". Mamyn Rafeeq tace "ina ji dazu har tsine miki akayi". Daria sukayi tare. Nene tace "sai aje a ga su takwaran Zaidu bawan Allah ko?". Mancy ta dan rage annashuwa tace "Aa Nene". Nene ta sha mur nan da nan tace "bangane Aa ba? Ba zakije ki ga yaranki ba? Ke wai wace irin stupid ce? Me ke damunki? Baki da zucia? Wace irin uwa ce ke? Wallahi ki guji haduwarki da Ubangijinki, Allah yace dukkanku Makiyayya ne, kuma sai Allah ya tambayeki yanda kikayi da naki Kiwon, ya kikayi da kiwonsu? Daya ya zama dealan Wall kobo biyar ba zaki saye shi ba, ta macen Allah ya tsare miki ita, wallahi jiya naji a radio wata ta kashe kanta saboda bakinciki, ke kiyi hankali, ke kin ma ci uwarki in kikaje ganinsu, ke Aisha wuce mu tafi". Alhaji Abu Shamsu da Matarshi suka fito bakin Parlon da alama sun gama jin duk wani abunda suke tattaunawa. Mancy tuni ta sha jinin jikinta Alhaji Abu Shamsu yace "wallahi Mama, tun kafin na auri Hajia Maryama na nuna mata ina son rikon yayanta amma ta hanani, ta nuna min gwara ta barsu Gidan ubansu, na ce mata ko zata bar Namijin ta dauko Macen don Tarbiyar diya mace in ba Uwa to akwai Matsala". Nene tace " kai k'yale sakarar, ai maryama da kake ganinta muguwar sakara ce" Umman Jawad tace "ke ko Maryama har yau baki huce ba? Ai ba zaka dauki laifin uba ka shafa ma yaranka ba, wake fushi da 'ya'yan cikinshi, ke ko kije ki gansu ko so daya ne". Nene tace "sai wani aiken da take musu duk wata na banza, ce miki sukayi suna Son abun hannunki? Sunfi bukatar ki, yaro na nan ya zabge ya tsure, a lokaci guda sai ya shanye kwalin sigari daya,ga tabar wiwi yana zukarta kamar ba gobe har wani suna yan jagaliya ke ce mishi wai Mankasss". Mancy cike da kidima tace "ba dai Zaid ba". "Aa Ubana" Nene ta fada cike da fada. Mamyn Rafeeq tace "haba Nene kiyi shiru". Ita ko Nene kira take "ban yin shiru, laifin wa? Wallahi lafinki ne, da kyar in baida ciwon k'ofa dan wallahi fari yke fayau, in ya mutu Kurani ke kika kashe danki". Tuni Mancy kafa ya fara rawa, fitsari ya cika marar ta taf kamar ba yanzu tayi fitsari ba. "Alhaji, donAllah ka min izinin zuwa ganinsu, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, na shiga uku na, Zaidda shaye shaye?" Alhaji Abu yace "Maryama kinsan dai tun yaushe nake binki muje ki gansu ko? Kin san ba zan hana ba, ko yanzu kika ce su dawo Gidana ina maraba dasu". Ba ta tsaya jinshi ba ta shiga ciki ta dauko gyalenta tace da Mimi je ki wurin Yaya Aisha, yarinya ta mak'e kafada, Mancy bata da lokacin yi gardama ta fito a hargitse. Alhaji Abu yace "nima zanje" Umma tace "itama zata" haka Mancy ta shiga Motar Hajia Aisha Lema, su Alhaji Abu suna biye da motarsu a baya. Dama Abdulmajeed ya zagaya zance wurin Aisha, Abdulhafiz ya gaji yace zai dan kwanta so ba tare da sanin inda zasu ba Jawad yace bari ya kaisu, Abba yace ka bi bayan motar nan yabi Umurni yana tuk'i. "Abba ina zamu?" Abba yace "just drive". Bin bayan motar Mamyn Rafeeq yake, har ya ga Anguwar su Sanyin idaniyanshi ne, da niyyar in ya saukesu zaije ya ga Babynshi dama Allah Allah yake neman chance ya fito wayarta tun jiya kashe, duk ya damu. Sun zo Daidai Bencin Eskaley Nene tace "dan tsaya nan, kinga Bencin chan, chan suke zaman kashe wando, barin lek'a inga Zaid din na nan, ta lek'a tace "Kai Takwaran Zaidu bawan Allah na nan?" Master ya fara ganinta yace "Sai Nene". Aiko hankalinsu tero yayo kan Motoci Biyun nan. "Nene da me kika zo mana yau?" "da uwarku" nazo ta koma tace "baya nan, yana gida Muje Aisha" ita kam Mancy kallo daya ta ma Bencin Eskaley gabanta ya tarwatse wai Zaidunta ne ke rayuwa irin ta Mashaya, ta kasa yarda. Master yace "Wallahi Nene Solo zata mana yau, gata chan ta tafi ta kai ma Mankas, shegen ba bamu zai yi ba, ku mu bita". Nan fa Eskaley ya kulle shago suka biyan Motar Nene su hudu. ** Gabanta ya tsananta faduwa da ta hango gidan Alhaji Ali Zaki, duk abunda ya faru a shekarun baya suka dinga dawo mata kamar a lokacin abun ke faruwa. *** Yau Saturday, Mutanen Gidan sun tafi Daura Biki, Baba ma ya kaisu da kanshi, daga ita sai Uncle Hudu a gidan, Ya Zaid bata san ko yana daki ba, ta kira wayarshi bata shiga, Wani irin k'ishi takeji, amma bata son fita daga dakin, ta zabi tayi zamanta a daki hankalinta zaifi kwancia don har ga Allah bata son duk wani abu da zai hadata da Uncle Hudu. Ya fara wuce gona da iri, ita tsoronta kar ya mata wani mugun abun, kar ya dakusar mata da rayuwa, ya goga mata Fenti da ba zai taba goguwa ba. Saidai k'ishi takeji ba na wasa ba, har ta na ta shak'uwa, yanke hukunci tayi na tafia daukowa a kitchen ko ta diba a dispenser da ke parlo. Kamar barauniya haka tayi Sando har parlo tayi amfani da Cup din wurin diban ruwa. Ji tayi an mata wani irin chakulkuli a gefen cikinta wanda ya sakata sakin Ihu da k'arfi. Da sauri ya sa hannunshi a bakinta tare da rik'o k'ugunta. "Matsoraciya, meye abun Ihu" Gani irin rik'on da ya mata ya sa ta fashewa da kuka tana fadin "ka sakeni donAllah, bani so fa Uncle Hudu, donAllah sakeni" tana k'okarin kwace kanta shikuma yana sake rik'ota tare da tariyota jikinshi. ** Ya fito daga Dakinshi zai shiga ya ga Dalo kafin ya fita waje, ya ci karo da Nene da wasu mutanen da bai shaida ba, sai ‘yan Bencin Eskaley da mamaki yake binsu da kallo. Yace “Nene ta ya kika shigo da su Master? Meye kuka cika mana Gida”. Nene da bakinta ya dade a Bude tace “Takwaran Zaidu Bawan Allah, wannan wankan fa? Ina jallabiyar? Wa ya baka jamfa ka saka?”. Zaidu ya kalli Jikinshi yana murmusawa kafin yace wani abu master yace “yo ai Nene mun zata kece kika mishi kika mana solo, kwana uku kenan yana sa kayan nan”. Nene tace “Aifa kayan nan sun shiga uku, har sai sun fita hayyacinsu za a bar saka su”. Hajia Aisha Lema ta girgiza kai, ita Nene wai ta manta mai ya kawo su ne? Zata biye musu suna wasu maganganu. Jawad ya gane Zaid, Tsaf ya ganeshi, kallon kyama yake mishi. Mancy da ta gama karantar danta tsaf, duk ya fita hayyacinshi, ba yaron da ta bari bane shekaru 4 da suka wuce, mai makon yayi K’iba, sai ya rame yayi duhu, a k’azance. Baki ta cire ta kira sunanshi. “ZAID”. Inda ya ji kiran ya kalla, kallo daya ya mata ya shaidata. Baki na rawa yace “MANCYYY”.. **** Kasa kama kansa yayi, ya fara kokarin kai mata kiss a baki ta dinga kwacewa amma rikon da ya mata ba na wasa bane, ganin kiss din zai bata mai lokaci ga dama ya samu, kokari yake kawai ya cire mata zani, ya ko ci nasarar cire mata Zanin, tana kiciniyar guduwa ya daga hannu ya kamtseta da mari, ya sake marinta a gefe dayan, tuni ta sheme a kan kujera, ya sa guiwan shi ya danne ta, yahau kiciniyar cire belt dinshi, dogon wandon shi ya fadi, ta ga daga shi sai Boxers ya rage, hankalinta ya tashi matuka, duk wani k'arfin dake gareta ta tattara ta hado Kalmar "YaaaaYaaaaa". Duk wanda ya ji Ihun nan ya san ba na lafia bane,a sittin suka shige Parlorn har 'yan Bencin Eskaley, gani sukayi Hudu na niyyar haye Dalo da. Wani Tsalle Zaid yayi ya dira gaban Hudu. Mancy ta zube K'asa saboda gani take tata ta zo k'arshe. Umman Jawad tayi saurin zuwa gun Dalo ta rufeta, kwata kwata bata motsi da alamun ta suma. Zaid ya kai ma Hudu naushi yafi kala 10a baki lokaci guda. Nene kam ta shiga tsakaninsu tace kuje ku kai ta Asibiti ta juyo ga Hudu da yayi wik'i wik'i da ido charaf ta rik'e gaban Hudu tace "k'aikayi yake maka? Wallahi kaciya zan sake maka yanzu, gundule ka zanyi wallahi" Master cike da tasha yace "ga Aska Nene,danuwarka Kanwarmu ka danne?" Terro yace "yau sai ka bi uwarka Lahira". Nene cikin Muryar 'yan Daba tace "ku zo ku danne min shi". Kafin kace kobo yan bencin Eskaley sun yo kan Hudu. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa. [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉 BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI 2⃣7⃣ (HADARI) Ganin dai dagaske Nene ta sa an shimfide mata Hudu a k'asa zata yanke shi ya sa Alhaji Abu Ya tsawatar yace "ku bari donAllah" ya kalli Nene yace "Mama donAllah kiyi hakuri". Nene tace "bashi kwarto ba? Ai barin irinsu da mafitsara bala'i ne, irinsu ne masu fyade 'yan shekara 3, ka bari kawai na gilleshi". Alhaji Abu yace "aa mama kar ku yanke hukunci da kanku, ku bari Hukuma ta yi aiki". Nene tace "naci uwar Hukuma" Master cike da tasha yace "yo Baba ina mu ake kira da 'yan zaman banza Bata Gari? Marasa gata, mune mutanen banza, mune masu halin Akuyanci, to wallahi Baba ga mu nan dai, duk cikin mu ba shegen da aka taba kamawa wai ya danne wata, iskancin mu bai kai nan ba, mu dai barmu da shan Siga da World" Ya nuna Hudu da Hannu yace "amma don Uwarka kai da kake kallan mu a mak'askanta, in ka bi ta gaban mu ka 6ude mu da kasa da k'ura, kullum kanai mana kallon k'yama, ashe kaine dan akuya dan shegia". Terro ya dura mai wani irin zagin da kowa da ke gun sai da ya ji nauyin zagin "dan kaza kazanka k'anwarmu zaka danne?". Ya kaimai nushi a baki, kamar jira 'yan Bencin Eskaley suke suka rubduga mai suka dinga dukkan Hudu ko ta ina, jini ta baki ta hanci. Nene ta hau tafi, tace "ku ci Ubanshi wallahi, ku ci kutumar ubanshi". Alhaji Abu ya dinga ce ma su Terro su bari, suka k'i, ya je wurin Mankas da ke tsaye kamar gunki ya dafa shi yace "Zaid, donAllah ka musu magana, kar su kar shi". Zaid baya motsi. Jawad idonshi yayi ja alamun tashin hankali, yana tsugunne kusa da Mancy da Mamarshi da kan Dalo ke kanta, Mancy sai jijjigata take,Hajia Aisha Lema kuma tana ta mata firfita. Alhaji Abu Shamsu ya rasa abunyi, ya dafe kai ya dake juyawa ya tako gaban Nene yace "donAllah ki sa su bari, Mama in rai ya baci, hankali bai gushewa, in rai ya baci, hankali ke nemoshi, kiyi hakuri, yanzu in sun kashe shi, me kike tunanin zanyi faru? Sun kashe rai, ke da ke musu gata zaki iya cetansu baki daya a gidan yari?". Wani dan tunani Nene tayi kafin tace "kai ku kyaleshi". Ba su ji ta ba sai da tace "danuwarku ba ku jina? Nace ku cika shi ko?". K'yaleshi sukayi suna huci, Alhaji Abu yace "ku fesa mata ruwa". Jawad da dan sauri ya k'arasa gun dispenser ya bude ya dibo ruwa ya ba Mamar Rafeeq. Fesa ma Dalo tayi. A firgice ta farfafo, tana bude ido ta sauke su kan Mancy, a sittin ta zabura ta shige Jikin Zaid da ke chan gefen ta ruk'unkumeshi. Zaid ya rungumeta yana shafan bayanta, firgice Dalo take, jikinta be bar kakkarwa ba. "Yaya, Uncle Hudu ne". Zaid yace "Its Okay, he wont hurt you". "Yaya wata mai kama da Mancy". Zaid ya kalli Mancy ya kau da kai ga cigaba da lallashin Dalo. Nene ce ta rik'o hannun Dalo da Zaid ta tura cikin dakin Dalo, ta rik'o na Mancy ta turata itama dakin ta ja k'ofa ta rufe. Ta kalli Hudu da 'Yan Bencin Eskaley suka zagaye kamar a cage, ta kalli Alhaji Abu tace "sai ka kira police ko wallahi na barshi da su Eskaley". * Daidai da isowar Alhaji Ali Zaki kenan da Hajia Shafa da kuma Annah. 'Yan Parlorn suka bi da kallon Mamaki, basu gane kowa ba sai 'yan Bencin Eskaley, da mamaki suka kalli juna shi da matarshi. Idon Hajia Shafa ya sauka kan Nene da ta fara chakal chakal da baki kamar mai cin Cingam, haka take in balai da masifa na cinta, sai ta fara cin Imaginary chew gum. Hajia Shafa'atu bata kai ga magana ba ta ga wani sheme a k'asa kamar matattace yana fitar da jini ta baki ta hanci, ga ido ya kumbura, numfashi da k'yar yake fitarwa, kallonshi tayi sosai, hajinta ya kada, baki na rawa tace "Hudu?". Hudu da jin muryar yayarshi ya na son tattaro karfinshi ya tashi ya ji an take mishi hannu ya koma lakwaf. Hajia Shafa'atu ta k'araso gun shi da gudu tace "Hudu, me ya sameka? Uban wa ya tabaka?". Nene tace "Ubanki ne". Hajia Shafaatu ta fashe da kuka tace "Alhajina ba zan iya ba nidai ka sakeni, wannan matar bata bar bibiyanmu ba ko? Yanzu ta zo ta sa 'yan iska sun duka Hudu, wallahi ba zan yarda ba ka kira Police wallahi yanzu ya kwashe su duka". Nene ta daga hannu ta mareta tace "Barikin Sojoji zaa kaimu, nace a kaimu barikin sojoji, in baki bar kallona ba sai na tsokale miki ido, hatsabibiyar Mata, kai kuma sakarai hotiho soko, har yau asirin be bar kan ka ba? To kaji da kunnenka, wannan dan akuyan da ya gaji Akuyanci wurin Iyayenshi, shi muka kama dumudumu zai ma diyarka Sadiya Fyade, akan wanchan kujeran muka kamashi yana niyyan afka mata, da Alhaji ya kyaleni ai wallahi Kaciya zan sake mai". * Dalo da Zaid kallon Mancy sukeyi cikin Ido, ita kam Mancy ta kasa hada ido dasu, kanta a k'asa, ba ta san ta inda zata fara ba, lallai ita mai laifi ce. Zaid ne ya fara magana inda yake cewa "Kin gani ko Mancy? Kin ga abunda kika ja mana ko? Seconds 10 zamu k'ara rayuwar Dalo zata ruguje, wallahi da mun k'ara 10seconds da shikenan Hudu ya lalata ma Dalo Rayuwa, Mancy ba zan gaya miki abubuwan da suka faru ba a iya shekarun nan, amma Mancy baki kyauta ba da kika barmu a nan, musamman Dalo, da kin tafi da ita gabanki, Mancy 10secs fa zamu k'ara•" muryarshi ta karye. Mancy da Dalo suka sake fashewa da kuka. Mancy ta zube kan guiwowinta tana kuka tace "ku gafarceni 'ya'yana, hak'ik'a ni din mai laifi ce, na muku laifi gagarumi wanda ni a gani na Gata ne na muku, wallahi ba zanso kuyi Agolanci ba, a ganina duk bacin gidan Mahaifinku baku da inda ya fishi, balle ku ba yara bane, bansan na jefa rayuwarku a wani hali ba, ku yafe min don Girman Allah". Tsakanin Da da Mahaifi sai Allah, zuciyoyinsu ya tabu. Ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Dalo ta rungume Mancy kamar zata shige cikin cikinta tace "Mancy nayi Kewarki Sosai wallahi, i have missed you so much". Mancy itama ta rungumeta tana kuka tana "Ki yafe min Sadiya, ki yafe ma Mancy, a ganina ina yin abunda nake ganin shine daidai". Dalo tace "Mancy, wallahi bakiyi min komai ba, kewanki kawai nayi sosai, Mancy ki tafi dani". Gyada kai tayi tace "ba zan sake nisa da ku ba, aure da mutuwa kawai zai rabani da ku, wallahi daidai nake da Babanku yanzu, bai isa ya rabani da ku ba, bai isa ba wallahi, kafata kafarku". Zaid ya fashe da wani irin dariya mai hade da takaici da bak'inciki. A tare suka kalleshi. Mancy tace "Eh Zaid, k'afata, k'afarku". Zaid yace "k'afarki k'afar Sadiya, zan tabbatar da hakan, ko Baba bai isa ya hana ba, matarshi kuma ko da bak'ar Jaba take tsafi ba ta isa ta hana ba, zan tabbatar da hakan". Mancy ta kalli Zaid tace "Kai fa?". Yace "Ina zakije da Baligi kamar ni? Gidan Aurenki?". Mancy ta girgiza kai sai taji Zaid kamar Magana yake gaya mata tace "Aa Zaid, kuskure nayi a baya, zubar da ku shine babban kuskuren da na tafka, amma yanzu ba zan sake wanen kuren ba, da ku zan tafi, tuni maigidana yake son hakan". Zaid yace "its too late Mancy, zan Zauna a Gidan Ubana, zan zauna har sai ya dawo hayyacinshi, zan zauna ya dawo hankalinshi yace Zaid Allah ya maka Albarka, in hakan bai faru ba, zan mutu a Gidan Ubana, wata k'ila in ya ga Gawata ya mun Addua". Bata gane mai yake cewa ba tace "ZAIDD". Share mata hawaye yayi yace "Maigidanki na jira, ki tafi Mancy, ga Dalo nan ki tafi da ita". Dalo ta koma gun Zaid ta rungumeshi tace "ba zakaje ba? Ba zanje ba nima". Zaid ya murmusa yace "muje Parlor. * "Kutumar Uba ba Kaciya ba, Hudun zaku lak'a ma Sharri? Saboda tsana?". Mancy ta tako gaban Hajia Shafa'atu. Ganin hakan ya sa Nene yin shiru. Hajia Shafa'atu tace "ke kuma wacece?". Mancy ta murmusa tace "Hajia Shafa'atu, in har kin dauki Alhakin 'ya'yana Allah ya isar musu". Dan baya tayi Hajia Shafa tayi, gabanta ya fadi, tsoro da tashin hankali suka bayyana, mamaki take, anya itace? Ta ga alamun kudi da kwanciyar hankali a tattare da ita, tayi k'iba ta kara kyau, ta murje abunta, baki na rawa tace "Maryama, kece haka?". Murmushi kawai Mancy tayi. Nene tayi charaf tace "kina mamaki ne? Ai Allah ba ruwanshi, duk zakaran da Allah ya nufa da chara, ko ana muzuru Maryaman ce dai da kika raba da Sullutun Mijinki, tduba chan kinga wanchan Alhajin, shine Mijinta, ya fi Mijinki dattako, ya fi Mijinki kudi da kyau, kalleshi chan Fulanin usuli, dan babban Gida dan Anguwan Alk'ali, kinga ko sawun giwa ya badda na rakumi, ruwa ba tsaran kwando bane, kuma bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane". Nan da nan bakin ciki, k'yashi, hassada suka bayyana a fuskanta. Alhaji Ali Zaki ba abunda yakeyi sai Kallan Maryama, bakinshi na san magana, amma bai san mai zai ce ba, duk yadda yake so ya furta wani abu ya kasa. Master yace "ya zamuyi da dan akuyan nan?". Mancy ta juya ta kalli Hudu, ta ga yanda akayi jinajina dashi, tace "ku kyaleshi, mun gama da nan kuma". Hajia Shafa'atu ta fashe da kuka ta dinga jijjiga Alhaji Ali "yanzu kana gani a shigo cikin Gidanka a ci man mutunci? A wulakantani gaban yan Unguwa, a lakafa ma k'anena sharri, a mishi dukkan yan wanki, a ci mana fuska, kuma kana tsaye ka kasa cewa komai?". Kamar wanda aka jona da Electric Shock ya fara bambamai, "Iskancin banza, uban wa yace ku shigo min Gida? Ke tsohuwar nan ba na hanaki zuwa min Gida ba? Yau sai na kori Maigadin nan". Nene tace "kai arr dallah yi mana shiru, sai wani haushin kare kake mana a nan". Alhaji Abu Shamsu ya gyara Murya yace "Alhaji Ali Zaki, donAllah zauna". Baba ya kalli Abba yana jiran umurni daga gun Hajjaju. Nene tace "kai dallah zauna". Baba ya bi umurnin Nene ya zauna a daddare ba tare da ya lura da mugun kallon da Haj Shafa'atu ke jefanshi dashi. Abba yace "Hajiya zauna, magana zamuyi". Cike da rashin kunya tace "ba zan taba zama da ku ba, ai kunne ke ji, yi maganarka". Alhaji Abu Shamsu yace "hakane. Alhaji Ali Zaki, sunana Alhaji Abu Shamsu, nine Mijin tsohuwar Matarka Maryama, inda da yaram 3 da baiwar Allahn chan lokacin da na auri Maryama, tun a lokacin na buk'aci rik'on Zaid da Sadiya ya dawo guna, ta nuna min da Aa tafison Yaranta su tashi wurin Mahaifinsu, ban ja ba, to yau munzo ganinsu, muka ga k'anin matarka na niyar afka mata, Allah ne ya tsareta, to ganin hakan ya sa Thank na yanke hukuncin Tafiya da Zaid da Sadiya Gidana, ko Mancynsu na so ko bata So, daga ranar da na auri Maryama, 'ya'yanta suka zama nawa". Burinta ne Zaid da Dalo su bar mata gidan tunda dadewa, maimakon tayi murna da jin cewa zasu bar mata gidan sai ta tsinci kanta cikin wani matsanancin bakinciki. Barin su nan ya zama jin dadinsu ko? Zai zama sun fi Annah jindadi? Ranta ya dinga tuk'ik'i,har yanzu tana Kishin Maryama. Tace "yanzu Alhaji yarda zakayi a tafi da yaranka? Zaa rabani da su, duk sabo da shakuwan da mukayi, barin ma Dalo da muke kwana muke tashi tare, ya zaayi a rabani dasu bayan na fi kowa sansu?" Dalo da kanta ke kan kafadun Zaid ta dago ta kalleta jin furuncin nata wani iri, wannan ko k'arya bata iya ba ma. Kamar an jonashi "ba inda zaku tafin min da Yara, ba inda zasu, ku tashi ku fitar mina Gida". Alhaji Abu yace "da su zamu tafi, in kuma zaka bamu matsala sai muje gaban hukuma". Shafaa tace "Hukumar da zaka saye suyi abunda kake so?". Alhaji Abu yace "Sarkin Katsina fa? Ko shima sayeshi zanyi? Ni na ma fi so a je gaban Sarkin, na bashi labarin komai, Ya mallaka minsu, kinga k'aninki sai a yanke mishi Hukunci daidai da wanda ya aikata". Bubutai ta fara na borin kunya. Alhaji Shamsu ya kalli Iyalenshi yace "ku wuce mu tafi". Jawad ya saba Mimi a jiki, Umma ta fita, Abba yace "Zaid ku mu tafi" ba gardama Zaid ya ja hannun Dalo da ke ta kakkarwa ya rufa ma Umma baya, Mancy ta rufa mai baya, kafin Alhaji Abu Yace ma Nene "Mun tafi Mama". Nene baki har wuya tace "Sai munyi magana, Allah shi biyaka" Ya amsa da Amin ya sa hannu ya ciro dubu 3 ya ba 'yan Bencin Eskalay. Master ya sa hannu zai karba Nene ta fizge tace "yi tafianka Alhaji, sigari zasu sha". "Wallahi Nene ba shi zamu sha ba". Alhaji yayi gaba abunshi yana murmushi, shi bai taba gani tsohuwa irin Nene ba. Nene ta galla ma su Harara ta mika musu kudin tace "Shiryayyu, ku raba, ban yafe ba kuka sha Sigari". Suka hau shewan sai "Nene". Sun manta da wasu halittu bayansu a gurin, suka fice suna murna. Nene ta galla ma Shafa ta Mijinta Harara, tace ma Aisha Lema "mu tafi Maminsu" kamar jiran umurni take ta fita suna fita Hajia Shafa'atu ta bi bayansu ta rufe k'ofar Parlo ta saka Ihu. Me ke faruwa ne? Duniyarta ta fara juya mata, Mancy ta zarce tunaninta, ta ya akayi haka, zuciyarta wani tuk'ukin bakinciki yake,me zatayi Ta huce, wani hutu da ta gani jikin Mancy ranta na sosuwa matuk'a, me zatayi? Me zatayi? Hudu ya rarrafo gun kafarta yace "Aunty wallahi karya suke min" haushi ya bata kamar ta halbeshi, ita ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta bai wuce Jin dadin da ta gani jikin Mancy ba, tsallake Hudu tayi ta shige daki tare da rufo kofar. Annah ta shigewarta Daki itama tana jin zafin sharrin da aka ma Uncle Hudu. Alhaji Ali Zaki zaune kan three seater yana kallon Hudu, so yake ya tashi ya shak'eshi, amma bai san mai ke danneshi ba, tsanar Hudu ke rufeshi, amma ba zai iya komai a kai ba, ganin mugun kallon da Alhaji Ali ke mai ne ya sashi mikewa sum sum yana jan kafa ya shige daki. A Babban Parlorn Gidan suke zaune. Alhaji Abu yace "Ni zan rik'eku amana, duk abunda zan ma dan cikina inshaAllahu zan muku, baku da matsala dani, na tabbatar ba zaku samu matsala daga sauran mutanen Gidan ba". Dalo dai na chan k'udundune, har yanzu ba ta dawo daidai ba, ta kan firgita lokaci zuwa lokaci, kuma a tsorace take. Mancy sai zabga fara'a take jin furucin Mijinta a kan 'yayanta. "Wannan shine Yaya Abdulhafiz sai AbdulMajeed sai Jawad sai Ummanku ga ta nan". Zaid ya murmusa yace "Alhaji". Alhaji Abu yace "Abba daii". Zaid ya sake murmusawan yace "Abba,mungode Allah ya biyaka da Aljannah, mungode kwarai, amma ni gaskia zan tsaya nan Katsina". Mancy tace "Zaid.." Zaid yace "Kiyi hakuri Mancy, amma ba zan iya binku Abuja ba". Mancy zatayi magana Alhaji ya dakatar da ita ta hanyan daga mata Hannu. Yace "Zaid, kwanakin baya, da Allah da Annabi kake hadawa a tafi da kai Abuja, yanzu kuka kace baka so? Mai ya sa?". Zaid yace "Abba, Mahaifina yana zaune da wata Hatsabibiyar Mace, ba zata taba barinshi ya dawo hayyacinshi ba, zata cigaba da cutanshi, ina so na tsaya a kusa dashi, tafianmu na nufin mun rabu dashi kenan, baya da wani hope din dawowa daidai, ni na san Akwai Son mu a wani Sashe na zuciyarshi, ba duka ta mutu ba, zan jira har sai wannan shashen ya mamaya sauran sassunka, zan jira har sai ya kalleni da so da kauna, ba zan bar Baba ba gaskia, na san yana nan a makale". Duk sai da suka tausaya mai Alhaji Abu yace Allah ya maka Albarka, Allah ya dawo muku da Mahaifinku daidai, ya shiga tsakaninshi da muguwa azzalumar Mata". Suka amsa da Amin. Yace "Oya kowa yaje ya kwanta gobe da safe zamu wuce" Suka amsa mai. Umma tace AbdulMajeed ya kai mata Mimi dakinta, yau tare zasu kwana. Abba yace "Zaid sai ka bidaya daga cikin yanuwanka gasu nan". Umma tace "ai mai raba Zaid da Mancy yau sai Allah". Sukayi daria, hakan kuwa akayi Zaid da Dalo da Mancy daku daya suka shige suna firan yaushe gamo. Har Dalo tayi bacci akan cinyan Mancy Zaid ya ba Mancy rayuwarshi bayan rabuwarsu kaf Sosai tayi kuka da nadama, ta kuma yi ma Shafa'atu Allah ya isa yafi cikon kwando. Jawad ya so ganina Labiba amma ta mishi karya wai tana Dutsinma. Be ji dadi ba don sosai ya so su hadu ya tamvayeta kan chanjinda ta mishi cikin kwanakin nan. W A S H E G A R I Bakinciki da Hassada basu barta tayi bacci ba. yanda taga rana haka taga dare. Ta kira numbern Er Rabi wayarta Kashe. Gari na wayewa ta isa Gidan Er Rabi, sai dai Maigadi ya tabbatar mata da cewa Er Rabi tayi tafiya zuwa Agadez, gobe zata dawo. Kamar tayi ihu don haushi, meyasa Er Rabi bata gaya mata irin tafiyar nan? Yanzu ya zatayi? Wa zai share mata kukanta? Haka ta koma Gida rai a bace, bari Er Rabin ta dawo, dole ta dinga barin mata kayan aiki incase of Emergency. * Gabaki dayansu suka tafi Gidan Daddy Usman don duba jikinshi da yi musu bankwana Jikin da sauki sosai. Suka musu sallama Sukaje Anguwan Alkali family house. Harda Zaid aka yi zagayen. Daidai Tollgate na Farewell from katsina suka tsaya, duk suka firfito. Alhaji Shamsu ya ba Zaid numbernshi da na Abdulhafiz yace "duk abunda kake so ka kirani ko ka kira yayanka". Zaid ya amsa mishi da "to" AbdulMajid sukayi Musabaha yace "take care of yourself bro". Zaid yace "i surely will big bro". Sukayi daria Zaid da Jawad dai Basar da juna sukeyi. Dalo kam tayi kukan rabuwa da yayanta. Mancy ta ja Gefe tace "Zaid DonAllah kar ka sake shan World ne ko meye kuke ce mishi" Yace "Mancy na bari". Tace "Zan shirya yanda zaka koma School, you need to start afresh". Wani School? Shi da ke daf da mutuwa? Shi yasan ciwo na cinshi ta ciki, amma me zai ce? Murmushi kawai ya mata". Har saida ya bar ganin Motarsu ya tsaida Machine don tafia Gida. Lokacin da Zaid ya shigo Gida ya yi mamakin ganin Babanshi zaune A bukka shi kadai, har zai wuce ya dai karasa gunshi ya zauna, idon Baban ya kalla yace "Ina kwana?". Baba ya lumshe ido ya bude yace "Baka bisu ba?". Zaid yace "ba zan tafi na barka ba Baba" Baba zaiyi magana yaji harshenshi yayi nauyi. Zaid yace "Na san ka nan, fight it, overcome it". Ya tashi ya shige cikin Gida, Baban ya bi bayanshi da kallo. Kamar Gadinshi take ta window, ta shiga da Asubar fari baya nan, dakin ma baiyi kama da wanda aka kwana ba, yana shiga daki ta faki idanuwa ta shiga. Da mamaki yace "Beebs?". Tace "Me ya faru da kai? Ina kaje jiya? Me yasa wayarka kashe? Mankas kayi Jiya ko?".. Murmushi yayi yace "Good Morning Sunshine, i love you". Hararshi tayi tace "Start Talking". Yace "Abubuwa da yawa sun faru, Mancy Was here jiya, tazo ta tafi damu". Murna Labiba harda tafi tace "Finally Mancynmu tazo garemu, Dalo must be happy, ta na ina yanzu?". Zaid yace "sun wuce Abuja". Tace "da wuri haka?". Yace "Eh sunzo dubiya ne dama". Ta dan rage girman idanuwanta tace "kai meyasa baka bisu ba? Baka son missing dina ai?" Yace "ashe kingane + ba zanje agolanci gidansu saurayinki ba". Tace "ban gane ba". Yace " Mancy na auran Babansu Jay ne ko Kay". Zaro ido Labiba tayi "kana nufin Mancy ma auran Babansu Jay?". Hararata yayi yace "so kike na maimaita? To ba zan ba". Tace "Wow, Its a small world indeed, jiya ya kirani wai yana Kt nace mishi naje Dustin Ma". Zaid ya kashe mata ido yace "you did well". "Ke, yau ba Sunday ba? Baban Amira ba ya nanan ba? Sai ya nemeki?". Tace "eh fa, ba zai ganni ba". Suna dan fira sai ga Yasmin ta kira. Sai da ya kalli Labiba ya ga ta tsura mishi ido kafin ya Amsa tare da sa Speaker. Muryarta ya cika dakin "Zaidun Bibbs". Labiba ta sake wani murmushi jin furuncin Yasmin. Zaid yace "K'amshi, k'amshi yana tashi". Tayi 'yar daria tace "kana lafia?". Yace "Lafia lau, Dama yanzu nake shirin kiranki". Tace "ta samu ne?". Yace "Albishirinki" Tace "Goro" Yace "Mancy came for us, tazo har ta tafi da Dalo". Yana jin sautin dariayarta mai dauke da murna sahihhiya. Tace "Alhamdulilah, naji dadi, Dalo na jikin Mancy right now am so sure about it". Yayi daria tace "i need details daga farko". Yace "i will fill you in, ga wata ku gaisa". Labiba ta girgiza mai kai, ya gyada mata kai alamun tayi magana. Labiba tace "Assalam Alaikum" Wani shewa taji Yasmin tayi tana daria tace "waalaikum salam Beeeebsss dinmu oh my God kece?". Tace "Eh Aunty Yas nice ina kwana ya aiki?". Yasmin tace "Lafia lau, ya School? Ya kike ya su Yaya Muhammadu?". Tace "kowa lafia lau, yaushe zaki zo?". Tace "Yau nike call, gobe ma haka inshaAllahu Jibi Tuesday kenan, zan zo na ganki, yauwa akwai wata colleague dita da ta kawo wasu Malaysian Shoes, size nawa kike sawa? In dauko miki random colors". Kunya ya cika Labiba tace "ki barsu". Yasmin tace "'yar kauye, come on tell me size dinki". Labiba cike da kunya tace "37-38". Yasmin tace "Oh oh, na tuna fa our biebbs is a small person hahaha, to inshaAllah zan dawo miki dasu jibi kinji?". Labiba tace "Nagode Aunty Yasmin". Yasmin tace "abunda zakiyi kawai ki kula min da Zaid sosai, love him endlessly, take good care of him, and kiyi fushi in ya sha Sigari ko world". Labiba da Zaid suka kalli Juna, idon Zaid ya cika sosai da ruwa, ya kawar da kanshi, har yanzu yana jin Yasmin a ranshi sosai, soyayyar da take mishi mai tsafta ce, ita burinta kawai Zaid ya samu Farinciki". Sukaji muryarta tana cewa "Ohh, bibbs, kina gabanshi ko? Kar ya ji sirrin mu, ki karbi numebrna donAllah ki min flashing zan kiraki zuwa anjima" Labiba tace "Tou Aunty Yas, zan karba". Zaid yace "Me ake ce mata?". Yasmin tace "ina ruwanka ba sai ka ji ba". Yayi daria yace "kun fi kusa". Labiba ta mishi alama da zata tafi. Ya daga mata hannu tare da muting Yasmin na two seconds yace "I love you". Labiba ta amsa mishi ta fita ta fada gidansu da sauri. Zaid suka cigaba da waya da Yasmin. Har ya bata labarin Hudu da duk abunda ya faru Jikinta rawa yake tayi tana Tsine ma Hudu, wallahi da kun kaishi Police station" Yace "Mancy tace a kyaleshi, tunda Allah be bashi nasara a kanta ba". Yasmin tayi ta fada, kafin tace "kai wallahi all needs to stop, bari dai na zo Katsina Jibi InshaAllah" Murmushi yayi yace "Allah ya kawo ki K'amshi k'amshi". Sunyi fira fiye da 1 hr kafin sukayi hanging. Cikin Gida ya shiga don hado breakfast. Yana kallon Shafa'atu na ta sintiri. Tace "Dan Makaho baku tafi ba? Amma na ji dadi ina Dalo?". Mugun Harara ya zabga mata ya shige kitchen. * Bari ta shiga ta gaida Yayanta da Aunty Asey. Ta shiga da Sallama, ba wanda ya iya amsa mata, ganinsu tayi a kafe kamar an kafasu, ba mai iya motsi sai dai kallo daya zaka musu ka san cewa ransu a bace yake. Labiba tace "Yaya lafia? Aunty Aseey meya faru?". Babu wanda ya amsa mata sai chn yace "Labiba, Zauna". Jin muryarshi tayi ba wasa ta zauna kan kujerar da ke kallon Gadon da suke. Yace "Yanzu Labiba, tsakaninki da Allah, mai ya kaiki dakin Dan Makaho?". Ta dan tsorata amma sai tace "Yaya, wallahi tun jiya nake ta kiranshi wayarshi a kashe, kuma banji duriyarshi ba, shine na je duba shi naji ko lafia ashe mamarshi ce tazo jiyan". Ba wannan yake son ji ba. Yace "dama chan kina zuwa dakinshi?" Kai ta saddar k'asa tace "Eh Yaya". Yace "Wallahi Labiba kin bani mamaki, kin ban mamaki matuk'a banji dadi ba, Labiba da na ga kin fito dakin dan makaho wallahi sai da zuciyata ta tsaya, wai kanwata da na fi so a rayuwa ta fito daga dakin Namijin da ba muharamminta ba, Labiba me kike so ki zama ne wai? Me kike maida kanki? Ba kya tsoron ya miki wani mugun abun?". Da sauri ta giirgiza kai tace "aa yaya ba abinda zai min, na yarda dashi, ba zai min komai ba ba haka yake ba". Baban Amira a kausashe yace "Labibaa, kar na sake ganinki kin shiga dakinshi, Labiba kar na kuma jin an ganki da DanMakaho, Labiba ki fita idona, na gaya miki sadakinki na gurin Abbanki, shekarunki 18 ke ba yarinya bace, Labiba kar ki yarda in sa miki ido a gidan nan". Labiba ta sauka kan guiwowinta tace "Yaya kayi hakuri donAllah, ka yafe min, amma ni wallahi ina son dan Makaho Yaya, shi nake son aure, ka san labarinshi, danMakaho abun tausayi ne". Ya sausauta murya yace "kinsan me kike cewa? So fa kika ce? Aure? Tab, Tausayinshi kike na tabbata, ki rufa ma kanki Asiri, banso mu bata dake Labiba". Labiba tace "kayi hakuri Yayana Babana, inshaAllah ba za ka sake ganina a dakinshi ba, kayi min hakuri, ba zan kara ba, Aunty ki ba Yaya hakuri, ba zan sake ba". Ta tashi ta fita daga dakin. Suka bita da kallon tausayi, kamar ba a hayyacinta take ba, lokaci daya ta zama wata zararrara. "Ta na Sonshi" inji Aunty Aseey. "Wani irin so" Aunty Aseey tayi murmushi tace "Baban Amira So gaskia ne". Yayi shiru yace "ya zanyi? Kar Labiba ta bamu kunya". Aunty Aseey tace "donAllah kayi kokari dai ka rufe Wurin chan". Yace "Aseey Bulo tsada , wurin chan zai ci Bulo 50 zuwa 60". Tace "ko zaka ma Alhaji Zaki magana, tunda ba bayan yake zuwa ba na tabbata ya manta da tuni ya gyara". Yace "gaskia ba zan mishi magana ba, kwanaki bakiji me yace ba". Yanzu dai barinyi buga buga na ga zan iya siyo Langa Langan nan a rufe kafin na samu kudin Blocks, ya fita ta mishi fatan dawowa Lafia. Aunty Aseey ta shiga gun Labiba ta ganta zaune ta na kuka. Aunty aseey ta dafata tace "Labiba". Labiba ta dago kanta ta kalleta. Aunty Aseey tace "Me zakiyi da dan shaye-shaye?". Da sauri ta share hawayenta tace "ni na san me zanyi dashi, Sonshi nike, Sonshi nake domin Allah Aunty Asiyah, Allah ka sa ya aureni, Allah ka sa in zama matar ZAID ALI ZAKI". Da tsananin Mamaki take kallon Labiba, tafi zaton wani abu ya tabeta a k'wak'walwa. ** Ta na zaune ta ga Message din Zaid, numbern Yasmin ya turo mata, kiranta tayi. Yasmin na jinta ta kashe ta sake kiranta, sun dade suna waya. Kafin ta kashe ta kwanta don yin bacci kafin Azahar. * "Hello, gani k'ofar gida" Hargowanta yaji "toufa, ba kuje Habujan ba? Sai yaushe?". Zaid yace "donAllah nidai ina waje". Baa yi minti 3 ba sai gata ta fito ko mayafi babu. "Danubanka baka daina kirana kace kana waje, budurwarka ce ni? Zance kazo guna?". Zaid ya harareta "wallahi zan danneki na dura miki World". Harararshi tayi tare da kawo hannu kusa dashi, da ba dan ya gota ba da ta mareshi "Ubanka zaka dura min ba wall ba". "Gaya man, kun fasa zuwa Habujan ne?". Yace "sun tafi fa, suna hanya". Tace "toufa, kai ya bakaje ba". Yace "ni Nene? Ina zani? Babba dani, ni ina nan Gidan Babana" Ta harareshi "ka zauna nan matar uba ta cigaba da gasa ma aya a hannu". Yace "yo ai Nene ko da chan bata gasa min Aya a Hannu ba". Tace "Ina dan shegiyan nan, kanenta, ai da Alhaji ya barni sai na gilleshi, na gunduleshi". Sai yanzu abun ya fado mishi yace "wai da an barki sai ki yankeshi?". Tace "Chab, takwaran Zaidu Bawan Allah har yau baka sanni ba, tsaf zan yankeshi billahilazi". Zaid yace "Ni Yunwa nikeji Nene". Tace "aiko yanzu na jefa Danwake, bakaji dadin da yayi ba". Bata fuska yayi yace "Danwake kukayi?". Tace "Kai wannan abun sukayi Macaroni, ban fa ci, shine fa na jefa danwaken". Yace "Ni Macaroni zanci" Ta bata fuska tace "Jibeka uban yan iyayi, wanda iyakan ka Nigeria, ko iyaport baka taba zuwa ba, ka tsaya feleke, to jikata Nasiba na chan Ingila tana bina na aika masu da Garin danwake". Zaid ya girgiza kai yace "Zaki ban Abincin ko ba zaki bani ba". Kallon Sama da kasa ta mishi tace "Zan baka, Ubana, Mamman, Macaroni ko? Jira na zubo ma, kar ka juyan baya na shiga duniya, naga sai wani kallo kake man kamar zaka zagar min Uwa". Da hannu biyu ya dafe kai yana Nadamar duk abunda ya sashi zuwa Gidan Lema Gun Nene. * Ta tashi bacci, ta fito yin Alwalar Azahar ta ga Gidan duk Langa Langa, an rufesu, ta san aikin Ya Muhammad ne, girgiza kai kawai tayi ta shiga Toilet. Zaid ma ya sha mamakin ganin an katange Gidan da langa langa, haka kurum sai ya ji ba dadi, amma ya zasuyi?. Da Laasar suka hadu a Masallacin Bakin Titi. Gaishe shi yayi ya amsa ba yabo na fallasa. Yace “DanMakaho, meke tsakaninka da Labiba? Ka gaya min gaskia tsakaninka da Allah”. Zaid ya dan murji Idonshi yace “Yaya Sonta nikeyi, kuma ina son Aurenta”. Baban Amira yace “Ashe sonta kake? Dan Makaho kayi nauyin baki, akwai wani mai Sonta, sunje chan Gida Edo, an bashi Labiba, karshen magana ma, Sadakin Labiba na hannun Babanta”. Gaban Zaid ya fadi, yace “Yaya, na san ba zaka so tarayyata da Labiba ba, amma dagaske nake sonta, kuma wallahi na bar shan komai, har sigari, donAllah kar ka raba ni da ita Yaya”. Tausayi ya bashi yace “kayi hakuro Zaid, wallahi dagaske nake, an bayar da Labiba, wallahi sadaki naira dubu 50 na gun Baba, daurin Auren cikin kwana 40 da wani abu, wallahi kaji na rantse ma”. Jiri ya ji yake dibanshi sosai, sai da Baban Amira ya tallafo shi, kwacewa yayi yayihanyan Gida, sauri sauri gudu gudu. Hankalinshi in yayi dubu ya tashi. Gadonshi ya fada, zuciyarshi wata irin zafi take. Wayarshi yayi ringing, ‘yar halak ce, ya dauka. “Hello Soulmate”. Da kyar ya iya cewa “Bibbs, meyasa ba ki fada min you are engaged ba”. Gabanta ya dan fadi tace “Inji wa?”. Yace “ba Inji wa ba, gaya min dagaske ne?” Tace “Eh dagaske ne amma..” Bai tsaya jin mai zatace ba ya katseta yace “babu amma, abunda nake sonji kenan, ina miki fatan Alheri, Allah ya sa Alheri ya baki dauwammen Farinciki a rayuwa”. K’it ya kashe wayar. Hankalin Labiba in yayi dubu to ya tashi, ta kira wayar kashe, da sauri ta tashi ta fita, karo sukaci da Baban Amira, ta dan ja birki, me ta tuna me ta tuna ta koma cikin daki. Shikam Zaid Zuciyarshi wani irin tafasa take. Mai zaiyi? Ji yayi kamar zata tarwatse, abu daya ya zo mishi, ba tare da wani dogon tunani ba, ya janyota daga karkashin Gado, sai da ya hadata sosai kafin ya kyasta, shegiar ce World, abunka da an dade ba a hadu ba, ya zuketa kamar ba gobe, yama gamawa ya hada da sigari, nan inda yake yayi Mankasss sai bacci. Baban Amira zaune yayi a kan kujera tsakar Gida Labibata fito, kamar ba abunda ya faru tace “Yaaya, Babansu Aisha yayi Accident, ina so naje na duboshi”. Yarinyan nan wayau take so ta mishi, kila wani wuri zata hadu da Zaid. Yace “Muje na rakaki, nima sai na duboshi”. Mamaki ya kamata, meye haka? Don dai kar ta fita ita kadai? Tace “to muje”. Haka suka fita, ya tsaida musu Napep, suka shiga tare sukaje Gidansu Aisha, tace da Yayanta suke, aka mishi iso, ya shiga ya gaidasu ya musu Allah kyauta gaba, ya tusa keyar Labiba suka koma Gida. Ba abunda ke fitar dashi sai Sallah Maghrib da Ishai, har yanzu wayar Zaid kashe. A B U J A 7:45pm Masu Aiki sun musu setting Abinci a kan Table, kowa ya samu guri ya zauna, banda Dalo da tace ta k'oshi. Alhaji Abu yace "Ina Sadiya?". Mancy tace "wai bata jin yunwa". Alhaji Abu yace "yo me taci? Tun lemun da kowa ya sha a Mota? Ban yarda ba". Ya kalli Jawad da shine k'arshen shigowa yace “Jawad, je kira man Sadiya”. Mik’ewa yayi ya tafi dakin Mancy. Tana zaune ta tana Waya da Yasmin ya shigo da Sallama. “Aunty Yas, ina zuwa”. Ta kashe wayar ta amsa Sallamarshi. Zama yayi kan kujera yana kallonta. Yace “me kika ci da zakice bakiji Yunwa”. Murmushi tayi tace “dagaske bana jin Yunwa”. “Oya tashi muje dining table ke kadai muke jira” Bambarak’wai taji abun, bata saba ba, ita yau ake jira a dining? Tafi sabawa da zaman Daki. Muryarshi taji “Sadyyy”. “Tashi mu tafi, stand up” Kallonshi kawai tayi, ya tisa k’eyarta suka fita. Gabaki daya ‘yan table din suka juyo suna kallonsu, sai da ta zauna Abba yace “to Bismillahnmu, Sadiya, kiyi serving dinmu”. Ta tashi a tsanake ta shiga zuzzuba ma kowa abinci. K A T S I N A Abun ya tsaya mishi a rai shiyasa ya kasa bacci. Karfe 11:30 ya ji ana bude kofar dayan dakin. Tashi yayi ya leka, yaga Labiba ta fito tana Sanda kamar me shirin shiga sata. Mamaki abun ya bashi. Ya bita da ido yaga ta nufa Hanyar Gidan Ali Zaki, wurin Langa Langan, ido ya zuba mata yaga gudun ruwanta, ta ina zata bi?. Gani yayi ta fara girgiza langa langa tana daddako kusoshi da suka danneshi. Baki Baban Amira ya bude. Aunty Aseey ta tashi tace “lafia?” Bai bata amsa ba, ta tashi tazo bakin Window, baki ta bude da mamaki. “Labiba?”. Baban Amira yace “Shhh, tsaya muga mai take shirin yi”. A hankali suka bude kofa suka bi bayanta a hankali, ta langa langa suke kallonta tana gaban dakin Zaid tana magiyar ya bude mata. “DonAllah Soulmate ka bude min, zuciyana zafi, hankalina ya kasa kwancia, donAllah ka taimaka ka bude min na maka bayani”. Kusan minti 20 tana mai magiya, sauri duk sun bi kafafunta. Dabara tazo mata ta leka wurin ramin jikin kofar ta hangoshi sheme kan gado yayi baje baje. Ta dan yi daria tace “au ashe bacci yakeyi, zan dawo gobe i love you”. Baban Amira ya kalli Asiya suka jinjina kai, a hankali suka koma daki, suna kallonta ta shigo, ta gyara langa langan, harda daukan dutse ta bubbuga wurin kusa, ko tsoro batayi, ta lallaba ta shige daki. Ai mamaki kashe su yayi, Aunty Aseey dai ta kwanta ta barshi zaune. Jikinshi sanyi Yayi, Labiba tayi nisa haka bata jin kira, ya santa, kafiya gareta, in ba rabata yayi da garin ba, ba zasu rabu da junansu ba, yanke hukunci maidata Gida zaiyi Gobe InshaAllah. Da Asuba ya gaya ma matarshi shawarar da ya yanke, bata ji dadi ba amma wannan ce hanya mai bullewa Baban Amira ya sameta kan dardumarta a dakinta, ta gaishe shi, yace “Labiba, tashi ki hada kaya, Edo zamu tafi”. Tace “Yaya Lafiya? Wani abun ya faru?”. Yace “Eh to ina jin wani abu ya faru, amma sun ki gaya min, kuma na san in na ce musu zamuzo Abba zai hana, gwara muje kawai mu gani”. Gabanta ya fadi tace “Mami ce ko Yaya?” Ya girgiza kai yace “aa ba ita bace”. Wayarta ta wawuro, ya fizge ya jefata Aljihu yace “na gaya miki banso su san zamuzo, in ba zaki tafi ba in yi tafiya ta”. Da sauri ta tashi tace “Yaya wallahi ba zan iya zama ba, hankalina yayi Gida kuma muje”. Yace “kiyi sauri kiyi wanka”. Tace “Aa Yaya, mu tafi kawai, ka siya min Bread a Tasha”. Baya son ta chanza raayinta, yace hado kayanki, tace “Akwatin a shirye yake, jiya na shiryashi”. Yace “to mu tafi” Yara na Bacci, Aunty Aseey tana ta hawaye, hawayen rabuwa da Labiba, sosai take son Labiba, bata so rabuwa da ita ta wannan hanyar ba. Ganin Aunty Aseey na kuka, ya sa jikin Labiba yin sanyi sosai, ta rungumeta itama tana hawayen tace “Aunty Aseey inshaAllah bakomai, ki bar kuka, Yaya mu tafi da ita”. Yace “Labiba ga yara, ba kudi sosai hannuna, kudin dawowa ma sai Abba ya bamu”. Ta share mata hawaye tace “Ba zamu dade ba kinji Aunty Aseey?”. Har bakin Kofa ta rakasu, suna fita bakin Titi suka samu Express guda biya. Ya tsaida su ka tafi Tashar KTSA don hawa motar Suleja, kasancewar babau Motar Edo daga Katsina, daga Suleja zasu hau Motar Edo. Allah ya tsare Hanya. * Wurin karfe 1 na rana ErRabi ta kira kawarta tace mata ta dawo da Asuba, ance mata tazo. Tace “gata nan zuwa yanzu yanzu akwai matsala”. Aiko suna gama wayar ta ciri gyale ta fita ko Annah bata gaya ma fitarta ba. * Garin Kankia yayi dadi sosai sakamakon yayyafin da ake ta yayyafawa mai dan k’arfi, a gajiye ta dawo Call Room ta zauna, ta cire wannan takalma irin ta likitoci tana matsa k’afarta da wuyanta, wani doctor da suke cema Chief ya na mata daria “You look tired doc?”. Tayi daria tace “Chief i am so exhausted Allah, i want to go home today but i cant drive, but first thing in the morning tomorrow InshaAllah”. Ba ta ji mai Chief yace ba saboda wayarta da ta shiga ruri. Ta dauka taga Sam ne. Sam mai aikinsu ne kuma amintaccen Mummynta ne don cikin gidan ba inda bay shiga, shi Er Rabi ke aika yana kaima mabiyanta magani. Dan tsaki tayi, kiran me yake mata? Ta dauka da “Hello Sam, what is it?”. Yace “Ehn small madam, na you talk say make i holla you anytime wey Aunty Shafa show ba?(Eh Hajia karama kece kika ce na gaya miki duk ranar da Aunty Shafaatu tazo ba?”. Da sauri ta gyara zama tace “Ehen..” “She don come house, and she dey vex, i greetam sef she no answer me(Ta zo gida, tana cikin bacin rai, har gaidata nayi ma bata amsa ba”. Yasmin tace “Sam, where them they?(Sam suna ina?”) Yace “them dey Madam’s room”. Tace “Abeg Sam, hurry enter the room on that switch wey i give you the other day, puttam for their front, send your account number nownownow” (danAllah Sam ka shiga Dakin nan, wannan abunda na baka kwanaki ka kunna minshi, ka ajeshi gabansu, ka turo min Account number dinka yanzu yanzun nan”. Daria yayi yace “no wahala madam”. Sai da yayi Knocking ya shiga da tray din karfe a hannu ruwa ne da juice, a jikin tray din ya manna recorder din, kamar magnet take ‘yar karama, in baka san da ita ba ba za ka gane zamarta ba, ya aje a gaban Aunty Shafa’atu ya fita. K’amshi ta ciro wani abu kamar Mp3 a jakka ta sa earpiece. Ta dauki Jakkarta ta rataya tana tafiya zata tafi dakinta a Doctors quaters tana sauraran maganganunsu wanda duk hargowa ce ta zuwan Mancy da chanzawarta da jin zafinsu, sunfi minti 30 suna magana daya, har k’amshi ta isa dakinta ta zauna tana jinsu. Ta na jin Muryar Mummynta na cewa “Yanzu Shafa’atu ki fadi abunda kike so, da bakinki kawai zaki ce ga abunda kike so”. Ta ji Aunty Shafa’atu tace “Wallahi na tsani Maryama da duk wani abu da ya danganceta, kinga kallon kaskancin da ta min? Nidai ta mutu, a kashe min ita, ke Dalon ma ta mutu, Dan Makaho yayi hauka ya mutu shima”. ErRabi ta bata fuska tace “Ke ban san iskanci, ba Yasmin ke son shi ba?” Shafa’atu tace “ke Wallahi baya sonta, dazun nake gaya miki aka kama shi da budurwarshi ko karuwarshi a daki, da na mishi maganar Yasmin cewa yayi kar na sake mishi maganarta, ya tsaneta ba abunda zaiyi da ita”. Er Rabi Ta lula wata Ashar, tace sai ko yaci Ubanshi, diyata zai yaudara? Bayan son da take mishi? Aiko yanzu zan aiki aljani ya shakeshi har sai ya mutu, anjima zanyi na Maryama”. Tuni Jikinta ya fara rawa, wani fitsari taji a jikinta na gangarowa, kanta ya sara, ta rasa me zatayi, fita tayi daga dakin, sauri sauri bata san lokacin da ta arta a guje ba, bata damu da kallonta da mutane keyiba, ta na gudu tana neman layin Mummynta, wayarta bata shiga, Aunty Shafa’atu ta nema. Itama haka wayar tata. Sai a kira Sam. “Sam where you dey, take your phone to Mummy now”. “Ahh small madam i don commot”. Cikin Ihu tace “Sam, go home now, call me ASAP”. Dafe kai yasmin tayi cikin rashin sanin abunda zatayi. Sama ta kalla taga ruwan sama akeyi yafi k’arfin yayyafi. Da gudu ta shiga ruwan nan, ta sa hannu a Aljihu ta ciro key ta wuce inda tayi parking Motarta. Ta shiga ta cigaba da kiranta not reachable, ta sake kiran Sam yace ya kusa. Tura ma Mummy messages tayi kala kusan Biyar, saboda rashin sanin abunyi harda voicenote ta mata na kuka a whatsapp. Ganin kamar tana bata lokacinta yasa ta bar Asibitin a guje. Wadanda suka ganta sun nemi layinta. Bata iya daukar wayar kowa ba, asali ma rejecting takeyi tana neman numbern Mummynta hankali a tashe. Abu na Allah, Cikin Garin Kankia Ruwa akeyi sosai, baka ganin Motoci na tafia, da yawa sunyi Parking Motocinsu a gefe sai ruwa ya tsagaita, amma ita cikin ruwan nan take tafia, kuka takeyi sosai da karfi kuma, driving takeyi Kacokam, speeding takeyi kuma, burinta daya ta ganta a garin katsina, cikin gidansu kafin a ma Zaid komai. Wayarta ta yi ringing Sam ne. Da sauri ta dauka, mai makon ta tsaya tayi parking ta amsa wayar, sai ta cigaba da tukinta ko gudu bata rage ba. “Hello Sam” Muryar Mummy ta ji “Yas” Kamar jira take ta fashe da kuka “Mummmmy, dont do it, Mummy kar ki kashe min Zaid, wallahi Allah Ina son shi, Zaid shine farincikina, in kina son Farincikina kar kiyi komai da zai taba shi ko wani nashi”. Yasmin DanMakaho be sanki wata yarinya yake so, me zakiyi da wanda bai san mutuncinki ba, upon all the sacrifices you made for him? Wallahi he must pay with his life”. Kamar a gabanta tayi ta girgiza kai kamar kadangaruwa hawaye na kwaranyowa a kumatunta. “Wallahi Mummy ki kayi wani abu da zai sa na rasa Zaid ko farincikinsa, ba zan taba yafe miki ba” kamar zautatta chan kuma ta koma lallashi “MUMMY, donAllah ki bari, mummy ki dauka wannan rokon da nake miki roko na karshe da zaki min abinda nikeso, ko meye kar ki min amma ki min wannan, this is all i ask, ki rabu da Zaid, ki zare hannunki daga lamarinsu, mummy for me please”. Bata ga Katon dutsen Checkpoint din da ke gabanta ba, Sai ji tayi kawai ta bigeshi. Motar walwalwal tayi ta sake fadi, sai Wuta, duk da Ruwan Saman da akeyi, bai hana Motar Yasmin ci da wuta ba. Er Rabi taji Gbam kamar an bugi wani abu. Sai taji Yasmin ta bar magana sai faman “Hello Hello take cewa ba amsa”. Amma wannan bugun da taji ya bata tsoro, sai chan kuma taji dif. Trying Wayar Yasmin ta shiga yi amma ya k’i shiga, nan hankalinta ya k’i kwanciya. Mutanen gari suka firfito, babu wanda ya iya zuwa wurin, ga Ruwan Sama ana yi, amma Mota na ci da wuta, to wani taimako zasuyi? Amma duk da haka yan kwana kwanan Kankia sunzo da motarsu, don kashe wutan nan, Ikon Allah ya tsahirta wutan nan, ruwa ya dauke. Sai hayak’i, duk da sun san cewa ba lallai bane akwai rai, haka jamian suka daga motar suka kifar, aka bude ga mutum zaune, amma sun kasa gane Mace ce ko Namiji saboda k’onewar da gawar tayi”. “Inalillahi wa ina ilaihir rajiun” kalmar da duk wanda ke wurin ke fada kenan. Wani tsoho yace “Ba rai, wannan bawa ya amsa kiran Mahalicci, Allah ka karbi shahadar wannan Mammaci, wutan duniya ta ci bawan nan, InshaAllah ya kubuta daga ta Lahira, Allah ka sa muyi mutuwar Shahada” yan wurin suka amsa da “Amin”. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉 BABI NA ASHIRIN DA TARA 2⃣9⃣ (ZAN RAYU DA KAI ❤ ZAN MUTU DA KAI 😭 ) A tasha tayi Sallahr Asuba, Motar Suleja ta hau, tunda ta shiga Motar suka fara tafia gabanta yake faduwa, fargaba da tsoro suka cika mata zuciya, kar suyi Accident fa, ji take kamar ta sauka, amma zuciyarta ta riga ta kitsa mata, bacci takeji amma bata ga ta bacci ba haka tayi zaune tana sak'e a ranta. Allah ya kaisu Suleja Lafia, daga nan ta hau Motar Katsina. A B U J A Mancy na dakin Abba, Dalo ita kadai ke zaune a Dakin Mancy ta na neman wayar Zaid ta kasa samunshi, a duk lokacin da ta tuna Yasmin da Alherinta sai ta zubda hawaye, sallama yake tayi, bata ji ba, har yazo gabanta ya zauna. Hannu ya tafa, ta dan firgita. "Ina kwana?" Ta gaisheshi kanta a duk'e. Bai amsa ba yace "tunanin me kikeyi?". Murmushi ta dan kirkiro tace "bakomai". Yace "Ba nace a daina kukan nan haka ba?". Marairaicewa tayi tace "fa ba kuka nakeyi ba?". Irin muryarta yayi yace "to me kikeyi? Da sauri ta kalleshi jin yanda yayi magana kamar wani dan auta, au danauta ne ashe, dauke ido tayi saboda kallon da yake binta dashi. Yace "Kin gaya min matsayin Yasmin a wurinku, zan sake gaya miki kamar yanda na gaya miki jiya, shi mamaci addua yake so fiye da komai, kuka baya kara musu komai sai nauyi, ki roka mata rahama, balle ita da muke sa ran inshaAllah tayi mutuwar Shahada, ki bar mata kuka please". Duk jikinta ya mutu da yanayin maganarshi, shi haka yake? Haka yake magana? Muryarshi sanyi? Wannan in ta cigaba da sauraran muryarshi sai ya sa ta shiga wani yanayi". Yace "dama Abba yace muje na miki register Catering School kafin a samo miki Admission a Nile University". Cikin jin dadi tace "Dagaske?". Ya langwabar da kai yace "eh dagaske". Ta sa hannu ta rufe fuskanta, ta lura Ya Jawad na san zolayarta. Ya mik'e tsaye yace "ina jiranki a waje". Ya fita, ta bi bayanshi da Ido. FIKRA Catering School ya mata register, maimakon su wuce Gida, sai ya shiga Yawon nuna mata gari, don ya san in suka koma Gida daki zata shige tayi ta kuka, shi kuma har ga Allah baya son Kukan nan. Sai da ya ga tayi daria kafin ya daina k'okarin sanyata daria. Akwai wani abu da yake ji a game da ita, yana ganin kamar Tausayi ne, amma cikin zuciyanshi ya san ba haka bane. Na wani dan lokaci Dalo ta manta da damuwarta, yanda Jawad ke ji da ita ya sa take jin wani abu game dashi, ta san shi ba tsaranta bane Hmm, a dai bar maganar. K A T S I N A Tarin da Dr Ali ya ji Zaid nayi jiya ya tsaya mishi a rai, yana tsoron kar stage din TBC dinshi ya kai ga Liver Transplant, wayarshi ya dauka ya latso Zaid amma wayarshi is switched off, sak'e sak'e yayi tayi daga k'arshe ya yanke hukuncin zuwa ganin Zaid, daga nan ma ya zo ya mishi tests a ga yaua matsayin ciwonshi yake yanzu. Maigadi ya tabbatar da cewa Zaid na cikin gida, ba tare da jiran komai ba Dr Ali ya nufi Boysquaters, yana shiga dakin ya ga Zaid kwance murus k'asa, da sauri ya karasa gunshi yana jijiga shi, da alamun ba yanzu yayi collapsing ba. Da yake Dr Ali Giant ne, haka ya saba Zaid a baya ya fita don kaishi Asibiti, a kagauce yace da Maigadi "donAllah je ka fada cikin gida Zaid baya da Lafia, na tafi dashi General Hospital" Bai jira cewar maigadi ba ya bude motar ya tura Zaid shi kuma ya shige motarr. Maigadi yayi cikin da gudu don sanar da su. Hannah kadai aka samu, Shafaa na chan gun Er Rabi. Da aka gaya ma Hannah tabe baki kawai tayi yo su ina ruwansu da wani rashin lafian Zaid? Allah sa ma ya mutu. A Asibiti tuni an kaishi Emergency Room Likitoci suka dukufa kanshi, abunda Dr Ali ke gudu shi ya faru, Kusan rabi da kwatar Hantar Zaid ta lallace, kuma in har baa mishi dashin Hantar ba, to Hantarshi zata fashe, ga Hak'ark'arinshi duk sunyi bak'i saboda hayak'i dake bi ta wurin. Dr's suka yanke shawaran yi mishi aiki cikin gaggawa saboda kar lallacewan Hantar ya tabo Huhunshi. Wani daki a ka kai Zaid don a kara mishi ruwa da jini saboda he is very weak. Har ya farfado Dr Ali na dakin yana kallonshi cike da tausayawa. Muryar Zaid baya fita, amma sai da yayi karfin halin cewa “Na kusa mutuwa ko?” Sai da ya kasa kunne kafin yaji abunda yake cewa. Dr Ali yace “Zaid ba wanda ya san gawan Fari, zaka samu lafia”. Zaid yace “kar ka boye min, ka gaya min”. Dr Ali yace “Zaid, liver dinka is damaged, you will need a transplant”. Zaid ya lumshe jajayen idanuwanshi yace “tawa ta kare kuma, zani bi Yasmin”. “Aa donAllah, kar kace haka, zanje gidanku na samu babanku, an san wanda zai baka hantar a diba, da anyi transplant din shikenan inshaAllah, duk da your ribs are infected once you quit smoking, you will be fine by God”. Zaid ya murmusa yace “ina kace zaka? Gidanmu? Waste of time, kar kaje, nikam da drip dinnan ya kare zan koma Gida”. Duk da ya san abu ne mai wahala, but zai koma gida ne kawai ya jira ajalinshi ***** E D O Har Bayan Azahar Mami bata ga Labiba ba. Abun ya k'ular da Maminta, don Ubanta fushi take don an mata fada? Shiyasa bata fito ta gaishesu ba? Bata tunani ko Sallah ma tayi, tashi tayi a fusace, ta kama Labiba sai ta mareta, bude labulen dakinsu Labiba tayi, sai gani tayi wayam ba kowa. Mamaki ya kamata, tun dazun take Prlo, yaushe labeen ta fita? Haka kawai ta tsinci kanta da lek'a kasan gadon. Da sauri ta bar dakin ta shiga dakinsu Samira, suna nan zaune duka. "Samira ina Labiba?" Samira tace "tab, yo ai ni duk yau banga Labee ba". Mami tace "tashi duba man Gidansu Jamilu ko ta shiga". Kuiwa garesu, sai da ta dan bata lokaci tana zumbura baki kafib ta fita. Jim kadan ta dawo tace "mamarsu jamilu tace ba ma su san Labee ta dawo ba". Mami tace "Ikon Allah". Mamarsu Samira tace "fushi tayi fa, kila tana Gidan Zainaba, sai kunyi biko zata dawo." Maminta tace "Aiko Zata ci Ubanta" Ta koma dakinta ta dauki wayarta takira diyarta Zainaba. Ko amsa gaisuwarta batayi ba tace "Maza kice Labee ta hau A daidaita sahu ta dawo Gida yanzu ina jiranta". Zainaba tace "Mami wace Labeen? Labee ta dawo ne?". Mami tace "bata Gidanki?". Zainaba tace "ai ban ma san ta dawo ba". Kit Mami ta kashe, kiran Mai bi ma Baban Amira tayi Hamza, tace "Hamza labee na gidanka?" Hamza yace "Aa Mami, sai dai in gidan Zainaba". Ruwa idon Mami ya kawo tace "Hamza Labee ba ta gida, bata gidan Zainaba, in ba gidan Zainaba ba, gidanka, in ba ta nan ban kuma san inda take zuwa ba". Hamza yace "Kar ki daga Hankalinki Mami, kinsan Labee dai, ba zata wuce Gidajen Yayyinta ba, barin kira su Hashim, sai naci Ubanta in tana fita bata gaya miki ba". Mami tace yauwa Kirasu. Daya bayan daya Hamza ya kira Yayyinshi da Kannenshi masu aure, daga wanda ba su ma san Labeen ta dawo Edo ba, sai wanda suke ceea aa bata zo ba". To shima fa nan Yaya Hamza ya kasa Zama, ya hau dan babur dinshi ya burko zuwa Gida, da niyyar in ya kama Labee, wallahi babu abunda zai hana shi zane ta da Belt din Jikinshi. Abu kamar wasa Duk inda aka san Labiba zata iya zuwa sai da aka bincika amma ba alamun wani ya ganta, an kira wayarta a kashe. Hayaniya ya firdo da Yaya Muhammadu da Abbansu "Mai ya faru?" Suke ta tambaya Maman Samira tace "kunga tun dazun ne muke neman Labiba ba mu ganta ba, ba inda ba mu dibata ba, duk gidan da muka san Labiba na zuwa munje bata ba alamunta, wayarta a kashe kuma". Abba ya saka salati, ya ma rasa me zaiyi, baban Amira kam kwallah ya fara yana tunanin tana ina. Ba mai zama, kowa aka barbazu neman Labiba, babu wanda ya kawo ta koma katsina. A bayyane Abba yace "kina ina Labiba?Allah ka tsare min Labiba a duk inda take". K A T S I N A Farfadowa tayi ta bi masu zaune a dakin da ido. Ganin ta bude ido ya sa su mikewa tare da matsowa bakin gadonta suna mata sannu, barin ma Shafa'atu da ta fi kowaccen su zak'ewa. Er Rabi bata iya ce musu komai ba, ta cigaba da binsu da ido daya bayana daya kafin tayi yunkurin tashi, zasu riketa ta daga musu hannu. Da kanta ta tashi ta zauna kan Gadon ta kalli ta gefenta tace "yau wace rana?". Alhamis aka ce mata. Murmushi tayi tace "yau kwanan Yasmin Uku da rasuwa? Ina nan kwance kamar gawa? Meyasa baku tadani ba?". Ba wanda yace mata komai, sauka tayi da kan Gadon ta sa Slippers ta fita daga Dakin. 'Yan kwarakonta suka bi bayanta da gudu suna mata magana bata tsaya amsa kowa ba. Sam na ganinta ya bude mata K'ofar Mota ta shiga ya Ja Motar zuwa Gida. **** Dr Ali bai ji cewar Zaid ba ya nufi Gidansu, zuwa gidan ke da wuya ya ga Shafaatu da Iyalanta zaune a bukkan gidan, ya gaidata ta amsashi tana son jin ko waye. Yace “Alhaji Ali na nan?” Tace “aa baya nan, wake nemanshi?”. Dr Ali yace “ni ne” Tace “lafia?” Yace “dama Zaidu ne baya da lafia sosai, yana chan kwance, emergency surgery zaa mishi inda zaa chanza mishi Hanta, shine ake son relative ya zamana shi zai bada hantarshi” Galala take kallonshi kafin tace “oh ashe baida lafia, yo ai bamu sani ba, mu kwana runfa daya ace har yana Asibiti ace bamu sani ba? To ba ruwanmu, kar wanda ya sake zuwa mana gida batun Zaid”. Dr Ali yace “ni babanshi na zo gani, in baya nan ku bani number dinshi in nemeshi”. “Shafa ta harareshi tace ai bayyi nisa ba, Annah je ki kira min Daddynki”. Annah ta tashi tana harare harare ta tafi cikin gida jim kadan sai gashi sun dawo tare. Dr Ali dai na ganin ikon Allah. Yana zuwa yace “ina wuni?” Kafin ya amsa Shafaatu ta fara bambami “Wai Zaid zaa ma dashin Hanta shine aka zo tafiya da kai a bude cikinka a farka ka a cire naka a saka mai kai kuma sai mutuwa”. Dr Ali yace “Aa wallahi ba haka bane, Baba, Lafiyayyen Hanta kamar bishiya ne, in aka dibeshi bayan wani lokaci da kansji zai tsiro ya dawo normal form dinshi, ba duka ake cirewa ba, diba zaayi”. Baba yace “me ya samu Zaid din ne?”. Jin haka Shafaatu tace “Ya kashe hantar shi da Hayaki, ya lallace shine za a zo wurinka ka bada wani Hanta, kar ka sake ka yarda”. Kamar wanda aka sa ma battery ya fara bambamin fada. “Ni dan Iska ne? Ni zan bada Hanta na? Kar Allah ya sa ya warke in ni yake jira”. Dr Ali kamar yayi Ihu yace “Baba Danka Ne fa”. Baba yace “donUbanka ka fitar min A gida”. Dr Ali ya kasa motsi, da gudu ya dauko wani gatarin da ake saran flowers ya bishi da gudu Dr Ali ya fita. Nan Shafaatu ta samu fagen Aibata Zaid. %%%%% Er Rabi na zuwa ta ga Gidan kamar ba ayi zaman gaisuwa ba, ba kowa a gidan, ta shiga ta bada umurnin "kar wanda ya shigo mata Gida, tana son kasancewa ita kadai a wannan gabar". Dakin Yasmin ta shiga, ta na shiga ta saka jam lock tare da sulalewa k'asa, kuka kawai takeyi, kuka mai taba zuciya, ashe Baban Yasmin na nan zaune kan Gadonta, ganin Er Rabi ta shigo ya sashi yin Lamo. Sai da ta dau lokaci mai tsawo tana kuka kafin ta share hawayenta. Wayarta ta shiga tana scrolling Messages din Yasmin. Inda duka rok'o takeyi kar ta taba mata Zaid dinta. Hajia Er Rabi ta yi mamakin irin wannan So da Yasmin ke ma Zaid, yanzu ta mutu kenan tana son cetar Zaid ko? Amma dai wannan ba. Sumbatu take "wai ta yaya zata mutu? Ta yaya zata tafi ta barta? Bata san ta na sonta ba? Bata san tana sonta fiye da rayuwa da kanta ba? Ya take so ta rayu bayan ba ta a duniya? lallai duniya abun tsoro, ko daren rasuwarta sai da sukayi Chatting fa. Kila ma ta bar mata message yau da safe, bata bude ma, data ta kunna,messages suna ta shigowa. Karanta last chat dinsu take kafin taga Voice note kusan 7. Na farkon ta bude. "MUMMY, kinsan Zaid ne farincikina ko? Mummy ki rabu da Zaid, in kika mishi wani abu wallahi ba zan taba yafe miki ba, ". Kuka Er Rabi ta sake tare da playing Voice note na biyu inda tace "Mummy, Ina son Zaid fiye da rayuwa da kanta, ki ka kashe Zaid, daidai yake da kin rasani". Duk sai da tayi playing Voicenotes dinnan tas, tana jin muryar diyarta tana kuka tana nadama. Messages din ta cigaba da bi inda wani tace "Wai yanzu Aunty Shafa ce zata dinga juya ki, ba zaki bar Bokanci ba? Mummy har kin kai matakin Kisa? Waiyoni Mummy i am driving and its raining heavily, kin ki daukan waya, in har dagaske ne kina so na, in har dagaske kina sona fiye da komai, in har komai don ni kikeyi, zaki tayani Son abunda nike so, zaki tayani kare abunda nake so, zaki tayani Son Zaid, in har dagaske kike Mummy, zaki min Alfarmar nan". Ta karanta wannan last message din yafi so 20, tana kuka sosai tana "Yasmin ki yafe min, na kasance banzan uwa, sakarya da bata san meke mata ciwo ba, lallai Shaidan ya kada min kidi na kuma tika rawa sosai, na tsani kaina, na raina kaina, tir da ni wallahi, duk karfina da ikona, na kasa baki abu daya da kike so a rayuwa. Zaid kadai na kasa baki a rayuwa, yanzu ina mai matukar nadama da na kasa baki Zaid. Baban Labiba yace "Kayya Er Rabi, kaiconki, tir da ke kam K'arfi? Iko? Wani karfi kike dashi da iko? Bokanci? Shirka? Wayace miki rayuwa a hannun ki take? Da har zaki zabi wanda zaki raya da wanda zaki kashe, gashi garin neman ran dan wani kin nema naki, Kin kashe diyarki da kanki, wallahi ke kika kasheta". Tsinuwar Allah su tabbata a gareki hatsabibiyar Mace, wurin gaisuwa da yawa cewa sukeyi ashe Yasmin na da Uba, kin maidani wani hoto mara amfani, banda ikon amsa sunan Uban Yasmin, don ma Yasmin na So na, mutuwarta ce silar kubutata daga duk wani kaidinki, nayi imani duk wani asirin da kika min ya rushe, saboda daga ran da Yasminta koma ga mahallincinta naji na tsaneki, na bar tsoronki, na kuma bar shakkanki. Kuma na san mutuwa hutu ce ga Yasmin, bata da yanda zatayi nayi imani da sai ta chanza Uwa, ke annoba ce, yanzu sai ta huta lafia. Allah ya Isa Er Rabi, Allah ya isa da kika rabani da kowa, da dangina da asalina kika maidani kamar bawanki, Allah ya isana da kika dauki shekaru kina maidani Mace sai yanda kikayi dani Allah ya isa tsakanina da ke, duk da kin gama dani, na sakeki saki Uku, abu na karshe da zan ce miki, in kinga dama kar ki fasa, ki cigaba da neman ran abunda diyarki har ta mutu tana So". Ya tsallaketa ya fita daga dakin Yasmin ya barta zaune kamar an dasata, ta kasa motsi, banda hawaye babu abunda ke sintiri a idaniyarta, yau itace duniya ta juya ma baya?". ***** LABIBA FA? Tunda ta shiga Motar Suleja ta ke kuka sosai, abu 3 take ma kuka. Na farko Mutuwar Yasmin, in ta tuna ta Mutu sai ta ji ranta ya sosu wanda tunatan na zuwa mata da hawayen ido. Na biyu kuwa rashin sanin halin da Masoyi yake ciki, ta kira ta kira wayar a Kashe. Na Uku kuma fitowan da tayi ba tare da sanin Iyayenta ba, fitowar da tayi ita kadai, babu wani muharammi, tafiyan awa 12 tayi jiya, gashi ta dasa. Awa 5 zuwa 6 ya kawo su Suleja don ita ta da fito tun asuba sai 12 suka isa, ta fara galabaita tun kafin su shigo Suleja. Tunda suka shiga ta nemi Abinci a Tasha ta ci kafin taji cikinta ya dan dauka. Bayan awa daya suka tashi don tafia Katsina. Da gangan ta kashe wayarta, don ta san ba zaa dade ba za a san bata gida, tafia suke ta ci sosai, idanunta duk sunyi luhuluhu saboda kukan da ta keci. Tafian wani Awa 6 zuwa 7 ne daga Suleja zuwa Katsina, in ta tuna tsawon awannin da ya rage da zai kaita Katsina sai ta ji jikinta duk yayi sanyi. Suna ta cin tafiya, ba sa tsayawa komai sai Sallah. Karfe 3 suka tsaya don hada Sallah Azahar da Laasar. Wata tafiyar awa 4 ce kuma, sa kai yafi bauta ciwo, haka suka sake daukan Hanya suna ta tafia, suna ta sharara gudu, Labiba ta cigaba da zikirinta. Tsautsayi ya samu Motar, tayar su ta fashe gab da Maghrib a daidai Wajajen Gidan Mutum daya, an dauka minti kusan 40 ana gyara, karshe akace Motar ba zai gyaru ba, sai dai su kwana, matsalar Motar haya kenan, ya zata kwana a nan? Zaid fa? Wani hali yake ciki? Ya zata kwana cikin Maza? Matansu ba su wuce 3 ba, bata damu da tafiya ita kadai wani abu ya sameta ba, ta fara tafiyarta, ganin Signboard wanda ya nuna arrow din zuwa Charanci sai taji kamar dama ta iso Gida. Tafiya kawai take, bata san adadin tafiyar da tayi ba, ita dai ta san ta dade tana tafiya har kafarta ya fara ciwo, amma bata tsaya ba, saboda ta bar inda mutane suke, ta shigo daji, ita ko tsoro bama ta ji, ba ruwanta, batayi nadama ba, ita dai ta ganta a Katsina gaban Masoyi. Jefi jefi ta kan sa hannu don tsaida Mota don samun Lift, amma babu wanda ya tsaya da Motarshi, tsoro ya fara mamayeta a lokacin da duhu ya soma yi, kiran Sallahr Magrib taji, da sauri ta kara sauri don isa ga Masallacin. Tun bata hango Masallacin har ya kai ga tana hangowa. Ta ci uwar tafiya tana isa Masallacin Matan ta zube a k'asa, tana mayar da numfashi. Wata mata na Sallah,yaranta biyu na zaune, daya ta idar da Sallah daya yarinya ce tana shan ruwa mai sanyi. Labiba tace "ki tsanmin ruwanki in sha donAllah". Yarinyar ta mak'e kafada alamun "aa". Yayarta ta ma Labiba murmushi tare da ce ma kanwarta "Give her the water". Yarinyar tace "No". Labiba ta dan kwantar da kai tana ajiyar zuciya lokaci lokaci tace "Sweetheart, i am really thirsty, can you give me please?". Yarinyan tace "Noo, its mine". Labiba da dan karfi tace "Arrggh" tare da kwantawa rigingine tana kallon ceiling tana maida numfashi. Daidai da Sallame Sallar Mamarsu ta kalli Labiba dake maida numfashi sosai. Zahra duba Mota kiga sun idar da Sallah? Akwai Ruwan Sanyi ki dauko mata". Yar budurwar ta tashi ta nufi Motarsu da ke waje ta dauko ma Labiba ruwan sanyi. Tunda Labiba ta kafa kai a robar Faro, sai da ta shaye shi tas, ta aje tana mayar da numfashi, ta dade a wannan halin, kafin ta daidaita numfashinta. Matar kam Kallon Labiba kawai takeyi. Labiba tace "Ina wuni?". Hajiar tace "Lafia lau Yanmata". Labee tace "Wallahi tafia naci a k'asa, shine fa duk na gaji". Hajiar tabi Labibs da ido, tana karantar ta, to ko dai 'yar kauyen ce? tace "Okay, ke 'yar nan ce?". Labiba ta gyada kai tace "aa wallahi, Daga Edo nake motar mu ta lallace wai sai dai a kwana a hanya, nikuma Wallahi ba zan kwana da Maza cikin Mota ba, mu ka san abunda zasu mana in dare ya tsala? Allah ya tsareni daga masu warin baki sai masu warin hammata, nan kaina duk ya gama sarawa, ya fiye min na kwanta a Masallacin nan da safe in nemi Lift". Hajiar ta kalleta tace "Ina zakije ne? Kaduna?". Tace "Aa, Katsina". Shiru tayi tana kallon Labiban dake danna k'irjinta, bata san wacece ba amma ita da ta barta a nan ta kwana gwara ta tafi da ita". Matar tace "Katsina Zamu yanzu". Labiba tace "lah ashe chan kuka nufa, sallah kuka tsaya kenan". Matar tace "Eh daga Abuja nike nima, ni da Iyalina zamuje Bikin diyar Wa na" Labiba tace "Allah sarki". Hajiar tace "muna iya tafiya dake". Farinciki ya mamaye Labiba tace "Allah Hajia? Ba zan takura ba?". Tace "haba ba wani takura, kiyi Sallahr ke dai". Da sauri Labiba ta fita ta doro Alwala tazo ta hada Sallahr Magrhib da Isha'i. Motar High Lander ce. Yaranta suka shige chan baya, ita kuma da Labiba suka shiga mai bi mishi. Driver da Yaron Hajia suka zauna gaba. Yar budurwar ta zunguri Labiba da Ledar takeaway tace "ga snacks". Labiba ta murmusa ta amsa tare da amayo godia. Dadi kasheta, yunwa takeji, rabonta da Abinci tun a Tasha. Ham ham take cin Meatpie dinnan kamar mayunwaciya. Sai da cinye da donut ta sha Cway Juice taji tayi k'at. Sun danyi tafiya na minti 10, Hajiar duk na nazarinta, tace "Sunana Hajia Bilkisu, kinga wannan yara na ne, na gaya miki biki zamuje Katsina, tsakaninki da Allah mai ya kawo ki Katsina tun daga Edo ke kadai, guduwa kikayi ko?". Labiba tace "aa wallahi,zan koma". Hajiya Bilki tace "kinga, zakiyi saar babbar yarinyata, kuma ki gaya min gaskia, bana son karya, zan taimakeki in kika gaya min gaski, in kika min k'arya in sa driver ya saukeki a nan Dajin Allah". Window Labiba ta kalla taga bata ga Gida ko daya ba sai Bishiyoyi tace "Wallahi Aunty nidai ba duniya na shiga ba, Katsina nake karatu, Wannan ne baya Lafia kuma wayarshi bata shiga,hankalina ya kasa kwantawa shiyasa nazo ganinshi". Hajiya tace "Saurayinki?". Labiba ta sadda kai ta dan murmusa. Hajiyar tace "tsakaninki da Allah iyayenki sun san kin taho?". Cike da rashin gaskia tace "Aa". Matar tace "guduwa din dai kikayi, kika taho dubiyan saurayi, anya kuwa ba karya kike min ba lafiyarshi lau ba? Soyyaya zai sa ki zo wurinshi ku gudu ko?". Da sauri Labiba tace "aa wallahi, wallahi ni ba mutuniyar banza bace, wallahi dan shaye shaye ne, sai mu fi hours a dakinshi amma ko hannuba bai taba tabawa ba". Labiba kam ta gama kashe matar a zaune, baki a bude take bin ta da ido. "Dan Shaye Shaye? Kike so? Har kike zuwa dakinshi?". Ta kalli diyarta dake back seat tace "yo in diyata ce ai da na yankaki naji kina shiga dakin namiji, meyasa kike kai kanki wurin namiji? Wallahi wasu matan su ke kashe kansu". Da sauri ta girgiza kai tace "Aunty donAllah kar ki man Mummunar fassara da fahimta, tsaya kiji". Tiryan tiryan ta kwashe duk wani labari da ta sani game da Zaid ta ba Aunty Bilki. Da mai saurin kuka ce da tayi amma irin dakakkun matan nan ne, diyarta dai tana ta hawaye. "Allah ka mana tsari da kishiyoyi irin Hajia Shafaatu, Allah ka mana tsari da mummunar kishi, Allah ka mana tsari da yi ma 'ya'ya mugun Alkaba'i, tabbas naga mutuwar Dr Yasmin a Social Media sosai kuwa, kila mutuwarta ce ya taba lafiyarshi. Labarin Zaid abun taussyi ne amma Labiba what you did is very wrong, kowa ya ganki yanzu he will give you a bad impression na kin baro gida zakije Katsina gun Namiji, ba wanda ya ga niyyarki, kowa zai daukeki a matsayin mutuniyar banza, ba ma haka ba, yanda kika fito ba da sanin kowa ba, wani abu ya sameki a hanya Allah shi kyauta wa gari ya waya? Me zakice? Laifin waye? Duk laifinki ne". Sosai ta ma ta fada da nasiha, ta kuma bata baki akan tausar zucia, don a dan labarin da taji ta lura she's an extrovert, tana fadan abunda take so a lokacin da take so babu dam sakayawa, saboda gatsau tace mata "Aunty ina sonshi don ni na fara furta mishi So". Sosai Aunty Bilki ta yi ma Labiba fada har ta sha kuka. Aunty tace "to wallahi da kinga lafiyarshi wallahi ki kama hanyar Edo gobe ki koma Gida, ki rok'i gafarar Iyayenki, ga dubu 10, ki mayar ma Maminki kudin da kika sata, sauran kiyi kudin Mota". Labiba ta murmusa tace "inshaAllahu Aunty, na daukar miki Alkawari, nagode sosai". Suka iso Katsina Lafia, har tudun matawalle suka kaita, har gaban gidan Alhaji Ali Zaki. Labiba ta bude Mota. Tace "Ba zaki shigo ku gaisa da Matar Yayana ba?" Aunty Bilki ta girgiza kai tace "aa Labiba munyi dare". To nagode kwarai, Allah ya saka miki da Alheri ya tsareki ya tsare miki 'ya'yanki, yanda kika taimakeni Allah ya taimakeki, inshaAllah yaranki zasu zama abun Alfahari a dunia baki daya". Ta amsa da "Amin Amin nagode da adduoinki, naji dadinsu Allah ya amsa" Labiba tayi sallama da yaran Hajia, har ta juya zaya tafi gida Hajia ta dakatar da ita. Labiba ta dan Matso bakin window, Hajia tayi rubutu a wani takarda ta ba Labiba tace "Ina So na samo ma DanMakaho aiki, ina da hanyar Civil Defense, in yana da raayi ki bashi email address dina gashi nan ya tura min CV dinshi ko da secondary certificate ya samu ai yafi mishi zaman banzan nan, ga number nan kuma ki kirani inji ko kin koma Edon". Hajia bata tsaya jin Godiar Labiba ba tayi whinning glass shi kuma Driver ya ja mota aka bar Labiba tsaye da mamakin Hajia Bilki. Haka Allah ke abunshi, haka Allah ke sa jinin mutane haduwa ba tare da jini mai gudana ba. Ita ta san haduwarta da Hajia Bilkisu Alkhairi ne. "Hajia Bilkisu Beebbs nagodia, Allah ya baki farinciki a duk inda kike" mai makon ta shiga Gidansu kawai ta fada gidansu Zaid. Yau ta Gate Beebs aka shiga Gidansu Zaid. Ba ta tsaya ko ina ba sai dakin Zaid, Wayam bashi ba alaminshi, wayarshi ta gani a k’asa da sauro ta dauka, tana kunnata ba charge, ta tura toilet taga baya ciki, yana ina? Ko yaje Bencin Eskaley, da sauri ta fita waje ta nufa Bencin Eskaley. Suna ganinta suka mimmike, “Yayarmu ina wuni” Bata amsa ba tace “donAllah ina Zaid?” Sukace “Yo ai duk yau bamu ga Mankas ba”. “Baku ganshi ba?” Be fito ba gaskia, bamu ganshi ba, jiya dai mun ganshi har muka mishi Taaziyar Yasmin”. Bata tsaya gama jin zancen ba ta koma Gidansu Mankas din. Ba tsoro ta shiga Parlorn suna zaune. Alhaji Ali tace “Ina wuni?”. Zai yi magana Hajia Shafa tace “wacece ke?”. Tace “sunana Labiba, ina neman Zaid ne”. Shafaatu kamar an watsa mata garwashi tace “ba zaa bashi Hantar ba, ya mutu dole ne?ina ruwanmu”. Labiba bata gane inda ya dosa ba tace “Mene? Ni Zaid na zo nema”. Annah tace “Dallah Mallama ki fitar mana daga Gida” Labiba ta kallesu tace “Ni fa ba wai zuwa nayi ku daga min jijiyoyin wuya ba, tambaya ce na muku, in baku san inda yake ba, ku gaya min, sai na je wani gu na tambayeshi”. Annah tace “Karuwa har Gida kike biyoshi?”. Sosai Labiba taji zafin zancen cikin fushi tace “Uwarki ce karuwa”. Shafa’atu tace “kam bala’i uwarta ni kenan?”. Labiba ta rausayar da kanta ta kalli Baban Zaid, sai taji ya bata tausayi”. Fita kawai tayi a Parlon ta bar gidan, har zata shiga Gidan Yaya Muhammadu ta fasa ta dawo Gidan Alhaji Ali tace da Maigadi “DonAllah ko ka ga Fitar DanMakaho?”. Maigadi yace “Eh, bai da lafia sosai wallahi dazun ni na kama ma wani abokinshi muka sashi Mota Abokin ya tafi da shi General. Da gudu Labiba ta fita, bata shiga Gidansu ba tayi hanyar bakin Titi hankalinta a tashe. Yan Bencin Eskaley nata mata magana tayi banza dasu. Keke Napep ta tsaida tace a kaita General Hospital. Ta na isa ta nufa Accident and Emergency, ta bada sunanshi gun reception akace anyi moving dinshi an bashi gado Amenity room 7. Bata san ina ne Amenity ba amma bata ma tsaya tambaya ba. Da taimakon Signboards ta gano Amenity, ta shiga ta fara neman dakuna. Tana ganin room 7 ta karasa a guje ta bude da karfi. Chan kan Gado ta hangoshi kwance kamar tabarma, da sauri ta karasa gunshi kamar zata daukoshi daga kan Gadon. A hankali Zaid ya bude idonshi ya saukesu fes kan Labiba a wahalace da sauri yayi yunk’urin tashi, tayi saurin maida shi ta sakar mai murmushi mai ciwo, kauda kai yayi bai so ta ganshi cikin ciwo, bai so ta san weakeness dinshi. Sannu ta shiga jera mishi, bya juyo ya kalleta yana niyyan magana bata ji meya ce ba, ta sa kunneta a daidai bakinshi yace “Yasmin ta tafi Beebs”. Tace “Yasmin ta tafi Allah ya gafarta mata, lets focus on you now, you are sick”. Yace “I am dying”. Tace “shuttup gashi ana kara maka ruwa da jini inshaAllah kafin su kare ka warke”. Murmushi kawai ya mata. Socket ta nufa tace “Wayarka ba charge, daga gidanku fa nake”. Da charger dinta ta jona mishi charge. Ta dawo ta zauna a kan kujeran da ke gabanshi. Tace “Sannu” Yace “ya kamata ace kina Edo”. Tace “Masoyin baida lafia”. A hankali yace “Ta yaya kika zo?”. Tace “in ka warke zan baka labari”. A hankali aka bude Kofar. Labiba ta juya ga k’ofar Drs ne su biyu suka shigo Ta mike da fara’arta. Tace “Sannunku”. Dr Ali yace “Zaid bak’uwa akayi?”. Zaid ya kanne idonshi yana so ya ma Dr Ali inkiya da kar ya gaya ma Labiba. Labiba tace “Yauwa Dr, ya mai jiki? Stress ne ko?”. Dr Habib yace “dama Stress ne da sauk’i, he is very sick wallahi”. Tace “toufa, what exactly is wrong with him?”. Dr Habib yace “Liver is damaged, he needs a transplant”. A firgice tace “He Needs a Whatttt?”. Zaid yui saurin runste Ido. Da sauri ta kalli Zaid kafin ta kalli Dr Ali kafin ta kalli Dr Habib. “Bangane ba Dr”. A gajiye, a galabaice Zaid yace “Beebs”. Ta san da kyar muryar ta budu, amma ta ki kallonshi tace “Dr kamin bayani?”. Dr Habib yace “Are you a Family”. A kagaucd tace “Ni zai aura, mun kusa aure, and i think i deserve to know what is wrong with my Fiance”. Dr Habib yace “follow me”. Bata jira komai ba ta bi bayanshi. Zaid yace “Ali, donAllah ka hanashi magana”. Ali yace “Budurwarka ce?”. Zaid yace “it doesnt matter ka taimakeni kar ta san komai, tell her malaria ce kawai”. Dr Ali ya fita ya bi bayansu, ko da ya shiga Labiba na zaune tana sauraron Maganganun da ke fita daga bakin Dr Habib. Hawaye tuni sun wanke mata fuska, Zaid na dauke da ciwukka all this while bata taba sani ba? An fi shekara da akayi diagnosing dinshi amma ko da wasa bata taba sani ba? Ya Illahi, zuciyarta ta dafe dake barazanar fitowa. Cikin Kuka tace “To a mishi surgery din mana me ake jira? Da bakinka kace Emergency ne”. Dr Ali yace “Wallahi ba mai donating, naje Gidansu na gaya ma Babanshi baki ga wulakancin da suka min ba da gatari suka bini, Mamarshi kuma bata nan, nace zanyi contacting dinta yace baida contact din Mamanshi tunda suka rabu, nace kanwarshi yace “ta tafi Ghana wurin kakansu, nace dangin Babanshi ya ki magana tun dazun”. Labiba tace “K’arya, yanzu what will happen in be samu Surgery din ba?”. Dr Habib ya dauko Xray ya na nuna mata yace “he will slowly Die, dont forget his Ribs are Infected, and its close to the Heart, when he breathes in the Heart touches the veins of the liver, its risky”. Da sauri tace “then mai ake jira, muna bata wani lokacin ne, lets have the surgery now”. Sukace “who is donating?” Tace “Me, prepare for the surgery now”. Ta mike ta fita ta barsu su biyu suna binta da kallon mamaki. Dakin ta koma. Ta karasa da kallon tausayi tace “Kayi hakuri, duk wannan wahalar ka shata kai kadai, i am sorry you went through this alone, i am here for you now”. Ko bata fada ba ya san me take shirin yi, yasan mai zatayi Ya girgiza kai yace “Labiba Dont, karki yarda a budeki, mutuwa zanyi, theres a possibility ko an yi surgery din ba zan rayu ba, kuma donor din will be at risk, kar kiyi, ba zan yarda ba, i am dying”. Murmushi take mishi mai tarin ma’anoni daidai ta digar hawayenta tace “ZAN RAYU DA KAI, ZAN MUTU DA KAI”. Hankalinta kasa kwanciya yayi kwata kwata, kiran number takeyi yafi so nawa amma kwata kwata wayar bata shiga, me zatayi? Me ya samu diyarta? Ko ta aika Aljanni ya dubo mata Yasmin? Gani tayi process din zai bata mata lokaci ya sa ta kira Driver Mallam Haladu don tafiya Kankia. Mutanen Kankia an rasa abunyi, babu abunda ya tsira bayan Plate number na Mota. Muhawara aka tafka na tafia da gawar Asibiti ko police station, 'yan kauyen suka sa baki aka tafi da gawar Asibiti don kaiwa Mortuary, tuni aka gane mai Rasuwar ta hanyar Plate Number din. Kafin kace kobo Mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye garin Katsina da kewaye ta hanyar Social Media, wane ya gani ga wane haka mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye Nigeria baki daya. Mutuwarta Abin tausayi ne, in ka duba Statuses din mutane Hoton Dr Yasmin ne, da yawa masu sakata ma basu santa ba. Shigowar Hajia Er Rabi Asibitin Kenan ta ga tayi wata irin cikowa, a hanyarsu ta zuwa taga wata Mota tayi accident a bakin titi ta wurin Gidan Mutum daya, ta fi zaton ko wanda sukayi Accident din ne aka kawo Asibiti. Reception ta tsaya tana tambayar Dr's Quarters. Receptionist cikin rashin walwala tace "wa kike nema? Duk suna common room". Da murmushinta tace "Diyata Dr Yasmin". Receptionist ta rasa mai zatace mata, ta kalleta da kallon tausayi, ba huruminta bane fadan mutuwa, tace "zo muje". Er Rabi ta murmusa tace "yauwa nagode". Receptionist tayi gaba Er Rabi ta bita a baya, ba su tsaya ko ina ba sai common room, nuni ta mata da ta shiga ciki. Er Rabi bata tsaya wani tunani ba ta shiga cikin Dakin. Doctors ne a ciki Maza da Mata wasu zaune wasu tsaye, Matan kuka suke wi wi, Mazan kuma akwai masu hawaye wasu dai idonsu yayi ja. Er Rabi batace ma kowa komai ba ta bisu da ido, da ta gama rarraba idanuwanta tana neman diyarta bata gani ba ya sata magana. Doctorn da ya fi kusa da ita ta kalla tace "Dr, danAllah ina Dr Yasmin?". Hankalin kowa dake common room ya dawo kan Hajia Er Rabi. Tambayar ta sake yi, wani yace "wacece ke?". Da faraarta tace "Nice Mummy, Mummyn Dr Yasmin". Jin sautin kukan wasu matan ya k'aru. Tace "wai ya? Meke faruwa ne?". Wani Dr yayi ta maza yace "Mummy saidai muyu hakuri, Dr Yasmin ta rasu bayan Accident din da tayi 1hr ago". Er Rabi tace "kutumar Uba ne, meye rasuwa? Kai dallah baka santa ba". Taje kusa da wata ta mace da ke kuka tace "ke kawar Yasmin ce? Ta na ina? Muna cikin waya wayarta ta mutu, muje ki nuna min ita please". Dr ta fashe da kuka mai sauti. Wani Dr yace "Mummy zo muje ki gani". Ba gardama ta bi bayanshi Tace "Haladu, fito zo" driver ya bi bayansu da Mota, a tunaninta Wurin Yasmin zaa kaita taji yana cewa "Mummy, kinga ruwan saman nan bai dade da tsayawa ba ko?" Ta gyada kai yace "ba mu dade daga fitowa daga OR ba ni da Yasmin, wallahi Mummy sai gawar Yasmin nagani da idona". Mummy ta buge mai bakitace "kai bakinka ya sari danyab kashi, Yasmin nawa gareku? Ba dai tawa ba, ni fa yanzu yanzu muka gama waya da tawa Yasmin din". Yace "kiyi hakuri, yanzu yanzu sai Allah, in ta Gidan Mutum daya kika biyo zaki ga wata Motar da ta kone bakin Titi, wallahi motar kamshi ce" Wani irin razanannen Ihu tayi wanda duk wanda yaji ya san ba na lafia bane, zubewa tayi k'asa Sumamma. Tuni Drs sukayi kanta aka basu Gado. Haladu Driver ya kira Mijin Er Rabi ya sanar gasu a Asubiti Hajia ta suma Yasmin ta mutu. An dade a kan Hajia Er Rabi amma bata san wake kanta ba, ba ta farfado ba. Baban Yasmin yazo da wani kanenshi, hankalinshi ya tashi, dalili daya da ya sa yake zaune da Er Rabi saboda Yasmin ne, Yasmin na sonshi, in Mamarta ta guma mishi bakinciki ita ke lallashi tana bashi hakuri, yayi kuka kamar zai shide da ya ga gawar Yasmin. Karban gawar sukayi suka wuce Katsina ba tare da ya damu da duba halin da Er Rabi take ciki ba. Duk Doctors sun biyo don suma a samu Taaziya dasu. Ya gama waya da Yanuwa da abokan Azziki da ya isa zaayi janaiza, gata daya zai ma Yasmin, da an isa Katsina a mata sallah a kaita makwancinta kafin Er Rabi ta farfado ta musu jahilci, don yasan ba zata taba bari a rufe Yasmin ba. Messages dinta ya gani na ban hakuri sai na karshe na tafiyarta Edo gida amma zata dawo ba da dadewa ba, Zuciyarshi ta gama karyewa da jin ta tafi, kila ba zata dawo ba, amma layin karshen message dinne ya bashi tabbaci inda take cewa "Na maka Alkawari zan dawo, kasan kuma Labiba Kaifi daya ce, nace Zan dawo, zan kuwa dawo ma". Da tunanin Beebbs dinshi ya shiga cikin Gida don girka abinda zai jefa a bakin shan Sigari. Hudu da Shafa'atu na zaune a parlo, bakinta har kunne tana jira ta ji haukacewar Zaid ko mutuwarshi kamar yarda Er Rabi ta shaida mata. Wuce su kawai yayi ya shige kitchen. Hajia Laraba ta fado Gidan ko Sallama babu. Hajia Shafa'atu ta rikota tace "ke lafia? Me ya sameki?". Cikin tashin hankali tace "Daga Gidan Er Rabi nake, kinga mutane sunfi 1000, wai Yas ta rasu, tayi accident ta kone". Hajia shafaatu ta kar kade kunnenta tace "mene mene mene?". Tace "wallahi wai Yasmin din Er Rabi ta mutu". Zaid ya ji wani jiri na dibanshi, parlorn ya fito ya kalli Matar yace "me kikace?". Shafa'atu tace "ke yanzu yanzu fa daga gidan Er Rabi nake? Ina kikaji wannan karyar? Kun iya baza rumors wallahi". Hajia Laraba ta goge zufan da keto mata tace "Wallahi ba rumors bane, naje anso sakona a Gidan Er Rabi, naga mutane cike, na tambaya akace diyar Gidan tayi accident ta rasu a hanyar Kankia, yanzu haka babanta yaje daukota zaa rufeta, ko Er Rabi na da wata diyar ne bayan Yasmin?". Ihu Shafa'atu tayi ta daura hannu a kai, babu abunda takeyi sai Ihu, Hudu ya rada abunyi sai ji yayi zawo yazo mai, da gudu ya shige toilet ya bar Shafa'atu na chanyara Ihu tana neman Layin Er Rabi.. Zaid Fa? Zaid? Zaid na nan zube zaune a k'asa, hannunshi rike da kanshi wanda ke barazanar ballewa, Daga bisani kwakwalwarshi ta soma kai mishi cewa Yasmin ta mutu, nan kuma duk wata na'urar jikinshi suka soma tsayawa, fuskarshi tayi Ja, Yasmin ta mutu? Ya zaayi Yasmin ta mutu? Anya kuwa Yasmin ce ta mutu? Ya kamata ya tabbatar fa, amma in karya ne sai ya shake matar nan. Zuciyarshi tace "To wanene ba zai mutu ba a duniyar nan? Kullu nafsin za ikatul maut, shima dai ba abun mamaki bane ya ji shi a kabari ya mutu, inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Ya Illahi. Ya Salamu. Ya Rabb. Tashi yayi yana tafia kamar mai koyon tatata, wani Okada ya sauke wata mata, tsaidawa yayi kawai ya haye, a kan machine din yace "Goruba Road". Tafiya sukeyi duk iskan Machine dinnan bai zuwa mishi. Ana Kwanowa Unguwar su Yasmin zuciyarshi ta dinga mishi zugin zafi, daidai zuciyarshi ya dafe, so yake yayi kuka, ya kasa, bai san ta ina zai fara ba, mutanen da ya gani ya tabbata dai Yasmin ta mutu. Bai da kudin ba mai Machine, don daga shi sai shi ya fito, ganin bai cikin hayyacinshi mai Machine yayi tafiyarshi. Ko Minti daya Zaid baiyi ba da zuwa gurin Motar Baban Yasmin ya tsaya. A nan waje, ba a shiga ciki da ita ba, aka nadeta a cikin Likafani don ta riga ta dunkule ta kone ba batun wanka, a nan waje aka mata Sallah, aka tafi makabarta don kaita Makwancinta. A yayin da ake haka k'abarinta, Mallam ya fara tunatarwa. Mallam yace "Ya ku Al'ummar Musulmi muji tsoron Allah, Mutum ba komai bane, farat daya zaka wayi gari kajika a k'abari, ba ciwo, in ajali yayi kira ba makawa sai mun tafi, mu kasance masu tsoron Allah a duk inda muke, mu kuma roka Allah yasa mu samu kyakyawan k'arshe". Zaid yace "wallahi wallahi mutum ba komai bane ba". Mallam ya cigaba da tunasar wa da jan hankali, har aka rufe Yasmin, Zaid na daga gefe yana kallon komai kamar Film. Gida suka koma don karban gaisuwa kamar yanda akeyi, Yasmin tayi mutane kam ta ko ina zuwa ake gaisuwa. Mallam yace "DonAllah wani abu nagani yanzu a wayan wani bawan Allah, naga abun shi ake yayi yanzu, kamar jira ake mutum ya mutu, a yi ta yada hotunan mamaci, wasu ma har daukar gawa suke hoto su daura a kafafan sada zumunci ta yanar gizo, wallahi mu daina, hakan baida wani amfani, mu guji sanya hoton mamaci, ku bar mamaci ya huta, addua kadai mamaci ke bukata, sunfi bukatar ta fiye da komai yada hotunansu karin nauyi ne, donAllah mu gyara mu daina, na lura abunda ke faruwa kenan, in akwai wadanda suka saka hoton wannan mamaciar a daure a cire, a mata addua, kuna iya posting wance ta rasu a sata addua donAllah banda hoto". Kamar jira ake, da yawa suka ciri wayarsu suka cire hotunanta da suka saka a Status. Zaid dai na takure wuri daya, yana bin kowa da ido. Duk masu shiga yana kallonsu, masu fita ma haka. Katsina aka dawo da Er Rabi duk da bata san wake kanta ba, Asibiti Baban Yasmin ya umurta akaita don baison ta farfado da tashin hankali ta tada ma yan zaman makoki hankali. Aiko ta na farfadowa ta fasa Ihu, ta sake suman, su Hajia Shafa da mutanensu duk sun garzayo Asibiti wurin Bokanyarsu nan suke zaman makokinsu, duk da tana kwance kamar matatta, haka suke zuwa ganinta, ba wani dangi nata sai abokan shedanarta, tana cikin semi coma, Shafaatu ke karbar mata gaisuwar. Har bayan Isha'i Zaid na Gidansu K'amshi, da k'yar Dr Ali ya lallabashi ya maidashi Gida. Ya kaishi har dakinshi ya zaunar dashi ya bashi baki tare da shawartarshi da duk lokacin da ya tuna Kamshi ya mata addua. A B U J A. Wani Whatsapp group mai suna NationWide a ka turo BC. Idan Dalo ya kai ga *Dr Yasmin Hamza died @27* She was a Beautiful Doctor from General Hospital Kankia Katsina State.... Bata iya karasa karatun ba ta furta "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun". Mancy tace "Dalo mai ya faru?" Hawaye takeyi jikinta ko ina ba inda baya bari, tace "Mancy Aunty Yasmin ta rasu". Sanin wacece Yasmin tace "Meye? Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, ciwo tayi?". Dalo ka amsawa tayi. Da sauri ta rungumo tana lallashinta tare da shafa bayanta tace "ki ta Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, ki mata addua Sadiya". Dalo cikin kuka tace "Mancy.. Yaya. Yaya Zaid". K A T S I N A Ita fa ta tadashi dazun da safe wurin 9, tace "daga jin muryarka bakayi sallah ba, Allah ya shirya ka Zaid, nikam na tafi OR, zamuyi ma wani Yaro aiki zamu cire mai appendix, zamuyi CS ma ka min addua, in bangaji ba zan taho yau, in kuma nagaji sai gobe in Allah ya kaimu, ka kula da kanka, Be Happy". Ko tak bata bari yace ba fa ta kashe wayar, bai sake kira ba, bata sake kira ba. Tun daga ranar da ya fara ganinta a UK zuwa yau da yaji muryarta ya soma tunowa, yanda take Sonshi bai bace mai ba, yanda take daria bai bace mai a fuska ba, yanda take kiranshi bai manta ba, ya rasata wallahi rashi na har abada. Yanzu Yasmin ta rasu? Ta tafi? Ta barshi? Yasmin ta tafi kwatakwata, Ya Allah, mai son shi ta tafi? Wallahi da sonshi ta Rasu, bai taba furta mata so ba, bata taba fushi ba, ba ta taba gajia ba, bata taba kosawa ba, burinta daya, burinta ya ji dadi, burinta ya kasance cikin jin dadi, ta zabi farincikinshi a kan nata, shikenan ya rasa Masoyiya ta hakika, zai iya rantsewa ba zai taba samun mai mishi irin son Yasmin ba. Wayarshi ta yi vibrating, ya dauka jiki a mace. Dalo ce. Jiki a mace ya dauka " Dalo". Cikin Kuka tace "Yaya, Aunty Yasmin ta rasu dagaske?". Zaid ya hadiye bakin miyau mai daci da kyar yace "a gabana aka rufeta". Dalo ta fashe da kuka tace "Kayi Kuka?". Murmushi mai ciwo yayi yace "banyi ba Sadiya, na kasa". Cikin kuka tace "Kayi Kuka Yaya, cry it all out". Ta kashe wayar sakamakon wani kuka da ya ci karfinta. Shima Zaid din kamar jira yake a bashi umurninya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. "Yasmin, Yasmin, Allah ka yafe miki, halinki na gari ya biki, Allah ka yafe mata Allah ka yafe min nima". Abunda yake ta cewa kenan yana kuka, ji yayi kamar shima zai mutu sakamakon zafin da zuciyarsa ke mishi, bai san awanni nawa ya dauka yana kuka ba, bai son kukan da yake harda Majina ba, ba sauti, hawaye ne kawai, mai zaiyi? World zai sha? Allah shi kyauta ya sha World ranar da Yasmin ta rasu, Yasmin bata son yana sa ma cikinshi wuta kamar yanda take cewa, wallahi ya bari ma gabaki daya, ba zai kara ba, bai iya bari tana da rai ba, amma yanzu ya bari. *Mamaci baya son Kuka, kukan da kukeyi kuna k'ara ma mamaci nauyi ne* Maganar Mallam ta dazu da dawo mishi. Zumbur ya tashi ya fada toilet. Abunda bai taba yi ba yayi in yana cikin damuwa. Alwala. Alwala yayi ya na mai jin kunya ya fuskanci Alkibla don yin Sallah. Saboda bai iya tuna ranar da yayi raka'a biyu kacal ba farilla ba. Salloli yayi da baisan yawan su ba, shi dai ya san duk sujjada yana ma Yasmin Addua. E D O "Ga Labee Ga Labee" abunda manyansu da yaransu suke fada kenan. Gida mai dadi, wani farinciki da jin dadi ya mamaye zuciyanta, oyoyo ake ta mata, ta duba fuskokinsu don ganin damuwa, babu sai tsantsar farinciki dake fuskokinsu. Rungume Maminta tayi tana tambaya ko lafiyarta lau, Mami ta harareta tace na miki kama da mara lafia ne? Kai ta girgiza tace "Allah baki hakuri Mami" ta sake rungume Mahaifiyarta. To ko Abbanta ne? Da sauri ta nufi dakinshi, ganinshi zaune yana jiran isowarta ya sata nufarshi da gudunta, suna hada ido ta durkusa a gabanshi tana zuba mishi gaisuwa tare da adduoi, ya shafa kanta yace "Labiba wannan zuwan bazata haka? Ina Muhammadun?". Tayi daria tace "Lafia lau, gashi nan shigowa, suna waje da Su Yaya Ali". "Abbanmu kana lafia?" "Abbanku na lafia Labee, ya Mamarsu Amira da su Amira? Lafiya lau Abbanmu". Abba yace "ai banyi zaton yanzu Yayanku zai maido ki ba, na fi zaton sai kunyi hutu, ashe shima jira yake a bayar dake ya cireki". Labiba ta kalleshi da sauri tace "ya cireni a ina?". Abba yace "a makaranta mana, bikinku ai wata mai kamawa ne". Sallamar Baban Amira ya sa ta kallon Kofar ta inda zai shigo, sai yanzu abun ya zo mata, sai yanzu ta gane, kowa lafia, babu abunda ya faru a Edo, wayau Baban Amira ya mata, dawo da ita Gida Yayi, ya rabata daga Katsina". Be kalleta ba ya durk'usa a gaban Abbansu "Abbanmu barka da dare". Gaisawa sukayi sosai kafin yace "ashe kuna tafe". Labiba kallonshi kawai takeyi har sai da Baban yace "yaya dai Labee?". Baban Amira yace "tagaji ta sha hanya, tun asuba fa muka fito". Abbansu Yace "ai sai ki tashi kije kici abinci kiyi bacci ki huta". Idonta ya kawo ruwa ta tashi, ta fita, tana fita kuma ta watsake ganin danginta nata haba haba da ita. Samira ta janyota suka shiga dakinsu don a buga cikinta. Ga yayyin Samira da Mamarsu ana ta mata gyatsine, amma ita ko a jikinta, tsakaninta da Allah take son su. "Wai ke ina kika samo wannan?" Labiba tace "wa?" Tace "wanda suka zo rannan, wanda Abba ya ba su ke". Labiba ta dan zaro ido, har ta manta dashi". "Gayamana ina kuka hadu, naga masu kudi ne" Labiba ta harareta tace "ke kika sani". Tace "ko dai hadaku akayi?". Labee tace "ba wanda ya hadamu, shi ya ganni". Ta mike tsaye zata fita taji mamarsu Samira na cewa "ba a gaya mana inda aka samo shi, ko ba a so mu sani?". Chak Labiba ta tsaya tace "yo ai ba wani abu bane, Mama, Yaya kawata da muke karatu tare ne". "Wani aiki babanshi yakeyi?". Labiba tace "ban taba tambayarshi ba, ga numbernshi ko zaku nemeshi? Barin in je dakin Mami". Ta tashi ta fita. Ba su manta ba, ba su manta rashin kunyar Labiba ba, Samira da mamarta suka hada ido, suna mamakin rashin chanzawar Labiba. Haushi duk ya kama Labiba, ganin Yayanta ya yaudareta, aikam ita ba zata iya tsiya ba, komawa dakin Abbansu tayi ba kowata durkusa gabanshi. Yace "yadai baki kwanta ba?". Tace "Abba naji Labarin su Jawad da Babanshi sunzo, har ka sa bikin rana daya dana Samira". Abba ya murmusa yace "Eh Labee, raba bikin duk wahala ce". Tace "nifa Abba ba na son Jawad, hasali ma ban san sunzo ba". Daidai da shigowar Maminta Parlon. Abba ya muskuta yana kallonta. Labibarshi ce wacce bata barin abu a ranta, ko meye damuwarta zata fito dashi fili, bata nuk'u nuk'u". Maminta tace "tashi ki fita". Abba yace "taje ina? Magana muke, ina jinki Labee". Ko shakka babu tace "Abba, Zuwan Jawad biyu Katsina Yaya ya turo shi nan, nifa gaisawa mukeyi". Abba ya kalleta sosai yace "kira min Kowa". Fita tayi kanta tsaye, bata damu ba, gwara ta warware komai once and for all. Haka Abbansu yake, in yana da magana, baya ware 'yan daki ya musu magana,Iyalenshi ne, insani abu ya faru, zaunar da kowa yakeyi ya zartar da hukunci. Haka Labee ta dinga Kiransu har sai da aka cika Parlon. Baban Amira na shigowa gabanshi ya fadi, yasan wannan zaman Labiba ne. Kowa ya zauna Abba yace “Labiba, yi magana”. Numfashi ta ja tace “Abbanmu, Jawad Danuwan Aisha ne, mun hadu sanadiyar Aisha, yana kirana muna gaisawa har wata rana yace yana son zuwa Gida, na barshi yazo, a zuwa na biyu ne suka hadu da Yaya, shine fa ya turo su nan”. Abba ya saurareta da kyau yace “to naji haduwarku Labee, to sai me?”. Tace “Abbanmu Aure fa, ni gaskia son da nake mishi bana aure bane”. Yace “Me kike nufi Labee?”. Tace “Abba, a bar maganar Aurena da Jawad”. Abba yace “Labee har Babanshi ya zo Cikin Parlo na, har ince na bashi ke? Har in karba Sadakinki yanzu kuma kice a bar maganar aurenku, ki sani karamar magana? ai ba zai yiwu ba Labee, ki maza ki fara mishi irin Son Auren, ba zanyi karamar Magana ba?”. Labee tace “kayi hakuri Abbanmu, Auren dole kenan”. Mamarta tace “Labibaaaa”. Labiba tace “Abba aure ana so in anyi shi to zaayi zama na har abada, an fi so a aurar da Mace ga Zabinta”. Abba yace “kina da wanda kike so ne? Da sauri Baban Amira yace “Abba banso kowa yaji maganar nan ba, wani dan shayeshaye yake hure mata kunnuwa, wai shi take so”. Tuni ‘yan Parlo sun fara tofa albarkacin bakinsu. Abba yace “Labee, me nake ji? Dan shaye shaye kikeso?”. Tace “Abba tsaya kaji, ba yin kanshi bane wallahi, k’addara ce ta maida shi haka, amma ya bari Baban Amira kai ka san waye Zaid a da, kai ka san ba halinshi bane, akwai dalilin da ya sa yake haka, ku tsaya kuji Labarinshi”. Da alamu ta manta wa take ma magana. Maminta ta jefeta da chazbin hannunta. Shiru Labiba tayi. Yaya Ali yace “Sigari kadai Abdulfatah ke sha, kika ce baki taba sonshi ko wani mai shan sigari, amma yanzu kice ga wanda kike so dan Shaye Shaye ne, baki isa ba to, bikin ki tare da Samira gwara ki shirya”. Mamar Samira tace “Ku bar yarinya mana ta zabi wanda take so”. Ita gwara Labiba kar ta auri mai kudi a barta da watsatse shiyasa ta fadin haka. Ta k’i yarda ta hada ido da kowa ta ke cewa “Abba kai fa ka mana Alkawarin aura mana wanda muke so, kayi alkawarin ba za ka mana auren dole ba, haka ka ma yayyinmu da suka gabata”. Abba ya gyaran murya yace “tabbas nayi ma diyana Alkawarin ba zan musu auren dole ba, wanda kika kawo shi zaa aura miki madamar baya da matsala, amma Labiba ke matsalar ta ki daban ne, da ba dan Shaye shaye bane, da na je har Gidansu Jawad na bawa Mahaifin shi hakuri na maida musu sadakinsu, na jaddada musu hakuri, amma auren dan Shaye shaye akwai illa sosai”. Tace “Amma Abba..” Ya katseta ta hanyar cewa “Ya Isa Labee, da dai wani ne ba wannan ba, in ba ki son Jawad din sai na samu mahaifinshi kafin ayi auren ki hanaku zaman lafia, na san halinki in har baki so abu ba, da kuma in kika sa kanki abu, to kar kisa mutuncina ya zube a idon jamaa, maganin kar a fara, kar ayi, amma ko kin ki auren Jawad dinnan, ba zaki taba samun wannan da kike so ba, don ni da hankalina ba zan aura ma Diyana dan shayeshaye ba, nagama magana, duk ku tashi ku ban wuri”. Tuni hawaye sun wanke mata fuska, da gudu ta tashi ta fita daga parlon ta shige chan cikin dakin mamarta ta fada kan gado, kuka take sosai, zuciarta na mata zafi, haka daren ranan ta kwana kuka, Maminta na jinta tayi banza da ita don ta bata haushi sosai gaban mutane, ita ba a isa a gaya mata abu ta ji ba, sai abunda ta sa kanta tayi niyya. Washegari haka ta kasance sukuku jikinta duk yayi laasar, ba ta jin dadin Maminta da Yaya Muhammadu, kyararta suke da tsangwamarta, duk ta fice musu a rai, to ba dole ba, tunda ba isa a saka ko a hanata ba. Dakinsu Samira ta shiga nan ne take samun kwarin guiwan Samun Zaid don Mamar su Samira zugata takeyi kan ta nace ta dage sai Zaid, in ba ta auri wanda take so ba, zata dade tana nadama, ai ba zan yarda ba. Haka ta yini a dakinsu Samira suna mata famfo, ta san da biyu suke bata shawaran nan, don dai kar ta auri mai kudi. Zaid Fa?. K A T S I N A Jiya zaune ya kwana, bai kwanar Lafiya ba, baya da Lafia, jikinshi zafi sosai, massassara ce ta rufeshi, amma bai yarda ya kwanta ba, komai bai saka a cikinshi ba ya tafi Gidansu Yasmin , ji yake kamar zai ganta ta fito daga wani wuri, yanaso ace duk mafarki ne, wuri ya samu ya zauna, da yaji ance “ashe Yasmin lokaci yayi” sai ya fashe da kuka. Har wani abokin Baban yasmin ya nunashi yana tambayar shi waye wanchan? Ko danuwansu ne? Baban Yasmin ya kalli Zaid, ya yafito shi da hannu. Jiki a mace Zaid ya mike ya karaso su ya durkusa, daga inda ya durkusa suna iya jin hucin zafin jikinshi. Baban Yas yace “kai wannan ma baka da lafia”. Zaid ya murmusa yace “Ya k’arin Hakurin mu?”. Baban yace “hakuri sai maaiki, kai zan tambaya haka, ina kula da kai jiya kowa ya tafi ya barka, yau kam tunda kazo kake kuka, Mamarta bata dangi nasan baka cikinsu, ba kuma ka cikin dangina, yaya kuke da Yasmin?”. Gaban Zaid ya fadi, mai zai ce? Ya suke da ita? Zaice tana sonshi shikuma bai sonta? Wannan shine tsaka mai wuya”. Kasa amsashi yayi, abokin yace “kai ko Alhaji, ka san dai Mace ba a rabata da samari”.- Alhajin yace “hakane, ko kaine Zaidu?” Mai Zaid zaiyi? Ya fashe da kuka kawai, har babanta ya sanshi? Wani irinso take mishi?. Allah sarki Zaid ashe dole kake kuka,haka kurum Yasmin na min maganarka, Allah ka gafarta ma Yasmin” abokin ya amsa daAmin. Jiri Ke diban Zaid, da kyar yace “zan zauna”. Alhajin yace “aa ka tafi Asibiti, baka da Lafia”. Zaid yace “lafia na kalau”. Alhajin yace “ka zauna” Zaid ya koma chan wurin zamanshi a daddafe. Yana zaune sai ga Doctors na General hospital katsina sunzo mazansu da matansu. Gaban Baban suka gurfana. Suka ma juna gaisuwa. Dr Ali ya hango Zaid, ya karaso gunshi yana dafashi, da sauri ya janye hannunshi yace “Zaid you are sick”. Kallo daya Zaid ya mishi ya dauke ido. Zama yayi kusa dashi, yace “Zaid wallahi baka jin dadi”. Zaid cikin fada yace “Yasmin ce ta mutu, ta yaya zan ji dadi?”. “Ba haka nake nufi ba, baka da lafia” A takaice yace “Lafiata lau”. Shiru yayi be sake ce mishi komai ba. Drs sukayi mata Addua a bayyane suka tashi zasu tafi Baban Yas yace “DonAllah Drs ga dana chan ku duba min shi” Wasu sukace “me ya sameshi?”. Dr Ali yace “abokina ne, zan ganshi”. Zaid tashi muje Asibiti, bai mai gardama ba ya mike, ya kalli Baban Yasmin yace “zan dawo anjima”. Baban Yas yace “Yasmin ta yafe, ka dawo gobe”. Zaid bai yi magana ba ya tafi luu kamar zai fadi, sai da Dr Ali ya tallafo shi. Suka shiga Mota. “Gida zaka saukeni”. Ya fada cike da umurni. Dr Ali yace “Zaid” Yace “aa donAllah, banda karfin gardama kawai saukeni Gida”. Dr Ali bai ce komai ba ya nufa Gidansu Zaid. Tunda Zaid ya kwanta kan Gadonshi yake ji kamar ana sakko mishi da wani irin azaba, a hakarkarinshi da cikin cikimshi, wani irin tari yakeyi mai jini, ya na dafe kirjinshi, ga yunwar da ke cinshi, rabonshi da abinci, tun kafin yaji mutuwar Yas. Bai ma da karfin fita, haka dare ya riskeshi, yayi Sallah, Sallahr Isha’i ciwon ya lafa ya samu bacci.. Ita kam yau ta kasa bacci, karfe daya saura ta gani, cikin kayanta ta ciro wayarta, rabon da ta kunnashi tun Jiya, ta kunna. Ta shiga whatsapp. Besty dinta online tana tambayarta me ya sa yau bata je School ba? Tace mata ta zo Edo amma weekends zasu dawo, besty tace ta gaida Gida Labee ta tambayeta yaya jikin Baba? Ta amsa da ya ji sauki. Status ta shiga, ta ga Post din Soulmate wanda yayi 18seconds ago, da sauri ta bude. *Ya Allah ka gaffarta ma Yasmin, ka sa ta Huta, Allah ka yafe mata kurakuranta, I miss you Yas, alot*. Gaban Labiba ya yanke ya fadi, wace Yasmin ta rasu? Wacce? Jikinta na rawa yana bari, ta dialling number Zaid kamar jira yake ringing daya ya dauka. Ya na dauka tace “Wace Yasmin ta rasu, donAllah ba Aunty Yasmin ba”. Zaid yace “Ta rasu Beebs, Yasmin ta rasu” ya fashe da wani irin kuka da ya sa Labiba Kuka. Tace “na shiga Uku, inallilahi wa ina ilaihirrajiun, Ya Allah, ta rasu? Ya Rabb, me ya sameta?Shekaran jiya fa mintinmu Arbain muna waya”. Yace “Accident fa, Motar ta ci da wuta, Wuta ya kasheta Beebs,”. Tace “Alhamdulilah, tayi shahada, da wanda Gini ya fado mishi, da wanda aka kashe, da wanda wuta ta kashehi, da wanda” bai bari ta kai aya ba yace “nasani Beebs, na sani, Allah ka karbi shahadarta”. Wani sabon Kuka ya sake, ta san yanda yake son Yasmin, ta san yana cikin tashin hankali, jibtake kamar tayi tsuntsuwa ta duro katsina, ta lalasheshi tace “How are you now?”. Kusan da sauri kamar jira yake a tambayeshi yace “Beebbs i am not fine, i am Sick Wallahi, beebs ina ji cikin jikina i am dying”. Hankalinta ya tashi, tace “in maka addua?” Kamar yaro k’arami yace “ki min Addua”. Hawaye take sharewa tace “ka dafe inda ke maka ciwo” Da sauri ya dafe saitin zuciyarshi yace “na dafe”. Tace “bismillahi Bismillahi Allahumma La Sahla illa ma ja’altahu sahla, wa anta taj alal hazana iza shi’ita sahala”. So bakwai ta maimaita mai. Tace “kayi hakuri, zakaji sauki kaji?”. Yace “ki kwanta” Tace “To, in ka kasa bacci ka tashi kayi sallah ka rokar mata Yafiya gurin Allah, shi ta fi bukata kaji? Banda kuka, ka min Alkawarin ba zaka sake kuka ba”. Yace “Beebs, ba na mata kuka mai sauti, ba zanyi magana ba kuma, amma Yasmin ce, yau kwananta biyu a k’abari”. Labiba ta rufe baki sakamakon wani kuka da ya ci karfinta,tace “bye” ta kashe wayar. Tana aje wayar ta fashe da wani irin Kuka mai tsuna zucia, Yasmin ta rasu, Allahu Akbar, Allah mai yanda yaso, Allah mai rayyukan mutane, duk lokacin da ya bukaceka sai kaje, shekaran jiya ta kirata fa, sun dade a waya har ta kosa Yasmin din ta kashe wayar don ta gaji da waya da ita maganganun da suka ba Labiba haushi a lokacin da take gaya mata su suka soma dawo mata *ki So Zaid da duk wani abun da kike dashi, da zuciyarki da jikinki, da ruhinki, ki soshi, ki kuma kula dashi* Ta fada haka yafi so goma, ashe maganarsu ta karshe kenan? Ashe wasiyya ma ce kenan? Ya Allah, bata san Yasmin da dadewa ba, amma ta san tana da kirki sosai. Tashi tayi ta dauro Alwala ta hau Sallah har karfe ukun dare, sosai ta ma Yasmin Addua. Kasa bacci sukayi su duka, Labiba tace bari muga ko yayi bacci, kiranshi tayi a waya, ya dauka, a lokacin wani tari yake mai karfi, ya dauka beebs, muryarshi taji tace “ka fara bacci ne?”. A wahalce yace “aa beebs” “Ya naji muryarka haka?.” Yace “bani jin dadi, i naji kamar zan mutu, tarin Jinina ya karu”. Da dan karfi tace “tarin jini? Wani irin tarin jini?” A ranshi yace ashe bata sani ba, kafin yace wani abu wayarshi ta mutu Low battery. Labiba ta kira ta kira kamar tayi ihu wayarshi kashe, nadamar duk wani abun da ya sa ta biyo Mallam Muhammadu Edo, da bata biyo shi ba da yanzu tana gefen Zaid, hankalinta kacokam yayi gun Zaid, jikinta duk ya mutu, me zatayi? Ta rasa abunyi. Shi kuma ciwo yafi karfinshi ya sheme a daki yana jin ciwo ko ina a jikinsa. Baccin da baizo idon Labiba ba kenan, zuciyrta ta gama yanke mata hukunci, katsina Zataje, katsina zata, ko biyar bata da shi. Abunda bata taba yi ba tunda uwata ta haifeta yau tayi, Sata. To sata ne mana tunda ba bata akayi ba, ma’ajiyar Maminta ta bude ta dauka naira dubu biyar. Asubar Fari ta faki ido, ta fita, daga ita sai side bag, ko tsoro bata ji ba, ta tsaida Okada tace a kaita Tasha. #1love #DM #anatare #FWASonSo #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉 BABI NA TALATIN 3⃣0⃣ (FASA K'WAI 🥚) (YAFIYA🤗) (FARINCIKI😃) Zaid ya runtse ido hawayenshi na fita, yace "Beebbs ina sonki da duk wani numfashin da nake ja ina saki, na san kina sona, ba sai kin sadaukar min da ranki ba, ba sai kin min haka ba, beebs donAllah ki bari, na rok'eki da Allah". Labiba ta kyafta idanuwanta so biyu tace "Ina Sonka Sabida Allah, abin Alfahari na ne ace yau akwai ni a jikinka, in Allah ya sa an dace, zamu rayu tare, in ba haka ba, zamu mutu tare". Yace "kinsan hakan na nufin kin kashe kanki da kanki, kinsan hukuncin wanda ya kashe kanshi?". "Ni ba haka nake nufi ba, Allahn da rai na ke hannunsa ya san Zucia na, ya san niyyata, zaa dibi Hanta ta a dasa maka, end of discussion ". Kyaleta yayi ya runtse ido tare da juya mata baya, gwalo ta mishi tare da maida hankalinta kan k'ofar da aka turo. Dr Habib ne, Dr Ali yace "za a tura kudin Surgery account din Asibiti before a shiga da shi Operation Room". Labiba ta dan kalleshi tace "Ohh, I thought Government Hospital ne, gwamnati ba ta biya ba?". Dr Habib ya kalleta, yana son Confidence dinta yace "Gwamnati na dai tallafawa, amma ai ana biyan Aiki, ba kamar private hospital ba, sosai ba zaki hada kudin da na chan ba, akwai sauk'i rangwame sosai". Tace "Okay nawa ne?". Yace "ga takardan nan kije bursary department, ki basu zasu baki bank details da transaction slip ki biya sai ki kaima cashier ta baki receipt dai ki kawo mana". Zaid na jinsu yayi lamo, hankalinshi ya dan kwanta, ya san bata da kudin da zata biya, ko da 20k ne balle ya san sai ya fi. Direct chan ta nufa da taimakon sign boards. Ta bada slip din, a computer akayi danne danne aka mata printing. Expenses din naira dubu dari uku da saba'in. Gaban Labiba yayi mugun sarawa. Chabda, in ba a biya kudin nan ba zata iya rasa Zaid ko? Aikam ba zata iya jure rashinshi ba, ya kama ko meye zatayi don ta samo kudin nan, dakin Ta koma hankalinta a dan tashe. "Kanaji ba?". Banza yayi ya kyaleta. Tace "Masoyin, na fa san ba bacci kake ba". Ya juyo fuska daure yace "Meye?". Tace "Wai kudin Aikin 370k". Yace "Alhamdulilah, your Liver is safe". Tashi tayi tace "kayi ka gama, zan je neman taimako". Yace "Ina? Tace ko ma ina ne, ko bara ne i will do it, but ganin bamu da time zan rok'a su mana bashi zamu biyasu". Zaid kallonta kawai yakeyi, sonta na tsaga hantarshi mai ciwo, komai nata na burgeshi, wautarta na kayatar dashi. Cikin wasa yace "ke kika aje su da zasu miki aiki Kyauta? Ohh bashi kika ce ko? Tsoron ki sukeji Ko?". Ganin yana son maida abun wasa tace "ka yi ka gama, banda lokacin wannan yanzu barin je in ga Dr Ali". Har ta kai gaban k'ofa ta choge ta tsaya, mai ta tuna oho, maida kofar tayi ta rufe ta dawo cikin Dakin Zaid na kallonta. Mai take shirin yi? Wayarshi ta dauko ta kunna, har tayi 19%. Har gabanshi ta tako ta dauki yatsarshi ta dangwala a wurin thumbprint wayar ta bude. Hoto yaga ta daukeshi kusan guda uku, kafin ta dauki takardan hannunta hoto. Kallon Mamaki yake binta dashi. Matsawa tayi dan gefe amma yana kallonta taka danne danne a wayarshi. Baayi minti 3 ba yaji wayar tayi ringing. Amsawa yaga tayi ta sa wayar a Kunne. Tana jin muryar ta san hankalimta a tashe yake "Hello? Zaid meya sameka? Me ya faru?". Labiba ta amsa a ladabce "Assalam Alaikum Mancy, Sunana Labiba Ahmad Dakata". Da sauri Zaid yayi yunkurin tashi amma ya kasa. Mancy tace "wacece ke? Me ya samu Zaid? Ina yake?" Labiba tace "Ya na bukatar Emergency Open Liver Transplant Surgery". Kusan da karfi Mancy tace "Lahaula wa la kuwatta illa billah, Zaid din? Me ya sameshi haka?Liver Transplant fa kikace" Labiba tace "Emergency ne,Hantarshi ya fara damage, suna so a cire infected area a saka wani, an samu donor, amma ba a samu kudin Aikin ba". Da sauri Mancy tace "DonAllah zan kiraki, Ina zuwa". Mancy ta kashe wayar ta fita,dalo ta bi bayanta. Wai Beebs ke baa gaya miki magana kiji? Ba kya jin maganata ko? Ba a isa a hanaki abu ba ko?". Kulle idonta ta tayi ta bude, murya ta sassauta tace "ya kake so ayi?". Shima ya saukar da murya yace "kar ki wahalar da kanki, ki bar Hantarki, Hanta fa ba kamar k'oda bane, aka samu matsala, akwai yiwuwar daga ni har ke babu mai tsira". Tace "to ai yafi nayi ta zaman jiran gawan shanu, yafi ace na zauna banyi komai ba, yafi ace na kasa taimaka ma wanda nikeso, donAllah mu bar maganar nan, Mancy tace zata kirani". Zaid yace "Beebs ba kya jin magana". Ta murmusa tare da mikewa don amsa kiran Mancy tace "nima ina sonka". Harara ya galla mata ta fits tana daria. Alhaji Abu Shamsu ya karbi wayar yana magana da Labiba, itama Office din da ta bar Dr Ali da Dr Habib ta nufa, ta ba Dr wayar, nan ya ma Alhaji Abu Shamsu bayani, da cewar an samu Donor wani bawan Allah, kamar yanda Labiba tacr musu su ce. Alhaji Abu yayi ma Dr Ali Transfer din kudin, tare da basu go ahead din yin aikin. Hankalin Mancy da Dalo ya kasa kwancia, sun kasa daurewa sai kuka suke, Alhaji Abu yace "Ku shirya ku bi jirgi gobe, sai Jawad ya rakaku". Mancy ta dan ji sanyi, don gobe da sassafe zasu tafi, duk nadama ta mata katutu, bata ganin laifin kowa sai nata, itace sila, da bata barsu a Kt ba, da baiyi shaye shaye ba, da bai jama kanshi cuttutikan zamani ba, laifinta ne, in ta rasa Zaid yanzu bata san ya zatayi ba. Alhaji Abu ya cigaba da kwantar mata da hankali yace "InshaAllah komai zai wuce, zai warke, Allah zai tada kafudunshi. Bayan an gama komai ance su shirya kasancewar taci Abinci shima yaci suka kara 5hrs kafin su yi aikin, sai gab da Asuba zaayi aikin. Zaid ya dan runtsa, ita kam ta fito waje. Zama tayi kan kujera tana tunani. Tsoro ya dan kamata, data ga dai dagasken aikin zaayi, ba zata fasa abunda tayi niyya ba, ba kuma tayi nadaman zuwa katsina ba, amma In bata rayu ba bayan aikin? Ya kenan? In ta mutu fa? Iyayenta fa, ya kamata ta nemi yafiyarsu, gwara su san halin da take ciki k'ila adduarsu ta bita. Da sauri ta kunna wayarta ta ga messages da yawa bata bude ko daya ba, ta shiga create message ta hau typing, tana yi tana kuka, ta kusa daukan minti talatin tana yi kafin tayi marking ta tura ma Maminta da Abbansu. Sai da ta tabbatar sun shiga kafin ta kashe wayar. E D O Cirko Cirko sukayi, Mami har tayi kuka ta gode Allah, ba wanda bai zo ba, kowa tambayar kanshi yake ina Labee ta shige. Da yawa sun zata kidnapping Labiba akayi, Amma kidnapping har gida? Ko ta fita baa sani bane suka ganta suka sace, maganganu kala kala dai, kowa da abunda yake sak'awa. Message ya shigo ma Abbansu lokacin wayar na hannun Abba yana amsa gaisuwar jaje da ake kira ana mishi. Da dan murna mai sauti yace "Labee Ce, Labee ta yi sak'o". Tuni aka yayyabeshi aka zagaye shi kowa na son jin meye a cikin message din. Abba bai yi boko ba amma ya iya karatun hausa da k'arfi ya fara karanta message din *"Abbanmu da Maminmu, zan fara da neman yafiyanku, ku yafe min don Girma da darajan Allah, kar kuyi fushi dani, ku saka min Albarka danAllah Abbanmu da Maminmu, yanzu kuce Allah ya miki Albarka Labee" Abba ya kalli Mamin a tare suka ce "Allah ya miki Albarka Labee". Abba ya cigaba da karantawa *kunce? Yauwa".* *"Allah ne shaida, kun min tarbiya kun nuna min So amma na muku laifi babba, na fita bata da saninku ba, nayi abunda mutane da yawa zasuyi tunanin banda mafada ne ko banda magayanmasu min fada, na manta da halin da zaku shiga, na tsallake na fita, na san hankalinku dole ya tashi, to wallahi ina Katsina, eh fa Katsina na zo ni daya".* Nan duka parlorn suka dau sallalami. Ja'ira ashe Katsina ta tafi. *"Kuyi hakuri, kuce Allah ya shiryaki Labee" Abbansu ya girgiza kai cike da takaicinta yace "Ya Allah ka shiryaki Labee" ya cigaba da karantawa "yauwa kunce?".* *"To, Wallahi Abbanmu, nazo Katsina naga Zaid baya da lafia, bansan yanda zan muku bayani ba, amma wallahi baida lafia sosai, Hantarshi ta baci shine ake neman wanda zai taimaka a diba nashi a dasa a nashi, shine ba a samu wanda zai bashi ba, shine fa nace a diba nawa".* A tare suka "Lah Illah ha illallah Muhammadan rasulillahi sallalahu alayhi wa salam". Mamin wani jiri taji ya debeta. Da kyar Abban ya iya mik'a ma Yaya Haruna wayar ya cigaba daga inda ya tsaya. *Gabanku ya fadi? "DonAllah kuce Inalillahi wa ina ilaihir rajiun*". *donAllah kuyi hakuri, bansan me zanyi bane, taimakon da zan iya mishi kenan, ku sakani a addua, bansan ko zan tashi ba bayan aikin, bansan ko zan rayu ba, shiyasa nace barin sanar daku, ku sanyani a addua, in akwai abunda nafi yarda dashi a rayuwan nan wallahi be wuce Adduarku ba, ku min Addua Iyayena, in na mutu ku yafe min ku sanya min Albarka, in kuma Allah ya sa na rayu in na dawo ku hukuntani wallahi, zan dauka, ni din mai laifi ce* *"Mami wallahi dubu biyar dinki na dauka, nidai wallahi karki ce sata ne, amma dai ki yafe min, in Allah ya sa na warke, na fara aiki zaki fi kowa jin dadi a rayuwa, zan zame miki abin alfahari, kuce ma Baban Amira yayi hakuri ya yafe min, na bashin ciwon kai da yawa, Mami in mamansu Samira na miki fada ki daina mata shiru, in samira ta miki rashin kunya ki mareta, in Yaya Zaliha ta haihu ta samu mace kice a sanya mata Labiba, ace kar ta zama kamar goggonta, ta rayu da kyau, haha kamar ina bada wasiyya ko? ba fa wasiyya bace, zan dawo inshaAllah, nasan Mami zaki gurji rayuwata da dorina zaki bugeni? Ina sonki, donAllah kar hankalinku ya tashi, ku mana addua, Allah ya sa a dace, karfe 4am zaayi aikin, addua donAllah, kar ku manta, a gaida min su Samira, ina son su duka, Abbanmu Maminmu, kuce Allah ya miki Albarka Labee".* Kafin a kai karshen Wasikar, an kira layin wayar kashe, masu raunin zuciya tuni suka fara kuka, barin ma Samira da ke kuka wiwi kamar an ce mata Labeen ta mutu, sai da Abbansu ya tsawatar, yace "kai ku kwashi iyalanku ku koma gidajenku, ku kuma ku wuce ku kwanta". Ba wanda ya iya cewa komai aka fara fita daya bayan daya. Yaya Hajara wanda mamarsu daya da Labiba ta rik'o hannun Mami ta jata zuwa dakinta. Mami ta ci kuka sosai, ranar batayi bacci ba tana kan dardumarta tana kai kukanta ga sarki mai Sama, Allah ya raya mata diyarta ya kareta a duk inda take. K A T S I N A 4:40am Batayi bacci ba itama, Zaid dinne yayi gyangyadi ya farka, har nurses suka shigo dauke da kayan da ake ba marasa lafia su saka in zaa musu aiki. Labiba ta amsa Zaid ya mata Alama da ta zo taji. Matsowa tayi da kunnenta daidai bakinshi. Yace "beebbs, kina da halin chanza hukuncinki, kina da halin cewa kin fasa, ki chanza tunani kafin ki makara". Labiba tayi murmushi tace "ni dai na gama magana, ina kan bakata". Zaid ya girgiza kai yace "Allah ya shiryaki mai taurin kan tsiya". Daria tayi sosai tace "Nima ina sonka Masoyi". Ta shige toilet. Jim kadan Labiba ta fito daga toilet sanye da kayan theater, murmushi tayi data ga an chanza ma Zaid irin kayan sunyi anko, gadon gefe da aka tanada don ita ta hau, nurses kam suka gungura Zaid da Labiba a kan Gado zuwa Operation Room. Kowacce Adduar da yazo bakin Labiba yi takeyi. A cikin OR idanunsu akan junansu bacci ya kwashesu sakamakon allurar da aka musu ta Drs suka dukufa kansu suka farka su sukayi duk wani abunda suke bukata cikin kwarewa kafin suka dinkesu. A zahirance aikin ya tafi daidia, zaace it's successful sai a jirayi farfadowansu.. %%^^ Ana Sallahr Asuba Mutanen Edo suka shiga Mota, Baban Amira ne da Abbansu da Mami, da an biye ma Mutanen Gidan, sai kowa ya bisu, Maminma da k'yar Abbansu ya yarda ta biyosu, wani tsohon direban Abbansu ke tuka motar a Golf din Abbansu. Su ko mutanen Abuja karfe 9 jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Kano, daga Mancy sai Dalo sai Jawad, Abba yace in basu dawo zuwa jibi ba zasu biyosu. Da suka isa Kano Yaya Usman Yayan Mancy ya zo ya dauke su a Airport. Sai da suka biya Gidanshi kafin ya ba Driver Mota ya kawo su Katsina basu tsaya ko ina ba Sai General Hospital. Ba su sha wuya ba suka gano Dakin da aka kai Zaid da Labiba bayan am fito da su daga OR. Basu farfado ba nurse ta sanar dasu. Mancy tace "DonAllah zan shiga in ganshi". Nurse tace "da dai kin bari sun farfado". Mancy ta matsa, nurse ta bata umurnin shiga ita kadai, tana shiga ko ta saka kuka ganin yanda Zaid yake kwance lifeless, gefenshi ta kalla ta ga wata yarinya kyakyawa kwance itama a dayan gadon. Mancy sosai ta ke jin haushin kanta, ba zata daina jin laifinta bane, itace sila, itace ummul abaisin shigan Zaid wannan yanayi, da bata barsu ba, da bai tagayyara ba haka, da kyar ta iya fita daga dakin. Ta dawo inda su Dalo da Jawad ke tsaye. Jawad yace "Mancy muje Gidan Uncle Usman muyi Sallah mu ci Abinci, in yaso sai mu dawo Anjima". Mancy ta girgiza kai tace "Aa Jawad, bana jin zan iya tafiya na bar Zaid, zan jira ya farfado, ka tafi da Sadiya". Dalo ta mak'e kafada tace "zan jira farfadowan Yaya Zaid". Jawad yace "To bari naje Gidan, zan taho da Abinci, naga famfo chan kuyi Alwalla kuyi Sallah, sai na dawo". *** Hudu ne a Gidan Hajia Er Rabi don yi mata gaisuwan Yasmin. Ya shiga Parlon yana ta tafka uban Sallama, muryoyi yake ji amma zai rantse ba na Mutane bane. Tashi yayi zai fita yaji an daka mai tsawa. "Hudu, Shafa'atu ta tarwatsa min farincikina, Shafa'atu ta sa na rasa Farincikina, wallahi sai ta gwammace bata shigo duniyan nan ba, sai tayi nadamar sani na, ta jirani kawai". Yanayin yanda ake maganar ya sa Hudu fita gidan a Guje fitsari na bin wandonshi. Yanda ya koma Gida hankali a tashe ya tabbatar musu cewa ba lafia, Shafa'atu tace "Wai Hudu uban me ya sameka? na lura tunda ka so danne Dalo ka fita hayyacinka, duk ka zama wani lusari, barinje Jifatu na dawo". Ya bita da ido, Annah ta galla mai harara ta wuce dakinta. Yafi minti 10 zaune kafin ya tashi ya nufa dakin Alhaji Zaki. Dakin yaji a kulle, sai ya fada dakin Yayarshi. Direct Wardrobe dinta ya nufa. Ya bude yan kunne da sarkanta zinari ya kwashe kusan set 4 ya zurasu a wando. Yayi 'yan bincike bicinkenshi duk abunda ya gani wanda zai kawo mishi kudi sai da ya dauke, kudi kau ya kwashe tas kusan 200k. Ya samo leda ya cikashi da karikitai ya fita. Ya fita jikinshi na bari. Ya hadu da Anna, tace "Uncle Hudu ina zaka da kayan Mummy?". Banza yayi ya k'yaleta, tayi saurin rikoshi, ya juya ya mareta tare da sake mata nushi a ciki dama ya dade yana jin haushinta. Tana kaiwa kasa ya fita a guje, maigadi na mai magana yayi banza dashi, saarshi daya ya ci karo da dan Achaba a kofar Gida ya hau yace "muje kawai". ** Shafa'atu ta shigo gidan a fusace sakamakon kiran da Annah ta mata tana ambaton sunan Hudu. "Wallahi Hudu kace zaka ma Annah Tumasancin da kakeyi sai naci ubanka, in wannan tsohuwar ta kyaleka ni ba zan kyaleka ba, ina Hudun yake?". Annah da ke rik'e da kumatunta ta na kuka tace "Mommy Uncle Hudu ya kwashe miki kaya, duba dakinki ki gani". Hankali tashe ta shiga dakin kamar zata kife, maajiyarta ta gani a hargitse, ta dubata ga babu kudinta, babu zinarints, babu duk abubuwa masu mahimmanci, wani ihun sunanshi tayi "Huduuuuuu, ni zaka ma Sata? Wallahi sai na kasheka". Wayarshi ta shiga nema tana kiranshi amma baa dauka ba, daga karshe taji wayar a kashe. Sosai hankalinta ya tashi domin tas Hudu ya yasheta, bata da komai a dakin, huci take kamar kura cikin fushi tace wallahi ko birnin sin kaje, sai na sa Er Rabi ta dawo min da kai, shege butulu mara godian Allah". Garin zai bari, zai je ta fara rayuwa inda ba wanda yasanshi. Bank ya nufa ya ciro kudi kafinya wuce Tasha ya hau Motar Kano. A kano ya sayar da sark'okinshi a wulakance a wurare daban daban.v Jawad ya dawo Asibitin wurin k'arfe 3 da coolern Abinci. Zaune ya ga Mancy kan wata tabaarman da bai san inda ta sa mota ba, Dalo kuma na kwance kan cinyarta. Jawad yace "Bai farfado ba? Mancy ta gyada kai alamin eh, yace "to ga Abinci kuci, Antisco na gaidaku tace "inshaAllah in mutane sun ragu zata zo ganinshi". Mancy murmushin karfin hali tayi tace "Yaya jikin Uncle Usman din?". Jawad yace "ah da sauki yace ran Monday zai fara Azuminshi". Tace "Allah ya k'ara Sauk'i". Yace "Ameen, wai wannan barci take?". Mancy tace "Eh bacci takeyi". Tsugunno yayi kusa da ita a hankali yace "Sadyy, tashi ki ci Abinci". Bude ido tayi ta zube kanshi. Mancy tace "Oya tashi kuje chan ki ci Abinci kinji Dalo?" Baki ta turi cike da Shagwabab ta tashi. Jawad yace "Mancy ke fa?" Tace "Jawad, wallahi ba zan iya ba, bari dai Zaid din ya tashi". Jawad ya kada kai ya bi bayan Dalo da ta fita daga Amenity zuwa wani wuri da aka tanada don fira. Yace "Oya zuba kici" Dalo ta shagwabe fuska tace nifab na k'oshi, banson Mancy tayi magana ne kawai amma wallahi banjin yunwa". Hararta yayi yace "baki isa ba". Ya bude coolers din ya zuzzuba mata a plate yace "Eat". Zata yi magana ya sha mur yace "ina wasa dake? Ki cinye duka ko na miki dure". Shagwabe fuska tayi tace "Ya Jawad ba fa haka akeyi ba". Ya harareta yace "haka akeyi, eat up". Murmushi tayi ta sa hannu tana cin abincin, shi ko Jawad kallonta kawai yake yana mamakin yanda yake sakewa gabanta. Sai da yayi Sallahr Laasar kafin ya shiga Asibitin. Suma zaune suke kan tabarma, Dr da nurses suka ga sun nufo dakin da Gudu. Mancy tayi saurin mikewa ta rufa musu baya. Tana shiga ta ga idonshi a kan nata "Alhamdulilah Zaidu na ka farfado". Ta nufeshi da sauri ta rungume yana a kwance ta shiga kissing dinshi cikin jin dadi, Dalo ma ta rukunkume yayanta tana kuka. Shidai yana kwance yana binsu da ido. Nurse tace kuyi a hankali kar ku fama mishi aikin da akayii. A galabaice yake kallonsu, ya ma Dr Ali ido da yazo yaji Dr Ali ya matsa tare da daura kunnenshi saitin bakinshi. A wahalce yace "Labibaaa". Dr yace "Sorry bata farfado ba, Alluran bai saketa ba". Mancy ta kalli Labiba da ke kwance kamar Matatta takawa ta farayi zuwa gadonta tace "wai itace ta yi donating Liver dinta?" Dr Ali yace "Eh itace, ta damu jiyan nan har sai da dai aka yi Aikin nan". Dalo ta matso wurin tace "Lahh Mancy, k'anwar Mallam Muhammad ne". Mancy tace "Wa?". Dalo tace "Makwabcinmu, Mijin Aseeyah". Mancy tace "yana da kanwa ne?". Dalo tace "eh daga garinsu ta zo karatu ne". Jin haka ya sa Jawad yin sauri zuwa gadon idonshi ya gane mishi Labiba. Gabanshi ya fadi, yayi saurin kallon Zaid da yake kallon gadon amma baya iya komai, ya hango hawaye kwance a idon Zaid. Jawad yaji jiri na dibanshi. Da bango ya jingina. Mancy tace "Dr, akwai wanda yazo gunta?". Dr yace "anya kuwa babu fa". Mancy tace "to ya haka?" Chan ta mik'e tsaye tace "ko dai ba su sani ba? Kar dai yarinyar nan ta bada Hantarta ba btare da sanin Magabatanta ba?". Dr ya k'ara da cewa "Gaskia bana tunanin sun sani, ita kadai tazo jiya, ta sha kuka, ta kuma nace kan sai anyi aikin cikin gaggawa, nikuma gaskia i had no choice saboda i was desperate to help my friend recover, shiyasa mukayi operating kanta". Mancy tace "Without consulting her Parent or Guardian? Is this how you do things here?".m Ganin Ran Mancy ya baci ya sa Dr Ali yace "Sorry, amma she's an adult, ita ta zabi hakan". Mancy tace "Dubeta Yarinya ce fa, banji dadi ba gaskia sam". Dr Ali ya ma Nurses ido suka fita shima ya sabe don ya saba dokar Asibiti. Mancy tace "Sadiya zo kije Gidan Mallam Muhammadu donAllah kice yazo Asibiti, kira Drivern, no ba time ki hau keke napep". Sadiya tace "to ta fita". Mancy ta rik'o hannun Labiba tana jin Son Labiba na ratsa duk wani bargo na jikinta. Zaid kam baida karfin yin komai,hawaye kawai ke sintiri a idanunshi. Dr Ali ya sa nurses maida Zaid Amenity tunda ya farfado, aka gungurashi kan Gado aka bar Labiba a ICU. Dalo ta bi gadon Zaid. Mancy kam ta tsaya tana leken Labiba ta window don ba a so ana shiga ICU. Jawad kam bai san mai ke mishi dadi ba. Duk wani karonsu da Zaid ya shiga dawo mai, sai yanzu ya gane, ashe Son juna suke? Ashe kishinshi Zaid yake in ya ganshi da Labiba yayi ta wasu abubuwa." Itama Labibar, Wani irin so take mishi haka? Da zata sadaukar mishi da rayuwanta. Haaa ga matar da zai aura kwance magashiyan rai hannun Allah, matar da zai aura ta ba Saurayi Hantarta, saurayin ma wani bashi ba? Lallai akwai matsala, akwai babbar Matsala". Yana ganin wucewar Dalo, ya kasa binta domin jikinshi yayi sanyi sosai. *** Sadiya ta isa Anguwarsu, ta dade tana kallon Gidansu, kafin ta shige Gidan Mallam Muhammadu da Sallama. Aunty Aseey ta fito da Amsa sallamar tana wata kamar Dalo. Dalo ta murmusa suka gaisa. Tace "ya Abuja? Ance kin koma chan". Dalo tace "Eh,Aunty Aseey Baban Amira fa?". Tace "yana chan Edo fa". Ta yi shiru, da dukkan alama ba su san meke faruwa ba. Aunty Aseeyah tace "Lafia kuwa?". Dalo tace "Mancy ce ta aiko ni, Labiba na Kwance a Asibiti". Aunty Aseey tace "wace Labibar?". Dalo tace "Labiba taku". "Ban fa gane ba, Labibar mu ai tana Edo". "Aa ta na nan, a Asibiti, an mata operation". Cikin rashin gamsuwa tace "tsaya kiga na kira miki ita". Aunty Aseey ta kira number Labiba tajita kashe, tace "barin kira baban Amiran". Da kyar ta sameshi. Yana dauka suka gaisa tace "Ina Labiba wayar ta be shiga". Yace "Afuwan Asiya, ban kiraki ba, gamu nan a hanya, inshaAllaj kafin Maghrib mun iso Katsina". Tace "kai da wa? Da Labiba?" Yace "Aa, da su Abba da Mami". Tace "Labibar fa?". Tana jin karaya a muryarshi yace "Asiya Labiba na nan Katsina, sai munzo zakiji komai". Aunty Asiya ta kalli dalo, ta amince da maganarta tace "ga Dalo nan tazo wai Labiba na Asibiti wai har operation an mata, meke faruwa Baban Amira? Dama Labiban bata da Lafia?". Da sauri yace "Wai har anyi? Wani Asibitin ne?" Ta tambayi dalo, tace "General Hospital". Yace "Ga mu nan InshaAllah sai munzo". Ya kashe waya. Aunty Aseey tace "me ya faru da Labeen? Menene?". Dalo ta warware mata zare da abawa. Da gudu da shiga daki ta fizgo Hijabinta ta ciro mukullan gida tace "Muje, dalo muje". Tace "Yaran fa? In sun dawo?" Tace "muje in sun ga gida kulle sa shiga makwabta, inallilahi Allah ka tashi kafadar Labiba, wallahi Labiba bataji". Ita dai Sadiya bata tofa komai ba suka hau Napep suka nufa Asibiti Suna Isa Asibitin Mancy ta rungume Aunty Aseeyah. Ta window aka nuna mata Labiba Kuka take tace "Wallahi Aunty Maryam Labiba bata jin magana, babu yanda ba ayi ta rabu da Dan makaho ba amma ta ki ji, daga Edo fa ta saci hanya tazo, zataci ubanta na sani, bari su Abbanmu su zo". Mancy dai yak'en dole takeyi, ta na jin yanda ake kyamar danta kamar wani mai najasa, da alamun Asiya ta manta wacece ita a wurin Zaid da batayi wasu zancen ba. Mancy tace "ni in ga ta farfado ya fi man komai, ta farfado ko meye zai biyo baya". Suna zaune jigum jigum. Gidan Kakansu Jawad ya wuce, bayan sun gaisa ta tambayeshi sanadiyar zuwa, ko wannan karon ma budurwa aka zo gani, dan tsaki yayi yace "wace budurwa? Yaron Auntynmu akayi ma Aiki dashen Hanta, shine na rakosu, Abba bai kiraku ba? Suna General a ICU be san surutu ya shige chan k'urya yana ta fira da zuciyarshi. Kakar tashi ta kira Abba ya kara mata bayani, haka tayi ta kiraye kirayen wayan 'yanuwa ta na cewa suje su dubo Dan Mancy a Asibiti. Da yawa 'yan Anguwan Alk'ali sunje ganin Zaid amma an hanasu ganinshi saboda yau ya fito daga OR, zasu iya stressing dinshi, saidai su gaisa da Mancy, su koma, sosai su ka ma Mancy kara a matsayinta na matar danuwansu. ** Antisco da Aisha sunzo, ta kawo musu Babban Darduma da Basket din Abinci suka shimfida daga Waje don baa zama a cikin ICU. Mancy tace "ai da baki wahala ba Antisco, wanda Jawad ya kawo dazun da saura, ya jikin Uncle dinsu". Antisco tace "haba ai ba wani abu, ke dai Allah ya basu Lafia". Aisha tace "Aunty Aseey, me kike yi a nan, waye be lafia?". Aunty Aseey dai cikinta ya duri ruwa bata iya cewa komai ba. Antisco tace "kin santa ne?" Aisha tace "Lah, matar yayan besty ce" Antisco tace "Ah haba, Allah sarki, Mancy surikarki ce, kanwarsu Jawad zai aura". Gaban Mancy ya fadi tace "Labiba Jawad ke So?". Antisco tace "kin ma san Labiba kenan,ah Lallai Jawad baya jin kunya ya baki labarin budurwarshi?". Mancy ta girgiza kai tace "na shiga uku na, dazun Jawad naga ya fita rai bace, ashe dalili kenan?". Antisco tace "me ya faru da Jawad?". Mancy tace "Antisco, Matar da Jawad zai aura, ita taba Zaid Hantarta aka diba aka dasa mai". Aisha tace "Kaiii, Labiba ta ba danki Hanta? Ina ta sanshi Mancy?". Ikon Allah. Mancy dai bata sake magana ba, Aishar ma haka, ba wanda ma dai ya sake cewa komai. Anty Aseey ta rafka uban tagumi tana jiran isowarsu Mijinta. Har su Antisco suka karashi zamansu suka yi musu Sallama tare da tabbatar musu da cewa zasu dawo gobe. Tafiyarsu Antisco ba dadewa ba Mutanen Edo suka iso, kasancewar suna wajen ICU yasa basu sha wahalar ganesu ba. Su ka k'araso. Aunty Aseey ta rik'o hannun Mami saboda da kyar take tafia kafarta ta kumbura sosai saboda zaman Mota, sai sannu Aunty Aseey ke jero ma surukarta. Ko ba a fada ba ansan Mamin Labiba ta sha kuka. Mancy kamar ta goya su sai gaisuwa take kwasa. Yaya Muhammadu yace "Hajia ashe kina nan, ina Labibar?". Mancy tace "kuyi hakuri bata farfado ba". Mami tace "Labiba ta mutu ko?" Mancy tace "aa wallahi, allurar ce bata saketa ba". Mami tace "amma shi dan naki ya farfado?". Mancy cike da kunya tace "eh ya farfado". Abba yace "muje mu ganta". Lokacin Visiting ya wuce wai ba zasu barmu mu shiga ba. Baba Muhammadu yace bari na ma security magana. Da kyar aka samu ya bari suka shiga da niyyar suna ganinta zasu fito. Mami ko sai da tayi magana ta na kuka tace "Labiba in kin Tafi na yafe miki, wallahi na yafe miki, Allah ya rahamsheki, in kuma baki tafi ba Allah ya tashi kafadunki, Zuciyar Mami na zafi, ki tashi ki lallasheni, kice Mami zuciyar ta bar Zafi haka nan ga ki nan, donAllah". Da kyar Baban Amira ya fitar da ita ganin kuka take sosai. Abba yace "Labiba kin san dai Dukkan nan sai kin sha shi ko? Ki tashi in zaneki, ki tashi hakan nan". Ganin shima kukan zaiyi ya sa shi fita da sauri. Mancy tace "Sannunku kun sha Hanya, ku zauna donAllah ku ci Abinci gashi nan". Yaya Muhammad yace "Mami kiyi hakuri ki zauna ki ci Abinci" Mami ta kauda kai. Mancy da durkusa a kan guiwowinta tace "ba dan ni ba, kiyi hakuri donAllah, laifi laifina ne da banzo da wuri ba, wallahi da ina nan ba zan taba yarda a bude diyarki har a diba wani sassa na jikinta ba, donAllah Mama kiyi hakuri, dole ranki ya baci, donAllah kiyi hakuri ki ci Abinci". Abba yace "ashe mutum be san ya dauki k'addara ba? To ko cewa akayi Labeen ta mutu ne? Amina bani son dogon zance, zauna ga Abinci kici". Zama tayi, Abba ya zauna, Yaya Muhammadu ya zauna, sai kanenshi Hamza shima ya zauna. Jikina rawa Mancy ta bude cooler din Abincin Gidan Auntisco ta zuzzuba musu Faten Dankali da Shinkafa. Ko wanne ta kai mishi gabansh, tayi serving dinsu. Ta ja hannun Dalo suka wuce chan Amenity dakin da Zaid yake. Sun gama cin Abinci Abba yace "muje mu gano shi Masoyin Labeen". Fit Mami tace "ba inda zani". Abbansu yace "kinga Amina ki shafa ma zuciyarki salama, to in Allah yace lokacin Labiba yayi kumburin da kike shi zai maidota? Ke baki san kaddara ba, maimakon ki ta rokon Allah ya bata lafia ya tashi kafadunta kin tsaya kina fushi? Har kina ma da lokackn Riko? Haba itama kinga hankalinta ba kwance yake ba, danta na chan shi kadai, amma ta na nan zaune gun diyarki har sai da mukazo, wallahi ki natsu". Nasiha ya mata kafin ta yarda zataje ta ga Zaid. ** Zaid na ganin Mancy yace "ta farfado?" Mancy ta girgiza kai cike da tsoro. Rufe ido yayi kawai ya kawar da kai. A ranshi yana fata in mutuwa Labiba tayi Allah ya dauki ran shi, ba zai iya rayuwa babu ita ba". Mancy na ganinsu ta mik'e tana taba Zaid, Zaid bude idonka kaga Baban Labiba ne da Mamarta. A hankali Zaid ya bude idanunshi, yana ganinsu yayi yunkurin tashi Abban ya maidashi, yace "ka adana k'arfinka, zaka buk'aceshi". Zaid yace "donAllah kuyi hakuri, laifi na ne, wallahi laifi na ne, Labiba batayi komai ba, nine mai laifi, ni zaku hukunta, ni zakuyi fushi da, Labiba batayi komai ba". Mami ta ji son Zaid da tausayinshi, tace "inshaAllah zata farfado, kayi hakuri". Ba su k'ara minti Uku ba aka gunguro gadon Labiba. Duk suka mik'e suka tarbesu. Ta farfado, daga kallon fuskarsu kasan suna matukar farinciki. Kwance fa take ba ta wani k'arfin kuzari tace "Ina Zaid? Yaya jikinshi, Dr yace ya farfado, yana ina". Da dukkan alamu sambatu ne, bata san su waye ke kanta ba. Mami ta kalleta sosai, kallon da take mata in tayi laifi. Kamar zata gudu tace "Lahh, Maminmu, kiyi hakuri kar ki bugeni, wallahi aiki aka min yanzun na farfado". Daria ta ba Mami, Mami tace "Allah ya baki lafia Labee, sai na miki dukan tsiya, bari dai ki warke". Labee ta turo baki tace "kuyi hakuri". Nurse tace "haba Mama, ya kuna haka ne? Daga farfadowanta kun fara sa ta kuka? Abeg ku fita visiting ya kare sai gobe kuma". Haka nurse ta tarkata su ta kora waje. Mancy ta dawo wai tayi mantuwa, ta duka kan Labiba ta na murmushi tace mata "In maminki ta gama dukanki nima zan miki nawa, waya ce miki ana satan hanya a zo gun saurayi? Kika bashi Hantarki? Da icce zamu bigeki". Ta durkusa ta manna mata kiss a goshi tare da gyara mata kwancia zuwa gefen Damarta. Mancy na kaucewa idonta ya fada kan na Zaid da ya tsura mata ido, wani Sonta na cizgarshi. Nurse ta gama duba ruwa da jinin hannun Labiba, kafin ta fita ta barsu su biyu cikin daki irin na mutum biyu daya. Lumshe ido sukayi a tare Zaid yace "kin wahala ko?". Ta murmura tace "aa ba wahala, kai fa?". Yace "Sannu Kinji". Tace "Nagode" Yace " for what?". Tace "for Staying alive, nagode daka warke, ina ma Allah Godia da ka rayu". Zaid yaji hawaye na zuwa mishi, wannan wani irin So take mishi, like yanzu fa ta samu kanta ta farfado amma she's still worried about him. Murmushi yayi yace "focus and recovering and take that beating from Mami". Ta marairaice fuska tace "Zaka karbar min Bulala?." Yace "aa gaskia, bulala fa na kine, ke za a zane, ni meye nawa na shisigi? Kawai ki karbi bulalanki da kanki kizo muci gaba da gashi". Tace "yanzu Masoyi ba zaka iya tsayawa a dakeka mai makon ni ba?". Zaid ya girgiza kai yace "Nope". Tace "waiyo heartbreak, let me just die now". Ya wani zaburo yayi saurin komawa sakamakon zafin da yaji gefen na mishi, ya cije baki, ta na lura dashi. Yace "Kar ki sake, kinsan how worried you got me? Labiba da baki farfado ba, da bansan ya zanyi ba". Ya kalli Sama yace "Allah kar ka barni da iyawata ban iya komai ba, Allah ka bar min Labiba". Tace "Ameen Masoyi". Yace "Ina Sonki". Tace "Ina sonka Masoyi". Soyayyarsu suke zabgawa a gadon Asibiti, ba su da wata damuwa. Su ko Darduman Waje suka zauna suna dan fira jefi jefi. 0000000000 Tun da garin Allah ya waye take surkullenta. Wani k'ok'o ta dauka ta fita dashi a hannunta, ta kira aljannarta da ke binciko mata abunda take so tace "je duba man kiga ina Dan Makaho yake?". Ko minti daya batayi ba ta sanar da ita cewa Dan Makaho na Asibiti kwance. Hankalinta ya tashi "kar fa ya mutu, diyarta bata mutu ba don shima ya mutu, dole ya rayu ya ji dadi kamar yanda Yasmin ta mishi fata, ta manta rayuwa ba a hanunta yake ba. *** Tun da ya dawo take mishi mitan Hudu, bai ji dadi ba sam, hakuri yake bata yana cewa kar ta damu, zai siya mata sabbi, chan sai taga yayi shiru tare dafe kanshi, wani irin Ja Idonshi keyi, zufa ke keto ma Alhaji Ali Zaki kamar yana dakin Gidan Biredi. "Alhaji baka lafia? Tashi mu tafi Asibiti" Bai iya ce mata komai ba ya tashi ya fita ta bi bayanshi, Annah ma ta bisu a baya. Mota su ka shiga, har yanzu kwakwalwarshi juyawa take yana ganin abubuwan da suka faru kamar film. Tuni ya fara tari ba k'ak'autawa, ganin ya amayo wani K'aton dutsi ya sa Hajia Shafa'atu kara gudun motarta don ta tsorata sosai. Sai sannu suke jero mishi ita da Annah. General Hospital suka nufa. Emergency suka nufa. Fitowar su kenan suka hango Er Rabi da ke tunkarosu ta kallesu daya bayan daya. Shafa'atu tace "Er Rabi ina kika shiga tun jiya wayarki bata shiga , Daddyn Annah na kawo Asibiti baya jin dadi". Cike da umurni tace musu "ku biyoni". Tayi gaba rungume da k'ok'onta a kirji, tafia sukayi a k'afa har Amenity ba wanda ya tambayeta din me kamar ta rufe musu baki. A bakin k'ofar ta gansu zaune da alamun Sallahr Isha'i suka idar. Mancy da Dalo na ganinsu suka mike tsaye. Alhaji Ali yayi saurin durkusar da kai , Shafa'atu kuma na ma kawarta ido don me suka zo nan?. Er Rabi tace "Yauwa, nayi farincikin ganinku a nan, ni da na zo gurin Zaid na fasa k'wai ashe kuna nan". Shafa'atu ta tabo kawarta. "Menene? Bangane ba Er Rabi, me ke faruwa ne?". Er Rabi ta murmusa tace ina Zaid? Ina so komai zaayi a gabanshi?". Mancy a dan tsorace tace "me ya faru? Zaid na kwance bai lafia an mishi Surgery, menene?". Er Rabi tace "Kwai zan fasa, zan tona ma Shafaatu Asiri kuma zan tona ma kaina Asiri, ni dinnan nan da kuke gani, bokanya ce ni". Mamin Labiba da Aunty Aseeyah suka saurin mik'ewa cike da tsoro. Baban Muhammadu da Abbansu ma suka mik'e Er Rabi tace "duk kuyi mun shiru, kar wanda yayi katse man magana". Kamar ta sa kwado ta rufe musu baki ba wanda ya iya magana, duk wanda yayi yunkurin magana sai ya ji ya kasa da alamu siddabarun ta musu ta fara magana. "Sunana Hajia Er Rabi, ke Maryama kinsanni." Ta kalli Alhaji Ali tace "A yau Zan fasa k'wai, Matarka Shafcy bata da Aminiyar da ta wuceni, bayan ka mata kishiya, ta haihu ka so danka fiye da kowa da komai, bayan ka saketa, na kaita wurin wani bokana, baban Annah kenan". Annah ta gwalalo ido. Er Rabi ta harareta tace "Eh Babanki Boka ne, babanki shi yace ta dawo bayan shekara Sha biyar zata samu Alhaji Ali Zaki, zata juya shi yanda take so, ba zai mata gardama ba, zata mallakeshi amma sai bayan Shekara 15, bayan shekara 15 ta dawo Dakinta sakamakon Asirin da baban Annah ya tafka, shiyasa a ranar da ta dawo gida aka ma Maryama Sakin Wulakanci, ya juya ma 'ya'yanshi baya sai abunda tace yakeyi, ta rabaka da Danginka da komai sai abunda tace kake so". Shafa'atu so take tayi ihu, so take ta sa Er Rabi yin shiru, me yasa take mata haka? Meyasa take tona mata Asiri?" Gashi ta kasa ko da motsi, Er Rabi ta kafe su, ta sa sun k'ame k'am. Alhaji Ali Fitsari yaji kawai na zuwa mishi ta k'afa. Mancy da Dalo kam hawaye ke kwaranyowa daga idanuwansu. Sauran kam sai zare idanuwa suke. Er Rabi ta cigaba "Ni ba wannan bane damuwa na, damuwa na shine Zaid, zuwa nayi na rok'eshi gafara na kuma cika burin marigayiya Diyata da ina jin ta fi son Zaid a kaina, Sonshi take har ta koma ga Allah, har ta mutu tana rok'ona na kare mata Zaid, na tayata sonshi, ta na so na kula mata dashi, ta na son Zaid, ni kuma ina son abunda Diyata take so, yau na fasa k'wai, zan kuma zare hannuna daga duk wani abunda zai sa Zaid din Yasmin ya cutu ko wani masoyinshi". Er Rabi ta fasa k'ok'on hannunta wani bak'in ruwa da k'adangare suka fito daga ciki. Er Rabi ta kalli Sama tace "Yasmin... kinji dadi? Na cika miki burinki". Er Rabi ta kalli Shafa tace "Dalilinki na rasa diyata, dalilina duniyarki zata juya". Ta wuce ta k'yallesu chan suka fara motsi. Aunty Aseey tace "K'urungus k'aryar 6era ta k'are". Shafa'atu ta ja hannun Annah da gudu suka shige Mota babu wanda ya kulasu. Alhaji Dakata ya musu nuni da su koma ciki, Mamin Labiba da Aunty Aseey suka matsa gefe don ba su wuri tare da barin Alhaji Ali, Mancy da Dalo kamar ba su da lakka a jiki. Alhaji Ali ya kalli Dalo da rinannun idanuwanshi yace "Sadiya, Ina Zaid?". Dalo ta fashe da kuka ta rungumo Babanta. Kamar jira yake ya fashe da kuka. "Baba nayi kewanka". Baba yace "Darlingg". Sadiya tace "Ba darling ba dalo". Cikin hawaye suke daria. Baba ya kalli Mancy zuciyarshi yaji kamar zata tarwatse. Yana son Matarshi sosai, Shafa'atu ta rabashi da ita har tayi wani auren. Yace "Maryam, yaya kike?". Mancy kasa magana tayi tana cin kuka. Ina Zaid? Yana ina? A zo a diba Hantata a bashi, in ma Zuciyata za a sa mishi, a cire nawa a samishi donAllah, ku ceci yarona, ina son mishi magana". Mancy na kuka tace "Baban Zaid, an riga anyi Surgery din, Zaid na nan ya farfado, nurses ne suka koromu wai sai gobe". Baba yace "ku kaini wurinshi donAllah". Da kyar aka barshi ya shiga. Yana bude kofar ya hada ido da Zaid. Kallo daya Zaid ya mishi ya hango k'auna, soyayya, nadama, ban hakuri a ciki. Baba kuwa karasawa yayi gadon Labiba, kamar zai fashe da kuka yace "Sannu ko? Sannu, Allah ya baki lafia". Labiba tace "Ameen nagode". Baba yace "kin gode? Da me? Ki bari kawai yarinya, Kiyi shiru donAllah". Labiba ta bishi da ido har ya karasa gadon Zaid. Dafa goshin Zaid yayi yace "Sannu, me ke maka ciwo?" Da tsantsan mamaki Zaid yake kallon babanshi yace "babu komai, ban dai da karfi". Baba yace "dama karfi ba yau ba, yau fa akayi aikin, dole kaji kasala, sannu". Zaid kai ya daga, Baba ya kallesu a tare yace "Ku warke da wuri kunji". Kai suka sake dagawa. Ya fita. Labiba ta ja dogon numfashi tace "I think this is actually your Father, he is back". Zaid da ma ya rasa abunyi yace "Wannan shine baba na, tabbas, Allah Nagode".' Ya na fita ya ci karo da Mancy ta na waya, da alamu da Mijinta suke waya don ya dan ji maganar samasama inda take cewa "Goben zaka taho? To Allah ya tsare min kai ya kawo min kai Lafia Mijina". Dam ya ji gabanshi ya fadi wani abu ya sokeshi a zuciya. Tana waigowa ya kirkiro murmushi. "Sannunku, kun sha fama". Murmushi kawai yayi. Ya wuceta ya nufa Gunsu Alhaji Dakata, Sallama ya musu ya mika ma Abbansu hannu kamar zai durkusa, Abban Labiba duk tausayinshi ya kamashi. Ba abunda Alhaji Zaki yake sai zuba Godia yana gode musu. Kan darduman suka zazzauna. Alhaji dakata yace to ai dare nayi, ba zamu ta zama a nan ba, Muhammadu dauki matarka ku wuce Gida, yaranku na chan na zaman makwafta". Baban Amira yace "to Baba da wai ni na kwana da Labiba, ai ba a barsu su biyu a Asibiti ba". Alhaji Dakata yace "aa sam, ni da Maminku zamu kwana, kai dai ka dauki Matarka da Haruna". Alhaji Ali yace "Aa Alhaji, ya zaayi ka kwana? Mallam Muhammadun ya kwana". Mancy tace "aa duk ni zan kwana duk ku tafi masauki". Aunty Aseey tace "Mami muje Gida". Mami tace "ni zan kwana gidanki?". Aunty Asy tace "Mami lalura ce, ni bama ki taba zuwa Gidana ba". Mami tace "ba kuma zanzo ba ehe". Daria sukayi, wai ita bata zuwa gidan danta na fari. Dalo ta rada ma Babanta a kunne "Baba daga Edo State suke, ba su da inda zasu kwana". Alhaji Ali yace "to Abunda Za ayi, Shi Muhammadu ya tafi da Matarshi gida, Alhaji da Hajia ku tafi Masauki, Hajia Maryama kema ki tafi Masauki, Asibiti ne, ICU baa jinya, amma yana da kyau wani ya tsaya a nan". Baban Amira yace "Ni zan kwana". Mancy tace "Aa fa ni zan kwana da yarana". Alhaji Ali yace "kin tambayi Mijinki? Ba zaki kwana ba gaskia". Be jira amsar kowa ba ya matsa gefe, yana waya ya dan jima yana waya kafin ya dawo. Cikin Mintuna da ba su wuce 20 ba Motoci 3 suka zo harabar Amenity. Alhaji Ali yace "Alhaji ga Mota chan, Driver zai kaiku Masauki Please, kuje chan ku huta, gobe da safe zai maidoku". Zasuyi gardama Baban Amira yace "donAllah Abbanmu kuje ku huta, kun sha tafia". Abba yace to shikenan Muhammadu muje ka bude mota ka bamu kayanmu" Mami tace "Sai da safenku". Mancy tace "to mungode kwarai". Alhaji Ahmad Yayi gaba Matarshi na binshi a baya. Alhaji Ali ya kalli Yaya Haruna yace "kaima bisu, akwai wurin kwananka" da sauri ko ya bisu. Ya kalli Dalo yace "ku ina zaku kwana?". Dalo tace "Baba in zo muje Gida?". Kallonta yayi, beyi mamaki ba don ta nemi izinin binshi Gida. Yace "Dalo kizo muje Gida". Mancy ta mata ido, alamun kar taje, har ta manta abunda Hudu ya so mata? Ga Shafa'atu. Dalo tace "kar ki damu Mancy, Babana zai kareta daga sharrinsu". Alhaji Ali ya kawar da zancen yace "Dalo ki raka Mamarki Masaukinta, driver zai kawo ki Gida, kuje da Matar Muhammadu". Ba tare da ya kalli Mancy ba yace da Baban Amira "Sai da Safenku". Mancy ta masu Sallama suka shige dayar Motar ita da Dalo da Aunty Aseey. Suka tafi Gidan Uncle Usman, gidan Antisco. Baban Amira ya gunguro Motarsu ya kawota gaban Asibiti, Alhaji Zaki kuma ya fada Dayar Motar driver ya ja, suna fita daga Asibitin baki daya ya fashe da wani irin Kuka. Yafi 1hour yana rike kukanshi, yafi 1hour yana son kukaye bakincikinshi, yafi 1hour daya yana son samun salama ta hanyar kuka. Driver ya dan tsorata yace "Alhaji" Alhaji ya goge hawayenshi yace "ka hau Machine ka tafi Gidanka" driver ya bi umurni. Da ya tuna abunda ya ma yaranshi shekaru kusan 4 da suka wuce sai ya fashe da kuka mai tsuma zucia. Shafa'atu itace ta rabashi da dukkan wani farincikin shi, sai da yayi kuka son ranshi kamar wani dan k'aramin yaro kafin ya ja Mota don isa gida kafin Dalo taje ta iske baya nan. ***** Bata da damuwa don ta san aikin da Mallam ya mata ba zai taba karyewa ba, ta yaya ma zai karye? Don Er Rabi ta yi barazanar fasa wata er k'ok'o sai ta tsorata ta karaya? Haba dai, Aikin da akayi shekara 15 ana yinshi? Ai bata da haufi har yanzu Alhaji Ali na bayan tafin kafarta zata takashi ta murje hannunshi ba tare da komai ya faru ba. Ita ba komai ya bata haushi ya bata mata rai ba irin yanda Hajia Er Rabi ta tona mata asiri gaban mutane, yanda Diyarta ta tsareta da tambayar in ita diyar bokace, ita Er Rabi zata ma haka? Aiko zatayi mugun nadama, don wallahi sai tayi maganinta. Yana isa Gida yaga Motar Shafa'atu. Lallai matar nan bata da kunya, mai ta dawo yi? Ko kayanta tazo kwashewa?". Tsayawa yayi a bukka yana jiran Zuwan Dalo, kusan 20 minutes sai ga ta ta iso Driver ya sauketa. Ta shigo tace "Baba ya baka shiga ciki ba?" Ya murmusa yace "ke nake jira" Tace "to mu shiga". Yace "ina Matar Muhammadu?". Tace "ta shiga dayan gidanchan kwaso yaranta". Baba yace "Halimattus Sadiya". Dalo ta kalleshi da sauri, da wayonta bata zaton ya taba kiranta da sunan nan. Yace "Baba Mutumin Banza ne ko? Kin tsani Baba ko?" Da sauri ta rufe mishi baki tace "Baba donAllah kar ka fara, kar ka fara". Yace "Sadiya, ban kasance Uba nagari a gareku ba, na wofintar daku, na fiffita bare a kanku, na zabi wasu a kanku, na laanceku, na zalunceku, kuyi hakuri, ku yafe ma tsohon banzan nan". Dalo na kuka tace "Haba Baba, meye haka kakeyi? Wallahi wallahi ban taba tsanarka ba a rayuwata, kai Mahaifinmu ne, mun son kai mai son mune, kar ka bari komai ya tsaya maka a rai, mun san komai da ya faru ba yin kanka bane, asiri gaskia ne, yayi tasiri a kanka, wallahi ko kadan ban rikeka a rai ba ko a da, na dauka hakan kamar fim ne a shafin rayuwata, fim din kuma ya kare, Babana ya fi na kowa kuma ina sonshi fiye da kowa". Ta ja hannunshi suka shige Gida ba tare da barinshi yayi magana ba. Suna shiga Gidan suka ga Shafa'atu zaune kan kujera tana karkada k'afa. Tana ganinsu ta mik'e tsaye. "Alhaji wani irin iskanci ne zaka dade a waje kuma yanzu ka dauki Sadiya? Uwar me zata mana? Ba ta koma gun uwarta ba". Wani Mari da ya mata ta rantse taga taurari kusan dari lokaci daya. Cikin k'unanrai yace "baki da kunya Shafa'atu, kunya bata isheki ba, har kina iya dawowa Gidana?". A tsorace da fargaban da zuciyarta bata gama aminta dashi ba tace "ni zaka mara? Nan ba gidan aurena bane? Ina zani!". Yace "Ke Jahila ce wallahi, to in sai na miki gwari gwari, daga lokacin da Asirinki ya tonu, aure ya kare tsakaninmu, ki fitar min daga Gida". Aiko da sauri ta fita, ina ta ga ta zama? Ai chan zata nemo hatsabibin boka ya kashe mata Er Rabi, ya mallake mata Alhaji Ali, ba zata dawo gidan nan ba, sai ta mallake Alhaji Ali kaf dinshi". Bata bi ta kan Annah ba da ke ta kwala mata kira. Annah ko ta dinga binta kamar Jela. ^****^ Jawad kam tun da ya bar Asibitin bai koma ba, a daren rannan ya yanke ma kanshi hukuncin rabuwa da Labiba. Aure? Ba zai iya aurenta ba ma, bayan ya san ga wanda take so, ai babu ma maganar aure, ba zai yiwu ace ya aureta amma zuciyarta da ruhinta suna wurin waninsa, gwara ya barta ta auri wanda take so, shima Allah ya hadashi da nashi, Allah ya hada kowa da rabonshi. A Gidan Er Rabi. Sam ya shiga dakin Uwargijiyarshi don yaji ta shiru, kwance ya ganta shameshame kan carpet kumfa na fita daga bakinta. Ga wani magani a hannunta cikin er kwalba da alamu maganin ta sha. Ajali ne yazo? Kashe kanta tayi? Lokacinta ne yayi? Allahu Aalam, ba wanda ya san mai ya kashe Er Rabi.m Shi dai Sam ya bude Wardrobe dinta ya dau abunda zai dauka ya cika wa bujenshi iska. Bayan Barinsu Gidan Alhaji Ali, Gidan k'awarta Hajia Clean suka tafi, ta gaya mata yanda Er Rabi taci amanarta, Hajia Clean tace karki damu, ni ai bana zuwa ma Er Rabi da matsalata, ina da bokana aikinshi kamar yankan wuka ne" donAllah muje ki rakani". Tace "ki bari gari ya waye, dare yayi fa". Tace "aa wallahi, da zafizafi ake bugun karfe, so nake na ci uban kowa wallahi". Tace "kina da kudi?" Tace "ina dashi a account". Tace "kwaso su tas, yanda zai miki aiki da kyau". Tace "Annah ta zauna a nan, zataje ta dawo". ATM tayi ta zari makudan kudin a bankinta, tas ta kwashe kudin. Ta koma gida Hajia Clean. Hajia Clean ta dauketa suka hau kauye chan gaba da Ajiwa. Boka sarkin k'arya har bayan kwana sukayi wai yana aiki sai wurin karfe 12 na safe ya gama aikin, sai da ya karbe mata kudinta, ya bata wata 'yar hoda yace da ta shafa shi gaban goshin Alhaji Ali Zaki to ko kisa kika ce yayi sai yayi. Da murna suka koma. ..... A daren Jiya Alhaji Ali baiyi bacci ba, zuciyarshi zafi take, zai iya rantsewa ya kamu da hawan Jini. Da farar Safiya aka kawo musu breakfast, Alhaji Ali ya umurci Dalo da tayi wanka zasu fita. Bayan tayi wanka suka fita hannu rike da juna. Gidan Mahaifanshi ya fara zuwa. Da mamaki aka dinga zuwa daki daki aka tada masu bacci aka sanar dasu ga Yaya Ali yazo. Nan da nan gida ya kaure da Yaya Ali ya dawo garesu, cikin lokaci k'alilan, dangi duk suka zo gidan, don yin barka. Alhaji Ali ya ba 'yanuwanshi Labarin abunda ya faru. Su Aunty furera sai da sukayi kukan jin dadi suka dinga tsine ma shafaatu. "Wallahi Yaya da Police station ka sa aka kulleta, Shedaniya ce, barin irinsu masifa ne". Yace "Bakomi, Allah zai mana Sakayya". Ya nemi gafararsu suka ce bai musu komai ha, tunda ba yin kanshi bane. Ya dade tare da Danginshi, ina zaa saka dashi da dalo akeyi, kowa na son ya burgeshi, nan da nan aka fara cika cooler don zuaa ganin Zaid ya gaya musu Zaid baiji dadi ba, suna ta yabon Zaid don yana zagayowa jefi jefi. Nan aka sanar dashi Mijin Mariya diyar kanwar Mamarsu ya rasu. Da mamaki yace "Mariya tayi Aure?" Shiru sukayi, basu manta wulakancin da ya musu ba da sukaje neman taimako suna so ai mata kayan daki. "Kai Kai, Allah ya tsine miki Shafaatu, ban yafe miki ba, kin shiga tsakanina da Yanuwana, Allah ya mana sakayya suka amsa da Amin". Zuwa sukayi suka mata gaisuwa, Goggonshi ta kebe dashi tace "Mariya ta kusa fita takaba, in kana so ka nemeta". Alhaji Ali yayi saurin kallon Dalo. Dalo tayi daria tace "Allah Baba ka aureta, ai Aunty Mariya mai kyau ce". Ya harareta, bai dai ce komai ba. Goggo tace "Mariya na da hankali, da kuruciyarta, ko shekara 34 bata yi ba, yaruwarka ce, tun da kai ka ki auren zumunci, amma yanzu shi zamu maka, ko ka ki ko ka so". Yayi daria yace "Ban ma k'i ba ina so". Tayi daria tace ja'iri. Bai bar Family house ba sai da aka kawo mus trailer na kayan abinci, ko wani gida sun samu buhu uku uku na shinkafa da kwalayen taliya, jarkan mai, har ta ashanar da zasu kunna sai da aka kawo ***** Mancy ta iso Asibitin dauke da breakfast wanda Antisco tayi, bayan sun gaisa tace ya masu jiki, Baban Amira yace "ah jiki da sauki". Ta kallesu tare da murmusawa bacci suke gabaki dayansu". Tace "Mallam Muhammadu ka tafi gida kayi wanka, zan zauna dasu". Yace "to ya tafi Mancy ta zauna ta jira har farkawansu". Suka gaisheta Labiba tace zata shiga toilet Mancy ce ta taimaka mata har toilet, ta dawo da ita, ta basu breakfast, ta ba Zaid na shi ta hada ma Labiba tea ta na bata a baki, kunya duk ta kama Labiba. Zaid kam yaji dadin yanda ya gansu. Ta isa Gidan maigadi yace ai sun fita, Asibiti ta nufa bata ga kowa ba sai Mancy. Mancy tsoro ya kamata. Kar ta musu wani abu, waya ta kira Sadiya tace "ina Babanta? Ga Shafaatu nan tazo". Aiko dalo na gaya ma Baba suka nufo Asibiti a sittin. #1love #DM #anatare #SonSoFWA #nagode Biebee Isa [14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉 💃🏻AURE 💍 K'ARSHE Zaid ya kalleta yace "me kike yi a nan?". Tace "ashe baka mutu ba, naji haushi". Yace "Ki fita daga dakin nan". Shafaatu tace "Ubanka nike jira yazo, in yazo sai na tabbatar da ba zaku sake ganinshi a rayuwarku ba". Mancy tace "Ashe abunda kika min da 'ya'yana bai isheki ba?" Shafaatu tace "kar ki sake ki dameni, bari zan jira shi a waje". Mancy ta basu labarin abunda ya faru jiya da daddare sosai sukayi Al ajabi. Sai ko gasu sun iso da danginshi kusan su 12. Tana ganinshi ta warwaro Powder din ta nufeshi gadan gadan zata shafa mai a goshi. Tuni K'anin Alhaji Zaki ya tande mata k'afa ta fadi k'asa, kamar jira suke suka fara dukkanta Mazansu da Matansu, ko wannensu na fanshe bakincikin da suka k'unsa sanadiyarta. Ihu takeyi sosai. Tuni sun mata Habo baki ya kumbura ido ya kumbura jini ta baki, ita burinta ta shafa mai Powdern nan a ka. Rirriketa sukayi Alhaji Ali ya tako gabanta yace "Tsakanina dake sai Allah ya isa, ba abunda zance miki, sai tsinuwar Allah su tabbata a kanki, Allah ya saka mana tun a duniya, da ni da yarana ba zamu taba yafe miki ba, Allah ya sa ki wulakanta ki kask'anta anan dunia, Allah ya isa, mai sama mai kowa mai komai zai mana maganinki". Wani daria ta fashe dashi wanda duk wanda yaji ya san bana lafia bane. Chan sai taji muryan Mallaminta Baban Annah yace "ba na ce karki hada aikina da nakowa ba? Karshenki yazo". Kamar an kunna mata battery ta fashe da daria "Hahahah, Alhajina, ni ce fa Matarka Shafaatu, ka manta ka tsani Dan makaho, ka tsine mishi ko zan ji dadi". Da k'arfi kamar Lasfika ta fara tona ma kanta Asiri. Nan dangin Alhaji Ali suka sake rufeta da duka kamar dama jira suke, mutane suka zagayesu suna kallo kamar film. Daga dakin su suna jiyo duk abunda ke faruwa a wajen Amenity. Ba me ce ma kowa komai, suna mamakin irin aikin sharrin da Shafaatu ta tafka. Zuwan Alhaji Ahmad Dakata ne ya tsaidasu, yace "haba, ku kyaleta, so kuke ku kasheta? Kar ta mutu a hannunku, ku badata ga Hukuma". Saketa sukayi, ko zafin da jikinta yakeyi bataji, mikewa tayi ta kakkabe jikinta tace "K'uran ko a jikina , ta musu gwalo". "Alhajina tsaya in shafeka da hodar nan mana, boka yace "da ya taba goshinka zakayi duk abunda na saka". Danginshi ka sa jurewa sukayi, wani k'anenshi mai zafin rai ya fincikota ya sata Mota, ya shiga ya Jata ya je ya yasar a wajen Asibitin kamar wata Bola. Nan ta fara tsince tsince tana tattarawa a rigarta, chan sai ta ji wani shagon saida films na tashi da sautin kida, rawa kawai ta saka mai karfi, hankalin mutane ya dawo kanta, tunbur tayi haihuwar uwanta, wani maigadi ya biyota ta arta a guje, lokaci guda ta fita hayyacinta duk ta haukace ta susuce. * Hajia Clean aka gaya ma angs Hajia Shafaatu ba bin bololi a Hanya, Hajia Clean ta tsorata da taje ta gane ma Idanunta, dawowa tayi ta fattataki Annah tace ta fitar mata a Gida. Annah taje ganin Mamarta a inda Hajia Clean tace ta ganta, tana ganinta ta kasa karasawa saboda warin da Mamarta keyi, Shafa ko na ganin Diyarta ta dinga binta da Gudu, Annah ta zabure ta ruga a guje tana kiran a taimaketa Mahaukacia na binta. Annah ta samu wani shago ta boye, nan taji wani dan daudu na cewa yana da ikon sa yanmata yin kudi, Annah tace "ya taimaka mata" yace to baki da damuwa zakije ko ina ne? annah tace "ko ma ina ne zani wallahi". Yace "kar ki damu, ni zan chanza miki rayuwa, zakiyi kudi". Washegari Annah ta bi dandaudun nan Lagos tafiar Mota ce, dukta wahala. Wannan shine Silar shigan Annah Dunia. **** Kwanansu Zaid bakwai a Asibiti sosai suke jin dadin jikinsu, kullum zuwa ganinsu akeyi, har 'yan bencin eskaley sunzo, ana gobe zaayi Sallama Dr Ali ya bukaci a je a ma Zaid Xray a ga status dinshi. Nurse tazo ta tafi dashi. Akayi aka dawo dashi sai bayan 4hrs Dr Ali ya bukaci Labiba da Zaid a office dinshi. ** Dr Ali yace "Zaid, na kiraku ne nan don na gaya muku status dinku duka". "Labiba you are fit, amma kai Zaid akwai wata 'yar karamar matsala wanda in ka kiyaye to ba wani abu bane, ribs dinka is affected yayi bak'i, in baka bar hayak'i ba it can backfire anytime and you wont be lucky as you are now, amma in dai zaka dinga shan magani, kuma ka daina shan Sigari to lafia lau, and then zaka dinga samun frequent attacks, in dai kana shan magani, komai zai zo da sauki". Zaid ya murmusa yace "Nagode Babana, na bari wallahi". Dr Ali yace "Allah Sarki Yasmin, da kina nan da sai kin fi kowa jin dadi Zaid ya bar Hayak'i". Zaid yayi murmushi mai ciwo yace "Yasmeeen, Allah ya rahamceki, Allah ya biyaki da Aljannah". Labiba ta amsa da Ameen. Dr Ali yace "barin je round" Ya mik'e ya tafi ya barsu. Labiba tace "kayi Missing dinta ko?". Ya girgiza kai yace "fiye da tunaninki, nayi missing Yasmin, banda abunda zan biyata da shi, Yasmin ta mutu lokacin da ban taba zato ba, amma na ji mata dadin Shahadarta, Allah ka amshi Shahadar ka sa Yasmin na cikin walwala yanzu". Labiba ta amsa da "Amin, sai ka mata takwara in mun haihu". Zaid ya dan kalleta yace "Aure? Aure zamuyi?". Ta daga mai gira tace "Yesss". Yace "bakiji yanzu ance zan dinga samun attacks ba? I can die any time in nayi wasa da magani". Tace "Sai mu jira mutuwarka, sai nayi takaba". Ya kalleta confidence din na nan, sarcasm din na nan yace "i am serious, nifa ba zanyi aure ba, kar nayi aure na mutu at young age, na bar matata maybe da diyata ko yaro a karamin lokaci". Labiba ta harareshi tace "aure kam zamuyi". Yace "ba zan iya ba, zan ha'inceki na aureki yanzu, i am still sick wallahi, aurenki saura wata daya ke da Jawad". Tace "to ka na nufin na baka Hantata a Banza? Kai tsaya ma kaji, wallahi baka isa ka zauna ba aure ba, ba kuma ka isa ka auri wata ba ni ba, Hantata a jikinka sai ka auri wata banza chan? Chabda, shi kuma Jawad ai he is not stupid, na san wallahi ba zai aureni ba, ya zaayi ya aureni bayan ya san abunda nayi, bayan ya san akwai wanda nikeso?". Zaid ya kalleta cike da kauna yace "wa kike so?" Tace "Zaid Ali Zaki nakeso". Yayi daria yace "In Abbanki zai bani ke ina so". Tace "Abbana zai baka ni InshaAllah, ehen Mallam, kadai ji ance ka bar shan hayaki ko? Wallahi duk randa na kamaka da ko lighter ne sai mun dawo Asibiti an sake budeka an ciro Hantata an mayar min cikina, ba zan yarda ka kona min Liver ba". Yayi dariya yace "au Gori zaa min?" Ta harareshi cike da k'auna tace "an maka goruba ma ba gori ba, kaidai ka kiyaye". Yace "Yes Ma". ** Suna fitowa daga Office din suka ci karo da Jawad. Zaid ya dan kauda kai tare da yin gaba. Jawad ya rik'o shi tare da cewa "Masoya, soyyayan har a office din doctor?" Ba wanda ya iya cewa komai. Yace "Ya jikinka Brother?". Zaid yace "Na ji sauk'i Alhamdulilah" Jawad yace "Thanks to Labiba ko?". Zaid yayi shiru kafin yace "Yes, thanks to Labiba kam, kar ka damu i know shes your wife to be". Jawad yayi murmushi yace "Nooo, You can have her". Sukayi saurin kallonshi ya gyada "kai yace kai take so, ko ba shi kike so ba ni kike so?". Da sauri ta gyada kai "aa shi nakee so". Yayi daria yace "Allah ya barku tare, in an dauko maganar zan gaya musu na bar maka ita". Zaid zai yi magana Jawad yayi gaba abunshi. %%%% A tare aka sallamesu. Alhaji Dakata ya tattara Iyalanshi suka tafi Masaukin da Alhaji Ali ya basu. Alhaji Ali ya kalli Dalo yace "zamuje gidan ne?". Sadiya tace "Baba lets go on a date, ni da kai da Yaya Zaid". Baba yayi daria yace "Ni Masoyinku ne da zaku date dani?". Dalo tace "sosaii Ma". Baba ya kalli Zaid yace "Muje?". Murmushi yayi yace "Muje Baba". Alhaji Abu yayi murmushi tare da mik'a ma Alhaji Ali hannu yace "to Alhaji a sha Soyayya da 'ya'ya lafia, mu bari mu isa gidan Hajia". Yak'e kawai yayi tare da gyada kai. Mancy ta ma yaranta byebye ta shige motar Mijinta, Jawad ya rufa musu baya. Alhaji Ali yaga Mancy ta shige Motar Mijinta sosai ranshi ya sosu, ya kamata ya cireta a ranshi, ya san cewa ta mishi nisa, don yana da tabbacin ba zata rabu da Mijinta ba don ta dawo gunshi, abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ya san ta wuce mai nesa ba kusa ba, dole ya cireta a ranshi, ya zama dole ya hakura da ita **^^** Dakin ya zamana daga Labiba sai Maminta da Abbanta, tunda suka zo sai yau suka kebe. Labiba cike da kunyansu tace "wallahi na san ban kyauta ba, wallahi Mami nasan na tada nuku hankali ranku bace yake". Mami tace "Labiba baki da hankali, baki san ciwon kanki ba, ance miki So Hauka ne? Wani irin rashin tunani ne haka, namiji kike ma wannan zazzafan So? Baki san Namiji ba dan goyo bane". Abba yace "Amina, godiar da zakiyi ma Allah kenan?" Tace "dole fa a mata fada, bata kyauta ba, wani irin abune wannan? Yarimya ta task tundaga Edo State, tazo wai Katsina gun saurayi? Haba wannan rayuwa da mai tayi kama". In akwai abunda Labiba bata so to fushin Iyayenta, nan tashiga basu hakuri tana kuka. Tsakanin da da mahaifi sai Allah, nan suka yafe mata tare da mata fada sosai. @@@ Zama sukayi a k'ayattacen wurin cin abinci, kowa ya fada abunda zai ci, a ka kawo musu, sai da suka gama ci kafin Baba yace "Zaid, ni fa kunyarka nikeji, ban san ta ina zan fara ba". Zaid ya murza idonshi yace "Baba kunyan me fa?". Baba yace "Zaid, ban kasance uba nagari wanda zakuyi alfahari dashi ba". Zaid yace "Nagane inda ka dosa Baba, ba zan yarda ka nemi gafara na ba, ni wanene da zaka roki gafara na". Baba yace "Zaid, na zalunceka, da bakina na laanceka, nine silar fadawan ka shayeshaye, na maka Illah". Zaid yace "ba a hayyacinka ba, na san Babana na sona, a hayyacinshi ba zai taba furta min mummunar kalma ba, ban manta ba a da kana fada da duk wanda ya kirani da sunan DanMakaho, a cewarka sunan Banza ne, ta yaya zaka furta wani zagi da bakinka? Baba wallahi ko a da na san cewa ba yin kanka bane, shiyasa ban taba rikeka a raina ba". Dalo tace "Baba nagaya ma tun ranar, wallahi muna sonka fiye da duk wani Namiji a duniyar nan, kar ka roke mu komai, mu zamu rokeka yafiya in bamu kasance 'ya'ya nagari ba". Baba yace "Haram wallahi, kune ko 'ya'ya nagari, ina sonku fiye da komai wallahi, ku yi hakuri na kawo wacce ta rusa mana farinciki, ba zan taba yafe ma Shafaatu ba, gashi tun a dunia ta fara ganin sakamakonta, ina da Labarin ta haukace an kamata an tafi da ita Asibitin Mahaukata. Tabe baki sukayi irin ko a jikinsu. Yace "donAllah ku rokar min Mamarku gafara, ta yafe min". Dalo tace "Allah Baba bakomai, kowa fa ya san duk abunda kayi ba yin kanka bane". Yace "nidai please ku ce ta yafe min". Zaid yace "InshaAllah Baba". Baba yace "Zaid ka tuna Aunty Mariya?" Zaid yace "Eh Baba, Mijinta ma ya rasu". Baba yace "ka sani ohh nine dai bansani ba". Zaid yace "me ya sameta". Baba yace "wai Goggo wai na aureta". Daria suka sa gabaki daya Zaid yace "to Baba ayi mana, ai dama ba zai yiwu ka zauna haka ba ba mata". Baba yace "kun Amince?". Sukace "dari bisa dari". Yace "Allah ya muku Albarka ya sa ku gama da dunia Lafia". Suka amsa da Amin. Baba yace "Zaid Credentials dinka na nan, Alhamdulilah ban salwantar da su ba, Masters dinka kana da shaawar komawa London kayi ta?". Zaid yace "Aa baba, barni in huta for now". Baba yace "to shikenan, da degree dinka ai zan samo maka aiki mai". Zaid ya yi alwashin tashi ya tsaya da k'afarshi yace "Baba, zan gabatar maka da abunda nike so nan ba da dadewa ba". Ya kalli Dalo yace "ke kuma fa? Karatu ko Aure". Dalo tace "Lahh Baba aure fa kace? Chab nawa nike ni? Ni gaskia Baba ka bari". Baba yace "amma na fa ce ko karatu, bance aure zan miki ba, why are you focused on the last option?". Zaid yace "because its what she wants, Aure take so Baba". Baba yace "Exactly". Dalo ta turbune fuska wai zatayi kuka. Baba yace "wallahi Zaid ba zan kyaleka ba ka sa min yarinya kuka". Sukayi daria, tare suka kasance aranar gabaki daya kafin suka koma gida Gab da Maghrib. A na Gobe 'yan Edo da 'yan Abuja zasu koma garinsu suka hadu a wakeken Parlorn Alhaji Abu Shamsu dake nan garin Katsina. Alhaji Abu Shamsu ya bude taro da addua. Yace "To abubuwa da yawa sun faru, wanda duk abunda ya faru yana daga cikin pegin layin k'addararmu, dubararmu ba zata iya hanata faruwa ba. "Alhamdulilah Allah mungode maka, Allah ka sa duk mu ci wannan jarabawar, Allah kanyafe mana duk mu yafi Juna, kuma wannan zumuncin Allah ya riga ya hada babu mai rabawa". Alhaji Ahmad Dakata "ya dora nashi jawabin yana kuma mai bada hakuri, tare da cewa Jawad yayi hakuri da Labiba, don kamar ya kwareshi ne in ya bashi Labiba, Labiba zata cigaba da Makaranta har Allah ya kawo mata wani Mijin". Alhaji Abu yace "wani Miji? Ai Allah ya kawo mata tuni da dadewa". Sun san inda ya dosa Alhaji dakata yace "anya amma Jawad Adalci in aka ba Zaid Labiba?". Alhaji Abu yace "yo saboda me? Da Zaid da Jawad duk 'ya'yana ne, ko ni ba zan aura ma Labiba kowa ba sai Zaid, Sadakinta na hannunka ka manta wanchan mancewa nayi da naje Edo, so nayi nace nazo neman auren ma Zaid Aure na ce Jawad subutan baki ne". Alhaji Ali Zaki yace "wai ya ake ta min passing passing da diya ne? In ba ku so ku bar min ita, na kaita madina tayi karatu ta kawo min balarabe, ha'an". Sukayi daria Alhaji Abu yace "Allah baka hakuri su masu diya". Alhaji Dakata yace "ni dai koms meye sai naji daga bakin Jawad, in har be amince ba, wallahi sai dai ciwon so ya kashe Labee, sai dai ta auri wani ba Zaid ba". Jawad yace "Abba wallahi bakomai, na bar mishi ita, na yarda, Zaid ai danUwana ne, Allah ya kara musu Son So".. Alhaji Abu yace "Fak'at, Hajiyoyi me zaku ce?". Mancy tace "ai kun dai gama Magana, in aka raba Zaid da Labiba ai Nigeria ta mana kadan, don wallahi guduwa zasuyi". Mami tace "in dai ba so kuke kunmata wani auren ba, Zaid ya zo yana bukatan dashin Zuciya Labee ta kaso aurenta ta je ta bashi ba to wallahi tun wuri ku aura mata shi, tunda dai ta ji tagani 'yar kutsun uwa. A kayi daria yace "Na bawa Zaid Labiba". Alhaji Abu yayi daria yace "na amsarwa Zaid Labiba". Duk sukayi Hamdala. Zaid ya saukar da kanshi yana ma Labiba Signal tare da kashe mata kannenen idonshi, ita ko bata ma kalleshi ba balle ta tankashi. %%% Da Yamma Aisha tazo wurinta ranta bace tace "wai ke yanzu Besty shikenan ba zaki auri danuwana ba?" Labiba tace "danuwanki fa yace baya sona, ba zaiyi ba wai". Harararta tayi tace "kafin yace baya so ai ke kikace ba kya so". Labiba tayi murmushi tace "Allah zai ma Jawad zabi nagari, nidai ya min". Aisha tace "dan Shaye shayen?". Dif Labiba ta dauke wuta tace "kar ki sake bana so Aisha". Bata taba ganin baci ran Labiba ba sai yau hakan ya sa Aisha wayancewa. "Yi hakuri, yanzu Abu Sadik ai dole ya hakura da ke". Labiba tace "bawan Allah". Aisha tace "yanzu wai har da ke zaaa tafi Edo? Makarantar fa?". A takaice tace "Abba ya cireni". ^^^^ Alhamis Aunty Mariya ta fita takaba, Jumaah aka daura mata Aure da Alhaji Ali Zaki. Bayan anyi gyare gyare a Gidan ta tare tare da 'ya'yanta biyu wanda Alhaji Zaki ya bukaci ya rikesu. Zaid da Dalo sun tafi Kano gidan Yayan Mancy Daga chan suka nufa Abuja. B A Y A N 'yan kwanaki. E D O Labiba ta kira Aunty Bilkisu Matar da taimaketa a hanyar Katsina. Bayan sun gaisa tace mata "Labiba ce". Aunty tace "Allah Sarki Labiba, ya kike ya jikin Dan Makaho?". Tace "Aunty baki manta ba?". Tace "ina Zan manta beebs? Ai dan Makaho ya tsaya min a rai, tausayinshi nakeji". Labiba tayi daria tace "Aunty wallahi jikinshi ya warke sosai, next month aurenmu". Aunty tace "ke haba bari donAllah". Labiba tace "wallahi kam". Sosai Aunty Bilki ta tayasu murna ta musu fatan Alheri. Tace "baya da raayin Civil Defense dinne?". Labiba tace "kinga ko gaya mishi ma banyi ba". Tace "to InshaAllah, in yana so ki bashi Email address dina yanzu zan turo miki, kice ya turo CV dinshi da address din". Labiba tace "yanzu kuwa zan Aunty, zan sake kira, gaida min da kannena". Aunty Bilki tace "zasuji inshaAllah". Numbershi ta latso. Dauka yayi full of energy yace "Yes bee to the beebs bae to be". Daria tayi da jin iyarshegenshi. "Wai Masoyin kana son aikin Force?". Yace "Soldier?" Tace "Nope Civil Defense". Yace "Sosaiii ma, zaki samo min ne?". Ya tambayeta cikin wasa. Tace "eh in kana so". Cike da zolaya yace "ina so Comptroller Labiba Ahmad Dakata". Tace "Send your CV to the email address din da zan turo maka yanzu". Yaji she sounds serious yace "babe are you serious ?" Tace "stop asking too much, just send the cv, zan kiraka anjima i love you". Kita ta kashe wayar, ko 30seconds baayi ba ta tura mishi email adress din, da mamakin Labiba ya tura Cv dinshi ma address din. Aunty Bilki ta kirata, Labiba na dauka tace "Zaid Aliyu Zaki? Age 27". Labiba tace "wai har ya turo?". Aunty tace "eh wallahi, ina son masu zafin nama, inshaAllah zanyi kokari naga ya samu, inshaAllah". Labiba tayi ta zabga godia tare da sa mata Albarka. K A T S I N A 'Y A N B E N C I N E S K A L E Y. Su 4 Zaid ya ma jagoranci har Parlon Baban. Cike da Ladabi da biyyaya suka gaida Alhaji Ali Zaki tare da zama kasan Carpet. Alhaji Ali yace "duk ku gaya min A ina karatunku ya tsaya". Eskaley yace "ni ban taba zaman Aji ba". Terro yace "Ni tun Primary ban cigaba ba". Haruna yace "ni ina da Diploma". Master yace "ni ina da Secondary School Certificate. Alhaji Ali yace "Alhamdulilah, ina so kuje kuyi tunani ku dawo ku gaya min burinku, wani sanaa kuke so ku fara? Zan baku jari". Dadi ya mamayesu. Master yace "ai Baba a nan zamu gaya ma, ba wani tunani". Yace "ina jinku". Yace "nidai Baba shago nike so a bude min a sa ka min lemuka da yogurt a sawo min blender da generato, a saka min freezer , zan dinga dama fura da yogurt ina saidawa, a sama ko a buga min tambarin Master Fura da Nono and juices". Daria suka sa, Baba yace "an yi an gama". "Kai fa Eskaley?" Yace "Baba ni dai so nake a fadada min Kiosk ina a cika min Shago a habaka min shi, duk unguwan nan nikadai ke da shago". Baba yace "ba kiosk ba, wannan shagon gefenka Empty naji ance ana neman me siya, zan kama maka in cika maka shago da provisions kayi ta saidawa". Terror yace "ni dama Baba chan da na iya irin Takalma da Jakka Handmade, ina so a bani jari da shago na dinga yi". Yace "to naji" Kai kuma Haruna me kake so? Haruna yace "Baba ina da diploma na, ina so na koma Makaranta na hado Degree dinnan, sai na dinga bussiness". Baba yace "bussiness din me?". Haruna yace "ko Shadda haka". Yace "to naji, dukkanku zan baku naira dubu dari biyar, miliyan biyu kenan." Ina Aljannah su sakashi, godia kawai suke kwasa, suna sanya mishi Albarka, "suna cewa sai Baba, mungode, Allah ya kare mana kai, ya sa ka fi haka, Allah ya maka Gwamnan Katsina, Allah ya kareka daga sharrin Mahassada". Baba yace "To Amin nagode, amma fa da sharadi". Suka natsu yace "ba cash zan baku ba, Idrisu zan sa duk ya siyo muku abubuwan da kuka lissafo da kudinku, don kar ku kashe su a banza". Suka ce "mun yarda wallahi, mun fi so dama a siyo mana komai". Yace "kuma duk wanda na sake naji ko na gani yana shaye shaye, to zan amshe abuna". Haruna yace "nidai Baba na bar World na bar Sigari, dama wallahi rashin abun yi ne ya sa nake sha, amma yanzu haram". Master yace "ni tun da naga Mankas kwance ya kusa warewa nace na bari don kar na baro ma kaina aiki uwayena basu da kudin biya a man aiki, Allah nidai na bari". Terror yayi shiru, don ya san karya ne yace zai bar shan sigari lokaci guda, ya riga ya zame mishi jiki yace "nidai baba kar na ma karya, InshaAllah ba zaka ji ko ka gani ba, amma dai ka sani a addua, zan bari" Baba yace "Allah ya sa, nidai na gaya muku, randa na ganku ko naji labari, zan amshe abuna ne, kaifa Eskaley ance kai ke sayar da world din yace "Wallahi Baba na bari". Yace "kaifa Mallam Zaid?". Zaid ya murmusa, Soyayyar Mahaifinshi na tsaga bargonshi da jinin jikinshi ya murmusa yace "Baba ni ai na bari, Labiba tace in ta kamani ina shan sigari wai zata sa a budeni a ciro mata hantarta A maida mata cikinta wai ba zan kone mata hanta ba". Sukayi daria ga baki daya yace "Diyata ta min daidai, to ku tashi ku tafi Allah ya muku Albarka". Nan suka dinga shi mishi Albarka suna Gode mishi. Cikin kwana biyu ya cika musu Alkawarin da ya daukar musu. Kamar Shekarun Baya, haka aka dawo, ko wani Gida a Tudun Matawalle akwai kwanon Abincinsu a Gidan Alhaji Zaki, amaryarshi bata da kyashu bare hassada, duk wani mai neman taimako gidan yake zuwa, ya taimaki Danginshi, ya taimaki Na waje, kowa na yabawa da Alhaji Ali Zaki. A B U J A Jawad ya shigo Parlorn ya iske Mancy da Umma sai Abdulmajeed, Mimi na bacci. "Jawad yadai?" Yace "Mancy wai Sadyy har yanzu bata dawo ba?" Ta kalleshi tace "Jawad Chan zata kwana". Ya zaro Ido "don me zata kwanar musu a gida kamar basu da gida, nidai ta dawo". Mancy tace "kamar dai wani gida taje? Gidan Abdulhafiz ne fa, matarshi take tayawa aiki ka sam tayi nauyi, ya gaji ne ba zai iya dawowa da ita ba yace sai gobe". Jawad yace "yo ita 'yar aiki ce da zaa dinga daukarta tana tayin aiki? Nidai barinje in daukota gaskia". Mancy tace "kayi hakuri Jawad gobe zai dawo da ita". Jawad yayi dan guntun tsaki ya latso wayar baban yayanshi yace "Hello Yaya, ga Abba nan na ta fada wai ka dauke mishi diya, yace gobe da sassafe ka maido mishi diyarshi kar ya bata maka rai". Jin muryan Abba sukayi a baya yace "karya ake mun, ni da bansan ma anyi ba?". Umma tace "Wai Jawad, Wai Abbanku zai maida Dalo Katsina gun Babanta". Gaban Jawad ya fadi ya zaro ido yace "Abba wai dagaske? Meyasa? DonAllah kayi hakuri, ba Babanta yace ya bar maka ita aure ya rabaku?". Abba shima ya biye yace "ai Auren zan mata a Katsina". Ya zaro ido sosai, sai chan yaga suna dariya, sai ya gane ashe zolayarshi suke Jawad ya bubbuga k'afa cike da shagwaba Su Mancy suka sa daria baki daya. Abdulmajeed yace "ana so ana kaiwa kasuwa" Ya murguda baki yace "ina ruwanka?". Abdulmajeed yace "ko kayi making move, ko ma hadeta da Aisha nayi Mata biyu rana daya". Jawad yayi hanyar kofa yace "in ka fasa". Dariarshi sukeyi sosai Abdulmajeed yace "Mancy Your Boy is In love". Mancy tace "ai na lura da kanwar taka itama ta na yinshi" Alhaji Abu ya kalli Iyalanshi cikin dadi yace "Alhamdulilah".. Washegari Yaya Abdulhafeez ya dawo da Dalo da safe don daga gidansu zai wuce aiki. Suna kan table suna breakfast. Sukayi Sallama tare da gaisar dasu. Abba yace "Yadai? Wannan sammako haka? Kamar ana tsiranku". Abdulhafiz yace "Abba ance kana ta fada, shiyasa nace in zan wuce aiki zan maidota". Jawad ya dinga ma Abba Signal da yace eh don in ya gane karya ne zai bata mai rai. Abba yace "yo eh, sai a dauke man 'Yar yainyata haka akeyi?". Dalo dai tayi ta daria. Umma tace "kuzo kuyi breakfast". Dalo tace "wallahi a koshe muke". Mancy tace "zo ki kwashe wanda aka ci". Tace to Ta zo tana hada plates din da aka bata iya daukanta ta nufa kitchen. Kamar an tsunkureshi ya mik'e yana hada cups yace "dama kitchen din zanje". Ba wanda yace komai Illah murmushin da suke ta zabgawa. A Kitchen ya isketa tazo wucewa ya rufe mata hanya. "Sadyy kikaje gidan Yaya kikayi zamanki ko, kin sa zuciana wahala, yana ta missing dinki". Bude idanuwanta tayi alamun hakuri tace "i am sorry, zuciyar ta daina Zafi, maganin tazo". Yace "ni dai kar ki yarda ki sake nisa dani, jiya su Ya Majeed har da zolayana suke". Shagwaba yake ta zuba mata shi ala dole dan auta. "Ina ruwansu da kai da zasu zolayeka? Ka rabu da su, zanyi maganinsu". Yace "Ina Sonki kinji?". Murmushi tayi ta sadda kai k'asa tana daria. Yace "wallahi sai kin fada yau, kullun in ta fada ba kya fada?" Hannu ta sa duka biyu ta kulle fuskanta. Ya sa cokalin hannunshi ya k'wankwashe mata hannu budewanta yayi daidai da futar "Ina Sonka nima". Lumshe ido yayi yace "Princess" Lumshe ido tayi tace "Prince". "Umma, Mancyy wallahi ga su nan suna soyewa a Kitchen". Umma tace "Me suke soyawa kuma?". Mancy dai daria take kasa kasa Dalo kamar ta shige k'asa saboda kunya. Alhaji Abu yace "to abu yayi kyau, barin gaya ma Alhaji Ali, in zaa iya hade bikinsu Zaid wallah duk aurar da ku nake in huta" Da gudu Dalo ta shige Daki. Alhaji Abu ya kira Alhaji Ali, a handsfree aka saka wayar bayan sun gaisa Alhaji Abu yace "wai wasu sabbin tsuntsayen soyayya muka samo, nace ko dai mu aurar dasu mu bige aiki?". Daria Alhaji Ali yayi yace "Wa da wa?". Alhaji Abu yace "Diyata da Jawad" Cike da jin dadi Alhaji Ali yace "Sosaiii ma, ai kawai a buge aiki". To sai ka gaya ma su Labaran cewa Su uncle Usman dinsu zasu zo neman aure da saka ranar ran jumaa" Alhaji Ali yace an gama. Haka ko akayi, a karshen satin aka kai kudin neman aure, da sa rana Family house dinsu Alhaji Ali zaki. Shirin Biki ake tayi gadan gadan. Kullum sai Umma da Mancy sun shiga kitchen. Alhaji Ali ya turo 2mil wai a ma Dalo kayan daki. Alhaji Abu ya kirashi yana fada "diyarka ce da zaka turo kudin kayan daki?". Alhaji Ali yace "Allah Nagode, diyarka ce, wai da gudummuwa ce na turo, amma in ba a so a maido min abuna". Alhaji Abu yace "baka isa ba, wanda yace ka turo". Sukayi daria. A Gidan Yaya Abdulhafeez, Flat ne Uku 3 bedrooms each, Abba ya gina ma 'yaranshi gida tun kafin Abdulhafiz din yayi aure, nan zasu zauna duka. Sai ya kira Zaid a waya yace "to Ni dai bansan inda kake son zama ba, zaka zauna a Abuja in samo maka aiki ka hadu da yanuwanka?". Zaid yace "Abba, nidai Katsina nake so, nan nake son Zama, aiki kuma akwai abunda nike jira". Abba yace "to ba laifi, ka nemo gidan da ya maka, ni zan siya". Zaid yace "Abba Baba ya bani Gida a Goruba road". Abba yace "shifa Baban naku karambani, wa ya aikeshi baka Gida? To dama abunda na yi ma su Jawad nike son yi maka, to amma tunda an rigani, zan siya maka Mota kai da Matarka, sannan na samaka chanji a account". Cike da jin dadi Zaid yayi ta zuba godia. Alhaji Ahmad Dakata ya ma Labiba da Samira kayan daki, duk abunda aka siya ma Samira an siya ma Labiba, komai iri daya ne. Zaid yace "ba sai sunyi komai ba, Baba ya gyara gidan". Tace "ai da bakuyi wahala ba, nan ma anyi komai". Yace "kuma sai anyi wahalar daukosu daga Edo?ai kawai a barsu" Hayyakoewa tayi Labiba tace "a yi yaya dasu? wallahi, sai an sa min kayan da Abbana ya min". Ganin rigima take neman tada mishi yace "to Baby, ba abun fada bane, sauki nake nema". Tace "to angode amma sai an kawo". Yace "Allah ya kawo lafia". Ita fa zuciyarta a wuya yake, kowa ya tashi zai ce "wallahi ki rage son Zaid, wata rana zai miki wulakanci, namiji butulu ne, da ka nuna mishi So, wulakanci ke biyo baya" Da sun fara maganar nan tashi takeyi ta barsu sai suce ba ta son gaskia.. Yan Bencin Eskaley suka hado mishi gudumuwar naira Dubu dari 25k suka hada each. Da farko yace "ba zai ansa ba". Master yace "kai yaro ka amsa wallah mun fika kudi don business mukeyi kai ko mai baka saidawa". Daria Zaid yayi yace "Yan dunia, ku zo musha World don murna". Master yace "uwar World zami sha, kana so Baba ya anshe tallafi ne ne" Daria yayi ya musu godia. Suka ce ka kaimu Gidan Nene. Yace "wallahi Nene damuwa ce". Suka mishi magiya ya rakasu. Ashe leda sukayo mata. Sai da sukayi drama a gidan Nene tace wallahi ka bar ganin zakayi aure, sai na saka daki karfe ukun dare na ci ubanka dariya suka saka. B I K I B U D U R I Katsina Duk suka gangado. Ba tare da yin wata bidiah ba Ran Asabar din Satin aka daura Auren AbdulMajeed Abu Shamsu da Amaryarsa Aisha Usman Da kuma Jawad Abu Shamsu da Amarayarsa Halimatu Aliyu Zaki a sadaki naira dubu hamsin. Da Aishar da Sadiyar duk Abuja a ka kaisu gidajensu. Sati na sama suka garzaya Edo don daurin Auren Labiba. Duk da ance ma dangi yan katsina an hutarshe da su ba sai sunje ba duk wahala ce amma Edo ta kwashi mutanen Katsina da yawa. Bayan an daura auren Aminu Shehu da amaryarsa Samira Ahmad Dakata aka daura auren Zaid Ali Zaki da Amaryarsa Labiba Ahmad Dakata da Sadaki naira dubu hamsin. Text ya mata _Burina ya Cika, Alkawarin Allah ya cika, ina tayaki murna Mrs Zaid Zaki, ina tayaki murnan zama matata_". Murmushi kawai tayi kafin ta yi sujudul shukur, wai yau itace ta amsa sunar Matar Zaid? Allah mai iko. A ranar Hajia Bilki ta kirata tana neman afuwa bata zo bikinta ba. Labiba tace "haba Anty ai ba komai, babu ma abunda akayi sai Wedding Fatiha". Tace "to Albishirinki, consider this as my Wedding Gift, Anyi recruitment, Zaid ya samu One Star 🌟". "Allahu Akbar Allahu Akbar, nagode Aunty Allah ya biyaki da Aljannah". Tace "Ameen, Allah ya bada saa, in kun gama Amarcinku nan da 3months zaije training". Dadi kamar ya kashe Labiba, kasa hakuri tayi sai da ta kirashi ta bashi good news. Duk da mutane sun mishi yawa sai da ya matsa gefe ya nuna murnarshi yace "wai ke ina kika samu hanyar CD?". Tace "wallahi wata baiwar Allah ce take sonmu take son taimaka mana". Yace "Alhamdulilah, Allah ya biya baiwar Allahn nan da Aljannah". Ta amsa da amin Yace "zan kiraki, muna pictures da mutane, ina sonki kuma". Kit ya kashe wayar". A ranar aka dauki Samira aka kaita gidanta da ke Birnin Edo, washegari kuma aka tafi da Labiba zuwa Abuja daga Abuja aka dauketa a Jirgi zuwa Kano, daga Kano suka iso Katsina duk a gajiye ba a tsaya da ita ba ko ina sai gidanta. S O Y A Y Y A R U W A N Z U M A Tana zaune a bakin gado, shi kuma yana daga ƙasa akan rug mai laushin gaske. Hannunsa na kan cinyarta. Wani karamin kurji ya fito masa wajen gemunsa, a hankali take kokarin fasa mashi kurjin, ba abunda yakeyi sai shagwaba da lalaci a dole zafi yake ji. "Wasshhh" ya sake fadi a karo na kusan goma. Amma wannan karan harda tura baki sosai tareda jan kansa baya. Kallonsa tayi tareda sakin masa murmushinta wanda ke kawatar mata da fuska. "Haba Mijin, ka tsaya na gani mana, Haba Masoyi." Ta karasa maganar tareda tallabo mashi fuska. "Ni gaskiya banaso" "Just this once, I promise." saita daga hannu daya sama alamar ta rantse. Langwabe kai yayi ya tsaya.. kafin ya kafeta da kannannen idanuwanshi, Wai yau gashi ga Labiba a matsayin ma'aurata. Kallonshi tayi ta ga yana kallonta. "MIJIN" tace cikin muryan da bai wuce raɗa ba. Bai amsa ba saboda hankalinsa baya kanta. "BABE" ta sake kiranshi, amma bai motsa ba, bakinta ta hura mashi iska kadan a wajen fukansa wanda yayi zumbur ya dawo hayacinsa. "A penny for your thought," tace tana murmushi. Riko hannunta biyu yayi ya daura kan fuskarshi, ya shafa kumatunshi da hannunta sannan ya sumbacesu su biyu. Idan da sabo yaci ace ta saba da irin kallon da Zaid ke mata, kokuma wani abin dayake mata na nuna so da kauna. Amma kullum kamar sabon shafi ake budewa. Kullum sanshi yana daɗa ƙaruwa daga ɓargonta har duka ilahirin jikinta. Kowane Sonsa na gaɓoɓinta yana amsa irin soyayyar da Zaid yakeyi mata. Janyonta yayi ƙasa zuwa inda yake zaune, ya tallabo fuskarta Ya hada idanuwansu. Baice komai ba bayan kallon kallon da sukeyi. Duk jikinta yayi sanyi, Zaid yanada wani kwarjini wanda bata taba ganiba. A murya ƙasa ƙasa yayi magana. "Ki daga fuskan ki." bata kula ba illa murmushi. Wai yau itace take kunyansa sosai. Tama rasa ganewa da gaske ta kasa kallonsa ne ko tsabaragen iya shege ne. Ta tuna irin liver dinta lokacin datake zuwa dakinsa, amma yau gashi a matsayin mijinta amma tayi bala'in laushi. "Ki daga please, badan halina ba sai dan soyayyar danake maki." Bin umurninsa tayi ta kalleshi. "What are you doing to me beebsss?" yaja sunar sosai chan cikin makoshinsa. Kai zaka zata shiya rada mata shi. Ita kanta a lokacin tasan cewa tunda tazo duniya babu wanda ya taba kiran sunan haka, Yafi zama akan bakinsa kamar danshi aka halicce ta. _Dan shi mana aka halicce ta, she's surviving for him. Rashin sa zai zame mata barazana a rayuwarta_ ta tuna. Magrib aka soma kira, ba ita kadai ba harshi yana bukatar hutu sun sha jigilar hanya, a gajiye suke, ba abunda zasu iya yi, yau hutu kawai zasuyi. Labiba ta zame mashi tamkar world wanda he is addicted to a da. Duk yanda yake muradin shan World ko wani Sigari duk yanda yake san sha ko kadan, input dinta duk yafi mashi zugi. Har tsoro yake ji saboda soyayyar ta yayi mashi babban kamu. Idan yaje sallan magrib zama yakeyi a masjid yana tilawa har a kira isha. Text ya tura mata kafin ya dawo. We were once on separate paths We knew nothing of each others existence I agonise by the thought of that Indeed they were my darkest time Fast forward to the present You have become part of me Like my very own DNA.... Bata karasa karantawa ba ta lumshe ido sai murmushi takeyi. Kalaman Zaid yana dama mata lissafi sosai. Tana kan sallaya sanda ya dawo. Dakin yana kamshin turaren wuta wanda ke ci daga burner a chan kurya gefen socket. Sannan ga AC an kunna madaicin. Dole duk fushinka da gajiya idan ka shiga zakiji ka soma sauka. Gata itama fuskanta yana glowing, yasan ba komai bane illa yawan alwala daya haskaka mata shi. Idon ta a rufe yake, amma zakaga karamin murmushi yana tashi daga kasan leɓanta. Shima kwanciya yayi gefenta ya sakalo mata hannu yayi wrapping dinta sosai. Sunfi minti kusan biyar a haka. Saiya juya da ita ya kwantar da kansa akan kirjinta, bata hana shi ba illa matse ido tana murmushi. Shima rufe idon yayi numafshin sa yana hawa da sauka. Hannunta ya saka hannunsa saiya harde biyu. A zuciyarshi yana son Labiba. Labiba Alheri ce, itace Alherinshi, Cikin ransa baya komai illa gode mata yanda take sonshi, yanda ta tsaya tareda shi a lokacin da yake ba kowa ba, a lokacin da bai da wani gata ko galihu, yanda ko sau daya batayi judging din mugayen ɗabi'unsa ba. Yanda koda yayi mata wani abin take tausasa zuciyar ta ta kuma yafe mashi. Lokacin da yake dizgata amma bata hakura ba, yanda ta take maganar kowa don ta kasance tare dashi, bata guje shi ba. Yasan ba zai taba biyanta ba, Babu wani abin duniya dazai fanshe abinda tayi, saidai zaiyi amfani da karfinsa yayi kokarin ya kawo mata duk wani jin dadin rayuwa.. Ta mashi halarci sosai, ba zai taba taking dinta for granted, shi ba butulu bane, zai gwada mata Namiji dan Goyo ne. Duk da ba zai biyata ba, amma alkawari ne, tana cikin adduarshi a kowacce sujaddarshi .Addu'a ya ke binta dashi da fatan zata gama da duniya lafiya. "I love you Babe," ya fada a bayanne. "I love you more Sugar," ta fada itama. "Ina Sonki Matar". "Ina Sonka Mijin". "Ina Sonki Sosai". Tayi daria tace "Sosai nake Sonka". "I love you baby" tun tana amsawa har ya ji ta shiru. Haka yayita nanatawa wanda saida dukan ilahirin jikinsa ya gasgata abinda ke fita daga bakinsa. Komai na jikinsa ya aminta da soyayyar ta. Daga kansa yayi ya kalleta yanda take barci cikin natsuwa, wai har tayi bacci, gajiya ce ba komai ba. Wani hawaye ya ziraro masa daga idanu. Bai share ba ya barshi yana zuba. Tausayinta ya kamashi. Allah kar ka bashi ikon zaluntarta, Allah ka bashi ikon biyan Soyayyarta da k'auna. He needs her now more than ever, itace battery din rayuwar sa. Kamar yadda waya ba zatayi aiki idan babu battery ba, shima haka yake ji da ita. A hankali ya tashi ya sumbaci goshinta, daga nan sai kumatun ta, sannan ya daura akan bakinta. Bayan nan ya daga ido ya kare mata kallo saiya daura kansa kuma akan kirjinta. Bazai taba gajiya da sauraran yanda Zuciyarta ke bugu ba. Bugun bana komai ba illa bugun sunanshi watau ZAID. ***^^^ Yau Babbar Bak'uwa garesu Hajia Aminene Mamman zata zo, Tun Safe ta rasa me zatayi don ta burge Nene. Bata sanwa, amma don ta burge Nene sai da ta sa Zaid ya jona mata Gas. Yace "really? 3days after your Wedding zaki fara abinci?" Gira ta daga mai alamun Eh. Yace "Dagaske Beebbs ki daina matsa ma kanki, wannan Tsohuwar baki iya mata, wallahi gwasule ki zatayi". Tace "nidai ka barni, sai na mata, ka kira min Balele na aikeshi kasuwa". Yace "to Allah ya bada Saa". Ta murguda mai baki tace "Ameen". Parlo ya koma bayan ya aiki Balelle kasuwa ya fara kallo. Balele yaje ya dawo ya kawo mata duk abunda ta aikeshi. A sannu sannu ya dinga jin kamshin abinci na shigo mishi. Sai da tayi kusan 3 hours a kitchen kafin ta fito tayi setting table. Zaid yace "Whats Cooking? Ya bubbude coolers, yaga cooler daya pepper chicken, daya Fried rice, daya tuwon semo da egusi da ya ji kayan miya da k'amshi. Yace "Lallai Beebs, baa ma Mijin abinci ba, shine aka ma Nene?". Ta langwabe tace "kar ka damu, zaka ga shagalin da zan maka kai kadai". "Okay oo I hope she will be impressed though". "Nikam kana kada min gaba, ka kyaleni". Yace "okay oo, sai muje muyi wanka, kafin ta karaso". Drivern Gidan Lema ya shigo gidan Zaid da misalain karfe 2:30 na rana. Nene ta fito rik'e da Basket din Abinci a hannu. Ta shiga Gidan da Sallama. Tsaytsaye sukayi suna jiran shigowarta. Idon Labiba ya kai kan Basket din hannun tsohuwar da ta shigo. Sannu da zuwa ga Nene ga Nene. Zaid ya karbi Basket din, Nene ta rungume Labiba. "Yau ga ni ga Matar takwaran Zaidu bawan Allah". Labiba ta durkusa ta gaidata. Nene ta amsa cike da kulawa. Har kan kujera ta jata suka zauna suka sake sabon gaisuwa. Nene tace "Wallahi kina min kama da jikata Nasiba, don dai Seebi ta fiki dogon hanci". Labiba ta murmusa tace "Allah Sarki". Zaid yace "in ma so kike kice Seebinki tafi Matata kyau ba yarda zan ba, matata tafi kowa kyau". Tace "Kai dai ka sani dan nema,". Labiba tace "Nene muje kan table muci Abinci". Nene tace "wallahi yunwa kau nikeji, da na gama Abincin ko ci banyi ba nayi wanka na taho". Ta mik'e tsaye tace "takwaran zaidu bawan Allah dauko Baskyat din". Kan dining suka nufa gaba ki daya. Zaid yace "wannan Coolers din fa Nene, me ke ciki?". Ta amsa daga hannunshi tace "Abinci na dafa mana muci mana, me ake zubawa dama a cikin cooller". Da sauri ya kalli Labiba yace "ai ta miki abinci, kala kala ma, gasu nan kan table". Nene tace "Too, daga kawoki shekaran jiya har kin fara sanwa? Wace amarya ke abinci a wannan lokaci". Yace "sai da nagaya mata fa, tace sai tayi na tarban Nene". Nene ta murmusa tace "Allah sarki, kuma gashi nima nayi Abinci, nace ma Aisha bari na dafa ma Matar takwaran Zaidu bawan Allah abinci, amma tunda kin dafa, ai sai ku aje ku dinga dumamawa kuna ci". Da sauri Zaid yace "Aa mu dai ci yanzu dake". Harara ta zabga mishi tace "wannan fa da na dafa, ya kake so nayi dashi?". Yace "Amma kya ci abincin Amarya ko?" Tace "ba zanci ba, nace ba zan ci ba". Ta bubbude coolern ta dauki cokali ta dibo miyan kubewanta danye ta riko hannun Labee ta lasa mata tace "lasa kiji". Labiba ta sa a baki. Nene tace "tsakaninki da Allah abincinki ya kai nawa dadi?". Labiba tayi daria tace "ina ma zaa hada? Ai ban taba jin miya mai dadin wannan ba". Cikin dadi Nene ta tafa hannu tace "yauwa 'yar gari, shi mijinki da baa mishi gwaninta har ya fara yan surutai, nifa ba kowa nake ma abinci baa, amma ina ji dake shiyasa na dafa miki". Labiba tace "aiko nagode sosai". Labiba ta sauke Abincinta na kan table, ta daura na Nene, ta kai mata kitchen. Zaid ya bi bayanta, yana cewa "kin gani ko? Na gaya miki, matar nan ba a iya mata, kinga ta wahalar min da ke". Labiba ta harareshi tace "meye wahala? Chabda, nikam burgeni tayi, ba ta da bakunta". Zaid yace "kyab, nenen zata miki bakunta? Shes full of wonders". Tace "oya muje tana jira". Suna fitowa suka ga har ta zuzuba musu a plate. Tuwo ne miyan kubewa danye da yaji tantakwashi ga man shaniu na tashi. Zaid yace "ni fa ba zan ci tuwo ba, abincin Matata zanci" Nene tace "Alkuran ba zaka ci ba, ni na dafa maku abinci kace ba zakaci ba? Uban kutura yayi kadan". Yace "wai ya Nene zakizo Gidana ki min iko". Tace "a gaban Matarka zan lakada maka shegen duka, ka zauna ka ci tuwon nan, ko na danne ka na maka dure". Baki ya bude, ya san zata iya, ya san zata aika, ya zumburo baki ya zauna. Labiba ta dinga Daria. Nan fa suka kwashi mulmula bibbiyu. Nene tace "ahap sai gashi an cinye ana tande hannu, waya ce ma borno gabas take?". Zaid yace "aidai an fi karfinmu ne". Tace "kai Arr, bangaya ma ba sai ga 'yayan albarka Tero, haruna Eskaley da su Master sun kawo min abubuwan arziki, turmin Atamfa jiya da leshi da turarruka, da takalmi da mai da sabulun wanka da na wanki, wai na sanya a Albarka a sanaarsu". Yace "kin manta ni na ka wo su? Kuma atamfa ne ba leshi, kuma ba kwanan na bane an kusa wata daya da yi, amma kina magana kamar jiya suka kawo". Harara ta zabga mishi tace "ai dai sun fi wani da ko hakin ashana bai taba siyo man ba". Yace "ba zai taba siya ba in jiranshi ake". Tace "kai dai ka sani mak'on na mak'ok'o masu cin katako". Yace "eh din naji". Labiba ba abunda takeyi sai daria, ai kawai taji tana son Nene kuma ko kadan bata 6ata mata rai ba Nene tace "Kinsan haka mijin Jikata Seebi yake da shegen feleken tsiya, don dai shi dunkum ne, be magana". Labiba tace "Allah sarki, Katsina suke aure?". Nene tace "Katsina? Haba, jikata na Landan, Ingila take aure, nima ai na taba zuwa". Zaid ya ma Labiba ido alamun tsaya kiga ni. Yace "mu fa an ishemu da wata Seebi, wai seebi na aure a London" Nene tace "wallahi tana Landan, tambayi mamarka kaji,chan take aure". Zaid yace "Mu dai ba mu yarda ba, yanzu haka tana Kano zaa raina mu ace tana London". Nene tace "Wallahi aa London suke, tsaya ma ka ga hotonmu da naje muka dauka". Ta mike ta koma parlorn don daukar wayarta. Daria yake kasa kasa yace "so nake na k'uleta fa". Labiba tayi daria chan k'asa tace ai na ga alama, na dagoka. Nene ta dawo, har ta dauko wayar Ta nemo hotunan don ba inda bata shiga da Android Phone dinta. Ta nemo pictures din da suka dauka a chan zata nuna musu kenan. Zaid yace "ai rana bata karya, a nuna mana mu ga Zahiri". Nene ta tsaya, tana kallon Zaid, ya ma rainata, ita kuma harda biye mishi. Zaid yace "In dagaske ne a nuna mana mana mu ga Seebi a London". Nene tace "karya nake danuwarka". Ya fashe da daria Labiba dai ta dan sha mur. Nene tace "zanci ubanka takwaran Zaidu bawan Allah, zan gurza maka rashin mutunci". Yace "Haba Neneta". Ta harareshi tace "Gidanmu zani". Labiba ta riketa tana kyaleshi Nene ai ba wurinshi kika zo ba. Nene ta harareshi tace "Uziless (useless) muje daki mu barshi, mai tsamin jallabiya, Allah ya sa baka taho dashi ba dai nan". Daria Zaid yayi yace "Naji, ya san ta k'ule, yau haka zaa karashe ranan da mitan Nene. Har bayan Magrib Nene na gidan. Sai chan aka zo daukarta. Labiba ta je yi mata take away din gara. Akayi akayi Nene ta tafi da Abincin da akayi dominta tace "sam ba zata dauka ba, kawai sai a ga na koma gida nikiniki da abinci, ba zan dauka ba to". Zaid yace "haba Nene ta bata lokaci ta miki abinci ba ki ci ba, kika hanamu ci kuma sai kice ba zaki tafi dashi ba? Haka akeyi?". Tace "wani ya sata? Iyayi, wace amarya ke abinci? Ba zan dauka ba wallahi". Zaid yace "to wallahi nan gaba kika sake zuwa ko ruwa ba zamu baki ba". Tace "naci ubanku kuwa daga kai har ita din". Yace "haba Nene, kar ta jiki mana". Tace "yo sai na kirata na fada a gabanta". Yayi saurin cewa "yi hakuri, kina iyaawa. Labiba ta shigo dauke da ledoji gara cincin da dubulan da alkaki cike da ledoji. Nene tace "Thank you Thank you". Ita Labiba taga Nene 'yar gayu tace bari ta burgeta irin da turancin nan tace "Nene mungode, we appreciate your visit, May God Bless you". Nene tace "Keeee, ni zakiyi wa turanci? Baka gaya mata baa turanci a gabana ba? Ko zagar min uwa kikayi?". Labiba tayi saurin girgizai kai a daburce tace "wallahi Aa, ba zaginki nayi ba". Ganin hankalinta ya tashi ya sa Nene daria tace "ja'ira har ta tsure, to nasan ba zaki zageni ba, turancin ne banso, wanda ya man turanci gani nake kamar ya zagar min uwa". Labibs ta murmusa tare da sakin ajiyar zucia. Nene tace "To Thank You, Sorry, Byebye". Ba ta jira cewarsu ba ta fada mota Driver ya jata. Zaid ya rungumo Labiba yace "Yau dai kin ga Nene". Naunauyar Ajiyar zuciya tayi tace "Yau naga Nene". Yace "Haka fa take, ai Nene damuwa ce, yanzu zata kwance maka zani a kasuwa, kuma ta manta ma ta gurza ma". Tace " hahaha i love Nene already". Ya sungumeta in bridal style ya na tafiya da ita. Yace "Wanchan Abincin ya zamuyi da shi?" Tace "mu kai gidan Baba". Yace "nikadai zanje". Tace "harda ni" Yace "Nope". Tace "pleasee". Yace "Naqi wayon". Tace "Haba Mijin". Yayi daria cike da kauna. Washegari ta karbi ziyarcin yan Bencin Eskaley. *** B A Y A N S H E K A R A D A Y A Duk Amaren bara sun haihu. Ko wacce da diyarta Mace Diyar Dalo Ummansu Jawad aka ma takwara. Diyar Abdulmajeed kuwa taci Maryam. Samira ta samu Fatima Sai Labiba, Labiba ta haifi YASMIN. ** Bai manta lokacin da Labiba za ta haihu ba, tana kallon Dadin kowa a arewa 24, ta kalla na minti 30 nakuda ta taso mata gadan gadan, baya Gida yana Chan Tudun Matawalle gun Baba, ta kirashi tace “ka dawo”. Sai ko gashi ya dawo ya dauketa suka tafi Asibiti, motsi dubu sannu yake mata, tun karfe 9 suke abu daya sai karfe 12 ta haihu, da Zaid aka karbi Haihuwan don kin fita yayi, fitowar kan jariri kadai ya kauda kai saboda ya kasa jure ganin Labiba cikin azaba irinta haihuwa. Kukan Jariri yaji. Da sauri ya amsheta tare da rungumeta Mace ce “Mace ce?” A kunne ya rada Mata “Barakallahu Fiki YASMIN, Allah ya miki Albarka”. Sannu da godia ya jera ma Labiba ya kai 1000. Zaid ya zauna ya tsantsara text ya tura ma Contacts dinshi. *Alhamadulilah Allah has blessed me with a beautiful girl. The Father, Mother and daughter are in good condition.* Asubar Fari Aunty Mariya, da Aunty Aseeyah suka zo Asibitin dauke da ruwan Zafi da kayan tea. “Ja’iri jiya da na ke cewa ka daina barin diyar mutane ita kadai me kace?” Yayi daria yace “Aunty kinsan muna gama maganar nan da ke ko minti 3 banyi ba ta kirani, ina shagon Eskaley kawai na wuce”. To tunda garin Allah ya waye Zaid ke amsa kiran yan barka Asibiti kuwa tururuwar zuwa ake, bayan an ga lafiayarsu aka sallamesu suka koma Gida. Jawad ya kira yi ma Zaid barka. “Haba Bro, ya zaku kira mu yanzu? Ka san dai babyta batayi kwari ba? Jiya sukayi 40days, yanzu ka sa dole Princess tace sai tazo wani Katsina Suna”. Zaid yace “ka ma isa ka hana, Matata da tsohon cikinta kuka sa tazo Abuja Suna, ai wallahi sai kun rama mana bamu yarda ba”. Jawad yayi daria yace “harda wani cewa The father the mother and daughter are all in good condition, kamar kai ka mata haihuwar”. Zaid yayi daria yace “Ai ina jin na fita wahala, ni nayi nakudar na ji jiki sosai”. Daria sukayi yace “to Allah ya raaya” Ya amsa mai da Ameen. Ran suna yarinya taci sunanta *Yasmin Zaid Ali Zaki* Wannan kenan. Shafa’atu? Babu wanda ya san inda take babu wanda ya san ko tana mace ko a raye, babu wanda ya san duriyarta abunda yafi ko wanne mahimmanci, babu wanda ya damu ya san duriyarta. Tuni sun mance da rayuwarta kaf. ^^^^ Labiba ta gama Diploma dinta zatayi joining Umaru Musa Yaradua zasu bata level2. Dalo kuma tana Nile University inda take karantar Biology, gida take kai Lubna in zata lectures. * Jiya Yasmin ta shiga Shekara 1 da haihuwa, a gida suka mata celebrating 1year birthday. Zaid ya fito sanye da kayan shi na civil Defense ya fito fes abunshi. Kallonshi kawai Labiba takeyi, sai kamshi yake zubawa, tace “Wallahi Ni dai ban taba ganin wanda Uniform suka mishi kyau ba kamarka, kamar don kai a ke yin khaaki dinnan”. Daria yayi tare da manna mata kiss a baki ya, ya amshi Yasmin a hannunta tare da manna mata kiss a goshi. Bacci take amma sai da yayi mata magana Yace “Daddy zaije aiki, ina son Yasmin da Mummynta“ Labiba na kallonsu cike do Soyayya. Tace “Zanje Gida, Aunty Mariya tace Baba bai ji dadi ba”. Zaid yace “Ciwon kai ne fa, kuma stress ne, aunty maria can exaggerate ehn”. Labiba tace “kai ko Mijin, dole ta damu, Miji ai ba wasa ba”. Ya kalleta tare da ida kashe mata kannanne idonshi yace “haka akeji in banda lafia?” Tace “abunda ya fi haka ma”. Daria yayi sosai ta rakashi har Mota tace “Motar nan tayi dattii fa, ka dauki tawa”. Yace “ko jiya an wankeshi, k’ura ne”. Tace “kar ace ma dirty dirty” Yace “in dai ba ke zaki ce min ba ni ina ruwana da mutane?”. Tayi daria tana kallonshi zaune a mita yanda yayi kyau, Khakin nan ya kara mishi girma da kwarjini a idonta”. Wani tunani tayi tace “kasan bamu taba Zancen Mota ba? In short kafin aure me ma mukayi wanda couples keyi? Nothing, dama a dawo min da yanmataccina”. Dariya yayi yace “i am late, sai na dawo, i love you kinji baby?”. Tace “i love you too”. Yayi daria yayi horn Maigadi ya bude mai Gate. Wurin karfe 4 ta ja Motarta zuwa Tudun Matawalle da Abinci Basket biyu, daya na Gidan Aunty Mariya daya na Aunty Aseey. Sai da ta fara shiga gaida Baba Aunty Mariya tace “yo ai tun safe ya fita wai yaji bacci”. Ashe Zaid na gidan ya fito daga dakin Baba don shi yake mishi shara yace “ba na ce miki ya warke ba? Aunty kawai ta zata mijinta zai gangara ne”. Aunty Mariya ta harareshi tace “zan bata ranka”. Dariya yayi sosai Labiba tace “kyaleshi Aunty zan tayaki miki maganinshi”. Daria sukayi yace “nidai na tafi, a gaida Baba”. Zaid ya masu byebye ya tafi ya barsu nan, ta dan jima kafin ta shiga gidan Baban Amira Kafin Maghrib ta koma Gida daga Gidan Aunty Aseey, tace su Amira su zo mata weekends ita da Sabit. Bayan Isha’i ta tsanyara wankanta ta shirya cikin wani Material fitted gown, kamar bata haifi yasmin ba, yasmin barcinta takeyi. Ta daura dankwalinta tana jiran dawowan Mijin. Taji dirowar Motarshi. Ta feshe jikinta da turare, mai makon ta ji shigowarshi, sai ta ga wayarshi. Dauka tayi tana mamakin kiran “Hello”. Yace “Beebs, gani nazo, ina waje?”. Shiru tayi me yake nufi? Taji yace “Ko jan aji zai hanaki fitowa? Zaki shanya Saurayin?”. Tace “Oh My God, sorry boyfriend gani nan fitowa”. Da sauri ta bude wardrobe ta dauko wani karamin gyale wanda take sawa da Jallabiya ta yafa a kafadarta, ta sake feshe kanta da turare, ta sa ma Yasmin Pillow ta kareta a tsakiyar gado ta fita waje tana rangaji kamar Bishiya. Daga Mota yake kallonta, Sonta kamar ya fasa zuciyarshi, yana kallon yanda ko wani gaba na jikinta ke motsawa. Fitowa yayi ya bude mata Motar ta shiga ya rufe ya zagaya ya zauna”. Kara musu Ac yayi. “Ina Yasmin?” Tace “sleeping”. Hannunta ya rik’o yace “Girlfriend” Tace “boyfriend” Yace “to nazo Zance, a min Tadi”. Daria tayi ta ga Ledar Havillah Ice cream tace “Lahh Ice cream”. Yace “dallah ba haka sukeyi ba, jan aji zaki dinga yi, ni zan miko miki ki karba”. Tace “oh okay to bani”. Yayi daria yace “Baby ga Ice Cream na siyo miki”. Kamar dagaske ta kawar da kai ita kunya. Daria suka fashe a tare. Ice cream din ya fasa yana bata a baki yace “haka saurayi da budurwan zamani sukeyi ko?”. Tace “ni ina zan sani, nima yau na fara”. Yace “a sannu zamuyi k’ara’i” Tayi daria Ice cream din lebenta ya lashe, sun nisa da abunda sukeyi suka ji Yasmin ta chanyara Ihu. Ai sakin Ice cream din sukayi suka fita a guje gudun ko wani abu ya faru da ita. Zaida ya riga shiga dakin Ashe Farkawa tayi taga ba kowa. Da sauri ya dauketa ya rungumeta a kirji yana rurrugata. Labiba ta harari Yasmin da tuni tayi lamo ta koma bacci a kafadar Babanta tace “Yas you ruined our date, ina Zance da dan Saurayina kin katse mana Jin dadi”. Zaid yayi daria yace “i love you both”. Labiba ta rungumesu duka tace “ina sonku ku duka”. *Tabbas Wannan Zaidun Labiba ne* THE END? Yes Mankasss ya k’are. *Alhamdulilah, Allah nagode maka da ka bani ikon gama wannan Labari na DANMAKAHO, Allah ka yafe min inda nayi kuskure, abunda na rubuta daidai Allah ka sa alumma su amfana dashi*”. *DAN MAKAHO na ku ne Ma su yin Soyayya domin Allah* *ALLAH KA KARA MANA SON MASU SON MU*

0 Comments