Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA CHAPTER 23

ZUCIYA CHAPTER 23

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 23
Ya dade a waje kafin zuciyarsa ta daidaita ya dawo gida, har ya kusa isa gida ya kira Anisa, ta d'aga cikin tsananin farin ciki, yace " Nisa kina ina?" Tace " ina nan gidan su Zee." Yace " bari nazo na daukeki." Wani dadine ya kamata suna kashe waya ta saki wani ihu na farin ciki gaskiya yanzu ta aminta da san da Ashraf yake mata, nan Zee taita tsokananta wai ta dinga ja mai class, itakam ita kadai tasan abinda ta gani da yanda taji asanda ya juya mata baya.+ Ashraf yai shiru bayan sun gama waya har yanzu yana mamakin kawu, ya sani sarai mutum ne mai tsananin ambition sai dai bai taba tunanin haka b'oyayyun halayensa suke ba, da har zaiyi threatening din mahaifiyarsa da yakeso akan laifin da yayanta dashi suka aikata akan ta aureshi, shiru yai yana tunani kafin yai gwafa sannan ya kira Dan Litti, bugu biyu ya daga. Ashraf yace " Dan Litti ka nutsu sosai ka ji mai zanje maka." Nan ya shiga mai bayani da ni kaina bansan me suke cewa ba sai dai sunkai kusan minti 20 suna waya kafin daga bisani Ashraf yace " Ka fahimceni?" Dan Litti yace " yes sir, yanzu zakama Lawyer din maganar ko inje?" Ashraf yace " karka damu kai dai ka samo mutanen da zamu yarda dasu wanda kuma baza'ai suspecting dinsu ba." Nan suka karasa bayanansu sannan sukai sallama. Gidansu Zee ya wuce ya d'auko Anisa tana ta zubamai sakalci a hanya shidai sai kokari yake kawai yana biye mata. Nafi na zaune a barandar b'angarensu tana jiran taga shigowar Ashraf dan sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin yanayin da ya fita. Shigowar motarsa ce yasa ta saki ajiyar zuciya tare da mikewa tana kallo yai Parking sannan taga ya fito. Murmushi ta saki ganin fuskarsa dauke da fara'a, sai dai me? Anisa taga ta fito ta d'aya b'angaren ta matso kusa dashi ta sakala hannunta cikin nasa, kallan juna taga sunyi suka sakarma juna murmushi. Jitai wani abu ya tokare mata a makoshinta da sauri tai ciki tana kokarin kakaro numfashi. Da kyar ta samu numfashinta ya daidaita kafin ta saki wani irin kuka, tace " ni ina nan hankalina ya kasa kwanciya saboda kai amma kai kana gun matarka kuna soyayya? Yaya ya kakeso inyi da rayuwata?" Wajen karfe shabiyu na dare taji ta kasa bacci wani irin ciwo cikinta yake mata, dakyar ta iya daukan waya ta kira Little. Little ta dauka da sauri tace " Feenah tun dazu nake nemanki, yau bazan dawo gida ba ina hostel, gobe 7 zamuyi text ga malamin ba shida sauki." Da kyar Nafi ta iya cewa "to" Ta yarda wayar tanaji Little na kiranta sai dai azaba ta hanata dauka. Little da sauri ta kashe ta kira Yaya, wanda shikuma alokacin suna kwance da Anisa ya samu dakyar ya lalabata tai bacci wai ita adole sai sun gwada ko ya warke, da kyar ya samu ya shawo kanta ta hakura. Yanajin ringing din wayarsa ya zare jikinsa daga nata yai falo, ya daga cikin mamakin ganin number Little. Cikin rud'ewa Little tace " Yaya inaji Nafi bata da lafiya dama tun jiya na kula ba tacin abinci sai ruwan zafi to yanzu kuma ta kirani naji muryarta ba dadi." STORY CONTINUES BELOW Cikin rud'ewa yace " kedin kina ina?" Tace " makaranta." Tsaki yaja sannan yai waje da sauri ya manta ko kaya bai canza ba, yana zuwa ya bud'e kofar yajita kuwa a bude da alama ta barma Little kofar ne inta dawo. Da sauri ya shiga ciki ya bude kofar d'akin. A durkushe ya ganta a kasa tana murkusus, da sauri ya karasa gunta a kid'eme ya d'agota cikin tsananin firgice. Nafi kam azaba kawai takeji, hannunsa ta rike kam tace " yaya cikina." Kara rud'ewa yai yace " Nafisa? Me yasamu cikin? Bakici abici bane?" Kasa bashi amsa tai a rude ya dawo falonsu ya hada mata tea mai kauri ya dawo gunta ya kwanto ta jikinsa ya fara bata, sha kawai takeyi dan bazata iyamai musu ba, haka yai ta bata har ta shanye sannan ya d'auketa ya maida ita kan gado ya kwantar tare da ja mata bargo. Kanta ya shiga shafawa a hankali bacci ya dauketa. Ido ya kura mata cikin wani yanayi na dana sani da yakeyi, idanunsa ne suka kada sukai jaa a hankali yace " Am sry Nafisa, it's all my fault." Ganin kamar baccin ya fara nisa yasa ya mike a hankali zai tafi, hannunsa ta riko, wanda hakan yasa ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Nafi ta bud'e ido a hankali tace " Yaya ina rokon Allah ya kawomin cuta a kullum indai har hakan ne kadai zaisa inganka a kusa........." Saurin matsowa yai gunta yasa hannunsa ya toshe mata bakinta yace " Nafisa me kike fada haka? " Lumshe ido tai ta bud'e sannan ta zare hannunsa daga bakinta tace " in har hakane zai sa inganka zan iya horar da kaina da abinda yafi yunwa ma." Kallan mamaki ya mata yace " Kada ki kuskura ki sake dan kuwa bazan yafe ma kaina ba inhar wani abun ya sameki." Kallansa tai tare da daura kanta kanta kan cinyarsa a hankali tace " Yaya ban iya san abu ba, in har nai nisa asan abu jinake bazan iya rayuwa ba tare da abun nan ba, tunda nake a rayuwata ban taba san abu ba kamar kai, juyamin bayan dakai jinake kamar duk duniyar ta juyamin baya, sam..........." Matsowa yai da kansa batai auni ba taji bakinsa cikin nata,lalai sunyi missing din juna, jiyai sam ya kasa tsaida hankalinsa nan kowa ya shiga nunama dan uwansa tsantsar rashin junansu da sukai......... Sai bayan komai ya kammala sannan bacci mai nauyin gaske yai gaba da ita bayan sunyi wanka, kura mata ido yai yanaji a ransa shifa yafi santa akan yanda takeji akansa, shikadai yasan ya zuciyarsa takeji inya ganta. Ya dade a gunta sai wajen karfe 3 sannan ya fito daga d'akin yai bangarensa. ************* A kwance ya tada Anisa da alama ma ko farkawa batai ba kallanta yai yanajin tsantsar tsanar mahaifinta na kara ratsashi. Falo ya fito ya kwanta yadanyi bacci kadan kafin asuba. Nafi kam tunda ta tashi taji ciwon cikin ya tafi sai wani tsantsar farin ciki da takeyi, idanunta a rufe ta fara shashafa gado dan jin masoyinta, jin ba alamunsa yasa ta farko baki ta turo ganin ba ya nan, a ranta tace "mayb masallaci yaje." Sallah tai sannan tadan kishingida, wani bacci ne ya kara gaba da ita. ********** Asim yaje shiga office yaji wasu mutane daga gefensa suna magana. "kai amma na tausayama Zakari, yanzu duk girman company din nan nasa haka zai saidashi da arha?" D'ayan yace "nikaina tausayinsa nakeji, to ya zaiyi duk kadarar tasa ta karye." Matsawa kusa dasu Asim yai yace " wani Zakarin?" Wanda ya fara magana yace " Yallabai Zakari dai mai company din sabulai da mayuka na jiki, lotion da sabulu." Asim yace " garin yaya?" Mutumin yace " wlh karayar arziki ce ta sameshi komai nashi ya kare sai company din gashi dansa ba lafiya." Asim cikin zakuwa yace " kuma nawa zai saida?" Mutumin ya danyi shiru kafin yace " million 190 dai naji ana cewa, shiyasa kowa yake tausaya mai ganin guri ne babba mai kyau ga kayan aiki da komai a kalla gun nan yakai million 250 amma mutumin nan ya karyar da shi." Asim yai shiru kafin daga bisani ya shiga office dinsa, shiru yai yana tunani kafin yace " in nasai company din nan lalai ba karamar garabasa zan samu ba, yanda zan nunama Abba nima na fara abin kaina ba wai dashi na dogara ba." Ya danyi murmushin mugunta yace " gaba ko Ashraf ya kwace company dinsa nidai inada makafa" wayarsa ya zaro ya duba account dinsa, million 30 ne a ciki kansa ya dafa cikin takaici yace ina zan samu kudi bayan ko rabi bandashi?" Sauri yai ya kira Anisa yace " kanwata wannan takardun haryanzu sunanan a inda suke?" Ta mike tare da dubawa tace " eh." Ajiyar zuciya yai yace " guda nawa ne ma?" Ta fito dasu tace " da alama ma ya kara wasu a gun da guda biyar ne yanzu kuwa sunkai 8." Yace " ganinan zanzo yanzu in amsa." Tace " amma yaya....." Yace " karki damu bazai gane ba, inma ya gane sai musan karyar da zamuyi ko kuma yau da yamma kiyi kuka ki kirashi kice barayi sun shigo." Tace "to." Can kuma yace " a'a ba haka ba yau da daddare zansa a shigo gidan sai ki bar kofar a bud'e muyi kamar yan fashi ne suka zo." Tace "yauwa hakan dai yafi." Shiru yai yana tunani dole duk da haka yana bukatar wasu kudin ya tabbata wannan bazai isheshi ba, fitowa yai ya samu Secretary dinsa yace " yana bukatar account book na Company din nan." Nan yai waje dan amsowa, Asim yai murmushi yace " ko na dau kudin Company ba abinda Abba ya isa ya min." Nace hmmmm ********* Nafi kam sunyi waya da Ferry tace " Little ta kaimata kudin, harta je kasuwa ma ta siy musu." Nafi tace "to ina amarya?" Ferry tace " tana gun dangin mamanta taje sallama." Jin ance mamanta yasa jikin Nafi yai sanyi, haka dai sukai ta waya har suka gama, Nafi tana kashe wayar ta kwantar da kanta kan kujera tace " ko ina Ashraf na tasowa daga gun aiki ya wuce ban gareb Mumy, bai sameta a falo ba sai Afra ce tace mai tana d'aki tun jiya batajin dadi, nan ya wuce d'akin. A kwance take sai dai jin kwankwasawa yasa ta mike ta bud'e, Ashraf ya shigo tare da zama a kasa ya gaisheta, ta amsa a hankali sannan ya kalleta yace " Mumy tambaya nazo da ita." Gabanta ne ya fadi dan itakam tsoron tambayoyin Ashraf take, ya kalleta yace " gidajen Dady na waye?" Kallansa tai bakinta yadan motsa kadan tace " wasu nawa ne wasu kuma nashi ne." Kallanta ya sakeyi yace " asibitin Dady ya akai shima yaje hannunsa?" Gabanta ne ya fadi ta kallu Ashraf cikin dan rawar murya tace " Mahaifinka ne........" Katseta yai yace " sanda Abba yaki taimakama Dady har abin yazama ajalin Mahaifinki bakiji haushin Abba ba?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana, Murmushi yai sannan yace " Kince bakyasan kawu saki yai kika aureshi a dole saboda Dady meyasa kina aurensa kika hada zuri'a dashi bayan a fadarki ba sanshi kike ba ga haushin ya yi sanadin mijinki?"+ Idanunta ta runtse a hankali hawaye ya zubo mata, Ashraf ya mike tsaye yace " no matter what i can't understand u Mumy, ke kanwar Dady ce, sannan matar Abba ta da sannan matar Kawu ta yanzu, duk inda na duba kina tsakiya." Mikewa yai jiki a sanyaye yai waje har yaje fali ta fito da sauri tace "MUHAMMAD." Tsayawa yai jiki a sanyaye idanunsa sun rukid'e, tace " zo." A hankali ya koma d'akin ta zauna a bakin gadi shikuma ya zauna kusa da ita a kasa,Mumy tace " Ashraf duk na fahimceka sannan koma wanene dole ne indai yanada zarfafa tunani yai mamakin wad'an nan abubuwan." Ashraf cikin zafin rai yace " bayan mahaifinki ya rasu ba shine dalilinki na fara kula Kawu ba har ya jawo zargi tsakani........." Batasan sanda ta mareshi ba, bai dago ba sai dai yana ji dole ne ya fada mata abinda zai kona mata rai ko dan ta sanar dashi abinda ke b'oye. Mumy ta share kwallarta tace " Kana nufin da aure na nai tarayya da kanin mijina? Dan kawai in rama abinda yamin kome?" Ashraf a ransa yace " kiyi hakuri nima maganar ba har raina na fada ba." Jin yayi shiru tacigaba " Tunda nake ban taba shakkar wani abu ba kamar ka, gashi dai ni na haifeka amma ina tsoron halayenka na zuciya da fadar magana ta yadda kai ra'ayi, ko Mansir da nasan zai iyayin ko menene a rayuwarsa bana shakkarsa sai dai ina tsoron abinda zai maka." Kallanta Ashraf yai, tai murmushin takaici sannan tace " tabbas idan nace maka banji haushin Abbas ba alokacin nasan dole bazaka yarda ba ko ince ba ma mai yarda da ni." Tai ajiyar zuciya kafin ta cigaba " Bayan rasuwar mahaifina ga mahaifiyataba kwance yasa ya Hisham ya kirani cikin fishi yacemin Ruma haryanzu kina tunanin Abbas nasanki?duk abinda ya mana?" Kallansa nai cikin kunar abinda ya faru sannan nace " Yaya amma......." Ya Hisham ya katseni da cewa " Abbas dukiyarsa ce kawai ke rudarsa in bakiyi wasa ba nan gaba kadan kema zaki rasa matsayinki a gunsa." Kalamannan sun tsorata ni matuka wanda yasa na kalli Mansir wanda yake zaune a falon, Mansir yai ajiyar zuciya yace " ke kanwar Hisham ce ta jini dolene ki taimakeshi ya samu ya farfado dan kuwa makarantar da Abbas ya bashi ba abinda zata iya mai." STORY CONTINUES BELOW Na dau kudirin taimakama ya Hisham wanda hakan yasa nabarmai gidajen da Abbas ya dinga bani kadan kadan tun farko da ya sai karamin gida na haya dama ni yaba, tun daga nan yake bani kusan duk shekara. Bayan naba yaya ne nace zan dawo gida sakamakon hakurin da Abbas yai ta zuwa yana bawa yaya. A wannan lokacin shine Mansir ya daukoni dan Abbas baya kasar a lokacin. Ban taba tunanin Mansir ya shiryamin gadar zare ba ya kaini Tahir guest Palace da sunan dauko abu ashe yasa a dau hotonmu a ba Abbas. Ashraf ya kalleta yace " amma wa yasa?" Tace " Driver din Abbas yanda yasan in har Abbas ya gani dole yai zargina saboda yasan yaron bazai kai karya ba, sai dai abinda bai sani ba, Mansir da Ya Hisham sun riga sun siye zuciyar yaron." Tai dan hucci sannan ta cigaba " maganar gidaje kenan." Maganar asibiti kuma wannan tabbas nasan laifinane dan nina sanar ma yaya zan sa Abbas ya bashi asibitin sai dai a ranar da zan sanar da Abbas a ranar yai hatsarin mota, gashi a lokacin ya Hisham ya gama sanar da matarsa da wasu nashi na kusa akan an bashi asibiti, bayan rasuwar Abbas ne yaya ya samen yace ban kyautamai ba sai dana bari kowa ya sani ashe ni ko fadama Abbas banyi ba. Jiki na yai sanyi, shine mansir ya bamshawara akan tunda kai yaro ne sannan d'anane ba wani abun bane in na dauka na ba yayana. Sunje sunsa anyi rubutu irin na Abbas wanda ni kuma nai shaidar hakan. Kwallarta ta goge tace " Ashraf nasani nayi ba daidai ba sai dai ina tsoron abinda ya samu Abbana ya samu dan uwana, iyayenmu duk sun rasu shi kadai ya ragemub wanda nakeji bazan iya yarda abin duniya yasa in rasashi ba. Ashraf ya kalleta sannan yace " Mumy kina tunanin saboda kunyi amfani da dukiyar da take gado na nake fadar haka? Ko kadan dukiyar nan bata gabana dan wlh zan iya barinta in dauki matata in bar garin nan, sai dai abinda ke damuna ya zakuyi da zunubin da kuka daukarma kanku? In ni ina raye zan iya yafemuku Abba fa? Ya kuke tunanin Little da Habib zasuji in suka ji komai?" Idanu ta runtse tace " Nasani munyi ba daidai ba sai dai ba yanda zamuyi tunda abu ya riga ya faru." Ashraf yai shiru kawai yana kallanta, ta nisa sannan tace "maganar zuri'a kuma dana hada da mansir nasani shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa sai dai ya zanyi? Allah ya riga ya rubuta akwai 'ya'ya a tsakaninmu dashi." Mikewa Ashraf yai ya shafi kansa sannan yace " kujira hukuncin da Kuto zata muku dukanku, banaji zan iya yafe muku dan kun ci amanar Mahaifina sannan hukuncin da za'a muku shi kadai ne zai sa a kama kawu akan babban laifin daya aikata." Yana kainan yai waje. Sama ya kura ma ido zuciyarsa na tafasa lalai shikam ya gaji da jin abubuwa kala kala, sai dai yanzu komai ya ware mai kuma tabbas ne ya gurfanar da kawu gaban hukuma ko da kuwa komai nasa zai kare. ************ A ranar kuwa da daddare Asim ya turo 'yan fashi suka sashe takardun nan Ashraf kam ya nuna da gaske yaji ba dadi sai dai a ransa yana mamakin lalai Asim sam kansa baya ja, ace mutum duk yanda aka nemi ayi amfani dakai ba ka wani tunani sai ka bi? Anisa kam kuka tasa wai ita a dole tana tayashi bakin ciki, ya jawota jikinsa yace " karki damu Nisa sai dai please karki fadama kowa abinda ya faru banasan azo ana kace nace." Kai ta daga alamar to. ****** Asim yaje ya ga filaye manyan gaske sannan ga gonaki, nan ya ba wani dilallinaka sasu a kasuwa, bai wani tsula musu kudi dayawa ba wanda hakan yasa aka sai dasu cikin kankanin lokaci, ya amshi kudinsa Million 20 cif ya hada da nasa yaga million 50, takaici ya kamashi ganin ko rabi bai hada ba, gun Umma yaje ya mata bayani har ta gamsu itama ta dauko tata kadarar aka harhada aka saida, ansamu an hada 90 million, nan fa ya shiga neman yanda zaiyi ya samu ragowar gashi yaje yaga Company din ya birgeshi sosai wanda ya kara rinjayarsa, sannan ance akwai mutane da sukeso dayawa, nan ya samu Zakari ya bashi 90m yace zai ciko nan da 2dyz. ************ Nafi kam tun daga ranar da Ashraf ya tafi ya barta washegari bayan sunyi waya da Ferry akan shagalin biki Ferry take tambayarsa Ashraf, Nafi tai ajiyar zuciya tace " Ferry sam yanzu ya canzamin, jinake zuciyata kamar zata fashe." Ferry tai tsaki tace " wato nema kike ki koma Nafi ko?" Cikin mamaki tace " bangane ba." Ferry ta kara ja mata tsaki tace " kin manta yanzu Feenah kike ba Nafi ba? In ya canza miki kema ki canza masa an fada miki kowani namijine yake so yaga an like masa?" Nafi tace "Ferry bazaki gane bane yaya na cikin......" Ferry tace " ni kin bani kunya ma wlh shiyasa yake miki abinda yaga dama tunda kin gama nunamau shine rayuwarki gaba d'aya." Nan ferry tasata a gaba da fada. Tundaga wannan rana Nafi bata kara bari sun hadu da Ashraf ba, sai dai tana ganinsa a b'oye ganib hankalinsa kamar a kwance yake yasa itama ta kara kwantae da nata. ********** Yau Ashraf na zaune a office Salin ya kirashi ya sanar dashi tabbas Auwal Max an ganshi yanzu ma suna tare da wanda yasa ya nemoshi suna hanyar zuwa kano tare. Dadi sosai ya kama Ashraf ya kira dan sandan nan abokinsa yace " ka nemomin Dan siyasan nan dana ce maka?" Yace " haryanzu dai ranka ya dade ba labari." Ashraf yai ajiyar zuciya. Nan sukai sallama, Ashraf ya kalli Dan Litti dake tsaye yace " ana azahar kazo mu tafi." Yace " ok sir, amma maganar Asim." Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ya d'ebi kudin company din?" Dan litti yace " inaji dan d'azu Zakari ya kira yace yakaimai cikon kud'in." Ashraf ya hada hannayensa yace " good, kace ya bashi takardun company din ya kuma yi signing." Dan litti cikin mamaki yace " amma in akai haka ba a bashi company din ba?" Ashraf yai murmushi yace " ai dama so nake ya zama nashi." Dan litti yamai kallan mamaki sannan yace " ko da yake Ina ni ina sanin abinda Kake tunani?" Dariya sukama juna kafin Dan Litti ya fita. Nace Hmmm Ana azahar Dan Litti yazo suka fita shida Ashraf, gidan Salim suka wuce. Falo suka nufa inda Salim yace musu Auwal max na ciki, Ashraf ya kalli Dan Litti yace " dole ne ka hade rai ka maida abu serious." Dan litti ya jinjina kai sannan suka shiga. Ashraf da sauri ya isa gun Auwal ya kama hannunsa cikin nuna tsananin kulawa yace " Uncle kana lafiya? Badai abinda ya sameka ko?"+ Auwal cikin tsananin mamaki ya ke kallan Ashraf. Ashraf yace " ko ba Auwal bane?" Yace " nine Auwal Max" Ashraf ya zaunar dashi sannan ya zauna a gefensa ya kama hannunsa yace " nine Asim, babban d'an gidan Mansir." Sai a lokacin Auwal ya saki fuska, Ashraf ya kara rike hannun sa Yace " Abba ne yace in tabbata na samoka kafin Ashraf ya fara samunka." Auwal yace "Ashraf D'an....?" Ashraf ya karasamai " dan Abbas marigayi." Idanu Auwal ya zaro cikin tsananin tsoro yace " ya akai ya sanni?" Ashraf ya dan saki fuska cikin yanayin damuwa, Dan litti yace " bincike yake akan abinda ya faru a baya." Auwal cikin tsananin rud'ewa yace " inalilahi ya zanyi? Nikam na shiga uku, banda masifun da suke afkuwa akaina yanzu kuma wannan?" Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Abba yace inkula dakai sannan yace in tambayeka ranar meya faru? Har dakai akai hatsarin ko yaya?" Auwal ya kalli Ashraf yace " mantawa yai? Ai na sanar dashi komai." Shiru Ashraf yai yana tunani, sai jin Auwal yai yace " bayan mun shiga mota ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, aikuwa tana kira yace inje shi bari yaja motar, da alama dai Mansir ya manta da hakan." Ashraf yai dariya yace " da alama kasan yanzu abubuwa sunmai yawa dole ne mantuwa ta dinga shiga." Auwal ya jinjina kai, Ashraf yace " amma ai ba wata hanya da Ashraf zai gane kaine ka lalata birkin ko?" Auwal yai shiru yana tunani kafin daga bisani yace " kai, babu sai dai in mahaifiyarka." Cikin mamaki Ashrad yace " Umma?" Auwal ya jinjina kai yace " ita kadai ce ta ganni lokacin da nake aikin, bayan ita gaskiya ba kowa." Ashraf yai murmushi yace " ai bakomai indai Umma ce, amma Dady fa?" Auwal yace "Dady?" "Hisham nake nufi." Auwal yai dariya yace " shi ai bashi ya sani ba shine dai ya bani kudin aikina." Ashraf yace " nasan wannan wai nufina baku kara haduwa ba?" Auwal yace " ina zanganshi nida na koma garinmu?" Ashraf ya kara rike hannunsa yace "karka damu Abba yace inkula dakai ba abinda zai faru." Auwal yai ajiyar zuciya sannan yace "tunda na taho gabana ke faduwa sai yanzu hankalina ya kwanta." Ashraf yamai murmushi. Auwal ya kalli Ashraf yace " Amma kafi kama da Abbas, sam baka kama da mansir." STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya shafi fuskarsa yace " duk ba jini d'aya bane su? Kowa haka yake cemin wai nafi kama da Marigayi, shikuma Ashraf din inka ganshi abin mamaki kamarsu d'aya da Abbana." Auwal yace " ikon Allah, ai nikam bazan taba mantawa da Abbas ba, naci amanarsa na yaudaresa shiyasa nake ganin ishara kala kala." Ashraf yace " karka damu ka kwantar da hankalinka." Auwal ya daga kai. Ashraf ya kalli Dan litti yace " ka maidashi gidana na Darmanawa." Dan litti ya amsa da to, sannan ya kalli Auwal yace muje ko? Ashraf ya mikamai kudi yace kasai mai abinda zai bukata na nan da sati d'aya. Kallansa Auwal yai yace "har sati zanyi anan?" Ashraf yace " tsoro nake kar mu maidaka Ashraf ya sa a kamaka." Jin zancen kamawa yasa yace "to ai ba laifi satin ma." Nan sukai waje Ashraf ya bishi da wani kallo na takaici, sannan ya zaro wayarsa dayai recording ya sa a computer ya yanke maganar daga inda yace " _Nine Auwal Max_" Ya tura ma Kawu da d'aya wayarsa. Kawu wanda ya fito daga meeting kenan ya ga anturo mai email yana bud'ewa yaji muryar Auwal da abinda yace. Mamaki ya kamashi, meye hakan kuma???? Bai kawo komai ba yai gaba. Salim ya kalli Ashraf yace " amma kana tunanin zaiji wani abu dan yaji suna kawai?" Ashraf yai wani murmushi yace " it won't be fun in na turamai komai a lokaci d'aya, so nake naga yanda hankalinsa zai fita daga jikinsa a kowace rana, yana wannan case din ga kuma na d'ansa." Salim ya dafa Ashraf yace " U are very smart Ashraf sai dai please kayi a hankali dan ina tsoron wannan kawun naka." Ashraf yace " karka damu Uncle, sannan ina tunanin Mumy ne, in barta anan ko inkaita wata kasar, kar ya hanani komai saboda ita." Salim yai shiru sannan yace " tabbas kayi tunani dan kuwa zai iya cewa zai mata illa inkaki bin umarninsa." Ashraf yace " shi nake tsoro." Uncle yace " ka sata kawai ta tafi umara, taje ma ta nemi yafiya tai ibada ko ta samu rangwame." Ashraf yace " nagode Uncle." Nan ya fito. ********** Su Asim an mallaki company murna a wannan rana ba'a magana, dashi da Anisa da Umma da sauran kannansa sunje sunga guri kowa ya yaba sannan ya kira mahaifinsa ya sanar dashi. Mamaki ya kama Kawu a ina Asim ya samu kudin siyan Company? Sai dai haka ya karasa company din dan tabbatarma idanunsa. Mamaki sosai yakeyi ganin wannan katon guri wai mallakin d'ansa ne, ya kalli Asim cikin zargi yace " ina ka samu kud'i?" Asim yai shiru yana tunanin karyar da zaiyi, sai dai kafin ya furta komai sai ga wasu mutane ne nan su hud'u sanye da kayan 'yan sanda sunzo kusa da Asim. Nan fa kowa ya matso ana san ganin menene. Na gabansu ya zaro id card dinsa yace " I am Sergeant Kabir." Asim ya mai kallan banza yace " me ya damen da sunan ka?" Ankwa ya ciro yace " u are under arrest." Asim ya kalli Kawu sannan ya kallesu yace " ban gane ba, me nai?" Kabir ya cafki hannunsa ya fara kokarin sa mai ankwa Asim na turgewa. Kawu ya rike hannun Kabir yace " me yai?" Kabir yace " an kai kararsa akan d'eban kudin company dayai " Kallan mamaki Kawu yama Asim yace " me kenan?" Asim ya shiga jijiga kai yana cewa " Abba ba Company dinmu bane, ai ba wani abun bane in na ranci kudi a ciki." Hankalin kawu ya tashi yace " ku tsaya ayi magana." Kabir yace " i am sry sir, bayan wannan yana dauke da laifin satar kayan da ba nashi ba." . Asim cikin rud'ewa yace " mena sata kuma?" Kabir yace " filayen daka saida takardun ba na gaskiya bane bayan kuma ka riga ka amshi kudin mutane." Asim ya rikice ya kalli Kawu yace " Abba." Kawu wanda gaba d'aya yama rasa abinyi yace " yanzu me kuke bukata?" Kabir ya karasa datsamai ankwa yace " am sry sir dole ne ya biyomu." Yana kai nan yaja hannun Asim. Umma wacce ta saki wani ihu tare da bin bayansu tana kira sai dai ina.....Sunyi gaba, Anisa ma kuka take sosai, Umma ta matso gun Kawu ta rikemai kwallar riga tace " malam ka wuce ka amsomin d'ana." Kawu ga runtse ido cikin takaici, Umma ta kara rikicewa tana masifa. Kawu ya fizge jikinsa yace " me yasa kwatakwata kwakwalwar yaron nan kamar ta kifi take? Bashida hankali ne ko me? Ke ma kina ina da kika kasa bashi shawara,?in har bazaki iya dashi ba ai sai ki sanar min, yanzu wani irin abune wannan?" Ya fada cikin tsananin takaici. Nikam nace 🤷🏻‍♀ ko a jikina. Lol masoyan Asim amin afuwa, duk da banaji yanada masoya.....Lol Asim kam duk ya gama rikicewa sai rokon Kawu yakeyi, Umma kam kuka kawai takeyi tana itadai a anso mata d'anta. Sun isa police station akasa Asim a wani dan karamin d'aki dan yin bincike kafin a rufeshi. Kawu ya karaso a tasa motar ya umarci a barshi ya fara magana da Asim, ba musu kuwa suka barshi. D'akin ya shiga ya kalli Asim yace " ina kasamo filayen gidaje da gonaki haka?" Gabansa ne ya fadi, ta ina zai iya cewa satarsu yai? Cikin rawar murya yace " siya nai." Kawu ya bugamai wani kallo yace " Asim kana wasa dani, wlh akan kai kadai bazan yi asarar abinda na tara da kyar ba, zan iya yanke tsakanina dakai in har naga kana neman zubarmin da kemata." + Asim ya kara rikicewa yana rokon Kawu akan yai hakuri, kawu yace " kasan nawa kaci kudin company kuwa? Banda zubarmin da mutunci dakai, dole haka nan nizan yi kashin wad'an nan kudin, kafi kowa sani dukiyar Abbas a karkashin Ashraf take ba ni ba ai." Asim ya sauka kasa ya rike kafafun Kawu yace " Abba dan Allah ka taimakeni, bazan iya zama a wannan gurin ba, kafi kowa sani kaf 'ya'yanka bamai maka biyaya dayin abinda kakeso farat d'aya kamar ni, saboda haka ko aure ban taba sha'awar yi ba karma matata tazo tanemi samin wani ra'ayi." Abba ya kwace kafarsa da karfi wanda hakan yasa Asim fad'uwa, yace " na rasa wace irin kwakwalwar tumakai gareka, mema ya kaika siyan wani company? Meka rasa na rayuwa?" Asim kuka kawai yake yana rokon kawu, kawu ya nunashi da yatsa yace " wannan damuwarka ce da alama zaka ziyarci prison." Yana fada yai gaba yakai wajen kofa Asim yace " wato ka gama shan mangwaro shine kakeneman yadda kwallan?" Kawu ya juyo ya kalleshi, Asim yace " me kake tunani Abba? Bansan komai game da kai ba? Nafa sani kaine ka sa aka lalata birkin Ashraf a sanda ya b'ata, ba kasheshi kaso kai........." Kawu ne ya matso cikin zafin nama ya toshemai baki tare da jinginashi da bango, yace " bakada hankali ne? Me kake fada haka?" Asim ya dan shiga kakari saboda yaji matsar, Kabir da yake zaune yana kallo da jinsu a d'akin da ake ganin komai through computer ya mike tare da kallan su ya kashe abin CCTV din da microphone din sannan ya kira Ashraf ya sanar dashi komai. Wani Murmushi Ashraf yai yace " karka damu ganinan ma shigowa gun." Suna gama wayar dama yana kokarin ajiye mota ne, nan ya fito hankalinsa a kwance yai ciki. Anisa ya gani a bakin kofar da Umma sun zauna a kasa kamar marayu, Anisa tana ganin Ashraf ta taho da gudu ta rungumeshi tana kuka, Ashraf yadan zare jikinsa tare da ce mata "Nisa a waje fa muke." Da kyar ta d'agashi sai dai haryanzu kuka take, Umma ta mike ta kama hannun Ashraf tace " Ashraf ka taimaka ka anso mana yaron can, da alama Mahaifinsa bashida niyar ansoshi." Ashraf ya kalleta cikin kulawa yace " karki damu Umma bari naje naji yanda ake ciki, amma ku me kuke anan?" Umma tace " banasan shiga ne, bansan da wani ido zan kalli Asim a cikib wannan gun ba." Ashraf yace " bari na shiga naji." Nan yai cikin station din. D'akin da suke ya kwankwasa, Kawu ya sake Asim sannan yace ya shigo. STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya shiga cikin nuna kulawa yace " Kawu meke faruwa?" Kawu ya kalli Ashraf sannan ya kalli Asim cikin takaici yace "ohon masa, nema yake kawai ya zubarmin da mutunci." Ashraf ya kallu Asim yace " Asim a ina ka samu takardun filayen? Wannan ita kadaice hanyar da zaisa a warware komai." Asim ya hadiye yawon wahala, ina zai iya furtawa da bakinsa yace shi ya turo 'yan fashi. Kawu takaici ya kamashi a zuciye yai waje. Asim ya matso kusa da Ashraf yace " Ashraf dan Allah ka taimakeni wlh bazan iya zama anan ba ko da na awannine ka taimaken dan Allah." Ashraf yace " karka damu zamusan yanda za'ai." Ya fito waje. Kawu ya gani yanawa Kabir magana, nan ya matsa gun, yanaji Kawu yace " kana nufin kudin Company din ma sai na biya double?" Kabir yace " sry sir amma haka ka'ida take, duk wanda yai embezzlement din kudin Company dolene ya biya double." Gumi ne ya karyoma Kawu, nan yai gaba ba tare da yace komai ba, aransa fadi yake lalai Asim bashida hankali, haka kawai baici ba baisha ba asashi biyan kudi har million 200 a yini d'aya? Ashraf ne ya d'au wayarsa dake aljihunsa ya turamai voice note din Auwal Max daya d'auka. Kawu yana ganin sako gabansa ya fadi, da sauri yai waje yanaji su Umma namai magana amma ko sauraransu baiyi ba yai waje, ya kunna sakon. _Ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, da alama dai Mansir ya manta da hakan._ 1 Gaban kawu ne yai mugun faduwa, cikin tsananin rikicewa ya shiga waiwaigawa, zuciyarsa ce tacemai Ashraf. Nan ya koma cikin station din da sauri, can yaga Ashraf zaune kusa da Kabir suna magana, matsawa yai gunsu jiyai Ashraf yace "Yanzu Officer ba yanda za'ayi?" Kabir yace" dolene sai ya biya kud'ad'an nan dan kuwa hakkin jama'a ne." Kawu yai ajiyar zuciya da alama dai ba Ashraf bane nan yai waje. Kabir ya kalli Ashraf ya sa dariya. Shima dariya Ashraf din yai yace " Kb ka tabbatar ka tsareshi dakyau." Kabir yace " karka damu mutumina." Ashraf yazo ya lallaba Umma da Anisa ya kaisu gida, yana fitowa zai shiga b'angaren Mumy ya hango Nafi daga nesa. Ta sha kwalliya sosai da sosai, ya shagala sosai wajen kallanta tana tafe tana lallatsa waya, gani yai kamar ta kara wani irin mugun kyau. Ya shagala sosai da kallanta yaji alamar sako a wayarsa. Nan ya duba, daga Nafi ne, _Yaya zanje gidansu Ferry._ D'agowa yai da sauri dan ya kara ganinta sai dai me? Wayam ya gani ba Nafi. Da sauri ya matso yana nemanta, sai dai bai ganta ba. Gun mai gadi ya nufa da sauri yace " Nafisa ta fita ne?" Mai gadin yace " eh yanzun nan." Ashraf ya leka waje da sauri, yana ganinta ta shiga motar Nabil, jiyai ransa ya sosu sai dai kafin ya karasa fitowa sunyi gaba. Motar yabi da kallo sannan ya juya jiki a sanyaye. B'angaren Mumy ya shiga, tana zaune a falo tana cin abincin rana. Fuska ya daure tamau sannan ya zauna suka gaisa. Ta amsa a hankali tace " kaje gun Asim ne?" Bai amsa tambayarta ba sai cewa yai, passport dinki nake so." Kallan mamaki tamai tace " me za'ai dashi?" Yace " umara zakije kida Nafisa." Tace " Umara?" Ya kalleta yace " garin nake so ki bari, saboda in na barki anan Kawu zai yi tunanin amfani dake wajen tsaidani daga kamashi, sai dai banaji akwai abinda zai tsaidani, shiyasa nakesan ki bar garin in na kamashi sai ku dawo." Kallan sa tai cikin wani yanayi, yace " karkiyi tunanin yafe maki laifinki nai, in kika dawo kema zaki je kuto a miki naki hukuncin." Hawayenta ta maida sannan ta d'aga kai tace " ni naji nawa dalilin amma nafisa fa?" Yace " Tsoro nake kar wani abu ya sameta, duk da na juya mata baya saboda banasan mutanen gidan su damu da ita, amma a zuciyata kullum da ita nake kwana nake tashi, ku tafi tare ko Allah zaisa ma taga mahaifiyarta." Mumy ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " Ya Hisham fa?" Yace " Duk wanda yai laifi dole ne ya karbi hukuncin shi a duniya, shine kadai gatan da zan iya muku." Yana kaiwa nan yai waje. B'angarensu Little ya nufa, dan yanasan ganinta. Daga lungun kofar ya ganta tsaye itada Habib, kasa karasawa yai yatsaya kawai jikinsa duk yai sanyi, ya zasuji in komai ya fito? Ya sani Habib ba wai san Little yake ba amma ita fa? Gata yarinya ya zatai??? ************* Nafi kam Nabil na jan mota yace mata " mutuminki fa ya fito, ina kallansa ta madubi." Murmushi tai tace " share kawai Ya Nabil, shima hidimar gabansa ta mai yawa." Nabil yai dariya yace " ko dai fadan masoya kuke?" Tai dariya tace " ba wani fada, ko dan kaga nace inzaka wuce kazo mu tafi? Wannan ma ai dan naji kana anguwarmu ne." Nabil yai murmushi yace " Feenah Allah nikam Ashraf ya gama kwafsamin, da ya kwaceki." Harararsa tai tace " Ya Nabil ba nace ka daina min wannan zancen ba? Nifa kanwarka ce." Yai ajiyar zuciya yace "ya zanyi tunda an maidani yayan karfi da yaji." Zatai magana taji sako ya shigo wayarta. Ashraf ne hakan yasa ta bud'e da sauri _Wajen karfe 4 za'azo a d'aukeki akwai inda za'akaiki._ Ta dan turo baki tace " ina za'a kaini??? Nabil ya kalleta yace " ya akai?" Tace "bakomai." Shikam Ashraf Dan Litti ya kira ya sanar dashi karfe 4 yaje ya d'auki Nafisa ya kaita inda akeyin passport akwai wani abokinsa daya kira yace suje 4 lokacin mutane duk sun ragu. Dan Litti yace "da alama yau zanga Nafinmu kenan." Nace lalai anfa dade ba'a gamu ba.....Lol😄 Da yamma kuwa Dan Litti ya nufi addreshin da Ashraf ya turomai na gidan su Ferry. Nan ya kira Ashraf ya sanar dash ya isa shikuma ya ma Nafi sako akan ta fita wanda zai kaita ya iso. Sunyi sallama dasu Umma sannan ta fito itada Ferry, ganin motar Ashraf yasa ta nufi motar.+ Dan Litti yana ganinsun iso ya fito sanye da sunglasses, zaresu yai ya kallesu, Nafi kallansa take cikin mamaki shima kallanta yake. Fuska ya hade tamau yace "malama lafiya?" Nafi tace " bangane ba?" Dan litti ya maida glass dinsa ya kalleta yace " Na fada miki bai kamata ki dinga bin mijin dake da aure ba, a kalla dai mutum ya dinga sanin darajarsa." Nafi ta hade rai itama tace " kai kuma a wani matsayin kenan kake sanar dani haka?" Mota ya bud'e yace " malama dan Allah kiyi gaba akwai wacce nake jira ne, tunda kinga ba mai motar bane ai sai ki kara mai." Nafi da Ferry suka kallu juna, ferry tace " ruwa zata kara ba mai ba, sannan kai wanene ma?" Ya kalli Ferry cikin isa yace " The Hand Right of Ashaf." Dariyarsu suka guntse Ferry ta kalli Nafi tace " ke kuma fa?" Nafi ta kalli Dan Litti tace " As his wife." Duk da kalmar taba Ferry mamaki sai dai ta dauka ko dan ta kular da Dan Litti ne yasa ta fadan haka. Idanu Dan Litti ya zaro yace " matarsa? Amma matan Ashraf ai na sansu." Kai ta juya, da sauri ya kira wayar Ashraf yasa a hands free. Ashraf ya daga yace " mutumin ya akai?" Dan Litti ya kalli Nafi yace " wata ce take tutiya wai matarka ce." Yace " wata kamar ya?" Ferry ta fizge wayar ta mikama Nafi. Nafi tace " Hello." Ashraf yace " Nafisa? Ya akai? Kinga Dan Littin?" Kallan juna sukai daga ita har Dan littin. Cikin mamaki tace " Dan Litti?" Shima yace " Nafisa?" Ashraf yai murmushi yace " Da alama baku hadu ba sai yau." ya kashe wayar. Dan Litti tsananin mamaki ya kamashi, kallan Nafi ya shiga yi. Nafi cikin mamaki tace " Dan Littin gayu? Kaine?" Kansa ya sosa yai kasa da kai yace " Hajiya Nafi wannan ko a mafarki naganki akacemin kece ai bazan yarda ba." Dariya tai, Ferry tace " au dama kunsan juna?" Nafi tace " Kauyenmu d'aya." Ferry tai dariya tace " lalai yau akwai hirar gida kenan, ni nayi ciki." Nan ta musu sallama tai gaba. Ashraf ya bud'ema Nafi gidan baya ta shiga. Mamaki har yanzu bai barsu ba. Ya ja mota yana tambayarta ya akai bai taba ganinta ba? STORY CONTINUES BELOW Tace " wai da gaske a nan gida kake? Nima ban taba haduwa dakai ba a gidan mayb shiyasa bamu fahimci juna ba." Hira suke sosai har suka isa inda zasu, waya ya kira akace su shiga. Nan suka shiga ciki aka mata hoto sannan aka basu form da sauran abubuwa. Ba musu take yin komai, sai dai tana bukatar amsar tambayoyinta daga bakin Ashraf. Sun dade sosai sai bayan magrib suka fito, akan sai zuwa gobe azo a amsa. Gida suka wuce, ta kalleshi tace " kana zuwa gida kuwa?" Yace " nadaije kwanakin can da dadewa." Tai shiru kafin tace " Baffa fa?" Shiri yai shima kafin ya daure yace " yayi aure sannan ya bata labarin zuwansu da kamashi da akai." Tayi dariya sosai jin turancinsa abinda ya ja mai. Suna isa gida sukai sallama sannan tai bangarensu, duk da tana san magana da Ashraf sai dai tana tsoron zuwa bangaren tagansu da Anisa. ********** Washe gari da safe, Ashraf yai wanka ya fito, bangaren Umma ya fara zuwa, tana kwance ba lafiya dan hawan jininta ya tashi, Anisa na zaune kusa da ita. Ya gaishesu sannan yace zaije station yaji ya ake ciki, Umma tamai godiya tare da rokon ya taimaka ma Asim. Ashraf yana fitowa ya kira Habib yace " mutumin kana ina?" Yace " ina gida." Yace " Dady fa?" Yace " wlh dazun nan ya fita wai banki zaije, nace zan rakashi ma yaki." Ashraf yai murmushi dan dama jikinshi ya bashi za'ai haka. Mota ya fada Dan Litti yace mu tafi? Ashraf ya girgiza kai yace " yanzu kawu zai fito so nake kabi bayansa ka sanar dani inda zaije." Dan litti ya amsa da to, sannan yai waje shikuma Ashraf ya ja motar yai gaba. Wayarsa ta jaka ya dauka ya kara turama Kawu sakob Auwal. Kawu wanda ke ta zirga zirga a falon, hankalinsa duk ya gama dugunzuma bacci ma kasa samu yai jiya, yanajin sakon Auwal hankalinsa ya kara tashi ainun, da sauri ya kira number Dady. Dadu ya dauka yace " Ya akai Mansir?" Kawu yace " ya ya? Ka ciro kudin?" Dady yace " ganinan na fito daga bankin yanzu sai dai ina za'a kawoma kudin? Sannan kana tunanin inkaba Auwal zai kyalemu kaga wlh duk na tattare kudina na sa a jakar nan." Kawu yace " ni zansan yanda za'ai, sannan karka damu nace zan san yanda za'ai wasu kudin su shigo." Dady yai ajiyar zuciya sannan ya kashe. Kawu ya runtse ido yace " yanzu na samu kudin da zan taimaki Asim, in na gama dashi sai in dawo kan Auwal." (Azahiri gaskiya Ashraf dama ya sani sarai, yasab duk yanda kawu yaso ga san Dansa bazai tava yadda ya tattare arzikin daya tara dakyar ba ya taimaki Asim ba, ya kuma san kawu zaiyi amfani da sakon magana na Auwal dayake turamai yai blackmailing din dady akan Auwal ne yake bukatar wannan uban kudi ko kuwa ya toba musu asiri.) _Wannan kenan_ Kawu ya fito da sauri ya fada mota sannan ya turama Dady sako akan inda yake so su hadu. Dan litti kam yana biye dasu har suka isa Mariri gun da gidaje ma kwayanune a gun. Nan ya kira Ashraf wanda ke zaune a office hankalinsa a kwance yanashan tea, jin inda kawu yai yasa ya kira Kabir ya sanar dashi inda suke tare da cewa " ku tabbatar kun kwace." Kb yace " karka damu abokina yaran danasa bazasu baka kunya ba." Nan ya kashe wayar ya cigaba da shan shayinsa cikin annashuwa. Kawu kam ya isa wani kango ya kira Dady yace " ya ya? Ka taho?" Yace " ganinan na gangaro." Daf da gun kadan Dady na tuka mota ga gun hanyar duk batada kyau wasu mutane ya gani a gabansa sanyi da kyalle baki sun rufe daga hancinsu, tsoro yasa ya taka burki tare da kallansu. Nan suka zo suka bud'e motar d'aya yasamai bindiga d'ayan kuna ya d'auke jakar kudin, suka hau mashin sukai gaba. Dady kam hannu kawai ya dora akai sam ya kasa komai. Wayarsa ce tai kara ya duba ganin kawu ne yasa ya daga cikin tsananin tashin hankali yace " Mansir na mutu, na shiga uku, million 80 din dana dauko an kwacesu." Yana kainan ya kasa magana. Kawu ya fito a rikice, nan ya hangoshi ya isa inda yake cikin tsananin tashin hankali. Ashraf ya gama shan shayinsa ya kwantar da kansa kan kujera tare da lumshe ido yace " Dady taya zaka bari Kawu ya dinga juya ka? Da na dauka kai ne mai wayau akansa sai dai yanzu na gane kai din a ido ne kake da cikar zati amma kawu ya fika nesa ba kusa ba." Kawu cikin kunci da bakinciki ya isa station shikam Dady dakyar ya karasa gida idanunsa da jikinsa duk sun nuna alamar damuwa Da karayar zuci. Kawu yana shiga station din wani tunani ya fado mai, ya akai aka kwace kudin da su biyu suka san da shi? Da sauri ya kira Secretary dinsa yace " dubamin ka gani Ashraf yazo?" Nan yaje ya dubomai aka sanar dashi ai tun safe daya shiga office ma bai fito ba. Hannunsa ya dunkule ya naushi bango wanda wani radadi da zugi suka ziyarceshi, yace cikin takaici "To waye? In har ba Ashraf bane wanene wannan da yake neman dimautani?yake neman ganin karshena?" Zufa ce ta karyomai ya karasa cikin station din ya samu kabir yace ya ake ciki? Kabir yace " yaki fadar inda ya samu wannan filayen, sannan wadanda suka bashi kudi sunce tabbas suna bukatar kudinsu yau zuwa gobe." Kawu yace "in aka ki fa?" Kb yai dariya yace " ai dole ne ma abiya dan kuwa kuto za'a shiga dashi wani satin dokene yabiya kudi sannan asan kuma hukuncin da za'amai " Kawu yace " hukunci?" Kb yace " kwarai dan in har satarsu yai to fa lalai sai ya ziyarci prison." Hankalin Kawu ya kara tashi, jiki a sanyaye ya fito ko Asim bai gani ba. Da yamma Dan Litti ya amso passport din Nafi nan Ashraf ya sa aka musu visa na umara wanda zasu tashi jibi nan, dan dama yafisan su tafi da wuri to sai yai sa'a ya samu International saboda ya tabbata daga Asim ya sanar da kawu a inda ya dauko takardun nan to fa babu makawa yasan shikenan Kawu zai san shine ya shirya komai... Hmmmmmm😷

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER 23"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...