BABBAN GIDA CHAPTER 3

BABBAN GIDA CHAPTER 3
Washe* *gari*.... Da sassafe around 6:22Am ' Fadwa da Ilham suka tashi sukayi Sallah, Bayan sun idar da sallah ne Ilham tayi wuff ta tashi tana k'ok'arin d'aura towel a jikin ta, "Ilham kada kiyi wanka yanzu ' saboda gyaran d'aki yana jiran mu." Cewar Fadwa, Ilham tsayawa tayi tana kallon Fadwa d'auke da alaman tambaya a fuskar ta, "Gyaran d'akin ina kuma? " "Gyaran d'akin Yaya Khaleel kuwa, domin kuwa ya ce yau da safe zamu gyara shi ' Ai auna arzik'i mukayi jiya don wallahi da jikinmu ya gaya mana." Tsaki Ilham taja ' tare da jan kwafa, "To wallahi ' babu wani gyaran d'akin da zamu tsayayi, don kuwa test garemu yau ' shi ya gama nashi karatun mu zaizo ya takura mAna, " "Tab!! To aini mantawa nayi banyi mashi bayani ba tun jiya d'in." Ya tsine baki Ilham tayi gami da buga cinyar ta, "ke kika sani, wallahi ki zauna nan harkisami Carryover ' shine na farko wanda zai jibge ki, " Fadwa mik'ewa tayi tsaye tare da yaye hijab d'in jikin ta, "To yanzu yaza'ayi kenan mu fita ba tare da kowa ya sani ba? " "Yanzu dai kibari inshiga wanka ' infito saike ma ki shirya. " Ilham harta juya zata shige bathroom Fadwa tayi saurin dakatar da ita da cewa, "Ilham Amma kinsan dai bazamu fita ba tare da ' mun shirya musu breakfast ba ko?" "Fadwa wai wane breakfast kuma? Bayan kinsan muddin muka tsaya tofa ' gyaran d'akin nan tamkar mun gama yin shine, kawai mubar musu Umma idan ta tashi saita had'a kokuma d'aya daga cikin su." Ta na gama fad'in haka ta shige bathroom ba tare da ta jira abunda Fadwa zata ce ba. A bakin gado ta zauna Tayi jugum ' babu abinda take tunowa sai irin marin da Tasha wajen Yaya Khaleel. "Anya kuwa Ilham zan iya bin shawarar ki kuwa? Haka ta fad'a idanuwan ta cike da tsoro. " *Some* *Minutes* *Later*+ Bayan Ilham ta fito daga bathroom ne Fadwa ta shige cikin sauri ' Tukunna Ilham ta fara Shiryawa. Yaya Farook saukowa yayi daga gado ' gami dayin mik'a sannan Ya fad'a bathroom cikin Sauri yayi wanka tare da yin Alwala, sannan ya fito yayi sallah. Bayan ya idar ne yaji cikin shi tamkar anyi mashi yasa aciki, Hakan yasa yayi saurin mik'ewa tsaye. "Ashhh wace irin yunwa ce da sanyin safiya haka? " Fita d'akin yayi cikin sauri, ya nufi kichen ' lipton ya fara nema baigani ba, ganin haka yasa Ya nufi d'akin su Ilham cikin sauri, "Ke zo ki had'amun Tea insha yanzun nan Yunwa nakeji, " Jitayi maganar ta daki zuciyar ta ' kallon shi ta juyo tayi, cikin k'unk'uni tace. "To, " Yaya Farook juyawa yayi ya koma d'aki ya cigaba da shiryawa, Ilham bayan ta kammala shirin tane ' ta je ta tsaya bakin Kofar bathroom, "Fadwa dalla kiyi sauri, inba haka ba wallahi Tafiyata zanyi ' kinga har Yaya Farook ya sani aiki ko? " Cewar Ilham, "Ke naji ' yanzun zan fito dalla, " Tsaki taja sannan ta wuce kitchen ' cikin d'an k'ank'anin lokaci ta had'a mashi ta kai mashi d'aki, "Yaya Farook ga tea d'in nan, " Nuni yayi mata da yatsa ' alaman ta aje saman side drower, Bayan ta ajene Ta juya ta wuce ' tana komawa d'aki ta iske Fadwa a zaune ta na Shafa mai, "Wai ke Fadwa kanki d'aya kuwa? amma kinsan dai sauri mukeyi ko?" Cikin hanzari ta tashi tasa kayanta sannan Tasha powder sama sama ' tukunna ta d'auki gelen ta yafa a kirji, "Tow Am done. " Ta fad'a rik'eda k'ugu ' sannan Ilham ta d'auki gelen ta itama ta yafa, suka fito parlor cikin sand'o har suka fita cikin garage ' Fadwa ce ta kwankwasa wa driver kofa, "Ka fito mun shirya! Cewar Fadwa, " Ba tare da wani b'ata lokaci ba driver ya fito, ya bud'e motar sannan suka shiga ' tukunna yayi hone mai gadi ya bud'e gate d'in suka fice. Bayan wuce warsu ne ' Yaya Farook ya fito rik'e da key d'in shi a hannu ya wuce Office,. Yana fita Umma ta fito daga sashen ta ita da Abba ' kallon dinning table tayi taga babu komai, "ha'a inasu Fadwa ne? Ya haryanzu basu Had'a breakfast ba?" Abba zama yayi a kujerar harabar parlor, "Kila basu gama bane da wuri, " Cewar Abba, Umma d'akinsu ta nufa ganin basa cikine yasa ta wuce kitchen domin duba, nan ma haka ' cikin hanzari ta Koma parlor, "Wallahi basa gidan, kardai sun tafi School ne yaran nan." "Kinga bara kawai in wuce wajen aiki ' zan karya acen, tunda kikaga haka to sunda uzri ne a gabansu." Yana gama fad'in haka ya tashi ya fita, Haka yai daidai da shigowar Yaya Khaleel parlor , a tsaye ya iske Umma tayi folding hannayen ta ' sannan ya zukunna cike da ladabi, "Umma ina kwana! " "Lafiya k'alau Khaleel ya gajiyan jiya? " "Lafiya lau Umma ' Umma lafiya na ganki haka? Yayi tambayar tare da mik'ewa tsaye, "Hm Khaleel al'amarin yaran nan ne yabani mamaki, School suka wuce ba tareda sun had'a breakfast ba." Cikin yanayi na mamaki yace, "what!! Lallai ransu zai b'aci yau, nasan wannan iskanci Wannan yarinyar ce Fadwa jikinta zai gaya mata. " Umma zatayi magana yai saurin taren numfashin ta da cewa, "Umma karki damu nima gwani ne a kitchen ' da lafiyata da komai bazaki shiga kitchen ba ina kallo. " Murmushi yayi mata sannan ya juya ya nufi kitchen ' indomie ya dafa cikin d'an k'ank'anin lokaci sannan ya kawo Ya aje a dinning table. Umma na zaune a harabar parlor ' tana kallon kai da komo wanshi, saida ya gama jera komai sannan ya dawo ya zukunna inda take zaune. "Umma ga abun karya war nan na kammala, " To Umma ta ce sannan ta tashi ta nufi dinning table ta zauna ' cikin hanzari yayi sarving d'inta sannan shima ya zuba, "Amm Umma Yaya ya tashi kuwa?" "Gaskiya banji motsin shiba Khaleel," Tashi yayi ya nufi d'akin Yaya Farook, ya murd'a kofar yaji a kulle sannan ya juya ya koma parlor. "Farook d'in na nan kuwa?" Cewar Umma, "a'a Umma k'ofar shi a kulle. " "Ohh Hakane yaune zai fara shiga Office," OK kawai yace sannan ya maida kallon shi a kan plate d'in indomie d'inshi ya cigaba da ci. *** *** *** *** *** *Around* *11:30am* Su Fadwa sun fito daga exam hall ' rik'e da handbag d'insu a hannu. "Yanzu inda munsan zamu gama da wuri ' aida mun sanarwa Driver, " Cewar Fadwa, "ai bari kawai in kirashi ' don naga inada Number d'inshi. " Ilham ciro wayarta tayi daga handbag d'inta tayi dailling number d'in Driver, "Hello, kazo ka d'auke mu daga school ' don munyi closing. " To kawai driver ya ce ' sannan ta kashe wayar, cikin hanzari driver yaje ya d'auko su daga school ' ya kawosu gida haka yayi daidai da fitowar Yaya Khaleel cikin Garage domin shan iska. Bayan su Ilham sun fito daga motor ne suna k'ok'arin shigewa gida, Yaya Khaleel ya dakatar dasu da cewa. "Where did you think you're going to????" Yayi maganar cikin yanayi na fad'a , a tsorace suka tsaya tare da juyowa suka kalleshi. "Yaya Khaleel ciki zamu shiga," Cewar Fadwa. "ciki ko? To kushiga!! Aike dama daga ganin kwayar idonki to baza kiyi kunya ba!!!. " Fadwa kallon Ilham tayi suka had'a ido sannan ta sunkuyar da kanta k'asa, "Ubanwa kuka mayar y'an iska??? Umma? Kokuwa Abba?? Ko kuma nida Yaya Farook?" "Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri ' zanyi maka bayani," Cewar Fadwa. "Zakimin shuru ko sai nazo na tattaka ki? To bari kuji infad'a maku, da zarar kun shiga ciki kun aje wannan kima kiman handbags d'in naku ku zarce d'akina ku jirani. " Tsoro duk ya gama cika Ilham idanuwan ta kuwa ' gabb suke da zubar da hawaye, d'ago kai tayi ta kalleshi gami dayin fuskar tausayi. "Yaya Khaleeel please.... Bata kaiga k'arasawa ba ya daka musu tsawa, "zaku b'ace mun da gani kokuwa?" Da gudu suka shige cikin gida ' cike da tsoro. Suna shiga cikin parlor suka iske Umma a zaune tana kallo ' basu san lokacin da suka tsugunna a k'asanta idanuwan su ciccike da hawaye, " Umma don Allah kicewa Yaya Khaleel karya dake mu! Cewar Ilham," Umma rage k'arar TV d'in tayi da remote sannan ta kalli Ilham, "Ai bansan bakida Kunya ba sai yanzu Ilham ' inbanda kun raina mutane kwatafi ba tare da kun had'a mana abin karya waba? " Sunkuyar da kai Ilham tayi Hawaye kawai ke zubo mata, "Umma don Allah kiyi mana Hakuri ' wallahi Uzri mukeda shiyasa amma insha Allah haka bazai maimaita kanshi ba, " Cewar Fadwa, "Au kema zaki nunamin taki rashin kunyar kenan ko? Ai Fadwa koma wane irin Uzri ne daku ' ai kamata yayi Wani cikin ku yazo yaimun bayani, bawai ku kad'a kanku ku fita ba." Umma na gama rufe baki Ilham taji saukar dundu a bayan ta, a kid'ime suka waiga domin suga waye ' Haba ido hudu sukayi da Yaya Khaleel, haka yasa suka tashi a guje tare da cillar da handbags d'insu zuwa d'akin shi. Suna shiga d'akin shi suka zube a k'asa Cike da tsoro, Yaya Khaleel kwafa yayi gami da girgiza kai sannan ya biso. "To banda mugun duka dai ' don nasan halinka. " Cewar Umma, Kai tsaye ya zarce d'akin shi ba tare da yacewa Umma komai, Cikin zafin nama ya bud'e k'ofar ganin su yayi a zukunne kowan nen su da hawaye sharkaf a fuskarshi, fuskar nan tashi a d'aure ya nufi wardrope dinshi ya zaro belt ' da Fadwa ya fara had'a ido sannan ya nufo kanta, ganin haka yasa tayi zambur ta mik'e tsaye. "Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri ' Karka dakemu please...." Cikin kuka ta k'arashe maganar ta cike da shash shek'a, "Ohhh Kokowa xamuyi koh? Aike dama nasan babu abinda bazaki iya ba.... " Jikake zafff zafff ' saukar belt a bayan ta, Da gudu ta nufi wajen gadon shi ta rakub'e cikin kuka tace. "wayyo!!! Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri please forgive us....." Komawa kan Ilham yayi wacce ko ina najikin ta rawa yakeyi, "Ke dan ubanki ' da hankalin ki da komai, zaki biyewa wancen tsageran? saboda kin manta wanene Yaya Khaleel ko? To jikinki zai fad'a maki kuwa." Sai da ya sauke mata belt shida a jikin sannan ' ya k'ara mata da hauri a jikin ta, saboda tsabar kuka Ilham ko hawaye ya daina fita daga idonta. "Tashi ki fita ki bani waje ' idan ba haka ba saina kakkarya ki a wajen nan. " Da gudu Ilham ta bar d'akin jin haka yasa Fadwa mik'ewa tsaye Cikin sauri zata fita, ya cafko ta A gigice ta juyo ta kalle shi. "ina kike tunanin zaki? Ba tareda jikin ki ya gaya maki ba? Mara kunya!!!" Jin saukar belt tayi a k'afa funta ' yasa tayin tsalle cikin rad'ad'i ta k'ank'ame shi jikinta sai rawa yakeyi, "Ya..Yay. Yaya please kaimin afuwa ' wallahi zan iya mutuwa...." Wani zirrr yaji tundaga k'afar shi har saman kanshi, shuru yayi nad'an lokaci sannan ya finciko ta da karfin tsiya har saida ta fad'a k'asa, a hankali yake takowa inda take ' ganin ya nufo ta da belt d'in ne hankalin ta ya k'ara tashi , "Yaya wallahi wannan ba plan d'ina bane Ilham ce tace muyi haka, please karka kasheni. Jin haka yasa shi tsayawa cak ' tare da wullar da belt d'in a saman gado, "Tashi ki fice mun da gani ' gobe idan Ilham tace ki shiga wuta sai ki shiga...." Da sauri ta mik'e tsaye gami da had'awa da gudu ta fice daga d'akin, ba ta tsaya ko ina ba sai a saman gadon su. Saida ta gama dawo wa normal sannan ta lura da Ilham rik'e da bucket d'in ruwan d'umi a hannunta tare da K'aramin towel tana gasa jikinta, "Ilham?" A gajiye Ilham ta juyo ta kalli Fadwa, "Ya akayi?" Fadwa tashi tayi ta zauna cikin jin zafin jikin ta, "Meyasa Yaya Khaleel ya tsane ni?" "Mtsww wannan wace irin banzar tambaya ce ' ni dalla ki kyaleni naji da d'aya mana aida kinsani kin tambaye shi kafin ki fito.!" Ya tsine baki tayi sannan ta tashi ta fada bathroom don yin wanka da ruwan d'umi, ko da ta fito bata iske Ilham a d'akin ba nan ta d'aga kai ta kalli a goge, "Ok! Lokacin girka lunch yayi 2:00pm Ilham na kitchen yanzu. Bayan ta zauna agaban mirror ne ta fara gyara jikinta ' wayar ta tayi k'ara, cikin hanzari ta d'auka ganin Yaya Farook ne yasata yin picking cikin sauri. "Hello Yaya.." "Baby na yakike? Hope kina lafiya?" A wahale ta ce, "lafiya kalau Yaya" "Meyasa meki naji kamar bakida lafiya Fadwa!" Jitayi kamar ta fad'a mashi abinda ya faru sai kuma ta fasa, "Well, Yaya Farook babu komai ' is just that nad'an sami bacci ne d'azun. . Ok yace tare da yinmata sallama sannan ya kashe wayar ' a tsanake ta tashi ta sanya kaya ajikin ta doguwar riga atamfa, sannan ta fito ta nufi parlor ganin Yaya Khaleel tayi a zaune ' nan take cikin ta murd'a ta juya xata koma ya dakatar da ita da cewa, "Kije ki gyaramun d'aki na yanzun nan kuma ke kad'ai. To tace sannan ta juya ta nufi d'akin shi, bayan y'an lokuta k'alilan ne ta dawo parlon ta zauna tare da cewa, "Yaya Khaleel na gama. ok ya ce ba tare da ya d'ago kai ya kalleta ba. *Around* *2:30pm*+ Ilham ta gama jera abinci da duk wani abun buk'ata a saman dinning table , sannan ta haura sama ta yiwa Umma magana ' hakan yayi daidai da dawo war Abba daga wajen aiki, Fadwa da Ilham da sauri suka tunkari Abba tare da yi mashi sannu ' sannan Fadwa ta karb'a bag d'in hannun shi ta kai sashen shi, Yaya Khaleel ya tare Abba cikin ladabi ya zukunna a gaban sannan ya ce, "Abba sannu da dawo," Yawwa Abba ya fad'a sannan ya nufa dinning ya zauna, tukunna Umma ta fito cike da fara'a a fuskarta ta zauna gami da yiwa Abba sannu da dawowa, Ilham ce ta tashi donyin sarving d'insu Fadwa tayi saurin karb'ar Spoon d'in tare da cewa, "Ai Abba nane so kibari na zuba mashi," Nan Ilham ta koma ta zauna gamida balla mata harara ' Abin haushi ya bawa Yaya Khaleel yasa yaje ya zauna awajen , "Ke kiyi ki zuba min yunwa nikeji!" Ya fad'a a gadaran ce ' Abba ya kalle shi, "banson takurawa fa Khaleel ' hannu biyu gareta ba takwas ba. Saida Fadwa ta zubawa kowa tukunna ta nemi waje ta zauna ta fara bawa ciki abinci , saida kowa ya kammala sannan Ilham ta tashi ta tattara plates d'in wajen ta wuce kitchen dasu. Umma da Abba tashi sukayi suka tafi sashen su ' Yaya Khaleel kuma ya fita harabar gida don shan iska, fitar shi keda wuya Yaya Farook ya dawo ' shigowa yayi tare da yin sallama, Fadwa da ke a zaune ta amsa mashi cike da fara'a. "Baby na ke kad'aice a parlon?" Yayi tambayar a gajiye gamida zaunawa, "Eh ni kad'aice Yaya, In zubo maka abincin ne?" Juyowa yayi ya sakar mata wani kallo ' tare da yin murmushi, "Yes, but ki zubomin ki kawomin d'akina." To tace mashi sannan ta yunk'ura ta nufi kitchen kasan cewar Ilham ta tattara komai ta kai kitchen, koda ta je kitchen babu kowa har Ilham ta gama ta wuce d'aki. Cikin hanzari ta zuba abincin d'an daidai a plate tare da d'aukar roban ruwan sanyi ta nufi d'akin Yaya Farook ta aje masa a saman side drower sannan ta juya zata fita ya turo k'ofar, a tsora ce taja dabaya ta tsaya Yaya Farook ya k'araso daff da ita gami dayin mata kiss tare da rungume ta. "i missed you so fucking much Fadwa!!" Nan take ta saki wani k'ara cikin sauri ya saketa gamu da tallabo fuskarta nan yaga idonta yayi jaaa Alaman daf take dayin kuka, "Babyna lafiya? Ko dai bakida lafiya ne?" Yayi tambayar yana kallon Cikin idonta, "Yaya Farook ' ka famamin inda aka dakeni ne d'azun!" Nan ya waro manyan idon shi ' cike da mamaki, "What!!! Waye ya dakeki??" Ranshi abace yayi tambayar ' sunkuyar da kai kawai tayi hawaye na d'iga a hankali...... Sake tambayar ta yayi cikin tsawa, "Nace waye ya dake ki!!!? Ranta abace ta d'ago kai ta kalleshi, " "Waye zai dake ni idanba Yaya Khaleel ba!! " Jin haka yasa jikin shi yin sanyi ' Cikin d'an k'ank'anin lokaci ya ce, "hm Fadwa ai bakwajin magana ne ' ni nasan Bro ba zai dake ki haka nan ba, sai idan kinyi laifi." Tsayawa tayi tana kallon cikin kwayar idon shi cike da mamaki, "I know that Yaya Khaleel d'an uwanka ne and ni ban fad'i haka da wata manufa ba and beside kai ne ka nemi kasani. " fuuuu ta juya zata fita yayi saurin rik'e mata hannu, "I know that you're hurt Fadwa ' but ki kiyi hak'uri bazan iya cewa Khaleel komai ba. " "Is OK, na fahimta. " Fizge hannun ta tayi ta fice daga d'akin , har ta nufi d'akin su sai kuma ta juya ta nufi d'akin Yaya Khaleel ' kasan cewar tasan cewar baya d'akin yasa ta bud'e Kofar a hankali gami da yin sand'o, ta na shiga ta tura ta rufe. Ciki ta k'arasa cikin izza ' ta hango Album a saman gadon shi tare da diarry d'insa a gefe. Cikin sauri ta hau saman gadon ' gami da d'aukan Album d'in ta d'ora a cinyarta, ( *Ohh* *Ni* *Seemaluv* *kodai* *Fadwa* *ta* *mance* *d'akin* *da* *shiga* *ne*?) Budewa takeyi a hankali ta na kallon hotunan shi da abokanan shi mata da maza, haka taita kallon hotuna daga wanda zai bata dariya sai wanda zai bata haushi ' a haka har ta bud'o wani hoto, ganin hotun yasa gabanta fad'uwa. "Dama Yaya Khaleel haka kake? Daman abunda kake tsina nawa a American kenan? Wannan kuma wacece to!!. " Hoton cikakkiyar mace ce kyakkyawa ' haihuwar Uwarta, wacce babu kaya ajikinta ta na zauna. Cike da tsoro Fadwa ta rufe Album d'in tare da jan dogon tsaki, "Mtsww wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu shi kuma Yaya Khaleel me yakeyi da wannan picture d'in?" Ta fad'a cike da takaici ' sannan ta jefar da Album d'in a gefe ta d'auki Dairy d'in. Bayan ta bud'e ne taga An rubuta, (Dear Diary...) A America ; ranar Litini ce na tafka babban kuskuren da ban tab'a tunanin zan tabka shiba a rayuwa ba, haka yasa duk idan na tuna dashi nakan zubda Hawaye..... Fadwa bata kaiga k'arasawa ba taji an bud'o k'ofa bamm , da k'arfin tsiya hakan yasa ta razana ta mik'e tsaye cikin rawar jiki rik'e da Dairy d'in a hannun ta, Yaya Khaleel tsayawa yayi cak yana kallon ta cikin mamaki cen ya hangi Dairy d'in shi rik'e a hannun ta hakan yasa shi k'arasowa wajen ta cikin zafin nama da b'acin rai, "Uban me kike min a d'aki? Ke wane irin stubbornness ke damun ki?" Ya fad'a tare da kama kunnen ta, "Ahhhggh Yaya Khaleel please am sorry ' zaka ciremun kunne!!!" Ta fad'a Idonta cike da hawaye, Yaya Khaleel ya fizge diary d'in nashi gami da cewa, "Bincike kike yimin dama? Da kikayi binciken ubanme kika binciko fad'amin, Iyee fad'amin nace!!!!" Ya k'arashe maganar cikin tsawa, hakan yasa ta fashewa da kuka ' don kuwa tasan idan har tayi wasa to kuwa wani dukan zata sake sha, "Yaya Khaleel don Allah ka tsaya kaji ' wallahi Allah ba bincike nake yi maka ba Yaya Farook ne ya ce inje in nemo masa biro, shine nazo nan ina dubawa....." Ta na gama rufe baki ya d'auke ta da mari tasss, a gigice ta dafe wajen tare da sakin k'ara, "Ahahhgg..." "Ke!! Ni zakiyiwa k'arya da rainin hankali? Kaff d'akin ku babu mai Biro sai kin shigo nan? Iyeee ba tambayar ki nakeyi ba??" Kwata kwata kasa magana tayi saboda kukan da yaci k'arfin ta, girgiza kai kawai takeyi Alaman a'a. "In banda ke kin gama raina mutane ' Diary na a hannun ki sannan ki dubi tsabar idona kice Biro kikazo nema, Kakkarya kine kawai yau bazanyi ba Fadwa." Sakin ta yayi ya nufa Wardrope d'inshi ganin haka ya bata damar fallawa a guje ta bar d'akin , kai tsaye ta wuce d'akin su cikin tsoro ta tura k'ofar ta rufe da key. Ilham wacce keta waya tun d'azu ne ganin halinda Fadwa ke ciki yasa ta yanke wayar ta cillar da ita saman gado, tayo kanta cikin hanzari. "Lafiya Fadwa? Meyasa meki?" Tayi tambayar tare da d'ago fuskarta, nan ta ga shedar hannu Alamun mari. "Subhanallah meya sameki? Waya mareki! Halan Yaya Khaleel?" Nin shi kawai Fadwa keyi sama sama ' saboda azabar da takeji a fuskar, Ilham rik'e hannun Fadwa tayi sannan tajata zuwa gado. "Fadwa idan akwai wanda ya dace ki fadawa damuwar ki to ni'ce, " d'ago kanta tayi ta kalleta da rinan nun idanun ta, "Ilham d'akin Yaya Khaleel na shiga ni karan kaina bansan meya kaini ba, Bayan na shigane ya iske ni aciki shine yayi mun wannan mugun marin ' Ilham wai meyasa Yaya Khaleel ya tsane nine? Meyasa kokad'an baya d'aukata amatsayin k'anwar sa?" D'an k'aramin tsaki Ilham taja sannan ta rungume Fadwa tare da bubbuga mata bayanta , "Amma dai Fadwa kinsan ko wajen Abba za'aje kece bakida gaskiya ko? Kuma tunda kinsan cewa ya tsaneki ai sai guji fad'awa tarkon shi, kuma sanin kankine gidan nan babu mai nuna miki banbanci ' yadda akemun haka kema ake miki.." Saurin share hawayen ta tayi tare da cewa, "Nagode Ilham ' lallai kin cika y'ar uwa, " Ilham tashi tayi ta wuce parlor, Fadwa kuwa a zuciyar ta tace . "Naji duk abinda kika ce Ilham ' amma ni gaskiya koda zai kakkarya nine kamar yadda yace, to fa saina binciko abinda Yaya Khaleel ke b'oyewa a diary d'innan. " Nan ta tashi ta fad'a bathroom ta wanke fuskarta sannan ta wuce parlor, suka ci gaba da kallo. *** *** *** *** *Around* *4:30pm* ... Su Fadwa na zaune a parlor suna kallo Umma ta shigo parlon ' bayan ta zauna ne ta ce, "Aikin ku kenan kallo ' to kun d'aura girkin yamma ko?" Fadwa cike da fara'a ta juyo ta ce, "A'a Umma ai d'azu tare muka had'a mukayi, "yawwa aiko kun kyauta, yanzu ku tashi kuje ku kira Farook da Khaleel ' Abban ku keson magana daku gaba d'aya. " To sukace a tare, sannan suka tashi suka tafi ' ba tare da wani b'ata lokaci ba suka iso parlon, Umma na ganin sun iso ta tashi ta haura sashen su don kiran Abba. Yaya Farook da Yaya Khaleel a k'asa suka zauna cike da ladabi, su kuwa su Ilham suna saman Kujera don ita Fadwa ma harda hard'e k'afafu d'aya kan d'aya Yaya Farook ya d'ago kai ya kallesu, "Wane irin iskancin banza ne? Ba ankira mun nan don su Abba zasuyi magana damu bane? Shine kuke zaune d'are d'are a saman kujera?" Jin haka yasa Yaya Khaleel juyowa ya watsa masu wani irin kallo ' ai tuni suka sulale k'asa cike da nutsuwa. Suna cikin haka ne Umma da Abba suka shigo parlon ' cikin kamala suka sami waje suka zauna daga bisani Abba yayi gyaran murya, "Ba komai ne yasa nace ku hallara anan ba ' illa maganar da zanyi wacce bata wuce uku zuwa hudu ba, wacce kuma ta k'unshi had'in kanku baki d'aya." Abba gyara zama yayi sannan yace, "Zan fara da kai Farook! Well Alhamdulillah yanzu ka sami aiki ' to me kuma ya dace kayi yanzu?" Sai Umma tace, "Aure!!" Yaya Farook yana jin haka ya d'ago kai ya kalli Fadwa, ya ga itama shi take kallo cike da fara'a sannan Abba ya cigaba da cewa, "nayi tunanin in had'a ku kai da Fadwa aure amma sai Umman ku ta ce had'in baiyiba ina ma laifin a had'a Khaleel da Fadwa? Dana duba sai naga Eh shawarar da ta kawo tayi, Amma nan da Two weeks kai Farook mukeso ka kawo mana wacce zaka aura!." Jin haka gaban Yaya Farook ya fad'a, ita kuwa Fadwa idanuwanta cike suke da hawaye ' Yaya Khaleel kuwa ai abun ba'a magana don kuwa zuciyar shi tuk'uk'i kawai takeyi. "Ke kuma Ilham yanzu kina iya bawa samarin naki damar zuwa domin ku fahimci juna ' amma mind you ba kowane zaki kawo cikin gidan nan ba!" Bayan ya gama ne Umma ta ce, "Ko kunada abun cewa game da wannan zabin?" Yaya Farook gyara zama yayi tare da kai zuciyar shi nesa ya ce, "Umma & Abba, bamuda abin cewa illa mu gode maku domin kuwa farin cikin ku shine farin cikin mu ' bak'in cikin ku kuwa! Shine namu, saboda haka wannan zab'in yayi." Abinda Yaya Farook ya fad'a yayi matuk'ar tab'a zuciyar Fadwa, hakan yasa ta farajin jiri na d'ibarta. Abba da Umma sunji dad'in kalaman Yaya Farook sosai ba kad'an, "Allah yayi maku albarka ' Allah kuma yasa naku y'ay'an suyi maku biyayya," Ameen suka ce sannan Umma tayi musu umarni da su tashi su tafi, bayan sun tashi Fadwa taji jiri na d'ibarta harta kaiga babu abinda take gani a gabanta face duhu ' hakan yasa ta yanke ji zata fad'i Ilham tayi saurin rik'eta. Cikin tashin hankali Umma da Abba suka yo kanta, "Innalillahi lafiya Fadwa? Meke faruwa ne?" Cewar Umma!, Yaya Farook ne yayi saurin sanya yatsun sa guda biyu wajen hancin ta, "Subhanallah bata numfashi, Khaleel yi maza kaje ka tada mota akaita hospital. " Cikin hanzari Yaya Khaleel ya fice ' Abba kuwa duk ya gama rud'ewa domin daka ganshi zaka gane cewa yana cikin tashin hankali, "Fadwa don Allah kada ki mutu ' banason rasaki amatsayin y'a kamar yadda Allah ya d'auke min mahaifinki amatsayin amini!" Cewar Abba, "Don Allah mai gida ka kwantar da hankalin ka ' insha Allah Fadwa rayayya ce in Allah ya yarda," Yaya Farook d'aukar Fadwa yayi cen caka kaff d'aukar jarirai, yaje ya sata a mota sanna ya dawo ciki ya Umarci Ilham taje ta d'auko gelenta, bata tare da wani b'ata lokaci ba tadawo rataye da gele a k'irjin ta sannan suka fice ita da Yaya Farook , har Umma zata bisu Abba yayi saurin rik'ota, "Bazakije a haka ba! Ki kintsa tukunna sai mufita tare . " Ya fad'a tare da samun waje ya zauna sannan Umma ta haura sashen ta domin kintsawa, cikin hanzari ta Umma sauko parlon sanye sa hijab d'inta a jiki, "A'a ki dakata tukunna harsai sun dawo sannan mu tafi baki d'aya," To kawai tace masa sannan ta sami waje ta zauna gami dayin tagumi. Bangaren su Yaya Farook kuwa tunda Khaleel ya tada mota suka wuce gudu kawai yake zabga wa ' cike da tausaya wa Fadwa. Cikin d'an k'ank'anin lokaci suka isa asibiti, bayan sunyi packing ne Yaya Farook ya fito cikin zafin nam ya d'auki Fadwa sannan suka shiga ciki, suna shiga ne sukayi kicib'us da Doctor zai shiga wani Ward d'in Yaya Khaleel ya tsaidashi, "Doctor!!! Please wait you have client here!!." A tsanake likita ya juyo ya kalle su sannan ya kwalawa Nurse kira ' cikin hanzari tazo wajen, "Yes Sir! "Ki hanzarta ki basu Ward ' kafin inzo yanzu! OK tace sannan tayi masu jagora zuwa d'akin, bayan Yaya Farook ya kwantar da ita Nurse d'in ta fita zuwa kiran Doctor ' Ilham na zaune a gefen Fadwa, "But Yaya baka tunanin Zab'in nan dasu Umma sukayi ne yajawo wa Fadwa wannan abin?" Cewar Yaya Khaleel, "What!!!? Karda insake jin wannan maganar daga bakinki Khaleel!! Ai duk abinda su Umma suka yanke shine daidai, " "But nifa Yaya gaskiya bana son ta," Yana gama rufe baki ya d'auke shi da mari tasss, "Ashe bakada hankali Khaleel?" "Kayi hak'uri Yaya, nayi kuskure insha Allah bazan sake ba!" Ya na fad'in haka ya tashi ya fice ya nufi wajen mota yayi zamansa, bayan fitar shine likita ya shigo ward d'in kai tsaye ya zarce inda Fadwa ke kwance ' stethoscope yasanya a k'irjin ta domin sauraron Numfashin ta, sai da ya kammala sannan ya cire ya juyo ya fuskanci Yaya Farook. "wato tayi doguwar suma ne, Amma insha Allah nan bada dad'ewa ba zata farfad'o." . "To likita thank you so much," "You are welcome ' yanzu zan turo Nurse tazo tayi mata settling IV fluid, " OK kawai Yaya Farook yace sannan Likita ya fita, cikin d'an k'ank'anin lokaci Nurse tazo tayi mata settling drip, sannan ta fita. + *Around* *6:42pm* Yaya Khaleel ya shigo cikin ward ' ya sami Yaya Farook zaune a kujera, "Yaya wai har yanzu bata farka ba?" "Eh wallahi Khaleel," "Yaya yanzu kamata yayi mutashi ita Ilham a maida ita gida ' don taje ta d'an shiryowa Fadwa abinda zataci , bayan Munyi sallah sai mu taho da su Abba gaba d'aya ' nasan kafin nan ta farka." "Hakane Khaleel muje!! Yaya Farook mik'ewa yayi suka fita Ilham ta bi bayansu, fitarsu keda wuya Fadwa ta bud'e ido cike da kasala haka yayi dai dai da shigowar likita. "Alhamdulillah ina y'an uwan naki?" Yayi tambayar tare da dafa k'arfen gadon nata, kai kawai ta girgiza mashi sannan ya ce. "Oh may be lokacin da kika farka basu nan ' bari inje sallah in dawo, Abinda ya fad'a kenan ya juya zai wuce tayi saurin tsaida shi da cewa, "Doctor!! Please meke damuna? Juyowa yayi ya kalleta tare da sanya hannun shi a aljihu, "A yadda na fahimta ' kamar kinsami wani bad news ne wannan ne kad'ai zai iya samar da shock a jikin d'an adam harta kaishi ga suma," "haka ne doctor tabbas bad news ne nasamu ' but please doctor can you do me a favor?" Tayi tambayar tana kallon kwayar idon shi, "For what? "Doctor please ' idan y'an uwana sukazo kace masu na suma ne saka makon ciwon kan da yasami cikin d'an k'ank'anin lokaci please." "is Ok i can do that for you ' akwai wannan sirrin tsakanin Doctor da patients d'insa, so you don't have to worry about that." Murmushi tayi masa tare da cewa thanks ' sannan ya fice. Bayan sun Isa gida ne ' Yaya Khaleel yayi packing motar Ilham ta fito sannan su kuma suka wuce masallaci, Ilham tana shiga ciki ta iske Umma a zaune ' jin motsine yasa Umma d'ago kai ta kalle ta a razane, "Haba Ilham ki shigo haka babu Sallama? Yaya jikin Fadwa?" Ilham samun waje tayi ta zauna ' sannan tace, "Umma Fadwa insha Allah zata sami sauk'i, likita ya ce zata farka bada dad'ewa amma mudai har muka baro ta bata farka ba😢." Umma hannu biyu tasa ta rufe bakinta, tare da yin salati. "Umma karki damu Insha Allah zata farfad'o, bari in shiga wanka kafin su Yaya su shigo. " Kai kawai Umma ta d'aga mata sannan ta tashi zata wuce sai kuma ta tsaya, "Umma ina Abba ne?" "Abban ku yana masallaci," To tace sannan ta wuce d'akin su.+ *Around* *7:00pm* Abba da su Yaya Farook suka shigo gida cikin nutsuwa, bayan sun shiga ciki ne Yaya Farook yace. "Abba i think ' ni kawai zan koma hospital d'in yanzu, don jiki na yabani Fadwa ta farfad'o kuma baza taji dad'i ba idan ta farka taga babu kowa." A zuciyar Yaya Khaleel kuwa cewa yayi, "Mtsww Don Allah ji Yaya kuma! To dama wane dad'i kuma akeso taji itada take a gadon Hospital? " "To shikenan Farook , maganarka haka take ' to amma ka ci abinci kuwa?" Cewar Abba, "A'a Abba wallahi banajin yunwa. "Haba Yaya yaza ai kace bakajin yunwa? Don Allah ka tsaya kaci abinci and beside likitocin nan suna iyakar yinsu ' am sure Fadwa zata sami sauk," Cewar Yaya Farook, Yaya Farook kallon shi kawai yayi tare da cewa, "Bani key d'in mota!" sannan ya juya ya wuce ' ba tare da yace masa komai ba. kai tsaye ya wuce hospital d'in, direct ya nufi d'akin da Fadwa take ' koda ya shiga a zaune ya iske ta hawaye kawai ke zubo mata a fuska, da sauri ya k'arasa kusa da ita tare da tallabo fuskarta gami da share mata hawaye. "Ko kad'an bana son inga hawaye na fita daga idonki, A fusace ta d'ago rinan nun idanun ta ' ta kalleshi cikin b'acin rai, "Hawaye?!! Hawaye fa kace!" Ya d'aga mata kai alaman Eh, "Ko dayake a fatar bakin ka kawai ya tsaya ' saboda nasan duk duniya babu wanda ya kaika son ganin hawaye na!!..." Ta k'arashe maganar cikin matsanan cin kuka, "Subhanallah Fadwa meyasa zaki jefeni da wad'an nan kalaman? Nasani wannan hukuncin da su Abba suka yanke ' dole zai yi mana ciwo amma we just have to accept the fact, dole zamu yarda da k'addara kumm..." Tun kafin ya gama rufe baki ' ta d'aga mashi hannu alaman dakatar wa sannan ta goge hawayen ta, "K'addara? K'addara fa kace! Wannan ai ba ita ake kira da k'addara ba Yaya Farook, Yaya Farook ko a yanzu zaka iya warware komai ' kafad'a masu cewa ni kakeso ' ka fad'a masu cewa akwai soyayya tsakanin mu ple...." Ba ta kaiga k'arasa maganar ta ba ya daka mata tsawa da cewa, "Me kike nufi!!? Kina nufin inkoma ince masu zab'inda sukayi baiyi ba ko kuwa mene? "Eh abinda nikeso kenan kayi ' idan kuma ba haka ba to Wallahi zan bijire , ba don komai ba sai saboda kwata kwata babu soyayya a tsakanin mu da Yaya Khaleel ' baka ganin yadda yake treating d'ina? Yaya Farook wallahi inasonka." "Wai meyasa bazaki fahimci abinda nikeson fad'a miki bane? Fadwa inason ki amma haka nan zan hak'ura dake, hakuri kawai ya dace muyi baki d'aya." Ya na gama fad'in haka ya juya zai fita tayi saurin rik'e mishi hannu, "Please Yaya Farook ' meyasa baka sona? Amma shikenan naji kuma na hak'ura zan aure shi, amma Yaya Khaleel bazai tab'a jin dad'in aure ba wallahi. " jin haka yasa shi juyowa ya kalleta cike da b'acin rai sannan ya fizge hannun shi ya fice, ya na fita suka had'e da su Umma a bakin k'ofar Ward d'in. "Ina kuma zaka je? Cewar Umma, Komawa ciki yayi sannan suka bi bayanshi, Umma na shiga taje ta zauna gefen Fadwa cike da fara'a. "Ina wuni Umma? " "Lafiya kalau Fadwa yaya jikin naki?" "Umma kada ku damu naji sauk'i ina Abba? Murmushi Umma tayi ' zatayi magana Ilham ta tari numfashin ta da cewa, "Haba wa ai Abba ya ce yayi fushi dake ' shiyasa ma baizo ba," "lalala Umma dagaske ne?" Cewar Fadwa, "A'a k'arya take miki Abban ku yana cen tare da Doctor suna magana." To kawai Fadwa ta ce sannan ta ballawa Ilham harara, Yaya Khaleel kuwa yana gefe a tsaye rik'e da waya a hannun. Abba ya shigo tare da doctor ' ya cirewa Fadwa canulla d'in hannun ta sannan aka sallame su sannan suka koma gida. *** *** *** *** ** *Around* *8:00pm* Suka koma gida ' basu wani zauna yin hira ba kowa ya tafi d'akin shi domin yin bacci.

0 Comments