Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMMI CHAPTER 15

UMMI CHAPTER 15

- - Post a Comment
UMMI CHAPTER 15
Gyaran muryar da yayi ce ta sanya ta zabura harda jefar da cokalin... Ko da ta dago kai ta gan shi gani nayi ta saki ajiyar zuciya yayinda ta dafe qirjinta... Lado wanda yake riqe da wasu manyan ledoji ne ya wuce yana dariya yayinda MK ya tsaya yana kallonta.+ Miqewa tayi tana qoqarin daukar cokalin da ta jefar tace "Sweetheart sannu da zuwa.." 'Sweetheart' shine sunan da ta zaba mishi finally! Shiru kawai yayi yana kallonta. He was carried away by her beauty.. Allah ma ya sani she is the most beautiful thing he has ever seen in his life...1 Qarasowa tayi wurin shi cikin shagwaba tace "uhm.. dagaske wannan ne kawai na sha yau" MK wanda ya girgiza kai yana murmushi ya janyo ta jikin shi yayi hugging dinta yace "Kin yi kyau sossai Babyna.." Yana shaqar qamshin ta yace "Allah ya sani ina bala'in son ki.. I missed you so much... ni kam gaskiya na gaji da kwana ni kadai.."1 Ummi dai tayi mamakin yadda baiyi mata masifa akan Ice cream din da take sha ba.. Kwanciya tayi a jikin shi yayinda tace "Yi haquri Sweetheart.. ka ga nima nayi kewar kasancewa tare da kai..." Ta turo baki cikin shagwaba tace "Kullum sai na fara bacci sai ka gudu ka bar ni.." Breaking hug din yayi sannan ya dago fuskarta yana qare mata kallo... Gashin gaban goshin ta wanda ya kwanta ne ya shafa yayinda yace "toh ko in dawo gidan nan da zama ne kawai.." Fashewa tayi da dariya tace "wallahi da na ji dadi.. dama fa duk duniyan nan na fi son ku da kai da Goggo.. ka ga kawai sai muyi zaman mu tare..." yayinda ta janyo shi suka koma kan kujera. Ko kafin su zauna MK ya hango empty robobin ice cream har uku da ta shanye already... Girgiza kai yayi yace "kin ce guda daya kika sha.. wa ya sha wadancan?" A rude tace "uhm.. Goggo ce ta sha.."1 A daidai lokacin ne Goggo ta shigo falon tace "ni na sha me??? ke Ummi ki ji tsoron Allah fa.. yaushe zan iya shan wannan kayan zaqin??" Ta kalli MK tace "aikuwa dai in fadi maka maganar gaskiya yau ta sha ya kai roba biyar kenan... nayi masifa har na gaji" Da sauri MK ya kalli Ummi yace "what?? baby??" Matsawa tayi daf da shi ta rungume shi tare da fadin "sorry sweetheart... bazan qara ba dagaske" Tayi mishi kiss a kumatu tace "I love you" tare da kashe mishi ido daya. Hararar ta yayi yace "ni dai babu ruwana... mura tana kama ki zan kira likita yayi miki allura" Goggo ce take ta dariya yayinda Ummi ta dinga turo baki tana bata rai. Cikin shagwaba tace "toh wai ba kai ka koya mun shan ice cream din ba??" Zaro idanuwa yayi yace "Ni? yaushe?? ni da sai inyi wata biyu ma ban sha ice cream roba daya ba Baby ta ya zan koya miki shan shi??" Kai tsaye tace "ka manta kafin muyi aure da nake gidan ka kana aiko mun da ice cream dayawa.. lokacin fa idan nace maka akwai saura basu qare ba ko sauraro na baka yi.." Sosa kan shi yayi sannan yace "toh amma dai ko da nake aikowa ban ce ki sha dayawa a lokaci daya ba.." Tana dariya tace "Sweetheart idan ban sha dayawa ba ta ya zasu ragu har idan ka aiko wasu su samu wurin zama a cikin freezer din?" Goggo dai sai dariya take yi musu.. Ji nayi tace "au ashe ma laifin ka ne Kabiru" Shima yana dariya yace "aikuwa nayi kuskure Goggo" Lado ne ya shigo falon ya zauna suka cigaba da hira. A cikin hirar ne MK yace "Umar ya makaranta?" Ko kafin ya amsa ne Ummi tace "Umar kuma??" can kuma tace "wai.. na manta fa sunan Lado na gaskiya Umar ko??" Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda MK yace "bawan Allah haka kawai kun boye mishi sunan shi na asali kun maaka mishi wani Lado.." Goggo tana dariya tace "toh ai sunan kakan shi ya ci shiyasa aka rufe sunan.." Lado yana dariya shima yace "wallahi idan an kira ni da Umar Musa a makaranta bana ma gane cewar da ni ake.." Ummi ce tace "toh ai da ka cigaba da amfani da Ladon ka kawai.." Kai tsaye yace "Mun baro Lado a qauyen Rugange.. Wannan Umar ne" Gaba daya suka fashe da dariya. MK ne yace "kayi qoqari ka samu result mai kyau idan ka gama sai in samo maka admission a qasar waje.." Cike da Murna Lado yace "dagaske Hamma?" MK ya girgiza kai yace "insha Allah.. ai zaka fi samun ingantaccen karatu a can considering the kind of course da kake son yi" Aikuwa cike da murna Lado ya dinga yi ma MK godiya. Haka Goggo da Ummi ma suka dinga yi mishi adduo'i iri-iri na fatan alkhairi. MK ya kalli Goggo yace "uhm.. Goggo dama ina so in fadi miki jibi insha Allah zamuyi tafiya ni da Ummi..." Ummi wadda ta cika da murna tace "dagaske Sweetheart?" Yana murmushi yace "yes Baby.. Ina so ki dan sha iska ki qara hutawa sossai" Cike da murna tace "yeeey... amma na ji dadi sossai wallahi.." Goggo wadda take kallon shi tace "yanzu Kabiru wane hutu take buqata banda wanda take samu a yanzu?" MK dai ya gane cewar Goggo ta gano yana so ne kawai ya kasance tare da matar shi don haka ne ya wayance yace "shawara likita ta bayar Goggo..." cikin tsokana yace "idan ma zaki je kawai ki shirya mu tafi tare" Hararar shi tayi tace "Ni?? rufa mun asiri.. kai dai dauki matar ka kuyi ta tafiya.. ai kayi qoqari ma da baka tare mun anan ba" Gaba dayan su suka yi dariya... ♧♧♧♧♧♧ Haka dai MK ya gama shirya musu tafiyar su yayinda suka je har gida suka yi ma su Abba sallama.. Har gidan Daddy sun je sun yi musu sallama kuma wani ikon Allah har suka bar gidan basu hadu da Maleeka ba sannan su Daddy basuyi mishi maganar ta ba. why??? Da suka je gidan Fahad kuwa Fatima ta janye Ummi dakinta ta hada mata turarruka da mayyuka kala-kala tayi mata bayanin yadda zata yi amfani da su. Shi kuwa MK ya dinga yi ma Fahad bayanin abubuwan da ya fara wadanda yake so ya kammala mishi su a office.. A yadda yake yi mishi bayanin abubuwa zaka gane cewar he is going on a long trip.. like seriously?? how long??? ♧♧♧♧♧♧♧♧ ♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune take a kan gadon dakin ta tayi tagumi tana ta tunani. A yau kwana goma kenan da MK yayi confronting dinta akan abinda tayi ma Ummi. Tun ranar da wannan al'amarin ya faru bata qara ji daga gare shi ba.. Infact ita kanta bata qara fita ba.. Gaba daya tayi disconnecting kanta daga outside world. A kullum maganganun MK ne suke yawo a qwalwar ta.. Tabbas laifin ta ne, ita ta janyo dukkanin abubuwan da ke faruwa a rayuwarta.. ita ta janyo matsaloli a rayuwar auren su.. ita tayi inviting third party (Ummi) a cikin rayuwar su. Da ta kula da al'amuran MK things would have been different.. tabbas ta sani cewar bata nuna mishi kulawa ba kamar yadda ya kamata infact she never cared about him... he has sacrificed so much for her amma in return she has done nothing for him.. he has been nothing but a good brother, cousin, husband and companion. Again, duk rashin mutuncin da take yi mishi bai nuna bacin ran shi ba... asali ma lallashin ta yake yi akan tayi haquri su cigaba da zama lafiya... but she ruined everything, she shattered his dream. A yanayin yadda MK yayi confronting dinta ta tabbatar ta kai shi bango.. ta tabbatar yayi fushi. Ai dole ma yayi fushi.. she killed his unborn child for crying out loud! Tambaya anan shine wane mataki yake shirin dauka a kanta?? sakin ta zai yi? zama zatayi ta jira har sai ya yanke hukunci akanta? Tana share hawayen fuskarta na ji tace "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, na tafka babban kuskure a rayuwata.. Yanzu ta ya zan gyara wannan kuskuren da nayi??.." Gani nayi ta janyo wayarta da sauri ta kunna.. tana kunnawa kuwa messages suka dinga shigowa.. A ciki kuwa harda na Jameela da kuma na Kamfanin Karen kane na qasar Carlifornia da kuma ma wadansu. ko da ta bude daya daga cikin messages din Jameela rubutu ta gani kamar haka: Hey Leek what's up with you? ina ta neman ki amma switched off.. hope you doing good? please call me as soon as you see this.. I miss you alot bestie. Regards.. Har ta kai hannu zata yi dailing lambar Jameela sai kuma tayi pause.. Meyasa a koda yaushe idan tayi shirme she always run to her for solution? A yanzu haka tun a day before the incident with Ummi ne Jameela tayi tafiya tare da mahaifiyarta zuwa qasar Chad don halarta bikin wata cousin dinta.. she must be occupied with things happening in her own life right now.. me zai sa ta dame ta da shirmen da ta tafka? Gani nayi tayi scrolling ta bude lambar MK wanda tayi saving da 'Honey' Jikinta ne yayi mugun sanyi yayinda take ta kallon lambar tana tunani.. Ajiyar zuciya ta saki sannan tayi dialing.. To her suprise wayar a kashe.. dayan layin shi tayi dialing nan ma a kashe. Cike da mamaki tace "na shiga uku.. ba dai yayi blocking dina ba??" zaiyi wuya ka kira layin shi bai shiga ba don haka ne tayi tunanin yayi blocking dinta! Daga nan ta fashe da sabon kuka tare da jefar da wayar. Bata ankara ba ta ji wayar tana ringing. Da sauri ta janyo ta duba. Kamfanin Karen Kane ne suke kiran ta. Kamfanin Karen Kane dai wani kamfani ne a qasar California wanda suka yi fice wurin yin women's designer tops, dresses, jumpsuits, pants, loungewear da accessories.. Asali dai wannan kamfanin suna shirin hada gwiwa ne da Kamfanin Leek don su yi creating wasu special collection. For the past years Leek have so much been looking forward to wannan collaboration din domin kuwa sossai Brand dinta zai qara suna sannan zata samu kudade sossai.. STORY CONTINUES BELOW Dalilin da ya sanya Maleeka ta je gida don dauko wasu takardu na kamfaninta kenan wadanda ake buqata wurin signing deal din (which ofcourse scanning zata yi ta tura musu tunda dai Daddy ya hana ta zuwa qasar waje). Har ta dauko documents din zata bar gidan ne ta ji Ummi tana waya da MK a ranar wanda tayi confronting dinta har ta kai tayi sanadiyyar abinda ya faru da ita din.. Har ta gama ringing bata yi picking ba.. ba tare da bata lokaci ba suka sake kira. Tana share hawayen fuskarta ne tayi answering. Wata mata ce tace "Good day Ma'am, I have been trying to reach you with regards to our business deal... we've not heard from you for over a week now and.." Maleeka wadda maganar matar ya ishe ta ne tace "I am sorry I wont be able to join you on this.. I have a serious issue to take care of right now"+ Cike da mamaki matar tace "But ma'am why.." Maleeka ta katse ta tare da fadin "Please just cancel our collaboration for now.. thanks" Bata jira komai ba ta jefar da wayar yayinda ta dafe kanta.. Ji nayi tace "I have only one mission right now.. getting back together with Honey. Dole ne inyi suspending duk wani abu a rayuwa ta no matter how important it is... Miji na comes first henceforth"7 nikuwa nace 'ihu bayan hari' Gani nayi ta koma ta kwanta a kan gado yayinda tace "yanzu ta ina zan fara??" Shiru tayi tana tunani mai zurfi sannan na ga ta miqe tace "I have to take this off my chest.. tunda har bai fada ba dole ne in fadi musu.." Daga nan ta sauka daga kan gadon ta fita. Ina zata je?? ************** Zaune suke a falon Daddy suna kallon news yayinda suke hira. Labaran Yaqe-yaqen da ake yi a jihar Maiduguri suke yi na qungiyar boko haram da take ta kisan gilla a garuruwa sannan take kwashe mutane musamman mata da yara. Ji nayi Mummy tace ".... ina matuqar tausaya ma sojojin nan namu. Yanzu ka duba fa ka gani haka suke barin iyalinsu su shiga daji suyi ta fafatwa da mugayen mutanen nan... abin haushin ma makaman da ake ba sojojin namu ba wasu na arziki ba.. toh ba dole ayi ta kashe su ba.. babu shakka gwamnatin nan tamu bata rasa hannu a cikin harkar nan ta boko haram domin kuwa abu ya qi ci ya qi cinyewa sannan tayi shiru.." Daddy ya girgiza kai yace "ai abin babu dadi gaskiya.. yanzu dai ki duba ki gani fa bugu daya sun tayar da bomb wanda yayi sanadiyyar mutuwar sojojin mu guda talatin da bakwai.. yanzu fisabilillah haka za'a cigaba da sa musu idanuwa suna yi mana abinda suka ga dama? ki ga fa sojojin mu masu hazaqa suke jajircewa a fagen yaqi suna qwato garuruwan da boko haram take mamayewa amma tashi daya sai a hada surqullen da zaki ji an kashe su.. shin kina gani abubuwa zasu gyaru a hakan??.." Mummy wadda ta cika da tausayi ce tace "Allah sarki bayin Allah... Ubangiji Allah ya jiqan dukkanin sojojin da suka sadaukar da rayuwar su a wurin yaqe-yaqen nan..., Allah yasa ayyukan su na qwarai su bi su.. Allah ya sada su da gidan Aljannah sannan ya raya zuri'ar da suka bari baki daya.." Daddy yace "Ameen ya Rabbi.." Ameeen.. Suna cikin hirar su ne ta shigo falon jiki a sanyaye. Mummy da Daddy dai bin ta suka yi da ido har ta samu wuri ta zauna a qasa. Gaba dayanta a hargitse take.. abin mamaki shine ko da na kalli fuskokin iyayen nata ba wani damuwa suka yi da halin da take ciki ba.. STORY CONTINUES BELOW Why?? Mummy ce tace "Maleeka lafiyar ki kuwa na gan ki haka?" Muryarta qasa-qasa tace "uhm.. dama akwai maganar da nake so in fadi muku amma don Allah kuyi haquri... wallahi nayi nadamar abinda nayi kuma bazan qara ba.." Daddy ne yace "what have you done again this time?" Da qyar Maleeka tayi gathering courage sannan tace "uhmm.. dama akan abinda ya faru da Ummi ne...." Daga nan ta fara basu labarin abinda ya faru daga farko har qarshe... Babu abinda su Mummy ke yi banda salati... ita kuwa tunda ta fara basu labarin take rusa kuka. Cikin fushi Mummy tace "Yanzu fisabilillah ke ce kika yi sanadiyyar abinda ya faru? shine muka yi ta zarya zuwa asibiti yarinyar tana kallon mu a matsayin iyayen wadda ta raba ta da cikin da ke jikinta? Gaskiya Maleeka baki kyauta ma rayuwar ki ba.. kin cuci rayuwarki.." Daddy ne yace "toh wai tsaya.. kina nufin MK ya san aika-aikar da kika yi shine yayi shiru bai fadi ba? toh me yake nufi da hakan?? ai wannan babban laifi ne that cant go unpunished.. infact na gaji da wannan iskancin don haka dole ne in raba auren nan" Gani nayi ya fara laluba wayar shi yana fadin "bari in kira shi..." Cike da nadama Maleeka tayi kneel down tare da hada hannuwan ta biyu alamar roqo tace "don Allah Daddy kuyi haquri ku yafe mun... wallahi ba da gangan nayi ba.. Honey yayi fushi da ni.. don Allah ku taya ni bashi haquri.. Daddy please kar ka raba auren, a yanzu duk abinda yake so zanyi kuma bazan qara yin abubuwan da nake yi ba a baya.. I dont want to lose him because I love him.. idan ya sake ni wallahi mutuwa zanyi.." Kuka ne ya ci qarfin ta yayinda su Daddy suka yi shiru suna kallonta. Gaba daya jikin su yayi sanyi ganin yadda take shesheka kamar zata mutu.. A zahiri basu taba ganin this side of Maleeka ba.. one thing is for sure, sun tabbatar tayi regretting abinda ta aikata.. but it could be too late.. right?? Gani nayi Daddy yayi ma Mummy signal.. Mummy ta janyota tayi hugging dinta tana lallashin ta. Da qyar Mummy ta shawo kanta tayi shiru amma fa har a wannan lokacin hawaye na zuba daga idanuwan ta. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Tabbas abinda kika aikata baki kyauta ba, kin tafka babban kuskure. Ke kin qi ki haifo mishi Baby kuma ga wadda take shirin haifo mishi kin je kinyi sanadiyyar zubewar shi.. Ba sai na fadi miki munin laifin da kika aikata ba, ke da kanki kin sani don haka you should be ready to face the consequences.. bazan raba auren ku ba amma ki sani babu ruwana da hukuncin da MK zai yanke miki idan ya dawo because God knows yaron nan yayi haqurin zama da ke.. at this point in time duk decision din da zai yi taking I will support him.." Cikin kuka tace "Daddy don Allah.. wallahi idan baka sa baki ba zai sake ni, ka ga har yayi blocking layi na don ina ta kira baya shiga" Mummy wadda take rungume da ita ce tace "ba blocking din ki yayi ba Maleeka.. yayi tafiya ne baya qasar.. Shekaran jiya da daddare suka zo shi da Ummi suka yi mana sallama.." Zuciyar Maleeka ce ta buga yayinda jikinta yayi mugun sanyi.. kenan MK ya fita batun ta kwata-kwata??? kenan ita a wane matsayi ya barta?? ya yafe mata ne ko kuwa idan ya dawo zai sake ta? Qara fashewa tayi da kuka yayinda tace "na shiga uku yanzu ya zanyi da rayuwa ta? toh yanzu sai yaushe zasu dawo??" Shiru ta dan yi sannan tace "don Allah Daddy ka kira shi kace su dawo.." STORY CONTINUES BELOW Daga Daddy har Mummy wannan maganar ta so ta basu dariya amma suka matse.. Ba tun yau ba sun kula baqin kishin Maleeka da taurin kanta shi ya jefa ta halin da take ciki a yanzu. Mummy ce tace "Shawarar da zan baki a yanzu ita ce.. ki tattara kayanki ki koma gidan mijin ki tunda dai ba sakin ki yayi ba... try and work on yourself before they return.. idan har ya haqura sai ku cigaba da zaman ku" ta kalli Daddy tace "ko ya ka gani?" Daddy yace "it's a good idea.. idan kuma ya dawo ya sake ta sai ta dawo gida.." Cike da tashin hankali Maleeka ta kalli Daddy wanda ya miqe yace "...good night" Komawa tayi jikin Mummy ta kwanta tana ta rusa kuka.. Sossai Mummy ta tausaya mata. Haka dai ta dinga yi mata nasiha masu sanyaya zuciya har ta dan kwantar da hankalin ta. Mummy dai a ranta addu'a take yi Allah yasa ta canza hali for good... that's idan lokaci bai qure mata ba kenan..1 hmmm... ♧♧♧♧♧♧♧♧ Aikuwa washegari tun da safe Maleeka ta kira masu aiki suka hada mata kayan ta tsab.. Da yamma ta tattara ta koma gidan ta. Sossai su Daddy suka ji dadin step din da tayi taking.. Sun tabbatar cewar she has redeemed herself.. kamar yadda Daddy ya fada he is not going to interfere with MK's decision but they are hoping hukuncin da zai yanke bazai yi ma Maleeka tsauri ba..1 Maleeka dai ko da ta koma gidan ta a kullum haka take yini ta kwanta cikin tunani.. a koda yaushe tana tunanin MK yana can tare da yarinyar suna more rayuwar su.. Ko da ta sanar da Jameela abinda ya faru sossai abin ya bata tsoro.. ta sani sarai getting MK back is going to be very difficult toh amma dole ne ta cigaba da consoling qawarta musamman ganin yadda tayi nadama. Ko da Jameela ta dawo daga Chad kullum suna tare tana ba qawarta shawarwari wadanda suke taimakawa wurin sanyaya mata rai. Jameela ce ta ziga ta akan ta samo contact din MK wanda yake using ta dinga tura mishi text message na ban haquri sannan ta dinga gwada kiran shi... A wurin Hafsah ne Maleeka ta samu lambar wayar da yake using a qasar waje domin kuwa ta kasa tambayar su Mummy su bata lambar.. a kullum sai ta tura mishi text message na ban haquri amma babu reply. Lokutta da dama takan zauna tayi ta rusa kuka wanda daga qarshe take lallashin kanta da kanta ta haqura.. Kullum tana fama da matsanaicin ciwon kai da radadin zuciya. Tabbas da zata kai kanta asibiti za'a gaya mata jinin ta ya hau. Gashi her parents are not helping matters.. gaba daya ma ko maganar shi basu yi mata idan ta je gaishe su. Haka idan ta je gidan Mamy zasu sha hirar su har ta tafi amma sam basu kawo zancen MK da Ummi.. takan tambayi kanta why are they not bothered about her anymore?? Dukda tana cikin tsananin damuwa na tunanin matsayinta a wurin MK haka nan ta cigaba da haquri.. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Kwance take a kan lafiyayyen Chinese rug na dakin ta yayinda take kallon hotuna a wayarta.. Ko da na leqa hotunan MK ne birjik take kallo.. wasu ma tun kafin suyi aure lokacin da suke qasar Ingila.. Maleeka dai a 'yan kwanakin nan abinda take bata lokaci tana kallo kenan don ta ji sanyi a zuciyarta... Sossai tayi missing din MK, har mafarki take yi ya dawo ta bashi haquri sannan ya haqura suna zaman lafiya. Gani nayi hawaye na bin fuskarta yayinda tace "don Allah Honey kayi haquri... wallahi na tuba" Sallamar qawarta Jameela ta ji a dakin. STORY CONTINUES BELOW Tashi tayi zaune tana goge hawayen ta tare da amsa sallamar. Jameela wadda take kallonta ce tace "haba Leek.. ba dai kuka ba?? don Allah ki bari" Ta qarasa ta zauna a gefenta ta janyo ta zata rungume.. kamar wadda aka yi ma shocking na ga ta dafa kan Maleeka wanda yayi mugun zafi tace "Subhanalillah Leek.. kina running temperature.. baki da lafiya ne??" Maleeka dai babu abinda take yi banda kuka. A rude Jameela ta miqe tsaye tana riqe da hannun ta tace "tashi mu je asibiti.." Cikin kuka tace "bazan je ba Jay.. please leave me alone" Jameela wadda take a rude tace "na ji toh idan bazaki je asibiti ba zaki sha magani.. tashi ki koma kan gado ki kwanta" Haka ta lallabata ta koma kan gado ta kwanta tana kuka yayinda Jameela ta je ta dauko first aid kit da bottled water. PCM ta bata ta sha sannan ta koma kusa da ita ta zauna tana kallon ta. A haka har bacci mai ya kwashe ta.. da ganin yadda take baccin ka san tana cikin damuwa don ba wani nisa tayi ba.. A haka Jameela ta rufe ta da duvet ta rage mata qarfin AC sannan ta fita. Kicin ta nufa ta dafa mata abinci mai rai da lafiya don ta tabbatar hatta abinci ma bata ci ba. Bayan ta kammala ta jera komai a tray ta wuce dakin Maleeka da shi. Ko da ta shigo ta tarar Maleeka har ta farka daga baccin tana ta share hawaye... da alama ma ta kasa yin baccin ne. Girgiza kai tayi ta qarasa wurinta ta zauna ta ajiye tray din akan bed side drawer sannan ta dauki plate ta zuba mata tace "ki ci abincin nan kuma bana so in ji kin ce komai.." Ba tare da ta musa ma Jameela ba ta karba ta fara ci.. Ta ci ya wuce rabi ne ta ajiye plate din sannan ta dauki ruwa ta sha. Daga nan kuma ta jingina bayanta da board din gadonta ta runtse idanuwan ta yayinda hawaye suka cigaba da wanke mata fuska.. Cike da tausayawa Jameela tace "kin ga fa yakamata ki sassauta ma kanki kar ciwon hawan jini ya kama ki... ni fa ina ji a jikina cewar Ya MK bai manta da ke ba... da ace zai sake ki da ya sake ki tun kafin yayi tafiya.. maybe he is just trying to punish you ne.." Maleeka tana kuka tace "Wallahi qawa ta idan dai punishment ne na horu hakannan.. yayi haquri ya sassauta mun.. dagaske bazan iya jure fushin nan nashi ba"1 Jameela ta janyo ta jikinta tayi hugging dinta tare da bubbuga bayanta tana fadin "ssshhh.. ki cigaba da haquri Leek, I assure you things will fall into place Insha Allah" Tace "nagode sossai qawata.. what would I have done without you??" Jameela tana murmushi tace "it's okay bestie.. kin ga fa ina da shawara ma.. why not kafin ya dawo ki fara qoqarin gyara dukkan flaws dinki.. as in try and become a wife material" Maleeka tayi breaking hug din ta tashi zaune tace "ban gane ba..." Jameela ta gyara zama sannan tace "Ina nufin ki koyi yin abubuwa da kan ki kamar su girki, gyaran gida musamman bangaren shi.. ke na sani a baya hatta Cappuccino dinshi baki iya hadawa ba.." Maleeka ta saki ajiyar zuciya sannan tace "na tabbatar da na iya wadannan a baya da abubuwa sun kasance daban.. da na kyautata mishi a baya she wouldn't have come into his life.." Ta kalli qawarta tace "but what can I do? it's too late to cry ko?" Jameela ta girgiza kai cike da tausayin qawarta tace "kar ki damu qawa ta.. ki manta abinda ya faru a baya. Yanzu dai abinda zamuyi shine we will hire a chef to come teach you everything.. it will even keep you busy" Maleeka tace "nagode sossai Jay.. Allah ya bar zumunci.." Jameela tace "Ameen my dear friend" Canza topic tayi tace "wai ya maganar shirye-shiryen bikin ki ne?? I cant believe lokaci na ta matsowa and my problems are getting in the way of shirye shiryen da yakamata mu fara" Jameela tana murmushi tace "Ke dai dama don ba candidate dinki na zaba ba shiyasa kika yi watsi da ni.." Maleeka ta girgiza kai tace "eh toh gaskiya qawata ban ji dadi ba da zaki auri mai mata amma kuma it doesn't mean cewar bazamu yi plans din da suka kamata ba" Dariya Jameela tayi tace "bazaki gane bane qawa ta.. it's not always about namiji yana da mata ko baya da.. na so ace kin fahimci wannan.." ta fiddo Tablet dinta daga cikin jakar ta tace "to partially change the topic, kin ga dama fa na zo ne ki taya ni zaben outfits din da zan sa... kin san ke din akwai dress sense babu qarya" Maleeka ta dan yi murmushi tace "okay Jay.. let's do this" Daga nan fa suka fara dudduba kaya iri-iri. A dan wannan lokacin kuwa Maleeka took her mind off her problems wanda hakan yayi ma qawarta dadi.. Jay qawar arziki!! ♧♧♧♧♧ ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ One month later!! MALTEZA PRIVATE VILLA SANTORINI- GREECE A yau kwanan su uku da zuwa qasar Greece. Tun ranar da suka bar Nigeria Umrah suka je a qasar Saudia, watan su daya a can sannan suka zo qasar Greece.+ Tsaye take a jikin railings na balcony din executive suite din da suka sauka wanda yake dauke da sea view mai kyan gaske. Ummi dai tunda suka zo qasar kullum da safe sai ta tsaya a wurin tana kallon Sea din.. sossai view din yake birge ta. Ta yi nisa sossai a kallon Sea din da yadda tsuntsaye ke shawagi sannan ga wani iska mai dadin gaske da yake kadawa... MK ne tsaye a jikin sliding door din da yake leading to the balcony yayinda ya sanya mata idanuwa.. tunda ya farka daga bacci bai gan ta ba ya san tana wurin. Ya kula she spends alot of time a wurin tunda suka zo.. da alama dai tana son wurin sossai. Ummi dai bata ankara ba ta ji yayi hugging dinta ta baya yayinda ya kwantar da kanshi a bisa kafadar ta.. Gani nayi ta lumshe idanuwa sannan ta shafa fuskar shi tana murmushi tace "ina kwana" Yana shaqan qamshinta yace "shine kika gudu kika barni ni daya ko?" Tana murmushi tace "yi haquri sweetheart" Gani nayi ya sa hannu ya juyo da ita tana fuskantar shi yayinda ya qura mata idanuwa.. Ummi dai ganin kallon yayi yawa ne ta sa hannu ta dan ja gemun shi tace "wannan kallon fa?" Murmushi yayi yace "sonki nake yi baby" Kashe mishi ido daya tayi tace "nima ina sonka sossai.. A kullum qara gode ma Allah nake yi da ya bani kai a matsayin miji na.. in dai ina raye bazan taba barin ka ba.. A rayuwar nan bazan taba bari damuwa ta zo kusa da kai ba. Addu'a na a kullum itace Allah ya bani ikon cika maka burin ka a duniyar nan.." Sossai ya ji dadin kalaman ta... he is very much lucky to have her.. tabbas Ummi Soulmate dinshi ce. Janyo qugun ta yayi ya hada da jikin shi sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "Nagode sossai masoyiya ta.. Maganar cika mun buri na kuma mu je toh mu qara gwada sa'ar mu.." Zaro idanuwa tayi tace "yanzu sweetheart??" Hararar ta yayi yace "what? kema fa na kula kin fi son na safen nan.. har wasu irin surutai kike yi mun na daban musamman idan..." Da sauri ta sa hannu ta toshe bakin shi tace "na shiga uku.. don Allah ka bari.." MK wanda ya kashe mata ido daya bai jira komai ba ya sungume ta suka koma ciki ya shimfide ta kan lafiyayyen gadon dakin.. Aikuwa nan da nan ta janyo shi ya fado jikinta yayinda suka fara sarrafa juna cike da shaukin soyayya.. Sai da suka gurji soyayya son ran su sannan suka sarara... Suna maqale da juna a cikin Duvet cikin tsokana yace "Baby wai yaushe zaki daina yakushi na ne?? kin ga fa baya na duk tabo ne na yakushin da kike yi mun.." Qirjin shi ta kai ma duka cikin shagwaba tace "don Allah ka bari mana.. dagaske idan kana tsokana ta zanyi fushi fa" Da sauri yace "yi haquri.. MK zai shiga uku idan Ummin shi tayi fushi da shi.." Ya qara matse ta jikinshi yace "Baby, na riga na saba da ke don haka ko kadan bana so kiyi nesa da ni.. idanuwa na sun saba da ganin ki, kunnuwa na sun saba da jin sautin muryar ki, na saba da kasancewa tare da ke a koda yaushe.. idan kika yi fushi da ni I swear zan shiga babba.." STORY CONTINUES BELOW Hannu ta sa ta toshe bakin shi tare da komawa bisa shi ta kwanta tace "wasa nake yi.. nima fa bazan iya yin fushi da kai ba.. kai ne farin ciki na a rayuwar nan... ina son ka sossai.." Yana murmushi yayi wrapping hannuwan shi around her sannan ya fara jefa mata kisses all over yayinda take amsar su cike da so da qauna.. Wayar shi ce take ta ringing amma sam basu ji ba.. sunyi nisa a smooching juna. A ringing na hudu ne Ummi ta ji.. Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace "ana kiran ka a waya.." Kai tsaye yace "Baby manta da wayar nan.." Stretching hannunta tayi ta janyo wayar sannan ta miqa mishi tace "yi haquri ka amsa, qila mai muhimmanci ce" Turo baki yayi yace "toh babyna" Ko da ya duba gani nayi yayi answering yace "Yeah morning..." Ya dan yi shiru sannan yace "just forward it to my mail.. I will get back to you when I look at it" Murmushi yayi yace "thanks" Bayan ya kashe wayar ne ya shafa fuskar Ummi yace "Baby mu je muyi wanka ki zo in nuna miki wani abu" Cikin shagwaba tace "toh ka dauke ni.." Ba tare da yace komai ba ya sungume ta sai bathroom.. sai da suka bata lokaci a ciki sannan suka fito.. yana riqe da ita a hannun shi kamar wata qaramar Baby ya zaunar da ita a kan Ottoman. Tana kallon shi ya koma gaban Vanity mirror yayi 'yan shafe-shafen mayyuka ya fesa sprays sannan ya wuce closet ya shirya cikin qananan kaya na three-quarter sweatpant da T-shirt. Tunda ya fito ta sa mishi idanuwa babu qyaftawa.. Yana murmushi ya qaraso wurinta tare da jan kumatun ta yace "yeah yeah na san nayi kyau.. a rage kallon kar idanuwa su zazzago" Fashewa tayi da dariya tace "Wallahi ban qi inyi ta kallon ka ba har abada.. kana da kyau sossai" Ta huro mishi kisses tace "I love you" Hancin ta ya ja yace "thank you my beautiful wife amma fa kin fi ni kyau.." Zata yi magana ne ta ji ya dauke ta cak ya zaunar da ita kan Vanity stool yace "ssshhhh.." Lotion dinta ya dauko ya fara shafa mata... bayan ya gama ne ya feshe ta da sprays sannan ya dauke ta suka nufi closet. Shi ya zabar mata inner wears din da zata sa sannan ya dauko wata transparent material gown... Bayan ya taimaka mata ta sa ne ya juyo da ita tana fuskantar dressing mirror Sossai tayi kyau.. Gaba daya rigar ta bayyana sirrin jikinta domin kuwa her body is clearly visible.. infact rigar dai da ita da babu uwa su daya. Tana kallon shi ta cikin mirror din tace "nayi kyau?" Yana murmushi yace "sossai ma.. ina son wannan rigar saboda ta bani daman kallon Baby na da kyau" Hararar shi tayi tace "ni kuma sai inyi ta zama tsirara kenan?" Ya kashe mata ido daya yace "Zaki samu lada Babyna" Tana shirin kama gashinta a tsakiyar kai ne yayi saurin dakatar da ita yace "bar shi haka Baby.. na fi son shi a sake" Ta turo baki tace "shine baka taba fadi mun ba?" Ya rungumeta ta baya sannan yace "toh ai na ga kamar yana damun ki ne a hakan.. kamar kin fi son shi idan kika daure" Hannuwanta ta dora a kan nashi tace "toh ai farin cikin ka shine nawa Sweetheart.. abinda kake so nima shi nake so, don Allah daga yau duk abinda kake so ka dinga fadi mun ka ji?" STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai yayi yace "toh Babyna.. yanzu ma akwai abinda nake so" Tace "Sweetheart me kake so??" Gani nayi ya sa hannu ya kwance wasu igiyoyi a rigar ta wanda hakan ya bayyana cleavage dinta har zuwa belly button dinta yace "ki zauna haka in cigaba da kallon beautiful body dinnan naki.." Zaro idanuwa tayi tace "Toh amma.." Da sauri yace "sssshhhh... amma nothing" sannan ya janyo ta suka fito daga closet din. Bisa kujera suka zauna... tana kwance a kan cinyar shi yayinda yake wasa da gashin kanta ne yace "Baby.." Tace "na'am" Yace "kin tuno alqawarin da nayi miki kwanaki akan zan cika miki burin ki na mallakar Charity foundation kamar yadda kike so?" Da sauri ta tashi zaune tana kallon shi tace "eh na tuna.. amma fa kar ka damu duk lokacin da ka shirya.." Yana murmushi yace "an gama hada miki komai Baby.. ke ake jira ki fadi irin tsarin yadda kike so abubuwa su fara aiki.." Zaro idanuwa tayi a rude tace "ban gane ba... dagaske?" Girgiza mata kai yayi alamar 'eh' yayinda yake murmushi. A rude ta miqe tsaye ta sa hannu ta rufe bakinta tana kallon shi cike da mamaki.. Daga nan kuma ta fado jikin shi da sauri ta rungume shi very tight tace "na shiga uku.. na rasa da wane kalamai zan gode maka a rayuwar nan sweetheart.." Ji yayi ta fashe da kuka yayinda ta cigaba da fadin "nagode nagode sossai.. Allah ya saka maka da alkhairi, Ban taba sa ran wannan burin nawa zai cika ba sai gashi kamar a mafarki ka cika mun shi.. A koda yaushe kana cikin yi mun abin alkhairi a rayuwar nan gashi ni kuma babu abinda nayi maka da..." Dakatar da ita yayi yace "abinda kika yi mun ya fi abinda nayi miki sau dubu Baby.." Ya dago fuskarta ya sa hannu yana goge mata hawayenta sannan ya cigaba da fadin "...don Allah ki daina kuka.. kin cancanci abinda ya fi wannan daga wuri na.. I love you soo much and thank you very much for coming into my life" Murmushi tayi tace "I love you sossai nima" Gani nayi ya janyo Macbook dinshi ya kunna sannan ya shiga mail dinshi ya bude hotunan da aka aiko mishi na tsarin ginin wurin.. Ya sa ma foundation din suna 'AL-IHSAN FOUNDATION' Ummi dai sossai ta cika da mamaki domin kuwa bata yi tunanin ganin qaton wuri mai kyan tsari kamar wannan ba... wurin ya tsaru matuqa, kai idan ka kalla sai ka rantse a turai ne.. Haka dai ya dinga yi mata bayanin sections na wurin yayinda jikinta ya bi yayi sanyi.. Muryarta qasa-qasa tace "Sweetheart toh wai ta ya zan kula da wannan wurin... wallahi yayi girma dayawa sannan na ji kana ta yi mun bayanin irin abubuwan da za'ayi.. kashe kudi ai zai yi yawa.." Fashewa yayi da dariya sannan yace "Zaki iya Baby.. sannan kar ki damu ba wasu kudade masu yawa za'a kashe ba.." A sanyaye tace "toh zamu samu wani ya dinga kula mun da wurin kenan?? ka ga fa ni ban yi karatu ba.. ban ma iya turancin nan naku ba.." MK dai fashewa yayi da dariya yace "wato turancin ma namu ne ko Baby?? ba shiyasa nace miki ki shiga school ba kika qi.. yanzu ya za'ayi? ko in samo miki lesson teacher a nan din ta dinga zuwa tana koya miki??" Zaro idanuwa tayi tace "har zuwa yaushe?? na ga ai ba dadewa zamuyi anan din ba zamu koma gida ko??" Kumatun ta ya ja sannan yace "wa ya gaya miki bazamu dade ba? zamu dade sossai.. infact sai kin qara hutawa.." STORY CONTINUES BELOW Ya shafa cikinta yace "Sai ma na sa Baby a nan ciki sannan zamu tafi.." Murmushi tayi tace "Allah ya kawo mana masu albarka.." Yace "Ameen Babyna" Matsawa tayi daf da shi ta riqo hannun shi tace "toh yanzu maganar karatun.. zaka dinga koya mun turanci please.." Bata rai yayi yace "ban gane zan dinga koya miki ba.. teacher zaki mayar da ni??" Kai tsaye tace "meye teacher???" Girgiza kai yayi yace "oh MK you are so in trouble" Turo baki tayi cikin shagwaba tace "dagaske duk abinda ka koya mun zan riqe a kaina... ka ga fa da kake maganar zaka kira wata ta zo ta koya mun ita ai bata jin hausa ko fulani balle idan muna yi tana fassara mun kuma fa idan ma makaranta ne ai na wuce shekarun da yakamata.. don Allah ka koya mun da kanka ka ji.." MK dai kallonta kawai yake yi yana tunanin ta ina zai fara.. shi yaushe zai iya zama koya mata turanci.. Bai ankara ba ya ji ta fara jefa mishi kisses irin wadanda suke birkita mishi lissafi yayinda take ta fadin "please please please teacher..." MK dai bai san lokacin da ya fashe da dariya ba jin ta kira shi da teacher.. Tabbas ya san Ummi is sharp and she grabs fast. Again at this point in time turancin ne kawai ya fi zama mata wajibi ta koya saboda ta iya communicating da mutane. She doesn't need any other knowledge tunda dai ba certificate take nema ba don tayi amfani da shi wurin securing aiki. Don haka ne yayi tunanin lallai they should give it a try.. Ji nayi yace "okay okay okay.. na ji zan fara koya miki turanci amma idan kika yi mun shirme zan daina.." Da sauri tace "wallahi zan dage bazan baka kunya ba... nagode sossai" Daga nan ta hade bakin ta da nashi ta fara kashe mishi jiki da sweet kisses dinta. Wayar shi tayi ringing.. da qyar Ummi ta qyale shi ya janyo wayar ya duba caller din. Gani tayi ya bata rai sannan yayi tsaki ya mayar da wayar ya ajiye.. Ni kuwa da na leqa sunan Maleeka na gani...11 Haka wayar ta gama ringing ta qara yi bai bi ta kanta ba.. Ummi dai ta kula da shi tunda suka baro Nigeria akwai lokaci irin wannan da idan an kira shi a waya baya picking.. tunda take tare da shi bata taba ganin an kira shi a waya baiyi picking ba but suddenly sai gashi banda qin picking da yake yi har ran shi yana baci... Ta sha sakawa a ranta Maleeka ce, tana so tayi mishi maganarta amma ganin yadda ranshi ke baci idan aka ambaci sunan ta ne ya sanya ta ja bakinta tayi shiru. Deep down within her tana tausaya ma Maleeka domin kuwa duk macen da ta saba rayuwa tare da MK bazata so daidai da rana daya ma su rabu ba... MK is the kind of husband that every woman would want to spend the rest of her life with.1 Hannunta ta sa a bisa kanshi ta birkita gashin shi tace "bazaka amsa wayar bane??" Kai tsaye yace "eh" Tace "meyasa??? Adda ce??" Ran shi a bace ya gyara gashin nashi da ta birkita ya yunqura zai tashi yayinda tayi saurin cafko hannun shi tace "sweetheart don Allah kayi mata haquri.." Zare hannun shi yayi daga nata yace "bana son wannan maganar please..." Daga nan ya wuce ya nufi wurin balcony yayinda ta bi shi da idanuwa.. Da sauri ta miqe ta qarasa wurin balcony din ta shige jikin shi ta bashi tight hug ta baya tace "Yi haquri sweetheart bazan sake yi maka maganar Adda ba... Yanzu dai ka zo mu je ka fara koya mun turancin ka ji" STORY CONTINUES BELOW A siyasance ta janye shi suka koma dakin. ♧♧♧♧♧♧♧ Kamar dai yadda Ummi tayi ma MK alqawarin zata dage wurin koyon turanci sossai ta dage din.. Abin ya bashi mamaki sossai yadda da zarar ya fadi kalma sai ta riqe a kanta.. wurin rubutu ne suka dan samu matsala amma shima ahankali ta dinga picking. Sun zo Santorini ne don su huta suyi yawo amma abun sai ya canza.. A kullum suna daki yana koya mata turanci, idan sun gaji kuma su sha soyayyar su suyi ordering abinci son ran su sai kuma bacci... Rayuwarsu suke yi gwanin ban sha'awa.. babu hayaniya, just the two of them... sun qara shaquwa da juna, soyayyar da take tsakanin su ta qara qarfi, sossai suka damu da junan su.. thier connection grew much stronger... tabbas they cant live without eachother, it's as if they were specially made for eachother!! A bangaren Maleeka dai tana nan kullum tana sa ran dawowar MK amma shiru.. tun tana qirga kwanaki har ta koma qirga satutuka, yanzu ta koma qirga watanni... bata fasa kiran wayar shi ba sannan bata fasa tura mishi saqonnin text na ban haquri ba... kullum tana fama da ciwon kai da radadin zuciya saboda mugun damuwar da take ciki.11 Dukda MK ya daina turo mata kudi kamar yadda yake yi a baya batada wata matsala ta kudi domin kuwa Mummy ce take tura mata daidai ma yadda MK din yake turo mata a baya.. Iyayenta da nashi suna providing mata duk wasu needs dinta amma kuma abinda yake bata mamaki shine yadda suka qi sa baki a al'amarin ta da MK.. suna yi kamar everything is okay.. I am wondering why.. At a point in time ta so tayi giving up amma qawarta ta dinga lallashin ta akan kar ta gaji.. Kamar yadda qawarta ta bata shawarar koyon household chores da duk wani abinda bata iya ba a baya sossai ta mayar da hankali.. Yanzu kam Alhamdulillah Maleeka ta iya girke-girke kala-kala.. hatta favorite Cappuccino din MK ta iya hadawa, duk wani gyara na gida ta iya.. Babban burinta shine MK ya dawo ta bashi haquri ya yafe mata su cigaba da zaman su kamar da.. hmmmm... ♧♧♧♧♧♧♧♧ two months later!! ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a dinning daddare suna dinner. A yau Abba da Mamy sun zo gidan don duba jikin Mummy wadda bata ji dadi ba. Suna cin abinci suna ta hira ne Mamy tace "gaskiya wannan farfesun yayi dadi" Mummy wadda take murmushi tace "aikuwa dazu Sirikar ki ta aiko mun da shi.. kin san yanzu ta duqufa akan koyon girki" Mamy tana murmushi tace "Masha Allah.. ai kam babu shakka ta gama qwarewa" Abba ne yayi gyaran murya ya kalli Daddy yace "wai ya ake ciki da zancen yaron nan?? har yanzu baku gama hora yarinyar nan bane?? yau watan shi nawa da barin qasar nan?? kuma na ga tunda Allah ya qara ba Ummi wani cikin ai sai kuyi haquri ku yafe mata laifin da tayi ko" Daddy yayi murmushi yace "haba dan uwa.. duka fa watan su uku.. don Allah ka barsu su qara hutawa" Abba yace "wane irin hutu kuma? ka san da an biye mun dukda abinda ya faru bazan amince da wannan tsarin naku ba ko?? Yarinyar nan tayi laifi mun sani.. toh amma ai idan kuka yi la'akari da irin nadamar da tayi ai sai ku tausaya mata.."3 Mamy tace "wallahi duk lokacin da ta zo gaishe ni sossai take bani tausayi.. dukda tana qoqarin boye damuwarta na sani cewar she is not okay. duk tayi sanyi ta rame... Ni tsoro nake yi kar ciwon hawan jini ya kama ta" STORY CONTINUES BELOW Mummy wadda tayi murmushi tace "Ai gwara a hora ta sossai yadda zata yi hankali.. Sannan yarinyar nan Ummi tana buqatar hutu sossai.. kun ga cikin nata duka wata biyu yanzu ba wani qwari yayi ba.. don Allah ku bar su su qara hutawa.." Daddy yace "dan uwa kamar yadda na fadi muku MK shi ya san irin laifukan da Maleeka tayi mishi.. he needs to clear his mind, idan yau ya dawo yayi deciding zai rabu da Maleeka wallahi I will respect his decision.. Yarinyar nan tun tana qarama yake dawainiya da ita amma a bangaren ta babu abinda take yi mishi banda lalata iri-iri.. Kuyi haquri ku bar su har su dawo" ●●●● flashback!! ...Lokacin da Fahad ya ba MK shawarar lallai kar ya rabu da Maleeka gaba daya bai yi niyyar daukar shawarar ba.. daga baya ma he decided to just tell their parents abinda ke faruwa because baya so ayi blaming dinshi for anything that will happen daga baya.. Bayan an sallami Ummi daga asibiti kuwa ya tara iyayen su ya fadi musu komai... Gaba dayan su basu ji dadin abinda ya faru ba musamman Daddy da Mummy.. a nan take kuwa cikin bacin rai Daddy yace ma MK ya rubuta takardar saki ya ba Maleeka domin kuwa ba tun lokacin ba ya gaji da iskancin da take yi.. Abba ne ya hana, dukda shima ranshi ya baci akan abinda tayi na destroying unborn jikan shi baya so ko alama MK ya rabu da ita don ko babu komai 'yar uwar shi ce sannan duk qarfin zumuncin da yake tsakanin su idan har saki ya shiga tsakanin yaran su toh fa lallai zumuncin su zai samu rauni.. don haka ne ya dinga ba MK haquri on behalf of Maleeka amma sam Daddy da Mummy suka qeqashe akan lallai MK ya saki Maleeka kawai kuma insha Allah idan hakan ta faru zumunci su bazai taba lalacewa ba.. Abu kamar wasa dai haka suka dauki lokaci suna ta muhawara akan wannan zancen.. Abba da Mamy sun dage akan lallai kar MK ya rabu da Maleeka yayinda Mummy da Daddy suka dage akan lallai sai MK ya sake ta. Haka MK yayi ta sauraron iyayen nasu da yadda suke ta lallashin juna akan su amince da shawarar junan su.. Tabbas Maleeka is his first love.. ya so ta, yana sonta kuma bazai taba daina sonta ba but She has hurt him alot.. ko ba komai yana da zuciya ai kuma yana so a kyautata mishi.. he wants to be happy and on the contrary babu abinda take yi banda bata mishi rai..she shattered his dream.. akan wanne dalili zai cigaba da zama da ita?? Toh amma points din da Abba ya kawo a game da rashin son rabuwar nasu are strong.. Tabbas ya sani cewar idan ya rabu da Maleeka zumuncin da yake tsakanin su bazai taba zama daidai ba.. infact lalacewa ma zai yi.. he has always seen her parents as his', sun nuna mishi soyayya fiye da yadda suka nuna mata.. sun dauke shi tamkar dan da suka haifa da cikin su.. kamar yadda Fahad ya fada 'the least he could do for them is yayi haquri ya cigaba da zama da ita' Toh amma ya zai yi da halin ta?? Da qyar Abba ya shawo kan Daddy ya janye batun sakin amma fa ran shi a bace. Shi ya kawo idea na lallai Maleeka has to be punished severely for what she did don haka ne ya ba MK shawarar ya dauki Ummi su bar qasar.. they should go away from everybody har zuwa lokacin da zaiyi clearing mind dinshi because he still believe cewar an shiga haqqin MK da aka hana shi sakin Maleeka dukda kuwa ba wai ya fito fili ya fadi musu cewar yana da niyyar sakinta din bane... Ya shaida ma MK cewar a matsayin shi na mahaifin Maleeka he is asking him to feel free akan duk wani hukuncin da zai yanke mata.. idan bazai iya zama da ita ba he should feel free to talk.. shi kam he will be more than glad to separate them. A wannan lokacin kuwa shi kan shi MK ya zama confused.. Shawarar Daddy ita ce mafita because dukda yayi making up mind dinshi zai rabu da Maleeka yakamata yayi la'akari da zumuncin da yake tsakanin families dinsu plus one thing is for sure, soyayyar Maleeka is stuck inside him.. bazai taba iya yakice soyayyar ta daga zuciyar shi ba no matter how hard he try.. Dukda Abba bai so degree na punishment din da sukayi niyyar yi ma Maleeka ba he is glad MK bai sake ta din ba... ya tabbatar lallai idan yayi clearing mind din shi zai haqura ya yafe mata.... ●●●● ♧♧♧♧♧♧♧♧ ♧♧♧♧♧♧♧ Haka kwanaki suka dinga tafiya yayinda Maleeka take cikin tsananin damuwa.. Kullum tana fama da ciwon kai da radadin zuciya. Ta kai ga har likita ya sanar da ita jinin ta yana hawa don haka ya bata shawarar ta rage damuwa gudun kar ciwon zuciya ya kama ta. Dukda Maleeka bata sanar da iyayenta abinda yake faruwa da ita ba they are aware of her condition (Dr. Davis ya fadi musu a matsayin shi na family doctor din su) but they still didn't say anything.. suna dai samun update report dinta daga wurin likita. Ana cikin wannan halin ne aka fara bikin Jameela.. Dukda halin da Maleeka take ciki haka nan ta zage ta taka rawar gani a bikin domin kuwa Jameela is not just a friend to her.. she is like a sister. Abin mamaki few days to bikin MK yayi ma Jameela transfer na kudi har 2million naira gudumuwar biki.. Sossai tayi mamaki da ta ga wannan alert din.. Ita bata ma san ya tuna da bikinta ba sai gashi ya aika mata kudade masu yawan gaske. Ko da ta gaya ma Maleeka tayi mata murna sossai.. Abu daya da yake birge ta da shi kenan, yana da hannun kyauta.. abun hannun shi bai taba rufe mishi ido ba.. Ta tuna tun bayan da ya auri Ummi da suka samu problem he never stopped sending her money as usual... infact har qara mata yake yi. A lokacin da tayi sanadiyyar zubewa cikin Ummi ne ya daina tura mata kudi.. that alone shows that lallai yayi fushi da ita. Abinda bata sani ba shine kudaden da Mummy take tura mata duk MK ne yake turowa a bata.. afterall she is still his wife and akwai haqqin ta a kan shi..1 Jameela dai a wurin Maleeka ta karbi lambar wayar shi ta kira shi. Abin mamaki kuma yayi answering suka sha hira sannan ta dinga yi mishi godiya na kudin da ya aika mata.. Yayi mata fatan alkhairi tare da bata haquri akan bazai samu damar halartar bikin nata ba. Maleeka wadda ta nace mata akan ta sa a speakerphone kuwa tana jin conversation din su daga farko har qarshe... Hankalinta yayi matuqar tashi jin har suka gama magana a waya he didn't ask of her.. Haka ta dinga rusa kuka da ta ji muryar shi.. she realised she missed him so much more after listening to his voice.. Jameela kuwa tayi regretting amince mata da tayi na sanya wayar a speakerphone.. aikuwa haka ta dinga aikin lallashi. ************* Jameela dai an kai ta gidan mijinta Engr. Umar Farouq Danbatta wanda yake nan a Maitama. Engr. Umar Farouq dai ya kasance yana da mata daya mai suna Dr. Bilkisu da yaran ta biyu Ahmad da Asma'u. Asali dai Engr ya qara aure ne a bisa amincewar matar shi domin kuwa ita din babbar likita ce a nan National hospital na Abuja.. a dalilin bata cika zama ba sannan bata ba mijin nata haqqin aure kamar yadda ya kamata shiyasa ta shawarce shi akan ya qara aure kar su cigaba da zama cikin qwarar juna musamman a bangaren shi. Tunda ya hadu da Jameela kuwa ta kwanta mishi a rai sossai.. haka a bangaren Jameela ma tuni ta aminta da shi.. Maleeka dai bata so qawarta ta fada ma mai mata ba domin kuwa a tunaninta kishiya ba abokiyar zama bace... Ni kuwa nace da ta ajiye baqin kishinta na banza a gefe ta rungumi nata kishiyar sun zauna lafiya da duk bata shiga halin da take ciki ba a yanzu... ah toh!! ********* After a while... Fatima matar Fahad ma tuni ta haihu.. ta samu 'yar ta mace wadda ta ci sunnan mahaifiyar Fahad wato Khadija amma ana kiran ta Mimi. STORY CONTINUES BELOW Lokacin da ta haihu kuwa murna a wurin Ummi da MK kamar su ne suka haihu.. Ummi har ce ma MK tayi su koma Nigeria amma ya lallashe ta akan tayi haquri lokacin dawowar su bai yi ba... Haka take yin Video call da Fatima ta zauna tayi ta kallon Babyn... Ummi dai tayi sa'a wannan karon bata samu matsala da cikin ta ba.. banda morning sickness da take having, cikin walwala take qarasa the rest of the day... Sossai MK yake kula da ita. Har Suite dinsu likita take zuwa tana duba ta.. it meant incurring extra cost amma it was no big deal for him... for Ummi, he can spend his entire savings. A bangaren karatun da yake koya mata kuwa sossai take dauka.... Ummi dai sossai ta iya turanci, rubutu ma babu laifi amma dai ta fi iya karatu akan rubutu. MK ya koya mata yadda ake operating laptop da tablet.. ya koya mata elementary stage na business and ahankali they were getting to the complicated aspect of it. Yayi mata bayanin what her charity foundation is all about da yadda zata tafiyar da shi.. Tuni dai anyi putting komai into place.. Foundation din ya fara aiki wanda itace take tsara duk wani abinda take so... Lado shine yake kula mata da harkokin foundation din kafin ta dawo. *********** Wasa-wasa dai MK da Ummi basu bar Greece ba sai da suka yi kusan wata biyar. Sossai suka ajiye beautiful memories na zaman su a qasar dukda they spent most of their time indoors... Santorini is no doubt a home because they lived a beautiful married life a wurin. Ko da suka bar Greece straight Switzerland suka wuce saboda Hafsah wadda ta nace musu akan su zo din... Hafsah dai last month sun je Nigeria sunyi sati biyu a dalilin hutu da mijin ta Sadiq ya samu.. A dalilin su MK basu nan ne ta dinga roqon su akan lallai kar su koma Nigeria basu je Switzerland sun duba qanwar su ba.. wannan ne ya sanya MK yayi arranging tafiyar su zuwa Switzerland din. Aikuwa they were very happy to see each other.. itama Hafsah tana dauke da cikinta wata biyu.. Haka ta dinga tsokanar Ummi tana kiran ta da Maman biyu. Shi kuwa MK ya dinga fadin Ameen... Cewa ma yayi idan har 'yan biyun Ummi ta haifa toh lallai zaiyi ma Hafsah kyauta ta musamman.. Aikuwa Hafsah ta dinga zabga musu addu'a akan Allah ya kawo 'yan biyun don ta san ba qaramar kyauta zai yi mata ba. Sati biyu suka yi a Switzerland sannan suka dawo gida Nigeria. they returned after 6 months!!1 ♧♧♧♧♧♧♧♧ ENGR. UMAR FAROUQ DANBATTA RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a falon Jameela suna shan fruit suna hira. Da ka kalli Maleeka a wannan lokacin kasan she is not okay.. ta rame ta zama so confused.. she even looked sick.1 A yau sati biyu kenan da su MK suka dawo amma Maleeka bata sa shi a ido ba. Cikin damuwa na ji tace "wallahi qawata tunda suka dawo ban gan shi ba.. I thought Asokoro zasu sauka but it's like ya dawo da ita nan Maitama.." Ta fashe da kuka tace "...na shiga uku Jay, ya zanyi? gashi fa su Daddy basu ce komai ba har yanzu.. Wallahi zuciyata zafi take yi, I cant take this anymore. The doctor keeps telling me in rage damuwa kar ciwon zuciya ya kama ni.. toh ta ya zan rage bayan mutum daya da nake so a duniyan nan baya sona kuma.." Jameela dai ta san qawarta tayi qoqari matuqa.. ta sani cewar a dalilin damuwar da take ciki ne jinin ta yake ta hawa wanda a yanzu haka tana daf da ciwon zuciya ya kamata.. surprisingly Mummy da Daddy sun sani kuma they did nothing about it!! STORY CONTINUES BELOW Cike da tausayawa Jameela ta janyo ta jikinta ta rungume ta tare da fadin "don Allah ki daina kuka Leek.. tunda dai sun dawo ina sa ran abubuwa zasu daidaita. Ni yanzu akwai shawarar da nake so in baki.. amma fa daurewa zakiyi because I think right now it's the only way out for you" Da sauri Maleeka tace "ina jin ki qawa ta.. no matter how difficult it will be for me as long as it will make Honey to forgive me wallahi zan yi" Gyara zama Jameela tayi tace "kin ga dai for like six months kenan kina roqon Ya MK ya yafe miki amma ya qi sauraron ki.. dukda dai a text messages ne. he doesnt even pick your call balle ya saurare ki.. again your parents are not helping matters shawarar da zan baki shine you should go through Ummi.."3 A firgice Maleeka tace "what???" Jameela ce ta dakatar da ita tace "Listen to me Leek.. you have to do it. Kar ki manta fa Ummi deserves an apology from you for what you did to her sannan a halin da ake ciki yanzu ita ce 'yar gaban goshi a wurin Ya MK.. na tabbatar duk abinda tace mishi yayi zai yi, A halin da ake ciki yanzu idan har kin shirya komawa tare da shi dole ne ki tausa zuciyarki ki rungume ta a matsayin kishiyarta ku zauna tare.." Ta riqo hannun Maleeka ta cigaba da fadin "...Leek please I beg you.. ki cire wannan zafin kishin naki daga cikin dictionary dinki ki je ki nemi sulhu da Ummi.. trust me things will get better afterwards.." Shiru Maleeka tayi yayinda tayi zurfi a tunani.. how will she do that??? Bata ankara ba ta ji muryar kishiyar Jameela wato Dr. Bilkisu wadda ta shigo tana fadin "Qanwata i am all set.. zan tafi asibiti ina da emergencies to attend to, babu mamaki ma a can zan kwana. please take care of our D sossai.." Jameela tana murmushi tace "insha Allah yayata.. Allah ya taimaka. Zan aiko driver ya kawo miki dinner.. me kike so?" Dr. Bilkisu tace "duk abinda kika dafa qanwa ta.. nagode sossai" Maleeka dai bin su tayi da idanuwa tana ta mamaki.. how is it possible?? Ba tun yau ba idan ta zo gidan takan ga yanayi na zaman lafiya a tsakanin su.. Can she ever live like this da Ummi a gidan MK?? Dr. Bilkisu wadda ta kula da Maleeka ce tace "au ashe Leek ce a gidan mu.. yi haquri hankali na yayi nisa ban gan ki ba.. ya gida??" Maleeka tace "Lafiya lau" Dr Bilkisu tace "Madallah.." ta kalli Jameela tace "qanwata kar a manta da maganin Ahmad" Jameela tace "insha Allah bazan manta ba.. you just take care of yourself" ta dan turo baki ta cigaba da fadin "...saura kuma anjima mu kira ki a waya ki qi picking" Dr. Bilkisu tana dariya tace "I promise zanyi picking idan I am free... yaran naki ne duk su cika mutum da surutu" Jameela tana dariya yayinda Dr. Bilkisu tace "toh ni dai na tafi..." tayi musu sallama ta wuce. Jameela tana kallon Maleeka wadda tayi zurfi a tunani tace "Leek kin ga haka nake so in ga kuna zama tare da Ummi... ina so ki mayar da Ummi tamkar qanwar ki.. ki cire kishi gaba daya daga ran ki.. Ki ja ta a jiki sossai. ina mai tabbatar miki zaki ji dadin zama da ita. I swear Ummi batada matsala.. wannan respect din da take baki a baya babu abinda zai hana ta baki shi a yanzu.. just give it a shot and I promise you baza kiyi regretting ba" ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA Kwance yake a kan cinyarta a babban falon qasa yayinda take yi mishi head massage. STORY CONTINUES BELOW MK dai rabon da kan shi yayi ciwo har ya manta domin kuwa ko alama Ummi bata barin shi yayi stressing kanshi.. Tunda suka dawo yayi resuming aiki ya zama very busy... Dukda Fahad ya jajirce sossai aikin ya tafi daidai akwai abubuwa dayawa da suka zama pending wanda shi din ne dai zaiyi attending to.. MK being the hardworking one kuwa duqufa yayi wurin aikin wanda within two weeks duk yayi clearing table dinshi... hakan ya sanya yayi carry over na stress da ciwon kai... Thank Goodness he has a wife wadda take da magic hands.. Da zarar Ummi ta fara yi mishi massage yake samu sauqi.. A yanzu ma tun qarfe goma sha daya ya dawo daga ofis din.. Idanuwan shi a rufe yayinda take ta yi mishi massage din tana ta masifa.. Ji nayi tace "dagaske sweetheart baka jin magana.. sai da nace maka kada kayi aiki dayawa amma ka qi ji. bazaka qara fita ba sai ka samu sauqi" Yana murmushi yace "yi haquri Baby na.. aikin ne yayi yawa, I needed to take care of everything before su qara taruwa" Kumatun shi ta ja sannan tace "ni dai na fadi maka.. you are not going anywhere until you get better"1 Har a wannan lokacin idanuwan shi a rufe yana murmushi yace "toh maman biyu" Dariya tayi tace "da kai da qanwarka kun nace mun da 'yan biyun nan... toh wai ta ya ma zan iya kula da yara har biyu a lokaci daya.." Kai tsaye yace "zan taya ki Baby.. I will always be there for you and the kids" Duqowa tayi da fuskarta saitin nashi tace "thanks for being so sweet.." Daga nan ta fara jefa mishi soft kisses irin wadanda yake so... Motsin da ta ji a falon ne ya sanya ta dagowa da sauri.. Gani nayi ta zaro idanuwa a dalilin ganinta da tayi a tsaye nesa kadan da su tana kallonsu... Maleeka!! Rabon su da ganin juna tun ranar da wannan al'amarin ya faru... Daga Ummi har Maleeka kallon juna suke yi na yadda suka canza... Ummi dai ta qara haske.. kalar fatarta ta canza tayi kyau sossai sai glowing take yi, ta dan yi 'yar qiba alamar ta samu hutu.. Maleeka on the other hand ta rame sossai infact she looked tired and stressed out.. kallo daya zaka yi mata ta baka tausayi domin kuwa ba sai an fada ba tana cikin tsananin damuwa ... Cike da mamaki Ummi tace "Adda???" MK ne ya bude idanuwan shi yayinda ya dan juya ya hango Maleeka a tsaye.. the first time he has seen her after that very day da yayi confronting dinta.. Gaban Maleeka ne yayi mugun faduwa a dalilin ganin MK da tayi.. Gaba daya ya canza mata, ya qara wani irin kyau.. da ganin shi ka san ya huta sannan he is very much happy in his life. Tashi yayi zaune ran shi a bace yace "what the hell are you doing here?" Zuciyarta ce ta buga.. Sossai ta rude a dalilin ganin yanayin shi- yanayin da ke masifar bata tsoro.. Tuni hawaye suka fara bin fuskarta yayinda bakinta yake rawa amma kuma ta kasa fadin komai.. Miqewa yayi tsaye yace "fita mun daga gida.." Ummi ce tayi saurin riqe hannun shi tace "Sweetheart please.." Juyowa yayi ya kalle ta yace "Baby just shut up... after what she did, me take so kuma? I..." STORY CONTINUES BELOW Maleeka ce ta katse shi muryar ta tana rawa tace "don Allah Honey kayi haquri.. ka bari in dan yi magana da Ummi, please I beg you" Cike da mamaki yace "what?? a tunanin ki zan barki da ita ki sake maimaita rashin hankalin da kika yi a baya??? Maleeka just leave before I kick you out myself.." Da sauri Ummi ta miqe tsaye wanda har sai da cikinta ya dan motsa yayinda ta dafe shi.. A wannan lokacin ne Maleeka ta kula da cikin da yake jikin ta.. she is pregnant again?? Gani nayi Ummi ta shiga gaban shi tare da riqe hannuwan shi biyu tace "don Allah sweetheart kayi haquri and let her talk to me.. I promise you our conversation won't even take long" MK dai ko kallon Ummi baya yi.. Fuskar shi sossai tayi displaying fushi da bacin rai.. Maleeka kuwa sossai tayi mamakin yadda ta ji turanci a bakin Ummi.. e shock her..🤣14 Gani tayi Ummi ta tallabo fuskar shi cikin shagwaba tace "Sweetheart please???" Lumshe idanuwa yayi ya bude sannan yace "I really cant say no to you, can I?" Girgiza mishi kai tayi alamar a'a tana murmushi. Yace "okay.. but I will be very close by..." Ya danna ma Maleeka harara yace "because I dont trust leaving you all alone with her.." Yayi mata kiss a kumatu sannan ya juya ya bar falon ba tare da yayi sparing Maleeka another glance ba.. Maleeka wadda take tsaye tana ta kuka ma kasa motsi tayi.. she doesn't even know idan har zuwan nata will be of any use, duk yadda take tunanin abun ashe ya wuce nan. Bata taba sanin MK yana da fushi ba sai wannan lokacin.. and Ummi?? yanzu har tana jin turanci kuma tana yi? kenan alot has changed and she is right where she has always been... that too as a loser?? Muryar Ummi ta ji tace "Adda bisimillah.. qaraso ciki" Da qyar ta daga qafafuwanta wadanda suka yi mugun sanyi ta qarasa gaban Ummi... Ko kafin Ummi ta zauna sai gani tayi Maleeka ta tafi qasa alamar zata durqusa don bata haquri... She is so desperate wurin neman yafiyar MK da Ummi.. Da sauri Ummi ta riqo ta yayinda take girgiza kai tace "kar ma ki fara Adda.." ta janyo ta suka zauna a kan kujera. Bayan sun zauna gani nayi Ummi ta sa hannu ta fara goge mata hawaye yayinda tace "don Allah ki daina kuka Adda..."1 Maleeka ce tace "dole inyi kuka Ummi.. na cuci rayuwata na cuci Honey sannan na cuce ki.. nayi muku laifi.. na wulaqanta ki, na zage ki sannan na yi sanadiyyar zubewa cikin ki duk saboda baqin kishinta na banza... Wallahi Ummi tunda abin nan ya faru nayi nadama, na gane kure na.. tsawon lokacin nan ina fama da radadin zuciya.. Honey baya sauraro na.. ya fita harka ta, da alama so yake ya rabu da ni.." Ta matse hannun Ummi a cikin nata yayinda sautin kukan ta ya qaru... da qyar ta bude bakin ta tace "wallahi idan ya rabu da ni mutuwa zanyi..." Da sauri Ummi ta toshe bakinta tace "kul Adda... kar ki sake fadin wannan, tabbas Sweetheart yayi fushi amma kuma bai daina sonki ba..." Cike da mamaki Maleeka ta kalli Ummi wadda tayi murmushi tace "yes Adda... your Honey never stopped loving you.. he is just angry ne so yanzu shawara na daya shine ki tashi mu je mu bashi haquri.." Ummi ta yunqura zata miqe ne Maleeka tayi saurin riqe ta tare da fadin "da ke yakamata in fara Ummi.. idan da hali don Allah ki yafe mun dukkanin abubuwan da nayi miki a baya.. nayi miki munanan abubuwa da dama, na wulaqanta ki babu iyaka amma wallahi nayi nadamar dukkanin abubuwan da nayi miki.. please ki yafe mun" STORY CONTINUES BELOW Murmushi Ummi tayi tace "Adda ai abinda ya faru a baya ya riga ya wuce kuma ni dama ban shigo rayuwarku don in tarwatsa tsakanin ki da Sweetheart ba.. ke ce dai baki fahimce ni ba kuma I dont even blame you for that saboda ko ni ce aka yi ma kishiya dole ne abin zai yi mun ciwo. Na yafe miki Adda... nima ki yafe mun abubuwan da nayi miki da kuma shigowa rayuwarku da nayi na..." Maleeka tayi saurin fadin "ki daina fadin haka Ummi.. shigowar ki rayuwar Honey alkhairi ne.. kin bashi abubuwa da dama wadanda na kasa bashi.. a ciki harda wannan" Ta shafa cikin Ummi sannan ta cigaba da fadin "...Ina fata Allah ya sauke ki lafiya.. I cant wait to finally see him happy for a dream come true"1 Murmushi Ummi tayi tace "Ameen Adda nagode.. yanzu dai ki zo mu je mu bashi haquri" Ko da suka tashi ji nayi Maleeka tace "Kin tabbata mu je?? wallahi tsoron shi nake ji Ummi.. gaba daya fa ya canza" Ummi tayi dariya tace "Haba dai Adda... babu wani canzawar da yayi, bai ma fa iya fushi ba.. bari ki gani muna zuwa wurin shi zai yi sanyi.." ******** Tsaye yake a falon shi riqe da wayar shi yana typing wani abinda ban samu damar gani ko meye ba.... Ummi ce ta shigo riqe da hannun Maleeka wadda qafafuwan ta sukayi mugun sanyi yayinda zuciyarta take ta bugawa.. Gani nayi ya dago kai ya kalle su.. At this particular point in time sossai suka birge shi a yadda ya gan su a tare.. he has always wished to see them like this- his two wives living peacefully together... 'I could only wish this right??' he thought!! Yayi nisa a kallon su ne da har suka qaraso kusa da shi bai sani ba... bai ankara ba ya ji Ummi ta qwace wayar da ke hannun shi sannan tace "Sweetheart gamu mun zo biko.." Daga mata hannu yayi yace "please Baby stop this drama..." Zaro idanuwa tayi tace "drama kuma?? hey.. maganar gaskiya Adda ta zo ta baka haquri kuma nace dole ka haqura idan ba haka ba..." Cike da mamaki yace "what? idan ba haka ba me??" Cikin shagwaba tace "zan yi fushi.." yayinda ta bata rai. Maleeka dai sai kallon ikon Allah take yi.. Ta kula kamar hankalin shi ya tashi jin Ummi tace zata yi fushi... tabbas Ummi tana affecting rayuwar MK fiye da tunanin dan Adam.. Ji tayi MK yace "Baby please dont make this any harder than it is for me right now.." Ummi ta turo baki tace "really?? toh listen to me carefully" Hannun Maleeka ta kamo sannan tace "Adda tayi nadamar abinda tayi mana... Har ga Allah na yafe mata and I expect you to do thesame, please Sweetheart.. Ka ga fa muna yi ma Allah laifi kuma mu roqe shi gafara ya yafe mana, who are we not to forgive eachother... please forgive her"+ Jikin MK ne ya fara yin sanyi a dalilin tight spot din da Ummi ta sa shi... shi fa dama bai taba daina son Maleeka ba.. infact son da yake yi mata bai taba raguwa a zuciyar shi ba.. Matsalar shi daya her attitude.. she has hurt him alot, so much that he just cant tolerate her anymore... Basu ankara ba suka ga Maleeka ta durqusa a kan gwiwarta yayinda hawaye ke bin fuskarta.. Hada hannuwan ta biyu tayi alamar roqo tana kallon shi yayinda muryarta take rawa tace "Please Honey.. forgive me..." Ko kafin ta qarasa magana ne na ga MK yayi saurin duqawa ya miqar da ita tsaye yace "hey.." Bata jira komai ba ta fada jikin shi tayi hugging dinshi very tight like her whole life depend on the particular hug yayinda ta fashe da kuka.. MK dai freezing yayi.. jikin shi yayi mugun sanyi, A yadda Maleeka ta rame ta lalace its obvious ta horu.. idan ma baiyi haquri ba ya zai yi da ita?? tunda dai har ya kasa rabuwa da ita ai dole ne ma ya haqura. Ummi kuwa ta cika da tausayin ta... Har ga Allah zata ji dadin wannan reconciliation din tsakanin MK da Maleeka saboda dai ko kadan bata so tayi sanadiyyar rabuwar su.. A tare ta gan su kuma ta sani cewar MK yana bala'in son Maleeka, Dukda abubuwan da suka faru a baya ta sani cewar idan har suka rabu dangin MK zasu dinga kallon ta a matsayin wadda ta raba kan su, ita kanta bazata zama comfortable ba da su.. and she wouldn't want that. Cikin kuka Maleeka tace "don Allah Honey kayi haquri ka yafe mun... wallahi I have changed, duk abinda kake so zanyi amma don Allah ka daina punishing dina haka nan.. I love you so much and I can't live without you.. wallahi mutuwa zanyi idan ka rabu da ni" MK wanda har yanzu bai motsa ba ne ya sa ma Ummi idanuwa kamar wanda yake neman shawarar ta akan what to do.. Ummi wadda itama take kallon shi ce tayi mishi sign alamar yayi wrapping hannuwan shi around Maleeka- meaning he should also give her a hug. Girgiza kai yayi yana murmushi yayi hugging Maleeka back yace "I forgive you Babe.. now please stop crying kin ji?"1 Wani irin sanyi zuciyar Maleeka tayi yayinda farin ciki ya mamaye ta fal.. the first time in months da ta ji wani yanayi mai dadi a zuciyarta. Cike da tsananin murna tace "nagode Honey.. thank you very much" Ummi wadda tayi murmushi ce ta daga mishi hannu alamar thumbs up ta kashe mishi ido daya yayinda tayi blowing mishi kisses ta juya zata fita.. Da sauri yace "...and where do you think you are going to?" Maleeka tayi breaking hug din tana kallon Ummi wadda ta juyo tana murmushi tace "giving you both a moment ofcourse.." Ita dai Maleeka sossai tayi mamakin yadda Ummi ta iya turanci haka.. Hararar ta yayi yace "what's celebrating the moment without the one who created it?? come on zo nan" Ummi ta qaraso wurin su ya janyo ta yayi hugging dinsu su biyu yace "I love you both.. please ku kasance a haka kamar 'yan uwan juna.. make me happy kun ji??"3 Maleeka ce tace "Insha Allah Honey.. I will make sure to maintain a happy family henceforth" Ummi tace "welcome back to the family Adda..." Tace "nagode Ummi... thank you for everything.. you wont believe me but you just saved my life" Ummi tayi murmushi tace "please stop it Adda.." MK yayi breaking hug din yana kallon fuskokin su yace "Allah yayi muku albarka.." Suka amsa da "ameen.." ♧♧♧♧♧♧ And yes.. Finally, MK ya yafe ma Maleeka all thanks to Ummi and partially Jay da ta bata shawarar ta zo din.. Ummi is so matured and sensible.. You would agree with me that she is a Living Legend right?7 Ina da tambaya: Shin dagaske Maleeka ta gyaru?? Dagaske ta rungumi Ummi a matsayin kishiya?? Shin da rabon mu ga zaman lafiya a gidan MK??6 Me zai biyo bayan wannan shiryawar ta MK da Maleeka???

Post a Comment for "UMMI CHAPTER 15"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...