Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA CHAPTER 22

ZUCIYA CHAPTER 22

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 22
Bayan sun zauna Malam ya kalli Ashraf wanda ya nutsu yana kallansa.+ Ashraf ganin Malam na kallansa baice komai ba yace " Malam ya akai?" Malam yai murmushi yace " tunowa nai lokacin da mukai wannan tafiyae bakafi dan haka ba " ya fada yana gwada tsayin Ashraf a lokacin. Ashraf yai kasa dakai yana murmushi. Malam yace " A wannan rana munje kauyuka da dama na kusa da na nesa, a karshe muka isa wani gungurmin kauye, wanda 'yan garin kana ganinsu kasan suna cikin tsananin wuya da talauci, nan muka isa gun mai garin aka tara 'yan garin aka fara basu sadaka, kaima kana mikawa. Gun yayi cunkoso wanda ya janyo turereniya agun, wasu suka dinga faduwa saboda karfin da kowa yake gwadawa. Ganinka mukai kabar gun rabon da dan gudunka. Nan Abbas ya leka ya ganka gaban wani bawan Allah, tsoho ne tukuf gaba d'aya gashin kansa fari ne ya tsufa sosai, wanda aka tureshi garin rigima ya fadi kasa. Da saurinka ka karasa kana neman d'aga mutumin, tsohon wanda kowa yake kyararsa sai cimai mutunci akeyi. Nan Ashraf ya taimakamai ka maidashi gefe, wani mutum ne ya jawoka yace " kai yaro ka raba kanka da wannan tsohon maye ne." Ashraf ya kalleshi shikam yarinta baisan ma me ake nufi da maye ba ya koma gunsa tare da d'auko abin sadaka guda biyu ya kaimai. Duk inda Ashraf yai sai mutumin nan ya bishi da kallo wanda hakan yasa muma jikinmu yai sanyi. Bayan kowa ya watse mutumin nan na nan a zaune ya taso dakyar yazo gun mu. Abbas ya kalleshi yace "Baba lafiya?" Tsoho ya kalli Ashraf wanda ke gefe yana alwala ya kalli Abbas yace " kaine babansa ko?" Cikin mamaki Abbas yace " ya akai ka sani?" Tsoho yai danyi dariya sannan ya kara kallan Ashraf ya kuma kalli Abbas yace " kwanakinka basu da tsayi, ko ince kwanakin ka sunzo karshe." Malam cikin b'acin rai ya kalli tsoho yace " kai miye hakan? Ta yaya zakazo ka samu mutane ka dinga fadamusu zancen banza haka?" Tsohon ya girgiza kai sannan yace " ko d'aya ba kuma na fada bane dan ranka ya b'aci ba sai dai kanada makiya dayawa na jikinka kuma." Abbas ya kalleshi cikin shakkun kalamansa tabbas yasan yanada makiya amma bayasan aminta da maganan wannan tsohon da ya kai kusan shekara 100. Tsoho ya kalli Ashraf yana murmushi yace " kayi dacen d'a sai dai rayuwarsa zata zama a kewaye take da makiyansa." Abbas da Malam kawai kallan tsoho sukeyi, tsoho yacigaba " sai dai akwai farinciki a rayuwarsa in har ya rike matarsa ta farko, in kuwa ya rabu da ita banaji akwai wani farinciki da zai samu a rayuwarsa." Abbas ya mike cikin mamakin mutumi yace " malam wani irin zance kakeyi haka? Tayaya daga ganin yaro zaka fara cewa wai ba farinciki a rayuwarsa? Kasan me kake fada kuwa?" Tsoho yace " kamar yanda makiyanka na jini basa sanka kana tunanin zasuso d'anka?" Yana kainan ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yace " D'anka zai zama abin alfahari ga mutane, matar da zai aura ta farko itace zata zamar mai farincikinsa nan gaba." STORY CONTINUES BELOW Yana kainan yai gaba, Abbas ya bishi da kallo kafin cikin tsoro yabi bayan mutumin sai dai babu shi ba alamar sa. Mai gari dake zaune yanajin komai ya kalli Abbas yace " Mutumin nan da kake gani ba wanda ya sanshi, shekararsa kusan d'ari ba aure ba zuri'a ba komai, ba wanda yake kusantar ko da magana dashi ne, sannan abun tsoro ga mutumin in dai ya fadi abu to fa sai dai wani iko Allah, shiyasa muke tsoron harka dashi, wasu sunce maye ne, wasu sunce baiwa gareshi wasu sunce kambun baka wasu sunce aljani ne, a zahirin gaskiya kowa da abinda yake fada sai dai Allah ne kadai masani." Malam ya kalli Ashraf wanda gaba d'aya shi hankalinsa nakan Malam. Malam yai murmushi yace "munyi mamaki kwarai da abin al'ajabi na wannan tsohon sai dai abinda ya tsoratamu shine mun gama sadaka muna kokarin tahowa aka sanar da mai gari mutuwar wannnan tsoho." Idanu Ashraf ya zaro yace " muna garin ya rasu?" Malam yai ajiyar zuciya yace " ban taba ganin abin al'ajabi irin wannan ba." Ashraf yai shiru yana kallan malam. Malam yace " shiyasa dakazomin dazancen rabuwarka da matarka ta farko naki aminta saboda inaji a jikina itace farin cikinka, bawai dan na yarda da abinda wani bawa na Allah ya fada ba sai dai shi dan Adam Allah ne kadai yasan baiwar dayama kowa." Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " to inkuma da ace Anisa na fara aure fa?" Malam yai murmushi yace " shiyasa nacemaka baiwar dan Adam Allah ne kadai yasan yawanta, dama can Allah ya tsara ba ita zaka fara aura ba." Ashraf yai shiru, tunaninsa ya tsaya cak. Malam yace " muje inada gun zuwa." Ashraf ya fito jiki a sanyaye ya shiga motarsa, idanunsa ya lumshe a zuciyarsa yace " kaddarace ta kaini kauyen garinsu, shi dama d'an adam rayuwarsa a tsare take." Sako ne ya shigo wayarsa ya d'aga wayar ya karanta kamar haka " _yaya inasan zuwa gidansu Ferry in ka bani izini, sannan zan kai mata kudin anko_" Kallan sunan daya sa mata yai Baby Feenah, a hankali ya goge sunan ya maidashi Nafisa. Yana kallan sunan daya canza mata ya furta a fili, I Am sorry Nafisa sai dai wannan ce hanya kadai dazaisa inyi fooling din kowa, inhar na sanar dake plan dina ba zakiji pain ba akan abinda zanyi sai dai hakan zai sa a gane ba gaskiya bane. Yai ajiyar zuciya tare da cewa " I am sorry for using u." Mota ya tada sannan yai gaba. Gidansu Habib yai ya tsaya a wajen gidan ya kurama gate din gidan ido, bakincikinsa yanda yakesan Dady da Habib, yanda yakesan kannen Habib, ya kara kallan gidan yace " Dady kaci amanata." Ya dade kafin daga bisani yaja motarsa yai gaba. Gida ya wuce, direct bangaren Umma yai, Umma tanajin sallamarsa mamaki ya kamata cikin zumudi. Bayan ta bud'e ya shiga kamar yanda ya saba fuskarshi a daure. Zama yai sannan ya kalli Umma tare da gaisheta. Umma ta baje baki tace " Ashraf yau da kanka?" Kasa yai dakai yace " Umma hakkinane ai." Ta kara washe baki yace " Anisa fa?" Tace " tad'an fita dazu." Murmushi yai yace " ok ba damuwa bari na wuce." Tace " a'a ka zauna insa a kawoma abinci." Ba musu ya amince da hakan." Da sauri Umma ta fita kamar ya sani sai ta sanar da Mumy, yana zaune kuwa ya fara cin abinci kenan sai ga Afra. Ta gaisheshi sannan yaga ta juya, ya sani mumy ce ta turota akan ta tabbatar ko yana can d'in. Ashraf yai murmushi ya cigaba da cin abincinsa. Ya kusa gamawa sai ga Asim. Asim mamaki ya kamashi cikin tsananin mamaki ya karaso yace " Kai kuma me kakeyi anan?" Ashraf ya kalli Umma. Da sauri Umma tace " ni nace ya zauna yaji abinci." Asim ya mata kallan mamaki, kallansa tai tamai alama da yaje d'akinta. Nan yai gaba ta bishi a baya suka rufo kofa. Ashraf ya mike ya bi bayansu. Asim ne ya kalli Umma yace " Umma meye hakan?" Tai dariya tace " Asim bansan meyasa kanka baya ja ba yaron nan yanzu ya san matsayin Anisa a zuciyarsa baka tunanin lokacine daya kamata muyi amfani dashi dan jansa a jikinmu?" Cikin fada yace " mujashi a jikin mu kamar ya?" Tai dariya tace " yanda zai saki jiki damu har ku gama gano komau kafin musan abinyi akansa." Asim yai dan tsaki sannan yace " Ni Abba ne ke ban haushi sam yana nuna ni ba komai bane." Umma ta kalleshi tace " kamar ya?" Ya kara tsaki yace " share, amma Umma menene a cikin wannan akwatin na kasan d'akin Abba?" "Shiiiiiiii" tamai alama da hannu tace " bakada hankali ne? Sai an jika? Ni kaina saboda wannan akwatin yasa inaji baya barin matansa sudinga shiga mai d'aki, inaji akwai wani sirri babba a ciki." Ashraf ya kalli kofar kafin ya juya yai gaba, akwati??? Ya maimaita a ransa. B'angarensa ya nufa, a bakin kofa ya hango kamar Nafisa, hakan yasa ya had'e rai tamau. Ko kallanta baiyi ba ya bud'e kofa ya shiga. Nafi wanda ganin yanda ya shareta kamar shara yasa jikinta ya kara sanyi, yau tun safe ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin ko abinci. Ganin ya shiga yasa tabi bayansa, ta ajiye masa tiren abincin data kawo mai akan dinning sannan ta tsaya daga nesa tana kallansa. Gani tai ya d'auke kai daga kanta kamar baisan tana gun bama. Har ta bud'e baki zatai magana taga ya mikr ya shiga d'aki tare da rufo kofa. Hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta fito a hankali tai b'angarensu. A falo taga Little tana kallo, bata ce mata komai ba tai d'aki. Little ta taso ta shigo tace " Yaya yace kije sannan in zakiyi amfani da kudi ki daina tambayarsa." Nafita dago a hankali ta kallu Little. Little tace " wai fada kukai? Akan me zai turob text bayan kinada waya?" Mikewa Nafi tai ta shiga toilet. Tsugunnawa tai sai kuka. Kuka take sosai a cikin band'aki tana tuno irin soyayyar da Ashraf ya nuna mata a 'yan kwanakin nan, ko dai da gaske ne dan ya riga ya santa a mace shiyasa yake mata haka?+ Jin yanda wayarta taketa kara ga Little sai kiranta takeyi yasa ta daure ta share hawayenta ta fito. Wayar ta d'auka tace " Ferry ya akai?" Ferry cikin zumudi tace " albishrinki?" Nafi ta daure tace " goro." Ferry tace " 8 credit gareki including math and English." Wani sanyin dadi ne ya kamata tace " haba?dagaske?" Ferry tace " wlh goegraphy ne kawai kike da pass." Nafi tai hamdallah sannan tace " kefa?" Ferry tace " 7 credit nima da maths da English." Nafi ta kara hamdallah sukai sallama. Little ta fadawa nan little ta taso da sauri ta rungumeta tana tayata farinciki. Nafi kam murmushi kawai take yi aranta fadi take inama yaya na kusa da farincikin yafi min dadi. ********** A b'angaren Ashraf kuwa tun bayan fitar Nafi ya zauna shiru yana tunanin ta anya kuwa ya dace abinda yake aikata mata? To amma ya zaiyi? Yasan sarai zata iya taimakamai wajen plan dinsa sai dai yana ganin in har tasan ba gaske bane yana ganinta a kusa dashi bayaji zai iya jure wulakantata, yafisan tai fishi dashi har ya cimma burinsa sannan ya nemi yafiyarta ya kuma amshi punishment din da zata bash na using dinta dayai. Anisa ce ta shigo d'akun ba ko sallama ta zo ta zauna kusa dashi tana zubamai shagwaba wai tun safe bata ganshi ba sai yanzu. Daurewa yai yace " nima nayi missing dink ai sosai." Kwantowa tai kan jikinsa tace " Yaya kaje asibiti?" Cikin mamak ya kalleta yace " Asibiti kuma?" Kallansa tai cikin dan hade rai tace " ba kace bakada lafiya ba? Jiya da daddare." Tunowa yai ya dan mike da sauri yace " eh naje anma ban magani." Ta dan turo baki tace " ka warke?" Ya juyo tare da dafata yace " daga shan magani sai warkewa?" Ta zumburo baki tace " nifa....." Waskewa yai ya jawota jikinsa. Bayan sun kwanta tana jikinsa itakam tayi missing dinsa, Ashraf cikin dabara yace " nikam kina shiga d'akin Kawu?" Kallansa tad'anyi tace " ba sosai ba dai." Yadan yi shiru hakan yasa tace " menene? Wani abu kake so?" Kai ya girgiza alamar a'a yace " bashi kawai banasan kowa yaji ne." Mikewa tai ta zauna tace " me kakeso?" Yace " dama akwai akwatin Abba na a kasan gadansa ne to kuma naga kamar Kawu bayasan in dauka, kinga in yaji na dauka ba da saninsa ba zai iya jin haushi." Anisa cikin rashin damuwa tace " menene a ciki?" Yace " kayan Abba ne na da can, su kadai ne ba'a bada ba na rasa me yasa kwanan nan nake san ganin su." STORY CONTINUES BELOW Tausayinsa ne ya kamata tace " karka damu zan daukoma amma sai dai kana gama gani mu maida yanda bazai ma san ka dauka ba." Ashraf yai murmushin tausayi ya jawota jikinsa yace " Nisa nagode." Wani dadi ya kamata tace " yaya in akwai wani abu da kakeso ka sanar dani." Yace " abinda yasa ma ban fada miki da wuri ba banaso ne kowa ya sani, na kuma sanki komai sai kin fadama umma." Kai ta girgiza da sauri tace " wlh wannan bazan fada mata ba ko da kuwa kamani Kawu yai bazan taba fadan kaine kakesan gani ba." Cikin sanyin murya yace " Nagode Nisata." Nan sukai murmushi dukansu. ************ Washe gari kuwa kafin kawu ya fita gun aiki Anisa ta shiga d'akinsa, bayan sun gaisa ya kalleta cikin kulawa dan yanasan Anisa sosai yace " Anisa ta yau kuma ganina aka zo yi?" Kusa dashi ta zauna tace " Abba ba kai bane ka daina nemana?" Yai dariya yace " ina na isa in daina neman 'yata Anisa?" Itama dariya tai tace " Yaya na koma fa." Ya kalleta yace " Ummanki ta fadamin amma ni hankalina bai kwanta da Ashraf ba kina ganin fa abinda yamana akan yarinyar can." Dariya ta sakeyi tace " Abba kenan bakasan yanda Yaya ke kula dani ba yanzu komai nakeso shi yake min." Kawu ya kalleta yace " shiyasa ai banyarda dashi dinba." Anisa tadan tabe baki tace " Abba kenan." Kallan agogo yai yace " mu tafi ko?" Ta kwanta akan gadonsa tace " ni bacci ma zanyi anan." Cikin mamaki yace " anan din?" Kai ta daga tace " ina missing din kanshin Abba nane." Dariya yai yace " ni inada meeting bari naje inkin tashi kya kullemin kofar ki ajiye makullin agunki, karkuma ki bari kowa ya shigo, ki rufe kofar kafin ki kwanta." Tai dariya tace waye ma agidan dazai shigo. Yace " tashi muje ki kulle kafin ki kwanta." Ta tashi yana fita ta kulle sannan ta kira Ashraf tace "Yaya kana ina?" Yace " ina d'aki." Tace " in kawo ma." Da sauri yace " A'a Nisa in kika fito dashi wani ya gani fa?" Tace " ah haka ne, to ya za ai?" Shiru yai kafin yace, bari nazo nan din in yaso sai kije gun Umma in na gama gani sai in kiraki." Tace "bazan iya tsayawa mu gani tare ba?" Yace " banaso ne ki ga yanayin da zan shiga." Tai murmushin sannan tace " shikenan sai kazo." Yana fita ta leka karkashin gadon, karamin akwati ta gani dab kit, tai dariya tace " wannan ai karamin akwati ne nasan baifi kala daya bane a ciki " Ashraf na zuwa sukai canje ita tai bangaren Umma shi kuma ya shiga. Akan gado yaga akwatin jikinsa ne ya fara rawa a hankali ya karasa gun akwatin cikin shakku da tsoron abinda zai gani. Bayan ya zauna ya dade kafin ya daure ya bud'e akwatin. Idanunsa ya bud'e a hankali ya kalli cikin akwatin. Waya ya gani, da kuma envelope guda biyu. Wayar ya d'aga waya ce irin ta da jiki a sanyaye ya kunna wayar, hotonsa yana karami ne ya bayyana akan wayar idanunsa ne suka fifito, wayar mahaifinsa ce kenan? Envelope daya ya d'auko hotuna ne a ciki nan ya fito dasu, kana ganinsu kaga hoton da dan farare ne irin black and white din nan. Na farko hoton Kawu ne shida wani mutum suna tsaye jikin wata mota suna gaisawa da alama ma basusan an d'aukesu ba. Na biyu kawu ne da Dady da kuma wannan mutumin sun fito daga wani gida nan ma kana gani kasan basu san an daukesu ba. Na uku kuwa hoton Abbansa ne da Kawu ga Mumy a tsakiya. Kallan hotunan ya tsaya yi sai kuma ya d'auko wayarsa dake cikin jaka ya d'auki hutunan hoto. Sannan ya bud'e d'ayan envelope din, wasika ce. Mamaki ya kamashi ya kalli kasan wasikar an rubuta daga D'an uwanka Abbas. Idanu ya zaro da sauri ya zari takardar sannan ya nemo wata takardar a cikin jakarsa plain ya sa a ciki. Sannan ya sa waccan a aljihunsa. Wayar ya sake dauka, ya jujuyata sannan ya maidata, ya rufe sannan ya fito. Anisa yama waya ta dawo sannan yai office. Wanene wannan mutumin?abinda yake ta mai yawo kenan. Da sauri ya kira wayar D'an litti bayan sun gaisa yace " Dan Litti kana ina?" Yace " ka manta kace inje gidan Lawyer din nan inji ko mutumin ya dawo?" Ashraf ya dan shafi kansa yace " bar wannan kazo company yanzu akwai abinda nakeso kai da wannan dan sandan ku nemo min." Dan Litti yace " Yes sir." Nan ya juyar da kan mota yai gun Ashraf. Bayan ya shiga office dib Ashraf ya turamai hotob Kawu da wannan mutumin yace " wannan mutumin nakeso a nemomin inda yake, ni kuma zanje gub Uncle inji wanene shi." Dan Litti ya mai salute sannan ya fita. Ashraf ya zaro wasikar nan daga aljihunsa ya kura ma wasikar ido, a zahiri tsoron karantawa yake dan baisan mai zai jiyo wa kunnensa ba. Sai dai ko dan ya dawo da Nafisan sa kusa dashi dole yai saurin yib solving din wannan case din. ************ Nafi kam ita kadai tana kwance a d'aki yau ma ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin komai taji an banko mata kofa. D'agowa tai a hankali dan ganin wanene. Anisa ce da Umma hakab yasa tadanyi tsaki kadan tare da maida kanta. Umma da Anisa suka shigo, Umma tace " ha'a su bora ashe ananan? Ko da yake anci jan miyan anci nama anci shinkafa inafa za'a yarda a koma riga a sha fura da kunu?" Nafi ba tanka musu ba, Anisa tai dariya tace " Umma ina tunanin ince yaya ya d'aukeni muje honeymoon ko paris ne muyi ko 1week ne." Nafi barasan sanda ta dago ba ta kalleta wani irin kalli wanda ita kanra batasan ta yi ba." Umma ta sa hannu ta hankadata kan gadon tace " me? Kishi kike? Ji kike kamar ki daketa?" Nafi kam shiru kawai tai, Anisa tai dariya tace " karki damu zan kawo miki takardar sakinki." Nafi ta mike tsaye ta musu wani kallo tace " in kun gama please kuyi waje." Anisa tace " mene?" Nafi tace " inda saura kuma ku gama kafin ku fita." Tana kainan ta kwanta akan gado tare da rufe idanta. Haushi ya turnukesu, Umma tace " Kyale ta zamugani ko bakin nanan in har aka bata takardarta." Dariya suka sa sannan sukai waje. Nace uhmmmmm _Zuwa ga Muktar_+ _Ba sai munja duguwar magana ba, na sani bazan tashi daga kwanciyar nan ba._ _Da farko dai ina mai baka hakuri abisa rashin sanina na san Ruma da kakeyi wanda kai baka aureta ba ta kuma zama matar yayanka, Allah shine shaidata ban taba sanin kana santa ba ko da kuwa da wasa ne._ _Abu na biyu shine kayu hakuri abisa rashin kula dakai da banyi ba, ganin yanda ka canza hali ka rikid'e zuwa mutum mai tsananin buri da kuma neman sai ya samu abinda yakeso ko ta halin ka ka ne yasa na shiga tunanin laifinane da ban kula dakai da kyau ba, Muktar ita rayuwa da kake ganinta ba'a mata buri mai yawa, ba kuma a cewa komai sai an samu, na sani sarai kaine kai manakisa ka sanar da abokinka da yake aikin custom akan su Hisham sun saro miyagun abubuwa, bayan rasuwar mahaifin Ruma nai bincike akai anan na gano kaine kasanar da abokinka, na fahimci so kake ka hadani fada da Hisham da iyayen Ruma wanda harzai sa su rabani da Ruma._ _kai ka zuga dan siyasa wato Chirman Santa akan ya ba Hisham makudan kudi ya kuma nemi ya taimakamai da saro miyagun abubuwa, sannan ka karkata ka sanar da abokinka, duk daga baya na gane trap ne ka shirya dan rabani da Hisham da iyayensa._ _Muktar na dade ina mamaki akan wannan al'amari, na d'auka ka hakura da Ruma ganin akwai zuri'a a tsakaninmu, sai dai daga a yayin da nai hatsari na gane lalai ba hakura kai da ita ba shiri kakeyi ta yanda zaka sameta ko ta halin kaka ne._ _Muktar na sani sarai da kai da Hisham kune sanadin wannan hatsarin nawa, domin kuwa na san komai, kun samu Auwal Max akan ya lalata birkin motata sai dai a lokacin da na sani lokaci ya riga ya kuremin domin kuwa ina cikin mota nayi nisa da fara tafiya, Isma'il ya turomin da hotunan ku gidana wanda Ruma ta kirani cikin gaggawa sai dai lokaci ya riga ya kuremin, ko ince dama can kwanana ya kare._ _Ban taba tunanin tsanar da kakemin zatakai ga hallakani ba, na maka komai na rayuwa, na kuma nemi 'yarka da ta zama matar d'ana, sai dai a wannan lokacin na janye zancen auren Anisa da Ashraf, banaso d'ana ya fiskanci kiyayya da wahalar danasha a gunku, ya rayuwarsa zata kasance inhar yaji Mahaifin matarsa shine yai sanadiyar nasa mahaifin?_ _Muktar nayi iya bakin kokarina wajen farantamaka da janka a jiki duk da nasan tsananin kiyayyar da kakemin akan Ruma da dukiyata sai dai ina rokonka kar wannan kiyayar ta koma kan d'ana, na yafe maka duk abinda kamin, amma bazan taba yafemaka ba in har ka cutar da Ashraf._ *Daga D'an uwanka Abbas* Da sauri Ashraf ya saki takardar yana girgiza kai cikin tsananin firgice, lalai Kawu mutum ne wanda dole aji tsoronsa, kasa ya sauka jikinsa sai rawa yake ya jingina da bango tare da hade kafafunsa yana girgiza kai kenan Kawu shine yasa aka kama kayan su Dady dan yasan halin Abbansa bazai taba taimakon su ba akan harkar miyagun aiyuka ba. Kansa ya cusa cikin cinyoyinsa a hankali hawaye ya fara zubo mai, wayarsa ce take ta kara sai dai sam ya kasa ko da mikewa, yanaji wayar har ta gaji ta katse. Ya dade a wannan yanayi kafin ya daure ya d'au wayarsa da taketa faman kara, Dan litti ne da kyar ya daga batare da yace komai ba. Dan litti yace " Oga Auwal Max ne a hoton nan." Kai ya daga kawai dama jikinsa ya gama bashi nan ya katse wayar tare da yin shiru, ya akai hotunan da aka ba mumy suka kare a hannun kawu? Da sauri ya mike ya zari makulli yai waje cikin tsananin rudani. Bangaren Mumy ya nufa zuciyarsa na masa wani irin radadi, banko kofa yai da karfin tsiya wanda ita kuma tana zaune rike da karamin hoto, tana jin yanda aka banko kofar ta mike da sauri hoton ya fadi kasa, kallan hoton yai ganin Abbansa ne a jiki. STORY CONTINUES BELOW Wata irin dariyar takaici ya saki ya matso kusa da ita ya tsugunna ya dau hoton ya kalleta cikin tsananin takaici yace " me kikeyi da wannan?" Kallansa take cikin wani yanayi, ganin yanda ya rikid'e gaba daya, tace " Ashraf." Kallanta yai idanunsa sunyi jaa sosai yace " me kikeyi da hoton mahaifina? Bayan da ke aka hada baki akai komai?" Kallansa tai tace " Ashraf wai meke damunka ne kwanan nan da baka iya boye emotion din ka?" Ha ha ha ha! Yai tafi da hannunsa yace " Emotion? Kamar yanda kikeyi? Ku halaka min uba sannan ki wani dauki hotonsa kina kallo?" Idanu ta runtse cikin wani yanayi, wayarsa ya bud'e ya shiga nuna mata hotunan nan, yace " hoton nan ke Isma'il yaba shaidar shirin da Dady da kawu sukeyi na halaka mahaifina, tambaya ta anan shine tayaya akai hotunan nan suka isa gun Kawu?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana sai hawaye kawai takeyi, Ashraf yace " Good! Dama nasan bakida amsa, sai dai Mumy dukanku sai kun amshi laifinku a gaban hukuma an muku hukunci." Yana kai nan ya juya zai fita, haryaje bakin kofa yaji tace " Kana tunanin duk a san raina nake komai?" Tsayawa yai cak ba tare da ya juyo ba, tana kallan bayansa ga hawaye na zuba sosai a idanunta tace " me kake tunani? Banasan Mahaifinka? Ashraf na auri mahaifinka ne saboda soyayya ba dan komai ba." Juyowa yai yace " a'a kin aureshi ne saboda kudin sa." Cikin zafi tace"lokacin dana auri Abbas kana tunanin yanada kudi? Mahaifina shine ya neman masa aiki har ya zama abinda ya zama." Ashraf ya kalleta baice komai ba. Mumy ta zauna jabbas akan kujera ta share hawayenta tace " Zauna." Jikinsa a sanyaye ya zauna yana kallanta. Mumy ta kara share kwallarta sannan tace " Muktar bakasan wanene shi ba haryanzu, mutum ne wanda inyace yanasan kaza to fa sai ya sameshi ko da kuwa ta wani hali ne, bayan aurena da mahaifinka har Allah ya azirtashi ya gina wannan gidan baisan Muktar na sona ba, ni kaina sai bayan mun zauna tare sannan nai dana sani sosai dana amince da wannan hadin gidan. Muktar haka zai zo bangarena ya dade duk yanda naso ya tafi bazai tafi ba, anan zaici abinci ni kuma sai dai in shige d'aki. Danama Abbas magana sai yace kar in damu ba komai. Tsoro na ya fara yawa ne daga sanda Muktar ya shigomin d'aki ina bacci ya zauna kusa dani, idona a rufe na dauka Abbas ne inaji yana ta shafamin kai ina murmushi, sai dai daga sanda na bude ido na ganshi na mike da sauri na sa hijab na fara mai masifa. Abinda ya tsoratani shima cikin masifa ya matso ya turani jikin bango gaba daya idanunsa sun canza kamar bashi ba yace " Ruma kinsan tun yaushe nake dakon kaunarki? Banaji duk duniya akwai wanda ya isa ya rabani dake, wlh kinji na rantse miki sai na mallakeki ko ta wani hali ne." Ya sakeni yai waje a fusace. Tun daga wannan rana na fara rufe bangarena sai kuma awannan lokacin Abbas yasan komai sai dai bai taba kawowa Muktar zaiyi tunanin mun wani abuba." Mumy taja wani numfashi tacigaba, a sanda suka hada plan din halaka mahaifinka matar Dady taji komai, sanda aka kawomin hoto ina kokarin kiran Abbas matar ya hisham ta kirani nan ta sanar dani komai. Cikin rikicewa na kira Abbas na sanar dashi sai dai alokacin yana mota, bayan yayi hatsari ne ya sanar dani inyi a hankali da muktar lalai zai iya yimaka illa." Ashraf jin Mumy tayi shiru yasa yace " naji na kuma fahimta sai dai tambayata anan shine ta yaya hotunan nan suka je gun Kawu?" Tace "Dauka yai da ina asibiti." Ashraf yace " menene dalilin dayasa kafin Abba ya rasu ya bar zama dake kullum sai dai ya zauna dani?" Kallan Ashraf tai cikin wani yanayi tace " Ashraf wlh sharri akamin, Muktar ne ya d'aukoni daga gidan Ya hisham sai yace yanada abinda zai kai Tahir Guest palace shine muka shiga, ni a mota ma na tsaya ya shiga ya fito amma bansan ya akai ba wani ya dau hoto ya turama Abbas, tundaga lokacin naga ya daina shiga harkata sam nikuma ban kawo komai a raina ba, sai bayan yayi hatsari ya sanar dani dalili." Kallan rashin aminta Ashraf ya mata sannan ya mike tsaye yace " kinsan yana sanki akan me zaki yarda har ya daukoki? Sannan akan me zaki aureshi bayan kinsan shine ajalin mijinki?" Kuka Mumy tasa sosai tace " Ashraf bazaka taba fahimtata ba, Na auri Muktar ne dan na kareka, na auri Muktar ne dan na kare yayana na auri Muktar ne dan kare dukiyar da mahaifinka ya tara da guminsa." Ba tare da ya zauna ba ya mata kallan mamaki. Mumy kuka take sosai tace " Muktar shi yaba Ya hisham shawarar a halaka Abbas sai dai ya Hisham shine ya sanar da Driver din Abbas, wanda ashe cikin shirinshi ne ya dau recording din maganar Ya hisham a sanda yake bada umarni, bayan anyi sadakar bakwai ya kawomin ya bani naji yace bazai kuma yadda da kashemai dan uwa da hisham yai ba, sai dai alokacin banida evidence da zai nuna hardashi, shi kuma yanada wanda inyakai kotu kama ya Hisham ba wani abu bane." Ashraf ya kalli Mumy baice komai ba. Tacigaba " Ashraf." Idanunsa ne suka ciciko da kwalla yace " what about me?" cikin wani yanayi yake maganar, yace " nifa? Wanda baki taba ba kulawa ba, baki taba sanin matsalata ba? Nifa?" Hawayenta ya tsananta sosai da sosai, sai dai ta kasa magana, Ashraf ya daki inda zuciyarsa take yace " yanda baki taba kula da halin da nake ciki ba banaji kinsan matsalar mahaifina, tunda har shima zai dauke miki kafa amma baki tambayeshi dalili ba, wace irin rayuwa kuka jefa Mahaifina a ciki? Ke da kike matarsa bakisan matsalarsa ba kamar yanda bakisan ta danki ba, shi da yake dan uwansa yana neman illatashi, kamar yanda yake neman illatani." Ya juya cikin wani yanayi ya fara tafiya yana hard'e kafa saura kiris ya fadi yaji an rikeshi. A hankali ya dago ya kalleta, kuka take sosai, ta taso da niyyar zuwa gaida Mumy taji maganar Ashraf cikin b'acin rai daga bakin kofa. Kallan ta ya tsaya yi zuciyarshi na tafasa, dagewa yai yana neman maida kwallarsa, Nafi kuka take sosai idanunta na kansa. Lumshe idanunsa yai ya bude su ya kalleta yace " Nafisa ya akeso inyi da rayuwata? Me yasa ba wanda yake fahimtar kuna da radadin da zuciyata keyi?" Kuka takeyi cikin kuka tace " Yaya Allahn daya hallacemu yafi kowa sanin halin da kake ciki kuma shi zai kawo maka mafita." Murmushi yai sannan ya zare hannunta daga jikinsa ya mike yai waje. Mota ya fada yai waje da gudu, tafiya kawai yake, babban burinsa bai wuce yaga Nafi a jikinsa ba tana lallashinsa sai dai ya zai yi? Ya fahimta Mumy ba da ita akai komai ba sai dai bazai taba fahimtar selfishness dinta ba na kin kula da mijinta da danta ba. *********** Mumy kam yana fita ta tsugunna tana kuka, cikin kuka tace " Ashraf nasani sarai laifinane sai dai tsoro nake in nuna maka soyayya kishin Muktar ya motsa ya nemi halakamin kai." Nafi ta kalleta tace " Mumy na fahimceki sai dai duk da ba hurimina bane zance abu daya, rashin nuna soyayyarki ga Yaya bai hana Kawu tsanarsa ba da san halakashi, wannan dalilin shi zai sa Yaya ya kasa fahimtar dalilin ki na kin nunamai kulawa." Tana kainan tai waje tana share hawaye. D'akinta ta nufa ta zauna ta bude wani shafin kukan, ya zatai da Ashraf? He is soo pitiful, ita tsoronta ma kar wani ciwo ya kamashi. Jitai gefen cikinta ya rike, ta san matsalar sarai rashin cin abincine sai dai ta ina zata iya tauna abinci bayan yanzu tasan yaya ko ruwa bataji zai iya hadiya a halin daya tsinci kansa?"

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER 22"